*_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ BOOK 2 🅿️➖1️⃣ ______________ *_Assalamualaikum. Barkanku da wannan lokaci, fatan ansha ruwa lafiya? Anyi salla lafiya?. UBANGIJI ya karɓi ibadunmu, ya yafe mana kurakuranmu, yasa muna a cikin ƴantattun bayi. Ina mana Barka da dawowa filin daga, ya rabbi ka bani ikon rubuta abinda bazai cutar dani da ku ba. Ka tsarkake min alƙalamina domin rahamarka. Ka gafarta ma iyayenmu da malamamu damu baki ɗaya. Ka ɗauramu a bisa tafarki madaidaici da bazamuyi dana sani ba. ALLAH ka hanamu cutar da junanmu koda da kalma mara daɗi ce.🙏_* _Ayi mana afuwa da jinkirinmu yau da gobe sai ALLAH 🥰🥰❤️._ *Ƴan ƙungiyar Bati ku matso nan munada meeting 😂. Kun san dai AZUMI aka gama ko, goman ƙarshen nan hummmm 😂 karki yarda ki zama a cikin wanda na ɗaga hannu nace ya ALLAH gasu nan....* _Bazan dai ƙarasa ba amma gaskiya kada ki yarda sister dan in dai an amsa akwai cakwakiya gaskiya 😂😂😂😂🏃_ 500 kacal ne 😘 _____________ ........Sosai ciwon kai yay ma Maanal rijib a wannan yinin isowarsu Abuja, shima kuma AA ɗin zuwa yamma dole aka saka masa drip ma, dan sam baya jin wani ƙarfin jikinsa. Har cikin dare ba'a gama saka masa ruwan ba dan kusan leda uku ne. Dole Fawzan ya kwana tare da shi bisa umarnin Abah. Oum taso yin magana amma tai shiru, dan ita so tai ta kawo Maanal a daren sashen AA ɗin, amma ta fahimci take-taken Abah so yake ya kawo wani sharaɗin hora AA ɗin, dan dama shine ya bata umarnin wucewa da Maanal sashenta sanda suka iso. Bayan sun baro sashen AA bin bayan Abah tai nasa sashen ta masa magana, amma sai ya nuna mata shi barci yake ji ta barsa dan ALLAH. Haushi ne sosai ya kamata, dan haka fuuu ta baro sashen. Da kallo ya bita ganin yanda ta wuce, sai kuma ya shiga girgiza kansa a fili ya furta, “Fateema son yaranki yayi miki yawa, in dai fushi ne ƙyama sakko dan sai na hora Ajwaad a gidan nan”. Daga haka ya shige toilet yana murmushi... ___________★ Zuciyar Babban Yaya cike da wasi-wasi ya nufi sashen Oum ganin har goma saura na dare yau ma Maanal bata koma sashenta ba, ga AA ɗin kuma ma jikin nasa ya dawo dan yanzu haka wani ƙarin ruwa aka cire masa. Ganin bata a falo ya nufi bedroom ɗinta. Sai da yay sallama ta amsa tare da bashi izinin shiga sannan ya shigan. Yanayin yanda take a zaune da fiskarta dake cike da damuwa yasa gabansa faɗuwa, duk da yasan akwai damuwar yanayin da Auta ke ciki dai. “Oum baƙya jin daɗi ne?”. Ya faɗa cike da damuwa matuƙa yana kaiwa kusa da ita zaune. Idanu ta zuba masa kawai, dan duk yanda taso yin murmushi ko sassauta damuwar tata hakan ya gagara sam. Sai ma ƙwalla kaɗan da suka taru mata a idon. Ai sai babban Yaya ya sake rikicewa matuƙa. Hannunsa ta riƙo tana girgiza masa kai, “Kaga kwantar da hankalinka bafa wani abu bane ba.” “Haba Oum yazan yarda da hakan, kalla fa yanda damuwa ta bayyana a fuskarki sosai. Dan ALLAH in ma dan ciwon Auta ne ki daina tada hankalinki komai zai wuce kamar ba'ayi ba in sha ALLAHU. Dan yanzu hakama barci yake yi na cire masa drip ɗin dan ya ƙare. Jikinsa sam kuma babu zafi da ganin yanda yake barci ma kasan Alhamdullah babu wani damuwa ba kamar jiya da yinin yau ba. Yanzu haka ma nazo ne akan batun Maanal, nazata zata kwana a can ne yau ai tunda jikin da sauƙin itama?”. Sosai ɓacin ran Oum ya ƙara bayyana akan fuskarta, ta ce, “Akan hakanne ai Abanku ya ɓata min rai Fadeel, yace wai bazata koma can ba yanzu sai bayan salla ya koyama Ajwaad hankali. Wane hankali kuma ake buƙatar koyama yaron nan bayan wanda ya koya. Kama ajiye batun wahalar ciwo da yasha a shekarun baya, a kwanakin nan kawai kaga hanlin daya shiga fa da wanda yake a ciki yanzu. Kowa fa a rayuwa da irin yanayinsa da kuma ƙaddararsa, amma Abanku ya kasa fahimtar hakan, ya kasa fahimtar Ajwaad nada zurfin ciki ne. Yanda Maanal keda muhimmanci a garesa bana tunanin dole sai ya buɗe baki yace wani abu za'a yarda dashi. Shin so yake na rasa yarona ne saboda wannan tsaurin nasa?”. Ta ƙare maganar muryarta na rawa kamar zata saki kuka. Cikin sake rikicewa sosai Babban Yaya ya shiga girgiza mata kai nasa idanun na kaɗawa sosai shima. “Dan ALLAH Oum ki kwantar da hankalinki, ni bara naje na samesa yanzu. Ko kuma ki kira Baba ko Abba ki haɗashi da su.....” “Saboda ban isa da gidana ba kenan ko mai uwa?”. Atare babban Yaya da Oum suka juya da sauri suna kallonsa, ƙarasa shigowa cikin ɗakin Abah yayi, cikin nuna ɓacin rai sosai ya cigaba da faɗin, “Saboda biyan buƙatar taka uwar ni a kira nawa iyayen a haɗani da su. Lallai Fadeel sannu, nace sannu kaji ko!”. “Kayi haƙuri Abah ni ba haka nake nufi ba, amma Oum fa......” “Malam tashi ka wuce sai da safe.” Abah ya sake katseshi cikin sake nuna ɓacin rai. Kallon Oum Babban yaya yayi idanunsa na sake kaɗewa, kanta ta jinjina masa alamar yaje ɗin. Dan haka ya miƙe kawai ya nufi ƙofa. Da kallo Abah ya bisa, sai kuma ya girgiza kai a zuciyarsa yana ayyana (su dai akan uwarsu kowa ma ya mutu har liman babu ruwansu). A fili kam dubansa ya maida kan Oum data ɗauke kanta gefe tamkar ma bata san da shi ba a ɗakin. Sai kuma ta yunƙura zata miƙe. Yasan mi zatayi, dan haka cike da bada umarni ya ce, “Koma ki zauna”. Komawar tayi ta zauna, kafin ta ɗago idanunta da suka sake kaɗewa a karo na farko ta kallesa, aiko ya sake yin kicin-kicin da fuska harda ɗan willa mata hararar data sakata janye idanun nata a kansa sannan ya furta, “Oh ke yanzu saboda na yanke hukuncin daya dace akan ɗanki shine kika ɗauki fushi da ni kin kira babban ɗanki kina sanar masa kuyi min taron dangi saboda ban isa nace ga yanda za'ai ba”. Idanu Oum ta ɗan rumtse kaɗan, sai kuma ta buɗe a kansa. Baki ta buɗe kamar zatai magana sai kuma ta fasa saboda ƙwallar da suka cika mata idanu. Ɗauke nasa yay dan yasan yanzu sai ta karya masa zuciya, shi kuma a wannan karon ya ɗauka aniyar tauna tsakuwa dan aya taji tsoro, dolene ya hukunta Ajwaad kodan ya sake sanin muhimmancin Maanal. Bazai yiwu ya samu aurenta a ɓagas ba su kuma bashi ita a ɓagas. Ƙoƙarin barin ɗakin yayi, sai Oum kawai ta saki hawayen da take riƙewa cikin muryar kuka ta ce, “So kuke sai kun kashe min shi hankalinku zai kwanta ko Gadanga, yanzu horon da ƙaninka yay masa kawai bai wadatar a yafe masa ba”. Murmushi Abah daya tsaya cak tun fara maganarta ya saki a hankali, sai kuma ya maida fuskarsa ya haɗe kafin ya juyo yana kallonta daga inda yake tsayen. “Rafeeq bai hora ɗanki ba, takarar nema sukai yay muku adalci ya sadaukar saboda ƙyaƙyƙyawar zuciyarsa, da kuma nasan zai yi hakan sai na hana masa”. Ya ƙare maganar yana mai juyawa ya fice abinsa. Wani irin ƙululun abu ne ya sake tokare wuyan Oum, har zuciyarta na tunzurata akan takai Maanal sashen Ajwaad koma miza'ayi ayin mana....... ___________★ Alamun shigowarsa ya sata dakatawa daga kai-kawon da takeyi, zama tai kamar ba ita ba ta nutsu a bakin gadonsa tare da ɗaukar littafin addu'oin sa dake a bed side drawer ta fara karantawa. Da farko Abah daya shigo ransa a ɓace sam bai ganta ba. Sai da ta ɗago ta kallesa cikin tausasa harshe matuƙa ta furta, “Sannu da shigowa”. Sannan ya kalleta. Ciki-ciki ya amsa mata, dan haka ta taso da ƴar sassarfa tana faɗin, “Lafiya kuwa? Naga kamar ranka a ɓace?”. Tsaki yaja mai ƙarfi, sai kuma ya wullar da wayarsa a saman gadon nasa shima yana kaiwa zaune hannunsa akan goshinsa yana murzawa. “Fateema ce ke neman ɓatan rai Kamila”. Ɓoyayyan murmushi Mamy ta saki, a zahiri kam cike da damuwa ta ce, “A haba kodai baka fahimta bane, amma nasan bazata ɓata maka rai da son ranta ba yallanɓai.” “Mtsoww!! Bazaki gane ba Kamila, ita dai sam bata gajiya da rikici akan ƴaƴanta, dokar dana kafa jiya akan komawar Maanal sashen Ajwaad shine taketa faman fushi, yanzu naje mata sai da safe na samu ta tasa babban ɗanta gaba tana faɗa masa, shiko yana bada shawarar a haɗani da iyayena.” Sosai Mamy takai zaune yanzu kam, hannunsa ta kamo cikin nata cike da kulawa. “Kayi haƙuri, zan sameta muyi nagana ta yanda zata fahimta. Dan tabbas Ajwaad ya cancanci a fara horashi kafin a bashi yarinyar nan kodan halaccin iyayenta da basu duba abinda ya faru a baya ba suka sake bashi batare da ko tada magana ba. Taurin kan yaron nan ne yayi yawa, ya kamata ya fahimci ba komai akema taurin kai ba a rayuwa....” “Abinda nake son ta fahimta kenan ai nima Kamila. Amma tamaƙi ta nutsu ta saurareni, ni kuma so nake mu rabashi da halin kodan bambancin dake a tsakanin jiyansa da yau ɗinsa”. “Karka damu zata fahimta in sha ALLAHU. Ka bata lokaci ta huce yanzu sai mu haɗu muyi magana. Idan ma ta kama Maanal ɗin ta dawo sashena da zama to, dan in ba hakaba bazai damu ba” Ɗan jim Abah yayi, sai kuma ya jinjina kansa cike da gamsuwa ya ce, “Kumafa kinzo da shawara Kamila, dan in har Maanal na a sashen Fateema ba'a rabu da bukar bane an haifi habu za'ai. Dan ɗan nata dai can zai koma ya tare abinsa, kinga kuwa bazai damu ba.” “Tabbas hakan ce zata kasance”. Cewar Mamy wani farin ciki na ratsa mata zuciya na nasara. Abah kuwa da bai san dawan garin ba ya sake furta, “To ai zanyi maganin abun, bari dai ya samu lafiya”. “ALLAH ya bada iko, ina goyon bayanka kuma ɗari bisa ɗari a wannan gaɓar. Dan in aka biye ta Mamansu haka za'a mika masa ita kaga ya samu damar cigaba da mana abinda yaso tunda ta shagwaɓa shi daga ita har ƴan uwan nasa. Sun nuna masa komai ya nema sai ya samu komai girman sa”. Sosai kalaman Mamy ke shigar Abah, yana kuma jin gamsuwa da su da tasirinsu ƙwarai da gaske a zuciyarsa fiye da yanda take ma fatan ya fahimta ɗin.........✍️ *(Mamy😏. Mamy☹️. Mamy😮‍💨. Matar nan ko🤔. Hummmm😥.)* _Amin afuwa dan wlhy mura nake mai zafi, idan na samu sauƙi za'afi ganin page ɗin da tsaho..._ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖2️⃣ ______________ ........A safiyar washe gari har kusan sha biyu Abah baiga idon Oum ba a gidan. Dan haka ya fahimci fushin nata fa na gaske ne. Shi dariya ma ta bashi, dan haka shima ya shareta. Har yamma dai bai ganta ɗin ba, ya dai daure har akai sallar magrib da isha'i sannan ya nufi sashenta. Ko'ina tsaff yake da ƙamshi, sai masu aikinta daya samu a falon ƙasa suna hira. Suka gaisheshi da girmamawa ya amsa musu da kulawa ya wuce. Oum na zaune a doguwar kujera Maanal kwance ta ɗora kanta a cinyarta su duka idanunsu a tv. Sallamar Abahn ta saka Maanal ta shi zaune, kanta a ƙasa tai masa sannu da gaida shi. Shima fuska ɗauke da murmushi ya amsa mata tare da tambayarta ciwon kanta. A tausashe ta ce, “Ya daina Abah Alhamdullah”. “Masha ALLAH ai haka ake so ɗiyar Abanta ƴar albarka.” Murmushi Maanal tayi mai faɗi, sai kuma ta miƙe tsam, dining area ta nufa ta ɗakko ruwa a freight tazo ta ajiye gabansa, cike da dabara ta shige bedroom ɗin Oum. Shi ko Abah cike da mamaki sosai ya ke kallon Oum ganin tunda ya shigo falon bata ko ɗaga ido ta kallesa ba. Sai ma wani sake ciccin magani take. Ji yay kamar ya juya ya fita ya bar mata sashen. Har yay kamar zai juyan sai kuma ya dakata, ruwan da Maanal ta ajiye masa ya ɗauka ya sha kafin ya dubeta da ƙyau. A ɗan kausashe yace, “Har yanzu fushin ne kenan? Dan na hana ki bama ɗanki matarsa shine nima kika ɓiye min ganinki yini guda Fateema? Ni kenan ban isa sharɗanta doka a fahimceni ba ashe dai?. Miyasa kike da son kanki da yawa akan ƴaƴanki ne wai?”. Karo na farko ta ɗago ta kallesa, idannunta cike da hawaye. Muryata na ɗan rawa ta ce, “Miye abun son kai anan Abahn su?. Yaron nan kodan halin daya shiga ai ya cancanci a yafe masa a kuma fahimcesa. Eh naji shi mai kuskure ne, amma koda bai fito yace yana son Maanal ba halin daya shiga kawai amsa ce. Amma sai ace baza'a bashi matarsa ba har sai bayan salla. Haba Gadanga ka fahimta mana, baifa da lafiya, yana buƙatar mai kulawa da shi.....” hawaye suka shiga ziraro mata batare data kai ƙarshen zancen ba. Shi Abah sai abun ma ya fara bashi dariya. Yanzu dan kawai yace Maanal bazata tare ba sai bayan salla shine abin kuskure har ta zauna tana kuka. Oh ya rabba, Fateemansa sarkin daru kenan. Kansa kawai ya girgiza, batare da yace komai ba ya juya zai bar mata ɗakin, dan dole ya turza sosai ta yanda ita da ɗan nata zasu san ba wasa yake akan al'amarin ba. Da sauri ta ce, “Gadanga!”. Tsayawa yay, tare da ɗan waiwayowa ya kalleta. Sai kawai ta sake sakar masa kuka. Da sauri ya fice abinsa, dan in tana irin wannan darun nata yafi buƙatar yin nesa da ita, idan ba haka ba sai ta karya masa zuciya ta sakashi yin abinda bai niyyar ba. Kai tsaye daga sashen Oum ɗin sashen AA ya nufa, dan son sake duba jikinsa, saboda yau ma a kwance ya yini ko salla bai fita ba sakamakon rashin ƙwarin jiki da yake fama da shi har yanzu. A sashen ya samu babban Yaya da Fawzan a tare da shi, sai dai shi barci ma yake AA ɗin, su kuma suna ƴar hirarsu. Cike da girmamawa suka gaisheshi, ya amsa musu da kulawa yana taɓa goshin AA dake barci. Jikinsa babu zafi kamar jiya, dan da ganin ma yanda yake barcin zaka san Alhmdllh. A hankali ya sauke ajiyar zuciya, sai kuma ya ɗago idonsa akan su Babban Yaya ya ce, “Alhamdullah yanzu kam babu zazzaɓin ai. Ya kamata kuje ku kwanta ku huta kuma ni bara na zauna da shi yau”. Idanu Fawzan ya ɗan waro waje da faɗin, “Haba Abah da kanka. Ai sai Oum ta zane mu.” Dariya Abah yayi, hakama babban Yaya ya murmusa tare da faɗin, “A'a Abah mun yafe maka kaje abinka. Dan gaskiyar Fawzan Oum zata iya zane mu ne”. Nan ma murmushi kawai Abah yayi, sai kuma ya zauna suka ɗan tattauna akan jikin AA ɗin da tun shekaran jiya da suka iso daga Kano sai a hankali, dan duk dauriyarsa sai da ya sake kaiwa kwance. Gashi ya kuma kafe bazai je asibiti ba, sai nan doctor yazo yake duba shi. Bayan Abah ya musu sallama ya fito babban Yaya ya biyosa da sauri. Dakatawa yayi yana kallonsa harya ƙaraso. “Lafiya dai ko Fadeel?”. Cike da ladabi babban Yaya ya ce, “Eh Abah, kawai dai akan batun tarewar Maanal ɗin ne dai, dan ALLAH kayi haƙuri a bashi matarsa, ALLAH bana jin daɗin yanda nake ganin Oum a cikin damuwa. Abubuwan sun mata yawa, ga ciwon Ajwaad ɗin ga kuma wannan batun. Abah harfa rama naga tamun yau ALLAH ”. Babban yaya ya ƙare maganar kamar zai yi kuka. Murmushi Abah yayi, sai kuma ya ɗan furzar da iska tare da faɗin, “Wato Fadeel ya kamata muma kammu adalci muyima yarinyar da iyayenta suma. Dan tabbas da nasan Rafeeq zai zagaye yay wannan aikin sai na hanashi, saboda nifa har yanzu ina akan bakana sai Ajwaad ya sauke kansa ƙasa yazo da bakinsa ya nema na bashi Maanal bayan ya nema afuwarta, idan ma ta kama ya faɗa mana dalilinsa na wannan dagewar”. Kai sosai Babban Yaya ya jinjina, ya ce, “Na fahimceka Abah, kuma nima ina bayanka. Sai dai hakan bazai hana na baka haƙuri ba na kuma nemawa Auta afuwa. Kasanshi da zurfin ciki, maybe akwai abinda bamu sani ba game da al'amarin, amma wlhy mu shaida ne Ajwaad na son Maanal matuƙa. Kuma sai nake ga mata da miji sai ALLAH, kamar barinsu su kasance a taren zai sa su sasanta kansu kodan soyayyar da suke ma juna su duka” “Humm wace soyayya kuma Fadeel, yana sonta zai watsar da al'amarinta ya zauna jan jiki a sanda ya sake ganinta, to Miye na girman kan, aure abin wasa ne? Barshi dai a bata tare ɗin ba, zai fi jin zafin wannan bulalar fiye da wadda kake hangen. Ina son hakan ya zama izina a garesa ya canja wannan halin nashi kodan yanzu shi mai iyali ne nanda wani lokaci haihuwa za'a fara masa”. “Tabbas aure ba abin wasa bane Abah, mu kuma masu biyayya ne ga kowanne irin hukunci daga gareku. Amma idan mukai dubi da halin kawai daya shiga akan tsoron rasata abun muyi nazari ne. Ta wani ɓangaren ina tsoron kar dangin mahaifinta ne fa sukai masa wani abun tun wancan lokaci tunda dama kakarsu ta nuna bata son aurenmu da su Shaheedeh. Abah kasan zata iya bin kowacce hanya domin cin nasara, sannan shi kansa asiri gaskiya ne fa”. Sosai Abah ke kallon babban Yaya. Zuciyarsa nata faman kai-kawo akan kalamansa. Sai dai kuma baice komai ba akan hakan illa nufar hanyar fita da faɗin, “Zanyi nazari, amma ina akan bakana na bazata tare ba yanzu ku cigaba da jiyyarsa ALLAH ya tashi kafaɗunsa”. Daga haka ya fice abinsa. Da kallo kawai Babban Yaya ya bishi, shi kansa al'amarin Autan nasu na damunsa, da rikita shi, amma dai koma miye ai ta ƙare tunda an ɗaura, komai mizai biyo baya mai sauƙi ne insha ALLAHU...... Murmushi mai faɗi da yalwa Mamy ta saki, dan dukan tattaunawar Abah da su Babban Yaya a cikin kunnenta ta kasance. Tayi matuƙar yin farin cikin yanda shirinta yay tasiri akan Abah cikin sauƙi haka, dan sam batayi zaton zai amshi batun da muhimmanci ba duba da sanda take tsara masa yin hakan yi yay kamar maganar tata bata tasirantu a gareshi ba. Shiyyasa taga ƴar gwal ɗin tashi har yanzu babu fara'a ashe an sake wargaza mata shiri ne. Wani murmushin ta sake saki haƙoranta na bayyana sosai, sai kuma ta gimtse fuska da gyara yanayinta ta ƙarasa shigowa falon sosai tana sallama. A tare Fawzan da Babban Yaya suka ɗago suna kallonta tare da amsa sallamar. Cikin yanayin da take nuna musu na kawaici ta amsa gaisuwar da suke mata, tare da tambayarsu yaya mai jikin. Suma cikin girmamawar da suke bata suka tabbatar mata da sauƙi, yanama yin barci ne. Kai kawai ta jinjina musu, batare data sake cewa komai ba ta nufi bedroom ɗin AA ɗin. Barcin kuwa yake har yanzu, fuskarsa tayi fayau. Guntun murmushi ta saki a hankali, dan tasan tabbas ƙaunar da takemasa dabance a cikinsu, tun daga ɗaukar cikinsa har haihuwarsa duk da wahalar data sha shi ɗin na musamman ne a gare ta. A karo na biyu ta sake sakin murmushin, sai kuma ta kai zaune kusa da shi gab tare da kai hannun ta shafa yalwatacciyar sumar kansa dake a hargitse. Addu'ar samun lafiya tai masa mai ɗorewa tsahon mintuna kafin ta tashi ta fita.... A hankali AA da tun tsaiwar Mamyn a kansa ya farka ya buɗe idanunsa ya bita da kallo, sai da ta maida ƙofar ta rufe ya sake maidasu ya lumshe luuuu. Ya jima kafin ya sake buɗesu, sai dai sun masa nauyi sosai alamar barci bai gama sakinsa ba. So yake ya tashi zaune, sai dai kansa juya masa yake yi, dan haka dole ya sake maida idanun ya rufe barcin ya ƙara yin awan gaba da shi cike da mafarkin Mamy da haka kawai ganinta a kansa tsaye ya tsaya masa a rai duk da yasan ba wani abu mara ƙyau tazo tayi a garesa ba, amma dai zuciyarsa ta riƙe abun matuƙa..........✍️ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖3️⃣ ______________ ........Mamy kam a inda tabar su Fawzan anan ta samesu, sai dai yanzu Nibras ta ƙaru. Ɗan tsurama Nibras ɗin datai mata wani iri idanu tayi, sai kuma cikin tausasawa ta furta, “Nibras baki da lafiya ne?”. Kallon Nibras ɗin Fawzan da Babban Yaya suma duk sukayi saboda jin furicin Mamyn. Cikin damuwa Fawzan ya ce, “Mamy gara kam ki tambayeta ke, dan tun jiya nima nake fama da ita amma sai tace ba komai gajiyar biki ce wai.” Cikin jinjina kai Mamyn tace, “Itama gajiyar bikin akwaita ɗin ai, dama sai a hankali zata saki kowa duk da ga wani na tunkarowa kuma dai. Kinga kije ki samu ki gasa jikinki da ruwa mai zafi sosai sai kisha pracitemol ki kwanta abinki kiji. ALLAH ya ƙara sauƙi”. Ji Nibras tai kamar ta zageta, amma sai ta daure ta jinjina mata kai kawai da faɗin, “To Mamy”. Daga haka ta juya ta fita zuciyarta na mata zafi da ƙuna matuƙa. Tazo ne dan taga fuskar AA ko zataji sassaucin abinda ke cizon zuciyarta, amma Mamyn ta wani korota. Ba komai zata dawo ne, dan in har yau Fawzan anan zai kwana ALLAH sai dai su kwana tare a sashen AA ɗin. Koba komai ta rage raɗaɗin kishin dake dafa mata zuciya. Sau ƙin ma har yanzu ko sau ɗaya bataga Maanal a sashen nashi ba.. Fitar Nibras ya saka Mamy ma yunƙurin tafiya, amma sai Babban Yaya ya dakatar da ita cikin ladabi. Tsayawa tai tana kallonsu su duka. Fawzan ya ce, “Mamy dan ALLAH magana zamuyi ne”. Wani irin sanyi mai silalar da kuzari ne ya shiga bin jijiyiyin jininta yana gauraye jikin ta. Yayinda wani farin ciki ke cika zuciyarta tamkar kumfar omo a cikin ƙaton bahon wanki. Yau itace yaranta ke faɗa mata suna son yin magana da itane iya su kaɗai babu matar can a tsakkiyarsu. Ya rabba, ita kam mizatace da UBANGIJI yau. A zahiri kam sai ta dake babu wani alamun komai a fiskarta ta dawo ta zauna. Babban Yaya ne ya fuskanceta da ƙyau cikin nutsuwarsa. “Mamy akan Ajwaad ne dama muke son dan ALLAH kisa baki a tsakanin rikicin Abah da Oum. Dan ALLAH ki taushi Abah akan ya bari Maanal ta tare a ɗakinta gobe idan ALLAH ya kaimu, dan gani yake kamar Oum ta kasa fahimtarsa ne saboda soyayyarmu ta rufe idonta, Auta na buƙatar matarsa a kusa da shi ya fahimci Oum dan ALLAH”. Sosai kalmar soyayyar nan ta daki zuciyar Mamy, dan saida ta maimaitata a zuciya yafi sau uku. A fili kam sai ta sake raunana fuskar tata ta ce, “Oh dama wani abune ke faruwa? Ai ni na zata dan bashi da lafiya ne kawai bata tare ɗin ba. Yau gajiya tasa sau ɗaya kawai muka haɗu da Oum ɗin. Amma gaskiya ai Abahn naku ya faɗa, Mamanku ta cika rigima akan al'amarinku.....” Cikin ƴar dariya Fawzan ya ce, “Kai Mamy kema haka zaki ce”. “Ai gaskiya ne Fawzan, ita idan kaga tana fushi a gidan nan abu ya shafi ɗayanku ne. Karku damu zan sameshi muyi magana in sha ALLAHU. Itama zuwa da safe zan zauna da ita. Ni bara naje na ɗan kwanta nima kamar Nibras ɗin gaɓɓaina duk ciwo suke min”. Godiya sukai mata da sai da safe. Fitarta babu jimawa Oum ta shigo itama. Su duka miƙewa sukai sukai kanta ganin har yanzu fiskarta a cinkushe, ga idannunta kamar wadda tayi kuka. Take suma duk fuskokinsu suka sauya. Murya a rauanne Babban Yaya ya ce, “Oumna Please ki cire damuwar nan, kin san fa Abah wani lokacin dan kawai ya kunnaki ne bawai abinda ke ransa kenan ba.” “Amma Fadeel ya tausaya masa mana, kwance fa yake baida lafiya. Shin ALLAH ma ba muna masa laifi ba ya kuma gafarta mana saboda rahamarsa”. “Hakane Oum shima zai huce”. Cewar Fawzan yana mata murmushi da kama hannunta ya sumbata. Haka sukaita lallashinta har sai da tayi murmushin itama. Kafin su nufi bedroom ɗin AA ɗin. Ganinsa zaune a bakin gado yasa ta ƙarasa shiga ciki da sauri, kusa da shi ta zauna tana mai riƙo hannunsa daya dafe kansa da shi, dan yaji duk zancen Mamy da su Babban Yaya. Mamakin Mamy da halinta ke sake raunana masa zuciya, amma yana mata fatan shiriya kafin lokaci ya ƙure mata. Yasan duk abin nan fa Abah keyi daga cikin shirinta ne, zai kuma bama kowa mamaki in sha ALLAHU cikin sauƙi. “Auta yaya akayi? Kanne har yanzu dai?”. Karan farko ya kalla Oum ya sakar mata murmushin ƙarfin hali, sai kuma ya kwantar da kansa a saman kafaɗarta. “Ya daina Oum”. Ya faɗa acan ƙan maƙoshi. “To Alhamdullah, ALLAH ya ƙara lafiya baby na kaji, yanzu mi kake son ci?”. “Oum tea kawai”. “To ba damuwa bara Fawzan ya haɗa maka”. Kansa ya jinjina mata, sai kuma ya kalla Babban Yaya da Fawzan. Murmushi yay musu kaɗan, suma dake kallonsa suka maida masa murtani suna tambayarsa yaya jikin nasa. A samman laɓɓa yace da sauƙi. Daga haka Fawzan ya fita haɗa masa shayin. Kallon Oum ya ɗanyi, har ya janye idanun sai kuma ya tsira mata su, kafin tai ƙoƙarin dai-daita fiskarta har ya furta, “Oum kinyi kuka”. “Kukan lafiya Auta ”. Ta faɗa tana ɗan harararsa cikin yanayin son basarwa. Ina bai gamsu ba, cikin rashin kuzari ya zamo ƙasan lallausan carpet ɗin gaban gadon ya zauna yana mai zuba mata idanunsa dake a shanye. Zatayi magana ya girgiza mata kai, “Oum Please ki daina damuwa, nasan a kaina ne ko? Dan ALLAH ki bari naji sauƙi fa, ki tambayi babban Yaya ma”. Ya ƙare maganar yana kallon babban yaya a raunane. Cike da tabbatarwa babban Yaya ya jinjina kansa shima yana kaiwa zaune kusa da Oum ɗin, Fawzan ma yazo ya miƙama AA kofin tea ɗin daya haɗa masa suka zagayeta kowa na mata nashi daddaɗan kalamin, idan ka gansu abin sha'awa da birgewa sojojin yaƴanta zagaye da ita, basu barta ba har sai da fiskarta ta washe da fara'a kamar yanda suke so. Shima AA sai ƙoƙarin ƙarfafa kansa yake yanda hankalinta zai ƙara kwanciya. Ganin dare yayi Oum da babban Yaya suka baro sashen suna ƙara tattaunawa aka bar Fawzan da zai kwana da shi. Bayan wucewar tasu ne Fawzan ya zayyanema AA komai dake faruwa ana rikicin da Abah keyi akan tarewar Maanal kamar yanda ta buƙaci ji. Murmushi AA yayi mai faɗin da har ya saka Fawzan zuba masa idanu baki buɗe. “Oh abin ma kai nishaɗi ya baka kenan?”. Cewar Fawzan cike da mamaki. Murmushin AA ya sake saki a karo na biyu, sai kuma a hankali ya jingina da fuskar gadon yana kai hannu ya ɗan shafo gashi kumatunsa. “To yaya Fawzan in bai sakani nishaɗi ba kuka kake son nayi, banda ma abin Oum minene abin ɗaga hankali anan, ta bar masa ƴarsa mana”. Dariya Yaya Fawzan yayi da faɗin, “Oh hakama zakace? ALLAH yasa ya jika, kaga idan sati ɗaya yay niyyar horaka sai ya maida shi wata uku kadai san halin Abah”. Murmushi kawai AA yayi kaɗan batare daya sake cewa komai ba. Fawzan kuwa ya tasashi gaba da tsogumi... __________★ Washe gari da safe Alhamdullah Oum ta tashi da sauƙin damuwa ba kamar jiya ba. Dan tunda ta kira Mah-mah a ɗazun da asuba ta sanar mata sai Mah-mah ɗin ta tausheta da mata nasiha akan ta sakama Abah ɗin ido, ta bashi damarsa matsayin mahaifi dan ko yaya shima bazai yi abinda zai cutama Ajwaad ɗin ba ai, sannan kuma tunda a gida ɗaya suke ai babu wani abun ɗaga hankali in dai yaran yanzu ne masu ƙarancin kunya, shi da kansa ma zaice ya ɗauki matarsa basai ta ɓatama kanta rai ba. Ji tai zuciyarta ta rage jin haushin Abah ɗin, ta kuma ɗau alwashin daidaita komai a tsakanin AA ɗin da Maanal ta yanda Abahn da kansa zai tattarasu ya kora sashen nasu batare da alwashin nasa ya cika ba. Yau ɗin yanda Manaal take ta faman sinne-sinnen kai ya saka Oum kamata ta duddungure da faɗin, “Wai Auta ni kike son maidawa surukarki a gidan nan, jiya na saka miki ido ne kawai naga iya gudunki, to kar naji karna gani. Maza tashi muje kitchen ki haɗama mijinki abinci yau kije ki duba jikinsa dai kada mu take doka”. Murmushi Maanal tayi tana ɓoye fuskarta a jikin Oum ɗin, itako Oum na mata dariya. Atare da Oum suka shirya abinci mai sauƙi ma AA ɗin har kala uku, sai wanda suma zasu ci, dan yauma Abah a sashen Mamy zai karya. Suna kammalawa Oum tace taje tai wanka, yayi da masu aiki keta faman kimtsa sashen kamar yanda suka saba. Ba wata kwalliya Maanal tayi ba, ta dai gyara fuskarta ta ɗan saka kwalli da lipsgloss, sai tai simple ɗaurinta daya zauna mata ɗan kwantaccen gashinta ya ɗan fito ta gaban goshi kaɗan. Tana ƙoƙarin saka turare kiran Amaal ya shigo mata. Ɗagawa tai cike da shagwaɓa dan haushinsu take ji a Kano sunce zasu dawo amma sukai mata wayo. Dariya Amaal ɗin taita mata, sannan ta kwantar mata da hankali akan ai next week in sha ALLAHU suna nan tafe da sauran kayanta, dan Daddy yace sai zuwa ƙarshen sati za'a kai kayan gararsu ita da Huznah. Duk da dai Oum tace a ɗan saurara akwai sauran biki da zasu yi anan Abujan shiyyasa ma bata tare ba. Sosai ita Maanal ma abin ya bata mamaki, yanzu duk wancan kaikawon da akasha na Kano bai kuma isa ba. A fili kam sai suka cigaba da maganar su da Amaal. Tana ajiye wayar mai aikin Oum ta shigo tai kiranta, mayafi ta ɗauka ta sanya, dan haka kawai taji tana jin kunyar fita a haka matuƙa. Tayi ƙyau sosai, duk wanda ya ganta kuma yaga amarya, dan ƙamshinta daban ne, ga ƙunshinta raɗam yanata ɗaukar ido daga baƙin har jan, fatar jikinta kam da tasha gyara ba'a magana, sai wani irin glowing take a idanun mai kallo kamar ka lasheta. Ita kanta Oum kallonta kawai take tana murmushi, ta jima bataga ma'auratan da suka dace da juna ba irin Maanal da Autanta, sai dai ai musu fatan zama lafiya mai ɗorewa kuma. ALLAH ya kawo zuri'a masu albarka..........✍️ 🏃Da suwa zamuje sashen AA ɗin ne?. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖4️⃣ ______________ .......Basket ɗin da aka shirya masa kayan abincin Maanal ta ɗauka, kai kace wani anguwa zasu je ba cikin gidan ba. Sun fito gwanin sha'awa daka gansu kaga uwa da ɗiya ba uwar miji da matar ɗa ba. Oum tasan Mamy na sashen Abah dan haka bama tace Maanal taje ta gaida su ba, shiru ma gidan alamar kowa na sashensa, sai ma'aikata dake ta ƙoƙarin kimtsa ko'ina, sunta gaishesu har suka isa sashen AA. Haka kawai Maanal ke jin kamar tace bazataje ba, amma bazata iyama Oum musu ba duk tsanani. Kai tsaye Oum ta shige dan tasan bazasu sami kowa a falon ƙasan ba, Maanal dai biye da ita zuciyarta na mata wani nauyi. Dan kana shiga da sallamar sabon fenti dana sabbin kaya zaka fara cin karo. Tabbas dole ne mai kallo ya furta Masha ALLAH, dan kuwa dai Daddy yayi matuƙar ƙoƙari, daga Maanal ɗin har Huznah ya zuba musu dukiya. Duk da asace Maanal ke kallon komai sai da taji hawaye sun cika mata ido sosai, wata irin ƙaunar Daddy da Ammie na ratsata, falon ƙasa ma kenan, bata san yaya kitchen yake ba, kuma su Didi sun sanar mata daga saman har ƙasa Daddy ya cika mata su da kaya. Zuciyar Maanal bata ƙarasa fashewa ba sai da suka hawo upstairs ɗin, ya subahannallah komai yaji, a hakan ma nan ba'a kammala aikin ba dan ga manyan kwalaye nan a ajiye gefe an tule, zama sukai a cikin kujerun dan su an riga an shiryasu, dai-dai nan Fawzan ya shigo shima da alama yaje sashensa ne. Cike da tsokana yace, “Inyee kaga Lilly amaryar Auta”. Da sauri Maanal ta ɗan waro masa idanu, sai kuma ta ɓata fuska. Dariya Fawzan yake yi, Oum dake tayashi ta ce, “Ni ban taɓa ganin yaya irinka ba Fawzan, anya kuwa bazan turaka hutu Kano ba ka bar min yara su shaƙata”. Dariya sosai Fawzan yake yi, ya kai zaune kusa da Oum ɗin yana gaisheta, itama Maanal ɗin sai ta gaisheshi. Oum ce kawai ta tambayi yaya jikin Autan nata, Maanal kam kunya ta hanata yin hakan. Fawzan ya ce, “Da sauƙi sosai Oum, dan tare mukaje massallaci ma da asuba yau. Ku shiga mana ai ya tashi”. Murmushi Oum tai da faɗin, “Alhamdullahi”. Sai kuma ta juya ta kalla Maanal da kanta ke'a ƙasa. Cike da kulawa ta ce, “Auta tashi ki shiga masa da abincin gamu nan zuwa”. Kai kawai Maanal ta iya ɗaga mata, sai dai ji take kamar tace ma Oum ɗin a'a amma babu dama. Haka ta ɗauka basket ɗin kanta a ƙasa, Fawzan ne yay mata nuni da ɗakin yana tsokanarta, ita dai yau babu bakin maida murtani sai Oum ke kare mata. Sai da tai ɗan jimm a tsaye kafin tai knocking da yatsanta ɗaya kamar mai jin tsoro, tabbas badan bazata taɓa iya musu da Oum ba komi za'ai bazata je inda yake ba, duk da kuwa har cikin ranta tana jin damuwa da rashin lafiyar tasa. Jin shiru ta sake yin knocking ɗin, sai kawai jitai daga falo Fawzan nace mata ai ta shiga kawai ba lallai yajita ba. Nan ma jitai kamar ta saki hawaye, amma haka ta danne kamar mai tsoron shiga wuta ta tura ƙofar ɗakin a hankali. Sai da ta ɗan rumtse idannunta taja numfashi kafin ta saka ƙafarta a hankali lips ɗinta na motsawa alamar sallama. Bata kalla cikin ɗakin ba ta maida ƙofar ta rufe, yayinda wani sassanyan ƙamshi ya daki hancinta, ɗan sanyin acn da aka saka kaɗan yay wani shiga jikinta. Sosai ta saki ajiyar zuciya a cikin ƙirjinta. Sai kuma ta shiga bin ɗakin da kallo jin alamar kamar babu mutum, babu kowa kam, sai dai gadon babu gyara alamar yanzu aka tashi a kansa, ɗakin ya tsaru matuƙa, ga komai dai-dai misali babu wani tarkace, duk da safiya ce babu yawan haske a ɗakin, dan labulayen duk a sake suke, fitulun kuma a kashe sai mara haske sosai kalar blue. Hakan ya saka launin ɗakin sake zama mai ɗaukar hankali. Nanma ajiyar zuciya ta sauke, sai kuma ta cigaba da takawa a hankali kamar mai sanɗa da nufin ajiyewa ta fice abinta tunda ALLAH tasota baya ɗakin, sai dai kuma da'alama shirin nata zai bi ruwa, dan tana gab da isa tsakkiyar ƙaton bedroom ɗin ƙofar bathroom dake daga can cikin closet ɗinsa da zaka iya hangowa ta cikin ɗakin ta buɗe, harga ALLAH da farko tsorata tayi dan haka ta kalla wajen, sai dai kuma da gudu ta ɗauke idanun nata zuciyarta na wani kalar bugawa saboda saukarsu a kansa. Ba ƙaramin jin ta gama rikicewa tayi ba, dan daga shi sai ƙaramin towel daya ɗaura a ƙugunsa, buɗaɗɗen jikinsa jiƙe da raɓar ruwa alamar wanka yayi, dan hatta sumar kansa a jiƙe take itama dai da alama wanketan yayi. Shima dai cak ɗin ta tsaya, dan ganin nata ya saka shi jin shock na rashin zato dan tunda suka dawo bai gata ba, duk ciwon nan bata shigo dubashi ba. Kamar zai ɗauke kai dan jin haushi. Sai dai ganin yanda tai tsammm kanta a ƙasa ya sakashi sakin wani shegen murmushin gefen baki yana ɗan yin luuu da idanun nasa kamar zai lumshesu. Ƙaramin towel ya cira dake rataye a jikin wani ƙyaƙyƙyawan hanger dake gab da ƙofar bayin, dan an tsara su ne a wajen kala-kala ta cikin closet ɗin gwanin birgewa. Saman kansa ya kai towel ɗin kafin ya fara takowa harya fito daga closet ɗin gaba ɗaya. Bedroom slippers ne a ƙafarsa masu taushi, duk da ba ƙara sautin takun nasa ke badawa ba sai take jin sa ita har tsakkiyar kanta, karo na farko a rayuwarta da taji wani mashahurin tsoron kasancewarsu su biyu kacal a waje, da ace zata iya da ɓacewa kawai zatai a ɗakin ta huta. Amma babu damar hakan gareta tunda ita ba aljana bace. Yana isowa gab da ita batama san wani ƙarfi yazo mata ba tai saurin juya masa baya tana sake ƙarfin rumtse idannunta hannayenta biyu data riƙe basket ɗin na ƙara damƙe shi da ƙyau. Cak ya tsaya shima dariya na neman cika masa zuciya, dan yanda ta juya ɗin da saurinta sai ka ɗauka wani kumurcin maciji ta gani ko zaki. Da ƙyar ya iya danne dariyar dake cinsa a rai ya matsa jikinta sosai, tsabar neman magana sai ya zagayo da hannayensa ta gefe da gefenta ya ɗaura akan nata hannayen dake riƙe da basket ɗin, badan ya riƙe hannun nata da ƙyau ba da sai basket ɗin yayi faɗuwar da abincin zai tarwatse a wajen. Yanda ta takure jikinta waje guda ya sake bashi damar manne jikinsa da bayanta sosai tare da duƙo kansa saman kafaɗarta yana busa mata numfashinsa a saman dokin wuya da cikin kunne, sannu a hankali ya sake matsar da fuskarsa jikin tata idanunsa a lumshe, kwantaccen gashin kumatunsa dake da damshin ruwa na gogar gefen fuskar tata. Da sauri ta zame hannunta dake riƙe da basket ya koma nasa hannun gaba ɗaya. Karo na farko ya saki ɗan murmushi mai sautin da har taji, har yanzu kuma idanun nasa a lumshen suke yana shaƙar ni'imtaccen ƙamshinta. Cikin matuƙar raɗar da koda wani ne a kusa da su da wahala yaji miya faɗa a hankali can ƙasan maƙoshi ya furta, “Good morning Bestie”. Tsabar yanda maganar tashi taima Manaal shigar zuruff bama tasan ta zabura ba tana ƙoƙarin tureshi, dolensa ya bata damar fita a jikin nasa, dan duk ta daburce har tana neman kaɓe basket ɗin abincin hannun nasa. Hanyar fita ta nufa da sassarfa, muryarta na rawa, harshenta na sarƙewa ta furta, “Su Oum na falo”. Kafin yay wani yunƙuri harta fice. Kansa kawai ya girgiza yana mai sakin murmushin da har sai da haƙwaransa suka bayyana, a ransa kam ayyanawa yake (Zamu haɗe ne ai yarinya). 😂Tace maka ita ba yarinya bace yanzu kana sake maidata baya🏃 ★ Sarai Oum ta lura da yanda Manaal ta dawo kamar wadda aka biyo, sai dai batai magana ba har sai da Manaal ɗin ta sanar musu cewar ya tashi. A dai-dai nan ma kiransa ya shigo wayar Oum ɗin. Basu ji abinda ya faɗa ba, Oum tadai miƙe tana murmushi tace su shiga. Fawzan ne ya fara shiga, Oum biye da shi, itace ƙarshen shiga dan maƙalewa tayi a bayan Oum. Sosai Oum ta nuna farin cikin ganin yanda jikinsa yay sauƙi yau sosai fiye da kullum, shima ganin fara'a a fuskarta sai zuciyarsa ta masa sanyi. Fawzan kam ya tasashi gaba da tsokana shi da Maanal data zauna a cikin yanayin takura, dan tun haɗa idon farko da tayi da AA ta ɗauke kanta bata sake kallon sashen da yake ba. Yanzu ma da Fawzan ɗin ke tsokanarsu kanta a ƙasa sai Oum ke kare musu. A dai-dai nan Saheeba da Nibras sukai sallama. Kafin a basu iznin shigowa Naufal da Anum sun shigo. Kai tsaye yaran inda AA yake suka nufa cike da farin cikin ganinsa a zaune, shima fuskarsa da ɗan sakewa ya ɗaga Anum ya zaunar a jikinsa, Naufal kuma ya zauna a kusa da shi. Da kai kawai ya amsa gaisuwar da Saheeba da Nibras sukai masa. Ba haka Nibras taso ba, amma har ranta taji daɗin ganin jikinsa da sauƙi sosai yau ɗin. Wani gefe na zuciyarta kuma najin zafin ganin Maanal a tare da shi, gashi data kallesa sai taga idanunsa akan Maanal ɗin suke, ita kuma ƴar ranin hankalin sai wani latse-latsen waya take yi ita adole ga mai aji. Oho ita Maanal bama tasan tanai ba, hasali ma jinta take duk a takure, da Oum zata barta ma da tuni ta wuce abinta ta koma sashenta ita kam..... ________★ A lokacin da anan ahalin gidan ke sashen AA a ɓangaren Mamy tana can tana waya da babbar yayarsu akan batun auren AA ɗin da Nuratu da sukaji su Abah sunyi shiru sunƙi cewa komai ga shi har yau laraba, a yanda tsarin nasu yake kuma daga gobe alhamis ya kamata ace biki ya fara musamman tasu ɓangarensu, amma sunji ɗif babu wani bayani. Shine tai kiran Mamy ɗin dan jin mike faruwa. Bayanin da Mamyn ke mata rai ɓace yasa tace yau zatazo Abujan dan tana Kano. Da wannan sukai sallama. Zama Mamy tai tana mai dafe kanta. Eh lallai taci nasara akan Abah na hana Maanal tarewa a sashen AA, sai dai tana jin fargaba akan tunkararsa da batun bikin nan kuma. Musamman idan akai dubi da halin da AA ɗin ke'a ciki na ciwo. To amma kuma itama fatanta ai ayi bikin ne. Numfashi mai nauyi ta sauke sosai, tana mai tattara batun gefe ta jingine har isowar yayar tata dai, dan gara su tunkari Abahn tare zatafi samun ƙwarin gwiwa.... Kusan ƙarfe uku na rana kuwa yayar Mamy ta iso gidan. A lokacin kusan kowa yana a sashensa, dan hatta AA yana sashen Oum, daga sallar azhar daya samu iya fita yau shi da sauran yan uwansa suka wuce sashen Oum ɗin. Manaal dai na ɗakin tunda taji motsinsu taƙi fitowa, sai ma tayi kwanciyarta barcin dole, daga baya na gaskiyar ya ɗauketa. Mamy da kanta ta fito ta tarbi ƴar uwarta, kai tsaye kuma sashenta suka wuce, suna dai-dai gifta window ɗin Oum dake kallon sashen Mamy ɗin sautin dariyar su Fawzan ta shiga kunnunwansu, kasa haƙuri sukai sai da suka leƙa. Aiko idanunsu suka gano musu zaratan mazajen ƴaƴan na Oum zagaye da ita tana bama AA abinci a baki, dai-dai kuma lokacin Babban Yaya shima ya buɗe nasa baki wai ta bashi, shine suka saka sanya dariya, shima Fawzan yace bazai yarda ba ya je aka bashi. Kai da kaga fuskar Oum kasan cike take da farin ciki, haka suma su babban Yayan, farin cikin Oum ɗinsu ya saka fuskokinsu bayyana murmushi na musamman, musamman ma shi da AA da ba cika son yin dariya sukai ba sai sun so. Fuuuuu Mamy ta wuce sashenta zuciyarta na tafasa. Koda suka shiga ɗaki saita sakar ma yayarta kuka. Ita kanta yayar tata wata irin masifa take ji na tafaso mata daga ƙirjinta, amma dole ta danne ta shiga lallashin Mamyn da nuna mata kuka fa ba shine mafita ba. Dole suzo susan abinyi dan al'amarin na Oum fa na neman zame musu ɗan zane. Dan tabbas ta rigada ta gama mallake zukatan yaran nan da salon makirci (kamar yanda suke fassara soyayyar Oum ɗin akan su AA. Sai dai kuma wannan nasu mummunan zaton ne kawai, dan ita dai baiwar ALLAH Oum har cikin zuciyarta ne, hasalima takan manta da cewar ba itace ta ɗauka cikin su AA tai naƙudarsu ba saboda yanda ta sakankance matuƙa).........✍️ _Dangin Mamy ina gaisuwa 🙄🥱🏃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖5️⃣ ______________ 5 ......Sun tattauna sosai kafin su yanke shawarar yayar ta tunkari Abah da batun bikin cikin hikima. Hakan kuwa sukayi, bayan sallar la'asar Abah ya dawo gida Mamyn tai mata rakkiya har sashensa. Bayan sun gaisa cikin mutunta juna dan akwai ƴar kunyar surukuta a tsakaninsu duk da kuwa Abah ya girmeta sosai, amma yana kawaice mata saboda dattako. Cike da kissa tana murmushi take faɗin, “Kukam kamar a kanku aka fara aurar da auta, yanzu bayan shagalin Kanon bazaku barmu mu huta ba wani satin kunce zakuyi wancan kuma?”. Cikin danne takaici da ƙyar Mamy ta ƙaƙaro murmushi tana ɗan laɓe baki, “Ai jikinsu ne zai gaya musu dan nikam dai nayi na ALLAH da naje muku Kanon ma. Amma da zaku tausayama kanku da kun barshi ku haɗe duka”. Cikin rashin damuwa Abah yay ƴar dariya shima da faɗin, “Ai ku kwantar da hankalinku bikin ma Saturday ɗin dama da wahala ya yiwu. Dama yau nake son zama daku akan zancen dan yau da safe Baba ya kirani, ya kuma tabbatar min zuwa gobe shima zai samu mutanen gidan naku dan bammayi zaton Aunty Babba zatazo ɗin ba”. Ya ƙare maganar yana kallon Aunty Babba datai wani irin ɗagowa tana kallonsa. Wani irin harmutsawa zuciyar Mamy tayi, da ƙyar Aunty Babba ta iya saita yanayinta cike da dakiya ta ce, “Lafiya dai ko Aban Fadeel? (Dan haka take kiransa)”. “No lafiya Lau, Baba ne yace a ɗan dakata Ajwaad ɗin ya ƙara samun lafiya sosai, dan yaron nan ya bugu sosai dan ma ALLAH ya bashi ƙarfin hali ne. Ga kuma mutane sunyi ƙoƙari na zuwa wancan ɗin, ga azumi yana gabato mu kwana goma sha kawai ya rage, sai yace a bari kawai bayan salla idan muna da rabon kaiwa sai ayi. Amma nima naso ayin kawai a huta, damma uwarsa taƙi bani haɗin kai amma ina son horasa akan yarinyar nan ita kanta, idan son samuna ne kada ta tare yanzu har sai bayan sallar itama da kansa ya magantu ya faɗa mana dalilin ƙin amsar aurenta da yay har yana neman kashe kansa, amma nasan da wahala ta bari duk da dai jiya da yau naga ta daure ana son aga gudun ruwana, kuma zasusha mamaki ita da ɗan nata dan na shirya musu sosai....” Gaba ɗaya takaici ma ya hana Mamy magana, jitake kamar ta falle fuskar Abah ɗin da mari ta huta daga ita har yayar tata. Amma dai suka danne da ƙyar suna ƙawata fuskarsu da murmushi kaɗan. Da ƙyar Aunty Babba ta ce, “Uhhm kaima kasan dai bazata bari ka horashin ba Aban Fadeel, amma kuma hakan shine dai-dai, ya kamata yasan muhimmancin yarinyar, kar yaga an bashi a ɓagas ya ɗauka arha ya samu ”. “Ato kema dai ƙya faɗa Aunty, amma bazata yarda ba, shekaran jiya fa kuka ta sanya min ma wai ina son na maida masa ciwo baya. Tunda dai anyi ya wuce a haƙura mana. Kai ban san irin son da Fateema kema yaranta ba wlhy.” Shiru Aunty Babba tai masa dan maganarsa ta ƙarshe sake sukar mata zuciya take, ita ko Mamy ma sai ta miƙe abinta. Shima kiran wayarsa da akayi ne ya sashi miƙewa ya fita. Da kallo suka bishi, yana fita Mamy ta miƙe a fusace har idannunta na tara ƙwalla tana faɗin, “Ashe da rigima kuwa a gidan nan Aunty......” Da sauri Aunty Babba ta rufe mata baki, sai kuma ta kama hannunta suka fice ta baya zuwa sashenta..... __________★ Har dare Oum bata san yayar Mamy na gidan ba. Sai kusan takwas su AA sun dawo massallaci, shi kaɗai ya wuce sashen Oum. Babban Yaya da Fawzan kowa sashensa ya wuce. Abah kuwa sun barsa a waje yana gaisawa da maƙwafcinsu. Kai tsaye upstairs AA ya haura, dan ƙasan masu aiki na gyarawa kasancewar anan suka tashi. Shiru falon babu kowa sai ƙamshi mai daɗi na turaren wuta da aka saka ke tashi. Cikin yanayinsa na wanda yasha faman jiyya ya kai kwance a doguwar kujera, a haka ya jawo remote ɗin tv dana ac ya kunna, yana cikin searching channel Oum ta fito daga bedroom. Zama tayi tana ɗan matse fuska da faɗin, “Auta kun dawo?”. Remote ɗin tvn ya ajiye tare da juyowa ya kalleta. Maganar da yay yinƙurin yi ya haɗiye tare da tashi zaune idanunsa akanta. Fahimtar kamar ya gane yanayin da take ciki ya sata saurin gyara fuskarta, cikin murmushi ta ce, “Lafiya? Ya naga ka tashi?”. “Oum muje asibiti”. Ya faɗa cikin sanyi da damuwa maimakon amsa tambayar datai masa. Murmushi ta sake saki tana gyara ƙafafunta, “Asibiti kuma? Ni lafiyata ƙalau”. Idanunsa da suka ɗan kaɗe ya tsurama ƙafafunta, sai kuma ya zamo ƙasan lallausan carpet ɗin falon ya zauna gab da ita. Ƙafafun nata ya kamo ya ɗora a saman jikinsa. Duk sun ɗanyi fushi kuwa, cikin sauri ya ɗago yana kallonta. “Oum dan ALLAH ki tashi muje asibiti, see your leg! fa”. Murmushi sosai Oum tayi da faɗin, “Oh oh! Look, there's nothing wrong, my dear. I'm okay fa. Kawai dan kwana biyu ban ɗan motsa bane ba. Sannan yau na manta bansha magani na da yamma ba sai yanzu na tuna nasha bayan idar da salla. Ina mai tabbatar maka zata sauka yanzun nan”. Sam bawai zuciyarsa ta gamsu bane, amma bazai iya jayayya da ita ba. Sai kawai ya shiga mammatsa mata ƙafafun. Idanu kawai Oum ta zuba masa tana murmushi, dan tasan yayi shiru ne kawai badan ya gamsu ba. Cikin son kwaranye masa damuwar data bayyana akan fuskarsa ta ce, “Auta ya kamata kaci abinci fa, sai kasha maganinka, doctor yace 8 amma gashi har ta shige baka nema ba.” Fuskarsa a narke sosai ya ce, “Oum bana jin cin komai fa, zan sha maganin a haka kawai”. “A'a bazai yiwu ba, bara na haɗa maka ko tea to.” Da sauri ya maida ƙafafunta da take neman janyewa a jikinsa. “No Oum zan haɗa da kaina zauna ki huta. Naji sauƙi fa sosai”. “Haka ake so ai my baby ALLAH ya ƙara afuwa, amma wannan jikin naka da sauran ƙarfinsa. Bara kawai na kira Inte ta haɗa maka”. Fuska ya yamutsa, dan shi fa baya son masu aiki su masa abinda zaici. Bawai dan basu da tsafta bane ko yana ƙyanƙyamin su, a'a kaf ma'aikatan gidansu da iliminsu da kuma tsaftarsu. Kawai shi abinci idan bana Oum ba baya so sai idan ta ƙure. Dan ko abincin Mamy yakan daɗe baici ba a gidan balle masu aiki, su Saheeba kam ai da wahala su girka abinci ya cisa, shi kallon ma basu iya yake musu ba. Oum data fahimci baya so sai tai murmushi. Dai-dai nan Maanal ta fito daga bedroom ɗin Oum hannunta riƙe da novel, sai waya manne a kunneta tana magana da Didinta Shahidah. Sam hankalinta bai kai kan AA ba sai Oum dake zaune a kujera, sai da tazo gab da su fuskata ƙawace da murmushi daya ƙara mata ƙyawu sosai tana faɗin, “Kai Didi to ga Oum ɗin” sannan idanunta suka sauka akansa, ai da gudun tsiya ta janyesu tana haɗiye murmushin nata. Shima nasa idanun daya ɗan zuba mata ya janye, dai-dai nan Oum takai wayar data amsa a hannunta kunnenta. Ƙoƙarin juyawa tabar falon tayi, Oum ta riƙo hannunta tana mata alamar ta tsaya. Sai kuma ta ɗan janye wayar a kunnenta a hankali tace, “Haɗama mijinki tea”. Maida wayar tai ta cigaba da amsa gaisuwar Shahidah tana murmushi. Manaal dai ta kasa motsawa, dan haka kawai furicin Oum ɗin ya ratsa mata jiki da ƙyau. Kalmar *Mijinki* ɗin nan da Oum ya ambata sai taji ta mata nauyi sosai a ƙirji. Juyowar da Oum tayi taɗan kalleta ya sata ajiye novel ɗin hannun nata ta nufi hanyar stairs cikin sanyin jiki tamkar wadda aka saluɓema kuzari. Ƙasa-ƙasa ya bita da kallo, sai kuma a hankali ya ɗan lumshe idanun nasa yana mai sakin ajiyar zuciya acan ƙasan maƙoshinsa ya cigaba da matsama Oum ƙafafun nata. Sarai Oum na lure da su da yanayin da suka shiga. Amma sai ta basar ta cigaba da wayarta da Shahidah... Kusan mintinan goma sha sai ga Maanal ta dawo. Ta samu har yanzu Oum na waya, yayinda shi kuma ke riƙe da novel ɗinta kansa a ƙafar Oum dai-dai gwiwa ya ɗan kwantar daga zaunen da yake. Murmushi Oum tai mata da nuna mata gaban AA ɗin alamar ta ajiye madaidaicin tiren dake a hannunta anan. Kanta ta gyaɗa, tare da kaiwa duƙe gabansa ta ajiye tray ɗin a hankali. Sai a lokacin ya ɗago idanunsa ya ɗan kalleta. Fuska taɗan ɓata tana kallon littafinta dake hannunsa, sai kuma tai masa yuuu da idanun irin na jin haushin dake nuni da wayace ka ɗauka min novel?. Laɓɓansa da ciwo ya sakasu sake komawa pink sosai ya wani ɗan laɓe mata, tare da ɗage gira kaɗan irin na (An ɗauka ɗin nan) sai hakan ya sake tunzurata ta miƙa hannu zata warce novel ɗin. Janyewa yay yana mai ɗan zaro idanu waje na mamakinta. Harara ta sake dalla masa ta ɗauke kanta. Shayin ta shiga haɗa masa, tasan baya shan suger sosai tun zamanin ƙuruciya, dan ko sanda yay tashen shan chocolate baya shan mai suger sam dan baya shiri da shi sam. Gwara-gwara ma zuma ita kam yana masifar so, shine ma ya koya mata sonta itama. Amma dan neman magana yanzu saita ɗibo har huɗu kasancewar mai ƴaƴa ne zata afka masa. Ai baima san ya cafke hannunta ba yana ɗan waro idanunsa da faɗin, “Oum kinganta ko? Zata saka min suger”. Oum data basar da su kamar bata san mima suke yi ba ta kallesu, cikin shagwaɓa Maanal data ƙwace hannunta daga riƙon da yay mata ta ce, “Oum nima fa novel ɗina ya ɗauka min”. Ita Oum ma sai suka nema sakata dariya, dan idanun Maanal har sun fara ƙyalli alamar taruwar ƙwalla. Ta fahimci sufa idan suna a gabanta mantawa ma suke yanzu bada bane sun girma. Dai-dai nan Mamy da yayarta sukai sallama batare da Oum ta raba faɗan ba. Kusan a tare Oum da Maanal suka amsa sallamar, sai dai ita Maanal a hankali. AA kuwa a maƙoshi ya amsa yana kai tea ɗinsa ɗaya ɗauka baki. Yayinda yaƙi yarda ya kalla su Mamy da tun shigowarsu ita nata idanun ke'a kansu a kaikaice. Dan ba ƙaramin dukan zuciyarta ganinsu a taren yayi ba, ga yanayin zaman nasu kusa-kusa dan tray ɗin nan ne kawai ya rabasu sai ƙafar Oum ɗaya dake kusa da AA gab, ɗayar kuma kusa da Maanal. Manaal ɗin ce ta fara ƙoƙarin gaishesu, yayinda shi kuma ya ɗan basar da farko, sai Oum dake sallama da Ammie. Da ƙyar Mamy ta danne zuciyarta ta amsa gaisuwar Maanal ɗin, yayarta kuwa dan makirci tuni ta washe haƙwara tana tsokanar AA da Maanal. Wai autoci sunzo sun saka babarsu a gaba. Ƴar dariya Oum tayi da faɗin, “Aunty harda ke kema bazaku bar min yara su huta ba? Saukar yaushe haka babu labari?”. Kafin Aunty ta bada amsa AA ya gaisheta. Amsawa tai da kulawa tana jajanta masa jiki. Kansa kawai ya jinjina mata yana bin Maanal data miƙe da kallon ƙasan ido. Hakama Mamy da yayarta a kaikaice Maanal ɗin suke kallo, kowa kuma da abinda yake kissimawa zuciyarsa akan yarinyar. Yayinda Oum kam hankalinta ke akan AA ne kawai. Babu jimawa Maanal ta dawo, ƙaramin tray data saka ruwa da lemo da kofi akai ta ajiye a gaban Auntyn Mamy. Itako sai ta shiga saka mata albarka cike d makirci. Harda faɗin, “Eh lallai na ƙara yarda autar Hajiya Fateema ta girma”. Kunya ce ta kama Maanal, dan haka ta sulale zata bar wajen, yayinda Oum ke dariya Mamy na tayata da murmushin yaƙe. AA kam novel yake karantawa hankali kwance yana shan tea ɗinsa. Oum ce ta tsaida Maanal ganin ta nufi hanyar ɗaki. “Auta dawo kici abinci, nasanki daga wannan shigar zaki iya neman wajen kwanciya”. Kan Maanal a ƙasa ta ce, “Oum bana jin yunwa ALLAH. Sannan ba kwanciya zanyi ba yanzu zan dawo”. Kai Oum ta jinjina mata, ita kuma ta shige tana istigafari akan ƙaryar da taima Oum, dan harga ALLAH batai niyyar dawowa ba sam... Hira ta ɓarke sosai a tsakanin Oum da su Mamy, sai dai ita hankalinta ya rabu biyu da rashin dawowar Maanal falon, sam bata son yarinyar ta takura kanta. Dan ta fahimci har yanzu Maanal ɗin bata gama dawowa Maanal ɗinta ta baya ba. Ba komai ta saki jiki ba kamar yanda suke a da, yanzu ma wata kunya take neman ƙirƙira a tsakaninsu ne, shiyyasa take ta ƙoƙarin ganin ta kauda mata da yanayin. AA ma dai har yanzu yana zaune yana saurarensu, sai dai a zahiri zaka ɗauka gaba ɗaya hankalinsa akan novel ɗin da yama Maanal kwace yake. Sai dai sam ba haka bane ba, mamakin su kawai ke nuƙurƙusar masa zuciya da ruhi, dan su duka biyun ya musu farin sanin da harda wanda basu bayyana a gabansa ba. Haka yake, mutum ne shi mai tsartar tsiya, ALLAH ya azurtashi da saurin gane halayyar mutane a ƙanƙanin lokaci balle su. Kuma wannan halin nasa tun yana yaro yake tare da abinsa, miskilancin sa da rashin yawan magana yasa ba'a fahimtar hakan kai tsaye, sai Oum ɗinsa data gama masa sanin in and out. Duk da hankalinsa nakan su Mamy ya fahimci hankalin Oum kuma a rarrabe yake. Ganin yanda take faman kallon hanyar bedroom ɗinta yasa shi ajiye novel ɗin hannunsa ya ɗauka kofin daya gama shan tea yanzu ya haɗa wani shayin, cike da kulawa ya kalla Oum. “Oum bara na kai mata wannan naga duk kin damu”. Murmushi tai masa tana mai jinjina kanta, sai kuma ta shiga sanya masa albarka. Shi dai ya wuce yana amsawa fuskarsa da ɗan murmushi. Daga Mamy har yayarta da kallon takaici kuwa suka bisa, suna ganin Oum ta juyo garesu suka basar.......✍️ _Mun tafi kai tea. Saura kuma aci amanar Abah🙄🏃🏃🤣🤤_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖6️⃣ ______________ .........Babu knocking babu komai ya tura ƙofar ya shiga, tana zaune a gaban mirror tana shafa mai daga ita sai towel. Cikin yanayinta na rashin gaggawa ta juyo duk da kuwa tsoro taji, amma miskilancinta ya ɓoye hakan akan fuskarta. Shima dai saukar idanunsa a kan nata ya saka zuciyarsa motsawa, duk da jarumtar da yake nunawa a kanta da danne yanayinsa da tsiya-tsiya saboda miskilancin nasa shima da iya taku, a yanzu kam zuciyar ƴan maza da gangar jiki duk sai da suka motsa da ƙarfin ikon ALLAH. Da ƙyar ya iya lumshe idanunsa ganin taja hijjab ta saka a yanayin ko'in kula da shi. Busashen yawun daya haɗiya na samun sassauci daga kasalar dake neman zagwanye ɗan ƙarfin daya fara samu a yau ya saka Adam's apple ɗinsa motsawa sosai a cikin wuyansa. Cikin tasa dakiyar da basarwar shima ya cigaba da takowa cikin ɗakin, a gabanta saman mirror ɗin ya ajiye kofin shayin, batare daya sake kallonta ba ya ɗan jingina bayansa a mirror tare da harɗe hannayensa a ƙirjinsa. “Kinsan bazaki dawo ba miyyasa kikama Oum ƙarya?”. Shiru tai babu alamar zata tanka masa, hakan ya sashi karkatowa ya kalleta, dan abune daya san tafi kowa sanin ya tsana, wato yin magana a masa banza. A kausashe ganin tana neman miƙewa ma ya ce, “Ni nake miki magana kina min banza?”. A halayya irin ta AA babu abinda Maanal bata sani ba, kai sai dai ma ta bama wani labari. Dan ko Oum badan ita uwace ba zatace akwai abubuwa da yawa data fita sani game da shi. A yanda yay maganar kawai ta fahimci ya hau zuciyar tasa, dan haka itama a ɗan tunzure ta juyo tana kallonsa cikin ido. Girarta ɗaya a ɗage ta ce, “Kai da ka shigo ka min sallama ne balle neman izini? Ko an gaya maka dabba ce a ɗakin!”. Ta ƙare maganar da balla masa harara ta murguɗa baki. Yanda kasan robbot haka ya tsaya hana kallonta kawai harta ƙarasa cikin closet ɗin Oum. Da wani irin salo ya shiga girgiza kansa irin na ɓacin ran nan yana cizon lips, a ransa kam rayawa yake (Wato yarinyar nan duk randa na tashi gyara mata zama zata banbance akwai tazarar shekaru a tsakaninmu masu yawa ƙwarai da gaske.) a zahiri kam closet ɗin ya nufa shima. Sam Maanal bata san da isowarsa wajen ba hankalinta na'a zaɓar kayan barci da zata saka. Dan tun shekaran jiya Oum ta saka Inte mai aikinta ta shirya kayan Maanal ɗin cikin closet ɗin ta tunda babu ranar komawarta nata sashen. Sama taka kawai taji nutsatstsiyar muryarsa mai cike da zurfi da fitar isa a cikin kunenta. “Amma kin san zan iya dirje bakinki a ɗakin nan har sai yayi jini batare da sanin kowa ba ko? Bar ganin Abahnki ya tsaya miki tsaf zan koya miki yanda akema miji magana cikin tausasawa da ladabi nabar masa ke na ƙara gaba har sai kin HAIHU zan dawooo....” yanda ya ƙare zancen cikin ƙasan maƙoshi da busa mata numfashinsa akan dokin wuya zuwa cikin kunne ya sata kasa daurewa ta saki kayan a ƙasa tare da juyowa gaba ɗayanta dan sam batayi zaton a kusa yake da ita gab-gab ba. Aiko sai kawai gata a jikinsa gaba ɗayanta. Daburcewa tayi, wajen mutsu-mutsun janyewa ta ruƙunƙumesa gaba ɗaya saboda motsa jikinsa da yayi ya ƙure duk space ɗin dake a tsakaninsu suka mannu da katakon wadrob ɗin bayanta. Bata da zaɓin daya wuce yimasa zobe da hannayenta saboda shiga ɗimuwa. Gashi ta motsa gabas da yamma kudu da arewa babu ko ɗan ɗigon space ɗin barin jikin nasa balle fita. Mayataccen ƙamshin turarensa kam ya gama gauraye ilahirin hijjabin Oum data saka zuwa hancinta har ya ratsa fatar jikinta. AA kam ɗan duniya, tunda ta shige jikin nashi yay wata kalar tsaiwar sojan badakkare kawai ya lumshe oily idanunsa masu hasken tsiya kamar an watsa madara a ciki ya wani kalar tura lips ɗinsa cikin baki ya matse yana sauke numfashi a hankali. Sai da ya tabbatar ɗumin jikinta ya gama ratsa nasa gangar jikin har ƙofofin gargasar jikinsa na bubbuɗewa, wata ƴar zufa ta taru masa a goshi sannan ya ɗan ja jikinsa baya gudun kar'a tafka abun kunya a ɗakin tsohuwa. Dan yasan kansa ƙwarai-ƙwarai da gaske, ALLAH ya azurtashi da ƙarfin buƙata, sai dai ya masa rahama da jarumta da dauriyar iya shanye yanayinsa koda ta ƙarfi ne. Sam bai shirya yin kowanne kalar yunƙuri a gareta ba a yanzu, ya ɗauka ɗammarar bama Abah damar horashin daya ɗauki alwashin yi, itama zai bata damar manta bayan data riƙe a ranta, itama Mamyn zai bata dama akan nata yunƙurin, daga haka sai ya fara dama tashi damar a yanda yake fata da tsarawa da kansu zasu bashi ita da gudun tsiya. Tunanin da yay zurfi a ciki yasa bai ankara har Maanal ta surare daga wajen ba, sai da ya motsa ƙafarsa yaji ya taka kayan data yadda sannan ya farga da hakan. Juyawa yay kaɗan ya dubeta, zaune take a bakin gado ta dafe kanta da duka hannayenta. Fuskarta a duƙe take shiyyasa bazai iya sanin a wane hali take ba. (Ga tsiwa ga tsoro) Ya ayyana a ransa yana mai duƙawa ya ɗauka kayan data ciro ɗin, tare da rufe closet ɗin. Inda take ya iso, batare da yace komai ba ya ajiye mata kayan a gefenta ya wuce abinsa. A tunaninsa su Mamy sun jima da barin sashen, amma sai ya samu a yanzu ma harda Abah, da alama kuma magana suke mai muhimmanci. Sai dai fitowarsa ta sakasu ɗagowa duk suka zuba masa ido amma banda Oum. Sosai ya karanci kallon tuhuma da zargi a idanun Abah. Yayinda Mamy da yayarta suke masa na takaici da ɓacin rai. To yaya lafiyar kura... Dama, ai sai ya wani fiske abinsa yama shiga gaida Abahn. Abah yasan wanene ɗan nasa da halayyarsa, dan haka shima sai ya basar ya amsa masa tare da tambayar jikinsa. Ya amsa cewar da sauƙi, daga haka ya nufi hanyar fita abinsa dan fahimtar zaman nasu iya nasu ne... Sarai Oum ta lura da kallon da Abah yabi AA ɗin, dan haka ta sake cuskule fuska tamau. Murmushi kawai Abah ya saki ya basar shima, a ƙasan ransa mamakin Fatemansa na sake mamayesa. Tama kwantar da hankalinta bazai mata magana ba. Amma yasan matakin da zai ɗauka. Dan yanzu kam ya sake aminta da zancen Kamila ƙwarai da gaske...... ________★ Maanal tana tabbatar ta daina jin motsin su Mamy a falo ta miƙe ta fito ɗaukar ruwan sha. Ganin Oum ta nufi hanyar stairs kamar mai tafiya da ƙyar tai saurin nufarta da faɗin, “Oum!” a raunane. Tsayawa tayi tare da juyowa, ganin Maanal ya sata sakin murmushi. “Oh kinji sun tafi shine kika fito daga ɓuyan? Auta sokike dai ki maidamu surukanki a gidan nan ta ƙarfi da yaji ko?”. Kai Maanal ta duƙar tana murmushi. “A'a Oum nayi wanka ne, naga kuma zakuyi magana shiyyasa”. “Za'aima Oum wayo kenan”. Murmushi Maanal tayi tana rufe fiskarta da tafukan hannayenta. Oum ma dai dariya tayi. Sai kuma ta ce, “Kinga bara na bama su Inte wayar nan su kaima Aunty ta manta da ita”. Da sauri Maanal tace, “Kawo nakai musu Oum”. Babu musu ta bata, dan itama tasan bazata iya sauka ƙasan ba ƙarfin hali ne kawai irin nata. Gittata da Maanal tayi yasa taji ƙamshin turaren AA sosai a hancinta fiye da sama-sama da take ji. Hakan ya sake tabbatar mata a jikin Maanal ɗin ne. Murmushi tayi sosai, a ranta tace, (Ai nasan za'a rina. Irin hakan nake gudarma Abanku amma ya kasa fahimta). Koda Maanal ta nufi ɗakin masu aiki samu tayi har sun kwanta. Sai kawai ta maida musu ƙofar ta rufe a hankali. Ta kitchen tabi ta fita dan zai fi mata sauri. Gidan fayau yake da haske dan tako ina akwai security light kwanyar, kanta tsaye ta shige sashen Mamyn, babu kowa a ƙasa sai Haule dake a kitchen, jin motsin Maanal ya sata leƙo. Murmushi ta sakarma Maanal, tare da fitowa gaba ɗaya cikin girmamawa ta ce, “Aunty Amarya barka da dare”. Guntun murmushi Maanal tayi mata da miskilar fiskarta dan sunan da Haulen ta kirata da shi ya mata wani iri, musamman daya kasance Haule zata girmeta, dan zasuyi sa'anni da Amaal. Cikin yanayin rashin sakewarta tace, “Mamy fa?”. Upstairs Haule ta nuna mata. “Suna sama”. Kai kawai Maanal ta jinjina mata ta nufi hanyar, bayan ta buɗe ƙofar ta shiga ta maida ta rufe, dan tsarin sashen irin na Oum ne komai da komai, na AA dai ba haka yake ba, to bata sani ba ko nasu Fawzan ma da nasu tsarin. A hankali take taka stairs ɗin kamar wadda bata so, tana a kusan na biyar ɗin ƙarshe taja ta tsaya cak sakamakon shashshekar kuka, faɗuwa gabanta ya shiga yi, sai dai kafin tayi wani yunƙuri ta tsinkayi muryar Aunty Babba na magana cikin takaici. “Wai Kamila kina da lafiya kuwa? Tamkar wata ƙaramar yarinya ki zauna kinama kishiya kuka! Ina jarumtar taki ne ta tafi?. Har wacece Fateema yanzu a gareki da zata baki tsoro. Sanda ma take jin kanta a Fateema Darma ɗin kin shigo gidanta kinyi rayuwa da mijinta, kin haihu sai yanzu ne zaki zama sususu akan ƙananun abubuwan nan.....?” “Bazaki gane ba Aunty, wlhy Matar nan ta wuce dukkan yanda kike zato da tsammani. Ni wlhy a wannan gaɓar ƴaƴana nake buƙata tako wane hali, idan ba hakaba kuwa zan iya kashe Fateema.....” Kaɗan ya rage Maanal takai ƙasa dan firgita. Dan wata muguwar hajijiya ce taji tana neman zubar da ita. ALLAH dai ya taimaketa ta dafe glass ɗin stairs ɗin da ƙyau. Anya bayan ƙaddarar data faru da ita tsakaninsu abaya akwai wani abu data taɓa jin ya girgiza zuciyarta kamar wannan? Mamy fa? Mamy dai Mamy dai ke furta zata iya kashe Oum. Mamy dai Mamy dai kalamanta ke bayyana akwai ƙullaliya tsakaninta da Oum.... Tunaninta ne ya katse jin abinda Aunty Babba ke faɗa. “Kamila ki kwantar da hankalinki, na ɗau miki alwashin a wannan gaɓar sai munyi maganin Fateema. Babu maganar kisa a ciki, amma wlhy da ƙafafunta sai tabar miki gidan Aliyun da take taƙamar nata ne, ɗan uwanta ne tare da ƴaƴanki. Dan babu abu mafi ciwo a gareta kamar a shekarun nan ace Aliyu ya saketa, ya kuma rabata da ƴaƴan data gama wahala da su da sakankancewa nata ne....” “Aunty bana katseki bane, amma tayaya Aliyu zai saki Fateema? Kada ki manta da jininsu ɗaya, iyayensu ɗaya. Zasu yarda ne ya saketa?”. “Da gudun tsiya ma kuwa. Ko an faɗa miki haka zamu barshi ne? Ai sai mun juya masa kai daga garesu gaba ɗaya, ta yanda su duka babu wanda ya isa sakashi balle hanashi”. “To ita kuma wannan ƴar iskar yarinyar da aka aurama Ajwaad fa? Kin fa san halin yaron nan da baƙin taurin kan masifa. Yanzu kina ganin tunda yasan a ƙulle nake da shi ko dubashi naje sashen sai ya hau barcin ƙarya. Kuma jira nake ya gama warkewa sai na sillesa tas, kuma ko yaƙi ko yaso sai ya rabu da annobar yarinyar nan. Dan har abada bazan taɓa son abinda ke tare da Fateema ba. Ba kuma zan haɗa jini da Asiya ba dan na mata tsana mai girma itama saboda kusancinta da Fateema”. “ALLAH na tuba idan mun gama da Fateema wacece ita kuma wannan abar da uwarta. Ai ki fahimta wannan masifaffen son da Ajwaad kema yarinyar nan ba banza ba ne, tun suna yara suka tsafacesa ai. Shiyyasa ta tsara duka yaran su auri nata tsarin wato ƴaƴan munafukarta mai zuwa mata bin bokaye Asiya, kinga ya tabbata ke da su sai dai kallo. Matar nan fa yanda kika san NASARA haka take akan iya tsari, ke kuma sai ki sakankance sai abu na neman kwaɓewa. Yanzu dai ki muje ki kwanta dare yayi, ki ƙara nazari nima zanyi nawa. Amma dole ne Nuratu ta dawo gidan nan tai azumi. Wani ƙaramin wasa nake son a buga tsakaninsu da yarinyar nan, har itama waccan sakaran matar Fawzan dole ta shigo tawagar, facalanci nake so su buga ɗan gaske ta yanda sai ta tsani kanta a gidan nan daga ita har uwar ɗakin nasu. Tarewarta kuma ki riƙe wuta babu ita......” “Ai ni so nake ma ta dawo nan gabana ta zauna, dan Ajwaad da kike ganin yaron nan hummm. Kuma tsarin nan naki yayi. Ai dama nafi son na fara gasama Fateema aya a hannu sai ta gama firgicewa da ni kafin tabar min gidan”. “Yauwa ashe kin fahimceni, yanzu dai wayata nacan a sashenta na bari dan ta naɗar min maganganunsu, da safe nasan zamuji abubuwa da yawa”. Ƴar dariya Mamy tayi da faɗin, “Kai aunty shiyyasa nake sonki”. Idanu Maanal ta tsirama wayar, sai kuma tai murmushi tana mai kai hannu ta share hawayenta dake rige-rigen sakko mata........✍️ _Tofa yau dai Maanal taji ainahin Mamy, mi kuke tunani?🏃🏃🏃_ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. 🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖7️⃣ ______________ .......Tsam ta miƙe daga zaunen da take a step ɗin, babu buƙatar ta bada wayar yanzu, dan haka ta fice a sashen. Da alama Haule ma ta shige ta kwanta dan har ta kashe wuta. Maanal taji daɗin samun Oum na wanka, sai kawai ta adana wayar ta kwanta. Koda Oum ta fito likimo tayi kamar mai barci, duk maganar da tayi kuma ta fiske. Hakan yasa Oum ɗin fahimtar tadaiyi barcin. Shirin barci tayi, dan Abah sai kiran wayarta yake. Babu yanda ta iya dole ta kimtsa ta tafi. Saboda ya tabbatar mata yau idan batazo sashensa ba shi zaizo a gaban Maanal ya ɗauketa. Tasan halin kayanta, dan haka ta haƙura kawai tai shiri ta tafi. Sai da tama Maanal addu'a ta shafeta sannan ta rage mata hasken ɗakin ta daidaita mata ac kamar wata ƴar Baby. Aiko tana fita Maanal ta rushe da kuka. Wani irin tausayin Oum mai tsanani na ratsa mata zuciya matuƙa. Tabbas ta taɓa jin Oum ba ita ta haifi su Babban Yaya ba Mamy ce, amma bata taɓa sake tuna hakan ba ko kallon hakan a zuciya balle a zahiri saboda babu wani alamu dazai nuna hakan koda ga Mamyn ne balle Oum data gama sakankancewa. Itafa ganin komai take tamkar almara ko mafarki. Duk yanda taso yin barci hakan ya gagara, dole ta zauna kawai a zaune tana nazartar abubuwa. Daga ƙarshe ta ɗakko wayar nan ta goge recording ɗin da suka saka, yako naɗa da yawa dan harda maganganun Abah da Oum bayan fitar su Mamyn. Batamayi nisa a ji ba ta goge kawai ta ajiye wayar. Mikewa tai ya shiga bayi ta ɗauro alwala tazo ta shiga miƙama UBANGIJI kukanta. Kusan ma dukkan addu'oin ta akan Oum ne.... WASHE GARI yanda su Mamyn sukazo gaida Oum cike da makirci bakuna a washe sai Maanal ta shagala a kallonsu. A ranta tana jinjina lallai maƙiyin ɓoye shine ainahin maƙiyi, dan zai taima rayuwarka illa batare daka sani ba. Balle ace yana a jikinka, tare da kai matsayin masoyi na zahiri. Gara wanda zai zo ya kalleka ya ce maka wane BANA SONKA BANA ƘAUNARKA. Kasan baya ƙaunar taka zaka kiyaye komai tsakaninka da shi. Koda suka nema waya sai ta basu, da Oum tai magana sai tace ai taje kaima su Inte ɗin ta samu sunyi barci shiyyasa ta dawo da ita. A cikin zuciyarta kuwa faɗi take (Oum baki san su wanene waɗan nan mutanen ba. Sunfi duk wani abinda kike kallo a matsayin haɗari haɗari. Amma kada ki damu, ba sunce YAƘIN SUNƘURU bane abun, muje zuwa yanzu ne za'ai wasan na gaskiya. KAREN BANA SHINE ZAI MAGANIN ZOMON BANA. Ni Maanal Habib Giro, na ɗauki ɗammara da alwashin sai waɗan nan mutanen sunyi nadamar sake dawowata RAYUWARSU. idan su aya sukai alwashin gasa miki a hannu ni zan gasa musu ƘARFE ne a tsakiyar kawunansu. Sai sun san ZURU BATA CIN ZURU SAI SAI DAI A HAƊU AI ZURU-ZURU. Ƴaƴa kuma tunda ALLAH ya mallaka niki tofa naki ɗin ne. MUJE ZUWA WASA). 🤣🤣Tofa nace ba. Ƴar mutan Giro fa tace muje zuwa wasa, da alama ainahin MAANAL zata dawo🥱. (Maanal dama in an MUTU ana dawowa😜?) 😂😂🏃🏃🏃 ____________★ KANO Tsaye yay kawai yana kallon ƙofar daya gama mummurɗawa ya ji a rufe. A karo na farko ransa ya fara ɓaci da salon iskancin Huznah. Wai mi take nufi da shine halan? Ɗan iska ta ɗauke shi ko mi? Yau kwana ɗai-ɗai har takwas kenan da kasancewarta a gidan, amma tunda baƙi ƴan biki suka tafi da magriba tayi sai ta shige ɗaki ta kulle kanta. Da rana kuwa ita da kowa dake shigowa faran-faran. Hatta shi da rana tsakaninsu normal ne, da farko ya dauka kunya ce da kawaici irin na yaranmu, duk da baiyi zaton samun hakan daga Huznah ba, musamman idan akai dubi da shekarunta da wayewar zamani.. Wani ɗan murmushi yayi a karo na farko, ya sake sakin murmushin a karo na biyu saboda abinda zuciyarsa ta sake hasko masa. Baice komai ba yau ma ya juya ya koma ɗayan ɗakin dan dama bedrooms ɗin biyu ne a gidan sai falo, kitchen, ƙaramin store. Gini ne dai irin na mai rufin asiri ba irin wanda su Hajiya Basariyya suka jima suna fata ba. Yana barin wajen Huznah da duk ke ankare da motsinsa ta ballama ƙofar harara. Cike da tsana ta ce, “Maye, in dai nice mu zuba, wannan jikin kuma ƙwalelenka na AA ne. Dan wlhy sai na sameshi, sai na sabauta rayuwar agolar yarinyar can ta yanda bazata taɓa moruwa ba. Idan Ummi tabar uwarta tana yanda taso a gidanmu ni sai na tabbatar mata KAREN BANA SHIKE MAGANIN ZOMON BANA. Daga haka ta koma ta kwanta tana cigaba da charting dinta da take yi daman. A dai-dai nan kira ya shigo wayarta. Zaune ta tashi ganin wanda ke kiran. Sai da ta gyara zama sannan ta ɗaga. Murya ƙasa-ƙasa ta ce, “Sille ya akayi?”. Daga can wanda ta kira Sille ɗin cikin muryar ƴan daba ya ce, “Normal ne uwar ɗaki. Kawai zance miki Nurry fa babu wani bayani a ƙasa kan bikin nan nata da AA. Dan a majiya mai ƙarfi ance har yanzu bashi da lafiya yana gida yana jiyya sai an kwantar sai an tayar. Babu kuma wani yunƙurin ma za'a sake biki a gidan a wannan satin. Kai ita ma agolar gidan taku tana sashen babarsa bata tare turakarsa ba”. Sosai hankalinta ya tashi da jin har yanzu AA ba lafiya. Cike da mamaki kuma ta ce, “Amma Sille kai bala'i ne, dan ALLAH ya akai ka samo wannan sirri mai girma haka?” “Hahaha uwar ɗaki kenan, karki manta a hannun Nurry kika ƙwaceni, amma bari na baki a buɗe, ina da yarinya a gidan dake aiki ta dalilin Nurry.” “Anya Sille bai kamata na fara tsoronka ba”. Dariya ya ƙyalƙyale da ita jin abinda Huznah ta faɗa. Kafin ya ce, “Haba uwar ɗaki, ai ke ta dabance. Kin ganni nan duk rintsi bana manta alkairi. Sannan amana ɗaya ce”. Sosai Huznah ta sauke ajiyar zuciya. Tai masa godiya da tabbatar masa zaiga saƙo ta account ɗinsa daga haka sukai sallama..... Wayar na yankewa daga can Sille ya ƙyaƙyace da wata muguwar dariya. Sai da yay mai isarsa sannan ya ce, “Yaro bai san wuta ba kenan sai ya taka. Daga ke har Nurry ɗin kune kuke min aiki bani ke muku ba. Ina amfani da kune kawai na samu kuɗaɗe. Kuna nan kuna jira baku ankara ba sai dai kuga gawar shegen AA ɗin naku kwance a gabanku. Wannan alƙawari na ne, sannan gaba ce ta tsawon shekara takwas ni da shi.. kai yama kamata nasan agolar yarinyar nan ta gidan ku da akace ya aura”. Wayarsa ya sake ɗauka ya shiga tafa saƙo. Babu jimawa akai masa flashing. Kiran number ɗin yay black, kafin ma ta gama ringig ɗin farko an ɗaga. Daga can ƙasa-ƙasa muryar mace ta bayyana. “Baby miya faru ne naga kace na maka flashing idan ni kaɗai ce? Faka-faka kafin wannan ƴar sa idon ta fito wanka”. “Ke nifa yarinyar nan idan tace zata takura miki a gidan nan ALLAH zan aikata barzahu”. “A'a ka rufa min asiri babu ruwan ka da ita. Sannan itama tana da nata amfanin da take mana ai. Yanzu dai miya faru?”. Tsaki yaja mai kauri, kafin ya ce, “Hoton amaryar gidan nan nake so?”. Hankali a ɗan tashe ta ce, “Wai Matar AA”. “In ba ita ba akwai wata amarya ne a gidan?”. A sanyaye ta ce, “A'a. Amma Baby kasan hakan akwai haɗari ko? Taya zan ɗauketa hoto nikam?”. “Kefa wasu lokutan gaja ce wlhy, kuna gida ɗaya baki san yanda zaki shiga jikinta bane?”. “Tab wlhy Baby hakan zai yi wahala. Itafa irin miskilayen mutanen nan ne na gaske. Sannan zan iya ƙirga maka ganinta da nai a gidan nan. Koda yaushe tana ɗaki ko falon sama kuma a sashen Oum take bana Mamy ba”. “K ni hakan bai dameni ba. Kawai hotonta nake buƙata na kuma baki kwana biyu kacal”. Daga haka ya yanke wayar yana huci. Itako daga can sai ta zuba uban tagumi zuciyata na kai-kawo. Sille ya zamewa rayuwarta bala'i, itako miya ja mata shigowa bariki. Ƙiri-ƙiri da uwarta da ubanta a duniya saboda neman duniya su sun kasa tanƙwara rayuwarta ga wani ƙaton banza ɗan daba na juyata yanda yake so kuma dole tabi. Tabbas ta ƙara yarda da kalmar nan ta malam bahaushe dake cewa WANDA BAIYI SHARAR MASSALLACI BA YAYI TA KASUWA. To ita a ganinta ta kasuwar ma ai mai sauƙi ce, TA BARIKI yafi dacewa ace.... __________★ KADUNA A Kaduna ƙiri-ƙiri Ammie ta hana Daddy sukuni sai rigima take masa akan dawowar su Hajiya Yaya. Shi kuma yayi biris da ita. Da yaga tana neman saka masa rayuwa gaba sai ya shirya yabar mata kasar ma. Wannan abu kuwa ya masifar ƙona mata zuciya. Harda kiran Nene tana kuka. Sai da Nene ta gama saurarenta tsaf sannan ta ce, “Ai ni hakan da yay ya min dai-dai Asiya, tunda nace ki fita a maganar su kin ƙi ko. Su idan sune hakan ta fari dake har fati inaga sai sun shirya bama murna kawai ba. Ba gaban iyayensu suke ba? To ki nutsu idan zaki nutsu kinji na faɗa miki. Kuma nima kada ki sake zuwa min da zancensu. Haka kawai ki dinga ɓatama kanki rai da mijinki akan waɗanda basu ƙi ki faɗi ki mutu ba.... Haka Nene taima Ammie tas sannan ta yanke kiran. Ta kuma tabbatar mata ta kira Daddy ta bashi haƙuri idan ba haka ba zatazo har gidan ta sameta. Wannan faɗa na Nene shine ya kawo ƙarshen rikicin Daddy da Ammie suka shirya ta waya. Sai dai duk da hakan rashin dawowar matan gidan na damunta kodan yaransu dake zuba mata rashin mutunci. Dan ma bata kulasu bata shiga harkar su. Amrah ce kawai babu ruwanta.... __________★ “Mabera! Wai nikam mike damunka kwana biyun nan? Gaba ɗaya baka da sukuni sai tunani da lissafe-lissafe”. Numfashi mai nauyi Daddyn Nazeefa ya sauke, kafin ya juya yana kallon abokin nasa shaƙiƙi da shi da shi suka san juna na haƙiƙa dan kar-tasan-kar ce. “Himm Bakori kenan, kaima ai kasan maganar gizo bata wuce ƙoƙi. A lissafin auren Nazeefa da yaron Alhaji Usman Chalawa wata uku kenan yau cir, kasan dai lokaci yayi da aikina zai fara a kansa ai. Wannan shine lissafe-lissafen da nakeyi. Sai kuma baban naman dana hango yanzu ya shigo a tarko”. “Tofa babban nama kuma? Waye hakan?”. “Ba yanzu zaka sami ba. Sai na gama da Chalawa tukunna. Jiya nayi waya da Nazeefa tace azumi na goma zasu dawo gida. Dan yace mata zasuyi Umra. Dan haka nake shiri, da sun dawo zata fara min nata aikin”. Murmushi Bakori dake kallonsa yayi, a ransa yana mamakin hatsabibancin aminin nasa, ta gefe tausayin yarinyarsa da yake son jefawa a ramin zamba cikin amincinsa yake. Shifa duk iskancinsa ALLAH bazai iya hakan ba. Dan iyalansa nada muhimmanci mai girma a wajensa...... (Humm dan baka san iyalin naka tare kuke raba dai-dai da aminin naka bane Alhaji Bakori🏃🏃🏃🏃) _________★ Alhamdullah jikin AA yay sauƙi sosai, koma muce ya warke sai abinda ba'a rasa ba na tsakanin ruhi da gangar jiki. Kamar yanda yay alƙawarin bama Abah dama ya bashi ɗin. Dan ya tattara al'amarin Manaal ya ajiye gefe kamar ba shine yasha ciwo akan rasata da yaga zai yi ba. Gefe kuma baice komai game da batun ɗaga aurensa da Nuratu sai zuwa bayan salla ba. Sai dai yaƙi yarda su zauna da Mamy duk yanda taso. Da zarar ya fahimci zasu keɓe sai ya zille abinsa. Fahimtar akwai gaɓar da za'azo ya nema mafita ya rasa ya sashi shirin komawa kan aiki. Itama kuma Maanal yace ma Oum ya kamata ta koma kan aikinta, dan shi ba ruwansa idan ta taka doka zai bari kamfani ya hukuntata ne. Hutun kwana goma aka bata, gashi yau suna neman sati biyu. Azumi saura kwanaki bakwai a fara shi kacal. Ita Oum ma tsayawa tai kawai tana kallonsa. Yayinda Maanal tai kamar bata falon ma. Dan tunda ya shigo ta gaida shi ta maida hankalinta ga karatunta, sai shi da Oum ke hirar. Yanzu haka take masa, idan dai ya shigo sashen zata gaida shi, daga wannan gaisuwar ko kallon inda yake bata sake yi komai tsahon zaman da zai yi. Ko kuma tana fahimtar lokacin shigowarsa yayi sai ta koma ɗaki abinta. Wannan abun na cimasa zuciya da ƙona masa rai, amma ya share kamar bai fahimceta ba. Dan ya riga ya sakama ransa daga ita har Aban nata zai iya dasu. Shiyyasa da Oum ta nuna damuwa akan rashi bashi Maanal ɗin zai shiga lallashinta da nuna mata shifa babu komai ta kwantar da hankalinta ta bama Abah dama yay yanda yake so. A ransa kuwa shi kaɗai yasan abubuwan da yake shiryawa.........✍️ _😂Dan Oum mi kake shiryawa? Dan bamu musha mana._ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. 🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖8️⃣ ______________ .......A ɓangaren Mamy kam ranta fes akan hakan. Burinta ɗaya yanzu shine Maanal ta dawo sashenta da zama kamar yanda ta zunguri Abah da zancen. Sai dai kamar ya yarda da farko sai kuma taji bai sake maganar ba. Ta ɗan bashi kwana biyu ne ta sake zuwa masa da zancen, dan idan ta cika matsawa zai harbo jirgin ta ne kasancewarsa mutum mai tsarta. Ajwaad kuwa data fahimci kauce-kaucen sa zata tattarashi ne ta watsar, akwai gaɓar data tanada masa ne. Sun gama tsara Nuratu zatazo nan gidan tai azumi. Acewarsu mamanta zata shirya ta tafi umrah sai ace Nuratun tazo nan ta zauna kafin ta dawo. Gefe kuma cike suke da alwashin bayan salla da sati biyu koda tsiya-tsiya sai an ɗaura auren Nuratu da Ajwaad idan ba haka ba kuma suyi maganin Oum... Oho ita bama tasan sunai ba. Duk da bata son haɗin auren Nuratu da Autan nata bata taɓa ji a ranta zatai wani yunƙurin hanawa ba. Fatanta ma ALLAH ya daidaita komai ya canja rayuwar Nuratu ɗin su zauna lafiya da Maanal da shi kansa Ajwaad data san baya son haɗin auren nan. Kai ko Mamy gani take bata so dan haka take nuna mata a zahiri. Da yake zuciyar Oum ɗin a tsarkake take kuma sai bata taɓa bin ƙwaƙwƙwafin Mamy akan komai ba sam... Yau ta kasance lahadi, dan haka Oum ta samu Abah da batun komawar Maanal aiki gobe idan ALLAH ya kaimu. A cewarta da zaman nan gara ta koma aikin sai ta samu nutsuwa sosai. Da farko Abah shiru yayi, dan sai ya dinga hango ai zuwa office ɗin zai saka Ajwaad yaga ya samu wata dama akan Maanal ɗin ne. Shiru ya ɗanyi na wasu sakanni, sai kuma cikin jinjina kai ya ce, “Okay zan yi tunani akan hakan”. Miƙewa Oum tayi tana masa sallama, dan har yanzu basu koma dai-dai da Abah ɗin ba. Ta dai daina fushin da take yi da shi. Da kallo kawai ya bita yana murmushi da girgiza kansa. A ransa yace (Fatete na rigima kenan) da murmushin Oum ɗin Mamy dake da shi yau ta shigo ta samesa. Koda yake tun ma bikin su AA ɗin Oum tace ta bar mata Abah ɗin har sai Maanal ta tare. Hakan ba sabon abu bane ga Oum. Dan haka kawai idan ta bushi iska sai tace ta barma Mamy Abahn na sati biyu koma na sama da hakan. Wani lokacin Abahn ne ma ke gajiya ya balbaleta da masifa yace shi bai yarda ba kamar dai yanda ya sakata kwana a gunsa dole randa yayar Mamy ta kwana a gidan. Sosai ran Mamy ya sosu da murmushin nasa, wanda tasan akan Oum ɗin ne tunda sun haɗu a waje. Tarasa ya zata raba wannan shaƙuwa da soyayyar, duk da haihuwar da tayi, da kwantar da kai tana musu bauta su duka biyun har yanzu Oum ta fita matsayi da girman iko a wajen Aliyu. Sam baya iya ɓoye ƙaunar da yake mata koda a gabanta ne ita Kamila. Baya shakkar yabon Oum ko sanya mata albarka ko yin kwatance da ayyukan alkairinta. Hira goma zaka zauna da shi zai ambata maka sunan Fateema so takwas ne kansa tsaye. Cikin takaici ta haɗiye ɓacin ranta ganin ya juyo gareta, a hankali ta maye fuskarta da sassanyan murmushi cike da makirci take tambayar fitar Oum ɗin wai taga ranta a ɓace. Ikon ALLAH sai Abah ɗin yay nauyin baki yau, dan murmushi kawai ya mata baice komai ba. A ƙasan ransa kuwa hankalinsa na'a kan Oum ɗin ne, buƙatarta yake a jikinsa ƙwarai da gaske, yana kewar sassanyan ƙamshinta da kulawarta a garesa. Badan wai Mamyn bata masa ba ita, kawai dai yana jin na Fateema a garesa special ne. ALLAH shine kaɗai yasan irin son da yake ma Fateema da ƙauna a rayuwarsa, shiyyasa yake kallon al'amarin Ajwaad da Maanal tamkar nashi da Fateema ne. Dan soyayyar yaran gaba ɗayanta tamkar gado ne daga tasu soyayyar, abinda kawai ya banbanta shine shi da Fateema jini ɗaya ne... Haushin ganin ya tafi zurfin tunanin nasa wanda Mamy tai imanin akan Oum ne yasa ta miƙe ta wuce bedroom ɗinsa. Dan tana fara ganin irin wannan signing ɗin a garesa a duk lokacin da Oum ta bar mata shi take fahimtar ya gundura da ita hankalinsa nakan matarsa. Tasha zargin kodai Oum tana musu hakan ne dama dan wani tarko nata ko shiri, amma idan ta nutsa a bincike sai ta gano sam ba hakan bane ba.. Abah ya jima kafin ya dawo daga duniyar tunanin nashi, sai sannan kuma ya farga babu Mamy. Ajiyar zuciya kawai ya sauke ya ɗauka wayarsa ya tashi ya fita domin kiran ɗan uwansa suyi shawara akan batun Oum ɗin na komawar Maanal aiki. Wato Uncle Mahmud..... ____________★ Kuka bana wasa ba Nurry tasha da jin batun ɗaga bikinta dana AA har sai zuwa bayan salla. Wani irin tsanar Oum da Maanal ta ƙara faɗi da kauri a zuciyarta. Nanfa ta shiga ɗaukarma kanta alwashi kala-kala na gasama Oum da Maanal aya a tafin hannunsu. Dan ta tabbatar kamar yanda taji iyayenta na faɗa makircin Oum ne kawai. Bata sami nutsuwa ba har sai da sukai waya da Mamy da Saheeba da suka kwantar mata da hankali da tabbatar mata aure na nan babu fashi. ALLAH dai ya kaimu bayan sallar da sati guda za'ai ma ba biyu ba.. Sannan a gidan zatai azumi kuma... Hakan ya ɗan sakata jin sanyi da sassauci a cikin ranta. Harta ɗan saki jiki ta cigaba da harkokinta musamman a media. Harda su tsara write-up ta turama ƙawayenta da abokan arziƙinta cewar biki sai bayan sallah saboda har yanzu ango babu lafiya..... ___________★ WASHE GARI. Safiyar yau Litinin har Oum ta fidda ran Abah zai bar Maanal ɗin ganin tun jiyan baice mata komai ba. Haka shima AA ɗin baima saka ran komawar Maanal ɗin yau ba. Kawai dai ya tashi da nasa shirin ne. Bayan sallar asuba daga massallaci Abah sashen Oum ya nufa. Kasancewar yasan yanzu ita da Maanal ne a ɗakin ba kai tsaye yake shiga ba. Dan haka yay sallama bayan yin knocking a ƙofar bedroom ɗin sannan ya koma falo ya zauna. Babu jimawa kuwa sai ga Oum ta fito daga ɗakin sanye cikin dogon hijjabin sallarta. Tunda ta doso shi ya zuba mata idanunsa da suke a narke. Itako sarai data san halin kayanta da gejin da yake kawai na haƙuri da rashinta a kusa da shi sai ta basar kamar bata fahimci magiyar da yake mata da idanun nasa ba. Ɗan nesa da shi ta zauna, sai kuma ta ɗan zamo a kujerar kaɗan cike da neman magana ta ce, “Yaya Aliy ina kwana” (haka take kiransa lokacin ƙuruciya). Hararta yay da faɗin, “A'a baba Aliy ba yaya ba. Saboda kina son a faranta ran ɗanki zaki ce dani wani yayan gulma”. Ƙaramar dariya Oum tayi, amma batace komai ba. Shima fuskarsa da murmushi ya ce, “Kun tashi lafiya?”. “Alhamdullahi”. Ta bashi amsa. Kansa ya jinjina cike da gamsuwa. Kafin ya cigaba da faɗin, “Akan maganar ki ce ta jiya. Na bada dama Maanal ta koma aiki, amma da sharaɗin driver zai dinga kaita ba ɗanki ba. Dan bana son wata alaƙa ta haɗasu. Ki kuma gargaɗesa babu ruwansa da yarinyata a office balle ya takurata, na saka securityn da zan san duk motsinsa akan hakan, idan ya karya min doka kuma zan ƙara yawan kwanakin suspension ɗin”. Murmushi Oum tayi a karo na farko. Hakama AA da yazo sashen sai dai yana hawowa stairs ɗin yaji muryar Abah dan haka ya dakata. Idanunsa ya lumshe, tare da motsa lips ɗinsa a hankali ya furta, “Ayya Abah koba security ba. Badai ka yarda taje ba, ai sai abinda ka gani kawai Aban Maanal”. Daga haka ya juya ya koma abinsa domin yin shirin office ɗin.... Oum ma bayan tafiyar Abah ɗaki ta koma tace Maanal tai shirin office Abah ya bari. Duk da zama waje ɗayan dama ya isheta sai taji gabanta ya faɗi. Na farko dai tana jin kunya da tunanin yanda zata kalla ƴan company a yanzu. Dan tasan dai sun gama sanin ita ɗin matar ogansu ce a yanzu. Na biyu yaya rayuwarta a companyn zata kasance a yanzu kuma tsakaninta da mai kamfanin. Tunda a gida ya rasa kowace dama a kanta acan da babu idanun Abah kuma fa?..... “Ko baki son komawa ne Baby?”. Oum ya katse mata tunani. Ƙasa tai da kan nata tana ƙaƙaro murmushi. Sai kuma ƙasa-ƙasa ta ce, “A'a Oum. Kawai dai ina jin nauyin ƴan kamfani ne”. Dariya sosai Oum ta sanya da faɗin, “Oh oh! Har yanzu dai Babyna na nan da wautarta. Ina ruwanki da su bayan yanzu ke oga ce. Matar oga ai oga ce ko. Tsakaninki da su sai girmamawa ai. Dan haka ki kwantar da hankalinki ki riƙe girmanki, ki ƙara ƙwazo da himma akan aikinki. Kiyi abinda ya dace na rike martaba da girmanki domin kare mutincinki dana mijinki. ALLAH yay miki albarka”. Cikin jinjina kai Maanal ta ce, “Amin”... Wanka ta shiga, Oum kuma ta fita zuwa kitchen haɗa musu breakfast dan tasan Auta baya wasa da fita akan lokaci, duk da Abah ya kafa dokar ba tare zasu tafi ba tana son Maanal ɗin ta koyi yanayin fitar tashi tunda na ɗan lokaci ne zasu koma fita a taren.. Zuwa bakwai ta kammala komai daya kamata. Ta fito fes da ita cikin Abaya maroon color datai mata matuƙar ƙyau da haska chocolate color skin ɗinta data sha gyaran aure ta sake kwanciya luff-luff. Ga wani ni'imtaccen sassanyan ƙamshi dake tashi a jikinta. Sam batayi wani kwalliya ba a fuskar, iya hoda ce sama-sama sai kwalli da ɗan lips-gloss kaɗan. Dan ko taje girarta ma batai ba. A dining ta zauna kamar yanda Oum ta bata umarni, ta ajiye ƙaramar handbag ɗinta saman table ɗin dining ɗin itama. Dai-dai nan shima AA ya shigo, tun kafin su ganshi mayataccen ƙamshinsa daya gama manne jikinsa da komai nasa ya iso hancinansu. Yayi matuƙar ƙyau cikin Maroon suit shima sai long sleeve shirt fara tas. Harga ALLAH sai da zuciyar Maanal ta ɗan motsa. Amma sai ta dake abinta tama fara ƙoƙarin zuba abincin a ranta tana ƙunƙunin (wayace ya sake airin kayanta) “Auta har an fito?”. Oum ta faɗa dai-dai isowar AA dining ɗin. Kansa ya jinjina mata, tare da kamo hannunta ya sumbata yana mai ɗan bata side hug. Sai kuma a ƙasa-ƙasa ya furta, “Barka da safiya my everything”. Murmushi Oum ta sake masa, tana mai amsawa da, “Ka tashi lafiya ya ƙarfin jikin?”. “Alhamdullahi Oumna, ai ɗanki ya warke sarai in sha ALLAHU ”. “Masha ALLAH haka muke fata ai Auta”. A hankali Maanal data ƙi sake kallon inda yake duk da zuciyarta na cike da zumuɗi da maradin hakan ta ce, “Ina kwana”. Batare daya kalleta ba shima ya ce, “Lafiya”. Daga haka ya kalla Oum a ɗan shagwaɓe ya ce, “Oum yunwa zata cinye hanji na”. Ƙaramar dariya tayi tana kallon Maanal, itama Maanal ɗin dai-dai ta ɗago ta hararesa. Dan itace ke faɗar haka idan tana jin yunwa. Gira ɗaya ya ɗage mata irin (Ni ɗin kike harara?) sai ta sake murguɗa masa baki sannan ta ɗauke kanta. Ita dai Oum wurin tai ƙoƙarin bar musu tana faɗin, “Bestynka ta zuba maka abincin zanje nayi wanka ne”. Kamar Maanal zatai kuka tabi Oum da kallo. Sai dai batace komai ba. Sai da ta shige sannan ta ɗauke idanun nata. Tsohon minti ɗaya kafin tace, “Me zaka ci?”