Showing 1 words to 3000 words out of 4609 words

Chapter 1 - BAKAR ANIYA Book 1 By Aminudden Ladan Abubakar Alan waka.docx

BAƘAR ANIYA

Book 1 Part A

Writing by

Alan Waka Aminudden Ladan Abubakar

Ɗaukar Nauyi

arewanovels.com.ng

Haƙƙin Mallaka

Mansur Usman Sufi

08137237071

1988

JUMA'A BAYAN LA'ASAR

Hauwa'u Allah Ya bani ubangida mai karamci, adali kuma masanin ya kamata, wanda hakanne -ya bani damar hawa kowacce irin mota da ke gidansa, har mutane ke yi mini ganin mawadaci. Ba kuma shi da bakin ciki, ko kadan akan yaransa, a kullum burinsa ya gaun wadatu, kuma mun ci gaba, abun ki a gurishi ne ya gammu a cikin kaskantattun tufafi, sai ka ga yana ta yi mana fada sabanin wadansu mawadatan da idan suka hangi kana canzawa, sai su ga kamar zagon kasa ka ke musu, ko kuma girman kai ya ayyana rausu kana hada kanka da su ne, don haka dolenka ka zauna cikin datti, domin a shaida yaron gida ka ke, ko a koreka.

Duk da haka ina yi maka shawara Auwal, da kar ka kuskura ka sakankanee da zama karkashin wani, ko babu sabani akwai mutuwa, haka zalika kuma akwai juyin juya hali, ka yi kokari ka mallakar mana muhalli da sana'a saboda gaba.

Don yanzu ka ga 'yan kwanakin da suka rage a daura mana aure sun kusanto, daga an daura auren kuwa nauyi ya karu a kanka, tunda ka ga a da baka biyan haya, idan ka aureni

kuwa zaka biya, haka kuma da larurar iyayenka kadai ke kanka, sabanin an ka yi aure, kuma ai ba ci kadai aka sa a gaba ba, akwai suttura, akwai rashin lafiya, sa'annan daga zarar ka ji an ce an yi aur zuwa wani lokaci ka ji an ce an haihu, nauyi kara yawa yake, da bukatu, ba tare da kuma abin da ka ke samu yana habbaka ba, tun da albashi ka ke dauka. Idan kuma ka sakankance, sai dai wata ran ka ga mun wayi gari da 'ya'ya bakwai a gidan haya."

Ta dube shi a yayin da ya yi kasake! yana sauraronta, irin juyowar da ya yi da gaggawa da kuma yadda ya yi da fuskarsa a lokacin da ta furta kalmarta ta karshe, shi ya sanyata tuntsura dariya.

Allah Ya kiyaye.' Ya ce.

A to ka kiyaye Allah Ya kiyayema, ni dai na baka shawara tuntuni, da tsarabe-tsaraben da ka ke shirin yi na al'ada, da basu zama dole ba a addiri, ai gara ka kafe akan sadaki kawai zaka biya, in ya so sai ka hada da kudin da ka ke tanadin buga kalanda, da fati, ko dan fili ka saya daga baya idan kura ta laf ai ka rinka gina abinka a hankali.

Amma mutukar ka daka ta rawar jama'a, sai ka rasa turmin daka taka, kana gudun kada a yi maka surutu, to, duk irin abin da ka yi, sai an kusheka, taron jama'a da ka ke gani kushe da yabo, duk na dan lokaci kankani ne, jama'a su watse su barka da abin da ka ke ciki. Ba zaka taba gane kuskurenka ba sai lokacin da ka shiga muwayacin hali, a lokacin ne zaka nemi ranar taron jama'a ka rasa wadanda ke zigaka a lokacin da ka ke burga da bushasha, sune farkon masu zundenka.

Auwal kana ina mutum da iyalinsa da karfinsa, kuma za ka gan shi yana bara, yana kukan ba shi da abin da zai kai wa iyalinsa a cikin wannan hali da muke ciki na rashin aiki. To, kana tsammanin shi wannan mutumin bai taba taron jama'a ya yi musu alkhairi ba, wacce rana suka yi

masa da ya shigo halin ha ula't. Me ya hana aytgan ba shi jari ko aiki? Ka yi ta kanka Auwalu, abin da duk aka yi shi ba don Allah ba, riya sunansa, babu lada ga hasara da rashin albarka.

