Showing 120001 words to 123000 words out of 131392 words

Chapter 41 - WUTA A MASAKA COMPLETE NOVELS BY AYSHERCOOL .pdf

ruwana da abinda ya
sameta kai ta shafa kai da ita, kuma hakkina ne ya kama ta, dama ƙarshen karuwa kenan, Allah
ne ya tashi kamata"

Imran ji yai zuciyarsa tana wani irin tafasa, yaji kamar ya shaƙo Ihsan ya kakkaryata kowa ma
ya huta.

Ya dage ya daidaita nutsuwarsa, kawai ya bar falon.

Ta raka shi da harara tace "ai baƙi ciki yanzu ka fara, sema kaga ana ɗaɗɗaure ta, ana kai ta
gidan mahaukata tukuna za kayi bayani"

Ta tashi taje ta sake kunna television ta cigaba da kallonta.

Washegari da asubar fari, ko sallama Imran be wa Ihsan ba ya tafi, ya koma Lagos.

Abba ya dawo Kaduna, ko gida beje ba ya tafi gidan Alhaji Hashim, dan duba Amira, Sedai
shima yayi mamakin ganin yadda Amiran ta koma.

Yaga da gaske sam ba ta son zancen Imran, ga duhu da rama tayi.

Suka tatauna da Anty, suka tsaya akan ai ta mata saukar Alqur'ani ba abunda ya gagari Allah.

Imran yana gurin aiki amma hankalinsa na Kaduna kan halin da Amira ke ciki, kullum cikin
addu'a yake Allah ya yaye mata abun da ke damunta.

Kusan watannin Amira biyu a haka, aka samu ta dena guje guje da ƙoƙarin cire kayan jikinta,
sedai ba ta Magana, dan seta wuni ba tace uffan ba.

Abba ya samu Ammi da faɗa, ya nuna mata matuƙar ɓacin ransa akan rashin nuna damuwa da
halin da Amira ke ciki, dan ko duba ta ba ta je ba.

Ba shiri Ammi tai shirin zuwa duba Amira, saboda tijarar da ta sha a gurin Abba.

Ta fuskanci yadda ran Abba ya ɓaci komai ma ze iya aikatawa, dan haka ta lallaɓa shi, ya kaita
gidan Anty da daddare ta duba Amiran.

Tun da su Ammi suka shiga falon, ta zubawa Ammi ido, Abinci ne a gabanta tana cakala, Anty
na ta takura mata ta ci.

Ammi tayi mamakin yadda cikin Amira yai girma sosai.

Tunda suka shigo, Amira ta ƙurawa Ammi ido.

Abba yace "Amira, ya akayi ne?"

Amira ta fashe da kuka tace "Abba ka ganta ko, ta hana Imran ɗina zuwa gurina, ya dena zuwa
in da nake, ya dena kulani ya tafi ya barni" tai maganar kamar ƙaramar Yarinya tana kuka.

Anty tace "Amira dagaske kina son ganin Imran?"

Amira ta jinjina kai tana kuka tace "bayan ya dena zuwa gurina, kuma ina son in ganshi"

Abba yace "to ai ke kika ce ba kya son yazo in da kike"

"Ni bance ba, ina son in Ganshi"

Abba yace "Alhamdilillah, sauƙi ya fara samuwa, Allah ya krɓa mana"

Ammi tace "haka dama ta koma?"

Anty tace "mhmm, me zamu ce Jamila? Ai naga baki damu da halin da take ciki ba"

Ammi za tai Magana aka kira Abba a waya, yana ɗagawa aka sanar da shi, Imran ya faɗi a
gurin aiki, an kai shi Asibiti jininsa ya hau, baya gane wanda yake kansa ma!!!

Amin afuwa ban editing ba, kuma ina cikin sabgar biki ne, ayi haƙuri.

Ayshercool
07063065680
[2/22, 7:21 PM] Ayshercool:    


WUTA A MASAƘA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND
ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

The experience writer of

*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* WUTA A MASAƘA

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_c
ampaign=in

❌❌❌
Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.

