Showing 1 words to 3000 words out of 31845 words
Chapter 1 - Masarautarmu Book 2 Hausa Book By Takori Kabara .pdf
MASARAUTAR MU!
2
Littafin
SUMAYYAH ABDULKADIR
SADAUKARWA
Ga Bilkisu Askira, (Billie Askira), Maiduguri, sabida gudummuwar ki yayin rubuta wannan
littafi.
JINJINA
Har kullum jinjinar taku ce dukkan members na TAKORI'S ONLINE FORUM whtspp, littafin
MASARAUTAR MU jinjina ne a gare ku, nagode da kauna da kwarin gwiwa, ni da ku hadin Allah
ne. Allah ya bar mana zumunci har gidan aljannah. You are my source of inspiration.
GARGADI
Ban yarda a karanta wannan littafi a kowacce kafa ta sadarwa ba batare da iznina ba, tun daga
radio, facebook, whtsp idan har ban yi izni ba, yin hakan karya doka ne kuma abin tuhuma ne
daga lawyer na Barrister Sadiq Rufa'i Wali.
MASARAUTAR MU 2
Ya kara tattaro dan sauran karfin gwiwar da ya rage masa, yace cikin kwantar da murya,
kodayake kodayaushe muryarsa a kwance take.
"Baturiyar Asia ce, Jew (bayahudiya), ta yarda zata karbi addinin muslunci in dai zan aure ta".
Daga sarki har Ya Gumsu a razane suka dube shi. Mai martaba ya kasa cewa komai kamar
an dinke masa baki. Ya mutu a zaune cikin kujerar sa. Ya Gumsu ta mike tsaye tana nuna shi
da dan yatsa "....ka yi kadan Yarima, karya kake ka tozarta ni a idon duniya da idon kishiyoyi na
masu son ganin faduwa ta!. Ko mata sun kare ban yarje maka auren nan ba, da yawun baki na
bazan taba saka albarka ta ba!!!".
Sarki Yusufu ya ce "kana iya tafiya Yareema zamu yi shawara, duk abinda muka yanke
Waziri zai kira ka". Ya Gumsu ta zaro ido tana kallon Mai Askira tamkar idanun ta zasu fado.
Tunda har ya amince zai tattauna zancen nan da Waziri ta san karshen alewa kasa.....ba ya kai
zance ga Waziri sai ya fara yin na'am da shi a karan - kansa. Ta fashe da kuka ta tashi ta bar
falon. Yarima ya mike zai bi bayan ta. Sarki ya ce ya kyaleta sai ta huce yanzu bazata taba
sauraron sa ba.
Ya koma ya zauna jikin sa a sanyaye, da wannan damar Sarki Yusufu yayi amfani ya dinga
tambayarsa abubuwa akan Rose din, da yadda suka hadu, shi kuma ya gaya masa duk abinda
ya kamata ya sani banda wanda bai kamata ba. Ya kare zancen sa da cewa yana mata
kwadayin musulunci ta hannun sa don jihadi, sabida kyawawan halayen ta, sannan ita din ma
tana sha'awar addinin muslunci a karan - kanta. Ta zabi ta bar kowa nata in dai za'a bar shi ya
aure ta.
Alanguburo ya fahimce shi sabida saukin kansa, a lokaci guda yana kokawar ture nasa
BURIN akan Yarima Sageer can gefe daga zuciyar sa, yana fadawa zuciyar sa ya bar shi yayi
jihadin; wani ya shiryu ta hannun ka yafi a baka jajayen Rakuma tunda Allah bai haramta ba. Ba
duk abinda muka yi burin tabbatuwar sa ne yake tabbata ba. Wasu mafarkan a mafarkai kawai
suke tsayawa, ba sa zama REALITY yadda muke burin su. Wasu kuma Allah kan jinkirtawa
bawa zuwa lokaci mafi dacewa. Ya sallame shi da cewa ya saurari kiran Waziri idan sun
tattauna gobe.
