Showing 9001 words to 12000 words out of 13980 words

Chapter 4 - ZUCIYA DA KWANJI BOOK 4 Hausa Novels by MAIMUNA IDRIS SANI BELI .pdf

yanzu ma ai Allah ya saka maka
tunda
ga shi nan za ka haihu ka barni. Ya kada kai
sannan ya kuma dorawa. "To na
hakura,shawara
ta gaba da zan ba ki ita ce,ki rage kishi ki
rage
zafafa al'amura,dan su suke rushe dukkan
son da
nake miki. Ki daina yaudarar kanki da zaton
zan

auro 'ya"ya mutane in ki son siu dan ki ji
sanyi,ke
na so,so mai karfi sadiya. Hindatu aka aura
min
ba tare da ko ganinta ba taba ba, amma
wallahi
ban taba jin na tsani hindatu ba, kullum
samun
matsayi take a zuciyata saboda yadda take
darajani take kuma yarda na isa da ita.
Sannan
fatima kaddara ta kawo ta aure
na,shekarunmu
kusan daya tana da kyau tana da
kudi,amma
fatima ta san na gaba da ita,yaddana so
haka
nake juya ta. Shin sadiya ke me kike taka
da kike
ganin kowa bai isa ba? Kuma ki bawa kanki
yarda dole a fifita ki? Wannan ragon azanci
ne,ki
yi shawara da zuciyarki ki canja kanki
tsari,in kika
dage da kyautata min da bin umarnina ba sa

kin
dagawa kanki hankali ban, zan ba ki hakki ki
da
yake naki kamar yadda bai kamata ki dora
ido a
kan hakkin wata ba". Ta fara kuka. "Amma
dai
abu turab yanzi cin fuskar da kuka yi min
hakki
wa ne? Ya amsa. "Sau nawa ina furta miki
kalaman kauna gaban hindatu,kina ma
gwsale ni?
Ina kuma ga wadda ta zo tana furta min da
bakina? Ba fa zan rufe ki ba,ina son
hindatu ina
son fatima, duk suna abin da zan habaka
soyayyarsu ke ce kawai kike neman taki da
kwanji.ina shawararki ki canja". Ba ta
tanka ba
illa shesshekar kuka.
1 · Like · React · Report · May 21, 2015
Amierah S-Man
11)***************************
******************
******************************

********** Sai da
hantsi ya daga sosai wajen sha daya sabban
ya
sami sararin zuwa dakin fadima saboda
abokan
da suka rika zuwa masa jaje. Hindatu dai ta
zo
ta kwashi gaisuwarta tun da sanyin
safiya,dan
haka babu ita cikin gaisuwar safe. Da dokin
yadda za ta kasance a tsakaninsu ya shiga
dakin.
Akwai alamun ko tsinke ba ta sawa dakin da
sunan gyara ba,amma ita ta fice ado kamar
mai
zuwa wani fatin gasa,tana zaune tana kallo
da ta
sa gugguru a cinyarta. Yana lalube ta inda
zai
faro mata bayan sallama,amma sai ta riga
shi ta
hanyar tattaro masa dukkan fara'a ta ce.
"Barka
da safiya". Ya nemi gurin zama da sauri
dan kar

jirin da ke kwasarsa ya yi nasara a kansa,ya
amsa. "Barkan ki dai,duk da na raina
gaisuwar".
Ta mayar da ganinta t V ta ce. "Ko? Kar ka
manta fa hausawa sun ce maraina
kadan.....
Barawo". Ta karasa da dariya. Ya jinjina
lokacin
da mamakinsa ya ci gaba da hayyaka ya ce.
"Kuma fa haka ne, amma ai sun ce inda
aka karbi
dariyar almajiri nan yake fasa kokonsa". Ta
dan
yi kasake sannan ta kada kai. "Haka ne,ci
gaba
da fasawa ni kuma na yi alkawarin kin
kosawa
zan ci gaba da baka sababbi......" Ya yi
saurin
tare ta a dokance. "Ba fa zaurance nake
ba". Ta
yi dariya. "Nima ba shi nake ba". Ya dan
ware
ido. "Amma. Kike ambaton alkawari?" Ta
kuma

