Showing 1 words to 3000 words out of 4208 words

Chapter 1 - KUNDIN TSATSUBA Book 2 By Abdulaziz Sani Madakin Gini .pdf

KUNDIN TSATSUBA
Book 2 Complete
Writing by
Abdulaziz Madaki Gini
07032707179



Sarki yai murmushi ya ce "Ai wannan ba bako ne kuma ba mutum ba ne aljani ne, Markahul
Sabus kenan... Sh ne wanda zai yaye mana bakın cikin da ya addabı uniravuwarmu na rashin
saman magaji.
Fatisa ta sake yin duba izuwa ga Markahul Sabus ta yi murmsuhi ta ce "Kai amma wannan
aljani da kyau kake."

Ko da jin haka, sai Markahul Sabus ya ji farin ciki ya lullube shi, bai san sa'adda ya maida mata
da martanin murmushi ba, saunan ya ce "Na rantse da darajar iyayena, kaf iyakar yawona a
duniya ban taba ganin mace mai kyawunki ba walau a cikin mutane ko aljanu."

Cikin fushi sarki Lu'umanu ya dubi Markahul Sabus ya daka masa tsawa ya ce "Ya kai wannan
aljani ka sani na sa hijabi tsakaninka da matata, ba kai ba ita, ban kirawo ka nan ba don ku yi
hira. Na umarce ka da ka bace mini da gani."

Rufe bakin sarki ke da wuta, aljani Markahul Sabus ya bace yana mai kyalkyala dariya tare da
yiwa Fatisa sallama ta hanyar daga mata hannu. Daga nan sarki ya sallami bokayensa da
sauran jama'a kowa ya watse.

Alamarin aljani Markahul Sabus kuwa, tunda ya bar fadar sarki Lu'umanu ya kasa samun
sukuni, sakamakon tunanin al'amari guda biyu da suka addabi zuciyarsa. Abu na farko shi ne,
wannan gagarumar tafiya da zai yi izuwa kogon Zuhurum don debo tsumin dodo Kirayanu.
Tabbas ya san cewa wannan tatiya ba karamin hadari gareta ba, domin bai taba yin tafiya mai
nisan ta ba, kuma ya san cewa akwai abubuwan hadara akan hanyar wadanda ka iya janyo
asarar rayuwa gaba daya. Tun Markahul Sabus na yaro karami yake jin labarin dodo Kirayanu a
wurin tsofaffin aljanu, an tabbatar da cewa dodo Kirayanu ya sha jinin aljanu sama da dubu arba
in, biladama kuwa ba a lissafinsu. Da yawan jarumai da sadaukai sun rasa rayukansu wajen
kokarin zuwa

kogon Zuhurum don debo tsumin dodo Kirayanu. Shi dai wannan tasumi an ce yana da sihiri
dubu saba in. kuma ba a shan sa sai an san daya daga cikin sihirinsa, sannan asha da wannan
niyyar. A halin yanzu sihiri daya aka sani daga cikin guda dubu saba'in din, wato sihirin samun
hathuwa. Sauran sihirin kuwa, babu wanda zai iya saninsu face wanda ya karance littafin
Kundin Tsatsuba

Bayan aljani Markahul Sabus yayi dogon tunani, sai ya yanke shawarar ya koma gida ya sanar
da mahaifiyarsa wannan gagarumar tafiya da zai yi, ko ta taimake shi da abin da zai kiyaye

kansa daga abubuwan hadarin kan hanya. Nan take Markahul Sabus ya juya da baya ya nuti
kasarsu. Tsakanin birnin Teheren zuwa garinsu Markahul Sabus, tafiya ce ta shekara arba in,
amma a cikin sa'a hudu da 'yan dakiku kadan Markahul Sabus ya shafeta.

Yau shekara biyu kenan rabon Markahul Sabus da gida, tun sa'adda yai bankwana da
mahaifiyarsa kan cewa, ya tafi neman aure ba zai dawo ba sai da mata. Mahaifin Markahul
Sabus ne wazirin sarkin garin nasu, kuma ya mutu shekaru dari da hamsin baya.

