Showing 3001 words to 6000 words out of 34797 words

Chapter 2 - ZUCIYA DA KWANJI BOOK 2 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI.pdf

ba ki ji
ba?"
Sai ta juyo ta nemi kujera ta zauna ba tare da
ta
dube shi ba, ta fara kurbar ruwan cittarta
fuskarta
a bace. Ya yi nazarinta a nutse sannan ya kara
kyautata murya ya ce. "Wai komawa zaki yi ki
kwanta ba zaki yi wanka ki karya ba? Ta shere
kamar da dutse ya yi batunsa. Bai damu ba sai
ya kuma dorawa. "Kin san kuwa abin da ya jaza
miki murara nan ba zai wuce kunshe kanki da

kike a daki kina fama da sanyin A C da iskar
fanka,amma ba kya gaurayawa da hasken rana
da sassanyar isaka ba? Ta kuma sharewa,sai
kawai ya tashi ya shige toilet ya hada mata
ruwan wanka,sannan ya fito ya mika mata
hannu
ya ce. "Ba ni wannan cittar, shiga ki yi wanka".
Ba ta musa masa ba ta dure cup ta mike ta shige
wankan.kafin ta fito ya tanadar mata shayin
tafarnunwa da zuma ya kai mata har daki
sannan
ya koma mata da madara peak wadda zata
dusashe waurin tafarnuwar. Bayan ta shirya da
kansa ya shasshafa mata man zafi a
makogwaronta zuwa kirjinta, sannan ya rike
hannunta ya yi kokarin kallon kwayar idonta ya
ce. "Don Allah ki zo mu je ki sha hantsi kinji?
Kar
ki daka ta ni ki duba lafiyarki kinji?" Ta kawar
da
kai tana shakar hancin,da sauri ya saki
hannunta
ya yago tissue ya mika mata. Wannan
dawainiyar
da yake mata ce ta hanata yi masa musu wanda

ta ke ji kamar yana mata ne domin saihiyar
kaunar da yake mata tunda babu abin da yake
amfana daga gare ta. Ya daukar musu darduma
da ruwa da filo ya bata rikon ruwan da
tambulan,shi kuma ya dauko mata lemon citta
guda biyu suka tafi. Sun sami sadiya zaune a
daya daga cikinb kujeru da ke rumfar tana
danne
danne waya,Abdullahi ya yi mata sallama tare
da
dan zolayarta amma ta yi fuska. Ya shimfida
dardumar ya sanya filon sannan ya karbi ruwan
hannun fatima yana cewa. "Sannu da
kokari,zama
ban da kwanciya". Ta yi murmushi a kasalce ta
kwanta,ba tare da ta tayar da kanta akan filon
ba. Ya bita da kallo kafin ya yi magana ta riga
shi da taushin murya. "Ka yi hakuri don Allah.
Ya
ji sanyin maganar har cikin ransa,ina ma tare
da
sadiya ko hindatu suke wuni su kwana? Ya
zauna
yana mika mata filom yana cewa. "To na
hakura

sa filon". Ta girgiza kai,ta ce. "Zauna akai ka
karanta min magazine. Kafin ya yi magana sai
ga
hindatu cikin shirin fita.ta yi musu sallama tare
da gaishe da abdullahi,ita kuma fatima ta
gaisheta,Abdullahi ya ce. "Kin ga kuwa hindatu
gaba dayanku ya kamata ace kun je ganin
jariri,fadima muwadda. Matar yaya abdullahi
ce
ta haihu na manta ne ban sanar da ke ba.ya
kamata kuma ki je barka,ko bari zamu yi da
dare
na kai ku gaba daya? Kamar gaske ta ce. "Ai
tunda ba ka sanar da ni akan kari ba ka
makara,Allah ya kai mu suna, hindatu ki shafo
min kan baby...... Ya tare ta. "Idan na ce sai
kun
je sai a yi yaya? "Sai ka aikata abin da bai
kamata ba, ka. Debe ni da mura na je na
shafawa
mutane". Hindatu ta ce. "Ni fa Abu Turab ko
me
ka tsara ba zan fasa fitar nan ba tunda na
shirya,sati biyar fa ban ga waje ba..... Haba kai
har yanzu ba ka tsufa da kulle ba". Ta karasa

