Showing 6001 words to 8503 words out of 8503 words
Chapter 3 - KOGON ANNOBA True Books Available Complete Na Mansur Usman Sufi Sarkin Marubutan Yaki .pdf
da kun
kasance jarumai kamar yanda har kullum kuke muradi sa'adda Yarima Nazmar yaji amsar
wannan tambaya sai ya cika da mamaki yace wacce hanya zanbi in samu taimakon
ubangijinka Huzaifal yace ai abune mai sauki kawai duk sa'adda wani abu ta taso maka kace
kana neman taimakon ubangijin gaskiya ubangijin da yayi rana da wata yayi mutum da aljan
dabba da tsuntsaye ruwa da iska
ubangijin da babu wani ubangiji bayan shi a ranka ba tareda ka furta wani yaji ba lallai kai da
yar uwarka inason ku boye mini wannan sirri dake tsakanin mu Yarima
Nazmar da yar uwarsa sukace ai kuwa babu wanda zaisan da wannan sirri har sai gaskiyar
abinda kake gaya mana ya baiyana daga wannan kuma Huzaifal ya shiga basu daddadan
labarai masu sanyaya nishadi da annashuwa
haka dai aka cigaba da wannan tafiya babu sassauci ana cikin tafiyar ne kwatsam ba zato
babu tsammani sai aka hango jibga jibgan mutane masu tsawo da kauri qirar mutanen farko
yawansu yakai dubu biyar suna da
miyagun makamai masu baraza ga rayuwar mutane da aljan nan fa gaba daya dakarun sarki
Siyamul ansar suka firgice sukaji tamkar su cika wandunansu da iska amma sai sukaga
mutanen sunyi musu kawanya suna masu fitowa daga kusurwar dajin. Lokacin da mutanen
suka kammala yi musu kawanya sai aka fara kallon kallo daga can sai akaga
mutanen sun ɗane sun sake bayar da wata yar siririyar hanya a tsakiyarsu da mutum zai iya
wucewa sai ga wani garjejen qato ma'abocin kwarjini da ban tsoro ya ratso hanyar
ya fito izuwa gaban mutanen ya dubi su sarki Siyamul ansar a wulakance sannan ya bushe da
mahaukaciyar dariya mai kama da haniniyar doki sannan daga bisani ya
turbune fuska tamkar an aiko masa da sakon mutuwa ya bude wawakeken bakinsa mai dauke
da wadansu wargatsattsun hakora cikinsa marasa kyan gani cikin kakkausar
murya yace yaku wadannan kwari maza ku sallama kanku izuwa gareni kafin in zare muku
ruhinku daga gangar jikinku kafin garjejen
qaton ya gama rufe bakinsa jarumi Huzaifal ya tari numfashinsa yana mai maida masa da cewa
shin wanene kai kuma menene
nufin ka agaremu garjejen qaton ya bushe da dariya a karo na biyu sannan ya kurawo Huzaifal
idanu masu kama da garwashin wuta yace eh lallai da kyau yan samari shin
har kanason kasan wanene ni to inaso kai da abokan tafiyarka kusani cewa nine sadauki
RAUZAM shugaban yan ta'addar
wannan nahiyar baki daya amma fa na yaba da jarumatarka matuka ganin yanda ka iya yin
magana baki da baki dani amma
lallai bazan bar dayanku a raye ba jarumi Huzaifal ya katse shi da cewa amma idan har ka cika
namijin duniya muyi fada da juna
kuma kada dayanmu ya rike makami a gwada yar qashi idan nayi nasara akanka na cinye ka da
yaki idan kaine kayi nasara
ka kashe ni sai ka kashe abokan tafiyata. Koda jin abinda Huzaifal yace sadauki Rauzam ya
takarkare ya kwarara uban ehu da ya
firgita gaba daya jama'ar dake wajen sannan yace da kyau jarumin kwarai haka akeson namiji
da zuciya irin ta manya yana gama
fadin hakan sai kawai ya daga annayensa sama ya falfala da gudu izuwa inda Huzaifal ke tsaye
duk sa'adda ya ajiye kafarsa daya sai dai kaji kasa na amsa kuwwa tamkar zata rufta
Yana gama fadin haka kawai sai ya daga hannayensa sama ya falfala da gudu izuwa inda
Huzaifal ke tsaye duk Sa'adda ya ajiye kafarsa daya sai sai dai kaji kasa ta amsa tamkar zata
rufta koda ganin haka sai Huzaifal ya sauko daga kan dokinsa yana mai gyara tsayiwarsa