Ya dan yi zugum maganar ta ratsa shi.

Wannan luk gaskiyane ki ke fadi, amma yanzu ke duk za ki iya daukar a ce ban yi kaza da kaza ba, ban yi miki lefeba, ba kya jin tsoron surutun jama'a?"

Eh, na ji na gani matukar dai za a toshe waccan Ganrakar da na hango. Don ni mai burin haihuwa ce da yawa, ko domin in kasance daga cikin wadanda suka bada gudunmawar habakar al'ummar ta annabi don ya yi alfahar da mu, ranar alkiyama, kuma bana fata a ce ana tsangwamar "ya'yana saboda gidan haya, ko ana gudun bamu haya saboda yawansu, ko suna matakin ilimi mu dora musu nauyinmu, su kasa karatu su hau neman kudi.

Na yarda duk irin kunci da rashin da zamu yi a yanzu mu yi shi, in ya so 'ya'yanmu su tashi cikin kulawa da rayuwa gari.

Hauwa'u na ji kuma na dauka, amma duk da haka, wannan ba zai hana ni in yi miki lefe ba, don ka yiwa matarka sutturama yana cikin ka' idodin aure. Amma game da tara 'ya'ya Hauwa'u a halin da ake ciki ban goyi bayan ki ba, masu tsarin haihuwa ma bisa hangena gami da hujjojin da na dogara da su, na ganin ba su da laifi."

Auwal baka son haihuwa?" ta fada a lokacin da ta rike baki, fuskarta ta canza.

Ba haka nake nuti ba Hauwa'u, ina nutin a halin da mu al'ummar kasar Nijeria muka tsinci kanmu a ciki, bana bukatar yawan 'ya'ya mutukar ba ina da arzikin rikesu ba, 'ya'ya biyu rak! Sun isheni zuwa gaba idan Allah Ya buda kuma, sai a nemi wasu, kamar dai yadda a aurema, nake da burin mata daya."

tasne har yanzu cike take da mamakinsa.

Bisa waece hujja Auwalu? Ka manta Allah ne ke arzutuwa, shi kuma ke ciyarwa, shi ke kashewa da rayawa? Kuma ga hadisin da na kawo maka a baya na alfahari da yawanmu da annabi ya ce zai yi ranar Kiyama, don haka ya umarcemu da mu yi aure mu hayayyafa.

Wannan hadisi (saha) ya inganta, ba ina kokarin tunkude shi bane, a'a, wajibine ya kau da sunna bisa larura. Hakika kam Allah shike arzutawa Ya kuma arzuta, Allah shi ke ciyarwa ya ciyar.

Abin nufina a nan Allah ta'ala Ya albarkaci kasarmu Najeriya da ni'imomi daban-daban har ma basu kirguwa a gareni, mafi yawa daga kasashen duniya, suna bugun gabane, da ma'adanai na karkashin kasa, misalin man fetur, a yau an wayi gari a Nijeriya, son jiki da son zuciya da rashin kishin kasa, mun ta'allaka akan man fetur, shi ne kashin bayan arzikinmu, abin dogaronmu saboda rauni da rashin hangen abin da ga za ta haifar.

Yau a duniya mun makara mun zama koma baya, a harkar kere-kere, (technology). Bayan kuma Allah Ya albarkacemu da komai na mu tafi kafada-da-kafada, da sauran kasashen duniya. Kasashen da suka zama (super Powers) kashin bayan arzikinsu a yau. (Technology). Da akwai kasar da ba su da isashiyar rana, Nijeriya muna da ikon kere-kere, ta (sun light) akwai kasar da bata noma, akwai kasar da ba su da ruwa, akwai kasar da basu da ma adanai na karkashin kasa, ke hatta fatar dabbobin Nijeriya ta fi ta sauran kasashen duniya nagarta, babu abin da Allah Ya ragemu da shi, face mu muka tauye kanmu, muka tare a bangare daya a bangaren dayanma shumagabanninmu kansu suka sani da 'ya'yansu. Allah Ya bamu arziki Ya bamu abinci, face dai wasu 'yan tsirarun

mutane ne suka katantange, suka hana shi isowa ga al' umma a dalilin aka muka afka cikin halin musiba da bala'i. Yau a duniya wadanda suka yi fice a gurin (419) yan Nijeriya suka fi kowa iya sata da fashi 'yan Nijeriya. Wadanda suka fi kowa fantsama cikin kasashen duniya ta barauniyar hanya, yan Nijeriya a yankin Africa, yau ko laifi aka kama wani da shi sai ya ce shi dan Najeriya ne.

