Showing 1 words to 3000 words out of 8503 words
Chapter 1 - KOGON ANNOBA True Books Available Complete Na Mansur Usman Sufi Sarkin Marubutan Yaki .pdf
KOGON ANNOBA
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi
Littafinyaki.com.ng
08137237071
©️ Haƙƙin Mallaka
Mansur Usman Sufi
Shekarar bugu:- 2024
Website:- littafinyaki.com.ng
GARGAƊI
Ban yarda wani ya sarrafa min littafi ba ta hanyar yaɗa shi a soshiyal midiya, karantawa a
rediyo ko manhajar YouTube, website da sauran su ba tare da izina na ba, yin hakan zai kai mu
zuwa ga hukuma a kiyaye.
Ko kuwa zuwa ga babban mai sakamako Allah (SWT).
Sako daga
MANSUR USMAN SUFI
GODIYA
Ta tabbata ga Allah SWT bisa iko da ya ba ni na rubuta wannan littafi mai taken KOGON
ANNOBA.
Tsira da amincin Allah ya ƙara tabbata ga Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi
Wasallama da iyalanshi tsarkaka.
SADAUKARWA
Na sadaukar da wannan littafi ga dukkanin masoyan Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi
Wasallama a ko ina suke a faɗin duniya.
Bugawa da yaɗawa SUFI PUBLISHING COMPANY
R/lemo Kano state Nigeria.
08137237071
BABI NA ƊAYA
Ƙananan yara ne mace da namiji kyawawa na gaban kwatance ke ta faman tsala
matsanancin gudu babu sassauci, saboda matuƙar gudun da suke yi idan ka gani sai ka yi
tsammanin za su fita daga duniyar ne.
kai duk sa'adda suka waiga bayan su idan suka yi arba da abin da yake biye da su, sai kaga
sun ƙara ZAGE DAMTSE ƙarfin gudun su ya ƙaru ainun fiye da ɗazu.
Babu abin da zai bawa
mutum mamaki face idan ya ga yadda suke gudun sai ya rantse ya ce ba su kasance bil'adama
ba, kallo daya zakayi masu ka fahimci cewa sun kasance 'ya'yan wani hamshaƙin attajiri ko
BASARAKE, saboda tufafin da suke sanye da su masu tsadar gaske ne.
Haka dai suka cigaba da gudu domin tsira da rayukansu daga sharrin abubuwan da
suka biyo su babu alamun tsoro ko firgici a tattare da fusakunsu, har suka iso wani ƙasaitaccen
birni
ai kuwa sai suka kunna kai ta cikin wata yar mitsitsiyar taga ba tare sa sun jira masu gadin ƙofa
sun buɗe masu ba.
Lokacin da abubuwan suka biyo yaran suka
sauka a birnin nanfa jama'a suka dinga guje-gujen gami da iface-iface kafin ka ce me gari ya
kaure da ihun jama'a mutane suka dinga rugawa izuwa gidajensu suna ɗebo
makaman yaƙ.
A wannan lokacin sarkin dake mulki a birnin yana zaune akan karagarshi ta mulki fadar
ta ƙawatu ainun da nau'ikan kayan ƙawa da alatu nau'i daban-dabam dangin zinare da azurfa
har da ma abin da ido bai taɓa gani ba. Duk inda ka duba a fadar kawunan jama'ane rututu
tamkar dandazon kiyasai babu masaka tsinke.
A gefe guda kuwa sarki SIYAMUL-AMSAR na zaune akan ƙasaitaccen karagar mulki
yana sanye da doguwar alƙyabba akan shi yana ɗauke da KAMBUN MULKI da aka sana'anta
shi da zallar zinare da lu'u lu'u.
