Showing 42001 words to 45000 words out of 49786 words

Chapter 15 - ZAKI COMPLETE BY MAMAN TEDDY.pdf

19 Oct 2025

2211



Gaba Ɗaya David ya gama ruɗewa da jin wannan zancen , Wannan yasa shi cikin sauri cewa “ King
Alexander wannan Wani irin Abun kunya ne kake ƙoƙarin yi mana? Zaka jefa mu cikin nadama , Wannan fa
musulma ce ? Itace kake farin ciki don ta Ɗauri cikin ka . Wani irin wawan tsawa Alex ya daka ma David
kana yace “ Nayi farin ciki da hakan ba matata bace? ”. Jin haka yasa David yin shiru cike da biyayya ga
uban gidan nashi ya furta “ Sorry Boss ”. Shiru Alex yayi kana yace “ ka fara mana Shirin komawa Nigeria
Gobe nake so mu koma ”. Ok . Ya furta a sanyaye ransa duk ya gama ɓaci , don yanda yake ji tabbas aka
bashi wuri daga shi sai A'ieeee to zai iya kashe ta duk ya huta .
*
Cikin sauri Ahlaaan ta miƙe tare da Furta “ Alright gani nan zuwa ”. Tana magann tare da gyara mayafi tana
nufo falon Hajiya Rahima.

Ahlaan lapiya kika fito kina zabga wannan uban saurin haka? Ina kuma zaki je da Wannan yammaci haka? .
Mom aiki ne na ujila ya kamani, Hummmm jan numfashi tayi tana saukewa kana tace “ Alex ya shiga hannu
, yanzu zan ga da mai yake taƙama ”. Kallon ta Hajiya Rahima tayi tana girgiza kai kana tace “ Ban fahimce
ki ba? Me kike nufi ? Mom a yau an kama babbar mawakiyar King Alexander wacce take masa safarar yara
. Yanzu haka tana hannun hukuma, kuma ita ce ta bada hujjoji akan shine uban gidan ta.........”

*️ZAKI️*


Na
*Aunty Ayshatou Mamanteddy*

Book 3

55-56

_________________________
The Writer of :
1)Ƙwarton manya
2)the Sexy Boss
3)Gidan ƙwarata
4) Walijaam
5)ƙwarton manya
6)siyasata
7)my Lady boss

8)Ƴar tsakar gida
9)fyade
10)Ƴar aikina
11)ƴar waye
12)dijama yar Fulani
13)Bintoto
14) zuma da maɗaci
15)the virgin maid
16)Rainon soja
17)Duniyar shahara
18)Sadaka yallah
19)Gidan zaurawa
20)Ƙwayar sama
21) Bafullatanan Ruga
22)Taɓarah
23)x world duniyar shahara.
*And now ZAKI......*
_________________________
Littafin na kuɗi ne Regular payment ₦500 Vip payment ₦1000 SPC payment ₦1500 via 6037312299
Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932

*
Allah mai iko! Ahlaaan wai ba zaki dakata daga wannan.....Mummy sai na dawo! Ahlaan ta furta cikin sauri
tana ficewa daga falon ba tare da ta jira jin mene Hajiya Rahima zata ce mata ba ”.

A hankali take ware Idanunta tare da buɗe su tana sauke su bisa Fuskar Alexander wanda ya tsaya yayi
mata ƙurrrr tsawon lokaci yana kallon kyaƙyƙyawar fuskar ta ,wanda a zuciyar sa da tunanin sa babu abin
da yake tunanowa face Rayuwar sa da A'ieee da kuma yaran su da zasu haifa ”. I love You dear, ya furta
yana sakar mata murmushi mai sanyaya zuciya . Hummmm jan numfashi Tayi tana saukewa kana ta motsa
hannun ta tana yunƙurin miƙewaa da Sauri ya matsa Gareta yana tallabota jikin sa tare da Faɗin “ Sorry
,bari na taimaka Miki , yana magann tare da gyara mata pillow yana mai zaunar da ita kamar yanda take
ƙoƙarin yi . I really love you baby Uhmm .....ya kai bakin sa yana kissing lips ɗin ta . Rintse ido A'ieee tayi
tana kauda kan ta gyefe , a zuciyar ta tsananin tsanar Alexander ne fal bata ƙi ace Yau ya bar duniyar duka
ta huta ba ”.

