Showing 1 words to 3000 words out of 5666 words

Chapter 1 - KARNI UKU littafin Yaki Complete By Mansur Usman Sufi .pdf

KARNI UKU Book 1
Writing by
MANSUR USMAN SUFI
SARKIN MARUBUTAN YAƘI
08137237071





ƘASAR MADINATUL-BARNAWIY



Kasaitaccen ɗakin taron ya cika ya batse da manyan sarakuna,Bokaye,matsafa haɗe da
jarumai.

Duba ɗaya zaka yi musu ka fahimci cewa akwai wani muhimmin al’amari daya taru a wajen.

Tsawon daƙiƙa talatin ana cikin wannan hali babu wanda yace ƙala.

Daga bisani ne wani dattijo ma’abocin ƙasumba da gemu farare sol!, Mai ɗauke da yanayin
ɗaure fuska.

Yayi gyaran murya ya dubi jama’ar dake ɗakin taron yace “yaku yan uwana sarakuna da
sauran mahalarta wannan taro mai albarka, dafarko ina yiwa kowa Barka da zuwa.

Babban abinda ya tara mu anan shine tabbatar da tsafi a doran ƙasa, wanda hakan bazai
taɓa tabbata ba face an ɓatar da ma’abota addinin Musulunci a doran ƙasa.

Sanin kanku ne cewa dakushe hasken musulmi abune mai matukar wahalar gaske, matukar
muna son cimma wannan buri namu dole sai mun jefa musulunci cikin saɓon Ubangijinsu.

Daga lokacin da na fara wannan nazari da sauran Yan uwana sarakuna, mun fara cimma
nasarori masu yawa, sai dai a halin yanzu ne zamu kama aikin gadan-gadan ta hanyar haɗa
karfi da ƙarfe, domin masu iya magana na cewa hannu ɗaya baya ɗaukar jinka.

Ubangiji na faɗa a cikin littafinshi mai tsarki cewa “idan Musulmi suka bauta mashi yadda
yake so, zai basu rayuwa mai daɗi tare da ‘ya’yansu da jikokinsu.

Sannan a sunnah ya tabbata cewa su musulmi kamar ginin daƙi ne mai kusurwa huɗu,
kowace katanga tana karfafawa ne da yar uwar ta, ma’ana dazarar rabuwar kai ta shiga
tsakaninsu kodai ta fahimtar addini ko kabilanci da al'adun yau da kullum,to daga nan zasu
samu nasara murƙushe.

Lokacin da dattijon da ake kira da suna urwat ɗan Abbas yazo Nan azancenshi sai dukkan
wanda ke cikin ɗakin taron ya cika matukar mamaki jin yana karanta littafin Allah tamkar
yakasance musulmi.

Urwat ya cigaba dacewa “Dukkaninmu yan uwa ɗaya ne kuma dangi ɗaya, koda akwai
babban jinsi da birane,amma kada mu manta abune ɗaya ne ya haifemu shine, tsafi, bautar
gumaka.

Fiye da shekaru arba’ina lokacin ina samartaka, ina rayuwa.

A cikin musulunci,babu wani abu nasu dabani da sani a kanshi walau ta fuskar ilimin addini ko
zamantakewa.

Lokacin da yazo nan a jawabinshi sai dukkan wanda ke cikin ɗakin taron ya cika da matuƙar
farin ciki,urwat ya gyara zama bisa kujerarshi ya, shiru ne ya kuma mamaye ɗakin taron a karo
na biyu.

Sarki sha’aran yayi gyaran murya yace “Bayan dukkan bayanin da sarki urwat ya kawo
yanzu, akwai waɗansu muhimman abubuwa da ya kamata mu lura dasu anan, mafi yawan suna
burin ganin sabon al’amari na cigaba a wajen su koda ta hanyar karama(almara).

Ko kuwa ta ƙirƙira, bazasu taɓa damuwa ba koda ya saɓa da addinin su zasu ƙarɓeshi hannu
biyu, har wasu ma na ganin idan malami baya karama,to bai cika mai tsoron Allah ba.

Yanzu dukkan shiryen mu sunyi nisa, mun tura dukkannin mutanenmu izuwa biranen manyan
dauloli musulmi, bayan sun samu horo akan dukkan da muka ɗora su akai, daga cikin nasarorin
da muka samu.

Akwai kwaɗaitawa mata da son wassanni, koyarwa da mata dubarun zama da mazajen su na
tsarin zamani da al’adunmu, Domin gurɓata zaman su da mazajensu,

Sannan duka Littattafan da muka wallafa Dake yaƙar gaskiyar dake cikin addininsu, yanzu
abinda ya rage mana a gaba shine a mako mai zuwa zamu tura rukuni na ƙarshe daga
jama’armu ta zasu tafi ƙasashen a matsayin yan gudun hijira, waɗanda a cikin su ne zamu basu
muhimman makamai masu barazana ga dukkan wata halitta mai numfashi, gami da sirrikan
tsafi.

