Showing 3001 words to 6000 words out of 13980 words
Chapter 2 - ZUCIYA DA KWANJI BOOK 4 Hausa Novels by MAIMUNA IDRIS SANI BELI .pdf
wayoyinsa a kashe.sai ya yi waya ya tambayi
sakatarensa wanda ya tabbatar masa Alh ya
jima
ba ya gari. Sai dai ya kasa rinjayar da ita.
Da aka
kwana biyu ya lalubo kasar da Alh yake,
wadda
kuma ya ga yana da lambarsa ta can kasar
sai
ya shiga neman sa a wayar, nan kuma
kememe
Alh ya ki daga wayarsa. Daga nan fa ya
rinjayar
da yakinin lallai akwai hannun Alh cikin
kamun da
aka yiwa Abdullahi. Sai shima ya canja
dabarar
fafutuka,amma cikin sirri har ya tarar da
gasjiyar
cewa Alh ne ya sa aka sakace Abdullahi bisa
tuhumar cin amanarsa a wani kasuwanci da
suka
kulla. Sai dai abin takaici an ki sanar da shi
nau'in kasuwancin Dan haka ya koma
fafutukar
ganin Alh,nan ma abin ya faskara har wanke
kafa
ya yi zuwa gidansa da ofis dinsa,inda aka
tabbatar masa ya dawo daga mexico
shekaran
jiya ya koma kazakunstan,kuma watanni
biyu zai
dawo. Shine fa ransa ya baci,wato ya kulle
mara
gata ya yi tafiyarsa,Allah basshi idan ya
mutu sai
a fito da gawarsa. Dole abdulwahab ya ware
lokaci na musamman ya ga malam a sirri.
"Anya
matsalar nan ta abdullahi ba ta siyarsar
cikin
gida ba ce? Ina tsammanin an lullube kura
da
fatar akuya ne fa?" Malam ya yi shiru yana
kallon
sa cikin damuwa da doki,sai dai bai ce komai
ba
har abdulwahab din ya dora. "Alh sulaiman
shi ne
tsohon mijin amaryar abdullahi,a sanin da
na yi
masa bai kwallafa rai a kan komai ba a filin
duniya sama da fatima, Kuma har Allah ya
yi
rabuwarsu cikin mayen sonta yake. Ya sha
neman
fatawa a gurina game da yadda za ta
halatta a
gare shi saboda ya yi mata saki uku ne lokaci
daya. Da na ki ba shi kofa ma sai muka so
mu
sami sabani da shi,daga baya na samu
labarin
yana tura samari gidansu dan su yi auren
kisan
wuta,amma da yake kawunta tsayayaye na.
Sai
ya ke shatale kafarsa. Na daina samun
labarinsa
tun dai dai lokacin da ka sanar dani
Abdullahi ya
kara aure, ban san ma wace ce matar tasa
ba sai
watan da ya gabata na je na ganta,kuma
daga
nanZuciya d kwanji 4
5
Ne na fara zargin akwai hannun Alhaji cikin
kama
abdullahi. Illai da na bincika sai na tarar da
hakan. tsoro na daya malam, Allah dai ya sa
ba
hayar abdullahi Alh ya yi dan ya halatta
masa
matarsa fatima ba, shi kuma ya gaza aikata
aikin
da ya sa shi. Musamman da yake na ga
jami'an
tsaron na ta kumbiya kumbiya da laifin da
ake
tuhumarsa da shi, sai wani saye shi
suke.....".
Malam ya katse shi cikin jimami da
sallamawa.
"Ai zancen ke nan ma abdulwahab.....
Innanlillahi
wa'inna ilaihi raji'un,ka ga irin
tarangahumar ta
abdullahi ko?" Abdulwahab ya tare da cewa
"A'a
kar mu yi saurin yanke hukunci mu jira mu ji
daga bakinsa ko? Malam ya kada kai tare
da
fadin. "Manzon Allah (S.A.W). Ya yi gaskiya.
Ya
ce. "Karshen duniya fitintinu A su
yawaita,kana
gudun fitina tana binka har cikin gidan ka,
cikin
dakinka,amma mafi girman fitinar da maza
za su
shiga a kan mata ne." "Ubangiji ya kubutar
damu". A sanyaye malam ya ce. "Amin,sai
ka yi
kokari ka ganshi gobe, daga nan sai mu san
matakin dauka tunda ba zamu bar ransa ya
salwanta bisa son zuciya ba". Abdulwahab ya
rusuna yana cewa. "To Allah ya nuna
mana".