Samaratu mahaifiyar Markahul Sabus na zaune a farfajiyar gidanta, kuyangi sun zagaye ta
suna ba ta labarai masu dadi don debe mata kewar tunanin danta, sai kwatsarım! Suka ga
Markahul Sabus ya bayyana a gabansu. Cikin tsananin farin ciki, Samaratu ta mike zumbut ta
ruga gare shi suka rungume juna suna kukan inurna.
Bayan sun nutsu, sai ta janye jikinta daga nasa ta duba gabas da yamma, kudu da arewa, ba ta
ga komai ba.

"Ya kai dana ina sirikar tawa? Ashe ba mun rabu akan cewa ba zaka dawo ba sai da matar da
zaka aura?"

Markahul Sabus ya jinjina kai ya ce "Kin yi gaskiya ya ummina. Hakika na gano matar da ta
dace da ni, amma mallakarta daidai ya ke da tashin yakin duniya."

PLAY Ba tare da bata lokaci ba, ya kwashe labarin Fatisa matar sarki Lu'umanu ya zayyana
mata, da kuma batun zuwansa kogon Zuhurum. Da ya kare, sai ya ce "Ya ke ummina, ki yi sani
cewa na aiyana a zuciyata babu abin da zan bida a wajen sarlki Lu'umanu a matsayin ladan
aikin da nai masa, face ya sallama mini wannan mata tasa, idan kuwa ya ki zan sace ta na taho
da ita nan a daura mana aure. Na rantse da darajar sarautar gidan nan, na kamu da mutukar
son Fatisa, son da ba zan iya rayuwa ba sai da ita. Ki yi sani cewa ban dawo gare ki domin
komai ba, sai don ki taimaka mini da shirin da zan kare lafiyata yayi wannan tafiya, domin na
san kin gaji sihirai da dama a wajen mahaifina."

Saladda Markahul Sabus ya zo nan a zancensa, sai Samaratu tayi shiru gami da sunkui da kai
kas, ba tace komai ba tsawon lokaci. Daga can sai ta dago kai ta dubi dan nata, idanunta cike
da kwalla ta ce "Ya kai dana, ka yi sani cewa a cikin duniyar nan kaf babu abin da nake so
sama da kai, kuma kome ka bukata a gare ni in dai ina da shi, sai na ba ka. Ka sani cewa,
wannan bukata taka daidai take da bukatar masunci a cikin ruwa. Ma'ana idan ya jefa komarsa
bai san abin da zai kamo ba. Tabbas zan taimaka maka, kuma zaka sami nasarar debo tsumin
dodo Kirayanu, amma ina jiye maka sharrin sarki Lu'umanu. Lallai wannan mutum ba karamin
hatsabibi ba ne, domin yana iya sarrafa aljani kamar

yadda ake sarrafa kwayar hatsi a turmi. Ba ni da wani sihin da zan iya kareka daga sharrinsa.
Hakika idan ka kusanci matarsa, sai ya boycka a cikin kurkukun da ba mai iya fito da kai. Ka ga
kuwa idan haka ta faru, shi kenan an raba ni da kai har abada. Ina mai ba ka shawara da ka

cire son Fatisa daga ranka, ka sake fita neman wata. Ka sani cewa duniya na da fadi babu
mamaki ka gano wata wadda ta fi ta a wani bangaren na duniya."

Yayin da Samaratu ta zo an a zacenta, sai Markahul Sabus yai murmushi ya ce "Ya ke ummina,
ki daina tsoron komai, ki sani cewa ni Markahul Sabus na kai wani matsayi da ba ki taba zato
ba. Ina tabbatar miki da cewa babu wani bil'adama da ya isa ya sarrafa ni yadda yake so a
doron kasa, sai dai dan'uwana aljani, ko kuma irin su dodo Kirayanu Nai miki alkawari babu abin
da sarki Lu'umanu zai iya yi mini. Ke dai kawai yanzu ki taimaka mini na je kogon Zuhurum na
dawo lafiya."

Samaratu ta yi ajiyar numfashi ta ce "To shike nan ai ance ba a kwacewa yaro garma, amma
wanda bai ji bari ba zai ji hoho. Yanzu ka zauna zan tafi jeji na samo wadansu ganyayyaki da
saiwowi wadanda zan jika su su kwana a tsume, sannan ka shanye. In dai ka sha wadannan
saiwoyi da ganyaye, babu wani hadari da zai sameka yayin wannan tafiya. Al'amarin dodo
Kirayanu kuwa ba ni da wata dabara akansa, sai dai hikimar ka ta kwace kam nista

Da jin haka sai Markahul Sabus yai murmushi ya ce "Na san da haka, kuma na amince, ke dai
kawai ki tafi aiwatar da naki shirin."