Sarki SIYAMUL-AMSAR ya kasance dogon mutum mai ƙirar samudawan farko yana da
kyakkyawar fuska da ɗan siririn gemu mai tsawon kamu biyu wanda shine ya ƙara tona asirin
kyawun surarshi.
kallo ɗaya za ka yi mashi ka fahimci cewa ya kasance GWARZON JARUMI. 'Yan majalisar sarki
na zaune a bisa shimfiɗu na alfarma waɗanda
idan mutum ya taka su saboda matuƙar taushin su sai ya ji tamkar ƙafafuwanshi za su nutse a
ciki a wannan lokaci babu abinda kunne ke ji face guje-gujen jama'a da kuma shirun da ya
wanzu a fadar tamkar mutuwa ta gifta, daga can ga dakaru masu tsaron ƙofa sun shigo fadar
hankulansu a tashe. Koda ganin halin da suke ciki sai sarki ya dube su ya ce ''shin me ke faruwa ne ?
Cikin rawar murya ɗaya daga cikin dakarun ya buɗi baki daƙyar ya ce ''ya shugabana muna
cikin gudanar da ayyukanmu na tsaron ƙofa sai ga su yarima NAZMAR sun janyo mana wata
gagarumar masifa, ban tsammanin cewa akwai wata halitta da ta tsira da rayuwarta, mu kanmu
tsananin razana ya hana mu mu tantance wace irin masiba ce''. Kafin badakaren ya gama rufe bakinshi sarki SIYAMUL-AMSAR ya zare sharɓeɓiyar
takobi a gadon bayanshi ya sare mashi wuya, nan take kanshi ya yi fitar burgu daga gangar jiki
jini ya yi tsartuwa ya kwaranya a ƙas.
kawai sai sarki SIYAMUL-AMSAR ya taƙarƙare ya kwarara uban ihu wanda ya firgita
gaba ɗaya jama'ar dake fadar kuma ya amsa kuwwa izuwa cikin birnin, sai daga bisani ya
murtuke fuska tamkar an aiko mashi da saƙon mutuwa. Nan take ya yi umarni aka busa ƙahon
yaƙi kafin wani lokaci MAYAƘA sun yi cincirindo a Ƙofar gidan sarauta. Shi kuwa sarki sai ya
shiga izuwa gidan sarauta jim kaɗan sai gashi ya fito cikin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar
kwarjini da ban tsoro.
Jim kaɗan da faruwar hakan sai ga boka ZULWAL ya bayyana cikin alƙalumman sihiri,
sanye yake cikin shigar yaƙi irin ta manyan hatsabibai.
Kawai sai ya faɗi ƙasa ya kwashi gaisuwa sarki
ya dube shi cikin matuƙar fushi
yana mai dakamashi tsawa ya ce ''shin kana ina ne masuba ta tunkaro birnina? Ina so ka
gaggauta nemo mana mafita domin tserar da rayukan al'ummata".
Cikin ladabi boka zirwal ya ce ''ya shugabana ka yi sani cewa mafita ɗaya ce, shine mu
fita mu tari wannan masuba tun kafin ta iso gare mu ina mai tabbatar maka da cewa zamu
samu nasara''.
Gama faɗin hakan ke da wuya
sarki ya kaɗa linzamin dokinshi ya shige gaba boka Zirwal ya mara masai baya, take miliyoyin
dakarun yaƙi suka yi koyi dashi
Babi na biyu
Sarki Siyamul-amsar ibn Fannas ya kasance mashahurin BASARAKE kuma
GAWURTACCEN attajiri da babu tamkar a kaf nahiyar Baitul-Wahid.
Yana da matar aure guda ɗaya hal! Wata kyakkyawar gaske mai suna NUZRA BINTU
SHA'ARAN.
A rayuwar Siyamul-amsar babu wani rayuwar jin daɗi da ya nema ya rasa face rashin haihuwa,
duk da irin tarin dukiya da ƙarfin mulki da yake da shi ya tashi a banza domin ba shi da wanda
zai gaji karagarshi.
