Showing 36001 words to 39000 words out of 46557 words

Chapter 13 - HAUWA KULU YAR CIKIN BADALA 2 Hausa Novels .pdf

for
everything, musamman karatuna na sakandire, wanda (against all odds) sai da Allah yasa na
kammala shi. A kullum inna sare da karatun, saboda wahalar zirga-zirga ta rashin idanu, kalaman ka nake
tunawa suke zame min ‘inspiration’, kuma madubin dubawata a rayuwar lalurar dana tsinci
kaina.
Kalaman ka likita sunyi tasiri sosai wajen karafafani domin ina matukar jin dadin su a lokutan
da na bukacesu, cewa da ka yi “akwai iyawa cikin nakasa”, kuma ka ce min “ba nakasashshe
sai kasashshe”. Wadannan jimlolin naka guda biyu su suka zame min food for thought; su suka
sa na dage na jure da zuwa makaranta ba ido. ‘Obstacles’ da ‘hindrances’ da ke cikin lalurar
makanta duka basu sa na bari ya salwanta ba.
Babu wani abin karaswa cikin labarin namu a bayan tafiyar ka, sai na bacin rai da wahala na
zallan zalunci wanda kanin mahaifina ya sanya mu a ciki, a dalilin kwace gidan mu ya rusa shi.
Ni ban sani ba ashe tun lokacin batan Baba, Inna ta fara ciwon zuciya, don likitan dazu ya
tabbatar min ramin ya dade a zuciyar ta yayi akalla shekaru biyar, tana dai yin cuwuka a
tsaitsaye tana kuma kula da shan magungunan gargajiya dake kara mata ‘immunity’, shiyasa
bai ci karfin ta da wuri ba, bamu ankara ba sai da ya kayar da ita kasa warwas.
Likita rayuwar da muka yi gabadaya kaji-ka ji….” ta zayyano masa daga farko har karshe har
labarin bugeta da Yaya Jamilu yayi da mota ya kuma dage daga baya zai aure ta, wanda duk
shi ya janyo musu komai.
“Yanzu ina Jamilun? Me zai aura a wannan kankanuwar yarinyar? Bana jin lokacin ko SS2
kin gama, haba! This is sheer abuse. To ya san abinda Baban nasa yayi muku?”
Sarham ya tambayi Hauwa, (furious in anger), ji yake idon sa idon Jamilu da Babansa Zakari
sai ya shake su. Hauwa ta ce.
“Yaya Jamilu ban kara haduwa da shi ba, bamu kara jin duriyar sa ba tun tafiyar sa Delta,
kuma bana jin ya san abinda Baba Zakari ya yi wa gidan mu, saboda a lokacin yayi tafiya, ban
dai sani ba ko idan ya dawo daga tafiyar da yayi wani ya bashi labari”.
Sarham ya dade kan sa a sunkuye, yana tunanin ta wace hanya zai gayawa Hauwa ya sake
gine musu gidan su, da gini irin na zamani? Jira yake a sallami Inna daga asibiti ya dauke su ya
maida su gidan su na asali, ya kuma yi karar Baba Zakari kan abinda yayi, ko ba’a yi masa
komai ba hukuma ta shiga tsakanin sa da su”. Sun dade a wajen suna labari shi da Hauwa, irin yadda bai taba jin tayi magana mai tsayin ta
yau ba, sai da mamakin sa ya kasa boyuwa yace.
“Maijiddah, ashe dama kina magana haka? Da ni ne ba kya yi? To meyasa Maijidda? Me nayi
miki haka da zafi?”