****
Sarki Yusufu da Wazirin sa Ibrahim suna tattaunawa akan al'amarin Yarima bayan sun
kadaice a falon ganawar sirrin su, Waziri yace su bar Yarima yayi auren su samu ladan
muslunci, amma bisa sharuddan cewa zata biyo shi gida su zauna tare dasu cikin MASARAUTA
a matsayin sa na Yarima mai jiran gado. Dole ya dawo gida gabadaya ya zauna cikin ahalin sa. Lokacin da Waziri ya kira Yarima ya gaya masa hukuncin da suka yanke, Yarima Sageer yayi
dan jim! Domin nan kusa bai shirya dawowa gida ba, ba zai iya rayuwar karamin gari kamar
Askira ba, zai takura, ba zai shana yadda ya saba ba, sannan Rose ma zata takura, ga zafin
Maiduguri, bata taba zuwa Africa ba haifaffiyar South - Korea ce. Aiki ya kai iyayenta
Amsterdam. Ba abinda ya tsana irin ace shine 'mai jiran gado', bayan ba shikadai ne namiji ba,
shi sarauta sam bata cikin tsarin sa, Yarima Sageer bakin bature ne kawai wanda ya rungumi
affluent western lifestyle ya manta da asalin sa tsayin shekaru masu yawa, wannan kuma ya
faru ne da laifin su iyayen sa da suke ganin yin nisa da gida fintinkau shine abinda zai nutsar
musu da shi; don nutsuwa ya nutsu irin wanda tarin shekaru ke haifarwa da namiji, amma ba
nutsuwa irin wadda su suke zato ba.
Karewa ma, ya goge ne yayi mastering akan harkar neman mata, har wadanda ba addinin su
daya ba. Amma in ka gan shi a fuska tsammani zakayi wani saint ne shi din (waliyyi) sabida
tsabar iya badda-kama a gaban iyaye. Abu daya Allah ya tserar da Yarima akan sa shine shan
giya, ko sha'awar ta bai taba yi ba. Yana matukar kyamar ta. A cewar sa ai sai da hankali ake
sallah dai-dai, kuma a yi ta akan lokaci. Hatta sigari tun lokacin tashen samartakar sa ya bar ta.
Amma da ya duba wannan alfarma da iyayen sa suka yi masa wadda bai taba zaton zata zo
masa da sauki haka ba, sun bar shi ya auri zabin sa dai-dai da ra'ayin sa, sannan sun toshe
kunnuwan su daga duk abinda zasu ji akan auren nasa, auren da a tarihin masarautar su ba'a
taba yin irin sa ba, sai ya ga cewa ya zama dole shima ya amince da tasu bukatar na dawowa
Askira tare da matar sa. Kafin nan zai roke su su bashi lokaci, ya kammala phd din sa, ya
tattaro kasuwancin sa zuwa Nigeria ya kuma nemi aikin da zai rike shi in ya dawo, ba zai zo ya
dogara da mahaifin sa ba kamar yadda akasarin 'ya'yan sarauta ke yi.
Koda ya yiwa Waziri wannan bayanin take ya amince, ya kuma ce sun bashi shekaru biyu ya
kammala komai, ya dawo tare da matar a musuluntar da ita a daura auren su. Awaisu was
shocked lokacin da yaji labarin nan domin bai taba zaton iyayen su zasu amince da zancen
Rose ba, haka bai taba zaton Yarima is serious akan maganar Rose ba, ya dauka yana fada ne
kawai for fun irin nasa. Shikam tuni Ba'ana ta zaba masa mata 'yar kanwar ta mai suna Asiya
suna dawowa za'a hada auren nasu lokaci guda shi da Yarima, don yarinyar bata kare
sakandire ba ma.
Kwanan su bakwai suka koma Amsterdam with nostalgia (cike da begen gida) a yadda suka
tsammaci masarautar ta su sai suka tarar akwai cigaba na zamani sosai fiye da yadda suka tafi
suka bar ta. Suka kuma fara tunanin hanyoyin da zasu kara kawo mata daukaka da cigaba na
zamani ta kara zama zakaran gwajin dafi a masarautun jihar Borno tsararrakin ta. Tuni Yarima
ya tsara sababbin gine-gine da za'a kara cikin masarautar, da yadda za'ayi renovating din ta
daga kamfanin gine-gine da tsare-tsaren gidaje na COSIMCO na kasar Amsterdam
(Neitherlands).