. Shiru kamar bazai amsata ba hankalinsa akan waya. Kamar wadda taji haushi ta ɗago manyan idannunta ta zuba masa. Kaifin idanun nata da tasirinsu a garesa ya sashi kasa jurewa shima ya ɗago lumsassun nasa ya zubasu cikin natan. Bata iya ta janye nata ba suka shiga ma juna kallo mai taushi da kassarasa kuzarin jiki. Lips ɗinta ta sake motsawa a hankali batare data raba idanun nasu ba ta ce, “Nace mi kake so?”. Cikin kasala da tausasawa kamar baya so shima ya motsa lips ɗin nasa ƙasa-ƙasa ya furta, “Ke!”...........✍️ _Ehemm-eheem nace ba, 1+1 nawa kenan? An bamu assignment ne a makarantar islamiyyar mu ne ni kuma ban gane lussahin ba😌😣, shine nace bara na tambayeku🫣🏃🏃🏃🏃🏃🏃._ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. 🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖9️⃣ ______________ .......Daburcewa taso yi, ta kuma rasa yanda zata fassara amsar ta shi. Cikin suɓutar baki ta ce, “Ban gane ni ba!”. Wani ɗan iskan gajiyayyen murmushi ya saki a iya lips ɗinsa. Kafin ya sake narke idanunsa dake sarƙafe da nata har yanzu. “Kince mezan ci? Me nake so? Nace KE!”. Ya faɗi (ke) ɗin da wani kalar sanyin murya yana ɗan waro fararen oily idanunsa da ƙyau cikin natan. Ai babu shiri ta janye nata zuciyarta na bugawa da sauri-sauri. Sai taji gaba ɗaya ma jikinta na neman fara rawa. Shi ko tsaf ya fahimci halin data shiga, dan haka ya saki murmushi cike da ƙeta. A ransa kuwa rayawa yake (Ba Abanki yace bazai bani ba sai na horu. Kafin na gama horuwar kema sai kin horu yarinya) a fili kam harɗe hannayensa yay a ƙirji kawai ya zuba mata ido. Ita dai ta miskile tana haɗa masa abincin a gabansa. Can ƙasan ranta luguden daka kawai zuciyarta keyi, jitake kamar ta zura da gudu, amma bazata yarda ta zubar da kanta a garesa ba... “Ehheem! Ehemm!!”. Gyaran muryar Fawzan ta maido AA daya zubama Maanal idanu a hayyacinsa. Janye idanun yay luuu ya maida kansa, Fawzan ya ɗage gira yana murmushi. Shima sai AA ɗin ya ɗage masa tasa girar irin (Miye?) ɗin nan. Dariya Fawzan ya sanya, tare da jan kujera kusa da AA ya zauna. Maanal data ɗan rage ɗaure fuskar da tayi ta ce, “Good morning Yaya F”. “Morning Ƙanwar Yaya F, Baby Oum, Autar Abah, sannan kuma Bastyn Besty”. Duk yanda taso dannewa bai yiwu gareta ba sai da ta saki murmushi tana turama AA duk abinda ta zuba masa, sai dai bata yarda ta kallesa ba. Sai ma hankalinta data maida kan Fawzan ta ce, “Yaya miza'a zuba maka?”. “Ai duk abinda kika san yayi daɗi zuba min kawai Lilly.” Murmushi Maanal ɗin tai tana jinjina kai. Sai da ta kammala zuba masa sannan ta koma cin nata. Suna gab da kammalawa Oum ta fito, duk da Maanal dama ba wani tana ci sosai bane ba. Oum na fitowa ma ta miƙe kamar wadda ke akan ƙaya. Cike da tsokana Fawzan ya hau yima Oum kirari, kafin ya gaidata. Itako tana dariya abinta cike da farin ciki. Sai ga babban yaya da su Naufal dake cikin shirin makaranta. Saheeba biye da su. Suma Oum ɗin suka shiga gaidawa cike da girmamawa, yaran kuma sukaje suka rungumeta. Itama Nibras ta shigo cikin shirin aiki, da alama ta makara ne. Idonta akan AA ta gaida Oum cike da ladabi, hakama babban Yaya sannan ta juya tana gaida AA ɗin daya juya yana magana da Naufal. A taƙaice ya amsa mata batare daya juyo ba. Maanal dake karantar yanayin kowa musamman Saheeba da tunda suka shigo taga ta mata wani irin kallo ta ɗauke kai a taƙaice ta ce, “Auntys barkanku da safiya”. Babu yanda suka iya daga Saheebar har Nibras ɗin dole suka amsa. Sai dai kowanne da kalar zafin da yake jin Maanal ɗin a ransa. Yayinda shigar tata ta saka zuciyarsu sosuwa. Duk da bawani kwalliya tayi ba, babu kuma wani ƙyale-ƙyale a tare da ita kamar nasu. Amma tayi matuƙar yin ƙyau mai sanyi. Ga ƙamshinta na fita a nutse babu wata hayaniya. Tunda kuma tai musu kallo ɗaya ta watsar da su a tasu fahimtar. Yanzu kuma ta jefesu da gaisuwar raini. Oho ita bama tasan sunayi ba. Tama maida hankalinta ga babban yaya suna magana... Shigowar Abah ta saka kowa maida hankalinsa kansa. Sai Mamy dake biye da shi riƙe da briefcase ɗinsa. Sosai Abah dake kallon zuria'ar tasa farin cikin ya mamaye ransa. A ransa rayawa yake (Nanfa duk mallakina ne, zuri'ata ce. Idan kuma ALLAH yaba Fawzan haihuwa da Ajwaad shima Fadeel aka ƙaro masa sai mu sake yawa). Mamy kam zuciyarta ce ta sosu da ganin wahalarta zagaye da kishiyarta. Tayi-tayi ta hana wannan zaman safen a sashen Oum tarasa yanda zatayi. Dan ita inma sun shiga gaisheta sama-sama ne, amma Oum kuwa anan ma suke breakfast wasu ranakun koda matansu sun girka sai su ƙi cin nasu sai sun zo nan musamman Fawzan da matarsa ke malalaciya..... Tunaninta ne ya katse saboda gaisuwar da Maanal ke mata. Amsawa tai fiskarta da murmushi, sai kuma ta tsargu da yanayin shigar Maanal ɗin. Ta ɗan saci kallon AA dake tsaye kusa da Maanal gab batare da suma sun farga da yanda suke ba. Dan ya miƙe ne zai amshi number a hannun Babban Yaya, kasancewar Maanal ɗin na tsaye a wajen suna magana da babban Yayan kuma sai tsaiwar tasu ta kasance gab-da-gab. Itama daba kallonsa take ba sam hankalinta bai kai da kasancewar kusancinsu ba duk da mayataccen ƙamshinsa ya addabi hancinta. Hirama Naufal ke mata tanata murmushi. Itama dai Nibras hankalinta akan AA da kasancewar Maanal ɗin a kusa da shi yake. Zuciyarta na mata zafi da jin kishin hakan. Ganin Maanal bata tare a sashenta ba ita kaɗai tasan a farin cikin da take ciki. Dan yanda take farin cikin har sai da Fawzan yay mamaki ma ya tambayeta. Amma sai tace da shi babu komai... Gaba ɗayansu abin sha'awa a tare suka fito wajen da gwarazan motocin mazajen gidan suke duk a wanke. Dan tun jiya Bola ya wanke su fes kasancewar aikinsa kenan. Yara aka fara sakawa a motar su ta makaranta, sannan Baban yaya ya shiga tasa. Abah ya shiga shima tasa driver a gaba yace Maanal ta shigo kusa da shi. Murmushi AA yay a kaikaice kawai ya shiga shima inda nasa drivern ya buɗe masa. Shima Fawzan ya shige tasa hakama Nibras da taji wani kalar daɗi ganin Maanal tare da Abah zata tafi ba AA ba. Cike da mamaki Mamy take kallon motar Abah, dan bata san da komawar Maanal office ba. Sai da duk motocin suka gama ficewa maigadi ya maida gate ya rufe sannan Mamy ta kalla Oum dake murmushi. “Wai nikam ƴarki badai aiki aka koma ba?”. Ƴar dariya Oum tayi, ta ce, “Ai na manta muyi maganar jiya. Da ƙyar muka samu mijinki ya yarda, shine aka kafa mana dokar bazata bi Auta ba nace munji”. Dariyar yaƙe Mamy tayi, a ƙasan ranta tana faɗin (munafuka abinda kika ƙullo kenan jiya dama. Ba komai zan yi maganinku) a fili kam sai cewa tai, “Ai ina bayansa yay maganinku keda ɗan naki”. “Oh na manta ƴar adawa ce kefa. Nayi nan”. Cewar Oum tana barin wajen. Dariya Mamy tayi kawai, sai da Oum tai nisa da wajen ta gimtse fuska da rakata da harara. Sai kuma suka kalla juna ita da Saheeba dake cike fam da takaici itama. Dan ita sai yau da taga Maanal da ƙyau fiye da ko yaushe taji zuciyarta ta sake girgizuwa. Maanal ba fara bace ba, amma irin Black beauty ɗin nan ce da ALLAH yayma wani kalar sassanyan ƙyawun fuska dana jiki dana fata. Ga idanu masha ALLAH. Ba namiji ba ko mata da yawa sun sha yaba ƙyawun halittar Maanal, a hakanma tana da ƙoƙarin sututurta jikinta ne. Dan bata shigar banza, ko ɗinki bazaka taɓa ganinta da matsatstse ba sam. Gata ƴar ƙwalisa dan tasan sirrin kula da jiki matuƙa. Rashin yawan fara'arta a yanzu kansa irinsu Saheebar shakkarta, dan sai suga kamar ta cika girman kai ne, ita kuma sam a gareta ba haka bane. Maganar ce kawai yanzu bata cika son yi ba ne..... __________★ ZARIA “Mom please ki barni naje. ALLAH acan nake son yin azumi nidai”. Harara Hajiya Majdiya ta wurga mata. “Ni kinji nace karkije ne Najma? Ni nace ki kira Mah-mah ki sanar mata, tunda ita tace kije mata azumi kika kuma amsa. Sai yanzu ne zakice kin fasa Abuja zakije. Kina gani kuma tunda muka dawo Rufaidah kullum cikin kira take akan yaushe zaki koma. Ita kanta Mah-mah ɗin jiya muna waya sai da tace yaushe zaki taho.” Sosai hawaye suka cika idanun Najma. Haushin kanta ya kamata. Miyasa ma ta amsa ma kakar tata zataje can ne. Wayar da sukai ɗazun da Yaya Fawzan ta sake dawo mata. Yanda yake roƙonta akan tazo Abuja tai azumi inba haka ba kullum zai kasance a hanyar Zaria ne. Kuma tasan sunyi alƙawarin ɓoye komai har sai nan da bayan salla Babba ta kammala exam ɗinta... Kamar wadda tunanin nata ya zaburar da ita tai saurin kallon Mom ɗinta. “Mom na yarda zan kira Mah-mah ɗin, har ma da Aunty Rufaidah ɗin”. “Sai ki haɗa da Babanki ma. Tunda shima kin san Kano kika gaya masa, kuma ya tsani magana biyu.” “Mom dan ALLAH ki taimaka min ke ki sanar masa”. “Wa? Ni? A'a kema kin san ganganne wlhy. Babu abinda ya shafeni. Kinga tashi ki ƙarasa min aiki malama kafin yarana su dawo school da yunwa”. Sosai Najma ta zunɓura baki tana miƙewa. Kitchen ta nufa dan ɗaura girki. Tana girkin tana neman mafita. Dan bata san yanda zata tunkari babansu ba kasancewarsa mutum mai zafi. Dama da gyar ta samu ya barta zuwa Kanon dan shi kam bai son yaransa suyi nesa da shi ko yaya. Harta kammala tana faman ƙullawa da kwancenwa. Sai da ta fara zuwa ta sanar da Mom ta gama sannan ta nufi ɗakinsu. Miss call har biyu ta samu daga Ya Fawzan. Ta ɗan waro idannunta waje. Kiransa ta shiga yi, sai dai harta tsinke bai ɗaga ba. Tana ƙoƙarin yin na biyu kiransa ya shigo mata. Cike da shauƙi tai masa sallama. Daga can yay ɗan murmushi da faɗin, “Uhm-uhm wannan ƙanwa tawa dai bata jin magana”. Sosai ta sake kwantar da murya, “Yaya dan ALLAH kayi haƙuri, ina kitchen ne Mom ta sani girki”. “Ba damuwa na haƙura ai Mom ce”. “Yauwa Yayana. Dama fa yanzu zan kiraka. ALLAH akwai matsala......” tsaf ta zayyane masa yanda sukai da mamanta. Murmushi yayi kawai, “Kinga karki damu, ni zan kira Grandma ɗin da kaina. Sannan ki shirya zanzo Zarian na ɗaukeki in sha ALLAHU ”. Cikin waro idanu kamar yana gabanta ta ce, “Baba fa?”. “Shima ki barni da shi”. “Yauwa yaya Fawzan shiyyasa nake sonka”. “Da gaske?”. Ya faɗa da wani irin shauƙi. Ai da sauri ta yanke kiran fahimtar katoɓarar da tayi. Ita kuma kawai irin tayi maganar normal ne bada wata manufa ba. Duk kiran da yay mata ƙin sake ɗauka tayi kuwa. Shi kuma daga can yayta murmushi. Tabbas kasancewarsa da Najma na bashi farin ciki, duk da kulawar da yake samu a gareta iya ta kalaman baki ce ta ɗara masa Nibras. Shi kaɗai yasan irin haƙurin da yake akan rayuwa da Nibras. Amma yana addu'ar Najma ta zama sanadin sharuwar hawayensa...... Itama dai Najma cike take da wani irin shauƙi, dan har tsakkiyar rai jin son Fawzan take yi. Kafin yanzu soyayya take masa na ƴan uwantaka kawai, amma lokaci ɗaya da bayyana mata manufarsa sai taji al'amarin ya zarce hakan. Yaya Fawzan shine irin mijin da take ma kanta fata. Wato mutum mai sauƙin kai. Gashi ƙyaƙyƙyawa ga nutsuwa da dattako. Sai dai kuma wani gefe na zuciyarta na jin shakkar matarsa. Duk da a zahiri Nibras ɗin ba wata masifaffiya bace, sai dai irin matan nan ne marasa sakewa da mutane.... Shigowar kira a wayarta ne ya katse mata tunani, a zatonta Ya Fawzan ɗin ne ya sake kira, amma sai taga Uncle Rafeeq. Idanu ta waro sosai, tare da ɗagawa da sauri. “Lah Uncle R kai ne?”. “A'a bani bane”. Rafeeq ya bata amsa cikin gatse. Da sauri tace, “I'm sorry Uncle mamaki nayi ne. Ina yini? Ya Aunty Nuwaira”. “Lafiya Lau muke. Miya samu wayar Aunty inata kira a kashe?”. “Nah-nah ce ya shiga da ita bayi ɗazun da safe ta tsunbula a ruwa, shine aka sakata cikin shinkafa”. “Tofa ALLAH ya kiyaye to, jeki kai mata taki”. “Okay Uncle. Amma dan ALLAH kafin na kai mata na roƙeka wani abu”. “Banda kuɗi nayi brock”. “Kai Uncle nifa ba kuɗi nake nufi ba”. “To ina jinki”. “Uncle kaga so nake naje Abuja nai azumi, sai aka samu matsala nariga na faɗama Baba Kano zanzo tun kwanaki, yanzu idan nace masa na canja bazai yarda ba, zai ma iya cewa duka a fasa......”.......✍️ _Mu haɗe a Maawad da wanda suka shirya🏃🏃🏃🏃😲_ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. 🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖🔟 ______________ ........“To ke wace gulmar ta saki canjawar, bayan naji Mah-mah da Aunty Rufaidah na maganar zuwan naki ma”. Baki taɗan tura gaba, sai kuma cike da shagwaɓa ta ce, “Ni Abuja nake so yanzu Uncle please, idan akai salla su kuma basai nazo musu ba. Kaga nayi ma Ya Fa... Uhm uhm Aunty Maanal alƙawari itama”. Tai saurin waskewa jin katoɓarar da ta nema yi. Jimm Rafeeq yayi yana nazarin sunan data so fara ambata. Sai kuma tunaninsa ya ɗan koma baya akan ganinsu daya dinga yi a bikin nan tare da Fawzan. Tabbas ya zargi akwai wani abu kam, sai dai rashin hujja ya sashi sakin zancen tun a lokaci..... “Uncle Please mana...” Ta katse masa tunani. Ajiyar zuciya ya ɗan sauke. Tare da faɗin, “Ba ruwana, kije ke ki samesa ba babbanki bane”. Sosai ta sanya masa kukan shagwaɓa. Dan haka yace yaji zai yi tunani ta kaima mamanta wayar.... Badan taso ba ta fita kai wayar, tana addu'a a ranta ALLAH ya ɗaurata akansa, dan tasan yanama Baban nata magana zai amince...... _________★ Kusan a tare motar Abah data AA suka iso MAWAAD COMPANY. Maanal dake murmushin hirar da Abah ke mata tabi ko'ina da kallo. Komai yana a yanda ta sanshi. Sai da Abah ya ƙara mata nasiha na karta sakarma AA fuska da Addu'a sosai sannan ya barta ta fito. Hango AA tsaye jikin motarsa yana waya yasata tsayawa har sai da motar su Abah ta fita. Numfashi ta sauke a hankali, wata irin ƙauna ta ɗa da mahaifi na sake mamaye zuciyarta akan dattijon arziƙi Abah. Tabbas alkairin Abah a gareta mai yawa ne, da baki bazai iya musaltashi ba ma. Jinsa take a ranta shi da Oum matuƙa gaya a matsayin mutane masu muhimmancin gaske. Wani murmushi mai sanyi ya ɗan suɓuce mata hawaye na taruwa mata a cikin ido tunawa da nasihar Oum ita kuma. Ita fa dariya Abah da Oum ɗin ke bata ma a kwana biyun nan, Abah na nuna mata ta hora AA, Oum na lallashinta ta yafe masa komai ya wuce su koma kamar da can baya da suke..... Tunaninta ne ya katse jin an riƙo hannunta da wani tattausan abu da ta tabbatar hannu ne shima. Sai kuma ƙamshin turarensa yay mata irin shigar zuruff ɗin nan ya wuce har tsakkiyar brain ɗinta yabar maƙaƙinsa a maƙoshinta. Cikin ɗan motsawar zuciya ta waiwayo, sai ko idanunta a cikin nasa daya wani tsatstsareta da su. Ƙwacewa numfashinta ya nema yi, ta fisgoshi da ƙarfi tana mai saurin juyawa ta kalla harabar Companyn. Sosai ma'aikatansu ke shigowa ciki, wasu a abin hawa wasu a ƙafa. Da yawansu idanunsu a kansu suke, duk da dai sai wani sinne kawuna suke wanda ta tabbatar na munafuncine kawai. Ƙoƙarin sake juyawa garesa ta sakeyi, dai-dai ya kawo ɗayan hannunsa zai zare handbag ɗinta a ɗayan hannunta. Hucin numfashinsa ya wani irin sauka mata a fuska. Gaba ɗaya sai tai mutuwar tsaye kawai, harya gama zare handbag ɗin ya koma tsaye sosai hannunsa a cikin nata. Batare daya kalleta ba can ƙasan maƙoshi ya furta, “Let's go”. Ƙin motsawa tayi, dan haka ya waiwayo yana kallonta. Da wani salon ƙanƙance idanu tamkar ya manta a inda suke tsaye, muryarsa acan ƙurya ya furta, “Ko goyo kike so?”. Yay maganar da ɗan takowa gabanta kamar zai duƙa ɗin ta hau bayansa. Ai a zabure ta riƙo hannunsa jikinta har yana ɗan rawa. Hakama muryarta na rawa ta ce, “Ya ilahi mi kake yi haka?”. Karo na farko ya saki wani shegen murmushi da ita kanta sai da zuciyarta ta motsa. Girarsa ɗaya a ɗage yana wani wara mata fararen idanunsa masu ƙyalli a cikin nata. Sai taji tsigar jikinta na tashi. Da sauri ta ɗauke kanta. Shima bai sake magana ba yaja hannun nata. Dole ta bishi yanzu kam suka fara tafiyar a jere. A nutse suke ɗaga ƙafafunsu su ajiye kuma a tare. Hakan yasa ƴan gulma sake nutsuwa a kallon nasu, harda masu ɗaukar hoto a kaikaice. Sarai AA na lure da komai, amma da yake gwani ne a iya basarwa da kama kai yayi tamkar ma bai san da wasu halittu a harabar Companyn ba bayan shi da ita. Ita ko kunya da nadamar ƙin saurin shigewarta tuni duk ta baibayeta. Securitys ɗin ƙofar kansu sunyi kasare suna kallon abin mamaki, yau boss riƙe da handbag ɗin mace. Macen da kowa yake cikin ɗunbin mamakin aurensu. Dan tunda akai bikin a companyn gulmar kenan. Burin kowa wannan ranar da zasu dawo kan aiki, dan kowa jima yake kamar bai taɓa ganin Maanal ɗin ba. Cikin sauri suka shiga miƙa gaisuwa ganin suna neman gota su. Tare da yi ma boss murnar aure da jajanta masa yaya jiki. A mamakinsu ya amsa harda ɗan murmushinsa. Duk da dama can ba wai yana wulaƙanta kowa bane, amma ganin murmushin boss haka arhar banza ai sai mai rabo. To a cikin ma suna shiga kowa yay tsit, waɗanda ke leƙensu ta windows da musu video duk sun koma mazauninsu da gudu. Gaba ɗaya Maanal ji take kamar ta zura da gudu, dan gaba ɗaya attention ɗin kowa ya dawo kansu ne. Ta gefe ido take kallon ganin yanda duk suka miƙe a tare cike da girmamawa, shima sai yaja ya tsaya. Da ɗaɗɗaya suka shiga miƙo gaisuwa. Hannu ya dinga ɗaga musu fuskarsa da sakewa amma ba murmushi yake ba. A mamakinta sai itama suka shiga gaisheta. Karo na farko ta ɗan ɗago ta dubesu, ba wani yawane da su ba dan ba'a gama zuwa ba. Nan kuma iya waɗanda ke a ƙasa ne, mafi yawansu ma cleaners. Guntun murmushi kawai tai musu. Fahimtar a takure take yasa AA ɗan kallonta tare da matsa hannunta dake a cikin nashi. Dubansa ta ɗanyi, a saman lips ya furta mata, “Muje”. Yanzu kam bata musaba ta bishi, dan hakan zaifi mata sauƙi ita kam. Duk da dai a ranta bata son binsa office ɗinsa department ɗinsu take son wucewa. Suna shiga elevator ta wani sauke ajiyar zuciya tare da janye hannunta dake a cikin nasa. Dariya ma shi kam ta bashi, dan haka ya taɓe baki da faɗin, “Matsoraciya, nine kika raina kawai”. Kallonsa tai baki a tunzure ta ce, “Waye matsoraciyan?”. Kamar wasu masu faɗan yara ya juyo yana riƙe ƙugu idanunsa ware a kanta ya ce, “Ke mana”. Itama juyowar tai tana matsowa gab da shi idannunta cikin nasa da yanayin harara hannayen nata a ƙugu kamar yanda sukeyi a da in suna faɗa ta ce, “Niba matsoraciya bace sai dai idan kai”. Matsawa shima yay ƙoƙarin yi gabanta sosai idanunsa a cikin nata. Baya ta shiga ja yana binta har suka dangane da bangon elevator ɗin. Sai da ya tabbatar ya matse mata ko'ina ta yanda ko numfashinta a sarƙe yake fita sannan ya ɗaura hannunsa ɗaya a bangon shima ya sake mata rumfa, still dai idanun nasa na'a cikin nata da take mar-mar da su na alamar tsoro amma a zahiri a dakenta take. Ranƙwafawa yay a kanta da ƙyau tsahonsu ya dai-daita, kafin ya sake matsar da fuskarsa gab-gab da tata tamkar zai haɗe bakinsu waje guda. Gaba ɗaya sai Maanal ta rikice, fuskarta tai ƙoƙarin maidawa gefe cikin in-ina da sarƙewar harshe ta ce, “Wa....w. wai miye haka kake yi?”. Cikin son ƙoƙarin hanata janye idanunta a cikin nasa tamkar mai raɗa ya furta, “Kulawa da ƴar Abah mana.” ya ƙare maganar yana hura mata iskar bakinsa akan idanu. Baki ta ɗan tura tana ƙoƙarin tureshi da yin mar-mar da idanun saboda iskar da yake hura musu, “To ni nace maka ina so?”. “Ai basai kin faɗa ba, Abanki ma haka yake so naga”. Kasa cemasa komai tayi, ga idanuwanta sun fara tara ƙwalla. Dai-dai nan ƙofar elevator ɗin ta rabe biyu ta buɗe kanta. Daburcewa Manaal tayi ganin mutane har kusan uku tsaye saboda itace ke facing ƙofar, shi kuma ya juya musu baya. Ai babu shiri takai hannu gefen cinyarsa ta mintsina cikin rawar murya da raɗa ta ce, “Mutane fa”. Idanu ya ɗan lumshe dan har yanzu hannunta na'a jikinsa taƙi sakin mintsinin data masa sai ma sake matsewa take sosai. Kaɗan ya waiwayo kansa ya kalla ƙofar elevator ɗin. Sai kuma yay wani kalan luuu da idanun cike da basarwa ya miƙe tsaye da ƙyau. Maɓallin rigar suit ɗinsa ya shiga sakawa tare da kallon hannunta dake a jikinsa har yanzu. Silently ya ce, “Sai fatan ya cire ne Besty”. Da sauri ta janye hannun nata, sai kuma ta yunƙura zata fice ya cafko hannunta. Cike da takunsa na nutsuwa da ƙasaita tamkar komai bai faru ba ma ya fito, su HOD dake wajen suka shiga musu barka da dawowa cikin girmamawa. “Thanks you”. Kawai ya faɗa a taƙaice ya jata suka bar wajen kanta a ƙasa ita dai. Sai da suka ɓace a wajen gaba ɗaya Director Steven ya kalla HOD da CFO fuska da murmushi ya ce, “Uhm dama haka boss yake”. Dariya HOD ya sanya, tare da faɗin, “Ai irinsu daman yan babu sauƙi ne ina gaya maka. Ai kowa ya shirya, dan sai an mana ƙurmus a companyn nan da soyayya”. Dariya suka sake sanyawa a karo na biyu, banda CFO da zuciyarta ke mata zafi da raɗaɗi saboda kishi. Tsahon lokaci take jin son AA a ranta duk da ta girmesa a shekaru, sai dai tana matuƙar ƙoƙarin dannewa ta yanda kowa bai taɓa fahimtaba a companyn. Shi kansa ta fahimci kamewarta ya sashi bata amanna kai tsaye, dan duk wadda zata nuna masa tana sonshi in har tana a kusa da shi duk iya aikinta sai ya canja mata waje. Hakan data fahimta yasa ita tazo da sabon tsarin kame kanta. Ita ɗin bazawarace, mijinta rasuwa yayi shekaru biyar kenan, bata taɓa haihuwa ba. Bata sake wani auren ba kuma har yanzu. Tun randa akai musu interview a companyn ta ɗaura idanunta akan CEO taji duk duniya shi kaɗai take so. Ƙyaƙyƙyawace itama ta gaske, gidansu kuma gidan kuɗi ne ƙwarai da gaske, tayi karatu mai zurfi, ko aikin nan tana yinsa ne dan ra'ayi kawai bawai dan buƙatar albashi ba, duk da dai AA mutum ne mai ƙoƙarin kamantawa ma'aikatansa albashi mai tsoka dako gwamnati albarka musamman daya kasance ƙasar tamu zalunci yayi gaba ba'a wadata ma'aikatan da albashi mai ƙyau..........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. 🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣1️⃣ ______________ ........Cike da farin cikin aikar da Mamy tai mata ta fito, dan dama hanyar da zata fita a gidan take nema sai kuma ga mafita ta samu cikin sauƙi. Abinda ya ƙara mata daɗi da Mamyn tace ta hau taxi tunda drivers ɗin gidan duk sun fita. Ɗaya ya tafi kai yara makaranta, ɗaya ya tafi da Abah ɗayan AA. Ita kuma tana buƙatar akai mata saƙon ne yanzun nan. Ba komai Haule ta fahimta akan Mamy ba, amma ta daɗe da gane wasu abubuwanta a gidan musamman akan fuska biyu ga Oum, kawai dai ba abinda ya shafeta bane shiyyasa bata gaɓa ɗaɗara kanta da ƙasa ba. Sai dai duk wani aiken Mamy ita take sakawa, ta yarda da ita ɗari bisa ɗari. Tasan kuma hakan nada nasaba da kasancewar Maman Nuratu ce ta kawota gidan. Sai dai abinda Mamyn bata sani ba Maman Nuratun ta kawota ne dan tai mata aiki a gidan, yayinda ita kuma Maman Nuratu bata san Sille takema aiki ba a kansu su duka da AA. Can gaban wani tsohon Company Haule tace mai taxi ya sauketa. Ta zaro kuɗinsa ta basa sannan ta tura kai ciki babu ko ɗar. Kai kawai mai taxi ɗin ya girgiza zuciyarsa na sosuwa da ganin yanda yaran mu na hausawa suka lalata kansu. Kowa yasan wajen nan maɓoyar ƴan daba ce da manyan ƙasa ke amfani da su wajen ta'addanci, shiyyasa ko anzo an kama su basa wuce ranar ake sakinsu su dawo. Ya tabbatar yarinyar nan kodai kayan shaye-shaye zata saya ko kuma mu'amular banza. Shi dai yaja taxi ɗinsa yay gaba. Tunda Haule ta shigo cikin tsohon companyn sosai yaran Sille dake zaune daba-daba wasu na shaye-shaye, wasu na wanki, kai kowa dai na hidimar gabansa tamkar wanda suka samu gida suketa gaisheta dan kowa a cikinsu yasan yarinyar oga ce. Ita ko cike da jin kai take amsa musu harta dangane da idan ɗakin Sille yake. Bacher ce ta langa-langa, daga ciki kuma katako, sai dai an fenteshi tsaf ta yanda bazaka taɓa yarda katako bane ba. Ɗakin babbane sosai, akwai gado a ciki da kujeru set guda, sai freight da television harda speakers harda AC. Ƙasan ɗakin kuwa tils ne tsaf. Zaune yake a kujera ya wani barbaje gabansa kwalaben giya ne har uku, sai dai ba giyar yake sha ba taba ce a hannunsa kunnesa maƙale da waya alamar magana yake, daka gansa kuwa kaga Sillen na gasken gaske, dan sirrine sosai tamkar zai karye ko in iska mai nauyi zata iya yin gaba da shi. Tunda ta shigo ya zuba mata ido, tana ƙarasowa gabansa yasa ƙafa ya taɗota ta faɗa a kansa, matseta yay a jikinsa tare da manna mata kan tabar hannunsa a damtsen hannunta. Ƴar ƙara tai da ƙanƙame jikinta saboda zafin wuta, sai yay murmushi da yarda tabar a ƙasa ya shiga shafa mata wajen da har ya ɗashe dan ya ƙonata. A haka ya kammala wayar, ana yankewa daga can bai wani tsaya komai ba yay wurgi da ita gefe ya ɗauka Haule cak ya nufi gadon ɗakin da ita..... Sai da suka gama masha'arsu sannan ta miƙe a ɗan rikice tana faɗin, “Baby bara na wuce. Aikana matar can tayi gidan su Nuratu nakai saƙo”. Ta miƙa masa wayarta tana cigaba fa faɗin, “Gashi na ɗakko maka yau da safe, dan ita da shi duk sun koma aiki”. Kamar yanda bai tanka mata ba tun ɗazun yanzu ma batare daya ce komai ba ya amsa wayar daga kwancan da yake. A zabure yay wani kalar tashi zaune yana waro idanu waje. Sai kuma ya nufi drawer ɗin dake a ɗakin ƙarama ya buɗe, kayan ciki ya shiga watsowa a ƙasa har ya samu damar ganin abinda yake nema. Ita dai Haule tsoratama tayi da yanayin nashi, da sauri ta miƙe tsaye tana kallonsa. Juyowa yay inda take idonsa akan wani hoto daya ɗakko. “K duba min nan ko idona ne? Data cikin hoton nan da wannan duk mutum ɗaya ne?”. Karo na farko kenan dayay mata magana cikin buɗaɗɗiyar muryarsa mara daɗin saurare da tafi gangar jikinsa girma. Amsar wayar tata tayi da hoton ta zuba musu ido itama. Sai kuma ta ɗago tana kallonsa. “Baby tabbas wannan duk mutum ɗaya ce, kawai dai anan bata ƙarasa kaiwa mace bane ba. Dama kasan matar AA ɗin?”. Bai tanka mata ba, sai wani irin naushi daya kaima bangon katakon ɗakin yana faɗin, “Yanzu ne yaƙin na gaske zai fara”.. Sakare Haule tai tana kallonsa. Sai dai ko kallon inda take bai sake yi ba ya nufi bayin dake ɗakin ɗan ƙarami na wanka, wanda shima dai ɗin na langa-langa ɗin ne.. Wanka yake yana dariya sosai kamar mahaukaci sabon kamu. Jinsa yake a wani irin nishaɗi mai girman gaske daya daɗe baiji a zuciyarsa ba. Ajwaad ya auri Maanal fa? Eh lallai yanzu ne za'ai wasa mai zafin gaske tsakaninsa da shi. Tabbatacen alwashine wannan a garesa sai ya nakasta Ajwaad da Maanal. Dole ne yayi RAMUWAR GAYYA DA TAFI GAYYA zafi. Shine fa Sillen karan gero mai wuyar tsagewa, idan kai nasarar tsagewar baka yanke ba kai mai nasara ne. Uban daba yake a yanzu mai kujerar ƙarfin iko. Ajwaad! Maanal! Ku jira sakamako.... Ya kwashe da wata shegiyar dariya yana kaiwa bangon langa-langan duka har sai da Haule dake shirin tafiya ma ta firgita. Hakama yaransa dake can ta waje duk sai da suka kallo ɗakin da mamakin minene ya saka ogan nasu nishaɗi haka ne?... _Tofa, mike faruwa ne? Wanene kuma Sille? Miyake nufi da yanzu ne wasan zai fara? Menene tsakaninsa da AA ko nace Darma Family da har ya shafi Maanal yake ajiyar hotonta?. Hummm kumuje zuwa kudai cakwakiya ce ta gaske fa🏃🏃🏃😀._ ___________★ Suna ƙarasa shiga cikin office ɗin Maanal ta ƙwace hannunta daga cikin na AA. Babu musu shima ya saketa. Bai kuma ce komai ba ya nufi kujerarsa. Ko'ina a tsaftace yake ƙal a office ɗin. Ga wani ƙamshi mai kwantar da zuciya na tashi. Files ɗin dake a table ɗin nashi tule yabi da kallo, sai dai an ajiyesu a tsare dan kowa yasan shi ya tsani ganin waje rakwacam ba tsafta. Hannu ya kai a hankali ya kunna computer ɗin saman desk ɗin, kafin ya ɗago idanunsa ya zuba akan Maanal dake a tsaye har yanzu. Kallonsa take yi itama, sai dai yana ɗagowa ta kauda kanta. Baki yaɗan taɓe, sai kuma ya ɗauka kan waya ya danna 1 tare da kaiwa kunnensa. Dai-dai an ɗauka. A taƙaice ya furta, “Zo ciki”. Bai jira amsa ba ya yanke kiran. Maanal ya kalla fisha ya ɗauke idanunsa, ciki-ciki ya ce, “Malam sit”. Harararsa ta ɗanyi, sai kuma taje ta zauna dan bata son wanda taji yace yazo ya shigo ya ganta a tsayen kodan nasihar da Oum da Abah sukai mata na darajta kanta ga ma'aikatan companyn. Bawai tazama mai girman kai ko wulakanta kowa ba. A'a ta mutunta kanta da kame kanta yanda ya dace dai matsayinta na matar ogansu. Inba haka ba mutane da yawa zasu fara amfani da ita a yanzu domin cimmasa a ciki da wajen companyn. Hakama mata dake ƙulafucinsa a ciki da waje zasuji shakkar nunata koda da zunɗene balle isa gabanta. AS ne ya shigo bakinsa da sallama bayan yayi knocking AA ɗin ya bashi damar shigowa ciki. Batare daya kalleta ba saboda girmamawa ya wuce sum-sum kamar munafuki inda boss yake. Hankalin AA a computer shima, batare daya ɗago ba ya ce, “Daban kiraka ba bazakazo kamin bayanin abinda ya dace ba kenan Haneef?”. “Ayi haƙuri sir, naga kana tare da Auntynmu ne shiyyasa. Amma ai min afuwa”. Komai AA bai sake cemasa ba. Sai tulin documents ɗin dake zube ya kalla. Matsowa AS yayi kusa da shi domin fahimtar abinda yake nufi. Cike da nutsuwarsa ya shiga masa bayani yanda ya kamata. Shi kuma yayi shiru yana saurarensa. Hakama Maanal dake latse-latse a waya kunnenta na kansu ne tsaf. Fin minti ashirin kafin su gama magana da AS ya fita. Dan haka ta ɗago ta kalla sashen da yake zaune. Ganin zai fara aikinsa kamar ya manta da ita yasa ta miƙe. Wayarta ta saka a handbag ɗinta sannan ta nufesa, batare data ƙarasa inda yake ba ta ce, “Nifa zan tafi”. Yi yay kamar baijita ba tsawon sakanni kafin ya ɗago ya kalleta. Ganin yanda ya kafeta da idanu yasata ɗauke nata tana sake tsuke fuska. Shima janye nasan yay ya maida ga aikinsa yana faɗin, “Nace miki na gama dake ne?”. “Amma kasan fa aiki nazo ko. Kuma Abah yace ka fita harkata”. “Hakane Aunty Maanal yi haƙuri ƴar gidan Abah”. A yanda yay maganar tasa ta ɗan hararesa. Dan irin gatsen da yake mata kenan ko ada can idan tace yay abu kota takura masa idan yace bazaiyi ba sai ya dinga kiranta da Aunty...... Takaici ya saka Maanal ɗauke hankalinta daga gareshi gaba ɗaya. Tsohon mintuna arba'in yanata aikinsa kamar ma ya manta da ita akai knocking ƙofar. Sai da ya kalla sashen da Maanal take sannan ya bada izinin shigowa. AS ne ya shigo yanzun ma. Batare daya kalletaba yanzu ma yay mata sannu. Maimakon amsawa saita samu kanta da harararsa, dan haushin ogansa ya shafe sa shima. Shi dai da yake ba kallonta yake ba baima san tanayi ba. Cikin girmamawa ya ƙarasa gab da AA, murya a ƙasa yake masa bayani like ba'a son taji komai. Sai ta sake tunzura. AA ya jinjinama AS kansa, tare da faɗin, “Shike nan kuje ka kaita, su kuma su bari after break na ɗan rage aiki”. “Okay sir”. AS ya faɗa yana nufar inda Maanal take. Kansa a ƙasa ya ce, “Aunty bismillah”. Miƙewa tayi batare da tace komai ba, sai dai ta kalla inda AA yake zaune cikin yanayin harara. Sai ko akai sa'a shima ita ɗin yake kallo. Gira ɗaya ya ɗage mata, sai kuma ya kashe ido ɗaya cike da neman rigima da son tunzurata. Aiko fuska ta yamutse tare da janye nata fuuu tabi bayan AS bayan ta zuba masa harara. Rakata yay da idanu har ta fice gaba ɗaya. Guntun murmushi yayi yana mai lumshe idanunsa ganin yanda take cika da batsewa. A kan lips ya furta, “Ƴar gatan Abanta kenan” yay wani murmushin shaƙiyanci yana datse lip da haƙori.........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. 🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣2️⃣ ______________ ........ KANO Ganin yanda ya shareta kwana biyu bai sake gwada son kwana ɗakin ba yasa yau ta saki jiki, balle ma daya shirya ya fita wajen aiki. Su uku ne kawai a gidan, ita sai ƙannensa biyu ƴammata da suka zo mata wai yini. Dan yana fita babu jimawa suka zo. Sune suka mata gyaran gidan tsaf da tsohon kwana biyu bai samu shara ba. Dama dai yaran anguwa dake ɗan shigo mata take ritsawa su mata. Ko kuma baƙin da sukazo ganin gida idan taga ƴan tagajan-tagajan ne sai ta saka su. Wasu ma danginsu ne, amma da yake su dama ƴan gidansu an musu shaidar girman kai da raina mutane bata jin ko nauyi take cewa su mata aiki koda sun girmeta. Su kuma da shegen kwaɗayi da neman gindin zama sai suyi ɗin kuwa. Ƙannen nasa ma sai faman yamutse-yamutse take musu. Sajeeda sarkin zuciya har tace su tafi kawai, da ƙyar Khadijah ta lallaɓata. Aikin ma kinyi tayi sai Khadijan ce tayi mafi yawa a ciki. Huznah dai ana bedroom an ɓararraje ana barci, dan daga charting ta ɓingire a wajen. Ana idar da sallar Azhar Sageer ya dawo gidan. Yaji daɗin ganin babu kowa sai ƙannensa, ga kuma mutuniyar tasa na sharar barci. Hankalinsa kwance ya kaɗa su Sajeeda gida, yaje kuma ya kulle ƙofar gidan sannan ya koma ciki. Hajiya Huznah anji daɗin fanka barci yay daɗi sai taji hannu na yawo a jikinta. A firgice ta farko sukai ido huɗu kuwa da Sageer. Wani irin ɓacin rai ne ya sata yunƙurawa a masife, sai dai gogan yariga ya mata ɗaurin huhun goro da jikinsa. Ƙarfi kuma ba ɗaya ba, dan ko motsin arziƙi bata iya tayi ba, tana ji tana gani kuma ya shiga yin yanda yaso da ita batare daya nuna damuwa da hawayen da take ba. Cikin sauƙi da nuna mata mazanfa maza ne yay kiɗinsa yay rawarsa tare da more sadakinsa. Itako tana faman kuka da zaginsa, zagi kuma na rashin mutunci. Nunawa yay bai damu ba, dan ta ceci kanta data kawo mutuncinta, harga ALLAH bai kumayi tsammanin hakan ba daga gareta, musamman idan yay dubi da wayewar yan gudansu ta tsiya. Sai dai kuma mahaifinsu mutumin kirki ne, dan tsaye yake akan tarbiyyarsu babu wasa. Hakama Yazeed yana nasa ƙoƙari kasancewarsa babba kuma namiji. Yaso taimaka mata amma taƙi yarda, dan haka yay ficewarsa yabar mata ɗakin ransa fes. Kuka bana wasa ba Huznah taci, daga ƙarshe tai kiran wayar Hajiya Basariyya. A lokacin Hajiya Basariyya na zaria tare da ƙawarta cikin wani ƙauye wajen wani malaminsu. Sosai gabanta ya faɗi jin yanda Huznah ke kuka. A rikice tace, “Ke dan ubanki minene zakisa zuciyata ta buga”. Kasa magana Huznah tayi, sai da ta sake jan wani ƙugin kukan sannan ta ce, “Ummy fyaɗe yamin”. “Fyaɗe kamar ya?”. “Wlhy Ummy fyaɗe, ina barci a ɗaki kawai yazo ya haike min, nayi duk yanda zanyi na ƙwaci kaina amma na kasa. Kuma da yake shi tsinanne ne ya fita yana min dariya. Wlhy ji nake kamar na kashe shi Ummi, gashi nan ko tashi na kasa yi wata irin azaba nake ji a jikina”. Jagwab Hajiya Basariyya ta kai zaune, kafin ta ce, “Amma dai wannan yaro anyi matsiyaci ɗan iska. Munafiki sum-sum da shi. Wlhy Huznah kin cucemu kin cuci kanki. Yanzu duk faɗi tashin da nake na ganin kin baro wannan kurkukun gidan kin koma inda daula take ki huta muma ahalinki mu huta shine kikai saken da matsiyacin yaron nan ya ƙwace abinda shine kimar taki. Yanzu ubanmi zaki kaima AA Darma ɗin to?”. Kuka sosai Huznah ta sake fashewa da shi mai ƙarfi ma kuwa tana faɗin, “Na shiga uku Ummi, wlhy ina sonshi, bazan iya haƙurin rasashi shi ba. Ki taimakeni ALLAH ba laifina bane ba, kullum rufe masa ƙofa nake kamar yanda Aunty tace nayi shine munafikin ya dawo da rana azzalumi dan ya cutar dani. Ummi dan ALLAH ki taimakeni kada na rasashi.....” kuka ya sarƙeta. Kasa magana Hajiya Basariyya tayi, sai Maman Yaseerah ce ta amshi wayar...... _________★ Mamaki ne sosai ya kama Maanal ganin inda AS ya kawota. Wato sabon Office da aka bata kafin tafiyarta hutu, ita sam tama manta da batunsa. Office ne madaidaici da aka ƙawata aka kuma haɗa mata komai daya kamata da zata iya buƙata. Kujerar zamanta da desk mai ɗauke da computer guda ɗaya, sai visitors chairs dake gaban desk ɗin. Ta gefen damarta haɗaɗɗiyar kanta ce ta show glass da aka shirya kayan buƙata irin wanda mai zane zai buƙata...., Hatta da pensul gasu nan tari-tari kamar a shagon sai dawa. Sai daga ɗan gaba yan kujeru guda biyu suma da visitors zasu iya zama ko ita idan tana bukatar hutawa, daga bayansu akwai fright da wata ƴar kanta ƙarama an ajiye dispenser da coffee machine sai kofuna a cikin glass kanta ɗin na shan shayi dana shan ruwa. Office ɗin a cikin jerin officers na Designers Directors yake. Daga floor ɗin nasu kuma sai nasu oga kwata-kwata dake a floor ɗin ƙarshe. A tsakaninsu ma ba sai ka hau lifter ba su steps ne kawai. Sallama AS yay mata bayan sake tayata murnar sabon office duk da a waccan ranar duk sun mata. Karan farko tai guntun murmushi tare da amsa masa. Yana fita ta sakama ƙofar key, sai kuma ta jingina a jikinta tana murmushi. Wannan fa shine DARE ƊAYA ALLAH KANYI BATURE. Tayi wata biyar kacal matsayin Junior watch designer yau gata a wanan matsayin. ALLAH kaine abin godiya, kai ke maida bawa sarki, kai ke badawa ga wanda kaso a lokacin da kaso. Kai ke sauya al'amura daga wautar tsarinmu zuwa ƙyaƙyƙyawan ikonka. Ya rabbi ka cigaba da jagorantar rayuwata bisa ikonka ba wayona ko dabarata ko tsarina ba... Takawa ta cigaba da yi cikin office ɗin a nutse har zuwa kujerar zamanta mai laushi da ƙyau tanata sheƙi na sabunta. Sai da tai addu'a sannan ta zauna, ta lumshe idanunta tare da yin wani kalar juyi tana dariya ƙasa-ƙasa. Sai kuma ta tura kujerar jikin desk ɗin sosai ta ɗauka wayarta. Sai da ta duba taga Didi Shahidah da Amaal da Ammie duk a online sannan ta shiga group ɗinsu tai video call. Babu ko ɓata lokaci duk suka shiga yin joining. Sun san da zaman office su duka, amma basu taɓa ganinsa ba. Aiko ta shiga nuna musu komai daki-daki. Sai da aka gama murna sannan Ammie ke tuhumarta miyyasa ta dawo aiki haka da wuri, kwana tara fa kenan. A shagwaɓe ta ce, “Ammie su Oum ne fa sukace na dawo”. “Shi Ajwaad ɗin fa?”. Shiru tai ta kasa cewa komai. Ammie ta ce, “Humm. Maanal nidai zan baki shawara kibi mijinki, abinda ya faru ya riga ya faru, kar kiga Aban Fadeel nata baki kariyar nan kice kin samu damar bijirewa kema. Bance kada kibi umarninsa ba, amma ki ƙyautata alaƙarki da mijinki kinji”. Sosai idanun Maanal suka cika da ƙwalla. Muryarta na rawa ta ce, “Amma Ammie shike nan komai da yay min yasha ruwa? Har yanzu fa babu wata nadama a tattare da shi. Ganin komai yake tamkar ma dolene a tsakanina da shi. Idan shi dake namiji bai sauke girman kansa ba Ammie sai ni na zubar da kaina a garesa?.” “Ni bance ki zubar da kanki ba. Amma ki kula da duk abinda zai dinga kasancewa a tsakanin ku. Maanal kawai kinƙi yarda ne, amma Ajwaad ya jima da yin nadama, sannan yana sonki fiye da zaton kowa. Bafa dole sai namiji ya buɗe baki yace ma mace yana sonta bane zata yarda. Irin su Ajwaad a aikace suke nunawa musamman idan akai dubi da yanayin shaƙuwarku”. Baki sosai Maanal ta tura gaba, “Ammie kawai dai baya laifi ne a wajenki”. “Oh haka kikace? Shike nan nayi shiru. ALLAH ya daidaitaku cikin sauƙi. Ni bara naje gidan Nene zanje ALLAH ya sanya albarka. Sai a sake riƙe gaskiya a kumayi aiki tuƙuru”. Kai ta jinjina tare da faɗin, “In sha ALLAHU Ammie”. Ammie na fita Amaal da Shahidah da suke sauraren faɗan Ammie suka shiga tsarama Maanal abubuwa. Dan suma dai suna goyon bayan kada Maanal ta sake tayi sake har sai ya kwantar da nashi kan. A cewarsu ita Ammie bata san halin mazan zamanin nan ba ZUMA NE SAI DA WUTA. Balle ma irin su AA miskilai ga giyar kuɗi na hura su. Kiran wayar da akai ya saka Maanal tuna a office take, haka suma su Shahidahn duk suna wajen aiki. Ai babu shiri sukai sallama akan idan sun koma gida ayi zaman. Wayar ta ɗaga, Director Mustapha ne. Bayan sun gaisa yake sanar mata akwai meeting nasu na designers zuwa 12 inji HOD. Yanda yake mata magana da girmamawa sai ma abin ya bata dariya. Itafa su rufa mata asiri suna oganninta bai kamata suna mata haka ba. Maganar aiki daban da matsayin da suke kallonta da shi yanzu. Dan haka ta ɗauki aniyar yin maganar a wajen meeting ɗin in sha ALLAHU. Ganin akwai sauran lokaci ta fara duba ayyukanta na baya, wanda ta fara bata ƙarasa ba da wanda zatama gyara. Sosai take aikinta a nutse, cike kuma da shauƙi. Akwai aikin da suka fara fa Yaqub, basu kuma kammala ba, tana ganin kafin aje wajen meeting ɗin kuma ya kamata su kammala shi. Kan waya ta ɗauka bayan ta duba cote ɗin department ɗinsu tai kira. Bayan an ɗaga tare da gaisheta batare da tasan wanene ba ta buƙaci ganin Yaqub a office ɗinta, ba kuma tare da jiran amsa ba ta ajiye.. Cike da gulma daga can Zaharadeen ya ce, “Matar boss ce fa da kanta.” Kusan su duka idanu suka waro, Yaqub ne kawai yay kamar ma bai jisu ba. Zaharadeen ya cigaba da faɗin, “Yaqub kai take nema, dan ALLAH idan kaje ka nema mana damar ganinta, dan ya kamata muje mu miƙa gaisuwa mu taya murna muyi ALLAH yasa alkairi ko ALLAH zaisa ta manta da abinda ya faru baya”. Miƙewa Yaqub yayi yana mai girgiza kansa. A fili ya furta, “Oh ko kunya ku bakuji ba yanzu ko ita da kanta tace kuzo sai kuje dan neman kusanci da ita”. “Da gudu ma kuwa. Ko tunani ka kai kaɗai zakaci arziƙin?”. Cewar Ema.. Murmushin takaici Yaqub ya saki, batare da yace komai ba ya nufi hanyar fita abinsa ɗauke da folder ɗin daya haɗa drawing pappers ɗin daya san zata nema a wajensa. Yana gama ficewa Jameel ya ce, “Ɗan baƙin ciki, idan fa bamuyi da gaske ba guy ɗin nan sai ya kankane komai ta yanda ko kallonmu bazata ringa yi ba balle ta tuna munrayi tare anan matsayin abokan aikinta. ALLAH dai yasa ta manta da abinda ya faru baya. Ni damuwata ma randa ta kamamu muna gulmarta ni da Teemo da Hafiz”. Caaa kowa yay yana faɗar albarkacin bakinsa. Sai dai duk suna cikin fatan ALLAH yasa Maanal ta yafe musu sudai. Daga haka suka ɗora da gulmar ashe Maanal ɗin tasan abinda ta taka akwai alaƙa tsakaninta da boss shiyyasa take musu girman kai. Gashi nan cikin ƙanƙanin lokaci tazo ta samesu ta kuma shallake abinta matsayin ogarsu. Kai kai wannan al'amari da taɓa zuciya yake..........✍️ _😀 ALLAH ya shirya yan gulma a duk inda suke🤣😂_ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. 🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣3️⃣ ______________ ......A office ɗin Maanal kuwa sai da taima Yaqub magana sannan ya ɗan saki jiki suka ƙarasa aikin a ɗan gurguje saboda lokacin meeting ɗinsu yayi. A tare da shi suka fita a office ɗin. Hakan yay dai-dai kuma da sakkowar AA daga sama, da'alama daga office ya fito. Bayansa CFO ce da Bussines Director. Da alama suma wani abun zasuyi mai muhimmanci, dan elevator suke ƙoƙarin nufa. Wani irin zuba musu ido AA yayi ɗan guntun sakewar dake fuskarsa na ɓacewa. A ransa ko ayyanawa yake, (Yarinyar nan bazata fita sabgar yaron nan ba ko?). A zahiri kam yanda ya wani ɗauke kai sai ka rantse baima gansu ba. Amma ita Maanal tana gannin kallon banzar daya watsa mata na fisha ta ƙasan idon. Amma itama sai ta wani basar kamar bata gansu ba ta nufi hanyar conference room tana cigaba da wayarta. Dan magana take da Amrah data kirata suna fitowa. Shi dai Yaqub ɗan matsawa yay ya gaishesu. CFO ce kawai ta amsa da Bussines Director. Boss yi yay kamar baiji ba ta shige elevator. Kasancewar shi Yaqub ba kallonsu yake ba bai san yaya boss ɗin yake ba. Sai da suka shige ƙofar ta rufe sannan shima ya nufi conference room ɗin..... _________★ Rafeeq na zaune Nuwaira a jikinsa tana masa hira amma shi hankalinsa na wani tunani daban. Maganar zuwan Najma Abuja ce keta masa kai-kawo a rai. Kodai zai yi amfani da wannan damar ya sata tai masa wani aiki. Wani gefe na zuciyarsa kuma na farin ciki da fatan tabbatuwar abinda yake hasashe a tsakanin Najma ɗin da Fawzan. Dan auren wani ƙarin GARKUWA ne ga aunty Babba bayan na AA da Maanal. Tun jiya yake son yin waya da Maanal, dan yana son su tattauna wasu abubuwa masu muhimmanci sai dai bai san a yanda zata kalli al'amarin ba. Sannan alaƙarsa da ita kafin aure zai iya saka AA yaji wani abu a ransa idan yaga kiran duk da yasan har abada Ajwaad bazai kawo mummunan abu a garesu ba, amma yana da ƙyau ya kiyaye. To amma a yanzu batun Najma sai ya zaburar da shi, a ganinsa hakan wata hanya ce mai sauƙi da saƙon da yake so zai isa ga Maanal ɗin dan ita kawai yake so a wannan gaɓar tasan hakan saboda ya yarda da ita ɗari bisa ɗari, ya kuma gamsu da tarbiyyarta da soyayyar da takema ƴar uwarsa, soyayya ce irin ta ɗa da mahaifi..... “Babie!”. Nuwaira ta kirashi a cikin kunne cike da shagwaɓa. Kallonta yay da sauri, sai kuma ya sauke ajiyar zuciya tare da sakar mata murmushi ya sake jawota jikinsa. Hancinta ya kama ya ɗan ja. “Kefa yarinyar nan shagwaɓaɓɓiya ce. Minene kuma?”. Baki ta ɗan tura masa. “Bakai ne ka tafi tunani ba inata kiranka bama ka jina. Minene ke damunka wai? Ina lure da kai tun jiya baka da sukuni”. Sake lakace mata hanci yayi. Tare da faɗin, “Tunaninki nake fa”. Tai murmushi mai ƙayatarwa. Duk da tasan ba hakan bane cike da farin ciki tace, “Godiya nake Babie. ALLAH ya ƙara mana farin ciki da kwanciyar hankali”. “Amin my angel, harma da soyayyar juna”. Ya faɗa yana ƙanƙameta a cikin jikinsa. Wata irin soyayyarta na ratsa jini da ɓargonsa. A tabbas har randa aka ɗaura masa aure da ita zuciyarsa Maanal take so, amma ganin halin da suka samu AA ya sake sakashi ɗaukar ɗamarar yaƙi da zuciyarsa akan sadaukarwarsa. Dan ya sake tabbatar da AA ya fisa buƙatar Maanal. Shine kuma ya cancanci samunta ɗin. Koda ya shigo ya samu Nuwaira a ɗakinsa matsayin mallakinsa baiyi wani yunƙuri ko tunanin zasu sami juna ta sauƙi ba, sai dai kuma labarin ya canja saboda karfin tasirin nasihar iyayensu a garesu, gashi shi kuma yana a cikin wani hali na buƙatar abokiyar rayuwa. Cikin ƙudirin samawa kansa sauƙi kawai ya yarda ya tunkareta, sai dai a lokacin da komai ya kankama sai labarin ya canja, dan tamkar ya shiga sabuwar duniya ne da zazzafar soyayyarta. Na biyu haƙurinta da biyayyarta, Nuwaira bata da kwaramniya, ga sauƙin kai da kyakkyawar fahimta. A ɗan kwanakin da suka samu tare ya fahimci hakan sai soyayyarta ta ƙara tasirantuwa a zuciyarsa. Dan haka yake baje kolin amarcinsa yanda ya kamata, itako tana nuna juriya da dattako.. Ɗaukarta yay cak ya nufi bedroom. Zizzilewa ta farayi cikin dariya tana faɗin, “My R please Aunty Rufaidah fa zanje na taya aiki a kitchen”. “A nan ma ai aikin zakiyi, yama fi na Aunty Rufaidah lada”. Ya faɗa yana tura kai cikin ɗakin da sumbatar goshinta...... __________★ Tattaunawa ce sosai ta kasance a zaman meeting ɗin na su Maanal. Domin abubuwane masu muhimmanci da suke son kawowa na gyara a matsayinsu na artists ɗin companyn. Daga ƙarshe Director Mustapha ya sanar dasu batun da za'aje ƙasar Chaina a kansa. Wadda tun kwanaki CEO ya gabatar, ya kuma bada damar kowanne ɓangare su bada mutane biyu da zasu samu horaswar ta kwanaki goma kacal in sha ALLAHU. To zuwa yanzu kowane department na ƙoƙarin kai nasu, dan haka suma ya kamata sukai nasu ɗin. Dan haka aɗan nazari da su manyan sukayi cikin satin daya gabata, da ayyukan kowa da suka duba da ƙwazonsa sun yanke waɗanda suke ganin sun cancanci zuwa. Aifa nan kowa ya shiga gyara zama da fatan ya kasance shine. Duk da kuwa wasu a cikinsu an taɓa zuwa dasu wasu ƙasashen akan irin hakan. Dan ba sabon abu bane duk bayan wata shida Company na irin wannan zuwa ƙaro sanin kai da kai ɗin dan ƙaruwar ilimi ga ma'aikatansu. Director Steven ne ya miƙe yay bayanin waɗanda suka samu wannan dama. Wato Maanal Habib Giro da Yaqub Nuhu. Tuni fuskokin su Zaharadeen sun canja, ko tafin da akayi ma da ƙyar suka tafa. Maanal da Yaqub suka nuna farin cikinsu. Duk da ita dai Maanal bata so haka ba. Musamman data tuna maganar da AA ya taɓa mata akan tafiyar. Sai dai tana fatan ALLAH yasa bada shi za'ai ba. Suna tasowa a meeting ɗin yay dai-dai da lokacin break. Ransu Zaharadeen a ɓace suka wuce. Kowa naji a ransa akwai makirci a wannan tsarin. Dan a ganinsu kawai an zaɓi Maanal ne dan tana matar boss a yanzu, ita kuma ta zaɓi Yaqub saboda suna tare. To aiko lallai zasusha mamaki, dan ko zasuyi amfani da wannan damar akan Yaqub game da alaƙarsa da Maanal ɗin sai yabar Companyn nan da ƙafafunsa. Ai sun san dai boss ba mahaukaci bane ba zuciyarsa ba dutse bace zaiji kishi... Salla kowa yay ƙoƙarin zuwa gabatarwa. Bayan an idar masu tafiya cin abinci suka tafi, masu komawa office suka koma. Harda Maanal kuwa a masu komawar, duk da yau batazo da abincin nata ba. Hankalinta kwance ta fito daga elevator tana danna waya fuskarta da murmushi dan kuwa charting take da su Aneesa. Dai-dai ta danna zata ma Zeezah vn aka zare wayar a hannunta, da sauri ta ɗago idanunta, sai ko cikin na AA dake kallon wayar alamar karanta charting ɗin yake. Hannu takai zata amshe wayar, ya janye jikinsa batare daya daina karanta hirar tasu ba. Kamar zata saki kuka ta ce, “Amma dai haka babu ƙyau ALLAH”. Bai tanka mata ba bai kuma daina karantawar ba, sai ma fara tafiya da yayi, binsa tayi tana jinta duk a ruɗe, dan tsokanarta su Aneesan keyi a kansa. Acewarsu har an gama cin amarcin ne ta dawo aiki. Amasar data tura musu cewar (Ai ba sai an gama a gida ba zasu cigaba da ci a office) yasa suka tasata gaba da shaƙiyanci irin na ƙawaye. Itako tana bama kowa amsa dai-dai shi. Dan tafi sakewa tai musu surutu a charting fiye da zahiri. Son amsar wayar yasa Maanal bata ankara ba har sun shigo office ɗinsa. Sai da yakai zaune a rukunin kujerun ta ƙara kai hannu zata fige wayar batare daya daina abinda yake ba ya saka mata ƙafa ta faɗo jikinsa sannan. Da sauri ta kalla inda take, aiko dai a cinyarsa take ɗare-ɗare babu ƙarya. Miƙewa tai yunƙurin yi, yasa hannunsa ya sake rungumota da ƙyau, tare da saka idanunsa cikin tsakkiyar nata da wani salon ɗage gira sama. “Bake kika ce za'aci amarcin a office ba! Miye na pretending kuma amarsu ta ango?”. Yanda yay maganar kamar mai raɗa ya saka tsigar jikinta tashi, ga kunya na neman halakata tamkar ba tana tare da Bestyn ta dake goyata a bayansa ba ko bayan kekensa, wanda suke cin abinci a kwano ɗaya. Wanda yasha yimata wanka da mata tsarki, wanda yasha wanke mata underwears harda masu jini a jiki batare da ƙyanƙyami ba. Wanda y.....” Knocking ƙofar da akai ne ya katse mata tunani, bama tasan ta daka tsalle ta miƙe daga jikin nasa ba gaba ɗaya. Bai hanata ba, amma ya kamo hannunta ya zaunar a gefensa gab, kafin ya danna remote ƙofar ta buɗe a hankali ta hanyar rabewa biyu. Kallo ɗaya AS yay musu ya duƙar da kansa. A haka ya ƙaraso gabansu ya ajiye basket ɗin hannunsa yana faɗin, “Sir gashi in ji driver”. Bai jira amsarsa ba ya juya ya fice, ƙofar ta koma a hankali ta rufe kanta. Ajiyar zuciya Maanal da kanta ke ƙasa ta saki. Kallonta yayi, ganin ta kauda kai gefe ya ɗan laɓe baki, sai kuma ya gyara zama ya fara fiddo kulolin da ke cikin basket ɗin wanda babu tantama yasan na gidansu ne, kuma tabbas daga Oum suke. Sai da ya gama buɗe komai ƙamshin abincin ya bulale office ɗin sannan ya juya yana kallon Maanal dake satar kallon sa shi da abincin ta gefen ido. “Mrs Darma aikin kine wannan! Tashi ki bani abinci”. Kallonsa ta juyo tayi, ya ɗage mata gira ɗaya. Cike da neman magana ya furta, “Kin san dai anan babu Aban naki ai balle kice bazaki yi ba”. Sosai ta tura baki gaba. Batare da tace komai ba ta matsa kaɗan bakin kujerar ta ɗauka plate ta fara haɗa masa abincin. Idanu kawai ya zuba mata, ransa fes da kasancewarsu a hakan. Sai yanayin ke tuna masa wani lokaci acan baya daya shuɗe. Murmushi ne ya shiga ƙawata fuskarsa dan tamkar a yanzu ne komai ke faruwa. Harta kammala bai farga ba, sai da ta ɗan bubbuga spoon a plate ɗin sannan. Cike da basarwa ya haɗiye murmushinsa, batare daya ce komai ba ya gyara zama abinsa ya hau cin abincin bayan ya ɗauka wani spoon ɗin ya ƙara alamar nata. “Nifa na ƙoshi”. “Ɗura kike so kenan? Garama kici da arziƙi”. Tasan zai aikata kuwa. Dan haka ta ɗauka spoon ɗin kawai itama. Jujjuya abincin kawai take amma ta gagara kai lauma ko ɗaya, baice mata komai ba, face ɗibowa ya nufi bakinta da shi. Yanda yay wani kicin-kicin da fuska babu alamar wasa yasa ta amsa ɗin. “Gulmammiya dama abinda kike so kenan”. Ya faɗa yana dungure mata kai tamkar ba shine yay maganar ba. Ita sai abin ma ya bata dariya, amma bata dara ɗin ba ta dai yi murmushi dan ya tuna mata baya. Idan ya lallaɓata taƙi cin abinci musamman in tana fushi da shi sai ya ɗiba ya bata a baki tare da dungure mata kai sannan yace mata gulmammiya. Murmushin nata ba ƙaramin ɗaukar hankalinsa yay ba, amma yasan yana yin magana zata birkice masa, dan haka yay shiru ya cigaba da cin abinsa yana ɗiba yana bata kuma. A mamakinsu sai gashi su ci sosai abinsu. Sun kammala kenan tana gyara wajen kiran waya ya shigo masa, AS ne ya sanar masa ma'aikata fa sun taru domin masa murnar aure. Amsa ya basa da cewar suna zuwa. Daga haka ya yanke kiran. “Oya let's go mutane na jiranmu”. Da mamaki Maanal ta bishi da kallo dan ya nufi inda rigar suit ɗinsa take, “Wai mi?”. Ta faɗa cikin sigar tambaya. Batare daya kalleta ba yace, “Zasu tayamu murnar aure ne”. Kasa sake cemasa komai tayi, ta ƙarasa tattare komai kawai ta maida a basket ɗin sannan ta miƙe, veil ɗinta ta gyagygyara tare da ɗaukar wayarta a inda ya ajiye sannan ta nufi ƙofa inda yake tsaye yana jiranta.........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. 🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣4️⃣ ______________ .........HUZNAH Sosai gaɓɓan jikinta ke mata ciwo, duk yanda take tunanin iya daurewa hakan ya gagara. Kuka kam taci harta godema UBANGIJI. Zagi babu kalar wanda Sageer bai sha ba a wajenta. Gashi bata sake jin motsinsa ba a gidan sai bayan magrib. Tana zaune wujiga-wujiga har yanzu bata gyara jikinta balle sauke nauyin sallolon dake a kanta ya shigo ɗakin. Kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa, batare da damuwa da hararar da take binsa da shi ba ya wuce bathroom ɗin ɗakin. Ruwa mai ɗumi ya tanada sannan ya fito, batare da Huznah data cusa kanta a ƙafafunta tana sabon kuka na takaicin ganinsa ta ankara ba taji kawai an cicciɓeta. Mutsu-mutsu ta farayi na son sauka, amma da yake ƙarfi ba ɗaya ba ko gezau ya shige bayin da ita. Tana kai masa duka da komai da fisge-fisge ya taimaka mata. Sai da ya tabbatar ruwan ya ratsa mata jiki ta samu ƴar nutsuwar da yake buƙatar ganinta a ciki sannan ya fito a binsa muryarsa babu alamar wasa ya bata umarnin yin wanka tare da gargaɗinta mintuna biyar ya bata tazo tai sallolin data tarama kanta. Idan kuma ba hakaba zata sha mamaki. Haka kawai taji wata masifaffiyar shakkarsa, babu ɓata lokaci ta gabatar da duk abinda ya sanyata ta fito tana ɗingisa ƙafa ɗaure da towel. Duk da ta bashi dariya da tausayi duk sai ya danne, fuskarsa babu fara'a ya miƙa mata riga da hijjab, komai batace ba ta ɗauka ta sanya ta fara gabatar da salla. Sai da yaga har tayi raka'a biyun farko sannan ya fita domin zuwa massallaci shima...... ______★ Ƙarfe biyar Abah ya kirata yace ta fito su wuce. Lokacin tashi yayi, amma akwai aikin da take yi, sai dai bazata iya cema Aban haka ba, sai kawai ta tattara aikin da abinda duk zata buƙata ta tafi da su bayan ta kashe wutar office ɗin ta fice. Kai tsaye inda AS ya nuna mata zata dinga ajiye key dan masu shara da safe su gani ta ajiye. Batare da tabi takan AA ba ta fice abinta ta samu su Abah. Cike da girmamawa ta gaisheshi sannan ta shiga driver ya maida ƙofar da dama shine ya buɗe mata ya rufe. Fuskar Abah da murmushi ya danƙa mata tsarabar da yayo mata, dan shi fa har yanzu kallonta yake tamkar su Naufal a gabansa. Cike da jin daɗi tai godiya ranta fal farin ciki... Sam AA bai san da tafiyar Maanal ba. Aiki ya masa yawa harya shiga over time ɗin nasa na tsiya. Kiran magrib ya sashi kallon ƙawataccen agogon dake a office ɗin. Ɗan tsai yay cikin tunanin Maanal data faɗo masa a rai. Sai kuma ya ɗauka waya yay kiran AS dan yasan tunda bai shigo masa sallama ba shima yana nan bai wuce ba. Ilai kuwa hakanne. Yana ɗauka daga can AA ɗin ya furta, “Zo mana”. Ya yanke kiran. Babu jimawa sosai AS ya shigo, sai da ya masa sannu da aiki kafin yace, “Gani sir”. Batare da AA ya ɗago daga abinda yake ba ya ce, “Besty fa?”. Sam AS bai gane kan zancen ba, dan haka ya ce, “Sir Besty kuma?”. Karan farko AA ya ɗago ido ya kallesa, sai kuma ya dafe goshi ya ɗan murza. Cike da basar da suɓutar bakin nasa ya furta, “Maanal”. “Oh I'm sorry Sir, ai inaga tun five ta tashi”. Jimmm AA ɗin yayi, sai kuma ya jinjina kansa batare da ya sake cewa komai ba yay masa nuni yaje. AS na gama fita AA yaja numfashi ya fesar, sai dai a zahiri baice komai ba. Saima miƙewa da yay ya nufi bedroom yay alwala. Koda ya fito tattara dukkan abinda zai buƙata yay a cikin briefcase ɗinsa, dan dolensa yay aiki a gida kam daren yau. Yana fitowa AS ya amshi kayan hannun nasa ya haɗa da nashi shima, a tare suka sauka ƙasa. Sai da suka fara salla a massallaci su ƴan tsiraru dan akwai irinsa ƴan over time sannan suka nufi gida shi da drivern sa, AS ma tashi motar ya shiga ya nufi nasu gidan..... Lokacin da AA ya isa gida tuni Maanal ta jima da hutawa. Dan har taya Oum girki tayi kasancewar rigimar Abah ta tilasta mata komawa kan duty. Bayan sun kammala ne suka nufi ɗaki yin salla. Ana idarwa tai zaman yin karatun Alkur'ani Oum kuma na lazimi har akai isha'i sannan suka fito. Sashen Abah Oum ta tafi, hakan yasa Maanal zama ta shiga duniyar tunanin nata na fama. Gaba ɗaya kwanakin nan hankalinta ba'a jikinta yake ba. Dan al'amarin su Mamy yayi matuƙar jijjiga mata zuciya. Dauriya kawai take tana danne komai dan kar kowa ya fahimta musamman AA da Oum. Hatta a office yau dauriya kawai take da ƙarfin hali. Dan tasan idan kowa bai fahimci halin da take ciki ba shi zai fahimta. Shiyyasa ma ta toshe duk wata hanyar kasantuwarsu a waje guda a gidan kafin yau, yayinda shi kuma ta fahimci yana fushi da ita akan hakan duk da dai yanda suka kasance yau a office kamar ya huce... Bayan wucewar Oum zaman shurun ya isheta, gashi tana son yin waya da Didi Shahidah. Tasan kuma dole ta nemi inda zata kawaice idanun mutane kodan abinda zasu tattauna. Fitar Oum zuwa sashen Abahn ya bata damar ɗaukar novel ɗinta da glasses ta yafa ƙaramin veil a kanta batare data ɗaura ɗan kwalin atafar doguwar rigarta ba ta ɗauka ruwa da popcorn dake ajiye a dining. Compound ta fito, sai da ta gama bin ko'ina dake ƙwanyar da hasken security light da kallo sannan ta nufi hanyar inda AA ya taɓa kaita kwanaki dake da swimming pool, dan tasan can ɗin ma sharr ne da hasken tamkar rana. Shigarta wajen ya sakata lumshe idanu saboda busowar wata ni'imtacciyar iska mai ƙanshin furanni a cikin hancinta, murmushi tayi, zuciyarta na sake zumuɗin ƙarasawa gaban ruwan. Sai dai me tana ɗaga ƙafa dole ta koma ta tsaya cak, sakamakon saukar muryar Mamy cikin kunneta. Magana take a kausashe, cike kuma da bada umarni. Kai kawai Maanal ta girgiza cike da takaici zata juya dan bama ta buƙatar jin baƙaƙen maganganun da Mamyn ke faɗa akan Oum, amma mi sai taji Muryar AA a bazata yana faɗin, “Amma Mamy yanzu baƙya ganin hakan zai zama wani abu daban idan nace yarinyar nan ta dakata da zuwa Company na. A yanzu fa Maanal matata ce, a ganina ta wuce dukkan wata alfarma kuma sai iko ma da take da shi akan komai na. Kema fa gashi faɗa kike kullum akan Abah, dan na tabbata da ace baku haɗa miji da Oum ba amintarku har abada bazata taɓa rawa balle har kukai ga wannan matakin. Duk da dai daga ɓangarenki ne aka samu rashin fahimtar, dan har zuciya wlhy Mamy kina a zuciyar Oum da girma da daraja. Ni dai Mamy bazan gaji da baki haƙuri da faɗa miki gaskiya akan wannan al'amarin ba. Dan ALLAH ki ajiye makamanki akan Oum, bana son lokaci yakai ƙurewar da wani a gidan nan zai ji wani abu akan hakan, musamman sauran ƴan uwana da Abah. Sannan batun aurena da Maanal kiyi haƙuri, hakan wani hukuncine na UBANGIJI dake rubutacce a ƙaddararmu, kodan yanda abubuwa suka faru a baya, da yanda suke a yanzu yakamata mu fahimci al'amarin nan fa mai girma ne.....” “Hakane ubana”. Mamy ta faɗa cike da hasala da gatse kuma. Murmushi AA yayi na tsantsar damuwa. Sai kuma ya ɗan kalleta da idanunsa da suka kaɗe sosai. “Kiyi haƙuri idan kalamaina sunyi nauyi da yawa Mamy, har abada ni mai biyayya ne a gareku ku duka ukun nan. Sannan zan bama kowanneku kariya daga cutarwar ɗan uwansa.....” “Kai ka sani kuma wannan. Na baka kafin nan kafin fara azumi kazo min da cikakken bayani akan ma'anar Maawad kamar yanda na faɗa maka, tare da dukkanin takardun kadarorin ka...” “Mamy ki gafarceni, wlhy ban san yanda zan iya tunkarar Oum na amshi abubuwan nan a hannunta ba”. “Okay haka kace? Toni zan tunkareta na amsa tunda ba uwata bace ba ai”. “Mamy Please....” Ko kallonsa batai ba ta wuce fuuu. Ja baya Maanal tai ta laɓe a ɗan lungun da akai adon wajen. Dan bata buƙatar Mamyn ta ganta. Zuciyarta kuwa wani irin zafi take mata, matuƙar tausayin AA na ratsa mata ɓargon jiki. Kenan shi Mamy ta bayyana masa ainhinta, tana kuma amfani da damar tana tursasa masa yin abubuwa dan tasan yanda Oum keda muhimmanci a garesa. Murmushi ta saki mai matuƙar ciwo, sai kuma da sauri ta share hawayenta ta bar jikin bangon tamkar yanzu ne take shigowa saboda jin ƙarar taku alamar shine zai fito. Bayyanarta ya sashi tsayawa cak, itama sai ta tsaya ɗin tana kallonsa, dan duk yanda taso basarwa ta kasa hakan. Tausayinsa ne ke neman fin ƙarfin zuciyarta. AA da ganin Maanal ɗin ya sashi jin shock wani irin tsinkewa zuciyarsa tayi, addu'a yake ALLAH yasa yarinyar nan bataji tattaunawarsa da Mamy ba. Dan bazai taɓa son hakan ta kasance ba sam. Cikin son basarwa ya shiga haɗiye nannauyan abinda ke tsaye a maƙoshinsa ya daidaita fuskarsa. Sai kuma ya cigaba da takowa a hankali har zuwa gabanta. Kayan hannunta ya ɗan zubama ido, kafin ya janye ya maida kan fuskarta. Cikin tausasa murya da ƙanƙanceta ya furta, “Daga ina?”. “Sama”. Ta bashi amsa. Murmushi yayi a karo na farko, tare da lumshe idanunsa ya sake buɗewa a kanta. “Bakin nan dai bazai daina ma mutane baƙar magana ba ashe?”. Samun kanta tai da ɗan sakar masa murmushin itama sai kuma ta kauda kanta gefe tana mai laɓe bakin kaɗan. Shima murmushin ya sake saki dan nata murmushin wani sanyi ya saukar masa a zuciya. A hankali kuwa ya saki ajiyar zuciyar tare da matsowa gab da ita. Matsawa tayi baya tana mai waro masa idanun kaɗan, irin na (lafiya dai?) shima sai ya bita. Danganewa tayi da bango, hakan sai ya bashi damar dafe bangon da hannu ɗaya ya mata rumfa da jikinsa. Gaba ɗaya ta jita kamar a keji, ga wani irin watsal-watsal da zuciyarta ke mata, sassanyan ƙamshin turarensa kuwa na saukar mata da kasalar jiki da gaɓɓai. Shima ɗin wani irin haurawa yaji jininsa nayi a saman kai, a hankali muryarsa cike da taushi da nauyi ya furta, “Bestie, please give me a hug mana”. Sosai zuciyarta ta harba, duk yanda taso daurewa ta kasa, idannunta ta ɗago slowly ta sauke akansa, shima kallon nata yake, sai taga kamar idanunsa na ƙyallin hawaye, duk da tasan wannan normal ne a garesa, dan in har ma yana cikin farin ciki sosai idanun na fari tas-tas zakaga tamkar kuma an bisu da mai ne. Amma na wannan yanayin babu abinda take hangowa a cikinsu sai tsagwaron damuwa da ɓacin rai........✍️ _To bazawarin Huznah dai kazo da bidia, runguma kuma? Gaskiya wannan salon cin amanar Abah ne kawai 😂_ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. 🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣5️⃣ ______________ ........Samun kanta tai da sakar masa sassanyan murmushi, tare da buɗe hannayenta a hankali alamar bashi damar daya buƙata. Idan yace zuciyarsa bata nema tarwatsewa ba a wannan gaɓar yayi ƙarya, amma wannan ba lokacin tunani ko nazari bane. Duk da ya mata tsaho sosai cike da jin illahirin jinin jikinsa na narkewa ya wani irin shigewa jikin nata ya rungumeta tsam har sai da ta ɗan rumtse idannunta. Sosai tausayinsa ya shiga marmashe mata illahirin zuciya, dan kasancewar kanta kwance a ƙirjinsa tana iya jin yanda zuciyarsa ke bugawa da sauri-sauri, ga hucin numfashinsa na sauka a kunnenta da zafi-zafi. Sun kai tsahon mintuna biyar a haka, ita harma ta fara jin ƙafafunta sun mata nauyi. Sai taji shima kamar ya mata nauyin. Muryarta na wani irin komawa sanyi ƙalau ta ce, “You're sleepy?”. Maimakon bata amsa sai ya girgiza mata kai kawai. Sai kuma ya miƙe tsaye sosai ya ɗagota itama daga ƙirjin nashi ta tsaya da ƙafafunta. Fuskarta ya kafe da sassanyan kallo, ita sai ma ya bata kunya. A hankali ta risinar da idanunta ta koma kallon yatsun ƙafarsa dake fes-fes cikin tattaunsan baƙin takalmin daya sanya. Hannu yasa ya ɗago fuskar tata ta hanyar kamo haɓarta cikin hannunsa. Maimakon ta kallesan kamar yanda yake buƙata sai ta lumshe idanun nata. Murmushi ya saki kaɗan, cike da son tsokanarta ya ɗan ranƙwafo ya dai-daita fuskar tasu numfashinsu na sauka a fuskokin juna. Cike da shauƙin yanayin nasu ya furta, “Besty!”. Kasa amsawa tayi, dan gaba ɗaya jinta take kamar ta nutse a cikin ƙasa. Shima fahimtar bazata amsa ɗin ba sai ya sake sakin murmushi irin mai maƙalewa a gefen bakin nan. Cikin maida muryar tasa ƙasa-ƙasa sosai tamkar mai raɗa ya ce, “An bani Hug saura kis....” Ai baima kai ga ƙarasawa ba ta waro idanunta gaba ɗaya warrr a kansa. Sai dai kasancewarsu gab da juna ya sata maidawa kuma da sauri ta lumshe tare da janye jikinta baya tabar wajen da sauri. Dariya sosai ta bashi, amma sai baiyi ba ya saki ɗan murmushi yana miƙewa tsaye da ƙyau ya zuba duka hannayensa a cikin aljihun farin jeans ɗin wandonsa ya bita da kallo. Sai da ta zauna batare da ko waiwayensa tayi ba ta buɗe novel ɗinta ta sanya eyeglasses a idonta sannan ya shiga takawa a hankali zuwa inda taken.. ★ Ya jima tsaye a inda ta barshi yana kallonta, kafin ya tako shima a inda taken. Kujerar dake facing ɗinta ya zauna, batare da yace mata komai ba ya zuba mata idanunsa kawai hannayensa duka harɗe a ƙirjinsa. Yanda ya zuba mata idanun nasa masu kaifi ya sakata daburcewa ta daina fahimtar abinda ma ta fara karantawa. Amma a zahiri bazaka taɓa tunanin a rikicen take ba dan ta maze ƙwarai da gaske kamar bata san da shi a wajen ba. Dai-dai nan kiran Oum ya shigo wayarsa. Kasancewar ringing ɗinta na musamman ne ya saka shi dakatawa daga faɗar abinda yay niyya ma Maanal. Wayar ya ciro daga aljihu yana gyara zamansa da ƙyau. Sai dai idanun nasa har yanzu a kanta tamkar ya samu television ɗin kallo. Cike da tsokana ya furta, “Assalamu alaikum uwargidan Abah har a ALJANNA”. Murmushi Oum tayi daga can. Cike da jin shauƙin ƙaunar Autan nata tace, “ALLAH to ya tabbatar Autan Oum ɗinsa, sannan tare da ku Bestyn bestynsa.” Murmushi AA yayi mai faɗi, sai kuma ya ɗan saci kallon Maanal a miskilensa ya furta, “Shike nan dai Oumna kin rama 1-1 kawai.” Dariya sosai Oum tayi, sai kuma ta ce, “Dama zance kazo kaci abinci gamu nan zuwa tare da Abahn ku zaici abincin tare damu”. “I'm so happy, Oum! gamu nan”. Daga haka ya yanke batare da Oum ta fahimci inda (gamu nan) ɗinsa ta dosa ba. Yana ajiye wayar ya zare book ɗin Maanal tare da ɗaukar kwalin popcorn ɗin nata da goran ruwan ya ce, “Oya let's go Oum na kira”. Komai bata kawo a ranta ba ta miƙe kawai. A jere suka fito duk da ba wata hira suke ba. Sai da sukazo fitowa ne cike da neman magana ya gwargwaɗa mata magana a kunne. Da sauri tai gaba zata barsa saboda kunya, yayinda murmushi ya ɗan ƙawata fuskarta batare data shirya hakan ba. Shima murmushin yake yi dan haka kawai murmushin nata ya saka shi jin nishaɗi. Ai cak Abah da Oum dake fitowa daga sashensa suka tsaya. Galala Abah ya saki baki yana binsu da kallo, yayinda Oum ta gimtse dariyar dake neman suɓuce mata da ƙyar. Suna tsaye kamar gumaka AA da Maanal suka shige sashen Oum batare da su sun ma farga da su ba. Gyaran murya Oum tayi kaɗan, hakan ne yasa Abah maido da idanunsa kanta, harrarta yayi. Daƙyar ya iya gimtse dariyar tayi gaba tana faɗin, “let's go tunda gasu can.” bata jira cewarsa ba tai gaba tana murmushin data kasa riƙewa. Suna zuwa ƙofar sashen Oum Maanal ta zame tai hanyar baya ta kitchen ita adole bata son a gansu tare da AA. Bata san wanda take gudun su gansun ba sun riga sun gansu. Samun su Inte na haɗa abincin da zasu kai dining sai kawai ta shiga tayasu. AA kam daya shige shi kaɗai dariya ma ta bashi. A ransa yace (Magulmaciya, kina so kina kaiwa kasuwa). Fawzan kawai ya samu a falon yana kallo. Zama yay kusa da shi. Fawzan ya dubesa da ƙyau, sai kuma ya ɗan matsa da fuskarsa yana shinshina shi. Harararsa AA ɗin yayi, ciki-ciki ya ce, “Miye?”. Da ƙyar Fawzan ya gimtse dariyar dake cinsa, cikin ɗaure fuska shima kamar yanda AA ɗin yayi ya ce, “Yada tsarguwa haka Malam, ka bari na gama tantancewa mana. Naji ne kana ƙamshi kamar na turaren Lilly.” Irin ɗan waro idon nan AA ɗin yayi, ya ce, “Kai yaya Fawzan ido ka koma samin?”. “Oh da mikake tunani? Kasan dai bazan bari aci amanar Abah ba. Kuma zanma ƙanwata garkuwa”. Rasa ma abin cewa AA yay, sai kawai ya zubama Ya Fawzan ɗin ƙasaitattun idanunsa. Sosai Fawzan ya kwashe da dariya, dan yasan ya gama kaishi maƙura kenan. Ai idan kaga Auta ya rasa abin faɗa to yakai maƙura kenan... A haka Oum da Abah suka shigo suka samesu. Gaishesu sukayi, suka amsa Oum na faɗin, “A'a ina Baby na kuma?”. Fawzan ne ya bata amsa da, “Ai tunda na shigo ban gantaba Oum, maybe tana sama ko?”. Kai Oum ta jinjina tana jiran AA ya bada amsa, amma ya basar abinsa tamkarma baijisu ba. Sosai shima Abah ke satar kallon AA ta gefen ido ransa fal mamakin, dai-dai nan Maanal da su Inte suka fito a kitchen. Dariya taso kama Oum, amma ta danne da ƙyar idonta akan Maanal ta ce, “Oh ashe kina kitchen Auta”. Kai Maanal ɗin ta jinjina tana murmushi da satar kallon AA daketa latsa waya kanshi kwance a kafaɗar Fawzan hankalinsa kwance like baima san mike faruwa ba. Juyawa tai tana gaida Abah dayay Zuru yana kallonsu su duka. A ransa ko faɗi yake (Aiko zakuci ƙaniyarku ku duka) a zahiri kam amsawa yay cike da kulawa. Daga haka suka ɗunguma dining cin abinci..... A nutse suke cin abincin, yayinda Oum da Abah ke ɗan hira Fawzan kuma da Maanal. AA kam hankalinsa nakan waya komi yake oho masa. Abincin ma bawani ya maida hankali bane a cinsa. Wayar Oum ta zare daga hannun nasa, yako kalleta a shagwaɓe. Harararsa tayi tare da nuna masa abinci tana faɗin, “Ni tunda ka tashi ciwon nan kake neman maida abinci abokin gabarka Auta. Oya maza yanzu naga plate ɗin nan, in ba haka ba ɗura zan maka”. Dariya Fawzan yayi, Maanal ma ta kasa riƙe nata murmushin saboda ganin yanda AA ɗin yay da fuska. A dai-dai nan Mamy ta shigo sashen da sallama. Gaisheta Fawzan yayi bayan duk sun amsa mata sallama, tare da faɗin, “Naje sashen yaran nan sukace kina wanka”. Cikin danne takaici Mamy ta ce, “Eh sun faɗa min”. Ledar hannunta ta ajiye a gaban AA da tunda ta shigo ya maida hankalinsa ga cin abincinsa. Maanal kam sai satar kallon Mamyn take bayan ta gaisheta itama. Ajiye ledar ya saka AA ɗagowa ya kalleta a karo na farko, hakama su Abah kallon ledar suke. Murmushi ta ƙawata fuskarta da shi, tare da juyawa tana kallon Oum. “Bara na aiki ɗanki gidan Aunty tunda dai yaji sauƙi, na manta shaf har drivers ɗin gidan sun tafi gashi da sassafe zasu wuce lagos”. Fuskar Oum babu wani damuwa ta ce, “Eh ya kamata kam a kai mata su a daren nan. Auta sai ka maida hankali ka gama ko kar dare yayi, duk da dai kai ba tsoron fitar daren kake ba”. Kansa kawai ya jinjina batare da yayi magana ba. Dan shi yasan babu wani saƙo. Mamyn ce ta kafa masa sharaɗin zuwa yaga Nuratu ya kuma bata kayan da zata bashi yace inji shi wai Ramadan basket. Zama Mamyn tayi suka cigaba da hira da Oum da Abah, sai kawai AA ɗin ya miƙe badan ya kammala cin abincin ba, dan zuciyarsa gaba ɗaya jinta yake a ƙuntace, amma miƙewar da zai yi suka haɗa ido da Maanal sai wata dabara ta faɗo masa. Guntun murmushin iya shege yayi, cike da shagwaɓa ya dubi Abah. “Abah dan ALLAH ka bani aron ƴarka ta rakani tsoro nake ji”. Atare gaba ɗayansu suka ɗago suna kallonsa, ya sake narke fuska kamar zai yi kuka. “ALLAH Abah da gaske nake”. Ai kasa daurewa Fawzan da Oum sukai suka sanya dariya. Abah kansa da ƙyar yake iya danne tasa dake neman kufcewa. Maanal kam baki da hanci tama saki tana kallonsa, yayinda Mamy ta cika tayi fam fa takaici har hakan ya kasa ɓoyuwa a fuskarta. Cikin dariya Oum ta ce, “Please Abansu a taimaka mana, ai bazasu daɗe ba yanzu zasu dawo”. Fawzan ma yace, “Abah ayi haƙuri ta rakashi kada yay mana kuka ko kura ta cinyeshi a hanya dan tsoro. Kasan Besty da Besty duk tsanani tare suke zuwa aika”. Kai Abah ya girgiza, tare da faɗin, “ALLAH ya shiryeka Ajwaad. Jiba yanda ka wani ɓata fuska like zakama mutane kuka. Shike nan kuje, amma ina nan ina jiran dawowarku, idan kuka daɗe kwanakin zan ƙara”. “Thanks You sweet Abah”. AA ya faɗa a hankali. Nan ma kan Aban ya girgiza kawai, yayinda Oum ke faɗin, “Baby tashi ku tafi kinji”. Ji Maanal tayi kamar ta nutse dan kunya. Duk da kuwa a shekarun baya hakan ba komai bane a tsakaninsu. Dan ko tana gidansu aka aikesa zaije yace tazo ta rakashi kida cikin anguwa ne. Haka itama idan aka aiketa ko yana gida agaban su Abah ɗin zatazo tace masa (Besty zoka rakani aika) amma sai yau gashi tana jin hakan kamar sabon abu. Sarai AA na lure da mugun kallon da Mamy ke masa, amma ya fuske abinsa, sai ma nufar sama da yay ganin Maanal na niyyar warware ƙaramin veil ɗin kanta alamar da shi zatama fita take nufi. Da kallo duk suka bisa, Fawzan kuwa na masa tsokanar daya saba da kirari. Babu jimawa ya dawo da mayafin da yafi na kan nata da ke kamar na yara dan na Abaya ne. Wanda ya miƙa mata ɗin ta kalla, sai kuma ta ɗan tura baki gaba. Wancan ta cire ta amshi na hannun nata ta sanya, zata nufi saman itama ta maida Oum tace ta kawo kuje kawai kar dare yayi. Oum ɗin ta ba, shi kuma ya ɗauka ledar Mamy da takaici ke neman bombing mata zuciya suka fice..........✍️ _Abah da kasan kura kaba ajiyar nama da baka bayar ba😂🥱_ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. 🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣6️⃣ ______________ .......Wata Nurse da Sageer ya kira anan anguwarsu na tsaka da duba Huznah kiran Hajiya Basariyya ya shigo wayarta. Kasancewar yana a kusa da ita shi ya kai hannu ya ɗauka dan ita ana mata ƙarin ruwa ne. Shine ya fara yin sallama, dan haka Hajiya Basariyya tai ɗib daga ƙoƙarin maganar da tai niyyar yi. Da ƙyar ta iya amsa masa gaisuwar da yake mata. Kafin ya ƙara cewa wani abu ta yanke kiran. Murmushi kawai yayi baice komai ba. A ransa kam dariyar ƙeta yake da faɗin (Mama ai sai kuma haƙuri, ƙiyayya ta ƙare tunda ruwa ya gauraya da jini). A zahiri kam murmushi yayi kawai.... Wani irin malolon baƙin ciki ne ya sake tokare zuciyar Hajiya Basariyya. Dan ita kam abin ya zame mata goma da goma. Tana yaƙin ganin ta koma ɗakinta kafin Hajiya Yaya ta koma, Daddy kuma ya saki Asiya a randa ta koma dan alwashine sai tayi maganin Asiya a wannan gaɓar ga kuma batun Huznah da shima suketa faɗi tashin ganin wannan auren ya rabe tazo ta auri AA sun fiddo waccan shegiyar agolan daga ciki mai ƙwacen saurayi. Ita kuma sakaran tayi sakaci wannan matsiyacin ya kwace ɗan mutuncin. Zaune takai a bakin gadon ɗakin da take zaune a gidan yayanta, ɗakin da saida akai uban rikici matansa suka bari ta zauna duk da kuwa ɗakin baƙi ne. Kayayyakin data amso a Zaria tare da Maman Yaseerah take bi da kallo. Haɗi ne sosai tayoma mutane guda biyar. Daddy, Asiya, Hajiya Yaya, sai mijin Huznah da AA. Kuma duk ana son ta aiwatar da su daga nan zuwa gobe, shiyyasa ma tai kiran Huznah dan taji yaya za'ai nata ya iso a goben itama ta aiwatar, ko Sageer na yawo da ubansa ko sai ya saketa da hannunsa. Dan sunan maganin KANWA UWAR GAMI. Amma shine tantirin ya ɗauka mata waya.. Bumm!! Bumm!!! Bumm!!! Bugun ƙofar ɗakin da take aka shiga yi da masifar ƙarfi, a zabure ta miƙe tana yayimar kayan ta tura ƙasan gado, kafin ta mirza idonta ta nufi ƙofa kamar mai barci. Dan bata raba ɗayan biyu yayanta ne matansa sunkai ƙararta saboda yau ta zagesu tas wai suna saka mata nama biyu a abinci, duk naman dake gidan saboda an rainata ace biyu ne kawai kasonta... Tana gama buɗe ƙofar wani kakkauran mari ya ratsa mata kumatu. Da bala'in sauri da rawar jiki ta dafe fuskar da hannaye biyu gaba ɗaya. Bai dubi girman shekarunta ba ya sake wanketa dana biyu. Shi dama mutum ne mai zafi sosai. Ai yanzu kam ihu ta ƙwala dan azaba ta koma cikin ɗakin a guje. Bayanta yabi, ta maƙure jikin bango tana hawayen azaba a matuƙar gigice. Cikin wata irin tsawa mai kaɗa hanji ya ce, “Ina kukaje yau dan ubanki?”. Hawaye na ziraro mata ta ce, “Babu inda naje fa yaya, matanka sun haɗani dakai saboda su munafukai ne. Wankin kai da kitso fa naje kuma na gaya maka ka bani kuɗin da kanka”. “To mara mutunci, aiba maraina wayon naki bane ba ni da idona na ganki tare da Alhaji Usman a Zaria. Ko zakice min kitson acan akeyi?”. Sosai jikinta ya fara rawa na haƙiƙa kam yanzu, zuciyarta kamar zata faɗo cikin in-ina tace, “Yaya Zaria kuma?..” “Oh ƙarya nai miki kenan? Wlhy Basariyya ki shiga hankalinki a gidan nan. Wato har yanzu baki daina biye-biyen bokayeba ko? Shike nan karki fasa ki cigaba da yi, ki kuma haɗa inaki-inaki gobe kawu na Katsina zaizo ku tafi tare. Ki koma can wajensa dan ni bazan iya ba...” Wani irin gigitaccen ihu ta sanya tana roƙonsa ya taimaketa bazata iya zama gidan kawun nasu ba. Ko kallonta baiyi ba ya fice abinsa. Tashin hankali matuƙa Hajiya Basariyya ta shiga a wannan dare. Dan wlhy bazata iya zama gidan kawu Manu ba. A ƙauye yake bama cikin birnin katsinar ba, ita wlhy ko ruwan gidan bata iya sha idan sukaje gaisheshi na yini ɗaya saboda kiwon dabbobinsa na tsiya. Gashi masifaffe hakama matarsa, kuma su duka ƴan uwansu ne dan auren zuminci ne shida matar tasa. Tun babansu na da rai ake fama da shi ya baro ƙauyen amma yaƙi. Mahaifinsu kansa tsoronsa yake ji balle su, dan mutum ne azababbe na bugawa a kalanda, ga tsauri dan komai na gidansa da doka akeyinsa. Kuka sosai taci, daga ƙarshe ta yanke shawarar yin asubanci ta gudu. ALLAH gara ta koma gidan mijinta duk ma bala'in da za'ai ayi bazata fito ba koda Daddy zai daketa kuwa. Kayanta ta shiga haɗawa, tsaf ta kammala ta ajiye komai a ƙofar ɗakin, sauran kuma ta ajiyesu akan daga baya zata turo su Madeena yaranta su ɗaukar mata. Ko barcin kirki kuwa batayi ba, huɗu na bugawa zabar ta miƙe dama ba wani barcin kirki tai ba, a gurguje ta shiga bayi ta kimtsa ta fito, ta saɓi jakarta tana murmushin nasara, sai dai tana murɗa handle ɗin ƙofar taji gam, hakan na nufin an kulleta ta baya kenan. Ai jitai gaba ɗaya ta wani irin gigicewa, bama tasan ta zube a wajen ba ta fashe da kukan takaici, dan ta tabbatar yayanta ne ya rufeta tun fitar jiyan da yayi....... 🤣🥱Ba abun faɗa _________★ Sun fito a jere Maanal na faɗin, “Kai dai ka canja hali ALLAH”. Cikin ƙunƙuni take maganar, amma hakan bai hana AA ɗin jinta ba saboda ƙarfin ji da ALLAH ya bashi. Murmushi yay kawai, sai kuma ƙasa-ƙasa shima yace, “Inba tsoro ba a fito fili a faɗa mana”. Sarai itama Maanal ɗin ta jishi, sai dai bata tanka ba saboda isowarsu wajen motarsa. A dai-dai nan kuma Saheeba ta fito daga sashen Mamy, taje wajenta su Haule suka sanar mata tana sashen Oum. Sai ga Nibras itama ta fito daga sashenta, taci kwalliya abinta sai baza ƙamshi take kamar wadda zata fita. Itama dai sashen Oum zataje, kuma wannan kwalliya duk ta AA ce. A tare duk suka tsaya cak suna binsu da kallo, har Maanal ta shiga mota AA daya buɗe mata ya maida ya rufe sannan ya zaga mazauninsa, sai dai shima kafin ya buɗe da kansa Maanal ta buɗe masa ta ciki kamar yanda suke yi a da. Kallonta yay fuskarsa da murmushi mai sanyi, itama ta masa murmushin tana kauda kanta dan su duka zukatansu suna tariyo musu baya ne. A hankali ya baya mai gadi ya buɗe masa gate suka fice. Daga zuciyar Nibras har ta Saheeba tamkar zata kama da wuta ne. Cikin takaici da wani irin zazzafan kishi Nibras ta ce, “Wannan mayyar yarinyar sai nayi maganinta”. “Haɗa dani nan Nibras dan na tsaneta”. Saheeba ta faɗa itama a zafafe. Da sauri Nibras ta kalleta dan ita bata san nata zancen ya fito fili bane ba. Kai Saheeba ta jinjina mata batare da sanin manufar Nibras ɗin na tsanar Maanal ɗin ba. Ita kuma Nibras tasan dalilin Saheeban bazai wuce taya ƙanwarta kishi ba. Amma saboda takaicin da take ciki sai ta cigaba da faɗin, “To wai ina zasuje a wannan daren? Nine fa?”. Wata ƴar dariyar takaici Saheeba tayi, “Kin san tunda tarewa ta gagareta zatabi duk wata hanya ne yanzu na son ganin taja ra'ayinsa, balle an saba da bin maza a waje”. “Tabbas kumafa hakane. Shegiya mai zuciyar karnuka, mutum yace baya sonki amma ina, inba shashashar amarya ba mara muhimmanci wa ake kawowa a ajiye sashen surukai gana miji”. Nibras ta faɗa zuciyarta na mata raɗaɗi. Dariya sosai Saheeba keyi, ranta fes ta ce, “Ai Abah ne maganin ƴar iska, uwarta na murna bokanta ya iya aiki an mannota gidan da tsiya-tsiya shiko ya harba musu tsiya, Kinga ɗan maganin da aka ɗan cuccusa dan matse can duk ya sane. Ai wlhy sai mun dage munci ubanta a gidan nan ta yanda ko ruwa bazata iya sha ba sai a ɓoye, da ƙafafunta zata gudu ne”. Hannu Nibras ta bama Saheeba suka tafa, dan a ganinta ai gara su haɗa hannu da Saheebar su kori Maanal ɗin ita kuma sai tai yaƙin hana shigowar ƙanwar Saheebar ta bayan fage. Aiko a take ta bada goyon baya ɗari bisa ɗari. Sai da suka gama shirya mugunnyarsu sannan suka nufi sashen Oum ɗin. Acewarsu gara suje su zauna suga dawowarsu... A hankali AA ke murza steering tamkar baya so, yayinda Maanal tai shiru lafe a cikin kujera. Daga gani kasan duniyar tunani duk suka faɗa. Cikin son kauda yanayin AA yay ɗan gyaran murya. Idannunta dake lumshe ta buɗe ta kallesa, shima ɗan kallon nata yay fisha sai kuma ya maida ga hanya. So yake su dawo kamar da, amma yasan yaƙine babba a gareshi, dan haka maimakon zuwa mata kai tsaye zaibi wasu hanyoyin yin hakan. Muryarsa a tausashe ya furta, “Yaushe kika fara karatun novels? Bayan nasan haushi kike ji idan kikaga inayi ma”. Ɗan jimm Maanal tayi kamar bata jisa ba, har sai da ya ɗan kalleta. Ƙin kallonsa tayi ita, a taƙaice ta ce, “Kawai na tsinta kaina ne a karatun batare da wani dalili ba”. Murmushi ne yaso suɓuce masa, amma sai baiyi ba a bayyane ya tsaya masa iyakar cikin ƙirji. Zamansa ya ɗan muskuta da sake damƙe steering da ƙyau ya tsaya a danja data tsaida su, sai kuma ya koma ya jingina bayansa da kujerar ya juya yana kallonta. “Zuwa yanzu books nawa kika karanta?”. Kaɗan ta ɗan kallesa, cikin yin warrr da idannunta ta ce, “Suna da ɗan yawa fa. Damma Ammie na hanani ne”. “Ammie bata san karatun novels da daɗi bane shiyyasa. Kinga ni akwai wani book da nake nema saboda labarinsa da aka ɗan fara bani amma har yanzu ban samu ba, koda yake busy na ne ya hanani zuwa manyan books store na duba”. Yanzu kam muryar Maanal a sake ta kuma juyo tana kallonsa da ƙyau ta ce, “wanne ne?”. Sai da ya tada motar suka cigaba da tafiya saboda danja ta sake su sannan ya bata amsa. Murmushi tayi mai faɗi sosai har haƙwaranta na bayyana ta ce, “Hum'um kaga nikam na jima da karanta shi, dan tun ina shekarar ƙarshe a makaranta. Ina zaton ma kamar ina da copy ɗinsa yayi daɗi kam ba ƙarya”. “Woow da gaske Besty?”. “ALLAH kuwa bari zan duba maka, sai dai inaga yana cikin kayana da za'a kawo daga Kaduna”. Dai-dai nan yay parking gaban wani baƙin gate madaidaici yana bata amsa, gidan dai daga waje ba wani babba bane, dan kamar gidajen street ɗin ma duk sun fishi girma da ƙyau. Anan wajen gate ɗin ya kashe motar bayan yayi horn, wani ƙyamushashen mutum ya leƙo, alama AA ya masa da hannu na yazo. Bayan ya kunna fitilar cikin motar ta yanda zai ganshi da ƙyau kada ya tsorata. Aiko sai da ya leƙo daga nesa yaga wanene sannan ya ƙaraso yana famar washe baki. Cike da girmamawa ya shiga gaida AA ɗin, amsa masa yay shima da kulawa, kafin yace ya ɗan kira masa yarinyar gidan nan. Nanma da girmamawa mutum ya amsa masa, daga gani dai kasan maigadi ne. Maanal dai na jinsu, dan tunda ta amsa gaisuwar da mutumin yay mata ta ɗauke kanta gefe. Fitilar AA ya kashe, sai kuma ya ɗakko tab.. ɗinsa ya shiga dannawa, miƙama Maanal tab ɗin yay yana faɗin, “Kinga list ɗin novels ɗin da nake nema idan na samu lokaci na karanta su”. Amsar tab ɗin tayi, ta shiga duba list ɗin, cikin manta dawama take tare ta ɗan karkato tana nuna masa wanda ta karanta a ciki da wanda itama take nema ta karanta. Shima karkarowar yayi sosai har jikinsu na haɗuwa, ta shagala a nuna masa da yimasa bayani har ya ɗaura hannunsa a kafaɗarta ya sake kwantota a jikin nasa da ƙyau batare data farga ba, sai ma sake lafewa tayi sosai abinta tana zuba zance, dama can ta fishi magana, yanayine kawai ya maidata miskilar ƙarfi da yaji. Shi ko idan kaga ya saki jiki kamar haka yana magana to lallai tare yake da ita, dan sai kaga ma kamar ba AA Darma sarkin haɗe fuska da jefa magana ɗaɗɗaya ba da ƙyar. Sun shagala a hirarsu dake fita ƙasa-ƙasa dan ko ita Maanal ɗin da maganarta tafi yawa bawani tanayi zuuu bane ba, koda a cikin motar kake ma ba lallai ace ka jisu yanda ya kamata ba. Balle shi dake bata amsa kamar mai raɗa. Glass ɗin motar tinted ne, dan haka Nuratu data fito cikin matsananciyar kwalliya tana zuba wani shegen ƙamshin mayataccen turaren magani da babarta ta zazzage mata kanta tsaye ta nufi gefen mai zaman banzar fiskarta kamar ta yage dan murmushi. Wai itace yau Ya AA yazo wajenta hira, kai ita kam tafi kowa sa'a a duniya yau ɗin nan. Ta tabbata harta mutu bazata manta da wannan rana ba a tarihin rayuwarta. Sai da taja numfashi ta fesar tare da sake dai-daita kanta da ƙyau, dan babarta taja mata kunne matuƙa akan ta nutsu kada taje tana wannan rawan kan tunda tasan halinsa dai sarai. Sai da ta tabbatar ta samu irin nutsuwar da take buƙata kafin ta ɗaura hannunta a handle ɗin motar ta buɗe tana faɗin, “Assalamu aikum Yayan....” sauran maganar ya maƙale a maƙoshinta sakamakon saukar idannunta akan Maanal dake kwance a kafaɗar AA suna kallon abu a tab...........✍️ _😂😂Ni dai Nurry ƙawata ce bani da damar cewa wani abu anan🥱🤣🤣🏃🏃🏃_ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣7️⃣ ______________ ........Nurry tamkar wadda ta suma haka ta kasance, yayinda AA da maaanal suka ɗago idanu a tare suna kallonta kawai. Ta kuma ƙi tashi daga jikinsa sai ma ƙara gyara kanta da tayi. Jitai zuciyarta ta mata wani irin nauyi da ganin Nurry ɗin, dan tabbas da tasan gidan su yarinyar nan zasu zo da bazata biyo shi ba. Amma a zahiri babu ko ɗigon damuwa a fuskar tata, sai ma wani irin murmushi data sakarma Nuratun a karo na farko ta furta, “Hy” a hankali. Sai a lokacin Nuratu ta farfaɗo, a hankali ta zame hannunta dake ɗan rawa daga jikin murfin ta miƙe tsaye gaba ɗaya. Cikin kaushin murya AA ya ce, “K! Baki iya gaisuwa bane?”