kada kai cikin tabbarwa. "Eh,na yi da zuciya
daya". Sai ya rasa abin da zai ce saboda
dadi da
farin ciki,duk basirarsa ta toshe,ta sauke ido
a
tasar gurgurun da take ci. Sannan ya daga
kai ya
bi cikinta da kallo,dadi na neman kashe
shi,ya yi
kuma ta maza ya ce. "Fadima ya ya
babynmu?"
Ta kasa dago ido ta dube shi saboda tsabar
kunya,ta ci gaba da cin gurgurunta kawai.
Sai
can ta waske da cewa. "Wai ba ka cin
popcorn
ne? Ya yi murmushin basarwa ya dawo
kujerar
kusa da ita yana cewa. "Tunda yanzu kin
mun ta
yi sai in ci mana. Ta yi saurin sa tasar a
tsakiyarsu ta ce. "Da ka fara taimakonmu
da
ruwan sha". Bai tanka ba ya mike ya nufi
kicin

din,shima sai da ya bishi da kallo komai a
hargitse,watakila har wanke wanke abincin
jiya
suna zaune. Bai ga laifinta ba ko daya,dan
tun
asali ba ta saba ba, bare yanzu ga nauyin
ciki,dan haka ya fara tunanin lokacin ya yi
da za
ta sami mai aiki ko da ba ta gama canja hali
ba.
Ya shiryo lemuka da ruwa ya dawo dasu,ya
zube
mata tana yi masa sannu. Shi kuma ya fanso
abin da ke ransa da cewa. "Kin rasa ni
lokacin da
zan fi miki amfani ko fatima,abin da ya fi
min
ciwo ke nan a yanzu yadda na ga dakunan
ki,ban
yi a zanci ba ko daga can da na bayar da
damar
a kawo miki mai aiki duk da har yanzu ban
gama
sanin matsayina a wajen ki ba, wata za ta
iya

zama a tsakaninmu yanzu ko da sauran
lokaci?"
Ko kadan fuskarta ba ta sauya ba,ba tare
da ta
dube shi ba ta ce. "Me kake ci na baka na
zuba?
Duk zamu tattauna wadannan". Cikin
zakuwa ya
ce. "In ba yanzu ba zai yaushe?" Ta ce,"sai
ranar
da na karbi girki". Ya yi dariya. "Mene ne
hikimar
hakan?" Ita ma ta yi dariyar ta ce. "Kai ya
kamata ka amsa,duk lokacin da muke son
tattauna wani batu ka kan ce jira nake ki
karbi
girki, ka tuna?" Ya yi mata wani irin kallo
kawai
yana dariya.suka dauki shiru sai can ya ce.
"Fatima jiya me kuka tattauna da malam?"
Yana
rufe baki ta amsa. "Tsakaninmu ne". Ya
kada kai
yana kallon ta da gefen ido ya ce. "Ko?" Ta
kada

kai tana cika amsa tambata ba,na tambayi
baby
kin share,na tambayi yadda kuka yi da
malam
nan ma kina neman sharewa". Karaf ta
kuma
amsa. "Dacewa ne kawai ba ka yi ka tambaye
ni
abin da na san amsa ba". Ya ce, "dan bani
sata
amsa, kamar me zan tambaye ki?" Ta yi
tambaye
ni yadda na kewarka da yadda rashinka ya
yi min
ciwo idan na fara zuba sai ka danna purse".
Bai
dawo daga duniyar shaukin da ta watsa shi
ba
aka hau kwankwasa kofa.ya yi saurin riko
hannunta ya dubi kwatar idonta ya ce. "Zan
nemi
afuwarki,ki yi min hanzarin hidimat ki a 'yan
kwanakin nan,saboda yawan mutane,nima
kuma
na dan murmure ko?" Cikin sauri ta kada

kai. "Na
yi maka". Ya kara tausasa murya ya ce. "To
me
za ki bani da zai tabbatar min kin yi rashi
na?"
Fuskarta a sake ta ce. "Miko hannunka na
baka
kyautar sumba guda biyu". Ya jinjina.
"Hannu
kuma?" Ta yi dariya ta ce. "Au ka raina? To
kawo kuncinka na baka daya a maimakon
biyu.
Har sai da ran hindatu ya baci da dukan
kofar,duk da ta kasa zuciya ta koma. Ba
dan
Abdullahi ya gamsu da wannan sabuwar
gaisuwar
da suka bude shafinta a yau shi da fatima
ba ya
barta,sai dai ya ambatar mata I love u
addadi irin
na kamar anyi masa gorin fadar. Cikin
sanyin jiki
kuma ya yi mata sallama ya tafi.
***************