Kafin ya gama rufe bakinsa, tuni Samaratu ta bace.

Bayan kamar sa'a biyu, sai ga Samaratu ta dawo dauke da wasu ganyayyaki da saiwoyi iri-iri
birjik, wasu ma babu wanda ya taba ganin irinsu a garin. Da zuwa tasa aka dauko mata wata
katuwar kwatanniya ta zuba a ciki, sannan ta kawo ruwa ta zuba a kai. Zuba ruwan ke da wuya,
sai ganyayyakin da saiwoyin suka hau narkewa suna tafarfasa, kai kace kwatanniyar a
karkashin wuta take. Nan take ta kawo murfin kwatanniyar ta rufe, sannan ta dubi Markahul
Sabus ta ce "Ya kai dana, je ka abinka ka yi barci, don ka sami hutu daga nan zuwa asuba zan
zo na tashe ka don ka zo ka sha wannan tsumin nawa.

Ba tare da wata gardama ba, Markahul Sabus ya tafi izuwa dakinsa ya kwanta yayi ta sharar
bacci har da minshari, saboda gajiyar tafiya, nоwеd

Asubahin farko, Samaratu ta tashi Markahul Sabus suka tafi izuwa tsakar gida inda aka ajiye
kwataniyar nan. Da zuwa ta dube shi ta ce "Maza ka dauki kwatanniyar nan ka shanye abin da
ke ciki."

Nan take Markahul Sabus ya daga wannan katuwar kwatanniya da hannu daya, wacce nauyinta
ya wuce karti dari su iya raba ta da kasa, kawai sai ya kafa a bakinsa ya kwankwade ruwan ciki.
Gaba daya zuka uku yai wa ruwan abakinsa ya kare. Markahul Sabus ya jiye kwatanniyar,
sannan yai gyatsa. Faruwar hakan ke da wuya ya ji gaba dayan jikinsa ya dau dumi, kafin aji
ma zufa ta lullube shi, tamkar ruwa ake kwara masa. Nan da nan gumin jikinsa ya malala a kas
ya taru. Inda bil'adama zai fada cikin gumin, sai ya nutse a ciki ya ji kamar kogi ya fada. Bayan
gumin jikin nasa ya kafe, sai kuma ya ji wani irin sabon karfi ya

shige shi, tamkar zai iya daukar duniya bisa tafin hannunsa. Markahul Sabus yayi girgiza ya
daka tsalle gami da kururuwa, wadda ta farkar da duk mutanen garin gaba daya, kowa ya tashi
a firgice daga bacci. Kawai sai ya dubi mahaifiyar tasa ya ce "Ya ke ummina, hakika kin yi mini
kyakkyawan shirin da zan iya tunkarar komai da kowa. Ina mai godiya a gareki gami da yi miki
sallamar cewa, ni zan tafi izuwa ga neman biyan bukatata, kuma na dauki alkawarin cewa ba
zan dawo gare ki ba, sai da matata gimbiya Fatisa."

Ko da jin wannan batu, sai hawaye ya zubowa Samaratu ta rungume Markahul Sabus ta ce
"Inai maka fatan nasara dana. Lallai zan kasance cikin rashin kewa da tsananin begenka har sai
na ga dawowarka."

Nan take Markahul Sabus yai ban kwana da mahaifiyarsa, sannan ya bude fukafukansa yai
sama, ta bishi da kallo tun tana iya hangensa har ya kule a cikin sararin samaniya.

Markahul Sabus ya sha gwagwarmayar gaske a dazuzzuka da yawa kafin ya isa kogon
Zuhurum, domin sai da yayi dauki ba dadi da mugayen aljanu iri-iri, da kuma maridai, da
dodanni kala-kala. Sai da ta kai cewa yayi jinyar rashin lafiya sau sittin da biyar, amma ko kadan
bai tsaya da yin tafiyarsa ba. Ma'ana har ya isa kogon Zuhurum yana fama da rashin lafiya,
sakamakon raunikan da ke jikinsa. Shi kansa ya fitar da ran rayuwa, amma bisa mamaki sai ya
ga bai mutu ba.