Aƙalla ya ziyarci manyan bokaye sama da ɗari akan wannan matsala ta rashin haihuwa amma
abu ya ci tira, a wata shekara ne ya ziyarci wani boka a can birnin ƘUFA mai suna Zirwal.
Lokacin da sarki Siyamul-amsar ya bijirowa da boka zirwal da buƙatar shi ta samun
haihuwa, sai kawai boka Zirwal ya bushe da dariyar mugunta har sai da ya faɗo ƙasa tim! Daga
kan kujerar da yake zaune kuma idanunshi suka ciko da ƙwalla.
Al'amarin da ya ɗaurewa sarki Siyamul-amsar kai kenan kuma ya fusata shi ya dakawa
masjid tsawa ya ce da shi ''shin ina dalilin wannan dariya taka? Cikin nutsuwa da biyayya boka
Zirwal ya koma kan kujerarshi ya zauna ya yi gyaran murya, sannan ya fara magana a karo na
farko da shaƙaƙƙiyar muryarshi mai kama da kukan jaki yana mai cewa asi ya huci zuciyarka ya
sarkin sarakunan masu isa kayi sani cewa ba komaine
ya sanya ni wannan dariya ba face bisa ganin yadda ka wahalar da kanka wajen faɗin bukatar
da take tafe da kai, bayan cewa ka zo gaban uban bokaye, ya sarki mai cikakken iko ka yi sani
cewa tabbas a halin yanzu matarka
na ɗauke da juna biyu nan bada daɗewa ba zata haihu, kuma ina mai farin cikin sanar da kai
cewa 'ya'ya biyu zata haifa mace da namiji sai dai inda gizo ke saƙar shine 'ya'yan da za a haifa
maka za su kasance hatsabibai marasa jin magana waɗanda sune zasu zamo ajalinka.
Yayin da boka Zirwal yazo nan a jawabin shi sai hankalin sarki siyamul-amsar ya
dugunzuma fiye da kowane lokaci ya dubi boka Zirwall ya ce ''ya sarkin bokaye shin babu wata
hanya da za abi 'ya'yan da zan haifa ya zamto ba su kasance hatsabibaiba?
Zirwal ya nisa ya ce sannan ya ce ''ai bakin alƙalami ya bushe lallai wannan al'amari
haka zai kasance''.
koda jn wannan batun sai sarki Siyamul-amsar ya sunkuiyar da kanshi ƙasa yana mai
zurfafa cikin kogon tunani.
Abu na farko daya faɗo mashi a rai shine yanzu babu wata mafita face kayi murna da
waɗannan yara da za a haifa maka domin sune zasu gaje ka bayan ranka tabbas ba ka da
nadama koda sun zamo ajalinka ai da a ce wani ne zai gaji karagarka gwara a ce jininka ne.
Can kuma wata zuciyar ta ce ka cigaba da bincike ya za ayi a ce 'ya'yan mutum sune zamto
ajalinshi. Lokacin da sarki yazo nan a tunaninshi sai ya ɗago da kanshi ya dubi boka
zirwal ya ce ''tabbas na amince 'ya'yana su zamo ajalina matuƙar za su gajeni bayan raina''.
Gama faɗin hakan keda wuya sai sarki ya ɗebi dukiya mai tarin yawa ya bawa boka
Zirwal, saboda tsananin murna sai da Zirwal ya dinga birgima a ƙasa tamkar
wanda ya samu ciwon hauka, domin tunda yake a rayuwarshi bai taɓa samun dukiya mai
yawan ta ba kuma dama yana da wani babban buri akan adukiyar yana son ya haɗa
wansanadarin tsafi da ita.
Tun daga wannan rana
sarki Siyamul-amsar ya kasance cikin tsananin farin ciki kuma ya zamana cewa dare da rana
baya rabuwa da uwargidanshu Nuzra yana bata gudunmowa wajen rainon juna biyunta har ta
sauka lafiya
ta haifi 'ya'ya biyu kyawawa mace da namiji aka raɗa msu suna NAZMAR da HULAISA.