                          51_52



Gaban Abba ya faɗi amma ya dake, cike da jarumta yace "ok to shikenan ba damuwa, zan kira
insha Allah"

Ya ajiye wayar, Amira ta kalli Abba tace "da shi kake waya ko? Ka bani in masa Magana"

Abba yace "ba dashi nake magana a waya ba, wayarsa ba ta shiga amma insha Allah zan
masa magana yazo da kansa ya ganki"

Amira ta jinjina kai tana share hawaye.

Sukai musu sallama suka tafi.

Gaba ɗaya Amira ta zama ita ba me hankali ba, ita ba mahaukaciya ba, se ana zaune lafiya
seta birkice gaba ɗaya ta fara sambatu.

Jikin Abba gaba ɗaya a sanyaye yake, suna tafe a hanya Ammi ta kalli Abba tace "lafiya kuwa?
Naga duk jikin ka a sanyaye?"

Abba yace "lafiya ƙalau, kawai yanayin jikin Amira ne ya ɗagamin hankali gaba ɗaya"

"To ai Addu'a za kai mata Allah ya bata lafiya, bawai ka ɗaga hankalinka ba kasan kaima ba
cikakkiyar lafiya ce da kai ba"

Abba yace "hakane, Allah ya bata lafiya"

Haka suka tafi gida, jungun jungun kamar masu zaman makoki.

Minal tana falo tana kallo suka shigo, bayan Abba ya wuce ne Minal ta kalli Ammi tace "Ammi,
lafiya naga Abba a haka, me kuma ya faru?"

"Mhmm ke ni duk yadda nake tunanin lamarin Yarinyar nan abun ya wuce nan, abun nata ma
dai gashi nan kamar hauka ne dai ya kamata"

"Hauka kuma Ammi?"

"Eh hauka mana, banda haka me zesa ta dinga zabure zabure tana ihu, wai ƙadangaru take
gani, hadda ƙoƙarin yin tsirara?"

"Taɓɗijan kuma fa hakane, Yanzu shikenan ta haukace kenan?"

"To waye yasan mata? Amma abun nata ma hadda Iskanci, daga gani na ta hau kuka wai na
hana Imran zuwa gurinta, salon ta haɗamin wata kutungwilar"

"Kuma dai? Anya ba ƙarya take ba tana sane take wannan abun? In ba haka ba meye dan ta
ganki zata fara kuka tace kin hanshi zuwa gurinta"

"Oho ita ta sani, inma gaske take inma ƙarya take ita ta shafa"

"Ba fa abunda ba zata iyayi ba, kin san tsohuwar karuwa ce, ba duniyanci ko pretending ɗin da
ba zata iya ba, gara ma ai hakan Ammi sa rabu salin alin kinga base kin kashe Auren ba, tunda
baze zauna da Mahaukaciya ba"

"Hakane, dan nima ba zan lamunta ba sam, tunda ta haukace se a raba Aure ga uban ciki tana
fama ga hauka"

Minal ta ɗan taɓe baki tace "Allah ya kyauta, hadda alhakin Anty Ihsan ma da suke ɗauka"

Suka cigaba da hirarrakinsu.

Abba kam da ya shiga ɗakinsa zama yai yayi shiru, abubuwa suka cakuɗe masa yama rasa
wanne ze kama, wanne ze fara tunanin mafita a kai.

Wayarsa ta fara ringing, ya ƙurawa wayar ido, yana tunanin karya ɗauka a kuma sanar masa da
wani tashin hankalin.

Seda ta kusa tsinkewa sannan ya sa hannu ya ɗauka ya kai kunnensa.

"Assalamu alaikum"

Ya amsa da "wa'alaikum salam"

"Barka da dare, Abba Fa'iza ce yayar Amira"

Abba yace "ok Fa'iza kina lafiya? Ya gidan naki ya yaran?"

"Lafiya ƙalau Alhamdilillah, Abba na kira layin Amira ne baya shiga, 'yan kwanakin nan idan na

kirata sedai Antu ta ɗaga ko tace min tana bacci, ko kuma idan ta bawa Amiran sw inji tana
Magana wani iri, tace min bata da lafiya, amma 'yan kwanakin nan na kira wayar tata sam ba'a
ɗauka, na kira ta Imran shima bata tafiya sam, shine ma bugo a taka inji ko lafiya?"

