Showing 3001 words to 6000 words out of 8503 words

Chapter 2 - KOGON ANNOBA True Books Available Complete Na Mansur Usman Sufi Sarkin Marubutan Yaki .pdf

matattu kamar ana sassabe agonar auduga sarki Siyamul ansar ya
wanzu yana kare kansa yana saran tsuntsayen cikin bakin zafin nama juriya da jarumtaka.
Yayin da yaga yanda dakarunsa ke hallaka sai takaici ya turnuke shi ya takarkare ya kwarara
uban ehu ya dire daga kan dokinsa ya tari wani tsuntsu guda daya suka kacame da yaki idan
tsuntsun ya wangame bakinsa ya huro masa wuta sai kaga sarki Siyamul ansar ya kaucewa
harin cikin bakin zafin nama idan wutar ta zuba a kasa sai kaga wajen ya haddasa wani
wawakeken rami mai zurfin gaske Lokacin da tsuntsun yaga ya kasa samun nasara akan sarki
Siyamuk ansar ta hanyar kone shi da wutar bakinsa sai kawai ya dinga kai masa yakushi da
zaqo zaqon paratan hannunsa da nufin yayi fata fata da sassan jikinsa. Faruwar hakan keda
wuya sai sarki Siyamul ansar ya fara gano lagon tsuntsun domin yanzu takobinsa ya fara tasiri
akan tsuntsun dan ayanzu takobinsa na samun nasarar yankar jikin tsuntsun duk inda takobin
ya sara ajikin tsuntsun sai dai kaga ya dare jinina kwaranya. Abangaren boka zulwal kuwa yana
iyakar kokarinsa wajen yakar tsuntsayen amma babu abinda ya daure masa kai sama da yadda
karfin sihiri baya tasiri ajikin tsuntsayen face tsagwaron karfin damtse duk inda mai kallo ya
duba ba abinda zai gani face gawarwakin dakaru fululu kwance cikin jini wasu a babbake suna
kauri jini kuwa ya cakude da kasa babu kyan gani ana cikin wannan yaki ne wannan tsuntsu ya
samu nasarar yankar sarki Siyamul ansar da faratansa a cinya take inda ya yanke shi ya
haddasa wani qaton rauni jini ya kwaranya saboda zafi da zugin da sarki Siyamul ansar yaji bai
san sa'adda ya sandara uban ihu ba ya saki takobin dake hannunsa cikin tsananin zafin nama
ya daka tsalle daga inda yake tamkar an harbashi daga cikin baka ya dira akan wuyan tsuntsun
ya sanya hannayensa biyu ya kama kan tsuntsun ya murde iyakar karfinsa nan take wuyan ya
karye ji kake rukuss sarki Siyamul ansar ya daka tsalle karo na biyu ya sauka daga kan
tsuntsun take tsuntsun ya fadi kasa yiff tamkar an jefar da giwa ko shurawa baiyi ba. Yayin da
tsuntsayen sukaga abinda ya faru ga dan uwansu sai gaba dayansu suka tsaya cak da yakin
kawai sai suka bude fuka fukansu suka luluka sararin samaniya suna masu daukar gawar dan
uwansu da sarki Siyamul ansar ya kashe koda bacewar tsuntsayen sai akaga sarki Siyamul
ansar ya sulale kasa sumamme cikin tsananin kaduwa boka Zulwal ya ruga inda yake ya umarci
dakaru su dauko shi aka shigar dashi cikin gidan sarauta bisa wani kasaitaccen keken doki
lokacin da masu magani suka dukufa akan sarki Siyamul ansar domin ceto rayuwarsa sai da
aka shafe tsawon sa'a biyu ba tareda anga yayi wani kwakkwaran motsi ba al amarin da yayi
matukar dugunzuma hankalin masu maganin da boka Zulwal kenan kuma hankalinsu yayi
mummunan tashi babu abinda yafi dugunzuma hankalinsu sai bisa ganin yanda raunin ciwon
sarki Siyamul ansar din ke zubar da jini da ruwa mai doyin gaske kamar kurji yana zubar da
mugunya duk kuwa da kasancewar masu maganin sunyi iyakar kokarinsu wajen bawa ciwon
kariya da wadansu magunguna. A bangaren Nuzura kuwa lokacin da su yarima Nazmar suka
farka daga baccinsu sukayi arba da mahaifiyarsu tana kaikomo acikin turakar hawaye na zuba
daga idanunta sai suka rugo izuwa gareta suka fada kirjinta cikin matukar damuwa suka hada
baki sukace ya ummanmu shin ina dalilin zubar da wannan hawayen naki koda jin wannan
tambaya sai Nuzura ta kara kankame su ajikinta ta fashe da kuka a karo na biyu koda ganin
hakan su Yarima Nazmar suka fashe da kukan sai da suka dauki tsawon lokaci suna cikin
wannan hali sannan Nuzura ta janya jikinta daga nasu ta dube su cikin tsananin damuwa tace
yaku 'ya'ya na kuyi sani cewa ba komai ne ya sanya ni zubar da hawaye ba sai bisa takaicin
mugun halin da kuka jefa jama'ar wannan kasa da mahaifinku aciki kunsan cewa ba wannan ne

