Showing 1 words to 3000 words out of 5533 words
Chapter 1 - KUNDIN TSATSUBA Book 3 By Abdulaziz Madakin Gini .pdf
KUNDIN TSATSUBA
BOOK 2 COMPLETE
Writing by
Abdul’aziz Sani Madakin Gini
08137237071
ashirin baya ba a taba jin ranar da Zarazu ta ce ta koshi ba sai yau."
"To ai shikenan kin huta, mu bari mu cinye ragowar naman nan, in ya so da yamma sai mu fita
farautar wanda za mu ci da daddare."
Haka kuwa aka yi, suka cinye ragowar zakuna, da yamma kuwa suka sake fita farauta. A
sannan ne ta bude tsohuwar rijiyar nan ta fiddo aljani Markahul Sabus, ya ji kamar an tsamo shi
ne daga karkashin teku an dora shi bisa tsibiri, saboda tsananin zurfin rijiyar. Zarazu ta dube shi
tana mai yin hamma ta ce "Ka ga halin da na shiga a sanadin kare lafiyarka, ga shi ina
azabtuwa da yunwa. Tabbas idan na fita na barka a cikin kogon nan, sai sun fito da kai sun
cinye, domin kanshinka ya dame su. Idan kuwa ina nan za su ji kunyar su bude rijiyar don cin
kumallona."
Markahul Sabus yai ajiyar numfashi ya ce "Ai babu abin da zance da ke face godiya, domin kin
ceci rayuwata."
Zarazu ta bushe da dariya ta ce "Ba ni zaka godewa ba, sai dai ka godewa hikimarka ta
ambaton samo mini bil'adama dari. Na rantse da girman ubana, ba don ka yi mini wannan
albishir ba da tuni ka dade da narkewa a cikin cikina. Yanzu na san kai ma ka na jin yunwa, me
kake da bukatar ci na samo maka?"
Markahul Sabus yayi murmushi ya ce "Ai ni nan da kike gani zan iya rayuwa tsawon kwana
arba in ba tare da na. ci komai ba. Ban damu da kaina ba, ke kawai na ke ji."
"Tabdijan! Lallai ku aljanu cikinku baya wahalar da ku. Ai ni ba zan ya kwana biyu ba, ba tare da
na ci komai
ba. Yanzu dai zan san dabarar da zan bullo da ita don kada na azabtu da yunwa tsawon
kwanakin nan bakwai." Haka dai Markahül Sabus ya ci gaba da zama a cikin
rijiya, har tsawon kwana bakwai. Kullum idan su Kirayanu sun tafi farauta, sai Zarazu ta fito da
shi su sha hirarsu. Ranar da ta ji ba zata iya jure yunwa ba, sai ta roki Kirayanu da a rufe kogon
a tafi farautar tare da ita. Haka al'amarin ya kasance. A rana ta bakwai ranar da dodo Kirayanu
ya hada sabon tsumi a kaskonsa ne, gardama ta karke tsakaninsa da Zarazu, inda yake cewa
shi fa kanshin da ke cikin rijiyar nan ya ishe shi haka, ya kamata a bude rijiyar a debe abin da
Zarazu ta amayar a fitar da shi waje. Ita kuwa Zarazu sai ta dage akan cewa ba za a bude ba,
don babu komai a cikin rijiyar face doyin kasusuwan da ke ciki. Sai da aka shafe sa'a guda ana
yin wannan mahawara, a karshe dai Mashamu ce ta raba gardamar da cewa, idan suka tafi
farauta suka dawo suka kara jin wannan kanshi ba makawa sai an bude rijiyar an fito da duk
abin da ke ciki. Zarazu ta ce ta amince da wannan sharadi. A sannan ne dodo Kirayanu da
Mashamu suka dauki kayan farautarsu suka fice.
Sai da ta tabbatar da cewa sun vi nisa da tafiva, sannan ta bude wannan rijiya ta fiddo aljani
Markahul Sabus ta dube shi ta ce "To yau ne ranar cikar alkawarinmu. Yanzu za mu tafi izuwa
inda zaka ba ni bil'adama dari."
