Showing 3001 words to 6000 words out of 6283 words

Chapter 2 - KOWA YA DEBO DA ZAFI Book 1 Complete FREE PAGES BY MEENAT YANDOMA Da ZAHRA ROYAL .pdf

magana kowa d abunda yake sak'awa
a ransa. Babban asibiti ne mai girman gaske, mai cike da marassa lafiya, kota ina da y'an uwan
marassa lafiyar cike da hospital d'in. Kai tsaye da motar asibitin ta tsaya, wasu doctos ne da
Nurses suka nufo wajan da gadon d'aukar marar lafiya guda hud'u, saboda shugaban hotel d'in,
su duka sakkowa sukai akasa su Ammar dake a sume har yanzu basu farka ba. Kai tsaye cikin
ainahin asibitin aka wuce dasu, wani d'aki mai girma da tsari da kyau aka kwantar dasu. Wani
doctor ne ya shigo ya fara zuwa wajan shugaban hotel d'in yana kallon sa ya ce "George, kai ne
a nan, mi yake faruwa ne?" Dan ya mutse fuska George yayi yana k'ara dafe wuyansa da yake
jinsa yanzu kamar ana tsikara masa allura, bai amsa ba saima damk'e hannun doctor da yayi
da mugun k'arfi. Ba shiri doctor ya sake juyowa yana duban George, ganin yadda yake wata
jijjiga akan gadon, gadon na girgiza kamar zai rabe gida biyu, k'asusuwan jikinsa ne suka fara
wata irin k'ara kamar ana kakkaryarsu, idonsa a rufe, can aka ji ya daina wannan jijjiga, da sauri
Fu'ad ya ce "anya George shima ba komawa irin su Ammar zaiyi ba, izuwa yanzu na gane duk
wadda suka ciza ko suka karceshi zai iya komawa irinsu" Danda nan Haris ya k'ara ja da baya,
wani irin tsoro ya k'ara rufe sa, yana gaf fita k'ofa Ibina ta cafke hannunsa, wata irin zabura yayi
yana kiran "na shiga uku na, shikenan tawa ta k'are" Jijjigasa Ibina tayi tana cewa "kai Haris nifa
ce, ina kake niyayar zuwa naga kana niyar fita" Tana rufe baki suka ji ihun doctor, su duka da
mugun sauri suka kai dubansu a inda suke, ganin yadda George ya koma shiga ya cafke
hannun doctor ya kai mai wani mugun cizo, jini sai zuba yake a hannun nasa, ba shiri Fu'ad ya
tuna idan ka buga masu wani abu a kai suna suma, kuma suna dad'ewa basu farka ba, yasa ya
d'au wani k'arfe yana nufar inda suke, yana zuwa ya shammaci George ya kwad'a mai shi a kai.
Suma yayi, inda doctor ganin ya sakar mai hannu yasa ya fara yamutse fuska yana rik'e
hannunsa dake zubar jini, kallonsa Fu'ad yayi da tausayi, yana sharce gumi. Haris dake tsaye
Ibina rik'e da hannunsa, ya fisge yana cewa "cika ni na ce, na rantse bazan zauna a nan ba,
haka kawai idan zaku iya zama ku zauna kunga tafiya ta" Yana shirin b'ude k'ofar ya fice yaji
muryar doctor na magana cikin wata irin murya me kama da saukar aradun...




ZAHRA ROYAL STAR
KOWA YA ƊEBO DA ZAFI...

NA
MEENAT A 'YANDOMA
DA
ZARAH ROYAL STAR

WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE AKAN 500 KACAL! ZAKU TURO DA KUDIN TA WANNAN
ACCOUNT NUMBER 2294023532 UBA AMINA ABUBAKAR KU TURO DA SHAIDAR BIYA TA
WANNAN NUMBER 08133562798 KO KUMA KU DAUKI HOTON KATIN MTN NA 500 KU
TURO HOTONSHI
ƘIRƘIRARREN LABARI NE
Tun daga sunayen garuruwa har ma da wasu abubuwan da zaku ji.



FREE PAGE 7&8


"Ku kira min doctor Anna, da sauri ta taho da allurar nan mai sa dogon bacci". Cewar doctor
dake dafe da kansa yadda ya fara jin ya fara sara mai.

