Showing 12001 words to 14484 words out of 14484 words

Chapter 5 - KWARTON MANYA PART 1 COMPLETE by Maman Teddy .pdf

04 Nov 2025

613

Habab Shigowa mkrtn.

Sadeeq ne ya kwashe da dariya yana cewa " Sobreen kalli gaban ki kedai . Ke ɗan kalli gaban
ki". Habab yayi maganan cike da tsare gida ,wanda yasa Sobreen kallo n gaban ta tana juyawa
ranta a mache".
"Shamsiyya". Taji Muryar sa ya kira Shamsiyya ,wanda cikin sauri ta amsa tana cewa " Yes my
luv Habab". Ke meye Ruwa??? . Mamaki ne ya kama Sobreen tana kallon shi wai ruwan ma ya
manta ne ko iskanci ne ,sai dai kuma tasan baya wasa shi.idan yayi mgn to hakan take". Dariya
ta kwashe dashi tana dawowa daga tunanin da ta fara lulawa. Miƙewa Sobreen tayi a hankali
tana takawa haɗi da nufan coridour ɗin da Habab yake". Tana tafe tana ƙara tunanin lokacin da
malami na aji shi yana saman benen mkrntn yana bin sojojin barikin da kallo , shida abokanan

shi. Idan ko aka ce maka yau xa'a passing Out bala'i ai yana zuwa skul ɗin Saman benen yake
nufa. Tun da take bata taɓa ganin namiji mai taurin zuciya da kafewa irin Habab ba,shi da ya
shiga aikin Soja ba tare da kowa ya sani ba ,sai dai aka nemeshi aka rasa ,gashi ya fara da na
wahala lecrout ,da ya kammala ne mahaifin shi ya nema masa na sama babba". Wanda a
yanzu yake matsayin militry police". Su ba' yarda masu faɗa da Soja ɗaya ba ,sai idan sojoji
sun kai goma zuwa sama". Don idon sukace zasu yi faɗa da soja ko su bashi horo zasu kashe
shi har lahira". Niko Mmn Teddy nace " lallai Zainabu ta ɗebo ruwa ,ko ita da wani horo za'a fara
mata? .

Ji yayi Sobreen ta rungume shi tana manna kanta gyefen fuskar sa tana bin drwing ɗin da
yakeyi da kallo". I luv You Habab". Bai bata amsa ba sai mgna a hankali da yayi yana cewa "
tncuuu". Don a halin da yake ciki baya son damu ko bare mgn".

Idon ta ne ya sauka akan zanen Fuskar Zainabu da ya zanata hak kaman yana ganin ta tsaye
gaban shi,a zuciyar shi yana faɗin zan maki tarbiya zan maki iziyar sai kin nadama a rayuwar ki
...ware idanun ta Sobreen tayi tana kallon fuskar Zainabu ,blck beuty ce ,akasain ita da ta
kasance fara ƙarrr. Bata da wani kyau sai dai akwai Sanyayyar kuma ɓoyayyar kyau a tare da
ita . Bata da dogon hanci ,nata hancin gajerene yana da ɗan faɗi da ya saje da fuskar nata
,tana da kumatu sai ɗan ƙaramin baki don baka tunanin cokali zai iya shiga ba,bata da mnyn
idanu ƴan dai dai matsakaita. Tana da cikar gashin gira da ido ,wanda yaƙara ƙanƙanta mata
idanun nata amaimakon suyo waje". Wacce wannan?". Tayi mgnn tana nufowa gaban shi da
tambayar shi". Wani huci ya furzar yana faɗin Zainab". Itace Wacce zaka Aurar? Ni baka Sona
itace kk so Habab tun da har zanen ta kakeyi?? Sai kuka hawaye ya hau bin ƙumcin ta sharrr³ .
Bai bata amsa ba ya juya yana nufan tsakiyar falon. Da sauri tayo gaban shi tana ƙara buɗe
murya tana cewa " Pls Habab ka Soni nima". Shiiiii....na faɗa maki babu Soyayya a lissafi n
rayuwata ,dake da ita duka bana son ku a zuciyata ,ko wanne da dalilin auren ta da xanyi ,zan
Aure ki kuma itama xan Aure ta. Bana Son kowa ,mutum ɗaya naso A rayuwata Itace " Mom".
Ita naso na yarda da ita ,na buɗawa sirri na tasan damuwa ta ,daga kuma kanta na daina Son
kowa ,itama n daina Son ta da son kasancewa da ita a rayuwa ta. Hawayen fuskar ta Sobreen
ta goge a zuciyar ta tace " bai dame Ni ba,ka tsani kowa nidai ka Soni". Rungume shi tayi tana
kissing ɗin lips ɗin shi haɗi da murmushi tana cewa " Habab zaka Aure Ni?". Yeah". Ya bata
amsa a taƙaice. Juyawa tayi tana manna bayan ta da ƙirjin shi tana ɗaura hannun sa saman
ƙirjin ta tana matsewa haɗi da rungume shi tsam. Wani irin numfashi yaja yana saukewa
sakamakon jin ɗumin breast ɗin ta a hannun shi. A hankali yafara da taffan sa yana shafa su
kamin ya juyo da ita tana fuskar tashi....bakin su suka haɗe wuri ɗaya suna kissing kaman zasu
cinye kansu. Hannun shi na cikin rigar ta yana wasa da nonon ta ,gasunan fa ruguxa² . Dama
haka yake so".

