Showing 3001 words to 5666 words out of 5666 words

Chapter 2 - KARNI UKU littafin Yaki Complete By Mansur Usman Sufi .pdf

mai suna sheik Habib al-attad.

Kansancewarshi malamin addinin Islama ɗaya tara ilimi wannan yasa ya samu shiga a
wajen sarki Anwar har ya zama na hannun damar shi bisa wannanne ya sanya sheik Habib yayi
amfani da wannan dama wajen jefa sabbin gurɓatattun aƙidoji domin kawo rabuwar kan
Musulmi, saboda dukkan wata fatawa ta addini shine ke amsawa.
Kafin shuɗewar waɗansu shekaru yanayin al'umma ya canza al'adun su da kyawawan halaye
na musulmci sun fara rabuwa dasu

Bisa wannan dalili ne yasanya matsaloli ke bazuwa a cikin al'ummar musulmi da aka kasa
shawo kansu.

Wannan shi ne taƙaitaccen bayani game da sarki Anwar da rayuwar al'ummarshi a shekarun
da suka gabata.


****

Lokacin da Hakimi urwat da samarin uku suka yi turus! Bisa jin wannan motsi da suka yi na
takun sawaye a gidan sirrinsu.

Tsaye suka yi arba dashi fuskarshi rufe da rawani idanuwanshi kaɗai ake gani, matashi ne da
shekarunshi bazasu haura ashirin da uku ba,sanye cikin sulken yaƙi.

"Assalamu alaikum".

Saurayin ya faɗi a taƙaice.

" Wa'alaika-Salam warahamatullah".

Urwat ya amsa da yawun sauran matasan dake tare dashi.

Matashin ya ɗora hannunshi akanshi ya cire rawaninhi fuskarshi ta bayyana a fili ƙarara,
koda Urwat da samarin uku sukayi ido biyu dashi sai suka sakar mashi murmushi mai taushi.

Matashin ya risina ya kwashi gaisuwa gareshi sannan ya buɗi baki cikin ladabi yace"ya
shugabana mun sace dukkan fataken da ka buƙata da suka tafi izuwa birnin infaƙul-Maisur
domin yin kasuwanci, sai dai anyi rashin Sa'a a cikin waɗanda mukayi garkuwa dasu har da
yarima Affan ɗa mai martaba sarki.
Ya ƙare batun nashi cikin alamun damuwa.

Urwat ya bushe da dariyar mugunta gami da cewa ni a wajena hakan

Babban nasara ce a garemu, domin kuwa dukkaninku kun shaida cewa babu wani mai ƙoƙarin
kawowa aiyukanmu tazgaro a wannan birni tamkar yarima Affan, kun ga yanzu komai namu zai
cimma nasara,

Wani abin farin ciki ma baku sani ba shine a gobe ne da safe za'a yanke hukuncin kisa ga
manyan 'yan leƙen wannan birni a fada bisa laifin shirka wato (tsafi).

Sannan halin yanzu dukkan matasan da muka ɗauka aiki sun shirya fara aiyukan su na
zartar da kisa ga dukkan wanda bai yi biyayya ga tabbatar da aƙidarmu ta mujahidul' Haƙ ba.

Koda yazo dai-dai nan azancenshi sai samarin huɗu suka bushe da dariyar mugunta har da
kyakyatawa.

Sannan daga bisani matashi ɗaya daga cikin samarin ya buɗe wannan buhu sai ga waɗansu
miyagun makamai da kwalaben barasa haɗe da nau'ikan kayan maye.

Koda ganin hakan sai urwat ya cika da farin ciki, sannan ya dora dacewa ku tabbatar da an
bawa dukkanin matasan mu waɗansu kayan maye da makaman a daren yau kafin wayewar
gari.

Yana gama faɗin hakan sai ya miƙa tsaye kawai sai ya shafi wani guru a damtsenshi
yakaranto waɗansu dalasiman tsafi ɓace ɓat tamkar bai taɓa wanzuwa ba.

Wannan shi ne abin da yafaru Hikimi urwat.

Bayan ya ɓace cikin alƙalumman sihiri a lokacin da Sarki shaibat da tawagarshi zasu tafi
masallaci domin sauke farali.



Madinatul-barnawiy

Kashe gari tunda duku-dukun safiya fadar birnin madinatul-barnawiy ta cika ta batse da
jama'a

Kowa yayi jigum ana jiran fitowar sarki da muƙarrabanshi،Tsawon daƙiƙa talatin ana cikin
wannan hali, Sai daga bisani aka hango martaba da tawagarshi sun shigo fadar ta hanyar yin
sallama.