*************************** Duk yadda
abdullahi
ya shude da wasu kwanaki a duniya masu
cike da
doki da farin ciki,yana tsammanin bai taba
bi ta
kan irin kwanaki hudu da fitowar sa kurkuku
ba.
Fatima ta canja daga wadda ya sani,kuma
da
alama tana neman canja shi shima,komai da
ya
zagaye su shima ya canja,canjin da ya
tabbatar
in ya dore zai samar masa aljanna a
duniya. Cikin
kwanakin nan kafa ba ta daukewa a gidan
saboda
haka basa kebewa,amma fatima na zagen
kwanjin
da ba ya fito da kauna da soyayya kai
tsaye,amma yana fito da tsannanin tattali
da
kular ta da shi. Tana wanke kafa ta same shi
har

dakinsa cikin cire girman kai da isarta,ayi ta
karbar baki da ita,cikin girmamawa da
karramawa. A dan wannan lokacin ya
fahimce ta
da kyau,duk yadda sadiya ke jin kishi
fatima ta
ninka ta, sai dai nata akwai kawaici da
hankali a
ciki, ta iya hadiye shi, kuma ta iya basar da
bacin
rai. Wannan ba karamin dadi ya yiwa
abdullahi
ba,dan yana ji a ransa wannan ita ce
fatma,wadda ta wuce ta aro ce. Bai tashi
mamakin ta ba sai a kwana na hudun da
yake
kafa ta dauke da yawan baki,sun wuni dai
da
hajiya Atika matar babansu,da yamma da
za ta
koma sai ya shirya mayar da ita gida. Har
fatima
aka rako ta wajen mota,suna ta yiwa juna
godiya.
Ta faki idon mutane ta yi masa wata

alama,ta
rike yatsunta shidda ta saki ta nuna agogon
hannunta,sannan ta rike kunne tana girgiza
kai.
Ya fahimce ta,ma'ana kar ya wuce karfe
shida.
Ya yi mata murmushi kawai suka wuce. Dan
halak din kuwa shida saura minti bakwai ya
dawo,ya fado dakin kamar aguje. Ta tashi
da
sauri tana kare masa kallo da fuskar
tambaya. Ya
zauna a kujera yana haki ya ce mata.
"Shidan ce
ta kusa cika".12)Anya ni kuwa na taba zaman minti biyu a
kallon
kwallo? Ban san komai a kanta ba, dan haka
yanzu na ke ware ido kamar makauniya ko
zan ji
abin da kake ji. Ka ga har na fara
sabawa,kila
nan da wasu kwanaki saboda kai nima na
fitar da
club dina". Ta kare maganar da zolaya,
kafin ya

yi magana ta kuma dorawa. "Duk da ma dai
kamata ya yi na yi kishi da kwallon kafar
nan,haka kawaifa ka dauki daren farkona
ka kai
mata, amma dan bani da zuciya wai nake
son
faranta maka da ita". Ya tuntsure da
dariya ya
ce. "To ki sha kuruminki,da daddare da
ranakun
da duk ta lasar miki duk zan fanshe
miki,kamar a
yanzu ma sai sun fi armashi dan zamu yi
cikin
kula da kyautar da Allah ya yi mana ko? In
na
tuna mun kusa yin dan kanmu fatima ni
kadai na
san yadda nake ji a zuciyata". Nan fa ya
kashe
bakin tsanyarta yi dif,sai dai fuskarta da
murmushi,amma bai kara jin mruyarta ba
har ya
wanka alwala ya fice masallaci. Sai bayan
sallar

isha ya shigo musu da abinci kamar da
can,suka
yi dinner tare suna ta musayan kalaman da
ke
sabbabe musu shakuwa. Fatima cikin
fargabar
kawo kudurorinta,shi kuma cikin fargabar
zunguro
magana,har dare ya yi sosai suka wanzu a
dakin
kwana ciki shirin bacci. Yana kwance kan
gado
rigingine yana kallon samma,alamun rashin
ta
cewa. Ita kuma tana ta lakakin murza
turare
gaban madubi wanda shi kansa ya tabbatar
ba
abin da ya zaunar da ita ke nan ba, rashin
abin yi
ne kawai irin nasa. Sai can da hakura ta
janyo
dirowa ta fito da Envelop ta janyo stool zuwa
gabansa ta zauna ta ce masa. "Abdul tashi
mu yi

