Showing 1 words to 3000 words out of 155973 words
Chapter 1 - Kyawuna Jarabtata Hausa Novels by Maman Shakur.pdf
KYAWUNA JARABTA TA
✍️M SHAKUR
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAIJINKAI.
LITTAFIN NAN NAKUDI NE BUT FOR NOW INA FREE PAGE SO U ALL CAN SHARE.
subscription is 500 idan kinaso kibiya nasaki a group zaki turo 500 into 3107021073 aisha
Muhammad first bank saiki turomin evidence of payment ta watsapp number na 07012181461
sainai adding naki a group din danake posting.
S-SQAURE FASHION AND MORE GIDANE NA HIJABAI DA HADADDUN DOGAYEN RIGUNA
NA DINKAWA, KUNSAN MA MENENE TANA WANI PROMO NA FREE DELIVERY KOWANI
GARI KIKE IDAN KIKASAI KAYANSU ZATA AIKOMIKI DA KAYAN KYAUTA, DON MAGANA DA
ITA KO CHATTING NATA UP DAN SAYAN KAYAYYAKIN SU CLICK ON THIS LINK
wa.me/+2347030037697
Free page
EPISODE 1️⃣
Tudun Yola, Kano!
Baban Anguwace kuma sabuwa dan babu mutane haka sosai a anguwan, saidai irinsu
uncompleted building da ake kan ginawa dakuma sababbin gidaje da ba'a dade da tarewa
cikiba.
Baban gidane dayasha fenti milk color, kana ganin ginin gidan kaga ginin irin family house
dinan, tsakar gidan mai bala'in fadi, ga katuwar bishiyan mangwaro a tsakar gidan datai y'ay'a
sosai dudda basu nunaba, flat biyune agidan wani babban dankareren flat saikuma wani
karamin flat mai kamada boys quarters agefenshi, gidan kana ganinshi kasan bawani gidan mai
bala'in kudi bane gidan rufin asiri ne dai namai karfi daidai, motoci biyune parke atsakar gidan
wata bus mai kyan gaske milk color saikuma mota sienna ash da mai gadi ke wankewa ga
dukkan alamu motar maigida ne sabida yanda ya kuke yana wanketa yanabin wakan sangaya
dake tashi a karamin radio daya ijiye kan plastic chair.
Bude kofar karamin flat din dake kusada babban flat din akayi, wani Matashi ne baki dogo baida
jiki sosai yana sanye da jallabiya brown hannunshi rikeda makullin mota yafito, takalmi yasaka
sanan yasauko daga matattakalan bakin kofarsu yadumfaro babban flat din, da sallama yabude
kofa ya shiga ciki. Babban falo dakeda girman gaske, wani Babban Magidanci ne zaune akan kujera akalla zaiyi
60years kokuma 59, kana ganinshi kaga mai gidan, bakine yanada jiki, hannunshi rikeda jarida
dayake budewa yana karantawa.
gefenshi kuma wata Mata ce mai kiba Hajiya Balaraba akalla zatai 40yrs tasaka wani hadadden
lace tana kurban shayi a cup, saiga yara dasuke zazzaune akasan carpet suna breakfast
kowanne nashan tea da bread da soyayyan egg dinshi, Mata uku ne a tsakar falon da maza
biyu wanda duk kasansu daya, Amal that is 14, sai Asiya 13yrs, sai Aneela dakenan 11, Mazan
kuma Muhammad dakenan 11 sai Mudasir wanda shine autan gidan 6yrs, gabaki dayan yaran
kana ganinsu kaga mahaifinsu tundaga bakin fatar da jikin dan dukansu tuluka tuluka dasu very
fat gwanin ban sha'awa kana ganinsu kasan sunacin lafiyayyen abinci, dukansu suna sanyeda
uniform din makaranta da alamu hadda zasu danyau sunday.