Waiwayo cikin unguwarku ki dubi duk wadanda ke yin duk wani wulakantaccen aiki, za ki ga dan kasa ne. da idan aka ga mutum na ga ruwa, sai a ce dan Niger ne, amma yanzu la, mune ga ruwa, mu ne yankan kumba mune kwasar kashi.

A ean sama kuma sai a sami mutum daya rak wanda wani yanki daga cikin abin da ya tara ya isa a rabawa, kowanne mutum a Nijeriya, miliyan uku, irinsu kuma ba sa kirguwa.

Hauwa'u gaya min abin da zai hani sata, a gaya min abin da zai sanya kauna da zumunci a cikin al'umma ana cikin wannan ali, Hauwa'u duk wanda ya tsammaci halir da muke ciki talauci ne ya yi kuskure, mu muna cikin bala'ine da tashin hankali, wanda shi ya sanya ni gudun yawan 'ya'ya, don kada su zama fitina a gareni. Kamar yadda Allah ta'ala ke cewa ('ya'yanku da dukiyoyin fitina ne).

Can kuma cikin suratul Tahrim, yana cewa 'Ku kare kawunanku da iyalanku daga wuta.... wacce hanya za a bi? Tarbiyantar da su, umartarda su, su san yadda za su bautawa Allah, su kuma kaunaci manzo da ahlin gidansa, ga kuma hadisin annabi da yake cewa.

Ku ladabtar da 'ya'yanku akan abu uku, Kaunar annabinku da kaunar Ahlulbaiti da karatun alkur'ani tarbiyyar yara a musulunci wajibi ne, haka ilmantar da su ba za kuma ka yi uzuri da cewar varan sun yi maka yawa ba, ko kuma harkar neman naka da yanayin aikin ne ya tsawaita ba, addini a kullum baya tsauwalawa sai ka yi gwargwadon abin da zaka iya, ilan ka ga zaka iva kiyaye kanka ka tsaru ga barin zina, aurennma kana iva hakurcewa kanka, amma yin auren shi ya fi. Kuma kin san rayuwarmu a yau kacokan

sai da kudi ake komai. Wannan ita ce hujjata lauwa'u da fatan kin fahimce ni.

Ta gyada kai a lokacin da ta sauke numfashi mai karfi. Allah ya kyauta, Allah Ya shiryi shuma gabanninmu, ya cusa tausayinmu a cikin zukatansu.

Hauwa'u ta yi addu'a.'

Amin. In ji Auwalu

H auwa'u yarinya ce wacce a yayin da za a dungma izuwa bikin zaben gimbiya a fagen kyau, Hauwa'u -na bayan fage.

Haka zalika kuma a san da aka yi ayarin zuwa zaben mummuna, tun daga shirye-shirye, kafin akai ga zaben gudun ya da kanin wani, za a yi babu ita. A bangaren kyawun fuska, Hauwa'u kadaran-kadahan, baka iya kiran Hauwa'u kyakkyawa kai tsaye, haka kuma bata cikin munana.

Hakan bai rageta komai ba, domin kuwa Allah Ya yi mata wata baiwa wacce bai yiwa wata 'ya mace makamanciyarta ba, a yankinsu, ta wadatu da kisan jan hankali irin ta mata, dangane da cikar halitta na kyawun kira (diri), a nan sai in ce ka yi bincike cikin shu'ara a nan zaka ji fa idoji da ni'imomin da mata masu irin kirarsu ke dauke da ita. Hadarin da ke dauke da kadaicewar Hauwa'u da da namiji kuwa yan da yawa, mutukar ana da yakinin cikakkiyar lafiya a tare da shi, ba duka bane sukan iya hadiye mai tarsu, su ketare, siradi ba tare da sun nuna maitarsu a fili ba, sai dai wanda Allah Ya tsare, wato kamilai. Domin kuwa ko gilmawarta ka hanga, idan ka ga kallon da samari suke yi mata, zai iya tuna maka irin kallon da karan gidanku yake yiwa mai tallan nama, idan ya zo

shigewa. Yaushe za ki je gidan Abbas? Ya dameni da mita akan kin ki ki ziyarci matarsa. Auwal ya fada a lokacin da suka taho ta rako shi zai tafi.

