Showing 1 words to 3000 words out of 18070 words

Chapter 1 - DOLE KI SONI BOOK COMPLETE BY MAMAN SHAKUR.pdf

M Shakur   

09 Oct 2025

1135

DOLE KISONI 1 to 55
Posted on October 23, 2015
[09/09 11:21 AM] Aishat muh’d:
1DOLE KISONI
Students nagani dayawa kowa sauri yake yaje lecture theater saboda DOCTOR INDIA yace
yanada wani muhimmin announcement yau….
Hall din cike yake makil da dalibai an cika an batse kasancewar ansan doc india baida wasa
kuma yace karfe 9:00 ne saisa kowa yazo on time sai hayaniya dalibai suke ko ina a cike wasu
a tsaye wasu a zaune ………..
Chan sai ga wani kakkyawan matashi fari dogo yanada dan kiba dan daidai dan ba siriri bane
cikakken namiji ne ga saje hancinshi dogo siriri gashinshi sai kyalli yake bakinshi dan karami
yanada cikan kirji kai namijin yahadu kana ganinshi kaga cikakken dan India yanzu shekaranshi
30 yana sanye cikin bakin suit da takalmi cover baki sai farin glass dinshi oboy yeee dis guy na
fire ooo dan ko besty humairat sake baki tayi tana kallonshi miyau har yana diga
Yana shigowa jikake tsit ajin kaman ba mutane kowa yay shiru dan Allah yazubama dalibai
tsoronshi yanada kwarjini ga farin jini wurin mata ga haiba d guy na Prince charming oo
Maman shakur
[10/09 7:33 AM] Aishat muh’d:
2DOLE KISONI
Yanata murmushi students sunyi mamaki dan sunsan baya murmushi ko kadan yadau
microphone yafara magana Attention everybody kowa yay shiru …yafara magana da harshen
turenci yace yau na tsaya a gaban kune dan nafada muku wacce nakeso nakeson aura nake
sonta fiye da kowa da komi a duniyan nan i stand before u all to declare my luv 4 her i luv u
Aiman you are my happiness my life my joy my heart desire…..yakara cewa students i now
present u my wife to be in sha Allah Aiman imran kowa yafara tafi chan sai ga wata kakkyawan
yarinya yar shekara 19 ta shigo tana sanye cikin pink doguwan riga mai stones da dan karamin
hijabinta iya wuya shima pink takalmi pink komi pink taci make up tana wani irin murmushi da
ban gane nufinshi ba…tana karasowa gaban doctor india jikake tass tass tass ta wankama doc
india mari har uku…….
Maman shakur
[10/09 8:29 AM] Aishat muh’d:
3DOLE KISONI
Jikake tass tass tass ta wankama doc india mari har uku …..doc india ya rike kuncinshi Aiman
ta kalleshi tai tsaki mtswwwwww tace Allah ya tsareni na auri bunsuru mayen mata irinka wawa
banzaa kawai… duk soyayyan dakaga nayi dakai saboda kasoni ne nima na wulakantaka
kaman yanda kaima besty na Amina a public…but i never luv u and i will never will duk
maganan nan da turenci takeyi saboda doc india bayajin hausa tace u are nothing but a piece of
trash… tai tsaki taja hanun kawarta Amina suka fito har sunkai bakin hall din doc india yace
Aiman da karfi.. ta tsaya chak ya tako har inda suke ya kalleta da jajayen idonshi fuskan nan
tashi tai ja saboda mari bata taba ganinshi hakaba……yace mata u will pay 4 dis…..Aiman u
will pay 4 dis humiliation….u will pay 4 making me fall in luv with u deeply…..is a promise
…Aiman ta kalleshi shekeke ta tofa mishi miyau a fuska tace do u worse taja hanun kawarta
sukabar hall din…..