Kitchen aka bude, wata black beauty Matace dan itama ba yarinya bace akalla zatai 38yrs tafito
tana sanyeda doguwan rigan atampa mai kyau da akama stonework tana rikeda tray dawasu
hadaddun kwanuka ke kai, hada ido tayi da wanda ya shigo dakin dukbasu luradashi ba yasa
tace "this children zasusa kayi latti for your program Ya Hamad" kiran sunan shi datayi yasa
duka yaran dakowama na falo yadagokai ya kallai, atare duka yaran suka gaidashi "Ya Hamad
good morning" batare daya amsasu ba yakarasa shiga falon har gaban Abba yakarasa sanan
yazauna agefenshi yace "ina kwana Abba" sanan yakalli matar dake gefenshi yace "Ina kwana
Mum" daidai lokacin dayan matar taja coffee table zuwa gaban mijin nasu ta dauramai tray akai
tace "your food is ready Daddy Hamad" jaridan ya linke tareda mikamata, karba tayi dayan
matan tadauke kai Abba kuma yatura hannu a aljihun sanan yaciro wasu kudi yamikama
Hamad yace "inka kaisu kabiya musu kudin makaranta" sanan yajuya yakalli matar dake
gefenshi yace "me yaran nan sukeyi asama har yanzu basusan zasu makaranta bane"? dasauri
tace "kumafa su tuntuni sukai break, Nanaa, Hawwa" daga chan sama aka amsa, wasu yan
mata manya masu jiki guda biyune suka sauko daga stairs, yaran zaka dauka yan biyu ne dan
suna kama, irin kama na jini dinnan, Nana itace Babba 26yrs take tana final year a BUK tana
karanta Mass Com, sai Hawwa 24yrs tana 300level tana karanta international relation itama a
Ado Bayero, Hawwa na kama da Hamad sosai, dukansu suna sanyeda lemon green hijabi na
haddan, dukansu ransu abace yake dan sun tsani zuwa hadda suna uni amman suna wani
zuwa hadda shikuma Babansu yanuna babu wacce ta isa tabar hadda cikinsu kodako PHD
sukeyi, tashi duka yaran sukayi sukama iyayensu bye suka fice, sanan Ya Hamad din yatashi
yace "bari nakaisu Abba" gyadamai kai kawai yayi dan haka Babansu yake baifiye son magana
ba, sanan yawuce yafice.
Kaman ance tadaga kanta sama taga gittawan mutum dasauri an bude kofa anshige daki
batare da an bari sun hada ido da Mami ba. Ahankali Mami tasauke ijiyan zuciya dudda bataga
fuskanba but ko amafarki aka tadata tasan waye.
Duk suna zaune afalon harya gamacin dumamen tuwon yadauki ruwa yasha, Dan gyaran
murya matan dake zaune kusada shi tayi Mum tace "Alhaji nace bari namaka tuni, kaga duka
duka bikin Nana bayan Babban salla da sati uku ne, gashi lokaci nata matsowa yanzu baifi wata
daya bikin ba, nasan dama kariga kabada kudin kayan daki, cha kayi daman wanan satin
zakaban kudin kayan kitchen, kaga idan kabani nida Zainab saimu shiga kasuwa yau muyo
siyayyan koya kika gani Zainab"? Mum tama Mami dake zaune tana sauraransu magana,
gyadamata kai tayi sanan tace "eh hakane Abban Hamad" ruwa yadauka a cup yakara kaiwa
baki yasha sanan ya ijiye cup din, hannu yasa a aljihu yaciro bandir din yan dubu daya guda
biyu yabata yace "kinemi wata kijeda ita kasuwa, Zainab bazata iya zuwa ba itakeda girki,
kuma yau lahadi ina gida" yana fadin haka yatashi yawuce sama duk suka bishi da kallo, saida
taga yashiga dakinshi sanan tabata rai tace "Alhaji Alhaji bantaba ganin kafaffen mutum irin
shiba wlh" tashi tayi batare data kalli Mami ba tai stairs tabude bangaren ta tashige dan saman
bangare biyune nata dana Zainab saikuma dakunan yaransu guda uku, na maza kanana dana
mata kanana saikuma na yan matan suma dakinsu daban.
Ahankali Mami ta tashi ta tattare duka kwanukan takai kitchen sanan tasa Mai aikinsu Uwani
tazo tashare falon ta kunna turare sanan tai sama itama bude dakin mijin nata tayi tashiga bata
wani dade aciki ba sanan tafito, direct dakin yan matan tayi ahankali tabude kofar, dakin nada
dan fadi gashi a gyare Kal Kal, gadaje ne guda uku irin nayan boarding jere adakin kowanne da
bangaren nashi saiga wardrobe na bango da kayan kowa keciki, bin kan gadajen tayi da kallo
ganin babu kowa kai yasa takarasa shigowa dakin tareda maida kofan tarufo sanan tashigo ciki
takaraso tsakiyan dakin saikuma ta tsaya turus tai shiru tana kallon gaban gadon dake tsakiyan
dakin, wata faran budurwan yarinyace azaune akasa tabama dakin baya tana kallon bango
tadaura kanta kan kafafuwanta ta, nimai rubutu M Shakur banmasan mutum bane awurin ba
saida naga Mami ta tsaya turus tana kallon wajen, wani irin silk black gashin kaman na yar India
ne zube awajen yana taba tiles din kasan daki sabida yanayin zaman datayi tsabagen tsayin
gashin, sai farin kafanta sol mai bala'in kyau da dogayen fararen farcenta dababu komi akai sai
uban haske kaman ana wankesu da madara. "Du'a" jin ankira sunanta yasa tadago kanta daga
kifen dasuke akan kafafunta dasauri batare data waigoba jin muryan Mamin ta, dan Jim Mami
tayi tana binta da kallo sanan asanyaye tace "inkin gama kukan ki tashi ki tattare gashin nan
naki ki kulle kisa a hijabi kije Abban ki nakiranki yana dakin shi" tana maganan tawuce tafice
daga dakin tarufo musu kofan.
