Showing 1 words to 3000 words out of 131392 words

Chapter 1 - WUTA A MASAKA COMPLETE NOVELS BY AYSHERCOOL .pdf

[12/30/2021, 8:13 PM] Ayshercool: .🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥





WUTA A MASAƘA





Page 1







PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND
ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* Anda no WITA A MASAƘA


SADAUKARWA GA ƘUNGIYAR PERFECT WRITERS ASSOCIATION, DOMIN TAYA MURNAR

CIKA SHEKARU BIYU DA KAFUWA


jinjina ta musamman ga

Swt Sisyna (Nanatou) Allah ya bar ƙauna.
Me gayya me aiki shugaba a bar koyi Safna Aliyu Jawabi.
Sa'adatu Abdullahi Madubi (My red)
Anty Asmy Jafar
Mummyna Nafisa Ummu É—ahira
Da dukkan membobin ƙungiyar perfect writer's association




Godiya ta musamman ga, iyayena ƙawayena 'yan uwa da abokan arziki, tare da masoyana a
duk inda kuke a faÉ—in duniya.


Alhamdilillah, ina miƙa Godiya ta ga Ubangiji maɗaukakin sarki, yadda na fara a sa'a Allah yasa
in gama a sa'a.






https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_c
ampaign=in



Domin gyara, sharhi ko shawara
07063065680


            


_ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH, GASHI YA DIRA DA ZAFINSA, GAJEREN
LABARINE ME TARIN ILIMANTARWA DA NISHAÆŠANTARWA KAFIN ZUWAN LITTAFIN
RUƊUN ƘURUCIYA, COMMENTS ƊINKU KAWAI NAKE BUƘATA, BAZAN DINGA POSTING
KULLUM BA, SANNAN BABU LALLAI IK DINGA DOGON PAGE, SANNAN DAN ALLAH

BANDA BIYONI PC ANA DAGA FARKO, ZANYI IYA ƘOƘARINA INYI SHARING GROUPS,
KUMA KU DINGA TAYANI SHARE PLEASE, COMMENTS ƊINKU KAWAI NAKE BUƘATA, GA
WANDA BASU KARANTA LITTAFIN AƘIDATA BA, KARKU BARI A BAKU LABARI, KUZO IN
BAKU PART1 KYAUTA KU SAI 2&3 AKAN FARASHI ME SAUƘI, TAKU HAR KULLUM
AYSHERCOOL_


BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM







Da misalin ƙarfe goma na dare, Gari yayi shiru, wasu daga cikin al'umma sun adana kawunansu
a cikin gidajensu, domin hutawa rayukansu hidindimun da akayi da Rana.

Sedai a ɓangare guda kuma sautin kiɗane ke tashi a wani ƙaton ɗakin taro, mutane nata shiga
da fita kamar Rana, se kaiwa ake ana komowa da Abinci da abin sha kala kala, da gani base ka
tambaya ba kasan bikine ake na masu hannu da shuni, duba da haÉ—uwa da tsaruwar É—akin
taron, da kuma kalar mutanen dake zarya a gurin, da uwa uba danƙara danƙaran motocin dake
fake a harabar gurin taron.

Ango da amarya na kan high table suna kallon wanda suka halarci bikin nasu, Yayin da
ƙawayen amarya da abokan ango, dangi 'yan uwa da abikan arziki keta cashewa a filin rawa,
anata bajinta gurin zuba musu kuɗi, dj se ƙara zigasu yake suna ɓarin kuɗi yayin da matan keta
cashewa.
MC ne ya fara magana ta speaker yace "Masha Allah, gaskiya na yadda wannan bikine na
masu arziki, madalla ƙawayen amarya da abokan ango ina godiya da wannan bajinta da ku ka
nuna, da kuma kara da ku ka yiwa Amarya da ango, sedai ana tsaka da wannan shagali na
samu sanarwar, isowar wasu hamshaƙan jiga jigan baƙi da suka amsa gayyata domin tayamu
nishaɗi a wannan biki na 'ya'yan gata, wannan baƙin ba kowanne bane face DJ Sultan, tare da
'yan tawagarsa na rawa, ciki hadda wannan tauraruwar taku, wadda ludayinta ke kan dawo,
tauraruwarta ke haskawa a cikin manyan yara da suka yadda da kansu wajen iya cashewa,
wato gimbiya Amira, nasani ga dukkan wanda suka saba zuwa guraren taron biki, birthday da
makamantan su, da duk wanda yasan dj Sultan da tawagarsu nasan sun san wannan gimbiya,
kai ga wanda bema santa ba yau ze santa, zatazo ta baje mana baiwarta ta nishaÉ—antar damu,
ina fatan kuma zaku nuna mana farincikinku ta hanyar nuna bajintarku, DJ idan ka shirya,
Sultan da jama'arka muna buƙatar ganinku akan stage"

