Showing 3001 words to 5533 words out of 5533 words

Chapter 2 - KUNDIN TSATSUBA Book 3 By Abdulaziz Madakin Gini .pdf

la'anannen aljanin. Na antse da girman tsafi, sai na kulle ku
a cikin akwatunan tsati, sannan a kai ku kurkukun karkashin kasa, anan za ku yi la zama har
izuwa karshen rayuwarku.

Ko de baka sai Markahul Sabus ya bushe da dariya ya ce "Karya kake, ba ka isa ka yi mana
wannan wulakancin ba, muddin ina numfashi a doron kasa."

Ko da jin haka, sai sarki Lu'umanu ya dubi dakarunsa ya ce "Ku kama su! Ku aiwatar da
hukuncin da na yanke akan su!!"

Take dakaru suka afkawa su Markahul Sabus, nan fa wuri ya yamutse, aka fara dauki ba dadi.
Bisa mamaki, sai Markahul Sabus ya ga wadannan dakaru sun addabe shi, duk da cewar shi
aljani ne, su kuwa mutane ne. Abin da bai saníba shi ne, ba mutane ba ne aljanu ne
'yan'uwansa, kuma suna daga cikin jinsin bakaken aljanu wadanda abu marassa imani kamarsu
a doron kasa. Ko da ya ga al'amarin ya fi Karfin saninsa, soi ya fara jarraba karfin tsafi. Nan
take dakarun suka juye kamanninsu izuwa ainihin suffofinsu na bakaken aljanu, kawai sai suka
rufe shi da duka, cikin dakiku kadan suka yi masa luguden wahala ya fadi kasa sumamme. Ita
kuwa Fatisa suka kamata da karfin tsiya, suka tafi da su izuwa karkashin kasa inda aka gina
wata kurkuku na musamman. A nan ne aka sanya Merkahul Sabus a cikin wata battar karfe, ita
kuma battar aka jefa ta cikin wata bakar akwatu aka kulle, sannan aka sa katon kwado aka
datse.

Kamar yadda aka yi wa Markahul Sabus, haka aka yiwa Fatisa. Da yake ita bil'adama ce,
kwananta uku a cikin akwatin ta mutu, shi kuwa Markahul Sabus har yau har kwanan gobe yana
nan a raye cikin wannan akwatu, kullum ba shi da aikin yi sai kuka da rera wakokin begen
masoyiyarsa Fatisa. In da mutum zai shiga wannan wuri ya je kusa da akwatin, zai ji sautin
wakar, kuma zai ga hawayen Markahul Sabus na kwaranya daga cikin siririyar kafar akwatin.
Wannan shi ne dalilin da yasa aka kulle aljani Markahul Sabus a cikin akwatin karfe."

Sa'adda aljani Lubumaz ya zo nan a labarinsa, sai afar da Yelisa su kai ajiyar numfashi, sannan
suka dubi una, aka rasa wanda zai ce kala. Daga can sai Jafar ya ce "Yanzu kenan dole sai
mun je jejin Kalkim mun dauko takobin Sarjis mallakar maridi Magulus, sannan zamu iya zuwa
kurkukun sarki Lu'umanu mu kubutar da aljani Markahul Sabus?"
Lubulmaz ya ce "Haka wannan zance ya kc, dole sai kun tuntußi boka Jinshan mahaifin Yelisa,
sannan za ku keta ejin Kalkim ku fita lafiya."

Wannan batu ya sa hankalin Jafar da na Yelisa ya hi, suka nutsu a cikin tunani. Daga karshe sai
suka yanke Shawarar kawai su je su tuntubi mahaifin nata, in ya so komai ta fanjama-fanjam.
Nan take Yelisa ta dauki Kundin Tsatsuba ta yi waje. Jafar da aljani Gulzum suka bì ta a baya.
Ko da suka zo bakin kofar kogon, sai yanar nan ta nannade kanta sama kamar labule suka fice,
sannan ta dawo ta rufe. Ba tare da bata lokaci ba, Yelisa da Jafar suka haye bayan Gulzum, ya
tashi da su sama suka nufi gidan boka Jinshan.