Maman shakur
[10/09 8:40 AM] Aishat muh’d:
4DOLE KISONI
Doc india shima azuciye yabar hall din yawuce inda yay parking car dinshi ya shiga ya jata a
zuciya idonshi tsabagen baccin rai har sunfara baki baki……students ko sai ihu ake wasu suna
cewa Allah kara haka yake wulakanta mata dan yaga yanada kyau ga kudi wasu kuma suce
Aiman bata kyautaba koma menene ai yana bala’in sonta kaman ranshi ,mesa zata yaudareshi
ta gwada mishi son karya gaskiya bata kyautaba wasu dadi sukeji yanzu yabata da Aiman
maybe su samu shiga hakadai suka gama gulmace gulmacen su suka bar hall din….
Bangaren Aiman kuwa suna mota Amina ke mata fada haba Aiman wanan zagin dakika mishi is
too much niyayma laifi bakeba nariga nace miki nayafe kibar abunan amma bakiji gashi yace u
will pay ….Aiman ta kalleta shekeke tai murmushi tace wlh bazai iyamin komi ba saboda yana
bala’in sona wawan …tace besty bazaki gane bane na tsaneshi wlh abunda yamiki ya batamin
rai ba kadan ba Amina tace muje gida saina fadan ma dad abunda kikayi…ta daure fuska tace
wlh in kika fada mun bata dake har abada taja motan azuciye sukai gaba…..
Kubiyoni danjin Asalin labaarin.
Maman shakur
[10/09 8:18 PM] Aishat muh’d: [10/09 3:15 PM] aishat muh’d:
5DOLE KISONI
Asalin sunanshi Amir khan amma students suka samishi doc india……Babanshi haifaffen dan
India ne sai mamarshi yar Nigeria….Lokacin da mamarshi Asiya taje karatu India shine suka
hadu da baban Amir khan mai suna khan mirwan sunyi soyayya sosai daga baya aka barsu
sukai aure sun haifi Amir khan yanzu yanada 30 daganan sun dade basu haihuwa kwatsam
akaga ciki aka haifi yar kanwanshi mai suna simra yanzu shekaranta 5…..baban shi yanxu
shine sarkin india ya gaji sarauta…
Amir yarone wanda iyayenshi suka sangarta sun batashi kome yakeso shi yakeyi bazasu taba
cemishi karkayi kaza ba…saisa yake neman mata son ranshi babu abunda
yadameshi….zuwanshi yanzu ma Nigeria hutun shi naduk shekara ne yafara shine yana zuwa
ya sauka a kaduna yanemi lecturing a ABU bangaren medicine saboda dama shi likitane Wanan kenan…
Maman shakur
[10/09 3:26 PM] aishat muh’d:
6DOLE KISONI
Aiman imran yarinyar daya tilo ga iyayenta Alh imran maitama da kuma maman ta hj Aishat
sani…babanta yanada kudi sosai dan shahararren dan kasuwane….maman ta cikakkiyar yar
fulani ce tanada wani al’ada acewarta inkanada ya mace tun tana karama kake gyarata dan
bakasan ya auranta zai kasance ba tunda ta haifi Aiman kullum da jike jiken gyaran jikin da take
bata barinma yanzu datai girma na yau daban na gobe dabaan…Aiman yarinyace tanada
kamun kai batason raini kuma batason wulakanci…tanada zafi barinma inka tabota..
Akwai wata rana ta shigo ABU da motan ta kawai tsautsayi yasa ta bugi motar doc india tafito
dasuri dan tabashi hakuri shikuma yafito da zafinshi amma yana daura idonshi akan Aiman yaji
Allah ya jarabceshi da sonta kawai ya tsaya yana kallonta tace plz kayakuri mistake ne yajuya
kawai yace bakomi…ita alokacin bama tasan shine doc india dinba……