******

Abun da ya faru a gidan malam Auwalu abun tamkar almara". Don Alh Iblo ne yazo neman
Aurar nawa Ɗan nasa Habab Auren Zainabu,shida ƙanin su biyu. Nan Abba yasa akayi kirar
Baba Musa ,anan kuma suke sanar masu da Aƙidar gidan su Zainabu ,ashe indai anzo neman

aure ,aanan take ake tara mutane indai Angon a shirye yake a ɗaura aure....wanda aiko hakan
ya faru nan take aka biya komai na aure. Aka tara mutanen unguwa aka shaida auren Zainabu
da Habab,wacce take can tana tsula iskancin ta sam bata sani ba. Wannan ba sabon abu ne ba
don layin kowa yasan dama haka ake auren gidan Mlm Auwalu. Wannan yasa kowa ke sam
Barka , wasu na farin ciki da Tafiyar da Zainabu xatayi mu tane ma saji saƙattt.

Jin hakan da sanarwar da Alh Iblo yayi na auren Habab da Zainabu yasa Hjy Luba tada ƙura
akan itama a ranan sai an ɗaura na Sobreen ,wanda ba'a ɗaura ba sai a washe gari ,ana ɗaura
wa aka tsaida tarewa da shagalin biki bayan sati biyu masu zuwa inshaallh".

Wannan ya ƙwantar da hankalin Sobreen ,Abba ne yace " Bai yarda Habab ya tare a gidan sa
ba... Anan Estate ɗin gidan nasu ya ware part ɗin da zasu zauna da matan nashi ". Wanda
hakan yayi mawa Hjy Luba daɗi ,tana tunanin izayar da hantarar da zasu yi nawa Zainabu
wanda da ƙafarta zata bar gidan".
*****

Gidan Mlm Auwalu ko ba wanda ya samu Zainabu da mgnn har tsawon sati ɗaya gashi ko a
gari bataji wani magana ba, sai dai idon ta bugu ƴaƴan mutane sai iyayen suce " Saura kwana
nawa ne ?? Sam bata fahimci komai ba. Yau safiyar Laraba ita dai taga yayyun nata sun cika
gida da ƴan uwa na nesa da suka fara zuwa ,ashe wai saura kwana uku tarewan ta kuma ayau
xa'a kawo lefe". Ayau ne kuma malam Auwalu da Umma suka yanke shawar yi mawa Zainabu
mgnn auren da akayi mata".

