Showing 3001 words to 6000 words out of 131392 words
Chapter 2 - WUTA A MASAKA COMPLETE NOVELS BY AYSHERCOOL .pdf
da mutane da dama a ciki, ɓangare ɓangare ne a gidan, amma duk
'yan uwane.
Sashin su Amira suka dinga haÉ—uwa, suna maida yadda akayi na hanasu bacci da Amira tayi
daren jiya, fitinar Amira ta fara addabawa mutan gidan nesa ba kusa ba.
Suna cikin tattaunawarne wani babban mutum yai sallama shida wannan dattijon na jiya da
daddare wato Baba, suna ganinsa suka ce "Yawwa, barka da zuwa dama kai muke jira Baffa"
Sadiya tace "Ai wallahi Baba gara da kaje ka taho da Baffan, tunda shi tana jin tsoronsa, haka
kurum duk mutuncinmu ya zube a idon mutane saboda Amira, ta addabi kowa bata jin maganar
Kowa, ai gara da kazo daren jiya ko rintsawa bamuyi ba, saboda tijararta"
Wanda aka kira da Baffa yace "ku barni da ita, ina makirar take?"
"Tana É—aki tana bacci" cewar mahaifiyarsu Sadiya.
Baffa yace "tasomin ita dan ubanta, yau zata yabawa aya zaƙinta"
Sadiya ta tafi É—akinsu da rawar jiki, "Ke Amira ki tashi ana kiranki"
Tai maganar tana dukan katifar Amira, maimakon ta tashi sema taja tsaki, ta sake shigewa
bargonta.
"Ke Amira kirankifa ake yi"
"Ke dalla malama ƙyaleni, in kinga na amsa wani kira tona Allah ne, babu 'yar ƙatuwa ko ƙaton
dazesa in fita tsakar gida Yanzu"
Sadiya tace "jar uba, Baffa salahun ne ɗan ƙatuwa"?
Zumbur Amira ta tashi zaune, kafin tayi magana Baffa Salahu ya shiga bubbuga ƙofar ɗakin
yana cewa "zaki fitone kizo kiran da nake miki ko sena shigo?"
Cikin zumɓura baki Amira ta sakko daga kan katifarta, ta ɗau wayarta ta saka a aljihu, ta ɗau
kuɗaɗen ta suma ta saka a aljihun wandon dake jikinta ta fito, maimakon ta nemi hijjabi ta
suturta jikinta, amma ta fito a haka, gajeren wando ne a jikinta, da wata matsatsiyar vest, ta baje
kalbar attach dake kanta.
Baffa Salahu yace "Ke baki da hankali baki da É—a'a ko? Shine kika fito a haka saboda baki da
Kunya?"
"To waini ya zanyi? Idan na tsaya saka hijjabi masifa zakayi min, yanzuma kuma ban tsira ba".
Baffa yace "nine nake masifar ko? Amira ba kiwa kanki adalci ba wannan mumunnar rayuwar
da kika ɗauka, kina 'ya mace da iliminki da komai amma kika zaɓi yawon ta zubar, duk
danginmu bamu taɓa samun wanda yai abunda kika aikata ba, abun kunya kamar wanda kike
ba'a taɓa samu ba wallahi".
Amira tace "Baffa wane irin abun kunya kuma? Nifa ban taɓa cikin shege ba"
"Ni kike gayawa baki taɓa cikin shege ba? To je kiyo cikin shegen karki fasa dan ubanki, idan
akace a rayuwa 'yar Habiba zata yi karuwanci, za'a ƙaryata hakan amma segashi kina zubar
mana da kima da martaba a idon duniya, daga uwarki har ubanki babu mutumin banza kaiconki
Amira, kaico".
Wani irin abune ya tokarewa Amira a zuciyarta, taji kamar ta fasa ihu, amma tai shiru ta
sunkuyar da kai, Baffa nayi Baba nayi, su Yaya Usman ma suka saka baki, aka dinga mata faÉ—a
da tashin hankali a ka, gashi Amira ta tsani faÉ—a a rayuwarta.