Yana komawa abinda ya maida hankali akai kenan, wato project da cosimco akan
masarautar su. Daga can suka taho suka fara ayyukan su a masarautar Askira. Gininnika na
zamani masu tsayi da nagarta suka kara fiddo da martabar masarautar Askira. "Lallai dan zaki
an girma" Sarki ya fadawa Waziri cikin murmushi a lokacin da suke zagaye cikin masarautar da
wajen ta, suna kallon renovation din da Yarima ya tsara da kansa ya kuma turo COSIMCO
construction company suka yi. Waziri da sauran 'king-makers' sai albarka suke sanyawa
Yarima, fatan su bada jimawa ba ya dawo ya karbi sarautar mahaifin sa tun yana raye. Wanda
basu sani ba wannan baya cikin tsarin Yarima Sageer ko kadan. Bar shi dai a gogaggen dan
bokon sa. Awaisu ne kawai ya san hakan.
****
Hutun su Sa'ade na karewa suka koma makaranta, ashe wani abin alhini ke can yana jiran ta,
shiru-shiru tana zuba idon ganin dawowar Raheema amma har ta share sati biyu da komawa
Raheema bata dawo ba.
Sa'ade ta kasa sukuni, ta kasa walwala ta kuma kasa cigaba da harkokin karatun ta yadda ta
saba a dalilin babu Rahima, ta kuma rasa wanda zata tambaya ko ya san abinda ya hana
Rahima dowowa don kowa ita yake tambaya. Ga wani kuskure data yi bata taba karbar
adireshin Raheema ba, sabida tana ganin ko ta karba babu wanda zai kaita, Fulani bazata taba
barin ta ta je ba.
Da abin ya isheta sai ta tafi ofishin principal, tayi gaisuwa ga principal sannan ta soma share
hawaye. Principal tace "what's wrong Sa'adatu Hashim?" Sa'ade ta idasa fashewa da kuka a
gabanta sannan ta gaya mata yau sati uku kenan Raheema Kyari bata dawo ba.
Principal tasa aka yi bincike akan rashin dawowar Raheema, nan malamin dake kula da
dawowar dalibai ya sanar da ita sakon da mahaifin Raheema ya aiko na cewa sun bar kasar
Najeriya. Wanda ke nufin Raheema ta bar makarantar gabadaya.
Damuwar Sa'ade sai ta nunku akan ta da, me ya sa Raheema za ta bar kasar ba tare da ta yi
mata sallama ba? Laifin me ta yi mata? Amincin dake tsakanin su ya fi gaban haka. Bata san ta
yi mugun shaquwa da Raheema ba sai yau data wayi gari babu ita cikin kwalejin El-Kanemi.
Rayuwar Sa'ade gabadaya sai ta sauya a makaranta ta zama ba umh ba umh-umh. Haka ta
dukufa yi wa Raheema addu'a ba dare ba rana kan Allah yasa tana lafiya, tana kuma rokon
Allah ya sake hada su cikin gaggawa.
Sannan a fannin karatu ta kara dagewa, don yanzun shi kadai ne abinda ke debe mata kewa.
Tana yawan tunanin Zarah da Fulani, amma kullum tana sawa a ranta Fulani bata son ta don
haka is a waste of time yawan tunanin ta data ke yi, har addu'a take yi a kowacce sallahr
farillarta Allah ya rage mata son da ta ke yi wa mahaifiyar ta Fulani Bilkisu! ****
BAYAN SHEKARA BIYU!
Abubuwa da yawa sun faru cikin shekaru biyun nan, wadanda yawanci rigingimu ne na kishi a
cikin gida tsakanin Ya Gumsu da Fulani Bilkisu. Sun ki zama lafiya da juna, amma kashi 80% na
rigingimun in ka bincika zaka tarar laifin Ya Gumsu ne, tana kishi da Fulani Bilkisu ba dan kadan
ba, a bisa abubuwa da dama; muhimmi shine son da Askirama ke mata wanda ya zarce na
kowacce cikin matan auren sa, kuma ba ya iya boyewa. Yayin da ita Ya Gumsu a wurin ta ita ta
cancanci wannan fifitawar a matsayin ta na uwar Yarima kuma uwar manyan 'ya'yan sa.
A haka dai ake rayuwar, da dadi ba dadi a gidan sarkin Askira, kamar kowanne gidan
sarauta, duk wani babban gida ko ba na sarauta ba ya gaji haka, girma na kara kama kowaccen
su, kamar kuma suna girma ana kara rura wutar kishi a tsakanin su.