Tafe take a hanya ta dawo ɗebo mawa umma ruwan fanfo da aka kawo a maƙota. Asabe ta
gani ,wacce tana ganin ta ta kauda kai gyefe". Asabe na ykk??. Tayi magana mgnn cike da
mance wai sun yi wani abu tsakanin su. Kuma dama haka take ƙaidan ta kowa zata kira sai
tace " wane na ko wacce na , haka Zainabu n take. Ai dai mun kusa hutawa sau ra kwana uku
ki tafi kibar mana unguwan mu....aje ruwar hannun ta Zainabu tayi kamin ta kama kwankwaso
tace " in je ina ?? Ai nan da kika ganni indai Ummana na nan unguwar to babu mai bardani ko
aure bazanyi ba saboda Nafison zama da Umma na. Hum'uhm taɓ di aure na nawa? Dama baki
sani ba? To ai an ɗaura auren ki da wani babba...kuma sau ra kwana uku tarewa. Bala'i Asabe
idan ƙarya kika mun wallahi dukan gaaba da xan maki bazan tsaya yi maki cincin ba ,hancin ki
ko idon ki ko haƙorin ki xan cire. Wallahi da gaske . Ai aje botikin Umma tayi da ruwan tana
nufan gidan da gudu". Dai dai su Adda Raliya suna isa tsakar gidan. Tabarma aka shimfiɗa
masu ,nan aka hau shigo da akwatina saiti uku.... Umma!! Ummaa!!! Zainabu ta shigo tana
kwaɗa kirar sunan Umma. Da sauri Nadiya ta kamata tana ɗakin Hansai da ita. Ganin akwati
yasa Zainabu gasgata maganan Asabe. Aiko nan ta hau ihu ,tana faɗin an yau dareta an
cuceta. Wallahi wanda ya Aureta sai yayi nadama. A ranan da aka kaita zai sako ta. Rarrashin
ta Nadiya ta ɗingi yi tana cewa a zuciyar ta ai dai dai ke ne". Soja ne zaki mawa iskanci ya
ƙyaleki?". Su Hansai da sauran mutanen gida ne aka shigo suna ta Rarrashin Zainabu ,kana
daga bisani Baba Musa yazo yayi nasa . Lamfa tamasu a Cewan ta ta haƙura ta yarda ,amma a
zuciyarta tana kisimawa da cewa a daren ranan da aka kaita zai dawo masu da ita da saki uku".

Sosai akayi masu Adda Raliya tarbar mai kyau ,anan kuma suke shaidawa ango zai zo ganin
Zainabu yaji koda abun da take buƙata anjima. A haka suka bar gidan ,itako Zainabu ta saki duk
ta ƙosa ango yazo ta tijara shi. Bayan mgriba ne aka shaida mata Zuwan ango. Yana zauren
gidan don yy prking moton shi acan farkon layi ,don ba hanyar shigowan ta. Anan ne su Nadiya
suka sa mata kaya sabo ,harda wani fesheta da turare. Humm ita dai murmushi kawai take tana
tunn ta yanda zata fara.


A zauren gidan su ta ga Saif ,don shi yazo sam Habab yace ba inda zai zo, shi kawai jira yake
akawota ya fara aikin sa. Kamin tajira jin mai Saif zaice kawai burin ta ta tijara Angon ,a tunanin
ta shine Angon nata ,nan ba ko gaisuwa ta faɗa shi da faɗa ta ci masa mutunci tafi minti arba'in
tana bala'i ko tsayawa bata yi ,shidai saif baki ya saki yana mmkin masifa irin na Zainabu .tana
dira aya ne ta juya tana yin cikin gida cewa yake " ki tsaya kiji ki saurare Ni ,amma ina tayi ciki
abunta tana cewa a zuciyar ta ai na isar da abun da nakeso ,idan kuma ka aure Ni can maka
kai ka sani ko me ya biyo baya".

_Kar ku manta da daga wannan page ɗin free page ya ƙare ku biya kuɗin ku Kuji yanda
badaƙalar zata kaya tsakanin Zainabu da Habab_

******
A yau asabar rana ce da kowani ɓangaren ke cikin farin ciki kasantuwar yau ce ranan yinin biki
da tarewa....hohoho Zo kuga Sobreen tayi mugun kyau kaman ka ɗauke ka gudu. Bakin ta
kuwa yaƙi rufuwa ,duk da Habab yace ba wani events da xaiyi ,amma su sai da sukayi nasu.
Ango yasha kyau ƙwarai ,fuskar sa sai fitar da Annuri yake na farin cikin zai fara izayar shi daga
yau . Ɓangaren Zainabu kuwa anyi ta godo da ita tayi wanka ta shirya firr taƙi har sai lokacin da
Aka zo Za'a tafi da amarya ne sannan Yaya Nadiya tayi mata don dole ta samu tayi wanka ,sam
ba ƙwalliya a Fuskarta ,wanda wani dandatsatstsen lace maroon tasa na cikin akwatin
ta....Mayafin babba ne aka ɗaura mata'. Sosai akayi mata nasiha da faɗan akan ta natsu aure
ba wasa bane ba. Idon ta ƙarr ba digon hawaye ,don da taga umma na sharar ƙwallar rabuwar
su murmushi tayi a zuciyar ta tana cewa" umma ki bar kuka goben nan zaki ga na dawo".