Seda suka yi me isarsu, Baffa yace "duk ranar data kuma fita gantali tayi dare, ko Usman ko
Zailani a cikin mazan gidan nan, a samu wani yai mata dukan tsiya, sannan duk randa ra kuma
yiwa wani rashin kunyar ko iyashege azo a gayamin, se naci mutuncinki Ja'ira mara kamun kai,
kuma daga yau ko ƙofar gida kar a sake bari ta fita, wuce kije ki tattare wannan kwanukan ki
wanke, ki É—ora abincin safe, dan matan gidan nan ba bayinki bane suda yaransu, a wanke a
É—ora a dafa a baki kici, kuma ki cika musu ciki da iskanci ba"
Amira ta kalli uban wanke wanken dake zube a gurin, da uwar tukunyar da ake É—orawa a gidan
dan girka Abinci, ta kalli furfurar dake kai da gemun Baffa Salahu, tabbas ba dan wannan
furfurar ba da seta yanka masa rashin mutunci.
Amma lokaci ɗaya ta sauya kamar ba ita ba, cikin ladabi tace "zanyi insha Allah, zan wanke
kwanukan sannan zan dama kunun karyawar, Allah ya baku haƙuri"
Kamar gaske ta nufi inda murhu yake, masu zagi na cigaba da zaginta, suna faÉ—ar albarkacin
bakinsu, taje ta iza wuta ta miƙe tai hanyar banɗaki, tana zuwa ta suri hijjabi a jikin katanga, tai
waje da gudu....
Ayshercool
07063065680
[1/2, 11:06 AM] Ayshercool: í ½í´¥í ½í´¥í ½í´¥í ½í´¥í ½í´¥í ½í´¥í ½í´¥í ½í´¥í ½í´¥í ½í´¥í ½í´¥
        WUTA A MASAƘA
       Â
             Page 2
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND
ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P. W. A
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* Anda no WITA A MASAƘA
SADAUKARWA GA ƘUNGIYAR PERFECT WRITERS ASSOCIATION, DOMIN TAYA MURNAR
CIKA SHEKARU BIYU DA KAFUWA
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_c
ampaign=in
   Â
         Page2
Amira na jin yadda aka biyo ta ana ƙwala mata kira, amma ta arta da gudu tayi waje, a ƙofar
gida ta ƙarasa saka hijjabin data ɗakko akan katanga, tai titi a guje, ta hango wani me napep ta
É—aga masa hannu, ya tsaya ta shige tai gaba abunta.
Baffa ya tasaya yayi saroro, yace "haka yarinyar nan ta zama? Inyi mata magana amma ta zari
hijjabi ta gudu"
Baba yace "kaɗan ma ka gani, ba abinda ka gani kai kana gefe, mutanen dake cikin gidan nan
mu zamu ƙarar da iya shegen da yarinyar nan take yi, iskanci da rashin mutunci iri iri, haka take
aikatawa"
Ya jinjina kai yace "lallai lamarin yarinyar nan ya gawurta, idan ta dawo gidan nan, ɗaureta
za'ayi a mata shegen duka, duk inda taje zata dawo ai, koma a sakata a mari kowa ya huta"
Nan suka cigaba da kwashewa Amira Albarka, Amira kam taiwa me napep kwatancen inda ze
kaita.
Ana zuwa inda zata sauka, ta sauka ta bashi kuÉ—insa, ta shiga wani layi.
Allah ya temaketa, da kuÉ—inta da wayarta suna cikin aljihun Wannan wandon nata.
Ƙofar wani ƙaramin gida taje, ta ƙwanƙwasa ƙofa, ta buga ya kai sau uku sannan aka zare
sakata aka buɗe, namijine ya buɗe wanda aƙalla ze kai shekaru talatin da biyu, ya kalleta yai
murmushi yace "Anty Amira ashe kece, sannu da zuwa"
Yai maganar yana bata hanya, tace "Yawwa, tana nan kuwa?"
Yace "Gaskiya taje kai Khalil Asibiti baya jin daÉ—i, Khairat kuma na makaranta"
Abunda ya faÉ—a É—in be hana ta sa kai ta shiga cikin gidan ba, kai tsaye ta wuce falo ta samu
guri ta zauna, sannan tace "Abban Khalil meya samu É—ana, da har aka kaishi Asibiti?"
Abban Khalil yace "wallahi zazzaɓi yake yi, bari inje in dawo yanzun nan"
Amira tace "to shikenan"
Yasa kai ya fita, ta kunna kallo ta miƙe akan kujera abunta, ya kai mintunta goma sha biyar
sannan ya dawo, daya dawo É—inma yai sallama ta amsa kitchen ya wuce.