A yau Litinin, gidan sarautar Askira an tashi da hidimar shirin tarbar Yarima Sageer wanda zai
sauka a yammacin yau tareda matar da zai aura, 'Rose Hathaway'. Labari ya gama baza cikin
gida na inda Yarima ya nemo aure. Surutu ba irin wanda ba'ayi a sassan kowacce daga cikin
matan gidan in ka dauke unguwar Fulani Bilkisu, ita kadaice ta goyawa Yarima baya akan auren
da yake so kuma bata yi Allah wadai da zabin nasa ba, ko dama kusan koyaushe ra'ayinta na
zuwa daidai dana maimartaba ne.
Yamma lis Yarima Sageer da dan uwansa Awaisu da Rose wadda ta sha doguwar riga har
kasa da mayafinta kamar balarabiya suka iso masarautar Askira karkashin rakiyar dogarawan
fada masu yawa, wadanda suka dauko su daga filin jirgi daga Maiduguri a mota civilian ta
Askira Emirate.
A wannan lokacin Sa'ade na makaranta tana zana jarrabawar shiga aji biyar SS 2. Ya Gumsu
ta yi tsalle ta dire tace ba dai baturiyar Yarima a sassanta ba, babu ita babu wannan auren koda
za'a sa mata wuka a makoshi. Don haka Mai Askira ya ce a kaita unguwar Fulani Bilkisu ta
zauna karkashin kulawar ta. Dakin Sa'ade ta sa Fanna ta gyarawa matar Yareema, duk abinda zata bukata Fulani ta
tanadar mata, to saidai hira ta gagara tsakanin su don Fulani bata iya turanci ba, saidai ta yi
magana da Yarima a waya shikuma ya kira Fulani ya gaya mata abinda ta ce. Kwanan su biyu
da dawowa aka musuluntar da Rose a masauratar Askira aka daura auren ta da Yarima Sagir,
babu wata gayya ta kunya da sarki yayi iya jama'ar gari ne kawai da king-makers suka shaida
auren Yarima Sagir, bai gayyato 'yan uwan sa sarakuna ba, shi kansa bai san meyasa a can
kasan ran sa baya farin ciki ko kadan da auren ba, duk da cewa bisa amincewar sa da yardar
sa ne. Ya dauka Rose zata zo tare da wani nata, sai ya ganta zikau daga ita sai jakar kayan ta...
sai ya soma tambayar kansa ranar da 'ya'yan Yarima suka tambayi dangin mahaifiyar su me zai
ce musu???
Ko dai uwar Yareema, Ya Gumsu, ta fi shi gaskiya ne???
****
Babu wani shagalin biki kamar ba auren Yarima guda ba, haka aka dauki amaryar aka kaita
gidan da Maimartaba ya ginawa Yarima wanda ke gefen masarauta. Gida ne tankarere ginin
sarauta kuma ginin zamani, wanda ya lashe miliyoyin kudi har ya zarta ginin masarauta tsari
sabida an yi amfani da hikimar kamfanin cosimco. In ka ji ana aljannar duniya to gidan Yareema
Sageer ne. Auren Awaisu sai bayan shekara biyu don matar da aka bashi bata gama
makarantar sakandire ba.
Rayuwar Yareema da amaryar sa Rose wadda ta karbi suna (Aisha - Sultana), sun dora ta ne
daga inda suka tsaya a Amsterdam, wato rayuwar nasara zallah, don su kan manta cikin
masarautar Askira su ke, Yareema na matukar son Sultana yayin da ita kuma ta karbi muslunci
ne don son data ke wa Yareema ba don tana ra'ayi ba, don ya ce mata shine kadai hanyar da
iyayen sa zasu yarje mishi auren ta.
Don haka kusan zamu iya cewa addinin ta karbe shi ne kawai a baka, amma daga sanda
suka bar cikin gida zuwa nasu gidan ta jinginar da sallahr data fara a sassan Fulani Bilkisu, ta
gayawa Yareema ita bazata iya kullum ba, akwai wahala sai ta saba tukunna, yayin da Yareema
ya nuna ba zai lamunci hakan ba sai take yi a gaban sa, in baya nan kuwa a hadu a gaba. Sati hudu ana barzar amarci, an cika musu gida da bayi da hadimai, Sultana sai a lokacin
take lakantar ko wanene Yareema Sageer Yusuf Askira? Ashe a baya bata san komai a kan shi
ba? Banda kasancewar shi abokin shashancin ta, ta fahimci a yanzun tana sahun gaba na mata
masu sa'a a rayuwa, domin Sageer daya ne cikin dubu, wanda irin sa ta fannin nunawa matan
su soyayya tsiraru ne a