What do you want now baby? Ya furta cike da nuna soyayya da kulawa , a kuma natse”. Kafe sa tayi da
idanun ta don bata san ma mene yake cewa ba , wannan yasa alex fahimtar ba Hausa yayi mata ba ”. Me
kike da buƙata yanzu , watsa ruwa ,ko abinci wanne kike ganin.......Hannun ta ta ɗaga alamun ya dakata .
Wannan yasa Alex yin shiru yana kallon ta . Idanun ta ne ya ciko da Ƙwallah a nan take suka fara biyo
kuncin ta , a hankali ta fara motsa laɓɓanta tana cewa“ Bana buƙatar ganin ka a Rayuwa ta , Ka taimake Ni
ka mayar Dani wurin danginsa da ƴan uwa na . Bana son ganin ko kaɗan wallahi ....”


Wani irin nauyi ne yaji ya tokare masa a ƙirji, Sam ya rasa yanzu ta ina zai fara Magana don ta fahimci
tsananin soyayyar da yake mata ”. Please stop saying that, Ki yarda Ina sonki mahaukacin So! Mene zan
Miki ki yarda dani, da zan cutar dake da tuni nayi hakan ,amma ban yi ba , Na rabu da kowa don na zauna
dake , Duka matana da nake Jin daɗi dasu na barsu na zaɓi ke kaɗai , Please A'ieeesha ki fahimce Ni ki
yarda dani Ina sonki kuma ina so na Rayu dake , ina Tsoron kai ki dangin ki ne ba don komai ba sai don kar
ki rabu dani ki ƙini ki guje Ni ....na rasa ki Nima zan rasa rayuwata ,wannan tabbas haka yake . Ɗago da
lulun idanun sa yayi yana kallon ta , a dai dai lokacin itama ta ɗago da idanun ta , Mamaki ne ya kama
zuciyar ta , ƙwallah ne tagani ƙwance a idanun sa da suka kaɗa suka yi jah kamar Jan Yalo . A hankali taga
ya sauka daga gadon yana tsugunawa gaban ta gwiwowin sa a ƙasa yana furta “ Please A'ieeesha ki amince
ki zauna dani, zan chanja duka rayuwata wanda kika ga bai miki ba , a taƙaice har Addinina na ce zan sauya

just because I want to be with you ”. Please baby! Ya furta yana riƙo hannun ta , Wasu irin zafafan ƙwallah
na gangaro masa . Ƙirjinta ne ya buga da Ƙarfi wannan yasa ta Saurin kallon sa tana girgiza kan ta tare da
fashewa da kuka itama tana jijjiga na tsananin damuwa tabbas ta rasa mafita a yanzu . Miƙa taga yayi yana
Furta “ Kiyi haƙuri Ban so na faɗa Miki wannan zancen ba ,amma dole ce ta saka Ni yin hakan ”. Ina sonki
sosai, kuma kina ɗauke da cikina ni ALEXANDER ina alfahari dake ......” buɗe baki A'ieeee tayi kawai sai ta
fashe da wani irin kuka mai ban tausayi , Ganin ba zai iya jurar ganin ta a hakan ba ne yasa shi saurin
ficewa daga wurin yana nufar ɓangaren da Su David suke ”.

Hankalin su tashe ya gan su a fuskokin su kaɗai ya fahimci da akwai damuwa . Kallon su yayi kana ya zauna
bisa kujeran kagaaran sa na BOSS , Yana Jiran jin mene David zaice dashi a halin yanzu. Boss da Kwai
matsala babba , dake tuna karo mu , Ƙasar mu Nigeria tana neman ka , kuma hukunci ne babba za'a yanke
maka bisa ga Tonuwar duk wani miyagun harƙallolin mu da muka saba. David! Alec ya kirasa da Wani irin
dakakkiyar murya , Wanda jin hakan yasa David saurin sunkuyar da kai . Sorry boss”. Ka sani Ni Alex ina
harƙalloli mara sa ƙyau ,amma kuma ba duka kasuwanci na bane suke gurɓatattu . Ni surgical doctor ne ,
Na mallaki kadarori ta wannan hanyar marasa iyaka, Na mallaki campanoni sannan Na mallaki gidaje
komai na jin daɗin Rayuwa ,komai nake so tun ina ƙaramin yaro ina samun shi ne da ƙarfi na , ammma a
yau na kasa samun abu guda Ɗaya kacal , Shine Soyayya!