Da sauri wata Nurse ta fice domin aiwatar da abunda doctor ya ce.

Haris zare ido yayi ganin yadda doctor yake jujjuya kansa ya runtse ido. Da sauri yayi wajan
Fu'ad yana cewa "dan girman Allah kuzo mubar asibitin nan". Wani kallo Fu'ad ya jefama Haris
yana cewa "wai mi yasa Haris kake hakane?, y'an uwanmu ne fa ke cikin wani hali na rayuwa
da mutuwa in... Maganar ce ta mak'ale ganin doctor ya nufo wajansu. Wata irin zabura Haris
yayi yana komawa bayan Fu'ad "na shiga uku shima ya koma dodon hala?" Haris ya fad'a yana
b'oye fuskarsa a bayan Fu'ad. Fu'ad ya jawo shi yana cewa "banza lafiyarsa lau bai koma ba
tukunna, gaskiya ka cika tsoro da yawa, ka natsu mana".

Doctor dake kallonsu ya saki wani k'aramin tsaki yana cewa "ya kamata ku bamu had'in kai, ya
akai wannan abu ya fara, tun fari ku natsu kuyi mana baya ni". Da sauri Haris ya ce "mu natsu
fa ka ce ana cikin wannan hali ina wata maganar natsuwa, nikam iyanzu nayi dana sanin zuwa
wannan k'asar duk abunda ya same mu dasa hannun George a ciki duk yasan komai shida
wani ma'aikacin hotel d'insa".

Wani tsaki Fu'ad yaja ya fara magana yana ba doctor bayanin duk abunda ya faru, daga k'arshe
ya ce "kawai abun sha ne fa suka sha suka koma haka, sai dai idan wani abu akasa mana a
cikin abun shan nan"

"Tabbas akwai abunda akasa haka nan mutum bazai koma kamar dabba ba". Cewar doctor
yana girgiza kai alamar tabbatarwa. Daurewa kawai yake cikin jikinsa ji yake kamar ana yankan
naman jikinsa, Fu'ad dake kusa dashi bai lura ba da yadda yake shinshinarsa kamar yana son
kai mai cizo. Da sauri Haris ya ce "nifa ban yarda da wannan doctor d'in ba, na rantse muyi
nesa dashi ya kusa komawa shima",

"Wai Haris mi yasa ka zama haka ne wai?" Ibina ta idasa maganar tana kallon Haris. "Kinga laifi

na ne?, gaskiya fa nake fad'a, idan mukai wasa gaba d'aya sai mun koma irinsu wallahi".

Doctor jin shigowar Doctor Anna, yasa ya juya inda take cike da kulawa ta kama hannunsa
ganin jinin ya daina zuba sai fatar wajan data fara komawa bulu, cike da d'an mamaki ta ce
"doctor Daniel mi yake faruwa ne?. D'an bayani ya fara mata sana ya ce "yanzu karki damu
dani, ki fara masu allurar please dan suna gaf farkawa, and idan suka farka bana jin zamu iya
dasu, domin wani shegen k'arfi gare su, domin da George ya kama min hannu na rantse ji nayi
kamar ba'a duniya nake ba"

Dariya ce ta kama Haris jin yadda doctor ke bayani, saida ya dara da sauri kuma ya maze ganin
kallon dasu Ninaah suke mai. Allurar ta fara masu sana ta dawo wajan doctor Daniel. Ganin
yadda yayi shuru kamar baya cikin hayyacinsa kansa yayi k'asa, ta nufi inda yake takun
tafiyarta na buguwa da zuciyar Haris duk taku d'aya sai zuciyarsa ta buga. Domin shi ya tabbata
doctor Daniel ya kamu da irin cutar dasu Zuzuuh suka kamu da ita. Runtse idonsa yayi yana
faman cewa "Fu'ad mubar d'akin nan na rantse maka doctor d'in can shima ya koma". Sai
lokacin ma su Ninaah suka tuna an cizi doctor shima, da mugun gudu Ninaah da Ibina su kayi
bakin k'ofa, sai dai kamin ma su isa bakin k'ofar Haris ya rigasu isa, da mugun sauri ya
bangajesu yana niyar tura k'ofar jikinsa na kyarma.