Ya tsareta da ido cikin tuhumar dalili, kai kace kamar tana ganin sa, Hauwa ta rufe ido cikin
jin kunya, ta ce “ai don na dade ban ganka bane, daga yau zan rufe bakin ya koma kamar da”
Sarham ya lumshe ido kamar tana ganin sa, idonsa a kan zara-zaran ‘yan yatsunta ya ce “a’ah
ban yarda ba, a bude shi muyi ta shan hira abinmu, irin ta Yaya da kanwar sa da sukayi kewar
juna, kin san ni mai baki ne, mai yawan hira ne, shiyasa tamu ta zo daya nida Inna. Maijiddah
ina so in zama babban Yayanki daga yau, wanda kafin kowa ya ji damuwar ki nine mutum na
farko da zan ji.

Zan bar miki waya don mu dinga magana don zan koma wajen aikina babu jimawa, na rako
matata wankan jego ne, amma mun koma Jeddah da aiki tun da jimawa”.
Hauwa ta fiddo manyan idanun ta cikin mamaki ta ce “likita dama kana da mata?” Ya yi
murmushi ya ce “mamakin na menene haka? Amsarki a baya itace, a’ah, na dai aure ta babu
jimawa, bayan na kammala karatun dana tafi yi a Jeddah, a can muka hadu, duk da dai ba
haduwar mu ta farko kenan ba”. Hauwa tace itama likitar ido ce?” Dr. Sarham Yayi dariya yace
“exactly! Amma ya akayi kika sani?”.
Tace “na dade da sanin likitoci basa aure sai da liktoci ‘yan uwan su, watakila don kada a
shafa musu cuta?” Sarham me zai yi ba dariya ba yace “wato shi likita bashi da cuta a jikinsa
Maijidda?” Tace “da sauki dai” anan ma ta kara bashi dariya sosai, yace “ni kuwa da har na yi
miki takwara, na dauka kema likitar zaki so zama?” Kafin Hauwa ta kara magana sai Malam Isa
ya fito yana musu sallama zai wuce gida, tare da Salele.
Salele yaga Sarham, nan da nan ya shaida shi, ya hau yage baki don bai manta shi ba da
tarin alherin da ya dinga yi masa don ya dinga raka Hauwa Makaranta.
Suka gaisa da Salele suka yi sallama da su suka wuce, shi da Hauwa suka koma wajen Inna.
Hauwa na tambayar sa cikin mamaki.
“Da gaske likita ka yi min takwara da ‘yar ka?”
Zancen a kan kunnen Inna, ta dago tana kallon shi da mamaki itama, tace.
“Sarhamu kayi aure ne banida labari?”
Sarham ya sunkuyar da kai yana dan murmushi yace “eh Inna, har an samu karuwar
Hauwa’u, HAUWA-KULU!”. Ya dauko wayar sa daga aljihun sa ya nunawa Inna hoton
Waheedah cikin pink shawul daya dauketa dazu. A takaice ya basu labarin yin auren sa da Dr.
Madinah bayan ya kammala karatun da ya kai shi Jeddah, da irin neman da yayi musu kamar
ya zautu bayan dawowar sa.
A ranar ya jima tare da su suna ta labarin rayuwar su a kurna, rijiyar lemo da kuma unguwa
uku, da ta karatun Hauwa da aka samu kammalawa da kyar, da sudin ludayi, ta gaya masa
Hauwa ta fiddo da kyakykyawan sakamako sosai, wanda ba kokarin kowa bane nasa ne,
madallah da shi, madallah da haihuwar ’ya’ya irin sa, masu zamewa al’umma fitilar rayuwa
kuma bango abin jingina, madallah da tarbiyyar iyaye irin nasa, madallah da shigowarsa cikin
rayuwar su”.
Sarham (feeling overwhelmed with joy and happiness) saboda ya sha addu’a yau a bakin
Inna, ‘yar sa Hauwa ma ta sha addu’a, tace yadda ya tsayawa Hauwa-Kulu wadda a yanzu za’a
kira maariniya miskiniya ta samu ilmi daidai gwargwado duk da makantar ido, Allah ya tsayawa
tashi Hauwar ko bayan ransa, yasa tayi ilmin da zata zamo mai amfani ga al’ummar duniya. Ita da kan ta Inna data nisa, taji yadda lafiya ta wadace ta, bata san sanda ta ce ta tuba tabi
Allah ta bi asibiti ba! Daga yau ta daina kin asibiti tunda gashi ciwon shekara da shekaru ya tafi
cikin sati biyu. Ta kara da cewa Sarham “ashe abin naku dace ne!”.
