Showing 3001 words to 4609 words out of 4609 words
Chapter 2 - BAKAR ANIYA Book 1 By Aminudden Ladan Abubakar Alan waka.docx
ke baiwa idanu damar hango irin launin tufar da aka sanya daga cikin, shimi ko siket, kuma shine ya zama karin armashi mai kallo, da mai kwalliyar, musamman gangar jiki irin nasu Hauwa'u mai sanya zuciya makaki.
Tun fitowarta sai a yanzu ne take da nasanin irin wannan shiga da ta yi, don ganin irin daukar hankalin mutane da take yi, tare da hangen ma'kin da take a halin yanzu, na ganin cewar 'yar ratar dake a tsakaninta da matan aure kadan ce. Kuma ta yi zabinta na karshe, babu wani da namiji, da zai burgeta ko ya bata sha'awa, kuma ko babu komai dai wannan shiga, na iya sukar mutuncinta a idon mai mutunci, ga kuma uwa uba bayana tsiraici, don ganin shatin surar mace ma tsiraici ne.
Ta yi nadama, amma bai sanya ta komawa gida ta canza shiga ba, ta dai kudurce a ranta cewa wannan shine na karshe a gareta.
Ta kwankwasa kofa a karo na uku, sannan aka bude kofar kamshin turaren ta ne ya fara dukar haacinsa, ya ja numfashi, sai kuma ya yi ajiyar zuciya, a lokaci guda kuma sai ya washe baki yana dariya mai sauti.
Ah, ah! Yau muna da manyan baki. Marhabin, shigo ciki. Ya yi umarni a lokacin da ya fita waje yana *yan dube-dube.
Auwal! Ina Auwal din? yake fadl domin bagararwa, a lokacin da ya juyo cikin gida ya isheta.
Ai ni kadai na taho, Auwal baya gari. Ta fada a lokacin da ta jefa kafarta tsakar gidan, tare da sallama, amma babu wanda ya amsa.
'Dazu-dazun nan muka gama hirarku ni da Maryam, har ma mun fidda rai da zuwanku. Ina Anwalu ya tafi? ya tabaya a dai-dai lokacin da ya jagoranceta zuwa dakin shakatawa.
'Auwalu na Jigawa, yau kwanansa daya gobe kuma zai dawo, bai gaya maka bane?
Na san da tafiyar, amma na yi tsammanin ranar asbar din zai dawo.'
'Eh, da haka ya shirya amma daga baya kuma ya canza.
Bari a jima kadan ki dan huta, in bata shigo ba, in tura a kirawo miki ita, yanzu makwabta.' yanzun nan ta shiga
Ya fada a lokacin da ya dire hafadden zobo da aka tanada musamman domin ita.
Ta dauki cup daya ta kurba dadinsa da ni'imar sanyinsa ta ratsata, har sai da ta yi tahmida, saboda ranar da ta shiga, sai kuma gumi ya fara karyo mata, saboda samun nutsuwa ta ruhi.
'Amarsu ta ango, abin fa ya matso, Hauwa Kulu ta Auwału, Allah Ya kusa kawo karshen wahalar masu hakan rijiya, domin sun cimma jar kasa saura idaniyar ruwa. Tunda yau ina ga bai wuce kwana goma ba ya rage a yi bikin.'
Ta yi dariya. Abas da zolaya ka ke, ai alkawarin Allah ne duk wanda ka ji ya yi hakuri bai cimma buri ba, to ba hakurin ya yi ba. Don haka ma'am Bahaushe kan ce mai hakuri ya kan dafa dutse har ya sha romonsa.'
Idan maizon wuta ya jure ba.' Abbas ya karasa, san suka dan yi dariya baki dayansu.
Ina zuwa bari in leka waje, in sanya yaro ya kirawo ta. Ya fada a lokacin da ya yunkura ya yi waje.
***
Bata yi mamaki ba a lokacin da ta dafa kofar gidan ta tura, ta ji ta bude, ta shiga kai tsaye, izuwa falon, a inda ta iske matar a kwance bisa doguwar kujera mai dauke da mutum aku, ta yi tsaye bisa karta tanai mata kallon kurulla, amma har izuwa wannan lokaci bata fuskanci ko wacece ba, kuma matar bata tashi ba, ta sa hannu ta tabata, da niyyar ta farkar da ita daga baccio amma ko motsi ba ta yi ba. Ya yi dai-dai da lokacin da agogon dake manne jikin bangon dakin, ya hau burari, don saner da lokaci.
Ta daga fuskarta izuwa bigiren da agogon yake a makale. Karfe biyar ya harba, ta koma da ganinta ga wannan matar mai bacci, fuskarta babu walwala, sai tarın al' ajabi da mamaki.
Har yanzu zuciyarta bata yanke mata abin da ya dace ta yi ba, tana nan tsaye, sai ta ji alamun shigowar wani cikin gidan daga waje, ta dubi bakin kofar tana jiran isowarsa, kansa tsaye ya kutso kai cikin falon.
Daga idon da ya yi ya ganta a tsaye tana dubansa ido da ido, nan da nan sai ya yi turus! Ya dan dabar-barce, a lokaci guda kuma sai ya yi dariya.
Au....au har kin dawo?" yake tambayarta.
Bata tanka masa ba, har yanzu dai kallonsa kawai take da ido, yanayinta baibaye da alamun zargi
Abbas mutum ne mai karfin iko da nuna isa a cikin gidansa, ya kuma yi dace Allah ya bashi mata mai tsananin hakuri da biyayya.