. Sosai muryar tasa ta ratsa mata zuciya, sanin halinsa na rashin ɗaukar raini ya sakata sake duƙowa dole batare data yarda ta sake kallonsu ba muryarta na ɗan rawa kamar mai shirin fashewa da kuka saboda kishi ta furta, “Kayi hari Yaya ina yini”. Maimakon amsawa sai yaja siririn tsaki kawai. Maanal dai tama maida hankalinta ga tab ɗin gaba ɗaya tamkar bata san mi sukeyi ba. Maanal ɗin ya nuna mata, cikin harara ya ce, “Ita kin gaisheta ne”. Sosai hawayen baƙin ciki suka ciko idanun Nuratu, cikin matuƙar raɗaɗi da jin ƙunar zuciya ta ɗan kalla Maanal ɗin ta ce, “Ina yini”. Tsabar wulaƙanci yatsu biyu Maanal ta ɗaga mata, batare data kalleta ba ta ce, “Kina lafiya?”. Wata shegiyar ashariya Nuratu ta shiga mulmulawa Maanal ɗin a zuciya, a zahiri kam dole ta amsa. AA da bai sake ko kallonta ba juyawa yay sit ɗin baya ya ɗakko ledar da Mamy ta bashi. Ɗan kwantowa yay ta jikin Maanal sosai ya mika mata ledar yana faɗin, “Kiba mamanku inji Mamy”. Sake sumewar takaici Nuratu tayi yanzu ma, har sai da AA ɗin ya mata ƴar tsawa da faɗin, “Wai tunanin uwar mi kike”. Firgigit ta amshi ledar zuciyarta na hautsinawa. Da kansa ya jawo murfin ƙofar kamar a fusace ya rufe. Dole taja da baya da sauri gudun bugeta da murfin. Shi ko ko'a kwalar rigarsa yayma motar key yay reverse batare daya ko sake kallon inda take ba ya bar wajen... Gaba ɗaya Nuratu ta zube a wajen ita da ledar, wani irin kukan baƙin ciki irin mai babbake zuciyar nan a lokaci guda ta saki da iya ƙarfinta. Aiko da gudu mai gadinsu dana maƙwaftansu suka fito suna tambayarta lafiya. Amma bata ko kallesu ba. Maigadin maƙwaftansu yace, “Kodai mugu ne yazo wajenta a sanar da securitys ɗin shigowa?”. Kai maigadinsu ya girgiza masa, “A'a nasanshi, ɗan uwansu ne ma sai dai idan wani abunne ya faru. Kaga tsaya min a wajenta bara na sanarma su Hajiya.” baima jira amsar shi ba ya shige gidan. Babu jimawa kuwa suka dawo da Hajiya, basu kowa bane face Maman Nuratun da mariƙiyarta, dan jiya Maman nasu tazo daga Kano batare da ko sanin Mamyn ba. Rufuwa sukai a kanta da tambaya cikin tashin hankali. Ganin bazata basu amsa ba suka kamata zuwa ciki, maigadi ya bisu da ledar (Ramadan basket🤣). Tambayar duniya su Hajiya Turai sunma Nuratu dake kuka kamar wadda ake yankawa amma taƙi basu amsa. Sai da mamanta ta balbaleta da masifa sannan cikin kuka ta sanar musu komai. Suma duk shiru sukayi cikin tsananin ɓacin rai. Musamman ma mamansu. Hajiya Turai ta ce, “Amma dai Kamila bata ƙyauta ba, ni da mukai waya kinga ai tace min zaizo ne wajen Nuratun su ɗan zanta ya kuma bata hasaffin azumi da samari ke ɗan bama ƴammata a yanzu. Shine zasu bari ya taho da wata kuma?”. Ɓacin rai ya hana Maman su Nuratun iya cewa komai. Cikin fushi ta fisga waya da nufin kiran Mamyn Hajiya Turai ta riƙe mata hannu. “Mi zakiyi?”. Rai ɓace ta ce, “Kiranta mana yaya Turai, banda rainin hankali tasan har yanzu bata da power ɗin tanƙwasa ɗanta zata saka mutane yin asara a banza yazo yana wulaƙanta mana yarinya”. “Toke banda abinki keda bata san kina garin ba kuma. Ki barni kawai da ita. Dan ni ba Kamila zanmawa yarinyar zan wulaƙanta. Sai na sakata nadamar dawowa rayuwar ahalin Darma. Shi kansa Ajwaad ɗin zan koya masa hankali, dan banga mai taɓa min Nurry yay barci lafiya ba koda kece da kika haifeta. Dan ni ba yayar uba bace kawai uwa ce”. Sosai zuciyar Maman su Nuratu tai mata sanyi, shiyyasa take matuƙar son Hajiya Turai. Dan akwai mutunci da ƙaunar juna sosai a tsakaninsu tamkar ba yayar mijinta ba. Kai a kaf dangin uban su Saheeban da Hajiya Turai kawai suke ɗasawa, ba kuma komai ya kawo hakan ba sai halinsu ne da yazo ɗaya. Sannan Nuratun tun daga yaye Hajiya Turai ta ɗauketa ta riƙe kasancewar ita har yanzu ALLAH bai bata haihuwa ba, mijin ma ya jima da rasuwa shiyyasa suka baro Lagos inda suke zaune da suka dawo nan Abuja. Sai dai da yake tana bussines koda yaushe ƙafarta na hanyar lagos ɗin da Dubai da Chaina. Shiyyasa Nuratun ke zuba tsiyarta yanda take so a garin na Abuja, dan ƙazamin gata Hajiya Turai ke mata, sannan duk abinda ta nema saita mata shi. Wannan yasa take jinta a babbar yarinya ɗiyar manyan mata masu kuɗin Abuja. Dan ubansu dai bawani kuɗin arziƙi ne da shi ba, hasalima da bazar Hajiya Turai ɗin yake rawa shima.... Hajiya Turai data raka Nuratu ɗaki tace ta kwanta tana fitowa ta tashi, wayarta ta ɗauka tai kiran Sille. Bugu biyu kuwa ya ɗauka. Kamar yanda ya saba cike da yaudara ya shiga yimata kirari da fasa mata kai. “Kaga Sille yanzu ba lokacin kirari bane ba tsaya kaji”. Nuratu ta faɗa muryarta a shaƙe. Ɗan ɓoyayyen murmushi yayi daga can, a zahiri kam murya a dake kamar bai san komai ba ya ce, “Ina jinki uwar ɗakina mike faruwa? Waya taɓa min ke yaga fushin maza dan walle ina iya tada Abuja harda fadar shugaban ƙasa”. Murmushi tayi a karo na farko, shi yasa take matuƙar ji da Sille a rayuwarta, take kuma taɓa duk wanda taso hankalinta kwance dan shine garkuwar ta. Tasha sakashi ya nakasta mata duk wanda ya nuna mata yatsa a garin Abuja wallau namiji ko mace. Numfashi ta fesar mai raɗaɗi, kafin ta shiga faɗin, “Aiki nake so ai min akan jakar yarinyar can da tama AA ɗina asiri ta auresa”. “Angama uwar ɗaki. Ƙafafu za'a cire mata ko hannaye ko fuskar za'aima ɓalli-ɓalli irin wanda kikama Huznah take kowama”. Dariya Nuratu ta kwashe da shi, dan fuskar Huznah ɗin ce ta faɗo mata arai. Ta ce, “Kai Sille kai duniya ne, daɗina dakai baka da mantuwa sam. Ita wannan ai ta wuce ɓalli-ɓallin yarbawa, dan zunubinta mai yawan gaske ne. Zan turo maka abinda nake so ai mata. Kuma a satin bikina bayan salla zaka mata hakan, dan ina son aci shagalin bikina tana asibiti kwance rai a hannun ALLAH dan uban ubanta”. “An gama babbar yarinya, kune Abuja kune kuma masu riƙe da ƙasar gaba ɗaya, dan masu mulkinta a tafin hannunku suke tunda kullum tsaye suke a gabanku haihuwar tsoffinsu”. Sosai Nuratu ta sanya dariya harda kwanciya, cike da jin takaicinta ya ragu ta ce, “Zakaga saƙo a lalitarka Sille”. Daga haka sukai sallama ta yanke kiran..... Daga can dariya Sille ya kece da ita, sai kuma ya ƙara gudun motarsa mara fasali ya cigaba da bin bayan su AA dake tafiya a hankali kamar wanda baya son isa gida. Tun fitowar su AA daga gida yake biye da su har nan gidan su Nuratu, akan idonsa komai ya faru sai dai baya jinsu kasancewar can nesa yay parking dan kar AA ya lura da shi. Dan tun Mamy na waya da Hajiya Turai cewar ga AA ɗin nan zuwa wajen Nuratu Haule ta tura masa saƙo, shine yazo ƙofa gidan ya tsaya, a zatonsa AA ɗin ne kawai zai fito, amma sai yaga kamar shi da wani ne a motar, shiyyasa ya fasa aikata abinda yay niyya ya shiga binsa a baya har kofar gidan su Nuratun dan yana son ganin shi da wanene. Bai samu ganin ba tunda basu fita a motar ba, sai yanzu da Nuratun ke sanar masa. Dan haka yaji wani kalar karsashin abinda yake shiryama ransa. Yau fa in har bai kashe AA da Maanal ba to sai ya raunata musu wani sashe na jikinsu kuwa.... Tofa munga idi🏃😳. Sannu a hankali AA ya gangara gefen hanya yay parking, dan tunda suka baro gidan su Nuratu Maanal tai masa ɗif, tama ajiye tab ɗin ta kauda kanta gefe fiskarta a haɗe. Hannunta ɗaya dake ajiye a saman cinyarta ya kamo cikin nashi, ɗayan kuwa ta tallafe haɓarta tana kallon waje. Yanzu ɗin ma batako motsa ba balle ta juyo ta kallesa, hakan ya sake tabbatar masa fushi take yi. Lips ɗinsa ya ɗan ciza kaɗan, sai kuma ya matso kusa da ita gab yana sake rumtse hannun nata cikin hannayensa biyu gaba ɗaya. Da wata irin murya mai taushi da fitar sauti can ƙasan maƙoshi ya furta, “Besty!”. Ƙin amsawa tai yanzu ma, sai ya sake matso jikinta sosai, har buɗaɗɗen ƙirjinsa na kwanciya a kafaɗarta. Hannunsa ɗaya yasa ya kamo furkarta da shi, yana ƙoƙarin juyota inda yake. Amma sai ƙoƙarin hana hakan takeyi ita kuma. Bai barta ba har sai da ya juyo da itan a yanda yake so. Sai ta lumshe idanunta kawai. Guntun murmushin da ya tsaya masa a iya lips ya ɗan saki. Cikin sake sanyaya sauti yace, “Kin gaji?”. Juyar da fiskarta tai ƙoƙarin sake yi, ya riƙe da ƙyau. Tare da sake faɗin, “Barci ne?”. Shiru tayi nan ma. Ya ce, “Ni ne?”. Yanzu ma shiru. Yace “Oh kishi ne?”. Yanzu kam sai ta buɗe idannunta da suka ƙanƙance ta zabga masa harara. Sosai ya saki wani irin sassanyan murmushi daya daki zuciyarta. Babu shiri tai ƙasa da idanun nata tana tura baki. Murmushin ya sake saki, batare daya sake cewa komai ba ya jawota gaba ɗayanta ya rungume a jikinsa. Atare suka sauke ajiyar zuciya mai nauyin gaske, yayinda zukatan ke wani irin bugawa da sauri-sauri a tare. Sake ƙanƙameta yay, yana jin tamkar ya shigar da ita cikin jikin nasa ta narke kawai ta zama jininsa. Ita ɗin ta dabance a rayuwarsa, irin daban ɗin da baki yayi kaɗan a furtawa. Ya rayu da itane a irin rayuwar da baiyi da kowa ba, ya kusantu da ita a irin kusancin da bai samu da kowa ba. Ya shaƙu da ita a irin shaƙuwar da baiyi da kowa ba. Ita ɗin tamkar half ɗinsa ce a rayuwa. Itace abokiyarsa, abotar da bai taɓa yi da ɗan uwansa namiji ba. Dan zai iya cewa sai da suka rabu sannan yasan ya zauna tare da ɗan uwansa namiji har suyi mu'amula irin ta abota. A hakan ma kuma bai taɓa iya sakin jiki da kowa ba koda rabin kwatar yanda suka kasance shi da ita ne. Har garama Rafeeq, shima kuma dan ya kasance ɗan uwansa ne jininsa. Tsitstsinkewar da jinin jikinsa keyi sakamakon jin saukar ɗumin hawayenta a cikin ƙirjinsa ya sashi ɗagota daga jikin nasa, ƙoƙarin hana hakan takeyi, amma sai da yay nasarar ganin hawayen kuwa... “Besty kuka” ya faɗa zuciyarsa na wani kalar hanƙoro, kauda kanta tai yunƙurin yi, da ɗan hanzari ya riƙo fiskarta tata, bai wata-wata ba a karo na farko na rayuwarsa ya manna tausasan lips ɗinsa kan nata............✍️ _Wayyo ana cin amanar Abah. Jama'a kukawo ɗauki daga bashi aro yin rakkiya zai ci amanar Abah a titin gwamnati🤣🤣🤣🥱🏃🏃_ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣8️⃣ ______________ .......Sosai jinin jikinsa ya shiga wani irin harmutsawa har cikin brain ɗinsa, illahirin ƙofofin gashinsa suka shiga bubbuɗewa. Domin al'amarin yazo masa da wani irin girma na gaske sakamakon abinda ya ɗauki tsawon shekaru yana dannewa da tsiya-tsiya. Tsaf ya kanainaye Hajiya Maanalu ta yanda bata da damar yin wani yinƙuri koda na motsa kanta ne. Sumbatarta yake cikin rikicewar yanayi da birkicewar tunani, sai dai hakan bai sakashi kasancewa a rashin nutsuwar da ALLAH ya azurtashi da ita ba. Akowane irin yanayi AA nutsatstsen mutum ne mai cike da kamala da dattako, nutsuwa akan komai halittar AA ce, sannan a cikin jinin jikinsa take. Matuƙar nisan kiwo ƙwaƙwalwarsa da zuciyarsa suka tafi ya manta da inda suke, dan kuwa tuni ya fara ƙoƙarin warware mata veil ɗin jikinta da take ta ƙoƙarin ganin ta riƙe ta hanashi hakan, amma yanda ya matseta a cikin kujerar hakan ya gagara, har ALLAH ya bashi nasarar yakicesa ya tura hannunsa a bayanta ya fara kici-kicin sauke zip ɗin bayan rigarta. Zuwa yanzu kam matuƙar ƙololuwar tashin hankali da birkicewar zuciya Maanal ta shiga. Dan tsabar tsoro da firgici zuciyarta neman buɗewa take gida biyu. Abu biyu ne ke maimaita kansu a ƙwaƙwalwarta a wannan gaɓar. Tsoro mai tsananin gaske, da flash back na wasu shekaru da suka shuɗe a rayuwarsu, sai dai tarihin irin wannan gaɓar bazai taɓa gogewa ba har abada dan tabone da ya riga yay tammbari a RAYUWARSU na har abada. A hankali ta saki masa wani irin kuka da kaima bayansa duka dan ta fahimci kamar ya manta itace fa Bestyn sa. Sai dai babu alamar yasan tanayi dan har yayi nasarar sauke zip ɗin yakai ga hook ɗin b ɗinta yana kici-kicin ciresu suma... A dai-dai nan kira ya shigo cikin wayarsa, kiran daya saka komai tsayawa cak harda fitar numfashinsu. Bawai kiran ne yay tasiri ba ga AA, a'a sautin dake tabbatar masa da kiran daga waye ne ya tasirantu a garesa matuƙa. Yafi sakan goma bai iya ya motsa ba balle janye jikinsa kafin ya zare lips ɗinsa akan nata a hankali, sai dai ya kasa raba jikinsa a nata saima sake ƙanƙameta da yay na fin sakan ashirin. A lokacin daya ja jikin nasa baya ya koma a nasa mazaunin jagwab ne ya bama Maanal damar cusa kanta a cikin ƙafafunta ta ƙanƙame jikinta waje guda gaba ɗaya. Jikin nata kuma sai wani kalar rawa yake na tsorata da shiga firgici ga kunya mai tsananin gaske da bata taɓa shiga tsakaninta da shi ba a rayuwarta. Zuciyarta kuwa babu abinda take sai rabewa da komawa ta tsuke kanta da kanta.... Kiran Abah daya sake shigo masa ne ya sashi ɗaukar ruwan dake gefen sa ya ɓalle murfin ya shiga kwankwaɗa duk da uban zafin da yake da shi. Shi kansa ma bai san tun yaushe ruwan yake a motar ba. Sai da yasha kusan rabi ya kife kansa a steering yana maida numfashi, a karo na uku kiran Abahn ya sake shigowa. Sai yanzu ne ya sami damar dai-daita kansa da ƙyar ya ɗaga wayar. “Ajwaad! Kana kallon ƙarfe nawa kuwa? Sai ɗaya tayi zaku dawo?”. Nutsatstsiyar muryar Abah ta daki cikin kunnensa. Idanunsa ya sake lumshewa ya buɗe da ƙyar, cikin ƙoƙarin ganin muryarsa ta kuma samun nutsuwa yay ɗan gyaran maƙoshi kafin ƙasa-ƙasa ya ce, “Gamu nan in sha ALLAHU Abah”. Shiru Abah yay sautin shaƙaƙƙiyar muryar ta AA na dakar masa zuciya. Dan duk wanda ya sanshi ya jisa a yanzu zai fahimci akwai lauje cikin naɗi. Amma kasancewarsa dattijon arziƙi sai cewa yay, “Okay kuyi sauri Oum ɗinku nason kwanciya” daga haka ya yanke kiran. Idanu AA ya sake lumshewa ya buɗe a karo na barkatai, shi kansa ganin ƙarfe nawa sai da yaji zuciyarsa ta girgiza. Harga ALLAH bai san sun jima haka ba, dan sai yake ganin ma kamar basu wuce minti talatin da fitowar ba. A karo na farko ya maida birkitattun idanunsa kan Maanal dake a duƙufe har yanzu. Lallausar fatar bayanta da hasken fitilar titin ta hasko ya zubama idanu, sai farar b ɗin jikinta datai matuƙar dacewa da fatar gata fes babu wani alamar datti a tare da ita. Numfashi ya sake ja a fisge, kafin cike da kasala ya kai hannu kan zip ɗin zai ja mata shi saman. Zaram ta miƙe zaune sosai idanunta share-share da hawaye. Shi dariya ma taso bashi ganin yanda ta wani zazzaro masa idanun alamar gargaɗi. Ƙasan zuciyarsa kuwa sai yaji kamar yana jin nauyinta shima musamman da wani gefe na zuciyar keta maimaita masa kalmar (Bestynka ce fa! Amma ka rufe ido ka aikata mata wannan abin kunyar har kana neman sakin layi) kauda tunanin yay gefe murmushin gefen baki na neman suɓuce masa. Amma sai ya daure a tausashe ya ce, “Yi haƙuri zip ɗin zan rufe miki, idan kuma kina son Abanki ya gane to a barshi a hakan kawai kinga na huta sai yace mu wuce sashen mu kawai ya salllama”. Ai da gudun tsiya ta duƙe alamar ya rufe matan. Yanzu kam saida ya murmusa kaɗan, kafin ya kai hannun yaja zip ɗin, yazo dai-dai jikin b ɗin ta ya dakata, hook ɗin yay ƙoƙarin maida mata dan duk ya ciresu saura ɗaya jal ya rage masa. Rumtse idanu kawai Maanal tayi da ƙarfin tsiya harya kammala ya ƙarasa ja mata zip ɗin. “Oya wanke fuska mu wuce, idan kuma a samu hotel anan kusa muƙarasa to”. A baima gama rufe baki ba ta ɓalle murfin motar, batare data kallesa ba ta warce goran ruwan hannunsa ta juya ta fara wanke fuskanta. Murmushi ya saki, tare da kai hannu ya shafa lallausar sumar kansa dake lashe kuɗaɗe da shima bai san adadi ba. Koda ta gama bata kallesa ba, ta yarda goran a ƙasa ta maida murfin ta rufo, sai kuma ta matsa jikin murfin ta maƙure. Komai baice mata ba, sai handkacheff ɗinsa mai ƙamshi ya miƙa mata kawai. Ɗan kallonsa tayi, suka ko haɗa ido. Da sauri ta janye nata tana fisgar handky ɗin kawai. Nanma murmushi yay yayima motar key suka cigaba da tafiya. Sai dai yanzu gudu yake sosai saɓanin ɗazun. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa sai gasu a gaban ƙaton gate ɗin gidansu... Koda suka nufi sashen Oum salaf-salaf Maanal ke tafiya kamar wadda ƙwai ya fashewa a ciki. Gani take kamar tana shiga kowa zai gane abinda ya faru a tsakaninsu. Musamman ma Abah da Oum. Ɗan tsayawa AA yayi, ita kuma kanta a ƙasa tunanin da take yi ya ɗauke dukkan hankalinta har tazo gab da shi bata sani ba. Sai da ta bugu da bayansa sannan ta ɗago da sauri, tayi baya kuma zata faɗi. Saurin juyowa yay tare da riƙota a lokaci guda, cike da kulawa ya jinginata da jikin bango. Muryarsa a sanyaye saboda halin da yake ciki ya riƙe fuskarta, ɗayan hannunta kuma a cikin nashi yana kallon fuskar ya ce, “Tunanin mi kikeyi ne haka?”. Wata irin kunyarsa take ji shima, dan haka tana ɗan ɗago idonta ta kallai ta maida su ta risinar, shiko nashi yawo kawai suke akan ƙyaƙyƙyawar fiskarta. Kanta kawai ta girgiza masa tana ƙoƙarin janye hannunta dake a cikin nasa yaƙi bata damar hakan. Hawayen da take riƙewane suka ziraro, ya waro lumsassun nasa sosai. “Ya arrahaman, miye abin kukan kuma?”. Cikin rawar murya ta ce, “Yanzu idan Oum da Abah suka gane fa”. Ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke, a ransa yana faɗin, (Ashefa na manta yarinyar nan ɗanya ce, rinton aji yasata gama makaranta da wuri) a fili kam sai ya shafa fiskarta tare da faɗin, “Sai dai in kece kika so su gane”. Kallonsa ta ɗago tayi sosai a karo na farko, ya jinjina mata kansa yana ɗan laɓe baki da murmushin gefen baki a tare. Sai kuma ya shafa kanta cike da lallashi da tsokana ya rankwafa yana mai kai bakinsa saitin kunnenta da raɗa ya ce, “To ko mu tafi sashen mu kawai ki kwana acan, da asuba na miki alƙawarinkin rakoki da wuri kafin kowa ya tashi”. Tamkar wadda ya zaburar, ta sa hannayenta duka biyu a ƙitjinsa ta tura shi baya. Matsawar yayi yana dariya, ita ko ta kwasa da ɗan gudu cikin sashen Oum. Ko ganin Abah dake bayansu ma batayi ba sam. A falon kuwa akwai Oum, Mamy, Nibras, Saheeba da Fawzan harda babban Yaya a yanzu na zaune suna hira sai kawai ganinta sukai kamar walƙiya ta wuce hanyar upstairs. Da sauri Oum ta ce, “Munga idi Baby waya biyoki haka?”. “Oum fitsari-fitsari” ta faɗa batare data waiwayo ba. Dan tasan wannan dabararce kawai zata rabata da jin kunya. Saboda babu wanda zai kalleta bai fahimci wani abu ba a fuskar ta da lips ɗinta da yasha wahala a hannun wancan mutumin. Dariya Fawzan da Babban Yaya suka saki a lokaci guda, dan abinda Maanal ɗin tayi ya tuna musu da baya ne. Haka take yi idan suka dawo makaranta, sai ta riƙe fitsari tun daga can, mota na tsayawa ta fita a guje zuwa ciki tana faɗin, “Fitsari-fitsari”. Sai da Ammie ta zaneta wataran aka samu lafiya ta daina abin nan. Oum ma dai dariyar tayi, dan itama dai abinda yazo mata a rai kenan. Mamy da su Saheeba kam wani irin takaici ne ya ƙullesu, da kallon abinda Maanal ɗin tayi matsayin wani sabon bariki.... A waje kam, AA na gama dariyarsa dake fita a hankali ya juyo da nufin shigewa shima sukai ido huɗu da Abah daya harɗe hannaye a ƙirji ya tsaresa da idanu. Da sauri AA ya juya yana rumtse idanu da kai hannu ya shafa kansa, haƙoransa damtse da lips ɗinsa. A zuciyarsa faɗi yake (Ajwaad kaga takanka, tsohon nan ba raga maka zai yi ba....) katsewa zancen zucin nasa yay saboda taɓashi da akayi, juyowa yay kansa a ƙasa hannunsa a cikin sumar kansa, sai kuma ya ɗan buɗe ido ɗaya ya ɗan kalla Abahn. Abah da dariya ke cinsa a rai ya gimtse da ƙyar ya wani sake tsatsatsaresa da idanun. Sai AA ɗin cayay, “La Abah kai ne?”. “A'a bani bane aljani ne”. Abah ya bashi amsa cike da gatse. Bayansa AA ya koma ya tungumesa, ya tabbatar hakan shine rufun asirinsa dan wlhy tsaf Abah zai gane halin da yake ciki, musamman idanunsa da suka kaɗe. Cike da shagwaɓa ya kwantar da kansa a kafaɗar Aban yana faɗin, “Kaga ko Abah ALLAH ban lura time ya tafi haka ba. Na tuba! Na tuba! Na tuba!!”. Yanzu kam kasa daurewa Abah yay saida ya murmusa. Amma kasancewar AA na bayansa ba gani yay ba. Fuskar ya maida ya himtse a dake ya ce, “Ai na faɗa maka daman saina ƙara kwanakin suspension idan ka daɗe min da yarinya”. A sanyaye AA ya ce, “Abah holdup ne fa a hanyar”. “Na aljanu ko? Yo in ba na aljanu ba a daren nan wane huldup ne zai taru. Kaji tsoron ALLAH Ajwaad”. Ƙaramar dariya yanzu kam AA ɗin yayi da faɗin, “To Abah kawai abar kaza mana cikin gashinta. Kawai kayi murna mun dawo bamu ɓata ba ma”. Rankwashi Abah ya kai masa bisa kai, da sauri ya sakesa ya shige sashen Oum yana dariya. Shima Aban dariya yake yi da girgiza kansa. Wani irin farin ciki na ratsa masa zuciya. Rabon da yaga Ajwaad a irin wannan yanayin na farin cikin da har zai dinga wasa da dariya kai tsaye an ɗauki shekaru masu yawa. Ko tsokanarsa sukai sai dai yay guntun murmushi kawai yay shiru. Amma yau jiba yanda yake zuba masa surutu da shagwaɓa kai tsaye. Ya ɗan sauke ajiyar zuciya, sai kuma ya nufi sashensa yana mai jerama UBANGIJI kirari da godiya.........✍️ _Abah namu, anya! Anya kuwa🥱. Bara dai nayi shiru😂👍_ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣9️⃣ ______________ *_LADIES COLLECTION AND MORE_* 08169307477 SHIN MATSALARKI RAMA CE KO KINA SO KI GYARA BREAST DINKI NE? KINA SO KIYI HIPS HAJIYATA KIYI KYAU? KO KUWA KINA SO KI RAGE KIBARKI KO TUMBINKI? KINA SON INGANTATTUN MAGANIN MATA NA GARGANIJIYA? Kinason shape dinki ya fito kamar yanda kowace mace zatai alfaharin ganinki bare ma oga ko saurayinki da kansa, Shin kinason ko koma yar dagwas dinki batareda kashe kudin surgery ba kokuma hana kanki cima da dama da kikeso sbd kinason jikinki yayi daidai? To matsalarki tazo karshe indai ingantattu sahihan maganin gargajiya ne da muka san inganci da gaskiyarsane, MAZA KI ZIYARCI LADYS COLLECTION AND MORE ko ta waya ko ta asalin inda take ki tabbatar da Buqatarki tazo inda zata biya insha Allah, LADY'S COLLECTION AND MORE ANAN NE ZAKI SAMU DUKKAN ABUBUWAN DA KIKE SO KAMAR HAKA 👇🏻 Zumar kiba Zumar breast Zumar hips Zumar infection Zumar sliming Zumar sabon budurci Back to virgin Abayas Atamfa Less Hijabs Supplements Kitchen items and more Muna maraba da masu siyan Daya ko 08169307477 Address bayan gidan drugs katsina State Kayan mu masu inganci ne sosae Muna aika kayanmu a ko Ina ba tare da wata matsala ba🙏🏻🙏🏻 SIYAN NA GARI MAIDA KUDI GIDA💯 *********** ________________ ......Su babban Yaya na dariyar Maanal AA ya shigo. Duk kallonsa sukai, musamman Mamy dake masa kallon ƙurulla, hakama Nibras ji take kamar taje ta rungumeshi ta fashe da kuka saboda kishin Maanal dake ruruwa a zuciyarta. Gashi yanda lips ɗinsa suka wani ƙara zama pink duk sai taji ta tsargu, zuciyarta ta shiga wassafa mata abinda ya faru. Cike da basarwa AA ya kai zaune. A nutsensa kamar bashi ya gama yima Abah shagwaɓa ba ya ce, “Ikon rabbu, miya saku nishaɗi haka?”. “Bestynka mana” cewar Fawzan, sai kuma ya shiga bashi labarin abinda tayi. Wani ɗan murmushi ya saki tare da girgiza kansa. Ba ƙaramin dukan zuciyar Mamy da Nibras murmushin nasa yayi ba. Amma sai ya katse yanayin nasu da faɗin, “Mamy mun kai”. Batare daya kalleta ba. Dan yasan tana nan tana tuhumarsa da ido. Kafin ta amsa masa Fawzan ya dawo kusa da shi neman tsokana, sai dai yana zama ƙamshin sassanyan turaren Maanal daya manne a jikin AA ya shiga hancinsa, idanu ya waro tare da sake matsawa yana shinshina shi. Cike da raɗa Fawzan ya ce, “Ehem-ehem malam yau dai babu zancen dojewa ALLAH ƙamshin turaren Lilly kake yi?”. Harararsa AA yayi, shima ƙasa-ƙasa ya ce, “Yaya Fawzan ka rage gulma wlhy, mutum da matarsa dan anji ƙamshinta a jikinsa sai mi?”. Sosai Fawzan ya saki baki da hanci yana kallonsa, shima AA ɗin kallon nasa yake da wani irin salon ɗage gira sama irin na (Eh ɗin nan). Jinjina kai Fawzan yayi, a hankali yace, “Ashe za'a bajeta a gaban Abah gobe. Dole a ƙara maka kwanaki sai after babbar salla”. Yanzun ma ƙasa-ƙasa shima AA ya ce, “Yo a bajetan mana, zuwa babbar sallar kun fara jiyyarta dan ta fara laulayi kuwa, kunga sai ku bari sai ta haihu ku bani”. Daga haka ya miƙe cike da basarwa tamkar bashi ya faɗa ba. Fawzan daya saki baki yana kallonsa ya kwashe da dariya da faɗin, “Kai wannan yaro tantiri ne kai, ALLAH sai na tona”. Gwalo AA daya nufi hanyar fita ya juyo yayma Fawzan, kafin yace, “Oum! Mamy! Babban yaya good night”. Ya fice a binsa. Cikin ɗaga murya Fawzan yace, “Muma da bakace mana good night ɗin ba lafiya lau zamu kwana, kuma gobe sai na fasa ƙwai a gaban Abah”. Wani kalar ƙululun takaici ne ya kume Mamy, dan kallon da takema Fawzan da AA ta gefen ido tsaf ta fahimci abinda suke tattaunawa da juna ta hanyar motsin bakinsu. Gittawar AA a yanzu kuma sarai ta ji ƙamshin turaren Maanal itama. Hakama Nibras data sanya musu ido. Saheeba dai tsarguwa kawai tayi, shiko babban yaya da Oum dariya ma suke musu dan Fawzan da Ajwaad tamkar tom and jarry haka suke. Komansu irin na asalin sako-da-sako ne basa ragama juna. Ta wani gefen kuma kamar wasu abokai.. Fitar AA ɗin ta saka hirar tashi gaba ɗaya, dan dama dai rashin dawowarsu yasa hirar tsaho haka da sha biyu ta wuce... Lokacin da Oum ta shiga ɗaki samu tai Maanal harta kwanta. Murmushi kawai tayi itama ta shiga kimtsawa domin tafiya wajen mijinta. Taje zuba kayanta a laundry basket taji ƙamshin turaren AA matuƙa a wajen, kayan cikin basket ɗin ta kalla, kayan Maanal ne data cire yanzu. Kasa daurewa Oum tai ta ɗakko doguwar rigar takai hancinta. Itace kuwa ke ƙamshin na gasken gaske. Kai Oum ta girgiza dariya na suɓuce mata, sai yanzu ta fahimci dalilin gudun Maanal da ƙin tsayawa a wajensu da wannan kwanciyar saurin. Ƙasa-ƙasa ta ce, (Wannan nake jiye maka Abansu, karka bashi matarsa dai a juri zuwa rafi) daga haka ta ajiye rigar ta ƙarasa shirinta ta tafi wajen mijinta... _________★ Sille ya jima akan titin bayan wucewar motar AA. Dan abinda ya gani na faruwa daga nesan da bayansu da yake kasancewar gilashin motar a sauke yake kaɗan ya sashi canja shawara. Waya ya fiddo ya shiga yi musu video. Dan wata shegiyar waya ce dashi mai ƙarfin camara ta yanda yake iya zooming abu mai nisa sosai. Yako yi nasarar ɗaukar komai yanda ya kamata, daga ƙarshe ya adana videon a wayar tasa yana murmushin cin nasara. Dan yaci alwashin sai videon nan ya zame masa kadarar tatsar mutane da yawa kuɗaɗe kafin yasa ai masa editing ɗinsa ya bazashi a media ta yanda sai ya kunyata rayuwar AA da Maanal dan zai canjama al'amarin siga ne ta koma matsayin kafin aurensu ne hakan ta faru. Sauran alwashinsa kuma zai biyo baya dan baya yafiya ba kuma ya canja tsarinsa akan maida murtani saboda sabon idea..... Hummm wannan Sille! Wannan Sille wai mike damunka ne🙄🥺. ________★ Murmushin da Oum keta faman yi ne ya saka Abah dake binta da kallo faɗin, “Wai shi wannan murmushin na miye?”. “To Gadanga miye a murmushi ko dai ka tsargu ne?”. “Tsarguwar ma sai nayi, dan nasan halinki sarai”. Dariya Oum ta sakeyi, sai kuma takai zaune a kusa da shi tana faɗin, “Abansu ka fahimci a yanayin da Ajwaad da Maanal suka shigo kuwa?”. Kansa ya girgiza alamar (a'a) Cikin ɗan waro idanu Oum tace, “Gadanga kaji tsoron ALLAH”. Murmushi kawai yayi baice komai ba. Oum ta ɓata fuska. “To ALLAH ina gaya maka idan baka bama Auta matarsa ba za'a haifi ɗa mara ido, kadai gani da idonka sau biyu”. “A haifi ma mara kunne, ai nasan dai duk rashin kunyarsa bazaiyi abinda kike tsoron ba. Fateema da kike ganina sarai nasan abinda nake yi, dan haka ki daina damun kanki ina kan ra'ayina. Saboda ni nasan dalilina nayin komai”. Shiru kawai Oum tai tana kallonsa, sai kuma ta kai kwance cike da haushi. Baki kawai Abah ya taɓe ya cigaba da duba littafin hannunsa daya kasance na addu'oi.... ★Washe gari Abah ya tashi da uzirin fita da wuri, dan haka ya bada umarnin driver yakai Maanal wajen aiki. Yauma kamar jiya bayan sun kammala breakfast da Maanal bataci ba tace azumi take kowa ya shiga motarsa. Driver ya buɗema Maanal mota itama. Oum batace komai ba dan a gabanta Abah ya sanarma driver ɗin. AA ma yi yay kamar baiga komai ba ya shiga tashi motar nasa drivern ya jasa. Sai da suka fito ko street ɗin basu gama bari ba ya saka drivern sa tsaida na Abah. Fitowa drivern yay yazo saitin inda AA ɗin yake zaune yana faman duba wasu takardu. Batare daya kalla drivern ba sai gilashin daya ɗan sauke a dakensa ya ce, “Buɗe mata ta dawo nan”. Daburcewa sosai drivern yayi, dan ba ƙaramin gargaɗi Abah ya masa ba akan hakan kasancewar yasan AA ɗin zai iya aikatawa. Cikin tashin hankali driver yace, “Ranka ya daɗe Alhaji fa yace...” Wani banzan kallo da AA ɗin ya ɗago ya watsa masa ya saka shi kasa ƙarasa faɗa, sai ma duƙar da kansa da yay ƙasa da sauri. Shi kam dai sun sakashi a tsaka mi wuya. Kusan minti ɗaya AA ya ajiye takardun hannun nasa ya ɓalle murfin motar ya fito. Yayi ƙyau matuƙa cikin baby pink color ɗin suit, fuskar nan babu walwala sai kwarjinin kamala dana ibada ke fita. Maanal da haushin tsayawar tasu ya kumeta taja tsaki tana ƙoƙarin ƙarasa abinda take a laptop ta fito kawai taji an buɗe side ɗin da taken, ɗagowa tai cike da masifa dan son ganin wanene suka haɗa ido da AA da yay kicin-kicin da fuska. Itama dai tayi ƙyau sosai cikin lass da akaima doguwar riga, ta kafa ɗaurin zarah buhari sai veil ɗinta da yay dai-dai da tsarin shigar tata. Tana ƙoƙarin rufe laptop ɗin kawai ya duƙo cikin motar a kanta, kafin ta samu damar magana ya ɗagata cak ya fito da ita. Idan tace al'amarin AA bai fara girgiza tunaninta ba ma ai tayi ƙarya, yanzu banda ikkanci a titin ALLAH zai ɗakkota a mota da safen nan mutane nata kai-kawo. Koma tace a anguwarsu data tabbatar ko wani bai sanshi ba wani ya sanshi duk da ana rayuwa ne irinta ba ruwan wani da wani ɗin nan a anguwar. Da sauri kuwa nasa drivern ya fito ya buɗe masa ɗayan side ɗin da yaga ya zagaya, a ransa kuwa dariyar halin ogan nasa yake, yayinda suka matuƙar birgesa duk da yanata wani sinne kai. Ajiyeta AA ɗin yayi ya gyara mata rigarta ya rufe ƙofar, ita kam ai tamayi sumar zaune ne ko mi zatace oho. Dan sam tama kasa masa magana dan al'ajabi. Shigowarsa wajen da yake zaune hannunsa riƙe da tarkacenta da drivern Abah ya kwaso mata ya sata kallonsa ta gefen ido, sai wani ɓaɓɓata fuska yake kamar ba shine daren jiya ya gama aikata mata abin kunya ba. Aikinsa ya cigaba da yi batare daya sake kallonta ba yana cema drivern sa, “Muje” a daƙile. Yanda ya basar ya cigaba da aikinsa itama sai ta basar ta cigaba da nata aikin. Har suka iso Company wani magana bai shiga tsakaninsu ba. Kai babu ma wanda ya kula ɗan uwansa. Koda motar ta tsaya kuma kasancewar tana tattara kayanta shine ya fara fita. Tayi zaton zai yi tafiyarsa ne. Amma sai a mamakinta ya zagayo ta inda take ya buɗe mata. Koda ta fito kuma sai ya saka hannu ya amshi kayan hannunta harda handbag ɗin kamar jiya. Ya kuma kama hannunta da ɗayan hannunnsa. Nashi kayan kuwa sai drivern sa daya bisu da kallo yana murmushi ne ya tattara yabi bayansa da su. Yau ma cike da gulma wanda suka iso ke binsu da kallo suna kuma gaishesu da girmamawa. Yayinda wasu ke gwada son amsar kayan hannun AA ɗin amma sai ya girgiza kai kawai alamar (a'a). Kamar dai jiya harda masu leƙensu ta windows dan gulma. Suna shigowa kuma kowa ya nutsu aka shiga miƙa musu gaisuwa... Yau dai kai tsaye office ɗinta suka nufa. An gyara komai fes an saka air freshener masu daɗi, shine ya kunna wutar office ɗin dake a kashe, har saman desk ɗinta kuma yaje ya ajiye kayan hannun nasa batare daya kalleta ba ya nufi hanyar fita, ita dai tana tsaye tana kallon ikon ALLAH. Har yaje ƙofar sai kuma ya dawo gabanta yaja ya tsaya. Cike da gargaɗi fuskarsa a tamke murya a dake ya ce, “Daga yau wannan ya zama first and last da zaki bishi in har ba tare da Abah ba. Azumin mi kikeyi kuma”. Yanzun kam kallonsa tai cike da mamaki, sai kuma ta tura baki gaba ta ce, “Na nafila mana”. “To sai kisan yanda zakiyi da shi tunda baki sanar min ba.” ya ƙare maganar da dalla mata harara ya juya zai fita..........✍️ _Oh oh AA rigima azumin ne kuma sai an sanar maka munga idi🏃🏃🤣_ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖2️⃣0️⃣ ______________ *_LADIES COLLECTION AND MORE_* 08169307477 SHIN MATSALARKI RAMA CE KO KINA SO KI GYARA BREAST DINKI NE? KINA SO KIYI HIPS HAJIYATA KIYI KYAU? KO KUWA KINA SO KI RAGE KIBARKI KO TUMBINKI? KINA SON INGANTATTUN MAGANIN MATA NA GARGANIJIYA? Kinason shape dinki ya fito kamar yanda kowace mace zatai alfaharin ganinki bare ma oga ko saurayinki da kansa, Shin kinason ko koma yar dagwas dinki batareda kashe kudin surgery ba kokuma hana kanki cima da dama da kikeso sbd kinason jikinki yayi daidai? To matsalarki tazo karshe indai ingantattu sahihan maganin gargajiya ne da muka san inganci da gaskiyarsane, MAZA KI ZIYARCI LADYS COLLECTION AND MORE ko ta waya ko ta asalin inda take ki tabbatar da Buqatarki tazo inda zata biya insha Allah, LADY'S COLLECTION AND MORE ANAN NE ZAKI SAMU DUKKAN ABUBUWAN DA KIKE SO KAMAR HAKA 👇🏻 Zumar kiba Zumar breast Zumar hips Zumar infection Zumar sliming Zumar sabon budurci Back to virgin Abayas Atamfa Less Hijabs Supplements Kitchen items and more Muna maraba da masu siyan Daya ko 08169307477 Address bayan gidan drugs katsina State Kayan mu masu inganci ne sosae Muna aika kayanmu a ko Ina ba tare da wata matsala ba🙏🏻🙏🏻 SIYAN NA GARI MAIDA KUDI GIDA💯 *********** _______________ 20 WANNAN SAƘONKU NE😊 LA'ILAHA ILLA-ANTA SUBAHANAKA INNI KUNTU MINAZZALUMIN!! ......A tunzure Maanal data cika tai fam da wannan mulkin mallaka ta ce, “Kamar ya nasan yanda zanyi da shi? Yanzu ibadar ce kuma dan zan yi sai na sanar maka?”. Sai da ya buɗe ƙofar sannan ya waiwayo ya kalleta, cike da izza ya furta, “Ya rage naki”. Daga haka yay ficewarsa. Harara ta rakashi da ita. Sai kuma tama ƙofar gwalo dan shi dai ai ya riga ya fice abinsa. Kujerar zamanta ta nufa ta zauna tana ƴar dariyar ƙeta. Dama babu wani azumi da takeyi, tayi hakan ne dan gujema halinsa na salon tattaɓata daya ɗauka. Handbag ɗinta ta buɗe ta ciro ƙyaƙyawan bottle mai kama da cup ɗin nan na zamani dake cike da tea, sai gasashshen bread a ƴar bowl data sanyo batare da ko sanin Oum ba. Dan Inte tasa ta haɗa mata su. Hankalinta kwance ta fara aikinta tana karyawa. Sai zabga murmushi take da bata san na miye ba itama. Kawai dai ta tsinta kanta a cikin nishaɗin yin hakanne.... Kusan ƙarfe goma takarda ta iso mata daga office ɗin HOD. Bata komai bace sai ta tafiyarsu. Komai an kammala, sannan iya su da zasuyi tafiyar an basu hutun zuwa aiki gobe, idan ma daga yau mutum zai wuce gidan duk an basu dama amma sai zuwa break bayan anyi zama da su, suyi shiri kawai dan jibi in sha ALLAHU ƙarfe biyar na yamma jirginsu zai ɗaga. Ajiyar zuciya kawai ta sauke a hankali, zata ƙarasa ayyukanta kawai yau ɗin ita kam bazata tafi yau ba. Ƙarfe sha biyu suka shiga meeting. Sai a lokacin taga sauran wanda zasu yi tafiyar da su. Ashe harda cikin manyan ma. Dan akwai CFO, sai CMO, WCD da sauransu..... Sunyi nisa a meeting ɗin kafin CEO ya shigo shida Assistant ɗinsa. Bayan sun zauna ya nema afuwar jikinrinsa, acewarsa yana da baƙi ne. Maanal na ɗagowa suka haɗa ido. Da sauri ta janye nata. AS ne yay musu bayanin abinda zasuje yi, dan kowa da fanin sa, tare da karanto musu dokokin tafiyar. Zasu yi kwana goma ne, kenan zasu dawo azumi nada kwanaki takwas, dan yau saura kwana huɗu a fara. Daga ƙarshe yace kowa zaiga alert na kuɗi a cikin account ɗinsa domin shirin tafiyar. Bayan komawa ya zauna AA ya dubesu a dakensa, idonsa ne ya sauka akan Maanal a karo na barkatai, sai dai yanzu ita ba kallonsa take ba, tana magana ne da Yaqub ƙasa-ƙasa, da'alana akwai bayanin da yake mata da bata gane ba a maganar AS. Shima janye nasan yayi yanayinsa na canjawa sannan ya fara musu nasa jawabin mai cike da gargaɗin daya saka Maanal ɗagowa ta dubesa, harara ya sakar mata a kaikaice, wani gefen kuma nasiha ce. Ya rufe da addu'a daga haka meeting ɗin ya tashi. A tare Maanal da Yaqub dake mata sallama suka fito, sai kawai jitai an riƙo hannunta, juyowa tai da sauri, sukayi ido huɗu kuwa da mai gayya da aiki. Wani banzan kallo yay mata, sannan ya zubama Yaqub wani kallon gargaɗi daya sakashi barin wajen da sauri....... __________★ اَللَّهُمَّ اكْفِنِيهِمْ بِمَا شِئْتَ. Allahummak finihim bima shi'ita. _Ya ALLAH! Ka isar mini su da abin da Ka so._ _________★ AIRPORT Cike da farin cikin dawowarsa ƙasar haihuwarsa bayan dogon hutun daya sha na watanni uku yake fitowa a jirgin. Yayi fresh da shi dan ma tsufa ya cinye komai. Ƙarfarsa na gama sauka bisa ƙasa idonsa ya sauka kan amaryarsa, gefe kaɗan Oler ne da Rabilu sai sauran yaransa dai na siyasa. Sen... Bukar Kaugama yay wani murmushin jin daɗi mai cike da ma'anoni. Dan kuwa abu biyu ke ɗawainiya da shi, farin cikin dawowa ƙasarsa a gaɓar da zai mallaki ƴar shilar amaryarsa Maanal, da kuma kewar ƙasarsa ta haihuwa. Babu kunya amaryarsa tazo ta rungumesa tana masa barka da dawowa cike da farin ciki. Cikin irin nasu salon na manyan ƙasa ya wani ɗan bubbuga bayanta da ɗan mata ƙaramin kiss a gefen fuska sannan ya janyeta daga jikin nasa ya riƙe mata hannu. Sai lokacin su Rabilu sukayo wajensa suma. Fuskokinsu da farin ciki suke masa barka da zuwa. Shi ko yana amsa musu da kulawa. Basu wani ɓata lokaci ba suka ɗunguma inda jerarrun motocin da sukazo tarbarsa suke. Aka buɗe masa wadda tafi kowacce daukar ido shi da amaryarsa suka shige. Motocin na fitowa a airport ɗin tawagar uwargidansa na isowa itama tarbar tasa. Sunata sauri ganin sun makara, sai dai kuma basu dace ɗin ba. Drivern ta daya lura da motocin ne ya ce, “Ranki ya daɗe ai kamar ha Excellency ɗin ma can fa har sun fito”. Da sauri ta kalla motocin itama, tabbas kuwa motocin gidansu ne, sai dai motar da ta tabbatar yana a ciki tasan tana a gidan amaryarsa ne ajiye. A take ranta ya ɓaci matuƙa. Cikin fushi da jin zafin kishi tace, “Mubi bayansu”. Babu musu yay reverse, hakama drivern daya ɗakko yaranta shima, sai ma'aikatan gidanta, motar ƙawayenta ce ƙarshe, dan kuwa shiri tai na musamman akan dawowar tasa yau tare da shirya masa wani ƙwarya-ƙwaryar liyafa dan ranar tayi dai-dai fa Anaversary ɗin aurensu. Motocin su amarya na gama shiga maigadi zai maida gate ya rufe na uwargida suka iso. Dole ya dakata dan aguje suke. Fuskar Sen... Bukar da murmushi ya fito a motar, dan amaryar tasa ce ke zuba masa iskanci a motar, shiko ya narke mata. Da ƙyar ma ta bari suka fito. Sai dai me yana gama fitowa Uwargida ran gida na tsayawa a gabansa kamar wadda aka jeho. Hamshaƙiyar mace data amsa mace, dan kuwa sune manyan mata. Amma (iyayi na mutum nan yace bai son ƙiba🙄, shima kuma fa ƙaton gaske ne🥱). Yanda uwargidan ke kallonsa cikin ido dole ya ƙaƙaro murmushi tare da ɗan rungumota yana faɗin, “A'a ku kuma maimakon airport nan kuka yo?”. Itama a maimakon bashi amsa ɗagowa kawai tayi daga jikinsa, sai kuma ta kama hannunsa a dake ta ce, “Muje ko! Ga mutane a waje na jiranmu”. Gaba ɗaya daburcewa sen.. Bukar ya nema yi, dan kowaccensu da shirinta take an kai sunansa wajen teacher na zaure, ya kalla amarya ya kalla uwargida. Kowacce ta haɗe fuska abinta kamar dai a film. A ransa faɗi yake (wadda duk zata ɗaukeni gaba ɗaya daga hannunku ta kusa zuwa ai tula-tulan banza). Amaryar ƴar tsiyace ya sani, ita kuma uwargidan bata da yawan magana amma itama fa ba daga baya ba tasan ta inda take dafa shi duk rashin mutuncin da yake musu musamman ma ita da babu kalar da bata gani ba. Fuuu amaryar ta shige ciki ita mai zuciya, a zatonta ai zai biyota kamar yanda yake mata idan su kaɗai ne musamman ludayinta na akan dawo, (bata san yanzu akwai Manaal ba😂), wannan ya bama uwargida dama ta jashi suka wuce...... _________★ اَللَّهُمَّ مُنْزِلَ الْكِتَابِ، سَرِيعَ الْحِسَابِ، اهْزِمِ اْلأَحْزَابَ، اَللَّهُمَّ اهْزِمْهُمْ وَزَلْزِلَهُمْ. Allahumma! Munzila-l-kitabi, sar'a-l-hisabi! Ihzimi-l-ahzaba. Allahumma ihzimhum wa alzihlum. _Ya ALLAH! Mai saukar da littafi, Mai gaggawan sakamako! Ka karya kungiyoyin abokan gaba. Ya ALLAH! Ka karya su, ka girgiza su._ ________★ Idan Maanal tace yanda taga fuskar AA hankalinta bai tashi ba ƙarya tayi, ita shaida ce tun suna ƙanana ya tsani yaga tana kula wani, ko ƴan uwansa su Fawzan dan baida yanda zai yi ne kawai. Addu'a ta shiga karantowa a zuciyarta ita dai, dan yanda ya damƙi hannun nata ma ji take kamar ta fasa kuka. Suna shiga office ɗinsa a kusan tsakkiya ya sakar mata hannu, batare dako kallonta ya sakeyi ba ya wuce kujerarsa ya zauna. Aikinsa ya cigaba da yi tamkar yama manta da ita. Itama tun tana basarwar harta koma satar kallonsa, tama kai ta zuba masa idanun kai tsaye. Kusan mintuna ashirin taji ƙafafunta na neman sagewa, zuciyarta kuma nata angizata akan taje kawai ta bashi haƙuri, dan itama abinda yay ɗin ya sake fargar da ita alaƙarta da Yaqub fa dole ne ta tsaya a iya matsayin daya dace, ba kamar ada da suka ɗan fara ba kodan darajar aure da kare mutuncin wanda yake a matsayin mijin nata kuma ogansu a ma'aikatar gaba ɗaya. Sai kuma nasihar Ammie da Nene da ma Oum take mata faman kai-kawo a rai, basuce ta wulaƙanta kanta ba, amma sun gargaɗeta ta sauke nauyin dake kanta musamman a gaɓar data san abu kuskurenta ne. Gyarawar tata shima zaisaka ya gyara nasa kura-kuran su gina ƙyaƙyƙyawar rayuwar aure mai nagarta, dan ita wannan rayuwar tasu ta yanzu tana da banbanci da wadda sukai a baya ta ƙuruciya musamman ga ita dake ƙarama sosai, tunda ko acan bayan tasan nagaba yay gaba, kawai dai ita dashi haɗuwar jini ce bawai abotar kai da kai ba. A hankali ta fara takawa zuwa inda yake tamkar mai koyan tafiya, maimakon zama a visitors chair kai tsaye inda yake zaune ta zagaya. Kusa da shi kaɗan taja ta tsaya, hakan datai ya saka ziciyar AA ƙara gudu a ƙirjinsa, dama can bawani aiki yake yi ba, dan ji yay bama ya fahimtar komai. A yasan shima yana da kishi mai karfi a kanta, dan haka yake so ta gane kuma ta kiyaye, duk da kuwa sanin hakan a gareta game da shi ba sabon abu bane ba ai, amma ya fahimci kamar ta manta ne.... “AA!”. Ta kirashi da sunan da abakinta ya fara jinsa, ga shi nan kuma ya bisa dan wasu da yawa a yanzu bama su iya tantance ainahin sunansa sai AA Darma kawai. Duk da harbawar da zuciyarsa ta shiga yi a ƙirjinsa saboda tasirin kiran sunan nasa da tai bai kalleta ba, aikinsa kawai yake kamar gaske. “Besty fushi fa ba ƙyau!”. Ta faɗa tana leƙa fuskarsa cike da shagwaɓa. Nan ma tamkar dutse haka yay mata shiru. To itama fa zuciyar tata ta fara hawa, dan haka tai shiru kawai tana kallonsa. Tsahon mintuna uku taga ba kulatan zai yi ba kawai saita nufi barin wajen. Karan farko ya ɗago ido ya bita da kallo, itako ta wuce fuuuu alamar dai itama ta hau sama. Shima ai yasan yanda ya tsani yay magana ai masa shiru haka itama ta tsani ɗabi'ar. Har ita zai nunama zuciya da kishi, ita jiya ba ɗaukarta yay ya kaita wajen budurwarsa ba dan wulaƙanci, amma mitace masa, sai shi dan kawai ya ganta da abokin aikinta, to shike nan kuma bazata dinga mutunci da mutane ba'a Companyn?. Tana gama fita yay wani irin watsar da file ɗin hannunsa akan desk ɗin, sai kuma ya buga shi ya juya kujerar ya kalla bangon wajen daya kasance glass.... Manaal na shiga office ɗinta kayanta ta tattara tsaf tai fitowar ta. Duk inda ta gitta gaisheta akeyi, ita sai suka ma ƙara bata haushi. ALLAH ya sota sanda ta fito harabar kamfanin duk ana ciki, sai securitys ne kawai ke ɗan kai-kawo. Suma duk wanda ta gitta sai ya gaisheta, drivern AA dake cikinsu yana hira yana hangota ya taso da sauri, gaisheta yay, tare da faɗin bara ya ɗakko mota. Amma sai sai tace da fa shi karya damu su Abah na jiranta a waje. Jin tace Abah ya sashi dakatawa, haka ta fita a ƙafa a kamfanin. Tun fitiwarta harabar kamfanin sosai idon AA ya sauka a kanta, har maganarta da drivern sa da gaisuwar da securitys suke mata duk ya gani, kawai dai baya jin mi suke faɗa ne. Ji yay zuciyarsa ta ƙara hasala. Da ga zaunen da yake bazai iya ganinta ba yanzu saboda ta fita a kamfanin, dan haka ya miƙe tare da matsawa jikin gilashin. Sai ko ya hangota ta tsaida wata taxi ta shiga. Idan AA yace zuwa yanzu zuciyarsa batai kumburar da take neman fashewa ba yayi ƙarya. Shi yarinyar nan zata wulaƙanta da mutuncinsa a garin nan tana matarsa ta shiga taxi, shi zatama laifi ta fishi zuciya kuma. (Amma ai ta zo lallashinka kaƙi kulata) Wani sashe na zuciyarsa ta faɗa. Ji yay kamar ya kaima zuciyar naushi, amma dai ya daure, wajen ya bari gaba ɗaya, sai ma ya koma rukunin kujeru ya zauna, dan yasan ko aikin yace zai cigaba shirme kawai zaita tafkawa.........✍️ حَسْبُنَا اللهُ وَنِعْمَ الْوَكِيلُ. Hasbunal-lahu wani'mal-wakeel. _ALLAH ne mai isar mana, kuma madalla da shi abin dogaro._ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖2️⃣1️⃣ ______________ .........Maanal dai ta isa gida lafiya abinta, ALLAH ya sota a wallet ɗinta akwai kuɗi, haka ta cire ta biya shi tai ciki. A ƙasan maƙoshi AA dake bibiyarta ta hanyar GPS tracker ya sauke ajiyar zuciya. Sai kuma ya kife wayar a saman desk ya kwantar da kansa da bayansa jikin kujerar da yake ya lumshe idanunsa. Maanal na shiga Nuratu da Hajiya Turai na fitowa a mota, da alama zuwansu kenan. Idon Maanal ne ya sauka akan ƙaton akwatin da Bola ke fitarwa a booth. Tayi niyyar wucewarta, sai zuciyarta ta gargaɗeta da hakan kodan Hajiya Turai dake babbar mace. Dan zata iya sa'a da Ammiensu koma ta girmeta. Duk da ta lura da kallon banzar da Nuratu ke mata saita watsar da ita, kaɗan taɗan matsa kusa da su ta gaida Hajiya Turai dake kallonta itama irin kallon ƙasan idon nan na ƙurulla. Bata kuma jira jin a yanda ta amsa mata ba tai gaba abinta. Daga Nuratun har Hajiya Turai binta sukai da kallo, tsakin da Nurry taja yasa Hajiya Turai faɗin, “Ko itace Maanal ɗin?”. Baki Nurry ta taɓe, a gadarance ta ce, “Waifa Momy itace, shegiya baƙar banza, tana tafiya tana murguɗama mutane ɗuwawu dan asan tana da su ko”. Hajiya Turai dake bin Maanal ɗin da kallo har yanzu ta ce, “Yoni Baby yarinyar nan ma nada muhimmanci kuwa a gidan nan? Kamar fa daga wajen aiki take a ƙafa alamar taxi ce ta ajiye ta, ace duk motocin gidan Darma ace surukar gidan na hawa taxi kuma matar AA duk dukiyarsa”. “To Momy dama ba aikin asiri bane yasa ta shigo gidan, tunda ya riga ya gama da ita tun a titi wace soyayya zata gani kuma. Ba dai na shigo gidan ba, sauran asirin ma dan ubansa zan ƙarasa karyashi ne. Ana gama bikinmu zata ware dan sai ta sha ƙi baƙin cikin shagalin da za'a sha kafin na sa ya saketa.” Sosai Hajiya Turai ta sanya dariya. Tamkar wasu ƙawaye ta bata hannu suka tafa. Daga hakan suma suka nufi sashen Mamy cike da nishaɗi... Oho Maanal ma bata san sunai ba, tana shiga sashen Oum sama ta wuce abinta. Ta samu Oum da baƙuwa. Maanal ta gaishe da matar ƙyaƙyƙyawa da ita. Itako cike da kulawa take tambayar Oum, “Hajiya Fateema ko ɗiyar tamu ce?”. Murmushi Oum tayi, ta ce, “Itace Hajiya Shuwa”. “Kai Masha ALLAH, yarinya dirarriya ƙyaƙyƙyawa haka ga nutsuwa. A ruwan idon autanki bai tafi a banza ba ashe, ashe yasan miya taka, ɗaya yake son tsamowa a cikin dubu, to ALLAH ya sanya albarka a cikin auren nasu”. Oum dake ta murmushi ta ce, “Amin ya rabbi”. Sai kuma ta kalla Maanal dake nufar hanyar bedroom. “Baby wai har kun tashi ne? Ina Bestyn naki?”. Cikin danne komai Maanal taima Oum bayanin su an basu damar zuwa suyi shiri ne saboda tafiyar jibi. Oum ta ce, “Tofa tafiyar ta tashi ke kenan?”. Manaal ta ce, “Eh Oum.” daga haka ta shige ta barsu. Hajiya Shuwa da gaba ɗaya Maanal ɗin ta ƙara birgeta ta ce, “Kai masha ALLAH, jiba yanda ta saki jiki dake kamar ba surukai ba, haka naso mu rayu da Amisha amma ƙawayen banza sukai mata huɗubar tsiya. Shiyasa yanzu nace masa aure zai ƙara, dan na gaji da ɓacin rai wlhy Hajiya Fateema. Wani lokacin idan aka juya min kan yaron nan ko kallo ban isheshi ba, shiyyasa kikaga nai tafiyar nan marocco ko sallama ban miki ba. Shi ma kansa bai san na tafi ba sai bayan kwana uku”. “Kiyi haƙuri Hajiya Shuwa jarabawa ce, kowa da irin tasa kuma. Amma Amisha ta bama kowa mamaki, dan nidai ina ganinta shiru-shirun nan banyi zaton haka a gareta ba. Ni kaina yanzu saboda tasan yanda muke dake bata shigowa gidan nan, har mukaci bikin nan muka tsare bata leƙo ba, shima Ameer ɗin Fawzan yace baije mana ɗaurin aure ba, shine ma ya haɗasu faɗa shine yake cemasa ai dama Amisha tace ba sonsu muke ba, nice ke zugaki kina wulaƙanta masa mata. Nace ma Fawzan ya barsa baya cikin hayyacinsa ne kawai”. Kwafa Hajiya Shuwa tayi, ranta na sake mata zafi da halin da ɗan nata yake ɗaya tilo namiji. Su Hajiya Shuwa sune makwaftan su Oum ta hannun damar su, asalinta ƴar marocco ce girman Libya, daga can mijinta Alhaji Mubarak KT ya aurota, yara biyu suka haifa kacal a duniya, Ameer shine babba, bayan haihwarsa ma ta jima bata sake ba harta haƙura ma sai ga ciki. Sunyi farin ciki sosai ita da mijinta, ALLAH ya sauketa lafiya ta haifi mace ƙyaƙyƙyawa itama suka saka mata Ameerah, bayan haihuwar Ameera bata sake ba kuma, yarinyar nada shekara goma a duniya ALLAH yayma Alhaji Mubarak rasuwa sakamakon bugawar zuciya na dare ɗaya daya samu. Shi ɗin babban ɗan gwagwarmaya ne kuma ɗan siyasa ta wani gefen, duk da dai bai saki jiki a siyasar ba gaba ɗaya. Yana kuma kasuwanci sosai. Ya tafi ya barta da yaran su biyu, ita ga cigaba da kulawa da rayuwarsu har girma, duk da dai sanda ma ya rasu Ameer har ya shiga University yana first year ɗinsa. Ameera ce ke primary 4. Tasha wahala da dangin mijinta dan dukiyar ƴaƴanta komawa tai tsole musu ido, acewarsu ai ɗan uwansu ne ya tara, bazai yiwu ya aurota daga wata ƙasa ba daga sama tazo ta mamaye komai, aiko suka ƙulla mata akan ta basu yara su cigaba da riƙewa da dukiyar ita kuma ta koma ƙasar ta. Hankalinta ya tashi, dan babu wanda take tausayi irin Ameera. Nanfa ta shiga faɗi tashin ganin hakan bata kasance ba, tana neman taimakon abokan mijinta, amma mi, kowa sai ya nuna sai in ga amince zata auresa zai yi hakan, wasu ma da iskanci suke zuwa mata. A cikin wannan kai-kawon nata ne suka haɗu da Ambassador Aliyu Darma, ta dalilin nashi abokin shima da ya kasance abokin mijin Hajiya Shuwa. Shima dai yayi mata maganar banza ne, ta fito ranta a ɓace shine sukaci karo da Abah da yaji komai dan yay ƙoƙarin shiga office ɗin ne yaji kalaman abokin nasa sai ya tsaya, amsar da Hajiya Shuwa ta bashi yay matuƙar birgesa, data fito kuma ya ganta mace mai kamala da nutsuwa. Baice mata komai ba a lokacin ta wuce ya shige, bai kuma nunama abokin nashi yasan komai ba shima. Sai da ya dawo gida ya sanarma Oum komai, hankalinta ya tashi baiwar ALLAH harda kukanta. Itace ta ƙarfafa Abah suka shirya taimakon Hajiya Shuwa, washe gari taje har gida ta sameta, zuwa ranar kuma Hajiya Shuwa ta sallama ma dan Oum ta sameta tana haɗa kayanta, tana shirya nasu Ameera domin danƙama dangin uban nasu kamar yanda suka buƙata. “ALLAH sarki na ALLAH baya ƙarewa duk rintsi”____wannan itace kalmar da Hajiya Shuwa ta faɗa bayan Oum ta gama mata bayanin abinda ya kawota, daga haka ta rungume Oum tana kuka... Wannan shine sanadin tarayyar su, Abah ya tsaya mata akan komai har sai da aka mata tsakani da dangin Alhaji Mubarak, aiko sai akaita gulma ai sonta Abahn keyi, dan har Mamy ma ba sonta take ba ta kuma tsargu da hakan, musamman data roƙa Abah ya sayi filinsu dake a kusa da su dan lokacin su suna a zone 4 ne. Da farko Aban yaƙi, gudun kar ace ta basu ne shiyyasa suka taimaketa, sai da taita roƙonsa da tabbatar musu zamansu a kusa zai zamar mata garkuwane sannan ya amince. Ƙaton filine amma sai da Abah ya ƙara da wani a bayansu shine ya gina wannan babban gidan suka zama makwaftan juna. Anta jira aga Abah ya aure Hajiya Shuwa amma akaji tsit har ma shekaru suka ja. Ameera ita ta ɗan ragema Oum kewar Maanal a lokacin, har ALLAH yasa ta wuce karatu waje ita, yanzu haka tana can, amma tana gab da dawowa ƙasar haihuwarsa. Amisha ƴar ƙanwar Hajiya Shuwa ce, auren zuminci ne ita da Ameer, duk da kuwa su sukaga juna suka gina soyayyar su ba iyayen suka haɗasu ba. Farkon auren kowa nata yabon Amisha musamman data kasance da suffar mutane masu shiru-shiru da haƙuri, sai da tafiya tai tafiya sai komai ya canja, yanzu Amisha aya take gasama Hajiya Shuwa a hannu, har takai wataran idan ta juye kan Ameer ɗin sai ya manta da Hajiya Shuwa na a gidan ma tare da su gaba ɗaya. Sai ta dage da addu'a sai abin ya sassauta. Watanni kusan bakwai kenan abubuwa suka rikice a tsakaninsu shine kawai ta tattara ta wuce marocco sai jiya ne take dawowa, bata nan akai bikin su AA ɗin, sai bayan wucewarsu aiki ta shigo shine suketa hira da Oum ɗin dan ƙawaye ne sosai... Baƙi da aka kira Hajiya Shuwa a waya cewar tayi ya sata tafiya gida, sai lokacin Maanal ta fito falon, tayi wanka abinta fes sai ƙamshi take. Takardar da aka basu a wajen aiki ta bama Oum ɗin, tare da zama gefenta ta ɗaura kanta a kafaɗarta. Shafa kan nata Oum tayi tana murmushi, cike da kulawa ta ce, “Ko azumin ya fara duka?”. Shaf Maanal ta manta da ƙaryar azuminta, ta kalla Oum tana dariya. “Lah Oum ƙarya fa nayi dama babu wani azumi ɗazun ban son karyawa ne kawai”. Idanu Oum ta zaro waje, sai kuma ta dungure kan Maanal ɗin tana dariya itama. “ALLAH ya shirya kin Baby na to da har yanzu bata canja hali ba”. Dariya itama Maanal tayi, tare da ɓoye fiskarta a jikin Oum ɗin. Itama Oum na cigaba da dariyarta ta ce, “To aiko tare zamu shiga kitchen yanzun nan idan munyi sallar zuhur”. Haka ɗin kuwa akai, bayan Oum ta kammala duba takardun ta riƙe a hannunta akan zata nunama Abah, duk da dama ta masa bayani akan tafiyar amma bai ce mata komai ba. Salla suka je sukayi, koda suka fito kai tsaye kitchen suka nufa, sun fara aikin kenan Mamy da Hajiya Turai da Nurry suka shigo sashen. Oum ce kawai ta fita suka gaisa, basu wani jima ba Hajiya Turai tace bara ta wuce tunda taga Oum ɗin aiki suke itama zataje wani waje ne. Godiya Oum tai mata, sunzo zasu fita Maanal ta fito ta gaishesu. Tana kallon hararrata da Nurry take bata kula ba ta koma kitchen ɗin abunta. Sai da zasu fita Mamy ke faɗin, “Lafiya ƴarki ta dawo aiki da wuri haka yau?”. “Lafiya Lau, daga office ɗin ne aka basu damar zuwa suyi shirin tafiya ne”. Sai Mamy ta rasa ina zata kamo zancen tafiya kuma. Amma bata nema ba'asi ba dan tana son su fita su ƙarasa zancensu da suke da Hajiya Turai. Ba kuma tason ma Hajiya Turai ta fahimci bata san da zancen da Oum ɗin keyi ba dan yanzu ta gama cika mata baki akan batun dawowar Maanal a taxi. Ta nuna itace ta kafa sharaɗin sai dai Maanal ta hau taxi amma ba motocin gidan ba, shiyyasa sukaga hakan. (Mamy an iya ƙayya🤣🙏) Tsulum Nuratu taja ta tsaya tana faɗin, “Momy bye nima zan zauna taya Oum girki, bara naje wajen sis.. Manaal ɗin”. Daga haka ta juya ciki ta nufi kitchen tabar su Oum na murmushi. Duk da dai abinda Nuratun tayi ya bama Mamy takaici, amma sai ta danne... Maanal na cikin aikinta ita da su Inte dake musu ƴan yanke-yanke a work table Nurry ɗin ta shigo. Ko kallon inda take Maanal batai ba, sai su Inte ne ke gaisheta a girmamame, itako tana amsa musu a yamutse. Sun riga sun san halinta shiyyasa basu wani damu ba. Dai-dai nan Oum ta dawo, dan haka Nuratu ta nufi wajen Maanal cike da makirci tana faɗin, “Sis.. Maanal mizan tayaki da shi?”. Wani shegen murmushi kawai Maanal ta saki tana kallon Nurry ɗin a tsakkiyar ido, a zuciyarta faɗi take, (Yarinya ai indai makirci ne baki yar a ƙasa ba, idan kuma kikace ni dake ta haka zamu buga wasan ƙasa zaki sha kuwa a hannuna). A fili kam maimakon bata amsa fruits da za'a gyara ta nuna mata da hannu fiskarta da murmushin har yanzu. Oum data ƙaraso inda Maanal ɗin take ta ce, “Yauwa gyara su kam Nuratu, sai a gama da wuri dan yau nasan Auta a jigace zai dawo gidan nan ba'a aika abincin rana ba hira da Hajiya Shuwa ta ɗauke min hankali”.........✍️ _Hhhhh gaskiya Maanal baki ƙyauta ba, ya zaki bama Nurry ɗinmu gyaran fruits 🤣🤣_ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖2️⃣2️⃣ ______________ ........Matuƙar tiƙe Nuratu takaici yayi, amma bata da damar cewa bazatai ba tunda itace ta kawo kanta. Sannan duk iskancin nan nata mugun shakkar Oum take ji, sosai matar na mata bala'in kwarjini, ga son da kowa yasan AA na mata tana son tai kamun ƙafa da ita. Kai bama ita ba, ko iyayen nata kan faɗi irin cika musu idon da Oum ɗin keyi, dan duk yanda suka shirya tunkararta da rashin mutunci suna yin arba da ita komai ke ƙwace musu. Cike da son ƙular da Nurry Maanal ta shiga yima Oum hira suna dariya. Aiki sosai Nuratu ta shaƙa, dan ji ta dingayi kamar ta juya ta caka ma Maanal wuƙar hannun nata. Sunata aikinsu da hira, dan Maanal ma dai ke girkin Oum hira kawai take tayata, Nurry kuma anata aikin gyara fruits da take yi cikin takaici shiyyasa bata wani sauri, koda yake ba aikin ta iya ba dan bayi take ba sam. A gida komai masu aiki ne ke mata shi, idan iskancinta na ka ma hatta underwears ɗinta basu take su wanke sai tace matching baya wankewa da ƙyau. Su Inte dai sun gama sun gyara wajen sun fita suna gyaran falo da saka ƙamshi. Dai-dai nan AA ya shigo da sallama. Da sauri Nurry ta juya har tana neman yankewa da wuƙa, sai Oum da itama ta juya tana masa murmushi. Maanal kam tamkar batana san mike faruwa ba aikinta kawai take yi. “Lallai yau Auta ne da tashi a office ko five baiyi ba ma?”. Oum ta faɗa tana miƙa masa ruwan data tsiyaya masa a cup. Amsar ruwan yayi, tare da jan kujerar work table ɗaya ya zauna. A kasalance ya janye idanunsa dake akan ƙullin da Maanal tai ta bayanta na rigar girki dake jikinta. Kamar wanda baya so ya ce, “Oum na gaji ne ALLAH shiyyasa na gudo”. Murmushi kawai Oum ɗin tayi, dan tasan ba hakan bane ba, ta tabbata dan Maanal ta dawo ne. Cike da ɗan rawar murya Nuratu data tsaresa da kallo ta shiga gaisheshi. Ikon ALLAH, to shifa sai yanzu ma yasan akwai wani a kitchen ɗin bayan Oum ɗinsa da Maanal. Waiwayowa yay ya kalleta, sai kuma ya ɗauke idanun a taƙaice ya amsa, cikin kuma halin ko'in kular nan nasa kai kace baima gane Nuratun ba. Oum da bataji daɗin yanda yayma Nuratun ba tace, “Nuratu ce fa baka ganeta ba ne Auta?”. “Na ganeta mana Oum! Nifa yunwa nake ji”. Sarai Oum ta fahimci zancen Nuratun yake so a kawar, dan haka ta girgiza kai kawai da juyawa ta kalla Maanal dake ta aikinta. Juyowa tai ta kalla AA kuma, sai taga ya zubama Maanal ɗin ido ne a kaikaice. A take Oum ta fahimci akwai abinda ke faruwa a tsakaninsu, dan da wuri take gane idan sunyi faɗan nasu. Nan ma kanta ta ɗan girgiza, batare da tace komai ba ta buɗe ƙaton freight ɗin kitchen ɗin ta fiddo kwalin fresh milk, a gabansa ta ajiye tana faɗin, “Fara da wannan ga Baby nan na mana girki an kusa kamallawa”. Idanu ya waro waje, “Kai Oum ana dai mana jagwalgwalo, miyasa baki mana da kanki ba?”. Dariya Oum tayi, ta nufi hanyar fita tana ƙoƙarin ɗaga wayarta dake ring, ta ce, “Oh jagwalgwalo ko? Babyn ce ke jagwalgwalo! ALLAH yasa ta hanaka abincin nan mu gani”. Ta fice batare data jira mizai ce ba. Shima bai ce komai ba, sai ma ajiye kofin fresh milk ɗin daya ɗauka zai fara sha yay ya miƙe. Nuratu da gaba ɗaya jikinta ke wani irin tsuma, tana jin kamar ta daka tsalle ta rungumesa take ji ta bisa da kallo, duk da tun kwalliyar safe ce a jikinsa yama cire jacket ɗin samna suit ɗin sai fara tas ɗin long sleeve shirt dinsa dake clean harda karin gugarta kamar yanzu ya sakata wani irin ƙyau yay mata, ga ƙamshinsa mai saka kasala na tashi kamar a yanzu ne ya saka turaren. AA kam ko kallon inda take baiyi ba, hankalinsa kwance, kansa kuma tsaye ya ƙarasa inda Maanal take ya tsaya dab da ita. Ita ko da yake ta juya masa baya bama tasan da zuwansa wajen ba, tadai ji yawaitar ƙamshin turarensa sosai. Hannayensa duka biyu ya zagaya a saman cikinta ya rungumota, tare da ɗora kansa a wuyanta duk a lokaci guda. Harga ALLAH tsorata tayi, dan haka tai wata ƴar zabura tana ƙoƙarin juyowa. Amma sai ya sake riƙeta da ƙyau ta yanda hakan ya gaggareta. “Ni kika wulaƙanta kika tawo a taxi ko? Ki saurari hukuncina dan sai na saɓa miki”. Ya faɗa a cikin kunnenta cike da isa babu alamar wasa a furucinsa. Amma irinsu Nuratu dake a gefe sai su ɗauka wata maganar soyayya yay mata a kunnen, dan daya gama faɗa harda su manna mata ƙaramar sumba a kan wuya ya ƙara faɗin, “Ai dama kinfi kama da Kukun”. Haushi ya saka Maanal ɗaga ludayin hannunta kamar zata ƙwala masa saboda yace tafi kama da kuku. Sakinta yay yaja baya yana murmushin ƙeta na cin nasarar ƙular da ita, dai-dai ta juyo gaba ɗaya yay mata gwalo kuwa, zaburowa tai kansa da ludayin. Aiko da ɗan gudu ya ɗauka fresh milk ɗinsa ya fice a kitchen ɗin yana dariyar data saka Nurry yin sumar tsaye dan mamakinsa da al'ajabi da yanda dariyar tasa tai bala'i bala'in tafiya da imaninta. Dan zata iya rantsewa bata taɓa ganin yana dariya kamar haka ba a rayuwar sanin datai masa kaf. Bawai yana ƙyaƙyalƙyalawa bane sosai a yanzun ma, amma illahirin haƙwaransa sun bayyana a waje. Oum dake shigowa itama tana dariyar yanda AA ɗin ya fito a kitchen ɗin da ɗan gudu ce ta riƙe ludayin Maanal, tana dariya ta ce, “Amasa haƙuri babyna bazai ƙara ba”. Cike da shagwaɓa Maanal ta ce, “Oum gwalo fa ya min, yace nafi dacewa da kuku, kinga yana sake yimin gwalon ko”. Tai maganar tana nuna bayan Oum da AA yake tsaye daga can waje. Juyowa Oum tai ta kallesa itama, sai ya haɗe fuskar kamar bashi ke yin tsokanar ba. Oum data tabbatar yayi ɗin ta ce, “Okay na bari ta kwale ka ko”. “Tadai fasan kai Oum, kuma dan ALLAH kinga na kulata tunda na shigo?”. “To ya zan sani tunda fita nayi, sai dai a tambayi Nuratu.” Oum ta faɗa. Maanal ce ta amshe da faɗin, “ALLAH Oum yayi, kuma a tambayi Nuratun ma ai tana ganinsa”. Ai kafin ma Nuratu da takaici ya kume tsigar jikinta har wani tashi take yi tayi magana ya sake ma Maanal gwalo yabar wajen. Karaf kuwa a idon Oum. Salati Oum ta ɗauka da faɗin, “ALLAH ya shiryaka Auta ka daina tsokalar min yarinya kaikuwa. Sai kuma ta kama hannun Maanal, kinga manta da shi zaki rama ne, badai zai dawo cin abinci ba taron dangi zamu masa harda Fawzan in ya dawo”. Daga haka suka koma Oum ta tayata suka ƙarasa girkin aka bar Nuratu da takaici. Gashi babu damar barin kitchen ɗin kuma. Dole ta haƙura suka kammala ikin duka suka shirya a dining sannan suka tafi salla. Sanin AA nan zai dawo yasa ta maƙale abinta, acewarta sai ta sake ɗaura ɗammara na maganin Maanal ɗin, hakan kuma bazai faru ba sai ta nutsu ta fahimceta.... ________★ Shagali sosai aka sha a gidan Sen.. Bukar, sai dai shi gaba ɗaya hankalinsa nakan Rabilu ne dan ya fahimci akwai magana a bakinsa. Duk kuma yanda yaso su kebe da Rabilun hakan ya gagara, dan uwargida yau tayi masa kane-kane. Kuma tsaf ta fahimci inda hankalin nasa yake dan haka taita dariya a ranta. Zuwa yanzu babu abinda bata sani ba game da Maanal. Tun sanda mijin nata ya kawo mata batun ƙara auren nasa ta shiga bincike da bibiyarsa har sai da ta gano akan wadda yake rawar ƙafar. Da farko ta shirya tsaf domin nakasa rayuwar Maanal ɗin, dan ta ɗaukama kanta alwashi wata bazata sake shigo mata gidan miji ba, wanda suke a cikin ma tana shirin ficewarsu ne. Sai kuma UBANGIJI mai hikima ya nuna mata ikonsa rana tsaka ta samu labarin auren Maanal ɗin da AA Darma, yaron data taɓa ji a bakin mijin nata yana aibantawa da ɗaukar alwashin wulakanta rayuwarsa saboda yafi su kusanci da shugaba ƙasan. Dariya sosai sukaci ita da ƙawayenta masu ɗaurata a hanya, dan ita babu abinda ya dame ta da wata matsalar mijinta da AA Darma, ita AA Darma ma ya biyata a yanzu tunda ya ɗauke Maanal. Farin cikin wannan aure yasa ta shirya wannan liyafar ta Anaversary ɗinsu, abinda bata taɓa yi ba kuwa. Shi kansa Sen yayi mamaki, amma sai shanye a ransa yana faɗin (Hakan dai bazai hana ƴar shilata Maanal shigowa ba). Bayan an gama shagali yanda ta kanainaye shi dole ya haƙura, dan ya ma nema Rabilu ya rasa. Bai san ita ta kora Rabilun ba dan dama ta mugun tsanarsa saboda tasan shine mai nema masa matan auren kuma kawalinsa na matan banza. Ta jima da son rabasu sai dai hakan ya gagara.... “Sen... Namu”. (ALLAH sarki Uncle ɗina KA BARI YA HUCE MAI RABON YA ƊAUKE🤣) __________★ Daga sashen Oum AA sashen Mamy ya nufa domin gaisheta, dan ƙa'idarsa ce yin haka daga shi har ƴan uwansa. Da safe zasu shiga su gaisheta, hakama idan sun dawo aiki, sai dai da wahala kaga sunyi zaman mintina ashirin a wajen nata. Saboda tun farko bata jasu a jikinta ba, ita a dole tanama Oum kawaici. Wanda sai daga baya AA ɗin ya fahimci ba hakan bane ba... Zaune ya sameta a falo Haule na gyara mata ƙumba suna kallo, glass bowl ne a gabanta tana shan fruits da aka yanka ƙanana a ciki. Cike take taf da haushin zaman Nuratu a sashen Oum. Da sauri Haule ta shiga gaisheshi. Batare daya kalleta ba ya amsa ciki-ciki yana kaiwa zaune a kujerar kusa da Mamyn, ganin yanda taketa faman ɓata fuska ya sashi yin murmushi a zuciyarsa. Shi wlhy wani lokacin yanda ta saka kanta a ƙunci babu gaira babu sabar tausayi take bashi. Da ace zata ajiye makanamta dai zata kasance cikin farin ciki ne da nishaɗi ta kuma samesu fiye da yanda take so su da take faɗan a kansu. A hankali ya matsar da jikinsa kusa da ita gab, batare da yayi magana ba ta zare spoon ɗin dake hannun nata ya ɗauka yanka ɗaya na apple ya kai mata baki. Ƙuri tai tana kallonsa kamar wadda ta suma. Domin abune da bai taɓa kwatanta yimata ba sai dai taga yanama Oum. Shi kuma ya ɗauka aniyane a ransa na canja salon mu'amularsu ko hakan zai sassauta zuciyarta ta ajiye makaman yaƙinta akan Oum, dan baya fatan wani a gidan ya fahimci halayyar nan ta Mamy. Ganin yanda take kallon nasa tamkar hawaye na son taruwa mata a ido ya sashi jinjina mata nasa kan tare da sakar mata murmushi mai sanyi, sai kuma ya ɗan buɗe bakinsa alamar (haa). Kamar sakarai a hankali ta buɗe lips ɗinta kuwa ya saka mata yankam apple ɗin, ta shiga taunawa tana kallon nashi. Sai ta samu kanta itama da amsar spoon ɗin ta ɗauka kankana ta bashi. Babu musu ya amsa yana mata murmushi, kafin ƙasa-ƙasa ya furta,.....✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖2️⃣3️⃣ ______________ .........“Jazakhallahu khairan Amaryar Abah, aminiyar Oum, Maman Fadeel da Fawzan da Auta Ajwaad”. Yanda ya jero kalaman nasa masu kama da kirari ya sata sakin murmushi a bazata, sai kuma a hankali takai hannunta ta shafa kwantaccen gashin fuska tana sakin murmushi mai haɗe da ƴar dariya. Samun kansa yay shima da yin dariya, ya kama hannun nata ya sumbata. Ji Mamy tai tamkar zuciyarta na ɓaɓɓarewa gida biyu, cike da shauƙi mai girma ta sake kai hannun nata saman sumar kansa ta barbaza. Nan ma dariyar yay mata. Tare da faɗin, “Thanks you Mamy. Dan ALLAH ki daina damuwa akan komai, nafi son kullum nazo naga fuskarki cikin farin ciki. Na tabbata kuma idan kika ajiye komai zaki samu fiye da haka. Bakiga Oum ba, koda yaushe tana cikin farin ciki, saboda tana da ƙoƙarin ɗaukar jarabawa da sauƙi. Mamy muna sanki kamar yanda muke son Oum, yanda kuke treating ɗin rayuwarmu ne ya banbanta. Dan ALLAH ki ajiye komai kinji Mamyna”. Kanta kawai ta jinjina masa, duk da kalamansa sun mata daɗi matuƙa a zuciya wani yanki na cikinsu sun mata zafi da ɗaci, ba komai ya kawo hakan ba kuwa sai jingina Oum da yayi a ciki har yana nuna mata yin koyi da ita. Cikin basar da komai ta ce, “ALLAH ya shige mana gaba Ajwaad! Kaga Nuratu?”. “Amin ya rabbi, na ganta tana sashenmu”. Ya bata amsa a tausashe cikin danne komai, dan harga ALLAH ko sunan yarinyar nan baya son yaji ta ambata masa. Cikin tausasawa Mamyn ta katse masa tunani da faɗin, “Ajwaad kaga dai komai kace zan yisa domin samun farin cikinka, kaima ina son ka kula da Nuratu domin samun farin ciki na a ɗan zaman nan da zatayi da mu na azumi, Hajiya Turai ce zata umrah shiyyasa ta dawo nan ta zauna. Idan ka kwantar da hankalinka zaku fahimci juna a ɗan zaman nan da zatayi kafin bikinku. Ajwaad Nuratu na sonka sosai, irin son da duk yanda ka taƙwanrata zata maka biyayya, bar ganinta haka a tsaitsaye tana da hankali, gata ne kawai da Hajiya Turai ke mata na tsiya ya mata yawa. Amma nasan kai ɗin jarumi ne, zaka gyarata a yanda kake so yarona”. Kansa kawai ya jinjina mata, dan baya son raunana mata zuciya, sannan yana son binta da wannan salon ko ALLAH zai taimakesa ta canja. Itama dai kusan tunani iri ɗaya sukeyi, dan tana ganin AA ɗin ya amshi batun nata da muhimmanci a yau, dan haka zuciyarta gaya mata take lallai tana da buƙatar canjawa, canjawa irin wadda Ajwaad ɗin keso kodan samun nasara a kansa, dan ta ƙarfin tsiya tabbas bazata taɓa samunsa ba, tunda ta gwada hakan tsahon shekaru kenan babu wani canji saima caɓulewar abubuwa. Ita dama bata jin su Fadeel, a ganinta duk a tafin hannunta suke. Ajwaad shine uban taurin kai da kafiya, sannan shine baisha nn ɗinta ba, zaifi mata wahalar janyewa fiye da su Fawzan da suka sha daga jikinta bayan dakon ɗaukar ciki dana haihuwa. Dan bazatace raino ba wannan kam Fateema tayi tare da cin kashinsu da fitsari. Dan in har batai ƙarya ba zata iya irga adadin wanke musu koda kashi da fitsari ne, shima sai in Oum ta fita wani uzirin ne ma. AA nason tashi ya tafi sashensa ya watsa ruwa amma hirar da Mamy ke jansa da ita cike da farin ciki yasa ya haƙura ya zauna har akai kiran magrib, ƙarshe alwala ma catai yaje ɗakinta yayi. Haka kuwa ya haura saman yayo duk dan sanyata a farin ciki. Daya fito taita sanya masa albarka jitake kamar kada ta barshi ya tafi, sai dai hakan ya zama tilas babu yanda ta iya. Bayan fitarsa da wannan farin cikin ta kasance, tana idar da salla kuwa ta kira Maman Saheeba ta sanar mata komai. Suna yanke wayar daga can Maman Saheeba tace “Ina yaya Kamila bazai yiwuba, lokacin samun irin wannan farin cikin naki baiyi ba, ai idan har na bari kikai nasarar jawo Ajwaad jikinki to tabbas aurenshi da Nuratu bamai yiwu bane ba, nasan halin MAKIRIN yaron nan, tsaf zai juya miki tunani da hatsabibancin sa, dan yafi sauran ƴaƴanki taƙadaranci kema kina faɗar hakan da kanki. Kansa a buɗe yake matuƙa da sanin duniya, in har ba a yanayin da kuke ciki a baya ba lallai zai botsare ne”. Nanfa ta shiga kai-kawo na neman mafitar hanyar ɓata komai.... ★Ana idar da salla AA dole gida ya dawo domin yin wanka kafin isha'i, tunda Mamy ta cinye masa wancan lokacin. A tare suka shigo da Ya Fawzan, babban yaya bai dawo gidan ba har yanzu. Sashen Mamy Fawzan ya nufa domin gisheta, shi kuma AA ya nufi nasa sashen dan yin wanka. Bayan Fawzan ya gaida Mamy zai tashi sai ta ɗakko masa hira, mamaki ne ya kama shi, dan sam babu hakan a tsakaninsu tun suna yara. Tsakaninsu da Mamy umarnine nayi ko bari kawai sai gaisuwa. Amma batun shaƙuwa ko hira ko wasa da dariya Oum ce kawai ke musu da Abah. Daurewa yay yana amsa mata sama-sama, tsulum sai ga Saheeba da yara, da yake fita tayi Mamy bata kawo komai a ranta ba. Dan sai yanzun ne suke dawowa, zama Anum tai a jikin Fawzan tana masa labarin inda zukaje, yayinda Naufal ya nufi Mamy, a mamakin Mamyn sai Saheeba ta nema wajen zama tana faɗin, “Washa Mamy na gaji”. Murmushin yaƙe Mamyn tai mata kawai da sannu a taƙaice dan harga ALLAH batayi murna da zaman Saheeba ɗin ba, dan zuwanta ya katse mata kasancewa da Fawzan. Kiran sallar isha'i ya saka Fawzan miƙewa ya ajiye Anum data fara barci saman gadon Mamy, cike da kulawa yace ma Naufal, “Tashi muje massallaci my boy”. Da kallo Mamy da Saheeba suka bisu, suna gama fita Saheeba ta saci kallon Mamy ta gefen ido. Baki ta taɓe kaɗan, sai kuma ta ƙawata fiskarta da murmushi dan kaf MAKIRCIN Mamyn ta iya itama. “Lah Mamy wai ina ƴar hutun taki? Banji motsimta ba”. Ta faɗa baki a washe. Miƙewa Mamyn tayi, sai kuma a ɗan yanayin jin haushi ta furta, “Tana sashen ƙanwar uwarta Fateema”. Cike da mamaki Saheeba tace, “Tomi ya kaita can Oum?”. “Oho mata”. Mamyn ta faɗa cike da takaici tana kabbara sallarta. Harara Saheeba ta dalla mata cike da jin haushi ta fice a ɗakin zuwa nata sashen.... ★Nuratu dai tunda aka idar da sallar magrib ake dakon dawowar AA sashen, sai dai kuma taji tsitt. Sai faman hararar Maanal dake karatun Alkur'ani takeyi, itako bama tasan tanai ba. Lokacin isha'i yayi suka gabatar, suna idarwa Maanal ta shiga bayi da nufin yin wanka. Hakan da Nurry ta gani itama sai ta fito ta nufi sashen Mamy. Oum ca take ta tafi kenan, sai take cemata ya zata tafi bataci abinci ba. Batare data tsaya ba tace, “Oum ina zuwa yanzu zan dawo”. Daga haka ta ƙarasa ficewa da sauri. Sanda Nuratu ta koma sashen Mamy bata sani ba, sai da ta fito cikin kwalliya da uban ƙamshi daga ɗakin data sauka sannan Mamy ta ganta. Harara ta zuba mata, zata fara mata faɗa tai saurin rungumeta tana faɗin, “Mamy ki fahimceni, na zauna ne dan nayi maganin shegiyar can, kin san kuma Ya AA ma acan yake, dole na nema mana kusanci ai. Yanzu ma komawa zanyi. Sai na dawo”. Daga haka bata jira cewar Mamy ba ta fice a sashen. Sai Mamy ta samu kanta da sauke ajiyar zuciya kawai, ita kanta rawar kan da Nuratu keyi akan Ajwaad na damunta, dan tasan halinsa baya son mace a haka... A falo Nuratu ta sami su Oum, Maanal na zaune a ƙasa ta baje takardu da laptop tana aiki, sanye take da simple riga mara nauyi tashan iska milk color, sai veil ɗin rigar siriri data naɗa a kanta, ɗan zamawar da yay baya ya bama kwantaccen gashin goshinta damar fitowa. Sam babu ɗigon kwalliya a fuskarta, babu alamar ma ta shafa mai dan fuskar tai irin fayau ɗin nan. Hatta lips ɗinta a ɗan bushe suke kaɗan. Sai ƙamshi mai sanyi dake fita ƙasa-ƙasa. Gaba ɗaya sai Nurry tai sororo tana kallon ta, dan tayi tsammanin zata dawo taga Maanal ɗin ta caɓa kwalliya ne kamar mai shirin fita waje. Amma sai ga akasin hakan. Itako Maanal ɗin ma kallo ɗaya datai ma Nurry ɗin sai ta bata dariya. Kwalliya fa ta ciwo sosai abinta. Anci uban shadda da yaji aikin stones sai ƙyalli suke. Kwalliya sosai a fiskarta harda lipstick ja da brawn sama gira tasha jagira, gashi ido a tsaitsaye an baza masa maskara a hakan ma na ƙari ne dan sunyi dogaye sosai. Anci ɗaurin ture kaga tsiya harda ɗan karkatashi gefe akai. Ƙamshi kam ba'a magana duk ta bulbule falon. Ita Maanal ma sai ta bata dariya, a zuciyarta tace (Aiki ja) a fili kam murmushi ta saki mai sanyi hankalinta a aikinta bazaka taɓa cewa da Nuratun take ba. A haka babban Yaya da sai yanzu ya shigo gidan ya samesu. Shi kansu sai da ya kalla Nuratun da ƙyau, ganin kallon da yake mata ta shiga gaisheshi. Amsa mata yay da kulawa tare da tambayarta mutanen gida. Dan shi a zatonsa ma yanzu ne tazo shiyyasa. Sannu da zuwa Maanal tai masa, tare da gaisheshi. Itama ya amsa mata da kulawa yana tsokanarta da cewar “Lilly yau kuma aikin office ɗin ne har a gida haka?”. Fuskar Maanal da murmushi ta ce, “Yaya ina ragewa ne, saboda yau na taso aiki da wuri”. “Masha ALLAH haka ake so, ai gara kada ki koya over time ɗin tsiya ɗin nan na Auta”. Sosai Maanal tai ƴar dariya tana nufar freight ɗin dining da faɗin, “Ai bazan koyaba Babban Yaya”. Dai-dai nan Oum ta fito daga hanyar upstairs. Itama dai kallon Nuratun tayi da ƙyau sai kuma ta janye ta maida kan babban yaya tana murmushi irin na manya. Ruwa Maanal ta miƙama Babban Yaya ya amsa yana sanya mata albarka, cike da farin ciki ta gyaɗa masa kai ta koma wajen zamanta ta cigaba da aikinta. Shi kuma suka fara gaisawa da Oum. A haka AA da Fawzan suka shigo sashen. Zama duk sukayi, cike da iyayi Nuratu tai musu sannu, sai kuma ta miƙe ta nufi freight kamar yanda taga Maanal tama babban Yaya suma ta ɗakko musu ruwan. Fawzan ne kawai yace mata “thanks”, shima kuma rabin hankalinsa naga duba takardun Maanal datai zane daya ɗiba yana kallo. AA kam ko kallon ma inda take baiyi ba, magana suke da babban Yaya ƙasa-ƙasa. Koda Babban Yaya ya miƙe Oum tace ya bari suci abinci tukkunna tunda Saheeba sai daren nan ma ta dawo gidan shi kuma yace ya gaji kwanciya zaije yayi yau bazai dawo hira ba AA bai tashi ba har sai da su dukansu suka isa dining ɗin. Maanal ma dai tana haɗa takardunta ne. Ita bama tasan AA ɗin bai tashi ba, sai da ta yunƙura zata miƙe suka haɗa idanu. Harrarta yay ita kuma ta taɓe baki. Dan tasan bawai ya daina jin haushin nata bane daman, ko ɗazun saboda ganin Oum ne. Bata sake kallon inda yake ba ta nufi dining ɗin, sai lokacin shima ya miƙe. Kujerar kusa da Maanal ɗin yaja ya zauna, Fawzan dake kallonsa cike da neman tsokana ya wani ɗage masa gira ɗaya. Harararsa AA ɗin yayi ya ɗauke kai. Shima Fawzan ɗin sai yay gyaran murya, kallonsa duk sukai, sai kawai ya basar. Babban Yaya daya san halin tom and jarry ɗin ƙannen nasa kansa kawai ya girgiza, dan ya tabbatar da AA Fawzan ɗin yake. Kowa zai fara ƙoƙarin zuba abinci karaf Nuratu ta miƙe acewarta bari ta saka musu. Babu wanda ya hanata, dan haka ta fara zubama Oum, sai babban yaya da Fawzan, gaban AA ta dawo har tana ɗan duƙo masa wai zata ɗauki plate. Wani irin zafi ne ya turniƙe zuciyar Maanal, shiko AA ɗin ma hankalinsa ba'a nan take ba, waya yake latsawa, tabbas yana jin ƙamshin turare mai ƙarfi a kusa da shi, amma baima san na wanene ba duk da ya fahimci baƙon ƙamshi ne bai taɓa jinsa a wajen kowa ba a gidan. Nibras ce ta shigo da sallama a cikin tata kwalliyar.........✍️ _Maanal tamu kenan, gaki kuma a tsakiyar kuraye😂, bari muga yaya wasan zai kaya🏃🏃🤣_ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖2️⃣4️⃣ ______________ ........Cikin ladabin son birge AA ta shiga gaida Oum, da kulawa Oum ɗin kuwa ta amsa mata tana tambayarta yaya aikin? “Alhamdullah Oum, tumma ɗazun na tashi na biya ta gida ne ganin Mom da tace ƙafanta na ciwo”. “Wayyo ashsha ALLAH ya bata lafiya, yaya jikin nata?”. “A Alhamdullah da sauƙi sosai, bama a kwance take ba”. Ta faɗa tana harrar Nuratu dake zubama AA abinci, tunda ta shigo akanta idannunta suka fara sauka, ji tai kamar ta shaƙo shegiya, dan tayi ma mamaki ubanmi ya kawota gidan. Maanal da itama dai ta shaƙa ɗin da iskancin Nuratu amma ta fiske babu wani alamar komai a fuskarta atare ita da babban yaya suka jajantama Nibras ɗin batun jikin mamanta. Sai Nuratun itama tayi mata jajen. AA dai kamar ma bai jisu ba sai da Oum ta kallesa, a taƙaice batare daya ɗago ba ya ce, “Sorry ALLAH ya bata lafiya”. Cike da sanyaya lafazi Nibras ta amsa, kallonta Maanal tayi ta gefen ido, dan bata sani ba ko ita kaɗaice ta fahimci Nibras ɗin ta canja murya wajen amsa AA ɗin. Sai ko amamakinta taga hankalin Nibras gaba ɗaya akan AA yake. (ikon ALLAH) Ta faɗa a ranta, a zahiri kam kamar ma bata san mike faruwa ba a wajen. Sai ma Nuratu data kawo hannu zata zuba mata itama, fuskarta da murmushi ta girgizama Nuratun kai murya ƙasa-ƙasa ta ce, “No barshi ma na Besty zai ishemu”. Tai maganar tana ɗaukar spoon ɗin da Nurry ta sakama AA, ita kuma ta ɗauka wani ta saka masa. Idan Nuratu tace bataji kamar ta shaƙo wuyan Maanal ba tayi ƙarya, dan tuni annurin daya cika fuskarta sanda take zubama AA ɗin abinci a yanzu ya ɓace ɓat. Ɗauke kai Maanal tayi kamar bata ganta ba, sai ma kai hannu da tayi ta zare wayar AA ɗin ta ajiye a gefenta. Ɗagowa yay ya kalleta, itama kallon nasa take, dan haka suka ɗan zubama juna idanu har sai da Fawzan yay gyaran murya. Maanal ce ta fara janye nata cike da basarwa ta ɗauka spoon ɗin ta fara cin abincin, shiko yaƙi daina kallon nata. Fiiiyyy Nuratu tabar wajen ta koma wajen zamanta, Nibras ma sai da taji ƙwalla sun cika mata idanu. Zuciyarta raya mata take anya bazata kashe Maanal ba a gidan nan wataran. Dan sam idanun AA basa iya ɓoye abinda ke cikin zuciyarsa game da ita. Jitai gaba ɗaya abincin ya fitar mata a rai, amma tasan tana ƙin ci Oum zata dameta da tambaya ita da Fawzan. Duk abinda kowa keyi Oum na karance da shi. Oum ta jima tana auna abubuwan da Nibras kema AA, musamman idan ta shagaltu da kallonsa ko idan tana masa magana. Sai dai duk da abinda zuciyarta ke fassara mata takan ture hakan a ranta. Amma a kwanakin nan sai irin kallon da take jifan Maanal da shi ke tsaya mata a rai, dan kallon yana kama da irin kallon kishi da jin zafi. A ganinta ko kishi ne irin na facalanci bai kamata a yakasance haka ba, dan kishin facalanci ga wanda ya saka kansa kusan na hassadar mijinki yafi mijina ne, ko mijinki yafi miki hidima fiye da nawa. Abu na ƙarshe yanda sam Nibras bata acting irin na matar gida ga mijinta a wajen Fawzan. Fawzan kullum a nan sashenta yake cin abinci safe da yamma, weekend harda na rana, itama kuma nan ɗin take zuwa taci. Sannan ko zaman cin abincin akai bazata tashi ta zuma Fawzan ba, sai dai ya zuba da kansa. Kai zasu iya zaman awa biyu a sashen ma bakaga sunyi magana da juna ba, amma idan AA na nan da yayi magana ko bada ita yake ba zata saka baki. Idan kuma har AA baya sashen ko yay tafiya to bazaka ƙara ganin Nibras a sashen ba. (Ya ilahil alamin, ALLAH kada kasa abinda nake hasashe akan yarinyar nan hakane. Lallai data cika mara hankali kuwa, da auren Fawzan a kanta ta ringa jin son wani namiji, namijin ma ɗan uwansa. Kai kai wannan kwamacala basa fatanta kuwa koda a mafarki).. shigowar Saheeba da yara ya katse Oum daga tunani, fuska cike da murmushi ta kamo su Naufal jikinta, Saheeba kuma ta zauna tana gaisheta. Itama dai abincin ta zuba, Oum ta girgiza kai kawai. Wannan lalace na surukansu na bata mamaki, matsayinsu na tsoffi su basu dafa sun kawo musu ba, sai dai kullum suzo sashensu su ci. Koda yake nan ɗin ma dai ne suke zuwa, dan ita Mamy bata ɗauka ma kanta hakan ba. Hasalima faɗa take akan ya kamata Oum ɗin ta taka musu birki. Itako sai dai tayi dariya kawai dan bazata iya ba, koba komai da yaranta su wahala da rashin abinci daga matansu gara suzo nan su ci ɗin hankalinta zai fi kwanciya. Kowa nata cin abincinsa hankali kwance, sai dai hankalin Saheeba, Nibras, Nuratu, duk akan AA da Maanal ne, yayinda su kuma hankalin baya kan kowa, abincin su suke ci kawai a plate ɗaya, ƙasa-ƙasa AA na takalarta wai abincin babu wani daɗi. Itako tana harararsa ƙasa-ƙasa batare data tanka masa ba. Sai da ya isheta ne takai hannu ta ƙasan table ɗin ta mintsinesa. Idanu ya ɗan rumtse tare da cije lips dan yaji zafi, kafin yasa shima nashi hannun ta ƙasan table ɗin ya riƙe natan dake mintsininsa, tayi-tayi ta kwace yaƙi saki, dole ta haƙura. Shi ko ya cigaba da murza hannun dan wani irin laushi da santsi yake masa. Yanda yake mirza hannun sosai tsigar jikin Maanal ke tashi, amma ta dake abinta.. Abinda Maanal bata sani ba tuni ƴan sa'idonsu sun fassara abinda hannayensu keyi a ƙasan table, musamman daya kasance lokacin da Maanal ta mintsini AA ya lumshe ido da cije baki. Itama kuma yanayinta ya canja da ya kama hannunta yana murzawa. Su duka ukun zukatansu yi suke kamar zasu babbake. Yayinda sam babban Yaya da Fawzan da Oum su basu san ma mike faruwa ba. Hasalima hirarsu sukeyi. Rashin saka bakin AA a hirar kuma sun san wannan normal ne daga halinsa. Ba kowace hira bace zakaji bakinsa sai idan yaso tankawa, balle ma su Saheeba na wajen, kowa yasan baya hira da su, daga gaisuwa babu abinda ke sake shiga tsakaninsa da su.. AA neman harmutsama Maanal jiki yake, dan haka babu shiri ta miƙe tana fisge hannunta wai ta ƙoshi. Kallonta Oum, Babban Yaya da Fawzan sukai, yayinda AA yay wani shegen murmushi yana cigaba da cin abincin sa. Murmushin nasa ya ƙara tabbatar ma da ƴan saka ido abinda suke hasashe, ta wani gefen kuma ya motsa zukatan Nuratu da Nibras dan abune da basu saba gani ba. Lallashin Maanal Oum keyi akan ta ƙara ko kaɗan. Cike da shagwaɓa tace, “ALLAH Oum da gaske na ƙoshi zan yi amai idan na ƙara”. A mamakin kowa sai ji sukai AA yayi ƴar dariya. Shagala matan sukai a kallonsa, dan har Saheeba ma dai mamaki ne ya dabaibayeta wai AA da dariya. Babban Yaya kam murmushi yayi, zuciyarsa fes da ganin farin cikin Autansu nata dawowa. Fawzan kuwa tsokanar tasa daya saba yayi. Yayinda Maanal ke kallon Oum kamar zatai kuka. “Oum kin ganshi yana mun dariya ko”. Kallonta AA ɗin yayi, “Kefa matsalata dake sharri Besty, shike nan bazanyi dariya ba, to inba tsargar kai ba mi kikayi da zan miki dariya?”. Harararsa tayi, fuuu tabar wajen. Dariyar ya ƙara sanyawa, cikin ɗan ɗaga murya yace, “ALLAH ya raka taki gona”. “Amma fasa tafiyar to”. Manaal ɗin ta faɗa tana dawowa. Sai dai kujerar gefen Oum ta jawo ta zauna yanzu. Hatta Oum dariya takeyi, hakama Babban Yaya da Fawzan. Su dai matan da alama abin haushi ma ya basu, dan kowacce ta ɗauke kai. Cike da lallashi Oum tace, “Kinga ƙyaleshi Babyna, ya kamata zuwa yanzu ki saba da halin Auta, dan yaga ma kina fushi shiyyasa yake tsokalarki. Kin bari yaga lagonki ne, amma ki bari muma zamu gane nasa ai”. Gwalo Manaal ta masa tare da kashe ido ɗaya. Sai ya haɗe fuska yana harrarta. Akan lips ya furta, “Zan kama ki ne ALLAH ya kaimu Chaina”. Tsaf taga abinda ya faɗa, dan wannan sigace da sukema juna magana a baya idan basa son wanda ke kusa da su ya fahimta. Sosai taji gabanta na faɗuwa. Ita dai wannan Chaina da tana da yanda zatai sai ta cire kanta a ciki ALLAH. Gashi taga Abah baida niyyar hanawa.. Babban Yaya ne ya fara barin sashen, dan yace ya gaji barci yake son yi. Sai Oum ta kora Saheeba ta bisa. Maanal ma bata zauna ba ta tattare kayanta ta wuce ɗaki, acewarta aiki zatayi. AA ne ya zama na huɗu, acewarsa shima zaije yay aiki ne. To dama dai Nibras da Nurry dan shi suke zaune, sai dai da kunya ai su ce suma zasu wucen. Dan haka suka ɗan daure suna taya Oum hira. Dan AA yaja hannun Fawzan sun fice tare kamar zasuyi magana ne ya dawo shima dai shiru. Dole suma cikin dabara sukama Oum sallama suka gudu. Da kallo kawai Oum ɗin ta bisu, sai ma duk taji sun fara bata tausayi musamman ma Nibras, zata cigaba da mata addu'a ALLAH ya cire mata shaiɗancin nan a zuciyarta, za kuma ta dinga bata shawara a cikin hikima ko ALLAH zai sa ta gane ta tsaida hankalinta waje guda ga mijinta..... _________★ Matuƙar zafi rayuwa tama Hajiya Basariyya. Dan tana dira gidan Kawu Manu dake wani ƙauye a ingawa local government ya ƙwace wayoyinta duka. Ya kuma shimfiɗa mata sharuɗan zaman gidansa. Zata hau yimasa magiya daban haƙuri yace baya buƙata. Lokacin da suka iso dambun tsakin masara sukai mai daɗi, yaji zogale da gyaɗa abinsa kuwa ga man ƙuli mai ƙamshi ɗan asali. Amma ita ƴar rainin wayo sai cewa tai bazata ci ba. Babu wanda ya kulata kuwa. Da dare akai tuwo na dawa mai daɗi nan ma. Harda naman zabuwa a miyar, dan duk da Kawu Manu na ƙauye miyar gidansa kullum da nama. Kiwo yake sosai na dabbobi kala-kala. Nan ma ƙin ci tayi, taci biscuits ɗin data ɓoyo a kaya da drinks. Duk bawai ya isheta bane ta dai daure. Washe gari da safe ana idar da sallar asuba da kansa ya kwankwasa mata ɗaki, yanda ta fito ya fahimci bama tayi salla ba. Aiko ya balbaleta da masifa, ya kuma tabbar mata shi ba'a masa lallaci a gida musamman na ibada. Dan haka ta tattara ta koma ɗakin Iya matarsa. Sosai hankalinta ya tashi da jin hakan, amma babu yanda ta iya. Haka taje tai salla, tana idarwa yace ta fito, tsintsiyar kwakwa ya jefa mata ya nuna mata tsakar gidan alamar shara, ya koma kan ɗan dutsen da yake zama a tsakar gidan daga can gefe ya zauna. Ba ƙaramar raunana zuciyarta tayi ba, dan tasan babu abinda ya damu Kawu Manu da shekarunta horata zai yi yanda ya kamata. Shiyaysa taso ta gudu gidan mijinta. Babban tashin hankalinta kayayyakin da suka amso da Maman Yaseerah suna can ta baro a Kaduna gidan yayanta, ga Huznah bata san a halin da take ciki ba a yanzu. Haka dai tai sharar s jigace saboda abune da ita kanta basan adadin shekarun data ɗauka batayi ba, ga tsakar gidan ƙaton gaske kun san dai gidan ƙauye akwai yalwar albarka. A gidanta komai yan aiki ke mata. Wataran ma suyi tace baiyi ba sai sun maimaita. Tana gama share ƙaton tsakar gidan yace ta shiga turken dabbobinsa dake zagaye da danni na itace. Wani irin amai ta dinga ji na masifa na taso mata, dan sunyi ɗanyen kashi ya haɗe da fitsari abin ba'a magana. Sai kawai taji hawaye sun ciko mata ido. Haka ta duƙa tayi sharar, da ƙyar ta gama, sai da ta koma tayi amai sosai. Yi kawu Manu yay tamkar bai jiyota ba, balle kuma Iya daketa hada-hadar ɗora wainarta ta sayarwa ta safe da take yi. Gefe kuma ta dama koko ta ɗaura ɗumamen tuwo na gida. Hajiya Basariyya na kammala sharan Kawu ya shigo turken, ɗakin dake a gefen wajen ya nuna mata, yace ta fiddo abinci ta raba musu, ta kuma wanke manyan kwatanniyar dake wajen guda biyar ta haɗa musu ruwan dusa a ciki. Daga haka yay ficewarsa ya barta..........