Abba yace "lafiya ƙalau, kin san shi Imran yana fama da wannan aikin nasu, babu isasshen
lokaci, wani lokacin kuma ba lallai in da yake da service ba, ita kuma Amira ba ta da lafiya ne
amma anata ƙoƙari akanta insha Allah zata warware nan kusa"

"Innalillahi wa innalillahi raji'un, Abba meya sameta haka? Ni gaba ɗaya hankalin fa ya kasa
kwanciya na rasa abunyi gaba ɗaya,jikina yana bani akwai matsala"

"A'a ki kwantar da hankalinki ba wata matsala, tana Gidan Alhaji Hashim kuma matarsa tana iya
yinta akanta, kin san tana da juna biyu shine yake bata wahala"

Fa'iza ba dan ta yadda ba tace "To shikenan Abba, ai mata sannu dan Allah"

"Za taji insha Allah mu kwana lafiya"

Tace "Allah yasa"

Abba kam ko bacci kasawa yayi, dan rashin sanin takamaiman halin da ɗansa ke ciki, ga Amira
itama tana fama da tata larurar.

Abba ya tashi yaje ya ɗauro alwala, ya tada salla ya kaiwa Allah kukansa akan iyalan sa.

Allah sarki Anty, Tunda Abba ya tafi basu rintsa ba, saboda ta shiga matuƙar damuwa ganin
yadda Amira ke neman ta sake rikicewa, ta hanasu bacci da koke koke, ita Imran ɗinta.

Sa iya kiran hakan samun cigaba akan lafiyar ta, ko kuma sauyin salon rashin lafiyar ta ta, a
baya bata son ko jin sunan Imran ɗin, amma yau ta birkice ita shi take son gani.

Da fari da murna Anty ta kira wayar Imran, da niyyar yi masa albishir akan cigaban da aka
samu, Amira tana nemansa tana son ganinsa, amma fafur wayar Imran taƙi shiga.

Ta kira yafi sau a ƙirga amma bata shiga, Fadila ma ta kira a wayarta ammma sam ba ta shiga,
ga Amira nata kuka kamar jaririyar goye.

Ƙarshe Anty se allura tai mata sanna n aka samu tai bacci.

Washegari Abba ya fara booking ɗin jirgin da ze tafi Lagos, ba tare da ya gayawa Ammi halin da
ake ciki ba.

Bayan Abba ya dawo Katsam Ihsan ta faɗowa Abba a rai, dan shi wasu lokutan ma mantawa

yake da ita.

Yace "Nikam ina abokiyar zaman Amira ne Ihsan?"

Ammi tace "tana nan lafiya"

"Taje ta duba Abokiyar zaman nata kuwa, nifa ko ɗuriyarta ba na ji"

Ammi tace "eh taje ta duba ta, kasan tana zuwa service ne, shiyasa bata samun zama"

Abba yace "shikenan"

Washegari da sassafe ya bi jirgi ya tafi Lagos.

A cikin Asibitin bariki aka kwantar da Imran, a can ya tarar da Khalid abokin Imran, da yake
shine last wanda sukai waya da Imran, dan haka shi aka fara kira aka sanar masa halin da
Imran yake ciki.

Abba ya kaɗu da ganin halin da ɗan nasa yake ciki.

Yana kwance unconcsoius, se ruwa da yake shiga jikinsa a hankali.

Abba yai shiru yana cigaba da tasbihi da fatan lafiya ga 'ya'yansa.

Imran yayi rama sosai, se tsawon amma duk jikin babu.

Aka rubutawa Abba tasa tasan da ake son aiwa Imran.

Abba yace shi Kaduna ze koma da Imran, yana da ƙwararrun likitoci da suke duba shi da
iyalansa, idan abun yafi ƙarfinsu za su turasu ƙasashen waje.

Khalid yace "to Yanzu Abba haka za'a ɗauke shi mu koma Kaduna?"