da
dariyar zolaya. Shi kuma ya saci kallon fatima
ya
ce. "Kina korafi akan wata daya,me wata uku
ta
ce me?" Fatima ta juya baya tana shakar
hanci,ta
ce. "Kai za a tambaya tunda kake jin zaka iya
maye min gurbin duk wani hali da aboki" "Dan
ma
yana kwatantawa". Inji hindatu cikin
raha.fatima
ta dan yi dariya kawai,shi ma abdullahi haka
yana kallon fatima da ta juya musu baya,ya ce.
"Ita ma dan ba ta sai da turaren wuta a gidan
biki ne shi yasa ba ta matsa min sai ta fita ba"
Ba ta damu da juyowa ba ta ce. "Ka dai samu
dama a kaina kawai,amma nawa uzurin ai ya
zarce na turaren wuta.na kuma zuba maka ido
nan da wata uku masu zuwa in sabuwar
amaryaka zata shigo ka barni na fita". Ya jima
kafin ya samo inda wannan maganar ta
samu,sai
can ya tuna ganinta,dan haka da kyar ya samo
abin cewa. "Ni ban san wata amaraya ba ban da

ke shekaru talatin nan gana ba watanin uku ba"
"Allah ya nuna mana". Inji hindatu da ta so
katse
hirar bayan kishi ya sosa ranta.ta nufi sadiya
tana cewa. "Kin ga sadiya dan Allah rabi
kanwata
zata zo yau mun yi waya da ita yanzu suna bisa
hanya, ni kuma na riga ba shirya ban son fasa
fita,kuma da yake dama hutu zasu zo min sai
kawai na ce su sauka a wajenki. Dama sadiya a
wuya ta ke,neman me taba ta take ta fashe a
kansaa. A wulakance ta ce. "Ni ma fita zan yi".
Abdullahi ya dan kalli sadiya amma bai tanka
ba,
sai fatima da ke jinsu ta ce. "Idan babu
damuwa
ba sai ta zo wajena ba, Allah ya sa matara aure
ce mu samu mai gidan nan ya barni mu sarara".
"To addu'arki ba ta ci ba". Suka hada baki shi
da
hindatu suna yi mata dariya,hindatu ta yi
mata
godiya,shi kuma ya dubi fatima da muryar
rarrashi ya ce. "Bari na kaita titi na samar
mata

taxi". Ta amsa masa. Suka fice aka barta da
sadiya wajen ya yi dif! Kamar babu masu rai a
wajen, wannan ya ba wa fatima damar bacci
mai
nauyi saboda kasalar jiki. $ can hayaniyar
abdullahi da sadiya ta farkar da ita,Abdullahi
da
sadiya ta farkar da ita,Abdullahi na cewa.
1 · Like · React · Report · May 15, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji
8) "Sadiya dama ana tambayata unguwa ranar
da za a yi ta ne da kike neman ki zage ni dan
na
hanaki fita?" A tsiwace ta ce masa. "To da
wanne
KWANJIN zaka ce sai na yi abin da kake so
alhalin kai ka take dukkan adalcin da ya
kamata
ace ka yi min? Ai babu wani dalilin da zai sa ka
ce sai na bi dokarka" Cikin alamar sikewa ya ce.
" Ai dama ke batunki ba ya wuce nan, kullum ke
an bata miki. A'a ba a yi miki adalci ba, komi
aka
yi miki ba a burge ki alhalin ke kin gaza da taki

biyayyar. Ni na rasa wamnan mugun son mulkin
naki wallahi....." A kule ta katse shi da cewa.
"To
idan an yi min makauniya ce da ba zan gani
ba,ko kana tsammanin gara ce ni irin hindatu
wadda za mayar borar gida ta kasa damuwa? Ka
ga tun da abin ya fara kawo mun irin wannan
bakaken maganar kafin ka kai ga sa hannun ka
dake ni..... Sallame ni, tunda ba kwai na ajiye a
gidan ba, sai ma na ba wa wasu sarari su shigo
idan sun ga zasu iya su zauna su haifi
kashi,idan
ba zasu iya ba su ma su ci taya". Fatima ta gaji
da sauraronm wannan hayaninyar sai ga ta
zaune
tana mutsuke ido,sannan ta dubi sadiya ta ce.
"To ke baiwar Allah akwai wanda ya yiwa
Ubangiji rawa ya ba shi tsatso ne? Na tannatar
kin san inda gadar haihuwa ake da yanzu mun
cika gidan nan da ya'ya.mts! Ina mamakinki
wallahi, ke babu wani mutum mai mutunci a
idonki da ya fi karfin ki dagawa harshe. To
tsoronki za a ji ayi miki abin da kike so? Ai duk
mutumin da yake jin kowa ya tsane shi,to ya
binciki kansa halinsa ne ba shi da kyau". Kawai