Maman shakur
[10/09 3:35 PM] aishat muh’d:
7DOLE KISONI
Tun daga ranan doc india da tunanin Aiman yake kwana ya tashi gashi bai kara ganintaba….
Wata ranan monday tashigo school taga mutane antaru ta kutsa kai cikin taron dan taga mai
ake kallo tana kutsa kai dai dai Lokacin doc india ya shararama Amina besty dinta mari har
guda biyu sanan yace mata ana so dole ne nace miki bana sonki leave me alone yay tsaki
yakara gaba..yabar Amina sai kuka take azuciye Aiman takarasa ciki takamo Amina ta share
mata hawaye tajata suka fita suka shiga mita Aiman tace besty maiya faru??? Amina tace
naganshi zai wuce shine nai mishi magana yaki amsamin saina kamo hanunshi nace i really luv
u sir shine ya mareni wai karna kara tabashi takara fashewa da kuka Aiman zuciyarta tafasa
kawai take tace dena kuka besty wlh zaisan ba’a tabaki azauna lpy ya tsokaloma kanshi tsuliyar
dodo zai gane ruwa ba tsaran kwando bane zai gane yatabamin besty…:evil::evil::evil::evil:
Maman shakur
[10/09 3:45 PM] aishat muh’d:
8DOLE KISONI
Tace i will humiliate him d same way he did to u in public i will disgrace him in such a way that
he will not even dream of coming back to dis school again….Amina ta share hawayenta tace
besty nasan halinki niyamawa bakeba kuma nayafe dan nasan laifi nane dan haka abar
maganan nan Aiman tai dariya tace wlh bazan bar maganan ba kema kin sanni da
naci….Amina ta kalleta tace to meza kimishi???tace karki damu i have a perfect plan…..Amina
tace kinsan dai baida mutunshi ko kadan plz kiyi da kowa amma banda mutumin nan…Aiman
tace kinga mubar maganan nidai nafada miki saina rama miki das all taja motan sai gida…..
Da daddare takasa barci tunani kawai take taya zata wulakanta shi agaban jama’a itama ta
mareshi kaman yanda yay ma kawarta…zuciyarta tace by making him fall 4 u tai wani murmushi
tace yessss……sai kuma tace hw can i make him fall 4 me????tai shiru tana tunani chan tace
yanzu dai i have to know his every move saboda nagane abunda yafiso sai na fito mishi tahaka
wata kilaa yasoni din tai murmushi daganan barci yay gaba da ita…
Maman shakur
[10/09 3:57 PM] aishat muh’d:
9DOLE KISONI
Washe gari da sassafe ta shirya tashiga school duk dan dai doc india dukda department din su
badaya ba ita home economics takeyi shiko bama tasan maiya ke koyarwaba amma tadaisan
doctor ne so tasan yana department dat are related to medical stuff…aikowa tana zaune gaban
laboratory taga yazo zai wuce ga wasu dalibai a bayanshi da sauri tasa glass dan batason
yaganeta yanzu haka tazauna a wurin misalin 1 taga yafito yay salla ranan dai bata shiga class
ba kawai gadin doc india take nafarkon abunda ta lura dashi shine baya wasa da salla komin
lecture din dayake dashi ko kuma yana class dazaran tym din salat yayi zaifito yatafi
masallaci….bayan antashi tadinga binshi saitaga ya tsaya a area E yadau wata mace a mota
suna tafiya tana binsu taga suntafi shagalinku hotel yasauka yarike mata hannu yarinyar harda
mai kiss Aiman tai tsaki tace ashema dan iskane…..
Aiman kwata kwata tama dena attending class kawai all her eyes are on doc india Amina tai
fadan harta gaji….

Maman shakur
[11/09 10:43 AM] Aishat muh’d: [11/09 9:51 AM] aishat muh’d:
10DOLE KISONI
Washe gari karfe 10 tabar gida taci gayu sosai riga dasket tasa na perper less red and black
sumata kyau saita dauko flat shoe dinta shima black and red sanan tasa hijab dinta iya cinya
black saboda dad yahanata sa gyalle cos yarinyar akwai hip sosai ga boobs sosai shima kaman
na namesake zagi tahau motanta sai school
Tana zuwa office din Amir doc india tawuce tana zuwa tai knocking saida tai kusan sau goma
sanan yace tashigo ahankali ta shiga shi yana danne danne laptop saida tai kusa mint goma
atsaye sanan ya dago sai da kirjinshine ta buga yarinyar da tun ranan databuge motarshi yake
nemanta yadade yana ciwon sonta yau gata a office dinshi amma saiya fuske abunku da dan
sarauta girman kai yace yes can i help uuu???
Maman shakur
[11/09 10:02 AM] aishat muh’d:
11DOLE KISONI
Yanda taga yawani kara kyau yay mata kwarjini yasa taji kirjinta ya buga dummm tadanso ta
daburce amma saita tattaro natsuwanta tace sorry sir ina neman doc Muhammad ne nazaci nan
ne office dinshi batajira maizai ce ba tajuya dagudu tana kaiwa daidai saitin kofa kawai tasaki
purse dinta da gangan tabude kofa da sauri tafita…..shikuma yataso yana tsabagen tsoro ta
yarda purse bata saniba yadau purse din ya leka waje amma yaga harta bata yakoma office ya
zauna….yana zama yaji yanason bude purse din yabude yaga card dinta mai dauke da address
dinta da phone number dinta sai byro dakuma wasu pics dinta datayi ba hijabi…wani ma daga
ita sai towel tayi pic din….dakuma ID card dinta na school……
Aiman tana fita ta dinga dariya tace nasan mayen matane dazaran yaga pics nasan dole saiya ji
wani irin …tai kwafa tace zan nunama ba’a taba nawa akwana lpy. ..
Maman shakur
[11/09 10:13 AM] aishat muh’d:
12DOLE KISONI
wuraren 1 Amir yakasa hakura dan jiyayi yakara son yarinyar yadau phone number din yay
dialing saida yakira kusan sau 4 ana 5 dinne ta dauka tawani kashe murya ahankali tace who is
speaking????Amir jiyayi tsigar jikinshi tatashi tundaga kanshi harya tsanshi yace mata wani
masoyinkine kinbar purse dinki a office dina dazu shine nakeson na kawo miki gida daganan sai
muyi magana ko???tai tsaki azuciyarta ..tace ok saikazo kaduba card dina u will see my
address yace nama gani sainazo…
Tatashi tai wanka ta tsantsara kwalliya cikin doguwan rigan abaya tai kyau sosai wuraren 3 yazo
takawo mishi abu sha
Yabata purse din yay mata tayin soyayyarshi bata batallokaci ba ta amince saboda ta kosa
hakonta ya cimma ruwa…zuna zuba soyayya kaman hauka inkaga yanda take mishi saika
rantse son gaskiya take mishi shiko bawan Allah ya mutun mata jiyake komi zai iya mata
aduniya Allah yazuba mishi sonta fiya da tunanin mai karatu….ayaune yadameta yanason yaje
gaida iyayenta kuma yatambayi aurenta
Masu karatu kubiyoni danjin ko zata yarda….

