Showing 18001 words to 18685 words out of 18685 words

Chapter 7 - AMANI BOOK 4 END HAUSA BOOK COMPLETE BY SUMAYYA TAKORI.pdf

rantsuwa da Allah yau ko ki sallama ko gobe a kawo Sa-dakokin
nan, ina dalili? A kan ki a ka fara ciki? Wannan izaya fa ta ishe ni.
Yadda Mukhy ya fitittike yana fadan, ta san da gaske ta kawo shi bango, ta kuma san ya
kwatanta mata adalci yadda bata zato, duka daga samun cikin ta zuwa yanzu sau nawa ta
kasance dashi bai fi a kirga ba, ita ma kuma shakiyanci ne ta fara kewar sa sosai a kwanakin
nan, duk wadancan abubuwan sun sake ta, don cikin har ya shiga watanni na biyar yanzu, duk
abubuwan da take ji sun lafa tuntuni, don haka yana mika mata hannu ta kama ba musu, sai ya
sa karfi ya ciccibe ta ya daga ta a kan hannayen sa zuwa main turakar sa. Amani ta amincewa
ran ta in sha Allahu yau zata faranta ma Mukhy irin yadda bata taba yi masa ba a rayuwar
auren su.

You add weight, more weight, Oh! Koda yake ba dole ki kara nauyi ba, bayan girman Baby
ina jin daga samun cikin nan zuwa yanzu kin ci buhun Dawa da bokitin daddawa, Zabbi hamsin,
Dawisu hamsin, ni kuma na ci ukubar da bana yiwa kai na fatan sake afkuwar ta.

The whole night for Mukhy!!!
**** **** ****


C
ikin Amani na da watanni takwas yanzu, ba abinda Ummami take sai shirin tarbar haihuwar ta,
duk abinda ya dace a tanada hatta feeder din jariri sun tanade shi, wasu kayan baby da yawa
daga Guinea Saadiyya ta aikowa Ummami don tana shiri da Mukhy sosai. Sau biyu yana zuwa
kasar Guinea duba ta da bata da lafiya. Haka Yayar shi Sayluba ma ya je Tahoa sabida sada zumunci da ita.
A wannan hutun ne aka kawo mata Fajur, hutu, zata zauna har sai ta haihu, a bakin Fajur ta ji
wani labari da ya gigitata, wai Mamma Jalan ma cikin ta ya tsufa.
A gigice Amani ta kira Mamma tana son tabbbatar da abinda ta ji daga kanwar tata, Haj.
Jalan ta rasa inda zata tsoma ran ta don kunya sai ta hau Amani da fada tana cewa ni abokiyar
wasanki ce ko Amani? Don kin ga tsayin mu daya girman mu daya ko? Shikyasa kika maida ni
saar ki. A shekaru na ai na wuce haihuwa yanzu, ki zauna Fajur tana gaya miki abinda bazai
yiwu ba.
Ita kuwa Fajur tayi rantsuwa ta maya cewa cikin Mamma yanzu yafi nata girma, kuma kusan
kullum sai ta je asibiti awo.
Amani sai ta kira Alhaji da kan sa.
Daddy da gaske ne? mamma zata baima su Fajur kanne?
Hawayen farin ciki suka tsirgowa Alhaji Usman Faskari na godiya ga Allah. Ya ce da gaske
ne Tafisu, da gaske ne!
Uwa sai ta saka kuka don dadi.
A halin farin ciki dana bakin ciki duka, Uwar su Alhaji ta fi gane ta yi kuka.

Amani har katon Sa da rago tasa aka kayar, ta rabar da shi sadaqa ga bayin gidan ta, tana
mai taya Daddyn ta godiya ga Allah, da adduar ita da Mamma Jalan duka, Allah ya sauke su
lafiya cikin koshin lafiya.

**** **** ****

EPILOGUE

5
6
7

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login