Sai bayan kwana uku da yin haka aka sallami Inna, Sarham ya zo da mota ya dauke su zuwa
gidan su na unguwa uku yace “Inna koda abinda zaku dauka a gidan ku dauka, ku fito ina jiran
ku” Inna tace “ai nan ne gidan mu likita, yanzu anan muke zaune tun da jimawa” ya ce “na sani
Inna, zaku raka ni unguwa ne bazamu jima ba, amma dai in har kin yarda da ni, to ki kwaso
komai naku”.
Inna ta hau kwasar kayan tana kaiwa boot din motar Sarham tana fadin “yarda da musulmi

irin ka wajibi ne!”. Haka Hauwa ma, ta dauki kayan ta tsaf, suka kama hanya, Hauwa na gidan
gaba Inna na baya. Sarham na tuki cikin nutsuwa da kwarewa, bai tsaya a ko’ina dasu ba, sai a
kofar gidan su, gidansu na BADALAR Kofar Na’isa, dama sun riga sun shirya gidan dai dai
gwargwado da taimakon Malam Isa da Salele. An zuba komai na amfani mai saukin kudi. Inna tunda taga an doso kofar Na’isa ta soma hawayen tuna baya, kirjinta ya hau yin sama
da kasa, ita ta dauka zai kaita ta gaisa dasu Maikosai ne.
Amma sai ta ga anyi fakin a kofar wani sabon gida a bayan Badala, in har bata yi kuskure ba,
kuma idan har ba idon ta ke mata gizo ba nan din lungun su ne kuma unguwar su, da ko daga
makanta irin ta Hauwa ta warke itama zata gane su, tunda ga gidan Malam Isa nan ba abinda
ya canza shi. Sai ta kalli Sarham a gigice, bayan ya kashe motar a kofar gidan. Sai a lokacin yayi musu
bayani cewa gidan su ne ya karba musu.
“Ka karba mana kamar yaya?” Inji Hauwa, (sounding extremely puzzled). Inna kuma tace “ko
dai ka gina mana?” Muryar Inna ta tambaye shi cikin kuka, don dai a kan idon ta taga lokacin
da aka rushe gidan nasu wato gidan Malam Bilyaminu.
Sarham yace “Allah ne ya nufa gidanki ya dawo gare ki Inna, ni kawai na taimaka ne, kuma
kiyi hakuri zan yi wani shishshigi, a gaskiya zan yi karar kanin Baban Hauwa akan abinda yayi”.
Inna ta fara kukan farin ciki da dariya a tare, ta ce “Dan nan me zan ce maka? Wace irin
addu’a ya kamata in yi maka? Na rasa kalma a bakina da zata gode min kai.
Amma ka bar maganar Zakari, ni kam me zai sake hada hanyata da Zakari? Na roke ka ka
rabu da shi Allah na kaiwa karar sa kuma na tabbata zai saka mini. Na bar shi da fitowar rana
da faduwar ta”.
Ta share hawaye da habar mayafinta ta sake cewa. “Dan nan me zan ce maka?” A karshe
Inna ta fashe da kuka tana ce da Hauwa “gidan mu ne Hauwa-Kulu! Sarhamu ya kwato mana
da karfin mulkin Allah”.
Hauwa wani irin shock ta shiga na wucin gadi bayan fahimtar hakikanin halin da ake ciki. A
yau ma dakacen nan ta kara yi na shekara da shekaru, mai fatan “INAMA TA GA FUSKAR
LIKITA SARHAM!”
