Showing 48001 words to 49786 words out of 49786 words

Chapter 17 - ZAKI COMPLETE BY MAMAN TEDDY.pdf

19 Oct 2025

2222

wasun ta .

Ɗago da ido Ahlaan tayi tana Sharɓan Hawaye , cikin dasushshiyar murya ta furta “ Yanzu kenan babu
yanda za'a yi a fito da Ɗan Uwa na daga kurkuku ?, Tabbas nayi nadama na kuma danasanin kasancewata
ta ƴar jarida . Kiyi haƙuri Ahlaan ƙaddara ce , tabbas Wannan haka Allah ya rubuta , Fahad ya furta idanun
sa sunyi jajir shima dagani kasan yana cikin ƙunar rai da rashin jin daɗin Al'amuranta su .
Tabbas daga yau na ajiye Aikina ta ƴar jarida, na bar jarida bari na har Abada!

Kallon duka suka yi , har da Hajiya Rahima wacce sam bata yi la'asar ba , don dawowar Mom juliana
rayuwar ta tabbas ta kudurci yin Abubuwa da yawa na daukar fansa na kuma ganin ta bar da ita Rayuwar
ta dana mijin ta ,ga kuma uwa uba sabon labarin da taji a yanzu wai Ahlaaan ba yar ta bace yar Hajiya
Maryam ce wato Mom juliana .
Haba Ahlaan ki kwantar da hankalin ki please, Aliyu zai dawo ,duk yanda zamuyi a yanzu babu yanda za'a yi
mu fito dashi daga wannan halin , har sai nan da Wasu watanni a lokacin da Mahaifin ku ya zama president
, sannan ba daga zaman sa ba ne zamu fito dashi dole sai ya dau wani lokaci tukuna ”.

Kamin Ahlaan ta ba ma A
Hajiya Rahima amsa ne suka ga A'ieeee ta mike tsaye idanun ta a kumbure murya a ɗashe tace “ Yayi ina
maku fatan ALLAH yanada sa'ar siyasa Ni zan wuce garin mu yanzu , saboda banga amfanin zama daku ba
sam ”. Ba zaki tafi ba Ai'eesha! Ba zan taba barin Matar yayana ta koma Kauye tayi rayuwa ba , A taƙaice
tayi nesa damu , Bamu san halin da kike ciki ba da kuma yaron cikin ki , don haka Nima nagama yanke
hukuncin barin kowa nawa....zan bar Nigeria Mom Maryam kuyi mun afuwa ba zan taba dawowa ba har
sai ranar da Dan uwana ya zama ƴantacce , Don haka zan tafi da A'ieeesha don cika ma Ya Aliyu mafarkin
sa .......!

Hummmm muje zuwa












*️ZAKI️*

*69-70*
_________________________

Jikin su ko ina Rawa yake yi banda A'ieeee wacce ta tsaya kurum tana zubawa sarautar Allah ido .
Tsohuwar kin san wannan menene? Ɗaya daga cikin su ya furta yana ɗaura ma Mama Abu Bindiga a ka ,
wanda jiki na kyarma mama Abu tace“ Kuma girmansa Allah kar ku cutar damu....mene muka yi maku?”.
Wannan itace tambaya ta masu hankali ,wani ya furta yana takowa zuwa inda A'iee take tsaye itama sun
daddaura mata Bindogogi aka ,tamkar wacce tayi kisan kai ”. Ke yarinya! Ki taimaki tsohuwar ki da kuma
jaririn cikin ki , Ki bamu dukkan wani abu da Sir Alexander ya baki , idan kuma kin ƙi zamu tafi daku muyi
maku kisan wulaƙanci ”. Hmmmm Shine Abin da ya kawo ku? Koda ban sani ba kuna daga cikin Yaran sa
,wanda ashe dama ba zamar ALLAH kuke yi dashi ba , don ya garere ku ne da ba don haka ba da tuni shima
Kun nemi tasa Rayuwar , To Ni kam a yanzu sai da kuyi mun duk abin da zakuyi ba zan bada komai ba ,don
ba zaku sami komai daga gareni ba ”. A'iee ta furta Muryar ta a dake babu alamar tsoro,don ita gaba daya
taji zuciyar ta ta ƙeƙeƙashi tun daga Ranar da ta rabu da Alex , Sau da dama tana mamakin kan ta itama ,
don cewa take me yasa take jin sa a ko wani rufe ido da zata yi ta bude ,mai yasa a kullum take ganin sa a
barcin ta ,tabbas tafi alaƙanta wannan da Tausayin sa ne ya ɗarsu a zuciyar ta .