Ahankali takai fararen hannuwanta tashare fuskanta sanan tamike tsaye ahankali, wani iri
mahaukacin cokacola shape Allah yamata gawani irin pointed curvy ass gareta daya fito sosai
cikin doguwan rigan material din dake jikinta, itama kaman sauran yaran gidan tanada dan jiki
danbazaka taba kiranta da mara kiba ba amman batakai su Nana kibaba, saidai tafisu diri, ga
gashin kanta dabaida banbanci dana yan India har waist dinta, juyowa tayi ahankali TSARKI YA
TABBATA GA ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA WANDA YA HALLICI SAMAI DA KASSAI
DAKUMA HALITTUN DAKE CIKINTA!!!! yarinyar nan koda ace itace tayi kanta banjin zatai
kanta tai kyan datake dashi yanzu hakaba dan My Lord!!! dan itace definition of tacika goma cip
cip tamakai sha uku, farace Kal fuskanta babu pimple ko daya idanunta sun kumbura sunyi ja
sabida kukan datayi wanda haryau takasa sabawa dan by now yakamata ace tasaba duk sanda
yan uwan ta zasu makaranta boko ko islamiyya saitai kuka, tanada wani irin long pointed hanci
ga pink lips, gashin idanunta dogaye kuma acike sun jikeda ruwa, ga kirjinta awani irin cike
kaman wacce taje tai surgery ga flat tummy kaman bata tabacin abinci ba, Allah yamata ass
amman waist dinta kona jariri albarka her waist is so tiny, ahankali take tafiya har zuwa gaban
madubin dakinsu ribbon dinta dake wajen tadauka sanan ta kulle kanta da kyar sanan tashiga
bayinsu wanko fuskanta tayi tafito tadauki dogon hijabin ta maroon tasaka tafito daga dakin
ahankali.
Cikin wata irin siririyan cool melodious voice tai sallama gaban dakin Abban su, daga ciki taji
yace "shigo" ahankali tabude kofa tashiga kanta akasa, yana zaune kan couch din dake dakin
yabita da kallo tazo gabanshi tazauna tareda saukar da kanta kasa ahankali tace "Abba gani"
zama ya gyara tareda bude Al Qur'ani dake kan cinyanshi sanan yace "biyomin haddanki" gyara
zama tayi sanan tafara rairomai suratul Yusuf shafa'i ukun dayabiya mata last week, shi karan
kanshi idan tana biyamai hadda baiso tadena dan muryanta Allah yay mata dadi saida tagama
tsaf sanan yakara mata wasu shafa'i ukun kafin yamata tajweed sanan yace "tashi kitafi" tashi
tayi ahankali tai hanyar kofa yasake binta da kallo harta daura hannunta kan handle din kofa taji
yakirata anatse. "Du'a" dasauri tajuyoda kanta ta kalleshi saikuma tasauke idanunta kasa tace
"na'am Abba" ahankali yace "nariga nasaman miki wata sabuwar malama, daga gobe zata fara
zuwa In sha Allah, ki shirya" gyadamai kai tayi sanan tajuya zata bude kofan saikuma tajuyo
ahankali batare data budeba ta kalleshi hada ido sukayi hakan yasa takasa magana tajuya zata
bude kofan tafice cikin muryan nan nashi nabawasa yace "mekikeso ki fada"? Dan juyowa tayi
ta kalleshi saikuma tasauke kanta kasa kirjinta na bugawa fat fat tashiga wasa da yatsunta
tsabagen how nervous she was tama kasa magana, dan idan Abban su yakureka da ido
zamaka iya fitsari ajiki baka saniba, shifa kokadan baida wasa kuma yanada zafi sosai, gashi
kaifi daya saisa duka yaranshi ke tsoron shi. Ganin takasa magana yasa yace "I'm listening"