"Eh Khalid, dole haka zamu koma Kaduna, ni bana son zaman garin nan, nayi mamakin meke
damunsa haka har ta kai shi ga shiga wannan halin"

Khalid yace "kasan yana cikin damuwar rashin lafiyar matarsa, munyi waya da shi ba daɗewa
aka kirani aka cemin ya faɗi"

"Allah ya tashi kafaɗinsa"

Khalid ya amsa da Ameen.

Sukai processing abun da Yakamata suka koma da Imran Kaduna.

Kai tsaye aka wuce da Imran Asibiti, aka kuma rubuta masa tasa tasai, duk aka kaishi a kai
masa, sedai ya nuna babu Matsala a ƙwaƙwalwarsa partial stroke ne, sedai ana ta ƙoƙarin
samu aga jinin sa ya sauka.


Ammi hankalinta ya tashi, ganin Abba ya fita tun farar Safiya be gayamata in da za shi ba, gashi
har ƙarfe sha ɗaya na dare, be dawo ba kuma baya ɗaga wayarta.

Se sha ɗaya da rabi ya dawo, yana shigowa cikin damuwa tace "Abba meyasa zaka ƙi ɗaga
wayata, kuma ba ka gayamin in da ka tafi ba, duk Hankalina ya tashi"

"Imran ne ba lafiya, naje na ɗakko shi ne daga Lagos, yana nan Kaduna a Asibitin doctor Nura"

A gigice tace "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Imran ɗina ba lafiya amma ka kasa gayamin?
Meya sameshi haka?"

"Kinga ki kwantar da hankalinki, ba wani abun tashin hankali bane, kawai dai damuwa ce ta ɗan
masa yawa, amma yana samun kulawa ta mussaman"

"A'a gaskiya se naje na ganshi, akan me zaka ɓoyemin kaƙi gayamin?"

"A'a ba in da zaki fita, ki bari Allah ya kaimu gobe se kije ki ganshi"

"To Yanzu waye ze kwana da shi?"

"Khalid yana gurinsa, tare muka taho, shine ze kwana da shi"

"Amma wace irin damuwa ce zata dame shi haka har ta kai shi ga shiga wannan halin?"

"Ahh halin da matarsa ke ciki mana, idan ke be dameki ba ai dole shi ze dame shi, tunda yana
zaune da ita tare suke kwana suke tashi, tana masa biyayya daidai gwargwado ai ta cancanci
ya shiga damuwa saboda ita, yanzu da yake naki ɗan ne a kwamce ba lafiya, kalli tashin
hankali ƙarara a fuskarki, kalli damuwa amma waccan da yake ba taki ba ce ba, seda nai surutu
nai mita sannan ki ka je dubata, ban da tsangwama da takura da barazanar zaki sa a saketa da
kike mata, duk ina sane Jamila kallon ki kawai nake yi, bata taɓa zuwa ta sameni ta cemin ga
laifin ɗana ba, ko ga abunda kike zuwa kina musu ba, amma labari yana dawowa kunne na, ki
ƙaddara Ba kya raye Imran yake kan gado Asibiti a kwance ba me temaka masa alhalin kina da
ɗan uwa a raye, amma a barshi ba me kula da shi, kwatankwacin abunda ya faru da Amira
kenan, har in koma ga Allah ba zan dena nanata matata da mu kai Aure sama da shekaru
talatin da wani abu ta kasa min alfarma ba, duk da tarin Alkhairan da ni nai mata ba"

Jikin Ammi ne yai sanyi, tai shiruu tana nazari, Yanzu kenan ace ba ta raye Imran ze iya shiga
wani hali makamancin wannan ace bame zuwa kansa balle ya kula mata da shi? To amma ta
yaya zata riƙe Yarinyar da ta gama lalacewa, bayan ga ta da ɗiya mace ita ma, idan ta koya
mata Mugun hali fa? Haka tai shiru tana cigaba da tunani, ga batun Imran na kwance a gadon
Asibiti ga wannan maganganun da Abba yai mata.



Washegari tun da safe Ammi ta shirya, tai girki ta sanar da Minal halin da Imran ke ciki, ta kira
Hadiza ma ta sanar mata, taita kiran wayar Ihsan amma ba ta shiga dan haka ta ƙyaleta.