Amira tana ta chatting É—inta, aka jima segashi ya shigo da faranti É—auke da kayan tea, harda
soyayyan ƙwai yace "tunda naga kin mana dirar safiyar nan, nasan baki karya ba kuma mu
mun cinye namu"
Amira ta kalleshi tace 'dana san wahala zakamin haka da tabbas bazan bari kayi ba"
"Wannan É—inne wahala? Tashi ki karya malama kafin in fushi Yanzun nan"
Amira tai murmushi tace "Allah ya baka haƙuri, Nagode".
Ya fita ya bar mata falon, ta zauna ta karya, ta fito da kwanukan tsakar gida ta tarar yana ta
harhaÉ—a kwanuka ze wanke.
"Abban Khalil, me zakayi haka? Ka bari idan ta dawo tayi mana"
Yai murmushi yace "ahh haba dai, ya za'ai ta tafi kai yaro Asibiti ban rakata ba, in bar mata aikin
gida bayan ban san lokacin da zata dawo ba, ai gara in rage Mata"
Amira tace "kaga É—an aljanna, ka barshi zan mata aikin kafin ta dawo".
Yace "A'a, ke ai baƙuwa ce"
"Kaji ka wai baƙuwa, Allah ka bari zanyi ka tafi kasuwarka"
Da ƙyar ya yadda ya tafi, ta tarar har wake ya dafa saura shinkafa, ya bar kuɗin siyan salak, ta
jinjinawa haƙuri da tausayi irin na Abban Khalil.
Se sha biyun rana Sannan matar gidan ta dawo, tai sallama Amira ta amsa, ta shiga falon ta
tarar da Amira.
"Ke kuma saukar yaushe?"
Amira tace "tun safe nazo, ba kya nan se Abbansu Khalil, kin tafi kin barshi da aikin gida
saboda rashin tsoron Allah"
"Ke dalla yimin shiru, ba É—ansa na tafi kaiwa Asibiti ba?"
"To kuma se akace ki bar masa aikin gidan?"
"To dakeni uwata, kona sa shi, ko ban sashiba in dai Abban Khairat ne se yayi, ba ruwansa"
Amira tace "Allah Sarki, Anty Fa'iza kinyi dacen miji wallahi, ana cewa da anyi aure wata É—aya
biyu ake dena wannan soyayyar da kulawa, amma ke gashi haihuwar ki biyu, shekaru shida da
aurenku, amma haryanzu sonki yake kamar lokacin da yake neman aurenki"
Fa'iza tace "bari kawai Amira, shiyasa tun a wancan lokacin na dage seshi, su Baffa suka sani
gaba da zagi da cin mutunci dan nace bazan auri Alhaji Yahaya ba, kin san ɓarin kuɗi ya dinga
musu, kowa ya juyamin baya a gidan nan, Inna ma ƙiri ƙiri ta dinga zagina da cin mutumci wai
na mannewa matsiyaci na liƙe ni se Bashir nake so, Wallahi da Alhaji Yahaya na aura baze
dinga tarairayata haka ba"
Amira tace "bari Anty Fa'iza sha'anin gidanmu se Allah kawai, amma munyi rayuwar wahala,
kamar ba'a gidan aka haifi iyayenmu ba, ni kaina yau da Sassafe akaje aka taho da Baffa zasu
min tijara, yazo yana wassafamin wasu ƙa'idojinsa na banza, ni kuwa na zari hijjabi na arto nan,
se sun sake ganina a gidan ai, sun taru a kaina suna ta cin zarafina suna zagina, danma Allah
ya temake ni Inna bata nan, tsohuwar nan kallonta kawai nake, idan naje da abun duniya na
kaimata, ta karɓe tana dariya, idan wulaƙancinta ya ciyota kuma ta kama cemin karuwa, ni
kuwa nace ta dena cin abina"
Fa'iza tace "Amira maganar Allah da ma'aiki, abubuwan da kike aikatawa basu dace ba, kuma
kema kin sani Amma....