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. 🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖2️⃣5️⃣ ______________ 25 .......Sosai Rabilu ya gigice da tsawar da Sen.. Bukar ya buga masa. Shi ko cikin matuƙar rufewar idanu da shiga tashin hankali mara misaltawa ya cigaba da faɗin, “Kai wawan inane da bazaka kirani ka sanar min ba tun a lokacin Rabilu, sai yanzu zakazo kana gaya min wannan shashashar maganar. Aiko wlhy ko ɗan uban wanene wanda ya auretan sai ya saketa, dan ban taɓa san wata mace kwatankwacin yanda nake son yarinyar nan ba”. Cikin girgiza kai Rabilu ya ce, “Ranka ya daɗe kayi haƙuri, nima na rasa ta yanda zan isar maka da saƙon nan ne wlhy, tunda kaga tunda ka tafi bamuyi waya ba balle na samu lambar. Amma ka gafarceni. Auren yarinyar kuma yazo da ƙura, dan in har akace za'a ƙwatota akwai rikici. Saboda AA Darma ta aura”. “AA what?!!”. Sen.. ya faɗa cikin matuƙar zabura jijiyiyin jikinsa na mimmiƙewa. Dan baya jin a kusan nan an taɓa faɗa masa abinda ya girgiza masa zuciya kamar wannan da yaji a yanzu. AA Darma ne ya aura ƴar shularsa fa. Eh lallai akwai yaƙi kenan a Abuja. Tsabar yanda Rabilu ya sake firgicewa da yanayin ogan nasa shi kansa jikinsa rawa yake yi. Sai da yaji dana sanin ma sanar masa zancen. To amma yasan dole ne ya sanar masan, kodan yanda tun jiya ya fahimci yanda ya matsu da jin wani abu a bakinsa game da Maanal ɗin. Yau kuma yana fitowa a gida shi ya fara nema yace yazo office ya samesa. A ɗarare kuwa yazo amma bashi da damar zillewa dole ya faɗa. “Munafuki tashi ka fitar min a office. Kuma karna sake ganin fuskarsa sai na nemeka”. A rikice Rabilu ya fara bama Sen.. haƙuri, amma bai sauraresa ba, sai ma cewa yay idan bazai fitan ba zai sa security suzo su fidda shi. Yasan zai iya, dan Sen.. bashi da kirki, shi kansa alaƙarsu tayi tsaho ne saboda yana samo masa irin matan da yake so ne a kuma duk lokacin da yake buƙata. Haka ya tashi ya fito jikinsa a sanyaye. Dan wannan hanya dai shi kam itace hanyar cin abincinsa. Gashi tafiyar Sen... Ɗin wata da watanni ta sashi a halin rashin kuɗi, ya dawo da tunanin yanzu zai jiƙe ga kuma wannan akasi ya shigo. Amma ba komai zaije yay tunanin hanya mai bullewa, yasan wutar da zai kunno ta yanda dole Sen... zai nemosa da wuri-wiri...... _______★ Washe gari kasancewar Maanal tasan ba fita aiki zatai ba tana idar da sallar asuba ta sake komawa barci bayan taba Oum saƙon wani document taba AA. Oum bata hanata kwanciyar ba, dan taga raba dare tai jiya tana aiki, sai da ma tace ta kwanta sannan tace to. Amma badan haka ba ai bazata barta kwanciyar nan ba. Dan ta ɗauki ɗamarar hana Maanal zama irin su Nibras a gidan, tana son babynta ta horu da kula da mijinta, duk da tasan Ammie ma ba wasa bace wajen tarbiyyar yara, hakan ma a bayyane yake ga Maanal ɗin. Yau Oum ita kaɗai ta haɗa breakfast ɗin da taimakon su Inte. Bayan ta kammala ta bar musu su shirya a dining ita kuma ta nufi yin wanka, dan tasan itama Abah na hanyar dawowa tunda yace shigar safe zaiyi. Har yanzu Maanal na ƙudundune a duvet tana barcinta hankali kwance... Bayan kammala wankan Oum ta shiryawa ta samu Fawzan kawai a falon yay zaman karyawa, dan yana son fita da wuri-wiri ne acewarsa. Gaishe da Oum yayi, ta amsa masa da kulawa tana tambayarsa iyali. Shima ya tambayeta Maanal tace tana barci. “Oh na manta Oum tace yau bazata aiki ba tana hutu”. “Eh, ai kasan saboda tafiyarsu gobe ne”. “Wai Chaina ɗin dai?”. “Eh, duk da bamu da matsaya dan Abanku baice komai ba har yanzu”. “A Oum karki damu zaima barta, ai aiki ne”. “To ALLAH yasa Fawzan Abanku ne rikicinsa yawa garesa”. Ƴar dariya Ya Fawzan yayi, dai-dai lokacin kuma AA ya shigo da sallama. Yau dai normal shiga akai ta yadi ruwan toka mai duhu sosai. Kai daka kallesa kasan an sayesa da kuɗaɗe masu tsada, dan ya kwanta luff-luff kamar ajiyayyar ƙanƙara. Rigar ba wata mai tsaho bace, hakama hannunta gajere ne ko gwiwa bai kai ba. Babu dai hula amma yayi ƙyau sosai. Briefcase ɗinsa ya ajiye a saman kujera kusa da wadda ya ja zai zauna cikin muryar nan tasa mara hayaniyar sauti ya ce, “Good morning Oum, Ya Fawzan morning”. A tare suka amsa masa, Ya Fawzan ya ce, “Ya dai Autan Oum naga kanata kunbura?”. Ƙin kulashi AA yayi, sai ma jan flaks ɗin gabansa da yay ya buɗe dan yasan maybe kunu ne. Sai Oum ce ta bama Fawzan ɗin amsa da, “Fawzan kadai sakama autana ido a gidan nan”. Da ƴar dariya Fawzan yace, “Oum babu wani sa ido, shi ɗin ne sai a hankali, yanzu haka fushin nan dan Lilly bazata aiki bane yau.” “Oum ALLAH zan bar masa wajen”. AA ya faɗa cike da shagwaɓa. Dariya Oum ta danne ta ce, “Kaga manta da shi my baby, ci abincin ka. Ni zan maka maganinsa. Dan kawai mutun ya tashi da ɗan rashin son maganarsa sai kuma a fassara shi”. Dariya sosai Fawzan yake yi, sai ma ya miƙe abinsa dan ya kammala karyawa, duƙowa yay saitin kunnen AA ɗin cike da raɗa ya ce, “Saboda kai kwar-kwar ne shine ka tsara su Oum da sunan aiki kai da Lilly a Chaina ko, to ka turan hundred k kona tonaka cewar honeymoon zakaje ehe”. Yana gama faɗa yay gaba, sai da ya je ƙofa sannan ya juyo, kamar yanda yay zato kam harararsa AA ɗin keyi. “Harareni da ƙyau nidai inji alert, idan ba haka ba zakaga tone-tone yau”. Yay ficewarsa. Karan farko AA ya saki murmushi tare da girgiza kansa. Har cikin ransa yana ƙaunar ya Fawzan ɗinsa. Dan soyayyar ƴan uwansa ta musamman ce a garesa. Abincinsa ya cigaba da ci suna ƴar hira da Oum, shigowar Nuratu ya sashi yin shiru. Sosai ƙamshin turaren data bulbula ya fara hawa masa kai, dan ko kaɗan bai kalla ma inda yasan take ba. Gaisheshi ma da tayi hannu kawai ta ɗaga mata. Tabbas yana son ƙamshi, amma ba irin wannan mai hawa kan ba na mahaukata, balle ma ga mace, shiyaysa kaf turaren da Maanal ke amfani dasu suna masa daɗi da saukar masa nutsuwa, musamman ma traditional. Sallamar Nibras itama da nata salon gayun yasa shi miƙewa badan ya kammala cin abincin ba, matsawa yay inda Oum take ya kama hannunta ta sumbata. “Oum yimin addu'a”. Addu'ar ta masa harma da sauran ƴan uwansa sannan ya mata sallamar tafiya. Har ya nufi ƙofa ta ce, “Af Auta na manta. Akwai takardu da Baby ta ajiye na baka, suna nan a side drawer na manta na fito da su. Kansa kawai ya jinjina mata, a ransa kuwa faɗi yake, (Lallai ƴar Oum ta gama rainani, ina boss ɗinta a wajen aiki amma ni zata aika na kai mata aikinta. Ba komai zamu haɗe ne). Da wannan tunanin ya shiga bedroom ɗin Oum. Saukar idanunsa a kanta ya sashi sauke ajiyar zuciya duk da bawai yana ganin fuskarta bane. Sai kuma ya shiga takawa a hankali har zuwa gaban gadon. Dai-dai fuskata ta ya tsaya cak, samun kansa yay da zubama ƙyaƙyƙyawar fuskarta datai wani fresh fararen idanunsa. Yanda ta ɗan tura baki gaba baima san ya saki murmushi ba. Sai kuma ya kai duƙe gaban gadon a saitin fuskar tata. Yatsarsa manuniya ya ɗaura a saman lips ɗin da suka ɗan bushe suka sake takurewa waje guda ya shiga shafawa, kafin ya janye ya maida saman goshinta ya gyara mata gashinta da suka ɗan barbaje har saman idonta. Duk yanda yaso daurewa ya kasa, sai da ya kai nasa lips ɗin a slowly ya sumbaci natan. Sai ko kamar tasan mike faruwa ta motsa, idanunsa ya ɗan rumtse dan sam baya son ta farka ta ganshi. Sai kuma ALLAH ya taƙaita abun kwanciya aka gyara. Shima miƙewa yay ganin ta cigaba da barcin, inda Oum tace file ɗin yake ya ƙarasa ya ɗauka. Daga haka ya fito. Oum kawai ya cema “bye”. yay ficewarsa ko kallo Nurry da Nibras basu ishesa ba. Da baya ya dawo, hakan yasa su duka sake kallonsa. Ya ce, “Oum idan Besty ta tashi Please ta min shara. Sashen yayi daty”. “A'a bola fa? Yanzu ya daina gyarawa?”. “No Oum na dakatar da shi, saboda akwai banbancin da da yanzu ai ko”. “Eh gaskiya hakane kuma Auta na. Babu damuwa zata share in sha ALLAHU. ALLAH ya bada sa'a”. Da “Amin” ya amsa yana wucewa. Oum ma sai ta miƙe tabar Nibras da Nurry dake ta faman ƴar hararrar juna..........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖2️⃣6️⃣ ______________ ........Manaal bata gashi ba kuwa sai 11, wanka ta fara yi sannan ta fito. Babu kowa a sashen sai motsin su Inte a kitchen. Kitchen ɗin ta nufa, suka shiga gaisheta da girmamawa duk da kuwa ta tabbatar zasu girmeta. Amsa musu tayi da tambayar ina Oum. “Tana sashen Abah daya dawo babu jimawa”. Cewar Joy. Maanal tace, “Oh Abah ya dawo, bara na gaisheshi to”. Daga haka ta fice. Hijjab taje ta ɗauka sannan ta nufi sashen Abah ɗin. Bayan tayi knocking tai sallama, sai da aka bata izini sannan ta shiga. Yana zaune da matansa, tunda ta shigo yake mata murmushi, itako cike da jin kunya ta zauna a ƙasa kusa da ƙafafun Oum ta shiga gaisheshi. Amsa mata yay da kulawa sosai, kafin ya ɗora da faɗin, “Yau ana hutu ko ƴar Abah, shiyyasa na shiga sashen Mamanku kinata barci”. Murmushi Maanal tayi cike da jin kunya, sai kuma ta juya ta gaida Mamy data cika tai fam. Ko'a kwalar rigar Maanal dan ita a yanzu kallonta kawai take yi. Da ƙarfin hali Mamyn ta amsa mata, dan cike take taf da takaicin maganar tafiyar ta da Oum ke tuntuɓar Abah yanzu. Kuma Aban baiyi wani jayayya ba yay addu'a da fatan alkairi. Ita kanta Oum tayi mamakin sallamawar tasa kai tsaye, balle Mamy da sai yanzu ne take sanin fa tafiyar. Ita dai Maanal sallama tai musu ta koma sashen Oum. Bayan ta zauna ta gama breakfast kitchen ta nufa domin shirya lunch. Wayarta dake kashe ta kunna, sai ko sakwanni suka fara rige-rigen shigowa. YouTube take ƙoƙarin shiga domin duba girki ko zataga wani tai sha'awa, sai kawai taci karo da numbern AA ta notification alamar ya tura mata saƙo. Duk yanda taso ta share hakan ta gagara, dole ta shiga WhatsApp ɗin domin duba saƙonsa. “Your hand is soft😋, and it reminded me why you're the one I want to hold on to forever”. Iya abinda ya tura kenan da emojin lasar baki. Da alama kuma tun daren jiya ya tura saƙon. Bayan gama cin abincinsu kenan koma tace bayan tashin ta. Samun kanta tayi da sakin murmushi, batare da bashi amsa ba ta fito abinta ta shiga YouTube ɗin datai niyya. Girki tayi masu daɗi, tana ƙoƙarin kammalawa Oum ta shigo. Tako ji daɗin ganin Maanal ɗin a kitchen. Albarka ta sanya mata, sannan tace ta haɗa wanda za'a kaima AA office ya kirata zai aiko driver shiyyasa ma ta taso nema masa abincin, ashema Maanal ɗin ta hutacceta. Da to Maanal ta amsa mata, ta shiga haɗawa kuma komai yanda ya kamata cike da tsari. Har zata rufe ƙular saita tsaya, cokali ta ɗauka ta rubuta (ACICI) a kan abincin sannan ta rufe.. Bayan an wuce da abincin tai salla ta nufi sashen nashi tare da su Inte domin su tayata gyaran da Oum tace taje tayi masa... ________★ Yau ɗin nan sosai aiki yay masa yawa, sai dai hakan bi hanashi yawan duba wayarsa ba kuma WhatsApp, shi kansa ya kasa fahimtar abinda yake jiran gani, sai dai wani sashi na zuciyarsa na tabbatar masa reply ɗin Maanal yake jira. Kuma yaga ta buɗe saƙon awa biyu data shige amma babu amsa. Haka dole ya haƙura lokacin sallah ya wuce massallaci. Bayan ya koma office babu jimawa drivernsa yazo masa da abincin da yay kiran Oum. Zama sosai ya gyara domin cin abincin dan yunwa yake ji. Yana buɗe kula ta biyu yaci karo da rubutun da tayi, shi da farko ma baiyi zaton abu aka rubuta a kan abincin ba ta hanyar zanawa sai da ya saka ido sosai da tunanin ko wani ne ya saka hannu ya jagwalgwala masa. Sai kawai yaci karo da (ACI-CI). Shiru kawai yayi yana kallon rubutun, zuciyarsa na faman masa kai-kawo. Shi dai yayi imani wannan ba aikin Oum bane ai. Amma duk da haka sai ya ɗaga waya yay kiran Oun ɗin. Sannu da aiki yay mata kamar yanda ya saba a duk lokacin data aiko masa da abincin. Daga can tace, “Ai Bestyn ka ce ma ta girka bani ba. Sanda ka kira waya naje dan nema maka na samu harta kammala girkin”. Godiyar dai ya sake ma Oum sukai sallama. Yana ajiye wayar ya sauke ajiyar zuciya, sai kuma yayi murmushi mai sanyi. Samun kansa yay da tsayawa yana kallon rubutun kawai, daga ƙarshe ya ɗauka wayarsa yay hoto sannan ya fara zubawa. Sai da ya gama haɗa komai sannan ya sake ɗaukar wayar, hoton ya tura mata, a kasanshi ya rubuta. “Meaning”. Kawai.... Maanal na zaune a bakin kadon ɗakinsa data gyara tsaf bayan ta canja bedsheet dan ita kaɗai ta shigo nan su Inte na ƙasa suna gyarawa waya a hannunta suna charting da Waleed saƙon ya shigo. Yanzu kam bata buɗe ba, ta notification ɗin taga abinda ya turo da wanda ya rubuta. Murmushi kawai tayi tana sake maimaita kalmar (meaning) ɗin daya turo a zuciyarta. Daga haka ta cigaba da hirarta da Waleed ɗin kawai. Tabar AA acan da kallon waya. Dan ko da ya kammala cin abinci ya koma kan kujerar aikinsa kaɗan-kaɗan sai ya dauka wayar ya duba kamar ɗazun. Amma har lokacin bata buɗe ba kuma tana a online. Ransa ya sosu amma ya danne, daga ƙarshe ma ya kashe wayar ya ajiye tunda dama iyakar mutanensa ne masu muhimmanci koma yace family ɗinsu kawai keda no ɗin... Da yamma koda ya dawo gidan ya samu sun fita ita fa Oum. Bai san ina sukaje ba bai kuma tambaya ba. Dan sashen Mamy ma ƙin shiga yayi kasancewar yasan tana tare da Abah daya yini a gida. Sai da Fawzan ya dawo sannan suka nufi sashen Oum ɗin a tare. Sai dai kuma Nuratun da yake gudun su haɗu a sashen Mamy sai suka sameta a sashen Oum ɗin kwance tana kallo. Yi yay kamar ya fasa zaman, sai kuma akai sa'a su Oum suka shigo. Tunda ya kalla Maanal sau ɗaya ya fahimci gyaran kai sukaje, dan idanun mutuniyar sunyi ja alamar tayi kuka. Kansa kawai ya girgiza yana kallon Oum. Sai kuma yakai zaune a kusa da ita murya a ƙasa ya ce, “Oum daga ina haka?”.. “Wankin kai nakai Baby dan nasan sanda zaka dawo ka gaji balle ka kaita. Aiko ansha daru, ashe har yanzu bata daina kukan wanke kai da kitso ba. Tamaƙi yarda ayi kitson sam”. Lumsassun idanunsa ya zubama Maanal daketa ɓata fuska, itako taƙi yarda ta kalla kowa sai ma Fawzan dake lallashinta ta kula. Idanun ya ɗauke a hankali. “Ai inaga sai randa aljanun kan nata suka barta zata daina wannan halin”. Yaba ma Oum amsa cikin sanyin yanayi. Murmushi Oum ɗin tayi, yayinda Maanal da taji abinda ya faɗa ta dallo masa harara. Sai kuma ta miƙe fuuu tai ɗaki. Oum tace, “Kaga ka Koreta auta”. “Oum dama mai son yin kuka ne aka jefesa da kashin awaki kawai”. Daga haka ya maida kansa ya kwantar a kujerar. Iya wuya Nuratu takai da iskancin Maanal a gidan, shegiyar yarinya gansamemiya ta zauna tana ma mutane taɓara su kuma suna biye mata kamar wasu makafi. Amma ai ta iya zura hannu a ƙasan table tana taɓa maza ko. Ita kaɗai take surutanta a zuciya, fuskarta kuma na bayyana halin da take ciki... Da wuri Maanal tayi barci dan kanta ciwo yake mata. Tunda Oum ta bata magani tasha sai barci. Ita dama ƙarshen taɓa mata kai kenan ai. Musamman idan bata so kamar mai aljanun dai tabakin AA ɗin. Washe gari ta kama ranar tafiya, shima AA baije office ba. Amma zuwa goma ya fita a gidan. Bai dawoba sai azhar. Ya samu Maanal harta haɗa kayanta, sai kuma a lokacin ne su Nuratu suka san da tafiyar da Saheeba. Nibras ko dake wajen aiki bata sani ba. Kai tsaye AA daya shigo sashen Oum ya nufa. Daga ita sai Maanal a falon sama. Bayan ya gaida Oum Maanal ta gaisheshi batare data kallesa ba. Shima kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa. Dan wani irin ƙyau yaga ta masa a bayyane, bai san tun daren jiya Oum kema yarinyar tata gyaran jiki da kayan haɗi na musamman da Hajiya Shuwa ta kawo ba, ta kuma bata abubuwa tasha, ita dai Maanal ta tsargu da abinda Oum ɗin ke bata, dan tasha gani a wajen su Didinta suna sha. Amma sai bata nuna ba ta dake kamar bata gane komai ba. “Kaya nawa kika ɗiba?”. AA yay maganar idonsa akan Maanal muryarsa a dake dan ransa a ɓace yake, rashin walwalarsa yau a bayyane take. Mamy ce kuma ta haddasa hakan a gareshi, dan kaca-kaca yau tai masa akan wannan tafiya tasu da Maanal, harda cewa ma da sai dai a fasa da Maanal ɗin ko shi ɗin ya fasa, sai da ya mata alƙawari akan Nuratu data kafa masa sharaɗin kiranta kullum sannan kuma tai masa ALLAH ya isa idan ya mu'amalanci Maanal a shimfiɗa..... Tunanin nasa ya kauda gefe, ya sake maimaita maganar ga Maanal datai kamar bata jisa ba cikin yanayin ɗan tunzura. Kallonsa Maanal tayi dan harga ALLAH sai yanzu taji abinda yace, da farko hankalinta nakan charting da take da su Didinta ne, ganin yanda ya tsatstsareta da nashi kaifafan idanun a gaban Oum kuma ko kunya babu sai ta ɗauke nata da sauri. A sanyaye ta ce, “goma”. Komai bai sake cewa ba, sai miƙewa da yay ya fita. Da kallo duk suka bishi, Oum kuma ta fahimci ransa a ɓace yake, amma sai tai tunanin ko daga waje aka tunzuro shin. Babu jimawa ya dawo da madaidaicin traveling bag na trolling mai shegen ƙyau. Baice komai ba ya wuce ɗakin Oum da shi, fin mintuna goma sai gashi ya sake fitowa da shi. A falon ya ajiye sannan ya ɗan kalla Maanal ɗin ya ɗauke ido yana ƙoƙarin ficewa. Ciki-ciki ya furta, “Ki bar wancan”. Daga haka yay ficewarsa. Kallon juna Oum da Maanal sukai. Fuskar Oum da damuwa ta ce, “Akwai abinda ke damunsa”. Ƙasa Maanal tai da kanta, dan ita kam bata san mi zatace ba. Itama ta fahimci akwai damuwa a tare da shi, duk da tasan wannan normal ne a halinsa, dama idan kaga sakewa a tare da shi to lallai suna tare ne, dan ita sam bata son yanayin baƙin miskilancin nashi, shiyyasa duk yanda zata sakashi magana ta sani. _________★ 4:30pm Su AS suka iso domin ɗaukarsu. Shine ya fara fitowa daga sashensa. Sanye yake cikin ƙananun kaya normal wandon jeans black da t-shirt black data kwanta masa a jiki sosai, dan irin mai santsin nan ce da laushi jiki. Yaci zanzaro brawn belt daya fidda ainahinsa na dogon mutum dake tsaye sosai a suffarsa ta zakin. Sai jacket da itama ta kasance brawn color a hannunsa ya saƙale batare daya saka ba. Sosai fuskarsa data sha gyara gashin sajensa ya kwanta luff-luff ke'a ɗaure, kamar ko yaushe idanunsa manne da sirrin fari tas ɗin gilashinsa dake sake ƙawata shi. Tafiya yake ɗai-ɗai a kuma nutse cike da ƙasaita yana ɗaura agogo a tsintsiyar hannunsa takalmansa masu matuƙar ƙyawu sau ciki na bada ƙarar sauti kaɗan-kaɗan. Sosai Nuratu ta shagaltu da kallonsa, ji take kamar ta haɗiyesa ta huta. Dan daya ɗan gittata zuwa gaban Mamy mayataccen ƙamshinsa ya daki hancinta jitai illahirin jikinta na rawa. AA da bai san ma tana yi ba dan shi ko lura da ita baiyi ba a wajen ya ɗan zubama Mamy ido kafin ya risinar cike da girmamawa ya furta, “Zamu wuce Mamy”. Ƙin yarda Mamyn tai ta kallesa, kasancewar su Oum a wajen kuma yasa tai masa addu'a cike da nuna rashin kulawa kamar yanda take musu. Muryarsa a sauƙaƙe ya furta, “Thanks you” a hankali. Sai kuma ya matsa gaban Abah. Murmushi Abah yay masa, tare da ɗaura hannunsa a kafaɗarsa. Sai kuma ya matsar da bakinsa kusa da kunnen AA ɗin ƙasa-ƙasa ya furta, “A rufan asiri a dawo min da yarinyata lafiya Oum's boy, kaga dai gudun rigimar uwar taka yasa na baka salin-alin”. Idanu AA ya lumshe tare da sakin guntun murmushi kansa a duƙe. Batare da ya yarda ya kalla Aban ba ya gyaɗa masa kai, muryarsa a sanyaye yace, “In sha ALLAHU Abah zan cika alƙawari”. “ALLAH yay muku albarka”. Abah ya faɗa yana murmushi da ɗan bubbuga kafaɗar tasa. Gaban Oum AA ya ƙarasa..........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖2️⃣7️⃣ ______________ ........Gaban Oum AA ya ƙarasa, Maanal na gefenta sanye cikin Abaya red color datai mata matuƙar ƙyau, tai rolling kanta da mayafin, sai mitsitsiyar handbag a hannunta. Suna haɗa ido ta kauda nata, shima nashin ya maida akan Oum, cike da kulawa ya rungumeta, “Oumna zan yi missing ɗinki”. Ya faɗa cikin maƙoshi. Murmushi Oum tayi, tare da ɗan bubbuga bayansa. Sai kuma ta ɗagoshi cike da kulawa fiskarta da murmushi ta shafa fuskarsa. “Nima haka Auta, amma karka damu kamar yau ne ai zaku dawo. Ga Baby na nan zata kula min da kai”. Tai maganar tana juyawa ta kamo hannun Maanal. A cikin nashi ta sanya, a tare suka saki ɓoyayyar ajiyar zuciya kuwa. Sai dai a zahiri kowa a dake yake, dan Maanal ma kanta a aƙasa yake, shine ma dai ke kallonta ƙasa-ƙasa. Addu'a sosai Oum tai musu, tare da damƙa ma junansu amanar kansu. Daga haka tace suje lokaci na ƙurewa. Gashi jirginsu 5:20 zai tashi. Sai yanzu ne Saheeba ta buɗe baki da ƙyar tai musu addu'ar dawowa lafiya, hakan ne ya zaburar da Nuratu, itama ta ce, “Ya AA ALLAH ya tsare”. Hannu kawai ya ɗaga musu, tare da kai ɗayan hannunsa ya amshi trolling ɗinsu da Maanal ta kama zata ja. Ɗan ɗagowa tai ta kallesa, suna haɗa ido ta janye tare da sakar masa akwatin. Shima bai ce komai ba ya turashi yay gaba, ita ko Maanal sai da ta sake rungume Oum sannan ta wuce idannunta cike da hawaye. Ji take kamar zasuyi tafiya ne mai jimawa. Da sauri AS ya zaburo ya amshi akwatin hannun AA ɗin domin sakawa a booth dake buɗe. Shi ko jikin motar ya nufa ya tsaya har Maanal ta iso, ganinsa tsaye ya sata fahimtar ita yake jira ta shiga. Dan haka ta nufi shigar, hannu yasa ya tare mata saman kai dan karta buge, sai kuma akai rashin sa'a abayarta ta nema taɗeta. Riƙota yay da hannunsa ɗaya bayanta ya jinginu da jikinsa. Muryarsa a ƙasan maƙoshi can ƙasa sosai ya ce, “Are you okay?”. Kanta ta jinjina masa tana ɗan sauke ajiyar zuciya, sai kuma ta matsa daga jikinsa ganin su Oum duk suna kallonsu har tana iya hango yanda fuskar Mamy, Nuratu da Saheeba ta canja, shiga tayi sai dai tana ɗan yamutsa fuska dan ƙafarta na ɗan mata zafi. Lurar da AA yayi saboda idonsa a kanta yake ya sashi kaiwa tsugunne irin na yanayin maza ya ɗaga Abayar kaɗan ya kamo ƙafar dake a cikin ƙyaƙyƙyawan baƙin takalmi fes-fes da ita. Takalmin ya zare ya ajiye, batare da damuwa ba ya ɗaura ƙafar a saman jikinsa. Ji Maanal tai kamar tayi kuka dan nauyin Abah da Oum. Amma yaya zatai tunda tasan ba fasawa zai yi ba. Duk da haka sai da tai magana a sanyaye ta ce, “Bafa da yawa bane”. Bai kulata ba, sai ƙoƙarin ɗan jajjan ƙafar kawai yake yi, sai da yay kusan na minti biyu sannan ya maida mata takalmin ya gyara mata ƙafar a cikin motar tare da rigarta ya miƙe. Da kansa ya rufe mata murfin sannan ya juya ya kalla su Oum dake kallonsu cike da jin daɗi, sai dai banda su Mamy. Dan ji tai wani irin ƙududu ya riƙe mata zuciya katamaumau. Nuratu kam ƙwalla ne suka cika mata ido ma. Hannu ya sake ɗaga ma iyayen nasa sannan ya zagaya ɗayan side ɗin da AS ya buɗe masa ya shiga ya zauna. Suma su AS sukai sallama da su Oum ɗin suka shiga motar ta fice. Sannu a hankali Maanal ta lumshe idanunta da hawaye suka ciko. Jin suna neman zubo mata ta buɗesu tare da kai yatsarta ta ɗauke su tana kallon waje. Sarai AA na hankalce da ita, dan haka ya kai tattausan hannunsa ya kamo nata dake ajiye a kan cinyarta, saman tashi ƙafar ya dawo dashi yana mai harɗe yatsunsu waje guda. Ta gefen ido ta ɗan dubesa, ganin ba ita yake kallo ba ta shagala sosai a kallon nashi, dan harga ALLAH idan tace bai yi mata ƙyau ba ma tayi ƙarya. Ta shagala sosai a bazata ya waiwayo suka haɗa ido, cike da borin kunya ta kauda nata gefe tana ɓata fuska. Shi dai baice mata komai ba, kuma bai daina kallon nata ba har sai da wayarsa ta motsa alamar shigowar kira. Ɗauka yay ya duba, babban yaya ne. Dan haka ya ɗaga tare da kai yatsansa ya gyara zaman bluetooth ɗin kunnesa baƙi, cikin yanayinsa na rashin son ɗaga sauti yay sallama... Tsabar yanda yake magana can ƙasa su kansu su AS dake a gaba ba jinsa suke ba. Ita kanta Maanal dan kawai ta nutsu ne ta maida hankali a kansa duk da ba kallonsa take ba. A haka suka iso airport dan gudu sosai sukayi. Bai motsa domin fita ba, ita kuma ya riƙe hannunta bai bata damar ta fitan ba. Magana suke da AS. Ita Maanal ma tayi zaton bada shi za'a ba. Sunja kusan mintuna biyu a haka sannan aka buɗe musu. Juyawa yay ya ɗan kalleta, kafin ya saki yatsun hannunta dake sarƙale da nashi a hankali sannan ya yunƙura ya fita yanzu ma jacket ɗinsa da bai saka ba har yanzu a hannu. Itama ɗin fitar tayi, dai-dai driver na rufe side ɗin data fito ɗin AA ke isowa wajenta. Yayinda AS daya fiddo akwatinsu da wani da bata san na waye ba ya tura su yay gaba. Shi kuma da yake binta da wani kallon ƙasa-ƙasa hannunsa ya miƙa mata. Hannun ta zubama ido, sai kuma ta ɗan ɗago ta kallesa. Ita ɗin dai yake kallo idanunsa na komawa ƙanana. Yau dai ta fahimci kurumtar ce ta motsa ta miskilanci, dan haka ta ɗaura hannun nata a hankali saman nashi, shiko ya haɗesu da ƙyau sannan suka fara takawa a tare. Dole duk wanda ya kallesu su burgesa, dan kallo guda zai tabbatar maka da su ɗin ma'aurata ne. Sun matuƙar dacewa da juna kuma, duk da ita ɗin ƴar ƙarama ce a gabansa, dan koda take da tsaho tsahon nata gaba ɗaya bai wuce kafaɗarsa ba. Arba da ma'aikatansu su Yaqub ya sakata jin nauyi da kasancewar a yanda suke. Shi ko ko'a kwalar rigarsa. Sai ma amsa musu gaisuwar da suke masa yake ta hannyar jinjina kai. Itace ke amsawa cike da jin nauyin da su kuma suke fassarawa da jan ajinta. Dai-dai nan kuma aka fara shelar neman matafiyan da zasu tashi a jirginsu zuwa Qatar. Gaba yay riƙe da hannun nata su AS da su Yaqub da yaƙi yarda ya kalla ko inda Maanal take biye da su. Sai da sukai ƴan abubuwan da suka kamata kafin wucewa inda jirginsu yake. A haka yana riƙen da ita suka shiga, su sun wuce vip ne. Ganin hakan sai da yasa Maanal sauke ajiyar zuciya a ɓoye. Duk da ya jita bai nuna yaji ba, sai ma taimaka mata da yaya ta zauna a nata sit ɗin kafin shima ya zauna a nasa dake kusa da ita. Ta inda suken keɓantaccen waje ne madaidaici zaman mutum biyu tamkar wani falo ko ɗan ɗaki, zaka iya maida kujerun gado idan kaso. Ga television da kayan dai ƙawa yanda ya kamata. Tuni Maanal ta zama baƙauya, dan ita kam bata san akwai hakan a jirgi ba. Kai masu kuɗu na sha'aninsu. Bata tsinke da al'amarin ba sai da AA ya danna wani ɗan bottom ta gefen kujerar belt ya saka kansa da kansa a jikinsu. Dai-dai jirgin na tashi zuwa sama dole ta lalubo hannunsa a cikin nata. Kallonta yayi, sai kuma ya buɗe tafin nasa ya maida natan a ciki ya sargafe yatsunsu cikin na juna. Sosai ta sake ƙanƙame masa hannun har tana kafa masa ƙubunanta da ba wani tsahone da su ba dan bata wasa da yankewa a kan fatarsa. Aiko sai da ta fasa masa fata abinka da ba'asan wahala ba. Bata fargaba kuma sai da jirgin ya gama dai-daita ta buɗe idanun, hannun nasu ta ɗan kalla tana sauke ajiyar zuciya, har zata janye sai kuma tai saurin sake kallo. Sosai taji gabanta ya faɗi, babu shiri ta juyo da shi ganin yana ƙoƙarin juyarwa dan karta gani. A sanyaye cike da damuwa ta ce, “Ya ALLAH na ji maka ciwo”. Komai bai ce ba, ya dai ɗan kalli hannun ya kauda kansa. Yayinda ita kuma ta buɗe yatsun nata tana matso da hannun saitin bakinta ta shiga wura masa iska da baki kamar wanda ya kone. Ai ba ƙaramin ratsa jijiya da jinin AA hura hannun nan yay ba, a take ƙofofin gashinsa suka shiga bubbuɗewa. Dole yay ƙoƙarin janyewa yana faɗin, “It's okay”. Kanta ta jinjina masa idannunta na cika da ƙwalla, sai kuma taja tissue ɗaya dake ajiye a kwalinsa ta shiga goge jinin daba wani zuba yake ba ya dai nuna alamar fita ne kawai. Dai-dai nan ma'aijaciyar jirgin ta shigo bayan tai ɗan knocking, tray ɗin hannunta mai ɗauke da coffee ta ajiye, sai kuma ta dubesu domin jin ko suna buƙatar wani abu ne. Cikin harshen turanci Maanal tace suna buƙatar First aid box. “No...” AA ya faɗa yana ƙoƙarin dakatar da ita, amma sai maanal ɗin tace taje ta kawo. Itama ganin jinin yasata fita, babu jimawa ta dawo da wata matashiya kamarta da first aid ket ɗin a hannu. Kai tsaye inda suke tayo, ta ajiye box ɗin tana ma AA sorry. Shi ko kallonsu ma baiyi ba. Maanal ɗin da duk ta rikice kawai yake kallo ƙasa-ƙasa. Mata ta kawo hannu zata kama hannunsa Maanal tai mata tsawa batare da ita kanta tasan mi tayin ba. Cike da masifa tace ta bata zata masa. Karo na farko AA yay wani ɗin killer smile na gefen baki ya lumshe idanunsa kawai. Sai dai yana kallon yanda take goge masa jinin a ɗofane tana kuma hurawa da baki wai kar yaji zafin spirit. Sai yaji kawai abin ya masa suger. Ƙoƙarin tsokanarta yay, dan haka ya ɗan ja hannun baya kamar wanda yaji zafin. Ai da sauri Maanal ta kallesa a raunane ta ce, “Da zafi ko, I'm sorry”. Yanda tayi kamar zatai kuka yasa shi ƙara girman idanun nasa a kanta yana kallonta ciki-ciki. Kansa ya girgiza mata ganin yanda ta zuba masa idanun dake tara ƙwalla. Kan nasa ya girgiza mata kaɗan, sai kuma ya juya nasa hannun nata ya koma sama, ya matso da shi tare da ɗan duƙowa ya sumbata. A hankali ta lumshe nata idanun tare da jan ajiyar zuciya. Su dai ma'aikatan jirgi sun shagala suna kallon ikon rabbu, wannan al'amari kamar a film, dama a baƙaƙenmu akwai masu irin wannan shagaltacciyar ƙaunar, dan wannan ta wuce soyayya sai tsantsar ƙauna mai zafin gaske da sam bata ɓoyuwa a idanun masoyan. Da ƙyar ɗaya tai ƙarfin halin miƙama Manaal plaster ɗin data yanko tare da ƴar audiga. Maanal ɗin ta amsa ta sanya masa sannan tasa plaster ɗin a sama. Tattarwa sukai suka wuce suna waigensu..........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖2️⃣8️⃣ ______________ .......Matuƙar saka rayuwar Huznah gaba Sageer yayi a wannan tsakanin da buƙatunsa. Tabi kowacce irin hanya na bijirewa amma ya nuna mata namiji yake. Sai dai taci kukanta da zaginsa a zuciya dan tsoronsa ALLAH ya dasa mata. Ko fita yay da zarar taji motsin dawowarsa zuciyarta ke fara dukan uku-uku. Gashi yanzu ya hana kowa shigowa gidan dan kullesu yake ta ciki, mutum ya ƙaraci bugunsa dole ya haƙura. Wayarta ya amshe ya kashe tun ranar da sukai waya da Hajiya Basariyya. Girki kam tunda tayi sau ɗaya ta ƙwaɓa musu hauka ya koma yi da kansa. A rana ta uku yasata shiga kitchen ɗin ya fara koya mata. Dan ya tabbatar mata yana da mata bazai dinga zuwa gidansu cin abinci ko saye ba. Idan zata zage ta zage babu abinda za'a fasa. Tako tabbatar da babu abinda za'a fasa ɗin kuwa. Dan tako ina baya raga mata yanzu. Hatta da gyaran gidan tsaye yake mata akai sai tayi komai yanda yake so. Sau biyu tana satar wayarsa ta gwada kiran Hajiya Basariyya sai taji tata wayar a kashe itama. Ba ƙaramin tashi hankalinta yay ba da rashin jin uwar tata. Shiko sarai yana sane da ita, abinda bata sani ba yaji komai akan abinda ya faru da Hajiya Basariyyar a kwanakin nan Daddynsu na faɗa ma Babanshi saboda haƙurin daya bashi akan ya barsu su koma ɗakinsu suyi azumi. Shine yake sanar masa abinda Hajiya Basariyya ta aikata, da idonsa ya ganta shi da ƴaƴanta a wani ƙauye bin malamai, su kuma sunje cinikin gona ne a kusa da ƙauyen. Amma yay masa alƙawarin maida Hajiya Yaya idan tayi azumi koda goma ne a gidansu. Sosai Huznah tai ramar dole a wannan gaɓar, ga shi kota kulle ƙofar ɗakin ma yanzu a banza ama wofi zai buɗe da wani key ɗin ne. Gida kuma in zai fita ta baya yake kulleta. Tun tana masa girman kai harta fara tunanin saukewa ta bashi haƙuri kozai taimaka ya bincika mata Umminta, dan tana son sanin wane hali take. Kamar kullum yau ƙarfe biyar ya dawo kasuwa. Tana falo zaune idonta a tv sai dai bata fahimtar komai kallon kawai take yi. Shigowarsa ta sata zabura tana masa sannu da zuwa. Sosai ya zuba mata ido dan mamaki. Amma sai baice komai ba ya gyaɗa mata kai kawai. Kitchen tai saurin nufa, a wani mamakin nasa bata jimaba sai gata ta fito da ruwa ta ajiye gabansa. Badan ruwan leda bane ALLAH sai ya tsargu wani abun mutuwar ta zuba masa. Amma yasan bazai yiwu ba tunda fure water ne.... “A kawo abinci?”. Ta faɗa cikin katse masa tunani. Sai ya samu kansa da sakin murmushi. “Kina lafiya kuwa Huznah?”. Ya faɗa yana tsatstsareta da idanu. Kanta ta jinjina masa alamar eh. Iska ya ɗan furzar, sai kuma ya gyaɗa kansa da miƙewa yana faɗin, “Okay bara na watsa ruwa to, kibar abincin sai nayi sallar magrib tukkunna.” Murya a ƙasa ta ce, “To”. Nan ma sai da ya sake kallonta kafin ya wuce ciki abinsa yana kwasar dariya a zuciyarsa..... Ni kaina dai abin ya bani dariyar Man Sageer 🤣😜 _________★ Gaba ɗaya Oum kewar yaranta take ji, dan ma babban Yaya da Fawzan sun ɗauke mata kewarsu. Nibras ma da farko ta shigo, amma jin hirar da su Fawzan keyi akan tafiyar su AA ɗin saita miƙe tsam kamar ma wadda jikinta ke rawa. Sallama tai musu cikin danne kukan dake neman zuwa mata tace zataje ta kwanta ta gaji. Da kallo kawai Oum ta bita. Hakama babban Yaya da tuni shima ya fahimci take-takenta. Amma a mamakinsu shi Fawzan ɗin da suka ji tausayinsa ya kama su shi hankalinsa ma nakan waya abinsa sai zabga murmushi yake dan charting yake da Najma. Sai sukai tunanin ai bai fahimci matar tasa bane saboda sonta ya rufe idonsa. Sai dai abinda basu sani ba Fawzan ya riga kowa fara fahimtar matar tasa da inda haukanta ke ɗawainiya wajen kaita. Ya barta ne kawai bisa wasu dalilai dan yasan wane Autansu. Sannan yafi son kowa ta fahimta da kansa musamman Mamy data haɗa auren nasu. Dan yayi alƙawarin in sha ALLAHU da bakinsa dai bazai cema kowa a gidan ga halin da yake zaune da Nibras ba, har sai idan sune suka gani sukai magana.... Kuka sosai Nibras ta shiga yi a sashenta, ba komai ya kawo hakan ba sai jin matsanancin kishin AA akan Maanal. Yanzu ita har rashin muhimmancinta a gidan nan yakai AA ya shirya tafiya da wannan ƴar iskar yarinyar amma bata sani ba har sai bayan tafiyarsu. AA ɗinta, sanyin idaniyarta. Aiko har abada bazata yafe ma Maanal ɗin wannan tafiyar ba, sai ta mata hukunci dai-dai da hakan.... A ɓangaren Mamy ma dai ranta a jagule yake ita da muƙarrabanta su Nuratu. Dan Nuratu ma tun bayan tafiyar su Maanal data shige bedroom bata sake fitowa ba. Ita kanta Mamy sai da Abah ya fahimci bata cikin walwalarta. Koda ya tambayeta sai ta nuna masa kawai yanayi ne sannan kamar kanta zai mata ciwo take ji tasan kuma zafin gari ne dake sirkawa. Sannu yay mata tare da bata magani yace tasha ta kwanta yau yama yafe mata zuwa sashen nasa kawai. Aiko wannan freedom ɗin data samu kusan raba dare sukai suna waya da yayarta da maman su Saheeba. Sun tsara yanda zasu tarwatsa Oum da Maanal sosai a gidan. Daga ƙarshe suka birkice zuciyar Mamy musamman akan AA. Tare da tunzurata akan batun ƙara auren Fawzan wai dan a tantance waye baya haihuwa shi da matar tasa tunda idan sunje asibiti sai ace musu duk ƙalau suke lokacine kawai baiyi ba. Su dai sam basu aminta da hakan ba dole akwai lauje cikin naɗi. Tsaf kuwa zuciyar Mamy duk ta hau akan shawarwarin nasu. Duk da ita dai Aunty Babba har cikin ranta tana yaƙine da kishin ƴar uwarta wato Mamy, yayinda Maman Saheeba ke komai da zuciya biyu, dan itafa fatanta ƴaƴanta su kasance a gidan su mamaye komai na dukiyar su Babban Yaya ta hanyar baza ƴaƴa. Kunga ko komai ai ya dawo tafin hannunsu. Dan ita kanta Saheebar ido a rufe maganin haihuwa ake neman mata tunda tun daga cikin Anum shiru kake ji bata sake ko ɓatan wata ba ga Anum na neman cika 5years. Ita ko Mamy ɗauka take duk sonta suke yi musamman ma Maman Saheeba, dan wasu lokutan ita Aunty Babba kan ɗan faɗa mata gaskiya shiyyasa tasu bata tsaho a tare..... _________★ Bayan sallar magriba da isha'i da su Maanal suka gabatar ita da AA da har yanzu bai sake ba wajen zamansu suka koma. Ganin ya buɗe laptop itama sai ta ciro novel a bag ɗinta kawai ta hau karatu. Koda aka kawo musu abinci daga ita har shi babu wanda yabi takai duk da shine da kansa ya bada umarnin a kawo ɗin. Ɗan ɗagowa yay ya kalla Maanal jin kamar ta daina motse-motse, aiko dai gyangyaɗi take. Shi sai ma taso bashi dariya, yo tun ba'aje ko ina da tafiya ba, Chaina fa suka nufa tafiya mai nisan awanni. Wani ɗan bottom ya danna a gefen kujerar a take ta wani kalar buɗewa ta zama gado, abinda ya raba tsakkiyarsu mai kama da hannun kujera ya naɗe kansa wajen shima ya zama flat. Laptop ɗin ya matsar gefe ya kwantota a jikinsa tare da zare novel ɗin hannun nata ya ajiye. Fuskarta data fito so cute a zagayen rolling ɗin veil ɗinta ya zubama ido, sai kuma ya janye cikin lumshewa ya kuma buɗe a lokaci guda. Veil ɗin ya shiga warware mata a hankali bayan ta cire pin ɗin data riƙe da shi. Yana ko gamawa ta gyara kwanciya tana sauke ajiyar zuciya. Shima sai ya samu kansa da sauke ajiyar zuciyar acan ƙasan maƙoshi. Ɗan takurewar da tai waje guda ya sashi ɗaukar lallausan farin mayafin dake gefensu kaɗan ya lulluɓa mata har a kafaɗa, sai kuma ya zare ribbons ɗin data kama kanta da su a tsakkiya gashinta ya tarwatse masa a hannu, kamawa yay ya tattaresa cikin hannun nasa ya shiga tufkewa a hankali ta yanda bai tsamke tushen ba balle taji zafi. Veil ɗin ya ɗauka ya ɗaura mata a kan kamar ɗan kwali cike da dabara, daga haka ya ɗan ranƙwafa ya sumbaci kan nata sannan ya ɗauka laptop ɗinsa ya cigaba da aiki duk da kuwa wani ɓangare na jikinta yana a jikinsa ne... Sosai ya raba hankalinsa biyu a kallon fiskarta da aikin, dan yanda ta ɗam tsuke baki zaka fahimci kamar tayi barcin ne da faɗa a zuciyarta. Yasan halin mutuniyar tasa ba rabo take da masifa ba har a cikin barci tanayi faɗa. Kawai dai kura ce tai lafiyar dole. Eh lafiyar dole mana tunda dai risinar ta dole ce ai.... ★Barci sosai Maanal tasha, dan bata tashi farkawa ba sai kusan 9:30, zuwa sannan awa ɗaya da rabi ce ta rage musu su sauka cikin ƙasar Qatar domin yin canjin jirgi. A hankali ta shiga motsawa, sai kuma tai juyin daya bata damar komawa tana fuskantar lafefen cikin AA, rashin nauyin rigarsa da yanda ta kwanta masa a jiki har yana jin saukar nunfashinta a kan fatar cikin nasa. Sosai tsigar jikinsa ta fara tashi. Cikin wani irin motsawar zuciya ya lumshe idanunsa a slowly sakamakon sake motsawa da tai ta kife ƙirjinta da ƙyau a cikin nasa tare da zagayo hannayenta ta bayansa. Daga ganin yanda tai ɗin ka tabbatar ta ɗauka filo ne ta rungume. Cigaba da saukar numfashin nata mai ɗumi a jikinsa ya sashi jin ina bafa zai iya ba. Da ƙyar ya iya jawo busashen yawun da ke neman suɓucemasa a baki ya haɗiye, maƙoshinsa yay wani irin yin sama da ƙasa a lokaci guda cikin wuyansa. Idanun da yake faman rumtsewa ya buɗe, sai kuma a hankali ya ture laptop ɗinsa gefe can ƙuryar maƙoshi ya shiga kiran sunanta cikin taushi da sauƙin sauti dake fita cike da kasala da ƙyar..........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖2️⃣9️⃣ ______________ .......Tun Maanal najin tamkar ana kiran sunan nata a nesa ko cikin barci harta fara jin saukar sautin a cikin kunnenta. Numfashi irin na mai ƙoƙarin farkawa ta sake tare da fara buɗe idannunta a hankali. Tun tana ɗan jansu luuu ta maida kuma ta lumshe harta buɗe gaba ɗaya a kan fuskarsa daya ɗan duƙo yana kallonta shima. Sake maida idanun tai ta lumshe, sai kuma ta buɗesu da ƙyau, cikin sa'a kuwa suka shige cikin nashi dake a kaɗe daya zuba mata. Itama nata ɗin sun kaɗe tare da ƙara girma sun ɗan kumburo ta fatar saboda barci. Samun kansu sukai da kallon juna, kallo irin mai shiga jikin nan da tsinka jini. A tare yanayin jikinsu ya fara canjawa, cikin ƙarfin hali AA ya motsa nashi lips ɗin can ƙasan maƙoshi da sauti na mai raɗa girarsa ɗaya a ɗan ɗage ya furta, “You still pretending to be sleep?”. Baki ta ɗan tura tana lumshe idannunta, sai kuma ta ɗan kifa kanta a jikinsa tamkar wadda taji kunya ƙasa-ƙasa da murya irin ta wanda ta tashi a barci ta ce, “Uhm… sorry. Ban san na kwanta haka ba.” Gefen lips ɗinsa ne ya motsa kaɗan alamar son yin murmushi, sai dai baiyi ba, Da wani irin sake sauƙaƙa murya ya ce, “Hmm kinji na tambayeki yanda kika kwanta ne?. Barci yay daɗi kin haye VIP jiki.” A yanda yay maganar ya sata ɗan ɗagowa ta ɗan kalle shi da ido ɗaya, cikin ɗan waro masa idanun da shagwaɓe fuska ta ce, “Na haye? Ni wlhy sharri kamun”. Ɗan sunkuyowa yay fuskarsa gab da tata yana kallon cikin idonta a hankali, cikin zolaya ya furta, “To ko jikina ya janyo ki ne? Dan da alama yana da ɗumi sosai tunda har kika zaɓeshi fiye da bargo.” Idanunta ta janye daga cikin nasa tana mai kai hannu ta sosa goshi dan kunya, sai kuma ta ɗan juya gefe tana jin kamar ta saki kuka dan kunya ciki-ciki ta ce, “Ni dai sharri aka mun tunda ban hau ba, ƙilama bugar dani akai dan a ɗaura ni”. Yanzu kam sai da ya ɗan murmusa tare da lumshe ido, yana jin daɗin yadda take jin kunya. Cikin sake sauke murya ya ce, “Shiyyasa naga an kanannaɗe ni ai ko Madam pretender! Maimakon ki ce (thank you for being so comfortable Besty) ki bani sumba mai zafi na godiya”. Hannunta dake jikinsa tai saurin warwarewa, sai kuma ta yunƙura zata tashi. Maidata yay ya hanata hakan, cikin son ɓoye fuskarta ta ce, “ALLAH ni ka daina kana bani kunya”. Cike da basarwa cikin magana ɗaɗɗaya kamar ba daga bakinsa take fitowa ba ya ce, “Kunya mai ƙyau ce musamman idan tana zuwa daga fuskar da na fi son gani.” Yanzu kam kasa jurewa tai sai da ta kallesa, shima kallon nata yake, suna haɗa ido ya wani ɗage mata gira ɗaya sama. Ai babu shiri ta ture hannunsa dake riƙe da kafaɗarta ta tashi zaune. Komai bai sake ce mata ba, sai ma laptop ɗinsa daya ɗauka ya cigaba da aikinsa jijiyiyin jikinsa na wani mimmiƙewa. Amma ya danne komai da tsiya-tsiya kamar ba shine ya gama zuba zance ba. Itama tashi tai ta shiga toilet batare data yarda ta sake kallon ko sashen da yake ba. Ta jima a bayin kafin ta fito. Batare data yarda ta kallesan ba ma yanzu ta ɗauka book ɗinta ta zauna ɗan nesa da shi. Ganin yanda tai kamar bataga abincin ba ya sashi yin ƴar gyaran murya, ƙasa-ƙasa yana kallonta da idon daya san sirrin zuciyarta. Cikin yanayin rashin walwalar da har yanzu ke mamaye da fuskarsa ya furta, “To Madam barci, za ki ci abincinki ne ko har yanzu jikina ya fisa daɗi?” Baki ta ɗan tura gaba tana kallon shiryayyen abincin, “Wannan abincin ai ya huce tuni fa. Kawai bana ma jin ci”. Idanunsa da ke lausashe da wani yanayi mai wahalar fassara ya zuba mata, sai kuma ya janye su a slowly ya maida ga screen ɗin laptop ɗin yana kai hannu ya gyara zaman glashinsa. “Na tashe ki kice na miki rowar lallausan jiki bayan na sanki da mita”. Yay maganar cike da basarwa. Koda ta ɗago ido ta kallesa yama fiske abinsa sai ka rantse ba shine ya faɗa maganar ba. Jitai bazata iya barmasa ba itama, cikin nata yanayin basarwar ta ce, “Humm sai cika baki, kana jin kamar jikin naka wani katifa ne”. Kaɗan ya taɓe baki batare daya bar aikin da yake ba ya ce, “Ai ni sai dai ma nakira kaina 'His Royal Mattress'.” Rasama abin cewa Maanal tayi, sai kawai ta zaɓi yi masa shiru. Shima bai sake tankawar ba, sai danna abu da yay a hankali table ɗin da aka shirya abincin ya matsa gabanta zuu. Kallonsa tayi, shima dai-dai ya ɗago ya kalleta bayan ya kalla agogon dake ɗaure a hannunsa. “1:7min ya rage mana sauka Doha”. Kanta kawai ta ɗan jinjina, sai kuma ta ajiye book ɗin ta fara bubbuɗe abincin. Tana cin abincin kaɗan-kaɗan shi yana aikinsa da kallonta lokaci-lokaci batare da yayi magana ba. A haka ta tsakuri abincin ta ajiye dan sam jitai ma bai mata wani daɗi ba ita kam. Ganin lokaci ya gabato shima ya tattare aikin ya ajiye tare da maida komai inda yake. Itama veil ɗinta ta ɗauka ta naɗa bayan ta maida ribbon ɗinta. Dai-dai nan aka sanar da isowarsu ƙasar Qatar. Sun sauka a Hamad international airport dage birnin Doha. Babu wani zaman jira da zasu yi, dan daga jirgin ma wani jirgin suka shiga da in sha ALLAHU shine har ƙasar Chaina. Nan ɗin ma dai vip section ne ita da shi, sai dai na wannan jirgin ma yafi wancan matuƙa, dan harda gadon barci da yaji shimfiɗu na alfarma. Sai Maanal taji duk ta samu kanta da tsarguwa. Amma a zahiri ta wani dake abinta sai gajiya da jikinta ya fara nunawa na zama waje ɗaya. Sosai Doha ta birge Maanal, duk da bazata iya ƙarar da komai na cikinta ba daga jirgi ma take kallonta, gashi dare ne sai dai tako ina akwai haske fayau kamar ka yarda allura ka ɗauka abarka. A wannan tafiyar an samu canjin yanayi, domin kuwa AA ne yay barci a yanzu, yayinda Maanal tai zaman kallon wani american film da yay mata daɗi sosai, daga ƙarshe itama dai ta sake ɓingirewa barcin a kujerar da take. Tafiya ce ta awanni takwas daga Doha zuwa Shanghai da zasu sauka ta ƙasar Chaina. Dan haka AA ya samu barci isasshe, dan sai asuba ya farka, ganin itama Maanal barcin take sai ya samu kansa da zuba mata ido. Ya jima yana kallonta kafin ya miƙe domin gabatar da alwala. Koda ya fito itama tashinta yayi tayo alwalar, duk da inda son samu ne zataso yin wanka ma, amma a wannan jirgin babu alamar akwai wannan damar, dan haka ta ɗan gyagygyara inda zata iya sannan ta fito. Salla suka gabatar, bayan sun idar kamar yanda ta saba ta ciro Alkur'ani dake a handbag ɗinta ta fara karatu, idanu kawai ya lumshe yana sauraren daddaɗan sautinta dake fidda ƙira'a dalla-dalla. A haka lokaci yayi, aka fara sanar da saukarsu nan da awa ɗaya kacal. Addu'a tayi tare da azkar suka kimtsa komansu duk da ba wani tarkace bane ba iya na hannu ne bag ɗinsu na ƙasa.... ★An buɗe ƙofar jirgi da sanyi mai ɗauke da iska mai ɗan zafin canjin yanayi na sabon gari ya bugi fuskarta. Ita tana kallon komai da yanayin sabo, mamakin ganin rana ce yanzu anan Chaina , mutanen da ke tafiya da sauri, harshen da ba ta fahimta ba, da kuma sautin rayuwar da bata saba da shi ba. Shi kuwa gogan naku, ya sauka kamar wanda yazo gida – a yanayi na izza mai nutsuwa, cikin shigar da ba ta da yawa amma tana da nauyin kamanni. Ba ya magana da yawa, amma idanunsa na bin komai cikin salo. A tare su Yaqub suka iso inda suke suna gaishesu cike da girmamawa. Ita dai kanta a ƙasa, dan girmamawar da suke bata kunya take bata musamman su CMO. CFO dai taƙi yarda ta kalla inda suke, dan ba ƙaramin danne zuciyarta take ba akan wannan ƴar tatsitsiyar yarinyar dake neman ɓata mata aiki. Sai dai a zahiri bazaka taɓa fahimtar yanayinta ba dan mace ce wayayya mai kuma wayo da iya taku. Taji matuƙar daɗi data fahimci a hotel ɗaya zasu zauna su dukansu. Manaal tayi mamakin motar da tazo ɗaukarsu, ƙyaƙyƙyawar gaske baƙa wulik mai aiki da caji ba fetur ba. Kasare tai tana kallon chainawan da suka fito su biyu suna gaishe da AA cike da girmamawa. Shi ko ya amsa musu cikin yanayinsa na riƙe girma, sai kuma ya ɗan kalla Maanal dake gefensa da harshen Chaines da Maanal bata san ya iya ba sai yau ɗin nan ya sanar musu ga matarsa. Sosai farin cikinsu ya sake bayypana, suka juya suna gaishe da Maanal cikin harshen turanci da girmamawa. Ita kam da ƙyar ma ta iya fahimtar turancin nasu, ta amsa musu a taƙaice sai dai da kulawa. Sake maida hankalinsu sukai ga AA, cikin yaren da ba fahimta take ba sukai masa magana. A mamakinta sai taga yay ɗan guntun murmushi kawai. Samun kanta tai da ɗan shagala a kallonsa, yana yin kamar zai juyo ta kauda kanta gefe. A mamakinta daga ita sai shi ne suka shiga motar, sauran kuwa bata san yanda suka kare ba..... Sannu a hankali motar ke tafiya bisa lafiyayyen titin mai faɗin gaske da yalwa ta yanda motoci keta kai kawonsu cike da watayawa. Motar tayi shiru. Hankalin AA naga tab ɗin da ɗaya a ƴan cainar suka bashi, Maanal kam ta maida nata hankalin ga waje tana kallon gine-gine masu ban mamaki da ƙawa. Eh lallai ga inda gini ke amsa sunan gini, duk da kuwa Abuja ba daga baya ba a ƙyaun gine-gine da tsarin anguwanni sai taga can ya koma mata local. Duk yanda taso danne shauƙinta hakan ya gaggara, a bazata batare da tasan da matsowar AA gab da ita ba da murya mai laushi, amma cike da basarwa ta tsinkaye sa a cikin kunenta yana faɗin, “Kar kiyi kamar zaki ɓata mana. Ina nan a kusa dake, ki tuna.” A hankali ta ɗan murmusa a ƙasan maƙoshi. Sai kuma ta ɗan juyo ta kallesa cikin ido tana mai ɗan ɗage gira sama ta ce, “Lah nazata ai a Nigeria na baroka ma ni, kasan abinka da baƙauye yazo birni.” Yatsa ya kai zai ɗalli hancinta, tai saurin juya fuskarta gefe ta hanashi damar hakan. Lips ya ɗan cije, sai kuma ya koma ya zauna da ƙyau cike da basarwa. Sai da suka iso hotel ɗin taga su Yaqub, sai dai basu tsaya a inda suke ba su sukai ciki bisa jagorancin yan chaina ɗin nan. A jere ita da shi suke tafiya a dogon corridor ɗin dake shiru babu hayaniyar komai, sai dai komai a tsaftace yake ƙal kamar kaci abinci a ƙasa. Card ɗaya ya miƙa masa yana nuna masa ƙofar ɗakin da suka tsaya cikin yaren su. Shi kuma ya gyaɗa kai kawai yana amsa batare da yace komai ba. Hannu suka ɗaga mata alamar bye suka wuce. Ita kuma tai ɗan murmushi da jinjina kanta kawai a taƙaice. Matsawa AA yay jikin ƙofar ya saka card ɗin. Ita kuma ta ɗan tsaya sororo.........✍️ _To mun ido Chaina kuma, bari nima na shiga nawa ɗakin na watsa ruwa sai mu ɗora labari 🏃🏃, karku damu ɗakina kusa dana su Maanal ne komai zan jiyo muku 😂._ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖3️⃣0️⃣ ______________ .......Cikin mamaki da ɗan daburcewa ta ce, “Wai ɗaki ɗaya?” ta tambaya fuskarta cike da rauni. Juyowa yay yana kallonta kai tsaye, sai kuma ya basar cikin zurfin furuci ya ce, “Basai kin damu ba, sunansa ɗakin barci kawai, ba ɗakin yin wani abu ba.” Baki ta tura gaba tana ɗan kau da idanunta, shima sai ya tura ƙofar kawai ya shiga, ɗan juyowa yayi, ganin tana tsaye cikin yanayin ƙaulani har yanzu, “Ko ɗauka kike so?” “Ni ban ce ba”. Ta bashi amsa idonta a ƙasa, sai kuma ta motsa a hankali zuwa gaban ƙofar, jatai ta sake tsayawa, batare data kallesa ba ta ce, “Amma ba gado ɗaya ba?”. Yanzu kam kansa ya ɗan girgiza yana kallonta da ƙyau, sai kuma ya ɗauke idanun ya ɗan kalli gefe. Da alamun ƙosawa ya ce, “You can sleep on your pride if the bed makes you nervous”. Daga haka ya matsa mata alamar ta shiga. Haka kawai ta samu kanta da sanyi jiki. Cikin ɗari-ɗari ta shiga, numfashinta na sizen, zuciyarta kam rawa take a hankali kamar wadda ke jira ace mata ar ta feta a guje. Tana jin ya maida ƙofar ya rufe ta wani lumshe idanunta. Sai kuma ta samu kanta da matsawa jikin window ko zata samu iska ta bugeta abinda ya tokare mata nunfashi ya narke. Shiru tai tana kallon hasken rana daya fara buɗewa dan yanzu ana nufar kusan ɗaya na rana ne a ƙasar. Cike da takunsa na ƙasaita da izza ya ƙaraso inda take, tsaye yay kawai a bayan ta yana cire agogon hannunsa kamar wanda ba ya cikin gaggawa. Shima dai idanunsa na kallon garin ne zuciyarsa cike da wadatuwa da iskar dake buso su. Shiru ne ya mamaye ɗakin, ba motsi, ba rikici, sai shauƙi da tambayoyi dake cike taf a zuciyar Maanal marasa ma'ana da shiga ƙaulanin furta wa a bayyane. Tamkar mai raɗa muryarsa a ƙurya cikin kalamin dake fita ɗai-ɗai ya furta, “Hum! K! A komai sai kin yi kamar za ki gudu ne?”. Baki ta ɗan taɓe batare data juyo ba ta ce, “Kai kuma kullum sai ka dinga yi kamar kana son a biyo ka ba”. Yanzu kam murmusawa yay, sai kuma ya laɓe baki kaɗan, da murya ƙasa sosai ya ce, “Ba kullum ba ne. Amma a wannan gaɓar ya kasance tare da ke watakila.” Da sauri ta juyo tana kallonsa. Sai kuma kamar a tsorace ta ce, “Wai me kake nufi?”. Gira ya ɗage sama yana wani ƙanƙance ido ya bata amsa da, “Duk abinda zuciyarki ta baki. Dan anan babu Aban naki dai kin sani. Garama ki lallaɓa a rabu lafiya in ba haka ba kuma jiki magayi”. Yana gama faɗa ya wuce yana wani shegen makirin murmushi irin mai saka kaɗuwar hanjin wanda ya tsargun nan...... __________★ Cikin ƴan kwanaki kaɗan Hajiya Basariyya tai wata irin rama da baƙi, ba komai ya jawo mata hakan ba sai zafin rana da uban aikin da take lafta a gidan kawu Manu. Dan takai yanzu har gona idan zaije tasa ƙeyarta yake su tafi tana taya shi da ƙananun ayyuka. Taƙi sakin jiki taci abincin gidan, ga biscuits ɗin nata sun ƙare. Sarai iya na lure da ita, amma tai kamar bata ganin ba dan itama ba shiga dabgarta take ba, ai yunwa ba ƙanwar uban wani nace ba, magana ma sai ta zama dole yake haɗa su. Tun Hajiya Basariyya na dauriya da tunanin ai kawun zai barta koda a sati guda ne harta fara gazawa. Hankalinta a tashe yake sosai da ganin ana niyyar ma ɗaukar azumi a jibi idan ALLAH ya kaimu. Ita ko tasan idan aka ce a gidan nan zatai azumi ai tagama mutuwa.... Da daddare ta yanke shawarar samun Kawu Manu ta bashi haƙuri ta tabbatar masa tayi nadama kuma ta amshi laifinta. Haka ɗin kuwa akayi, bayan sallar isha'i yana zaune yana cin tuwonsa suna ƴar hida da iya dake gefe ta fito daga ɗakin iyan. Su duka kallonta sukayi, kafin Iya ta janye nata cikin taɓe baki. Shima Kawu Manun janye nasa yay ya koma ga cin abincinsa. Sum-sum tazo ta tsugunna a gabansu kamar wata munafuka, yi yay kamar bai ganta ba, dan haka ta fara magana cike da rawar muryar son yin kuka. “Kawu dan ALLAH kayi haƙuri na tuba. Wlhy nabi ALLAH na biku bazan sake ba. Na maka alƙawarin zan zauna lafiya a ɗakina. Ba kuma zan sake biyema wata ƙawa ta kaini wajen kowa ba. Wlhy Kawu wasu abubuwan dole ce ke sani aikatawa. Tunda Daddyn Huznah ya auro amaryarsa gaba ɗaya baya mana adalci, ya tattare komansa ya tare gareta. Agololin ƴaƴanta sune kawai ƴaƴa a gidan. Koda kwatance baya yima ƴaƴanmu irin gatan da yake musu. Ni babu kamar ma nawa, dan ita Hajiya Sadiya yana tsoron mahaifinta tunda tana goranta masa sune tushen arziƙinsa. Sannan ɗanta shine akan komai na dukiyarsa, nidai nice a baya ga komai na gidan kamar mara gata. Yanzu kaga akan auren nan nasu Huznah, ƙiri-ƙiri ya ɗauka wanda zata aura ya bama agola dan ya birgesu. Ya haɗa Huznah da ɗan Sani bayan ko ku Kawu kun san Sani ba ƙaunata yake ba, tun ma kafin a auro ni ya nuna adawarsa, dana shiga gidan kuma suka haɗe kai da Hajiya Sadiya suka dinga cin mutunci na sai da na zama jaruma. Kawu ya ake so nayi, Huznah fa ita na fara gani a duniya matsayin gudan jini, bazan so ganinta a damuwa ba tunda na san bata son ɗan Sani, kuma kowa shaida ne a kan hakan tunda tun a shekarun baya bama ta gama Secondary ba yace yana sonta tace a'a nima kuma nace a'a....” Cikin katseta Kawu Manu daya gama wanke hannu yace, “To yanzu ya kike so ayi?”. “Ayi haƙuri Kawu a barni na koma ɗakina naje na rungumi ƴaƴana, sannan dan ALLAH kasa baki a raba auren nan na Huznah ALLAH nasan bata jin daɗin zaman nan”. “Ita da kanta tace miki bata jin daɗin zaman? Duka yaushe ma aka kaita gidan auren da zata fara banbance daɗinsa da akasinsa? In ce gaba ɗaya yau sati na huɗu muke, koma wata guda ba'a ƙulla ba cif. Basariyya ki kiyayeni, ki kuma fita idona, niba dattijon banza bane. Ai dama tunda Mairo (Iya) ta dawo daga bikin ta sanar min iya shegen da kike zubawa nasan kin shirya sheɗanci a zuciyarki, to ni bazan hanaki kashe auren ƴarki ba, amma ki sani, ana sakota ta koma gidan ubanta kema zan kira Usman ya sakeki ki dawo nan, kuma wlhy anan ƙauyen zaki samu miji na aurar dake. Komawa kuma ba yanzu ba dan har yanzu bakiyi hankali ba, karma ki sake samuna da wata magana anan zakiyi azumi tashi ki ban waje shashasha da bata da wani girma sai na jiki. Shekaru na nuna kansu a jikinki har kin aurar da ƴa amma hankali sam babu a tattare dake sai shaiɗanci fal a zuciya. Da kike cewa shi Alhaji Usman ɗin yana fifita amaryarsa fiye daku tafi ƙyautata masa ne shiyyasa, ku kuma kun zauna baƙin kishi, har kuna wani gorantawa yara da kiransu agololi, su waɗannan agololin zata iya yiwu ma sune zasu tallafi rayuwarku ta gaba kosu taimaki ƴaƴanku, dan ka kiyayi ɗaukakar wanda mutane suke son ƙasƙantarwa jahilcin banza da wofi kawai.... Hawaye sosai Hajiya Basariyya ta miƙe tanayi, zuciyarta kuwa tamkar zata kama da wuta saboda zagin ƙare dangin da Kawun yay mata. A ranta kuwa alwashi take ɗauka ko guduwa ne sai tayi wlhy. Dan bazatai azumi a wannan garin ba ta mutu a banza.... __________★ CHAINA (Shanghai) Sosai zuciyar Maanal ta shiga kai kawai. Kalamansa ta shiga son fassarawa, (Hum! K! A komai sai kin yi kamar za ki gudu ne?. Ba kullum ba ne. Amma a wannan gaɓar maybe ya kasance tare da ke watakila) jitai kamar zuciyarta zata ɓare dan tsoro, sai kuma ta shiga ƙalubalantar kanta aka amsar data bashi. Wayyo ita kam taga takanta, mi mutumin nan ke son maida ita ne, yama barta da gajiyar tafiyar nan ta awanni mana, amma sai ya takaleta da rigima. Waiwayawa tai ta ɗan kallesa, dai-dai yana zare shirt ɗin jikinsa, ay da sauri ta juya zuciyarta na bugawa, sai kuma ta rumtse idanunta da ƙarfi dan ingarman jikinsa yaƙi barin cikinsu. Eh sunyi wata rayuwa a baya a bigiren ƙuruciya, duk da ba sa'anta bane ko a wancan lokacin amma dai yaron ne shima. A lokacin da ƙaddarar rabuwa tazo musu yana a gaɓar kammaluwar zama cikakken namiji ne, kuma sam baya tu'ammali da gym a wancan lokacin, sannan bai taɓa yarda ya zauna a gabanta koda da dogon wando da singlet bane ba. Dan zata iya rantsewa bata taɓa ganinsa ba kaya jikinsa ba, sanin ma tana shigar musu ɗaki a wasu lokutan kafin ma Oum ta hanata idan zaiyi wanka sai ya kulle ƙofa, ko yace mata zaiyi wanka karta sake ta biyoshi, itama kuma data fara mallakar hankalinta ta fahimci mi yake nufi tuni ma irin waɗan nan yanayin take zille masa....... “Tunanin mi kike yi?”. A ɗan zabure Maanal ta juyo gareshi, dan a bazata taji saukar muryar tasa a cikin kunnenta. Babu shiri kuma ta sake juyawa tare da matsawa a kusa da shi ta koma jikin window ɗin sosai. Muryarta har ɗan rawa-rawa take wajen faɗin, “Wai dan ALLAH mi kake son maida kanka ne? Hakan fa baida ƙyau kana zuwa gabana babu kaya kai ko kunya ma baka ji”. A hankali AA ya kai hannunsa kan gashin gemunsa daya zagaye har zuwa kumatunsa yana ɗan jansa kaɗan-kaɗan, yayinda ya zuba mata idanu a wani irin yanayi. Jin shiru yasa ta ɗan sake juyowa a tunaninta ya bar wajen, sai suka sake haɗa ido, ai a sukwane ta sake juyar da kanta. Ji take kamar ta saki kuka, ALLAH kunyarsa take ji, haba jama'a Bestyn ta fa, wlhy al'amarin ya mata girma. Sai kawai taji hawaye na cika mata idanu ma, dan harga ALLAH ita dai wannan zuwa Chaina ya zame mata alaƙaƙai. Shi ko AA a wannan gaɓar dariya ma ta soma bashi, amma dai baiyi ba, fuskar tasa ma babu walwala kamar dai yanda ta kasance take tun barowarsu gida. Sai in yaso yin murmushin ne yake yin taƙaitacce. Barin wajen yayi yana ƙarasa kunce belt ɗinsa, dan shi da dogon wandon kawai suka rage sai na ciki. Belt ɗin kawai ya cire ya nufi bayi da dogon wandonsa, ƙarar rufe glass door ɗin ya saka Maanal da komai ke neman ƙwacewa sakin nannauyan numfashi. Magana ta ALLAH bazata iya zaman nan ba, wlhy a takure take matuƙar takura, ita dai bara ya fito, zata roƙesa ya barta ta koma wani ɗakin kawai, dan zamansu tare anan zai iya sakawa zuciyarta ta buga ne, sannan zai iya karya mata lago da shawarar su Didi. Jin ƙafafunta sun fara sagewa cike da sanyin jiki ta baro wajen window ɗin, a ɗaya daga cikin sofas ɗin ɗakin dake tsare matuƙa takai zaune, sai ta juya ma ta inda zai fito baya, wayarta ta ciro ta fara game, duk da ba fahimtarsa take ba gara tayi dai. Ƙarƙashin zuciyarta kuwa kewa take ji, kewar su Oum da Ammien ta. Ashe sanda tana Abuja dan suna waya ne da Ammien a koda yaushe shiyyasa take jin damuwar rashinta a kusa da ita kaɗan-kaɗan, yanzu kam sunyi nisa da juna, ta yanda bama tasan yaya zasuyi koda waya ba tunda ba layin ƙasar ne da ita ba..........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖3️⃣1️⃣ ______________ .......Maanal ta matuƙar shagala a tunaninta AA ya fito a bayin, sanye yake da bathrobe golden yellow, gaba ɗaya ƙamshin sabulunsa na shower gel ya mamaye ɗakin, ɗan kallon Maanal data juya baya yayi ya ɗan taɓe baki yana cigaba da goge kansa da ƙaramin towel. Hankalinsa kwance yaje inda take ya zauna a wata kujerar daban. A dakensa ya furta, “Ki tashi kije kiyi wanka dan zamu fita shopping ɗin abubuwan buƙata”. Batare data yarda ta kalleshi ba ta girgiza kanta. Sai kuma muryarta ƙasa-ƙasa kamar zatai kuka ta ce, “Ni ba sai nayi wankan ba, dan ALLAH mizai hana na koma wani ɗakin koda na kusa da kai ne, kaga zamanmu anan kai zan takura maka ai....” “Ni nace miki na takura?”. Shiru tayi dan yanda yay maganar miryarsa da ɗan tsauri sai taji wani kalar shakkarsa. “Dake nake fa! Kuma nasan kin jini”. Yanzu kam kanta dake duƙe ta girgiza masa, dan taƙi yarda ta ɗago ta kalla koda sashen da yake ma. Ciki-ciki shima yaja tsuki da yazo masa a bazata, kafin a daƙile ya ce, “In kuma kina da kuɗi sai kije ki kama wani ƙofa a buɗe take”. Daga haka ya miƙe ya bar mata wajen. A bakin gado ya zauna ya shiga gyara jikinsa zuciyarsa na zafi, haka kawai yaji haushin maganarta, wai miyasa bazata sassauta ma zuciyarta ba, miyasa bazata fahimcesa, abubuwa sun masa yawa matuƙa, yana son raba koda wani yankin ne na damuwarsa da ita amma taƙi bashi fuska, bai gajiya ba yana cigaba da binta dan yasan shi mai laifi ne a gareta, amma koyaya bazata tausaya masa ta sassauta masa ba ne. Maanal da tunda ya maka mata baƙar maganar in tana da kuɗi taje ta kama ɗaki taji hawaye sun cika mata ido, sai kuma suka gangaro a hankali. Veil ɗinta tasa ta ɗauke su, sai kuma ta ajiye wayar ta miƙe, bayin ta nufa. Ya ɗan bita da kallon ƙasan ido harta shige. Tana maida ƙofar ta rufe ya janye idanunsa yana sauke ajiyar zuciya... Kafin ta fito ya shirya abinsa tsaf cikin ƙannan kaya. Dogon wando ruwan ƙasa ya saka t-shirt mai v neck mara nauyi data kwanta a jikinsa matuƙa ta fiddosa a ingarmansa. Turare ya saka sannan ya shiga ɗan gyara sumarsa sama-sama da kwantaccen gashin kumatunsa. Ficewa yay a ɗakin bayan yayi sallar azhar dan ya tabbatar bazata fito ba in har yana ciki tunda har yanzu tana a ciki a maƙale, samun kanshi yay da girgiza kai kawai. Wai yau shine Maanal ke jin kunya, yarinyar da a gabansa ta fara dukkan abinda take ɓoye masan a yanzu. Yarinyar da yasha yima tsarki. Yarinyar da yasha wanke ma underwear. Yarinyar da yasha goyawa a bayansa. Oh-oh duniya-duniya, Maanal ɗinsa, Bestyn sa na jin kunyarsa. Koda yake shi hakan ya masa, yana son mace mai kunya, dan wannan noƙe-noƙen da take masa ƙara daraja take a idanunsa, irin wannan hallayar tatace tayi ƙaranci a tattare da ƴammatan yanzu shiyyasa ya tsani mafi yawancin su. Kaga yara ƙanana tun basu tafasa ba suna neman ƙonewa, masu ɗan ƙoƙarin ne suke gama Secondary da wannan yanayin, ana shiga jami'a sai a fifirce su wayayyu. Humm mutane da shirme, rawar kai da rashin kamun kai ne wayewa wai. Wannan abu na ƙona masa zuciya. Ai a baka yarinya a ɗanyarta bata san komai ba na rayu, koda ta sani ɗin wannan kunyar ta hanata iya bayyanawa a gabanka shine ka more alaji. Amma ka aureta kafin ka kai mata kiss ta miƙo maka baki, kafin ka kai hannu jikinta ta sallama maka jikin kaico. Ai yarinya ta dinga jin kamar zata nutse a waje idan kuna tare, koda ta san mi kake nufi ta nuna bata sani ba, duk iliminta duk wayewar zurfin karatunta a gabanka ta maida kanta bata san komai ba shine zaka dinga jinka a wani shauƙi da ƙasaitar cikakken namiji. Ka dinga kallonta tamkar wata baby doll a gabanka, ka koya mata karatunka idan akazo gaɓar da zata goge sai akai matsayar da ita zatai maka bita. Amma an kawo maka yarinya tana nuna maka ita tasan komai idonta a buɗe suke ai akwai matsala, idan kai wasa ma wata sai ta maka fyaɗe, ko kuma kaita zargin kanka da ita kodai tama taɓa yi ne a waje kafin kai. Dan ko ta kawo maka mutuncinta zuciyarka zatai ta tunanin an ɗan sha minti gaskiya..... Ƴar karar Maanal ta maidosa hayyacinsa daga dogon tunanin da ya tafi, ƙofar ya kalla, sai kuma ya murɗa handle ɗin a hankali ya tura ya shiga. Daga bakin ƙofar ya hango yanda take kici-kici da riga alamar zip ne ya sarƙafe mata a gashi. Numfashi ya ɗan furzan, sai kuma ya shiga takawa a hankali har inda take, hakan yay dai-dai da tuntuɓe da tai da bakin lallausan carpet ɗin gaban gadon saboda yawon da take ɗanyi a wajen na kici-kici. Riƙota yay jikin nasa, yay mata zobe da hannunsa ɗaya a kan ciki, ɗayan yana ƙoƙarin kaishi ya riƙe hannunta da take kici-kici cire rigar. A ɗan rikice ta ce, “Na banu waye?”. Sai kuma tai ƙoƙarin sunkuyawa, hakan ya bama ƙirjinta damar kwanciya a tsintsiyar hannunsa dake a saman cikinta. Harga ALLAH ji yay yana neman daburcewa, amma sai ya danne da ƙyar, cikin cije lips da ƙanƙancewar murya ya furta, “Mijinki”. Dama zuwa yanzu ta nutsu, dan ƙamshin turarensa ya isar mata shi ɗin ne tun kafin ya faɗa. Miƙewa tai tsaye sosai ta tsaya da ƙafafunta. Shima sai ya sauke numfashi a rarrabe ya kamata ya zaunar a bakin gadon shima ya zauna. A mayuƙar kasalance ya shiga zare gashin a zip ɗin. Ajiyar zuciya sosai Maanal ta sauke lokacin da ya gama zarewa rigar ta sauka. Suna haɗa ido ta kauda kai da sauri, ƙasa-ƙasa ta ce, “Thanks you”. Miƙewa kawai yayi batare da yace komai ba ya ɗauka jacket ɗinsa mara nauyi da scarf dan yasan zuwa anjima kaɗan zasu iya jin sanyi duk da garin Shanghai ba gari bane mai yawan sanyi ya nufi ƙofa. Sai da ya buɗe zai fita sannan ya furta, “Jiranki nake”. Daga haka ya maida mata ƙofar ya rufe. Duk ji Maanal tai babu daɗi, dan ta fahimci kamar a cikin fushi yake har yanzu, bayan kuma ya fara sakkowa lokacin suna a jirgin Nigeria zuwa Qatar, bata san kuma miya ƙara ɓata masa rai ba tunda suka iso. Jikinta dai duk a sanyaye ta ƙarasa shiryawa, dan sam bata son a dalilinta taga wani a ƙunci, kodan ta ɗanɗana zafin hakan taji a shekarun baya oho, tayi ƙyau sosai cikin doguwar rigar atamfar, daka ganta kaga cikakkiyar ba'afirikiya. Bayan tai ɗaurin zarah buhari ta yana gyalenta sannan ta ɗauka handbag ɗinta ta fito. A bakin ƙofa ta ganshi tsaye, ya jingina jikinsa da bango tare da ƙafarsa ɗaya, ɗayarce kawai a ƙasa, sai hannunsa ɗaya jacket ɗinsa ce a saƙale, ɗayar kuma yana latsa waya. “Na gama”. Ta faɗa cikin ƙaramin sauti ganin baiko motsa ba duk da tasan yaji fitowarta. Kaɗan ya waiwayo kansa ya kalleta, sai kuma ya ɗauke yana mikewa tsaye sosai ya zura wayarsa a aljihu. Tafiya suka fara yi a nutse, kowa zuciyarsa na tunani daban, har suka gama shanye rabin corridor ɗin sannan suka iso ga elevator. Shine ya danna ya fara shiga, kafin tabi bayansa sannan ya sake dannawa ƙofar ta rufe. Cikin abinda baifi minti ɗaya ba suka iso, ƙofar na buɗewa ta yunƙura zata fita ta tsinkayi shigar lallausan tafin hannunsa a cikin nata. Ciki-ciki kowa ya sauke ajiyar zuciya, sai kuma suka kalla juna a lokaci guda. Fin seconds goma suna kallon junan cikin ido, motsin masu jiran su fito suma su shiga ne ya maido su hayyacinsu, itace ta fara janye nata, kafin shima a slowly ya maida ga mutane biyu dake a ƙofar. Ƴammata ne su biyu, suka wani bishi da kallon ƙurulla, hannun Maanal ɗin ya sake damƙewa suka fice. Dai-dai suna barin wajen ɗaya a cikin ƴammatan ɗaya takai bakinta wajen kunnen ƴar uwarta tai mata gwargwaɗe daya sakasu yin ƴar dariyar shaƙiyanci daya tabbatar da maganar tasu akwai iskanci a ciki. Basu ƙarasa jin abinda suke faɗan ba dan sunyi nisa. Maanal dai jitai zuciyarta ta ƙuntata da dariyar yaran, dan ita yara zata kirasu duk da ta tabbatar bazasu girmeta ba dan suma dai bazasu wuce 20+ ɗin ba kamar ita. Ganin sun fito a hotel ɗin gaba ɗaya a ƙafa har sun fara tafiya a titi Maanal ta dakata. Shima tsayawa yay sai kuma ya ɗan kalleta. Cike da shagwaɓar da ta saka tsigar jikinsa tashi ta ce, “Wai babu a bin hawa?”. Idanunsa masu laushi ya zuba mata, cikin wani irin kallo dake mata tasiri a cikin jiki, ganin bashi da niyyar tanka mata sai ta sake narke fuska. Kamar zatai kuka ta ce, “Wai mi akai maka kaketa fushi ne tun a gida?”. Sosai yanzu kam ya lumshe idanunsa ya sake buɗewa a kanta, batare daya amsa maganar ƙarshe ba ya ce, “A ƙafa zamuje dan jikinmu ya warware da zaman jirgi”. Yana gama faɗa yaja hannunta kawai suka cigaba da tafiya. Harga ALLAH jitai zuciyarta ta raunana. Sam bata son ganinsa a damuwa. Hankalinta tashi yake. Musamman yanzu data fahimci irin wannan yanayin yana samosa ne daga Mamy. Dan lokacin da zasu taho ta lura da kallon gargaɗin da Mamy ke masa, wanda ta tabbatar ko rantsuwa tayi babu kaffara akanta ne game da wannan tafiyar da babu yanda zatai ta ya hana yinta da ita. Cike da son lallashinsa ta matsa jikin hannun nasa sosai ta kwantar da kanta. Cak ya tsaya yana kallonta, itama kallon nashi takeyi idanunta na ɗan tara ƙwalla. Kamar mai raɗa cikin motsa lips ɗinta a hankali ta ce, “Baka ƙyau idan kana fushi, Please kayi murmushi”. Idanunsa dake wani kalar raunana a cikin nata ya janye slowly, sai kuma yay ɗan murmushin gefen baki a taƙaice. Murmushin itama tayi, tare da faɗin, “Thanks”. Komai bai ce mata ba suka cigaba da tafiya. Duk inda suka gitta binsu ake da kallo musamman saboda shigar jikinta da ta zamewa wasunsu baƙon abu. Kai da abu yakai ya kawo ma har tsaidasu ake dan ayi hoto. Sai dai AA yaƙi bada haɗin kai dan sai yay kicin-kicin da fuska, ko kuma ya hana a tsaya ta gefen Maanal ɗin.........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖3️⃣2️⃣ ______________ ........Sunzo dai-dai gidan wani abinci ya tsaya, kallonta yay murya a ƙurya ya furta, “Kina jin yunwa?”. Dan kawai kar yaga ta gwalesa ta jinjina masa kai, dan bata wani jin yunwa ita kam. Ciki suka shiga, Maanal tabi wajen da kallo tana jinjina tsaruwarsa da ƙawatuwarsa. Sun kuma samu tarba ta mutuntawa da akema kowanne customer. Wajen zaman daya dace dasu aka basu, tare da takardar da tsare-tsaren abincin ke ciki. Shine ya amsa yana dubawa, dan su dai komai nasu da yarensu suke rubutawa. Hajjaju Maanal kuma ba'a iya Chaines ba. Shi kansa mamakin sanda ya iya yaren takeyi, duk da dai bata da tabbacin ko ya iya sosai-sosai ko sama-sama ne. Tana nan ta shagala a tunani har aka fara kawo abubuwa ana jera musu. Ganin yanda take bin komai da kallo sai a sannan AA yay magana. A taƙaice ya ce, “Komai dake anan Halal ne”. Ajiyar zuciya ta sauke kamar dama abinda takema waswasin kenan. Sai kuma ta ce, “Amma to musulmai ne masu wajen?”. Kansa ya jinjina mata, dai-dai waiter ɗinsu na sanar masa an kammala. Ya jinjina mata kai cikin harshen Chaines yace, “Thanks you”. Sai da tabar wajen sannan ya maida hankalinsa ga Maanal yana ƙoƙarin tura mata abinda yasan zata iya ci a gabanta. Tare da cigaba da amsa mata maganarta. “Musulmai ne ita da mijinta dake da wajen”. Kai Maanal ta jinjina, sai kuma ta saki murmushin daya sashi tsayawa yana kallonta. Tana ɗagowa suka haɗa ido tai masa alamar (miye) da ido tana ɗaure fuskar. Kansa kawai ya ɗauke ya fara cin abincin a nutse. Itama fara ci tayi, ba laifi da daɗi, sai dai test ɗin akwai banbanci mai nisa tsakaninsa da namu na gida. Haka dai ta daure taci batare da yin ƙorafi ba. Shi ko jira yake tai ƙorafin dan yasan zatayi, da batayin ba kuma yayi mamaki amma bai ce komai ba. Sun ɗan jima a gidan abincin kafin su fito, yanzun ma a ƙafa suka cigaba da tafiya, sai dai tafiyan bai nisa ba suka isa wani ƙaton Mall mai ƙyawu sosai. Dan bayan wajen shopping akwai wajen wasan yara, da ɓangaren games na manya, akwai wajen hutawa na masoya, kai da abubuwa daban-daban. Sudai wajen kasuwar suka nufa, ɓangaren tufafi ma. Anan ɗin ma sun sha kallo, dan Maanal har sai da taji kallon ya fara mata yawa ita kam. Dan haka ta ƙara maƙurewa jikin AA. Shi da kansa ya shiga zaɓa musu kayan daya kamata, na fita da na shan iska da sai dai a saka a cikin ɗaki. Sai jackets musamman ita duk da yasan ba garin sanyi bane sosai sai irin yamma haka da safiya, a yanzu haka ma yayi mamaki da batai ƙorafi ba, koda yake ƴammar bata gama yi ba rana ce da ɗan sauran zafi kaɗan. Hannunta yaja ɓangaren underwear. Maanal tai tsuru-tsuru kunya duk ta baibayeta. Cike da neman magana ya ce, “Anan aikinki ne ke zaki zaɓa mana Besty”. Cikin ɗan waro idanun ta ce, “Mi ɗin?”. Da ido yay mata nuni da underwear ɗin. Ai ba shiri ta juya baya tana faɗin, “Ni ALLAH ka daina min irin haka baida ƙyau”. Ɗan murmushi ya samu kansa da yi, sai kuma ya ɗan leƙa fuskarta. Da sauri taja mayafinta ta rufe fuskar. Abinm ma sai ya bashi dariya. Amma dai bai dara ɗin ba ya barta yaje yana zaɓa musu. Nashi ya fara zaɓa a ɓangaren maza. Sai kuma ya koma na matan. Dan tsabar son ƙureta parckeg na b&p ya ɗakko yazo gabanta, kamar ba daga bakinsa maganar ta fito ba ya ce, “Besty wane size?”. Ya subahannallah, mutum nan dai so yake ya kasheta kafin su bar ƙasar mutane, ai da gudu-gudu ta nema barin wajen amma ya riƙoto, hannun daya riƙetan ta kama ta ɗan ciza. Babu shiri ya saketa yana faɗin, “Ouch! Ke dai muguwa ce”. Gwalo ta masa tabar wajen. Cikin ɗan ɗaga murya kaɗan yace, “Zamu koma masauki ai zaki biya diyya yarinya”. Cak ta tsaya, shi kuma ya juya abinsa yana murmushi ya zaɓa mata wanda ya tabbatar zasu mata duk da dai ƙiyasi yayi da zuciya...... _________★ Yau RK ya kamo hanyar Abuja domin dawowa kan aikinsa. Kasancewar yana son ɗaukar Najma a Zaria ta mota ya biyo. Aiko bai ɓata lokaci a Zaria ɗin ba dan itama Najma ɗin a shirye take tsaf shi kawai take jira. Alhamdullah ƙarfe biyar a ƙofar gidan su AA tai musu. Lokacin da motar RK ke shigowa babban harabar gidan Saheeba da Nuratu da Mamy na zaune suna shan iska. Sai su Naufal dake yawo a motocinsu ƙanana shi da Anum. Oum bata nan tana maƙota gidan Hajiya Shuwa. Dan tunda ta dawo bata shiga ba sai yau. Nibras da babban yaya da Fawzan kam basu dawo aiki ba. RK na kallon irin kallon ƙurullar da suke bin motar tashi da shi, dan basu santa ba sabuwa ce dal daya ɓare saboda angwanci. Tinted glass ne shiyyasa basa iya ganin kowaye. Najma ce ta fara buɗewa ta fita, cike da ɗoki ta ƙwala kiran sunan Naufal da Anum. Atare yaran suka juyo motocin nasu kowa na rige-rigen isowa saboda ganin Aunty Najman Zaria. Suna isowa kowa ya fito suka rungumeta. RK na fitowa sukai arba da shi suka saketa sukai kansa, gaba ɗayansu ya ɗaga a tare yana dariya. Dai-dai nan motar Fawzan ta shigo gidan, kamar haɗin baki babban Yaya biye da shi. Sai a lokacin Saheeba da Nuratu suka taso suna faman taɓe baki dan Mamy ce tace suje kar ace basu tarbesu ba. Wani sassanyan kallo Najma da Fawzan sukama juna, duk da kuwa tare yake da Nibras a motar. Koda suka fito cikin ƴar basarwa ya ɗaga Anum dake masa oyoyo yana kallon Najma ƙasa-ƙasa yace, “Ba gaisuwa love?”. Da sauri ta kalla gefensu tana fatan kada wani yaji, sai taga hankalin kowa nakan Uncle Rafeeq. Maimakon ta fara gaida Fawzan sai ta fara gaishe da babban yaya. Cike da kulawa da ƙauna irin na ƴan uwantaka da aka san duk wani jinin Darma da ita yake amsa mata yana tambayar Mamanta da sauran ƙannenta. Ta ce, “Duk kowa lafiya yake suna gaishe ku yaya”. “Muna amsawa. Amma nan za'a mana azumi ba?”. Kanta ta jinjina masa tana murmushi. Shima murmushin yayi da sanya mata albarka, sannan ya maida hankalinsa ga RK da suke gaisawa da Fawzan. Itama sai lokacin Najma ɗin ta gaida Fawzan ɗin. Amsa mata yay normal kamar yanda ya saba a baya. Ta juya ta gaida Saheeba. Tasan Nuratu, sai dai basa shiri, dan Nuratu fa ita bata cika zaman lafiya da mutane ba musamman idan ta fahimci ka fita to in sha ALLAHU kai ka zama abokin gabarta. Ƙin gaida Nuratun tayi ta juya ga gaida Nibras. A daƙile ta amsa mata, wannan ita kuma halinta ne, dan haka Najma bata kawo komai a ranta ba. Inda Mamy ke zaune suka nufa, fuskar RK da murmushi yake gaisheta, yayinda Najma taje ta rungumeta tana faɗin, “Oyoyo Hajiya Mamyn mu”. Da ƙyar Mamy ta haɗiye abinda ta tokare mata zuciya, dan ranta a ɓace yake tun tafiyar su AA ta jiya. Gashi har yanzu basu kirasu ba balle ta tusa masa gargaɗin dake a ranta. Sun gaisa cike da mutunta juna ita da RK, kafin ta maida hankali akan Najma. A kuma lokacin ne Oum ke shigowa gidan. Wayyo tuni Najma ta saki Mamy ta sheƙa da gudu ita da su Naufal wajen Oum ɗin. Suma su Babban Yaya da Fawzan da RK ɗin duk wajen Oum ɗin sukayi. Haka suke mata ko yaya ta fita data dawo duk su zagayeta kamar wasu yara. Da mamaki Oum dake shafa kan Najma tana rungume dasu Naufal tace, “Lallai yau ango ne a Abuja? Ai mun zata kayi ƙaura ka koma Kano”. Dariya RK yayi da faɗin, “Dafa za'ace nai hakan ai da kun min gata Aunty”. Dariya Babban Yaya da Fawzan suka sanya, yayinda Oum ta riƙe baki. Babban Yaya yace, “Uncle ai babu damuwa barinka zamuyi ka koma abinka”. RK yace, “Yauwa Son kuyi taimako, ni dama za'a saya min ticket zuwa bayan isha'i ina Kanon dabo abina ai da yafi”. Da wannan dariya suka shige sashen Oum. Bayan su Mamy sun mata sannu da dawowa. Sai dai su basu bisu ba, sai ma takaici ne daya saka Mamyn wucewa sashenta tabar Nuratu da Saheeba anan suna gulma. Nibras kuwa tayi sashensu dan yanzu ba zuwa sashen Oum ɗin take ba tunda su AA suka bar ƙasar..... Najma na baza idon son ganin Maanal Oum ta sanar mata ai basa ƙasar, jiya suka wuce Chaina amma kwana goma zasuyi zuwa sati biyu su dawo. Sam Najma bata so hakan ba. Amma ta musu addu'ar dawowa lafiya. Shi ko RK dariya yay da faɗin, “Ɗanki ya samu lafiya dai, harda tafiya honeymoon”. Itama dariyar tayi, ta ce, “Aiki fa sukaje Rafeeq. Honeymoon ɗin nan ko za'aje shi sai dai bayan salla in sha ALLAHU. Ni nazata da Nuwaira zaku taho nan ɗin”. “Wlhy naso hakan Mah-mah ce ta hana, wai na bar mata yarinyarta sai bayan salla tunda bata jin daɗi”. Oum tace ALLAH ya bata lafiya. Fawzan cike da tsokana yace, “ALLAH ya raba lafiya Uncle”. Filo RK ya ɗauka ya jefa ma Fawzan, ya miƙe ya fice yana dariya. Shima RK da Babban Yaya miƙewa sukai suna dariyar suka fita dan lokacin sallah yayi. Oum dai nata murmushi, dan ita kanta da RK ɗin yace Nuwaira bata jin daɗin abinda zuciyarta ta kawo mata kenan har an samu ciki. Addu'a tai musu tare da miƙewa ita da Najma sukai ciki domin yin sallar magrib tana addu'ar ALLAH ya kaita randa zataga na AA da Fawzan haka.. Bayan sallar isha'i sukai zaman cin abinci, anata hira cike da farin ciki dan harda Abah duk da a sashen Mamy yake yau. Amma ganin ɗan uwansa yace anan zaici abinci shima. Saheeba da Nuratu dai suna sashen Saheeba ɗin sun ƙulle suna tsogume-tsogume, dan tunda AA ya wuce ko sashen Mamyn ma Nuratu ba son zama take ba, koda yaushe tana nane da ƴar uwarta ne. Itako Nibras tana sashenta, abin duniya ya isheta. Tun juya take dakon jiran jin AA ya kira waya amma shiru kake ji. Har gwada number sa da yake amfani da shi in yaje Chaina ɗin tayi amma bata shiga ba. Dama ta sata ne a wayar Fawzan, ta adana da wata ɓoyayyar number ɗinta data tanada dan AA amma tunda ta sai layin ta kasa kiransa balle masa ko text ne saboda tsoro. Ana cikin hirar Fawzan da Najma suka saci jiki kitchen kamar masu tattare kaya, anan sukai ɗan sabuwar gaisuwa da hira sama-sama. Gudun kada a gane su suka dawo. Shi dai RK ma dariya suke bashi, dan yanzu kam ya sake tabbatar da abinda yake hasashen..........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖3️⃣3️⃣ ______________ ......Sai da AA ya tabbatar ya tura dukkan siyayyar tasu masaukinsu sannan. Maimakon wucewa gida wani garden ya kaita. Wajen ya matuƙar birge Maanal. Anan sukai salloli suka huta har zuwa duhun dare kafin suka fito. Ganin yanda take naɗe hannaye a gyale saboda sanyi ya sashi cire jacket ɗinsa. Gabanta ya dawo ya tsaya, hakan yasata ɗago idanunta ta kallesa. Shima kallon nata yake. Cikin sanyin murya idanunsa a cikin nata ya ce, “Sanyi?”. Kanta ta jinjina masa tana ɗan lumshe nata idanun dan bazata iya jurar kallon nan nasa ba. Shima nasan ya lumshe ya kuma buɗe a hankali. Sai kuma ya dafa kafaɗarta ya matsota jikinsa sosai. Harta gama sallamawa rungumeta zai yi sai taji saɓanin hakan. Jacket ɗin tashi ya rufo mata ta baya, sannan ya ɗan matsa ya gyara mata ita a kafaɗinta sai ta rufeta ruf. Ajiyar zuciya ta sauke a hankali, sai kuma ta ɗan kallesa ta kauda idanun ta ce, “Kaifa? Riganka fa baida wani kauri”. “Karki damu bana jin sanyi”. Ya faɗa ƙasa-ƙasa yana kama hannunta suka cigaba da tafiya. Yanzun ma a ƙafa suka nufi hanyar gida, yasan ta gaji, amma gara suyi hakan dan in sun kwanta su samu damar yin barci da ƙyau. Sosai birnin Shanghai ya ƙara burge Maanal. Tana mamaki da jinjina fasahar mutanen nan wajen iya tsara gine-gine dogayen gaske. Ga wutar lantarki da ba'a maganar ɗaukewarta ma. Akan titi fa suke amma haske tako ina abin zabbirgewa. Suna isowa hotel ɗinsu taji zuciyarta ta fara rawa. Amma sai ta dake tana mai roƙon UBANGIJI hana tabbatuwar abinda take ma tsoron. Sosai tayi mamakin ganin dukkan shopping ɗinsu a ƙofar ɗakinsu. Card ɗin ƙofar yasa ya buɗe, kafin yakai duƙe ya ɗiba kayan duka ya shiga da su, ita kuma tabi bayansa. A hankali ta zare rigar tasa daga jikinta kamar bata so, dan wani irin nutsuwa da sanyin zuciya ƙamshinsa ke sakata. Zama tayi akan kujera, shi kuma ya shiga ƙoƙarin rage kayan jikinsa. Sai kawai ta duƙar da kai ƙasa. Yana lure da ita, sai dai baice komai ba ya gama ya wuce bayi. Ya ɗan jima kafin ya fito, nan ma bata kallesa ba. Tadai fahimci wanka yayo kodan mayataccen ƙamshin shower gel daya cika ɗakin. Shi ko hankalinsa kwance yay shirin barcinsa da ɗaya daga cikin kayan da sukai shopping dan harda na barci. Cike da godiyar UBANGIJI yakai zaune a bakin gadon yana ɓalle murfin robar ruwa yakai bakinsa. Sai da yasha kusan rabi sannan ya dubi Maanal dake zaune kamar wata marainiya. Kansa ya ɗan girgiza, kafin ya ajiye ruwan babu wasa a muryarsa ya ce, “A zaune zaki kwana kenan?”. Kanta ta girgiza, sai kuma ta mike batare data kalla inda yake ba. Wajen kayan shopping ɗin nasu ta nufa, tunda a gabanta ya ɗauka kayan barcin, a kayansu kuma ɗazun taga bai ɗakko mata nataba dan iya kaya kawai ya zubo mata kala shida. Sai b&p ɗinta ƙwara ɗaɗɗaya datai amfani da su ɗin nan da zasu fita. Cike da nuƙu-nuƙu ta ɗauka duk abinda take buƙata, ta wuce bayin sum-sum kamar za'ace ar ta fece. Shi dai ta ƙasan ido kawai yake kallonta, a ransa ko dariya yake da mamakin mutuwar bakin tsiwa. Ta jima a bayin dan shi har ma barci ya ɗaukesa sannan ta fito, dama kuma tayi zamanta ne dan har yay barcin. Daɗi kuwa taji sosai maganin yayi ɗin, kayan data cire ɗin ta ajiye, sannan ta zare ribbon ɗin kanta ta tifke gashin, veil ɗinta na abaya ta ɗauka ta ɗaura a kan, sannan ta juya tana kallon ɗakin. Bayan gadon babu wani abu da zata iya kwantawa akai, dan su kansu kujerun bazasuyi wani daɗin kwanciya ba. Sai dai carpet ɗin dake a ƙasa. Shi kuma tana tsoron sanyi, dole dai yau ko taƙi ko taso a gado ɗaya zasu kwanta kenan. Karan farko ta ɗan kai dubanta a gadon. Ba wani babba bane can, kamar dai 6-by-6, yanda ya kwanta a gefe ta sake fahimtar ya bar mata ɗayan wajen ne ta kwanta. Batace komai ba cike da kasalar jiki data gaɓɓai ta nufi gadon, kamar mai ɗofanuwa akan wuta ta zauna kaɗan a baki-baki, sai kuma ta zubama bayansa daya juya mata ido, shima dai wando ne da riga a jikin nasa masu taushi kalar blue. Sun masa ƙyau, sai ƙamshin turarensa ke bugunta. Numfashi ta sauke ƙasa-ƙasa, sai kuma takai hannu tana jawo pillows ɗin gadon dake da yawa ta shiga jerawa a tsakkiyarsu. Ɗaya daya rage ta ajiye shi saitin ƙafafunsa sannan ta kwanta suka kasance a kwanciyar kai da ƙafa kenan. Duvet ɗin ta ɗan ɗaga ta shiga ciki, ta lulluɓe har zuwa wuyanta saɓanin shi da iya ƙafafu kawai ya rufa. A haka tai addu'ar barci, tun zuciyarta na ɗar-ɗar har barcin dai na gaske yay awan gaba da ita. Zuwa can AA ya juya, yana kai hannunsa zai gyara duvet yaji ya tokari abu, idanun nasa ya buɗe dake cike da barci, ya ɗan zubama pillows ɗin data jera ido, sai ita kuma dake can ƙarshen gado kamar zata faɗa, dan ya tabbatar in har tai ƙwaƙwƙwaran juyi babu abinda zai hanata wantsalawa ƙasan. Kansa kawai ya ɗan girgiza, a ransa yana faɗin (yarinya idan nayi niyyar yin wani abu ba pillows ba ko block kika jera ai sai nayi) ya taɓe baki tare da maida idanunsa ya lumshe....... _________★ GIRO A fusace ta bankaɗe labulen ɗakinta ta fito har zanen jikinta na neman taɗeta, shi kuma ya nema kwancewa a jikin nata tai saurin yayumoshi ta soke. Cikin rawar murya data jiki ta ce, “Sailuba uban waye ya shigar min ɗakin yanzu dana fita?”. Da farko kamar Sailuba batama jita ba, tanata tankaɗen garin tuwo da zata ɗora, sai da ta shaƙi iska dan kanta ta ce, “To Gwaggo nikam ina zan sani, nima yanzu nake dawowa sashen ina ɓangaren su Zainaba ina jiran Audu ya kawo min niƙa, wani abu akai miki a ɗakin ne?”