magana ta fahimta don Allah. Ya yunkura ya
tashi zaune kirjinsa na dukan uku uku
kamar
yadda nata ke yi. Ta mika masa Envelop
tana
cewa. "Ga wannan,malam ya umarci na
rubuta na
baka". Hannuwansa na karkarwa ya bude
Envelop
ya zaro a gaggauce ya karanta salon da
takardar
ke dauke da shi,dan rudani kawai sai ya yi
zuru
yana kallon ta bayan ya gama karantawa.
Dan
haka ta ci gaba da magana cikin rauni. "Zan
fara
da neman gafararka bisa laifuffukan da na
dinga
yi maka abdul,zuciyata da kwanjina, wato
niyyoyina da abin da na aikata,wanda ka
sani da
wanda baka sani ba, don girman Allah ina
neman
gafararka" Yanzu mazantakarsa ta

dawo,dan
cikin dakewa ya tare ta "Za ki fi birgeni
idan kika
fada min wanda ban sani ba din, duk
muninsu na
yi miki alkawarin zan fahimce ki". Kai tsaye
ta
amsa. "Yunkurin zubar maka da ciki". Ya yi
ajiyar
zuciya ya yi murmushi ya ce. "Na yafe miki
dukkan laifin da kika yi min". Ta kada kai
kanta
na sunkuye sannan ta kuma nisawa. "A yau
zan
dawo da wuta magana da ka fada min in
nuna
maka gamsuwata a kanta,wato ka taba ce
min ko
ya ya akwai digon sonka a raina na
karyata,ban
kuma taba saka ran hakan za ta yiwu ba sai
dab
da za ka bata,wato lokacin da nake yunkurin
zubar da cikin yadda ka rika fishi dani kana
min

fada yadda kake so. Sai na dinga jin gaba
daya
duniyar ta yi min zafi fiye da yadda kake
tsammani a wannan lokacin,na dinga jin ka
bar
fishi dani mu zauna lafiya kamar shine
matsalata
kadai a duniya. Magana ta gaskiya tun a
wannan
lokacin na fara tunanin ya kamata na zauna
a
gidan nan saboda haka ba dole malam ya yi
min
ba, ya yi min nasiha ya kuma ba ni
zabi,dama
abin da ya kamace ni ke nan. Ko bana sonka
ina
zan tafi in. Kai maka da ko 'ya?" Ya yi
dariya
kawai yana kallon ta,sai ta yi fuska sosai ta
dora.
"Sai dai akwai sharadin gaskiya wanda nake
so
ka fahimce ni a kansa ba zan iya zaman
cikin

gidan nan ba abdul,dalilan da nake jin ni
dai
masu karfi ne a wajena. Ya tare ta shi ma
cikin
yin fuska. "Kamar kin taba fada min kuwa
mun
gama zube sharuda tun a waje". Ta dube shi
da
kyau ta ce. "Au abdul a kan wadancan
sharudan
kake so mu dore?" Ya girgiza kai. "In na
fada
maka dalilan na yanzu idan kana da neman
shawara kana iya tuntubar malam,in ma ba
za ka
tuntube shi ba ni ka bani dama in tuntube
shi".
Ya yi shiru yana kallon ta ita ma ta yi shiru
tana
kallon sa har sai da ya tabbatar ba ta niyyar
magana sannan ya ce mata. "Ina jin ki
mana
fatima". A raunane ta ce. "Wallahi da gaske
ba
zan iya zaman gidan nan ba sai dai a canja

min
gida,ina da kishi ba zan iya jure in dinga
ganinka
da wasu matan ba, ina son rayuwar walwala
da
abin hannuna. Hakan ba zai samu ba kila in
na yi
ya zama rigima,ban iya hayaniya ba,ba
kuma na
son in dore cikin balle har'ya 'ya su taso su
dauki samfur. A cikin gidan nan kuwa laifi
ba sai
ka yi niyyar yinsa yake zama naka ba.Abu na
karshe shine,ban yiwa kaina tanadin mutuwa
yanzu ba gaskiya,nima gara in zauna in yi
rayuwa
mai dadi a gidan aure,amma na tabbatar
sadiya
za ta iya kawo mu harin kisa ba tare da na
cancanci haka ba...." Ya tare ta fuskarsa
babu
yabo babu fallasa. "Haba fatima,kar kishin
ya.
Sanya ki wuce gona da iri mana....." Ita ma
ta yi