Muryar Wani inyamiri ne ya katse ta yana cewa “ Tabbas da ba don kar muyi abin da bashi ba ,mu karya
umarnin malam Silvaline to da a yanzu mun kar ki , mun raba ranki da jikin ki ”. Ku tasa su mu wuce dasu
duka! . Haka Aka tasa su Mama Abu suka fice dasu daga gidan ,suna tura su a motocin su tare da kai su
inda basu sani ba ”. *
Alhaji Bukar yau dai Allah yayi ka gani Allah ya baiyana mana Abin da muka dade muna jiran dawowan sa
,wato Hajiya Maryam . Don haka Yazama dole a cikin satin nan mu nemi malamai muji ya Auren ku yake ,
za'a sake mayarwa ne ko kuwa Auren yana nan? , Hajiya Turai ke maganar tana kallon Alhaji Bukar da yayi
zama a gaban ta cike da ladabi ta uwa da Ɗa . Hmmm Gaskiya ne Hajiya ,Nima kai na a kwanakin nan da
Wannan tunanin nake kwana da tashi . Sam hankalina baya natsuwa in gan ta a can wani gida da ban ba
gidana ba . Ƙaran shigowar saƙon wayar sa ce yasa shi kai idanun sa saman screen ɗin ,inda yaga an turo
masa saƙo kamar haka “ Barka da warhaka ranka yadaɗe . Yanzu na sami labarin sakin Yaron mu Aliyu daga
gidan kaso, akan wasu Ƙwaratan hujjoji, sannan ina ta kokarin kiran wayoyin sa duka basa shiga
”.....zumbur Alhaji Bukar yayi yana miƙewa tsaye tare da ƙara gyara zaman medicated glass din idon sa .
Lapiya wani Abu ne ya faru? . ALLAH yasa muji alheri ....Hajiya Turai ta furta tana kallon Alhaji Bukar tare
da jiran jin amsar me zai ce daga bakin sa .

Hajiya Yanzu Hajiya maryam ce ta turo mun da saƙon Aliyu baya gidan yari gomnati ta sake shi saboda
wasu hujjoji yanzu haka bata san inda kuma ya nufa ba. Alhamdulillah ALLAH mun gode maka , yanzu
meye na shiga tashi hankali kuma?. Hajiya Aliyu bai san Ni mahaifin sa bane , kar ki manta mun so gomnati
ta bar Ni nayi magana dashi amma suka ce a'a sai yayi sati biyu a gidan kaso sannan kowa ke da daman
ganin sa . Kar ki manta Ahlaan ce tayi sanadin Faruwar komai , Aliyu Haidar Ni nasan waye shi ZAKI ne
,wanda baya taɓa barin akai sa ƙasa bai rama ba . Ahlaan ce abin harin sa a yanzu ,kar ya cutar da ƙanwar
sa uwa ɗaya uba ɗaya bai sani ba ,yayi ba dagangan ba .

Tabbas maganar gaskiya ce , kayi kiran Ahlaan ka turketa a cikin gida kar ta fita har sai an ga Aliyu Haidar
sannan . Juyawa Alhaji Bukar yayi saurin yi yana faɗin tot,to to....Hajiya badamuwa bari naje....yana
maganar tare da Kiran layin Hajiya Rahima don yaji Ahlaan na cikin gidan ne!

*️ZAKI️*



*71-72*

_________________________


Tun a mota yake kiran Numbern Hajiya Rahima amma kuma kashhh bata shiga hankalin Daddy idan yayi
dubu yayi kololuwar tashi . A haka yake cewa da drivovin su kara gudu .