Fu'ad ne kawai yayi azamar nufar inda doctor Anna dake niyar isa inda doctor Daniel yake. Sai
dai kamin ya isa doctor Daniel ya d'ago idonsa ne ya koma fari fat hak'oransa sunyi masifar yin
tsini, ya wage baki yana faman yin wani irin gunji kamar mage ta samu nama. Wata irin zabura
doctor Anna tayi duk da haka tana gaf dashi tana faman yi mai magana, wai yana lafiya kuwa?
Miye yake yi haka?. Daga can wajan bakin k'ofa Haris dake hango su ya bud'e baki ya ce "zaki
ci uwarki ne kika tsaya tabbayar wadda zai hallakaki wai yana lafiya tabbas zai nuna miki yana
lafiya ai". Duk da halin da suke ciki bai hana sauran doctors d'in yin dariya ba, domin da
harshan turanci yayi maganar.

Fu'ad yana gaf isa inda take kawai suka ji ihun doctor Anna, doctor Daniel yayi kukan kura, wani
mugun tsalle yayi yana kada doctor Anna k'asa ya turmushe ta, kokowa suka farayi tana sun
kwatar kanta, shi kuma yana neman inda zai kafa mata cizo........



Nigeria....


Kwance yake kan makeken gadonsa, sai faman juye-juye yake. Can kuma ya zabura yana
faman kiran sunan Ammar. Da sauri Haj Maria dake kusa dashi a kwance ta tashi tana kunna
fitilar dake kusa da ita. Kallonsa tayi ganin duk yadda zufa ta wanke masa fuska, cike da kulawa
Haj Maria ta ce "Alh lafiya kuwa?". Sauke ajiyar zuciya yayi ganin cewa mafarki yayi ya ce "wani
irin mafarki nayi da Ammar". Kallonsa tayi da d'an mamaki ta ce "Alh Ammar ai yanzu na
tabbata yana d'akinsa a kwance". Da sauri Alh Lado ya sakko daga kan gado yana nufar k'ofar

fita yana cewa "hankali ya kasa kwanciyar wallahi wani fa mugun mafarki nayi dashi yana cikin
wani hali, dama tun jiya naga alamunsa kamar suna shirya wani abu shida abokansa kinsan
Ammar baya jin magana".

Da sauri itama tabi bayansa. Suna shiga d'akin nasa suka ja turus suka tsaya, ganin wutar
d'akin a kunne dubunsu suka kai akan gadon nasa babu komai akai ga waduruf a bud'e, hatta
durowar da yake aje kud'i a bud'e take an yashe komai na ciki. Wata irin zufa ce ta yanko ma
Haj Maria zuciyarta na bugawa da mugun sauri. Alh Lado kuwa wani irin jiri ne yaji yana neman
kayar dashi, ba shiri ya nemi waje ya zauna yana dafe kansa.

Kallon Haj Maria yayi idonsa yayi jawur gabanta ne ya fad'i ganin irin kallon da yake mata da
sauri ta ce "na rantse Alh bada sa hannuna a ciki banma san baya gidan nan ba". Tashi yayi a
hargitse yana nunata ya d'an yatsansa yana cewa "waye ya basa makullin duruwar kud'in nan
to?, bana amsheta a hannunsa ba? , kuma kinsan yaron nan baya jin magana ko kad'an mi
yasa baki sa mai ido yadda ya kamata ne?, yanzu wannan yaro ina zaize cikin uban ruwan nan
cikin dare haka?".

Haj Maria tama kasa magana sai hawaye dake zuba ta cikin idonta, domin bama fad'an Alh ne
yake damunta ba, tunda suka shigo d'akin jikinta ya bata akwai wani abu mummuna dake
faruwa da yaronta. Da sauri ta juya tabar d'akin tana nufar d'akinta. Wayarta ta d'akko tana
danna ma wata number kira. Tana jin an d'au wayar bata tsaya jiran jin mi za'a ce ba ta fara
magana tana cewa "Haj Aliya, ko Ammar yana gidanku yanzo wajan Haris ne?" Daga cikin
wayar Haj Aliya itama cike da tashin hankali ta ce "nima abunda nake shirin kiranki naji shin
Haris yazo wajan Ammar ne?".