Maman shakur
[11/09 10:25 AM] aishat muh’d:
13DOLE KISONI
Da farko bata yardaba saboda tasan dad baya magana biyu..saikuma tace amma inna barshi
yazo yaga iyayena zai kara trusting dina yakara sona har hakona ya cimma ruwa…tana tunanin
takirashi ya amsa amma yaki magana tace haba luv yimin magana konaji dadi mana yay shiru
tace mishi guess wot??ahankali yace wot tace kazo kugaisa nayarda yadinga murna harda
mata kiss a phone ranan Saturday ya shirya yazo gidan aka saukeshi a falo dad dan dad yace
akawoshi wurin yana zuwa harkasa ya tsugguna yagaida dad da mom….dad ya kurama yaron
ido haka kawai yaji yaron ya kwanta mishi arai yaji kaman yaron nada jininshi yaji yana bala’in
son doc india….dad yace kasaki jikinka my son am ur dad hakafa suka dinga fira da dad kaman
sun dade daga baya dazai tafi dad yarakashi har mota yatafi….
Maman shakur
[11/09 10:33 AM] aishat muh’d:
14DOLE KISONI
Ayaune Aiman ta tashi dawani irin mugun zazzabi ga sanyi datakeji dad sukai rushing dinta
zuwa asibiti likitoshi suka dukufa akanta Lokacin dad da mum ne a waje suna jiran doc sufito
amusu bayani meke damun yartasu…wayar Aiman ce keta ringing mum tace Amir ne kekira
dad ya karbi wayan yace mishi suna asibiti Aiman batada lpy arude kaman mahaukaci yashigo
asibitin ya rirrike dad yace dad ina Aiman dina take hawaye fita kawai suke daga idonshi dad
yace suna daki ya shiga yaga likitoci akanta bamata iya numfashi da kanta saida oxygen gashi
doc kasa komi yayi yadinga kuka saida wani doc yafito dashi daga dakin yakoma ciki..dad ya
karaso shida mum dad yace my son karka damu in sha Allah zataji sauki kadena kuka u have to
be strong
Maman shakur
[11/09 10:42 AM] aishat muh’d:
15DOLE KISONI
Dad yace u have to be strong zata warke kuka yake kaman karamin yaro dad jin kukan nashi
yake har cikin zuciyanshi mamaki yake mesa yakejin yaron nan haka aranshi????anya yaron
nan babu jinini ajikinshi kuwa???y is he soo attache to d boy lyk dis??muryan Amir ne yadawo
dashi daga tunanin dayake yariko hanun dad da mum yana kuka sosai yace dad mum plz
kubani auran Aiman dad zan kulada ita nima ai likitane dad wlh inasonta kaman zan mutu
komameke damunta dad nidai ina sonta haka yay matukar bama su dad tausayi ahankali dad
yashafa kanshi yace my son Aiman yatace ni amatsayin baban ta yau nabaka Auran Aiman
,,yanzu dai kadena kuka kabari inta warke saikaje india kutaho kaida iayayenka adaura muku
aure kajiko amma nabaka yata koda bayan raina ga mamanta shaidace nabaka ita ya share
mishi hawayen…
Masu karatu karku manta annabi (saw ) yace abu uku wasansu gaskene ,gasken su gaske ne
1 saki
2 yanta bawa
3 bada aure dazaran kace nabaka to tabadu…..
Kubiyo dan jin d mystery behind dis novel…
Maman shakur