karo na farko ba da hakan ya taba faruwa koda jin haka sai hawayen bakin ciki suka zubowa
Nazmar da Hulaisa dukkaninsu suka budi baki sukace ki gafarce mu ya ummanmu tabbas mun
aikata babban kuskure kuma munyi nadamar abinda muka aikata kafin su gama rufe bakinsu
Nuzura ta tari numfashinsu tace wai shin ma in tambaye ku wane laifi kuka aikatawo wadannan
tsuntsaye ina son ku sanar dani idan kuka boye mini gaskiya zan gudu in barku in tafi wata
nahiya in cigaba da rayuwa har ajali ya riske ni. Yayin da su Yarima Nazmar sukaji abinda
mahaifiyarsu tace sai idanunsu suka zazzaro suka shiga damuwa fiye da ko yaushe alamun
rashin gaskiya karara ya baiyana a fuskarsu har Nazmar ya bude baki da nufin yace wani abu
sai aka jiwo ihu da kururuwar sarki ta cika gaba daya gidan sarautar al amarin da ya sanya
gidan sarautar ya hargtse da guje guje da iface ifacen jama'a Nuzura da su Yarima suka fice
daga cikin turakar da sauri suka rugo izuwa turakar sarki cikin tsananin tashin hankali koda
isowarsu izuwa turakar sai sukayi arba da sarki Siyamul ansar akwance cikin mawuyacin hali
raunin cinyarsa na zubar da wannan ruwa mai doyin gaske koda shigowar su Yarima Nazmar
sai kawai akaga sarki Siyamul ansar ya mike tsaye zumbur ya ruga inda suke ya rungumesu a
kirjinsa al amarin da yayi matukar bawa masu magani mamaki kenan bisa ganin irin mugun
raunin dake cinyarsa amma har ya iya taka kafarsa ba tare da an bawo masu maganin umarni
ba suka fice daga turakar boka Zulwal yabi bayansu ya zamana saura su Yarima Nazmar da
sarki Siyamul ansar kadai koda ficewarsu sai sarki Siyamul ansar ya kama hannun su Yarima
Nazmar ya jasu har inda gadon sarautarsa yake ya zaunar dasu suka fuskanci juna sannan ya
juya ya dubi uwargidansa Nuzura yana mai kura mata idanu yace ya abar kaunata bazakiyi farin
ciki ba da 'ya'yanmu suka kasance cikin farin ciki da koshin lafiya. Koda jin wannan tambaya sai
Nuzura taje ta zauna a bisa lumtsattsiyar kujera da take fuskantar su sarki Siyamul ansar ta
dubesu cikin nutsuwa tace ya uban 'ya'yana kayi sani cewa ba komai ne ya sanya ni cikin halin
rashin walwalaba sai bisa tsoro abinda su Yarima Nazmar suka janyo mana yanzu gashi sunyi
sanadin yi maka mummunan rauni mutane da yawa sun rasa dukiyoyinsu da rayukansu ya
zama wajibi ka tursasa su Yarima su sanar dakai laifin da suka aikatawa wadannan tsuntsaye
sannan kuma a gano shin wanne irin tsuntsayene da matakin da ya kamata a dauka koda jin
wadannan tambayoyi sai idanun sarki Siyamul ansar suka ciko da kwalla sannan ya budi baki
cikin karfin hali yace tabbas maganarki gaskiyace ya uwargidana amma ki sani cewa matukar
su Yarima na cikin koshin lafiya bana nadama don na rasa wata gaɓa ajikina har kullum
tunanina shine wacce hanya zan bi domin ganin su yarima sun gajeni to amma idan su Yarima
suka cigaba da janyo masifu a wannan birni hakan zai janyo rushewar birni gaba daya a doron
kasa a kundin tarihin duniya Nuzura ce tayi wannan furuci ga sarki Siyamul ansar cikin tsananin
damuwa shiru ne ya mamaye turakar na tsawon lokaci shigowar boka Zulwal itace ta kade
shirun da ya wanzu a tsakaninsu boka Zulwal ya zube kasa ya kwashi gaisuwa sannan ya dago
da kansa cikin kakkausar murya yace ya shugabana kayi sani cewa bayan na fice daga wannan
turaka na gudanar da bincike bisa halarar tsafi nan take na gano wani mummunar al amari cikin
firgici sarki Siyamul ansar yace me ya faru ya dodon bokaye boka Zulwal ya hada fuska yace ya
shugabana kayi sani cewa ba komai ne al amarin da nagani ba sai gameda wadannan
tsuntsaye sude wadannan tsuntsaye sun kasance mallakin wani hatsabibin boka da ake yiwa
lakabi da suna JABARUL SIHIR bokayen duniya sunyi ittifakin a wannan karshen qarni babu
wata halitta mai tsananin zafin nama gamida karfin damtse tamkar wadannan tsuntsaye babban
burin boka Jabarul sihir shine ya tsafance wani sihirtaccen kwai wanda daya daga cikin