Suka karasa cikin gidan Inna rike da hannun Hauwa shikuma ya dauko bakko kayan su ya
kai su har dakin da ya zama na Inna, an saka katifa a kasan kafet dirkekiya an shimfide ta da
sabon zanin gado. A gefe ga kwabar saka kaya an yi mata. Haka dakin Hauwa ma amma ita a
daki aka yi mata toilet don kada ta sha wahalar fitowa tsakar gida. Ga safayan daki da ba kowa
yace na Baban Hauwa ne duk ranar da Allah ya dawo musu da shi. Sai kamshin sabon fenti da
suminti gidan yake yi gwanin dadi.
Dakuna uku ne aka yi musu kamar da, kitchen kuwa da toilets na zamani aka yi masu masu
tangaran (tiles) da Inna tayi ta shafawa da hannun ta a gaban Sarham tana shi masa albarka.
Hauwa duk jikin ta yayi sanyi musamman in ta tuna yadda ta ke share Sarham a baya, da
kullacin wai ya makanta ta, Sarham is beyond her imagination a kaunar fisabilillah da yake yi
musu.
Aka kai Hauwa nata dakin aka nuna mata direction na sallah dana zuwa toilet da madannin
flushing. Ga dan karamin firji a gefen katifar ta (bed side fridge) Sarham ya ajiye mata don ya
san ta da son shan abu mai sanyi tun baya, kai yau Inna da Hauwa farin cikin ya fi gaban ayi
masa kuka ko dariya sai dai kawai ayi kurum, kamar yadda Hauwa tayi kurum!

Bayan sun gama zaga gidan sun zauna suna hira shi da Inna. Ya ce “wai ta yaya ma aka yi
takardun gidan suka je hanun Zakari? Bayan kowa ya shaida ya sayarwa da malam Bilyaminu
gidan kamar yadda Malam Isa ya bashi labari?”
Inna ta ce “umh, ai in kana neman hatsabibi ka samu Zakari ka gode Allah, maiyuwuwa yana
da na kwarai dinne ya bawa Malam na jabu, ko kuma yasa an yi masa na jabu, oho, tunda har
gobe na gonar su Baban Hauwa ya gayamin suna hannun sa, gab da batan Baban Hauwa,
yace min sai ya karbi hakkin sa gun dan uwansa Zakari, wanda yake boyewa don a tunanin sa
ya dauka Malam bai san da su ba.
Ina nufin gonar mahaifin su ta Panshekara wadda girman ta ya kai na naira miliyan daya”.
Sarham ya shiga mamaki mai yawa, ashe shiyasa Baban sa baya son sake aure? Kullum sai
yace masa yana tsoron rarrabuwar kan su ne, shiyasa bai yi musu ‘yan uba ba.
Sun dade suna zantawa kamar Da da uwar sa, Hauwa kuwa tunda ta shige daki ta kwanta a
sabuwar katifa bata kara fitowa ba don daga baya ma wani ni’imtaccen barci ne yayi awon gaba
da ita, irin wanda rabon ta da shi tunda Inna ta fara kwanciya ciwo.
Da ya zo tafiya ne jin ta shiru ya dan leka dakinta, nan ya ganta tayi dai-dai tana kwasar barci
da nutsuwa da kwanciyar hankali, numfashin ta yana hawa yana sauka freely, ashe tafi kyau in
tana barci irin mutanen da ake kira sleeping beauty. Ya dan kalleta na ‘yan sakanni yana jin ta
kamar Sumayyah a ran sa, ya kudurce a zuciyar sa zai tsayawa rayuwar ta, zai ingantata, zai
mata abinda idan Sumayyah ce nakasar idanu ta sameta zai tsaya ya yi mata.