Nan take tasa koko ta kanfato tsumin mahaifinfa ta zuba a cikin wata battar fata ta cikata fal,
sannan ta daure bakinta tamau. Markahul Sabus ya miko hannunsa da nufio ya karbi battar, sai
ta janye ta ce "Haba samari, ya za ai na baka wannan tsumin ba tare da ka ba ni bil'adama dari
ba
Shin baka taba jin an ce dinyar makaho ta nuna a hannunsa ba? Idan ka ga na baka wannan
battar, ka tabbata ka ba ni bil'adama dari."
Markahul Sabuş yayi murmushin yake ya ce "To shike nan, na amince sai mu tafi.
"Na ji zamu tafi, amma ina son na san nisan tafiyar da za mu yi kafin mu isa inda zaka ba ni bil
adaman, domin ina son na je na dawo kafin sa'a uku. Ka sani cewa nan da sa'a uku cif iyayena
za su dawo nan kogon daga yawon farautarsu."
"Kar ki sami damuwa, tafiyar sa'a guda kacal za mu yi mu isa wajen, ni da kaina na boye bil
adaman a cikin wani kogo, kuma na ajiye wani hadimina yake gadinsu. Lallai zamu je mu riske
su a wannan wuri"
Ko da jin haka sai murna ta kama Zarazu, nan take suka fita daga cikin kogon Zuhurum suka
nausa wani bangare dabam a cikin jejin, ma'ana ba bangaren da su Kirayanu suka bi ba.
Zarazu tana tafiya da kafafunta a bisa doron kasa, hannunta guda na ruke da battar fata wadda
aka cika da tsumin dodo Kirayanu. Shi kuwa aljani Markahul Sabus na samanta cikin iska yana
yi mata inuwa saboda rana. Tunda suka fara tafiyar zuciyar Markahul Sabus ta cika da
sake-sake, yayi ta tunanin hanyar da zai bi ya raba Zarazu da wannan battar fata. Tabbas ya
san cewa wannan batta ba zata karbu ba da karfin tsiya, ga shi kuma ya san cewa karya yavi
mata cewar yana da bil adama guda dari da zai ba ta. Shin yanzu ta yaya zai raba ta da battar
fata? Kuma ya kwaci kansa daga sharrinta? Tabbas ya san cewa idan ta fahinici yaudararta
yayı, take zata yi loma daya da shi.
Haka dai aka ci gaba da wannan tafiya ba tare da Markahul Sabus ya sami mafita ba a cikin
tunaninsa, har suka shafe rabin sa'a. Kwatsam! Sai suka hango wani katon tsauni a gabansu, a
kan tsaunin kuma akwai wani babban kogon dutse. Tsakanin kasan tsaunin da hawa kansa, za
a yi
tafiya ta kimanin rabin sa'a. Ko da Markahul Sabus ya hango wannan tsauni, sai zuciyarsa tayi
fari, ya dubi Zarazu ya ce "Ina fatan kina iya hango wancan tsaunin ka?"
Zarazu ta ce "Kwarai kuwa, in ce ko dai ba a kansa kake nufin ka ajiye bil adaman ba?"
"Ko shakka babu a cikin kogon dutsen da ke kansa na ajiye su, sai mu karasa don mu je na
sallame ki."
Zarazu tayi duba izuwa kasan tsaunin zuwa samansa, tayi ajiyar zuciya ta ce "Tabdijan! Ta yaya
zan iya hawa kan wannan tsaunin, alhalin ba ni da fukafuki irin naku na aljanu? Ya kai wannan
aljani ka yi sani cewa a halin yanzu ba karamar gajiya nayi ba, sakamakon wannan doguwar
tafiyar da mu ka yi. Lallai sai dai ka hau da ni kan wannan tsauni, ko kuma na tsava a kasa ka
kwaso mini bil adaman ka ba ni ni kuwa na ba ka battar tsumi
Markahul Sabus ya ce "Yanzu dai mu bar tunanin komai, sai mun isa wajen tukunna.