[12/09 5:26 PM] Aishat muh’d: [12/09 12:48 PM] aishat muh’d:
16DOLE KISONI
Satin Aiman daya a asibiti ta warke maleria ne da typhoid mai tsanani yakamata….kullum Amir
natare da ita itako duk haushi takeji dan tama tsani ta bude ido ta ganshi……
Bayan kamar sati biyu da sallamarsu wataran yazo gidansu suna tare kawai ya kura mata ido
yace Aiman ina sonki sosai ta kalleshi tai fari wanda yake rudashi tace zaka iya fadama duk
duniya in public kana sona????yace mata y not wlh zan iya ta tabe baki tace banyardaba yace
to shikenan gobe karfe 10 mu hadu a lecture theater zan fadama duk duniya in front of all
students cewa ina sonki kece rayuwata abun alfaharina….harcikin ranta taji dadi dan tasan
gobe ne zata aiwatar da plan dinta ….tajuyo ta kalleshi tace to ya zakayi ka hada students a
wajen yace mata yanzu zanje na makala a notice board saboda kowa yazo ya mike yace
barima natafi tarakashi har mota harta juya taji ya janyota ya rungume tsam tsam abunda bai
taba mataba ta daure fuska ta tureshi:evil::evil:me haka??yace yakuri wlh ina sonkine sosai tai
tsaki ta shiga gida tabarshi a wurin…
Maman shakur
[12/09 1:04 PM] aishat muh’d:
17DOLE KISONI
Tana shiga gida tadinga tsaki shege dan iska mena rungume ai nakusa hutawa dakai daga
gobe….takara tsaki ita kadai tace wlh jinake kaman na kashe banzan wanda bai san darajan
mutane ba kawai …..daganan takira Amina tace besty gobe ne ranan dazan rama miki zan biyo
miki mu shiga school tare Amina tace wlh bantaba ganin mai taurin kai irinkiba niyama laifi
nayafe mishi amma ke yanzu kinsashi yana bala’in sonki alhalin yaudaranshi kikeyi besty anya
Allah bazai tambayekiba kuwa???Aiman tai tsaki tace zakifarako nidai nafada miki gobe zanzo
dawuri mushiga school dan haka ki shirya …
*************komawan lbr
Amir (doc India )yana komawa gida yafada kan gado yana wani irin kuka mai tsuma zuciya
yanzu dama yaudaranshi takeyi??? Why??saboda yamari kawarta shine zatamai wanan
wulakancinn??jiyayi ana shafashi yana dago kai yaga Kristina ce karuwarshi tace honey are u
okk???ta balla mata harara yace get out of here tace to menama da karfi yace i said get out
tare da wurgar da kasa da sauri ta mike tabar dakin
Maman shakur
[12/09 1:11 PM] aishat muh’d:
18DOLE KISONI
Da sauri tabar dakin shikuma ya zauna dabas a kasa ya rike kanshi da hannu biyu yama rasa
ina zaisa kanshi yaji dadi shibai damu da wulakantashin datayiba matsalanshi daya sonda yake
mata bazai iya rayuwa babu itaba baitaba son mace kaman Aiman ba yanzu yaya zaiyi
dasonta????ya dinga hawaye ya kwanta a wurin har bacci yadaukeshii bai tashiba sai bayan
isha..yatashi da mugun zazzabi saida yasha magani
Kwananshi biyu yadanji sauki sai dai raman dayayi… tundaga ranan bai kara lekawa ABU ba
Bangaren Aiman kuwa tama manta dawani Amir kuma bata fasa zuwa makarantaba itadai taga
bata kara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login