sai Abdullahi ya nemi guri ya zauna,ransa na yi
masa dadi. Fadima ta karbe shi fadan ya san
kuma yanzu zai mutu,don tana kulle sadiya da
takaici zata tafi ta ba shi guri. Sadiya ta kara
bala'I kamar zata cinye fatima danya. "Wai ke
ina
ruwanki? Ban yi miki kashedin kar ki kara shiga
sabgata ba? Ni iskar da ta kwaso ki ma idan ina
kaunar shakarta Allah ya tsine min...." Fatima
ta
yi saurin tare ta da rashin nuna damuwa. "Me
yasa za ki ce babu ruwana? Ki saka min miji a
gaba kin faman ci masa fuska ki ce babu ruwana.
To me ye amfanina? Idan ke ba kya so ni ina so,
saboda haka a kansa sai in da karfin ya kare,
ke
nan kina da bukatar canza tunanin,da ruwanan
har da komai nawa". Da sadiya ta rasa abin
cewa,sai ta harde hannu cikin rawar murya ta
ce.
"To daga nan ki sa shi ya sallame ni mana
tunda
da alama kamar ke ce mijin shi ne matar".
Fatima inda zaki, zama zaki yi ki ci gabna da
ganin abin da ba kya so, idan kin yi zuciya sai ki

canja halinki". Zuciyar sadiya ta tafasa ta
juya ga
Abdullahi ta ce. "Abu turab kayi min iyaka da
matar nan ko kuma ka bude baki ka sanr da ni
kai nake aure ko ita? "Allah ya ba ki hakuri".
Kalmar da ya fada mata ke nan cikin yanayin
cin
magani,sai ta yi kwafa ta kada kai ta bar
wajen.
Tana bacewa fatima ta tashi zaune tana hura
hanci,kafin ta yi magana sai ya riga ta, tare da
mika mata lemo. "Ungo sha makogwaronki ya
bude sai ki sauke taki rashin kunyar". Sai ya ba
ta dariya, dole ta koma ta kwanta dan kokarin
ta
hadiye dariyarta,ta ce. "Kai dai kawai ba ka
son
na fadi gaskiya, kuma sai na fada,ka kawo ni
cikin matanka suna koya min hayaniya,babu
gaira
babu dalilin ku dinga sa min ciwon kai. "Allah
yasa ya zame miki kaffara". Ya fada yana
hadiye
dariyarsa,sannan ya kwanta rigingine yana so
kadaita da tunanin hayoyin da zai canja

wadanda
za su kawo masa fatima a saukake. Babu jimawa
kannen hindatu uku suka zo ta jajibe su falonta
tana karrama su dai dai gwargwado,Abdullahi
ma
ya kwaso kafa ya biyo su,aka yi da shi inda ya
fake da murar da ta ke ya sanya su shiga
kicin,shi kuma ya ci gaba da more huldar arziki
da fatima tunda ba zata saka shi kwandon
shara
a gabansu ba. Ya dorar da ranar yau don har
abinci kwano daya ya ci da fatima.wanda rabin
su da hak ahar ya manta.
2 · Like · React · Report · May 15, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji
9)Da azahar ya
kamo hanyar gida,domin ya kai su gidan
suna,ya
ce su tsaya zai kai su ne saboda fatima,wadda
ya ke matukar kishinta da hujjar fuskarta mai
hadari ce ga maza. Har ya zo gida yana tunanin
da yadda za ayi ya raba musu tafiyar tunda ta
ce
ba zata da su ba, sai Allah ya taimake shi ya