Komai na Sobreen da Zainabu iri ɗaya akayi ,don Abba yace bai buƙatar komai na iyaye shima
uba ne a gare su ,shi zai masu komai. Part ɗaya suke ,sai dai kowa da falon ta bedroom da
komai da komai. Tun da su Nadiya suka kai ma Hjy Luba Zainabu take yaɓa masu baƙar mgn
,wanda anan jikin su yy sanyi . Koda suka koma bangaren Zainabu nasiha suka ƙara mata
,kamin ace su fito a maida su gidajen su.

Sobreen taso ta shigo taga Zainabu amma kuma sai ƴan uwa ta da ƙawayen ta suka hanata
,suna ce mata ta rabu da ita ba ayau ba.

Tun Zainabu na ganin ƙarfe 8:30pm nan taga tara shiru ba ango har goma da rabi , wannan
yasa miƙewa tana ficewa zuwa falon ta don yunwa takeji ,fridge ta nufa tana buɗe wa ba tsoro

,nan taga lemu kala² wani dariya tayi na shakiyanci n ta ,tana ɗaukan roba biyu haɗi d rufo
fridge ɗin tana juyowa don jin motsin shigowar shi... murmushi tayi a sarari ta furta yanxu za'a
fara wasan".

Kalla n ta Habab yayi yana tuno da marin da ta sharara masa , wanda a yanxu sanye take cikin
ƙananun kaya tuni ya cire na angoncin....shi kaɗai ya shigo don yace mawa su Saif baya
buƙatar kowa yy rakon sa". Wani irin farr da ido Zainabu tayi na tsiya don ta ɗauka Saif ne
ƙanwar lasar da ta tijara ya kasa ce mata uhm'bare uhm'uhm".
Ware idanun ta tayi tana sauke su akan na Haban da idanun shi ke akan ta ,fuska murtike
tamkar mala'ikan zare rai. Wani irin Addu'a taja wanda nikaina bansan me take faɗi ba. Sakin
lemun roban tayi a ƙasa tana faɗin na shiga uku na ,Don Allah aljan ka taimake Ni kabar Ni ,yau
nake amarya mu kwana da miji na lafiya...kabar nayi zaman Aure...kallon ta yayi yana tunanin
anya wannan tana da hankali ba mahaukaciya bane? Zama yayi yana ƙara murtike fuska ,yana
zama akan 2 str. Waye mijin naki Ni Habab? Kar ki ƙara tunanin zama mata a gareni ,na
Aureki ne don na azabtar dake , a haka zaki zauna har muddan Rai". La ilah haila'lhu kai su
Abba suka ɗauramun ,dama kaine mijin nawa??? Shknn rayuwata tazo ƙarshe Ni Zainabu, a
rasa wanda xa'a ɗauramun sai mai idon yahudawa". Miƙewa yayi yana jin wani ɗacin mgn nata
a zuciyar shi . Jah baya ta hauyi tana rintse idanun sa sai hawaye sharrrr³ don Allah ka rufe
idon ka wallahi tsoron su nakeyi , don Allah bana son ganin su wayyoooo Ummana!!!!. Tayi
maganan tana haɗuwa da bangon falon. Keee!! Da me ma zan fara maki?? Fara mun tsallan
ƙwaɗo a haka ki shiga har bedroom ki dawo". Buɗe idanun ta Zainabu tayi ta mance waye
lokaci ɗaya ,tana faɗin eiyeee" taɓ ɗijam Ni Zainabu ne xanyi tsallan kwaɗo. Ta ƙare maganan
ba tare da ta san ya iso gaban ta ba. Jikin su na gab da haduwa dana juna...don ɗayan su na
jiyo numfashin ɗan uwan shi. Manyan idanun shi ya ware akan ta ,wanda nan taga blue ash ɗin
sun ƙara turuwa. Wani irin ƙara ta saki da ƙarfi tana faɗin don Allah ka matsa tsoro nakeji
wayyoooo sai kawai tayi ƙasa luuuuuu idon ta na rufewaaaa!

*Free page ya ƙare ,ƙi biya kudin ki na antaya ki a Paid grp.....*



_Share to another grps pls_


*Littafin ƘWRTN MNY na kuɗi ne normal group ₦300 Vip group₦500 special payment₦1000
zaki iya Turo da katin mtn ta wannan number 08081202932 ko ki tura ta wannan account ɗin
6037312299 mohammed aisha keystone bank...ƴan niger kuma naku Normal payment 500f...
VIP pymnt 750f.... special payment 1250f*

*Mmn teddyn ku ce mai dubu na masoya*

3
4
5

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login