Shiru yayi yana numfasawa kana yace “ Bata SO na , Bata son gani na a rayuwa , ina Ƙaunar A'isha dana
Rayu babu ita gwamma na mutu , Don haka ita yarinya ce mai kirki , ba gurɓatacciya ba , A shirye nake zan
miƙa kaina ga ƙasata tare da amsa duk wasu laifuka na , Amma ina so kamin nan komai dana mallaka ta
hanya mai ƙyau na mallaka mawa A'ieeesha matata , Zan tafi wata ƙil a yanke hukuncin kisa , ko kuma
zaman gidan Kaso na har abada wato daurin rai da rai .

Wani dariya yayi tare da cewa “ Ina jin daɗi ko a yanzu naji na kammala , rayuwata tayi daɗi saboda Na
hadu da mata ta gari, kuma tana dauke da cikina wanda ko bayan Rai na ,zata kula da kanta da kuma babyn
da zata haifa mun ....na bar masu komai wanda ba ita ba har jikoki bazasu karar da abin dana bari ba .

David hummmm ka shirya mana komawa Nigeria zan miƙa
kaina.....!
*️ZAKI️*


Na
*Aunty Ayshatou Mamanteddy*

Book 3

57-58

_________________________
The Writer of :
1)Ƙwarton manya
2)the Sexy Boss
3)Gidan ƙwarata
4) Walijaam
5)ƙwarton manya
6)siyasata
7)my Lady boss
8)Ƴar tsakar gida
9)fyade
10)Ƴar aikina
11)ƴar waye

12)dijama yar Fulani
13)Bintoto
14) zuma da maɗaci
15)the virgin maid
16)Rainon soja
17)Duniyar shahara
18)Sadaka yallah
19)Gidan zaurawa
20)Ƙwayar sama
21) Bafullatanan Ruga
22)Taɓarah
23)x world duniyar shahara.
*And now ZAKI......*
_________________________
*Littafin na kuɗi ne Regular payment ₦500 Vip payment ₦1000 SPC payment ₦1500 via 6037312299
Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932*

Jikin su ne gaba ɗaya yayi sanyi bisa ga Maganganun King Alexander, A hankali David ke kajin wasu irin
Hawaye na zubo masa tabbas yasan abokin nasa kuma ubangidan sa jarumi ne namiji wanda babu shakka
miƙa kan sa zaiyi . Tabbas wannan yarinyar shigowar ta Rayuwar mu masifa ne , David ke furta hakan a
zuciyar sa . Kai David ! Namiji da kuka? Haba kar ka maza kunya mana , Alex ya furta yana miƙewa daga
tsaye tare da takowa zuwa inda David yake . Ina So yau zan je Ga Mom Juliana don na yi mata kallon
ƙarshe kuma na faɗa mata komai , A gobe kamin mu koma Nigeria zamu sauka a Egypt don Ina so kamin
na Bar duniya na amshi Addinin Musulunci Don ina so na mutu da biyayya ga Matata , Alƙawari nayi mata
kuma zan cika ”. Ya na gama faɗin haka ya juya yana ficewa daga Wurin tare da barin su David a tsaitsaye ”.

Tun da Alex ya fita Private room ɗin shi ya nufa , ta system ya fara aikin sa inda duk wasu kadororin sa ya
fara musanya sunan sa zuwa na A'ieeesha ...a haka har gari yayi duhu bai ci ba bai kuma sha ba . Da misalin
8:pm ne ya miƙe yana nufar Bedroom ɗin da A'ieesha take . Zama yayi yana kallon ta don a wannan
lokacin sallah ya tadda ita tana yi . Juyawa yayi yana kallon Abincin da aka kawo mata babu laifi ta ɗan
tsakura haka ma kayan marmarin tasha babu yawa . Yana zaune yana kallon yanda take yi , sai kaman
Wanda aka taimaka taga ya miƙe yana nufar toilet . Yanda yaga Mom juliana na Alwala yayi ba tare da
yasan yaya ake yin ba . Ya wanke fuska hannu da kafa ya fito . Fitowar sa ke da wuya A'iee na sallame sallar
ta , Miƙa tayi daga saman carpet din yana saka kafarsa tare da Kame hannu a kirji kaman yanda yaga tana
yi .