"Innalillahi wa'inna ilarhir raju'un" kawai Haj Maria ta take anbata ta sake cewa "tabbas duk inda
suke suna tare da juna, amma bari na kira Haj Bilki ko suna tare da Fu'ad". Da sauri Haj Aliya ta
tari hanzarinta tana cewa "ai yanzu na gama waya da ita suma suna cikin tashin hankali dan
shima Fu'ad d'in baya gida".
Haj Maria bata san sadda wayar ta fad'i kasa ba ta tarwatse. Dafe kanta tayi tana tunanin ina
yaran nan zasuje haka, tana tabbacin baza su zauna a k'asar nan ba, domin taga irin mak'udan
kud'in da Ammar ya d'iba.




Haj Salma dake zaune kusa da Alh Mande ta ce "yau ka dad'e baka dawo gida da wuri ba,
domin d'azo Zainab (Zuzuuh), ke tabbayar baka dawo ba". Kallonta yayi yana kai lumar abinci a
bakinsa yana cewa "yauwa kira min itama ina son ganinta", "amma yanzu baka ganin tayi
bacci". "Ki taso min ita". Shuru Haj Salma tayi tana nufar d'akin Zuzuuh, koda ta shiga sai da ta
kwanna wutar d'akin, ta kai dubanta akan gadon Zuzuuh, murmushi ta saki ganin kamar mutum
ne ke kwance akan gadon duk daukarta Zuzuuh ce kwance kai. Sai dai tana yaye abun rufar, ta

zaro ido tana kallon yadda aka jera fulillika a tsaye sai yayi kamar mutum ne akan gadon yana
kwance. Da mugun sauri ta fice daga d'akin tana nufar darning inda Alh Mande ke zaune,
ganinta a hargitse yasa ya ajiye cin abincin yana cewa "lafiya dai na ganki kin fito haka?"

"Alh ba lafiya ba wallahi, na duba ko ina na d'akin Zuzuuh ban ganta ba, dama tun d'azo na lura
kamar bata da gaskiya kamar tana shirya wani abu"

Tashi Alh Mande yayi ba shiri yana cewa "gidan ubanwa zata je cikin wannan daren da ake
tsula uban ruwan nan, maza ki kira k'awayenta su biyu ko suna tare........



ZAHRA ROYAL STAR
KOWA YA ƊEBO DA ZAFI...

NA
MEENAT A 'YANDOMA
DA
ZARAH ROYAL STAR

WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE AKAN 500 KACAL! ZAKU TURO DA KUDIN TA WANNAN
ACCOUNT NUMBER 2294023532 UBA AMINA ABUBAKAR KU TURO DA SHAIDAR BIYA TA
WANNAN NUMBER 08133562798 KO KUMA KU DAUKI HOTON KATIN MTN NA 500 KU
TURO HOTONSHI

ƘIRƘIRARREN LABARI NE
Tun daga sunayen garuruwa har ma da wasu abubuwan da zaku ji.

PAGE 9&10
...Hannunta Denial ya cafke tare da kafa mata haƙora. Ihu take tamkar ranta zai fita sakomakon
azababben zafin da yayi mata dirar mikiya. Fu'ad ne ya lura da allurar da suka jefar can gefe,
shammatar Denial yayi tare da daka masa ita a kai, nan take ya sulale a kasa sumamme.
Numfashi Doctor Anna fita ya rika yi da kyar cikin radadin ciwo take fadar a miko mata karamin
akwatin ta. Kafin ta rufe baki sauran likitoci sun shigo dakin a gigice. Nan suka hau ba Doctor
Anna taimakon gaggawa. Babban abinda ke tayar masu da hankali shi ne wannan wace irin
cuta ce da zaka riƙa cin naman jikin dan uwansa. Daga taimako ga shi suna shirin rasa
manya-manyan likitoci su guda biyu. Allurar bacci suka yima Anna nan take nannauyan bacci
yayi awon gaba da ita. Ninaah da Haris ne suka shigo dakin tamkar ka ce masu tak su tsere.
Tsattsaye suka yi ganin ana dibar jinin wadanda suke fama da cutar, "mutum biyu su biyo mu
don akwai binciken da muke sonyi" daya daga cikin likitocin ya fada. "Babu inda zanje, ta ya zan
fita in bar yan uwana cikin wannan halin?" Fu'ad ya fada ranshi a matukar bace. "Kaga Haris da
Ninaah su je mu sai mu tsaya nan" Bayan fitar su Haris Fu'ad ne ya matsa kusa da gadon