Jama'a suka miƙe tsaye domin girmama agaresu, sai da sarki da tawagar shi suka zauna bisa
wajen wajen zamansu, kuma jama'a sun kammala kwasar gaisuwa ga sarki, fadar tayi tsit
tamkar mutuwa ta gifta.

Sarki ya miƙe tsaye yayi gyaran murya sannan ya ɗora dacewa "Da farko ina yiwa dukkan
mahalarta wannan fada rawa mai albarka Barka da zuwa, Bayan haka a yau ne dukkan
jama'ata ke zuba idanu domin suga yadda za'a zartar da hukuncin kisa ga manyan'yan leƙen
asirinmu, kamar yadda labarin ya wakana.
Sai a wannan karon ba haka al'amarin yake ba, domin kuwa abinda zan sanar daku zai yi
matukar girgiza ku, yaku jama'ata kuyi sani cewa a daren jiya ne wani muhimmin sirri da na
daɗe ina ɓoye muku zai bayyana a gareku.

Fiye da shekaru uku ina tare da Amintattun 'yan leƙen asiri a dukkan wani rukuni na al'ummar
wannan ƙasa tawa, tun daga gidan sarauta, Unguwanni da kasuwa da ma manyan ƙasashen
maƙiyan Addinin musulunci, kuma a kowa ce rana dukkan aiyukan da na sanya su ya kammala,
ta wannan hanya ne a samu nasarar tarwatsa dukkanin shirin maƙiya.
Hanya ta biyu dana kawar da hakan shine gabatar da addu'o'i dare da rana tare da
keɓaɓɓun mutane, domin kuwa babu wani abu da yafi ƙarfin addu'a, Ubangiji na iya canza
dukkan abinda ake ganin ya gagara ta kowace fuska, amma sinadarin wannan canjin shi ne bin
dokokin ubangiji (SWT).
Sannan wani muhimmin abu da mutane basu sani ba shine a kowa ne dare bana iya rintsawa
da idanu na har sai na shiga cikin gari cikin ɓadda-kama ina mai sanya idanu akan aiyukan da
na sanya shuwagabanni akansu, kamar yadda na saba wannan al'ada ne ajiya ina yin rangadi a
cikin gari na shiga wata unguwa da ake ɗaukar matasanmu mayaƙan Mujahidul-Haƙ, Sai da
nayi shiga da siffa irin ta Mujahidul-Haƙ sannan na samu shiga gidan sirrin inda ananne na
ganewa idanuna Gaskiyar rahoton da ake bani akan Yan tawayen ƙasarmu.

A bisa wannan dalilai na yasanya Ni da kaina na ɗebi dakaru na shiga har cikin Daji na ceto
rayuwar Ɗana yarima Affan tare da sauran jama'ar da akayi garkuwa da su, A cikin wannan daji
ne muka samu nasara gano wani Ɗakin sirri da dukkan maƙiyanmu wato sarakunan
kafirai,bokaye haɗe da Musulmi maciya amana ke haɗuwa suna ƙulla makirci da sharri, mun

sha gwagwarmaya dasu ta hanyar fafata arbu tsakaninmu bisa taimakon Ubangiji muka samu
sanar hallaka su baki ɗaya.

Anan ma mun samu waɗansu bayanai muhimmai wacce da ita ne mu kayi amfani wajen kame
dukkan maci amanar mu a cikin dare kafin wayewar gari.

Koda yazo nan a jawabinshi sai yayi shiru Kuma idanuwanshi suka ciko da kwalla.

Al'amarin da ya jefa ruɗani a cikin zukatan al'umma kenan suka ƙara tattare hankulansu akan
mai martaɓa.

Sarki ya ci gaba da cewa "Sanin kanku ne cewa fiye da shekaru uku wannan ƙasa tamu na
cikin halin matsalolin tsaro da taɓarɓarewar matasan mu, daga lokacin da abubuwan suka fara
gudana ina saka idanu tare da tattara hujjoji domin tabbatar da zargin da nake yi domin ya
zamo gaskiya ba son zuciyata ba.
Sai gashi abinda nake zargin ya tabbata gaskiya, Daga cikin jerin mutanen dake hannu
wajen jefa kasar mu cikin tarin matsaloli sun haɗar da Sheikh Ɗayyib babban malamin dake
amsa fatawa a wannan ƙasa tamu da sauran biranen musulmi, sai Waziri Utbah,Hakimi urwat,
uwar gidana gimbiya Huwailah,sarkin dogarai, sarkin fada,tare da sauran jama'a da yawa
waɗanda zaku cika da matuƙar mamaki a yayin da kuka yi arba dasu a lokacin da za'a gurfanar
dasu.