A can birnin Laharım kuwa, magariba nayi waziri Kuddaru ya koma wajen gimbiya Sima ya
sanar da ita cewa shi kam ya gama shii kuma yayi sallama da iyalansa, don haka a shirye yake
su tati iziwa jejin Falwas don su sadu da Boka Sultaini. Da ma tuni Gimbiya Sima tasa an shirya
musu guzuri da 'yan rakiya wasu dakaru guda dari hudu da sittin. A cikin wadannan yan rakiya,
har da galadima, wani dattijon mutum da ake kira Abu Lajis. Ba don komai Gimbiya Sima ta
shirya wannan tafiya tare da Abu Lajis ba, sai don ya zama wakilin jama'ar gari, kuma idan ta
kama ta bar masa rikon garin ta ba shi. Ba tare da bata wani lokaci ba, Gimbiya Sima, Kuddaru,

Abu Lajis da sauran yan rakiya suka yi hawa suka fice daga cikin gari, suka dau hanyar jejin
Falwas.

Kwanci tashi su Gimbiya Sima suka isa jejin Falwas, ba su tsaya ko'ina ba, sai a bakin kogon
Ruhim. Da yake Kaddaru ne akan gaba, sai ya ja linzamin dokinsa ya tsaya cak a gaban
wannan kogo, sannan ya sauko daga kan dokinsa. Su kuwa su Gimbiya Sima ba su sauko
daga kan dawakansu ba, sai suka tsaya suna kallon abin da Waziri Kudduru zai yi. Yayin da
Kudddru ya zo daf da kofar shiga kogon Ruhim, saí ya tsaya ya ce "Ya sarkin bokayen duniya.
ya kai fitila mai haskaka duhun dare, ya magani mai warkar da kowace cuta, ka yi sani cewa
yau ga sarauniyarka Gimbiya Sima ta tako da kafarta ta zo gareka da wata babbar bukata. Ka yi
hakuri ya shugaban maisafa mun katse maka aiki ba don sun zuciya ba, sai don bin umarnin
sarauniya. Ga ta nan a tsaye tana sauraronka."

Kaddaru na gama fadın haka, sai suka ji wata murya ta ce "Lale marhaban da sarauniya, lallai
mu masu bauta ne ga ahalin gidanku tun fil azal. Bukatarku ta mu ce. Ga mu nan zuwa gareku
don mu share muku hawaye."

Ko da muryar ta zo nàn a zancenta, sai gaba dayan kogon na Ruhim ya tsage daga tsakiya ya
bude kansa kamar an bude tsakiyar littafi. Ta ke wani dogon mutum ya bayyana yana sanye da
warkin fata, a hannunsa na hagu akwai wata siririyar sandar tsafi, a hannunsa na hagu kuwa
isga ce. Babu takalmi a kafarsa, damatsansa kuwa a cike suke da gurayen tsafi. Kansa fari fat
ne, ko ina furfura ce ta luliube babu silin bakin gashi guda. Akalla shekarunsa sun haura casa
in, jikinsa a murde yake, wato yana da Kirar Karfi, kai da ganinsa ka san cewa da ca an yi
jarumta.

Mutumin ya tako a hankali har ya iso gaban Gimbiya Sima, sannan yai sujjada a gareta ya ce
"Gaishe ki sarauntyar duniya. Ke ce tauraruwar taurari. Ni ne bawanki Boka Sulbaini. Muna
sane da bukatarki, sauko ki biyo mu cikin kogo, lalłai akwai bayani mai tsauri da ke bukatar
sauraro cikin nutsuwa.
Ba tare da wata fargaba ba, Gimbiya Sima ta sauko daga kan dokinta ta biyo Boka Sulbaini a
baya. Kaddaru da galadima ma suka bi bayansu, sai Boka Sulbaini ya juyo ya dubi galadima ya
ce "Koma da baya, ba ma bukatarka."

Cikin alamun kunya galadima ya koma da baya. Yayın da Boka Sulbaini da su Sima suka shige
ciki, sai kogon ya koma ya rufe kamar an rufe littafi, kai ka ce tun fil azal dutsen bai taba
budewa ba, kuma babu wata halitta da ta taba shigarsa.
Sa'adda suka isa tsakiyar kogon Ruhim, sai Girabiya Sima da Kaddaru suka ga kamar sun
shigo wata sabuwar duniya, domin hatta irin iskar da suke shaka a wajen mai dan karan dadi
ce. Yanayin wajen kuwa madaidaici ne, malana babu zafi kuma babu sanyi. Komai da ke wajen
dabam yake da irin abubuwan da ido ya saba gani. Ko ina ka duba abubuwan al' ajabi ne birjik
a zuzzube. Halittu kuwa ga su nan iri-iri. A wajen ne suka ga mace mai nono hudu, sannan suka
ga jaki mai kawuna uku. A can gefe guda kuma sai suka ga wani kyakkyawan saurayi wanda
rabin jikinsa na dokin ne, daga cibiyarsa zuwa sama ya ke bil adama, amma gangar jikinsa da