Da wannan damar ne ya yi amfani, har yake cin karensa ba babbaka, Abbas ba shi da takamaiman lokacin komowa gida da niyyar kwanciya sai sanda ya ga dama, a kullum sai yalinsa ta yi bacci, talatainin dare yake shigowa idan ta yi wani juyun kuma wata ran ma ba a gida yake kwana ba, haka kuma kaso mafi rinjaye daga cikin takardun da yake ajewa a durowarsa, hotunan 'yan matane da letocinsu, ita ma da kanta ta sani cewa, bai damu da ya boye su ba, de kar ta gani, don ko ta gani ma babu abin da za ta iya yi a kai.
Wadannan abubuwa suna matukar kona mata zuciya, yau kuma ga shi abin har cikin gida, ta raya a ranta, a lokaci guda wani abu ya tokari makogoronta, ta ji wani irin bakin ciki mai kunshe da tsana da kiyayya, ta ayyana gaba mai tsananin karfi a ranta, a tsakaninta da mijinta. Yau tsawon shekara guda da watanni da yin aurensu Allah bai basu haihuwa ba. Amma a yau ji take yi ko da da akwai haihuwa a tsakaninta da Abbas, sai ta yi sanadiyyar mutuwar dan domin ba ta ga amfanin hada jini da mutum irinsa ba, don tsananin Çiyayya.
'Maryam wannan ita ce Hauwa'un Auwalu, da nake gaya miki cewa zata kawo miki ziyara, mantawa na yi ma ban gaya miki cewa van zata zo ba, na barki har ki ka tafi unguwa, sai bayan da ta shige ne na tuna, shi ne ta dan zauna jiranki. Ni kuma da na fita da zummar komowa yanzu-yanzu, sai yanzu na dawe baiwar Allah, har ta gaji bacci ya dauketa.'
Har yanzu ba ta yi magana ba, ta dai raka shi da kallo a lokacin da ya tafi izuwa zama yana surutansa.
'Eh, kwarai kuwa surutansa, tun da dai basu gamsheta ba.
Abin mamaki abin al'ajabi, yau Abbas ne ke kokarin kare kansa a gurin matar da bata da kwarjini ko na karfanfana a gurinsa.
Sai a yanzu ne Hauwa'u ta dan motsa da zummar gyara kwanciyarta, ta dan bude idanunta, sai ta tsinka yi mace tsaye bisa kanta a lokacin ne ta tashi zaune fatar idanunta sun yi mata nauyi, jikinta kuma duk ba karfi, kamar wacce aka yi wa duka.
Maryam ta saki fuskarta ta hadiye abin da ke damunta ba don ta gamsu da zancen mij ta ba.
'Hauwa'u don Allah ki yi hakuri, kin yi jira har kin gaji ban dawo da wuri ba, ban zaci zaki zo yau din ba.'
Hauwa'u mamaki take yadda ta saki baki a gidan mutane har ta yi bacci mai nauyi haka.
Babu komai Maryam, nai miki uziri, ai ba zaki yi hakan da ganganba.
Maryam ta saki jiki ta hidimta mata, kamar wani abu bai faru ba, tare da yi mata kyaututtuka na abin arziki har izuwa lokacin da suka yi mata rakiya har gida ita da mijinta Abbas.
LITININ
mahadar da ta nufi izuwa Wudil abin ya faru, a A lokacin da ya tako motar da gudu, sai wani yaro mai tallan rogo ya tsallako titin a guje shima a garin ya dauke kan motar, don kiyaye lafiyar yaron, sai motar ta doki tubalin dake tsakanin titi mai tafiya da mai komowa, motar ta hantsila, ta dan dauki lokaci tana tafiya a kife cikin wani irin kugi, sannan ta tsaya.
Can kuma sai motar ta fara hayaki tana shirin kamawa da wuta misalin karfe daya na rana abin ya faru, don haka aka sami karancin jama'a a gefen hanyar, saboda kwallewar rana, a warman lokaci.
Amma abin mamaki kafin zuwa wani lokaci tuni har an yiwa metar kawanya, tamkar kuda da sabon kashi.
Mutum daya ne a cikin motar, cikin hanzari aka fito da shi jini na zuba ta hanc da baki, a tare da shi babu wata alama da ta nuna yana da rai a wannan lokaci, face jinin da ke zuba a jikinsa da irin yadda ya saki jikinsa da ke kokarin bayyanawa jama'a cewa gawace a zahiri.
Wadansu kuka suke don tausayi da firgita, a yayin da wasu kuma ke yi ma gawar kallo daya su dauke kansu, saboda abin ba kyan gani, kadan daga cikinsu ne masu kekasashshiyar zuciyar da suka jurewa dawainiya da gawar, a kokarinsu na bada agaji.
'Yan kudin da aka samu a jikinsa babu yawa, tare da irin karamin kur'ani nan na aljihu, wanda aka samu wata 'yar sanarwa a bangon littafin daga ciki kamar haka:-
Auwalu Adam. Ni musulmi ne mai bin mazhabin sunnar Annabi (SAWW) A duk inda aka tsinci gawata a dankani hannun 'yan uwana musulmi ahlussuna, su sallace ni.
A tsakiyar littafin kuma, takardace, mai nuna alamun irin aikinsa da kuma direshin inda yake aiki, a gaggauce aka mika shi asibiti mafi kusa, don samun taimakon gaggawa, kafin a sami 'yan uwansa.
Mu hadu a littafi na biyu don jin cigaban labarin
Aminudden Ladan Abubakar
Sarkin Ɗiyan Gobir
Ɗan Amanar Kano
Ɗaukar Nauyi
Mansur Usman Sufi
08137237071