Turus tayi tana kallon sa , kawai sai taji dariya ya kamata Wanda bata san lokacin da ta hau yin ta ba .
Tsayawa Alex yayi yana shagala da kallon kyaƙyƙyawar fuskar ta. Ina Sonki, y furta ba tare da yana san
mene yake faɗi . Shiru tayi tana dakatawa tare da kallon Lulun idanun sa . Murmushi tayi wanda bata taɓa
yi masa ba sai a yau kana tace “ Ba haka ake sallah ba , kana so kayi ne? . Lumshe idanun sa yayi yana
buɗewa kana yace “ Eh , koya mun”. A'a ba zai yiwu na koya maka ba , Har sai ka amshi Addinin Musulunci
sannan zaka fara sallah Allah kuma ya karba ”. Shiru yayi kana yace “ Yanzu ba zaiyiwu nayi ba kenan ,
Kema amsar addinin kika yi , sannan ki fara Sallah ? .

Girgiza kan ta A'iee tayi tana cewa “ A'a Ni a cikin addinin Musulunci aka haife Ni ,kaine da aka haife ka a
wata addinin sai ka amsa sannan . Takawa yayi yana isowa gaban ta kana yace “ Yau kin yi mun magana
,wanda baki taɓa ba ,ko meyasa? . Nima ban san me yasa ba , Amma dai kawai dariya ka bani ”. Thank God
yau na sakaki kin yi dariya ko a yanzu na rasa rayuwata naji daɗi . A'a baka huta ba , saboda babu kafirin da
zai mutu a kifirci yaji daɗin lahira , har sai idan ya amshi musulunci kuma ya musulunta saboda ALLAH da
Manzon sa . Gani tayi Alex yayi baya kaɗan yana cewa “ Gobe zamu sauka a Egypt zan amshi Addinin
Musulunci,daga nan zamu koma Nigeria, Kiyi farin ciki zaki rabu da Alex amma zaki ga Iyayen ki”.

Cike da rashin fahimtar sa ta saki murmushi har hakoranta suna bayyana kana tace “ Da gaske , ka taimake
Ni don Allah , Mama kawai nake son gani . Hannun sa yasa yana Rungume ta tare da shafa bayan ta a
hankali kana cikin sanyin murya ya furta “ Zaki ga Mama, amma please A'ieesha kiyi mun alƙawarin zaki So
abin da zaki haifa nawa,sannan Zaki kula mun da kan ki da Babyna sosai ”. Cikin sauri A'ieeee ta gyada kan
ta tana cewa “ Nayi maka alkawari,indai zaka bar Ni nayi rayuwata Ni ɗaya ”. Ɗan raba jikin ta yayi da nasa
kana ya nufi inda ya tashi yana ɗauko wata jaka yana cewa “ Wannan Ki riƙe shi da kyau duka naki ne kar ki
ba kowa ,kar kuma ki bari kowa yasan meye a cikin sa . Ki kula sosai . Sannan Mom juliana ma na san ko
bayan Rai a Zata kula mun dake ”. Turusss tayi tana kallon jakar,kamin tayi wata magana taga ya juya yana
cewa “ Zan je gidan Mom juliana a wannan daren gobe da safe Flight din mu zuwa Egypt daga nan zamu
wuce gida.