Wata waƙa aka saka me sanyi, wasu mazane suka dinga fitowa, suna sanye da baƙaƙen

wanduna da fararen riguna, bayanta an rubuta Dj Sultan, sekuma sunayen su a ƙasa, su huɗu
haka suka zo suka jeru a tsakiyar filin, suka sunkuyar da kai, kamar masu jiran umarnin wani,
sumarsu duk ta sha dying, kowanne da kalar askinsa, wanine ya kuma shigowa filin shima,
sanye da shiga irin tasu, ga uwar suma akansa se ƙyalli take ya tsaya a cikinsu suka zama su
Biyar.

Mutane sun zuba ido  suna jiran ganin gimbiya Amira, kowa ya zuba ido wasu tyni sun zaro
wayoyi zasu É—auka, amma aka shafe wasu mintuna bata bayyana ba, se jan rai da ake yi, har
wasu suka fara ƙosawa.

lokaci ɗaya aka canza waƙa, aka saka wani kiɗa me sauti da ɗaukar hankali, Ta wata ƙofa ta
fito, sanye da crazy jeans, da baƙar riga, ta ɗaure kanta da siririn ɗan kwali ta zubo kitson
gashin doki da tayihar ɗuwawunta, ƙafarta sanye cikin wani uban takalmi kamar na sojoji, tana
da matsakaicin tsayi, idanunta kamar na Japanese, tana da dogon hanci, sedai ba fara ce tas
ba, tana da shape É—in jiki me kyau, dan kayan sun zauna a jikinta sun kamata tsam tsam a
jikinta, kana ganin duk wani shape na jikinta, kallo É—aya zaka yi mata kaga yarinya ce É—anya,
dan dudu ba zatafi shekaru sha shida zuwa sha bakwai ba, amma tana da jiki me kyau da
É—aukar hankali.

Yanayin tafiyar da take, yana tafiya daidai da sautin kiÉ—an dake tashi, shewa mutanen hall É—in
suka shiga yi, suna tafa mata dan yadda take tafiyar cike da É—aukar hankali da burgewa,
tsakiyar mazan nan taje ta tsaya, tana tsayuwa suka É—ago kansu daga sunkuyarwar da sukayi.

Wani irin kiÉ—a aka saki, aikuwa suka fara rawa a tare, sedai yadda Amiran take rawa kamar ba
jikin ɗan Adam ba, Kamar me jikin roba, tafi mazan nan iya sarrafa jikinta cikin ƙwarewa da jan
hankali, duk inda ta karya jikinta kota lanƙwasa haka mazan nan keyi, duk wani tsalle da juyi
haka itama ke yinsa, attach É—in kanta na bajewa.
Nan da nan hall ya ɗau shewa, masu video nayi Masu hotuna nayi, nan aka shiga ɓarin kuɗi
akan Amira.

Sunyi rawa kala kala Babu alamar Amira ta gaji da rawar nan, suka nishaÉ—antar da mutane
sosai, agogon hannunta ta kalla, ta silale daga kan stage É—in, se nemanta akayi aka rasa.

"Mungode mungode, DJ Sultan da tawagarsa, jinjinar ban girma ga Gimbiya Amira, munagodiya
da wannan gudunmawar da aka bamu, Muna fatan Allah ya maida gimbiyarmu gida lafiya"

Amira kuwa zuwa tayi ta canza shiga, ta saka doguwar riga akan kayanta, kamar ba ita tayi
wannan uwar rawar ba.

Zagayawa tayi inda dj suke zaune, tace  "Sultan, yau mun samu kuɗi sosai, bani 10k zan hau
Mota, senaji alert"

Sultan ya kalleta Yace "ke Amira, har 10k?"

"Eh ko ba zaka bayar bane?"

