Showing 6001 words to 6283 words out of 6283 words

Chapter 3 - KOWA YA DEBO DA ZAFI Book 1 Complete FREE PAGES BY MEENAT YANDOMA Da ZAHRA ROYAL .pdf

Na roke
ku mu aje komi a gefe yanzu ne lokacin da zamu rungumi juna ba lokacin fada ba, muyi wa
kanmu adalci na rokeku." Ninaah ta karasa maganar tare da sake fashewa da kuka. Samun
kansu suka yi jikinsu yayi sanyi, domin tabbas gaskiya ta faɗa, dama Fu'ad akwai saurin zuciya.

LAB
Tun bayan shigowar su abu daya suke yi, wato gwaje-gwaje akan jinin da suka deba. Duk iya
binciken da suka yi abu daya suke gani wato cuta mai haddasama kwalwa cin naman ko wane
iri ne. Babban tashin hankalin su ga George cikin mugun hali bare ya sanar da su inda ya sami
wannan kwayar cuta domin sanin inda zasu samu maganinta, basu baro lab ba sai da dare ya
raba amma duk da haka sun kira babban likita ya sanar masu yana zuwa da safe. Su Fu'ad
kuwa juyin duniya anyi da su akan su shiga inda aka tanada domin kwanan masu jinya amma

fur sunki tafiya sai ma suka kwanta saman kujeru dake daf da ɗakin da su Ammar suke. Dare
ya tsala asibitin tayi tsit baka jin karar komi sai ta karnuka alamun kowa ya yi bacci. Su George
tare da su Ammar dake kwance a gadajensu lokaci daya idanunsu suka bude. Dirowa suka fara
yi daga saman gadajensu suna jan kafa kansu ya karkace kafa a murgude tare da nufar kofar
fita. Cikin baccin Ibina ta ji kamar mutum tsaye a kanta, bude idanunta yayi daidai da sakin
gigitacciyar karar da ta saka su Fu'ad farkawa, bude idon da zasu yi su Ammar suka gane sun
zagaye da su sun saka su tsakiya idanunsu fari fat bakunansu na dalalar da jini....



Meenat yandoma

1
2
3

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login