Zarazu ba ta kara fadin komai ba, har suka isa gaban wannan tsauni. Da zuwa suka tsaya su
kai cirko-cirko, suna kallon tsayinsa. Markahul Sabus ya dubi Zarazu ya ce "Ya ke 'yar lele, ki ji
sani cewa ba ni da karfin da zan iya daukarki na haye da ke bisa wannan tsauni, domin nauyinki
ya linka nawa sau arba'in. Kuma ba ni da karfin da zan
i
kwaso bil'adama dari a lokaci guda na sauko da su nan kasa wajenki. Idan kin amince, zan hau
sama yanzu na rinka saukowa da bil'adaman daya bayan daya har su cika dari, sannan ki ba ni
battar tsumi, kowa ya kama gabansa. Yanzu zan fara bawa sarman don na duba lafiyar bil
adaman da kuma mai tsaronsu, in va so sannan na sauko na sanar da ke halin da suke ciki."
Zarazu tayi murmushi ta ce "Na amince da haka."
Markahul Sabus ya bude fukafukansa yayi sama har ya isa kan tsauni. Da zuwa ya shige cikin
wannan kogon dutste yayi shawagi a ciki bai ga komai ba, dama bai yi tsammanin ganin komai
ba, domin karya ya shirgawa Zarazu. Kawai sai ya fita daga cikin kogon ya sauko kasa inda ya
bar Zarazu, ya dube ta ya ce "Na same su lafiya, to amma abokan tafiya ta sun ce ki nuna musu
battar tsumi daga nan kasa don su hangota su tabbatar da akwai ta, sannan su sauko miki da
bil'adaman guda dari."
Da jin haka Zarazu ta dubi Markahul Sabus cikin mamaki ta ce "Au dama ba kai kadai ka shigo
jejin nan ba? Me ya sa tun farko baka sanar mini ba?"
Markahul Sabus ya ce "Ai kin san ba zan yi saurin sanar da ke sirrina ba, tun da ban san yadda
za mu karke ba. Ke dai kawai ki yi abin da na fadl, yanzun nan za ki ga abokan tafiyar tawa sun
leko nan kasa."
Ba tare da wata fargaba ba, Zarazu ta fiddo battar tsumi daga cikin aljihun rigarja ta fata, ta
daga sama saitin saman tsaunin, tana mai cewa "Ina abokan tafiyar aljanin nan! Ku leko kasa
ku ga abın muradinku.
Cikin abin da bai wuce rabin dakika ba. Markala Sabus ya yunkura cikin tsananin zafin nama da
shammace fisge battar tsumi daga hannun Zarazu vai sama, bai dita ko ina ba sai kan tsaunin.
Kawai sai ya leko kasa ya d Zarazu ya kyalkyale da dariyar mugunta ya ce "Ke yarin Daga yau
na koya miki hankali, domin na nuna miki co duk wanda ya riga ka kwana, dole ne ya riga ka tas
Tabbas na riga ki zuwa duniya, dole ne na fi ki wayo. Yan zan tafi da tsumin mahaifinki, domin
shi ne abin da ya kan ni jejin nan. Batun biladama dari kuwa, Karya na shin miki ba ni da su.
Kafin Zarazu ta bude baki ta ce wani abu, Markahul Sabus ya bude fukafukansa ya tashi sama,
nan nan ya luluka a cikin gajimare ya bace. Al'amarin da sawa Zarazu mugun bakin ciki a zuci,
kawai sai ta da hannayenta biyu masu zakwa-zakwan faratu ta caka a cikin ta farke shi, sai ga
tumbin cikinta ya fado kasa. Nan take tadi kasa matacciya, ko shurawa ba ta yi ba.