tsuntsayen ta haifa wanda da zarar kwan ya kyankyashe kansa zaiyiwa duniyar juyin mulki da
wannan tsuntsaye bincike ya kara tabbatar mini da cewa maganin da zai warkar da su Yarima
Nazmar yana cikin gidan Jabarul sihir wato ma'ul diya'u lallai ya zama wajibi a tura Yarima
Nazmar su maidawa tsuntsayen abinda suka dauko musu domin ina mai tabbatar maka da
cewa tsuntsayen zasu dawo wannan birni namu nan da wadansu kwanaki kasani cewa babu
wata halitta da zata tsira daga cikin jama'arka matukar suka dawo. Koda jin wannan jawabi
daga bakin Zulwal sai hankalin sarki Siyamul ansar ya dugunzuma ainun ya tashi ya dubi boka
Zulwal yace shin kanada tabbacin cewa zamu iya zuwa gidan boka Jabarul sihir har mu debo
ruwan ma'ul diya'u? wadanda zai warkarda su Yarima su daina rashin jin da sukeyi? boka
Zulwal yace akwai wani jarumi mai suna HUZAIFAL BN MASNUR ma abocin addinin musulunci
lallai kashe gari ya kamata mu gudanar da tafiya domin mu ziyarce shi domin ya amince da
bukatarmu da wannan nakeyi maka bankwana na barka lafiya ya shugabana koda boka Zulwal
ya gama wannan jawabi sai ya shafi kasa da hannunsa na hagu ya bace bat tamkar bai taba
wanzuwa ba a wajen take sarki Siyamul ansar da Nuzura suka cika da farin ciki mara
misaltuwa.


****


BABI NA UKU

Kamar yanda boka Zulwal ya fada haka al amarin ya kasance wato tun da dukun dukun safiya
sarki Siyamul ansar da su yarima Yarima Nazmar sukayi shiri bayan sun rabu da mahaifiyarsu
suna masu zubar da hawayen rabuwa
da juna suka dauki hanyar tafiya tare da dakaru masu yi musu rakiya mutum dubu biyu tafiyar
sa'a uku sukayi suka iso wani daji mai tattareda kayan ni'ima nau'i nau'i daban
daban koramai na gudana acikinsa atsakiyar dajin akwai wani dan madaidaicin gida shi dai
wannan gida da zallan duwatsun wuta masu kwarin gaske da isowarsu bakin kofar gidan
sai sarki Siyamul ansar ya sauka daga kan dokinsa yaje ya kwankwasa kofar gidan wanda ta
kasance mai tsananin tsawo da kaurin gaske saida ya kwankwasa sau uku
ba tare da yaji motsin alamun za a bude taba koda ganin haka sai su yarima da boka Zulwal
suka sauko daga kan dawakansu suka
tako har izuwa kofar gidan suna masu yin cirko cirko domin suga an bude kofar tsawon dakika
dari biyu shiru ba aji sautin bude kofar ba al amarin da yayi matukar dugunzuma
hankalin sarki Siyamul ansar ya dubi boka Zulwal yace ya sarkin bokaye shin yanzu me nene
abinyi? har boka Zulwal ya budi
baki da nufin yace wani abu sai kawai aka hango wani kyakkyawan saurayi mai cikar kamala
da annurin fuska ya tunkaro
kofar gidan kallo daya zakayiwa saurayin ka fahimci ya kasance gwarzon mayaki mai karfi na
Allah ya isa saurayin yana sanye da
kayan fata riga da wando takalmin dake kafarsa anyi shine da patar damisa akafadarsa yana
dauke da wata qatuwar zakanya.