******************************
************
Washegari da abdulwahab ya sami ganin
abdullahi ya gabatar masa da wannan zargin
sai
ya karyata. Abdulwahab ya dinga yi masa
dabaru
iri iri amma Abdullahi ya taurare kan
ra'ayinsa,ba
dan komai ya yi hakan ba sai dan dorar da
burin
fatima wanda ya san ta a kan kiyayyar
maganar
ta fasu. Kuma a ganinsa boye sirrin ya
taimaka
wajen riketa a cikin gida kila in da ya fasa
shi
tuntuni to da tuni ya zame mata jiki, shi
kuma ya
yi asarar makamin yi mata barazana. Ko
duk
babu wannan zai iya ci gaba da lullube aibun
fatima matsawar ransa ko da Kuwa
lullubewar shi
ba zai amfane shi da komai ba. Sai dai ya
cika
da mamakin yadda aka yi hankalin 'yan'uwa
da
abokai ya kai ga Alh,ko gane da hannunsa
cikin
kamun da aka yi masa. Shi dai sagiru ne ya
zantar da shi ya kuma sanar masa bai sanar
da
su yaya abdulwahab ba, jiyan nan kuma
kawu ya
zo shima ya ishe shi da magiyar ya sanar da
shi
idan akwai hannun Alh ko fatima cikin
kamun da
aka yi masa,ya tabbatar in dai akwai
hannunsu,to
duk sai ya maka su kotu. Shima dai kamar
yadda
ya ki sanarwa abdulwahab a yanzu haka ya
ki
sanar da shi,kalma daya yake maimaitawa.
"Nifa
ban san abin da na yi ba aka kama ni".
Abdulwahan ya ce. "Amma suna maganar
akwai
makudan kudade da aka karba daga gare
shi bisa
wata ajanda,amma ka cinye kudin ba tare
da ka
yi masa aikin ba". Abdulwahab ya dan ja
fasali
annan ya amsa. "Eh,sai a tambaye su idan
kuden
suke bukata ba raina ba a kawo musu,komai
yana nan ajiye kobo bai ciwon kai ba".
Abdulwahab ya mike zuciya a kule lokacin da
aka
yi masa inkiyar lokaci ya cika,ya subi
Abdullahi
ran a bace ya ce. "Shi ke nan zan turo maka
malam sai ka fada masa aikin da kuka yi
ajandar
a kai har ka karbi kudin". Abdullahi dai bai
tanka
ba,har yayan na sa ya gaji da kallonm sa
cikin
hudi ya fice. Abdulwahab na fita ya koma
wajen
ofisan da aka ce case din na hannunsa,suka
fara
dogon turanci na neman sanin aikin da aka
bawa
abdullahi ya yi zamaba. Cikin aminci,da
kuma
dalilan da suka sa har yanzu ake tsare da
shi fiye
da wata uku ba a kai shi kotu ba. Amma
ofisa
babu amsa sai zullewa yake da dabaru irin
nasu
na 'yan sanda,sai Abdulwahab ya koma
tambayar
yawan kudin tare da dorawa da cewa. "Zan
biya
Alh a sake shi" Babu ko kunyar shekaru da
na
aiki ofisa ya ce. "Alh aiki yake bukata ba
kudi ba,
ya tabbatar mana ko yanzu ya yi masa aikin
ya
yi alkwarin ninka kudin ya ba shi a kan
farashin
farko". Abdulwahab ya sauke numfashi cikin
cije
lebe ya ce. "Haka ne? To za mu bi hanyar da
ta
kamata don neman hakkinmu kamar yadda
ya bi
tasa hanyar dan cimman burin
zuciyarsa,wanda
munin abun yasa kuka kasa fada mana"
Like · React · Report · May 21, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji 4
6)****************************
*************** A
wannan satin malam ya yi abin da tutuni
yake
juyawa fuska,wato neman alfarma ga
tsofaffin
dalibansa wadanda suka zama kusushi yanzu
a
Nigeria game da matsalar dansa Abdullahi.