Ammar. Kafe shi da ido yayi cike da tausayin halin da suka tsinci kansu, kamar ba sune cike da
farin ciki a jiya ba. Tabbas rayuwar nan akwai ban tsoro, Ammar ne kwance bai son wanda ke a
kanshi ba, shin me zasu fadama iyayensu in suka koma gida, ina bazai yiwuba dole ku warke.
Maganar da Ibina tayi ma shi ce ta dawo da shi cikin hayyacina shi. "Fu'ad dubi jikin Zuzuuh ka
gani duk tayi fari ga inda aka cije ta yana fitar da wani irin ruwa mai yauki." "Jikinsu duk haka
yake tunda lamarin nan ya faru, anya ba zamu nemi transper ba mu tafi wata kasar da su?"
Turo kafor da aka yi ce ta saka su yin shuru, Haris ne da Ibina jiki a sanyaye. Duk faman
tambayar da suke masu amsa ta kasa samuwa sai faman binsu da ido suke. A hasale Fu'ad ke
magana "kada ku mayar da mu sakarkari mana, ya zamu yi maku magana amma ku kasa bamu
amsa" ya karasa maganar tare da nufar inda Haris yake gadan-gadan. Da sauri Ibina ta sha
gaban shi don tasan shi da zafin zuciya ba tun yau ba. "Fu'ad mun mutu, ku dauka mun mutu
kawai" Haris ya fada hawaye banin fuskar shi tamkar mace haka yake cizgar kuka. "Bangare
mun mutu ba?" Ibina ta faɗa cikin tashin hankali "Lemun da su Zuzuuh suka sha, hade yake da
wani acid mai matukar hatsari ga lafiyar dan adam." Ninaah ta karasa maganar tare da share
hawayen fuskarta. "Wa ya sanar da ku?" "Likitocin" Haris ya bada amsa. Yaraf! Ibina ta koma ta
zauna cike da tashin hankali tare da dafe kanta da take jin yana barazanar tarwatsewa. Tsit
dakin yayi kowa da abinda yake sakawa. "Duk wancan la'anannen ne Goarge ya haddasa mana
wannan masifar, don haka banga amfanin rayuwarsa ba." Fu'ad ya karasa maganar a fusce tare
da nufar inda Goarge yake kwance." Saurin shan gabansa Haris ya yi. "Mi zaka yi ma shi,
wannan ba lokacin fada bane mafita ya kamata mu nema tun kafin lokaci ya kure mana" "mafita
fa ka ce? Wace irin mafita bayan ya salwantar mana da rayukan abokan tafiya biyu, bayan
raunin da ya ji ma Ibina. Ka matsa ka bani wuri tun kafin raina ya ba ci." Ya karasa maganar a
fusce. "Fu'ad ka dawo cikin hayyacinka, mafita zamu nema ba fada ba" tatss! Kake ji Fu'ad ya
dauke Haris da lafiyayyen mari. "Naga alamar bakinku daya da George, ko dai siyar da mu kayi
ka fada Mani." Fu'ad shaƙe da wuyan Haris ke maganar cikin ƙaraji. Ibina da Ninaah ne suke
kokarin ɓanɓare Haris amma sun kasa don ba rikon wasa yayi ma shi ba. Kuka suke suna
rokon su daina fadan amma ina bugun juna suke tare da farfasa duk wasu glass dake wurin.
Ganin zasu yi kisan kai ya saka Ninaah fita a guje ta Kira ma'aikata, da kyar aka raba su, nan
take aka koro su daga cikin dakin. Ibina Kuka take tamkar ranta zai fita "Yau suke ke fada bama
cacar baki ba, abinda tunda suke basu taba yi ba tun daga kuruciyarsu, anya basu debi ruwan
dafa kansu ba, domin hausawa sunce kowa ya ɗebo da zafi bakin shi." "Haris Fu'ad! muna cikin
wannan halin kuke fada, abinda tunda muke ko a kuruciyar mu bamu taba fuskanta ba.

1
2
3

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login