Insha'Allahu gobe ko jibi na je."

Kin ga ki tsaida rana daya. Ya fada yana kallonta.

To, Allah Ya kaimu ranar lahadi da hantsi na je mu gaisa, tunda ma'aikacine na san ma yana gida. Ta fadi.

'Kin ga kuwa da in "an ranar da mun tafi tare,

'Ina zaka?"

Zan tafi Jigawa amma ranar litinin zan dawo.

Allah Ya komo da kai lafiya."

Ameen. Ya amsa.

Cikin kankanin lokaci, suna shirin rabuwa, yanayin garin ya hautsine, wani irin kakkarfan hadari ya faso, sannu a hankali, ya mamayi ko ina, asararin samaniya, zuwa can kuma sai yanayin garin ya sauya, ta dalilin rikidewar hadarin da ya sauya launi izuwa ja, alama ta yana dauke da iska.

'Auwal ka dakata iskar nan ta lafa ko a dauke ruwa sai ka tafi. Ta ce da shi.

'Hauwa'u tana iya yiwuwa kafin a fara ruwan ma na isa gida, don ba lallai bane ya tabani, tunda a mota nake.'

Rufe bakinsa ke da wuya iskar ta, fara kadawa, a hankali zuwa da karfe, abu kamar wasa sai dada girmama yake, dan lokaci kankani sai aka daina ganin rana, a duk lokacin da ka yi namijin koka: ka bude idonka, sai ka ga garin ya rikide ya koma ja: karkakkarfar iskar ta ci gaba da kadawa, a inda har ta fara 6a66ago rufin kwanukan masu Karamin karfi, tana karya dashen bishiyoyin da ba su yi kwari ba.

Nan da nan suka koma inda suka fito, hankalinsu a tashe da ganin bakon al'amari suna masu 'yan karanto dan abin da ya sauwka a bakunansu na daga addu'a. a hankali sai yanayi ya koma dare, har yanzu kuma iskar ake ba a daina ba. Hankalin kowa a tashe, don ganin gari babu lafiya, sai kuma salati iri-iri da ambaton Allah ta siga daban-daban. Abu kamar wasa har sat da ta kai ga ko sanya tafin hannunka ka yi a fuskarka ka kalla da ido, hango tafin hannun sai ya ci tura, baka iya ganin dan uwanka, kai hatia rigar jikinta sai in ka laluba ka jita

Sai kuka da sallalami, kowa idan ya tuna cewa ana cikin ranar juma'a ne, sai ya yanke kauna da rayuwa, a saninsa na rewar ranar juma a ne dama za a tashi alkiyama, tun suna salatin a zuci har ya bayyana a fili, zuwa da karfafa sauti.

Auwalu!! cikin murya irin ta mai kuka.

'Hauwa'u.' shima ya kirata cikin rudani, suna masu laluben juna, ta rike shi kankam, cikin tsoro da firgita mai tsanani shima saboda tsoron mutuwa da ita yake garkuwa, jikinsa na bari daga inda suke suna jiyo satin koke-koke daga cikin gida wadansau kuma na ta salati.

Ka gafarceni Auwalu, Allah bai nufi zamu yi aure a duniya ba!!

Ki daina fadin haka. Hauwa'u wannan kudira ce ta Allah shi kadai ya san abin da yake nufi da faruwar haka, amma tashin alkiyama da sauran alamomin da basu bayyana ba. Kuma ko ba mu yi aure a duniya ba, da izinin Ubangiji ke ce matata a aljanna. Suna Kaunar junansu kamar su hadiye junansu dor soyayya, amma dai-dai da second ko minti basu taba haura iyaka ba, a fagen soyayya, hannnunsa bai taba sabanin ya gogi nata ba ko da wasa, saboda kawaici da tsantseni gami da tsoron Allah kowannensu, amma a yau saboda tsoron har ta kai su ga kankame juna don gudun mutuwa.