gamida dunkule hannayensa biyu da isowar sadauki Rauzam yakai masa wani wawan naushi a
fuska ya sunkuya hannun Rauzam ya naushi iska sannan duka kacame da azababben yaki mai
matukar ban al'ajabi da ban mamaki ana fara wannan gumurzu nefa Huzaifal ya fahimci cewa
Rauzum ya fishi tsagwaron karfin damtse domin idan ya naushe shi a fuska ko a jiki inda ya
nausa din sai jini ya taru Huzaifal ya daka tsalle tamkar an harbo shi daga cikin baka ya daki
kirjin Rauzum da kafafunsa biyu saboda karfin dukan sai da Rauzum yayi sama tamkar an
janye shi daga qugiya yayi katantanwa a sama sau uku cikin gwaninta jarumi Huzaifal ya daka
tsalle sama yayiwa Rauzum luguden naushi sau goma sannan suka sauko kasa a tare yana
mai dora kafarsa a wuyan Rauzum alokacin da jini ke juba a hannayensa a hancinsa da
bakinsa kuma numfashinsa ya fara sargewa Huzaifal ya dube shi yace yakai wannan dan
ta'adda kayi sani cewa matukar zaka bayarda gaskiya ga ubangijina kuma ka daina wannan
haramtacciyar sana'a taka zan kyaleka ka cigaba da rayuwa koda jin haka sai Rauzum yayi
murmushin karfin hali ya furzadda gudan jini a bakinsa cikin kakkausar murya yace ai da inyi
mubaya a agareka gwara ka kashe ni domin za a shaida cewa ni jarumi ne kafin Rauzum ya
gama rufe bakinsa Huzaifal ya zare takobinsa ya datse masa wuya. Koda sauran yaransa
sukaga abinda ya faru ga shugabansu sai sukayi kururuwa suka afkawo su jarumi Huzaifal aka
kacame da azababben yaki sai da aka shafe tsawon sa'a biyu ana wannan yaki sannan
Huzaifal suka samu nasarar hallaka gaba daya yaran Rauzum a inda kowanne daga cikinsu
Rauzum a kashe dakarun rakiya mutum saba'in dayake duhun dare ya fara kawo kai sai kowa
ya sanyawo kansa magani kuma aka kafa tantuna sannan akayi kalaci saida aka shafe tsawon
kwanaki biyu a wannan daji a iya wannan kwanaki jarumi Huzaifal ya koyawo su yarima yadda
ake yaki kuma bisa mamaki sai gashi suna rike duk abinda aka koya musu al'amarin da yayi
matukar bawo sarki Siyamul ansar mamaki kenan domin sau tari yana koya musu yaki amma
basa rikewa da hantsi aka sake yin shiri aka cigaba da tafiya saida suka shafe kwanaki hudu
ana keta miyagun dazuzzuka amma bisa taimakon ubangiji basu sake haduwa da wani abin
cutarwa ba sau tari idan miyagun dabbobi suka hango su sai kaga sun tarwatse sun bazama
izuwa cikin daji al'amarin da yayi matukar bawa sarki Siyamul ansar da boka Zulwal mamaki
kenan abinda basu sani ba shine kawai tsananin addu o in da jarumi Huzaifal ke karantawa ne
suka tsare su daga sharrin dabbobin a iya tsawon wannan kwanaki babu abinda ke tsaida su
face idan lokacin bacci yayi ko lokacin gabatar da sallan jarumi Huzaifal a ranar kwana na biyar
ne da yamma sakaliya suka hango gidan boka Jabarul sihir akan tsakiyar wani qaton dutse da
ba a ganin karshensa. Lokacin da ya zamana saura taku ashirin atsakaninsu sai kowannensu
yaja linzamin dokinsa ya tsaya suka sauko sannan suka raka da kafafunsu suka durfafi gidan
suna masu zare makamansu da isarsu izuwa bakin kofar gidan suka tarar kofar ta kasance
doguwa mai tsawo da fadi kuma anyi tane da zallar mulmulallen karfe Huzaifal ya matsa kusa
da kofar ya karanta ayatul kursiyyu da tsarkakakken sunaye yana mai tofawa ajikin kofar sai
gashi ya tura kofar da hannu daya tamkar ya yaye labule kawai sai ya kunna kai izuwa cikin
gidan sarki Siyamul ansar boka Zulwal yarima Nazmar gimbiya Hulaisa dakarun rakiya ne a
karshe suka bi bayansu da sauri da shigarsu suka tarar da wata hangamemiyar fada ta gaban
kwatance gaba daya fadar gidan anyi shine da zallar farin gilashi idan mutum ya kalli ko ina a