Lokacin da aljani Markahul Sabus ya dira a bakin kogon Zuhurum tsakiyar dare ne, dan haka
dodo Kirayanu da iyalansa na kwance a cikin kogon suna barci.

Kogon Zuhurum na da matukar tsawo, fadi da kaurin gaske. Kofar shiga kogon zagayayyiya ce,
kuma an rufe ta da wani katon mummulallen dutse. Babu mai iya janye wannan dutse, face
Kirayanu ko kuma matarsa wadda ake wa lakabi da Mashamu. Sa'adda Markahul Sabus ya iso
sai ya iske wannan mummulallen dutse a bakin kogon. Abin ka da mai takama da karfi, sai ya
kama dutsen da hannu biyu da nufin ya dauke shi, cancakas a hankali ya ajiye waje guda. Ko
da ya ciciba da niyyar dagawa, sai ya ji kamar yana shirin daukar sararin samaniya ne. Take ya
ji kamar jijiyoyin hannunsa za su tsintsinke. Ba shiri ya saki dutsen. ya koma gefe guda ya tsaya
yana mamaki. Daga can sai ya sake komawa ya dada jarrabawa a karo na biyu, abin da ya faru
da farko shi ne ya sake faruwa. Kai sai da Markahul Sabus ya jarraba daukar dutsen nan sau
bakwai, yana kasawa. Al'amarin da ya matukar tayar masa da hankali kenan, ya rasa abin da
ke masa dadi a duniya. Nan dai ya tsaya yana tunani, yace a ransa "Ba ni da wata dama da tafi
yanzu, domin a yanzu ne dodo Kirayanu ke yin bacci, inda na sami damar shiga kogon da sai
na sato tsuminsa salin alin na yi tafiyata ba tare da ya ganni ba, amma idan na kuskura gari ya
waye yayi arba da ni tawa, ta kare. To yanzu yaya zan yi tunda dai ba ni da ikon shiga kogon?
Me ya kamata na yi don kubuta daga sharrinsa?"

Wata zuciyar ta ce da shi "Kawai ka tafi cikin wannan jejin ka buya a wani wurin har izuwa wani
daren

sannan ka dawo, babu mamaki ka yi sa'a ka tarar ya bar kofar a bude, ai ma su iya magana sun
ce ba kullum ake kwana a gado ba. Yau da gobe ta fi karfin wasa, dole ne wata ran ya mance
da rufe kofar."

Da wannan shawara kuwa Markahul Sabus yayı aiki, amma sai da dare bakwai ya shude bai
taba zuwa ya atarar da wannan kofa a bude ba, kullum jiya yau. Nan fa hankalinsa ya kara
dugunzuma. A wannan dare ne ya kasa tafiya, ya tsaya yana shawarwarin abin da zai fisshe
shi. Shi kam ya tabbatar da cewa tunda ya zo wannan wuri ba zai koma ba, sai da tsumin dodo
Kirayanu, ko kuma ya rasa rayuwarsa a wajen. Haka dai ya ci gaba da tunani iri-iri, har asuba ta
doso kai. Nan take ya yanke shawarar ya sami wuri ya boya nesa kadan, inda zai rinka hango
kogon, da zarar ya ga Kirayanu ya fita sai ya je ya shiga ya debo tsumin ya kama gabansa.
Markahul Sabus ya tashi sama ya tafi can nesa kadan izuwa kan wasu bishiyoyi masu yawan
ganyayyaki da duhuwa, ya haye kai ya boye yadda yana iya hango bakin kogon Zuhurum. Yana
nan laße har gari yayi shar, rana ta fara huduwa, a lokacin ne gyangyadi ya fara dibar Marhakul
Sabus sakamakon gajiya bisa doguwar tafiyar da ya sha fama a baya ta tsawon kwana dari da
goma sha biyu. Tun sa adda ya baro gida kawo izuwa yanzu bai. rintsa ba, lallai kuwa akwai
tarin bashin bacci a kansa. Ba azato sai bacci ya sace shi, yai ta kwarara abinsa bai san abin
arda ke faruwa ba.