***

Wato duk irin masha'ar da kan aikata a ban kasa, Allah shi Ya so ya kyalemu da halinmu, idan ya so sai ya kamamu daga bava, da sakamakon abin da muka kasance muna akatawa da hujja.

Duk inda ka b samari ka ke hange tsibi-tsibi kowannen ciki ya duri ruwa, sun kadu da abin da ya alku jiva. Zaka gane hakan ne ta hanvar ganın wafansunsu, rirrike da carbi suna ja, wasu har da huluna, kai da langen wani ka san hular kawai dorata akai, amma ba mahallinta ba ne, wani ma ba zai iya tuna rabonsa da salla ba, amma a yau ga shi kwakume da tasbaha, yana murguda baki da sunan tasbihi.

Da alamar tunani yake, ya dan bada baya, hannayensa a rungume bisa kirjinsa. "Gudun mutuwa mai sa akwana gidan saurukai."

A lokacin ne ya kawo hankalinsa gareta, tana 'yar dariya.

Au ke har kina da bakin magana? Ke mai neman gafara.

Ta kara dariya har hakoranta suka bayyana.

Auwal dole abin ya di..autani, ban taba gani ba, ban kuma taba jin labarın faruwar makamancin haka ba a rayuwata.

Ni kuma dana dubi hadarin nan da kuma lokacin da na ji idona a bude amma bana gani, sai tsoro ya kamani, wata aya ta fado mini a cıkin Alkur'ani, sai nake ganin tamkar azaba Allah zai mana domin da yawa daga wadanda aka hallakar magabatanmu, da makamancin liaka abin ya fara.

Hauwa'u mu ji tsoron Allah a duk inda muke, a kuma kowannen irin hali muka kasanee, mu zuba jari, mu yi tanadin alkhairi tun gabanin haduwarmu da Allah. Ya girgiza kansa alamar kaduwa.

Allah Ka sa mu cika da imani. Shine abın da ta ce.

"To, Hauwa ni zan tafi Jigawar a yanzu amma sai ranar litinin zan komo, wanda yake idan na komo sai kawai mu fara rabon LV

Kai da ka ce kwana daya zaka yi Auwal, me zai sa ka yı kwana biyu, bayan kuma ka san halin damuwar da nake shiga, idan ban sanya ka a dona ba.

Kin fini bayyanata a zahiri, na fiki a zuci, amma in kin dauke wannan ma ai ina ga shirye-shiryen mallakar junanmu ne zai kai ni, haka kuma goben da jibin duk daya ne a gurin Allah. Duk inda na je ai ina tare da ke a cikin zuciyata Hauwa'u ba zan taba mantawa da ke ba, dai-dai da tsawon dakika daya, matukar ina numfashi a doron kasa, mutuwa ka raba.'

Ta dan yi murmushi da a kullum yake gamsar wa da zuciyarsa nagartar alkawarin da ke tsakaninsu na aure.

Auwalu ko mutuwa ba za ta rabamu ba, domin kuwa ko mun mutu muna saka rai da tashi a matsayin 'yan aljanna, ma auratan juna na hakika."

Allah ya cika maha burinmu, duniya da lahira."

'Ameen. Ta amsa da lallausan harshenta, ciki nuna muradin hakan, sai kuma ta yi kasake tana kallonsa, kallon da ita da kanta ta kasa gane dalilin yinsa, har ta ba shi tausayi. Bai sami ikon ce mata komai ba, sai ya shige mota, don gudun kada ta karyar masa da gwiwa, ko kuma ta bata masa lokaci.

Sai na dawo. Ya ce a lokacin da ya daga, ta bishi galala da kallo, ba tare da ta amsa ba, can kuma sai ta daga masa hannu tanai masa adabo. In ji 'yan yara.

LAHADI

S anye take da yadi tsadajje, irin na yayi, mai daukar hankali. Huda-hudar da ke a jikin yadin, shi

1
2

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login