fadar sai yaga hoton surar jikin gilashin aqalla girman fadar yakai gari guda kai tsayawa misalta
tsaruwa da kawaitar fadar yakan iya zamowa kauyanci sai dai abinda ido ya gani wani abin ma
idan mutum ya gani bai taba gani ko jin sunansa ba abangaren yamma afadar bisa wata
matattakala mai hawa shida aka ajiye wata qasaitacciyar karagar mulki ta gaban kwatance boka
Jabarul sihir ne zaune bisa karagar fuskarsa cike da annuri tamkar wanda aka bawo mulkin
duniya boka Jabarul sihir ya kasance garjejen qato mai tsawo da kauri tamkar toron giwa duk
da kasancewar shekarunsa sun dan ja kallo daya zakayi masa ka fahimci cewa ya kasance
gwarzon mayaki mai tarwatsa maza afilin daga a wannan lokaci boka Jabarul sihir na tsaye ne
cikin doguwar alkyabba da akayi mata cin baki da zaren lu'ulu'u akansa yana sanye da kambun
mulki da akayi shi da zallar zinare yana walwali da daukar idanun mai kallonsa duk inda mutum
ya kalla ajikinsa guraye ne da layun tsafi zaune bisa wadansu qayatattun kujeru afadar yan
majalisansa ne na jinsin mutum da aljan kuma gaba daya fadar kewaye take da wadansu irin
zaratan dakaru masu matukar muni da ban tsoro suna dauke da makami masu barazana da
rayuwar bil adama lokacin da boka Jabarul sihir yayi arba da su sarki Siyamul ansar sai ya mike
tsaye zumbur daga kan karagarsa ya tako matattakalar fadar ya sauko kasa yana mai takowa
da kafafunsa yana kusantar inda suke fuskar cike da annuri tamkar zai sadu da yan uwansa na
jini. Koda ganin hakan sai su jarumi Huzaifal suka dafe takubbansu lokacin da ya zamana saura
taku goma tsakaninsu sai boka Jabarul sihir yaja ya tsaya ya dubi su jarumi Huzaifal ya bushe
da dariyar farin ciki sannan ya budi baki cikin kakkausar murya yace lale marhabun da manyan
baki masu daraja na dade ina jiran zuwa wannan rana mai cike da farin ciki agareni yanzu sai
ku miko min kwan sihirin da su yarima suka dauke mini akogon Annoba koda jin wannan batu
sai sarki Siyamul ansar ya daka masa tsawa yace kai tsohon la'ananne kai sani cewa baka isa
mu damka maka kwan sihiri ba face ka amince zaka debo mana ruwan koramarka wanda dashi
ne zan warkar da 'ya'yana koda gama fadin haka sai sarki Siyamul ansar ya zura hannunsa a
aljihu sai gashi ya fito da wani kwai mai girma tamkar gwanda yayin da boka Jabarul sihir yayi
arba da kwan sihiri sai ya takarkare ya kwarara uban ihu paruwar hakan keda wuya sai gaba
daya duhun ya yaye sai ga boka Jabarul sihir cikin gagarumar shigar yaki a hannunsa yana rike
da wata zabgegiyar adda mai tsawo da tsinin tsiya koda ganin hakan sai sarki Siyamul ansar ya
zare takobinsa boka Zulwal yayi koyi dashi suka ruga izuwa kan dakarun fadar jarumi Huzaifal
kuwa ya zare takobinsa ya ruga kan boka Jabarul sihir aka kacame da azababben yaki ana
cikin hakan ne sai su yarima Nazmar sukaga wadannan miyagun tsuntsaye na ratsowa ta
saman fadar tamkar yadda danshi ke ratsa kasa suna dura a gabansu daya bayan daya koda
ganin hakan sai yarima Nazmar da gimbiya Hulaisa suka falfala da azababben gudu izuwa kan
tsuntsayen suna masu rayawa azuciyoyinsu cewa muna neman taimakon ubangijin musulunci
ba tare da sun riki wani makami ba suka afkawa tsuntsayen da yaki su kuwa dakarun rakiya sai
suka zare makamansu suka tari wadansu dakaru afadar dake bangaren yamma aka yamutse
da fada abu kamar wasa sai gashi jarumi Huzaifal da boka Jabarul sihir sun shafe tsawon sa'a
biyar suna yaki ta hanyar kaiwa juna miyagun hare hare. Lokacin da boka Jabarul sihir ya
fahimci cewa ya kasa samun nasara akan Huzaifal da karfin damtse sai ya fara amfani da karfin