rawa sosai muryanta yafara tanama bude baki maganan yakasa fitowa saikuma tasaki
hannunta ta shiga chakuda hijabinta da hannu duk yana binta da kallo hijabin tarike gamgam
sanan da kyar tasamu maganan yafito ahankali tace "Ab.....ba ni......maisa ake barina agida
kahanani fita kowaje, Abba ni nafison naje school kaman su Ya Nana......" saikuma tasake
hadiye wani irin dry miyau hawaye yawani zubo daga idanunta suka sauka akan hijabinta cikin
wata irin murya na wacce ke gabda fashewa da kuka kuma take a bala'in tsorace tace "Ab....ba
ni maisa baka sona kaman yanda kake son su Ya Nana da Hawwa da....d....." Du'a!! taji anwani
irin kirata da kakkausar murya dayasa tadaga kanta da sauri ta kalli inda taji muryan, Mami ce
tafito daga bedroom din Abba da alamu tuntuni take ciki maybe gyaramai dakin take dan taga
karamin rag na goge goge a hannunta, cikin wani irin tsananin bacin rai tace "Du'a are you
questioning your father? eh? mahaifin ki kika tasa agaba kina tuhuma haka?" girgixa mata kai
tayi dasauri saikuma tasaki kuka dasauri tajuya tabude kofa tafita daga dakin dagudunta.
KYAWUNA JARABTA TA
✍️M SHAKUR
UMMI COLLECTION is a whole world of turaruka, both na wuta dana feshi, exquisite burners na
electric dana charcoal, and oils, turarukan wanka da sauran su. kunkosan kwanan nan UMMI
COLLECTION na promo free delivery, hehehe banso kuyi missing this mad offer just click on
this link danyin magana da ita directly. wa.me/+2348186968736
free page
EPISODE 2️⃣
Azuciye Mami ta jefar da rag din dake hannunta tace "nikema yarinyar nan magana tafice
tabarni sabida batada kunya Dadyn Hamad" tataho cikeda bacin rai zatai wajen kofa tabita
Abba dake kallonta tunda tafara masifan yace "ina zaki"? Turus ta tsaya tana kallonshi takasa
koda motsi, anatse yanuna mata bedroom dinshi yace "koma kicigaba da abinda kikeyi" dasauri
tace "but......" "no buts ki koma kicigaba da abinda kikeyi nace" yay maganan babu alamun
wasa akan fuskanshi hakan yasa bata karacewa komiba tawuce takoma ciki ranta abace,
jaridanshi yabude ahankali yacigaba da karantawa bazaka gane takamaimen wani yanayi yake
cikiba dan fuskanshi bata nunawa.
Dakinsu tabude dagudu tashiga tafada kan gado tana kuka sosai, tayi kuka nakusan awa daya
sanan bacci yay awon gabada ita akan gadon.
Hayaniya yatadata daga baccin datakeyi, bude idanunta tayi ahankali saikuma ta yunkura ta
tashi zaune tana kallon dakin nasu, Nana da Hawwa ne kecire kayan jikinsu sundawo daga
hadda duk sunyi zufa, ahankali tace “Ya Nana kundawo daga makaranta” danjuyowa Nana tayi
takalleta tana kokarin daukan zanin dazata daura tashiga wanka tace “eh yanzu muka
shigo”"sannu da zuwa" tafadi ahankali sanan tajuyo da kanta Hawwa ta kalla taga Hawwa
tadauke kai dasauri tana batarai, daidai lokacin aka bude kofan dakinsu, Aneela ce tashigo
wacce take kanwarta, dan Du’a ce yar Mami tafarko, sai Aneela, sai Muhammad da Mudasir su
Hudu Mami ta haifa, itakuma Mum itace mahaifiyar su Hammad, Nana, Hawwa, Amal, da Asiya
yaranta biyar.