. A harzuƙe Gwaggo tace, “In ba wani abu akai min ba zakiga na fito ina tambaya ne. To wlhy bazan yarda ba, yanzu ƴan sauran kuɗin nan da suka rage mana ƙarshe da za'ai noma akeje aka lalube, kuma kema kin san ɗayan biyu ne, a cikin ƴaƴanki ko Haƙilah ko Sule, tunda ALLAH ya basu dogon hannu da bai iya zama waje guda sai sunyi ƴan ɗauke-ɗauke......” “A'a Gwaggo ya zakice haka, naga ɗauke-ɗauken nan kowa ya samu dama yi yake yi, sannan yaran wasu sashen ma bazasu iya zuwa su ɗauka bane. To Haƙilah ma bata kwana a gidan nan ba tana gidanmu ne balle ace itace, shi ko Sule tun safe yace min zai tafi Suru sayen kayan sana'arsa.....” “Siyen kayan sana'a ko sayen kayan shaye-shaye da yake koyama ƴaƴan mutane. Tunda kince basa nan sai ke ki fito da kuɗin tunda kema in kika faki ido ɗauke-ɗauken kikeyi shiyyasa gashi nan duk kin tsiyata min yaro. Lokacin da Habibu ke tare da Asiya arziƙi har zuba yake, amma ke da yake mai farar ƙafa ce bayan talauci da kika saka masa harda ciwo..” Cikin matuƙar ɓacin rai Sailuba ta miƙe tana nuna Gwaggo. “K! Tsohuwar banza ya isheki, kodan kinga kwana biyu na ɗaga miki ƙafa ne a gidan nan shiyyasa kike tunanin dawo da tujarar taki. To bari kiji Sailu na nan da kika sani ban canja ba. Kuɗinki ɗin banza da zanje na ɗauka, kuɗin ma da wani ne ya bayar ba guminki ba, sai dai idan ɗan naki ne ya ɗauka ko shi Baban tunda shima ɗan hauma-haumar ne ai”. Kafin kace mi rigima ta kacame tsakanin Gwaggo da surukarta Sailu. Hakan ba sabon abu bane a gidan, dan sau karo biyu Sailu na lakaɗawa Gwaggo duka. Ƴaƴanta kuwa idan kaji zagin ƙare dangi da sukema Gwaggo bazaka taɓa yarda kakarsu data haifi ubansu bace ba. Sosai sashen ya cika da matan gidan, maƙota ma na leƙe ta katanga. Abin zai baka mamaki yanda kowa Sailu kawai yake bawa haƙuri, duk da kuwa zagin da take surfama Gwaggo a gaban kowa. Kuka Gwaggon ta sanya yuuu-yuuu tana rantsuwar yau sai Habibu ya saki Sailu a gidan, idan ba haka ba sai ta tsine masa. Sailu dake ɗura mata zagi ta ce, “A hayye nanaye koba saki ba. To maza sakashi ya sake nin kiga idan zai iya. Ko an gaya miki ni Asiya ce kukarki mai daɗin hawa. Iyayenta sun muku bauta sun gina ɗanki kunci amanar zuminci, to wlhy Talle ni nafi ƙarfinki, ke wanda ma ya fiki nafi ƙarfinsa. Tsohuwar banza da bata iya komai ba sai sa ido, ɗanki na kwanciyar aure dani kina leƙenmu ta taga saboda ke kwartuwa ce....” Ai gaba ɗaya gida ya ɗauki salati da sallalami, yayinda Gwaggo ta fashe da kuka tana rantsuwa sharri Sailu take mata. Amma ina kowa yaƙi saurarenta sai aibantata akeyi akan wannan al'amari, saboda kowa dai ya tabbatar Gwaggo zatayi abinda yafi hakan. Ana cikin hakan wani matashi ya shigo, agaba ɗaya shekarunsa basu wuce goma sha ba. Amma abin tausayi da mamaki a kallo ɗaya zaka gane shaye-shaye ya gama kassara rayuwarsa. Ga raunuka a jikinsa na tabbacin wuƙace da sauransu. Sule kenan, da ake kira da AUTAN MASHAYA a garin na giro. Wasu kuma suke ƘARAMINSU BABBANSU. Dan kuwa Sule hatsabibin yaro ne na gaske, baya ji ƙwarai da gaske, ga sata ko ɓera albarka, dan duk iya tattalinka da kayanka idan Autan mashaya ya ƙyalla ido a kansu sun zama ba naka ba. Baya tsoron kowa a garin baya shakkar kowa. Idan ma ka cika takura masa koda da kallo ne kaɗan daga aikinsa ya maka zanen yarbawa a fuska koya tsiyayar maka da idanun. A ƙarancin shekarun nan nasa ƙaramin dila ne na kayan shaye-shaye anan cikin ƙauyen har ma da ƙauyukan kusa da su, babban tashin hankalin da ƴan garin suke ciki yanzu yanda yake koyama yaransu ƙanana masu tasowa shaye-shaye, a yanzu haka bawai ya gama kaiwa cikakkun shekarun balaga bane, amma yasan yanda zai tarfa mata a lungu ya mammatse koda kuwa matan aure ne, kai koda tsoffi ne. Dan ita kanta Gwaggon ya taɓa matseta a cikin ɗaki wataran taita ihu tana neman taimako, kafin wani ya shigo ya ware ta taga, daya faɗa uwarsa ta ƙaryata. “Wai lafiya naga an tarar mana a part ɗinmu ne?, kufa wannan zuri'ar na fahimci kun fara zama ƴan tsugudidi”. Sule ne ke maganar cikin yanayinsa na ƴan daba........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖3️⃣4️⃣ ______________ .......Cikin ƙanƙanin lokaci taron ya fara watsewa, dan tsoronsa kowa keji kamar mutuwa, tsabar makirci sai lokacin Sailu ta ɗaura hannu aka ta ƙwallara kuka. Cikin wani irin zaro idanu Sule ya ce, “Kai! Ikon wahabu, k! Tsohuwa ince dai lafiya kike irin wannan tsuwwar haka. Shin ko dai Baba ya wulla ne na fara shirya bikin fatin cin gado?”. Kukan Sailu ta sake fashewa da shi, sai kuma ta nuna Gwaggo da tun shigowar Sule tai lakur na tsoro. “Ba kakarku bace tace wai ka shiga ɗakinta ka saci kuɗi, shine ta tara mutanen gida tanata zagina, harda cewa sai ka shiga wuta kai da Haƙila da ni, wai mun zame mata jaraba babanku ya talauce sanda Asiya na tare da shi kuɗi har zuba suke a ƙasa..” “Kan uban can kai.. ke tsohuwar nan ko, to wai ma tsaya Babanmu, da take faɗar haka ita ma ai wutar zataje, bakiga fuskarta ba tafi kama data ƴan wuta. K! Wlhy Talle idan baki daina sanya mana ido a gidan nan ba sai na miki sabuwar kaciya da gatarina, shegiya mai suffar kwaɗi. Kuɗi kuma na ɗauka zan ƙara jari ne, idan kin isa ki ƙara magana ALLAH kinji na rantse ko sai na juya fuskarki daga gaba ta koma baya. Dalla shige daga ciki zanyi lissafi....” Ai da gudu Gwaggo ta afka ɗaki ta danno ƙofa, jikinta sai rawa yake kar-kar harda ɗan fitsarinta a cikin zani. A waje ko tuni sule yaja tabarma ya baje kayansa dake cikin jakar daya ratayo. Ba komai bane sai ƙwayoyi da ganyen tabar wiwi. Ko'a jikin Sailu ta koma ta zauna ta cigaba da tankaɗenta tana kallonsa. Idan ma taga wata tabar tafi wata da yake ƙullawa sai ta ce, “Waccan kamar tafi sauran yawa ɗan baba. Kodai wani ɗan ludayina ƙarami zan baka yanda zaka dinga gane gwajin?”. “Eh to kema kinzo da shawara kawo, idan naga kuɗin ya fita ribar da ɗan auki zan baki ƙulli ɗaya ki busa”. Dariya Sailu tai tana miƙewa. “A'a ɗan baba rabani da busawar nan. Wannan ai sai ku ƴan zamani, mukam tafi ƙarfin mu”. Dariya ya ƙyalƙyale da ita da faɗin, “Babanmu kefa dama tuni na fahimci kanki ƙarami ne, tun randa na baki zoɓon nan nawa da zaƙami a ciki kika baje kikaita barci har kwana uku nace tabb Babanmu fa ta bazu da yawa”. Nan ma dariyar takeyi daga ɗaki. A haka ta fiddo masa da ɗan ludayi na cikin madarar jarirai ta miƙa masa. Ya ce, “Yauwa uwa maba da mama, kinga ko gashi ɗan kif-kif abinsa. Zako kici burodi anjima da shayi da ƙwan wajen kalla”. Daɗi sosai Sailu taji, ta shiga sanya masa albarka. Duk abin nan da akeyi fa Babu na gidan, a kwance yake baida isasshen lafiya, dan ranar ma daga gona sai ɗakkosa akayi. Hawaye ne suka shiga gangaro masa, rayuwarsa da Ammie da ƴan ƴaƴansu uku ta faɗo masa a rai....... Hummmm, kowa ya tuba dan wuya ba lada😮‍💨😮‍💨🥱 ____________★ Alarm ɗin daya saita musu domin tashi sallar asuba ne ya farkar da su. Cikin kasala irin na mai barci ya buɗe idanunsa da sukai masa nauyi sosai. Fin minti biyu kafin ya yinƙura ya tashi zaune bakinsa na ambaton sunan ALLAH. Hannu ya kai ya kunna lamp dake a bed side drawer. Hasken ya bashi damar sauke idanunsa akan fuskar Maanal dake facing inda yake. Samun kansa yay da zuba mata idanun, fin mintuna biyu kafin ya matsa sosai, kishingiɗa yay akan hannunsa daya tokare kansa da shi yana facing ɗinta sosai fuskokinsu dab-da-dab dan sai da ya janye filon wajen. Yatsarsa ya kai saman tsukakkun lips ɗinta ya shiga zagayawa, yaja fin minti ɗaya yanayi kafin ta fara motsawa kaɗan-kaɗan, sai kuma idannunta suka fara rawa, da ƙyar ta shiga ɗagasu sama a hankali tana buɗewa. Da farko shaaa take iya ganinsa, sai kuma sannu a hankali idon ya washe ta ganshi da ƙyau. Cike da wani irin kasala da shauƙi ta zuba masa idanun nata da suka sake shanyewa saboda sanyi, shima dai kallon nata yake da nasa dake a raunane kamar wanda yasha kafso yay marisa. Wani irin kallo sukema juna mai kassara garkuwar jiki dana ɓargo, mai saukar da kasala da tsitstsinka jini. Illahirin gaɓoɓin jikinsu na sakewa a lokaci guda. Cikin wani irin motsa lips kaɗan ya furta, “Amarya mai rowa”. Sosai taji ƙirjinta ya buga sakamakon yin maganar tasa, babu shiri ta waro idanun gaba ɗaya domin tabbatarwa bafa a wancan yanayin bane, domin kuwa mafarkinsa take yi a like yanda yake a kusa da itan nan sai kuma gashi ɗin reality. Yanda ta waro idanun shima sai ya ɗage mata gira ɗaya sama yana mata irin kallon (Miye kike kallona ba haka bane?) ɗin nan. Hakan da yay ya sake tabbatar mata reality ɗin ne fa ba a mafarkin ba, ai da sauri tai yunƙurin juyawa zuciyarta na dumm-dumm. Hannunsa ya ɗaura akan jikinta ya taro fuskar tata ya hanata juyawa, jitai gaba ɗaya tama gama daburcewa, ga wani yanayi na saukar mata a cikin jiki. Wannan yanayin ta jima tana fuskartarsa a tare da ita musamman lokacin gabatowar asubahi har zuwa safiya. Wani lokacin takanji kamar tayi kuka saboda yanda take shiga matsuwa da son kasancewa kusa da abokin halittarta. Tsaf AA yake wani binta da kallo daki-daki, dan ya fahimci halin da take a ciki itama sarai a idanunta. Samun kansa yay da ɗan murmusawa kaɗan, sai kuma ya sake matsar da fuskar tasa gab da tata suna busama juna numfashi. Rawa jikin Maanal ya nema farawa, hakan ya bashi damar janye filon dake ta wajen cikinsu ya matsota jikinsa kawai ya rungumeta, bai wani jira maida ba'asi ba ko bata dama ya manne lips ɗinsu waje guda. Da wani kalar sanyi jiki da na yanayin asuba yake sumbatarta, yanyinda itama yanayin da take a ciki ya sata shagaltuwa ta fara ƙoƙarin miƙa masa wuya. Sai kawai yaji ya ƙara rikicewa... Tafiya tayi tafiya ya fara ƙoƙarin kai hari wani sashin daban, a lokacin ne ta nema dawowa a hanyyacinta, sai dai duk yanda taso janye jikinta hakan ya gagara. Kanta ta shiga girgiza masa tana ƙoƙarin ture masa hannu, sai ga hawaye sharrr-sharrr na sauka har a fuskarsa. Jikinta kuwa rawa yake na tsoro, dan brain ɗinta ƙoƙarin dawo mata da wani abu daya shuɗe a shekarun baya take yi. Sosai yanzu ta fara kicin-kici, a wannan yanayin ta buge masa ƙasan ciki da gwiwar ƙafarta batare da ta fargaba itama, dan da gaske AA tunaninsa yayi nisa da duniyar da take ciki. Babu shiri kuwa ya saketa, saboda wata azaba data ratsa masa jiki har zuwa tsakkiyar ƙwaƙwalwa. Jikinsa ya dunƙule a waje ɗaya ya riƙe cikin da duka hannaye biyu ya rumtse ido da matuƙar karfi. Dan tabbas badan ya kasance jarumin gaske ba babu abinda zai hana ya fasa ihu. Amma ina jikinsa ne kawai ke ɗanyi kamar yana rawa... Maanal kam data samu ta kuɓuta tsoro ne ya sakata direwa a gadon, cikin sauri ta wuce bayi. Tana maida ƙofar ta rufe ta jingina a jiki jikinta na karkarwar tsoro hawaye na bin fuskarta. Ji take kamar zai biyota, dan bata taɓa ganin AA a irin wannan mugun yanayin ba, tru-tru fa ya fita a yaccinsa ƙoƙarin isa inda zuciyarsa ke raya masa kawai yake yi. Ina bata shirya hakan ba, wlhy bata shirya ba, da gaske tsoro take ji, matuƙar tsoro. Duk yanda jikinta ke nuna mata buƙatuwa da irin wannan yanayin ko'a film in tana kallo taga kiss ya fara wuce na hankali sai kaga jikinta ya fara rawa tsoro ya kamata, dan wancan abun daya faru a waccan ranar ne yake dinga dawo mata, wani lokacin sai take jin ma kamar zata suma dan tsoro. Shiyyasa bata iya sakin jiki ta kalla film ɗin turawa musamman na soyayya. Gara na faɗa yafi bata kwanciyar hankali. Kai ko'a karance-larance novels ɗinta bata taɓa karanta irin wannan wajejen. Idan kuma ta fahimci book yayi shaiɗanci da yawa gara ta haƙura dan English novels ba komai zaka samu ana ɓoye ba... Ita kanta bata san adadin lokacin data ɗauka a wajen ba, dan ƙafafunta har sun fara sagewa. Sauran guntun hawayenta ta share, kafin cikin ƙarfin hali ta ƙarasa shigewa bayin. Dole cikin gilashin da ake wanka ta shiga, ta sakarma kanta ruwa kawai batare data iya cire kayan barcin ba. Ratsatan da ruwan keyi yasa ta fara sakin ajiyar zuciya a jajjere, wani irin tausayin duk yarinyar da akama fyaɗe na sake raunana mata zuciya, dan wanda ya fuskanci ƙalubalen kawai yasan mi ake ji koda gwada yimasa akai ba'ayi ba kuwa. Ta jima ruwan na dukanta, sai da taji nutsuwa matuƙa sannan tai wanka sosai ta kuma tsarkake jikinta dan dole tai hakan, bathrobe ta ɗauka ta sanya, ta ɗaure igiyar da ƙyau, taji daɗin yanda ya saukar mata ƙasa sosai. Sai kuma taja towel ta naɗe kanta sannan ta fito a ɗakin cikin ɗari-ɗarin zuciya. Sai da ta ɗan kalla cikin ɗakin taga babu alamar shi sannan ta fito gaba ɗaya, tayi ta wajen gado kaɗan dan ɗaukar kaya ta koma bayin ta sanya a mamakinta sai ta gansa duƙunƙune a yanda ya barsa, gashi babu alamar ma yana motsi. Gabata ne ya faɗi, cikin tsoro-tsoro ta shiga matsawa da sanɗa, har tazo jikin gadon bai motsa ba, ta ɗan duƙo ta leƙa fuskarsa, idanunsa a kulle suke, kuma sai taga kamar baya numfashi da gaske. Kamar mai tsoron taɓa wani mugun abu haka takai yatsarta saitin hancinsa a slowly. Tai ɗan jimm tana saurare, sai taji da gaske fa baya numfashi sam. “Na shiga uku ni Maanal”. Ta faɗa a gigice tana hayewa a gadon. Tsabar yanda jikinta ke rawa bama tasan ta kamo kansa ta ɗaura a cinyarta ba, ta riƙe fuskar da tafukan hannayenta biyu tana girgiza shi da kiran sunansa. “AA! Besty! AA! Ajwaad! Ajwaad!! Na shiga uku ni Maanal Ajwaad please ka tashi, miya faru? Ajwaad dan ALLAH ka taimakeni ka tashi”. Ina, AA baima san tanayi ba. Wani irin kuka ta saki ta kife kanta tanayi akan tashi fuskar.........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖3️⃣5️⃣ ______________ .........Hawayenta da damshin ruwan jikinta na wanka suka shiga sauka masa akan fuska. A hankali cikin ikon ALLAH ya shiga motsawa, sai kuma numfashinsa ya fisga alamar farfaɗowa. A yanda ya fisgi nunfashin ne ya sakata ɗagowa da sauri. Ga hawaye na cigaba da tarara akan fuskarta. Idanunsa ya ɗaga da ƙyar ya kalleta, ya zuba mata su kamar mai son ganeta, sai dai kuma kukan nata ne ke wani kalar tsinka masa zuciya, tausayinta yake ji matuƙa. “Dan ALLAH kayi haƙuri”. Ta faɗa hawaye na sake ɓalle mata. Duk da azabar da yake ji a nashi jikin dan kawai ta kwantar da hankalinta sai ya saki mata wani sassanyan murmushi yana ɗan lumshe idanunsa da sake buɗewa a lokaci guda. Cike da dauriya da jarumta ya motsa lips ɗinsa a hakali. “Taimaka min na tashi”. Kanta ta shiga jinjina masa tana share hawayen dake cigaba da gangaro mata. Duk da ya mata matuƙar nauyi da ƙyar ta iya kamashin ya haɗa da nasa ƙarfin halin ya tashi zaune. Yasan bazai iya zama a wannan halin ba, sannan kuma bazai iya cigaba da kwanciya baiyi salla ba, dan tabbas AA mutum ne mai kiyaye ibadarsa, duk runtsu bai yarda yin wasa da lokacin salla ba. Sannan ita kanta baya son cigaba da ɗaga mata hankali. Wannan wani irin yanayi ne daya ɗauka tsahon shekaru a cikinsa, haka kuma zakaga ya gama jigatarsa batare da kowa ya sani ba har ALLAH yasa ya samu sauƙi ya miƙe. Har gara ma sau biyu Fawzan ya taɓa riskarsa a halin, yayta masa faɗa tare da bashi taimako, daga nan ya sake kasancewa a takatsantsan ɗin kiyayewar hana kowa sanin a halin da yake ciki, kawai yayi imanin komai yana da lokacinsa, kowa kuma da irin jarabawarsa.. Duk da bawani iya riƙesan da ƙyau Maanal tai ba saboda ya mata nauyi haka ta lallaɓa sukaje har zuwa bayi ko miƙewa da ƙyau bai iyayi. Suna isa ƙofa ya dafe bango yace taje tai sallarta zai iya. Hawaye ta sake sharewa, ta juya kanta a ƙasa. Binta yay da kallo, sai kuma ƙasa-ƙasa ya furta, “Kina da alwala ko?”. Tsayawa tai cak, sai kuma ta jinjina masa kanta batare da ta juyo ba. Dan hawaye ne ke ta gudu sosai a fiskarta, saboda sarai ta fahimci minene matsalarsa. Ita kuma harga ALLAH tana jin tsoro, matuƙar tsoro ta yanda bata san ya zata iya miƙa wuya domin taimaka masa ba. Dan tasan hakan ne kawai samun lafiyarsa yanda ya kamata. Har ta kimtsa tai sallar asuba bai fito ba, tashi tai taje ƙofar bayin, tai shiru tana tunanin yanda zatayi, sai kuma ta kai hannu da niyyar ƙwanƙwasawa dai-dai nan ƙofar ta zuge ya bayyana. Baya ta ɗan ja kaɗan, ta sauke kanta ƙasa ganin daga shi sai towel, sai wani ƙarami dake a hannunsa. Sosai ya zuba mata idanunsa, sai kuma ya janye a hankali ya ƙarasa fitowa a ɗan duƙe dan bai iya miƙewa da ƙyau. Da ƙyar ya iya kaiwa cikin sofa yana cigaba da naɗe ruwan kansa batare daya sake kallonta ba ya ce, “Bani dogon riga”. Da sauri ta nufi akwatinsu, dan anan taga jallabiyu har biyu daya sanyo, ta ɗakko ta saman kawai ta iso inda yake. Amsa yay ya sanya kafin ya kunce towel ɗin a zaunen sannan ya miƙe. Kamar dai a yanda ya zauna a haka ya lallaɓa kan sallayar datai salla yayi shima. Tana zaune a bakin gado tana kallonsa cike da damuwa, hawaye kam har yanzu lokaci-lokaci sharesu takeyi. Yana idarwa baima iya yayi ko azkar ba ya lallaɓa ya dawo saman gadon ya kwanta, a waje guda ya dunƙule kamar ɗazun, kafin a hankali ya kalla Maanal dake kallonsa. Murya a shaƙe ya ce, “Zoki kwanta mana”. Kanta ta girgiza masa. Sai ya lumshe idanu ya sake buɗewa. Muryarsa na sake komawa can ciki ya ce, “Miyasa?”. Tata muryar na rawa ta ce, “Ban jin barci”. “Zoki tayani to”. Yay maganar da ƙyar yanzu kam. Kallonsa tayi, ganin haka ya sashi basarwa. Itama sai a hankalin takai kwance nesa da shi, sai dai suna facing juna sannan yanzu ba kai da ƙafa ta kwanta ba. Idanu kuwa suka zubama juna, tsahon lokaci kafin sannu a hankali nasa su lumshe, itama tun tana kallonsa har barcin ta kwasheta. Batayi wani barcin kirki ba ta farka, dan mafarki tai AA ɗin a cikin mummunan yanayi. A zabure kuwa ta tashi, sai idannunta suka sauka a kansa. Yanda ya sake dunƙule jikinsa waje guda ya sake tabbatar mata da mafarkinta. Jikinta har rawa yake ta matsa kusa da shi, tana kai hannu kansa taji wani irin masifaffen zafin da har sai da ta rumtse idannunta da ƙarfi.. gaba ɗaya sai taji tama rikice, ita ko ina zata kama a ƙasar mutane, gashi bata san inda sauran abokan tafiyarsu suke ba. Dabarar kiran wayar hotel ɗin ce tazo mata, duk da bata jin yarensu sai tai tunanin yin turanci. Haka kuwa akayi, ta sanar musu tana buƙatar wani a ɗakin da suke ta faɗi number ɗakin, bata jira amsa ba ta yanke wayar saboda yanda taga AA na yamutsa fuska da sake dunƙule jikinsa. ALLAH ko ya taimaketa sai gashi anzo anyi knocking ƙofar, babu shiri ta miƙe tana gyara veil ɗinta taje ta buɗe. Ma'aikacinsu ne namiji, bayan sun gaisa ta sanar masa mijinta ne baida lafiya ko suna da doctor dazai duba shi?. Da sauri ya ƙarasa shigowa ɗakin ganin yanda take magana a ruɗe, yana ganin a yanayin da AA ɗin yake ciki bai wani sake tambayarta ba'asi ba ya zaro waya a jikinsa yay kira. A mamakinta ko minti biyar ba'a cika ba wasu suka shigo sanye da kayan asibiti da ɗan abun ɗaukar mara lafiya. Gaba ɗaya suka ɗaga AA zuwa kan abun, shi kuma ma'aikacin yace ta ɗakko jacket ta taho dan akwai sanyi yauvkaɗan gashi safiya ce. Tashi ta jiya kawai ta yayuma ta biyo su, a tare suka shiga elevator, minti ɗaya da sakanni ta kawosu ƙasa harabar hotel ɗin, amamakinta ambulance ma na jiransu. Ciki aka saka AA itama akace ta shiga, sai ma'aikatan asibitin. Shi kuma ma'aikacin hotel ɗin da driver na gaba. Cikin sharara gudu na masifa suka iso wani ƙaton gini, da yarensu akai rubutu dan haka Maanal bata fahimci komai ba, amma dai ta tabbatar asibiti ne dan ga ambulance nan da yawa tako ina. Bata da lokacin tunani dan fitowa sukai aka shiga da AA ciki. Sai faman share hawaye take, ma'aikacin hotel ɗin nan na lallashinta da turancinsa mai fita da harshen Chaines. Sunyi zama yakai na mintuna talatin kafin cikin ma'aikatan asibitin wani ya fito. Da Chaines yayma ma'aikacin hotel ɗin magana, sai shi kuma ya juya yana kallon Maanal da turanci yace ga matarsa nan. Kallon Maanal ma'aikacin yayi, shima da turancin ya bata takardar hannunsa yace tai signing. Bata san mi aka rubuta ba tunda Chaines ne a jiki, dan haka tai tambayar ta miye? Dan bata iya yaren ba. Su duka biyun sun fahimci tasan abinda take yi, dan haka ma'aikacin hotel ɗin ya amsa ya ciro wayarsa yayma takardar hoto, miƙa mata wayar yayi ya nuna mata inda zatai translate ya koma mata da duk yaren da take so. Godiya tai masa tayi duk yanda ya nuna mata, sai ko gashi ya koma mata da turanci. Sai da ta kammala karantawa ta fahimci komai sannan ta amsa pen tai signing ɗin ma'aikacin ya koma ciki. Bayan kamar mintina ashirin ya sake fitowa yace zata iya shiga wajensa. Wata nannauyan ajiyar zuciya ta sauke tare da masa godiya. Ma'aikacin hotel ɗin yace mata zai koma bakin aikinsa shima. Idan suna buƙatarsa tai magana ga ma'aikatan asibitin zasu kira hotel ɗinsu zai zo. Godiya tai masa sosai shima sannan ta nufi ciki shi kuma ya juya ya tafi..... ___________★ Siyayya ce sosai yayo ta azumi, sai dai samun gidan shiru ya fahimtar da shi matar gidan barci take yi. Bai tasheta ba dan yasan wahalar data sha a hannunsa daren jiya. Sai kawai ya shigar da komai kitchen ya juya ya fita, dan yana son zuwa ya amso nama da kifi na gidansu da ya sayama iyayensa na azumi kamar yanda yay musu siyayya da kuma nasu na nan gidan. Kusan awa ɗaya da rabi ya sake ɗauka sannan ya dawo. Mamaki ya kamashi ganin har yanzu bata tashin ba kuwa. Ledojin hannunsa ya kai kitchen, sai kuma ya nufi ɗakin barcinsu. Barcin kuwa take a ƙasan tils, yay ɗin jim yana kallonta, kafin ya matsa ya ɗan taɓata yana kiran sunanta. “Huznah! K Huznah!!”. Motsawa tai, tare da buɗe ido sai kuma tai miƙa tana kallonsa. Zaram ta miƙe kamar wadda ta tsorata da ganinsa, sarai ya fahimceta amma sai ya fuske. Cike da kulawa yace, “Wannan wane irin barci ne? Da alama ma ko girki baki yi ba ko?”. Fuska ta ɗan yamutsa sai kuma ta jinjina kai alamar eh. “Okay, ki tashi kiyi salla ga nama can na kawo da kayayyaki ki adana su. Ni naje massallaci zan taho mana da abinda zamuci”. Bai jira amsarta ba ya fice. Da kallo ta bisa, sai kuma hawaye sharrr suka shiga rige-rigen sakko mata. Wlhy bata son mutumin nan, ko kallon fuskarsa bata sanyi. Tasan in har AA na wannan duniyar bazata taɓa son kowa ba. Ita kaɗai tasan a irin ƙuncin zuciyar da take kwana, ga Sageer ya maidata kamar jaka. Sam baya raga mata, safe da dare wani lokacin har da rana idan ya dawo gidan sai ya nemeta. In ma ta masa gardama ya murɗeta yay abinda zai yi ya ƙara gaba. Ya kwace mata waya ta rasa ta ina zataji Umminta, ta ina zataji labarin AA a bakin Sille. Ji take kamar ta kashe Sageer ta hutama ranta. Sanin halinsa na tasan inya dawo baiga ta yi abinda yace ba yasa ta miƙe. Sam bata jin daɗi, kwanciyar ƙasan tils ɗin nan ce kawai ke mata daɗi, kuma babu inda ke mata ciwo a jikinta. Wanka ta farayi tai salla. Sannan ta nufi kitchen ɗin, ta jima tana kallon kayan daya jibge mata kafin ta fara ɗaukewa cikin ɓacin rai zuwa store ɗinsu. Sannan tazo ta buɗe ledar naman. Rasama yaya zatai da shi tayi, dan aikin nan dai ba sabawa tai da yi ba a gida sai masu aiki, a yanzu ma sakata gaban da Sageer ɗin yayi ne aka ɗan samu canji. Ledan kifin itama ta buɗe, ai kamar jira ƙarnin na bugar hancinta ta wani rikice, a guje ta buɗe ƙofar baya ta fita ta fara sharara amai a ciki filawoyin wajen. Sageer dake shigowa ciki kakarin aman nata ya sashi nufo bayan cike da mamaki. Shi sai ma ya tsaya kawai yana kallonta. Sai da ta gama tai lagab a ƙasa sannan ya ƙaraso wajen, da yake akwai rijiya ata bayan ruwa ya jawo ya zuba a boket dake ajiye ya kawo mata yana mata sannu. Kanta ta jinjina masa ta ɗauka ruwan ta wanke bakinta da fiskarta, ta zuba akan filawoyin data ɓata sannan ta miƙe da ƙyar. Taimaka mata yay suka shiga, suna shiga kitchen ɗin tasa hannu ta toshe hancinta. Kitchen ɗin yabi da kallo, sai kuma baice komai ba ya shige da ita cikin falo. A kujera ta zaunar da ita, sai dai bata iya zama ba ta zamo ƙasa ta kwanta. Muryarta har rawa yake tace, “Bana son ƙarnin kifin can, dan ALLAH ka fita da shi”. Sosai yake kallonta da mamaki, dan shi dai yasan a zuwanta gidan nan yasha sayo kifi ya kawo suci har ɗanye suyi abinci balle yace bata ci tun fil azal. “Yau kuma kifin ne zaki ce baƙya so Huznah?”. Hawaye ya cika mata ido ta ce, “Wlhy bana so, dan ALLAH ka taimakeni ka fita da shi. In ba haka ba zan sake yin amai”. Shike nan ba damuwa zan fita da shi tashi kici abinci”. Yay maganar yana ajiye mata ledar takeaway daya yi musu. Shi kuma ya nufi kitchen ɗin ya shiga gyara kifin da naman dan a tunaninsa sabon iskanci ne dan kar ta gyara, tunda sarai yasan halinta dan ma baya mata da wasa ne. Tsaf ya gyara komai ya zuba su a freezer ɗinsu sannan ya koma falon shima.......✍️ Hajiya Huznaty😂🤣🤣bara dai nayi shiru. *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖3️⃣6️⃣ ______________ .......A zaton Maanal kwantar da shi sukai a ɗaki kamar dai a Nigeria, amma a mamakinta sai taga wajene da yake duk kujeru ne da zasu iya kai goma kamar wajen masu jiran ganin likita dai haka, babu kowa a wajen sai shi kaɗai, zaune yake a ɗaya daga kujerun bayansa jingine da kansa. Idanunsa a lumse, sai hannunsa ɗaya da kanula ana masa ƙarin wani ɗan mitsitsin drip da aka rataye. Gani tai kamar ya rame mata ma, dan fuskansa yay fayau sai glowing take. Gashin kumatunsa kwance luff-luff kamar ya gyara shi. Yanda lips ɗinsa suka ɗan tattare waje guda zai tabbatar maka yau fa maza sun jigata. Motsin zamanta a kujerar kusa da shi daf ya sashi buɗe lumsassun idanunsa datai tunanin barci yake. A hankali ya saukesu a kanta. Sosai zuciyarta ta jijjiga da ganin yanda suka kaɗe jazur har wani firi-firi suke kamar an watsa jan a cikinsu. Sai kawai hawaye suka gangaro mata, fuskarsa ya ɗan kawar gefe, alamar baya son ganin hawayen nata. Fin minti guda sannan ya ɗan sake waiwayo wa. Kan Maanal na duƙe tana wasa da yatsunta cikin juna dan ta kasa tsaida hawayen sam. Ita kanta kuma bata san miyasa take kukan haka ba, kawai dai tana jin tausayinsa. Cike da kasala irin ta mai ciwo AA ya sauke ɗayan hannunsa da babu komai a kan haɓarta ya ɗago fuskarta, babban yatsarsa yasa ya share mata hawayen sannan ya maida hannun nasa kan hannayenta da take cuɗawa cikin juna. Dai-dai hawayen da suka sake gangaro mata na zubowa sai suka sauka akan hannun nasa. Ƙasa-ƙasa ya zubama hawayen nauyayyun idanunsa, sai kuma a hankali ya ɗan rumtse hannayen nata cikin nashi ba wani da ƙarfi ba dan baida isasshen ƙarfi sam a yanzu. “Kin san fa bana son kuka Besty?”. Ya faɗa a can cikin maƙoshi da ita kanta ma da ƙyar ta iya jiyosa. Hannunta ɗaya ta janye a hankali ta shiga share hawayen da bakin veil ɗinta. Sai da ta goge tas duk da wasu sun sake cika idanun sannan ta ɗago ta kallesa. Shima dai ita ɗin yake kallo ta ƙasan ido. Sam bata son kallon jajayen idanun nasa, dan haka ta sake maida nata ta risinar, muryarta na rawa ta ce, “Yaya jikin?”. Maimakon amsawa da baki hannunta ya ɗan matsa alamar amsawar kenan. Dai-dai nan wata Nurse ta ƙaraso, sannu tama AA da Chaines, batare daya kalleta ba ya jinjina kansa, ta ɗan kalla Maanal ta ce, “Hello”. Kai Maanal ɗin ta jinjina mata tare da daga mata hannu, ita ma sai ta ɗaga mata hannun tana murmushi ta cigaba da aikinta, dan ita kam yau a karo na farko taji baƙaƙen fata sun birgeta dan gasu nan ƙyawawa da su. Ƙaramin roban ruwan ta janye ta saka wani ɗan babba amma bai kai babba na Nigeria girma ba, sannan tai allurai har uku a cikin ruwan, duƙowa tai ta kama hannun AA ɗin tana saita shigar ruwan fiye da yanda yake da. A ɗan daƙile Maanal ta janye idanunta daga kallonsu gefe. Sannan fuskarta ta ɗan canja. Dan murmushin cikin ƙirji AA yayi yana kallon Maanal ɗin data juya baya. Sai kuma ya lumshe idanunsa kawai. Ita dai Nurse ta gama tabar wajen batare data san laifinta ba. Fin minti biyu da tafiyar tata Maanal taƙi juyowa inda yake, kaɗan ya ɗan Matsa hannunta da har yanzu ke cikin nashi, shiru bata juyo ba. Ya sake matsawa, nan ma shiru. Sai kawai yay ɗan mitsitsin murmushin gefen baki da inba ma kallon ƙurulla kake masa ba bazaka taɓa sanin yayin ba. Dan kawai ta juyo cike da neman magana murya a dashe ya ce, “Wash....” Ai wash ɗin nasa ma bata gama fita ba ta juyo garesa, akan hannunsa da aka saka ruwan ta fara sauke idannunta, ganin komai lafiya lau ta maida kan fuskarsa, gira ɗaya ya ɗaga mata yana ɗan marairaice fuska. Fahimtar neman magana ce ta sakashi yin abinda yay ɗin sai ta dalla masa harara. Idanunsa ya ɗan lumshe ya sake buɗewa a kanta alamar lallashi. Baki ta tura masa cike da shagwaɓa. Sai shima yay kamar zai taɓe baki a yanayin murmushi amma ba murmushin bane. Barcine ke rinjayar idanunsa, tun yana kallonta ƙasa-ƙasa har barcin ya ɗaukesa.. Idanu kawai Maanal ta zuba masa cike da zurfafa a tunani. Dai-dai nan akace, “Hello Madam” a bayanta. Juyowa tai duk da batai tunanin da ita ake ba, a mamakinta sai taga ɗaya daga cikin mutanen jiya ne da suka tarbosu a airport. Kanta ta jinjina masa, ya ƙaraso wajen yana gaisheta da turancinsa mai wahalar fahimta saboda nauyi harshensa da yarensa ya cinye. Amsa masa tayi, kafin ta tambayesa yaya yasan suna anan ya fara mata bayani yaje hotel ne ake sanar masa. Cike da gamsuwa ta jinjina masa kanta. Ya jajanta mata rashin lafiyar sannan ya mika mata ƙyaƙyƙyawan farin mayafi na saƙa yana faɗin ta lulluɓama AA ɗin saboda akwai sanyi. Amsa tayi tai masa godiya, kafin a hankali ta yunƙura zata janye hannun AA dake cikin nata, idanunsa ya ɗan buɗe, cikin yanayin barci ya kalleta, itama dai kallon nasa take, Mr Li dake kallonsu sai ya shiga yimasa sannu. Luuuu ya ɗan kallesa, sai ya lumshe idon ya buɗe alamar amsawa. Da wannan damar Maanal ta miƙe ta lulluɓa masa mayafin tun daga ƙafafunsa har wajen wuyansa, hakan sai ya bama fuskokinsu kusanci sosai, ta ɗago da niyyar gyara masa mayafin daya ɗan haura zuwa lips ɗinsa suka haɗa ido. Yanda yake binta da kallon idanunsa a shanye da nauyin barci sai tsigar jikinta ta shiga tashi, jitai ta kasa janye wa, kallon juna suke da wani irin yanayi mai wahalar fassara, kafin a hankali ta janye jikinta baya, wajen zamanta ta koma tana fidda numfashi ɗai-ɗai daga ƙirjinta zuwa maƙoshi. Yayinda shi kuma ya maida nashi ya rufe ruf saboda barci da yaci ƙarfinsu. Shi dai Mr Li na kallonsu ta gefen ido cike da pretending ɗin ba kallon nasu yake ba. Ƴar bag ɗin hannunsa ta takarda kalar ruwan ƙasa ya miƙa mata, ganin taƙi amsa tana kallon jakan kawai sai yay mata bayanin coffee da milk tea ne a ciki. Amsa tayi tai masa godiya. Ya sake miƙa mata iPad nan ma ya sanar mata ta AA ce, ta ajiye masa. Shi zai koma hotel ɗin domin kai sauran abokan tafiyarsu wani waje. Nan da awa ɗaya zai dawo, tunda yaga sai nan da awa ɗaya da rabi zasu sallame su zuwa biyu. Yay maganar yana nuna mata ƴar computer ɗin dake jikin ƙarfen ƙarin ruwan. Mamaki ya kama Maanal, a ranta tace tab da'a Nigeria ne maybe mara lafiyar ne ma zai sace na'urar koda bai san amfani ta ba. A fili kam sai ta jinjina masa kai kawai... Zaman shirun ne ya ishi Maanal, dan haka ta ɗauka iPad ɗin ta duba, babu wani security a jiki, apps ɗin ta shiga dubawa tana neman games, babu ko ɗaya, dan haka sai kawai tai downloading a app store. Game ɗin ta fara bugawa tare da ɗaukar cup ɗin milk tea ɗin ta fara sha dan cikinta ya fara mata zafi. Ji tai batun azumi ya faɗo mata a rai, ko yanzu Nigeria sun ɗauka oho, dan bata san yanzu acan dare bane ko rana, anan dai tasan suma zuwa gobe zasu tashi da shi ne.... Kamar yanda Mr Li ya faɗa kuwa bayan awa ɗaya sai gashi ya dawo, bai wuce minti talatin ba kuma Nurse ɗin nan tazo ta cirema AA ruwa. Tare da sanarma Maanal Doctor nasan ganinta a office ɗinsa. Buɗe idanu AA yayi yana kallon Nurse ɗin, sai kuma ya maida kan Maanal, yanzu kam Alhmdllh sun rage mugun jan da sukayi, sai dai ɗan kumburowa irin na wanda yay barci. Kamar zatai kuka itama take kallonsa, sai batare da yayi magana ba ya jinjina mata kansa alamar taje. Miƙewa tai idanunta a kansa, shima dai kallonta yake har suka shige da Nurse ɗin. Basu sameshi a office ba, dan haka Nurse ɗin ta nunama Maanal wajen zama ta fita. Babu jimawa sai gashi ya shigo yana cire safar hannu alamar daga wani aikin yake, a abin shara ya jefa sannan ya zauna yana kallonta fuska da murmushi. Ita dai basarwa tayi, tare da jinjina masa kanta ciki-ciki ta ce, “Good morning”. Amsawa yay shima da nashi turancin mai fita da harshensa, “Ajwaad Aliyu wife right?”. Kanta ta jinjina masa. Shima ya jinjina nasan yana ɗaukar wani folder yana dubawa, fin mintuna biyu ya sake gyara zamansa, yanda ya maido gaba ɗaya hankalinsa a kanta sai ya sata nutsuwa itama. “Mrs Ajwaad baƙya son mijinki ne?”. Da mamaki ta kallesa yanzu kam sosai jin banzar maganarsa, sai kuma ta ɓata fuska taƙi magana. Shima sai yay murmushi yace, “Sorry! Nima ina da dalilin faɗar hakan. A yanayin da yake ciki nayi mamaki da akace min yana da aure harma yana tare da matar anan. Kin san mi yasa?”. Kai ta girgiza masa. Mijinki yana cikin wani hali sosai na buƙatar mace, a binciken da mukai masa ya jima a wannan takurar har takai yana sakashi suma ma idan abin yay tsanani, wannan babban haɗari ne ga namiji, dan yau da ace baku yi saurin zuwa asibiti ba zai iya shiga babbar matsala, kuma ko a yanzu matsalar bata kau ba a tare da shi gaba ɗaya, kawai dai mu mun bashi taimako ne ya ɗan dai-daitu”. Da sauri ta sake kallosa idannunta na tara hawaye. Sai kuma ta maida kanta ta risinar. “Karki damu zai samu lafiya, amma sai da taimakon ki. Dan babu abinda yake buƙata kuma zai taimakesa samun lafiya gaba ɗaya sai ke. Bama ta jikinsa kawai ba harda brain, dan a hanlin da yake yanzu yana fuskantar tsintar kansa a tashin hankali da damuwa (anxiety) saboda buƙatar ta yi masa yawa kuma bai samu wani taimako mai ƙyau na saukewa ba, hakan ya haifar masa da tashin hankali da rashin nutsuwa a brain ɗinsa dan ma na fahimci shi ɗin gentle men ne na haƙiƙa. Dan irinsu nada matuƙar ƙoƙari wajen kamewa akan abubuwa har sai kiga ma sun cutu wani bai sani ba. Dan matakin da yake ciki da mutum mai ƙarancin nutsuwa ne da tuni ya samu matsala babba. Amma kinga shi normal a zahiri ya iya riƙe damuwarsa shi kaɗai duk da yana fuskantar matsanancin ciwon mara da jin zafin fitsari (blue balls. epididymal hypertension), saurin fishi, koyaya akai masa abu ransa na ɓaci zuciyarsa na masa nauyi sosai sai ya ji damuwa da yawan bugun zuciya. Shiyyasa ma yake suma da gajiya saboda yawan tunani da damuwar. Yanzu abinda nake son ki fahimta ke kaɗai ce hope ɗinmu, kece zaki taimaka masa ta hanyar warware masa waɗan nan matsalolin idan ba haka ba zasu cigaba da girmama ta yanda matsalar da tafi hakan zata iya biyo baya. Dole ne ki dinga kwantar da hankalinki a duk sanda ya taɓaki, ki bashi haɗin kai batare da nuna firgita ko ruɗewa ba dan shigarki wannan yanayin zaisa ya ƙyaleki kuma shi matsala ne a garesa. Kasancewa da namiji ba mutuwa bace ko wata azaba mai girma. Wahalar kaɗance kuma ta lokaci ne kafin komai ya zama normal. Please ki taimaka masa zaki gode min wataran okay?”. A hankali Maanal da kanta ke a ƙasa ta jinjina kai, dan wlhy wani irin ji take kamar ta nutse a cikin ƙasa. Shi dai mai jan kunne babu ruwansa a kwai buɗe aiki kai tsaye. Wai a haka ma dan da turanci yake gaya mata komai, da ace a hausance ne ai sai ta gudu saboda girmansu.........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖3️⃣7️⃣ ______________ .........Tare da shi suka fito inda AA ke zaune har yanzu idanunsa a lumshe. Zama Maanal tayi kanta a ƙasa, shima doctor ya zauna a kujerar gefen AA daya ɗan buɗe ido yana kallon Maanal ɗin. Ya buƙaci Mr Li ya basu waje, dan zai yi ma AA magana ne da yaren da yasan Mr Li ɗin zai ji. Tsakanin likita da mara lafiya kuwa akwai babban sirri musamman irin wannan. Cike da kulawa Doctor ya kira sunan AA, a hankali ya janye idanunsa akan Maanal ya maida ga doctor. Murmushi ya masa, kafin cikin tausasawa ya fara magana da harshen Chaines da Maanal bata fahimtar komai, “Na tattauna da matarka, na kuma bata shawarwari, sai dai na fahimci a tare da ita akwai tsoro da kunya sosai. Ana samun irin wannan yanayin ga mata, musamman idan wani abu ya taɓa tsoratasu a baya mai kamanceceniya da hakan, da kuma haɗi da halittarsu ce kunya. Irinsu suna buƙatar a kasance da su cikin rashin da kulawa ba gaggawa ba, dan in har aka matsa zasu iya sumewa ma, ko jin tsanar namiji a kusa da su. Dan haka su a nasu tsarin ba'a zuwa musu kai tsaye da buƙata, ana binsu mataki-mataki ne, sannan ana basu lokacin sabawa da fahimtar dasu bawai tarayyar kawai akafi buƙata da su ba kai tsaye. Kai inda hali ma, a basu lokaci na hana zuwa garesu da tarayya sai romancing kawai. Idan aka bi wannan matakin zai cire mata damuwa da tsoron zuwa wancan matakin da take fargaba. Dan haka a yanzu matakin romancing, Hugging, nuna mata ma baka damu da abinda take gudun ba zai taima sosai. Yawan tausasa mata, kulawa, da tattalinta. Duk da nasan kai hakan zai sa ka cutu saboda a matakin da kake tarayyar kawai kafi buƙata, sai dai kaima hakan zai taimaka maka dan zuwa kai tsayen zai iya cutar da kai kuma ta wata fuskar. Zan baka waɗan nan maganin da in kaji rashin juriya sakamakon kusancin naku kasha zaka samu natsuwa har lokacin da zaka kai matakin daya kamata. Sannan ka ƙara ƙarfin motsa jiki da kake yi, ka rage cin abinci mai sugar da kitse, bada ƙarfi a ayyukanka fiye da shagaltuwa da kasancewar ku a waje guda ku kaɗai duk da dai na fahimci tuni kana bin waɗan nan matakan shiyyasa ka jima a cikin yanayin batare da ka cutu ba gaskiya. Dan da ace baka yin waɗan can abubuwan dolene ka samu matsala fiye da hakan, kai bama zaka iya riƙe ƙanka zuwa yanzu ba gaskiya. Ga card ɗina idan kana buƙatar wasu shawarwari zaka iya nema na. Nagode sosai”. Kai AA ya jinjina masa tare da faɗin, “Thanks you doctor” ƙasa-ƙasa dan duk abinda ya faɗa masan shi ya jima da sanin a binsa. Dan tun lokacin da al'amarin ya fara neman fin ƙarfinsa ya fara karance-karance a addinance da kuma likitance akan hakan, saboda yama kansa alƙawarin komai tsahon shekaru zai jirata, idan ma bai sameta ba zai ƙarasa rayuwarsa a haka. A dalilin wannan yanayin ne ya fara workout na tashin hankali, ya kiyaye abincin da zaici, ya sake kusanta kansa da malamai domin neman ilimin addini, ya ƙara ƙarfafa ibadarsa, ya koma azumi irin na Annabin ALLAH. Ya kauda idanunsa ga duk wani abu daya shafi mata, kai yama haramtawa kansa kallonsu da suffar matan gaba ɗaya, ya maida kansa busy a neman nakansa, ya yawaita alkairi ga mutane. Hatta ita Maanal ɗin yana ƙin shige mata ne a yanzu saboda hakan, ko a wannan gaɓar kawai tana tsorata ne amma shi baya zuwa gareta dan yin abinda take ma tsoron, to amma ya fahimci tunda a yanzu doctor ya buɗe masa aiki a wajenta kawai zai zauna da ita ne ya mata bayani ta kalar yaren da zata sake fahimtar..... Tunaninsa ne ya katse sakamako miƙewar doctor da zuwan Nurse ɗin nan wajen da ledan magungunansa. Amsa Maanal ɗin tayi, sannan sukai sallama da su dan Mr Li ma ya dawo. AA ya ɗan sake kallonta ya janye idanunsa, sannan ya fara ƙoƙarin janye mayafin data rufa masa, yana gama janyewa ya miƙama Mr Li, shi kuma ya waiwayo ya sake kallonta. Fiskarta a ɗan tsuke take, amma cike da kulawa murya can ƙasa ta ce, “Yaya jikin?”. Idanunsa ya ɗan lumshe tare da buɗewa a kanta, sai kuma ya miƙa mata hannu alamar ta kama shi. Ajiyar zuciya ta ɗan sauke itama, duk da tasan ba lallai ta iya kama shin ba haka ta saka hannunta cikin nasa daya miƙo mata. Ita ta fara miƙewa, sannan shima ya yunƙura tana riƙe da shi ɗin ya miƙe. Cikinsa ya saki gaba ɗaya, sai dai kasala da nauyin jiki irin na mai ciwo da zama a waje ɗaya. Sallama suka sake ma Nurse ɗin nan dan tana a wajen har yanzu, kafin su fara takawa a hankali, Mr Li na gabansu suna biye har suka fito. Motar da akaje ɗaukarsu jiya a airport ta gani. Mr Li ya buɗe musu ƙofa, AA ta taimakawa ya fara shiga, kafin itama ta shiga. Ya rufe su ya zagaya mazaunin driver ya tada motar suka fice a asibitin. AA dai tuni ya jingina da kujera ya lumshe idanunsa, sai dai hannunsa na riƙe dana Maanal yaƙi saki. Ita dai tana ɗan kallon waje ne da mutane dake ta kai kawai duk da rana ta ɗan ɗaga. Basu wani jima ba suka iso hotel ɗinsu, nan ma suna rike da hannun juna suka fito, Mr Li ya taimaka musu da kwasar ƴan tarkacensu zuwa ciki. An gyara ɗakin nasu tsaf an canja bedsheet. Mr Li dama daga ƙofar ɗaki bai shigo ba ya juya, sai itace ta amshi kayan ta shigo da su ciki. A bakin gado AA ya zauna, ita kuma ta ajiye kayan data amso inda ya dace. Kafin ta kallesa murya a ƙasa ta ce, “Ko zaka fara yin wanka ne?”. Idanunsa ya ɗan zuba mata, ganin tai saurin janye idanunta a kansa sai yay ajiyar zuciya. “Uhmm” kawai yace mata ya ɗauke nasa shima. Itama bayin ta nufa batare data sake kallonsa ba. Bata wani jima ba ta fito, kallo ɗaya ta masa ta ɗauke idanun ta dan ya cire jallabiyarsa daga shi sai boxer, muryarta har ɗan sarƙewa take wajen sanar masa ta haɗa. Shima sai baice komai ba ya miƙe ya nufi bayin. Itama kayan da zai saka ta fiddo masa, ta kuma fidda nata ta ajiye gefe. Fin mintuna ashirin sai gashi ya fito sanye da fara tas ɗin bathrobe. Baima gama zama ba ta ɗauki nata kayan ta wuce bayin, bata fito ba sai da ta shirya tsaf. Tako yi ƙyau cikin doguwar rigan, sai dai tana ɗan jin takura saboda yanda rigar ta wani lafe mata a jiki ta kuma fitar da shef ɗinta yanda ya kamata, duk da bata matse mata jiki bane, kawai taushin rigar da yanda aka fitar da ita da ainahin shef na mutum ya kawo hakan. Haka dai babu yanda zatai ta fito, sai dai ta saki mayafinta ya rufe mata ƙirji har ma zuwa cikinta. Bayan ne dai babu yanda ta iya. Fitowarta dai-dai ana knocking ƙofa, canta nufa, hakan ya bama AA damar ganin bayanta. Ai da saurinsa ya janye idanunsa a wajen maƙogwarinsa na wani irin kaiwa sama ya dawo ƙasa a cikin wuyansa. Maanal dai data buɗe ƙofa bataga kowa ba, sai ɗan abun nan na kawo abinci kawai a ƙofar. Ɗan juyowa tai ta kalla AA daya duƙar da kai yana danna iPad... “Abinci ne?”. Ta faɗa a taƙaice. Batare daya ɗago ya kalleta ba muryarsa a ƙasa kamar tatan ya ce, “Ni nai order”. Kanta kawai ta jinjina ta jawo ɗan keken ciki ta maida ƙofar ta rufe. A gaban gadon ta tsaida shi dai-dai inda yake. Ganin zata kai ƙasa ya kalleta, da ido yay mata nuni da gadon, tai ɗan jimm sai kuma ta miƙe ta koma ta wajen ƙafafunsa ta zauna. “Ko dai zaka koma can kaci abincin ne?”. Tai maganar tana nuna inda kujerun suke. Wajen ya kalla shima, sai kuma ya maido idanunsa a kanta. Batare daya janye ba ya ce, “Naki ne ai”. Itama kallonsa tai da ƙyau, “Kai da zaka sha magani ya dace kaci, ni bama najin yunwa nasha tea a asibiti ma”. Komai bai ce ba, sai ma ajiye iPad ɗin yay ya sauka a gadon, jan keken yay zuwa inda ta nuna, ya shiga fidda abincin yana jerawa a table ɗin wajen, sai da ya gama tsaf sannan, batare daya kalleta ba yace “oyaaa taso”. Ganin yanda yay da fuska batai musu ba ta miƙe ta nufi inda yaken. Kusa da shi ya nuna mata, zama tayi tana satar kallon fuskarsa, batare da yay magana ba ya fara ɗibar abincin yakai bakinta. Fuska ta ɓata, shi kuma ya ɗan harareta. Dole ta buɗe baki ya fara bata, kusan lauma huɗu taga shi baici ko ɗaya ba. Sai ta dauka wani spoon ɗin itama ta fara ɗibowa cike da jin nauyi takai bakinsa. Baiyi musu ba kuwa ya amsa, sai suka cigaba da bama juna har ta fara cewa ta ƙoshi. Bai matsa mata ba shima kuma bai cigaba da ci ba, taje ta ɗakko ledar magungunansa ta dawo, duk yanda suka rubuta ya mata bayani dan da Chaines sukayi, ɗaya bayan ɗaya ta bashi yasha. Yana gamawa yace mata zai kwanta. A marairaice ta ce, “Yanzu babu yanda zamuji ƴan gida su san mun sauka lafiya?”. Kallonta ya ɗan juyo yayi, sai kuma ya kai kwance. “Zamu kira su amma sai zuwa anjima dan su yanzu dare ne can suna gab da yin sahur”. “Lah anga wata ne?”. Ta faɗa fuskanta na washe wa da murmushi. Kansa ya jinjina mata murmushin nata na tasirantuwa a garesa. A cikin maƙoshi ya ce, “Na gani yanzu a net...” “Masha ALLAH”.. Maanal ta faɗa zuciyarta na wani irin sanyi. Wannan normal ne ga dukkan musulmi, muna jin wani irin farin ciki da nishaɗi da annashuwa ta musamman a cikin jininmu a duk lokacin da watan Ramadan ya zagayo mana. Muna jin kamar mun shiga wata sabuwar duniya ne, muna jin nutsuwa da ƙarfin zuciya mai cike da harsashi. Muna jin kamar a ranar muka fara riskar watan ne. (Ya rabbi kasa muyita ganin watan Ramadan cike da yalwar rayuwa mai tsaho da lafiyar jiki da tsarkin zukata. Ka gafarta mana kurakuranmu ka amshi ayyukanmu a bisa rahamarka da yardar ka, ka gafartama iyayenmu da al'ummar Musulmi baki ɗaya da suka rigamu kwanta dama🙏😭)...........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖3️⃣8️⃣ ______________ ........A yau ɗaukacin musulman Najeriya suka tashi da azumin watan Ramadan a wasu yankuna na ciki dama sauran ƙasashen Afrika. Sai kuma wasu tsirarun ƙasashe da basu da tazarar lokaci mai yawa da ƙasan ta Nigeria. Yayinda sauran ƙasashen duniya da lokacin ɗaukar bai kai ga ƙarasa musu ba suketa shirye-shiryen hakan suma. Anan Abuja ahalin Ambassador Aliyu Darma cike suke da farin cikin fara azumin da kuma kewar rashin jin AA da Maanal. Ga Mamy dai fargaba ce da damuwa cike fal a zuciyarta. A cikin ƴaƴan nan uku tafi kasancewar a fargabar al'amarin Ajwaad fiye da kowa. Yaro ne mai biyayya, amma kuma yana da taurin kai, sannan yana biyayya ne a gareta a iya abinda ya tabbatar bai saɓa shari'a ba. Ta wani gefe kuma tana tsoron kaidin mace, tare da masifaffiyar soyayyar da yakema yarinyar nan. Ta tabbatar zai iya mancewada wani gargaɗinta can, shiyyasa tafi kowa matsuwa da ƙagauta a jiran kiransa. Amma gashi har tsawon kwanaki biyu shiru kake ji, bayan duk inda Ajwaad yaje a tafiye-tafiyensa yana sauka baya rufa awanni biyar a ƙasar bai kirasu a waya ko video call ba. Amma a wannan karon sai gashi ba haka bane saboda ya tafi da mace. Macen ma yarinyar data tsana fiye da komai a ɗan tsakanin nan saboda ƙarfin abinda take gani a idanun ɗanta game da ita. Dan duk abinda kaga Ajwaad baya jin nauyin sakawa a gaba ya kalla a gaban kowa, baya shayin tattali da nuna kulawa a kansa, baya iya ɓoye feeling na farin ciki a kansa idan yana waje, baya iya riƙe miskilancin sa a kansa a gaban kowa. To lallai wannan abun ya kai ƙololuwar girma da daraja a garesa. Itafa yaron nan ya duba tsabar idonta ya sanar mata a yanzu Maanal nada power ɗin yin komai da dukiyarsa tunda matar sa ce, dan haka bazai iya cewa tabar kamfaninsa yin aiki ba. Tace ya faɗa mata ma'anar *MAWAAD* yaƙi, ita kuma a tsorace take da fassarawa bisa ga yanda zuciyarta ke hasaso mata. Shiyyasa take son ya faɗa da bakinsa, dan in har ya kasance hakane lallai za'a jisu da Ajwaad fiye ma da gidan nan... Shigowa Nuratu tana cin indomie tana magana a waya ya katse ma Mamy tunaninta. Binta tai da kallo dai-dai tana miƙo mata wayar. Ganin yanda tai wani getse-tse a gabanta babu ladabi babu risinawa irin na yaro da babba sai abin ya sosa mata rai. Amma batace komai ba ta amsa, Mamansu Nuratun ce, suka gaisa ta tambayeta ya ibadar azumi da aka fara Mamy ta amsa mata. Cike da siyasa Maman Saheeba ta ce, “Yaya ƴan tafiya an sauka lafiya kuwa?”. Sai da Mamy ta ɗan nisa kafin ta ce, “To zamu iya cewa haka, dan muma bamu jisa ba dai har yanzu bai kira ba”. Ɗan jimm Maman Saheeba tai, sai kuma daga can tace, “Hummm ke ko Aunty ai ya tafi da mace sai abinda muka gani kam. Kefa da kanki kike sanar min yaron nan duk inda zaije baya rufa awanni zai kiraku yace ya sauka. Amma wannan karon kinji shiru ƴar iskar ta hana shi kenan, koda yake keko ai bata yar a ƙasa ba tunda nn Asiya tasha kuma rainon Fatimah ce. To ALLAH dai ya jishemu alkairi kada a dawo ana ƴan amaye-amaye, tunda ta samu dama yanzu daga ita sai shi ai bazata yarda su raba ɗaki ba, sannan duk yanda zata hillacesa ya bata abinda ta saba samu a titi ai yi zatai”. Wani irin tiririn zafi ne ya turniƙe zuciyar Mamy, muryarta har rawa take dan fushi wajen faɗin, “Aiko dana tabbatar masa nice na ɗauka cikinsa wata tara nai wahalliyar naƙuda kuma. Ni na rasa yanda zan yi da yaron nan Nana, nafi shan wahala a ɗaukar cikinsa fiye da kowa, ki duba yayin haihuwarsa kamar bazan rayu ba jini ya ɓalle min, inaga tunda cikin Ajwaad ya kai wata biyar a jikina na daina barcin kirki har sai da na haifesa. ALLAH kuma ya ƙwalla fin sonshi a rai fiye da sauran amma sam yaron nan baya dubawa.” “Ta ina zai duba kuwa Aunty, gashi nan yanda kika sha wahalar ɗaukar cikin nashi da haihuwa haka kike shan wahalarsa a yanzu, ai ke dai bar hatsabibin yaro kinji. Irinsu ai sune zakka a cikin ƴaƴan da ake cewa. Dan basai yaro na rashin jin shaye-shaye ko makamancin hakan yake zama zakka ba a cikin ƴaƴa. Amma koni taƙadarancin Ajwaad na ban tsoro, kuma ba komai ya kawo hakan ba sai shegiyar matar nan ta gefenki data ƙara busar masa da zuciya baya kallon kowa sai ita, baya jin maganar kowa sai ita. Ko tafiyar nan bana raba ɗayan biyu itace ta shirya musu ita tunda Yaya ya hana ƴar gwal ɗinta ta tare, kinga in akai haka ai za'a samu abinda ake so. Shima Yayan da yake a ƙarƙashin umarninta yake ya kasa duba gaskiya ya hana. Ai wlhy shi zaki takurawa ya dame su da waya da gargaɗi, idan ma ta kama kwana huɗu su dawo gida”. Sosai maganganun Maman Saheeba ke shigar Mamy, jin abinda tace akan Abah kuma sai ta nisa, muryarta cike da damuwa tace, “Nana maganar Abansu ma a barta, kin dai san halinsa ba'a cika masa gari kamar tuwon gero yake sai yay nauyi. Tsartar jaraba ce da shi, dan halinsa kaf sune a jikin Ajwaad, sauran ƴan uwansa wasu abubuwa kawai suka ɗakko. Amma wlhy Ajwaad bai bar komai na mahaifinsu ba. Da haka cire ma batun shi na sashi a azalzala musu zai harbo jirgina ne da wuri, duk abubuwan dake faruwa badan na kasance mai takatsantsan ba da tuni ba wannan maganar akeyi ba ai. Ki dai bari muyi wani tunanin daban, sannan yanzu dakonsa nake ya kira waya na samu number ɗin komai mai sauƙi ne ai”. Badan Maman Saheeba taso ba ta ce, “Hakane kuma Aunty. Mu barsa to ya kira a samu number ɗib sai musan hanyar kamawar. Bara naje na ɗan kwanta naji azumin farkon kamar zai ɗan yi duka”. Ƙaramar dariya Mamy tayi, tare da faɗin, “Ke dai raguwa ce dai”. A tare yanzu sukai dariyar, Maman Saheeba tai mata sallama suka yanke wayar. Kallonta ta maida ga Nuratu, sai kuma ta ɗauke kanta tana mai girgiza kai kawai. Tunda asuba data tasheta yin sahur tace ita bazatai azumi ba jini yazo mata...... ★A ɓangaren Oum kam kewar su Autanta ta isheta, amma kasancewar Najma na rage mata. Dan barcinsu ma su suka sha sai kusan sha ɗaya suka tashi. Sannan ne suka fito falo Najma ta saka musu *SUNNAH TV* sukai zaman kallon tafsir, dan sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu zasu fara fita nan cikin anguwar inda malam keyin na mata da safe, na maza da yamma. Sallar azhar ce ta tashe su, bayan sunyi suka ɗan kwanta, kusan ƙarfe uku Najma ta tashi ta fito saboda kiran wayarta da Fawzan yayi cewar ya dawo gida tun azhar, gashi a falon Oum tun ɗazu baiji motsinsu ba. Koda ta fito ta gaisheshi zama tayi suna kallon tafsir, sai hira jefi-jefi da bata shafi komai ba. A haka Babban Yaya ya shigo shima, da'alama kuma ya ɗan jima da dawo gida, dama lokacin azumi basa daɗewa a wajen aiki. AA ne kawai idan bai gadama ba sai gab da shan ruwa zakaga ya shigo. Itama dai Oum fitowa tayi. Tana zama babu jimawa su Inte suna shigo dan tambayar miya kamata a rage na aiki, dan duk azumi gaba ɗaya nan sashen Oum kowa ke zuwa ai aiki, a kuma shirya komai a rumfar bunu dake can compound anan ake buɗa baki ko a tsakiyar gida, ana kammalawa su fice sallar asham anan masallacin kusa da su, inda harda AA a masu jan sallar, dan kuwa babban ɗalibi ne na imam ɗin massalacin. AA akwai ilimin addini, kuma har yanzu akan nema yake bai zauna ba. Kawai dai idan ka gansa a harkar neman kuɗi saika ɗauka bokon kawai aka sani. Amma Alhamdullah anan wajen dukansu Oum batai wasa ba a kansu, kowa kansa cike yake da ilimin addini tunda hatta babban yaya har yanzu bai daina zama gaban malamai ɗaukar karatu ba shiyyasa suke a nushe (KU SAN BOKO BA ILIMIN ADDINI TAMKAR NAMAN KAZA NE A DAFE BA'A WANKE ƘARNI BA🥱) ... Bayan sallar la'asar badan Mamy taso ba ta tattaro su Saheeba zuwa sashen Oum. Dan cike take da jin zafin Oum ɗin. Oho ita baiwar ALLAH bama ta hankalta da yanayin Mamyn ba, kawai abinda ta kawo a ranta azumi ne dai na farko da kowa sai ya ɗanɗana kafin a saba. Su duka sun kasance a kitchen harda masu aiki. Abah da Babban Yaya da Fawzan sai Naufal suna massallaci daga Asr basu dawo ba sukai zaman jin tafsir. Abinci mai rai da motsi suka shirya ana ƴar hira sama-sama. Wajen biyar na yamma sai ga tawagar ƴan hutu daga Kano sun iso. Abah ne kawai yasan da zuwansu. Tuni fuskar Mamy ta sake tsukewa, yayinda ta Oum ta yalwatu da farin cikin ganin ƴaƴan ƴan uwanta. Domin kuwa samarin yara ne biyar, na Uncle Mahmud biyu, sai na Uncle Modibbo ɗaya da mace budurwa ɗaya, sai ɗaya na Uncle Hussain, ɗaya na Uncle Hassan. Sai sauran ƴammata uku, Autar su Nuwaira, sai biyu da suka kasance jikoki suma ta ɓangaren Abbah mahaifin su Oum. Najma ma dai sosai take a farin ciki. Tuni aka buɗe ɗakunan ƙasa na ɓangaren Oum, samarin zasu zauna nan, su dukasu kusan sa'anni ne dan duk bazasu wuce 20, 21, 22, ba, su kuma ƴammatan wasu sun girmi wasu, akwai sa'annin Najma biyu, biyun kuma bazasu wuce 15 ba. A ɗakin Najma su suka haɗe, duk da Oum tace ya musu kaɗan a sake buɗe wani ɗakin sukace a'a. Samarin kuwa biyu suka rabu. Dan sunce akwai Hashim daya rage shima yana zuwa daga Sokoto ɗan ɗan uwan Oum ne shima dai ta ɓangaren Abbah. Shine wanda su AA suka taɓa zuwa gidansa lokacin da zasu je Giro. ALLAH yaso su Oum da yawa sukai abincin, dan dama Abah nata jaddada musu ayi abinci sosai akwai masu ci. Da suka tambayi su wanene yace sudai su ƙara kawai. Ashe yaran ne a hanya. Gida kam dai Alhmdllh, sai hakan ya sake ragema Oum kewar su Maanal duk da dai sunan manne a zuciyarta a dukkan motsinta. Da taimakon yaran aka shinfiɗa manyan carpet da dama ana tanadarsu ne dan irin wannan lokacin ne kawai. A compound aka baza su, sannan aka shiga fitar da nau'o'in abinci da suka shirya abinka da mutane da yawa. Dandanan wajen yay ƙyau daka kalla kasan a lallai Ramadan ya kama. Yaran sunata ɗauka a waya abinka da ƴan ɗore-ɗoren social media. Da farko Nuratu nata ɗauke-ɗauken kai, sai dai fa tasha jinin jikinta dan ita kanta tasan yaran a goge suke da ilimi sannan gidan iyayensu akwai kuɗi suma, dan sanin kanta ne ALLAH yayma zuri'ar Darma arziƙi tun na tushe daga iyaye. Hakama family ɗin su Oum ta ɓangaren Abbah, K. Kura yana ɗaya daga cikin manyan likitoci a ƙasar Najeriya ga shi kuma ɗan kasuwa, mahaifinsa shima dai ya tara ya bar musu. Abinda ya sosa mata zuciya yanda yaran suka wani watsar da ita amma su kansu a haɗe dan kamar su cinye Najma, haka ma sun janye Anum a cikinsu su adole ga ƴan haɗin kan dangi. Humm tasha jin Saheeba da Mamy suna faɗin haɗin kan Darma Family da masifar son juna da suke da shi, bata tabbatar ba sai a yau ganin ƴan yaran nan yanda suke 5&6 matuƙa. Gasu a nutse babu rawar kai sam a tare da su. A haka su Abah suka shigo bayan sallar magriba, lokacin kowa yaci dabino yasha ruwa sanata yin sallar magrib. Wani irin farin ciki a bayyane kowa ya gani a fuskar Aba, Babban Yaya, Fawzan. Dan tuni yaran sun wani zagayesu. Duk rashin fara'a da yawan magana ta Babban Yaya kamar zai cinye yaran a bayyane dan so. Kai wannan abu na kona ran Mamy, har mamakin irin haɗin kan wannan family take yi..... Abin sha'awa abin birgewa kowa ya nema wajen zama aka fara buɗa baki, maza na nan ɓangaren mata anan ɓangaren abinci a tsakkiya. Kuma duka harda masu aikin gidan ne, harda wanda bama musulman ba duk an jawosu. Wannan itace ainahin ɗabi'ar wannan gida, shiyyasa a cikin masu aikinsu mutum biyu sun taɓa musulunta a bisa jin daɗin wannan yanayin, dan haka suka kyautata rayuwarsu a yanzu haka suna zumunci da su sosai kuma suna zuwa gidan. Bayan an karya da gwargwadon abinda ya sauwaƙa marasa alwala suka tashi suka sabunta, masu ita suka kimtsa aka fice sallar asham anan masallacin dake kusa dasu dan jikin gidan su Hajiya Shuwa yake. Su kansu anan suka iske su Hajiya Shuwa suma sun fito. Massalacin upstairs ne. Ƙasa maza sama mata, kusan ƴan street ɗin duk anan suke salla, musamman da azumi cika yake tab, wani ma sai a lokacin yake tuna wanene makwafcinsa.......✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖3️⃣9️⃣ ______________ ........A ɓangaren ƴan chaina kam a yau su kuma zasu ɗauki nasu azumin. Dan kammala yin sahur ɗin Maanal da AA kenan. Yanda ta takura masa da batun kiran ƴan Nigeria ganin da sauran lokacin kammala sahur ma balle ai batun sallar asubahi yay zaman kiransu video call dan yasan a yanzu darene an dawo sallar asham acan. Hakanne kuwa, dan shigowar su Oum ɗin kenan sun sake zama anan compound masu ƙara abinci na shiri masu hira nayi saƙo ya shigoma babban Yaya a waya. Murmushi yayi tare da miƙama Fawzan dake kusa da shi waya. Fawzan na gama karantawa ya wani kwashe da dariya. Duk kallonsa kowa yayi, baima jira kowa ya tambayesa ba ya miƙe yana faɗin, “Oum ki shirya autanki zai kira video call yanzu”. Aiko tuni fuskar Oum ta washe da sabuwar fara'a, yayinda Mamy tai saurin duban Fawzan. Suko yaran suka shiga ɗoki zasu ga Yaya AA. Dan tunda suka iso suke tambayar yana ina. AA nada farin jiki ga yaran family ɗin, dan duk da bai sakar musu fuska indai suka ce suna buƙatar abu ko bashi suka tambaya ba in dai yaji zai yi musu abin yace wancan ya barsa. Sannan in dai sukai irin wannan zuwa hutun zakaga yana musu saye-saye na abubuwa daban-daban. Ranar salla ko zai sa a kaisu duk inda suke so koma shi ya kaisu. Nuratu kam jikinta har rawa yake, dan tunda Babban Yaya yaje ya ɗakko laptop a sashensa ya dawo compound ɗin ji take kamar taje ta fisge system ɗin daga hannunsa ta hana kowa ganin AA sai ita kawai. Sai dai babu wannan damar. Ita kanta Mamy abinda take rayawa a tata zuciyar itama kenan. Cike da girmamawa Babban Yaya yazo ya ajiye laptop ɗin a gaban Abah, Mamy da Oum na gefe-da-gefensa daman alamar sun gama shiryawa. Kasa haƙuri da yaran sukai duk sai sukazo suka zagayesu ta baya. Su dai su Saheeba basu motsa ba, amma hankalinsu na wajen, musamman Nibras da Nuratu ji suke kamar su fisge laptop ɗin. Tar-tar AA ya bayyana a screen ɗin, hakama su Abah sun bayyana masa fes shima. Wani irin bugawa ƙirjin Mamy yayi, dan haka kawai sai zuciyarta ta kissima mata ganin AA ɗin na wani walƙiyar mutumin daya sha angwanci. Abah da Oum kam murmushin da AA ɗin ya ɗan sakin musu suka mayar masa. Cikin nutsuwar nan tasa da rashin hayaniya ya furta, “Assalamu alaikum. Abah, Oum, Mamy barkanku da shan ruwa”. A tare Abah da Oum suka amsa masa, sai kuma ya shiga gaishesu, dai-dai nan Maanal dake cin abinci a gefensa ta matso jin ya ambaci sunan su Abah ɗin. Dan ita da farko a tunaninta ma aiki zai yi. Ganin su Oum da tayi sai tai saurin komawa baya dan abin yazo mata a bazata. Dariya Abah da Oum suka sanya, shima AA dai murmushi yayi, kafin ya furta, “Tun jiya fa take rigima a kiraku a kiraku, ni kuma ban samu zama ba saboda ɗan fita da mukayi shopping”. Sosai murmushin Abah ya sake faɗaɗa, cike da tsokana yace, “Haba Babyn Oum mune kuma ake ɓoye mawa, common zo na ganki”. Sosai kunya ta ƙara rufe Maanal, ta matso kusa da AA kanta a ƙasa, shiko yaƙi ya ɗan gyara ta samu ta zauna yanda ba sai ta raɓu da jikinsa ba. A haka ta gaishesu tare da yi musu barka da shan ruwa. Oum ta ce, “Naga takaina ni Fateema, Baby wannan boye-boyen fuskar na miye?”. Yanzu ko AA dariya yayi kaɗan, hakan yasa Maanal mintsininsa ta yanda su Oum bazasu gani ba. Fuska ya ɓata yana kallon Oum, “Oum kinga ta mintsine ni ba, na rama kuma Abanta yace na masa ba daidai ba”. Cikin dariya Oum ta ce, “Gaskiyarka Auta. Aba kama ƴarka magana ta kiyaye mu”. Murmushi Abah yayi, ransa fes, Mamy dai wani kalar kallo take ma AA da shi kaɗan yasan ma'anarsa, dan haka ma ya ɗan rage kallon sashen da take. Hira Abah ya dinga jan Maanal da ita, tun tana sinne kai harta ware tana basu labarin Chaina shi da Oum. Yanda take yi ɗin sosai farin ciki ya mamaye zuciyar Oum da Abah, yayinda AA ya zama ɗan kallo kawai gashi tana a jikinsa batare data farga ba. Tsaguwar da ƴan hutunsu sukai yasa suka haƙura aka miƙama ƴammatan dake kusa da Oum. Wani irin waro idanu Maanal tayi na mamakin ganin Najma, Meeno, Maimoon, Jiddo, da Lailah, sauran ƙananun bata ganesu ba. Yanda ta zano sunan kowa babu mantawa ya sakasu a farin ciki sosai. Shi kansa AA sai yaji daɗi, dan son ƴan uwansu a cikin jininsu yake. A dake AA da yaga ko takansa basu bi ba ya ce, “Baku iya gaisuwa ba ko? Auntynku kaɗai kuka sani”. Ai a tare suka shiga faɗin, “A'a Yaya kayi haƙuri!” sai kuma suka shiga gaishe shi da girmamawa. Ɗan mintsininsa Maanal tayi ƙasa-ƙasa tace, “Jealousy”. Kaɗan ya murmusa yana wani kallonta a ƙasan ido. Tasan saboda yaran ya wani kame, sai taji ya bata dariya. Dan AA akwai tsare girma. Daƙyar suka miƙama samarin suma, a mamakin AA suma duk Manal ta ganesu, dan babu wanda bata kira sunansa ba, tafa yi mugun sanin ƴan family ɗin Darma ɗin nan dan haihuwarta ne kawai ba'ai a cikinsu ba. Suma da ƙyar suka iya daina ma AA surutu dan sunata roƙonsa su dawo suna missing ɗinsa, sannan kowa yana lissafa masa abinda za'a saye masa. Lokacin da laptop ɗin takai gaban Nuratu, Nibras da Saheeba sai da sukai wani ɗan shock. Gashi hakan yayi dai-dai da AA ya ɗan duƙo a jikin Maanal yana mata magana a kunne, ita kuma ta irin juyawa da saurin nan ta saka yatsarta a saman lips ɗinsa alamar yay shiru. Shi kuma batare daya lura an ajiye laptop ɗin a gaban wasu ba dan ita tama juya baya tunda shi take fuskanta ya kama hannun nata ya tura yatsar nata a cikin bakinsa kai kace wani lollipop ya samu. Da sauri ta fisge hannun tana wata ƴar dariya da kai masa mintsini shi kuma yana murmushi da ƙoƙarin riƙe hannun nata zai maida a bakin. A bazata tana ƙoƙarin ƙwacewa da juyowa a lokaci guda saboda tsoron kar wani ya gansu idonta ya sauka a kansu duk kamar sunyi sumar zaune. Ba shiri ta ankarar da shi ta hanyar faɗin, “Besty su aunty fa”. Sai lokacin ALLAH ya bashi ikon ganin nasu, maimakon ya saketa sai ya basar kawai yama sake mannata da ƙirijinsa hannun nata dai da take son ƙwacewa bai sakin ba ya dai haƙura da sakawa a bakin. Dole ta haƙura dan tasan ba sakin zai ba. A haka ta shiga gaishesu, Saheeba ce kawai ta iya amsawa da ƙyar, Nuratu kam a bazata sai hawaye, dan numfashinta har ja yake kamar zai fice a ƙirjinta, sai ma ta miƙe tabar wajen kowa ya bita da kallo musamman sauran da basu san abinda ke faruwa ba, Nibras kam hannunta sai rawa yake tana ƙoƙarin riƙesa da ɗayan. A dake AA ya amsa gaisuwar Saheeba. Sai itama Nibras ɗin ta shiga gaisheshi muryarta na ƙoƙarin ƙwacewa tana riƙota da ƙyar. Maimakon ya amsawa Nibras gaisuwar a wani irin daƙile ya furta, “Ita matata laifi ta miki kika ƙi amsa tata gaisuwar?”. Kanta ta girgiza da dauri. Cikin zaro ido Maanal ta juya tana kallonsa tare da ɗamƙe rigarsa, irin (miye haka kake yi ɗin nan) shiko yaƙi kallonta. Dole ta juya tana amsa gaisuwar da Nibras take mata fuskarta da murmushi dan harga ALLAH bata ji daɗin abinda AA ɗin yay ba. Dai-dai nan Yaya Fawzan yazo ya ɗauke laptop ɗin daga gabansu. Ya wani ware idanu da faɗin, “Inye kaga amarya da ango”. Ai ba shiri Maanal da maganar ta sata jin kunya tai saurin duƙewa, ƙoƙarin kamota AA yayi ta zille tama tashi gaba ɗaya. Tana jiyo dariyar Fawzan cike da shaƙiyanci. A gado ta naɗe bata sake zuwa wajen ba balle gaida Yaya F. dan tasan halinsa na tsokana, yanzu haka ma tana jiyo yanda ya saka AA a gaba shi kuma ya kasa bashi amsa..... Zamansa a kusa da ita bayan ya kammala wayar ya sakata ɗagowa ta kallesa, gira ɗaya ya ɗan ɗage mata yana wani ƙanƙance idanu. Idannunta ta kawar, tana ɗan tura baki gaba. Murmushi ya ɗanyi tare da ɗan taɓe baki, sai kuma cikin taushin sauti ya ce, “Kinga Besty zo kiji wata magana”. Shiru kamar bazata tashi ba, sai kuma ta yunƙura a hankali zata zauna. Kamota yay ya kwantar a jikinsa, sai taji tsigar jikinta na tashi, ga wata kunya mai kassara jiki. Agogo ta kalla, gudun karsu shiga lokacin gama sahur. Tsaf ya lura da yanayin nata, sai yay ɗan murmushi a zuciyarsa. A fili ya furta, “Kwantar da hankalinki, awa kusan ɗaya ce damu gaba”. Hannu tasa ta rufe fuskarta kawai. Shi ya san tun Maanal na yarinya ta musamman ce, hakan yasa ɗabi'unta da yawa suke sakashi kallon mata da yawa a basu iya komai ba. Ganin yanda ta rufe ido ya sashi kai yatsarsa manuniya a kansu ya fara sosa mata samansu. Dole ta buɗe idanun a hankali, suna shiga cikin nashi tai ƙoƙarin janye wa amma sai ya hana hakan. Kaɗan yaja mata hanci tare da faɗin, “Yarinyar nan ke da kunyar nan taki ko......” Kauda fuskarta tai tana murmushi. Shima sai ya ɗan murmusa hannunsa riƙe da fuskrta cikin raɗa ya furta, “Na tambayeki wani abu?”. Kanta ta jinjina masa kawai. “Mi doctor yace miki jiya a asibiti?”. Ai da gudu tai ƙoƙarin tashi a jikinsa amma ya riƙeta, magana tai ƙoƙarin yi kamar zatai kuka yace, “Relax! Tunda baƙya son na sani. Amma kin yarda ni na faɗa miki wata magana?”. Shiru kamar bazata amsa shi ba sai kuma ta jinjina kai. Hannunta da take matsewa waje guda ya kamo cikin nashi, cike da lallashi da son kwantarta mata da hankali ya cigaba da magana da sanyin murya da tausasa lafazi. “Besty! Ina son ki kwantar da hankalinki tsakanina dake. Nasan akwai abubuwa da yawa da kike buƙatar ji daga gareni amma ban faɗa ba, nima akwai wanda nake buƙatar son ji daga gareki amma ban tambaya ba. Lokaci nake jira, akwai gaɓar da zamu zo wannan matakin ne in sha ALLAHU. Abu na biyu nasan a baya bamu taɓa kallon kammu a wannan matsayin ba, ko nace daga ɓangarenki, dan ni dai a gareni wannan shine burin rayuwata na farko daya fara ginuwa tun ma ban fahimci wanene ni ba.....” Karo na farko Maanal ta kallesa, wani irin lumshe mata idanu yayi ya sake buɗewa. “Kada kiyi mamaki, kada kuma ki tambaya, kada ki damu da son sani game da jin hakan domin ba yanzu ba. Abinda nake so daga gareki a yanzu kawai haɗin kai, kwantar da hankali, ki kwantar da hankalinki dani, bazan taɓa aikata wani abu a gareki ba bada yardarki ba Maanal! Duk yanda zan tsinta kaina a matsuwa ta buƙatar jiki kota rayuwa ki sani ke kinfi hakan muhimmancin da bazan fifitasu a kanki ba. Domin su na wuccin gadi ne, zasu iya samuwa su wuce sai wani lokaci a buƙace su, ke kuma ta har abada ce, akoda yaushe kece kaɗai Ajwaad, kece kaɗai nake iya buɗema zuciyata, ke ce kaɗai nake iya buɗema damuwa ta, kece ƙawa! Kece ƙanwa! Kece aboki! Kece aminiya! Kece abokiyar dariya! Kece abokiyar magana! Kece abokiyar kuka! Kece abokiyar karatu! Kece abokiyar sirri! Ko duk kin manta? Kin manta haka saboda nisa da ratar da ƙaddara ta bamu ne? Kin mance haka saboda jarabawa da UBANGIJINMU yay mana dan yaga ƙarfin imaninmu? Kin manta saboda a yanzu tunaninki na baki komawarki mace matancin naki ne kawai zan iya buƙata? Noo Manaal! Noooo! Wannan Ajwaad ɗin na nan a naki tun na waccan rayuwar, bakuma zai taɓa canjawa daga hakan ba domin a matsayin da dama na gina kenan tun fil azal. Ki sani tubalin ginin da kayan ginin an samar da su ne daga himmar aiki mai ƙarfafa ƙwanji tun daga ƙarƙashin zuciya da bigire na fitowar TSIRRAI daga HUKUNCIN UBANGIJI. Wallahil azim inda zaki ce Ajwaad bazan taɓa baka kaina ba mu rayu a haka yanda muke ni mai riƙe miki wannan ALƘAWARIN ne dan ba wannan nake kallo ake ɗin ba, ke! Ke! Ɗin nake kallo a matsayin Ke! Kawai Maanal.....”✍️ Hummmmmmm *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖4️⃣0️⃣ ______________ .........Gaba ɗaya sai Maanal taji ta sake rikicewa, hawaye kam gudu suke wasu na bin wasu dan sunanta kai tsaye a bakin Ajwaad babbar magana ce, jikinta na wani irin tsuma zuciyarta na rawa da sake rauni. Bata san sanda ta zabura ba lokacin da AA ya cigaba da faɗin, “Maanal! Har yanzu ke yarinya ce, shekarunki basu kai na fara banbance ƙarfin ikon zuciya dana ƙwaƙwalwa ba. Amma ina son daga yau, daga yanzu kisa a ranki, Ajwaad Aliyu Abubakar zai iya FANSARKI da kansa a kowanne irin TARNAƘI. Sannan zai iya MALLAKA miki kansa da komansa domin biyan buƙatar ki. Zai iya ƙwata daga hannun wani domin FARIN CIKIN KI. Zai iya bayarwa ga wani domin MUTUNCINKI. Zai iya sadaukarwa ga DUNIYA domin ɗaga DARAJAR KI. Koda kuwa kina kallon komansa a matsayin AJIYA A DUHU bazai damu ba Maanal, bazai karaya ba Maanal. Domin rauninki ne kawai ke iya karya lagon Ajwaad a bayyane da raunana shi har ya iya kaiwa ƙasa wanwar. Na rantse miki da ALLAH babu abinda ke iya dukan wannan zuciyar ya sata risina da sallamawa akan komai sai ke Maanal.....” yay maganar yana ɗaura hannunta a dai-dai saitin zuciyarsa, kafin a wani irin ƙaramin sauti ya sake faɗin, “Manaal...” ji tai bazata iya jurewa ba, dan sautin kukanta har ya fara bayyana waje, da sauri takai hannunta ta dafe masa baki jikinta na rawa sosai, idannunta a jikin nashi tana mai girgiza masa kai. Sosai nasa idanun shima sukai wani irin kaɗewa suka koma jaaa matuƙa, ƙyallinsu ya sake zama mai ƙyalli sosai tamkar wanda hawaye suka tararma a ciki. Ji yake tamkar ya tsaga jikinsa ya sakata kawai a ciki duk inda yaje akace ina Maanal yace tana a cikin jikina. Ganin yanda idannunta ke wani tafiya luuu-luuu kamar zata suma sai kawai ya jawota gaba ɗaya a jikin nasa ya rungume tsam-tsam hawayenta na sauka masa a kan ƙirji. Sun fi minti biyar a haka kafin ya kai lips ɗinsa kan kunnenta ya sumbata, ta ƙanƙame jikinta dan har tsakkiyar kai taji al'amarin, cike da raɗa ya furta, “Shagwaɓaɓɓiyar AA minti biyu fa doctor yace ki ringa rungumeni kawai in ba haka ba zan iya BOƘAREWA a tafi step 2 kin san ba mata bane kawai boƙararru”. Ƙaramin ƙulli (dundu) ta masa a baya tana ƙwace jikinta fuskarta da murmushi. Siririyar dariya ya saki shima yana biyota zai sake kamowa ta zille. Ganin ya tsare ko ina cikin shaƙƙaƙiyar muryarta irin ta mai kuka batare data kallesa ba ta ce, “Kasan dai na iya duka a ciki ko”. Yanda tai maganar tana dunƙule hannu kamar zata kawo naushin ya saka shi matsawa baya yana waro idanu. Sai kawai ta wani ƙyaƙyƙyale da dariya tana faɗin, “Matsoraci kawai Oum's boy”. Takai kwance tana masa gwalo. “Kinci bashi”. Ya faɗa yana ɗaukar wayarsa da kira ke shigowa. Ganin Āhōng Chen (Sheikh Chen) ne yasa shi miƙewa a wajen ya koma wajen kujeru. Ita kuma sai kawai ta kwanta ta zuba masa idanu. Wani irin dawo mata kalamansa keyi a zuciya, so take ta fasa komai dalla-dalla amma nauyinsu yay mata yawa. Sai ma wani irin barci mai ɗan karan daɗi daya fara fisgarta. Kafin kace mi ta lula a cikinsa cike da mafarkin AA. Bayan kammala wayar yazo ya tasheta dan lokacin sallar asuba yayi.... _________★ Huznah dai azumi ya gagara kaiwa yamma, dan anayin azhar tiɓis ta zama. Tsoron kar Sageer ya dawo batai komai ba ta miƙe cike da lallaɓawa tai gyaran gidan ita da Khadijah ƙanwarsa da tazo tayata aikin, sannan ta fara hada-hadar ɗaura girki dan ya tabbatar mata yau da ɗan yawa zatai abincin akai gidansu shiyyasa ma ya turo mata Khadijah, dan yana son iyayensa suyi buɗa bakin farko da abincin gidansa, baya son ta kwafsa shiyyasa yace Khadijahn tazo tunda har yanzu hannunta bai wani gama faɗawa da girkin ba. Haka ta lallaɓa sukai komai, abu na ƙarshe data bari yin farfesun kifi da yace yana so duk da bata son ko sunan kifin a kira. Ca tai Khadijah ta ɗaura ita bara taje tai wanka. Khadijah bata kawo komai a ranta ba tace to ganin komai an tanada haɗawane kawai. Abu kamar almara tayo wanka tana shiryawa kifin da Khadijah tasa a wuta ya tafaso sai ga ƙamshinsa har cikin bedroom ɗin da Huznah take. Wani kalar harmutsawa cikinta yayi, kafin kace mi tai bayi a guje sai amai. Kakarin aman nata Khadijah ta jiyo ta shigo a guje. Sosai tsoro ya kamata ganin yanda Huznah ke amai, gashi sai magiya take mata wai taje ta kashe gas ta fita da kifin. Ina ita Khadijah bata fahimta ba, sai da Huznah ta gama birkicewa da galabaita sannan tai hankalin kiran yayanta a waya ta sanar masa. Mamaki ne ya kamashi jin wai Huznah na amai saboda ƙamshin kifi, dama dai shirin tahowa gida yake, dan haka ya taho, ya sameta kwance duk ta saki, ya shiga mata sannu da tambayarta mike damunta. Idannunta cike da hawaye tace, “Dan ALLAH yaya Sageer bana son kifin can kace ta sauke shi”. Kallonta kawai ya tsaya yi, sai kuma ya juya ya fita zuwa kitchen. Ya samu Khadijah na kwashe kifin, sai kawai baice komai ba ya fice. Babu jimawa ya dawo tare da Nurse ɗin yarinyar dake makwaftan su, dan yayarta ce ta duba Huznah ranar first night ɗinsu yanzu kuma yayar na asibiti sai ƙanwar. Tambayoyi ta fara ma Huznah ɗin dake wani yatsine-yatsinen fuska, ita dai yarinyar bata kulata ba dan suna ganin irinsu Huznah har ma wanda suka fisu a iya iskanci. Dama kuma an cika anguwa da labarin Huznah bata da mutunci idan aka shigo gidan taga talakawa ne tata musu yatsine-yatsine. Fitsari ta buƙaci Huznah zuwa tayi, kamar bazata tashi ba sai da Sageer yay mata magana. Koda taje tayo sai ta canja wajan kwanciya. Ita dai yarinya batare komai ba ta bama Sageer tsinken gwajin ciki ta faɗa masa yanda za'ai. Bai wani je ko'ina ba anan gabanta yayi komai. Aiko a farko ma ya nuna akwai ciki. Wani ta ƙara bashi, shima dai haka, ta bashi na uku still shima haka. Ta ce, “Congratuletion Yaya Sageer Auntynmu na da ciki, ya kamata kuje asibiti gobe dan asan kwanakinsa, ga wannan tasha zai taimaka mata daina jin aman. Idan da hali kuma a daina dafa kifin da bata son”. Sosai Sageer da fuskarsa tai matuƙar washewa tun ambatawar Zubaidah cewar Huznah nada ciki murmushinsa ya sake faɗaɗa. Godiya ya shiga yima UBANGIJI, sai kuma ya shiga sanyama Zubaidah albarka itama. Yarinyar nada hankali da nutsuwa gata bata da yawan magana. Sosai ake yabama tarbiyyar yaran gidansu a anguwar, ga girmama na gaba dan duk wanda ya girmesu a Yaya yake ko Aunty a anguwa ko Baba ko Uncle. Koda ya bata kuɗi ƙin amsa tayi... Huznah kam tunda Zubaidah ta ambata kalmar ciki tai sumar kwance, so take brain nata ta banbance mata wake da ciki amma kamar bata wani fahimta da ƙyau saboda ruɗani da shiga gigita na bazata. A haka Sageer ya dawo ya wani rungumeta yana sake jera godiya ga UBANGIJI. Hakama Khadijah da Zubaidah ta sanar mata kamar an jehota ta shigo ɗakin, dole Sageer ya saki Huznah. Farin ciki suke shi da ƙanwarsa, yayinda ita kuma ta shiga halin ɗimuwa da gigita. Ina itace za'ace ma tana da ciki, cikin ma na Sageer ba AA ba. Wannan abune da bazai taɓa yiwuwa ba, dole wannan cikin yabi rariya kuwa. Hakan alwashinta ne dan bazata taɓa yarda ta haihu da Sageer ba koma mizai faru sai dai ya faru....... Tofa babbar magana, wai ɗan sanda yaga gawar soja🏃🏃🤣 _________★ Tsaf Manaal da AA sukai shirin fita. Duk da Maanal bata so tashi a barcin data koma bayan sallar asuba ba dan ya mata daɗi sosai. Suna fitowa suka ci karo da su AS da rabon su dasu tun randa suka zo. Gaba ɗayansu sun shiga gaishesu da girmamawa ne da tambayar jikin AA dan jiya Mr Li ke sanar musu dalilin fara fita abinda ya kawo su. Da yake anan ba kamar Nigeria ba haka suka haƙura basu je dubashi ba duk da sun so hakan. Maanal nason yima Yaqub magana tana tsoron fushin AA. Sai kuma yanda CFO Faseelat take dama-dama da AA ya ɗan tsayama Maanal a rai. Duk da tun a gida kai tun ma farkon zuwanta MAWAAD ta so fahimtar wani yanayi daga CFO ɗin game da AA. Sai kuma dai ta ƙaryata zuciyarta dan CFO Faseelat A Zakaria ba yarinya bace ba, a ƙalla zatai sa'ar Fawzan koma ta ɗan girmesa kaɗan. A tsakanin Fawzan da AA ma kuwa akwai ƴar tazarar haihuwa kamar yanda Oum take faɗa. Kawai sai Maanal taji ita abun ma ya bata dariya, batare data maida hankali ba ta taɓe baki kawai ta cigaba da istigafarinta a zuciya dan shine mai fishsheta da azuminta a baki. Sun isa *Nicolas G. Hayek Watchmaking school* da zasu samu horaswar. Tarba suka samu ta musamman ga matashin professor Zhang Kuma abokin karatu ga AA. Dan cike da tsokana ya ɗan kalla Maanal dake a sashen AA sannan ya ɗan kalla AA ɗin yana masa wani salon tambaya da ido. Ɗan kallon Maanal ɗin shima AA yay, sai kuma yay murmushi... Prof.... ya ce, “Wow Maanal right?”. Ƙaramar harara AA ya sakar masa, Prof.. ya sanya dariya. Hakama AA ɗin murmushi yake yi. Bayan AA ya gama doguwar jiyyar abinda ta faru da ƙyar su Abah suka samu ya koma makaranta a wancan lokacin, dan likitansa ya tabbatar musu hakan ne zai taimaka ma brain ɗinsa samun daidaito da heart ɗinsa datai breaking. Ga kuma matsanancin depression da yake ciki a lokacin. Haka kuwa akai AA ya zana SSCE ta online abinka da ƴaƴan manya, babu jimawa sakamako ya fita aka shiga nema masa admission, cikin sa'a aka samu kasancewar Abah matsayin ambassador. Sannan takardunsa sunyi ƙyau sosai dan ya samu result mai ƙyau sosai. A jami'ar ya haɗu da Zhang, a lokacin shi yana Masters ɗinsa ne, inda AA ke zuwa ya zauna ya ware kansa nan suka haɗu da Zhang, tun yana tsayawa yayta kallonsa daga nesa dan shi yanayin fatar AA ɗin ke ɗaukar masa hankali har takai ya fara ɗan masa magana.........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖4️⃣1️⃣ ______________ .......Da farko AA baya kulashi kamar yanda baya kula kowa a makarantar. Yakan dai shiga aji da an gama lecture zai fito yazo wajen ya zauna har sai lokacin wata kuma. Sai yazo yini guda ya fita baiyi magana da kowa ba a school ɗin. Wani lokacin Babban Yaya da RK ke zuwa ɗaukarsa, wani lokcin kuma Abah da kansa kuma su suke kawosa. Kamanin da suke da juna yasa Zhang fahimtar suna da alaƙa ne, ya kuma ji sunan Maanal ne a bakin AA, dan in yana zaune shi kaɗai ɗin nan yakan rufe idanunsa yay shiru a kujerar wajen kamar mai barci amma zakaji sunan Maanal na fita masa a baki ko yace Besty. Tun Zhang na ɗaukar AA nada matsala ta brain shiyyasa yake sambatun kiran abinda bai san miye ma'anarsa ba har daga baya ya gane AA yana cikin depression ne. Dan yayi course na karantar halayyar ɗan adam. AA ya bashi tausayi, dan haka ya fara zama kusa da shi koda bazai kulashi ba, dan wani lokacin ma tashi yake ya bar masa wajen. Shi kuma bai taɓa ce masa komai ba tsawon lokaci har AA ɗin ya daina tashi a waje idan yaga Zhang yazo ya zauna. Yau da gobe sai yake zama suyi gaisuwa kawai har dai shakara taja. Bayan sanin sunan AA abu na biyu da Zhang yaso sani shine miye ma'anar Maanal, sannan waye Besty da yake jin AA yana yawan ambanta. “Maanal suna ne, kuma itace Besty”. Ya bashi amsa a taƙaice. Ya ce, “Mace ne ko namiji?”. Anan ma AA bai kawai komai ba ya ce, “Mace”. Tun daga nan Zhang ya fahimci matsalar AA. Bai sake masa tambaya akan hakan ba kuma har AA ɗin ya fahimci abinda Zhang ya karanta, sai kawai Maanal tazo masa a rai da zane-zanenta. Wannan shine tushe kuma asalin kafa alaƙarsu, kuma shine ya taimaka masa wajen kafa Maawad Company dan da taimakon Professor Zhang. Ya taɓa zuwa Nigeria lokacin buɗe MAWAAD COMPANY. Hakama zanen dake a companyn yasan na Maanal ne dan anan Chaina AA yasa aka zana shi yana siffanta musu ita. Har zuwa yanzu AA bai taɓa bashi any labari akan Maanal ba, iya abinda ya sani kenan, amma da kansa ya fahimci ita budurwarsa ce, amma basa tare. Sanin AA baya kula mata sam ganinsa da mace a yanzu da kuma kamanin da Maanal tai masa da wani hoto daya taɓa gani a wallet ɗin AA passport ne ma yasa shi saurin ganewa duk da bai tabbatar ba ya dai canka ne kawai.... Rungume AA Prof yay cike da tayashi farin cikin jin ga Maanal a matsayin matarsa, cike da tsokana ya ce, “Wannan karon dai tunda Maanal ta dawo ya kamata nasan labarinta”. A mamakinsa murmushi AA yayi, bai kuma musa ba, amma bai ce komai ba dai a bayyane. Maanal AA ta zubama ido, tana son fahimtar mi Prof ke son faɗa, sai dai yaƙi yarda ma su haɗa ido har suka isa wani aji bisa jagorancin Prof ɗin. Sun fara gabatar da lecture ta awa ɗaya. AA na kusa da Maanal dan haka ta dinga masa tambaya akan abinda bata gane ba dan anayi suna rubutawa ne. Bayani yake ɗan mata, wasu kuma yace ta bari su koma masauki dan ta samu damar fahimtar Prof ɗin. Daga school ɗin wani companyn Prof ya wace da su. Su AS suna a motar su kamar yanda suka zo, ita da shi a mota Mr Li na jansu, sai Prof a gefen driver. Hira suke da AA da Chaines, dan haka Maanal ba fahimta take ba. Sai ta ma maida hankalinta a bitar abinda suka koya yanzun nan. Wani katafaran companyn agogo sukazo. Sosai wajen ya birge kowannensu, suka cika da fatan suma wataran suga companyn su a haka. AA da Prof ne suka jagoranci zagayawa dasu, Prof na musu bayanin komai yanda zasu fahimta su kuma ƙaru da ilimi. Suna ko ƙaruwar, dan duk sun nutsu yanda ya kamata. Maanal sai take jin kamar ana wanke mata brain ne, wani sabon karsashi take ƙara ji game da zane-zane bama na agogon kawai ba. Anan sukaci lokaci sosai. Bayan sun fito suka maida Prof makaranta, su kuma suka nufi wani wajen. Isowarsu yasa kowa ya fahimci massallaci ne. Sosai nan ma ya birge su Maanal, musamman ma ita da AA ke mata bayanin komai. Hakan ya fahimtar da ita lallai AA yasan Shanghai sosai, kuma da alama yayi zaman garin ma. A karo na farko ta fara kwaɗayin son jin wani abu game dashi bayan rabuwarsu. Lokacin sallar zuhur ne, ita da CFO Faseelat suka nufi sashen mata, su kuma su AA sashen maza. Itama Faseelat ta taɓa zuwa massallacin dan ita wannan shine karo na biyu da akai irin tafiyar nan da ita a ƙarƙashin kamfani, sannan a karan kanta tazo Chaina har cikin Shanghai yawon buɗe ido da tsohon mijinta. Kuma duk ta ziyarci massalacin dan yanada tarihi mai girma a wajen musulman Chaina. Koda aka idar da salla zamansu sukai, dan AA ɗin yace suna nan har magrib. Alkur'ani Maanal ta ɗauka tai karatu, sai Faseelat ta shagala a kallonta, daga ƙarshe ta ɓingire barci itako Maanal nata karatunta har Asr. Ita ta tada Faseelat ɗin ta fita ta canja alwala, sun gabatar da la'asar sai suka fito domin shan iska kamar yanda Faseelat ɗin ta shawarci Maanal. Bata musa mata ba, dan koba komai matar zata iya haihuwar kamarta idan auren wuri tayi. A mamakinta suna fitowa sai suka hango AA can cikin wata rumfa zaune tare da wani. Kamar ance ya juyo suka haɗa ido. Wani ɗan sassanyan murmushi yay mata itama sai ta samu kanta da maida masa murtani. Da hannu yay mata alamar tazo. Sai ta ɗan juya ya kalla CFO. Gani tai itama hankalinta akan AA ɗin yake, duk da dai tana kallonsa ne cike da basarwa na manyam matan Abuja. Cikin ɗan kwantar da murya na girmamawa Maanal ta ce, “Bara naje yana kira”. Kamar wadda ta daburce CFO ta amsa mata a ɗan daburce. Ita dai Maanal batabi takanta ba tai gaba. A zuciyarta ko faɗi take (Tsohuwar kawai ƙwalelenki wannan kayan sai Maanal) tai gaba abinta. Tan a isowa wajen AA ya kamo hannunta ya zaunar a kusa da shi, kafin cikin girmamawa ya kalla dattijon mutumin da sai yanzu Maanal taga fuskarsa ya nuna masa Maanal ɗin da alamu suka tabbatar ya riga ya masa bayani a kanta. Ita kuma ya juya yana sanar mata cewar shi ɗin malaminsa Āhōng Chen a lokacin da yay zaman Chaina na tsawon shekara biyu. Murmushi Maanal tayi, cikin harshen turanci ta rissina ta gaida shi. Shi ko dattijo ƙyaƙyƙyawa cikakken bacine da hasken addinin Islama ke zageye da kwarjininsa ya amsa mata da kulawa shima da harshen Ingilishi. Ya ɗora da addu'a a garesu. Kan Maanal a ƙasa take amsawa, yayinda AA ke amsawa kai tsaye. Āhōng ya shiga yi musu nasiha da bama Maanal ɗin labarin zamantakewarsa da AA, a labarin Maanal ta fahimci Āhōng ya taimaki AA sosai a rayuwa, dan har lokacin da suka haɗu AA na cikin depression, shine ya ringa masa addu'oi da shawarwari ya jashi a jiki har ya bayyana masa damuwarsa, cikin ikon ALLAH kuma kafin yabar garin sai gashi abubuwa sun dai-daita masa. A cikin labarin yake basu shawarwarin gina ƙyaƙyƙyawar alaƙar rayuwar aure mai tsafta da danƙo. Sosai Maanal ta jinjina ilimin wannan bawa, ashe mu baƙaƙe musamman a Nigeria da muke ɗauka kamar mune kawai musulmai ashe namu wasa ne, dan da yawanmu bama ƙoƙarin neman ilimin addini akwai dai son addinin a tare damu wannan ta shaida kam... Kiran sallar magrib ne ya tashesu a wajen, ita ta koma sashensu na mata su kuma suka nufi na maza. Alwala tayo dan bataga CFO ba. Sai da ta shiga massalacin ta ganta a sahun gabansu, batayi magana ba tasha ruwa da dabinon da aka basu sannan aka gabatar da sallar magrib. Bayan an idar suka fito domin yin buɗa baki anan harabar massallacin da ake shiryawa gwanin birgewa. Ɓangaren mata daban na maza daban. A yanzu sun gaisa da mutane daban-daban dan matan basu da yawa sosai. Daga ita dai CFO ne kuma baƙar fata a wajen, duk da Faseelat farace tas-tas da alamar ma ana ƙarawa da skincare, amma hakan bazai hana a kirata baƙar fata ba. Itako dama baƙar ce, kuma Alhamdullah tana alfahari da fatan ta. Kaɗan ta tsakuri abincin, lokacin isha'i yayi suka koma cikin massallaci. Anyi sallar isha'i akai asham. Sun gaisa da mutane akai sallama kowa ya fito domin kama gabansa. Sosai rayuwa a massalacin taima Maanal daɗi, duk da wani gefe na zuciyarta na missing ƙasarta ta haihuwa da yanda azumi ke kasancewa musamman na farko da ake kaishi cike da ɗoki da buri. Waccan shekarar iyanzu suna a Jos ita da su Zeezah, acan sukai azumin sai da yakai tsakkiya suka dawo Kaduna. Sai ta ƙara jin wani kalar kewar mutanen gida... “Mi matar Ajwaad ke tunani? Bayan gashi a gefenta”. A bazata taji saukar lallausar muryarsa a cikin kunneta, fiskarta da murmushi ta juyo, yana daga bayanta ne ya ɗan duƙo, sai ta samu kanta da kai yatsa ta ɗan dungure masa kai da faɗin, “Miyasa mijin Maanal ya cika sa ido ne?”. Murmushi yayi mai faɗi da ƙyatarwa, ya miƙa sosai tare da kama yatsar nata cikin hannunsa. Sosai abinda ta faɗa ya wani ratsa masa zuciya da cikata da farin ciki. A hankali ya jawota gabansa, batare da tunanin komai ba balle kunyar mutanen dake ɗan kai-kawo ya rungumeta, dan su AS har sun wuce wajen mota. A hankali ta kumshe idanunta, shima haka, suka saki ajiyar zuciya a tare zukatansu na sauka a kankali daga nauyin da su kayi. Cikin ƙaramin sauti mai marmashe zuciya AA ya furta, “Barka da shan ruwa ZUCIYAR AJWAAD”. Wani irin zuuu Manaal taji a jikinta. Sosai kalamansa na ƙarshe suka mata nauyi. Akwai shaƙuwa mai girma tsakanin da AA, irin shaƙuwar da zata iya rantsewa bata taɓa yi da wani ba. Ɗaya baya ƙaunar ganin ɗaya a damuwa, hatta da ciwo sun sha yi a tare. Abubuwa da yawan gaske nasu a tare ne. Amma basu taɓa danganta al'amarinsu da wata kalma ta soyayya ba koda ƙanƙanuwa. Sai dai suji a bakin mutane na ambatawa amma basu da kansu ba. Zata iya cewa wannan itace kalma ta biyu a rayuwarta da taji daga bakinsa da zata iya kamantata da hakan bayan kalaman ɗazun da asubahi, amma sai ta basar, kamar yanda suka saba ta ɗago fuskarta da dariya tana kai masa mintsini.... Da sauri ya ce, “Ouch! Besty wai a ina kika koyo muguntar nan ne?”