sami hindatu da kannenta su Rabi duk za su,
dan
haka.ya fake da cewa motar ta yi musu
kadan,idan ya kai su ya dawo ya kai fatima. Ko
rabin awa bai yi ba ya dawo ya dauke ta. "Wane
sauti zan sa miki?" Da batun da ya kau da
shirunsu ke nan bayan ya tashi motar,sai ta
juya
masa keya, yana dariya a ciki ya ce. "Kar fa in
sa
wanda raina yake so ki kalubalance ni". Yana
rufe
baki ta amsa masa. "Sa min dan'anace" Ya
tuntsure da dariya,sannan ya latsa sautin
wakar
bala anas "masoyiya ke ce tawa' yana cewa. "Ai
kin kawo kuka gidan mutuwa,kin ji inda na fi
kauri". Ta yi banza da shi ta kawar da kai,ya
dinga yi mata dan biki yana bin wakar yana
inkiya
da ita kamar ba tuki yake ba. Sai da suka gota
sahad store da ke zoo road sannan ta juyo ta
dube shi,ta ce. "Mu shiga zan sai kayan baby".
Ba tare da ya dube ta ba ya ce. "Ki ba ta
kudin".

Ta tara gira,ta ce. "Don me?" Ya bude ido ya
amsa. "Dan ba ki yi shirin za ki shiga wani guri
bayan gidan suna ba, in kin shirya shiga store
sai
ki sanyo hijab har da nikab tun da akwai mazan
da zaki dinga cin karo da su. Ta ce,"ga ni ga
ka?"
Ya dage gira,yana mata wani kallo ya ce. "A
matsayina na wa dinki?" Sai ta kawar da kai ta
share,sannan ta nisa ta ce. "Mu koma sai ka
shiga ka siyo min,babu komai...." Abdullahi ya yi
gudun gara ya fada zago, domin shigarsa store
din ke da wuya fatima ta hango direban Alh na
tashin mota zai fita,da sauri ta ya fito shi ya
taho jikinsa na bari kamar manta cewa,yanzu
ba
shugabarsa ba ce. Ya rankwafa sosai ya gaishe
ta,a rikice ta saurin katse gaisuwar,ta ce. "Ya
ya
Alh?" Cikin ladabi ya amsa mata. "Ayya! Alh
jiki
ya ki Hajiya,yau satina biyu a jamani. Ta fara
karanto,'innalillahi wa inna ilaihi raji'un' a
zuciyarta, fuskarta na nuna kololuwar
tausayawa,Abdullahi na shirin kisan kai, abin

da
ta dora a ranta ke nan. Tana tuno Abdullahi sai
gabanta ya fadi, wanne irin zafin kai zai mata
idan ya zo ya tarar da ita da direba? Cikin
yanayin tsoron da damuwa ta ce. "Shi ke nan,
Allah ya ba shi lafiya. Idan kun yi waya ka fada
masa an karbi wayar hannuna ne shi yasa ba ma
samun gaisawa". Ta bude jaka ta debo kudi babu
ko kirga ta ba shi. Ya yi mata godiya ya
bace,yana tunanin wa wannan matar 'yar zafin
kai ta ke shakka haka? Matar da ya sani ba a sa
ta ba a hana ta, mulkin mallaka har ga wanda
ya
ajiye ta. Gaba daya ta sauya,wani mugun jin
haushin abdullahi ya mamaye mata
kirji,tsanarsa
ta ishe ta. Ta dinga jin gara ma mutuwarta da
rayuwar da ta ke a gidansa, kawai sai ta rafka
tagumi cikin hakakin bacin ra. Ya dawo ya miko
mata kayan,ta karba a fusace ta watsa baya.
Sai
kawai ya yi saroro yana kallonta,sannan ya
kada
kai ya zagaya ya shiga motar. Yadda ya ga
yanayinta sai ya sha jinin jikinsa,sai huci kawai