Lokacin da sarki sha’aran yazo nan azancenshi sai yayi kowa dake ɗakin taron ya cika da
matukar farin ciki maral misaltuwa.

Daga wannan kowa ya tattare tawagarsa ya fice daga ɗakin taron.

*****

Yanayin gidan sarautar ya ƙawatu ainun da fiye da misaltawa, idan mutum yakai dubanshi
izuwa ga wani ɓangare da yafi ko ina ƙawatuwa zai yi arba da kuyangi,barorin,hadimai gami da
dakarun shirye cikin shigar yaƙi na ta kai komo,suna aiyuka.

Wata kuyanga ce matashiya ɗauke da kayan marmari dangin ridda, ayaba da jini, a cikin
wani kwandon kaba, ta doshi wata turakar, tana iso masu gadi suka bude mata kofar shiga ta
kunna kai izuwa cikin gami da yin sallama.

Shiru taji batare da an amsa mata ba, kuma tana iya jiyo alamun motsi a turakar,haka dai ta
cigaba da tafiya sannu a hankali tana huce kofofin turkar, har ta iso inda take sa rai zataga
gimbiya.

Salati gami da tasbihi ta dunga karantawa a ranta, har idanun ta sun fara cikowa da kwalla,
tana mai runtse su tamkar tayi arba da mutuwarta ƙirjinta na bugawa da sauri,ta saki kwandon
dake hannun ta kayan marmarin dake ciki suka tarwatse ta hanyar watsuwa a turkar.

Duk da motsin da ya bayyana na tarwatsewar kayan marmarin, bata sanyasu dawowa cikin
hayyacinsu daga saɓon Ubangijinsu ba.

Da sauri ta juya domin komawa da baya, zuciyar ta cike da matuƙar ɗimauta, taya ya za’a
aikata wannan mummunan saɓon Allah a gidan sarautar musulunci, tabbas sai na bayyana
wannan al’amari ga mai martaba sarki koda kuwa hakan zai zamo ƙarshen numfashina a
duniya.
Haka dai ta cigaba da tafiya da sauri har tana tuntuɓe, domin ta isa hanyar da zata sadata da
fada.

Fadar ta cika ta batse da manyan fadawa, talakawan gari haɗe dakaru, kowa na zaune cikin
ladabi da girmamawa.

Sarki Anwar na zaune a bisa karagarshi ta mulki,sanye da tufafin alfarma irin na hamshaƙen
sarakai, hannunshi riƙe da cazbaha,yana jan addu’o’i,

Ana tafiyar da sha’anin mulki cikin lumana.

Wani dattijo ma’abocin tarin shekaru da cikar kamala yayi gyaran murya cikin ladabi ya dubi
mai martaba sarki yace”ya shugabana ina wani labari da na samu daga shugaban masu kula da
hidimar masallaci cewa, kwana biyu an samu raguwar matasan mu wajen fitowa sallar asubahi,
Haƙiƙa hakan babban abin takaici ne sosai,a shawarata kodai a faɗakar da iyaye illar Hakan ko
kuwa a sanyawa dukkan wanda yaƙi fitowa sallar asubahi haraji matsawar bada wani uzuri da
addini ya amince dashi ba.

Wani mutum daga cikin fadawan sarki da shekarunshi basu gaza arba’in ba, yayi gyaran
murya yakawo Gwauron numfashi ya ajiye ya dubi dattijo mai suna Salman yace” Allah ya
shugaban majalissa a rawa fahimtar a cikin littafi da sunna, babu wani waje da ake iya tilasta
mutum ibada, ballantana ace idan yaƙi yi a sanya mashi haraji, domin ita ibada ana yin ta ne
cikin daɗin rai .

Ko da jin wannan batu daga bakin Hakimi urwat sau fadar tayi shiru tamkar mutuwa ta kawo
ziyara, duk wannan tattaunawa da ake yi sarki yana ji bai ce uffan ba, sai da ya fahimci
tattaunawar zata haifar da damuwa, sai yayi gyaran murya yace” yaku fadawana kuyi sani cewa
wannan magana da shugaban majalisa ya kawo na da matukar muhimmanci ainun sai dai ni
akwai wata matsala dake ganin tana gaba da wannan kuma dare da rana da ita nake
tashi,wannna matsala ba wata ba face yawaitar yan gudun hijira daga waɗansu birane dake
zuwa wannan ƙasa tamu, domin samun mafaka, hakan baya rasa nasaba da tashe-tashen
hankula da ake samu a birnin Nuraniyyu.