. Dariya tayi tana ɗan tafiya da baya, girarta a ɗan ɗage ta ce, “Da zafi ne?”. Hararta yay da ɗan haɗe fuska ya ce, “Kina son sani?”. Gira ta ɗaga masa. Ya ce, “Okay bari sai munje makwanci zan banbance miki”.. Duk da gabanta ya faɗi sai ta sanya ƴar dariya, “Besty ai nasan kai bawan ALLAH ne baka faɗa cikin azumi”. Yanzun kam dariya sosai tazo masa amma ya daure baiyi ba ya saki murmushi tare da takawa ya riƙe hannunta daga ƴar tafiyar da take da bayaya. Tafiya suka fara a tare cike da nutsuwa har zuwa wajen motarsu, Mr Li ya buɗe musu suka shiga. Kusan a tare suka sauke ajiyar zuciya, sai kuma suka kalla juna. Murmushi sukayi a tare, gira a ɗan ɗage AA ya ce, “Yaya kin gaji ne?”. “Sosai ma, burina kawai nakai kwance yanzu. Gashi kuma ina son duba lecture ɗin yau”. Kafaɗarsa ya ɗan matso mata alamar ta kwanta. Sai da ta kallesa sukama juna murmushi mai sanyi sannan a hankali takai kwance a kafaɗar tana sauke ajiyar zuciya acan cikin ƙirjinta. Sai kuma ta gyara zamanta tana lumshe ido. Baice komai ba illa ɗan kallonta da yay ya ɗauke idonsa. Cikin ƙanƙanin lokaci Maanal tai barci, har bata san sunzo sun tsaya gidan abincin ranar ba Mr Li ya fita yay musu takeaway dan yasan zuwa anjima dole zasu buƙaci abinci........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖4️⃣2️⃣ ______________ ........Lokacin da suka iso hotel su AS tuni sun shige, AA ya kalla Maanal dake barci sosai, sai yaji ta bashi tausayi. Ita da ya sani da ragwantar azumi, koda yake yanzu an girma maybe ta daina tunda yaga yau batai raki ba, amma a da duk randa aka kai azumin farko tofa Maanal da kuka take kaishi. Murmushi yayi komai na dawo masa a zuciya kamar film. Baya son takurawa Mr Li, da zasu cigaba da zama a motar ne harta tashi, to yakamata shima a bashi nashi Freedom ɗin yaje ga iyalansa. A hankali AA ya kamata ya kwantar kamar wata ƙwai, kafin ya fita a motar, ta side ɗin da take ya zagaya, ya ɗan duƙo cikin dabara ya kamata tare da juya bayansa ya ɗaurata, a duƙen ya miƙe tana a bayansa har tana gyara kwanci ya miƙe tsaye da ƙyau riƙe da ƙafafunta, ita ko ta sake sarƙe hannayenta a wuyansa ta lafe. Da sauri Mr Li ya tattaro musu kayayyakinsu ya biyosu da shi, a haka ya shiga da ita cikin hotel ɗin, rayuwa ce irin ta ba ruwan wani da wani babu wanda suka zamewa abin kallo, kowa harkar gabansa yake. A haka ya shiga elevator da ita. A bazata ya fito daga elevator ɗin yaci karo da CMO da HOD da alama fita zasuyi, kicin-kicin ya sake yi da fuska, suma duk sai sukai ƙasa da kawuna like bama su ganshi ba. Ko kallonsu baiyi ba balle ya nuna ya ma sansu yay wucewarsa Mr Li biye da shi. Aiko suka juya suna kallonsu cike da mamaki. Eh lallai mace dabance, mace sarauniya ce, mace duniya ce. In ba hakana CEO ne goye da mace, kai lallai babbar magana, al'amarin kamar wani film. Oho AA baima san anai ba, dan yayi gaba kaɗan can ma ya hango CFO tana waya, ɗauke kansa yay dan ta tsaya tsai daga maganar da take kamar wadda ta suma. Shi ko ya saka card ƙofa ta buɗe yay ciki. Mr Li ya saka masa kayan ta ciki yana daga waje ya juya, shi kuma ya saka ƙafa ya rufe ƙofar abinsa sannan ya nufi gadon ya sauke Maanal dake barci bil haƙƙi alamar ta gaji sosai. Takalma ta ya zare mata, ya warware veil ɗin ma ya cire.. Sai ta sauke ajiyar zuciya ta gyara kwanciya. Tsai ya ɗanyi yana kallonta na kusan minti ɗaya, kafin ya sauke ajiyar numfashi ya sake kai hannu ya fara buɗe botiran rigarta, ya ɓalle fin biyar kamar wadda aka ankarar ta farka, wani kalar cafke masa hannu tayi tana buɗe idanu da ƙyau irin na (lafiya kuwa?) shima sai ya zuba mata nasa a wani kalar kasalance, sai kuma ya shiga jansu ƙasa ya sauke akan hannayen nasu, ita kuma sai tai tunanin jikinta yake kallo ta inda ya buɗe botiran, hannun ta saki da sauri ta kama rigar ta cikuykuye a cikin hannunta ta rufe wajen ruf.... Sai kawai ya samu kansa da sakin wani kalar lalataccen murmushi. Baki ta tura irin na jin haushin dan mi zai mata dariya. Fahimtar hakan sai ya sake sakin murmushin tare da matsar da fuskarsa gab da tata suna busama juna numfashi. “Idan abinda kike tsoron zanyi ai idanuna a cikin naki zanyi ba kina barci ba fa, dan haka karki damu kanki saura ƙiris”. Fuskarsa ta ɗan ture ta juya masa baya, sai ya sake yin murmushi ya leƙa fuskar ta bayanta. Cike da son ƙureta ya ce, “Please ki tayani wanka mana na gaji sosai My EverBloom!”. Gaba ɗaya ji Maanal tai tama daburce ta rasa ina zata saka kanta. Yanda tai ɗin ya matuƙar bashi dariya, tsabar son ya sake ƙureta sai ya riƙota yana faɗin, “Okay! Okay shike nan na haƙura har sai randa aka kawo min ke har ɗakin barcina a lulluɓe like kowace sarauniyar amarya, ki kasance cikin shiri dan babu batun ɗaga ƙafa ranar fa, zan zama kurma ne, sannan makaho na haƙiƙa...” Ita dai tuni ta cusa kanta a tsakiyar ƙafafunta ne tana jin kamar gadon ya rabe biyu kawai ta shige ciki ya maida ya rufe da ita. Shima fahimtar ya gama kaita maƙura ya sashi duƙawa ya sumbaci wuyanta ta gefen kunnenta, wani kalar girgiza jikinta yayi dan har tsakiyar kai taji sumbar nan, sai kawai ya miƙewa yana ƴar dariyan shaƙiyanci yabar wajen. Kaya ya fara cirewa dan wanka shi yafi buƙata fiye da komai a yanzu. Ita dai tana rufe a wajen har sai da ya shige sannan ta koma ta buɗe iya fuskarta tabar jikin kawai a rufe, sai dai ta wani ɓata fuska abin dariya..... ___________★ Cikin dauriya da son nuna juriya Huznah ta tashi da azumi, duk da da farko Sageer yace mata idan bazata iya ba ta barshi. Ta dage akan zata iya, jin tace zata iya shima ya sameta yako more da asubar sannan sukai sahur, haushin abinda yay matan ya sata jin sake tsanar cikin. Tana samu ya fita sallar asuba ta saci wayarsa ƙarama ta ɓoye. Koda ya dawo sai ya kwanta a ɗayan ɗakin dan hakan shine samun lafiyarsa. Ba ƙaramin daɗi hakan yayma Huznah ba. Da wannan damar ta saka number Yaseerah cike da fatan samunta, dan bata son kiran ƙannenta wani yaji. Ɗagawa Yaseerah dake cikin ɓacin ran faɗan da suka sha da Abdull akan cikin data samu tayi. Jin Huznah yasata jin mamaki, tace, “Lallai Huznah, shike nan daga yin aure kin manta kowa”. “Humm Yaseerah bazaki gane ba, yanzu ba lokacin kace nace bane tura min numban Mama dan ALLAH”. Da mamaki Yaseerah tace, “Kai kece baki da number ɗin Mama kuma?”. Cikin rawar murya Huznah ta ce, “Ba rasawa nayi ba Yaseerah ƙwace wayata yayi, ni kuma ina son yin waya da wani a cikinsu ko ita ko Ummi, amma na gwada layin Ummi yafi sau a ƙirga bana samu, shiyyasa nake son kiran Mama dan koma minene nasan zata sani”. Sosai al'amarin ya daki zuciyar Yaseerah, amma Huznah ta riga tace mata bata son magana mai tsaho, dan haka ta ce, “Okay bara na tura miki. Amma idan kin gama da Maman dan ALLAH kimin ko flashing ne”. “Ba damuwa”. Kawai Huznah ta faɗa tana yanke wayar. Ko minti ɗaya kuwa ba'a rufa ba sai ga saƙon Yaseerah, jikin Huznah na rawa ta kwashe number a wani littafi ta goge daga massage sannan tai past ɗin wanda tai copy daga massage tai dailing tana shigewa toilet bayan ta murzama ƙofar ɗakin key. Toilet ɗin ma kullesa tayi. Dai-dai nan Maman Yaseerah ta ɗaga kamar a barci take. Kafin ma ta tambayi waye Huznah ta ce, “Mama nice Huznah”. Da sauri Maman Yaseerah ta tashi zaune, ta ce, “Huznah ina kika shige inata neman layinki?”. Kuka Huznah ta sanya mata, kafin ta fara bata labarin komai dake faruwa, tun daga ƙwace wayarta da yayi har zuwa satan tashi da take yi tana kiran Hajiya Basariyya bata samu da maganar ciki daya bayyana jiya. Ba ƙaramar sumar zaune Maman Yaseerah tayi ba, ta ce, “Ciki kuma Huznah yaya akai haka? Sake yarda kikai kika bashi kanki?”. “Mama ya zanyi? Idan ma ban yarda ba ta ƙarfi yake bina wlhy. Wlhy idan naji ko motsinsa ƴan hanjin cikina har kaɗawa suke. Sageer mugune sosai Maama, bar ganinsa shiru-shiru baida kirki da imani”. Ajiyar zuciya Maman Yaseerah ta sauke. Cike da lallashi ta ce, “It's okay! Kukan ya isa haka. Ai idan yasan wata bai san wata ba dan ubansa. Mamanki na katsina ne gidan kawunta.....” Cikin katseta Huznah ta ce, “Na shiga uku Kawu Manu?”. “Shifa! Yayanta ne ya kaita da tsiya-tsiya, amma ki kwantar da hankalinki jiya ta samu wayar yarinyar maƙwafta ta kirani, ta kuma tabbatar min bazata wuce nan da sati ba zata dawo. Kema ki kwantar da hankalinki irin ƴan iskan yaran nan su Sageer ta siyasa ake musu. Ciki dai bazaki haifesa ba dan uban shi, ki cigaba da kwantar masa da kai har ALLAH ya kaimu ya barki zuwa salla zamu san yanda zamuyi da shi, kema kuma kinzo kenan”. Wata wawuyar ajiyar zuciya Huznah ta sauke, ranta fes tace Nagode sosai Mama, ALLAH ya saka miki da alkairi. In sha ALLAHU zan dinga kiranki idan na samu sarari, amma karda ki kira dan zai iya ganewa”. “Babu damuwa in sha ALLAHU”. Daga haka sukai sallama Huznah ta sauke wayar tana murmushi. Gaba ɗaya sai taji kamar an zare mata dukkan damuwar ta ne. Bayin ta buɗe ta fito tana goge kiran da tayi, taje ta cire key ɗin data sakama ƙofar sannan ta koma saman gado ta kwanta....... ___________★ Gab da ƙarasawa lokacin sahur AA ya farka cikin matsanancin yanayi, wannan abune daya saba fuskanta a rayuwarsa tun a farkon girma, amma baya masa tsamari mai wahala kamar na tsakanin nan, musamman kwanaki biyun nan da kusancinsa da Maanal ya zama dab, suna kwana gado ɗaya, su yini tare cikin farin ciki, ta ɗan saki jiki da shi kuma duk da ba kamar asalin yanda suke a baya ba. Yasan duk yanda Maanal zata kai ga tsanarsa, da jin zafinsa dole ne shaƙuwarsu ta baya ta dinga yin tasiri a gareta da karya lagonta koda lokaci-lokaci ne. Balle kuma yarinya ce ƙarama ita har yanzu, zuciyarta bata gama ƙwarin iya riƙe abu ba irin da tsauri ɗin nan, ya taɓa ji a wani hasashen masana a shekarun ƙuruciya ɗan adam yana da rangwamen tasirantar da damuwa ko ɓacin rai wajen girmama shi a zuciya, ko ɓatama mutum rai kayi ko cutar da shi a shekarun ƙuruciya irin daga 15years na fara fahimtar kai da kai zuwa irin 26 to 7 haka wasu ma har 30 zakaga yana da sauƙin zafafa al'amarin, wani ma cikin ƙanƙanin lokaci yake hucewa abin ya wuce a ransa, wani kuma daka dawo ƙyautata masa ko lallashinsa shike nan ya bar abin koda zai dinga tunawa lokaci-lokaci ransa ya ɓaci. Ko ga rayuwar aure mafi yawan mata a shekarun farkon aure basu cika girmama wasu ƙuntatawa na miji ba, watama mijin ne zai mata laifi idan taga yayi fushi zata bashi haƙuri harma ta durƙusa. Amma da an shiga shekarun hankali 30+ in sha ALLAHU ita zata tafka masa tsiyar ta juya masa ƙeya a gado ta barshi da kallon bayanta ko'a kwalar rigarta. Sannan a lokacin ne zakaji a hira tana ai lamarin rijalu sai su, ko kuma namiji ba ɗan goyo bane ba. Kumafa kafin lokaci idan taji wasu na faɗa haushi ma take ji, watama kaji tana bada amsa da nata dai ɗan goyo ne, koda kuwa yana ƙuntata mata a lokacin. To ba komai ke jawo hakan ba sai rashin girmama abu irin na shekarun ƙuruciya. Ya tabba wannan shike ɗawainiya da Maanal. Dan da'ace tunda suka rabu basu haɗuba sai da ta shiga 30+ na shekaru wlhy da yaga rashin mutunci, kuma ko sama da ƙasa zata haɗe bazata yarda su sake rayuwa ba. Amma yanzu 21+ take da, shiyyasa yake iya raunana zuciyarta da canja mata tunani harta shagalta da shi duk da wancan yanayin bai gogu a zuciyarta ba.........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖4️⃣3️⃣ ______________ ........Tunaninsa ya katse saboda wani irin murɗewa da cikinsa ya ƙarayi. Sosai ya dunƙule waje guda yana mai ambaton sunan ALLAH. Wannan yanayin ne ke sashi riƙe kansa da tsiya-tsiya daga taɓata tako wace irin siga, dan ya tabbatar a ƙarshe wahala zai sha, ko kuma ya aikata abinda shi da kansa zai dawo yana ƙalubalantar kansa. Duk fitinarsa bazai iya ƙin biyayya ga iyayensa ba, wlhy koda ace zai cutu ya gwammace hakan. Ya tabbatar Abah bazai hanashi matarsa dan cutarwa ba, idan har zai iya juriya da haƙuri na shekaru, na ƴan kwanki ne zai nuna gazawa.... Dai-dai nan tunaninsa ya sake tsayawa, sakamakon kaɗawar alarm. A hankali Maanal ta fara motsawa, sai kuma ta shiga buɗe ido bakinta da addu'ar tashi a barci. Yau ma a kai da ƙafan suka kwanta, ta kuma jera filos a tsakkiya, dan bayan ta farka a barcin daya figeta saboda matsananciyar kunyar da ya sakata a ciki sai taga AA a gefenta har yayi barci, da alama kuma yayi wankan, tashi tai itama saɗaf-saɗaf zuwa bayi tayi wankan ta canja kaya, ta sake dawowa a hankali ta kwanta bayan ta jera filos ɗin, barci kuwa yay awon gaba da ita dan har yanzu jinsa take sosai. Tana ƙoƙarin tashi zaune idonta ya sauka akan AA daya juya mata baya, amma yanda ya ɗan dunƙule jikinsa kamar ranar sai gabanta ya faɗi, a ranta rayawa take kar dai baida lafiya?. Babu mai bata amsa, bata son kuma yin magana, sai kawai tai ƙoƙarin sauka, bayi ta nufa tana ɗan waiwayensa, harta shiga bai motsa ba. Duk abinda take AA na jinta amma ya daure har sai da ta shiga bayi sannan ya tashi zaune cike da jarumta da juriya. Abin tausayi idanunsa sun wani kaɗe, jijiyiyin kansa sunyi ruɗu-ruɗu. Yana zaune a haka cikin ambaton UBANGIJI Maanal ta fito, ganinsa zaune yasa ta sauke ajiyar zuciya, shima ɗan ɗagowa yay ya kalleta, sai kuma ya janye idanun dan wani irin ji yay kamar an dakar masa kai da hama sakamakon saukar idanunsa akanta. Wani irin ƙyau kayan barcin data saka sukai mata, duk da bawani sun matseta bane kasancewarsu masu santsi sun kwanta mata a jiki luf. Tana zama ya miƙe, batare daya sake kallonta ba ya wuce bayi dan baya so taga halin da yake a ciki. Yafi mintuna goma a bayin sannan ya fito, Maanal bata yarda ta kallesa ba sam, duk da bata kawo a ranta ma wanka zai yi ba. Shima yaji daɗin ƙin kallon nasa da batai ba, jallabiya ya ɗauka ya koma ta bayanta ya saka ya zame bathrobe ɗin. Sai da ya ɗauka maganinsa ya sha yana addu'a a ransa ALLAH ya taimakesa ya samu natsuwa sannan ya juya a karo na farko ya mata magana... Kallonsa ta ɗanyi itama, dan yanda taji muryarsa kamar mai mura sai da zuciyarta ta tsarga. “Baka da lafiya ne?”. “Mi kika gani?”. Kanta ta girgiza masa kawai, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya da faɗin, “Ba komai”. Shima numfashin ya ɗan furzar, cikin son kauda yanayin yace tazo suyi sahur barci yake ji, gashi fitar wuri zasu yau. Komai bata sake cemasa ba tazo ta zauna. Daga ita har shi basu wani ci abin kirki ba, dan kowa da abinda ya damesa. Shine ya fara tashi yaje bayi ya sake yin brush yayo alwala. A mamakinta maimakon kwanciyar da yace zai yi sai taga yayi salla raka'a biyu ya ɗauka Alkur'aninta ya fara karatu, gashi sai wani sauke ajiyar zuciya yake a jajjare. Itama dai gyara wajen tayi taje tai brush ɗin tayo alwalan.... Kamar yanda ya faɗa da wuri suka fita yau, sai dai fa sam baya a cikin walwala. Companyn jiya suka koma, shi baima shiga ba, a mota suka barshi yace mata zaije wani waje ne. Kai kawai ta jinjina masa da masa addu'a dan ta fahimci yau ƴan miskilan ne a ka. Alhamdullah yau ma sun samu ilimi sosai dan komai an musu ne a bayyane practical. A rai Maanal na jinjina mutanen nan da halayyarsu, sam babu mugunta a tare dasu. Baƙar fata ne zai iya abu ya koya maka cikin sauƙi harda wasu sirrika nashi tab ɗin. Duk da ta fahimci AA nada babbar alaƙa da companyn ne amma ta jinjinama halaccinsu. Dan ta fahimci hakkane a lokacin da idannunta ya sauka a hotunan dake manne a wani office da suka shiga na mutane goma harda hoton AA. Al'amarin nata mata kai-kawo a rai amma ta rasa yanda zata tambaya. Yau sunfi jiya daɗewa anan, suna fitowa kuma masauki aka maida su. Ita kaɗai Mr Li ya ɗakko, koda ta tambayesa AA sai ya sanar mata suna meeting ne. Bata tambayesa meeting ɗin mi ba kawai tai shiru. Har ɗakinsu yay mata rakkiya da kayayyakin da bata san na miye ba. Tana shiga ta sauke ajiyar zuciya tare da cire kaya tayo wanka ta fito tai sallar azhar da taga lokacinta yayi. Sosai take jin kewar su Ammie, dan haka ta jawo wayarta data koma bata da amfani, dan in tace ma tayi magana dasu ta net bata da data. Haƙura tai ta kwanta kawai, sai ko barci mai nauyi yayi awan gaba da ita. Bata farka ba sai la'asar, tana mamakin yanda lokaci ke gudu anan, abu kamar ba azumi akeba. ALLAH musulman ƙasar nan suna cin ɓagas. Tayi Asr ta zauna taita karatun Alkur'ani. Wajen shida saura akai knocking ƙofa, tashi tai da tunanin ko AA ne. Amma koda ta buɗe sai taga Mr Li. Gaisheta yay tare da sanar mata ta shirya zasu fita. Ɗan jimm tai, sai kuma ta tambayesa AA ya sani. Amsa ya bata da ai shine ma yace azo a ɗaukesu su duka. Ajiyar zuciya ta sauke, ta koma ciki ta hau kimtsawa. Abaya ta saka mai laushi da ƙyau fara tas, ta ɗan gyara fiskarta ta ɗauka handbag ta fito. Tana isowa motarsu Yaqub na wucewa, Mr Li ya buɗe mata itama ta shiga yaja suka fice a hotel ɗin. Tafiyar ba wata mai nisa bace sosai suka iso wani waje mai ƙyau. Ko ina tarwai da haske tamkar rana. Tana fitowa a mota idannunta suka sauka akan AA dake tsaye hannunsa ɗaya a aljihu ɗayan riƙe da waya yana latsawa, shigarsa ce dai ta safe sai dai yanzu akwai coat a sama, har yanzu fuskarsa babu walwala. Koda ya ɗago idanunsa yana kallonta sai taji wani iri dan idanunsa har yanzu basu washe ba. Takowa yay cike da ƙasaitarsa da nutsuwa zuwa gabanta, dan ta tsaya cak ne tana kallonsa. Dab da ita yaja ya tsaya, kallonta kuma yake ƙurr.. Nata idanun ta risinar tare da faɗin, “Ina yini”. Maimakon amsawa a ƙasan maƙoshi yace mata, “How are you?”. “Alhamdullah”.. Ta faɗa itama a taƙaice. Bai sake cewa komai ba yay gaba, binsa a baya tayi, sai kuma ya dai-daita tafiyarsu suka shiga a jere. Wani keɓantaccen waje suka shiga, an gyara wajen sosai anyi shimfiɗu an jera abinci da alama na buɗa bakinsu ne. Kallonta yay a karo na biyu sai kuma ya matso dab da ita ya kama haɓarta yana kallon ƙyaƙyawar fuskarta, ƙasa tayi da nata idanun. Ajiyar zuciya ya ɗan sauke, cike da kulawa ya furta, “Mike damun ki? Duk kinyi sukuku ko azumin ne?”. Kanta ta ɗan girgiza masa alamar a'a, sai kuma a hankali ta motsa lips ɗinta murya cike da sanyi ta ce, “Barci bai isheni ba”. Sake riƙe fuskarta yay sosai yanzu kam da hannu biyu, shima a maƙoshi ya ce, “Sorry my Babie. Ba zamu jimaba ai, muna yin salla sai na maidaki ki kwanta okay”. Kanta ta jinjina masa fuskarta na wani shagwaɓewa. Yanda tai ɗin sai ya sashi sauke ajiyar zuciya, cike da tsokana sai dai fuskarsa babu wani alamar wasa ya ce, “Karfa a dinga fakar idona ana karya azumin nan”. Karan farko Maanal ta waro idannunta sosai a kansa kamar yanda yara keyi idan abun ya basu mamaki, da ɗan karsashi ta ce, “Lah nice kuma zan karya azumi? Nafa girma”. Shima idanun ya ɗan waro waje kamar yanda tayi, sai kuma cikin raɗa ya furta, “Lah na manta ashe half ɗin Ajwaad ta girma ta zama ammatansa yanzu. Na fara shirin zama ango kenan?”. Kifa kanta tai a ƙirjinsa dan maganar ta bata kunya, musamman a yanda ya furta yana wani ƙanƙance idanu. Shima sai ya murmusa zuciyarsa cike da shauƙi. Fin minti ɗaya suna a haka kafin ya ɗagota tare da furta, “Kina da alwala ne?”. Kanta ta jinjina masa alamar eh. Shima sai bai sake cewa komai ba ya nufi wajen da kayan abincin suke ya ɗakko goran ruwa da ɗan bowl dake cike da dabino ya dawo wajan. Handbag ɗinta ya amsa ya ajiye a table ɗin kusa da su, sannan yay mata nuni da kujerar gaban table ɗin. Babu musu ta kai zaune, shima ya zauna a wadda take facing nata. Ruwan ya ɗauka ya kuskure baki itama ya bata, ya ɗauka dabino ya gutsira rabi ya kai rabin bakinta. “Wai ansha ruwa ne?”. “A'a zamu karya namu ne”. Ya faɗa cikin yanayin tsokana yana tsareta da idanunsa masu laushi. Sai baƙar maganar ta bata dariya. A cikin maƙoshi tayi murmushi sannan ta riƙe hannunsa suka saka dabinon a bakinta tare, itama ɗauka tayi ta kai bakinsa. “Fara ci”. Ya faɗa a sauƙaƙe. Kanta ta ɗan girgiza, “Kai ne babba ai”. Har cikin ransa yaji daɗin abinda ta faɗa, dan haka ya murmusa kaɗan yana kamo hannun nata shima ya gutsira rabin dabinon, cike da kulawa yace, “ALLAH yaya miki albarka! Barka da shan ruwa”. A saman lips ta amsa da amin tana ɗan murmushi da saka sauran dabinon a bakinta. Irin wannan yanayin kan karya mata zuciya matuƙa, takan ji abin da girma ta yanda har zuciyarta ke raunana taji anya zata iya aiwatar da shawarar su Didi a kansa. Sai dai wani gefe na zuciyarta kan kwaɓeta da gargaɗarta da tuna mata rayuwar da suka tsinta kansu a ciki bayan faruwar komai sai yaji ina.........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖4️⃣4️⃣ ______________ .......Miƙa mata ruwa da yay ne ya katse mata tunaninta, sai ta sauke ɓoyayyan nunfashi kawai ta amsa. Sun sha ruwa sannan ya miƙe yana faɗin, “Muje yin salla suna jiranmu”. A mamakin Maanal ta wata hanyar daban suka fito, sai taga masallaci madaidaici a wajen. A ranta tace wai ina yake samo irin wajajen nan? Dama akwai musulmai a Chaina kamar haka. A ƙarshen bango taga CFO, dan haka ta nufi inda take, ba'a kiran salla a massalacin, sannan ba'a salla da mic. Sai suka bata tausayi, amma koma miye UBANGIJIN da suke ibadar dan shi mai ji ne da ganine a kowane irin yanayi. Basu da yawa sosai, kusan ma zatace sune suka cika massalacin. Sunyi sallar magrib sannan suka fito. Wajen nan da AA ya fara kaita suka koma. Ganin yanda CFO keta shareta cikin kame kai itama sai ta watsar da ita, an gaggaisa da yima juna barka da shan ruwa suka zazauna. AA na kusa da ita, da kuma kansa ya zuba musu abinci ita da shi, ita dai duk sai ta jita a takure, shima ɗin bada wani sakewa yake cin abincin ba. Suko su AS kwasar girki suke hankali kwance duk da suna jin nauyin AA ɗin. Ita da shine suka fara tashi, dan haka sai ya jata kawai suka fito a wajen. Waje suka samu suka zauna, ya ɗan tsareta da idanu. “Mike damunki? Ko har yanzu barci ne?”. Kanta ta girgiza masa, sai kuma cike da shagwaɓa ta ce, “Ina jin kewar su Ammie, tunda muka zo banyi waya da su ba. Ko barka da shan ruwa ban musu ba”. Nauyinta yaji akan hakan. Dan shima ya fahimci bai kyauta ba, shi ya kira iyayensa sun gaisa amma ita bai kira nata ba. Duk da har ga ALLAH yayi niyyar yin hakan shafa'a yayi. Ƙasa-ƙasa ya ce, “I'm sorry”. Batace komai ba shima sai yay shiru. Cikar lokaci sallah ya sakasu tashi. Sunyi isha'i da asham. Koda suka fito anan suka bar su AS, shi da ita suka wuce, wani gidan abinci mai shegen ƙyau suka isa, ganin an saka halal ya sata sauke ajiyar zuciya. Abinci aka shirya musu na gani na faɗa, anan kam cike da kulawa ya rinjaye ta sukaci suka ƙoshi. Basu koma hotel nasu ba sai kusan ɗaya na dare. Shi kam a gajiye yake fiye da ita, dan haka yana kwanciya sai barci. Dama haka yake so shiyyasa yaba kansa wahala da zirga-zirga ko zai samu raguwar kusancin zamansu a tare idan sun dawo makwanci. Saboda shi kaɗai yasan abinda yake fuskanta a jikinsa da wannan zaman waje ɗayan nasu. Ya kuma fara fahimtar gangar jikinsa so take taƙi bashi haɗin kai bisa shirinsa...... _________★ 9-Ramadhan. A yau ɗaukacin musulmai suka kai azumi na tara-tara a wasu ƙasashe, wasu kuma na ƙoƙarin ƙarisa kaiwa irinsu Maanal dake a Chaina. Yau gaba ɗaya a busy suke, dan sunata shirin komawa ƙasarsu ta haihuwa. Babu abinda Maanal zatace da UBANGIJI sai godiya a kwanakin nan, domin kuwa ta ƙaru da abubuwa masu yawan gaske. Irin siyayyar da AA yayi mata har tsoro abin ya bata, wai iyaka ma wanda ta gani kenan. Dan bata sani ba ma ya tura wasu kayan Nigeria kusan kwana uku kenan. Duk da daɗi da Chaina tai mata hakan bai hanata jin ɗokin komawarsu gida ba. Dan tayi kewar kowa da Kowa. Duk da zuwa yanzu hatta su Ammie duk tana waya da su... A ɓangaren AA kuwa a matuƙar takure da azabtuwa yay kwanakin nan. Shi kaɗai yasan ɗunbin yaƙin da yay da kansa wajen kauda ido ga Maanal a tsakanin nan. Sai kuma azumi daya sake taimakawa ya zame masa garkuwa. Rashin walwalarsa a bayyane take, sai dai hakan bai hanashi bama Maanal kulawa mai tsayawa a rai da zuciya ba wadda shi kansa ya fahimci ta sakata ƙara zama mai laushi, shaƙuwarsu kuma nata dawowa kamar da duk da bawai tana sakin jikinta bane kamar da ɗin yanda ya kamata. Dan wataran idan ta miskile masa ma har mamakinta yake. Badan yana kewar iyayensa ba da ita kaɗai zai tura Nigeria shi kam sai bayan salla ya koma dai-dai sanda Abah ɗin ya yarda zai bashi matarsa. Haka dai ya daure yay musu shiri yanda ya kamata. A gajiye sosai suka koma hotel ɗinsu, dan sunje ƙarasa wasu yan abubuwa ne da suka rage. Kasancewar ya tsaya suna magana da CMO a waje ita kaɗai ta shige ɗaki, gudu-gudu ta hau zame kaya da planing ɗin shiga wanka kafin ya shigo. Dan harta fiddo kayan da zata canja a bayin kamar yanda take yi. A bazata kawai ta ɗaga riga zata cire bawan ALLAH ya shigo. Daburcewa tayi gaba ɗaya, ga rigar taƙi fita hasalima ta maƙale mata ɗan kunne dan atamface ga style ɗin ɗinkin wuyan irin ƙaramin nan ne. Faɗin rigar kuma yasa ba'a saka mata zip ba. Cak AA yaja ya tsaya ƙirjinsa na wani dokawa da sauri-sauri. Ji yay kamar ya juya ya koma, sai dai kuma yanda take kicin-kicin yasan zata iya buguwa da wani abun. Gashi ta gagara cire rigar, jikinta kuwa har rawa yake. Kamar wanda aka saluɓewa kuzari ya shiga takawa a slowly, yana zuwa dai-dai gabanta ya tsaya, dai-dai ta ɗan sake duƙewa ta ɗago cikin nasara ta zare kunneta ɗaya daya riƙe, motsawar da zatai kawai tai karo da mutum. Cak ta tsaya zuciyarta na mata gudu a ƙirji, sai taji hawaye ma sun cika mata ido. Dan tasan ya ma riga ya gama kalleta daga ita sai b&p tunda tayi sama da rigar ne gaba ɗaya. A bazata kuwa, matuƙar bazata taji saukar lallausan hannunsa a saman ƙugunta, kafin a hankali ya shiga matsar da shi har zuwa gadon bayanta ya zagayosa ta ɗayan gefen cikinta. Matsota yay ta manne da jikinsa. Ji tai ta ƙara daburcewa, shi kansa zuciyarsa tsitstsinkewa take, dan wannan shine na farko da yake ganinta a haka. Koma yace yake ganin mace a haka a gabansa. Tuni idanun ƴan maza sun juye cikin ƙanƙanin lokaci, sai faman taunar lips yake tamkar zai hudasu da haƙora. Hannunta da take ƙoƙarin turesa ya riƙe, sai ya maida shi baya ya riƙe a hannunsa dake gadon bayanta. Ɗayan kuma ya shiga zare mata rigar jinin jikinsa na narkewa. Rigar na gama fita Maanal tai ƙoƙarin duƙewa, cak ya kamota gaba ɗaya ya tsayar akan ƙafafunta, kafin ya fara tafiya da ita sannu-sannu suka dangane da bango. Bata daina ƙoƙarin turesa ba, ga jikinta na rawa hawaye na gangarowa, sai dai ta kasa magana. Jin ya manneta da bango sai kawai ta kife a jikinsa dan bata da wani zaɓin daya wuce yin hakan. Hawayenta yaji suna sauka a ƙirjinsa duk da akwai riga a tare da shi. Sake rikicewa gangar jikinsa tayi, sai ya dinga jin kamar bazai iya riƙe kansa ba yau. Kamar bazai iya haƙuri da juriyar daya ɗauka ɗammara ba. Kamar bazai iya riƙe alƙawarin Abah ba. Tabbas bazai iya ba, dan kuwa cikin yamutsewar tunani ya kai fuskarsa cikin wuyanta ya fara bata sumba masu zafi da shinshinar wajen yana busa mata numfashinsa. Ƙoƙarin ɗagowa datai a rikice zatai magana ya bashi damar riƙe lips ɗinta cikin nashi. Harga ALLAH Maanal bata taɓa tsorata da shi irin yau ba, dan kuwa a karo na farko hannunsa ya sauka a inda wani mahaluki bai taɓa kaiwa ba koda Ammie ko ƴan uwanta, dan ita ko kaya kunyar sakawa take a gaban Ammie, kai tunda tai hankali wlhy b ɗinta idan ta wanke bata yarda ta shanya inda wani zai ganin mata. Dama su Didi ke siya mata, suma sun san yanda take jin kunya sai su saka mata a cikin kaya bawai su bata hannu da hannu ba, ita kanta kunyar kanta take ji ta yanda koda wasa bata taɓa tsayawa gaban mirror ta kalla jikinta ba. Sosai taji mahaukaciyar gigita mai tarwatsa brain, ga azabar yanda yake mata na ratsata. Cikin sa'a ta ƙwace bakinta saboda yanayin da yake a ciki ƙarfinsa ya fara sanyi, amma inba hakan ba wane ita, ko a fuska ka kalla AA kasan a wajen mazan ma bazai daku ba balle ita ƴar tamatsitsi. Roƙonsa ta shiga yi cikin kuka har tana roƙonsa dan girman ALLAH yayi jaƙuri. Jin yaƙi sakinta ta koma tabbatar masa wlhy in bai bartaba bazata taɓa ta yafe masa ba.... “Kinji nace ki yafe min ne daman?”. Ya faɗa murya a shaƙe yana ɗagata cak zuwa gadon. Ina Maanal fa ta fahimci yau sai ta ALLAH wlhy, aifa jikinta ya shiga rawa ganin yana zame tufafinsa, gashi ya riƙeta da hannu ɗaya kawai amma ta kasa motsi. Sai ta shiga magiya da roƙo da ban haƙuri tana haɗashi da girman ALLAH. Abun yazo mata a bazata ne shiyyasa ta gigice. Gefe kuma zuciyarta na tuna mata wata rana data shuɗe, ranar da bazata taɓa goguwa a brain ɗinta da tarihin rayuwar su ba har abada. Dan ta zame musu tamkar tabo ne mai barin tambari a fuska na har abada. Wani gefe kuma nasihar likita da yace mata ta daina tsorata, tarayya da namiji ba mutuwa bace ba... Cikin shiɗewar kuka da sallamawa idannunta a rumtse ganin ya gama zare kayansa gaba ɗaya bakinta na rawa ga hawaye wasu na bin wasu ta ce, “Shike nan Ajwaad! Shike nan kayi duk yanda kaso, ai dama basan kana ɗaukata ne kamar wata dabba mara daraja, tunda ma ka iya keta min haddi a shekarun da ban wuce sha biyar ba taya zaka jini a yanzu, ta yaya! Ta yaya zaka jini. Wlhy tsoro nake ji! Tsoro nake ji Yaya Ajwaad ka taimaka min na tuba! Na tuba dan ALLAH kada ka aikata min komai!!”. Ai cak AA ya tsaya daga yunƙurin sake haɗe lips ɗinsu da yake yi, dan maiba wani ji kalamanta na farko ba balle su masa tasiri, amma kalmar _(Wlhy tsoro nake ji! Tsoro nake ji Yaya Ajwaad ka taimaka min na tuba! Na tuba dan ALLAH kada ka aikata min komai)_ har cikin tsakkiyar kansa suka dinga zirarawa kamar ana buga ƙusa a cikin bango, zuciyarsa ta wani shiga rartabewa gida daban-daban saboda wani tausayinta daya ratsashi, dan jikinta rawa yake sosai. Gaba ɗaya abinda yake ji a jikinsa komai ya tsaya kamar an daka musu tsawa. Jikinsa da ya ɗauka wani kalar ɗumin zazzaɓi lokaci guda ya janye daga nata, sauka yay a gadon gaba ɗaya, gaba ɗaya ji yake ɗakinma na juya masa, kalamanta na sake maimaita kansu a kunnensa cikin amsa kuwwa. Da ƙyar ya iya kai kansa bayi, baima san a yaya ya rufe ƙofar ba kawai ya tsinta kansa ne a ƙarƙashin shower..........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖4️⃣5️⃣ ______________ .......Maanal kam tunda ya raba jikinsa da nata taja duvet cikin rawar jiki ta duƙunƙune kanta waje guda, sosai jikin nata ke rawa. Ga hannunsa da take ji har yanzu a jikinta, ga wajen na mata wani irin zugi dan baiyi mata da wasa ba. Kuka take irin wanda ita kanta bata san na minene ba. Sai dai wani gefe na zuciyarta sai maimaita mata kalman roƙon da take masa tana kiran cikakken sunansa yau harda su Yaya. Ita kanta kalaman dariya suke bata yanzu, tare da jin kamar bazata iya sake haɗa ido da shi ba. Amma yaya zatayi? Wannan itace kawai hanyar kuɓuta daga garesa, tabbas taji bata so aurensu ba a randa aka ɗaura, badan komai ba sai dan cika bakin da yay mata a asibiti, amma halin daya tsinta kansa na kusan mutuwa ya lausasa mata zuciya har taji ita wacece da wani zai rasa rayuwarsa a kanta, ai kamar tayima UBANGIJI butulci ne da ni'imomin daya bata kashi-kashi na rayuwa, kamar ta nuna masa bata amshi jarabawarta da hannu biyu ba, tunda tasan ƙulluwar auren ikonsa ne ba wani shiri ba. Na biyu nasihar mahaifiyarta da Daddy da Nene da hujjojin da suka kawo mata akan aurenta da Ajwaad shine rufin asirinta da su kansu musamman yanda zancen ya fara fita a lokacin bikin Ya Yazeed shima ya taka rawar gani wajen haƙura ta amshi auren batare da yin wani bore ba bayan wanda tayi. Sai dai tuna zuwan irin wannan ranar na tayar mata da hankali, na sakata jin tsoro da ɗunbin fargabar da jin anya zata iya yin biyayya ta bashi kanta kuwa. Dan wannan shi kaɗai ne hope ɗin daya rage mata wajen hukunta Ajwaad tsakanin ita da shi kamar yanda su Didi suka tabbatar mata. Dan sun nuna mata suma tabi maganar su Ammie, ta kwantar da hankalinta koda mutunci da darajar Abah da Oum. Itama ta zama jaruma yanda ya share ya nuna kamar komai bai taɓa faruwa ba ta biye masa itama suyi pretending ɗin tare, idan sun kasance a irin wannan gaɓar sai ta hukuntashi dai-dai da laifinsa har sai ya sauke nasa girman kan ya nema gafararta da afuwarta a sigar da ita kanta zataji ta gamsu da hakan sannan ta sallama. Ko a randa ta samu damar faɗama Didi Shahidah abinda taji akan Mamy ta girgiza, ta kuma tabbatar mata to lallai akwai wani abu da ya kamata su sani kenan, a hakan ma dan bata sanar mata wanda taji Mamyn na faɗama Ajwaad ɗin ba fa. Amma kalamansa na ranar sun raunanata, sun karya mata zuciya da duk wani burin horashi yanzu tausayi yake bata kawai... AA ya jima sosai a bayin sannan ya fito, ko inda Maanal take bai kalla ba, dan ya tabbatar in yay hakan duk yanda yake jinsa a dauriya ALLAH sai ya mata fata-fata. Magungunansa da suka rage saura ya ɗauka yasha, daga haka ya koma ya kwanta batare da ya cire bathrobe ɗin jikinsa ba. Duk abinda yake kuma Maanal na jinsa, amma ta daure tai shiru, sai zuwa can ta miƙe dan jin alarm ya sake bugawa alamar lokacin gama sahur na gab da fita. Bayi taje tayo wanka itama, batare daya kalla abin sahur ɗin nasu ba ta ɗauka ruwa kawai tasha, dai-dai nan ya tashi shima daga kwanciyar da yay, sai taji kamar ta zura a guje, amma dai ta dake saboda sanin lokaci ya ceceta. Aiko shi sai baima kalleta ba, bathrobe ɗin ya zare ya ajiye, ya saka jallabiya ya tada salla. Itama sai kawai ta koma daga bayansa ta ɗauka Alkur'ani ta hau karatu. Suna a wajen har lokacin sallar asuba yayi ya jasu salla kamar yanda ya saba, kowannensu yay azkar. Batare daya kallesa ba tace, “Ina kwana”. Fuuuu ya wuceta batare daya amsa ba, itama sai ta taɓe baki. Gadon ya koma ya kwanta, dan tafiyar tasu ma sai 2pm ne. Itama sai tai kwanciyarta a sallayar kawai ta ƙudundune da hijjab ɗinta.... 12pm Ita ta fara farkawa, ta ɗan kalla gadon inda yake a kwance. Rufe yake da duvet har kansa, sai taji gabanta ya faɗi dan kasancewar bedsheet ɗin fari ƙal sai yay like gawa. Da sauri ta ture mummunan tunanin ta wuce bayi, wanka ta farayi ta fito bayan ta saka kaya daga can, ta gyara jikinta sama-sama ta kabbara nafila, tana cikin yi ya farka shima. Alhamdullah yana jinsa da sauƙi babu ƙullewar mara, kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kai, bayi ya shiga, sai kuma gashi ya fito lokacin tana tahiya. Kaf kayansu da suke da datti ya tattare harda underwear ya shiga da su bayin, a washing machine ya zubasu ya haɗa ruwan sabulai dake ajiye a bayin a ciki masu daɗin ƙamshi sannan ya kunna. Yana a tsayen har machine ɗin ya kashe kansa sannan ya shiga fiddosu ɗaya bayan ɗaya yana matsewa, sai da ya kammala tas ya sake ɗaurayewa sannan ya zuba a dryer dake a machine ɗin ta busar. Sannan ya fara wanka.... Maanal na zaune tana addu'a ta idar da salla ya fito da kayan a hannu. Mamaki ya kamata, dan tunda suka zo ita ke wanke musu. Sai dai batace komai ba ya ajiyesu inda akwatinsu yake sannan yay shiri kan Maanal a ƙasa harya saka jallabiya. Salla ya kabbara shima. Kasancewar ita ta idar sai ta miƙe zuwa wajen kayan nasu ta fara shiryawa, suka ɗai suka rage, duk wata siyayyarsu ya riga ya turata gida, tsaf ta kammala shiryawa kayan data ajiye masa dan ya sanya na gefe, ta shiga bayi ta sake duba komai nasu ta tattaro dan kar suyi mantuwa. Shima daya idar da sallar ba zama yay ba, shiryawa ya farayi a kayan data ajiye masa, hakan yasa ta koma gefe kanta a ƙasa harya kammala. Fita yayi daga ɗakin, ta ɗan bisa da kallo ƙasan ido, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya tana taɓe baki, daga haka ta maida hankalinta ga kallon tv. Fin mintuna ashirin sai gashi ya dawo, a wani ciki-ciki yace, “Muje” Yana kama hannun trolling bag ɗinsu da handbag ɗinta data ɗaura akai, zai ɗauka bag ɗin laptop ɗinsa ta rigashi ɗauka. A karo na farko suka kalla juna cikin ido, sai kuma kowa ya janye cike da basarwa suka fice.... Sosai Maanal ke jin kewar barin Shanghai, amma kuma tana matuƙar ɗokin komawa ƙasar haihuwarta. Ba wata tafiya mai nisa bace ta kawosu airport, bayan ƴan kunji-kunji na tsarabe-tsaraben tafiya a jirgi suka shige suka bar su Mr Li da kewarsu. Su duka su kowa yayi fresh abinsa, musamman ma mutuniyar taku da angonta. Dan ƴan kwanakin nan a Chaina kwanaki ne masu ɗunbin tarihi da suka taka rawar goge abubuwa masu yawan gaske a zukatansu musamman ga Maanal. Sosai ta ɗan rage jin zafinsa dake ƙasan zuciyarta, ta kuma sake fahimtar halayyen sabon Bestyn ta a yanzu. Shima dai hakan take, ya sake fahimtar abubuwa da yawa game da ita a yanzu. Sannan ya mata uziri akan abubuwa da yawa domin UBANGIJI ne kaɗai masanin gaibu. Kuma ko shine a matsayinta abinda zai yi kenan. Ya tabbata da ace su Maanal nada wani yaya namiji ba lallai ma ya yarda a sake bashi aurenta ba... A wannan karon ma dai ta Qatar suka koma, tafiyar kuma ta ɗauki sabon salo a tsakaninsu ba kamar a zuwa ba. A vip section suke kamar wancan karon, sai dai kowa ya nema wajen zamansa suka ƙi zama da juna. Alkur'ani Maanal ta ɗauka taita karatu ma abinta har suka iso Qatar, dan duk da tanata hamma haka ta jure. Sunyi canjin jirgi yau ma, kuma Alhamdullah kamar a wancan karon ne babu jira. Baccin da yaci ƙarfin Maanal yasa ta kai kwance, sai lokacin shi kuma AA daketa aiki a laptop tunda suka taho ya samu damar zaman nasa karatun Alkur'anin bayan ya lulluɓa mata mayafi. Shima dai zuwa can barcin yaci ƙarfinsa sai ya ajiye Alkur'anin ya kwanta. Su duka basu farka ba sai da aka fara sanar da sauran mintinan da suka rage jirgi ya taɓa ƙasa..... Alhamdullah sun sauka ƙasarsu ta haihuwa lafiya a cikin birnin Abuja. Kowa ka gani a cikinsu yay laushi, marasa juriya ma tuni sun karya azuminsu a hanya. Wanda basu karya ba irin su Maanal ganin safiya a Nigeria ne sai da suka girgiza, dan ƙarfe 7:30 na safe suka iso. Tab ɗin babbar magana, ga azumin awa kusan 15 a bakinsu. Wannan fa shi ake kira dare biyu. Manaal dake satar kallon AA sai taga ma shi daras yake mutumin nan babu wani rauni a tare da shi, suko duk sunyi yaushi abin tausayi. Cike da girmamawa su AS sukai musu sallama suka nufi motar company da zata kwashesu takai kowa gida. Sun fito suma da shirin hawa taxi sukaci karo da Ya Fawzan, RK, da Najma sunzo ɗaukarsu. Cak AA ya tsaya yana kallon RK, shima dai kallon nasa yake yana haɗiye murmushi da ƙyar, a ransa yana faɗin (Dole ne mu tsaida wannan wasan ɓuyan haka Ajwaad) a zahiri kam sai ya nufoshi dan Yaya Fawzan na waya. Najma ma da gudu ta sheƙo ta ɗane Maanal suna murna, ai take Maanal taji duk wata gajiyarta da kasala ta ware a jikinta, ta ji daɗin ganin Najma a Abuja matuƙa gaya duk da dama sun gaisa kusan sau uku. Sai dai kuma ganin RK ya wani saka gabanta bugawa, amma ta dake abinta tana ambaton sunan ALLAH. Dai-dai nan Ya Fawzan ya iso wajen, RK kuma ya rungume AA. Abinka da maza, shima AA ɗin sai ya basar kawai, har yana ɗan hararar RK dake faɗin, “Ƴan gayu, honeymoon da azumi, abin naka azimun Oum's boy”. Harararsa AA yayi, dai-dai shima Ya Fawzan na nako masa nasa sherin. Shima harararsa yayi, suka kwashe da dariya suna tafawa. Kafin su juya ga Maanal dake gaishesu a tare, dan taƙi yarda ta kalla sashen RK sam. RK bai damu ba, dan yasan dole su kasance a ƴar hakan kafin su saki jiki da juna kuma. Itama tsokanarta Fawzan ya fara, ta shiga ɓoye kanta a jikin Najma dake musu dariya.........✍️ To mun dawo NIGERIA, kowa yazo ya amshi tsarabar sa.💃💃🏃🏃🏃 *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖4️⃣6️⃣ ______________ ........Mota suka nufa, RK driver Ya Fawzan kusa da shi, AA ya shiga baya Maanal a tsakkiya kusa da shi Najma a gefenta. Tafiyar mintoci da bata kai awa ba ta kawosu gida, sun sami ko'ina shiru dan kowa na barci, Oum ce ma kawai tasan da fitarsu tarbo su AA ɗin dan RK ma a gidan ya kwana yau. Ma'aikatan gidan ne kawai dake gyare-gyare ke kai kawo, aiko motar na tsayawa suka iso suna musu barka da zuwa cike da farin ciki, ba'a dangi kawai ba hatta masu musu hidima ALLAH ya saka musu soyayyar AA a zuciya, ba komai kuma ya kawo hakan ba sai kasancewar sa mutum mai alkairi da sauƙaƙawa. Bai da yawan magana, da wahala ka ganshi a sabgar da ba tashi ba, amma mutum ne mai sauƙi gana ƙasa da shi. Ƙyawawan halayyarsa harga wanda ba musulman ba a bayyane take, dan yana iya ƙoƙarin sa wajen kamanta musu iya hurumin da UBANGIJI ya umarce mu yi a garesu. Tuni sun wuce sashen Oum, dan duk inda AA zaije a rayuwa ya dawo sai ya fara dangana da Oum sannan wani ya gansa a gidan, sai dai idan anyi sa'a ya samesu a tare ne. Duk da sashen a cike yake da ƴan hutu ko'ina a tsaftace yake su Inte sun gyara sun saka turaren wuta da air freshener masu sanyin daɗi kamar ba safiya ba. Dan har yanzu bai wuce tara na safe ba. Nan ɗin ma dai shiru dan samarin yaran dake a ƙasan barci suke yi. Su duka sama suka haura, hakan yay dai-dai da fitowar Oum daga bedroom hannunta riƙe da kaskon turare. Ina ai da gudu Maanal ta nufeta ta rungume, AA ma da yaji bazai iya haƙura sai Maanal ta gama nata ba haɗawa yay ita da Oum ɗin ya rungume. Aiko mi su RK zasuyi ba dariya ba. Tuni farin ciki yasa idanun Oum tara hawaye, wlhy ita kanta bata san irin ƙaunar da takema yaran nan ba, Ajwaad da Maanal daban suke a zuciyarta, tana jinsu ƙololuwa a ranta ta yanda ita kanta bata san ta yanda zata musalta irin soyayyar da takema yaran ba. Duk da gidan cike yake da zuri'arta zuciyarta cike take da kewarsu kawai tana daurewa ne. Sun jima a haka kafin ta ɗagosu, tare da kai hannu a tare ta shafa fuskokinsu tana murmushi. A tare suka risina domin gaisheta, sai kuma suka kalla juna dan yanda sukai ɗin abin yazo musu ne a bazata, murmushi sukayi ma juna kamar yanda Oum ke murmushin, su Yaya Fawzan kuwa na dariya. Fawzan harda juyawa ya kalla Najma ya ɗan ɗaga mata gira, ƙasa ta duƙar da kanta tana murmushi. RK godiya yakema ALLAH a zuciyarsa da bai zama sanadin raba wannan ƙauna mai ƙarfi ba, dan tabbas ya ƙara yarda Maanal sai Ajwaad, Ajwaad sai Maanal. Wannan haɗin ALLAH sai dai a bisu da ƙyaƙyƙyawar addu'a kawai. Ƴar hayaniyar ce ta tada yaran suka shiga fitowa a jere. Wayyo zokaga ihun murnar ganin su Yaya AA sun dawo. AA akwai farin jini kam Masha ALLAH. Rungume Maanal suka shigayi kowa na mamakin canjawar ɗan uwansa, kafin su shiga gaishe da AA dake kallon su kawai a dakensa dan ba sabgarsu yake shiga ba, baya sake musu fuska, amma a hakan sonshi suke dan shi mai alkairi ne a garesu, rashin yawan magana kuwa kowa yasan ɗabi'arsa ce shi da babban Yaya da ma wasu a yaran family ɗin da suka gado su. Tuni suma samarin suka shiga haurowa, sukam ai rungume AA ɗin suke, karan farko yay musu murmushi, yana binsu ɗai-ɗai ya shafa kansu. Fahimtar yanda sukai laushi yasa Oum tambayarsu suna azumi. Maanal ce ta amsa da eh, Oum tai mamaki ƙwarai da gaske, tare da jinjina ƙoƙarinsu dan awannin da yawa ai. Jin hakan tace to abarsu suje su watsa ruwa su kwanta su huta. Hakan kuwa akai, AA ya fito zuwa sashensa, yasan dai su Mamy na barci har ma Abah da su Babban Yaya. Maanal kuwa ɗakin Oum ta shige tunda dama anan take. Yaran kuma Oum ta kaɗasu suje suyi wanka lokacin tafiya tafsir yayi.... Su Mamy basu san wainar da ake toyawa a gidan ba. Dan ita bata san yau ne su AA ɗin ma zasu dawo ba. Saboda rabonta da shi tun shekaran jiya data gama zuba masa tujara, dan tunda ALLAH yasa ya kira waya kullum sai ta kirashi ta tisa masa gargaɗi a kan Maanal. Shi dai yakan bata haƙuri kawai yace ta kwantar da hankalinta. Ko a fuska bai taɓa bari Maanal tasan Mamy na kiransa a waya ba. Sai dai abinda bai sani ba Maanal ɗin ta taɓa jinsu har sau biyu, ta ga kuma text message ɗin Mamyn akan wai miyyasa bai cika mata alƙawari na kiran Nuratu ba. Bataga ya bada amsa ba, dan haka tai murmushi kawai tana mamakin al'amarin matar nan. Ƙarfe goma su Oum suka fito, hakama Mamy da Saheeba da Nuratu dan gaba ɗaya suke tafiya tafsir ɗin. Nibras ce kawai babu dan tana zuwa aiki. Kasancewar kuma yau ma juma'a ce sai gata ta fito zata bisu wai bazata fita aiki ba. Sai lokacin su Mamy ke jin dawowar AA da Maanal gidan. Wani abu ne ya tokare maƙoshin Mamy, har fuskarta ta gagara ɓoyewa, amma Oum na kallonta sai tai murmushi. Sai dai Oum ta riga ta ga canjawar fuskar Mamy ɗin, itama a ranta sai taji lallai basu ƙyauta ba, amma harga ALLAH tayi hakane dan tama kowa surprise a gidan, kuma shima AA daya sanar mata yace karta faɗama kowa har su Abah da Babban Yaya. Fawzan ma shine ya gaya masa. RK, ko Fawzan ya fito dan zuwa ɗakkosu yagansa a compound yana waya, shine dalilin tafiyarsu tare. Najma kuwa shine ya kirata yace yazo ta masa rakkiya wani waje, itama sai da akaje airport ɗin ta sani. Fita sukai massalaci, Maanal dai bata bisu ba. Dan tana gama wanka kwanciya tayi, hakama AA yana can ya kwanta. Har suka dawo daga tafsir basu tashi ba, lokacin sha ɗaya da rabi dan yau juma'a an tashi da wuri saboda sallar juma'a. A compound suka iske Babban Yaya da Abah da RK suna shan iska, Fawzan ma barci yake. Cike da tsokana Abah dake kallon Oum ya ce, “Ashe ɗanki ya dawo min da yarinyata, irin wannan bazata haka”. Dariya Oum tayi da faɗin, “Yanzu ai sai hankalinka ya kwanta, ka yarda mu masu cika alƙawari ne”. “Na yarda kam sosai”. Abah ya faɗa murmushi yalwace a fuskarsa su Babban Yaya na taya shi. Babban Yaya yace, “Ai nima Abah na ƙagara su tashi a barcin naga shi da Lillyn wa yafi wani ƙiba yanzu”. Dariya aka sanya, Oum tace, “Oh ni kowa dai ya sama Autana ido a gidan nan. Fadeel ina yabonka salla karka kasa alwala mana”. “To shike nan Oum na bari”. Babban Yaya ya faɗa yana dariya. Wucewa sukai ciki suma, dan Mamy dama tuni takai hanyar sashenta. A mamakin kowa Nibras da Nurry sashen Oum suka nufa suma. Dan tun ɗazu da sukaji wai su AA sun dawo ji sukai kamar ma su fasa zuwa tafsir ɗin, duk hararar da Saheeba ke zabgama Nuratu yitai kamar bata gani ba. ALLAH sarki Oum sai tai murmushi kawai tana nema ma Nibras shiryar UBANGIJI. Dan ita Nuratu idan tayi ai normal ne.... Alarm ɗin da AA ya saita ne ya tadashi saboda sallar juma'a. A lokacin sha biyu. Wanka kawai ya shiga. Yana fitowa ya shirya cikin wani ɗanyen yadi da yaji ɗinkin manyan yara ya kwanta luff-luff. Fuskarsa ya gyara tare da feshe jikinsa da turarensa masu sanyin ƙamshi kala kusan uku. Ya kawo hula data dace da tsarin adon nasa ya kafa. Matuƙar ƙyau kuwa yayi kamar ka sasheshi ka gudu. Kodan bai cika damuwa da saka manyan kayan bane balle hula oho masa. Wayoyinsa daya kashe ya kunna, ya zubasu a aljihu tare da wallet. Sai kuma ya ɗauka atm ɗinsa ya fiddo wallet ɗin ya saka ciki, duk da kuwa akwai wasu atms ɗin a wallet ɗin, da alama dai yana buƙatar wanda ya dauka ɗin ne a kusa, dan a ajiye yake alamar baya amfani da shi sai da dalili. Kai tsaye sashen Abah ya nufa, cike da takunsa na nutsuwa da rashin son hayaniya. Sai da yay knocking tare da sallama aka bashi izinin shiga sannan ya shigan. Wani irin murmushi Abah dake kallonsa ya saki, sai kuma ya buɗe masa hannayensa alamar yazo garesa. Murmushi shima AA ɗin yayi, tare da ƙarasawa gaban Abah ya zai zauna a ƙasa ya riƙoshi ya zaunar a gefensa, cike da kulawa da soyayya irin ta ɗa da uba ya bashi runguma ta gefe yana faɗin, “Irin wannan yin fresh haka Autan Oum ɗinsa. Har naji na ƙagu naga tawa ƴar yata koma”. Murmushi sosai AA ya sake yi, dan randa Abah kejin nishaɗi daban ne a rayuwa. Ƙasa-ƙasa yace, “Abah tayi fiye da yanda kake tunanin ganinta, dan na kula maka da amanarka yanda ya kamata”. Dai-dai nan Mamy ta fito riƙe da babbar rigar Abah da hula a hannu, karaf kuma a kunnenta zancen AA. Sai kuma akai sa'a suka haɗa ido da shi. Wani kallo kuwa ta zuba masa mai ma'anoni da dama. Shi kuma sai yay ƙasa da kai yana amsa addu'ar da Abah ke masa da sanya albarka. Gaishe da Aban ya fara yi kafin Mamy ɗin data wani basar da farko kamar bata ganshi ba. A mamakinsa sai ta amsa cike da nuna kulawa har tana tambayar yaya Maanal. Wannan hali na Mamy na girgiza zuciyar AA matuƙa. Kodan shi ALLAH yayisa ba mutum mai iya ɓoye abu bane oho, dan in har ka masa abinda yaji bazai iya shanyewa ba sai ya maka magana, sha yanzu magani yanzu yake, shiyyasa irinsu Sen.. Bukar Kaugama manyan ƙasar ke jin haushinsa. Dan sun so jan ra'ayinsa jikinsu ya nuna wannan ba shigarsa bace su sa'annin mahaifinsa ne, suka fito masa a buɗe game da muƙamin da shugaban ƙasa ya bashi na shugaban matasa, nan ma ya nuna musu shifa wannan muƙami baya a gabansa dan office ɗin ma sai ya gadama yake zuwa. Yana dai bibiyar ayyukan waɗanda ke ƙarƙashinsa daki-daki, amma shi ko sisi daya shafi aikin nan bai taɓa yarda ya shigo hannunsa ba hatta da albashi kuwa. Dan shi ya san kasuwanci duniya ne, duk wanda ya saba da neman na kansa babu ta yanda zai iya shagala da wani aiki na gwamnati koda na wucin gadi ne...........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖4️⃣7️⃣ ______________ .........Tare da Abah suka fito suka bar Mamy na binsa da harara, sashen Oum suka nufa, can suka samu su Babban Yaya cikin shiri suma. AA yaje ya rungume babban Yaya da shima dai yau yake tsokalarsa. RK da Fawzan kuwa na dariya. Zo kaga idanun Nuratu da Nibras kamar zasu faɗi a jikin AA. Gaba ɗaya sun susuce, a kwana goma kawai yay irin wanan sake zama fresh ɗin. Zukatansu suka shiga wassafa musu ba dole yay ƙyau ba yana more angwancinsa. Wani irin ture tunanin sukai rayukansu a ɓace, tun ɗazun suke a sashen amma basu ga Maanal ba. Wai tana ɗakin Oum tana barci. Jin AA na sashensa kuma baisa sun gajiya ba, dan sun tabbatar bazai iya wucewa massalaci bai zo sashen Oum ba. Aiko sai gashi ya shigo duk ya firgitasu da gayunsa. Tsabar sakawa rai masifa su duka biyun ba wanda azuminsa bai raunana ba saboda yanda suke siffanta wa kansu AA ɗin a zukata. Suko sauran ƴammatan da zukatansu fes suke kowama yayi musu ƙyau a yayun nasu bawai AA ɗin kawai ba. Najma da Fawzan kuwa sun wani kashe ma juna ido cike da shauƙi. Sai ko karaf a kan idon AA. (Kai mi Ya Fawzan ke shiryawa haka?) AA ya ambata a zuciyarsa, sai ya ɗan kalla RK daya fahimci shima hankalinsa akansu Ya Fawzan ɗin yake. Wani signal sukama juna da ido, RK yay dariya yana ma bakinsa zip. “Tab ɗin”. AA ya faɗa a ƙasan maƙoshi yana miƙewa abinsa batare da kowa ya fahimci inda tab ɗin ɗin tasa ta dosa ba. Fitowa sukai harabar gidan gaba ɗayansu harda samarin yaran nan duk suka shiga motoci. RK da AA da wasu a yaran suna a mota ɗaya. Babban Yaya, Fawzan da Abah da sauran yaran a mota ɗaya. Acan itama Oum ta kaɗa ƴammatan zuwa kowa yay wanka yay salla a shiga kitchen. Jikin babu ƙwari Nuratu da Nibras suka fito a sashen..... _________★ A lokacin da su Maanal suka gama hutawa anan airport Yazeed ne da tashi matar ke isowa tasu ƙasar haihuwar bayan kwashe watanni a ƙetare suna hutawa. Masha ALLAH na faɗa, ganin yanda Yazeed ɗin yay wani kalar yin ƙyau da sabuwar nutsuwa ya yi ƙiba irin ta matasan masu kuɗi. Sai dai fuskar kicin-kicin babu fara'a sam a tare da shi abinka da dama bamai yawan fara'ar bane. A gefensa Nazeefa ce cikin matuƙar gayu ta ƙara wani uban haske da ƙiba itama. Kai daka ganta kasan tana jin daɗi da alama kuma ta harbu. Babu wanda yasan da dawowarsu sai Aunty Sabuwa, dan haka ita da kanta ta tafi tarbosu Abujan. Nazeefa na hangota ta wani tafi da gudu ta tungumeta tana ihun murna. Hakan ya jawo musu idanun mutane kuwa. Oho ko'a kwalar rigarsu, dan Aunty Sabuwa ma ɗaga Nazeefa tayi tana juyi da ita abinka da siririyar mace, a hakan ma wai jikin ya murje ne. Ƙarasowar Yazeed da abun nasu ya bashi kunya ya sata sakin Nazeefa, sai kawai ji Yazeed yay an wani rungumesa. Tab ɗin, yau fa ake mutuwar tsaye, dan kuwa ita dai Yazeed ɗin yayi. Yayinda Aunty Sabuwa ke faɗin, “Oyoy my Son”. Yazeed na kama da mahaifiyarsa Hajiya Yaya, Aunty Sabuwa da Hajiya Yaya na kama da juna, shiyyasa mutanen dake kallon ikon ALLAH suka ɗauka ita ta haifesa, duk da dai wasu na ɗan wasiwasi na ganin kamar shekarun Aunty Sabuwa bazai kai ta haifi Yazeed ɗin ba. Nazeefa da abin ya sosa mata zuciya ta riƙo Aunty Sabuwa tana faɗin, “Kai Mom harda runguma kuma?”. “To dan ubanki ba ɗana bane shi, ko a lahira ba ance ɗan ɗan uwa kai yake gani ba. Kinga ko a lahira bazaiga Yaya ba ni zai gani”. Baki sosai Nazeefa ta tura gaba, tana kauda kanta. Oho ko'a jikin Aunty Sabuwa, sai ma amsa gaisuwar Yazeed da take yi. A haka suka rankaya zuwa lafiyayyar motar da aka sakama Nazeefa a lefe. Ba shi kawai ba ita kanta Nazeefar sai da tai mamaki. Ta kalli Aunty Sabuwa cikin waro idanu ta ce, “Mom! Wai motata ce ta koma haka? Hawa akeyi ne?”. Cikin rashin damuwa Aunty Sabuwa ta ce, “Eh mana my baby ina ɗan ɗanawa ne kafin ki dawo. Babanki yace idan aka barta a ajiye ba'a hawa saita samu matsala.” sai kuma ta sake rage murya yanda Yazeed bazai ji ba ta cigaba da faɗin, “Sannan banda ke shashasha ce yanda yaron nan ya moreki da ƙyau a hutawar nan taku ai kinsa zai saya miki wadda ta fita. Dan yanzu kinfi ƙarfin hawa wannan. Agolan gidansu fa tsohuwar budurwarsa motan miliyan 90 aka sako mata a lefe da ta miliyan 20+. Ke sai ki zauna kina hawan wannan ta 20m ƙaramar tata ma tafi taki”. Ai wani irin susucewa Nazeefa taji tayi, a zabure ta ce, “Wai kina nufin Maanal Mom?!”. “To inba itaba wa? Ba itace tsohuwar budurwar mijinki ba”. “Kambu Mom shi ɗan gidan KK kura ɗin ne yay mata wannan lefen?”. “Hummm! Ke dai fa labarin mai tsaho ne, amma ina gaya miki likafa taci gaba, kin san uwarta ta iya tsafi, ai a wajen ɗaurin aure komai ya canja, maimakon ɗan kura sai aka bama ɗan tsohon ambassador Aliyu Darma”. “Kuttun uban can kai, AA Darma fa kenan? Koba shine aka gaya muku ya mata fyaɗe ba tana yarinya”. “Shifa kuwa, kedai shiga mota muje ma ƙarasa a gida mijinki na kallonmu”. Tab ɗin gaba ɗaya jikin Nazeefa ya gama sanyi, ji take farin cikinta ya wani gushe a lokaci guda. Kai ina bazai yiwu ace ta ƙwace Yazeed a hannun Maanal ba, sannan Maanal ta aura wanda yafisa. Yo ba Yazeed ba ai ko Daddynsa kansa AA Darma ya fisa kuɗi kamar yanda taji ana faɗa, balle kuma suma babansu Aliyu Darma ɗin ƙurun kansa ne, hakama sauran brothers ɗinsa suma fa akwai kuɗin. Kai family ɗin Darma ma gaba ɗaya sai dai kawai ace wane yafi wane arziƙi saboda iyayensu sun tara musu. Gashi ba wani uban yawa ne da su ba dan a tarihin data bibiya nasu tushe zuri'ar gana ɗaya shi Harɗo Ishaq Darma ɗin ba ɗan asalin ƙasar Nigeria bane, tushensa da ainahin zuri'arsa na wani yanki na sudan ne. Mahaifiyarsa ce ƴar nan Yola ɗin, bata son Mahaifinsa shiyaysa daga haihuwarsa auren ya lalace ta gudo da shi nan. Shi kuma babansa yay fushi yace bazai biyo ta ba har abada ya bar mata ɗan. Dan haka ainahin dukiyar Harɗo Ishaq ta mahaifiyarsa ce daya gada, iyayenta suka bar mata kuma ita kaɗai, shima ya gada a wajenta.. Nazeefa na wannan tunanin suka iso gidansu. Mamaki sosai ya kama Yazeed ganin gidansu Nazeefa suke, shi a ganinsa ai gidansu ya kamata a tafi, sai dai yaji ya kasa magana sam. Lafiyayyan abinci kuwa suka samu an haɗa musu, dan Nazeefa ta gayama uwarta basa azumi saboda tafiya. Shi dai Yazeed hankalinsa duk a rarrabe, kewar mahaifiyarsa yake shima da ƴan uwansa, so yake ya gansu amma anzo nan an masa ɗaurin goro. Haka dai ya daure ya ci abincin sama-sama. Yayinda Nazeefa da Aunty Sabuwa suka kulle a ɗaki bai san abinda suke tattaunawa ba. Yanda suka barsa shi kaɗai ɗin kuma ya sosa masa rai, amma sai yaji ko'a fuska bazai iya nuna ɓacin rai ba. Sun fi minti talatin kuwa kafin su fito suna ƴar dariya, sai lokacin Nazeefa ta zauna taci abincin itama. Sun kammala Yazeed na shirin cewa su tashi suje gida sai ga Babanta. Wato mijin aunty Sabuwa. Ai da wani irin farin ciki ta daka tsalle ta ɗanesa tana ihu. Sai Yazeed yay kasare kawai yana kallon ikon ALLAH. Bayan sun gama murnar su sanan baban nata ya zauna suka gaisa. Babu kunya sai wani faɗi yake wai amarcin ya amshesu sunyi ƙyau abinsu. Kunya kamar ta kashe Yazeed amma bai iya cewa komai ba. Shima baban jan hannun Nazeefa yay suka haye sama, sunfi minti ashirin sannan ta dawo. Nan ma dai ran Yazeed ya sosu, amma ko fushi bai iya nunawa a fuska ga duk da kasancewar sa mutum mai zafi. Suna fitowa ana kiran magrib, aunty Sabuwa tace ko zasu koma sai anyi salla. Kan Yazeed a ƙasa ya ce, “Aunty ayi haƙuri dai mu tafin”. Ido Nazeefa ta ƙyafta mata, dan haka tai shiru. Yanzun ma Aunty Sabuwa ce ta tuƙasu zuwa gida, duk da kuwa shan ruwa ake kuma tace wai tana azumi.... Ammie na kitchen da Sakina da su Waleed suna ƙarasa aikin abincin buɗa baki Hameed da yaje kaima su maigadi abinci ya shigo da ɗan gudu yana faɗin, “Ammie Yayanmu ya dawo”. Kallon yaron kawai Ammie ta tsaya yi, sai kuma zuwa can ta ce, “Yazeed!”. Kai Hameed ya jinjina mata kuwa tare da faɗin, “Aunty Sabuwa ce ta kawosu a mota, gasu can suna buɗe sashen Yayan, su Aunty Basira sun fito sai kuma suka tsaya basu je wajensu ba suna kallonsu daga nesa”. Murmushi Ammie tayi. Sakina kuwa data kasa shiru, “Tofa ikon ALLAH, ita surukar ce taje ta tarbosu kenan? A dole kam yara su tsaya duk da uwarsu bata nan ai ince sashenta zasu fara sauka”. Ammie ce ta ce, “Ai maybe kuma daga can wajen Yayan suke tunda kika gansu da Sabuwa ɗin.” Sakina dai da kamar bata gamsu ba ta ce, “To ƙila hakane Aunty”. Daga haka suka fito a kitchen ɗin domin zuwa yin sallar magrib tunda kowa yaci dabino yasha ruwa.............✍️ _To labari ya waiwayo gidan su Ammie😄🏃🏃🏃_ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖4️⃣8️⃣ ______________ ........Maanal bata tashi ba sai da Oum ta tasheta ganin 2 na neman wuce wa. Daka ganta kasan sosai take jin azumin nan, duk ta yi laƙwam har wata ƴar rama tayi, to dama can Maanal raguwa ce akan azumi, kawai dai kura ce tai lafiya aka fara dauriya irin na mu mun girman nan. Wanka tayi tai salla, wasu skirt da riga masu taushi da rashin nauyi ta saka. Skirt ɗin ya buɗe sosai. Haka ma rigar bata wani kamata ba amma sun mata ƙyau. Cike da rashin ƙarfi ta sakko falon ƙasan, ƴammatan yaran duk suna zaune harda Nurry da tuni ta dawo hakama Nibras duk sun ci kwalliya abunsu kamar ba masu azumi ba. A dai-dai nan su AA suka shigo. Shine a gaba shi da Muhseen dake bashi labarin makarantar su, baya cewa komai yana dai sauraren yaron kawai. Su babban Yaya biye da shi, sai yaran RK da Fawzan a ƙarshe. Duka yaran hannuwansu da ledodin fruits, sai suka nufi kitchen suna ajiyewa. Shi ko AA da idanunsa suka fara sauka akan Maanal dake ƙoƙarin kaiwa zaune a kasalance inda take ya nufa ko kunyar ƙannensa har ma da ƴaƴa dake fallon bai jiba, balle tasu Nuratu da baima san dasu ba, gasu Babban Yaya kuma a bayansa da Abah. Zama yay a hannun kujerar da takai zaune bayan ta janye idonta a cikin nashi tana amsa maganar da su Meena ke mata. A ƙasan maƙoshi sosai ya furta, “Kina lafiya?”. Kanta ta jinjina masa fuskarta a marairaice. Shi ko yana kallonta da fararen idanunsa da ke kamar an watsa mai a cikinsu saboda yanda suke wani irin ƙyalli mai ɗaukar ido sosai gasu farare tas. Sai kuma ya kai yatsunsa biyu a goshinta alamar son tantance zafin jikinta. “Lilly ba lafiya ne?”. Babban Yaya ya faɗa idonsa a kansu. Da sauri Maanal ta ture hannun AA dake shirin kaiwa wuyanta cike da jin kunya ta kalla babban Yayan. Sai kuma taga ashe ma harda Abah, ai saita ƙara daburcewa ma harta so bama su Aban dariya. Dan tuni ta zamo ƙasa ta fara gaishesu. “Kinga tashi-tashi ƴar gidan Abanta, zauna abinki kinji. Fatan dai kun dawo lafiya, ɗan gidan Oum ko harararki baiyi ba tunda yaga bana kusa.” Murmushi sosai Maanal tayi ta ɗan kalla AA suka haɗa ido, sai ta maida kanta ta risinar tana girgizama Abah alamar eh. Yace, “To Masha ALLAH ɗan Oum ka fita ko ba sabulu.” dariya duk akai a falon banda Nurry da Nibras da kishi ya kume. Maanal ta gaida babban Yaya shima, sannan ta juya tana gaida su Yaya Fawzan da RK. Babban Yaya ne ya tambaye ta amma dai bata azumi ko, dan AA yace shi yanayi. Amsa ta bashi da tanayi itama, sai duk tausayinta ya kamasu. Abah ya shiga yima AA faɗan miyyasa ya barta ta ɗakko azumi tunda yasan awannin zasuyi tsaho. Cike da tausasasawa AA ya ce, “Abah ba laifina bane fa, kasanta tana da rigima”. Baki Maanal ta tura gaba kaɗan da faɗin, “Kaima kana da ita ai”. Dariya duk akayi, banda AA daya ɗan murmusa kaɗan yana wani kallonta ƙasan ido. Babban Yaya da Abah ma dai murmushin kawai sukayi. Hakama Oum dake fitowa. Miƙewa Nuratu tayi idannunta cike da hawaye, dan bata jin har yanzu AA yako kalleta. Oum ta tsaidata da faɗin, “A'a Nuratu ina zuwa? Ai ku wuce muje kitchen lokaci naja kada a makara yau. Muneer jeka sanarma Maman Naufal da Mamy suma dasu Haule”. Amsawa Muneer yay yana miƙewa, su kuma ƴammatan suka shiga tashi suna nufar kitchen. Miƙewa Maanal itama tai shirin yi AA ya maidata ya zaunar batare da kowa ya lura ba, sai kuma ma dai-dai hakan Oum ta ce, “Baby banda ke kekam zauna ki huta”. A marairaice Maanal ta ce, “Oum zan iya, zammafi ganin saurin lokacin fa”. “A'a bazakiyi komai ba, sai dai ki zauna kina tayamu hira”. Da sauri tace eh ta yarda. Tashi tai tabi Oum, sai AA ya koma ya zauna inda ta tashi ɗin yana amsa wayarsa da ake kira. Yanda kitchen ɗin ya cika kowa na ƙoƙarin fara aikin da aka basa sai abin ya burge Maanal. Tana matuƙar ƙaunar rayuwa family house musamman mai haɗin kai da ƙaunar juna irin haka. Sai taji tana ma Mamy addu'ar shiriya da nata halin, dan tabbas da itace babba a matsayin Oum lallai gidan nan da tuni ya tarwatse, irinsu Mamy basa iya haɗa kan iyali koda nasu kaɗai ne. Shigowar Mamyn ta katse mata tunani, cike da girmamawa ta gaisheta, amma sai Mamyn ta amsa sama-sama cike da gatse kuma ta furta, “Sai yanzu ake ganinki ƴan chaina”.. Gaban Maanal ne ya faɗi, tai saurin kallon sashen da Oum take sai taga hankalinta sam baya anan. Ajiyar zuciya ta sauke a hankali, dan duk wanda yaji a yanda Mamy tai maganar ALLAH sai ya tsargu, saboda kalamai ne a kaikaice amma masu tsauri. Cikin son kare kai ganin murmushin da Saheeba tayi Maanal ta ce, “Ayya Mamy yanzu nake shirin tafiya sashen ki sai Oum tace a kiraku”. Wani kalar tsaii Mamy tayi tana kallon Maanal ɗin, ita ko tayi fuska abinta tama maida hankali kan Batool da Maimoon dake zaman gyara fruits ta shiga nuna musu yanda zasu yanka kankana a sharp mai ƙyau. Suna a haka akai kiran la'asar, Oum da Mamy suka fita salla, sai Oum tace suma su rabu biyu idan sun dawo sai wasu suje. Maanal da taga ba aikin komai take ba sai itama ta miƙe kawai. Lokacin suma mazan sun fice sallar, daga can zasu zauna jin tafsir ne. Kowa yana dawowa daga salla aiki ya ɗora, zuwa shida an fara fidda komai waje, Maanal dai tuni ta dawo falo dan ƙamshin abincin sai suka fara hawa mata kai, ga ƙarfin jikinta ya sake raunana matuƙa har tana neman fara galabaita dauriyace kawai dan karta tayarma kowa hankali yasa ta dake. Amma duk wanda ya kalla idonta da yay zuru-zuru zai fahimci ƙarfinta ya fara ƙarewa. Aiko da ƙyar ta iya tashi tai alwala kamar kowa duk suka koma waje inda aka shirya abincin da wajen salla. Tana daga kwance aka kira salla, kowa ya fara ƙoƙarin cin dabino ita ruwa ta ɗauka mai sanyi sosai ta shiga sha. Saida ta shanye roba ɗaya tas, ta sake ɗaukar wata ta ɗora, ta sha rabi Najma ta amshe tana faɗin, “Easy mana Aunty Maanal”. Komawa tai ta kwanta tana lumshe idanun da sauke numfashi. Ta jima a haka kafin tai dauriyar tashi yin sallar itama, tana idarwa ta sake komawa ta kwanta. A haka su AA suka shigo suka sameta. Sosai hankalinsa a kanta yake, dan shi kansa a jigace yake balle ita, amma ganin Oum na ƙoƙarin kamata ta tashi ta jinginata a jikinta sai ya sauke ajiyar zuciya ya ɗauke kansa. Kaɗan taci abincin tace ta ƙoshi, Oum zata cigaba da lallashinta Abah yace ta barta haka kawai. Kwance Maanal takai har sai da aka fara shirin fita salla ta ɗan ƙarfafa kanta, Oum taso ta zauna gida ta huta amma tace zata iya. Haka suka fice hankalin AA a rarrabe. Ana idar da sallar isha'i dole Maanal ta haƙura, dan jiri ma take gani, ga abincin da taci sai juya mata yake kamar zata amayoshi. Ana idar da wutri itace farkon miƙewa. Oum ta bita da kallo, sai kuma ta miƙe ganin kamar Maanal ɗin na layi. Alhamdullah Maimoon na kusa da ita da sauri ta riƙeta. Cikin rawar murya Maanal ta ce, “Maimoon muje gida amai nake ji”. Babu musu Maimoon ta riƙota sukayo gaba. Sune farkon shigowa gidan. Sai Oum da tun fitowarsu ta biyosu, sai akai sa'a RK da AA sun fito suma suke tambayar Oum ɗin lafiya dan ganinta a ruɗe. Sama-sama ta ce, “Baby! Ina ga bata jin daɗi”. Kowa yasan wa take cema Baby, dan haka suka rufa mata baya, AA da kansa shima ke ciwo jiyake kamar ya rufe idanu ya gansa a gaban Maanal. Aiko shigowarsu gidan dai-dai da fara aman Maanal. Dan da wani irin ƙarfi ta fisge jikinta ana Maimoon tai wajen fanfo da akema flowers barruwa jikinta sai rawa yake ta fara aman. Su duka can sukayi kanta, yayinda Maimoon data bita ta riga su isa tana riƙe da ita. Ina AA na zuwa baima san ya janye Maimoon ba ya riƙo Maanal a jikinsa. Ganin yanda take yunƙuri sai kawai ya rungumeta ta cigaba da yi a jikinsa. Aman ma duk ruwa ne tunda ba wani abincin kirki taci ba. A wannan halin su Mamy suka shigo suka samesu. Dukansu sai sukai mutuwar tsaye ganin yanda AA ke rungume da Maanal tana amai a jikinsa. Zuciyar Mamy na rawa tace, “Ciki? Ciki Ajwaad yay ma yarinyar nan?”. Wannan furuci nata ƙasa-ƙasa karaf sai a kunnen Nuratu, a wani irin rikice ta ce, “Ciki kuma? Na shiga uku na”. A bayyane tayi tata maganar ita, dan haka ta shiga kunnen kowa harda Abah dasu Oum. Hatta AA ɗin ma yaji, amma da yake hankalinsa na kan Maanal ne bai kula ba. Nibras kam jitai kamar zata sume a wajen. Ajwaad ɗinta ne yama wata ciki! Kai ita kam ai itace ta shiga uku ba Nuratu ba. Saheeba ce ta kama hannun Nuratu ta damƙe domin maidota hankalinta.... Maanal dai data gama yin lagab idannunta na lumshewa ta kwantar da kanta a ƙirjin AA dake rungume da ita. Bawan ALLAH idanunsa sun kaɗa sosai damuwa ta bayyana matuƙa a fuskarsa. Kan nata ya dafe da hannunsa yana shafawa, sai kuma a hankali cike da raɗa dan babu wanda zaice a wajen yaji mi yake faɗa ya ce, “Sannu. Kin gama?”. Luuuu Maanal ɗin ta buɗe idannunta ta ɗan kallesa, sai kuma ta maida ta lumshe a hankali. Abah ne ya matso inda suken cike da kulawa yana mata sannu, sai kuma yace, “Ajwaad ɗagata a damshin ruwan nan kuje ciki ka gyara mata jiki kaima ka gyara naka sai Rafeeq ya duba ta?”. Kai kawai AA ɗin ya jinjina. Sai kuma ya miƙe ɗauke da ita camak abinka da dogon mutum da ya wadatu da ƙarfin jiki. Duk da kallo suka bishi, su Maimoon kuma suka shiga gyara wajen. Kansa tsaye sashen Oum ya nufa da ita, Oum na bayansu hakama Abah, can ɗin kuma kowa ya nufa dan Maanal ta basu tausayi, sai RK ne ya shiga mota yana faɗin bara yaje ya ɗakko kayan aiki. Ya Fawzan ne ya bisa domin masa rakkiya........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖4️⃣9️⃣ ______________ ........AA bai dire Maanal ko ina ba sai bedroom ɗin Oum, yana riƙe da ita ya daidaita ɗumin ruwan sannan ya buɗe shower kawai tana sauka a kansu. A tare suka saki ajiyar zuciya, ita kuma ya sake lafe masa a jiki dan bata cika son ruwa na sauka mata haka a jiki ba shima ya sani tun suna yara. Sai da ruwan ya dakesu da ƙyau sannan AA ya zaunar da ita cikin jacuzzi a hankali. Hular kanta ya fara zamewa, gashin ya jike shima jalab dan Oum ce tace ya saka mata ruwa sosai a cikin kai amma na ɗumi, shiyyasa ma ya tsaya a ƙarƙashin shower ɗin dan yasan bata son ruwa na zuba mata haka a saman kai. Idanunta a rufe suke, amma tana jin yanda yake warware mata gashi daga cikin ribbons ɗin data saka. Saukar hannunsa a saman ƙirjinta kasancewar rigar a manne take da jikin saboda jiƙar ruwa ta sata buɗe ido da sauri, bawan ALLAH ba abinta take tunani yake yi ba, botiran rigarta yake cirewa. Dai-dai ya kama wanda ke a saitin inda bata son a gani ɗin takai nata hannun cike da kasala da rashin ƙarfin jiki ta dafe hannunsa, dan waccan ranar ce ta shiga dawo mata a Chaina. Sai a lokacin ya ɗago shanyayyun idanunsa ya zuba mata. Baki ta taɓe kamar zatai kuka, sai kuma cikin rawar murya ta ce, “Ni dai ka bari zan cire, kaje waje”. Hannunsa ɗaya ya shiga janyewa kamar wanda yaji maganarta, harta fara murna a mamakinta sai gani tai ya cire hannun nata ne a wajen ya riƙe da ɗayan hannun nasa ya cigaba da cire maɓallin da ɗayan. Ya ILAHI, Maanal taji kamar tai ihu dan kunya, ga ciyo jitake kamar zata faɗi, amma bawan ALLAHn nan brozan su o'e ko'a jikinsa ya sauke su tsaf sannan ya saki hannun nata ya maida saman kafarta, ita tana ƙoƙarin rufe ƙirjin duk da akwai b a ciki shi kuma ya zame rigar gaba ɗaya ya sauketa ƙasa, ai sai kawai ta kife jikinta kan ƙafafunta tsabar kunya. Bai wani nuna ya damu ba ya shiga ɓalle hook ɗik b ɗinta shima. Ya ARRAHAMAN da sauri nan ma ta ɗago. Hakan ya bashi damar zame b ɗin itama. Bai kula yanda ta saka hannu ta rufe ƙirjin ba gaba ɗaya tama ƙi barin b ɗin ta fita duka. Tasa rigar ya miƙe ya zame, ya shiga zame wandon shima, dai-dai lokacin Maanal ta ɗan leƙo kanta a tunaninta ya ƙyaletane sai taga abinda yake yi. “Innalillahi... Ajwaad kaga mi kake yi kuwa?”. Ta faɗa muryarta na rawa, tana kuma sake maida kanta ta kife. Sai da ya kammala tsaf yabar boxer kawai sannan ya sake duƙowa gabanta, a cikin kunnenta ya raɗa ma, “A'a Aunty Maanal ban gani ba”. Daga haka ya ɗagata camak ya miƙe tsaye, kafin tai wani yunƙuri ya ƙara sakar musu ruwan shower ɗin ta yanda ta kasa magana. Ta kuma rikice saboda saukar ruwan ta saki hannunta dake rufe da ƙirjinta tana ƙoƙarin rufe fuskarta. To shifa bawan ALLAH AA dama ta samu, kallo-kallo ƙyauta daga ALLAH.... Tabbas badan halin da take ciki ba, ga kuma su Oum yasan duk zaman jiran fitowarsu suke, da yau babu abinda zai hanashi yin abinda ransa yaso. Tunda ga abinda ake hanasa gani da ɓoye masa available. Amma ba komai, idan kere na yazo zabo na yawo ai ya tabbatar za'a haɗe wataran. Maanal kam tunda ta fahimci abinda ke faruwa ta shige jikinsa kawai ta rungumesa duk dan hanasa kallar mata jiki. Hawaye kam sun cika mata idanu. Ga jikin nata babu karfi kona sisi. Da ƙyar ta yarda ya saka mata bathroom, ƙasan zuciyarsa kuma yana tunanin shi ya zai yi da kaya suna a ɗakin Oum ne fa. Karo na farko yaji wata kunya mai girma ya baibayesa, kai ya ilahi shine dayin wanka yau a bayin Oum tare da Mace. Rashin makama ya sashi jan towel ya ɗaura ya ɗakkota suka fito, dan ya tabbatar kowa babu a ɗakin. Aiko babu kowan, sai kayansa da ya gani a saman gado an ajiye. Ajiyar zuciya ya sauke, yasan Babban Yaya ko Ya Fawzan ne da wannan aikin. Bai ɓata lokaci ba ya shirya, itama ganin tana rawar sanyi duk da ruwan zafi ya saka musu sai yay saurin duba mata kaya ya saka masa masu kauri. Dai-dai nan akai knocking, sai kawai ya bada izinin shigowa. Oum ce sai RK biye da ita. Kawai sai ga Mamy ma ta shigo. Aiko dai-dai AA na maida hankali ga RK dake masa magana idonsa ya shiga cikin na Mamy, wani mummunan kallo kuwa ta zuba masa mai kaɗa hanji, haka kawai sai abin ma shi ya bashi dariya. Amma dai baiyi ba ya ɗauke idanun nasa tare da kaiwa zaune kusa da Maanal dan RK yace ya zauna ne ya mata komai da kansa. Oum ma na zaune ne ta ɗaura kan Maanal a cinyarta. Komai AA ya mata, RK na nuna masa yanda zai yi. Batare da damuwa ba RK ke faɗin, “Ka saka mata iya drip ɗin nan kawai da zai tsaida aman ta kuma samu ƙwarin jikinta. Dan bai kamata tasha kowanne magani ba ko makamancin hakan saboda kar ai ɓarna har sai zuwa safiya anyi gwajin ciki sannan”. Juyowa AA yay yana kallon RK, shima da yake kallonsa yake sai ya ɗaga masa gira. Ƴar harararsa AA ɗin yayi, shiko ya sanya ƴar dariyar mugunta, ba kuma dan kowa yayita ba sai Mamy, saboda yaga kallon data jefama AA sanda ta shigo. Sannan duk da shi ba likita bane fannin mata yasan babu wani ciki da Maanal keda galabaitar dogon azumin da sukayi ne dana wahalar tafiya, kuma sai ana kai azumin tasha ruwan sanyi maimakon na zafi, ta kuma sha shi da yawa sosai... Tsaf AA ya ɗaura mata ruwan, atake kuwa barci yay awan gaba da ita. RK yace a cire towel ɗin da aka naɗe mata kai da shi a busar mata da shi saboda mura. Daga haka ya fita a ɗakin. Su Abah ne da Babban Yaya da Ya Fawzan da sauran matasan yaran suka fara shigowa suka dubata. Ganin tana barci sai suka fita. Suma matan suka shigo, dai-dai lokacin AA ke amsar hand-dryer a hannun Oum yana faɗin ta barshi yayi sunje suci abinci tunda ta samu barci. Oum bata musa ta bashi, haka ya zauna abinsa batare da tuna akwai Mamy a ɗakin ba, balle matan yayunsa da ƙannensa ya ɗaura kan Maanal a cinyarsa ya fara busar mata da gashin a nutse tamkar ba shi ba. Ai sagade Saheeba da sauran sukai suna kallon ikon ALLAH. Zuciyar Nibras kam tamkar zata fashe dan bugun da take yi. Nuratu kuwa ji take kamar ta je ta daɓama Maanal dake barci wuƙa a ƙirji. Suko su Najma abin birgesu yay, Yaya AA sarkin ɗaure fuska da bayama kowa magana ne yau yake busar ma da mace kai. Tab ɗin abin dole ya zama mai ƙayatarwa. Yako zama ɗin, dan sunji sunama kansu addu'ar samun irin hakan daga mazajensu. A haka Oum ta kaɗo kansu duka suka fito domin cin abinci bisa umarnin Abah daya leƙo. Gaba ɗaya Mamy jitake juwa na ɗibarta, dan haka batai zaman cin abincin ba tace zataje ta ɗan watsa ruwa tukunna. Oum zatai magana Abah ya wani riƙe mata hannu ta yanda duk yaran bazasu gani ba. Da mamaki ta kallesa, sai kawai ya wayance ya ce, “Zarah na kodai mun kusa ganin jinin autanki ne?”. Murmushi Oum ɗin tayi, cikin raɗa ta ce, “Haka nake fata Gadanga. Shiyyasa ƙaninka yace baza'a bata komai ba sai anyi gwaji an tabbatar”. Murmushi mai faɗi Abah yayi. Ya sake ɗan matsa mata hannu. Tana ganin Babban Yaya ya juyi zaiyi magana ta zame hannun nata da sauri. Mamy data kasa tafiya tana kallon komai sai hawaye suka wani gangaro mata zuuuu-zuuuu. Wai ita kam yaya zatai da Fateema a rayuwarta ne? Ga kuma wani bala'in da bata taɓa tunanin tsintarsa anan kusa ba saboda yanda tasan Ajwaad na mata biyayya, amma sai gashi yaje ya kwanta da yarinyar nan harda ciki..... Tana shiga bedroom ɗinta ta zube a gado ta fashe da kuka kaikace mutuwa akayi mata, dan wlhy ta jima a rayuwarta bataji abinda ya nema fasa mata ƙirji a lokaci guda ba irin wannan al'amarin. In har Maanal ciki ne da ita, kuma cikin na Ajwaad ai Oum ta gama cinta wasa a wannan gaɓar, ita kuma abinda bazata yarda da shi ba kenan, dan haka ta rantse da ALLAH sai cikin nan ya zama JINI mai gudana a saman tiales ɗin banɗakin Fateema. Da wannan alwashin ta ɗauka waya tai kiran number Maman Saheeba. Tsaf ta zayyane mata komai, ita kanta Maman Saheeba ɗin sai da zuciyata ta sake wani girgizar tashin hankali, dan dama Nuratu ta kirata tana kuka take faɗa mata, sai dai bata fahimci komai ba saboda kukan da Nuratu ɗin ke yi. Ta kuma kira Saheeba bata ɗaga ba, da'alama wayar bata a kusa da ita.........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖5️⃣0️⃣ ______________ ........Numfashi mai ƙarfi taja, kafin cike da makirci ta ce, “Haba Aunty wannan har wani abin tada hankali ne har kina saka kanki kuka. Yo ALLAH na tuba cikin mi! Cikin ma da ƙila bai wuce kwanaki ba, kinga ko ba buƙatar zubarwa ake ba lalatashi kawai zamuyi cikin sauƙi”. “Nana ta yaya? Yarinyar da bata taɓa cin abincin sashena ba tunda tazo. Ke ni zan ma iya rantse miki ban taɓa zaman minti goma da ita ba”. “Wannan duk ba damuwa bane, ai azumi akeyi, kuma a irin lokacin nan abinci nasan duk a tare kuke yinsa, wannan aikin Saheeba ce zatayi mana shi, bama yanzu ba sai bayan salla. Sannan ya kamata Aunty kima Ajwaad tsiya gaskiya. Munafiki yana sum-sum da kai kamar bazaka saka masa yatsa a baki ya ciza ba amma yasan yay ma mace ciki. Idan wancan na farko yace kuskurene wannan kuma fa? To wlhy sai kin fito masa a mutum sannan, idan ba haka ba ko mun lalata cikin ma a banza tunda ba kunyace da shi ba zai iya sake mata wani a gidan kuna nan sake da baki, wama ya sani ko tun kafin su tafi Chaina ɗin yay wannan ɗin tunda shi dama taƙadari gagararren yaro n.....” “Uhmmm Nana! Please a dinga sassauta irin tsauraran kalaman nan akan yara basu da amfani, duk da Ajwaad nada taurin kai a kaf yaran nan babu wanda nake iya lankwasawa cikin sauƙi irinsa. Su da suka sha daga jikin nawa ma ya fisu min biyayya..” Sosai kalaman Mamy suka daki zuciyar Maman Saheeba, sai ta fahimci lallai dole ta dinga gyara kalamanta tunda har ƴar uwar tata ta fara nuna ranta ya sosu akan zagin Ajwaad da tayi. Cikin ɗan gyaran murya a fili ta ce, “Hakane aunty kuma kiyi haƙuri raina ne ya ɓaci wlhy. Kin san yaran nan da son fusata mutum. Ni dai yanzu abinda kawai nake gani kenan. Mu lallata cikin sannan ki ja masa kunne tunda wancan bai shigesa ba. Shima Fawzan kin masa maganar Amani ɗin kuwa? Wlhy yarinyar nada hankali Aunty, sannan tafi Nibras komai, ƙyan jiki, ilimi, harma da tarbiya. Itama dai uwarta ba wasa ba wajen kuɗi. So nake wlhy mu rikita zuciyar matar nan ai auren rana ɗaya dana Ajwaad da Nuratu..” Fuskar Mamy da murmushi ta ce, “Karki damu zan masa magana shima yau ɗin nan. Dama na bari ne ya nutsu naga kwana biyu yanata kai-kawo na kwangilar nan daya samu. Ki tura min hoton yarinyar ma kada na manta”. Cike da farin ciki Maman Saheeba ta ce, “In sha ALLAHU yanzu kuwa aunty. Harma da no ɗinta”. Daga haka sukai sallama Mamy na sauke ajiyar zuciya. Sai taji ɓacin ran nata ya ragu sosai. Shiyyasa take ƙaunar Nana sosai...... __________★ GIRO Zaune Gwaggo take ta zabga tagumi abin duniya ya isheta, yau ko abinda zasu ci basu da shi. Tunda Sule ya tattare ƴan sauran kuɗaɗen wajen Sen... Suka koma ƙarƙaf, ga Babu bashi da lafiya sosai. Haka kawai sai ya yanke jiki ya faɗi. Sun ɗan kira mai camix ɗin garin ya dubashi yace ulser ce ke damunsa, sai kuma hawan jini. Nan dai ya ɗan bashi magunguna yay masa ƙarin ruwa. Daga nan ne ma yake ɗan samu ya fita zuwa ƙofar gida. Amma daga ba nan ɗin ba baya iya doguwar tafiya, dan ko azumi ma baya iya yi. Kai zata iya cewa ma itace kawai mai yin azumin a wajen, dama ba'a maganar Haƙila da Sule, Sailu ko ta murje idanunta tace itama ulser gareta mai zafa bazata iya azumi ba. Dan haka da rana sai su dafa abinda ransu keso ita da yaranta suci, ko Babu sai sun gadama ma suke bashi. Itako in aka sha ruwa sai wanda yaga ALLAH yaga Annabi ya sammata kunu a gidan. Shi dama Baba ba magarsa ake ba, sauran matan nashi ma suke cida kansu. Sauran ƴaƴanta kuwa na ma'auri suma taimakon suke nema, tunda dama dai Babu ɗinne taƙamarsu a baya, tunda komai ya suɓuce kuma suma suka shiga halin shiga ukun. Haƙila ce ta shigo wajen tana taunar cingam tana waƙe-waƙe, kanta ɗauke da botikin cin-cin da take yi na sayarwa. Duk da azumi ne haka take fita da shi talla, idan akai magana tace yara take saidawa ai. Ko suma yaran azumin suke. Rashin mutuncin Sule dama ita Haƙilar kanta da uwarsu kesa babu wanda ya iya cigaba da magana. Dan suma mazan gidan yanzu tsoronsu suke ji. Muƙut Gwaggo ta haɗiye yawu tana bin botikin cin-cin ɗin Haƙila da kallo duk da azumin da take. Haƙila ko ko kallonta batai ba ta shige ɗakinsu ta ajiye botikin, babu jimawa ta fito da ɗaurin ƙirji alamar yin wanka, sai ƙunƙuni take a ranta wai Temo... ya bata wahala, shege gashi ba wani kuɗin kirki yake bata ba. Duk yanda zai gurjeta baya iya wuce dubu biyar yace ta bishi bashi. Kullum kuma aikin kenan, ita kuma tana zuwa ta bashi kanta ne kawai saboda yana mata yanda take so. Temo... Dai inyamuri ne irin masu shiga ƙauyukan nan su buɗe shago, sunansa Temoty ne. Mutanen Giro ke kiransa Temo.... Temo shine ya fara keta budurcin Haƙila saboda shegen kwaɗayinta, tun tana shan wahala harta goge, dan gaba ɗaya har zuwa yanzu shekarun haƙila basu wuce goma sha ba. Kai ko ƙirjin ma yanzu ne yake bayyana a jikinta sosai, ƙwailayen ma bata gama cika cif-cif ba amma idonta ya buɗe. Dan yanzu har cikin Suru samarine da ita kala-kala. Abin tausayi ga rayuwar yarinyar nan indai ta fita a gida to yini take daga ɗakin wancan saurayi zuwa wancan kango ko gajiya batayi, ba kuma komai ya sata zama karyar maza ba sai shan magunguna kamar ba yarinya ba. Sarai Sailu ta jima da sanin Haƙila nabin maza, amma kuɗaɗen da take kawo mata da ɗan shayi da burodin baba kalla da indomie da tsire yasa ta kasa yin magana. Kai bama ita ba matan gidan kansu sun sani, tsoron Sailu ya hana su cewa uffan... Gwaggo na ganin Haƙila ta shige bayi ta miƙe da sauri ta afka ɗakin. Cin-cin ɗin ta ɗebo a cikin zani ta fito, jikinta na ɓari ta afka ɗakinta ta ɓoye. Ta goge hannunta da man cin-cin ɗin ya ɓata ta dawo ƙofar ɗakin ta sake zama kamar batai komai ba. Babu jimawa kuwa Haƙila ta fito ta sake wuce Gwaggo. Tana ko shiga ɗakin su sai gata ta fito kamar an jehota. Zaram Gwaggo ta miƙe abinka da mara gaskiya, gashi data ɗauka cin-cin ta manta ta rufe botikin. Wani irin cin kwallar Gwaggo Haƙila tayi cikin ƙaraji kamar sa'arta tace, “To tsohuwar banza bani kuɗina, munafuka ɓarauniya”. Muryar Gwaggo har rawa take, “Kudinki kuma haƙila, ni na ɗauka miki kuɗi ne?”. “Wlhy zan iya sharara miki mari anan gurin kema kin sani, idan baki ɗauka min kuɗi ba ai kin ɗauka min kayan kuɗi ƙaramar ɓarauniya dako satar baki iyaba ma. Ban kuɗin cin-cin ɗina inba haka ba wlhy na saki zanen nan anan nai tsirara mu daku.....” “Haƙila! Haƙila! Uwar tawa kika shaƙema wuya haka kina jifanta da sunan ɓarauniya?”. Babu ne dake shigowa yay maganar. Baki sosai Haƙila ta gatsina, cike da tsiwa da rashin girmama iyaye tace, “Yo Babanmu ita taja, daga fa shigata wanka ta afka ɗakin Innarmu ta ɗiba min cin-cin, itama ba haka take kiranmu ɓarayi ba, bayan kuma a wajenta muka gaji satar tsohuwar alakwankwan kawai”. Wani irin runtse idanu Babu yayi ƙirjinsa na masa zafi. Cikin rawar murya ya ce, “To kiyi haƙuri ki saketa. Gwaggo miyasa kika taɓa mata kaya?”. Kuka Gwaggo ta fashe da shi itama. Dan harga ALLAH taji shaƙar nan ta Haƙila. “Yanzu Habibu ka yarda da maganar ƴarka kenan na ɗauka mata cin-cin ɗin?”. “To Gwaggo ni mizance. Kinga fa ranar sai da nai miki nasiha akan al'amarin Sule da Haƙila a gidan nan, na nuna miki ki daina shiga sabgarsu su ba kamar su Shahidah bane da kike iya tankwarawa. Uwarsu kuma ba kamar Asiya bace da zatai miki kawaici ta kauda ido. Kika min alƙawarin dainawa gashi tun ba'aje ko'ina ba kunayi.” “To wai dama kai baba kana tunanin wannan kilakakkiyar tsohuwar zata kama kanta ne a cikinmu. Mu dan ALLAH ma ka daina mata wata nasiha ka barmu da ita mu gurji ruɓaɓɓen bakinta da baya iya shiru jarababbiya kawai. Kuma wlhy sai kin biyan kuɗin cin-cin ɗina ko kuma yanzu na kira Hure dilalliya tasai tsohon gadon ɗakinki a kuɗina”... “Ai bama sai kin kira Hure ba ni kaina muyi ciniki ƙanwata dama na gaji da kwana ƙasa cinnaku namin walmakalifatu.” “To shike nan ma Yaya Sule”. Haƙila ta faɗa tana sakin wuyar rigar Gwaggo. Ƙarasowa Sule yay ciki batare da ko kallon Babu yayi ba, dan shi bama ya magana da Babu saboda ya masa faɗa gaba yake da shi. Gwaggo da Babu na tsaye kamar gumaka su Sule suka shiga ɗakin Gwaggo. Gadon ƙarfenta ƙarami suka ɓallo, bayan sun zazzage mata katifar rimi dake kai da ƴan tsummokaranta. A gabanta, a gaban Babu sukai cinikin gado Sule ya bama Haƙila kuɗi yace ta tayasa su kafa gadon a ɗakinsa dake tsakanin na Gwaggo da na uwarsu. “An gama babban yaya, amma tsaya abama Baba la'adar ganin ido mana”. Haƙila ta faɗa tana matsawa kusa da Baba ta saka masa ɗari biyu a aljihu, tako zo kim-kim suka kama gado zuwa ɗakin Sule suka haƙa. Katifarsa da taima gadon yawa dan ta 6by6 ce daya sato a wani gida haka suka ɗorata a gadon. Ya haye ya wani baje yana sauke numfashi. Itama Haƙila hawa tayi tana faɗin, “Yaya bara na ɗana nima”. Dariya ya sanya da faɗin, “Ƴar son banza, ai ni wannan satar cin-cin tamun rana. Wai ina babarmu?”. Baki haƙila ta taɓe, “Kaima ka sani tana can biye-biyen ƙauyuka wajen malamanta neman asiri”. “Ko kuma masu danneta ba”. Dariya Haƙila ta sanya, cike da shaƙiyanci tace, “To kaga laifinta ne, Baba ya riga ya ruɓe dole taje inda zata samu ƙarfi. Nidai tsorona kawai karta kwaso mana ciki wani susu can. Amma bari nasan maganinta, maganin hana ɗaukar ciki zan dinga jefa mata a ruwa bata sani ba”. Dariya sosai Sule ke kwasa. Kai bakace hirar uwarsu mahaifiya suke yi ba..........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖5️⃣1️⃣ ______________ .........A waje kam jiri ne ya nema kwasar Gwaggo, sai da Babu dake hawaye ya kamata ya zaunar sannan. Zama yay shima kansa a ƙasa yana kuka yace, “Gwaggo kinga sakamakon ko? Ni nasan hakkin Asiya bazai barmu mu zauna lafiya ba, hakkin ƴaƴana bazai barmu mu zauna lafiya ba. Baba Umar ya min komai na gatan rayuwa shi da Mama Lubabatu. Amma suka tafi suka barni da ƴarsu ɗaya jal na gagara riƙe amanarta, na cinye dukiyarta, na wulaƙantata, na ƙuntata rayuwarta, haka nake hanata hakkinta saboda karuwaina, nazo a ƙarshe ma nace ƴaƴan da muka haifa ta hanyar sunna ba nawa bane ba. Gwaggo duk kece kika ɗorani akan hakan, kika takura sai na auri Sailuba wai dan tayi maganin Asiya. Yau gashi ba maganin Asiya Saulu keyi ba maganinki da ni take yi ita da ƴayanta. Jiba yanda na koma, kamar ban taɓa sanin a daga ilimi ba, kamar ban taɓa rayuwa a birni ba, kamar ban taɓa yin aiki ba wai aikin ma na ƴan sanda harda matsayin dpo. Gwaggo hakkin Asiya bazai barmu ba. Jiba inda muka samu Asiya, jiba ƙyaƙyawar rayuwar da take ciki, ƙaton gida, tana auren babban mutum, ta ƙara komawa yarinya kamar ba ita ta haifi su Shahidah ba, ƴaƴa mazan da kike mata gori taje ta haifesu acan. Ni ga nawa nan ya zame min ƙadangaren bakin tulu. Nayi nadama Gwaggo, nayi ALLAH wadai da halina”.. Kuka ya sarƙeshi, itama Gwaggon kuka take sosai kamar numfashinta zai bar gangar jikinta...... __________★ AA na sashen Oum har sai da ruwan ya ƙare ya cire mata. A hakan ma bashi da niyyar tafiya sai da Abah ya kaɗa kansa. Badan yaso ba ya tafi. Alhamdullah itama Maanal ɗin da asuba sai ta tashi jikin bawani zazzaɓi. Sai ƴar ramar da tayi a fuska. Babu yanda Oum batai da ita karta ɗau azumi ba amma ta marairaice akan zata iya, dole ta ƙyaleta ta ɗauka.... Misalin takwas duk suka tashi, kamar yanda suka saba su matan suka fara shirin fita tafsir. Suna fitowa AA da RK na shigowa gidan a motar RK. AA ne ke driving ɗin, samun waje yay yayi parking hankalinsa duk akan Maanal da Oum ke gyarama hijjab wai ya natse mata wuya da yawa. A tare suka fito, RK ya tsaya yana amsa gaisuwar su Najma, AA kam hannu kawai ya ɗaga musu ya ƙarasa inda Oum da Maanal ke tsaye. Cikin muryar nan tasa mara fitar da sauti mai ƙarfi ya furta, “Oum ina zakuje haka da safe?”