Sheikh Ɗayyib an kama shi da laifin yin fatawa waɗanda suka saɓa da magabatanmu wanda
ta wannan hanya ne yayi amfani wajen zartar da hukuncin kisa ga dukkan Musulmin da ya saɓa
da aƙidarsu ta Mujahidul-Haƙ tare da dukkan wanda zai tsananta bincike akan abubuwan da
suke gudanarwa.
Kusan dukkan Musibun dake wanzuwa a wannan lokaci an samu ne ta hanyar Littattafan
addini daya wallafa kuma ya sanya su a cikin addini domin su kawo rabuwar kawunan musulmi,
sanin kanku ne cewa Babu wani hukunci da yazo a cikin alƙur'ani da sunnah da ya tabbatar da
cewa koda musulmi yayi kalmar shahada a hallakashi idan ya saɓa wa wata fahimta ta wata
jama'a a addini, Domin ubangiji shine masanin abinda ke wakana a zukatan bayi kuma shine ke
yi musu hukunci.

Bayan wannan ma fatawoyinshi sun yi tasiri akan matasan mu wajen samun damar saɓa wa
Ubangiji ta hanyar fakewa da rashin aikin yi har su karbi aƙidar Mujahidul-Haƙ, dake Kaɗaita
musu aljanna da kyakkywan ƙarshe,

Waziri kuwa an same shi da laifin taimakawa waɗanda ke Safar mutane daga wannan birni
namu ayi Garkuwa dasu domin a ƙarɓi dukiya mai tarin yawa da za'a bawa matasan
Mujahidul-Haƙ.

Sannan kuka kuma ya taimaka sosai wajen kawar da ainihin Littattafan magabatanmu da ke
da tsaftacciyar aƙida ta addinin Islama.

Sarkin dogarai kuwa ya cutar da al'ummarshi ta hanyar ƙarbar cin hanci ga dukkan wani
bafatake daya shigo wannan ƙasa tamu, ta hanyar ƙarɓar cin hancin ne masu safarar mutane
da shigo da miyagun makamai, da kayan maye suka samu dama akan mu, da kyale dukkan
wani nau'in kaya da suka shafi wani attajiri ko Basarake, batare da an binciki mene ne ake
ɗauke dashi ba.

Hakimi urwat da uwar gida kuwa sun ci amanar Allah da Annabin sa ta hanyar tallata saɓon
Allah da yaɗashi cikin al'ummar mu da sauran laifuka,

Lokacin da kuyanga ihsan ajiya tazo fada domin ta sanar dani irin nau'in sabon Allah da ake
gudanar a gidan sarauta shine urwat ya kurumtar da ita ta daina magana domin kada ta bada
hujja, sai gashi ta samu lafiya kuma ta tabbatar mini da hakan tare da waɗansu hujjojin daga
wasunta.
Daɗin daɗawa kuma

Dukkanin dai laifukan suna da yawa bazai yiwu mu bayyana su hakanan ba, domin annabin
rahama ya hore mu da ɓoye laifukan yan uwanmu musulmi, domin kuwa da yawan laifukan
dake yaɗuwa a wannan zamani na mu Suna da alaƙa da yaɗa alfashar da wasu ke yaɗawa da
'yan uwansu ke aikatawa
Bayan wannan kuma ina so jama'a su lura cewa bawai don kana cikin wata jama'ar ba ne
Abin da zai sa kaga cewa kai babu hannunka a cikin wannan Musibun dake damun duniyar
Musulunci ba, kowanne mu ana akaran kanshi yasan nau'in laifin da yake yiwa Allah to shi ma
na iya janyo dukkan wata musiba kamar yadda dai muka sani cewa saɓon Allah SWT shine ke
kawo gushewar dukkan ni'ima.

Kuma ku lura cewa tabbas Matsalolinmu mu musulmi daga kaɗan suka fara har suka haifar
da manya, saboda haka kada ku taɓa raina kuskure komai ƙanƙantarshi.

Yayin da bayi suka aikata zunubi sai Allah ya saukar musu da Musibun da zasu kankare
wannan zunubinnasu domin su haɗu da Allah (SWT) lafiya.