Ai ba
a kwana ba kuma ba tare da wanda ya dauki
nauyin ya tako da kafarsa ba,waya kawai ya
yi a
kan lallai kar a sake a bar Abdullahi ya kara
kwana a nan. Sai ga wayoyin ofisoshi na biyo
malam da yayyen abdullahi a kan su zo su
dauke
shi. Bayna sun zo aka zauna zaman gigita
biro
na kafa sharadai da neman dawo da
Abdullahi
duk lokacin da bukatar hakan ta taso, wato
in Alh
ya dawo Nigeria dan zaman sulhu ko bukatar
tafiya kotu. Umarnin da malam ya bayar
shine, a
kai abdullahi gida kar a kai shi gidansa.
Hakan
kuwa aka yi, aka wuce da Abdulllahi gadon
kaya.
Mata na ganin yadda abdullahi ya dawo sai
kuka,saboda abdullahi ya fita
kamanninsa,kasu
suwa a jikinsa sai ka kirga su suma ko ina
babu
kyan gani, kaya bakikkirin sai kwarkwata da
kudan cizo ke binsa. Har da malam a cikin
aikin
wannan bikin,aka dinga tanada masa ruwan
wanka kala kala da magungunan cututtukan
fata
ana binsa da shi yana canjawa. Ya sake
dukkan
gasusuwan jikinsa,ya yin da sahabi ya aske
masa
kansa.kafin wani lokaci ya tashi daga suffar
dodo
ya dawo mutum. Illa kasala da tsananin
ramar da
ta tafka,kayan da ya cire malam da kansa
ya sa
musu wuta. Aka ba shi abinci mai dumama
ciki,
sannan aka kira likita ya kula da shi, ya yi
masa
allura hade da magunguna. Sai da ya yi
ramuwar
wasu sallolin da suka tsere masa sannan ya
kwanta bacci. Bai farka ba sai daba da
magariba,aka yi sallah da shi sannan ya
zauna
sauraron karatun dole tunda malam bai
masa
izinin tafiya ba, duk kuwa da yanzu dukkan
hankalinsa na ga iyalinsa,musamman fatima
da
ajiyar da ya bar mata. Sai bayan karfe
goma
malam ya kebe da shi,ya yi masa doguwar
nasiha mai nuna mutum tawakkali da hakuri
yadda ya tsinci kansa a rayuwa,tare da
kiyaye
al'amura na soyayyar zuciya. A karshe ya
dire da
neman lallai abdullahi ya bayyana masa
kasuwancin da ya kulla da Alh, Babu yadda
abdullahi zai yi tunda ba yi yiwa mahaifinsa
karya, kuma dama can ba shi da abolon
shawarar
da ya fi shi tun yana karaminsa,dan haka
ma
kullum malam kan yi sharhi a kansa da cewa.
"Abu Turab na da taurin kai da
kiriniya,amma
yana da kaifin hankali da hangen
nesa,shawara
da rike sirri tare kuma da juriyar nacin abin
da ya
sanya gaba". To yanzu ma bai rufewa malam
komai ba, tun daga ranar da suka hadu da
Alh a
asibiti ya yi masa tayin auren, yadda ya ji a
ransa zai iya auren dan kubutar dasu ba
tare ma
da ya san wace ce matar ba. Yadda kawu ya
karbe shi,auren da kudade da Alh ya ba shi,
zamansa da fatima da kwanjin da yake
amfani da
shi a tarbiyarta tare da dumbin nasarar da
ya
samu a kanta har ya zaunar da ita a
gidansa
tsawon shekara. Haka zuwan bai rufe masa
komai ba yadda yake jin zafin soyayyarta
cikin
ransa da yadda yake jin duk runtsi ba zai
iya
rabuwa da ita ba. A karshe ya kulle masa da
batun tsohon aikinta. Malam ya yi suguri
yana
kallon ikon Allah kawai,ya ma rasa abin da
zai ce
masa. Ba ya so ya ce Abdullahi ba kyauta
ba,
idan aka duba kaddara zama da ta rabon
da
ubnagiji ya shirya a tsakaninsu,da kuma
jajircewarsa wajen hana aikata barna. Sai
dai ga
shi yanzu lamarin ya zama wani kantafi da
rayuwa. Na biyi bayan son namiji ya zafafa
soyayya ga mace,matan ma irin su fatima
kamar
yadda ya fahimci abdullahi ya fada tarkon
fatima,kamar yadda Alh ke jin jiki a cikin
tarkon
son. Mata shaidanu ne, yanzu sai su sanya
ka
wasa da addini matukar ba ka zama mai
shugabantar hankalika a kansu ba. Fiye da
mintuna ashirin malam ya kasa samo bakin
zaren
da zai warware sharhi a kan wannan labarin
na
abdullahi, a karshe sai kawai ya dube shi ya
ce.