saurin tare shi. "To ina ma kishin yake,ai
ban fara
shi ba tukunna.ina fada maka ne bisa abin
da ya
faru,bana son munafinci da kumbiya
kumbiya da
al'amura alhalimn ba za su amfane ni ba.
In
sadiya ta yi nasarar kashe ni duk yadda
kake
sona ba za ka iya dawo dani ba Abudl,sai
dai a
yiwa iyayena asara ta..." Ya tare ta da
tuntsura
dariya. "Haba fadima,ban da mayar da
allura
garma mana, a fadace fadacen a kike da
sadiya
ta taba ikirarin kashe ki? Kai tsaye ta amsa.
"Ranar da ka bata hankalina a tashe saboda
ina
ta jiran shigowar ka,sai na tashi na tafi in
tambaye hindatu ko ka sanar da ita za ka je
wani
gurin. Wallahi sai na sami sadiya a dakin da

galan da ashana tana hankoron sai ta zo ta
kone
mu saboda tana zaton ka dawo kana cikin
dakina
hindatu tana ta fama hana ta. Amma ka
fahimce
ni, ba na fada maka ba ne dan na bata ta a
wajenka, na fada maka ne dan shine dalilin
da
yake bukatar karin bayani,sai dai ko babu
shi da
gaske nake ina son a canja min gida,in kuma
zaman katya kake so mu yi sai in janye
gaskiyar
tawa". Ta dinga jan fasali saboda ya rasa
ta inda
zai bullo mata, ya tabbatar ba ya son bacin
ranta,musamman da ta ambato zaman
karya.
Amma batun canji gida wani gingimemen aiki
ne
a wajensa. Sai ya kamo hannunta ya janyo
ta
dawo kusa da shi ta zauna, ya dafa
kafadarta a

tausashe ya ce. "Kin karade lissafinki kuwa
a kan
canja miki gida fadima? Misali ko ina da
gidan
fadima? Misali ko ina da gidan da zan canja
miki
don Allah ni ba ki tawaye ni ba a matsayina
na
mayen kallon fuskarki kullum? Kuma
yaranmu ki
jaza mana wata dangantaka ta nesa dan
suifi
son ki da ni? Ta koma hannunsa ta rike tana
girgiza kai. "Abdul kana son kallon fuskata
tasa
ka farin ciki? Kana son ganin 'ya'yan naka
cikin
walwala? To in dai a cikin gidan nan muke
na
rantse maka da Allah ba zai samu ba. Ba
zan rufe
ka ba,nice tushen farin ciki,ni kuma na
tabbatar in
dai a cikin gidan nan ne ba zan yi shi ba".
Bai

taba tsammanin fatima tana da jayayya ba
sai
yau, kuma ya kusa yin jan ido ta bari,sai
ma ya
kuma bullo da wata lallabawar. "Na
yarda,amma
za ki bani dan lokaci na samar da gidan ko?
Bani
da sha'awar biyan haya", Cikin kyautata
murya ta
ce. "Gidan ba matsala bane ina dasu,sai ka
zaba
a ciki. Ya yi saurin tare ta. "Ba zan laminci
hakan
ba,ke nake so ba tare da kudinki ba,kuma
duk
wani abu na sarayar da hakki ba na cikinsa
fadima". Ta dan ja fasali sannan ta dube
shi.
"Wanne tsari za ka bi wajen sama min
gidan?"
Shima ya jima yana tunani sannan ya ce.
"Zan
nemi bashi sayan gida a ma'aikatarmu,na
zan ba

za su isa sayen gidan da za ki zauna ba,
saboda
haka zan yi tunani hanyoyin da za su kawo
wasu
kudin". A nutse ta ce. "To idan kyauta na
baka
gidan fa? Nan ma ya girgiza kai. "Bana so".
Yana
rufe baki ta karbe. "To maimakon ka je
ma'aikata
neman bashi ni ka zo gurina na baka mana,
sai
ka fadi tsarin da kake son ka biyani". Nan
ma ya
girgiza kai amma bai tanka ba. Ta jima cikin
tsura masa ido sannan ta sauke numfashi ta
ce.
"Abdul cikin biyun nan fa dole ka dau daya
wallahi, ko ka karbi gida kyauta ko kuma ka
karbe shi bashi, ban lamunci fita waje ciwo
bashi
ba. Kuma ni ko haihuwa bana so

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login