Jim kadan da fara baccin nasa ne, kofar kogon Zuhurum ta bude, sai ga dodo Kirayanu tare da
matarsa Mashamu da kuma yarsu guda daya Zarazu sun fito waje




suna masu yin hamma da mika. Kai da ganin su ka san cew. yunwar safe ce ta tashe su.

Shi dai dodo Kirayanu ba karamin zabgegen kato ba ne. Yana da manyan damatsa, da kuma
rafkeken kai, idan yai tafiya sai ka ji kasa na amsawa saboda karfin takun sawunsa. Idan kuwa
ya gifta wajen da bishiyoyi suke, sai ka ga suna rangaji saboda tsananin hucin iskar hancinsa
da bakinsa.
Dodo Kirayanu ya shaski iska, ya dubi matarsa da 'yarsa ya ce "Kai ku tsaya, anya kuwa ba mu
sami bako ba a jejin nan? Ni fa ina iya jin kanshin bil'adama."

Mashamu ta daga bututun hancinta mai kama da algaita ta shaki iska, sannan ta ce "Kwarai!
Mai gida ni ina na ji kanshinsa, lallai yau muna da kyakkyawan bude baki. Wai! Yaushe
rabonmu da cin bil'adama, ai akalla mun sami shekara ashirin, sai dai naman aljanu kullum da
shi mu ke kalaci har ma sun ginshe ni, gwara na ci naman dabbobin dawa."
Ko da jin haka, sai Zarazu ta bushe da dariya tace "Lallai na ga alama rikicin tsufa ya fara
riskarku. Ya za'ai ku ji kanshin mutum a jejin nan? Shin kun manta ne cewa babu inda
labarinmu bai je ba a duniya? Ai tuni bil adama suka sallama wannan jeji, suka Daina shigo shi.
Ku dai kara shinshinawa da kyau ku ji, ba mutum ba ne aljani ne amma kanshinsa na daban ne.

Take Kirayanu da Mashamu suka sake shakar numfashi cikin nutsuwa tsawon dakika biyar.
Kirayanu ya ce "Ai kuwa yarinya ta yi gaskiya. Yanzu mene ne abin yi?"

Mashamu ta ce "Abin da za a yi, ni da kai mu tafi farautar wannan aljani, ita kuma Mushamu mu
bar ta anan

tayı gadin kogon mu, ban son ka tsaya rufe kofa mu bata lokaci har aljanin ya tsere."

Ko da jin wannan shawara, sai Kirayanu ya amince, nan take suka nausa inda Markahul Sabus
ke laße, suka bar Zarazu a kofar kogo tana kai kawo da leke-leke, ko zata hango inda bakon
aljanin yake.

Yayin da aljani Markahul Sabus ya hango su dodo Kirayanu sun durfafo inda yake lebe, sai
tsoro ya kama shi har hantar cikinsa ta kama rawa, bai san sa'adda ya dauke numfashi ba
saboda tsananın razana. Dodo Kirayanu da Mashamu suka iso daf da bishiyar da Markahul
Sabus ke kai, suka tsaya. Nan suka yi duba iya dubansu ba su ga komai ba. Al'amarin da ya
matukar ba su mamaki kenan.

Mashamu ta dubi Kirayanu ta ce "Kai abin nan da ban mamaki yake. Kafin mu iso wajen nan
muna ta jin Kanshin aljani, amma kuma muna isowa sai na ji kanshin ya dauke. Ga shi babu irin
duban da ba mu yi ba, amma ba mu ga komai ba."

Kirayanu ya ce "Hakika haka al'amarin yake. Ina ganin aljanin ya gudu ya bar wajen nan, zo mu
kara gaba wata kila mu riske shi."

Ba tare da wata gardama ba. Mashamu ta bi Kirayanu a baya suka ruga da gudu cikin jejín
suna daga. bututun hancinsu sama, don su jiyo a inda kanshin aljanin yake. Abin da ba su sani
ba shi ne, aljanin na nan a inda suka baro. Dodo Kirayanu da iyalinsa ba sa iya ganin halitta
muddin halittar ba ta numfashi. Wannan shi ne dalilin da ya sa ba su ga aljani Markahul Sabus
ba, domin sa adıda ya gansu ya firgita numfashinsa ya dauke gaba daya, harta

1
2

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login