"Shi ke nan tashi ka shiga ciki ka kwanta,in
Allah
ya kaimu gobe sai ka je gida duk da nasa an
yi
musu waya an sanar dasu fitowar ka,amma
sai
na ga gara ka dan huta ka dan fara cikowa
zuwa
goben su ganka tsab,ka san mata da rauni".
Abdullahi bai so haka ba, amma babu halin
ya
muusa. Amma dai ya ci gaba da zama gaban
malam din kamar ya kwanta masa saboda
nuna
ladabi. Can ya kara rusunawa ya ce, "godiya
nake
malam, sannan ina neman alfarmar dan
Allah ko
su yaya kar a sanarwa magana nan,bana son
su
canja fatima a idonsu tunda ta zama uwar
'ya'yana, dole ta zama a halin gidan nan.
Kuma
ita ma na san ba za ta so fallasar maganar
nan
ba dan ku san da wannan damar na yi
amfanin
na kulle ta a gida na kuma hana ta waya da
mota". Malam ya yi murmushi ya ce. "An bar
maganar tsakaninmu mu biyu,sai dai ba
alkawari
ba ne don ina ganin dole ma a sako yayanka
Abdulwahab cikin maganar don yiwa tufkar
hanci,tunda abokin sa ne kuma shima na
tabbatar
zai boye sirrin hasalima nan ya zo min da
zarge
zargen amma ya lullube ya ce kar a sanar da
kowa gudun kar a fassara yadda rai ya so".
Fuskar abdullahi ta cika da walwala, ya
dinga
rusunawa yana zubawa malam godiya.
Washegari
da safe da ya je gaishe da malam sai ya ce
masa. "Ka jira bayan fitowar sallar juma'a
na kai
ka gidanka". Cikin. Tsannanin fargaba
abdullahi
ya ce. "Toh" A nan gidansu ya sake
wuni,wanda
ya dinga cika da dingi da abokan arziki
maza da
mata masu zuwa jaje da barka da arziki. Sai
karfe biyar direban malam ya jasu daga shi
sai
malam din zuwa gidansa. Tun daga nan
hantar
cikin abdullahi ta shiga kadawa,dan ya
tabbatar
malam ba zai kai shi gida babu wata hikima
ba.
Fatima na falonta a zaune cikin wata irin
rayuwa
mai kama da mafarki in aka kwatanta da
sauran
furannin rayuwarta da suka shude a baya.
Yau
tun safe maryam da ta zaku da son ganin
abdullahi ta tsere gida ta barta,suma sun zo
da
safen saboda zaton Abdullahi yana
nan,amma jin
yana can gidansu ko zama basu yi ba babu
walwala suka wuce suka barta. Tana jiyo
yadda
gidan ya yi tsit da hayaniyar dangin hindatu
da
na sadiya,ana ta gaisuwa a nutse kamar
jerin
kafafun bene,ta tabbatar abdullahi ya
karaso,kila
cikin rakiyar mahaifinsa. Haba! Sai ta ji
falon ya
fata zagayawa da ita. Ta yunkura ta tashi
tsaye
da kyar cikin rashin gane halin da take
ciki,farin
ciki take ko farbaga? Da wacce fuskar za ta
karbe
shi? Ta da can wadda suka saba ko wata
sabuwa daban? Duk biyun babu wanda ya
birge
ta,don ta san babu wanda karbe ta a
ciki,wanda
suka saba bai amfane ta da komai ba,
wanda za
ta canja kuma ba ta shirya
Like · React · Report · May 21, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji 4
7)Masa ba, yanzu yadda za ta kalle shi da
wannan
katon cikin ne ma ya fi damun ta. Ba ta
samui
amsar ko daya ba cikin tambaye tambaye
nata ba
sai kawai ta gada su duka tana ji dasu. Ta
kasa
zaune ta kasa tsaye sai kallon kofa take,duk
da
ta san mawuyacin abu ne ya shigo dakinta
yanzu
kamar yadda ba za ta iya daukar tata
kafar ta je
nasa dakin ba. Duk da haka sai ta sami
kanta da
dauko zundumemen hijabi ta sa,ko ba ta san
dalili ba dai ta yarfa ta fi kunyar ya ganta
da ciki
a yanzu. Malam na tare da su sadiya a falon
abdullahi,yana ta yi musu godiya da hakurin
zama gidansu da suka yi,yana kuma hada
musu
da nasihar hakuri da zama lafiya wanda ya
fi
zama dan sarki,duk dai a jirwayen yin
fadan da a
yanzu ya zama kwantai na korafin da sadiya
ta
kai masa ranar da abdullahi zai bata.