Murna a wajen sarki kuwa ba a cewa komai domin a wannan rana ya dinga rabon dukiya
da 'yanta bayi da barori sannan sai da aka yi kwanaki ashirin ana shirya walimar farin ciki,
manyan sarakunan duniya sun sauka a birnin domin taya shi murna. Hakan ya sanya a lokaci
ko ƙasa mutum ya kasa sai an siya saboda kawai ana farin ciki kuma ya zamana sarki ba shi da wani abokin shawara face boka Zirlwal.
Tabbas masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce sannu-sannu bata hana zuwa sai dai
a daɗe ba a je ba, sai gashi kwance tashi yarima Nazmar da gimbiya Hulaisa sun shekara uku a
duniya kasancewar yanayin jikinsu irin na mahaifinsu ne sai ya zamana idan ka gan su lokacin
da suka shekara uku sai ka ce sun shekara biyar da haihuwa. Tun suna waɗannan shekaru suke nuna hatsabibancinsu domin basa iya zama waje guda ko an
kulle su a daki sai sunyi dabaru sun fita, a wasu lokutan idan suka rasa hanyar da za su bi su
fice daga gidan sarautar sai su haɗa rigima tsakanin dakarun dake tsaron su sannan su sulale
su fice daga gidan sarautar, Domin akwai wani lokaci da suka je
suka tsokano wata qatuwar damisa ta biyosu har cikin gari ta dinga hallaka mutane sai dakyar
da sidin goshi aka samu akayi maganin damisar kai in takaice maka
kafin Nazmar da Hulaisa su shekara shida sun janyowa birnin masifu guda talatin
kuma duk
lokacin da hakan ya faru sai an samu salwantar rayuka da dukiyoyin al'umma
wani abu da zai baka mamaki shine tunda aka haifi su yarima Nazmar
arzikin kasar ya kara bunkasa amma sai dai mutane basu da kwanciyar hankali domin har
kullum gani sukeyi su Yarima nazmar zasu janyo masifar
da zata zamo ajalinsu ko asarar dukyarsu duk irin dakarun da sarki Siyamul ansar zai sanya
domin tsaron su Yarima amma
cikin hikima da basira sai Yarima nazmar sun samu nasarar gudowa shi kasansa sarki duk
lokacin da ya tuna cewa su
Yarima nazmar ne ajalinsa sai takaici ya turnuke shi har ya zubar da hawaye duk cikin mutanen
birnin walau yan majalisa
babu wanda ya iya kawowa sarki korafi su Yarima nazmar saboda ganin irin soyayyar da akeyi
musu kuma babu wanda yake kaunar su domin ta sanadin su attajirai sun zamo talakawa
wadansu sun zamo marayu.
Duk lokacin da sarki ya samu labarin su Yarima nazman sun janyo wata masifa sai ya kara
sanya matakan tsaro aturakarsa domin hanasu fita daga gidan sarautar.