Sultan yace "A'a, ni na isa ince bazan bayar ba? Ni a wa?"

"Dalla ka hanzarta ka bani, zan tafi gida inje mu fafata, kuma fitar yau tayi kyau, dan mun samu
kuÉ—i wallahi maga ba dai dai ba zanyi dirar mikiya a Chamber inyi rashin mutunci"

Sultan yai murmushi yace "ki huta gimbiya, bame miki ba daidai ba ai girmanki ne, in bake babu
mu" ya ƙarasa maganar Tare Da ƙirgo kuɗi ya bata.

Yayin da aka cigaba da shagalin biki, ita kuma ta silale tai waje abunta, agogon hannunta ta
kalla, sha biyu saura na dare, kuma gurin bikin ma basu da niyyar tashi yanzu.

Cikin hanzari ta fita titi, duk babu masu abun hawa, se  ɗaiɗaiku, ji take tamkar ta rufe ido ta
ganta a gida, dan ta san yau da drama.

Wata uwar ƙatuwar motace ta alfarma tayi parking a gabanta, aka sauke glass ɗin motar.

Wani Babban mutum ne a ciki, wanda a ƙalla ze kai shekaru hamsin da biyar, ya kalli Amira
Yace "Baby ina zuwane muje in sauke ki?"

Ƙare masa kallo tayi, ta ɗauke kanta.

"Haba Me kyau, be kamata kiyi ta tsayuwa a gurin nan ga dare ba, ina zakiyi".

"Hausawa zanje" ta bashi amsa.

"Ok shigo in saukeki Mana"

Ba tunanin komai, Amira ta buɗe gaban motar ta shige abunta, wani sanyi da ƙamshin turaren
jikinsa sun gauraye cikin motar.

Ya fara jan motar a hankali, ya kalleta Yace "Gimbiya Amira, kinci sunan naki gimbiya fa,
gaskiya kin nishaÉ—antar damu sosai, na daÉ—e banga 'yar baiwa ba kamarki"

ÆŠauke kai tayi kamar bata san meyake cewa ba, ya É—an kalleta Yace "magana fa nake
Gimbiya"

Maimakonsa ta bashi amsa, se tace "Idan kaje zoo road zan sayi abu"

"Meye abun?"

"In munje ka gani" ta bashi amsa

Yaita surutunsa amma taƙi Magana, suna zuwa gurin masu gasa kaji tace "yawwa ɗanyi
parking, zan sai kaza"

Yace "haba Amira, aiba girmanki bane, bari inje in siyo miki"

Bata kuma cewa komai ba, ya fita daga motar, ya É—an jima sannan ya dawo motar, hannunsa
ɗauke da manyan ledoji, ɗaya na kaza ɗaya kuma na abun sha, ya miƙa Mata.

Tasa hannu ta karɓe tace tagode.

Tai tayi masa kwatance har sukazo bakin wani layi, ta kalleshi tace "Nagode fa a nan zan
sauka"

"Ahh haba dai, mu ƙarasa inga gidannaki mana"

Ta kalleshi tace "gidana kuma? Kaga a nan zan sauka zan ƙarasa"

"Amma Yakamata muyi exchanging number, sannan ai Yakamata muyi sallama"

Amira tace "Yallaɓai wace sallama kuma?"

Ya wani matso daf da ita yana ƙasa da murya Yace "haba Gimbiya, wannan ai ƙwalele ne, duk
yadda kikaje kikayi wannan karairayar kice zamu rabu ba sallama haba Baby"

Yai maganar yana ƙoƙarin naniƙar Ameera, hannu tasa zata buɗe motar amma taji a rufe, ta
juyo a fusace tace "malam ka buÉ—emin in fita, bana son iskanci fa"

"Wane irin bakya son iskanci, nifa bana son wani kame kame, meye na wani damuwa ko ɓoye
ɓoye, bayan kin nuna wace ke, kinyi talla na biyo kuma kiƙi siyarwa, kinga in dai kuɗine baki da
Matsala, zan kashe miki ko nawa ne"

Zaro ido tayi tace "dagaske?".