Sadiya dai
ranta tas da rashin zuwan fatima gaishe da
malam, kawai dan ya ga bakin halinta, ga
shi dai
hindatu ta yi sawu biyu na aikin rabi ta
sanar da
fatima zuwan malam. Ba karamin dadi
hakan ya
yiwa sadiya ba, ita dai tana son fatima ta yi
bakin
jini a dangin abdullahi,gha shi kuwa malam
bai
damu da namen ta. Ba. Hasalima cikin
nasihar
da yake musu ta daidaiku bayan ta gaba
daya
sam bai sako da fatima ba. Amma abdullahi
duk
sai hakan ya dame shi,don tun da ya yi aure
yau
ne malam ya taba shigowa cikin gidansa, ba
ya
son zuwan ya zama na tarihi cewa fatima ta
warerantar da shi. Can ya yi badarar
muskutawa
ya ce. "Hindatu ina tsammanin rabi ta
shafa'a,je
ki kira fatima". A nutse malam ya ce.
"A'a,kyale
ta,a kaini wajen ta". Duk suka yi turus!
Abdullahi
kuma kirjinsa ya hau bugawa fat fat! Sai
dai bai
bari fuskarsa ta bayyana ba. Hindatu ta
mike ya
yi saurin dakatar da ita. "Bari na sanar
mata". Ya
murda kofar dakinta ya tura ya shiga kai
tsaye da
sallama a hankali,ya same ta zaune kan
kujera ta
yi tagumi da hannun da ta dogare da
hannun
kujera. Ya karasa gabanta a nutse ta mike
tsaye
suka tsaya suna kallon kallo,kowa zuciyarsa
a
rikice. Ta hada kallonsa da sassarfar
numfashin
da ya ki boyuwa,shi kuma yana kallon ta a
rikice
ne saboda tsannanin tausayin ta. Ta rame
kwarai
tamkar mai hadiyar allura,fuskarta ta yi
wani iri
da alamun kumburi irin na masu ciki. Ya bi
ta da
kallo tun daga sama har kasa saboda yadda
sautin bugun numfashinta ke fita a fili da
kyar ya
kokarta ya ce. "Sawa zuciyarki nutsuwa ki
kwantar da hankalinki fatima". Ta sauke
ajiyar
zuciya ta kawar da kai gefe,sai ta ba shi
damar
dan juyawa ya dinga bin falon da kallo
saboda
yadda komai ya canja,kura da rashin
isasshen
gyara. Tausayinta ya kara cika ransa,ta
rasa
matamaki a lokacin da take tsananin
bukatarsa a
tsawon lokutan da ta diba a duniya,me ya sa
ya
manta wannan raunin nata lokacin da yake
tsare
bai nemi a kawo mai kula da ita ba? Ya tari
inda
ta mayar da kallon ta da sauri,amma ya
rasa
abin da zai ce mata,kawai sai ya bige da ce
mata. "Sannu fatima". Kawai sai kwallar da
rikeka
suka subuce suka fara zubowa da sauri ta
nemi
guri ta zauna ta rufe fuska da hannu tana
shesshekar kuka. Ya yi saurin durkushewa
gabanta ya rike hannunta cikin barin jiki.
"Don
Allah fadima ki adana hawaye naki zuwa
lokacin
da zan sami sararin share miki su, ki jira
zuwa
lokacin da zan marabce su in ji zubar su kin
ji?
Jin yadda hannunsa suka sirance cikin nata
sai ta
kara rushewa da shesshekar kukan,ya dinga
girgiza mata kai kawai ya kasa cewa
komai,har
da kyar dai ya nuna mata kofa a raunane
yana
cewa. "Na fada miki yanzu ba lokacin kuka
ba
ne,ki shirya malam zai shigo yana son
magana da
ke. Nan take ta tsayar da kukan ta zaro ido
a
firgice ta dube shi, da razananniyar murya
ta ce.
"Ka fada masa ko abdul? Ya girgiza kai
yana
kallon fuskarta kai tsaye da idon da ya tara
cikin
dabara ya kai hannun kan cikinta yana
tabawa
kamar mai taba kwai. Da yake hankalinmta
ba ya
tare da ita