ta ke kamar ana taba ta fashewa zata yi. Bai yi
shawara da kowa ba ya raba kansa da
sauraron'masoyiya ke ce tawa'ya mayar da
karatun alkur'ani cikin suratul kahf da muryar
Abdullahi madarut.ya dinga bi cikin nutsuwa har
suka kai babu wanda ya tankawa wani. Bayan ya
faka motar sannan ya koma nazarinta,ya
tabbatar kashi hamsin na daga kunci da ta ke ya
zabge,ta bar huci ta koma tagumi da zubawa
gilas ido fuskarta,ya ce. "Fadimatu me ya faru
ne? Ko dan na hana ki shiga store? Haba
fadimatu wannan ai karramawa ce gare ki shiga
dan ni kuntata miki ba"m Kwallar da ta cika
mata
ido ta fado,ba ta damu da dauke ta ba ta dube
shi ta ce. "To wai don me ma zaka so ni ne
Abdullahi? Soyayyarka gare ni karan tsaye ce a
farin cikin ban taba shiryawa kaina auren miji
irinka ba saboda haka rike ni da kake a
matsayin
matarka zalunci ne gare ni' Ya yi shiru yana
kallonta cikin damuwa da tarin hasshen abin da
ya zunguro ta haka. Ya kife kai a sitiyari yana
nazarin ta inda zai sha kanta.Rarrashinta zai yi
ko kuna mayar da koken nata wasa zai yi kamar

yadda ya saba? Duk ciki bai ga na zaba ba
saboda shi ma yau kirjinsa ya yi nauyi a kan
lamarin. Kimanin mintuna biyar sannan ya
dago
ya dube ta ya ce. "Fatima so ba ya shawara
kafin
ya sami muhalli, sai dai ba shi ne mafi a'ala a
cikin zamana da ke ba, idan ma ya yi tasiri ba
zai
wuce na son tsarkake ruhinki da gangar jikinki
daga abubuwanki,so ba zai yafe min ba idan na
dauke hannu akan tarbiyyarki,ko kuma na
sallame
ki dan na gaji da dawainiyar neman soyayarki
har
ki sami damar zaman haramun da alh,kin san
wani abu? Ko halali ne aurenki da Alh musulunci
ya ba da damar a raba shi,saboda yadda Alh ya
shagala da soyayarki,ke kuma kike amfani da
wannan damar wajen dama garinki yadda ranki
yake so,ko da ba ya kan turba. Kin san tsoron da
nake jiye miki? Kar ki zama daga marasa
rabo,kyawunki ya zan silar shigarki wuta,kin
dauki
hakkin Alh a zamanki da shi, kun yi rayuwar

saki
uku,kuma kun fatalar da hakkin Allah kuna son
rayuwa cikin saba masa,na aure ki ina ta faman
dawainiya da hakuri da ke,fadima kar ki zama
daga cikin matan da ake saka mazajensu
aljana
saboda hakuri da munanan halayensu. Sin
fadima
an kagi halittar ki ne ba tare da wata manufa
ba?
Ki maida hankalin ki fa? Ita mutuwa ba sallama
ta ke ba bare ki ce kina da garantin lokacin tuba
ki kubutar da kanki,idan Allah a karbi ranki a
haka
ki ba ki da wani uzuri da zaki gabatarwa
ubangijin .......,ki sami lokaci ke da kanki ki yi
tunani,duniyar nan da kike ganinta ba ta kai
fikafikin sauro daraja ba a wajen Allah,inji
manzon Allah(S A W). Idan kyawunki ke rudinki
ki
farga fatima,ko kina raye shekaru kalilan kike
jira
ya gushe a sa'in da ido zai mutu kwalli ya kasa
tono shi,kuma akwai hadisin manzo Allah(S A
W )

da ya ce,'ka mori kuruciyarka kafin tsufanka'.
Akwai alamar maganganunsa sun shiga
kwanyarta da muhimmanci.hawayen ya tsaya
duk
ta yi wani wuri wuri da ita,ya jima yana kallonta
sannan ya kara tausasa murya,ya ce. "Fatima ki
taimakawa numfashinmu,mu zauna lafiya.... Ni
an
jarrabe ni da kaunarki..... Ba zan iya sakinki ba
fatima.... Kuma ba zan daina kaunarki....." Ya
kife
kai a sitiyari saboda hawayen da ya hana shi
magana,kawai sai ta sami kanta da binsa da
kallo,abin mamaki sai ta ji kukansa na taba
ranta,ita ma sai kwalla ta cika mata ido da
dinga
goge su suna kara dannowa tare da haifar mata
da makaki a zuci, abin ya yi mata yawa,ga
damuwar Alh ga ta Abdu
1 · Like · React · Report · May 15, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji
.10) Haka ta dinga nade kwallarta tana dokin
wannan lokacin ya wuce musamman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login