A makon da ya gabata labari ya riskeni cewa a wannan makon an kai wani mummunan hari
a masallaci a lokacin da ake gudanar da sallar asubahi, tabbas wannan abun baƙin ciki ne da
damuwa daya kamata mu kula sosai ta hanyar ƙarfafa tsaro tare da ba wa mayakan mu horon
yaƙi.
Uwa uba kuma shine tsayawa bisa tafarkin da magabata suka ɗora mu akai…..!

Kafin sarki ya ƙarshe maganar sai ya hango kuyanga ihsan ta shigo fadar hankalin ta a
tashe tana haki,tamkar numfashinta zai ƙare.

Sarki Anwar ya mayar da dubanshi izuwa gareta domin yaji shin mene ne ke tafe da ita.

Lokacin da yazamana cewa saura taku huɗu tsakanin ta da karagar mulki sai ta zube ƙasa
bisa gwiwoyinta ta kwashi gaisuwa.

Sarki ya ƙarɓi gaisuwar cikin annuri.

Ihsan ta buɗi baki ta buɗi baki da nufin tace wani abu amma koda ta haɗa idanu da Hakimi
urwat sai taji bakinta yakasa furta komai, tsawon daƙiƙa ashirin tana ƙoƙarin hakan amma ya
gagara, Al'amarin da ya sanya sarki da sauran jama'a suka cika da mamaki kenan bisa ganin
tana magana da Yaren kurame.
Sarki ya dubeta yace" yake ihsan shin ina dalilin wannan hali da kike ciki, me kike son
fahimtar dani?.

Hawaye ne ya shiga shata ta daga idanun ta bisa ganin halin da take ciki, tana mai tambayar
kanta akan ranta tana mai mai cewa shin ina dalilin rashin yin maganata, koda wani ne yayi mini
wani sihiri, amsar tambayar da ta kasa bawa kanta kenan.

Urwat ya saci kallonta gami da murmushin mugunta, wanda waziri ne kaɗai ya lura da hakan.

"Ta yiwu akwai wata rashin lafiya ce ta same ta, ranka ya daɗe ina ganin yana da kyau mu
tafi zuwa masallaci domin lokacin sallar azuhur yayi.

Hakimi urwat ya faɗa cikin ladabi".

" Zancen ka dutse yakai urwat".

Sarki ya faɗa tare da kallon in da hasken rana ya ratso a fadar.

Ya ɗorawa batun shi da cewa "A kai ihsan izuwa wajen 'yar mai ganye domin a duba
lafiyarta, Ka dawo da ita izuwa gareni, haƙiƙa na tabbata akwai wani muhimmin al'amari da take
son sanar dani, domin na aminta da ita matuƙa.

Ya ƙare zancenshi yana duban wani bafade, saurayin mai yanayin kazar-kazar dake tsaye a
hannunshi na dama.

" An gama ya shugabana Bafaden ya daɗi cikin ladabi, ya juya ya nufi kofar fita daga fadar
taɓa mai yafito ihsan da hannu dake yi mata nuni ta biyo bayanshi, Da sauri ta miƙe tsaye tayi
koyi dashi suka kule izuwa wajen fadar.

Sarki ya sauko bisa karaga ya taka matattakalar fadar ya sauko ƙasa ya durfafi wata kofa ta
musamman dogare da sandarshi, dakaru,hadimai tare da hakimai suka mara mashi baya,
sauran jama'a sukayi koyi dasu, domin isa zuwa masallaci.

Kafin a isa masallaci sai Hakimi shaibat ya shafi wani gurin tsafi a damtsen hannunshi na
dama ya ɓace ɓat!.

Sarki shaibat ya juya domin ya amsa sallamar da wani mutum yayi mashi, ai kuwa sai
idanuwanshi suka sauka a saitin inda Hakimi shaibat ke tsaye a can gefenshi, take yaga wayam
Babu alamun shi, Batare da bari wani daga cikin jama'arshi ya lura

Bai bayyana ako ina ba sai a daf da kofar fita daga gari, kai tsaye ya durfafi kofar, yayin da
dakaru suka hangoshi sai suka miƙa gaisuwa gareshi tare da yi masa sallama yana amsawa,
waɗansu dakaru a gefe ya hango sun tare waɗansu samari uku da fuskokin suke ke rufe da
bakin rawani suna ɗauke da waɗansu bujjuna a bisa kan amalanke.
Sannu a hankali yana takawa har ya isa gare su.

Mene ne ke faruwa ana ?

Urwat ya tambaya a taƙaice.

Wani saurayi mai tarin ƙasumba ya risina gareshi cikin ladabi ya buɗi baki Muryar na rawa yace
" ya shugabana muna binciken buhhunan da suke ɗauke da sune domin tabbatar da tsaro.

"Shin baka da sanin cewa dukkan kayan daga gareni suka fi to?".

Urwat ya tambaya fuska a murtuke.

Tuba nake ranka ya daɗe insha Allah hakan bazai sake faruwa ba.