Koda isowarsa inda su sarki Siyamul ansar ke tsaye sai ya bisu da kallo cike da mamaki ba tare
da yace da dayansu uffan ba yasa hannu daya ya tura gofar gidan ta bude ya kunna
kai izuwa ciki yayin da sarki Siyamul ansar da tawagarsa sukayi arba da qatuwar zakanyar dake
dauke akafadar saurayin kuma sukaga yadda ya bude kofar gidan da hannu
daya wanda sai karti majiya karfi mutum ashirin sun taru sannan zasu iya bude kofar sai suka
cika da tsananin mamaki domin basu taba gani ko jin jarumin da yayi wannan jarumtaka ba
suna nan atsaye a kofar gidan sai
sukaga saurayin ya fito daga cikin gidan ya tako da kafafunsa har izuwa inda suke ya dubesu
cikin nutsuwa yace aminci ya
tabbata agareku yaku wadannan baki shin menene ke tafe daku izuwa gareni koda jin wannan
tambaya sai sarki Siyamul ansar yayi
gyaran murya yace yakai jarumi Huzaifal bin masnur kayi sani cewa ba komai
ne ke tafe dani izuwa gareka ba face wata muhimmiyar bukata bukatar kuwa itace inaso kayi
mana jagora izuwa
gidan boka Jabarul sihir domin nemowa wadannan 'ya'yan nawa maganin da zai warkadda su
larurar dake damunsu ta rashin
jin magana kuma har su mayar da abinda suka daukowa wadansu tsuntsaye
wadansu tsutsaye inason ka fadi dukkan abinda kake bukata da ya danganci dukiya da mulki ni
kuwa zan baka shi. Koda jin wannan
jawabi daga bakin sarki Siyamul ansar sai.jarumi huzaifal yayi shiru yana mai sunkui da kansa
kas ya shiga dogon nazari daga
can sai ya dago kai ya dubi su Yarima Nazmar gimbiya Hulaisa sannan ya dubi sarki Siyamul
ansar yace yakai wannan sarki mai daraja kayi sani cewa fiye da shekaru goma ubangijina ya
baiyana mini cewa zakazo gareni da wata bukata
na amince zanyi maka wannan aiki amma sai dai bisa sharadi guda daya jal wanda sai ka
08137237071amince dashi zanyi wannan gagarumar tafiya
da jin haka sai sarki Siyamul ansar yace fadi sharadinka ya jarumin kwarai Huzaifal yayi gyaran
murya a karo
na biyu sannan yace sharadina shine bayan na samu nasarar debo ruwan ma'ul diya'u wanda
shine zai warkar da su
Yarima zaka yarda kayi imani da ubangiji kai da jama'arka baki daya idan ka daukar mini
wannan alkawari
shikenan ka biyani dukkanin aikina ba tare da ka bani dinare da ko wani yanki na masarautarka
ba koda jin wannan
batu sai sarki Siyamul ansar yayi shiru duk tattaunawar da akeyi tsakanin Jarumi Huzaifal da
sarki Siyamul
ansar boka Zulwal da su Yarima Nazmar suna sauraro koda Boka Zulwal yaji sharadin da
jarumi Huzaifal ya gindayawo
sarki sai hankalinsa ya dugunzuma ainun domin ya tabbatar idan sarki Siyamul ansar yayi
imani cewa zai karbi addinin
musulunci duk shirinsa zai tarwatse na son mallakar birnin SARIRUL AIWAN da ya dade yana
muradi yana cikin wannan hali ne wani tunani ya fado masa tunanin kuwa shine
tunda sarki Siyamul ansar umarninsa yakebi bana jarumi Huzaifal ba lallai akwai tabbacin