Daga nan gidan su ya koma, a falo ya tadda iyayen sa, kallo daya zaka yi wa Dr. Sarham
yanzu ka tabbatar yana cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ba kamar watannin baya ba, gashi
Madinah ta cika masa ciki da abinci mai dadi, so bai waiwayi abincin sa dake bisa tebir ba ya
zauna gun Abba Prof. amma ya killace bakin sa baiyi zancen su Hauwa ba, don ya lura bat un
yau ba Abban (is not interested) akan zancen su, musamman da ya ga ya dauki al’amarin su da
muhimmancin da yake neman wuce kima, kuma ya tambayeshi meye alaqar su ta hakika ya
tsaya yi masa kame-kame. Tun daga lokacin yace,
“to in babu wata kebantacciyar alaqa da musuluci ya yarda da ita, to ya cire damuwar rashin
ganin su daga ran sa, ya bar su a hannun Ubangijin da ya halicce su, tunda uban su ma da ya
bar su ai basu kasa rayuwa ba.
Don haka baima kowa zancen ya ga su Hauwa ba, bai sani ba tuni Mai Shari’ah wato
Barrister (Mama) ta dade da ramfo shi.
Kafin kwana uku duk makwabta sun san da dawowar Hauwa da Innar ta, aka yi ta shigowa
ana ma Inna barka da arziki, da dawowar ta gidan ta, ana hirar yaushe gamo, aka yi ta tuna
baya ana tattaunawa kan girman yara na yanzu, musamman ‘ya’ya mata da ba wuya sun girma,
dubi dai yadda Hauwa ta gandame, ana tattaunawa a kai, kusan duk jama’ar Badalar Kofar
Na’isa sun san Inna da abinda Zakari yayi mata saboda kyakkyawar mu’amalar ta da kowa,
sannan yanzu sabon gidan nasu ya fito da gidan sosai. Har an sawa gidan suna sabon gida. A
yanzu sai ya zamana babu gida mai zubin zamani da kuma kyawun nasu a bayan Badalar ta
Kofar Na'isa.
Washegari da suka wayi gari a kwana na uku da tarewar su. Inna ta ce da Hauwa zata shiga
gidan Malam Isa su gaisa da iyalinsa, tace saboda ta ga kowa ya shigo mata murna banda
Maikosai. Hauwa tace “toh Inna kada ki dade” tace “kada ki damu bazan jima ba”, ta fita.
Tayi sallama gidan Malam Isa, Maikosai, wadda sunanta na ainahi Talatu, ta gama suyar

kosan safe ta sayar, tana wanke kayan suyar ta a gindin rijiya ta amsa sallamar Inna, sannan ta
juyo don ganin mai shigowa sai ta ga Innar Hauwa, nan da nan ta yi fuska ta juya ta cigaba da
abinda take yi ta barta anan tsaye, sai da ta kammala tas ta zo ta zauna ta baiwa Innar Hauwa
kujera ‘yar tsugunne, itama ta samu waje ta zauna akan tabarmar kofar dakin ta, suka gaisa
kadaran kadahan sai Inna tace.
“Zuwa nayi mu gaisa Maikosai, naga kowa na zuwa muna gaisawa, ke kadai ce ban gan ki
kin zo ba, shine na shigo in gaida ke, Allah dai yasa lafiya”, inji Inna.
Mai kosai ta ce “in kinji shiru ai shine lafiya, lafiya ke buya ba rashinta ba, don haka ni lafiya
ta kalau, har kin yi GAIBAR ne kin dawo?”
Cikin rashin fahimta Inna tace “menene kuma GAIBA?” Maikosai ta kalle ta a lalace tace “kina
nufin ni zaki binne a baibai? Ko ba da hausa nake magana ba? Kin dauka ban ji me kuke
shiryawa ke da bazawarin ki Malam Isa Mai Itace ba, na kiyi Gaiba ki dawo ya aure ki?
Allah na tuba ko meye abin likewa tsoho kamar malam Isa oho, yana fama da kakhi da
majinar tsufa?”
Inna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login