*️ZAKI️*


Na
*Aunty Ayshatou Mamanteddy*

Book 3

59-60

_________________________
The Writer of :
1)Ƙwarton manya
2)the Sexy Boss
3)Gidan ƙwarata
4) Walijaam
5)ƙwarton manya
6)siyasata
7)my Lady boss
8)Ƴar tsakar gida
9)fyade
10)Ƴar aikina
11)ƴar waye
12)dijama yar Fulani
13)Bintoto
14) zuma da maɗaci
15)the virgin maid
16)Rainon soja
17)Duniyar shahara
18)Sadaka yallah
19)Gidan zaurawa
20)Ƙwayar sama
21) Bafullatanan Ruga
22)Taɓarah
23)x world duniyar shahara.
*And now ZAKI......*
_________________________
Littafin na kuɗi ne Regular payment ₦500 Vip payment ₦1000 SPC payment ₦1500 via 6037312299
Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932.

Wani irin sanyi taji yana ratsa zuciyar ta cike da jin daɗi ta sakin masa murmushi jin ya ambata kalmar Gida
. Hannun sa yasa yana warewa tare da rungumeta kaɗan , tamkar wanda baya son raba jikin sa da nata

yake zame jikin sa ,kana ya Ɗaga mata hannu tare da furta kalmar ki kula sosai ,zanje na dawo . Gyaɗa
masa kai tayi ba kuma tare da tace komai ba , har ya fice ”.

Ranka yadaɗe a yanzu me yayi saura jiran dawowan sa kawai muke daga nan Zamu yi raaam dashi ,kai
tsaye kotun ƙoli za'a wuce dake garin Abuja, a yanke hukuncin sa a kuma aika sa gidan kaso,idan na kisa ne
duka ya cancanta ”. Chief of judge ɗin ne ya gyaɗa kai kana yace ” Idan Muna so shari'ar ta tafi wurin yanke
hukuncin gaggawa ,shine kar a aika masa da Wani saƙo na ko yasan halin da ake ciki , mu bari yana isowa
ayi rammm dashi .

Jan dogon numfashi Ahlaan tayi bisa Tuno da bayan da suka yi da Alƙali , murmushi ta saki sam ta manta a
dinning table suke suna Yin break fast ”. Ahlaan lapiya kuwa? Kina ta murmushi ke ɗaya? .Fahad ya furta
yana sake duban Ahlaaan wacce ta farga da abin da take yi . Alh Bukar Macciɗo ne ya furta “ Nima dai tun
ɗazu shi nake ta gani .
Hummmm Daddy dole ku ganni haka, Dalili kuwa Ana gab da kama mai laifin da Aka daɗe ba'a kama ba,
wanda ƙasa ma ke shakkar sa Wato King Alex , Idan zaku iya tunawa shine yazo gidan nan yaci mana
mutuncin mahaifi a gaban idanun mu ,babu wanda ya iya tankawa, Alhmdlh a yanzu dukka wasu hujjojin
laifin sa suna hannun gomnati wanda Shari'a kuma ta hau kan sa , A kiyasce ƙila hukunci ne Ɗaya zuwa
biyu dole a yanke masa , Na ɗaya Kisa bisa abubuwan daya aikata,na biyu Ko zaman gidan kaso na har
abada ”.

Ajiye fork ɗin hannun sa Fahad yayi cikin sauri yana furta “ Ahlaan nikam sai naji banji daɗin hukunci da
za'a yanke masa ba tun a duniya, Cox Arne ne , ace yazo duniya ya mace a haka ,kuma a lahira ga makomar
sa . Why not a rabu dashi , Allah ya shiryar dashi sai naji ba daɗi sam duk da abin da yayi mana bai ƙyauta
ba .....Kai yi ma mutane shiru Fahad! Mutumin da yake lalata yara har yake safarar su kake magana a ƙyale
,ai kuwa da duk wasu masu faɗa aji na Nigeria zasu koma gurɓatattu wannan shine dai dai ....“Cewan
Hajiya Rahima cike da Tsawa , shi kam Alh Bukar Macciɗo tun da suka fara wannan tanka tankan sam bai
tanka ba , ganin haka yasa Mufidah kashe Maganar da cewa “ Ohh wannan fa bamu san shi bamu da wata
jiɓi ko alaƙa dashi ,to meye na damuwa dashi har muke nemar musu da rabuwar kai a tsakanin mu .
Wallahi Ni kam koda rataye shi za'a yi ba zanji komai ba ,saboda kafuri ne , mara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login