burinsa zai iya cika sa'adda yazo nan a tunaninsa sai ya cika da farin ciki a ransa sarki
Siyamul ansar ya kada shirun da ya wanzu a tsakaninsu ta hanyar bude baki yace yakai jarumi
Huzaifal hakika na amince da wannan sharadin naka matukar 'ya'yana zasu
daidaita yanda nake bukata amma kuma wani hanzari ba guduba menene batu a gameda
cewa su yarima sune zasu zamo ajalina da jin wannan tambaya sai murmushi ya subucewa
jarumi Hullzaifal har fararan
hakoransa suka baiyana farare qal ya dubi sarki Siyamul ansar cikin annurin fuska yace kada
ka damu ya shugabana kasani cewa matukar kana tare dani kuma kayi imani da ubangijin
musulunci mahaliccin sammai
da kassai da abin dake cikinsu babu yanda za ayi 'ya'yanka su zamo ajalinka yanzu dai abinda
za ayi shine ku biyoni izuwa
cikin gidana kudan shakata kafin abinda ya kamata ayi tunda na lura cewa kun gaji ainun kuma
a tsarin addininmu ubangiji ya
umarce mu da mu girmama ma'abota mulki matukar basu hana mu bauta masa ba. Koda gama
fadin haka sai jarumi Huzaifal ya juya ya shige gaba yana mai.kunna kai izuwa
cikin gidan yana mai yafito su sarki Siyamul ansar na hannunsa ba tare da bata lokaci ba sarki
Siyamul ansar Yarima Nazmar gimbiya Hulaisa boka Zulwal ne a karshe suka suka biyo
bayan Huzaifal yayi musu jagora har izuwa cikin gidan da shigarsu izuwa cikin gidan sai suka
cika da tsananin mamaki abinda
ya basu mamaki shine yadda aka tsara gidan bisa tsari da kayatarwa gidan yana dauke da
manyan dakuna guda uku masu girma da fadi suna da kofa ɗai ɗai da tagogi guda
biyu a wani daki ne dake kallon yamma cikin gidan jarumi Huzaifal ya sauki su sarki Siyamul
ansar aciki dakin cike yake da kayatattun
kujeru kuma an shimfide kasansa da kilisai masu taushi wani daddadan kamshi ya mamaye
turakar bayan jarumi Huzaifal ya sauke
su acikin turakar sai ya fice daga cikin dakin jim kadan sai gashi ya dawo dauke
da wani dogon paranti cike da nau'in kayan marmari da gasasshen naman zakanya
gamida tatacciyar madarar shanu ya ajiye agaban su sarki Siyamul ansar a bisa wani dan
madaidaicin tebur na katako a tsakiyar turakar yana ajiye abincin ya dubesu yace ai sai ku
dan kimtsa cikinku ko yana gama fadin hakan ya fice daga dakin sarki Siyamul ansar da boka
Zulwal suka bishi da kallo cike da matukar mamaki tayaya akayi har ya sarrafa
naman zakanyar da ya farauto acikin kankanin lokaci haka kuma a inama ya samu wannan
tatacciyaro madarar shanun al halin babu wata dabba dake rayuwa acikin dajin saida suka
kammala kimtsa cikinsu suka
huta sannan aka dunguma gaba daya suka fice daga gidan har jarumi Huzaifal suna ficewa ya
mayarda kofar gidan ya rufe ta ruf kawai sai suka ga ya kusanci wani
bangare adajin mai tattare da sarkakiya sai gashi ya janyo wani ingarman doki fari sol mai
kyawun launi bayan ya hau dokin ne
kowa ya hau abin hawarsa sai aka nausa cikin daji aka fara tafiya dakaru masu rakiya na biye
dasu ana fara wannan tafiya ne
jarumi Huzaifal yaki yarda ya jera da kowa face Yarima Nazmar da gimbiya Hulaisa yana mai
satar kallonsu fuskarsa
cikeda annuri ana cikin hakan ne Yarima Nazmar ya dube shi yace yakai wannan jarumi a dazu

da kuna magana da abbana
naji kace akwai wani ubangiji da kake bautawa wanda ya halicci sama da kasa bayan abin
bautarmu. Koda jin
wannan tambaya sai Huzaifal yayi murmushi ya dubi Yarima Nazmar yace tabbas akwai
ubangijin da ya halicci duniya da
abinda yake cikinta kuma yake aiwatar da duk abinda yaso da ace zaku gwada neman
taimakon ubangijin nawa

1
2
3

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login