Lokacin da sarki Siyamul ansar da dakarun yakin suka fita daga kofar gari sai sukayi arba da
wadansu irin jibga jibgan tsuntsaye
sude wadannan tsuntsaye sun kasance suna da jiki irin na zaki amma kawunansu sun kasance
na rakumin dawa suna dauke da kafafuwa guda shida akalla girman
kowannensu yakai na qatuwar giwa fuka fukansu manya manya ne masu dauke da wadansu
irin gashi mai kama da takobi
awajen kaifi da tsini hakika ba karamin jarumi bane zaiyi arba wadannan tsutsaye face sai ya
razana ainun yayi nadamar wamzuwarsa agaban kasa koda tsuntsayen
su kimanin dubu sukayi arba da su sarki Siyamul ansar sai suka saki fukafukansu suka sauka
aturba lokacin da dakarun sarki Siyamul ansar sukayi arba da wadannan tsuntsaye
sai suka razana ainun da yawa daga cikinsu basu san sa adda suka saki fitsari a wandonsu ba
kuma suka yunkura zasu koma da baya sai sarki Siyamul ansar ya daka musu tsawa
suka tsaya cak jikinsu na tsuma gaminda karkarwa shi kansa sarki Siyamul ansar sai da yaji
tsoro da razana sun darsu
a zuciyarsa domin a iya tsawon rayuwarsa bai taba gani ko jin labarin tsuntsaye masu tsananin
girma da ban tsoro
kamarsu ba nanfa dawakai suka dinga haniniya suna zubar da mahayansu suna nausawa cikin
daji saboda tsananin dimauta
su Yarima Nazmar kuwa lokacin da wadannan tsuntsaye suka biyo suka shiga birnin suka wuce
kai tsaye izuwa turakarsu suka fara sharar bacci abinsu kai kace
babu wani abu da ya faru agaresu al amarin da ya bawo kuyangi da barorin gidan sarautar
mamaki kenan har wadansu
suka raya zuciyarsu cewa anya kuwa su Yarima nazmar mutanene ba aljanu ba?
ita kuwa mahaifiyarsu sai hankalinta ya dugunzuma ta kasa tsaye ta kasa zaune
kawai sai ta dinga kai komo cikin turakar hawaye na zuba daga idanunta.
Lokacin da aka fara kallon kallo tsakanin su sarki Siyamul ansar da wadannan jibga jibgan
tsuntsaye sai ya zamana babu wanda yayi yunkurin afkawo abokin gabarsa
awannan lokaci gaba daya mayakan dake wajen hankalinsu atashe yake shi kansa sarki
Siyamul ansar hankalinsa atashe yake fiye da kowa yayi karfin hali ne na irin masu manyan
sarakuna koda sarki Siyamul ansar yaga tsuntsayen sunki yunkurin afka musu sai ya umarci
wasu dakaru dari biyar da su dana bakarsu su harbawa tsuntsayen take dakarun sukabi
umarnin suka dana bakarsu suka harbawo tsuntsayen yayin da kibiyoyi guda dari biyar suka
sauka akan tsuntsayen sai akaga tsuntsayen sun tsaya cak ko gezau basuyi ba hasalima idan
kibiyoyin suka sauka akansu sai dai tartsatsin wuta ya tashi kibiyoyin su zube kasa saida
dakarun suka karar da kibiyoyinsu sannan tsuntsayen sukayi wani irin kuka mai firgita manyan
jaruman duniya suka afka musu da yaki take tsuntsayen suka yanyame miliyoyin dakarun
kamar yanda dandazon kudaje ke yanyame kwallon mangwaro duk inda ka duba sune birjik
babu abinda suke face hurowa dakarun wata dunkulalliyar wuta abakinsu ko su hallakasu da
wadannan tsinin gashin dake fukafukansu masu tsananin kaifi da tsini. Cikin kankanin lokaci
waje ya cikada ihun mazaje gamida karar karafkiya karafe gamida haniniyar dawakai mutuwar
sadaukai ta cigaba da yawaita awajen nanfa aka kacame da azababben yayi tsakanin kowane
bangare har yazama an shafe tsawon rabin sa'a su sarki Siyamul ansar basu samu nasarar
kashe ko daya daga cikin tsuntsayen ba sai dai kaga tsuntsu ya wangame bakinsa ya hurawo
badakare wuta sai dai kaga nan take badakare da dokinsa sun kama da wuta sassan jikin
dakarun ya dinga shawagi a sararin samaniya kura ta turnuke kamar hadari ya gangamo akece
da ruwan sama mala'ikan mutuwa ya wanzu yana shawagi asama dawakai suka dinga haniniya
suna zubar da mahayansu kai duk inda daya daga cikin tsuntsayen ya sanya gaba sai dai kaga
dakaru suna zubewa kasa