Da sauri ya jinjina kai Yace  "ƙwarai dagakse mana"

Kamar abun arziki ta zira hannu a rigarta, ba zato ba tsammani ta zaro wata 'yar ƙaramar wuƙa,
se ƙyalli take ta kalleshi tace "Wallahi, idan har baka buɗemin motar nan na fita ba, sena yanka
wannan ubsn tumbin naka da wuƙar nan, kuma in toshe duk wata hanya da za'a gane nina yi".

Zaro ido yayi Yace 'ke kina mace kike yawo da wuƙa haka, har kike iƙrarin zaki kasheni?"

"Saboda irinka nake yawo da ita ai, dan naje nayi talla se akace maka kowane jaki nake
sayarwa, ko ana ciniki ta dole ne, na kasa ka taya, nace bazan siyar ba, base ka ƙyaleni ba, ni
harƙallata ba kowa nake siyarwa ba seme rabo ina fatan ka gane?".

Yadda Amira ke maganar cikin ɓacin rai da zazzaro ido, suka tabbatar da zata iya aikata Abinda
tace, cikin hanzari ya cire lock É—in, ta buÉ—e motar da sauri, ta É—auki ledar kazarta ta shige wani
layi me duhun gaske.

Tana shiga ta cire takalmanta, ta riƙe a hannu ta kasa da gudu tai cikin layin, a bakin ƙofar wani
gida tai birki, ta dinga sauke numfashi, seda ta dawo hayyacinta sannan ta shiga gidan cikin
sanÉ—a.

Babu kowa a makeken tsakar gidan, dan haka ta ajiye takalmanta ta shiga cikin wani É—aki ta
ajiye jakarta da ledar hannunta ta fito tsakar gidan.

Hanyar banɗaki ta nufa, cikin sanɗa amma taji ance  "daga ina kike dan ubanki?".

Cak ta tsaya ta juyo a hankali, wani matashine a tsaye yana huci, da zazzare ido.

"Nace daga ina kike?" Matashin Ya maimaita tambayar cikin tsawa.

"Daga neman na kaina" ta bashi amsa kai tsaye.

"Ni kike gayawa neman na kanki kika tafi? Kin tafi yawon karuwancinki shine se yanzu zaki
shigo mana gida, kina ta zubar mana da mutunci a idon duniya, to bari kiji in gayamiki daga yau
se yau idan kika kuma tafiya yawon iskancinki kikayi dare, to karki shigo mana gida, ko kuma ki
tarkata kayan ki ki shiga duniyar gaba É—aya ki bar mana gida, zefi miki kwanciyar hankali"
"Ai wallahi tallahi babu É—an matar daya isa ya koreni daga gidan nan, dan gidan ubanane, kuma
karuwanci sana'ane, wani idan ya kasa nasa kasuwancin ba'a siya, nikuwa Alhamdilillah, idan
na kasa har wawa ake, kuma wallahi yanzu na Fara"

A harzuƙe yace "ni kike gayawa haka?"

"An gaya maka É—in, haifata kayi da bazan gaya maka ba?"

Cikin zafin nama ya kai mata mari, ta goce da sauri, ta ware muryarta a wannan daren ta shiga
kurma ihu, ga gari yayi shiru saboda dare amma ta dinga kurma uban ihu.

Wani dattijo ne ya zare sakatar wani É—aki ya fito Yace "idan kanawa ma'aikin Allah Usman ka
ƙyale yarinyar nan, karta tara mana jama'a ni wallahi lamarinta tsoro yake bani yanzu"

Usman yace "wallahi Baba dan taga ana ƙyaleta ne, duk ta zubarwa da mutane mutunci
maimakon tayi iskancin nata a ɓoye amma seta nuna duniya ta sani, shegiya karya"

Amira tace  "wallahi niba karya bace, kuma wallahi ka kuma yunƙurin dukana sena maka illa, ko
in sa a zanemin kai wallahi, dan yanzu ba da bace"

Usman Yace "kana gani ko Baba?"

"Ƙyaleta duniya ce, wanda bezo bama jiransa take, rabu da ita abokin yi take nema"

Haka suka koma ɗakunansu suka ƙyale Amira.

Ta shiga banÉ—aki ta fito, taga yadda kowa ya rufe É—aki yana bacci, ta nufi inda ake girki, ta
bubbuÉ—e kwanuka, amma ba'a bar Mata Abinci ba.