Da wannan dama nake roƙon dukkan jama'ata daga Nan fada kafin su koma gida su yiwa
Allah alkawarin zasu daina duk laifukan da suke yi wanda tsakanin su da Allah ne kawai, tabbas
ina da tabbacin Ubangiji zai dube mu ya kawo mana gyara a cikin wannan Rayuwa tamu, kuma
mu riƙa kallon dukkan Musulmi a matsayin ɗan uwanmu kuma abu ɗaya ne ya haɗamu ita ce
kalmar shahada,

Ko da kaga ɗan uwanka yana aiwatar da wani abu da ya saɓa da fahimtar ka to kayi mashi
kyakkywan zato, domin baka san a ina ya samo hujjar yin hakan ba, saɓanin fahimta ba sabon
abu ne a cikin addini ba

Kada mu zama masu bincike abinda ke zukatan al'umma,domin Allah shine kaɗai yasan
abinda ke zuciyar bayinshi, kuma shi ne zai yi hukunci a gobe ƙiyama.

Kuma dukkan abinda musulmi zai yi bazai taɓa kafurtaba face ya yarda da abin azuciyarshi,
don haka ne idan mutum ya yi abin da ya saɓa da fahimtar mafi yawan al'umma ake neman shi
da ya tabbatar da Mene ne hujjarshi na aiwatar da hakan.

Kada muyi watsi da abin da magabatan mu suka rayu akai, kuskuren da sukayi mu nema su
gafara wajen Allah.

Sannan dukkan abinda kowannen ku zai aiwatar yaji tsoron Allah a ciki.

Tsira da aminci Allah su tabbata ga Annabin rahama Annabi Muhammad Sallallahu alaihi
Wasallama da jama'ar gidanshi.

Lokacin da sarki Shaibat yazo Nan a jawabinshi sai fadar jama'a suka ruɗe da kabbara masu
salati nayi, kuma kowa na ƙara jinjina wa sarki, bisa jawabinshi, suna masu cewa munyi yarda
mun amince zamu gyara halayenmu da tsakaninmu da ubangiji,

a dai-dai lokacin ne aka shigo da waɗanda ake tuhuma da cin amanar addini.

Nan fa jama'a suka cika da matukar mamaki a cikin waɗanda basu yi zato da hannunsu a
cikin al'amarin ba.

Suka shiga yi musu Allah wadai har sai da sarki ya tsawatar sannan komai ya samu dai-dai
ta.

Duk wanda ya kalli fuskokin su waziri a wannan lokaci zai ga alamun nadama da da nasani,
Da yawan su Har zubar da hawayen baƙin ciki da takaici su ke yi, wasu daga cikinsu ma har
faɗuwa ƙasa suke yi suna cewa "Haƙiƙa mun tuba munyi nadamar abin da mu ka aikata muna
neman afuwa.


Sarki ya ɗora da jawabin shi da cewa yanzu dukkan su za'a tafi dasu izuwa kurkuku,
waɗanda a cikinsu suka cancanta a yanke musu hukuncin kisa zamu zartar waɗanda kuma
waɗanda za'a bukaci tuban su, da waɗanda za'ayi bulala duk zamu zartar a sirran ce, nasan
yanzu da kanku kun ganewa idanuwanku waɗanda suka nuna Nadamarsu dama waɗanda basu
da alamun hakan, dukkaninsu zamu yi musu adalci

Da wannan nake yiwa jama'a fatan alkairi kuma na sallami kowa daga fada.

Koda gama faɗin hakan sai sarki ya juya ya shige izuwa gidan sarauta dogarai na biye dashi
a baya.

Nan take aka tusa ƙeyar maci amanar addini aka nufi hanyar kurkuku, fuskokinsu cike da
ƙunci da da na sani, ƙarƙashin jagorancin yarima Affan.

Bayan mako ashirin da biyar lamura sun fara dai-dai ta acikin ƙasar madinatul-barnawiy,
jama'a na ta ƙoƙarin ganin sun daina saɓa wa Ubangiji (s'w't).

Sannu-sannu bata hana zuwa sai dai adaɗe ba'a je ba, sai gashi dukkanin kawunan
ƙungiyoyin musulmi sun haɗu, zaman lafiya da aminci ya wanzu a ko ina albarka gami da
ni'imomi suka mamaye al'ummar musulmi.
www.littafanyaki.com.ng


Kuma sarki da kanshi ya dunga yin hawa izuwa ƙasashen sauran Musulmi yana sai-sai ta
musu matsalolin su, tare ƙone dukkanin Littafin addinin dake ɗauke da gurɓatattun aƙidoji,
gami da ɗorasu bisa turbar gaskiya.

Karshe

Alhamdulillah


Daga mai ɗebe muku kewa a kullum da ko yaushe

MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaki
Wthapp number
08137237071

1
2

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login