Abba a gajiye yake sosai, dan haka su Ammi ne suka fara yin gaba, yace ze zo daga baya.

Cikin ikon Allah ko da suka je Asibitin suka tarar Imran ya farfaɗo, har Khalid ya kai shi yai
alwala, ya Bashi Abinci ya kwanta.

Ammi ta ƙarasa gaban gadon Imran da sauri, tace "Imran sannu ya jikin naka"

Jinjina kai yayi alamar da sauƙi.

"Kai kam Imran me kasa a ranka haka kake neman ka halaka kanka da kanka, da ƙuruciyarka
amma ace jininka yai irin wannan hawan har abun ya kai ka ga faɗuwa"

Shiru Imran yai ya lumshe ido be ce Komai ba, shika ɗai yasan meyake ji game da Amira, yana
cikin tsananin fargaba da tashin hankali akanta, ga tausayinta da yake ji sosai, tun asalinta a
wahala ta tashi, ya Aureta nan ma bata sauya zani ba, lokacin da yake ƙoƙarin ya bata farinciki
iya iyarwasa kuma ga ƙaddara ta larura ta sameta, ga pressure Ammi da ta Ihsan, amma still a
haka Ammi ke tambayar dalilin da yasa ya shiga damuwa.

Aka dinga zuwa dubiyar Imran a Asibitin nan, wajen azahar Anty tazo duba Imran dan sam bata
san Imran ba lafiya ba.

Tunda Ammi taje Imran be Magana ba, sedai Anty na zuwa ya buɗe baki a hankali yace "Anty
ya jikin mata ta?"

Seda haushi ya kama Ammi, taji kamar ta kwaɗe shi amma ta dake ta basar.

Minal kuwa sallama tai musu, ta tafi gida domin ɗora sanwar rana.

Anty tace "jikinta da sauƙi Imran, ya naka jikin?"

"Alhamdilillah"

"Allah ya ƙara afuwa, ai se ɗazun nan Abban naka yake gayamin kana Asibiti, kuma an samu
cigaba sosai a rashin lafiyar tata, tana ta tambayar ka"

Murmushi Imran yai yace "yanzu tana son ganin nawa kenan?"

"Ƙwarai kuwa, dan tana ta faman daru, ita ka tafi ka barta bari in kira maka ita a wayar Fadila"

Ammi taxe "A'a Hajiya Nafisa, baya jin daɗi be kamata a sake ɗaga masa hankali ba"

Da sauri Imran yace "A'a ni dai Anty kiramin ita"

Ammi tace "a hakan kana kwancen zaka iya Magana?"

"Eh Ammi, a kirata yau watana biyu rabona da ita, a kiramin ita dan Allah"

Anty ta kira layin Fadila tace ta bawa Amira.

Amira tana kwance tana wasa da gashin kanta, Fadila ta miƙa mata wayar.

Amira ta karɓa ta kara a kunnenta, sedai shiru be ce komai ba, itama ba tace komai ba sukai
shiru na wani lokaci, Imran ne ya fara sauke ajiyar zuciya, da fari Amira ba ta san waye akan
wayar ba, seda taji yai ajiyar zuciya, tana jin ajiyar zuciyarsa ta fashe da kuka tace "Amran ka
tafi ka barni ko"
Lumshe idon sa yayi, sega hawaye na gangarowa daga idon Imran a hankali yace "Ai kece kika
ce ba kya son ganina"

"A'a ni bance ba, ƙadangaren jikinka ne bana son gani, amma ina son in ganka dan Allah ka
dawo, mu koma gida dan Allah, na daɗe ban ganka ba"

Ajiyar zuciya ya kuma yi, yana murmushi, duk da hawaye na bin gefen idonsa yace  "Nima ina
son in ganki, ki bari idan na dawo daga Lagos zan zo har gidan Anty in ɗauke ki mu koma gida"

Murmushi tai tace "to idan zaka dawo zan maka girki da kaina, zanje gida in wanke maka
kayanka, in

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login