Amira ta dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu tace "ba shawararki nake nema ba ko
wa'azi, indai zan samu namiji me kirki nagari kamar Bashir wallahi zanyi aure in dena abunda
nakeyi, muma ajiye wannan maganar aside Please karki ɓatamin rai, sakkomin yarona naga ya
tashi, kin bar yaro duka ya rame"
Fa'iza ta girgiza kai, ta sakko Khalil ta miƙawa Amira, Amira ta karɓeshi ta rungumeshi a jikinta,
tana shafa kansa tana "Sannu kaji My Boy, mamanka ta barmin kai duk ka rame"
Fa'iza tace 'tunda gaki kinzo ai shikenan, ki kula dashi"
Amira tace "tabbas zakiga yadda zan kula da Yarona, naga sha biyu da rabi, ban kayanki in
saka muje mu É—akkko Khairat daga makaranta, dan daga ni se kayan baccina na fito"
Fa'iza ta bawa Amira kaya ta canza, ta É—au Khalil ta goyashi suka fita.
************************
Sannu a hankali yake tuƙa motar, kamar yana jin tsoron hanyar, yanayi yana kallon agogon
hannunsa, lokaci lokaci yakan lumshe idanunsa, tare da buɗesu yana ɗan kalle kalle.
Sannu a hankali ya ƙaraso ƙofar wani ƙaton gida, sau biyu kawai yai hone ya ɗan tsaya, buɗe
gate É—in akayi ya shiga cikin gidan da motar tasa, ya É—an É—au lokaci a cikin motar sannan ya fito
daga cikin motar.
Megadi yana tsaye a jikin motar, yana jiran fitowarsa, koda ya fito ridinawa dattijon yayi yana
faÉ—in 'barka da dawowa ranka ya daÉ—e"
"Yawwa barka, mutan gidan suna ciki ne?"
Megadin yace "Eu yallaɓai, Suna nan"
Yace "Good, buÉ—e bayan mota akwai trolley É—ina, ka kaimin É—aki"
"To yallaɓai"
Sanye yake da wandon sojoji, sekuma baƙar shirt me gajeren hannu, dogone na gaske me
siffar ƙaƙƙarfa, kallo ɗaya zaka masa ka san bashi da fara'a sosai, dan ransa a haɗe yake babu
annuri, wani irin taku yake kamar wani boss, ya nufi ƙofar da zata sada shi da cikin gidan.
Yana tura ƙofar falon, sanyin AC da ƙamshin turaren wuta ya bugi hancinsa, ya ɗan lumshe
idonsa sannan ya shiga falon da Sallama.
Ba kowa a falon, ya nemi Guri yai zamansa, ya kwanta akan doguwar kujera ya ɗora ƙafarsa
É—aya kan É—aya, dan ko takalmin be cire ba.
Ya kai mintuna shabiyu sannan aka buɗe wata ƙofa a cikin falon, wata babbar mace ce ta fito
daga ƙofar hannunta ɗauke da ƙaramin robar youghurt.
Tana ganinsa a kwace tai turus, tace "kai dan ƙaniyarka saukar yaushe? Maimakon ka kirani a
waya kawai se in ganka?"
Murmushi yayi ya tashi zaune yace "Hajiya Ammi, maimakon amin sannu da zuwa amma an
tareni da ƙorafi, dama cewa nayi let me suprise you, Amma tunda bakya so bari in koma"
Tai dariya tace 'eh tashi ka koma É—in, dan tunda ka tafi 'ya'yana suka sake, dodonsu baya nan"
"Aikuwa gani na dawo, kowa ya kintsa zamansa"
Ammi tai dariya ta samu Guri ta zauna, tace "sannu da zuwa ya hanya?"
"Alhamdilillah Ammi".
"Ya fama da bindinga ya fargaba?"
Yai dariya yace 'haba Ammi, fargaba se mata, mu idan muka fita aiki ai mun san a É—ayan biyu
muke, ko mu kashe ko a kashe mu, dan haka Bama fargabar komai, ina Boss ne?"
Ammi tace "yau kuma Uban naka ne Boss? Yanzun nan ya fita Allah yayi bazaku haɗu ba,
mhmm Kodayake ma ban sani ba ko shi yasan yau zaka zo, dan naga kafi sonshi a kaina, jeka
kayi wanka ka canza kaya, kafin nan na kammala Abinci kazo kaci"
Yace "to Ammi, ina mutan gidan ne?"