Ko kadan Aneel bata kama da Du’a inba ma angayamaka ba bazaka zaci uwarsu dayaba dan
tafi kamadasu Nana black beauty ce itama, kyakkyawan yarinya bakutu da ita, zama tayi kan
gadon takalli yayartata tace “yauma saida kika kara kuka sabida muntafi makaranta banda
keko” Hawwa data zauna kan gadonta tana ciro wayanta daga jaka tana kunnawa tace “asheko
xakita kuka har karshen rayuwanki dan Abba yace konan da gate bazaki taba fitaba” turo baki
Aneela tayi cikeda rashin kunya ta kalli yayartata saikuma takai hannunta tadaura kan
kumatunta tace “karki kara kuka kinji Duudo, kinga ko yau Malam yafassara mana wata aya
yace duk wanda yadogara ga Allah to hakika Allah ya isar masa, ki dogara ga Allah and I
promise you Allah will be there for you, kiyita addu’a zakiga Abba zai chanza zaice kema kifara
zuwa school kaman mu kinji” gyadama kanwar tata kai tayi ahankali, Aneela tawani washe baki
tai murmushi hakan yasa itama tai murmushi, Subhanallah idan tai murmushi numfashinka zai
iya tsayawa sabida kyan datake karayi.
“In dauko mana abinci muci tare?” Aneela ta tambaye ta, Gyadamata kai tayi hakan yasa
tasauka daga gadon tawuce tafita, itakuma ta sauka daga gadon ahankali sanan tawuce
bathroom dinsu dan dauro alwala Hawwa tabita da harara wanda inda sabo tasaba tun suna
yara basa shiri sabida sako da sako nesu dan daga Hawwa sai ita aka haifa agidan, itakuma
Nana babu ruwanta bata shiga harkanta as per babban yaya in the house.
Fitowa tayi ta shimfida dadduma tadau hijabi tasaka ta kabbarta salla daidai lokacin Aneela
tashigo ajiye musu rice da stew din tayi akan gado itama tazauna tana jiranta ta idar, itakuma
Hawwa ta tashi tafita duk ranta abace yake sabida yanda tadawo Mum dinsu batanan.
Saida ta idar da sallan sanan tazauna sukaci abincin tareda Aneela batare dasunyi surutu ba
sabida Nana dake waya da wanda zata aura, sosai taci abincin suka gama tass Aneela tafita da
plate din takai kitchen sanan tasake dawowa dakin.
Wuraren 4 Mum tadawo daga kasuwa da mota guda na kayan kitchen yaran sai murnan ganinta
suke barinma yaranta dakin da ake tarin kayanta akakai komi bayan Abba yagani sanan daga
ita har Mami suka shiga kitchen sukahau girke girke sabida bakin da Abba zaiyi yan wajen
aikinshi da iyalansu, yaranma duk aka kirasu kitchen banda Du'a dakenan ita kadai adaki.
Tana zaune adakinsu har magrib ita kadai, dan tun dazu aka kira Aneela da Nana da Hawwa
duka batasan me akayiba but tadaiji kamshin girke girke kuma yawanci tasan ana irin girkunan
nan ne idan zasuyi baki, tashi tayi ahankali ta shiga bayi wanka tayo tareda dauro alwala tafito
daidai lokacin da Nana da Hawwa sun shigo dakin duksunyi zufa, dasauri tace “Ya Nana
mekukeyi?” “Girki” tabata amsa atakaice tawuce tashiga bayi dan wanka itakuma Hawwa
tazauna akan gado tana daukan wayanta tana dubawa ko ankirata, gaban wardrobe dinsu taje
tabude bangaren kayanta, wani doguwan rigan atampa black taciro tawarware sanan tasaka
dayamata kyau sosai sanan tadauki hijabi tajuyo hada ido tayida Hawwa dake kallonta suna
hada ido tadauke kai tacigaba da danne dannen wayanta, saka hijabin tayi tahaukan dadduma
tafara salla daidai lokacin Nana tafito daga bayin ta kalli Hawwa tace “tashi kije kiyi wanka
Hawwa kinga Abba yace mu shirya dawuri suna hanya fa” tashi Hawwan tayi tashiga bayi
itakuma Nana tashiga shiryawa cikin wata atampa.
Idar da sallan tayi ta tashi tazauna akan gadonta tareda cire hijabin ta ijiye agefenta tana kallon
yanda duk suke shiryawa agurguje, suna makeup abin na bata sha'awa dan ita mai kadai na
shafawa gareta sai body spray, batada sauran kayan kwalliyan dasuke dashi kuma bata isa ta
taba abinsu ba barinma masifaffiyan Hawwa nan. Daga Hawwan har Nana saka atampopi
sukayi iri daya suka shirya tsaf gwanin ban sha'awa sanan kowacce ta zauna kan gado tana
danna waya, sosai take kallon wayan dasuke dannawa, duk idan taga suna tabawa saita bata
shaawa