kafafuwansa duk na doki ne, an daure shi a jikin turke sai harbin iska yake. A can gefe guda
kuwa, wadansu kyawawan 'yan mata ne guda hufu, rabin tsagin jikinsu na bil adama ne, rabi
kuma na dodanni. Haka kuma a can bisa wani dutse sai suka ga wani jibgegen hankaka mai
kan bil'adama, har yana da dogon gemu mai shafar kasa, kuma yana rera wata waka cikin
murya mai zakin gaske da dadin sauraro, kamar haka:

Duniya da yawa take

Haka ma abin cikin ta yake

Komai sammakonka wani a tafe ya ana

Ina gwanin wani ga nawa?

Sulbaini kai ne gwarzo dodon gwarzaye

Ya masanin sirrin boye.

Kai ne mai duniya.

Kai ne kasan dukkanin tsatson da ke cikinta Kai ka san abin da aka harfa yau, Kuma kai ne ka
san wanda za a haifa gobe.

20

Ina mai neman labari?

Ya zo ga littafin da shafukansa ba su kirguwa.

Subaini kai ne haske mai kewaye duniya kaf a dakika guda.

Ya masanin adadin halittun duniya.

Kai ne farin wata mai sanyaya koramai.

Kai ne rana mai yada zufa.

Haka dai wannan tsuntsu mai kan biladama ya ci gaba da yiwa Boka Sulbaini kirari a cikin
wake, bai gushe ba yana yi har ya kai su Gimbiya Sima bisa katuwar karagarsa ta mulki suka
zauna gaba daya. Zamansu ke da wuya kayan marmari suka bayyana a gabansu, bisa wani
farabtin zinare, saman kuma sai ga tulunan ababan sha iri-iri, tare da kofuna na zinare. Duk
abin da mutum ke so da ya kai hannu, sai abin ya taso da kansa ya dira a hannunsa. Haka dai
Gimbiya Sima da Waziri Kaddaru suka ci, suka sha, suka yi hani'an

Bayan sun nutsu Boka Sulbaini ya dube su ya ce "Ya ku wadannan manyan baki, ku sani cewa
yau kwana ashirin kenan da fara halwata ta tsafi, wadda ba ni da nufin tsayawa sai na cika
kwanaki arba'in. Inda kun hakura da zuwa gare ni sai bayan na kammala halwar, da kuna zuwa
zan baku abin da kuka fito nema, to amma yanzu kun tarwatsa komai, ba zan iya mallakar abin
da nake so na mallaka ba, sai na sake shiga wata sabuwar halwar ta shekara hudu a maimakon
kwana arba in da ya kamata nayi a da. In kuka sake zuwar mini kafin cikar shekara hudun,
komai ya dagule, sai na sake shiga ta shekara dari hudu. Na sani cewa kun zo gare ni ba don
komai ba sai don ku san inda zaku

riski Kundin Tsatsuba, domin Gimbiya ta karanta shi ta sadu da abokin rayuwar da ya dace da
ita, ko ba haka ba ne?"

Kaddaru ya risina ya ce "Haka yake ya shugaban bokayen duniya."

"Hakika kun zo da babban al'amari, amma shi ne nafi sauki idan har za ku kiyaye da abin da
zan shaida nuku. A halin yanzu shi wannan littafi wato Kundin satsuba yana hannun wadansu
hatsabiban yara guda biyu a an birnin Sin, ana kiransu Jafar da Yelisa. Sun kasance nace da
namiji. Kundin Tsatsuba ba zai karantu ba, domin abu mai iya bude shi face da wata kuba da
ake kira Muftahul Zarbil. Ita kuwa wannan kuba, an raba ta gida uku, aso guda an kai shi
bangon karshen duniya da ke gabas, aya ka son an kai shi bangon kudu, dayan kuma an kai
shi angon arewa. Daga ko'ina cikin duniya zuwa wadannan urare tafiya ce ta shekara
hamsin-hamsin ga sadaukin aljani tai tashen balaga. Amma ku yi sani cewa, akwai wani aljani
ada daya wanda zai iya yin wannan tafiya a cikin kwana amsin-hamsin, ana kiransa Markahul
Sabus. Inda a kai shin dace, shi wannan aljani yanzu haka yana can a tsare kin kurkukun sarki
Lu'umanu na birnin Teheren da ke arkashin Kasa. Ku yi sani cewa, an saka Markahul Sabus a
kin bakin akwati an kulle da katon kwado, wanda ba shi uduwa sai dai a sare shi da wata takobi
ta musamman. Ita awa wannan takobi ana kiranta Sarjis, mallakin wani asurgumin maridi ne da
ake kira Magulus a cikin jejin alkim, jejin da babu wata halitta da ta isa ta shige shi ta fita raye,
ba tare da ta kiyaye wadansu tsauraran dokoki ba masu wuyar sha'ani."