Ta kalli kwanukan, ta sake kallon yadda kowa ya rufe ƙofa yana bacci, tace 'wallahi tunda aka ƙi
ajiye min abinci se kowa ya tashi"

Ta ɗakko ƙaton murfin tukunya ta fito tsakar gida, ta saita ƙofar ɗaki ɗaya ta jefi ƙofar da ƙarfi da
murfin babbar tukunya, nan take ya bada wani razanannen sauti, wanda ya sanya wanda suke
É—akin kurma ihu, kafin su gama ihun ta sake jefa wani murfin, nan da nan ta tashi da yawa daga
ilahirin mazauna gidan, ba iya na cikin gidan ba harda maƙota, suka tashi a firgice.
"Amira, baki da hankali? Wane irin dabbanci ne wannan? Meye haka kika yi?"

"Ba dole inyi rashin mutunci ba, dan wulaƙanci ace baza'a ajiyemin Abinci ba, sedai ayita sani
aiki kamar jaka a gidan nan, wallahi idan ba'ayi wasa ba sena tada balli, a raba gidan nan a
bani gadon ubana a ciki, idan yaso in dinga ci da kaina, tunda an maida ni mara galihu a gidan
nan"
Wata matace ta É—ora hannu a ka tana faÉ—in "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, wannan wane irin
bala'i ne? Wace irin annobace wannan? Shikenan bamu da kwanciyar hankali a gidan nan,
saboda wannan sheÉ—aniyar yarinyar?".

Usman Yace "ka gani ko Baba, daka bari ɗazu na jiƙa mata jikinta da duka, da duk haka bata
faru ba"

Baba yace  "duka kuma na nawa? Wane irin dukane ba'a mata ba, wannan yarinyar bata da
rabon shiriya, kamar jaka haka take, wallahi ina ga gurin 'yan Hisba zan kaita bazan iya ba taf"

"Kokuma ka tattara ka maida ita gurin wan uwarta ba, tunda yafi mu arziki"

Amira tace  "ba gidan uban da zanje in zauna, nan ne gidan su Ubana wallahi ba inda zani, in

kun gadama ku Kaini prison, ku zaku tonawa kanku asiri ba ruwan Amira".

Abun takaici ta shige ɗakinsu ta rufo ƙofa, harda saka sakata, ta barsu a tsakar gida suna
cigaba da masifarsu suka ɗai, ɗaya daga cikin wanda suke kwance a ɗakin ta kalleta tace  "dan
Allah karki shigo muma ki tayar mana da hankali, ki buɗe mana ƙofa zafi mukeji"

Amira tace "bazan buÉ—e ba, wallahi idan baki wasa ba, zamu zauna ba bacci yau se Asuba"

"Allah ya baki haƙuri"

Ɗayar kuwa da take cikin bargo tsaki tayi tace  "wallahi Allah ya isa hanamu baccin da kika yi"

"Asiya kika yiwa Allah ya isa bani ba"

A fusace ta yaye bargon ta tashi zaune tace "karki kuskura ki sake zagarmin uwa"

"To uwatace da bazan zageta ba, an zageta Asiya kikayiwa Allah ya isa, Allah ya ban haƙuri da
ake zagin tawa uwar"

Zata kuma magana ɗayar tace  "dan girman Allah Sadiya ki ƙyaleta, abokin yi take nema,
ƙyaleta da halinta"

Sadiya tayi ƙwafa tace  "matsiyaciya kawai"

Amira tace  "nice ma Usman, ba sana'a se zaman banza da sa ido da kurin dukan mace"

Haka suka ƙyale Amira, dan yanzu kusan ƙarfe biyu da rabi na dare ne, idan suka biyeta baza
suyi bacci ba.

Ta gyara zamanta, ta É—akko ledar kazarta ta shiga ci tana korawa da sassanyar madara, suna
jin ƙamshi da yadda take tauna ƙashi, amma ba wanda ta bawa.

Seda ta kammala, tayi gyatsa sannan ta nemi gurin kwanciya, Allah ya isa kam ta sha ta a gurin
mutan gidan harda maƙwabta.

Da Asubar fari ta tashi, ta gabatar da sallar Asuba, ta koma cikin bargo tai kwanciyarta.

Bayan gari yayi haske mutanen gidan suka dinga fitowa É—aya bayan É—aya, kasancewar gidan
family house ne, me É—auke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login