Al' amarin aljani Markahul Sabus kuwa, ko da yat ya sami nasarar karbar battar tsumi daga
hannun Zarazu. sai ya cika da farin ciki, ya kara kaimi a cikin tafiyarsa ya ta keta hazo cikin
tsananin gudu da kwanciyar hankali. da ya tuna cewa alkawarinsa da sarki Lu'umanu na kwan
dari da goma sha biyu ne, ga shi ya bata kwana bakwal Kokarın samo tsumin dodo Kirayanu,
sai hankalinsa ya tash domin baya son ya gota wadannan kwanaki ba tare da ya s fadar sarki
Lu'umanu ba. Nan fa ya shiga tunanin hanyar zai bi ya kara karfin gudunsa. Yana cikin tunanin
ne dabar ta fado masa. A ka'ida hayan kowa ne mako guda ya k
sauka ya huta, kuma ya ci abinci, amma yanzu sai ya yanke shawarar ba vai rinka saukowa
kasa ba, sai bayan mako biyu, kuma idan yana tafiya a sama zai rinka kada fukafukansa da
saurin gaske, don ya sha gaban lokaci. Haka kuwa al'amarin ya kasance. Aljani Markahul
Sabus ya kara Kaimi iyakar karitsa a cikin wannan tafiya
A ranar de kwanaki suka cika dari da goma sha biyu cif-cif, sarki Lu'umanu na zaune a fadarsa
tare da 'yan majalisarsa, da kuma bokayen kasarsa, da sauran jama ar gari, sai kawai aka ga
garin ya gauraye da hadari, nan da nan kasa ta kama girgiza. Ba zato ba tsammani sai ga aljani
Markahul Sabus ya ratso ta karkashin kasa ya bayyana a tsakiyar fada, hannunsa na hagu na
rike da battar tsumin dodo Kirayanu. Ko da ganinsa sai fadar ta rude da tafi da shewa.
Murna ta kama sarki Lu'umanu ya mike tsaye daga kan karagarsa ya taho ga Markahul Sabus
yana mar cewa "Lale marhabin da farin bako, Lallai ka cika alkawari akan lokaci, ba ni abin
muradina."
Sarki Lu'umanu ya mika hannu da nufin ya karbi battar tsumi, sai aljani Markahul Sabus ya
janye ya ce "Haba ranka ya dade, ashe ka mance da sharadin alkawarinmu? Ai ba zan ba ka
tsumin dodo Kirayanu ba, sai na fadi tawa bukatar ka biya mini
Ko da jin haka sai sarki Lu'umanu yayi murmushi va ce "Fadi bukatar ka na ji, in dai ba ta saba
sharadın da na gindaya ba kafin ka tafi, yanzu take zan biya ta."
Markahul Sabus ya numfasa ya ce "Ya kai wannan sarki ka yi sani cewa, ba na bukatar komai
daga gareka face ka mallaka mini wannan mata taka wato Fatisa."
Ko da jin haka sai sarki Lu'umanu ya murtuke fuska, ya koma kan karagarsa ya zauna,
hankalinsa ya dugunzuma ya rasa abin dake masa dadi. Daga can sai ya dago kai a fusace ya
ce "Ashe baka da hankali? Ya za ai ka bukaci abin da na turaka tafiya a dominsa? Ina
umartarka da ka fadi wata bukatar, amma ba wannan ba, ban da raina, da mulkina, ko mene ne
zan mallaka maka shi."
Markahul Sabus yai ajiyar numfashi ya ce "Ni kam in dai ba Fatisa zaka ba ni ba, ba na bukatar
komai, lallaj zan yita da tsumin dodo Kirayanu, in ya so ni da kai kowa yai asarar bukatarsa.
Cikin harzuka sarki Lu'umanu ya ce "Bace mana da gain! Ya kai wannan aljani!! Ka sani cewa
daga yau na haramta maka shigowa kasata, idan kuwa ka kuskura ka kara zuwa, zan tabbatar
dawancan hukunci da nai alkawari a kanka."
Ba tare da mai da wani martani ba, aljani Markahul Sabus, ya bace. Bacewarsa ke da wuya,
sarki ya shiga gida cikin tsananin fushi da bakin ciki, nan dai fada ta watse kowa ya kama
gabansa. A wannan rana ba wanda ya kusanci sarki Lu'umanu, sapóda ganin irin fushin da
yayi, tabbas zai iya hargitsa garin, gaba daya idan aka fusata shi. Hatta iyalansa ma, baya-baya
suka yi da shi a ranar, babu wanda ya shiga turakarsa face masu yi masa hidima, su ma a cikin
dari-dari suke aiwatar da aikinsu.