Badakaren ya faɗi.

Cikin hanzari samarin suka tura kayan suka huce gaba.

Badakaren ya bisu da kallo yana ƙarewa buhhunan kallo yana son fahimtar wani abu, har
suka ɓace gareshi ya daina hangoshi.

Wata unguwa urwat ya nufa data saɓa da wacce samarin uku suka bi, da shigar unguwar ya
durfafi wani gida yana isa tamkar an san da zuwanshi aka wangame kofar gidan ya kunna kai
ciki.

Zaune ya isar dasu suna shan barasa suna ta ƙyaƙyata dariyar mugunta, samarin uku da ya
baro a hanyar kofar gari ne

Waje ya samu ya zauna bisa wata kujera yana mai fuskantar su a lokacin da suka nutsu
domin suji bayanin dazai yi musu.

Ina fatan dukkan kayan mu mun kammala yadda ake buƙata?

Urwat ya tambaya.

Wani daga cikin matasan mai yanayin shiru- shiru shine ya yiwa sauran samarin biyu Indiya ta
wutsiyar idanu, da sauri suka miƙe tsaye suka nufi bangare a ɗakin sauko waɗannan buhhunan
suka zo suka ajiye a daf da inda urwat yake suka buɗe buhhun.

Urwat ya ɗora idanuwashi akan buhunan domin yaga abinda ke ƙunshi a ciki.

Motsin alamun sawaye suka ji na kusanto da ɗakin, al'marin daya sanya dukkanin su sukayi
turus kenan domin ganin abinda ya bayyana gare su zukatansu cike da matuƙar al'ajabi domin
kuwa a iya sanin su babu wanda ya san da wannan gida na sirri face su huɗun kacal.

Wannan shi ne abinda ya wakana a ƙasar madinatul-barnawiy.

****

Al'amarin Bafade da ya tafi da kuyanga ihsan izuwa gidan 'yar mai ganye domin zartar da
umarnin mai martaba na duba lafiyarta.

Lokacin da suka kaɗaita a cikin turkar 'yar mai ganye sai Bafaden ya zayyane mata dukkanin
saƙon da yake ɗauke dashi izuwa gare ta daga wajen mai martaba.

Ko da jin wannan batu sai yar mai ganye ta ƙura wa ihsan idanu kuma ta hanya hannunta ta
gwale idanun ta na dama, bayan ta kammala bincikenta, sai ta dubi Bafaden ta buɗi baki cikin
murya mai tattare da alamun dattijantaka tace.

"Dukkanin ƙoƙarin da nayi domin na gano irin nau'in cutar dake damun ihsan hakan ya
fasƙara, Kawai abinda na ɗan fahimta shine an yi amfani da sihiri ne a lalurarta.

"Ni kaina ina zargin hakan matuƙa.

Bafaden ya faɗi.

"Yanzu Ina ganin zan gwada yi mata addu'o'i ku Allah zai sa a dace.

'yar mai ganye ta faɗa, gami da sanya hannunta ta buɗe bakin ihsan, ta shiga karanta
Ayatul-kursiyyu tana Tofa mata a ciki.

Lokacin da ta kammala karatun bisa mamaki sai suka ji ihsan tayi Atishawa da ƙarfi ta buɗi
baki tace "Alhamdulillah.

Nan fa Bafaden da ihsan suka cika da matukar farin ciki maral misaltuwa suka yi salati ga
Annabi s'a'w domin nuna godiya ga Allah (SWT).

Su kayi sallama da yar mai ganye domin komawa ga mai martaba sarki.



Kasar Madinatul-barnawiy



Wane ne sarki Anwar ?

Kuma mene ne dalilin daya sanya Musulmi suka fara samun matsaloli a cikin al'ummar su tun
daga tushe?

Dalilin haka kuwa shine kamar haka.

Sarki Anwar ɗan Adam yakasance mutum mai matsakaicin kyawu da shekaru yana tarin
ilimin addini da son ganin ya kyautata al'ummarshi, bisa wannan dalili ne yasanya kowa ke
zaune lafiya, manya na tausayawa ƙanana, na ƙasa na girmama manya, babu cuta babu
cutarwa, kuma dukkan wani fabatake da ya shigo birni sai limamin dake yankin ya ganshi kuma
ya tabbatar da cewa ga daga inda yazo domin tabbatar da tsaro.

Miji na sauƙe haƙƙin iyalanshi, mata na yin biyyayya ga mai gidanta, duk wanda ya aikata
laifi tsakanin babba, Attajirai da talakawa ana yanke hukunci babu bambanci.

Bisa wannan dalili ne yasanya dukkan al'umma ke zaune cikin aminci, kwatsam sai aka
wayi gari da waɗansu a yarin fatake dake ɗauke da malaman addinin Musulunci ƙarƙashin wani
shehun malami

1
2

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login