sihirin tsafi har ya zamana yana yin amfani da dukkanin sirrikan tsafinsa tabbas boka Jabarul
sihir ya hadu da gamonsa dakyar da siɗin goshi ya samu nasarar zabgawo Huzaifal daushi aciki
ya bazadda shi kas koda Huzaifal ya fahimci halinda yake ciki sai ya kira sunan ubangiji karfi
yana mai neman taimakonsa take ya samu wani gagarumin karfi kawai sai ya mike tsaye
zumbur yayi tsalle sama tamkar an harbashi daga cikin baka ya dira akan boka Jabarul sihir
yana mai rarraba kafadunsa cikin zafin nama ya sanya hannayensa biyu ya murde masa wuya
sannan ya dako tsalle ya dira bisa kafafunsa cikin gwaninta adaidai wannan lokaci ne gawar
boka Jabarul sihir ta fadi kasa racaca jini ya kwaranya nan take dakarun gaba daya da suke
yaki da su sarki Siyamul ansar suka qame suka zama gumaka kuma komai na fadar ya sandare
ya zamana saura tsuntsaye dasu yarima suke cikin yaki nan fa jarumi Huzaifal boka Zulwal da
sarki Siyamul ansar suka zuba idanu suna kallon fafatawar da akeyi babu abinda yafi basu
mamaki sama da yadda su yarima Nazmar ke ragargazar tsuntsayen babu sassautawa a inda
za kaga sun kirbawa tsuntsu naushi sun karya kafa ko fukafuki nan fa ya zamana ihu da
kururwar tsuntsaye ya mamaye fadar jini kuwa ya dinga kwaranya yana malala tamkar an balla
teku su kansu su yarima sunyi matukar mamakin irin wannan gagarumin karfi da suka samu sai
da dakika dari da sittin ta shude sannan yarima Nazmar da gimbiya Hulaisa suka samu nasarar
kashe gaba daya tsuntsayen amma gaba daya jikinsu ya rine da jini tamkar an tsomasu cikin
tekun jini cikin matukar farin ciki sarki Siyamul ansar ya ruga inda 'ya'yansa suke ya rungumesu
a kirjinsa cikin tsananin farin ciki daga can su yarima suka janye jikinsu daga na mahaifinsu
suka dube shi sukace ya abbanmu kayi sani cewa dukkanin wannan nasara da kaga mun samu
akan wadannan tsuntsaye mun samu taimako ne daga ubangijin jarumi Huzaifal saboda haka
munyi imani da ubangijin musulunci koda jin haka sai sarki Siyamul ansar boka Zulwal da
dakarun tsakiya sukace muma munyi imani da ubangiji mahalicci cikin matukar farin ciki jarumi
Huzaifal ya karanta musu kalmar shahada suka maimaita.
Faruwar hakan keda wuya sai sukaji gaba daya fadar ta kama girgiza koda ganin hakan sai
jarumi Huzaifal ya falfala da gudu izuwa kofar fita dake fadar yana mai yiwa su sarki nuni da su
biyo bayansa ai kuwa suna kammala fita daga fadar sai gaba daya ginin fadar ya dinga
rushewa kuma gaba daya ya nutse cikin karkashin kasa Huzaifal ya dubi su duka su hudun
yace bamuda bukatar nemo ruwan ma"ul diya'u dan warkar da su yarima imani kadai da sukayi
da ubangijin musulunci ya warkar dasu daga lalurar dake damunsu ta rashin jin magana koda
gama fadin haka sai jarumi Huzaifal yaje ya kama dokinsa ya hau sannan kowa ya hau nasa
aka cigaba da tafiya sa'adda lokacin sallah yayi sai jarumi Huzaifal yayi umarni aka tsaya da
tafiya bayan an samu ruwa a wata korama anyi alwala su yarima sun sauya tufafin dake jikinsu
sai Huzaifal ya shige gaba yayi musu limanci sa'adda su sarki sukaga yana yin ibadar bisa tsari
mai ban sha'awa sai sukaji kaunar addini ta kara shiga ransu bayan an kammalane aka dauki
hanya yayin da aka isa birnin sarirul aiwan sai aka kafa tutar musulunci jarumi Huzaifal ya auri
wata baiwar sarki Siyamul ansar mai suna ZARIMAT BINTU FANNAS daga wannan rana
jama'ar birnin suka kasance cikin farin ciki da kwanciyar hankali ya zamana babu manyan
jarumai kamar su yarima Nazmar da sanin ilimin addinin musulunci.
ALHAMDULILLAH
Marubuci
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi
Wthapp number
08137237071