. Kallonsa Oum tayi tana murmushi, yayinda shi kuma suka haɗa ido da Maanal, sai kuma duk suka janye a tare cike da basar da juna. Dai-dai nan Oum ke bashi amsa da, “Tafsir mana Auta, koka manta ne? Kuma za'a tambaya ai daga ina haka da safe”. “Oh na manta Oum, munje nan baya ne ganin wani fili, wajen kuma ma dai sai a hankali bai wani min ba, amma Uncle R ya dage a saya sai a gyara”. Kai Oum ta jinjina alamar gamsuwa, Maanal kam dariya take a zuciyarta, ALLAH bata taɓa jin AA ya kira RK da Uncle ba sai yau. Shima RK daya iso wajen sai da yace, “Tab Aunty hakan ɗanki ya fara tsorona ne, wai ni yake kira Uncle yau imagen”. Dariya Oum tayi, haka itama Maanal sai da ta murmusa. Sai kuma a hankali tace ina kwananku?”. RK ne kawai ya amsa, tare da tambayarta yaya jiki. Shiko AA kallonta kawai yake. Haka kawai murmushin da tayi ɗin ya bashi haushi, a ganinsa miyasa zatai murmushi a gaban RK. Yi Maanal tai kamar bataga yanda ya canja fuska ba suka wuce abinsu, tunda dama tasan ai haushinta yake ji, jiyan ma dan kawai ya ganta a halin ciwo ne yasa ya sakko... Sai a lokacin itama Mamy ta fito da tata tawagar. Babu wani damuwa a fuskar RK ya gaida Mamy, sai ya ɗan matsa gefe kamar zai amsa waya. Risinawa AA yay yana gaisheta. Bata amsa masa ba, sai alama da taima su Nuratu da ido su wuce. Haushi Nuratu taji, gashi sun gaida AA ɗin daga ita har Saheeba babu wanda ya amsawa, dama kuma da baƙin ciki da tashin hankalin maganar cikin Maanal ta kwana ta tashi. Dan da catai ma zata koma gida harta haɗa kaya sai da uwarsu ta kiranta ta kwaɓeta, tare da tabbatar mata in dai ciki ne na banza dan sai sun ɓarar da shi. Wannan ne ya ɗan sanyaya mata zuciya harta fito domin binsu tafsir ɗin. Cike da isa da gadara Mamy dake kallon AA tace, “Saboda ban isa ba zuwa yanzu kasan daɗin mace shiyyasa bakaje har inda nake ka gaisheni ba sai anan?”. Wani kalar kunya ce ta ratsa AA saboda furicin Mamy, wai saboda yasan daɗin mace ya rabba. Kansa dake ƙasa ya girgiza mata, sai kuma a hankali ya furta, “Ba haka bane Mamy. Tun sallar asuba bamu dawo gidan ba ni da Rafeeq sai yanzu. Amma kiyi haƙuri”. “Kai ka sani dai, zamuje tafsir, idan mun dawo ina nemanka. Idan kuma kaƙi kazo zanzo har sashen uwar taka da kake ganin ta fini daraja na sameka ni....” Wani irin rumtse idanu AA yayi, zuciyarsa na wani kalar rarrabewa. Sai kuma kamar wanda aka tunatar yay saurin buɗe idanunsa da har sun canja launi yana kallon compound ɗin. Ajiyar zuciya ya sauke ganin babu RK a wajen. Wlhy baya fatan wani a kaf ɗin ahalinsu yasan wannan halin na Mamy sam. Sai dai kuma abinda AA bai sani ba komai a kunnan RK ya kasance, yana ganin AA ɗin zai juyo ne ya shiga bayan motoci ya ɓuya dan shima baya son AA ɗin yasan yasan halin Mamy a yanzun. RK na a wajen zuciyarsa cike da tausayin AA har sai da ya hangesa ya shige sashensa sannan ya fito. Shiru yay a wajen yana tunani, sai kuma zuwa can ya saki murmushi dan yana ganin zai fara aiwatar da plan a na shirinsa a yau ɗin nan. Shi ɗan faka-faka ne, dan haka kai tsaye sashen Abah ya nufa dan yasan yana gidan bai fita ba. Abah kuma bai wani damu da barcin safe ba sosai.... Cikin sa'a kuwa a falo RK ya samu Abah. Zama yay kusa da shi suka gaisa cike da ƙaunar juna. Sai kuma suka fara hira abinsu. A cikin hirar RK ya ce, “Yaya nikam sai yaushe zaka ba Ajwaad iyalinsa ne?”. Murmushi Abah yayi idonsa akan television. “Zan bashi Rafeeq, akwai abinda nake jira ne. Amma dai bayan salla in sha ALLAHU. Tunda kaga ma ya riga ya nuna mana ya daidaita da matarsa tunda har ga ciki”. Dariya RK yay a karo na farko, sai kuma ya ce, “Tom hakan dai yafi kam Yaya, a barsu haka nan kawai, na tabbatar komai zai ƙarasa dai-daita. Sai dai inada wata shawara”. “Okay ta micece?”. “Ba komai bane Yaya, inaga ya kamata a sake musu sabon biki, tunda kaga sanda akai wancan su kamar ma babusu a ciki Ajwaad na fama da kansa. Ajwaad mutum ne na mutane, ya kamata ace aurensa ya shiga lungu da saƙo na ciki da wajen ƙasar nan. Sannan yanda Ajwaad da Maanal suka rayu sun cancanci bikin aurensu ya ajiye babban tarihi a kundin masoya na duniya”. Dariya Abah yayi sosai. “Kai ALLAH ya shirya ka dai Rafeeq, wato a kundin masoya na duniya?. Shawaranka yayi sosai, dan ni kaina ina yi wannan tunanin kodan ita Maanal ma. Wlhy bazan ɓoye maka ba duk cikin surukan nan nawa nafi ƙaunarta, kuma wannan ƙaunar tun tana yarinyarta nake mata ita, jinta nake tamkar ɗaya daga ahalina. Shiyyasa ko maganar auren Nuratun nan ba sonshi nake ba sam, dan bazan so zamansu tare ba sam...” (Anzo wajen) RK ya faɗa a zuciya, a fili kam fuskarsa da murmushi ya ce, “A'a yaya ba'ace haka ba, tunda bamu san mi ALLAH ya shirya ba. Amma da zai yiwu kodan samun nutsuwar zamansu ka zauna da AA ɗin kaji ta bakinsa akan hakan. Idan ya nuna baya so to a bashi lokaci ana ƙara kwaɗaita masa auren Nuratun har komai ya dai-daita”. “Uhmmm kuma hakan fa yayi Rafeeq. ALLAH yay maka albarka, shiyyasa a kullum nake faɗan kai yaro ne da halin manya.” Murmushi RK yayi sosai, dai-dai nan babban Yaya yay sallama. Abah ya bashi izinin shigowa. Ganin su zaune kamar masu meeting ya ce, “Tunda meeting ake na ƴan uwan juna kona koma ne?”. Dariya Abah da RK sukayi. RK yace, “Shigo ai mun gama”. Fuskar babban Yaya da murmushi shima ya ƙaraso. Abinda suka tattauna ɗin RK ya tisa masa amma banda batun Nuratu. Aiko babban Yaya ya bada goyon baya shima ɗari bisa ɗari. RK ya ɗaga waya ya kira Fawzan shima. Babu jimawa ya shigo da alama baima jima da tashi barci ba. Anan suka dinƙule suna shawarar shirya bikin. Shi ko AA bai san anayi ba, yana can sashensa yay wanka ya kwanta al'amarin Mamy na cizon masa zuciya.... ★Bayan sun dawo tafsir har akai azhar Mamy bataga idon AA ba. Ranta sai ya ƙara ɓaci matuƙa. Ta ɗaga waya zata kirashi sai ga Fawzan ya shigo sashen. Duk yau basu gaisa da Mamyn bane shiyyasa yace bara ya shigo ya dubata dan fita zai yi. Ita kaɗai ce zaune a falon sai Anum na barci a kujera. Tunda ya shigo take kallonsa fuska da ɗan murmushi dan ta haɗiye ɓacin ran AA dake cimata rai da ƙyar. Zama yay yana gaisheta, ta amsa masa da kulawa, tare da tambayarsa fita zai yi?. “Eh wlhy Mamy zan ɗan je wani waje ne, tun ɗazun naso fita sai kuma zafin ranar nan ya hanani. Yanzu naga ta ɗan risina shine zanje na samu na dawo da wuri bana son tafsir ya wuce ni”. “Eh haka na da ƙyau kam. ALLAH ya taimaka ya bada sa'ar abinda za'a fita yi ”. Cike da jin daɗi ya amsa da Amin. Sai kuma ya yunƙura zai tashi idonsa akan Anum yace, “A'a Babyna kuma ana nan ashe?”. Cikin ɗan taɓe baki Mamy tace, “Tana nan ai yanzu ɗasawa muke yi, uwarce abu kaɗan ta make su gaba ɗaya ta koya faɗa kwana biyu, kuma ina zaton kamar ciki ne ya sata hakan”. Cike da farin ciki Ya Fawzan ya ce, “Wow! Ciki Mamy. Kai Masha ALLAH abu yayi ƙyau, abinda ake ta fata”. “Aiko dai ai dama komai lokaci ne da shi, balle ma tunda har anyi biyu dama sun so tada hankalinsu ne. Saura ku, ALLAH ya kawo muku naku.” Murmushi kawai Ya Fawzan yay baice komai ba. Sai kuma ya fara ƙoƙarin miƙewa. Dakatar da shi Mamy tayi, kafin ta fara magana muryarta na ɗan rawa. “Fawzan amsa min zaka yi da amin ba shiru ba, al'amarin nan naku na damuna, ni dai da ace zakabi ta tawa da aure ka ƙara, kwanaki na maka maganar hakan ba kace min komai ba. To gaskiya na fara zuwa bango da zaman nan haka babu haihuwa. Shiyyasa ma duba nan”. Ta miƙa masa wayarta. Bai musa ba ya amsa wayar. Hoton ƙyaƙyawar budurwace da zata iya kai 29years haka. Daka ganta kaga ƴar gayu sannan gogaggun ƴan boko fitsararru. Fara ce tas dan duk da a hoto ne a kallo ɗaya zaka tabbatar da farar ce. Batare da nuna wani yanayi ba ya ɗago ya ce, “Na ganta Mamy wacece ita?”. “Ita ce wadda nake maka sha'awar aure Fawzan”. Wani kalar, dumm-dumm zuciyar Fawzan tayi, cike da mamaki ya ce,........✍️ _Tofa aiki ya biyo takan yaya Fawzan yau. Bari muga zai amshi batun Mamyn ko zai mata batun Najma🏃🏃🏃🏃🏃_ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖5️⃣2️⃣ ______________ .........“Wannan ɗin Mamy?”. “Ƙwarai Fawzan. Yarinya ce mai tarbiyya sannan ƙyaƙyawa. Dan wlhy tafi Nibras komai. Za kuma ta baka farin ciki fiye da ita. Dan zuwa yanzu na sake yarda Nibras sakaran yarinya ce, uwarta ta riga ta mata tarbiyan banza da mugun gata. Sam bata da alƙibla ta kula da miji kamar ba mace ba, abinda kawai ta sani cin kwalliya ta tafi office...” A zuciya Fawzan yace (wannan kadai kika fahimta Mamy) a fili kam sai yay murmushi. Babu wani damuwa a tare da shi ya ce, “Mamy ai muna zaman lafiya, sannan haihuwa ta ALLAH ce kuma lokaci ne. Yau baga Ajwaad da Maanal ba, rayuwarsu ma aya ce a garemu bayyananniya.” Cikin ɗan kaushin murya Mamy ta ce, “Na fika sanin haka Fawzan, sai dai kamar yanda na faɗa na gaji da ganin ka haka babu yara, dan haka umarni nake baka akan yarinyar nan, sunanta Amani, a Kano take, ɗiyar ƙanwar sarkin Kano ce uwa ɗaya uba ɗaya, babanta ma nada tashi sarautar dan shima ɗan gidan ne kozin suke da Sarkin auren zumunci ne da uwarta. A U.S aka haifeta, can tai dukkan karatunta. Dan tana aikinta babanta yasata ta dawo Nigeria saboda auren yake son yay mata. Ni bance ka rabu da matarka ba, amma yana da ƙyau kayi auren nan don a tantance a ina matsalar take”. Gaba ɗaya Fawzan ya zama kamar wanda aka zaunar a wajen domin tarihi kawai yana kallon Mamy. Wani irin mamaki take bashi, miyyasa a komai na rayuwarsu bata nuna tana da alaƙa da su ne? Amma a kan aure itace mai zaɓa musu mata?. Kallafa yanzu akan Ajwaad, an wani ƙaƙaba masa Nuratu yarinyar da sam bata da tarbiyya. Kalla abinda Nibras ke masa, kwanciyar aure bai iya yayi da ita ba sai ya saka mata ƙarfi, sannan wai ƙaninsa take so saboda bata da hankali. Kalla Babban Yaya, duk da shi bamai yawan magana bane wasu lokutan akan fahimci ƴar tsamarsa da Saheeba a gidan. Dukansu fa zaɓin Mamy ne, amma bata taɓa hango illar yaran ba balle tunanin suna jin daɗin zama da su ko basa ji. Oum itace ta rainesu, itace dukkan wahalarsu a rayuwar nan. Duk wani abinda ɗa yake yi akan abin uwa da nata suke yi, a kwai wani lokaci daya shiga tarnaƙin ƙuɗi sunyi wata kwangila kuɗaɗensa suka maƙale gwamnati taƙi biya, ya shiga matsi sosai yaƙi kuma faɗama kowa Oum ce ta fara harbo jirginsa. Haka ta zauna ta dinga masa faɗa daga ƙarshe ta ajiye masa atm ɗinta tace yaje ya ɗiba ko nawa yake so, yama riƙe atm ɗin ya dinga amfani da shi har sai komai ya warware. Daya nuna mata bazai amsa ba sai ta saka masa kuka akan mi yake nufi tana mahaifiyarsa ta bashi abu ya maido mata. Haƙuri ya dinga bata ya ɗauka, haka ya dinga amfani da card ɗin tsahon watanni babu wanda yaji ko ya gani har sai da komai ya daidaita masa sannan ya maida mata, daya saka wasu ƴan kuɗi a ciki catai idan bai cire ba saita cimasa mutunci. Haka dole ya cire su. Amma wlhy Mamy zai iya cewa bata taɓa damuwa da kana da shi ko baka da shi ba umarni kawai zata baka ka tura mata kuɗi, ko ka turama cikin ƴan uwanta kuɗi kaza..... “Wai tunanin mi kake yi ne?”. Mamyn ta katse masa tunani. Ajiyar zuciya ya sauke. Sai kuma ya miƙe yana faɗin, “Shike nan Mamy ki bani lokaci zan kirata a waya naji idan zamu iya dai-daitawa.” “Ya dai fi maka”. Ta faɗa a gatsine tana ɗauke kai. Jiki a sanyaye ya fice a sashen. Sai ya ji bama zai iya zuwa sashen Oum a haka ba dan zata gane a yanayin da yake. Mota kawai ya shiga ya fice a gidan..... Mamy bataga AA ba sai gab da Asr, dan da shirinsa ma na fita massallaci ya shigo mata. Tasan yayi haka ne dan karya daɗe. Cike da takaici ta cije lips ɗinta tana harararsa. Shi dai sai ya ɗauke kansa kawai yana kaiwa zaune yace mata “Ina yini”. Bata amsa masa ba, sai ma cike da zafin rai ta ce, “Ajwaad ni zaka wulaƙanta ko?”. Jiyay gaba ɗaya zuciyarsa na masa ɗaci. Kansa ya girgiza mata. “Mamy har abada kinfi ƙarfin wulaƙanci ga wani ma balle ni. Ko takalmin da kike sakawa daraja ce da shi a wajena balle ke. Kiyi haƙuri ina kwance ne kaina na ciwo shiyasa ban shigo ba, na kuma san kema a ɗan tsakanin nan kina barci ne.” “Idan ka kare kanka anan shi kuma cikin da kaje kaima waccan ƴar iskar yarinyar ba wulaƙantani kayi ba kenan? Ajwaad har ni zan maka gargaɗi akan taɓa yarinyar can amma kaje ka taɓata harda ciki! Maybe ma tun kuna a gidan nan ne”. “Mamy a gidan nan kuma. Amma kowa zai iya zama shaidar tunda Maanal tazo gidan nan da sunan matata bata taɓa zuwa sashena ba sai sau biyu. Na farko ita da Oum ina cikin ciwon nan. Na biyu shara da nace Oum ta sakata tamin lokacin kuma ina office ma. Tunda kuma kika hana ban sake sakata ba...” “Idan bataje sashenka ba ai ka ɗauketa a mota kun fita ko. Sannan kuna zuwa office. Ranar daka nuna min ban isa ba agaban kowa na gidan nan ka fita da ita. Tunda kasan ba budurwa bace dan ka ɗauketa kunje kun sheƙe ayarku har wa zai gane. Balle tunda wancan abun ya faru dama ta cigaba da rabawa ƴan iskan Abuja waje duk ya buɗe.....” Wani irin runtse idanu AA yayi, zuciyarsa kuwa sai wani duka take a cikin ƙirjinsa da sauri. Amma bawan ALLAH cike da jarumta sai yay murmushi. “Mamy kiyi haƙuri, koma miya faru ko ta aikata dai duk ya wuce tunda yanzu a gidan aure take. Sunanta matar ɗanki. Abinda kuma kike tunanin shima nayi kimin afuwa.” “Haka ka iya amaka afuwa! A maka afuwa kullum, amma sai iya shege fal cikinka.” Murmushi kawai shi dai yay mata dan darun Mamy da ban ne. Aiko taji haushin murmushin nan, sai ta sake hawa ta balbalesa da masifa ta inda take shiga bata nan take fita ba. Faɗan kuma duk akan Nuratu ne da maganar kiranta data sharɗanta masa amma tunda ya tafi ko flashing baima Nurry ba, sai batun ciki da yaƙi cewa komai akai. Akwai randa ya kirata bayan sun gama magana tana cewa ga Nuratu ya yanke kiran da wayar ma gaba ɗaya. Shi dai kansa na a ƙasa harta gama. Ta dawo kan batun Documents ɗinsa da batun sunan Maawad. “Mamy dan ALLAH kibar maganar nan, shi sunan companyn minene amfanin saninsa? Sannan documents ɗin nan dan na amshesu a hannun Oum mi zakiyi da su? Su dai ba abinci bane balle ace za'a ci”. “Uwar ubanka zan yi da su!!”. Ta faɗa a tsawace. Ba ƙaramin dukan zuciyarsa zagin yay ba, dan abinda bata taɓa masa ba kenan zagi. Barta dai da masifarta da sharuɗɗa. Kalamanta ne masu tsauri suka cigaba da kekketa masa zuciya duk dai akan Maanal da Oum daya rasa mi suka tare mata a wannan rayuwar.. “Wlhy a wannan karon zan iya tsine maka Ajwaad, zan iya cireka a cikin ƴaƴan dana haifa na manta da kai. Badai ni kake nunawa karuwar yarinyar nan mai wulaƙantattun iyaye da Fateema sun fini ba, zanyi maganinka wlhy. Dan ubanka tashi kaban waje shashasha da bai san kishin kansa ba...” Tsam AA ya miƙe cike da girmamawa ya furta, “ALLAH ya huci zuciyarki”. Daga haka ya juya ya fice. A ƙofa suka ci karo da Abah. Gaban AA yay mummunar faɗuwa. Babu shiri ya haɗiye yanayinsa tare da fisgo jarumtar dole ya ce, “Abah barka da yamma”. Idanu Abah ya ɗan zuba masa na sakanni, sai kuma yay murmushi da amsa gaisuwar sannan ya ce, “Dama baka tafi massallaci ba ɗan Oum?”. Murmushi AA ya ɗanyi, “Yanzu zan wuce Abah, na shigo na gaida Mamy ne tun safe bamu gaisa ba saboda mun fita da Uncle, sanda muka dawo kuma zasu je tafsir”. Sam AA bai iya ƙarya ba, dan haka ko yaya yayita sai ka gane masa, shiyyasa akan abu koda bazai faɗi ainihin gaskiya ba, zai faɗi wani yanki na abun da bazai sa ka damu da son jin wancan ba. Yanzun ma murmushi kawai Abah yayi, sai kuma ya ce, “Okay muje to kawai idan na dawo na zo, dama zan ma Kamila magana ne amin farfesun kayan ciki wajen yin abincinsu.” “To Abah bara na gaya mata mana”. “Kaga barta zan tura mata saƙo gashi can za'a tada salla”. Daga haka yaja hannun AA ɗin suka wuce. Wata irin wawuyar ajiyar zuciya Mamy ta sauke. Dan tunda taji maganar Abah ta miƙe zambar zuciyarta na gudu a ƙirjinta...... __________★ KADUNA Al'amarin Yazeed ya girmi kowa a gidan, dan tsohon kwana uku kenan da dawowarsu amma ko leƙe bai shiga ya gaida kowa na gidan ba. To dama dai Ammie ce sai ƙannensa sai Daddy. Ko abinci da Ammie ta aika musu a randa suka dawo, dawo mata da shi akai tare da gargaɗin karta sake kawowa inji Aunty Sabuwa. Aiko Ammie bata sake maimaitawa ba. Hankalin ƙannensa a matuƙar tashe yake. Suna kuka suka kira Hajiya Yaya suka sanar mata komai. Sosai hakan ya bama Hajiya Yaya mamaki, amma sai ta danne tace su barshi ai zaizo gaisheta zatai masa magana. A randa suka dawo ne akai wanan waya, amma har yau kwana uku Hajiya Yaya bataga ƙeyar Yazeed ba a gidansu. Koda ta tuntuɓi mahaifiyarsu da maganar sai tace ita ina ruwanta kuma. Dan dama tunda Hajiya Yaya tazo gidan babu ruwanta da ita. Ita dai ba'a sakata aikin komai, amma babu mai mata magana a tsakanin Baba da Mamansu, aikinta kuma masu aiki bazasuyi ba ita takema kanta komai hatta girki.........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖5️⃣3️⃣ ______________ .........Yau daya kasance cikar kwanaki uku tana zaune shiru abin duniya ya isheta. Kiran Amrah ne ya shigo mata. Tai shiru tana kallon wayar kamar mai tsoron ɗauka. Har kiran ya katse sai ga na Basira. Shima bata ɗaga ɗin ba ya tsinke, kamar haɗin baki Nusaiba ma ta kira, yanzu kam zuciyarta sai da ta jijjiga. Hannunta na rawa ta ɗauka wayar takai kunneta bayan ta ɗaga. Kukan Nusaiba ya daki cikin kunenta sai da ta runtse ido. Kafin ma tayi magana Nusaiban ta fara mata bayani cikin kuka. “Mammah dan ALLAH ki dawo, Yaya Yazeed zai kashe Aunty Nasiba. Gata can ya rufeta a ɗaki sai duka yake wai ta zagi Nazeefa. Gashi su Daddy basa gida sai mu kaɗai”. Wani irin rawa jikin Hajiya Yaya ya shiga yi, ai bama tasan ta miƙe ta figi hijjab ba tai waje. A ɗimauce ta fice a ƙafa daga gidan cikin sa'a ta samu napep zai wuce ƙofar gida ya ajiye wasu ta shige tana faɗa masa inda zai kaita. Yanda ta azalzala masa gudu ya dinga zubawa bana wasa ba, cikin ƙanƙanin lokaci suka iso ƙofar gidan Chalawa. Sai lokacin ta fahimci ma babu kuɗi a jikinta. Mai napep daya fahimci hankalinta a tashe yake sai yace taje kawai ya zata mutuwa ce, dan duk wanda yaga Hajiya Yaya kam yasan babu lafiya, sannan gidan Chalawa ba ɓoyayyen gida bane, Napep ɗin ma sai suyi ƙyauta da su balle kuɗin hawanta. Burum ta buɗe kofar gate ta shige, maigadi daya zabura yana ganin itace ta shiga ya sauke ajiyar zuciya. Dan shima hankalinsa a tashe yake da irin dukan da Yazeed kema Nasiba tun daga sashensa har sashen Hajiya Yaya. Yarinyar kam yau ta daku sosai, koma yace sun daku, dan daga ƙarshe haɗawa yay har sauran yaran ya cigaba da jibga. Sai yanzu ne babu jimawa ya fito yana huci ya shige sashensa kaman wani bahagon zaki... Wani irin bugawa kan Hajiya Yaya ya kusan yi lokacin data shiga sashenta ta samu yaranta kwance a ƙasa kowa na kuka jikinsu duk sayin bulala Nasiba kam ma harda jini a goshinta da bakinta. Suna ganinta suka taso a guje suna kuka da nuna mata jikinsu. Jagwab Hajiya Yaya takai zaune a kujera, wani irin jiri-jiri take gani ma ita kam. Tafi minti biyu kafin da ƙyar ta iya furta, “Mi kukai masa?”. Cikin kuka Nusaiba tace, “Wlhy babu komai Mammah. Daga Nasiba taje sashen kiranshi dan muna son muyi magana da shi akan tunda ya dawo bai ko kallemu ba mi mukai masa, sannan kema baije inda kike ba, shine kawai ya hau jibgar Nasiba tun daga can wai dammi zatazo tace yazo muna nemansa shi sa'anmu ne.” Zuciyar Hajiya Yaya har kumfa take, ta ce, “Ina Daddyn ku?”. “Sun fita shi da matar can”. Cewar Umaimah...... Hajiya Yaya yanzu fa za'a fara wasan🤣😜🏃 ________★ Yau kam dai zaman buɗa baki bazai yiwu a tsakar gidan ba. Dan wani irin hadari ne mai nuna alamar cike yake da iska ya harɗe garin na Abuja musamman ta yankin su AA tunda nan ɗin suke gani. Dole anan sashen Oum aka gyara falo aka shirya komai. Sannan kowa ya fara ƙoƙarin zuwa yay alwala harma da masu son yin wanka dan ƴan mintuna ya rage a kira salla. Yau su kaɗai sukai aiki babu Mamy, tana sashenta wai kanta ke ciwo. Oum dai taje ta mata sannu tare da Maanal. Suma sauran yaran duk sunje. An dawo domin zaman buɗa baki mazan suma sun shigo kamar jira aka fara iska. A kuma dai-dai lokacin Maanal ta fito hannunta ɗauke da bowl da aka saka akan tray an juyo farfesun naman kai a ciki. Ga naman da zafinsa, gashi a kwanon glass. Wani irin murmushin mugunta Nuratu dake bayanta ta saki saboda abinda take shirya ma zuciyarta. Maanal na daga ƙafarta data rage a cikin kitchen ɗin ɗaya na a waje zata ƙarasa fita kawai Nurry ta take takalmin, gaba ɗaya Maanal ta tafi ita da tray ɗin aiko ta fasa ƙarar tsorata tana ambaton sunan ALLAH da runtse idannunta dan ta gama fidda rai kawai sai taje ƙasa kuma sai ta ƙone maybe ma harda raunuka.... Sai dai kuma mi, cikin ikon ALLAH da rahamarsa taji ta tsaya cak ita bata kife ba tray ɗin na a hannunta. Sai dai yanda jikin nata ke rawa romon farfesun ya hankaɗa mata akan hannun. Babban Yaya daya iso wajen cikin zafin nama ne ya amshe tray ɗin, shi kuma AA daya riƙeta ya ɗagota gaba ɗaya ya saka a jikinsa dan jikinta wani irin rawa take na tsorata tama ƙi buɗe idanun sai hawaye dake rige-rigen sakkowa. Tuni kowa ya miƙe cirko-cirko an zagayesu. Muryar Abah cike da damuwa ya ce, “Amma ya akai ma ta fito haka kamar wadda aka hankaɗo?”. “Nima dai abinda zance kenan Aban su, yanda ta taho gaba ɗaya sai kace an hankaɗota ai”. Cewar Oum itama. Caraf Menoo dake kitchen ɗin ta fito tana faɗin, “Aunty Nuratu ce ta taka mata takalmi, kuma tana sane dan sai da tayi dariya ma sannan. Dama tunda ta shigo muna kwashe naman ni da Aunty Maanal sai take faɗin__“Yau zatayi maganin rashin kunyar wata mayyar namiji da cikin jikinta na asiri a gidan nan”___ mu bamu kulata ba Aunty ta gama zubawa tace na ɗakko mata cornflakes a store shi zata sha, na fito sai naga Aunty Nuratun a bayanta ta taka mata takalmi”. Gaban Nuratu dake maƙale a kitchen ya faɗi, jitai kamar ta jawo yarinyar taita jibga, shegiya ƴar ƙarama da ita sai bakin magana, jin falon yay shiru tai saurin juyawa zatabi back door, amma a mamakin kowa cikin wata irin tsawa AA ya furta, “Idan kika fita sai na baki mamaki yau a gidan nan!!”. Sosai tsawar tasa ta saka yaran nan razana, kowa ya ƙara maƙalewa jikin ɗan uwansa. Manyan kuwa a tsorace sosai suke kallon AA ɗin dan sun san halinsa sarai, asu yaran family ɗin idan suna gulmar yayun nasu sukan ce kaji tsoron ALLAH kaji tsoron marin Yaya AA, dan marin tsoffin sojoji yake yi. Abah zai yi magana ya Fawzan da yaga inda AA ke kallo sai ya leƙa kitchen ɗin, Nuratu data tsaya cak saboda tsawar AA har fitsari ta nema sakata shima cikin ɓacin rai ya furta, “Oh dama kina a kitchen ɗin. To fito nan”. Ganin yanda Yaya Fawzan yay da fuska ya sake saka gaban Nuratu dukan tara-tara, cikin son nuna pretending ta haɗiye tsoron ta fito a dake. Tana buɗe baki zatai magana a bazata kawai AA ya wani ɗauke fuskarta da mari. Ya ILAHI, wani irin shiru falon yay na sakan irin kamar mutuwa ta ratsa waje ɗin nan da yara kance. Yayinda Nuratu da azaba ta ratsama fuska har zuwa cikin brain ganinta ya shuɗe na wucin gadi kunnenta ya toshe sai wani tsauuuu!!! Take ji a cikinsu like an daki irin ƙarfen nan yay ƙara a ƙarshen dai nawa yay tsaiii!! Ɗin nan. Ta wani kalar tafi taga-taga zata faɗi Mamy ta tareta. Cikin rufewar ido da ɓacin rai AA ya sake yunƙurawa zai mareta Oum ta riƙe masa hannu, dai-dai itama Mamy ta zaburo a tsawace ta kira sunansa, “Ajwaaadd!!!”. Duk da yanda tsawar Mamy ta ratsa kunnen kowa a wajen a ɓangaren AA ko'a jikinsa. Yabar Nuratu ne kawai saboda riƙe masa hannu da Oum tayi. Ya wani irin watsama Nuratun mummunan kallo... Hannunsa Oum taja ganin zai yi magana tace, “Kaga ya isa zauna a duba mata hannunta koya ƙone”. Wani kallon banzar ya sake watsama Nuratu dake a jikin Mamy ya ɗaga Maanal dake jikinsa cak zuwa saman kujera... Sai a lokacin Nuratu ta saki kuka. Tsaki Yaya Fawzan yayi yabar wajen zuwa inda AA ke zaune Maanal a jikinsa. Oum na gefensu zaune tana duba hannun Maanal ɗin da yay ja. RK kam tuni dama yabar wajen, inda yasan suna ajiye kit ɗinsu na magunguna ya nufa. A karo na farko Babban Yaya da ransa yay matuƙar ɓaci ya zuba ma Nuratu ido. Sai kuma ya watsa mata harara da faɗin, “Shashasha kawai mai zuciyan banza. Yanzu da ALLAH bai hankaltar da Ajwaad ɗin ba wane irin faɗuwa kike tunanin yarinyar nan zatayi? Zatafa iya rasa rayuwarta kodan abinda take ɗauke da shi tunda da akansa zata faɗi, ga zafi gashi glass. Wato shirinki zubar mata da ciki, to bismillah kada ki fasa dan ALLAH....” shima ya ƙara zabura zai kai mata marin. Hannunsa Abah ya riƙe kawai, batare da yace komai ba yaja Babban yayan suka bar wajen suma. Har lokacin Nuratu na'a jikin Mamy da ranta yay ƙololuwar ɓaci, sai Saheeba dake gefen Mamy ɗin kamar gunki. A kusa da ita Nibras ce. Suko sauran duk suna can zagaye da Maanal, tuni Hashim ya ɗakko ƙanƙara da RK yace ya kawo. A cikin bowl da Meeno ta ɗakko itama aka sanya, AA ya amsa yana saka hannun Maanal a ciki. Baiwar ALLAH idanun yanzu babu hawaye, amma sunyi jazur alamar tana jin zafi sai sauke ajiyar zuciya take jin hannun a ruwan sanyi. Sannu Abah ya mata, ta jinjina kai, hakama Babban Yaya. Ta ɗan ji zafin ya sassauta mata. Sai kuma duk suka bata tausayi ganin kowa baici komai ba sun tare a kanta. Cikin ɗan rawar murya ta kalla AA da idanunsa suka kaɗe tace, “Ya daina zafin ka barshi. Oum muje ayi buɗa baki”. Cike da kulawa Babban Yaya yace, “Kin tabbatar ya daina?”. Kanta ta jinjina masa alamar eh. Shi dai AA bai gamsu ba. Amma da yake RK ya nuna maganin da zata sha idan taci abincin sai ya barta. Zaman cin abincin sukayi. Azaba ta ishi Maanal dauriya kawai take, gashi hannun dama. Tana tunanin ta yanda zata ci abinci sai kawai taga AA daya zauna a kusa da ita ya zuba ya juyo gareta. Cike da kulawa ya fara bata, duk da tana jin kunya haka ta daure ta dinga amsa. Bata wani ci da yawa ba tace ya isheta. Maganin ya bata ta sha, hankalin Oum dama kowa na'a kansu. Mamy ce kawai ke faman lallaɓa Nuratu taci abinci wai, amma ko sannu bataima Maanal ba. Wannan abu ya bama kowa dake wajen mamaki, sai dai babu wanda yay mata magana itama balle kula Nuratun dake kukan iskanci, fiskarta raɗam da sayin marin AA..........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖5️⃣4️⃣ ______________ .........Har lokacin sallah Isha'i yayi ana zabga ruwa. Dan haka aka gyara daga can gefe don yin salla, dan falon ba ƙaramin falo bane ba. Babban Yaya ne yaja sallar isha'i. Bayan an idar ya miƙe ya dawo baya ya tura AA gaba. Kallonsa AA yay zai magana, Babban yaya yace, “Cmon malam yi mana salla”. Sai ya kalla Abah, daƙuwa Abah yay masa. Sai kawai AA ɗin ya murmusa. Yana ɗan kallon gefen matan idonsa ya sauka akan Maanal suka haɗa ido. Baice komai ba ya juya ya kabbara sallan. Shine yay musu asham, karatunsa na fita da wani irin daɗi mai karya zuciya, ga nutsuwa. Daga ƙarshe babban Yaya ya sake rufewa da shafa'i da wutri. Bayan an idar gaba ɗaya Aba ya tashi yay nasiha mai ratsa jiki akan abinda ya faru tsakanin Nuratu da Maanal. Ya kuma bama Nurry umarnin matsawa ta bama Maanal ɗin da AA haƙuri. Jitai ranta ya wani ƙara ɓaci, amma bata isa yin jayayya da Abah ba. Haka ta je har inda Maanal take ta bata haƙuri. A mamakin kowa murmushi Maanal ɗin ta mata tace ba komai ai tsautsayi ne ta yafe mata. AA kuwa ko kallonta baiyi ba ma. Sai da Abah yay masa magana sannan yace yaji. Daga haka yay shiru. Gaba ɗaya sai abinda ya farun yasa zaman babu armashi. Ga ruwa ana makawa kamar da bakin ƙwarya. Dan ba'a samu tsagaitawarsa ba sai kusan sha ɗaya. Miƙewar Abah tasa kowa ma ya miƙe ya nufi nasa sashen.... ____________★ KANO Tuni Huznah ta ajiye batun azumi a gefe, dan kuwa dai ya gaggareta, kwance take rijib babu lafiya tun azumi na kwana takwas. Zuwa yanzu kuma kowa na gidan su Sageer yasan tana da ciki. Wannan abu na ƙona mata zuciya kullum sai tayi kuka. Gashi zuwa yanzu ta kasa sake samun damar kiran ko Maman Yaseerah ɗin ce ma. Dan kamar Sageer ya fahimceta sam ya daina ajiye wayar da inda take. Ta rame sosai sai uban haske data ƙara, komai taci sai amai. Yau dai da jikin yay tsamari dole sukaje asibiti bisa ga shawarar Zubaidah da yayarta. Gado aka basu, dan Huznah ta galabaita sosai saboda amai. Maman Sageer ɗin ce da kanta take zaune da ita a asibitin. Tana son ta saci wayarta ta gwada kiran maman Yaseerah tana jin tsoro. Haka dai ta haƙura. Sai da tai kwana biyu aka sallamosu. Mama tace zata wuce da ita can gidansu ta ɗan ƙara murmurewa Sageer yaƙi. Ita ko Huznah harda kukanta dan taso ayi hakan ta samu ƙafar guduwa. Amma mutumin nan yay ƙememe yaƙi aminta da wannan batu. Yadai yarda Khadijah ta koma can ta zauna tana taimaka mata. Hakan kuwa akai, suka koma tare da Khadijah gidansu. Zaman Khadijah baya hana Sageer kasancewa da Huznah duk da dai ba kamar da ba, ga rashin jin daɗi jiki, ga fitinarsa, ga tsanar datai masa. Kullum itace mafarkin AA. Ta gwada amsar wayar Khadijah ta kira number AA amma ba'a ɗagawa, ta mamanta ma bata samu har yanzu. Da Maman Yaseerah kawai take ɗan samu tayi waya. Itako tanata ɗaurata akan shawarwari. Kuma Huznah ɗin na hawa a kansu yanda ya kamata. Ranar cikin sa'a Sageer ya kamata tana waya da Maman Yaseerah. Bai ce mata komai ba bai kuma nuna mata yaji ba. Washe gari ya amshe wayar Khadijah gaba ɗaya suka koma ɗaya da Huznahr. Wannan abu ya bama Khadijah haushi ta gudu gida. Da yay mata magana tace bata da lafiya. Dama shi haka yake so, dan zamanta a gidan na ɗan takurashi hutawa yanda ya kamata tunda da rana babu dama ana azumi. Kwananta biyu da komawa ya bata wayarta. Aiko data fahimci haka sai ta sake langarewa taƙi takoma Huznah aka koma ƴar gidan jiya. Ga laulayi ga fitinar uban ciki........ ___________★ Alhamdullah hannun Maanal bai tashi ba, sai dai wajen yayi ja sosai amma tace bata jin zafi. Haka suka shirya suka fita tafsir, amma banda Mamy, Nuratu, Saheeba. Hakan ya bama Oum mamaki, sai dai batace komai ba a tunaninta ko zasu biyosu a baya. Amma har sukaje suka dawo shiru. Oho su yaran ko'a jikinsu, dan suna ma ajiye hijjabai can inda swimming pool yake suka nufa acewarsu yafi sanyi. Oum bata hanasu ba, dan itama kwanciya tai danta ɗan huta.. Su Maanal sun zo zasu gita ta sashen Mamy Haule ta taresu tace Maanal tazo inji Mamy. Batare da wani damuwa ko kawo wani abu a rai ba Maanal ta bita, su Najma suka wuce abinsu. A falon ƙasa Maanal ta samu Mamy da Saheeba da Nuratu zaune. Batare data kallesu ba ta ƙarasa inda Mamy take, cike da girmamawa tace mata, “Mamy ina kwana”. Banza Mamy tai mata bata amsa ba. A tunanin Maanal bata jiba ta sake maimaitawa tana ɗan ɗagowa ta kalla Mamy ɗin. Amma nan ma bata amsa ba, sai ma dariya Nuratu da Saheeba suka sanya. Kawai sai abin ya soki Manaal. Wata irin zuciya ta shiga yunƙuro mata a wuya, amma sai ta danneta da ƙyar ta ce, “Mamy gani”. Ai batama rufe baki ba kawai taji saukar mari, kafin ta gama dawowa a hanyyacinta aka sake sauke mata wani. Cikin wata irin kaushin murya Mamy ta nuna Maanal da kanta ke a ƙasa dafe da kumatunta da duka hannu biyu. “Na farko wanda kika saka yayma Nuratu ne. Na biyu na gargaɗi ne. Wlhy! Wlhy! Daga yau idan kika sake zama sanadin da ko kallon banza Ajwaad yayma Nuratu anan gidan na rantse miki da ALLAH sai na sakashi ya miki saki uku. Banda ma jaraba da baƙin naci irin na yaron yanzu da baka isa ka tankwarashi ba mi Ajwaad zai yi da ke sauran wasu. Koda yake banga laifinsa ba dan aiki ne na asiri.....” Caraf Saheeba ta amshe da faɗin, “Wlhy nafa asiri Mamy, kuma lokaci ne zai warware dan uban mutum sai ya wulaƙanta. Cikin ma waya sani ko a waje aka yayo aka manna masa”. “Ke wulaƙanta ma kaɗai kike tunani Aunty. Wawuya jaka kawai ya kika gani yanzu. Yamin ɗaya an miki biyu, nan gaba ma ni ce zan miki ba Mamy ba karuwa kawai mai cikin shege”. A mamakin su wani kalar murmushi Maanal tayi, sai kuma ta sauke hannunta daga saman fuskarta ta kalla Mamy. Murmushi ta sake sakar mata batare da tace komai ba ta miƙe abinta. Cike da wani irin takun ƙasaita da isa taje gaban su Saheeba ta tsaya. Manyan idannunta ta sauke akan Saheeba data saki baki da hanci da ido tana kallonta. Cike da wani irin salo Maanal ta ɗan ranƙwafa kanta tare da kallonta cikin ido. “Madam kar kiyi gaggawa, kin san ita zuru bata cin zuru sai dai a haɗu a zuru-zuru. Shi kuma cikin shege da kike faɗi, ai tare muka roroshi a waje da ubansa dan kin san shine kwarton nawa, ɗan soyayya kenan ba haɗin gambiza ba auren haɗin iyaye da tsiya-tsiya”. Sai ta wani kashe mata ido ɗaya, tare da sake sakar mata murmushi. Ta kuma miƙe a nutse ta juya ga Nuratu. “Ita ai uwa ce, dan ta mari wannan fuskar tamkar ta isa ne kodan darajar wanda ta haifa min. Babu kuma babbar wawuya jaka kamar ke da saurayin da kike kwaɗayi da burin aure ya ɗaga hannunsa a lokacin da yake rungume da matarsa a ƙirjinsa, a gaban ƙannensa, mamansa, abansa da yayunsa, Uncle ɗinsa, yayarki, ƴan aiki, ya sharara miki marin da har ki koma ga ALLAH sayinsa ya zauna raɗam a cikin zuciyarki ne ba akan fuskarki ba. Kinga ko KARUWAI kawai akema irin wannan wulaƙantawar.” itama ta kashe mata ido ɗaya tai gaba. Har ta wuce sai kuma ta dawo, duƙawa tai dai-dai saitin kunnen Nurry cike da raɗa ta furta, “Idan kikace zaki zuba wasa da ni tofa fuskarki ce zatai ta shan maruka wajen Mijina har sai kin fara ɓoyewa daga kallon mutane ke har ni ma uban ubanki zanci. Dan Ajwaad baya iya ɗagama wanda ya ko harareni ƙafa, ga assignment zan baki, ki ajiye a ranki Mijina nawa ne ni kaɗai dan bako wane nama yake iya ci ba, dan wani naman wurinsa yafi mushen jaki cika waje. Na barki lafiya mayyar mijina, ki kuma kiyayi haɗuwarmu dan waɗan nan marukan biyu sai na dawo dasu taki fuskar....” Wani irin rawa jikin Nuratu keyi, a fusace ta wani irin yunƙurawa ta riƙo rigar Maanal, baya ta fisgota tana faɗin, “Kafin ki maido min su ɗin ni bari na ƙara miki da nawa dan ubanki”. Aiko a bazata Maanal na juyowa ta antaya ma fuskar Nuratu mari, ta sake ɗauketa da wani na biyu, zata ƙara na uku Saheeba ta zaburo, itama ɗaga hannu Maanal ɗin tai zata wanka mata marin, sai kuma mita tuna oho ta fasa tai murmushi kawai. Gira a sama ta ce, “Kinci darajar Babban Yaya”. Daga haka tai gaba abinta. Wani irin sake ƙoƙarin fisgota Nuratu da jikinta ke rawa tayi, kawai skirt ɗinta ya harɗeta sai gata a ƙasa wanwar. Wata banzar dariya Maanal dake ƙarasa ficewa ta saki. Mamy da Saheeba da sukai sumar zaune suna kallon Maanal suka zabura kan Nuratu a tare....... Sosai wani irin zuciya ke cin Maanal, ta kuma hana kanta yin kukan dake taho mata. Ba marin bane kuma ya sakata kukan, ba kuma maganganun su Nuratu bane dan ko kaɗan basu mata zafi ba. Mamakin Mamy ne ke cizon zuciyarta da tausayin su AA da tausayin Oum. Kai dama family ɗin Darma gaba ɗaya. Yanda ALLAH ya bama mutanen nan haɗin kai da ƙaunar juna al'amarin Mamy ba ƙaramin girgizasu zai yi ba duk randa suka fahimta, ita kanta Mamyn tausayi take bata, dan tabbas in har aka kai ga wannan gaɓar ta tabbatar zatayi loosing, komai zata rasa, miji, ƴaƴan da take yaƙi a kansu, dama rayuwar farin cikin gaba ɗaya..... “Ya rabb! Aunty Manaal miya samu fuskarki haka ne?”. Firgigit Maanal ta dawo hanyyacinta, kallon Najma tai mai maganar, sai ta saki murmushi cike da basarwa ta ce, “Ba komai inaga barci da na ɗanyi ne a massalaci”. Cike da rashin yarda Najma ta ce, “Barci ko mari, wannan mari ne Aunty. Waye ya mareki? Nuratu!”. Murmushi Maanal tayi, zatai magana a bazata sukaji maganar RK dake faɗin, “Lafiya!?”. Duk juyowa sukayi, cike da damuwa Najma tace, “Aunty ce aka kira sashen Mamy, kaga ta fito fuskarta duk sayin mari”. Kallon Maanal ɗin RK yayi, suna haɗa ido sai tai yunƙurin barin wajen. Cikin wata irin dakewar murya da Maanal bata taɓa sanin RK ɗin ya mallaka ba ya ce, “Maanal!”. Cak ta tsaya sai dai bata juyo ba. Takawa yay a hankali ya koma gabata, fuskar tata ya kalla da ƙyau, tabbas kuwa sayin mari ne. Sai kawai ya kauda kansa. Shiru na kusan sakan biyar kafin ya dawo da kallonsa kansu. Babu alamar wasa a tattare da shi ya juya ya bar wajen yana faɗin, “Ku biyo ni”. Ji Maanal tai kamar tace bazata je ba, amma sai ta kasa hakan, dan koba komai RK fa matsayin kawun su AA yake, ƙanen Oum ne uwa ɗaya uba ɗaya. Ƙanen Abah... Bama ta gama tunanin ba Najma taja hannunta suka bishi. Tacan bayan sashen baƙi sukaje. Ita Maanal ma bata taɓa sanin akwai wajen zama a wajen ba sai yau. Ya zauna suma ya nuna musu wajen zama. Zaman sukayi, batare da ya kallesu ba a yanzu ya furta, “Nuratu ce ta mareki?”. Murmushin takaici kaɗan Maanal tayi, kafin itama cike da girmamawa ta ce, “Uncle wacece Nuratu da zan zauna ta dake ni”. Kansa ya jinjina ya ce, “Saheeba ce?”. Kai itama ta girgiza masa alamar a'a.......✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖5️⃣5️⃣ ______________ .........Maimakon sake tambayarta wani sai kawai ya kaɗa kai dan ya fahimci wadda yake hasashen ce. Kansa tsaye ya furta, “Kin san wani ɓoyayyen abu daya shafeta ne dama kafin yau?”. Shiru Maanal tai ta kasa magana. Tsohon minti biyu bata da niyyar cewa komai. RK da yay mata kallo ɗaya ya ɗauke kansa ya ce, “Tsahon wane lokaci kika san ainahin ta?”. Idanu ta ɗago ta kallesa, ganin babu alamar wani wasa a tare da shi a Uncle ɗinsa yake yasata maida kanta ta duƙar, hannunta na wasa da ɗayan hannun ta ce, “Uncle miye amfanin tone-tonen? Taci darajar wanda ya ajiyeta da waɗan da take tada jijiyar wuyan a kansu. Ni harga ALLAH bana buƙatar wani ka-ce-na-ce a kanta. Matsalata da damuwata ɗaya ce ta yanda zan bama Oum garkuwa da ga sharri da tuggunta ita da ahalinta. Amma dama kai kasan ita wacece tuni?”. “Tabbas tun kusan shekara biyu da suka wuce wasu abubuwanta suka fara sakani a shakka. Sai dai akan auren ku na samu tabbacin da nake buƙata a baya gaba ɗaya hasashe ne kawai da zargi”. “Saboda haka ka aikata abinda ya faru?”. “Hakan da nai shine ya kamata. Maanal ki bar wani pretending, kina sonshi kamar yanda yake sonki. Soyayyar da AA ke miki bata wasan yara bace, dan na jima ban taɓa ganin soyayya irin wannan ba. Kuma har abada bazaki taɓa samun wanda zai soki kamar Ajwaad ba....” Ɗagowa tai ta kallesa. Ɗauke kansa yay daga saitin su, ya haɗiye wani abu mai nauyi a cikin maƙoshinsa, yana kuma addu'ar UBANGIJI ya nisantashi da sheɗanin dake kissima masa shi a zuciya. Dan yayima ALLAH alƙawarin har abada bazai sake kallon Maanal da wata siffa ba bayan ta matar ɗan ɗan uwansa. Jinjina mata kai yayi da cigaba da faɗin, “Yes da gaske nake Maanal bazaki samu ba indai a ɓangaren soyayya ce irin ta namiji da mace dake a buri da bigiren zama ma'aurata. Kema kuma kin san haka, idan ma baki sani ba duk randa aka bashi ke zai tabbatar miki nayi imanin hakan. Dan tun farko ƙuruciya dama kece kike kallon tarayyarku matsayin abokai kawai wanda suka shaƙu, amma ga Ajwaad sam ba haka bane, tun asali tun fari sonki yake. Domin tabbatarwa kije da wannan ki karanta, karki bari ya gani dan bai san na ɗauka ba nima shiyyasa na naɗe bayan book ɗin da wannan takardan, zuwa anjima kibama Najma ta kawo min”. Hannunta na ɗan rawa ta amsa, ƙaramin jotter ce an nannaɗe ta da farar takarda ta yanda ba'a ganin ainahin bangon. RK daya ɗauke kansa daga kallonta ya cigaba da faɗin, “Kince kina son bama aunty garkuwa, tofa ta hanya ɗaya ce jal zamu iya yin hakan, amma duk sauran da zaki hanga ko hasashe ba masu yiwuwa bane ba, dan koba komai zamu kalla darajar masu daraja a kanta.” Najma zatai magana dan ita duk sun rikitata RK yay mata alamar zipping, shirun kuwa tayi, tare da saka hannunta ta ma riƙe bakin. Maanal data fara jin nutsuwa da tattaunawar ta ce, “Wace hanya ce kenan?”. “Yafewa Ajwaad, yimasa afuwa daga laifinsa. Duk da nasan abune mai wahala kuma mai ciwon gaske, amma idan aka tuna alkairin baya sai a yafe wannan a kallesa a matsayin kuskure da ajizanci na ɗan adam da kuma jarabawa. Ke da kanki a diary din da kika bani babu inda Ajwaad ya taɓa ko gwada aikata abinda ya aikata a gareki koda da wasa, mizaisa baza muyi tunanin wannan daya faru akwai wani abu a ƙas ba musamman idan muka kalla shan zoɓo kamar daga shi komai ya fara....” Da wani irin mamaki Maanal ke kallon RK. Tace, “Zoɓo Uncle?”. Cigaba yay da faɗin, “Yes dole akwai wani abu a cikin wannan zoɓon da kuka sha, kuma koma minene Ajwaad ya sanshi daga baya ɓoyewa kawai yake yi. Akwai dalilin kuma da yasa ya zaɓi yin AJIYA A DUHU. A yanzu bayan haɗuwarku, zuwa yanzu da kuke ma'aurata ya taɓa tada miki waccan maganar?”. Kanta ta girgiza alamar a'a. “Ya taɓa baki haƙuri koda a wata siga ne balle nuna shi mai laifi ne babba a gareki?”. Nan ma ta girgiza kai. “To wannan ya isa ya zame miki hujja babba. Amma kuma na miki uziri, dan wancan abun ya faru kina da ƙarancin shekaru, shiyasa baki taɓa zama kinyi nazarin komai a kansa ba, kawai dai kinyi jiyyar shock da kika shiga, sannan rabuwarku ta haddasa miki ciwon zuciyar da kika sha fama, sai kuma jin zafin abinda ya farun dan dole ne hakan ga kowacce mace da irin haka zai faru da ita....” Da sauri nan ma ta kallesa. Ya ɗan ɗage kafaɗa ya ce, “Kar kiyi wani musu, shiyasa nace miki kina son AA kema har yanzu. Kin san kuwa ƙarfin da ciwon zuciyarki yayi Maanal? Kinfa je wani mataki ne da komai zai iya faruwa dake. Amma tunda Ajwaad ya dawo rayuwarki bayan farko-farko daya motsa ciwon ya ƙara motsa miki?”. Gaba ɗaya ji Maanal tai kunya ta lulluɓeta. RK daya fahimta ya cigaba da faɗin, “Duk da nasan an ɗoraki a magani mai ƙyau da inganci da ace baki sake haɗuwa da Ajwaad ba a tsakanin tasirinsa kaɗan ne kuma zai zama na ɗan lokaci ne. Amma da yake zuciyar ta samu abinda take so yanzu gashi komai normal ba. Bawai ke kaɗai ba shi kansa AA ɗin ya shiga makamancin halin da kike cikin ne, koma fiye da naki dan sai da ya shiga wani mugun depression fa a shekarun baya da kowa ya fara ɗauka brain ɗinsa ya taɓu ne ma, amma tunda yau akace kin zama mallakinsa kinga ya sake yin wani any cuta data shafi hakan? Bazaiyi ba saboda zukatan sun kasance a tare sun kuma samu abinda suke so. Dan haka ina roƙonki, ina kuma baki shawarar ɗaura ɗamarar bama mijinki haɗin kan zama lafiya, ki kuma ajiye komai gefe ki bashi irin soyayyar da yake so. Wannan shine kawai dafin da zaita cizon matar can ya kuma faranta ran Aunty Dan a duniya aurenku ke da Ajwaad da haihuwar Fawzan ce kawai damuwar dana san tana damunta. Na biyu auren Najma da Fawzan waɗan nan biyun zasusa ta samu cikar burinta na tabbatar”. A wani irin firgice Najma ta kalla RK. Ya harareta, sai tai ƙasa da kanta. Maanal da wani kalar farin ciki ya lulluɓe ta ce, “Uncle da gaske wai?”. Ƴar dariya RK yayi da faɗin, “Da gaske kuwa. Munafukai suna ɓoyewa ne kawai. Amma ni ina son komai ya fito fili zuwa bayan salla a haɗa da bikinku ayi nasu. To in dai mukai ma matar can wannan dukan zai gigitata ne bana wasa ba. Hakan ne zai bama Aunty garkuwa daga tarkon da take son ɗana mata, dan burinta ai yanzu ta yanda zata ƙwace su Ajwaad ne a hannun Auntyn, bayan kuma ita da hannunta ta bata, tasan kuma aikata hakan zai iya kai rayuwar Aunty ƙarshe ta mutu ta bar mata mijin da ƴaƴan shiyyasa, babu kuma ta hanyar da zata iya hakan sai ta aura musu matan da take so, su kasance kuma daga ɓangarenta yanda ko Aunty ta rasa ranta taci nasara akan yaran suma kansu ta yanda basu isa bijire mata ba ta kowace fuska, ƙaryarta kuma tasha ƙarya, tunda tai wannan ƙyautar har gaban abada bazata koma a hannunta ba wlhy, kuma in sha ALLAHU Aunty da Yaya da yaran nan uku suna tare da juna sai dai ita ta fita a cikinsu”. Cike da farin ciki Maanal ta ce, “In sha ALLAHU Uncle, ai zata sha mamaki dan wannan faɗan mu da ita ne Oum na barci abintama za'ayi sa”. Dariya yayi, tare da faɗin, “Wato tana barci?”. “Sosai ma kuwa. Ai yanda matar nan take ta yaƙar Oum ita kuma bama tasan tana yi ba ai AJIYA A DUHU kenan, babu faɗan daya kai wannan baƙin ciki, kaita zama cikin baƙin ciki da takaici mutum da shirya masa tuggu da mugunta shi kuma baima san kanayi ba kuma yana zagaye da farin cikin da baka ƙaunar ganinsa a ciki, ka kuma kasa cin nasara tako wace fuska wlhy AJIYA A DUHU kenan”. Dariya sukayi yanzu kam har Najma, sai kuma Maanal ta rungume Najma dake ɓoye fuska. Ta shiga jero addu'ar ALLAH ya tabbatar da alkairi ita da Yaya F. RK na amsa mata da Amin. Ɗari bisa ɗari Maanal ta gamsu da bayaninsa. Kuma ita harga ALLAH dama zuwa yanzu ta huce koba duka ba akan jin zafin AA. Kuma tama ranta alƙawarin zata bashi dukkan haɗin kai na kulawa da soyayya bayan tarewarta kodan farin cikin Oum ta kuma baƙantawa Mamy, dan wlhy wannan marin datai mata tayima ALLAH alƙawarin sai ta ramashi a zuciyar Mamy da salon ban mamaki akan AA.... RK ya katseta da faɗin. “Kasancewarku ku biyu Aunty zata samu garkuwa masu tare mata faɗan, dan na fahimci so take itama tai amfani da waɗan nan ƴan iskan yaran da take ta aurama su Ajwaad ɗin wajen tare mata faɗa. Kunga kuma sai ki zuba da su idan tai tsami a tsakanin ku da su sai mu tafi plan c. Abu na ƙarshe kuma Maanal dole ne ki dawo Maanal ɗinki ta asali ta baya, wato ƴar rikici, sarkin takalar faɗa, mai kuma tsiwa. Ki ajiye wannan sanyin da miskilancin, ki kuma ajiye wannan shiru-shirun da noƙe-noƙe, kinyi karatu, kin shiga cikin mutane masu mabanbanta halayya, na tabbata kina sane da komai miskilanci ne kawai ya sa kike nuna kamar baki san komai ba. To dan ALLAH ayi haƙuri a dawo kamar da dan wannan abun da muke gani ƙarami wlhy ba ƙarami bane ba. Babban yaƙi ne, kuma ba'akan komai zai kasance ba sai na kwatar Yaya (Abah) da su Ajwaad. To idan su suna shirin yaƙin hakan, mu zamu shirya na bama Aunty Garkuwa ne kamar yanda kika faɗa, hakan kuma bazai muku daɗi ba sai kun yi fito na fito da waɗan shegun su Nuratun”. Sosai sun gamsu da wannan bayani nashi, sai Maanal taji zuciyarta tai mata wani sakayau, duk wani ƙunci da nauyi ya tafi sai sauke ajiyar zuciya take. Sun sake tattaunawa sosai kafin shi ya fara tashi ya wuce, su kuma sai da suka tabbatar an tafi sallar azhar sannan suka fito a wajen dan yace baya buƙatar kowa ya fahimci komai..... __________★ Sosai Nuratu ta fasa lips, goshinta kuwa yayi irin ƙullutun nan abin dariya. Yanda take kuka da rantsuwar sai ta kashe Maanal yau a gidan nan ya saka Saheeba kiran uwarta a waya. Dan Mamy gaba ɗaya ta kasa dawowa a hanyyacinta, kalaman Maanal da marin data ma Nuratun ne kawai ke mata kai-kawo a cikin idanu. Eh tasan Maanal dama tun tana mitsitsiyarta bata da kunya yarinyar, amma bata taɓa kawowa a ranta fitsararta zai iso gareta ba. Lallai tayi sake, matuƙar sakacin da har yarinyar nan ta zauna a gidan na wannan lokacin har ma da ciki. Gabanta ya faɗi tuna zancen ciki... Dai-dai nan Saheeba ta miƙa mata waya dan tunanin da tai nisa a ciki yasa bama tasan su Saheeban na waya da uwarsu ba........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖5️⃣6️⃣ ______________ .........“Maman Saheeba ta ce, “Aunty miyasa kikai haka? Ni da kinyi shawara dani wlhy bazaki kira yarinyar nan har sashen ki ki wani mareta ba.” “Raina ne ya ɓaci Nana, babu kunya fa a gabana agaban kowa Ajwaad ya wani rungume yarinyar nan jikinsa na rawa, ya kuma ɗaga hannu ya mari Nuratu, Fadeel ya amshe kayan hannunta, yabi yarinyar nan da zagi shima. Haka ma Fawzan. Yanzu kodan ganin idona yaran nan bazasu raga ba. Su dukansu suka nuna goyon bayan ƴar iskar yarinyar nan......” “Na fahimceki, amma da kema kinyi pretending kawai a wuce wajen. Dan wannan faɗan ba naki bane na tsakanin su yaran ne ai. Yanzu kuwa abinda kuka kira yarinyar kukai mata kamar kin buɗe mata cikinki ne kai tsaye. Karki manta yarinyar nan idonta a buɗe yake, tunda kema shaida ce akan halinta na baya, dan yanzu ta koma wannan sum-sum ɗin bai kamata ki sakankance da yawa haka ba. Rainon Fateema da Ajwaad ce fa, sannan jinin Asiya ce. Dole fa ki dinga ƙoƙarin control ɗin fushinki Aunty idan ba haka ba zamuyi wahalar banza, dan in dai mutanen nan suka gane akwai wani abu a tare dake wlhy auren nan bazai yiwu ba na Nuratu da Ajwaad, balle kuma akai ga Fawzan, kuma na tabbatar bazasu cigaba da barin Fawzan a haka ba zasu nema masa matar aure, Ajwaad na auren yarinyar nan, mi kike tunani, ke da Saheeba kaɗai zaku iya wasan ne? Bayan sun rinjaye Ku? To dole fa ki cigaba da yin kamar yanda kike yi, shi wannan faɗan ki barma yaran suyi, suma kuma a yanzu karda su sake cemata komai su barta sai ta sakankance sannan dan wannan marin sai Nuratu ta rama shi. Haba Aunty kamar bake ba, ke da na sanki tamkar ƙuli-ƙuli babu mai iya gane gabanki balle baya. Karki bari abubuwa suyi miki yawa ki fara sakin layi dan ALLAH. Yarinyar nan kuma ki fita a sabgarta in ba hakaba zata zame mana ƊAN HAKKIN DAKA RAINA tunda bata da kunya sam, kota zame mana RAINA KAMA KAGA GAYYA”. Ajiyar zuciya mai nauyi Mamy ta sauke, cike da gamsuwa ta ce, “Hakane kuma Nana na fahimceki. Amma maganganun yarinyar nan sun min zafi, dan tabbas bada su Saheeba take ba dani take, amma lokaci ne, zan nuna mata uwarta ma da Fateemar da suke taƙama da ita basu kai ba balle ita haihuwar jiya.” “Karki wani damu lokacin cin ubanta na zuwa. Wannan cikin nata kuma na amso maganin zubar da shi amma sai zuwa bayan salla zai iso, dan so nake mu zubar da shi dai-dai sanda ake hidimar bikin Ajwaad da Nuratu”. “Miye ma'anar yin hakan? Ni gwara kawai ya ɓare yanzu dan idan na kalleta wani irin zafi nake ji a ƙirjina wlhy Nana”. “Karki wani damu ki kwantar da hankalinki Aunty, hakan da zamuyi nada ma'anoni masu yawan gaske. Ai gara cikin yay kwari ta yanda zataci azabar fitarsa, a kuma lokacin mu nuna tayi hakan ne dan kishi Ajwaad zai ƙara aure. Kai idan ma ta kama har Fateema sai tuggunmu ya shafa akan zubar da cikin nan”. Wani sassauci Mamy ta ɗan ji a ranta, ta sauke numfashi da faɗin, “Shike nan hakan ma yayi, ALLAH ya kaimu”.... _😂Wannan ciki dai da ake son a zubar kota ina aka samo shi. Koda yake AA ɗan baiwa ne maybe a mafarki ya lallaɓo🥱😜😆🏃._ ________★ Wannan tattaunawa ta RK da su Maanal ta taka matuƙar rawar gani akan abubuwa da yawa. Duk da tako wane ɓangare kowa akwai abinda ya damesa. Aranar dai Mamy da su Nuratu basu je aiki sashen Oum ba. Nuratu kuwa tasha uban bori akan sai taje har sashen Oum ta daki Maanal. Da ƙyar Mamy da Saheeba suka lankwasata bayan an kira Hajiya Turai a waya itama ta sake yin nata. Sai da Oum taje har sashen Mamy ta bata haƙuri da lallashinta sannan tace ita fa ba wannan bane ya ɓata mata rai bata jin daɗi ne. Ita dai Oum ta sake bata haƙuri ta taho. Sai kuma hakan ya damu Mamy ɗin, dan da ciwo kaga kanata hauka akan mutum shi ko'a jikinsa, (kamar dai yanda Maaanal tace AJIYA A DUHU kenan😂) washe gari suka fito akaje tafsir tare aka kumayi girki tare. A ɓangaren Fawzan shima dai ransa danƙare yake da al'amarin Mamy dan abin sai ya zame masa biyu. Wanda tai masa, da wanda ya faru akan marin Nuratu da AA yayi. Shi ko babban Yaya iya na marin Nuratun ne kawai ya bashi mamakin. Sai kuma ya ɗauka kawai Mamyn ta fusata ne saboda Nuratu na jininta. A ɓangaren Mamy kam abin da ya tsaya mata a zuciya Abah ne. Dan daga wannan nasiha bai sake cemata komai ba, hatta borin kin zuwa aiki da tayi na kwana ɗaya da ƙin zuwa shan ruwa sashen Oum ko'a fuska bai nuna mata ba balle ya tanka. Sai hakan ya girgizata ya kuma tsaya mata a zuciya taketa hasashe-hasashe ta kasa gane komai. Gefe ga tsanar Maanal da maganganun data gayama su Saheeba yana ƙara yima Mamy ciwo bama su Saheeba ɗin kawai ba. Sun kuma rasa ta yanda zasu rama duk da sun ɗauki alwashi kala da iri Saheeban da Nuratu. Na ƙarshe AA, matuƙar ciwo abinda ya farun yay masa. Dan haka ma a jiya ya shirya tafiya Lagos ya bar musu gidan. Dan baya buƙatar yin wata magana da Mamy in ba hakaba ALLAH sai zuciya ta kwashe shi yama Nuratu dukan mutuwa ya kuma koreta a gidan duk da Oum ta masa faɗa da nasiha sosai a washe gari. Itama Maanal karanta jotter ɗin da RK ya bata ya sakata kuka sosai jikinta kuma yayi sanyi matuƙa, dan haka ta ɗauka ɗammarar gyara abubuwa da yawan gaske... Kwanakin azumi sun cigaba da tirzawa, wasu na ibada wasu zukatansu cike da burikan sharri. A randa aka shiga goman ƙarshe AA ya dawo gidan, zuwa dare kuma ya sake barin gidan acewarsa ya shiga ittikafi. Bai yarda wata keɓantacciyar gaisuwa ta shiga tsakaninsa da Maanal ba itama kuma bata nuna ta damu ba a zahiri duk da hakan ya mata ba daɗi, dan yanzu so take su daidaita sosai. Ita kanta Oum bataji daɗin yanda AA yayi ba amma batace komai ba. Shi kuma a ganinsa hakan da yay zaifi alkairi dan a cikin wani irin matsananciyar buƙata yake shiyasa ya zaɓi duk hanyoyin hana keɓancewarsa da Maanal sam. A ɓangaren Abah da Uncle RK da su babban yaya kam suna ibada suna kuma shirya biki batare da sanin kowa ba. Yayinda suma dai ta ɓangaren Mamy bikin suke shiryawa acewarsu babu ɗaga ƙafa sati ɗaya da salla. A kwana a tashi babu wahala wajen UBANGIJI, azumi nata bankwana su Maanal nata ƙara dagewa a yin ibada. Duk da ita ma a farkon goman tai period, ALLAH dai ya taimaketa kwanansa uku ya tafi ta cigaba da azuminta. Tun azumi na goma sha biyar tela yazo ya gwada ƴan hutun su Oum bisa umarnin AA. Batare da kowa yaga kayan da za'a ɗinka ɗin ba kuma. Yau da azumi ke ashirin da bakwai ana saka ran salla nan da kwana biyu ko uku sai ga ɗinkuna sun iso kowa da sunansa. Zokaga murna da tsalle wajen yaran. Abinda ya ƙona ran Mamy babu Nuratu a ɗinki, duk da taga babu Maanal itama hakan bai dameta ba. Tako ƙara ƙullatar AA sosai a ranta, gashi dama ta fassara barin gidansa da wai yana haushi da ita ne. Bata san bawan ALLAH abinda ya damesa daban ba. A ranar shima Yaya Fawzan ya kwashe su da dare yin shopping na takalma da sauran tarkace. Harda Maanal da Oum akaje, nan ma baƙin ciki kamar zai kar Mamy. Duk da dai ta danne bata nuna ba a fili, harda kuma su Saheeba da Nuratu da Nibras. Kowa kuma ya zaɓo ra'ayinsa, Oum kuma ta zaɓo nata dana Mamy data ƙi binsu wai ita kawaici sai na Aba. Fawzan ya ɗauka musu shi da Baban yaya da AA dan Uncle RK ya fece Kano yace kansa bazai murfi ba ranar salla sabon amarcin shi da Nuwaira 🤣. Shi kuma babban yaya washe gari ya lodo uban cefane da kaji gyarru sai uban jan nama. Tuni sun hutar da Abah yin komai a gidan nan. Dan shi kansa bai san yaushe ne last da ya sai wani abu na abinci ko sutura ba koda ma kansa a gidan. Hatta da ƴan uwansa duk salla sai su babban yaya sun aika musu da kaji da cefane na abincin salla. Wannan sallar ma hakan ce ta faru, tuni nasu sun wuce Kano. Batare da sanin kowa ba kuma AA ya tura Kaduna da uban kaya ma Daddy kamar yanda suma su Babban yayan kanyi ga nasu surukan duk shekara... Tunfa a daren masu aiki suka iso, dan duk salla su Oum na ɗaukar masu tayasu aiki saboda abinci akeyi bana wasa ba kasancewar ana fita da wani wa bayin ALLAH, kuma a cikin azumin ma akwai inda ake dafa abinci a raba duk lokacin shan ruwa batare fa kowa yasan daga su bane. Bayan ɗanyan abinci da shi kansa AA ke rabawa duk shekara shi da sauran ƴan uwansa. Dan asusu garesu na tara kuɗaɗe domin hakan kawai sai shekara ake ciresu ai hidimar taimakon bayin ALLAH. Oum kuma kaɗai tasan suna yin hakan. Masu aiki sun kama aiki, Oum ta kaɗa ƴammatanta saloon da kitso. Mutuniyar taku dai nata daru, Oum tace babu fashi sai an mata. Itako aka fara wanke ma kan sannan akai kitso bamai yawan ba. Dan Oum tace a mata kaɗan tunda za'ai na tariya kwanan nan. Haka ma ƙunshi a yatsu kawai akai mata ja shike nan. Ta koma gefe yana sauke ajiyar zuciya ga haushin AA dama na cimata rai. Suma sauran duk an musu harda Oum, basu dawo gida ba sai la'asar, babu ɓata lokaci suka shiga haɗa abincin buɗa baki...........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖5️⃣7️⃣ ______________ .......Alhamdullah ƙarfe biyar akace anga wata a saudia, yara suka fara murna da fatan ALLAH yasa a Nigeria ma a gani. Hakan kuwa akai, kafin ma tara sanarwa ya iso kunnen kowa daga Sarkin Musulmi cewar anga wata muma a Nigeria gobe salla. Ai fa tuni gida ya yamutse da murna. Zuwa tara sai ga AA ya dawo gida. Tunda ya shigo Maanal kallo ɗaya tai masa ta ɗauke kai, yanda ƙannensa suka gaishesa itama ta gaishesa ne ta basar. Shi dai kallonta kawai yake ta ƙasan ido, Oum tace mizai ci ya miƙe yana faɗin, “Komai ma na samu amma mara nauyi, bara naje na watsa ruwa Besty ta kai min can dan zata amshi saƙonta daga can, idan kinzo ina sama”. Ya faɗa maganar ta ƙarshe idonsa akan Maanal Cikin rashi damuwa Oum data san da saƙon tace to. Shima sai ya fice bayan ya ɗan kalla Maanal ɗin karaf kuwa yaga hararar da take masa. Da sauri ya janye idanun yay gaba yana cije lips. Umarni Oum ta bata nata tashi ta haɗa masa abincin. Badan taso hakan ba ta amsa da to tana miƙewa. Shi ko AA sashen Abah ya nufa, acan ya samu Mamy tare da shi, ƙin yarda yay su haɗa ko ido. Kansa a risine ya gaisheta bayan ya gaida Abah. Idon Abah ya sakata amsawa kamar babu komai a ranta, amma ta ciki na ciki. Bai wani jima ba yace ma Abah zai je ya watsa ruwa yayi aski yana jin gashi duk a jikinsa. Abah ya sanya masa albarka ya fito. Sai da ya kalla sashen Oum sannan ya wuce nashi sashen. ★ Koda Maanal ta nema Najma tai mata rakkiya ƙi tayi, tace, “Tab, sokike Yaya AA ya koroni da tsarabar mari.” badan Maanal taso ba haka ta tafi ita kaɗai. Garin yayi sanyi sosai yau saboda hadarin da aka haɗa sai ya zama iska ba'ai ruwan ba. Sanye take da hijjab har ƙasa royal blue dayay mata ƙyau sosai, sai ɗan basket ɗin data riƙe na abincinsa. Tana gab da shiga idonta ya sauka akan Nibras dake zaune a barandar sashensu ta upstairs ko ubanmi take a wajen oho. Ɗauke kai Maanal tayi abunta ta cigaba da tafiya, batai wani zaman yin knocking ba ta shiga da sallama. Babu kowa a falon ƙasan kuwa sai dai ko'ina a gyare tsaf, har yanzu kuma dai sauran kwalayen kaya da ba'a gama shiryawaba suna nan. Saman da yace zata samesa ta nufa, duk da zuciyarta na wani ɗas-ɗas na tsoro tadai dake. Shiru falon saman ko wuta ma ba'a kunna ba, sai da ta haska fitilar wayarta ma sannan ta kunna wutar. Zama tai a kujera tana fatan fitowarsa, fin mintuna biyar shiru, gashi tana son zuwa ta kwanta kodan kasancewar gobe idan ALLAH ya kaimu salla. Akwai fita idi da wuri, kuma tana son ya barta ta wuce gidan Didi ta yini. Fahimtar bafa fitowar zai yi ba yasa ta miƙe, ƙofar ɗakin ranar taje tai knocking. Shiru babu ko motsi, sai ta tura ƙofar kawai ta leƙa. Babu kowa a ciki sai uban sanyin ac. Ɗan jimm tayi a wajen, sai kuma ta shiga kawai zuciyarta na raya mata ta ajiye masa kawai idan ma wanka yake in ya fito ai zai gani ita kuma sai ta koma falo. Tana maida ƙofar zata rufe kawai ta ganshi tsaye a wajen ashe bayan ƙofar ya ɓoye. Da farko ma ita tsorata tayi, dan har zata fasa ƙara yay saurin faɗin, “Hy relax! Hajiyar tsoro”. Baki ta tura sosai, kanta a ƙasa saboda daga shi sai towel a ƙugu ta ce, “Haa'a to miye na ɓoyewa anan ɗin?”. Gabanta ya taka ya tsaya, sai ta matsa baya saboda kusancin nasu yayi dab da yawa. Ƙara matsowa yay, itama ta matsa, sai kawai abin ya saka shi nishaɗi ya cigaba da binta har suka dangane da jikin katakon mirror. Sai data runtse idanu, sai kuma ta ɗaura duka hannayenta a katakon tai baya da jikinta kamar zata jingina da madubin. Shima nasa hannayen duk biyu ya dafe katakon mirror ɗin da su ya shiga biyota yana ƙoƙarin saka idanunsa cikin nata amma taƙi yarda da hakan. A yanda ya ranƙwafo ɗin da yanda take sai yay kamar zai kwanto a jikinta, ga fuskarsu dab da juna suna busama junansu nunfashi. “I miss you Everbloom”. Ya faɗa cikin raɗa yana hura mata iska a kan idanunta. Wani yarrr taji a illahirin jikinta. Dole ta buɗe idannunta dake wani mar-mar-mar. A cikin nasan da yake so suka shige, tai ƙoƙarin janyewa ya hana hakan. Dole ta shiga gaishe shi lips ɗinta na ɗan rawa. Matsar da nasa lips ɗin yay ya sumbaci nata kaɗan. Sai kuma ya sake ɗagowa yana kallonta. Cike da raɗa ya ce, “Na sha?”. Kanta ta girgiza masa alamar a'a. “Why?”. Ya faɗa a hankali idanunta a cikin nasa. Itama a hankalin tace, “Ba yanzu ba”. “Sai yau she?”. Duk da maganar na mata nauyi ta daure cikin raɗan tace, “Sai randa aka kawo maka ni”. Murmushi ya saki mai sanyi tare da lumshe idanun ya sake buɗewa a kanta slowly. Yanzun ma ƙasa-ƙasa yace “Anya zaki iya cika alƙawuran da kika ɗauka wannan ranar kuwa Besty?”. Murmushi tayi da jinjina masa kanta, sai kuma tasa hannu ta rufe fuskarta. A haka ta ce, “In sha ALLAHU duk zan iya. Kai dai kawai kayi fatan zuwan ranar”. Ajiyar zuciya ya sauke mai fita a hankali, sai kuma ya miƙe da ƙyau ya kamota kawai ya rungume a cikin jikinsa. Bata hanashi ba, itama tai luf dan zuwa yanzu ta ɗauka ɗamarar zama masa mar'atussaliha in sha ALLAHU. Sun jima a haka kafin ya ɗagota. Fuskarsu ya gaɗe a waje guda goshinsu, hancinsu na gogar juna. Ɗan sumbatar lips ɗinta ya sake yi kaɗan, sai kuma cike da shagwaɓa ya ce, “Please my Babie nayi missing ɗinsu ALLAH, nayi kaɗan?”. Cikin tata shagwaɓar ta ce, “Ai matsalan kai baka san kaɗan bane, kuma ma fushi nake da kai”. “Nasan kina fushi dani shiyyasa zanyi lallashi ai.” Kafin ma ta samu damar sake cewa wani abu ya mamane lips ɗinsu waje guda. Cike da nutsuwa da kewa ya fara sumbatar ta. Itama dai yau jin abun tai har tsakar kai, bama tasan ta fara bashi haɗin kai ba. Ya subahannallah ji AA yay kamar ana masa kiɗan general a sama. Baima san ya kamata ya ɗaga gaba ɗaya ya zaunar akan katakon mirror ɗin ba ya wani riƙe kanta da duka hannayensa biyu. Yi yake kamar zai haɗa har lips ɗin nata ya cinye kawai. Sunfi mintina shida a haka kafin ya haƙura ya rungumeta, itama rungumesan tayi tsam suna sauke numfashi a tare. Wata irin nutsuwa da farin ciki na zagayesu. Duk da shi dai oga AA ta ƙarƙashin ƙasa gobara ce ke niyyar tashi. Amma dai yanata ƙoƙarin tausar zuciyarsa da lallashin gangar jikinsa. Sai ALLAH ya taimakesa ya ɗan samu lafawar yanayin nasa a wannan rungumar. Maanal ce ta fara ƙoƙarin janye jikinta, bai musa ba shima ya barta. Sam taƙi yarda ta kallesa, kanta a ƙasa, jitake kamar ta nutse a wajen dan kunya. Cikin wani irin nishaɗi AA yaja hancinta kaɗan tare da sumbatar gefen fuskarta sannan a raɗa yace, “Sarkin kunya”. Murmushi tayi tana ƙara duƙar da kanta. Shima sai ya bar wajen yana murmushin. A zuciyarsa ko mamakin canjawarta yake yau. Dan zai iya cewa bata taɓa bashi haɗin kai yayi yanda yake so cikin salama irin yau ba. Duk da dai kunyar na nan babu abinda ya canja. Jallabiya ya sanyo a jikinsa, sannan ya dawo inda take. Cak ya kamata ya sauke daga saman mirror ɗin, sai kuma ya kama hannunta suka nufi bakin gado. Sai da ya zaunar da ita sannan ya zauna shima. Cike da kulawa ya ce, “Bani abincin yunwa nake ji”. Kanta kawai ta jinjina masa, ta jawo basket ɗin abincin ta zuba masa kunu, sai farfesun naman talo-talo da sukayi. Sai uban ƙamshi yake gashi gwanin sha'awa a ido. Kunun kawai ya amsa, naman ya buɗe mata baki alamar ta bashi. Ƙaramar harara tai masa, sai ya shagwaɓe fuska. Ta dungure masa kai tana murmushi. “ALLAH Besty ka canja hali”. Murmushi yayi mai ƙayatarwa, zai yi magana ta zuba masa naman data ɗebo a bakin dole yay shiru ya shiga taunawa. Sai wani kallonta yake, dan ji yake kamar an canja masa ita. Alhamdullah addu'arsa ta amsu kenan. Dan kusan a ittikafin nan addu'oi sa akan Maanal ne. Yaci naman sosai, itako da ya nuna zai bata tace masa ta ƙoshi taci abinci. Bai takura mata ba. Wani ƙyaƙyƙyawan leda dake gefen gadon ya jawo gabanta. “Ga kayan sallarki tashi ki gwada”. “A ina ɗin?”. Ta faɗa tana waro idanu waje. Cike da tsokana yace, “A gabana mana, ba mijinki bane?”. “Hu'um ALLAH bazan iya ba. Kadai bari naje sashen Oum duk wanda na gwada zan maka hoto”. Murmushi yayi mai faɗi, sai kuma ya ɗan laɓe baki yana fara fiddo kayan da faɗin, “Ni za'ama wayo kenan. To naƙi ɗin”. A marairaice ta ce, “Please Yaya AA”. Dariya yayi, sai kuma ya dakata da fiddo kayan yana kallonta. “Ni dai wannan yaya da aka saka min bai ma ko dace da ni ba. A kirani da Besty na nafi so”. “Oh dama ka samu nake cemaka Yayan”. “Na yafe bana so. Tunda dama badan ALLAH kika fara faɗa ba ko a waccan ranar”. Kanta kawai ta juyar tana murmushi batace komai ba, sai kayan data fara amsa tana dubawa. Kala biyar ne, duk kuma sunyi ƙyau dan sun sami ɗinki na nutsuwa kuma mai ƙyau. Godiya tai amsa sosai da addu'a. Yaji daɗin addu'ar tata kuwa... Dai-dai nan Oum tai kiran wayarsa. Yana ɗagawa tace, “Auta turo min yarinyata tazo ta kwanta da safe ba wani isasshen barci za'a samu ba”. Sai da ya ɗan murmushi yana kai hannu ya shafa fuskar Maanal ɗin sannan ya ce, “Okay Oum gata nan zuwa”. Daga haka ya sauke wayar. Kayan ya maida a ledan ya ce, “Tashi muje na rakaki kafin Oum ta biyo sahu”. Dariya Maanal tayi, shima yana murmushi suka fito hannunsa ɗauke da ledan ita kuma basket ɗin. A compound daga can jikin motoci Maanal ta hango Najma da Yaya Fawzan. AA da sam hankalinsa bai kai wajen ba ta taɓa. “Besty kalla”. Juyawa yay ya kalla inda ta nuna ɗin, aiko yay wani tsai yana kallon ikon ALLAH. Maanal dake murmushi tace, “Mika fahimta?”. Maimakon bata amsa sai ya kama hannunta suka nufi wajen. Babu zato kawai su Yaya Fawzan suka gamsu. Daburcewa Najma tayi, dan suna tsoron AA sosai saboda ba sabgarsu yake shiga ba. A ɗan rikice taima Maanal alamar miyyasa ta bari yazo. Murmushi Maanal tayi, AA kam yay wani kalar tsaiwa ne yana kallon Yaya Fawzan irin kallon wana kama ɗin nan............✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖5️⃣8️⃣ ______________ .........Dariya yay Fawzan yay tare da shafa kansa ya taɓe baki. AA ya wani ɗan ɗage masa gira. Harga ALLAH abun yazo ma Yaya Fawzan a bazata, dan haka yama kasa magana. Shi kansa AA yanda Yaya Fawzan ɗin yayi ya bashi dariya, amma sai ya dake dan yau shima sai ya ɗan rama ko yayane daga tsiyar da Yaya Fawzan ɗin ke masa kullum. “To Abah kallon ya isa haka mana”. Ya Fawzan ya faɗa yana hararar AA. Murmushi AA yay a karo na farko, cike da neman magana ya ce, “Yaushe aka fara?”. Baki buɗe Ya Fawzan ya ce, “Mi ɗin?”. Gira AA ya ɗaga masa tare da faɗin, “Ai ka gane. Yau dai ALLAH ya kama min kai”. Dariya sosai Fawzan ya sanya, sai kawai ya rungume AA ɗin. Shima AA ɗin sai kawai ya hau dariya. Kusan minti biyu suna a haka kafin Ya Fawzan yaja hannun AA ɗin suka shiga mota. Ran AA fes da farin ciki ya ce, “Amma Yaya bata maka ƙanƙanta ba?”. Murmushi Fawzan yayi idonsa akan ƙanin nasa. “Ajwaad ai ita mace bata ƙanƙanta wa namiji. Kamar yanda mace bata yima namiji girma. Najma sa'ar Maanal ce fa. Kai ba gashi harka galla ma Lilly cizo ba tana mana amaye-amaye”. Murmushi kawai AA ɗin yay shima ya girgiza kai. Shima Ya Fawzan ɗin sai yay dariya kawai, dan yasan Ajwaad da rashin son magana. Da ƴar damuwa ya ce, “Ina sonta sosai, dan tanada tarbiyya. Zan iya cemaka ma kusan tarbiyyarmu iri ɗaya ce. Dan abubuwan Aunty Majdiya da yawa suna kamanceceniya dana Oum. A lokacin bikinku muka dai-dai ta, Ajwaad sam bana samun farin ciki irin na magidanci a gidansa. Bawai bamu samu haihuwar bane damuwata, nasan wannan lokaci ne, amma ita Mamy wannan take kallo kawai, shiyyasa ta sake zaɓa min wata matar”. Da sauri AA ya kallesa, “Wata matar?”. Kai Fawzan ya jinjina masa yana murmushi. “Jiyan nan ta bani hotonta da number ta akan nayi magana da ita. Ajwaad bazan ɓoye maka ba, wasu abubuwa na Mamy a ɗan tsakanin nan na saka zuciyata girgiza. Miyyasa take damuwa da sai itace zata zaɓa mana matan aure? Miyasa Oum ita bata taɓa kwatanta haka ba. Sannan abinda ke cimin zuciya matan ma duk bana ƙwarai ba. Kalla Babban Yaya, ALLAH nasan sam baya jin daɗin zama da Saheeba, kawai dai bazaiyi magana bane. Kalla wannan yarinyar da ake neman manna maka Nuratu, wlhy ban ƙara jin tsanar yarinyar nan ba sai a wannan zaman. Kuna Chaina ɗin nan fa sai da naci ubanta wai ita zatama Oum rashin kunya....” Wani irin kallon ɓacin rai AA kema Yaya Fawzan, shifa da'a taɓa Oum garama duk uwar ubanda za'ai ayi. Fawzan ya cigaba da faɗin, “Wlhy kuwa, amma abinda ya bani mamaki da naje ina zaginta a sashen Mamy sai Mamy ta canja fuska, har tana faɗin muma ni da babban yaya yanzun mun fara koyon halinka na ƙin danginta. Nayi ƙoƙarin ta fahimta amma wlhy tama korini wai na bar mata sashe. Na jima abin nan na cimin zuciya. Ni yanzu babban tashin hankalina ban san yanda zan yi da wannan yarinyar data kawo ba, nama rasa ina tasan yarinyar wai daga gidan sarkin kano take, ko miye alaƙarta da ƴan gidan oho”. Gaba ɗaya ma AA ya kasa magana, dan bai taɓa tunanin Mamy zata bar sauran ƴan uwansa su fara fahimtar wacece ita ba. Ya jima shiru, kafin ya kalla Yaya Fawzan da shima ya tafi tunani. Cikin lallashi ya furta, “Yaya badai kana son yarinyar nan ba?”. Cikin sauke ajiyar zuciya Ya Fawzan ya ce, “Sosai Ajwaad, ɗan zan iya cewa bayan Amaal Najma itace mace ta biyu da nake jin sonta har ƙasan zuciyata.” “Tunda har kana sonta ka daina damuwa da batun Mamy, sannan kada kama yarinyar magana barni da su.....” “Uhm-uhm Ajwaad bana son kama nuna ma Mamy na maka wannan maganar, dan bayan ni ɗin bana son ta fahimci wani yasan wata matsala makamanciyar wannan game da ita, sannan ka sani Mamy duk da ta bama Oum mu na har abada hakkinta na uwa na nan a kammu bai kau ba, kuma dole ne mu saukesa in har muna son zama lafiya. In har auren yarinyar shine zai sakata a farin ciki zanyi sai na haɗa da Najma ɗin”. Murmushi mai ciwo AA yayi, sai kuma ya girgiza kansa. “Yaya in dai har ba kaine ke da ra'ayin tara matan haka ba baka da wani dalilin yin hakan saboda umarnin Mamy, eh ita uwace, komai zamu iya yi a gareta, amma addini bai yarda harda cutuwa ba. Koka faɗa ko kai shiru kai hakan a gareka cutuwa ne. Ban sani ba ko ni kaɗai ne keda wannan matsalar a cikinku, bazan iya zama da mace fiye da ɗaya ba dan ina da ƙyanƙyami, zan ma iya rantse maka bayan Manaal bazan iya haɗa jikina da kowace mace ba, dan ita kaɗai ce nake jin yin nutsuwar hakan batare da jin komai a raina na ƙyanƙyami ba. Amma mizaisa kace zaka haɗa mata uku kaje wajen waccan kai amfani da ita ka koma wajen waccen like wani namamajo haba. Ai ko addini daya bamu damar yin hakan yace idan zamuyi adalci, sannan ga waɗanda basa iya kauda kansu ga wasu mata. Ni kuma harga ALLAH ma nasan ko na sakan ɗaya bazan iyama wata adalcin haɗata da Maanal ba. Dan haka Yaya be a man Please, ka rasa soyayyarka ta farko kayi haƙuri kayi juriya daga kai har Babban Yaya da ni na kasa a cikinku, sannan kunyima Mamy biyayyar amsar zaɓinta, ya kama a wannan karon ka bama zuciyarka abinda take so kodan ka samu farin ciki, dan banga ta inda wannan wawuyar matar taka zata canja ba (Kayi hakuri na zageta a gabanka)”. Murmushi Fawzan yayi, wata irin ƙaunar ƙanin nashi na ratsa shi. Tabbas sune yayunsa, amma Ajwaad ya fisu ƙarfin zuciya da rashin tsoro, shi fa in dai addini bai hanashi abububa to babu mai tankwarashi yinsa. Ko iyayensu bazai ce bazayi ba kai tsaye, amma zai bi ta hanyoyi daban-daban ya gujema abin. Kalla aurensa da Nuratu, kusan shekara shida fa kenan ana abu ɗaya amma yaron nan yasan duk ƙulumboton da zai yi ya zame. A yanzu ma da yake tunanin ya miƙa wuya gashi yana tabbatar masa bazai taɓa haɗa Maanal da wata ba, shi ƙyanƙyamin ma matan yake, chai akwai badaƙala kenan a gidan nan, yanda dangin Mamy suka shiryama auren nan ashe AA zai taro musu match. Aiko duk ma mi za'ayi sai dai ayi suna bayan ɗan ƙaninsu.... A hankali ya kai hannu ya dafa kafaɗar AA dake danna waya yana wani ɗan munafukin murmushi. Sai kuma ya ɗan leƙa yaga uwar mi yake kallo. Hotunan Maanal ne da alama kuma yanzu take turosu, yana leƙowar AA ya kife wayar cike da shagwaɓa ya ce, “Yaya ba ƙyau fa leƙen asiri”. Dariya Fawzan yayi sosai, ya ce, “Ganin Lillyn ne leƙen asiri kenan. Kai ni fa wlhy kallon Maanal nake kamar tare aka haifemu a gidan nan, dan ko sanda bama tare sai na dinga jin kamar an cire mana wani ɓangare na gidan ne, data dawo sai naga mun cika cif, kai tsaye mu huɗu nake kallo a matsayin ƴaƴa a gidan nan. Ban sani ba kodan a gabammu ta tashi ne oho”. Murmushi AA yayi yana sauke ajiyar zuciya kawai. Yaya Fawzan ya cigaba da faɗin, “Na gamsu da shawarar ka Auta, amma kai ya kake ganin zamu ɓullowa al'amarin, ni bana son Mamy ta fito da al'amarin nan fili harma wani ya kalleta da wani abu daban, dan tunda har na fara wannan tunanin na miyasa take son zaɓa mana mata ALLAH wasu ma zasuyi. Ko kai na tabbata zakaje kaita tunane-tunane ne yanzu” Tausayin yaya Fawzan AA yaji a ransa, dan da yasan yanda yasan wacece Mamy da bai faɗi haka ba. A fili kam sai ya ce, “Karka damu ka bar komai a hannuna”. “Ka faɗa min me zakayi mana?”. “Zanyi magana da Aba, bayan sallar nan kawai ayi biki”. “Kai baiyi kusa ba Auta, yarinyar fa bata kammala makaranta ba”. “Ba wani kusa Yaya, makaranta kuwa ta gama a ɗakinta. Ai aure bai hana karatu, haka karatu bai hana aure. Mu shaida ne akan hakan tunda Oum hatta Secondary a gidan aure tayi”. “Hakane na fahimta. ALLAH ya shige mana gaba”. “Amin ya rabbi. Yanzu yarinyar mika bata na gift ɗin salla”. “To baban soyayya, ka manta nace maka ko Oum bata sani ba”. “Tadai barku Yaya, Oum ai ba uwar banza bace idonta na'a kan dukkan notsinmu. Manta da wani kar kowa ya sani muje a saya mata gift”. Yay maganar yana kallon agogon hannunsa. Murmushi kawai Fawzan yayi, a ransa yana jin daɗin samun Ajwaad a matsayin ƙani. Key ya lalubo a jikinsa ya tada motar suka fice a gidan...... _________★ YAU TAKE SALLAH Ta kowane ɓangare yau bakunan ɗaukacin musulmai a buɗe yake da murmushin farin cikin zagayowar wannan babbar rana da akan risketa ne sau biyu rak a shekara. Farin ciki ne da baya ɓoyuwa a fuskokin yara da manya maza da mata. Tako ina anguwanni sun kacame da ƙamshin girke-girke na musamman. Sai kuma shiri da kowa keyi na sallatar idi. Anan gidan Darma ma hakan take, dan tunda akai sallar asuba Oum bata bar kowa ya koma barci a yaran ba. Tuni masu wanka sun fara, masu taya aikin haɗa abinci sun fara. Zuwa bakwai kowa ya gama shirinsa gwanin sha'awa kamar ka sacesu ka gudu. Baka jin komai sai ƙamshin turarurruka masu ratsa zuciya. A irin wannan ranar tako wace shekara abincin da ake karyawa da shi kafin tafiya sallar idi ana samar da shi ne daga sashen Mamy, dan haka kowa na kammala shirinsa can yake tafiya. Dama masu aiki duk can suke tattaruwa a haɗa abincin. Su kuma masu haɗa abincin salla suna anan sashen Oum ne, idan an dawo anan ake yada zango. Tuni Hajiya Oum tauraruwar Abah ta kaɗa kan yammatanta zuwa sashen Mamy ɗin. Tayi ƙyau harta gaji, kodan Oum ɗin ba haihuwa tayi akai-akai ba tana nan da ƙyanta da ƙyawun jiki kai kace ma itace amaryar gidan. Dan koda suka shigo harga ALLAH sai da Mamy taji zuciyarta ta motsa da salon gayun Oum ɗin, ba yaune farko ba, koda fita zasuyi tare har shakkar kwalliyar Oum take ji dan Oum akwai gayu. Cike da dakewa Mamy ta ƙawata fuskarta da murmushin dole suka rungume juna ita da Oum ɗin tare da yin happy salla. Dai-dai nan Abah da Yaya Fawzan suka shigo, babu kunya ya rungume Oum yana raɗa mata happy salla a kunne. Murmushi tayi ta amsa masa cike da jin nauyin yaran. Matsawa yay ya rungume Mamy data cika tai fam a zuciya itama. A bayyane yace mata happy salla, sai hakan ya sake ƙuntata ta taji a ranta wani abu ya faɗama Oum ita bai faɗa mata ba. Fawzan ma Oum ya ɗan fara rungumewa yay mata Happy salla kafin Mamy, sai Nibras data shigo yanzu cikin kwalliya dan yin hakan kamar al'adar gidan ce a duk irin wannan ranar. Sam hankalin Nibras a son ganin AA yake kawai, dan haka a fisge tacema Fawzan ɗin happy salla kawai ta matsa ta rungume Oum sannan ta matsa ga Mamy, Abah kuma ta risina ta gaisheshi shima tamai happy salla. A lokacin da Fawzan ke rungume Nibras ido suka haɗa da Najma. Ta wani ɗauke kai gefe idanunta cike da kishi. Murmushin yayi, kafin ya nufi ta inda take cike da iya taku yay kamar zai ɗauka abu a dining, cikin kunneta ya ce, “Sorry love a huce happy salla”. Dai-dai nan Saheeba da Babban yaya da yara suma suka shigo........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖5️⃣9️⃣ ______________ .......Suma dai haka sukaje suka rungume su Oum Babban yaya harda Abah ita kuma ta risina ta gaida Abah, Fawzan da Babban Yaya ma suka rungume juna. Kamar an saita dai-dai nan AA ya shigo shima. Da Abah, Babban Yaya, Fawzan, AA ɗin duk farrar shadda ce da akaima ɗinkin babbar riga na zamani, sai dai kowa da kalar nashi design ɗin. AA bai damu da saka manyan kaya ba, shiyyasa idan ya saka sai su masa wani masifar ƙyau. A haka ma bai saka babbar rigar da hular ba duk suna a hannunsa. Sai wata ƴar shopping bag mai shegen ƙyau da tambarin MAWAAD a jiki a hannunsa. A kaikaice ya gama kalle falon amma bai hango zinariyarsa ba. Cikin dakewarsa ya ƙarasa ya fara rungume Oum tare da mata Barka da salla. Ta shafa fuskarsa da murmushi ta amsa masa. Shima murmushin yayi ya buɗe bag ɗin hannunsa ya fiddo wani ɗan ƙyaƙyƙyawan box fari tas ya buɗe. Haɗaɗɗen agogo ne new design daga MAWAAD ya ciro, hannunta ya kama ya cire agogon data saka ya saka mata wannan tare da zobensa shima mai ƙyau, sai ya kama hannun ya sumbata. Hawaye ne suka cika idon Oum, ta sake rungumesa tana sanya masa albarka. Gaban Abah dake kusa da Oum shima yaje, ya rungumesa ya masa Barka da salla shima ya saka masa nasa agogon. Albarka sosai Abah yake saka masa harma da sauran ƴan uwansa. Sai Mamy data gama cika da kishi da baƙin ciki, a ganinta ita ya dace AA ya fara yima haka ba Oum ba. Sarai ya fahimci hakan a cikin idanunta amma sai ya basar ya mata murmushi itama yay hugging ɗinta yay mata barka d salla ya saka mata nata agogon. A taƙaice tace ALLAH yay masa albarka. Bai damu ba ya ƙarasa ga babban Yaya, shima dai haka yay masa, sannan Yaya Fawzan. Dai-dai yana sakin Yaya Fawzan dake masa raɗar shaƙiyanci a kunne Maanal da Batool suka shigo. Dama ta tsaya yima Batool ɗin kwalliya ne saboda barci data koma da ƙyar aka tadata tai wanka. Wani irin harbawa zuciyar Nuratu da itama take fitowa a lokacin cikin matsananciyar kwalliya da Nibras da AA sukai a lokaci guda. Dan harga ALLAH Maanal ɗin tayi shegen ƙyau a Abayar data sanya fara tas da ɗan kwalliyar ash kaɗan like kalar aikin jikin shaddar AA, sai handbag ɗinta itama ash mai shegen ƙyau designer, hakama takalman ƙafarta, duka suna cikin kayan da AA ya bata jiya kuma shine yace ta sanya su yanzu. Bata fahimci ma'anar hakan ba sai yanzu ta gane ashe anko yake son suyi. Sai ma taji kunya ta kamata ALLAH. Amma sai ta basar ta dake. Suna ma haɗa ido ya wani ɗage mata gira sama sai ta kauda kanta tana guntun murmushi ciki-ciki. Abah ta fara risinawa ta gaida, ya amsa mata da kulawa, tai masa barka da salla ya sanya mata albarka. Sai ta matsa ta rungume Oum dake ta kallonta dan kwalliyar ta mata ƙyau sosai. To dama kowa ai yasan Maanal da shegen son gayu da ƙyale-ƙyale. Duk da Hararar da Mamy ke mata a kaikaice yitai kamar bata gani ba taje itama ta rungumeta. Kafin ta gaishe da Babban Yaya sai Yaya Fawzan. Ta haɗa Saheeba da Nibras da duk ciwon hassada ya kamasu da ganin kaya masu mugun tsada da Maanal ɗin ta sanya a jikinta tun daga kan abayar har bag zuwa takalmi. Dan a yau kam sun sake tantance lallai AA yafi mazansu kuɗi, saboda ita Saheeba tana saida kaya tasan nauyin kowane irin kaya. Musamman su abayas, lass's, atamfa, da shadda da yadi na maza. Ita ko Nibras uwarta ƴar gayu ce kuma ƴar ƙarya da son ƙyale-ƙyale dan haka irin wannan manyan kayan tun suna yara koda bala'i uwarsu kan haɗa ta siyama kanta, ko koda kuɗin cuwa-cuwa na mutane😆😜. Kan Maanal a ƙasa ta juyo domin gaida AA kawai bawan ALLAH ya rungumeta. A kunne ya raɗa mata, “Barka da salla and matsowar shiga daga ciki Mrs Ajwaad. You look great in white”. Gaba ɗaya sai taji ta daburce. Balle ma da Yaya Fawzan ya wani ce. “Aouwwwww!! Kaga Masoyan asali”. Sosai kunya ta sake dabaibaye Maanal. Ta janye jikinta tana ɓoye fuska da veil ɗinta da tai rolling yay mata ƙyau kamar ka saceta ka gudu. Hannu AA ya kai zai ƙwace wayar Yaya Fawzan dake musu video. Yay saurin sakawa a aljihu yana dariya. Ganin haka sauran yaran dake musu hoto da videos suma suka shiga ɓoye wayoyin suna gimtse dariya. Oum, Abah, Babban Yaya ma dai murmushi duk suke. Yayinda Mamy ke jin tamkar zuciyarta zata fito ta baki. Nuratu zata juya ta koma ciki Saheeba ta riƙo mata hannu ta hanata. Nibras kam sai da ta ya share hawaye... Zaman karyawa sukai, dama tea ne kawai sai ɗan abinda ba'a rasa ba. Kasancewar ciki duk a cinkushe saboda azumi da aka sha babu wanda yaci na kirki duk suka tashi. Kowa ƙara gyarawa yay suka fito domin shiga motoci. Maanal na ƙoƙarin shiga motar babban Yaya AA ya wani riƙo hannunta, juyowa tai ta kallesa dan a zatonta cikin su Najma ne. Ƙaramar harara ya sakar mata yaja hannunta kawai suka nufi tasa motar. Sai kawai Mamy catai itama Nuratu ta tafi can. Wani shegen murmushi Abah yayi, sai dai baice komai ba yay shigewarsa mota kusa da Oum dake waya bata san mike faruwa ba. Yayinda Babban Yaya da Fawzan sukabi Mamy da kallon mamaki. AA kam da sarai yaji Mamyn yi yay kamar baiji ba, sai ma buɗema Maanal yay ta shiga hannunsa na riƙe da bag ɗinta ya zagaya nasa mazauni ya zauna, ita kuma babbar rigarsa da hula na saman cinyarta ya ajiye. Wani irin abu ya tsayama Najma na takaici, dan tunda Uncle R da Maanal suka tattauna akan Mamy a gabanta duk da basu fito fili sun ambaci sunanta ba itama ta sakama dukkan motsin mamy ido. Sai kawai itama ta fasa shiga motar Fawzan datai niyya ta koma ta AA suka shiga a kusan tare da Nuratu. Kallon juna sukai, Najma ta watsama Nuratu wani shegen harara ta ɗauke kanta. AA kam baiyi kamar yasan bayan shi da Maanal akwai wasu a motar ba, yana gama zama bag ɗinta a saman cinyarsa ya juyo yana kallonta, sai kuma a hankali ya kai hannu ya kamo haɓarta ya juyo da fuskarta inda yake dan da ta shagala ne da kallon design ɗin jikin babbar rigarsa da yay mata ƙyau. “Nan zaki kalla zuciyar Ajwaad. Dan rigar da mai rigar duk naki ne ke ɗaya. Aikin ya miki ƙyau ne”. Wani kasalallen murmushi Maanal ta sakar masa mai taɓa zuciya, cike da shauƙi ta kai hannu ta ja masa hanci kaɗan, “Duk ƙyan aikin kaine zaka sakashi yay ƙyau dan kai ke saka ƙyawu yayi ƙyau zuciyar maanal. I like you in manyan kaya”. Ya arrahaman, ji AA yay kamar zai wani shiɗe, bai ma san ya matso da fuskarta gab da tashi ba ya manna lips ɗinsa kan nata ya ɗan sumbata kaɗan. Sosai kunya ta kamata sanin basu kaɗai ne a motar ba, shiko idanunsa har sun ɗan sirka. Maanal ta ɗan maida fuskarta gefe kawai tana ɗan murmushi. Dai-dai nan babban Yaya yayima AA ɗin horn dan shine a bayansa. Ajiyar zuciya ya sauke a kasalance yay ma motar key, Nuratu da zuciyarta ke neman tarwatsewa ta kama murfin zata buɗe dan ta yanke gara ta fita a motar kawai taji ya saka luck. Dole ta koma ta zauna dan tsoronsa take ji bazata iya cewa zata fita ba kai tsaye. AA kam da shi yama manta da zamanta a motar a hankali yake mirza steering motar kamar baya so, dan gaba ɗaya Maanal ta gama kashe masa gaɓɓan jiki. Hannansa yakai a hankali ya kamo nata, sai ta juyo ta kallesa, shima kallon nata yay suka sakarma juna murmushi mai sanyi. Sai kowa ya janye, shi ya maida ga hanya ita kuma tana kallon waje har lokacin da murmushi a fuskarta dan ita kaɗai tasan mi take hangowa a cikin idanun ƴan maza. Najma kam cike da munafunci take musu video, dan wannan gulmar bazata gani ita kaɗai ba sai ta gumtsawa su Maimoo.. Sai kuma uban murmushin shaƙiyanci take zubawa da son ƙular da Nurry. Tako ci nasara, dan zuciyar Nurry har wani tururi take yi. Wata irin nadamar shiga motar take ji, ga zuciyarta fal bala'i amma babu damar nunawa tana tsoron shan mari a hannun AA Maanal ta samu na nata gori... A haka suka iso massalaci. Nuratu ta fara ficewa AA na kammala parking, Najma ta bita tana ƴar dariyar ƙularwa. Maanal na yunƙurin fita AA ya riƙota. Juyowa tai tana kallonsa. Ya marairaice mata fuska kuwa da faɗin, “Idan kin fita wazai ƙarasa shiryani, bayan kin san ban saka bane saboda kema ki samu kada”. Murmushi kawai Maanal tayi da ɗan girgiza kai, batare da tace komai ba ta ɗauka babbar rigar dake jikinta ta shiga warwarewa yana kallonta ƙuri kamar ya haɗiyeta yake ji. Amma dai ya daure dan yana son tsira da alwalarsa. Nuni ta masa da idanu ya duƙo, babu musu ya ranƙwafo sosai yanda zata ji daɗin saka masa ta saka, cike da kulawa batare data yarda sun haɗa ido ba ta gyagygyara masa duk da yana a zaune ne harda naɗo duka gefen biyu ta ajiye masa a kafaɗa duk da bawai babbar rigan nada faɗi bane. Dan anyita ne ƴar cif-cif babbar rigar zamani dai da faɗin nata duka baya wuce gwiwar hannu. Hula ta ɗauka ta shiga mata kari dan ta iya, tun suna yara tana masa karin hula, shiko sai kallonta yake, nan ma kan ya duƙo mata ta sanya masa, cike da kunya tasa yatsanta tana gyara masa ɗan gashin daya fito gefe-da-gefe kaɗan. Batare data yarda ta kallesa ba ta ce, “An gama”. Wani ƙaramin box ya miƙa mata, cikin raɗa muryarsa na sake komawa ƙasan maƙoshi yace, “Saura agogo da turare”. Batace komai ba ta amsa box ɗin ta buɗe, irin na su Yaya Fawzan ne shima, hannunsa daya miƙo mata ta amsa a cikin nasa kunya na sake rufeta, tadai daure ta saka masa sannan ta ɗauka turaren dake ajiye a tsakkiyarsu ta shiga fesa masa. Sai da ta ajiye turaren ta ɗago ta wani kallesa, sai kuma ta kashe masa ido ɗaya ƙasa-ƙasa,...........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖6️⃣0️⃣ ______________ .........