Shi kuwa aljani Markahul Sabus bayan ya isa karshen gari, sai ya zaana yana ta tunani da
bakin cikin wannan abu da sarki Lu'umanu yayi masa. Ya tuno da alkawarin da ya faukarwa
mahaifiyarsa cewa, ba zai komo gida ba sai tare da batisa. Nan take ya ji zuciyarsa ta kekashe,
tsore ya kau daga cikinta, kawai sai ya yanke shawarar ya ko gidar sarautar sarki Lu'umanu, ya
sato gimbiya Fatisa, ba tare da wani ya gan shi ba.
Nan take Markahul Sabus ya bude fukafukansa yai sama, ya nufi gidan sarki Lu'umanu a cikin
tsananin gudun da bai taba yin irinsa ba. Kamar kiftawar ido, sai ga shi ya dira a tsakiyar gidan
sarautar, nan fa ya fara neman inda gimbiya Fatisa take. Duk ta inda ya bi ko da bango ne, sai
dai ka ga ya ratsa ta cikinsa ya wuce kamar yadda danshin ruwa ke tsattsafowa daga karkashin
kasa. Markahul Sabus yai ta shiga sako-sako, daki-daki, har ya iso bangaren da gimbiya Fatisa
take. A wannan lokaci dare ya raba, ga dakaru nan birjik suna gadi, amma babu wanda ya iya
ganin Markahul Sabus, duk da cewa gaba daya harabar gidan a haskake take da hasken fitilu
manya-manya irin na sarauta.
Sa'adda Markahul Sabus ya shiga turakar gimbiya Fatisa, sai ya iske kuyanginta a kwankwance
suna ta sharar bacci, kamar ba su da rai. Nan ya tsallake su ya wuce izuwa cikin kuryar dakinta.
Daki ne mai giman gasket, wanda aka kawata shi kayan alatu iri-iri. Ko ina ka duba shudin
kilishi ne a shimfide, mai tsananin laushi idan ka 'aka. A tsakiyar dakin aka girke wani katon
gado na zinare mai tudun taushi, an rufe shi da labulen alharini mai dajiyar baki da zubardaji,
sai
sheki da walwali yake. Gaba daya dakin ya dume da Kanshin turaren miski. A kan tsakiyar
gadon gimbiya Fatisa ce kwance cikin wata doguwar farar riga mai shara-shara, wanda ta
bayyana duk ilahirin surorin jikinta tamkar ba ta rufe jikinta da komai ba. Yayin da Markahul
Sabus ya ganta a cikin wannan hali, sai ya gigice, kuma ya dimauce, take ya kamu da matukar
sha'awarta. Nan take ya isa kan gadon ya zauna daf da ita. Zamansa ke da wuya ta bude
idanu, suka yi arba da juna, maimakon ta rafka ihu ko ta razana, sai ya ga tayi murmushi,
al'amarin da yai matukar ba shi mamaki. Har ya bude baki zai ce wani abu, sai ta toshe bakinsa
da tafin hannunta ta ce
"Kar ka ce komai ya masoyina, na san zaka dawo gare ni. Ka yi sani cewa tun ranar da muka
ga juna, ka tafi ka bar ni cikin mayen begenka. Dare da rana ba na iya bacci, saboda troaninka.
Hakika mijina ya ci amanarka bisa alkawarin Ja ku ka yi. Ina umartarka da ka hanzarta tarawa
da ni kafin ya san da zuwanka, domin burinka da nawa ya cika.
den A daidai wannan lokaci kwatsam! Sai suka ji kofofin akin guda takwas sun bubbude da
karfi. Dakaru suka yi ta tudowa cikin dakin, dauke da makaman yaki. Cikin Jakiku kadan suka
yiwa dakin kawanya. A wannan lokaci Fatisa da Markahul Sabus suna rungume da juna, suna
tsaye a kan gadon cikin firgici.
Gaba daya dakarun suka tsaya kyam suna kallon su Fatisa kawai. Ba zato kuma sai ga sarki
Lu'umanu ya bayyana a cikin shigar yakl, fuskarsa a murtuke, idanunsa sun kada sun yi ja
juwur.
Cikin fushi ya dubi Fatisa ya ce "Kaiconki matata, hakika kin ba ni кипув, кида kin zubar da
kimarki. Ki sani kin yi babban lahani ga darajat sarautata, lallai yau dayanku ba zai tserewa
azahate ba, ina nufin ke da wannan