"Yaufa ranar aikice, duk suna makaranta ai"
Yace "ok"
Daga nan ya fito daga falon yabi kan wata baranda, dan zuwa ɗakinsa. yana shiga ya ƙarewa
É—akin kallo, duk da baya cikin É—akin amma É—akin fes dashi, komai tsaf tsaf da alama ana
shigowa a gyara dukda baya nan, beyi mamakin hakan ba tunda dama tsafta É—abi'ar Amminsu
ce, be taɓa tafiya ya dawo ya tarar da ɗakinsa da datti ba.
ya ciro wayoyinsa ya ajiye ya cire kayan jikinsa, ya É—auki towel ya É—aura da nufin ya shiga
wanka, amma wayarsa ta fara ringing.
Ringing tone É—in wayar ne ya sanar da shi me kiran wayar, dan haka yai murmushi ya dawo ya
É—auki wayar yasa a kunnensa sedai beyi Magana yai shiru.
Muryar mace ce tace "Hello, Hello, My own kana jina kuwa?"
"Ina jinki Babyna, ya akayi ne?"
"Wai zaka dawo yau É—in kuwa?" Tai maganar a kasalance.
"Shagwaɓaɓɓiya kawai, ban taho yau ba, bazan samu dawowa yau ba, sedai zuwa jibi in Allah
ya kaimu zan dawo"
"Haba dan Allah, wai yanzu ma ba zaka dawo ba? Haba My ni gaskiya..
"Ke gaskiya me? Jibin ma ba tabbas na zan dawo"
"Wallahi ji nake Kamar inyi kuka, wallahi bakaji yadda nake so in ganka ba, wata huÉ—u fa bamu
haɗu ba, zanyi kuka, ni duk raina ya ɓaci duk na damu in ganka"
"Dallacan shagwaɓaɓɓiya kawai, na shigo gari anjima zanzo insha Allah"
"Wayyo Allah daÉ—i, dan Allah ka taho yanzu kaji my love?"
"Gaskiya sena huta, yanzun nan fa na dawo, Gashi Ammi zatamin girki"
"To naji, amma kaci na Ammi kaÉ—an, idan kazo kaci nawa kaji My Own"
Yai murmushi ya shafi sumar kansa yace "As you wish my Ihsan, yadda kike so haka za'ayi,
amma amin izini inzo anjima, in É—an samu hutu, saboda na sha hanya"
Ihsan tace "Shikenan My Own, ka huta sosai kaji, ina nan ina jiranka kazo inta kallonka, bari in
ƙyaleka ka huta"
Yace "Ba dan wanka zan shiga ba da mun cigaba da wayar, in cigaba da jin muryar nan taki me
saukar min da nutsuwa"
"Nima sauraron muryarka yana samun nutsuwar zuciya my, ka kasance cikin farin ciki semun
haÉ—un"
"Jinake Kamar kizo ki tayani wankan nan, Allah dai ya kaimu lokacin bikinmu, ya nunamin
Ranar da zaki zama mallakina Ihsan"
Katse kiran tayi, dan idan ta ƙyaleshi ze fara sakin layine, shima a ɓangarensa yayine dan ya
tsokaneta, dan yasan take zata kashe wayar, dan Ihsan akwai Kunya.
*********************
Amira tana gidan Fa'iza har yamma, dan bata da niyyar tafiya, Fa'iza taji daÉ—in zuwan Amiran,
suna zaune sunata uwar hirarsu suna dariya, wayar Amira ta fara ringing, sunan Sultan ne ya
fito akan screen É—in wayarta.
ÆŠaga wayar tayi tace "Ya ake cikine?"
Fa'iza tace "maimakon kiyi Sallama?"
Harararta Amira tayi tace "Ina jinka"
Sultan yace "Ke maimakon ki kirani, kiji ya ake ciki, ko kuma kizo ayi lissafi amma koki nemeni a
waya?"
Amira tace "nasan kuÉ—ina bazasu ciwu bane, idanma anci se an fitar dasu"
Sultan yace "waya isa cin kuÉ—in gimbiya? Ai anyi kyakkyawan samu jiyan nan, wallahi kina wuta
Amira kina bada kala fa, mun samu kuÉ—i sosai jiyan nan, sake turomin account Number É—inki,
zan turomiki kuÉ—i sannan akwai wani zazzafan News"
"Wait, nawa ma zaka turamin ne inji?"
"Dubu É—ari da hamsin ne".
Amira tace "meya cinye hamsin É—in su zama É—ari biyu"?
"Haba Amira, wallahi naki yafi na kowa yawa, kin san bazan cuceki ba, saboda in bake ba DJ
Sultan, wallahi ban cuceki ba,