Sa'adda Boka Sulbaini ya zo nan a zancensa, zucivar Gimbiya Sima da ta Kaddaru ta karaya,
suka fitar rai da samun bivan bukata. Yayin da Boka Sulbaim fuskanci hakan, sai ya dube su ya
kyalkyalle da dariva ya "Haba 'va van zamani, kar ku ba ni kunya mana, ba kui ce yaro bata
hankalin dare ka yi suna ba. Ai mai tsoro ba zama gwani. Inda ni matsoraci ne da ban san abin
da na s ba yau. Lallai ku karfafa zukatanku, ni kuwa na tajinake ku kai ga samun nasara."

Yayin da suka ji haka, sai Gimbiya Sima ta ce kai sarkin bokaye, hakika wannan kałami naka ya
kara m kwarin guiwa, don haka na rantse da darajar kara gidanmu, daga yau na sallama
rayuwata don samun biy bukata ta. Fada mana abin yi mu kuwa mu kasance ma bibiyarsa sau
da kafa."
Boka Sulbaini ya tuntsire da dariya a karo na biyu ce "Haka na ke so na ga mace mai zuciyar
maza. Na uma ku da ku yi dubi izuwa ga wancan allon tsafi."

Sulbaini ya nuna wani farin kyalle da sandarsa tsafi, sai ga Jafar da Yelisa bisa aljani Gulzum
sun din kofar gidan Boka Jinshan. Dirar su ke da wuya masu tsa kofa suka ba su hanya. Yelisa
ta kama hannun Jafar s shige cikin gidan suka bar aljani Gulzum zaune yana jiran Bayan 'yar
doguwar tafiya ta kimanin dakika dari biyar ga su sun iso cikin wata katuwar fada mai tarin
kayana na alfarma. A can saman wani gini mai tudu aka ajiye karagar mulki wadda aka kera da
yakutu. Bisa kan kan Boka Jinshan ne sanye da bakaken kaya, bakin rawan bakin takalmi
fyade, wanda aka yi shi da fatar damis
yan yatsunsa na hannun hagu da dama akwai zubuna guda shida-shida, wato adadinsu goma
sha biyu kenan. Bisa wata farar shimfida da ke gabansa, wani murgujejen zaki ne rayayye, sai
gurnani yake kamar ya ci babu. Ko da Jafar ya ga wannan zaki, sai jikinsa ya hau bari, ya
rukunkume Yelisa saboda tsananin tsorata.
Yelisa ta daka masa tsawa ta ce "Amma ka ba ni kunya. Yanzu duk irin rashin tsoron nan naka
da na sani, a ce zaki ya ba ka tsoro? To ka saki jikinka, ko kuma ya turmusheka ya cinye."

Da fadın haka sai Jafar ya nutsu ya daina rawar dari, amma sai ya daina kallon idanun zakin,
domin ba yayi masa kama da komai face garwashin wuta.

Tun sa'adda Yelisa da Jafar suka shigo wannan fada, Boka Jinshan ya bi su da kallo kawai
yana mai yin murmushi. Kai tsaye Yelisa ta je ta zauna daf da shi ta ce "Ya kai abbana, ka sani
cewa ni ce kadai ya a gareka a duk fadın duniyar nan, haka kuma na san kana matukar sona,
so ba na wasa ba. Tun tasowa ta duk abin da na bukata daga gareka kana yi mini, komai
wahalar al'amarin. Ka sani yau na zo gareka da wata babbar bukata wacce ban taba zuwar
maka da irinta ba. Ina fatan za ka taimake ni ka biya min ita."

Yayin da Boka Jinshan ya ji wannan batu na 'yarsa Yelisa, sai ya kyalkyale da dariya yayi ta yin
dariyar har sai da kwalla ta cika masa idanu ya fado kasa daga kan karagarsa. Alamarin da yayi
matukar baiwa Yelisa da Jafar mamaki kenan, suka yi kasake suna kallonsa kawai

1
2

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login