*
Kin sanni?
Ta furta tana sauke mata faskeken Gilashin idonta, ga wasu zaƙozaƙon eye lashes da suka sauko . Bin ta da
kallo A'ieeee tayi kana tace “ Ban sanki sai dai yanzu idan kin mun bayani”.

Juyawa Mom Silvaline tayi tana kallon su David kana tace“ hmmmm Ashe yarinyar cararrace bata da kunya
”. To ba sai na ƙara magana da ita ba , Domin ada nayi niyyar barin ta a raye , amma kuma a yanzu ku kashe
su duka da ƴar da uwar , shi kuma sauran duk abin da muke buƙata daga hannun su ,David ka tura Wasu
daga cikin Mutanen mu su nufi gidan suyi sanka sanka da komai a fiddo da su .
Ƙasa magana Mama Abu tayi , wanda A'iee itama da ido take kallon matar da a kallo Daya zaka fahimci
Bata da imani ko tsoron Allah. Ɗago da A'isha suka yi suna inguzata tare da tasa ƙyayarta suna kokarin fitar
da ita daga Wurin don su cika umarnin Ma'am Silvaline . Joshua dake gaba ne suka ga ya yo baya a tsorace
yana fiddo da idanun sa , gumi na karyo masa a lokaci ɗaya ..... Cikin daka tsawa Mom Silvaline ke
tambayar sa lapiya? Amma sai Muryar sa ya harɗe ya hau Rawa yana furta “ Boss ”.

Boss” , ta furta cike da rashin fahimtar ina ma ya dosa , ya kuma nufa . Kai dalla kayi mana magana , David
ya furta a zafafe yana yin gaba tare da jan labulen,inda shima da sauri yayo baya ji yayi kamar yayi fitsari a
wandon sa don tsoro . Muryar sa na Kyarma da Rawa ya kalli Ma'am Silvaline yana cewa “ Ya Dawo!
Shikenan mun shiga uku!
Cike da Shan jinin jiki ta furta wa kake so kace mun? Alex? .

Yes king is back......, Saurin Ɗagowa A'iee tayi tana kallon su jin an ambaci sunan Alex tasan waye suke nufi
, kamin suyi wani matso tuni jami'ai sun banko ciki , Alex na basu umarnin su kama su duka ”.

Bai tsaya bi takan kowa ba , cikin izzan sa ya taka yana isa zuwa inda Ma'am Silvaline take , kana yace “ Kar
kiyi mamaki Yaron ki ya wuce yanda kike zato , Na gode Da kulawar ki da kika bani na rabani da
Mahaifiyarta da ɓoye asalina na taso a Arne wanda rayuwar sa babu daɗi sam....tabbas shigowar ta
Rayuwata haske ne ta kasance mun fitila ,ya furta yana nuna inda A'ieeee ke tsaye ,kana ya cigaba da cewa
“ ita din wata babbar gudumuwace Allah ya turo ta rayuwata ,don na banbace baƙi da fari .... shiyasa nake
Son ta sosai . Ina Sonki A'ieesha . Matsawa yayi zuwa inda A'iee take yana kai hannun sa tare da shafa
gyefen kuncinta , a hankali ta ɗago idanun ta Da suke zubar da ƙwallah da ta rasa na mene ne? Ganin haka
bai tsaya duba ga jami'ai ba ko mama Abu da bai san wacce ita ba , kawai sai haɗa bakin sa yayi da nata
yana kissing yana Rungume ta tare da manna ta jikin sa .

Dpo ne ya furta “ Sir zamu wuce dasu yanzu . Don shi kam shi abin na Alex ya ƙayatar dashi ,tabbas yana
zafin son matar shi ko ba'a faɗa ba , a aikace zaka fahimci hakan. Ba tare da ya zare bakin sa daga nata ba ,
da hannu ya ɗaga ma D.p.o alamun yayi aikin sa . Haka aka tattara su Mom Silvaline dai dai su Daddy na
shigowa........

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login