“Ka cinye wannan zangon, kaine gwarzon shekara ƙyawawa na duniya my bestie”. Ta faɗa tana haɗe yatsunta babba da manuniya🤏. “Kin fini ƙyau ai Matar AA”. Ya faɗa cike da kasalar jiki data zuciya. Tare da kamo hannunta ya kunce agogon data saka ya saka mata wani mai shegen ƙyau dake tare da abin hannu sun sha stones farare sai ƙyalli suke, kaida da gani kasan ba normal stones bane ba. Baki ta saki kawai tana kallon hannun nata, sai kuma ta kallesa idannunta na ciko da ƙwalla. Tana motsa lips ɗinta da nufin yin magana yayma bakinsa alamar zipping. Dai-dai nan akai knocking glass ɗin motar. A hankali ya furzar da numfashi tare da cirar tissue ya miƙa mata sannan ya gyara zamansa ya sauke glass ɗin. Yaya Fawzan ne, cike da shaƙiyanci ya duƙo saitin kunnen AA yace, “Babu dai wajen canja sabuwar alwala anan a dinga tunawa ehe”. Rasama abin cewa AA yayi, sai kawai ya cije lips ya buɗe motar ya fito hannunsa riƙe da bag ɗinta. Itama Maanal fita tayi tacan. Kallon bag ɗin Fawzan yay cike da tsokana, sai kuma ya wani riƙe haɓa tare da faɗin, “Ni dai ka rufa min asiri karka cinye min ƙanwa ita kaɗai garan mace. Yau zan maka addu'a Abah ya baka ita mu huta dai kodan Baby”. Karaf a kunnen Maanal data matso domin amsar bag ɗinta a hannunsa, ai da sauri tai ƙoƙarin juyawa AA daya ɗan harari Yaya Fawzan ya riƙota. Bata juyo ba, shima baiyi magana ba ya saka mata bag ɗin kawai a hannu ya saketa. Kamar ƙyaftawar ido tabar wajen. Dariya Fawzan yayi kawai..... Anyi sallar idi bayan khuɗuba mai ratsa zuciya. An kuma sha addu'oi sosai. Koda aka idar ɗai-ɗai ahalin Darma suka dawo inda motocinsu suke. Salim ya fiddo Camara ɗinsa yace sai anyi hotuna. Babu wanda ya musa dan kowa yasan Salim mayen iya ɗaukar hoto ne. Tun ma Uncle Mahmud na masa faɗa harya haƙura ya saya masa camara ya kuma saka shi yay training class akan hakan. Tsaf ya saita camara ɗin ya ajiye shima ya dawo cikinsu akai hoton. Sunyi kamar biyar sannan suka shige motoci idan anje gida sai a cigaba. An dai yi waɗan nan ɗinne a filin idi domin tarihi... Yanzu kam babu wanda ya shiga motar AA, dan Mamy ma bata fargaba Nurry ta afka motar Babban Yaya. Ganin haka sai Najma ta shiga ta Yaya Fawzan daketa mata gargaɗi da ido. Aiko suna shiga abinka da gilashi mai duhu AA ya wani jawo Maanal ya rungume tsam, dan ɗazun yana sassautawa ne saboda alwala. Sai kuma ya ɗagota ya manne lips ɗinsu waje guda ya shiga bata zazzafar sumbata mai tsayawa a ƙahon zuciya. Sai da yaga yana neman sakin layi jikinsa kuma na neman canja yanayi sannan ya saketa. Sam kasa haɗa ido Manaal tayi da shi har ya tada motar yabi bayan sauran. Shima bai sake cemata komai ba har suka iso gida. Anan compound aka yada zango, hotuna aka fara ɗauka kamar babu gobe. Maanal nata dojewa kar suyi daga ita sai AA, sai dai hakan bai yiwu mata ba, dan an gama ɗaukarsu ita da shi da Oum, Oum ta juya zata bar wajen saboda magana da Babban Yaya ke mata itama Maanal ta yunƙura zata gudu AA ya riƙo hannunta, kanta ta juyo kawai a hanka ta kallesa shima yana kallon nata kawai Salim ya ɗauka ƙitt. Aiko hoton yayi masifar ƙyau. Ya juyo da ita tazo dab da shi kanta a ƙasa yana kallonta nan ma Salim ya sake ɗauka. AA ya ranƙwafo sai tin kunenta zai mata magana nan ma aka ɗauka. Matuƙar ƙyau hotunan nan sunyi. Takaici kamar Mamy zata haɗiyi zuciya ta mutu. Kowa fuskarsa da farin ciki itako tata sai baƙin rai. Ko hotunan ba kowanne ta shiga ba, ta koma gefe ta zauna tana ta sauke ajiyar zuciya. Koda ta turo Nuratu su ɗauka da AA Salim na shirin ɗaukar hoton dan wulaƙanci AA ya juya baya yana amsa waya sai bayansa da Nuratun aka ɗauka. Bai kuma tsaya ba yay gaba. Nurry ta bishi da kallo idannunta na ciko wa da hawaye. Sai kuma ya juya tana kallon Mamy. Wani irin daɗi Nibras taji da hakan ta faru, duk da zuciyarta kamar ga kama da wuta akan hoton AA da Maanal. Tana can tana kishi mara amfani Fawzan na nan yana ɗaukar nasa da Najma. Ɗaukar hoton data ja hankalin Abah da Oum kansu. Dan kai tsaye suka fahimci akwai wani abu a tsakanin yaran. Wani kalar daɗi Abah yaji, sai yaji kamar ya tashi ya goya Fawzan. Oum ma jitai hawayen daɗi na ciko mata idanu, koba komai Finally shima Fawzan ɗinta zai samu mai share hawayensa. Mamy kam baƙin zuciya da sakama AA da Maanal ido datai yasa bama ta fahimci na Fawzan da Najma ɗin ba sam. Fara shigowar motocin baƙi yasa hotunan sake ɗaukar armashi. Dama gidan Darma a ranar salla matattarar baƙi ce sosai. Isowar su Didi Shahidah ya saka Maanal kwasa a guje ta rungumeta. Dan bata sanar mata zasu zo ba. Tuni Barru da Haneef sun rungumeta suma Haneef harda kukansa dan yana bala'in son Maanal. Uncle Sadeeq kam sai suka bashi dariya. Dan da ƙyar suka bari Maanal tazo ta gaidashi da masa sannu da zuwa. Cikin ƙanƙanin lokaci gidan ya tara mutane. Tuni an gama shirya abinci a garden kamar yanda akeyi duk shekara. Can aka ɗunguma cin abinci. Manaal dake manne da Didi duk sanda ta ɗago sai sun haɗa ido da AA. Dan cin abincin sashin maza daban na mata daban. Anci ansha an godema UBANGIJI. Baƙi suka cigaba da zuwa, Maanal ta gaisa da Ammie ta video call, ta kuma kira Daddy shima tai masa barka da salla. Da Nene da duka kawunan su ƴaƴan Nene. Sai Didi Maanal itama da suka jima suna hira dan ɗakin Oum suka shige ita da Didi sukai hirarsu ta yaushe gamo. Sai ga kiran su Aneesa suma. Nan ma sun sha hira sosai. Bata sake ganin AA ba tunda suka shigo. Sai bayan sallar la'asar da su Didi suka tafi tai kira Mah-mah ta kano (Nasan kun gane Maman su Oum kuma tasu RK😀) harda Abbah suka gaisa da su Yaya da aunty Rufaidah da amaryar RK Nuwaira. Shima RK ɗin ya amsa suka gaisa cikin girmama juna. Hakan yayama Mah-mah daɗi ta dinga sakama Maanal albarka ita da Abbah. Maanal ta dinga amsawa a kunyace. Daga nan Baba Sardauna ta kira, shima suka gaida harda Ummah, su Uncle Mahmud, Hassan, Hussain duk suna nan tare da matansu suma duk suka amsa suka gaisa. Sosai abinda tai ɗin yay musu daɗi, dan su Saheeba basu taɓa ɗaga waya sun kira wani a cikinsu ba, sai dai in Kanon sukaje ko su sunzo Abujan. Itako Maanal a wajen Najma duk ta amshi numbers ɗinsu. Daga nan Baba ta kira. Wato mahaifin Abah shima ta gaisheshi shi da Mamma matarsa, nan ma ta gaisa da su Uncle Najeeb da matansu. Kowa sai saka mata albarka yake. Tana yankewa ta kira Gwaggo Khadijah, mahaifiyar su Nuwaira kenan, baiwar ALLAHr nan kamar ta zuƙo Maanal ta wayar ta goyata dan farin cikin wannan girmamawa datai mata. Itama ƴayanta na gidan suka gaisa. Hajiya Majdiya ce ƙarshe. Ita kam ai tamkar uwa take, nan fa ta fara mata hira tana sanar mata ta shirya salla da kwana uku zatazo Abuja da kayan gyara dan sai ta gyarata tsaf kafin tarewa. Kunya duk ta ishi Maanal. Suna yin sallama ta fara neman layin AA, ganin har biyar ta wuce a tunaninta ma baya gidan. A mamakinta sai taji karar wayar a cikin ɗakin, da sauri ta juya bayanta sai ganinsa tai tsaye a bakin ƙofa ya wani harɗe hannaye a ƙirji ya jingina da bango ya zuba mata idanu. Sosai ta waro nata idanun waje dan sai kamar taji tsoro, harga ALLAH bata san ya shigo ɗakin ba balle sanin tun yaushe yake a wajen. Ganin yanda ta daburce sai yay murmushi, cike da basarwa ya iso yana faɗin, “sarkin tsiro”. Cikin tura baki ta ce, “ALLAH ka bani tsoro fa. Babu ƙyau irin haka kaɗan ya rage na fasa ihu ALLAH”. Kusa da ita ya zauna ya jawota jikinsa ya rungume. Cikin magana ƙasa-ƙasa ya ce, “Sorry bazan sake ba.” kanta ta jinjina masa. Ya ɗagota yana kallonta cikin ido gira a ɗage. “Kina missing ɗina ne?”. “Bance ba”. Ta faɗa tana kauda kai gefe. “Uhyimm! To miyasa ake kirana? Bayan ba'a taɓa ba!”. “Ni bakai zan kira ba, kuskure aka samu”. Kwanciya yay ya ɗaura kansa a cinyarta, hannayensa harɗe a ƙirjinsa yana kallon fuskarta cike da shauƙi ya ce, “Ba ƙyau ƙarya fa, gashi nan idanunki sun nuna kina kewar ɗan saurayinki”. Murmushi tayi tana kauda kanta gefe. Yasa hannu ya dawo da fuskar ya hanata hakan. Dole ta haƙura ta tsaya. Bai saki fuskarta ba sai ma murza babban yatsarsa daya cigaba da yi a hankali kamar mai share mata hawaye, yana kallonta da wani irin sanyin yanayi ya cigaba da magana a hankali. “Ina can ina barci sai mafarkinki nake yi, da ƙyar na daure na fara zuwa sallar la'asar amma nazo ban ganki ba. Da ƙyar Oum da taga na damu taji tausayina tace min kina nan”. Samun kanta tai da ɗaura nata hannun itama akan lallausar sumarsa data sha gyara, yanda ta tura yatsunta cikin sumar yasa AA lunshe idanunsa a hankali yana sauke ajiyar zuciya. Sai kuma ya buɗe idanunsa slowly ya ce, “Thanks You”. “For what?”. Ta faɗa a hankali. “Everything Babie”. Ya bata amsa cike da raɗa yana lumshe idanun da buɗewa a lokaci guda. “Kin kira dukkan ahalina kin gaishesu, ke ta dabance a rayuwata Manaal”. “Oh ahalinka ne kai kaɗai?”. “No sorry ahalinmu”. Murmushi tayi, sai kuma tace “Nima ai Ammie da Daddy da Nene sunce ka kirasu ka gaishesu tun ɗazun”. Murmushi kawai yayi, cikin son kauda zancen ya ce, “Ina son mu ɗan fita yawon salla fa”. Ɗan jimmm tai sai kuma ta ce, “Yaushe?”. “Yanzu idan anyi magrib. Sonai tun la'asar ma, amma ba damuwa zuwa bayan magrib ɗin ma yayi”. “Amma kai zaka gayama Oum?”. “Babu damuwa. Sarkin kunya.” Yay magana yana ɗan jan lips ɗinta masu taushi da santsi..........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖6️⃣1️⃣ ______________ ........A falo kam a kusan dai-dai lokacin ne Ameeran Hajiya Shuwa ke shigowa gidan. Riƙe take da hannun ƴar gidan yayanta Ameer sai ƙaramin basket mai ƙyau ɗauke da ƙyawawan bowl a cikinsa. Mutanene sosai a gidan, dan haka kanta a ƙasa take gaida duk wanda ta gamu da shi harta isa sashen Oum. Anan ɗin ma dai da mutanen, haka ta daure ta shiga ciki bakinta da addu'a. Dai-dai tana saka kai ciki shi kuma babban yaya ke fitowa hannunsa riƙe da waya yana magana. Sai kawai sukaci karo dan su duka hankalinsu baya a gabansu. Cikin sauri tai ƙasa zata tallabe basket ɗin shima ya duƙo zai tallabosa batare dama yaga wacece ba. Wani kalar bugar hancinsa mayataccen ƙamshin turarenta yayi, ya wani irin zuƙa ya lumshe idanunsa irin na AA. Ita ɗin ma dai nasan ƙamshin ne ya wani kalar ratsata. Sai da taja numfashi kamar mai asthma ta haɗiye. A tare suka ɗago, yana ƙoƙarin ce mata sorry itama tana ƙoƙarin cemasa sai kowa yay shiru. Sai kuma ita ta saki murmushi da faɗin, “Lah Babban Yaya ashe kaine. Good evening fatan anyi salla lafiya”. Sosai wani abu mai girma ya tsargama babban Yaya, kasancewar sa ba gwanin murmushi ba shi sai ya tsareta da idanu kawai. Muryarsa a ƙasa ya furta, “Ameerah kece haka?”. Murmushi tayi tana mai duƙar da kanta cike da kunya. Shima sai ya wani lumshe idanu ya buɗe kamar mai shirin suma. Sai kuma ya bata hanya yana faɗin, “Kin dawo lafiya ya karatu?”. “Alhamdullahi Yaya an kammala.” “Masha ALLAH, ALLAH ya sanya albarka sai aure ko?”. Kalmar ta suɓuto masa batare daya shirya hakan ba. Ɓoye fuska Ameera tayi cike da kunya ta ce, “Yaya ba yanzu ba”. Murmushi yayi da ɗan taɓe baki ya ce, “Idan mun yarda mu yayye kenan. Oya shiga Oum ɗin na ciki”. Ai da sauri Ameerah ta shige. Dan harga ALLAH kallon da baban yaya ke mata ba ƙaramin rikita mata lissafi yay ba yau ɗin nan. Oum na ganinta ta fara murna da mata oyoyo, ALLAH sarki Oum uwa maba da mama kenan ita kowa nata ne, shiyyasa da wahala kaji mutum yace baya sonta. Rungumeta Ameerah tayi cike da farin cikin ganinta, dan itama tayi missing ɗin Oum sosai. Dai-dai nan Maanal da AA suka fito daga bedroom ɗin Oum. Ameerah ta ɗan kafe Maanal da kallo, sai kuma ta juya tana kallon Oum idanu a zare ta ce, “Oum Maanal ko?”. Oum na dariya ta ɗaga mata kai. Cikin wani kalar farin ciki Ameerah ta juyo tana sake kallon Maanal, dan tasan labarinta sosai a wajen Oum. Ta ce, “Woow Oum ƙyaƙyƙyawa da ita”. Sai kawai taje ta rungume Maanal ɗin tana faɗin, “My twin sister nayi farin cikin ganinki”. Murmushi Maanal tayi kaɗan duk da bata santa ba, suna haɗa ido da AA ya ɗauke kansa. Ameerah data ɗago itama sai ta kalla AA ɗin. “Oh Yaya AA shine koka faɗa min Bestynka ta dawo, bayan ranar har gaisheka nai ta WhatsApp”. Hararrata ya ɗanyi ya raɓasu zai wuce. Ameerah bata damu ba dan tasan halin kayanta. Har cikin rai ɗaukar su AA take kamar Yaya Ameer, suma kuma suna mata gata irin ta yayu da ƙanwa. AA ɗin ne ma dai bai cika sakewa ba. Kuma tunda ta fahimci halinsa kenan bata wani damuwa da wani ɗaure-ɗauren fuskarsa ko rashin yawan magana. Oum ce taima Maanal bayanin Ameerah, dan ranar data fara ganin Hajiya Shuwa a gidan ta bata labarinsu kaf. Oum nace mata su Najma ma nan cike da farin ciki taja hannun Maanal suka nufi garden dan su Najma nacan. Aiko suma su Najma na hango Ameerah suka taso a guje suna ihun murna dan abokiyar wasansu ce idan sunzo hutu. Nanfa hira ta ɓalle dan Ameerah babu ruwanta..... _________ Washe garin salla AA ya damu Abah da maganar Yaya Fawzan da Najma. Mamaki ne ya kama Abah sosai, amma sai murmushi yake na farin ciki. “Naji daɗin wannan al'amari ƙwarai da gaske Ajwaad. Kuma ina sha ALLAHU bazayi ƙasa a gwiwa ba a yau ɗin nan zan kira Baba na sanar masa. Idan so samu ne a satin nan akai kuɗi a haɗa bikin da naka ma. Dan na jima da fahimtar Fawzan na buƙatar ƙara aure”. Murmushi AA yayi shima, ya ce, “ALLAH ya tabbatar Abah, kaga shike nan ma an huta ta ƙarasa karatun a ɗakinta”. “Sosai kuwa haka za'ai in sha ALLAHU, in ma zai yi hakuri sai a ɗaura kawai idan ta kammala jarabawar tunda wata ɗaya ne sai ta tare. Kaima kuma dama ina nemanka akan naka auren da yarinyar nan Nuratu”. A take fuskar AA ta canja. Abah na lura da shi yay ɗan murmushin manya. Kafin ma yace wani abu AA ya fara magana murya a cinkushe. “Abah wai maganar yarinyar nan baza'a barshi bane. Nifa ko ƙaunar ganinta banayi a gidan nan balle kallonta a wani matsayi mai kusanci dani. Yarinyar nan bata da tarbiyya sam, sannan rawar kanta yayi yawa. Haba mace babu nutsuwa ai ba mace bace. Dan ALLAH Abah ni dai ka rufa min asiri ka rushe maganar nan matata ta isheni wlhy”. Sosai abin ya ba Abah dariya, dan kamar fa AA zai masa kuka. Amma dai ya danne cike da kulawa ya ce, “Karkace haka Ajwaad koba komai ƴar uwarka ce ita. Sannan bamu san inda rana zata faɗi ba nan gaba ALLAH ya jarabceka da sonta. Kuma kaga an riga an tsaida magana da iyayenta bai kamata mu zama ƙananun mutane ba ai ko”. Sosai zuciya ta tokare maƙoshin AA. Da kyar ya iya furta, “Shike nan Abah, amma dan ALLAH ba yanzu ba, a ɗan bani lokaci idan na shirya da kaina zan maka magana”. Ɗan jimmm Abah yayi na tunani, sai kuma ya jinjina kansa, “Okay ba damuwa, amma ina son ka kira Baba kai masa bayani da kanka, dan gaskiya bansan yanda zan tunkaresa ba. Tunda na hannun damarsa ne kai nasan zai saurareka”. “In sha ALLAHU zamma je Kanon gobe”. Nanma dariya sai da ta kusa kufcema Abah, ya ta dai danne da ƙyar. “Okay ALLAH ya kaimu, sai batun Maanal, zata koma gidan Shahidah...” “Saboda mi?”. “Saboda Oum ɗinku ta nema alfarmar hakan, wai zasu mata ko gyaran jiki na amare kasan dai mata.” Sam AA baiso hakan ba, amma har gaban abada bazai iya musu da Oum ba. Dan haka yace, “Shike nan Abah. Dama akwai kaya da suka iso na lefenta, suna hannun Babban Yaya. Amma da zai yiwu ba sai an kaisu ko'ina ba, kawai a ajiye mata Abah”. “Masha ALLAH, ALLAH yay maka albarka Ajwaad. Hakan yayi sosai, tunda ankai wancan na wajen Rafeeq kada mutane suga kamar wata fariyya ce. Amma in aka ajiye mata ƴan uwanta kawai suzo su gani ya wadatar.” “Nima abinda nayi tunani kenan”. Albarka sosai Abah ya dinga saka masa, daga haka suka cigaba da hirarsu.... WASHE GARI Da safe AA ya wuce Kano, lokacin Maanal ma na barci ko sallama basuyi ba. Kai rabon daya samu zama da ita tun daren salla da suka fita yawo sai 12 suka dawo. Jiya ita da su Oum da yaran duka a gidan Shahidah suka yini sai dare suka dawo. Yau kuma gashi zai wuce kano tana barci. Ashe Oum ta shirya masa, dan sun gama tsara komai ita da Hajiya Shuwa, dama Maanal ba gidan Didi Shahidah zata zauna ba, nan gidan Hajiya Shuwa ne. Oum ta ɓoye hakan ne dan kar ma AA yace zai dinga zuwa gidan wajenta ya ɓata musu aiki. Aiko a ranar da yamma Oum ta amshe wayar Maanal aka kaita gidan Hajiya Shuwa babu wanda ya sani hatta da Abah. An kuma gargaɗi Ameera. Gaba ɗaya sai Maanal taji ta damu batai sallama da AA ba. Amma dai ta dake ko'a fuska bata nunama Oum komai ba. A ranar AA bai dawo ba sai washe gari, yanata baza idon ganin Maanal shiru. Da ga ƙarshe dai ya daure ya tambayi Oum tace ba Abah ya gaya masa zataje gidan Shahidah gyaran jiki ba. Kasa cewa komai AA yayi, dan Oum ta wuce gaban ka-ce-na-ce a wajensa. Duk kuma yanda tayi dai-dai ne. Aiko bai ƙara magana ba bawan ALLAH, sai ma ya tattara ya koma aiki. Maanal kuma ya saka aka ƙara rubuta mata sabon hutu bayan wanda suka sha tun daga dawowa Chaina. Mamy ma dai bata ganin Maanal a gidan, bata tambaya ba amma abun naci mata zuciya. Gefe shirye-shiryen bikin da suke ya ɗauke mata hankali. A haka aka ci kwanaki sati ɗaya. Saura sati ɗaya biki kenan. Da yamma babu zato suka samu baƙuncin Baba Sardauna tare da Uncle Mahmoud da yay masa rakkiya. Saheeba ce ta shiga tana faɗa ma Mamy zuwansu. A take fuskar Mamy ta canja, cikin taɓe baki ta ce, “Uwar mi kuma akayi to?”. “Waya sammusu Mamy, kin dai san in dai kaga tsohon nan to ba alkairi ba ne”. Kafin Mamy ta bada amsa kira ya shigo mata waya, Abah ne kuwa, tana ɗagawa yace tazo ga Baba. Kafin tace wani abu ya yanke. Kwafa tayi mai ƙarfi, kafin ta miƙe tana tsinema Darma Family gaba ɗaya. Hijjab ta saka sannan ta nufi sashen Abah ɗin hannunta ɗauke da basket na abinci data saka Haule ta haɗa mata. (Munafukai) Ta faɗa a zuciyarta ganin Oum zaune kusa da Baba fuskokinsu cike da farin ciki, dakewa tai itama ta ƙawata tata fuskar da fara'a. Cikin girmamawa ta gaishe da Baba, ya amsa mata da kulawa kamar yanda ya saba. Sai ta koma tsokanar Uncle Mahmoud irin wasan ƙanin miji. Shiko yana ramawa. Haka dai aka gaisa cikin farin ciki kamar babu komai a zukata.. Bayan su Baba sunci abinci sun huta bayan sallar isha'i akai zaman meeting. Baba da kansa yay masu bayani cewar sun shiryama Ajwaad da Maanal bikin tarewa. Sannan batun Nuratu ga yanda suka tsara saboda abinda ya dinga faruwa a tsakanin Maanal da Nuratun da azumin nan. Dan haka yana roƙonsu su basu haɗin kai ayi komai a tashi lafiya, su kumayi fatan zuwan na Nuratun itama da kamar yau ne da an kammala ginin da za'a sakata ciki, saboda haɗasu waje guda bazai haifar da ɗa mai ido ba..........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖6️⃣2️⃣ ______________ ........Babu wanda yay musu akan hakan, tunda dai agaban idon kowa komai ya dinga faruwa. AA sai wani munafukin murmushi yake a kaikaice. Mamy na lura da shi sai ko ta ƙara ƙulawa. Amma dai ta dake yanda kowa yay addu'a itama tayi. A zuciya kuwa kaf family ɗin Darma sai da ta tsine musu yau, a ganinta munafunci ne kawai. Da ƙyar ta iya riƙe kanta aka tashi a wannan zama. Ko ganin hanya batayi sosai ta nufi sashenta, tana shiga sai ga Maman Saheeba ta kirata. Kamar bazata ɗauka ba tadai daure ta ɗauka ɗin, ko sallamarta Maman Saheeba bata amsa ba a haukace ta fara magana wai yanzu Baban su Nuratu yazo ya sameta da batun Baba Sardauna ya sameshi ɗazun da yamma ita bata nan yace masa ayi haƙuri a ɗan basu lokaci akan bikin nan suna neman alfarma. Ita kanta Mamy gigicewa tayi dan taso ace ita zata zauna ta tsara ma su Maman Saheeba ɗin ashe mugun tsohon sai da ya fara zuwa can, da alama ma daga gidan nasu sukayo airport. Cikin son kwantar mata da hankali ta ce “Nana!”. Ƙin amsawa tayi, ta cigaba da masifa, sai kan Mamy ya dinga wani irin sarawa na ciwo, ga masifar Maman Saheeba na haura mata har saman kan. Sai kawai jiri ya kwasheta ta zube a ƙasa. Sai Haule ce ta taimaka mata ta tashi da ƙyar, ta kamata domin takaita bedroom tace ta ƙyaleta. Haka ta taka zuwa bedroom ɗin nata da ƙyar ta kwanta. Wani irin ciwon kai kamar ana buga mata guduma na cikinta. Sai hawaye sharrr-sharrr. Waya ta jawo da ƙyar tai kiran baban su Nuratu. Bugu ɗaya kuwa ya amsa. Cike da girmamawar da yake bata ya shiga gaisheta. Ta amsa cikin sanyin murya tana tambayarsa miya faru? Yaya sukai da Baba Sardauna. Sai da ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce, “Aunty, Alhaji Sardauna magana yay min ta fahimta kuma ta gamsuwa. Kawai ƴar uwarki taso tada hankalinta ne da naki. Ya tabbatar min tunda Nuratu tazo gidan nan naku take jan rikici tsakaninta da ita matar Ajwaad, shiyasa suka ga za'a iya samun matsala ace an haɗasu a muhalli guda. Tun rikicin na iyakar su biyu zai koma ya taɓa zuminci ne tunda yau da gobe sai ALLAH. Shiyyasa shi Ajwaad ya nema alfarmar a bashi lokaci zai mata gini sai ya sakata a ciki, idan kuma tafi son nan gidan sai ita matarsa ta koma can ita Nuratu ta zauna nan kusa da ke. Dan ALLAH ina wuyarta ga daɗinta a wannan shawarar? In ce sauƙi ma aka samawa kowa. Amma ta yada hankalinta gata can harda yanke jiki ta faɗi sai da aka saka mata ƙarin ruwa. Ko saurarena na gama mata bayani ma batai ba fa ta hau bori tai kiranki”. Ajiyar zuciya Mamy ta sauke. Sai kuma a hankali tace, “Shikenan ka bari zan shigo Kanon gobe da safe.” Cikin jin daɗi yace, “ALLAH ya kaimu aunty sai kinzo”. Mamy na yanke kiran tai lamo, sosai take fassara maganganun baban su Saheeba ɗin dalla-dalla. Wani sashen na zuciyarta najin gamsuwa da zancen, wani ɓangare kuma na nuna mata yaudara ce kawai, ba kowa ya shiryata ba kuma sai Oum. Ko kuma ta kitsama Ajwaad ya faɗama Baba Sardauna, in ba haka ba ta ina Baban yasan wani anyi rikici da azumi? Koda yake akwai munafukan yaran nan ƴan hutu, suma zasu iya fa. Dan ita bata san AA yaje Kano kwana biyar da suka wuce ba. Kawai dai tasan yayi tafiya, amma bata san ina yaje ba. Sosai zuciya ke tunzurata akan taje ta samu Oum, amma wata na kwaɓarta akan ta fara bari Ajwaad ya dawo ta fara tuhumarsa sannan. Wani gefe na nuna mata ba lokacin fito-na-gito bane yanzu. Ta bari sai ƴaƴanta sun gama dawowa tafin hannunta ta hanyar auren zaɓinta gaba ɗaya tukunna. Dan haka ta cigaba da lallaɓawa ai auren nan na Nuratu da Ajwaad, shima Fawzan ya auri Amani dan yarinyar kullum sake shige mata zuciya take, kullum sai ta kirata a waya sun gaisa. Ganin haka bata taɓa tuhumarta batun Fawzan na kiranta ba, ita kuma Amani batai mata maganar ba itama. Shi ko Fawzan dan karma Mamy tai masa maganar Amani a tsaitsaye yake shigowa gaisheta da safe, idan ya dawo aiki kuwa sai gab da magriba shaf-shaf yazo ya fice. Ganin kuma bai sake cewa komai ba sai ta ɗauka yana kan lallaɓa Amani ɗin ne su daidaita. Taso yaje da sallar nan amma sai Maman Saheeba tace ta bishi a hankali, wataran ma bata sani ba zai je wajen Amani ɗin tunda har ya yarda suke waya.. _________★ Sosai akema Maanal gyara na fitar hayyaci, ciki da wajenta ga wani uban ƙamshi na bala'i a dukkan motsinta. Fatan ta kuwa wani irin santsi da take da walƙiya abin ba'a magana. Ita kanta ji take a jikinta komai ya canja. Hatta gashinta, ƙafafunta da tafukan hannunta gyara Hajiya Shuwa ke musu na balan bala'i. Kai Hajiya Shuwa tasan sirrin gyaran mace na bala'i ƙwarai da gaske. Dan hatta baki da lips ba'a bari ba. Ga wasu manyan lectures na zaman aure da take buɗema Maanal ɓaro-ɓaro. Idan ta nuna jin kunya ta mata daƙuwa da faɗin. “Kaniyarki, ba batun kunya muke ba anan, ki nutsu ki fahimci komai nake so. Kina dai ganin gogaggiyar yarinyar da ake so a aura masa mai ido a tsakiyar goshi. Mijinki ba ƙaramin mutum bane ba, sannan yana masifar sonki. Haƙurin da yay na shekaru karma kiyi zaton zai raga miki. Sannan yana zaga duniya yana gamo da mata kala-kala baki sani mugun halin wata ba, wasu matan da shirinsu suke kasancewa akan ƙwace miji wlhy. Mu kammu munsha wannan gwagwarmayar a lokacin ma duniya na barci balle yanzu da idonta ke a buɗe ƙyar”. Ire-iren irin wannan nasihar ke sanyaya jikin Maanal ƙwarai da gaske. Sai ta ƙara nutsuwa tana ɗaukar komai yanda ya kamata. Wani gefe na zuciyarta kuma najin kewar su Oum da su Ammie. Dan kowa ma Hajiya Shuwa ta hanata waya, acewarta so take ta bata hankalinta gaba ɗaya. Aiko ta bata ɗin, dan Maanal ɗin a kallo ɗaya zaka fahimci makarantar Hajiya Shuwa ba tasiri a gareta yanda ya kamata.... Ata ɓangaren Oum kuwa shirin biki suke mai ban mamaki, dan sai ka ɗauka ma sai yanzu ne za'a ɗaura auren. Ta ƙarƙashin ƙasa kuwa Abah da AA da RK da Babban Yaya na shirya na Yaya Fawzan, dan an gama komai amma su kaɗai maza suka san da auren ko su Oum basu sani ba. Ita kanta Hajiya Majdiya Baban su Najma kawai ya sameta cewar zaima Najma aure. Da farko rikicewa tayi, amma da ya zauna ta mata nasiha da tabbatar mata zatai farin ciki daga baya sai ta kwantar da hankalinta, dan tasan bazai cutar da ƴarsa ba, kuma yana da dalilin ɓoye matan. Za'a ɗaura aure ne kawai biki sai Najma ta gama jarabawarta da take shirin farawa nan da sati ɗaya. Dan haka su idan za'a kaita su zasuyi nasu bikin. Kuma hatta shi Fawzan ɗin bai san da wannan batu ba, dan AA da RK sun gama shirya komai da komai har gayyatar abokansa.... Mamy ma taje Kano, sai dai aranar ta dawo. Da alama kuma ta ciwo nasarar sasantawa da Maman Saheeba. Sai dai Nuratu babu lafiya wai tana ma asibiti an kwantar da ita. Dan tunda batun ɗaga bikin nata ya shiga kunnenta ta yanke jiki ta faɗi, tun kwana biyu da salla ta koma gida dan yin shiri biki dama. Baiwar ALLAH Oum, tana ji ta tasa ƴan hutunta gaba da bazasu koma ba sai anyi biki sukaje suka duba Nuratun. A can suka sami Mamy da Saheeba dan tunda rana suka tafi su. A mazan dai su Babban Yaya babu wanda yaje, shi AA ma baya nan yana Lagos, ya kuma ce bazai dawo ba sai ana saura kwana ɗaya.... ________★ Hakan kuwa ce ta kasance, ranar Alhamis ya dawo, a kuma ranar baƙin abokansa da bai san da zuwansu ba suka fara isowa. RK da Yaya Fawzan sun riga sun tanadar musu masauki. Anan ma gida tuni ƴan Kano sun fara isowa, zuwa yamma sai ga tawagar su Nene da sauran tarkacan Maanal, harda motocinta na lefe, sai kayan kawai aka sauke anan su a gidan Shahidah suka sauka. Dan itama Maanal can gidan Hajiya Shuwa ke shirin maidata. Ya subahannallah, kunga Maanal kuwa, tayi ƙyau harta gaji, ga ƙunshi ja da baƙi an zuba mata. Gashi yasha wanki duk da itama tasha kuka a wajen gyaransa. Ƙamshi ba'a magana ko kana nesa da ita ta gitta sai ka jishi. Bayan sallar zuhur Hajiya Shuwa da Ameerah suka kaita gidan Shahidah. Tuni ta faɗa jikin Nene tana murna, yaran kuwa suka zagayeta kowa na farin cikin ganin Mie-mie kamar yanda suke kiranta. Nene sai latsa jikin Maanal take tana santi. Su kansu su Amaal bakinsu ya kasa yin shiru. Dan gaskiya Maanal ta gyaru sai Masha ALLAH. Jin Ammie bazata zo ba Maanal ta samusu shagwaɓa, ta kira Ammien tana kuka. Lallashinta tayi da tabbatar mata nan da sati biyu zatazo in sha ALLAHU. Da ƙyar-da-ƙyar Maanal ta haƙura. Ranar kam ansha hirar yaushe gamo, dan su Maanal suna son junansu sosai. Washe gari juma'a Mothers event, na rana ne ƙarfe uku za'a fara. Kusan sha biyu sai ga su Aneesa sun iso daga Kaduna. Sosai Maanal tayi farin ciki, dan ba wasu ƙawaye tare da ita sai jikokin Nene da suma sai yau suka iso daga Kaduna ɗin. Isowarsu babu jimawa Najma da Maimoon, Batool, Lailah suka zo, suma sunce gara su dawo nan kusa da amarya cikin ƙawaye. Tare suke da akwatin kayan da zatai amfani da su. Kuma Uncle RK da AA ne suka saukesu. Sai da Maanal taji ranta ya sosu ganin AA koma ya nemeta, ba komai zata rama. Kamar wasa sai ga su Amraah suma sun iso, ashe Daddy ne ya tarkatosu kaf yace dole suzo ayi bikin da su. Ba ƙaramin girgiza sukatan su Nasiba yayi da ganin gidan Shahidah ba, dan ba taɓa zuwa sukayi ba har Amaal ma dake a cikin Kaduna basu taɓa zuwa gidanta ba. Su Shahidah kam tarba sukai musu ta mutuntawa, dan ko'a fuska basu nuna musu komai ba. Lokacin da suka iso ma har an fara shirya amarya, kowa kuma nata ƙoƙarin shiryawa sai kawai suma suka shiga ayari........✍️ To lokacin shoshalewa yayi, kowa sai ya tsuke ƙugu dan dole ne muyi rawar a ƙame ƙam🥱🤣🤣🤣🏃 *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖6️⃣3️⃣ ______________ .......Gaba ɗaya AA mamakin ganin sabon bikin da suka shirya yake yi, dan Oum kanta da su Hajiya Majdiya ko lokacin kansu basu da. Shima sai abun ya fara sakashi nishaɗi da jin karsashin ango fa yake sabo fil-fil a leda, dama a wancan karon bai gayyaci kowa ba saboda bai kawo Bestyn tasa ce zata zama matarsa tasa ba, shiyyasa ya sallama komai babu wani shiri da yayi.. Al'amarin Oum ɗin tashi da ƴan uwansa bai gama girmar kansa ba sai da Fawzan ya kaisa masaukin da suka tanadarma abokan nashi, yaje ya sameshi harma da wanda baiyi zaton gani ba. Aifa nan suka tasashi gaba da mitar rashin sanar musu auren nasa, dan sai da suka iso suke jin ai an rigada an ɗaura sure tun kafin salla. Bashi da bakin bayani sai kawai ya bar Yaya Fawzan da musu sharhi... ________★ A can gidan Didi Shahidah kuwa wani shegen kwalliya mai natsuwa akema Maanal, komai dai-dai misali ba'a cika shi da shirme ba. Dan mai kwalliyar ƙwararriya ce tun daga Lagos Hajiya Shuwa ta ɗakkota dan komai daya shafi amarya itace keyi. Hatta kayan da Manaal zata saka duk shirin Hajiya Shuwa ne. Matar ta gogu da sanin takan duniya ne ƙwarai da gaske. Ƙarfe biyu da arba'in an gama shirya amarya Manaal cikin doguwar riga na lass daya tsaru da ɗinki matuƙa. Fitet rigace a ciki har ƙasa ta wani irin fidda ainahin surarta tamkar zane a takarda, sai akai wata a sama tamkar after dress sai dai itama da lass ɗin akayita ta sauka har tana jan ƙasa. Matuƙar zaunuwa ɗaurin kan Maanal ya zauna. Sarƙa ƴan kunne zuwa bangles kam ba'a magana. Dan dan ƙareriyar sarƙa ce da akama ma wani irin adon fararen stones ya rabba. Dole ka kalla wannan amaryar ka sake kallo dan takai zama abin kallon. To dama Maanal gidan gayu ce, balle yau ɗin ta dabance a gareta. Ita kanta sai take jin kamar ba ita ba. Lokacin da mai kwalliya da Hajiya Shuwa data iso suke fito da ita falo sumar zaune su Basira sukayi, su Zeezah kuwa suka shiga faɗin, “Woowww!!“ Suna miƙewa. Kafin kace mi hasken camara ya fara hasketa tako ina. Dai-dai nan motar ɗaukar Maanal ke isowa, dan yau ba ango ne zaizo ɗaukarta ba. Babban Yaya da kansa ne yazo ɗaukar ƙanwarsa, a tare dashi akwai Uncle Najeeb (ƙanen Abah da suke uwa ɗaya uba ɗaya kun dai gane wanda akai bikinsu da su AA). Sai da kowa ya gama fita suka shiga motocin dake can waje suna jiransu dan Babban Yaya ne kawai ya shigo ciki sannan Amaal da Hajiya Shuwa suka fita da Maanal. Babban Yaya dake murmushi ya ce, “ALLAH na gode maka, yau ga Lilly ta fito a amryar ta, amaryar ma ta Auta”. Dariya Amaal da Hajiya Shuwa sukayi, Uncle Najeeb ma ya murmusa dan shima dai gwanin tsare gida ne. Kan Maanal da idonta ya cika da hawaye a ƙasa ta rissina ta gaishesu. Kafin Amaal ta sanyata a motar. Amaal ce kawai ta zauna tare da ita, Hajiya Shuwa motarta ta shiga sai ta ɗauka su Nene. Masha ALLAH waje kam ya haɗu, dan ko makaho ya laluma yasan an gyara wajen. Ga ƙaton symbol da ke rubuce da sunan AA dana Maanal ɗin, yayi ko masifar ƙyau duk da babu hoto a jiki dan Alaj AA ya hana. Abinka da manya komai yana tafiya cikin natsuwa da tsari, dan sai da mutane duk suka shiga sannan Oum ta fito ita da Hajiya Majdiya cikin kwalliya domin shiga da amarya. Ango dai ba yanzu ba kamar yanda aka tsara. Wani irin rungume Maanal Oum tayi, jitake kamar yau ne aka ɗakkota daga KD aka kawo musu. Ga madarar ƙyau da Maanal ɗin tai mata. Hajiya Majdiya dake murmushi ta shiga haska musu camara. Kafin itama ta rungume Maanal ɗin. Ashe daga wajen hall ɗin wasan yara ne. Sai ka shiga daga ciki zaka tabbatar da eh an shirya bikin ƴar gata. Mata ne zalla a cikin hall ɗin, ƴammata da manyan iyaye da sukafi kowa yawa. Yara ma ɗai-ɗai ne a wajen. Tunda mc ya fara zubama amarya kirari hall ɗin yay tsitt, kowa ya zubama ƙofa ido musamman ta ɓangaren Darma Family da dangin Mamy, dan daga ƙarshe dai sun ajiye komai a gefe acewarsu sai an gama biki suma sun shigo tawagar dan suna son komai ayi akan idonsu ta yanda idan na Nuratun ya tashi ba'ayiba su sami nayi ƙorafi. Hajiya Majdiya ce ta fara shigowa, bayan kusan minti ɗaya ƙofar ta sake zuge kanta Oum da Maanal suka bayyana. Oum na riƙe da hannun Maanal ɗin. Tuni hall ɗin ya ɗauka ƙananun ƙunƙuni na ambaton Masha ALLAH dan harga ALLAH ko maƙiyi yasan Manaal tayi ƙyau sosai. Mamy kam da ƴan uwanta babu wanda bai ji abu ya sokar masa ƙahon zuciya ba. Oum ta zaunar da Maanal a kujerar da aka tanada domin ita, ta ɗan gyagygyara mata rigarta kafin tai shirin barin wajen. Hannunta Maanal ta riƙo cike da shagwaɓa, Oum ta juyo tana kallonta. Sai kuma ta dawo ta riƙe hannunta cike da kulawa tace, “Miya faru?”. Idon Maanal cike da hawaye ta ce, “Oum dan ALLAH ki zauna tare da ni anan, ko Didi ta dawo, bana son kowa na kallona”. Murmushi Oum tayi sosai, tare da kai hannu ta ɗaukema Manaal ɗin ƴan hawayen da suka taru mata a gefen ido. “Yau ranar farin ciki ce Baby na ba ranar kuka ba, ki yi haƙuri yanzu Auta zai iso shima bake kaɗai zaki zauna ba ai. Kin taɓa ganin amarya ta zauna da mamanta ai sai a mana dariya ace ango yaƙi zuwa”. Yanda Oum ɗin ta faɗa sai ya bama Maanal dariya. Murmushi ta saki mai sanyi daya wani mata ƙyau. Oum ma sai ta murmusa tana tashi. Sosai Maanal ke jin idanu sun mata yawa, sam bata ƙaunar kallo, takurata yake yi. Tana ɗan bin mutane da kallo ƙasa-ƙasa itama ta hango wani kallon tsana da Mamy ke mata ita da danginta. Sai kawai yanayin nasu ya bata ƙarfin gwiwa taji wata dakewa ta musamman ta risketa. Aiko sai ta ƙara dakewa ta ƙawata fiskarta da murmushin da ya tsaya musu kuwa a ƙahon zuciya. An fara buɗe taro da addu'a, sai ɗan abinda ba'a rasa ba aka sanar da isowar tawagar ƴan discussion house. Hauwa'u Jidda, Ummul-Adnan. Ummu Fharuk. Oum Zarah. Maman afrah. Hafsy gayu (Mmn Ajmaal) (ر قية موس). Daddy's girl (Aysha). Hafsy Gayu. Leila. Mrs lawal. Mrs Bash. Fiddausi sani. Aunty Saliha. Aunty maryam. Maman faruk. Saraunia. Sharifa Ahmed. Maman meema .Oum shuraim. Mrs Affan. Maman Fa'izz. Meeno. Oummu nawal. Zubaida chiroma. Oum zarah & muhd. Fattu. Maman Hameeda, Aminatu, INDOBATIK NG. (Kai kuna da yawa, amma dole a dinner na antayo sauran😄👍🤏.) Ohhh ohhh zokaga mutanen nawa yanda suke shigowa cikin nutsuwa da ƙasaita, ƙyau iya ƙyau wanka iya wanka. Su ɗin na musamman ne, dan haka wajen zamansu ma ya kasance na musamman dan dama an tanada musu shi. Kamar jira suna gama zama ango ma ya iso da tawagar abokansa. Tuni kallo ya sake komawa sama wai shaho ya ɗau giya. Uhhhm uhhmm inji mai ciwon haƙori, kunga angonku kuwa, nace kunga ango AA Darma kuwa? Ya subahannallah, tabbas ranar aure daban take ga kowanne mata da miji. A yanda tsarin yake amarya ce zata je da kanta ta taro ango. Dan haka AA da tawagarsa suka tsaya a waje, Shahidah ce ta kama hannun Maanal suka iso har wajen ƙofa, sai da aka tsayar da Maanal MC ta gyara mata zaman rigarta sannan akace da ango bismillah ya shigo. Fin minti ɗaya bashi da niyyar motsawa, sai da RK ya tsungunesa. Hararrasa yayi kaɗan, kafin ya motsa a nutse ya shigo cikin hall ɗin. Wani irin shaaaaaah zuciyarsa tayi sakamakon saukar mayan oily fararen idanunsa masu kamar an watsa madara akan Maanal dake tsaye kanta a ƙasa. Tuni wani kirari da mc ta jeroma AA ɗin ya saka Maanal ɗaga idanunta slowly ta sauke a kansa itama, shima dai kallonta yake, zuciyarsa na ambaton sunan ALLAH maƙagi gagara misali daya mallaka masa wannan ƙyaƙyƙyawar halitta matsayin iyalinsa, lambunsa na hutawa. Mc ta kama hannun Maanal suka tafi a hankali har inda AA ke tsaye, wani irin lumshe idanu Maanal tayi, ta sake buɗewa a lokaci guda tare da motsa lips ɗinta kaɗan ta ce, “Barka da isowa mijin Maanal”. Shima cike da tasa ƙasaitar ya motsa nashi lips ɗin ya furta, “ALLAH yay miki albarka matar Ajwaad”. “Auuuwwwww!!”. Mc ta faɗa cike da salon iskanci daya saka hall ɗin ɗaukar hayaniyar ƙananun dariya. Mc ɗin kaɗai taji abinda suka faɗa, amma yanda tai ɗin sai mutane sukai tunanin wasu manyan magana ne daban. Cike da nutsuwa Maanal ta buɗe masa hannayenta kaɗan alamar yazo gareta ta rungume shi tana wani irin murmushi mai sanyi, AA da gaba ɗaya yaji yana narkewa ya shiga takowa a hankali garetan, yana gab da isowa ta wani juya masa baya da sauri tana sake ƙawata murmushinta, sai kuma tasa duka hannayenta ta rufe fuskarta. Miza'ai in ba dariya ba. AA ko ya wani kalar basarwa yana cije lips, batare da yace komai ba ya ƙaraso kusa da ita suka jera. Batare da ya riƙe ko hannunta ba suka shiga takawa a hankali har mazauninsu, sai lokacin ya taimaka mata ta zauna tare da gyara mata rigarta sannan shima ya zauna. Hannunta ya kamo a hankali cikin nasa ya rumtse. A tare suka saki ɓoyayyar ajiyar zuciya. Ƙasa-ƙasa ya ce, “I miss you my half. Irin wannan ƙyau haka ai sai kisa na hana bikin”. Maimakon ta bashi amsa sai tai murmushi kawai tana risinar da idannunta ƙasa. Dan wani annakirin kallo yake mata mai matuƙar ratsa ɓargon jiki. An cigaba da gudanar da abinda ya tara mutane. Matuƙar ƙawatarwa taron yayi, komai ya ƙayatar yanda ya kamata. Anci ansha amarya tasha kyaututtuka wajen iyaye su Umma matar babba Sardauna, su Mah-mah, su Gwaggo Khadijah, su Mom mahaifiyar Abah kenan. Mamy ma ta daure ta bayar😜 bisa shawarar babbar yayarsu. Sannan aka dawo kan ƴaƴa su Hajiya Majdiya, kai harda ƴammata da ƴaƴaye abin masha ALLAH. Daga ƙarshe Oum uwa maba da mama data saka nata sai da zukata suka girgiza. Gab da magrib taro ya tashi lafiya. Yanzu ma dai Babban Yaya da kansa ya maida Maanal, wannan tsari ya taimaki Maanal inji AA a zuciya, dan yanda yake jinsa ALLAH daga hall ɗin bikin zai iya wucewa da ita ya sauke matsalarsa, bai taɓa jin bazai iya jurewa ba irin yau, yanda Maanal tayi masifar ƙyau, ga wani irin ƙamshi mai marmasa gaɓɓai da ɓargon jiki. Ko a wannan zaman harga ALLAH girmama iyayensa dake cike da wajen da yayye ya sashi tsayawa a riƙe hannun kawai, shima a ɓoye yayi. Ya rabba! In ko haka wannan gyaran jiki yake to yata buɗe bakin aljihu kenan duk bayan sati biyu anama Maanal ɗinsa. Shi yasan Maanal kyakkyawa ce, sannan akwai tsafta da son gayu, amma a yau ta sake komawa wata ta musamman a cikin idanunsa. Ƙamshin da take kawai ji yake kamar zai suma. ALLAH ya dinga roƙo ya bashi ikon juriya yay kawaici. Dan yayi alƙawarin duk yanda suka tsara bikinsu shi mai biyayya ne..........✍️ A gurguje, zamuyi shagalin bikin kawai idan an kammala sai mu koma sauran ɓangarorin yanda abin zaifi tsari🏃🏃 *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖6️⃣4️⃣ ______________ .........Washe gari asabar ɗunbin al'umma suka shaida ɗaurin auren Fawzan Aliyu Abubakar Darma. Da amaryarsa Najma akan sadaki 1mil cass da AA ya biya. A lallai su Baba Sardauna sun girgiza zukata da yawa. Abune a bazata, bazata mai ban mamaki da wani bai taɓa hasasowa zai yiwu a family ɗin ba. Musamman ta yanda babu wata alaƙa makamanciyar haka a tsakanin Fawzan ɗin da Najma. Su Mamy na bedroom suna tattaunawa ana ƙara tausar Maman Saheeba da tun jiya take ƙananun magana da ita kanta Mamy ɗin kawai Saheeban ta faɗo musu kamar wadda aka jeho. A tare suka juyo suna kallonta. Babbar yayar su Mamy ta ce, “Haba Saheeba miyyasa baƙya sanin kin girma ne. Wane gudu kenan keda ke da ƙaramin ciki”. Cikin hakki Saheeba ta ce, “Gwaggo bazaki gane ba, kuna nan ciki baku san mike faruwa ba. Aure aka ɗaurama Yaya Fawzan”. A tare suka miƙe, Mamy ta ce, “Fawzan kuma? Wanne kenan? Ba dai nawa ba?”. “Tabbas shi kuwa Mamy, kuma da Najma”. “Wacece Najma?”. Mamy ta sake tambaya dan duk ta ma rikice. Kai tsaye Saheeba tace, “Ƴar Aunty Majdiya dake gidan nan mana”. Yuuu-yuuu Mamy ta dinga gani a cikin idannunta, lips ɗinta na rawa tama kasa fusta abinda take son fustawa. Babu zato sai gata a ƙasa wanwar ta baje..... Tofa Mamy ta baje a ƙar ku kawo ɗauki😮‍💨🏃🏃😌 _______★ A ɓangaren su Oum kuwa wani irin farin ciki ne mara misali zagaye da su. Dai dai Oum na share hawayen farin ciki, lokacin su Fawzan suka shigo shima idanunsa sun kaɗa sosai dan ana ambata ɗaurin auren da sunansa bai san hawaye sun zubo masa ba. Abu ne na bazata, bazata irin wadda ba'a taɓa masa ba a rayuwarsa. Dan koda AA yace zaima Abah magana a haɗa da bikinsa a waccan ranar bai wani ɗauki abin serious ba. Yau kuma Babban Yaya cayay masa wani ɗaurin aure zasuje na ƴar abokin Abah ya bashi kayan jikinsa yace ya saka, duk da yayi mamakin ganin ahalinsu da abokansa da yawa a wajen bai samu damar tambaya ba. Yana zuwa ya rungume Oum ya sakar mata kuka, ALLAH yaso ma daga ita sai shi da AA da RK sai Babban Yaya ne a ɗakin. Itama Oum hawayen take, a haka ta daure ta goge nata tas sannan ta ɗago Fawzan ɗin ta zaunar, shima goge masa nasa hawayen tayi tana murmushi. Albarka ta dinga saka musu, tare da addu'oi masu nauyi akan wannan aure. A haka Abah ya shigo ya samesu. Cike da tsokana ya ce, “Ja'iri, har yanzu kukan farin cikin bai ƙare ba kazo ka tasa uwaka kana cigaba da yi”. Dariya Oum tayi, su Babban Yaya na murmushi. Zama Abah shima yay, ya sanya musu albarka sosai dan shi kansa shi kaɗai yasan irin farin cikin da yake ciki a yau. A nutse yayma Oum bayanin ai Babban Yaya, RK, da AA ne suka shirya komai suka kuma roƙi alfarmar ɓoye zancen har sai an ɗaura. Tariya kuma sai nan da sati huɗu Najma ta kammala jarabawarta. Albarka itama Oum ta dinga saka musu. A falo ma dai da tsakar gida duk wani ahalin Darma yayi farin ciki da wannan aure. Hajiya Majdiya kanta sai da tai hawaye. Sai da su Mah-mah sukaita lallashinta dan harga ALLAH abin yazo mata a bazata kamar yanda ya zoma kowa ma.... ★Babu wanda zai ce ga halin da Nibras take ciki game da wannan aure, an daiga uwarta ta iso da wasu danginta sun shige sashen. Fawzan kam baima tuna da wata ita Nibras ba balle ya leƙata yasan yaya take... Sai dai abinda kowa bai sani ba koda Nibras ɗin taji wai an ɗaura auren Fawzan shiru kawai tai na ɗan lokaci, sai kuma ta ɗan taɓe baki batace komai ba dan hankalinta sam a nan ɗin yake ba duk da ƙirjinta sai da ta buga. Amma sai huɗubar da sheɗaniyar zuciyarta ke kissima mata tafi rinjaya a can. Sai da mamanta tazo ne su ransu a ɓace sannan ta sakar mata kuka da faɗin ita bazata zauna da Fawzan ba tunda ya ƙara aure miye-miye.... ________★ Su Maanal dake gidan Shahidah ma labari ya iske su, duk da Maanal tasan da shirin itama sosai taji farin ciki, aiko nan suka zagaye Najma. Kowa da abinda yake faɗa na farin ciki har sai da ta sanya musu kuka dan abin yazo mata a bazatar ne itama. Sai da Didi Shahidah ta ɗauketa a cikinsu ta maidata ɗakinta. Babu ɓata lokaci ta sanyata tai wanka, acewarta bashi yiwuwa amarya ta zauna a haka dole taci gayu duk da ba yanzu ne biki ba. Aiko sai ga kiran Oum ma ya shigowa Shahidah. Tace za'azo ɗaukar Najma ɗin yanzu. Su kuma shirya dan itama Maanal da wuri za'azo ɗaukarsu saboda ana son zuwa dinnar da wuri a tashi da wuri. Ana wucewa da Najma kuwa itama Maanal aka hau shiryata, dan zuwa lokacin la'asar tayi. Sai kawai ƴar shagwaɓar ta kama musu kuka. Dan wlhy jitake tamkar yanzu ne za'a fara kaita gidan su AA ɗin. Haka dai aka gama shiryata cikin atamfa datai matuƙar ƙyau ta kuma samu ɗinki na nutsuwa. Uncle Sadeeq, Daddy da ya zo ɗaurin auren Najma ya wuto nan, Uncle Ahmad mijin Amaal, sai su Nene sukai mata faɗa da nasiha mai matuƙar ratsa jiki da ɓargo. Daga ƙarshe suka sanya mata albarka da fatan alkairi a rayuwar aurenta. Ƙarfe biyar saura haɗaɗɗun motocin ɗaukar amarya daga manyan yaran Abuja suka iso ƙofar gidan Didi Shahidah. Ya subahannallah tsarin ya matuƙar haɗuwa, motar amarya a tsakkiya tasha flowers. Su Nusaiba dai ai tun jiya sun gama mutuwa a tsaye. Daga uhhm sai uhhm kawai kake ji a tsakaninsu. Haka suma rukunin ƙannen Huznah, abin duniya ya ishesu sai ƙiyastawa suke a ransu da yanzu fa Huznah ake ma wannan hidimar. A nutse Nene ta saka Maanal dake uban kuka a motar RK dan shine zai ɗauki amarya shi da Fawzan. Surukan Nene sai zabga guɗa suke, masu hotuna nayi masu videos nayi. Har motocin suka iso gidan Darma Maanal dake kwance jikin Nene na hawaye, dan yanzu kam tasan ba wasan yaran da akai a watannin baya bane zaman aure ɗan gaske aka kawowa yi a karo na biyu wannan gida. Har ciki motar amarya ta shiga, su Ummah tsoffi suka fito da kansu suka tarbi amarya. An fara kaita sashen Oum, Oum ta rungume abarta tana share hawayen farin ciki, Babynta ta dawo kusa da ita a karo na biyu matsayin matar ɗanta. ALLAH zai cika mata burinta. Bayan addu'oi aka fito da ita aka nufi sashen Mamy. Anan kam dai cike da bariki su Hajiya Turai suka tarbesu, sai dai Babu Mamy, dan tana can kwance a gado an saka mata ƙarin ruwa. Dan faɗuwar datai ɗazun sume musu tayi, shine Hajiya Turai ta kira wata ƙawarta Nurse tazo kamar ƴan zuwa biki, itace ta duba Mamyn ta tabbatar musu jinjinta yayi masifar hawa, dan haka bayan ta farfaɗo da ita tai mata allura mai ƙarfi aka saka mata drip kuma. Shine suke ɓoyewa dan basu son ko Abah yasan halin da ake ciki. Babu wanda ya tambayi rashin ganinta a wajen tunda ansan yanda takema Oum kara. Su sukai addu'oi duk da basu kai ciki ba. Daga nan aka dawo da Maanal sashenta. Bayan an sakata tayi alwala aka shiga da ita ciki bakinta da addu'a. Anan bedroom ɗin ƙasa suka ajiyeta bisa umarnin Nene... Gaba ɗaya yaran Hajiya Yaya dana Hajiya Basariyya sun gama sumewa a tsaye. Karo na farko na rayuwarsu suka fahimci ashe ubansu yaron masu arziƙi ne kawai, dan wlhy a dukiya irin ta wannan gidan da ginin kawai suka gani mahaifinsu ba komai bane. Dan wutsiyar raƙumi tai nesa da ƙasa. Saka motar 90m ba komai bace a lefe da sukai. Dole Huznah da Hajiya Basariyya ke haukacewa kambuuu... Basu ƙara raina kansu ba sai da aka fara shigowa da wasu irin haɗaɗɗun manyan bowl glass na abinci, yo in banda kasada irin ta mai kuɗi a ranar biki zaka fito da kayan gilashi matsayin kwanon bada abinci ga ƴan biki. Lemuka kam kala-kala ba'a maganar su coc.. fanta... Da ire-iren su ƴan biyu sha biyar, kai jama'a, ashe jiya da suke jinjina kwalliyar mutanen ƙaramin wasa ne, yau da take ranar dinnar zasu baza ido susha kallo ɗan gaske. Mamaki ya ishesu ta yanda su Ammie suka san waɗan nan mutane haka? Wai harma ace shi AA yama Maanal fyaɗe. Duk da ƴaƴan Ammie kaf ƙyawawa ne matan manya, amma yanda ƙasar nan ta koma ta bani gishiri in baka manda, auren ƙwarya tabi ƙwarya mai kuɗi ya aure ƴar talaka tsananin rabo ne wlhy, indai iskanci ne a sheƙe aya zasu yarda da ƴaƴan malam Shehu, amma a fagen raya sunnar MANZON ALLAH ba wannan maganar, in kikai wasa ma sai dai ki tsinta shagalin bikinsa na yawo a social media. Koki zama cikin ƴan aikin shirya bikin. Sai da kowa yaci ya ƙoshi dan kayan alatun da aka kawo musu duk ƙoshinka ka gani sai ka ci. Maanal ce kaɗai bata iya taci komai ba. Dan ita yau babban tashin hankalinta ace ita da AA zasu kwana. Addu'a take ALLAH yasa anan su Nene zasu kwana... Bayan sallar Magriba mai kwalliya ta iso tare da Hajiya Shuwa, atake ta saka Manaal tashi ta shiga sabon wanka da wasu irin haɗin turarurruka masu ƙamshin tashin hankali, data fito kuma aka saka wani a wuta aka lulluɓeta da ƙaton bargo ta ƙasa kuma ta zauna a kujerar tsuguno. Tafi mintina talatin aciki dan Hajiya Shuwa tana ɗagawa tana ƙara turaren ne a cikin rushin. Sallar isha'i da ake kira ta bata umarni tashi tayi, Maanal tai sallarta a tsanake sannan ta zauna mai kwalliya ta fara nata aikinta. Suma dai su Shahidah suna can suna nasu shirin dan Oum da kanta ta samesu, ta kuma tabbatar musu anan zasu kwana baza'a bar Maanal ita kaɗai ba karma suce zasuje gidan Shahidah jiyama tayi shiru ne kawai saboda Maanal zata kwana can Murmushi Nene tayi, tare da sake jinjina karamcin Oum. Hummm jama'a, nace kunga yanda ake zane muku fuskar amaryarku. Abin ba'a magana dan tayi mahaukacin ƙyau na'a tsaya aita kallo. Su kansu su Amaal sai hotuna suke zuba mata. Sosai tai ƙyau komai ya fita da fitarsa, sai ƙamshi take zabgawa kamar a kamfanin turare. Kora su Amaal waje Hajiya Shuwa ta sake yi, suka fara shirya Maanal ita da mai kwalliya da wadda tai ɗinkin Maaanal ɗin. Wato jama'a, Material ne aka samu akama wani shegen ɗinkin doguwar riga na tada kan maƙiyi, aka bisa da stones masu shegen walƙiya da ƙyalli ta yanda in aka kashe fitila suke wani bada kala. Idan baka da lura ma bazaka taɓa cewa Material bane saboda yanda aka tsara mata ɗinki. Gashi ya wani masifar bin jikin Maanal ɗin tamkar an zanata a takarda. Komai ya fita da tashi fitar. Cikakkiyar ƴar gatan amarya kenan. Hajiya Shuwa ta sake binta da ƙamshi bayan an zuba mata ɗauri dasu ƴan kunne da sarƙa. Ita kanta Maanal jinta take tamkar ba ita ba, kamar wata Maanal ɗin ce aka canja. Takalma kawai ta sanya Hajiya Shuwa tace suje a haka after dress a saka idan zasu shiga hall ɗin. Dan rigar tayi bala'in fidda komai na surar Maanal shiyyasa ma akai after dress da za'a ɗora saman su. Duk da itama after dress ɗin ba wani mai kauri bace ba, telar datai ɗinkin ce ta dinkata itama kuma an bita da adon Material ɗin ne kamar dai kayanta na jiya. Wato Hajiya tasan takan tsiya, ita tasan miyyasa tace Maanal ɗin ta fita a haka..........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖6️⃣5️⃣ ______________ ........Amaal ce ta kama Maanal ta fita da ita dan Oum ce tai kiranta a waya akan a fito da Maanal ɗin su AA har sun iso. Hakama mutane duk sun shiga motoci dan tafiyar gaba ɗaya ake son yi a jere a tsare kamar yanda aka tsara wajen dinner ɗin. A karo na farko Maanal taji zuciyarta na dukan tara-tara, tsakanin jiya da yau ɗin wani shakkar kasancewarta waje ɗaya da AA take yi, dan jiya wasu abubuwa masu nauyi ta dinga karanta a cikin ƙwayar idanunsa. Haka dai aka fito da ita babu yanda ta iya. Duk da kanta a ƙasa yake, an kuma rufa mata net har fuska hakan bai hanata jin idanun mutane a kanta ba, ga camaras na wayoyi da aketa binta da su, ji take kamar tai kuka. A dai-dai jikin falleliyar motar da RK ke tsaye ya juya musu baya da alama waya yake Amaal ta tsayar da ita. An riga da an buɗe musu dan haka ta taimaka ma Maanal ɗin da zuciyarta keta harbawa da sauri-sauri ta shiga. A hankali AA dake zaune a cikin motar yana binta da wani kallon ƙasan ido ya wani kalar lumshe idanun nasa daddaɗan ƙamshin turarenta na rige-rigen shige masa hanci. Itama dai nasa ƙamshin ne ya gama gauraye nata hancin tare da sanyin ac da motar ta ɗauka. Itama samun kanta tai da lumshe nata idanun nunfashinta na ɗan rawa. Sam bata yarda ta kallesa ba, har aka motsa da nufin tafiya, amma ta gaisheshi ƙasa-ƙasa, bataji ya amsa ba itama kuma bata sake magana ba. A bazata, matuƙar bazata taji shigar tattausan hannunsa da yay ɗan sanyi saboda acn da yake a ciki cikin nata hannun mai ɗumi da laushi, bata gama dawowa a hanyyacinta da riƙo hannun nata da yay ba taji saukar tausasa lips ɗinsa akan bayan hannun nata ya sumbata. Yanzu kam babu shiri dole ta ɗago ta kallesa, a cikin nasa dake mata narkakken kallo suka shige, sai ya sake shanyesu cike da ƙasaita ya motsa lips ɗinsa a raɗa ya furta, “You look great Mrs AA Darma, sai dai bazan taɓa iya barinki shiga a haka ba ina da matsanancin kishi kinfi kowa sanin hakan. Ke ɗin tawace ni kaɗai har a aljanna in sha ALLAHU”. Sosai furucin nasa taji ya daki zuciyarta da girman gaske, dan haka ta samu kanta da lumshe nata idanun tana ƙoƙarin janye hannunta dake a cikin nasa har yanzu dan wani yarrrr take jin tsigar jikinta na tashi saboda yanda yake murza shi a wani irin hankali. Lallausan murmushi ya saki a karo na farko, duk da iyakar laɓɓansa yay abinsa hakan bai hanata jin fitar ɗan sautinsa ba. Shi ko sai ya wani ja idannun luuuu kamar zai lumshe yana mai kauda kansa gefe kaɗan har lokacin fuskar tasa da ɗan murmushin. Ita dai hannunta ta janye daga cikin nasa, bai kuma hanata ba. Jikinsa cike da kasala ya koma jikin kujerar ya kwantar da bayansa tare da gyara zamansa. Daga haka bai sake magana ba har suka iso hall ɗin da akai matuƙar ƙawatawa, dan tun daga farkon shigowa street ɗin zai baka tabbacin ana wani babban taro na manya. Dan kuwa duk wani ɗan tara dake ji da kansa a cikin Abuja musamman ƴan siyasa da ma'aikatun gwamnati dama abokan kasuwa sun halarci wannan dinner, hatta da shugaban ƙasa ana saka ran zuwansa (saura wani yace Tinbunu nake nufi🙄 to Shugaban kasar Naya Ramadhan B. Hameed Taura😏). Cike da tsari da nagarta motocin suka kayantu a ƙofar hall ɗin, mutane suka fara fita a nutse suna shiga ciki, ango da amarya dai sai kowa ya gama shiga. Babu zato a karo na biyu Maanal taji AA na zame mata ɗan net ɗin da aka yana mata a kanta zuwa fuska, idannunta kawai ta lumshe zuciyarta na luguden daka, musamman saukar hannunsa a haɓarta dole ta sake matse idanun tsam. Babu zato ko tsammani taji saukar lips ɗinsa a saman nata lips ɗin. Ba gigicewa kawai ba jitai ita kanta motar da suke ciki kamar tana nutsewa a cikin ƙasa ne. Dole ta buɗe idannunta da sauri tana ƙoƙarin tureshi. Sai aka samu akasi hannun nata ya sauka a saman ƙirjinsa, ya kuma saka nashi ya riƙe ya hanata janyewar datai saurin son yi. Ɗayan kuma ya riƙe mata fuska ta yanda ta gagara janye lips ɗin nata. Sai da ya shanye lipstick ɗin da aka sanya mata yay mata masifar ƙyau kuma sannan ya janye nasa baya a hankali, sai dai har lokacin fuskokin nasu na'a gab-gab da juna kowa na busama ɗan uwansa numfashinsa. Ita dai idannunta dake cika da hawaye a rufe suke, wata irin kunyarsa take ji mai tsanani, ga tsoron yanda take ganin idanunsa a juye kuma a ƙanƙance alamar yana cikin wani yanayi mai girman gaske. Shi ko fuskar tata yake kallo kai kace yau ne ya fara ganinta, shi kaɗai yasan mi yake ji. Amma da yake gwani ne a kamewa ya fuske a binsa sam babu ko ɗigon zaƙuwar a kan fuskarsa da idanunsa a zahiri. Maimakon ma barin kunyar tata ta cigaba da tasiri a kofa zuciyar tasa sai yay yunƙurin ɓadda sawu ta hanyar kauda yanayin nasu gaba ɗaya. “Miyasa kika bari suka sanya miki bayan kin san bana son kina sakawa a duk sanda zaki fita?”. Ya faɗa da wata irin murya mai sanyi da zurfi ta yanda ita kaɗai ta iya jinsa. Dan koda ace da wani a kusa da su bazai ji abinda yace ɗin ba. Kauda fuska kawai Maanal tai ƙoƙarin yi gefe tana haɗiye hawayen dake neman zubowa daga idannunta na matsanancin haushi da firgici. Amma sai tayi jarumtar hanasu. Eh tabbas ta sani, dan sun sha yin faɗa a shekarun ma ƙuruciya idan ta saka janbaki idan zasu fita, yata takura mata kenan har sai ta goge, a wasu lokutan ma sai dai taji kawai yasa tissue ya kwashe mata shi da kansa, suyita faɗa dan ita harga ALLAH tana son jambaki, gata kuma dama ma'abociyar son kwalliya. Idan kuma ta saka shegen ƙyau yake mata musamman na yau ma dan ALLAH ya bata wasu kalar lips masu ƙyau da fitattacen shaf tamkar an zana mata shi. Gasu da zagayayyen baƙi kafin pink a tsakkiya, dan ko bata saka jan bakin ba sai kaga kamar ta saka ɗin ma a haka. Yanzun ma duk da ya shanye sai lips ɗin na nan da ƙyanzu kamar ma da lipstick ɗin har yanzu. Yanda ta kauda kai sai shima bai sake magana ba, sai ma ƙoƙarin warware after dress da Hajiya Shuwa ta bashi yayi tare da warware ta. Sosai rigar ke wani irin ƙamshi mai daɗin gaske. Kaɗan ya ɗaga daga zaunen da yake ya ɗan ranƙwafo kanta. A wannan gaɓar kam numfashinta neman ɗaukewa yay, dan kusancin nasu mai girman gaske ne ta yanda wanda ke a nesa dasu ma zai iya ɗauka rungumeta yayi. Shi ko ko'a jikinsa ya yafa rigar a jikinta sannan ya koma mazauninsa ya zauna. Dai-dai nan kuma aka basu damar fitowa. Shine ya fara sauka, sannan ya zagaya ta inda take ya buɗe murfin. Hannu kawai ya miƙa mata batare da yayi magana ba, ita kuma tai shiru taƙi motsi balle ma ta bashi hannun nata, hasalima kanta a ƙasa yake har yanzu. Hannun nata kawai ya kamo cikin nasa, dole ta ɗago sai dai babu alamar zata fito. Dan tana ma kallonsa tai saurin kauda idonta. Bakinsa ya ɗan taɓe tare da sake matsawa jikinta kaɗan, ta yanda ita kaɗai zata ji ya furta, “Goyo ki ke so ne?”. Batama bari ya kai ƙarshen zancen nasa ba ta yunƙuro domin fita, dama ta dakata ne saboda mararta data ƙulle taɗan saki, (Bafa ƙaramin gyara Hajiya Shuwa tama Maanal ba, sakamakon sanin Maanal ɗin ba cikakkiyar budurwa bace. Komai baice ba ya taimaka mata ta karasa sakkowar sannan ya gyara mata alƙyabbar yanda yake buƙata. Dan neman magana abokansa sai video suke musu kuwa. Dai-dai nan Oum ta ƙaraso, fuskarta cike da murmushin farin ciki ta haɗasu ta rungume hawaye na cika mata ido. Kafin ta ɗago su batare da tayi magana ba ta shiga tsakkiyarsu hannayensu a cikin nata su duka. Itace ta shiga da su har cikin hall ɗin abokan ango biye da su. Shigowarsu cikin hall ɗin hasken camaras duka ƙaru a kansu, sai Maanal taji daɗin after dress ɗin daya saka matan, dan daba dan yayi hakan ba gaskiya akwai damuwa, zata ji matuƙar takurar shigowa wajen da rigar jikin nata, ita kanta Oum taji nutsuwar ganin Maanal ɗin a haka, dan dama yanayin da taga rigar tayi mata a jiki sanda zata shiga mota ya tsaya mata a rai. Har inda aka tanada dominsu Oum ta kaisu, koda ta zaunar da su duk sai suka ƙi sakar mata hannaye. Musamman Maanal ma data riƙe da hannu biyu. Dariya ma suka bama Oum, da ƙyar ta danne ta saki murmushi kawai. Tare da ɗaura hannun AA a saman na Maanal ɗin ta rumtse sannan ta zame nata a hankali. Cike da tsokana da murmushi a fuskarta ta ce, “Banda faɗa, in ba haka ba asha bulalar Oum”. Murmushi sosai AA ya saki mai ƙayatarwa, haka itama Maanal ɗin ƙasa ta sake yi da kanta sosai. Ita dai Oum dake ƴar dariya ta bar musu wajen. Hannunta dake cikin nashi ya ɗan matsa ta yanda dole ta ɗago fuska a yamutse ta dubesa dan taji zafi. Shima kallon nata yake, dan haka ya ɗan ɗage mata gira irin na (kallon fa?) harararsa tayi kaɗan ta sake ɓata fuska tare da ƙoƙarin janye hannun nata amma yaƙi bata dama, sai ma sake damƙesa da yay da ƙyau. Duk abinda suke idanun mutane da yawa a kansu ne musamman ƴan ɗauka a waya, dan yanzu waya ta zamewa kowa jarabawa, ta bakin wani malami yace yanzu da wayarka kawai aka barka a yayin hisabi ka shiga uku, dan yanda muke ɗaukarta kawai abar muyi nishaɗi ko amfani mu ajiye abin ba haka bane ba, inma bamu sani ba mu sani, akwai hisabi tsakaninmu da abinda muka aikata da su waɗan nan dai wayoyin. Dan haka sai mu shirya, aikata alkairi ko sharri duk UBANGIJI na sane da motsin mu.........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖6️⃣6️⃣ ______________ ......Nibras da dole ta sakata zuwa wajen dinner ɗin dan tangazo ƙeyarta Fawzan yayi sai taji kawai hawaye na cika mata idanu, ita kaɗai tasan irin baƙin kishin Maanal da take ji a zuciyarta, ga maganar Najma ɗin nan, duk da bata zafafa ba sosai abun fa na damunta ta ƙasan rai. A kwanaki biyun nan ji take kamar ta ɗauka wuƙa ta kashe kowa daga ita sai AA su rayu a wannan duniyar. Tayi kuka har bata san adadin hawayen data zubar ba ma. Ita da Fawzan kam sam babu zaman lafiya tace sai ya saketa, shi kuma yace aurensu auren zobe ne ai ba saki ba yaji, sai ma ya tattarata ya watsar ya maida hankalinsa ga hidimar bikin kawai, gefe kuma ga Najma na girmama farin cikinsa, dan ma tana noƙewa wai tana jin kunya. Ba Nibras ke cikin irin wannan halin ba kawai, dan halin da Saheeba ke a ciki zamu iya cewama yafi na Nibras ɗin, dan abu goma da goma ne ita ya haɗe mata, sosai take taya ƴar uwarta kishi, gefe ga hassada da baƙin kishin nan na facalanci dake da tasiri a duniyar malam bahaushe. Na farko dai bama su dake kwana suna tashi da AA a gida ɗaya ba mutanen dake waje ma sun san AA yafi sauran ƴan uwansa arziƙi na dukiya duk da suma suna da gwargwadon nasu, yana da connection da manyan mutane a duniya ma ba Nigeria kawai ba a dalilin business ɗin nashi musamman na agogo. A gidan kaf kowa sonshi yake soyayya irin wadda bata ɓoyuwa, dan a zahirance da baɗini AA ɗan gata ne a wajen iyayensa da ƴan uwansa, kusan shine ZUCIYAR zuri'ar Aliyu Darma. Bazaka fahimci hakan ba sai wani abu ya taɓa rayuwarsa ko mai ƙanƙantarsa zakaga illahirin hankalinsu ya koma kacokan garesa ne. Yan uwansa sun fisa hasken fata, amma shi kuma ya fisu ƙyau ta yanda ko baka san ƙyau ba sai ka iya banbancewa. Shiyyasa tun farko takema ƴar uwarta fatan samunsa. A wani gefen kuma tana taya Mamy faɗa ne da kishin Oum da faɗa akan su AA. Ga ita kanta shegiyar Maanal ɗin wata irin ƙauna Darma Family ɗin ke mata bama iya su zuri'ar Aba kawai ba dan son AA ɗin ya shafeta ga kowa. Koda yake sun san aikin asirine wannan, lokaci suka bata komai sai ya rushe ta zama mujiya a dangin dan ubanta. Bari dai a gama bikin za'asha kallo dan sabon wasa ne zai tashi a gidan Aliyu Darma kamar yanda suka shirya... Mamy kam ji take kamar zuciyarta zata baro ƙirjinta ta fito ne kawai. Taso ƙin zuwa wajen dinner ɗin, Maman Saheeba ta tunzurata akan gara suzo ayi komai akan idonsu ai kamar jiya dan su san ta hanyar da zasu yaƙi Oum. Wannan dalilin ne ya sata zuwan duk da bata da lafiya ƙarfin haline kawai, yanzu haka kamar kanta zai fashe dan ciwo... Yau ma dai ƴan discussion house cike suke da wannan waje cikin kwalliya ta ƙasaita da aji da halin girma. Can na hango muku su Aisha yuguda. Asiya salihu. Fauzarh collection. Hafsat adam651. Maman khairy2003. Lubabatu miss. Maryam Muhammad. Zuwaira muktar limanci. Shafa'atu limanci. Sadiya Ibrahim merariya. Maman meema. Deryer012 Mrs Suraj. Bilqeesu. Oum moh'd. Sa'adatu ibrahim mua'zu . ام الصديق. Ummu aslan&asala. Fateema Umar.. kai sunada yawa fa masha ALLAH, dan hada ZAFAFANKU ba'a barsu a baya ba... Babban Yaya ne yay addu'a mai tsayi ga ma'auratan, Fawzan ya bada kaɗan daga tarihin ango da nasarorin daya samu a rayuwa. Ya kuma bada na amarya dan yace itama ƙanwarsu ce. Ya kuma ɗora da taƙaitaccen tarihin rayuwar ƙuruciya ga waɗan nan ma'aurata daya taɓa zukatan jama'ar wajen matuƙa musamman wanda basu san da hakan ba irinsu CFO, su Zaharadeen, su Yaƙub kai kaf ma ma'aikatan MAAWAD COMPANY jikinsu yay sanyi, CFO ta gama mutuwar zaune harda hawaye dan ta fahimci a lallai AA na Maanal ne. Yayinda ake nuna hotunansu a ƙaton magijin dake bango guda. Wani hoton dole mutane ke dariya, dan su kansu basu ma san an ɗaukesu ba a wasu wajajen, kuma ba kowa bane da wannan aikin sai Fawzan a wancan lokacin, dan yayi jarabar ɗauke-ɗauken hotuna da camara ɗinsa kasancewarsa mai son hakan shima, aka ce shi Salim ɗin Uncle Mahmud ya gado, shiyyasa wasu hotunan su kansu su AA ɗin basu san da zamansu ba sai yanzu. Maanal sai faman ɓoye fuska take dan AA sai tsokanar ta yake. Komai ya ƙayatar da mutane kamar yanda Fawzan yay fata, dan haka aka shiga tsakkiyar shagali cike da shauƙi. Komai ya tafi a nutse a kuma ilmance, babu wani rawar kai ko aikata abinda ya zarce Shari'a, hasalima ango da Amarya basu tashi daga wajen zamansu ba ko sau ɗaya balle yin rawa. Duk wanda zai musu liƙi anan wajen zamansu yake samunsu yayi. Aiko doller tayi kuka na gaske, dan abokan AA da manyan mutane sun nuna masa shi ɗin fa shine, yayinda matar shugaban ƙasa Raudha Ramadhan Taura ta danƙarama amarya ƙyauta ta musamman. Mawaƙa sun zuba capacity iya iyawa musamman Halifa sk ɗorayi daya maimaita mana waƙar bazani daina kuka ba, suma sauran mawaƙa irinsu Ado gwanja, Umar m Sharif, breaker, Sarkin waƙa, sun zubar mana galan-galan munsha rawa. Hotuna ba'a magana. Video kam tuni sun karaɗe media kamar ba gobe. Kafin kace mi wannan dinner ta zama on top a wannan dare. Al'amarin sai ya zama abin mamaki da tattaunawa musamman da ba kowa yasan da ɗaurin auren ba dinner ɗin ce kawai tayi girgizar bazata. Abinka da manya na waje ba'a wani daɗe ba aka tashi, dan shaɗaya da rabi da yawan mutane ma sun kama hanyar gidajensu. Su Oum ne ƙarshen baro wajen, yanzu kam Fawzan ne ya ja motar da suke ciki, dan haka Najma ta kasance a kusa da shi dan Nibras tuni ta koma gida wai kanta ke ciwo, su Mamy ma ba'a tashi da su ba. Ita Hajiya Majdiya ma sai al'amarin yaso fara bata dariya. Dan zuwa yau ta sake yarda lallai akwai abinda ya kamata su sani game da Mamy. Shin wannan aurerrakin take ma ƙiyayyar, ko kuwa bayan shi akwai wani abu a ƙasa daya kamata ace sun sani?. Najma ce ta taimaka ma Maanal suka shige, dan kan Maanal ɗin ciwo yake mata sosai jikinta kansa ya ɗauki zafi, dauriya kawai take yi koshi AA ɗin taƙi yarda ya fahimta. Dan tunda ta samu ya sakar mata hannu bata sake yarda sun haɗa jiki ba har aka tashi. Shima fahimtar a takure take ya sashi bata space ɗin da take buƙata, a gefe kuma akwai nauyi da kunyar su Oum dake a wajen. Ko yanzu Fawzan nata masa shaƙiyancin wai ko ƴar rungumar sai da safe baima Lillyn ba amma yaƙi kulashi. Dan shi bama wannan ba, gargaɗin da Mamy ke masa da idanu da mugun kallon da yaga sunama Oum ita da yayarta ne ya tsaya masa a zuciya. Dan tuni hankalinsa yabar kan dinner ɗin ma ya koma ga Oum kaco kan da da su Mamyn. Dan shi fa ya yarda komi Mamyn zatai tayi masa amma karta taɓa masa Oum ɗinsa, sam bashi da jarumta ko ƙarfin zuciya akan a cutar Oum ko Manaal, shi mai rauni ne akan soyayyarsu..... ★Gajiya sosai ta saka kowa neman makwanci domin hutawa. Alhamdullah Mannal tayi farin cikin ganin ƴan uwanta na tare da ita anan zasu kwana dan Oum ta hana kowa komawa gidan Shahidah, tace tunda amarya tazo gida anan ake biki anan zasu zauna har a kammala kodan a ɗebema Maanal ɗin kewa, ta kuma ji a ranta itama amaryace da aka kawo yau gidan miji ce kamar kowace amarya. Anan ɗakin da aka ajiyeta take tare da su Amaal dan suna so suyi magana da ita, duk da Nene ta shigo tace su maidata sama ɗakin mijinta itako ta sanya mata kuka da roƙon ita dai a barta anan dan ALLAH, dariya su Shahidah suka dinga mata, yayinda Nene ta saki baki tana kallonta. “Amma fisabillahi Maanal kada yaron nan yaga rashin hankalinmu, tunda aka kawo ki ance kina sashen Hajiya Fateema Alhaji yay masa ƙarfa-karfa ya riƙeki kin zaune a sashenta, yau kuma ace an kawoki inda yake mu mun riƙeki bayan yayi kawaici iya kawaici”. Baki sosai Maanal ta sake turawa gaba tana hawaye. Sai Shahidah da tausayin Maanal ɗin ya cikama zuciya ta ce, “Nene ayi haƙurin, shima ai yasan kamawa tayi tunda Oum ta maida bikin sabo fil. Ba yau bane kawai sai gobe. Shina kuma bana ma zaton yana a gidan nan dan ban gansa ba tunda muka dawo. Maybe ma bazai kwana a gidan ba tunda yasan da baƙi”. “To ai shike nan tunda kun zama yayun banza kuma”. Nene ta faɗa tana miƙama Maanal abu a kofi, koda ta tsaya kallon kofin sai Nene tai mata daƙuwa, dole ta amsa ta shanye abinda ke cikin. Amsar kofin Nene tai ta fice ta barsu suka cigaba da hirarsu. Ita dai Maanal ma kwanciya tayi abinta dan itafa komai yimata yake kamar a mafarki musamman yanzu da aka maidota wannan sashen wai da sunan sashenta da zata rayu matsayin matar aure, auren ma na Ajwaad Bestyn ta... Wajen ƙarfe ɗaya gidan ya ƙara zama shiru mafi yawa anyi barci dan an gaji. Hakan ya bama AA damar shigowa ya haye sama ya kwanta shima. Nene data gansa dan ta fito zata ɗauki abu data ajiye anan falo tai saurin komawa da baya. Sai da ya gama hayewa ta fito tai abinda zatai. Maimakon ta koma ɗakin da zata kwana sai ta nufi na Maanal, ganin har sun kwanta bai hanata ƙoƙarin tada Maanal ɗin ba ta hanyar kiran sunanta. Maimakon ita ta farka sai Amaal ce ta farka, barci cike da idonta ta ce, “Nene Lafiya dai ko?”. “Lafiya Lau koma barcin ki. Maanal nake son ta tashi ta wuce ga mijinta can dai a gida zai kwana, ɗazu nayi magana kum kakkare cewar ba'a gida zai kwana ba tunda yasan nan zamu kwana. Ni na taɓa ganin irin wannan ƙarfa-karfa yaro a hanashi matarsa tsawon wata biyu kamar aure fulani”. Amaal da abin yaso bata dariya ta danne da ƙyar tana tashi zaune. “Kai Nene wai kamar auren fulani. Nene a barta dan ALLAH, ba yau bane kawai dai, gobe iyanzu in sha ALLAHU mun bar musu gidan ai. Shima nasan bazai ce anyi ba daidai ba. Kuma bama tada lafiya sai da tasha magani ta kwanta taɓa jikinta kiji”. Rasa abin cewa Nene tayi ita kam. Dan ta kula wannan yayun na Maanal sai a hankali, sam basa ganewa. A taƙaice ta ce, “Shike nan sai da dafe” ta juya ta fice. Cikin raɗa Aunty Sakina data farka itama ta ce, “Da alama dai Nene ta ƙagara ango ya angwance, irin wannan damuwa haka”. Dariya Amaal tayi kaɗan, tare da faɗin, “Bata san tana sake firgita ɗiyar tata bane, dan gaba ɗaya auta a tsorace take tun ɗazun wlhy.” Murya a sanyaye Shahidah ta ce, “Nima tausayi take bani ALLAH. Ita da ba wani jikin azo a gani ba tana tafiya kamar zata ɓalle, sauƙin ma Ajwaad ɗin azumi ya ɗan sakashi raguwa, amma ya mata yawa ni dai nake ga mutum a murɗe haba jama'a”. Ta ƙare maganar a sanyaye kamar zatai kuka. Dariya sosai Aunty Sakina keyi, ta ce, “Yayun ƙarshen zamani kenan, dama namiji nama mace yawa ne? Kuna nan zata baku kunya nan da wata tara mu dawo suna. Balle ma Maanal mace ce, koda take da rashin ƙiba ai tana da jikin cikakkun mata. Ga gaba ga baya ko'ina Alhamdullah. Amma fin wata biyu an hana bawan ALLAH matarsa kai jama'a a tausaya masa mana ga uban gyara tasha”. Dariyar shaƙiyanci suka sanya, duk da da gaske har cikin ƙasan rai tausayin Autar tasu suke ji. Duk abinda suke faɗa Maanal na jinsu, dan itama tun shigowar Nene ta farka. Gaba ɗaya sai taji tsoron na ƙara tasiri a ranta. Dan da gaske gaba ɗaya a firgicen take, yau har addu'a tayi ALLAH yasa jininta yazo, amma bawan ALLAHn nan shiru kake ji. Sai kawai taji hawaye na ciko mata idanu, musamman data tuna abinda ya dinga faruwa a tsakaninsu a watanni biyun nan, musamman a Chaina daya kusa samunta har karo biyu ALLAH dai ya ƙwaceta da ƙyar. Gashi idonta ya rufe da soyayya har tana wani ɗaukar masa alƙawuran randa aka kawota zatai miye-miye ko ubanwa ya aiketa..........✍️ 🤣🤣😂😆Kya dai gayama ƴan Giro Manaaluwa😛 *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖6️⃣7️⃣ ______________ ........WASHE GARI kamar waɗanda ke akan ƙaya Nene ta azalzalesu suka fara shirin gyara gidan. Duk abubuwan dake a kwalaye aka ciresu, tun daga bedrooms na sama banda ɗakin AA saboda girmamawa, sunce in ma akwai abinda yake buƙata idan sun tafi ita da shi sa sanya a ciki. Amma bedrooms biyu nata da wanda ke matsayin na yara duk an gyara su, an shirya mata kayanta a closet, falon sama ɗin ma komai an saka har labuloli, aka goge ko ina aka saka ƙamshi. Ƙasa ma sun sake gyarawa, akama canja zaman kujerun gaba ɗaya sannan suka shiga kitchen, kayan da bazata buƙata a kusa ba aka danƙare su a store, sannan aka sake shara tsaf anan ma aka baza ƙamshi. Koda aka kawo musu break fast ma sun gama gyaran ko'ina. Suna gama ci aka shigo da kayan lefen Maanal da AA ya haɗa mata, mamaki ya kama kowa, ganin anfa kai lefe a wancan karon, amma sai Hajiya Majdiya ta tabbatar musu ango yace wannan nasa ne. Haukacewa ƴaƴan su Hajiya Yaya suka sake yi dan mamaki da ruɗani. Musamman da aka fara buɗe akwatina ana fiddo fitinannun kaya naban mamaki designers na manyan matan masu kuɗi ƴan gata. Ya subahannallah kowa sai ya rasa baki magana. A take Shahidah ta bada tukuyci ita da Amal, wannan tukuyci ya sake girgiza su Nasiba. Maanal ɗin kanta sai da lefen ya girgizata, dan tabbas ya ɗan tambayeta wasu abubuwa a Chaina, musamman colours haka da sauransu, amma bata ma kawo ma ranta mi zaiyi da shi ba. Haka aka gama murna da kallon kaya aka sanya albarka aka kumayi videos Dan nunama Ammie da Daddy. Maanal dai tun jiya bata sake saka ango a idonta ba har zuwa yanzu da za'a fara shirin walima, bata damu da rashin ganin nasa ba, ba kuma ta tambayi kowa ba. Ita gaba ɗaya ma kasancewar ƴan uwanta a tare da ita ya sakamata farin ciki da mantar da ita komai. A haka lokacin walima yayi, Hajiya Shuwa da mai kwalliya suka shigo, duk da dai yau ma Hajiya Shuwa tace bamai yawa za'ai mata ba. Amma kafin ayin ma tasha turare harda na tsiya, kai Hajiya Shuwa tasan sirrin ƙamshi na kata'i, tsaf aka kwalliyeta aka sakata ta shirya cikin Abaya mai ƙyau fara tas da adon golden. Matuƙar ƙyau Maanal tayi kam kamar ka saceta ka gudu. Ga wani ƙamshi mai azabar daɗi tana bulalawa. Anan harabar gidan aka shirya walimar, dan tabbas gidan su AA babbane matuƙa ta yanda basa jin ko ɗar idan sabga ta tashi. Idan ba irin su dinner ba da wahala kaga sun kama hall ɗa sunan yin wani event a yayin sabgar su. Sosai walima ta ƙayatar dan iya mata ne kawai, sai malamai da aka gayyata suka zuba lectures masu ratsa jiki da saka nutsuwa musamman akan ma'aurata da shi kansa ma zaman auren da daɗin dake cikinsa da ƙalubale. (Please muɗan yi magana anan mana. Akwai wani abu dake cin raina a duk sanda naci karo da shi a social media. Idan budurwa na nuna ɗokinta da farin ciki a ranar aurenta ko lokacin shagalin biki sai kaga ana faman zaginta ko tsoratar da ita akan al'amarin maza ko auren ma gaba ɗaya a comment section. Hummm jama'a mu fuskanci wani abu fa, ita rayuwa akwai jarabawa da ƙalubale a cikinta, sannan ba lallai abinda kai aka jarabceka da shi a jarabci wani ba. Ba lallai dan ke baƙya jin daɗin rayuwar aurenki kice kowa ma haka take ba ko haka zata faru ga wasu ba. Zata iya yiwuwa ita jarabawarta ba'a rayuwar mijin bane ko halayyar mijinta. Wallahil azim yanda muka san mata da yawa nashan wahalar rayuwar aure da rashin ƴanci a gidan aure to akwai mata da yawa kuma dake jin daɗin aure da farin ciki a cikinsa. Akwai matan da dayawa suke samun soyayya da kulawa ga mazajensu fiye da rayuwar novels. Dan ALLAH mubar karya zukatan yaranmu da ƙannenmu masu tasowa akan abinda UBANGIJI ne kawai mai ilimin saninsa. Mu dinga ƙarfafasu da hakan, koda bata samu yanda take hangeba zuciyarta zata wadatu da abinda taje ta samu, dan shi dama ɗan adam ai ba komai yake samu hundred percent a rayuwarsa ba. Dole idan aka baka farin ciki anan a jarabceka anan kuma. Yanda muka san akwai maza marasa adalci ga mata haka ma akwai adalai masu tausayi da nuna kulawa ga iyalansu da yawa a cikinmu. Akwai kuma hatsabiban matan da suke wahalar da mazan su kuma amma mazajen nasu na haƙuri da su. Dan haka yake ƴar uwa, kada ki wani bari zuciyarki ta raunana kota karaya da tunanin ko hangen gidan miji KURKUKUN AZABA ce, dage kiyi addu'a ki miƙama UBANGIJI lamarinki da zaɓinki ki tsarkake zuciyarki, ki yarda ALLAH mai rahama ne mai jin ƙai, kiyi addu'ar samuwar miji na gari mai addini, mai kamala, mai neman na kansa, wanda ya iya ƙyaƙyƙyawar mu'amula da mutane, mai tausayin iyayensa da ƴan uwansa wlhy in sha ALLAHU, ALLAH zai baki fiye ma da wanda kika roƙa ɗin in har kema kin kasance tsarkakkakiya, kin wadata zuciyarki da tsoron ALLAH, baki kusanci ZINA ba, kin nisanci MAƊIGO, kin nisanci shaye-shaye, kin nisanci ƙawayen banza da samarin banza ƴan aci duniya a titi. Kin ƙyautatama iyayenki kullum kina zagaye da addu'arsu, kin ƙyautata mu'amularki da kowa, kin cirema kanki hassada da gulma da aibanta wasu ko rayuwar wasu da danne hakkin mutane komai ƙanƙantarsa. Ajiye batun ƙyale-ƙyalen matan media duk buge ne wlhy, mafi yawansu hodace da zanen jagira dana jambaki sai filter da ƙaryar an tara amma komai fanko ne da haɗa-haɗe, mafi yawansu ƴan koda rigima da zubda mutunci ne sai na ɗinka na saka na saya na saka dan na burge mabiyana a media. Wata idan kika ganta a zahirinta da asalin rayuwarta da sanin wacece ita wlhy har gaban abada bazaki sake marmarin zama irinta ba in har kina jin tsoron ALLAH. Dan haka ki rufama kanki asiri, ki gargaɗi zuciyarki daga barin wannan ƙyale-ƙyalen banza da wofin dan ita MEDIA GIDAN KASHE AHU CE, sannan ALALAN GERO CE. Ki dinga tunawa ba farkon ba ƙarshen, da yawa sunyi tashen a mediar da fariyya da alfahari da ƙaryar amma tarihinsu ya shafe ko labarinsu baka sake ji, kuma suna a cikin duniyar ba mutuwa sukai ba, kawai dai an ƙyanƙyaso waɗan da suka fisu iyawa ne dan kowa fanɗarewar wani babban wani ne, wani ma sai dai a kira shi kakan wasu. To kwantar da hankalinki ki ɗaurama dokin rayuwarki sirdi da linzamin banbance abinda ya dace da ruɗanin duniya mara amfani ki rungumi mijinki ki godema UBANGIJI ki ɗaya baki shi, ki wadatu da ni'imar da ALLAH yay miki ta kasancewa a ƙarƙashin bautarsa dan aure dai ibada ce, sai ki zauna lafiya kiyi barci mai daɗin gaske, ana hayya-hayya, ke kina salama-salama saboda UBANGIJI ya tsaya miki. Mu dinga yawaita addu'ar samun zaman lafiya da soyayyar mazajenmu da rage zafin kishi, mu kama sana'a, mu rage buri, mu rage zalunci, wlhy zamu kasance masu nasarori bama nasara ɗaya ba. Karki sake wata banza ta canja miki tarbiyyar uwa da uba akan abinda maybe ita sai da ta saɓama ALLAH ta samu. Ɗaukesu ƴan a kalla ai dariya da mamaki a wuce kawai ba ƴan a ɗauki darasi ba ko yin koyi dan ke dasu tamkar nisan samaniya da ƙasa ne a daraja wlhy. Kina da ƴaƴa, in baki haifa ba ma zasu zo da ikon ALLAH, idan auren ne bakiyi ba zakiyi mijin aurenki duk nisanku sai ya isko ki kada kiyi tunanin sai kin ɗau waccan hanyar zaki sameshi shi mutunci madara ne idan ya zube ƙasa baya kwasuwa. ALLAH ya baku mazaje na ƙwarai, ya haɗamu baki ɗaya ya bamu farin ciki a gidajen aurenmu. Masu fuskantar jarabawa UBANGIJI ya sassauta ya samar da farin ciki da kwanciyar hankali a rayuwar aurenku da mu baki ɗaya. Mu dage da addu'a ƴan uwa, mu cirema zukatanmu son mallakar maza ta kowane hali, mu tashi mu nema sana'a, mu tsarkake zukatanmu mu yawaita istigafari, mu gyara ibadarmu da mu'amularmu da mutane. Dan wlhy a wasu lokutan sharrin da kake aikatawa ga mutanen dake a zagaye da kai ta fuskar rayuwa ko rayuwar social media ɗin nan da muka raina sai kaga ya dawo cikin rayuwarka ka gagara gane komai, harshenka ya kasance mai kaifi a wajen mutane, kai kuma sai mijinka ya zama mai kaifafa maka a cikin gida ko dangin miji. Mu kiyayi bakinmu da hannayenmu musamman a wajen comments ɗin nan na social media da muke rainawa, dan wlhy babu makawa sai an tambayemu, saboda ko (a) kika rubuta sai Mala'iku sun rubuta suma a littafinki. Abin tashin hankalin wani ma ko wata har abada bazaku taɓa haɗuwa ba a zahirin rayuwa balle ka roƙa gafarar sa, kai wasu ma ba karanta comments ɗin suke ba balle susan dake kin kuma ɗaurama kanki nauyi a banza a wofi dole kuma ki biya bashinsa da ayyukanki ko ke a baki nasu na sharr. Idan kuma ya karanta ɗin kin ƙuntata mata da comments ɗinki ko kin ƙuntata masa har ya kamu da wani ciwo ta sanadinki tofa aiki ya sameki dan sai kin amshi wannan sakamakon koda su ba mutanen kirki bane, balle bamu san tsakanin UBANGIJI da bawansa ba. Wlhy ƴan uwa idan Bamu kula ba muna cikin masifa, dan wayoyin nan dake a hannunmu hummm. Mudai sani bazamu iya biyan bashin zagi, ko aibantawa, ko cin hakkin mutane a ranar gobe kiyama ba, dan yanda muke tunanin lahira ta wuce da sanin mu, UBANGIJI ba abokin wasanmu bane. Hakkin mutane a kanka koda na kallon banza ne ba ƙaramin tashin hankali bane da nauyi mai girma da bazaka iya biyansa a ranar lahira ba. Tsaiwar mala'ikan mutuwa a kanka kawai ya isheka tashin hankali mai girma balle aje ga zare ran😭🙏, amsa tambayoyin kabari😭, kwanciyar kabarin kansa 😭, tsaiwar hisabi, ƙishirwa, zafin rana, karɓar sakamako daga littafinka, haye siraɗi, makomar gaba ɗaya data kasance zaɓi guda biyu na wuta ko aljanna. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un ya RABBI badan halinmu ba ka gafarta mana mu da iyayenmu😭🙏, dan ALLAH duk wanda na taɓa munanawa koda da magana ne, koda a rashin sani ne ya gafarceni, sai dai in kaima ka munana min ne na maida maka murtani, dan mutuwa kullum ƙawace ga mai rai, kamar yau ne zakuji ance babu Bilkisu, na tafi kamar ma ba'a taɓa yina ko yayina ba, na tafi daga ni sai ayyukana, ƙyale-ƙyalen duniyar da ake alfahari da faɗi tashi da wahalhalu duk anan zamu barshi kamar bamu wahala a nemansa ba. Ya rabba, ya arrahaman rabbi mun tuba. Mun tuba ya rabbi.🙏😭. Dan ALLAH mu bar tsorata yaranmu da ƙannenmu da abinda bamu da ilimin sanin gaibu a kansa, rayuwar aure rahama ce mai zaman kanta, ni'ima ce. ALLAH ka bama kowa zaman lafiya da mijinsa da zuri'arsa baki ɗaya. Ina muku fatan alkairi a duk inda kuke tare da fatan ALLAH ya karɓi ibadunmu yasa bamuyi kyakkyawan ƙarshe. ALLAH yasa muna a cikin ƴantattun bayi. Ya rabbi kasa abinda ya rage mana na rayuwa ya kasance mai amfani a garemu duniya da lahira.😭🙏........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖6️⃣8️⃣ ______________ .......Alhamdullah walima ta kasance cikin aminci, amarya Maanal tasha kuka jikinta yayi sanyi sosai, dan idan ta haɗa da lectures na nasihar iyaye da gargaɗi da wannan ya sake tabbatar mata da aure ba wasan yara bane. Dan duk abinda akace IBADA ne to lallai dole ne ka shirya da shiri na musamman. Dole ne ka yarda da dariya a cikinsa da kuma kuka a wasu lokutan, ita aljanna bata samuwa a kwance, kamar yanda kasan baka samun kuɗi a cikin mafarkinka sai ka motsa ka nema. Idan har duniya da take ba komai ba bata samuwa a garemu cikin sauƙi, taya zamu yi tunanin aljanna samunta zai kasance mana mai sauƙi. Mata ALLAH mu farka mu ajiye wani ka-ce-na-ce na hallayar maza mu nema aljanna kawai sune a ruwa. Dan aljanna duniyace malam, komai fa akwai a ciki, wohoho Bilyn ku a aljanna ai ba'a magana zamu tsula tsiyarmu in sha ALLAHU. (ALLAH kasa mu ɗin ƴan aljanna ne😭. ALLAH ka sani mun guji iskancin nan a duniya da gudun hakkin mutane duk da yanda suke da daɗi ALLAH kai mana sakamako da aljanna domin rahamarka😭🙏, mun tuba ka yafe mana kurakuranmu ka yafema iyayenmu ya rabbi ya arrahaman, ya arrahim, ya almalik, ya malikil mulki ziljalalu wal'iram😭🙏). Ba lectures ce kawai ta gudana a wajen ba, anci ansha tare da raba souvenirs masu ƙyau da ɗaukar idanu. Abinda zai baka dariya da birgeka hoton AA da Maanal suna yara ne a jiki. Sai mutane da yawa basu ma fahimci ango da amaryar bane ba a jiki, ita kanta Manaal abin ya bata dariya da birgeta, har sai da ƙwalla ta cika mata idanu dan kuwa hoton dake jikin ita kanta bazata iya tuna sanda aka yisa ba, tana ƙarama sosai, sai su Amaal ne keta ƙoƙarin ma tunowa suma suna dariya. Bayan kammala walima amarya Maanal ta koma ciki, yayinda su Nene suke shirin wucewa. Amma Oum tace ina ai saifa gobe da safe in sha ALLAHU kowa zai tafi, dan haka suma dole hakan zasuyi, anjima da dare ma akwai event na ƴammata da yaran Darma Family suka haɗama amarya. Rasama abin faɗa Nene tayi, wai su mutanen nan basa tausayin kuɗaɗensu ne... Dan shima dai acan ango wani ɗan biki-biki matasan Darma Family suka shirya iya su maza, shiyasa ma abokansa suma dai duk sai gobe zasu tafi. Shi dai dauriya kawai yake dan harga ALLAH a takure yake. Hajiya Shuwa ta haɗa masa bomb da turaren da take zazzagama Maanal a jiki, shiyasa ma yaketa kauce-kaucen haɗuwarsu a yau gaba ɗaya. Sosai abokan nasa suka saka shi a gaba musamman abokan karatunsu na primary da Secondary da suka san wacece Maanal a wajensa, tunda mafi yawansu sun sha duka da rashin arziƙinsa akan taɓa ta, ga rashin kunya itama ba raga musu tayi ba duk da sun girmeta. Haka suma dai wanda sukai karatu a tare na jami'a duk da bai taɓa zama ya bama wani labarin a cikinsu ba kai tsaye, sun dai tsinta wasu a cikin abubuwan da suka shafetan a wajensa sai kuma jiya sukaji komai da ganin hotuna a wajen dinner. Duk iskanci da shaƙiyancin da suke masan bai yarda ya kula ko wannensu ba, to kuma dama dai sun san halinsa na rashin son yawan magana. Yakan ɗan murmusa dai dan shi kam duk sun addabesa, badan Oum datace yau ya kwana anan ba dan su Nene sun kasa sakewa saboda jiya ya kwana a gidan da tuni ya fece gida abinsa..... __________★ Kuce dani ina hajjaju Mamy ne? Tana can a sashenta abin duniya ya matuƙar isarta, dole kuma ta danne ta haɗiye saboda wasu a cikin ƴan Kano a sashenta suke zaune. Badan ALLAH ba dole ta taushe tafashen azabar baƙin cikin dake zafafa zuciyarta tanata yaƙen dole ga ciwo na cinta a tsaitsaye jiya ma sai dare akabi aka saka mata drip da allurar barci a ciki sannan ta samu ta rutsa, amma abinda ya faru a wajen dinner ɗin nan ya matuƙar tsaya mata a rai. Kowa Oum yake tayawa murna matsayin uwa, komai za'ai ta ɓangaren uwa Oum Mc ke ambata. Babu mai kallonta, babu kai tunawa ita ta ɗauka cikin Ajwaad wata har goma sai a cikin na sha ɗaya ta haifesa. Tsabar ma an maida wulaƙantaciya ita aka dinga nunawa matsayin step Mom ɗinsa wai. Ya rabba wannan abu ya Zafafa mata zuciya. Har sai da taji idonta na gani bishi-bishi alamar jini ya haura mata sama sosai. Shiyyasa suka baro hall ɗin kafin ma a tashi. Koda suka shigo gida saita sakar ma Babban yayarsu dake riƙe da ita kuka dan can suka baro maman Saheeba tace sai taga komai. Ita kanta yayar tata wata irin masifa take ji na tafaso mata daga ƙirjinta, amma dole ta danne ta shiga lallashin Mamyn da nuna mata kuka fa ba shine mafita ba. Dole suzo susan abinyi dan al'amarin na Oum fa na neman zame musu ɗan zane. Ga tsagwaron rainin hankali a ciki, yo inba rainin hankali ba taya zata shirya wannan abubuwa haka batare da ita Mamyn an nuna wani matsayinta ba matsayinta na mahaifiyar Ajwaad balle su danginta, sannan ga auren Fawzan da shima akai matuƙar raina musu wayo a gefe, wanda da ƙyar suka taushi Mamy ɗin akan kar tace komai har a gama wannan taron kowa ya watse sannan su zauna da Abah. Dan basu so kowa ya tafi dasu a baki akan hakan. Yau ranar walima yanda Mamy ta nema ɗaga hankalinta yasa suka taru a kanta harda dangin mahaifiyarsu da sukazo wajen biki suka dinga tausarta. Wasu suna gaya mata gaskiya da tuna mata itafa ta ɗauka yaran ta bama kishiyar tata. Miyasa kuma zataji zafi dan yanzu an danganta yaran da ita. Wasu ko goyon bayanta suke da tayata kishi. Haka dai sukaita cece kunesu batare da su Oum sun ma sani ba. Koda lokacin walima yayi tace bazata fita ba ƙyaleta kowa yayi. Tabbas Oum ta lura bataga Mamy ta fito ba, sai kuma hayaniyar mutane da maƙwafta masu shigowa da abokan arziƙinsu nan cikin abujar ya ɗauke mata hankali. Ana gama walima kuma sallar magrib kawai akai aka shiga shirin faty na yaran family ɗin da suka shiryawa amarya. Anan cikin gidan shima akayi a garden, yanzu ma amarya Maanal tasha ƙyau harta gaji cikin doguwar rigar atamfa data mata ƙyau sosai. An gudanar da komai cikin aji da halin girma. Amarya Maanal tasha kyaututtuka daga ƙannen ango dan mafi yawan yaran family ɗin mata su AA sun girmesu, sai dai kamar iyaye irinsu Majdiya, ko su Nuwaira matar su RK matsayin iyayen su AA ɗin suke ai. Ƙarfe goma an tashi kowa ya nema makwanci. Yau ma cike da murna Maanal ta kwanta ƴan uwanta zagaye da ita. Washe gari kam da wuri Nene tasa suka gyara ko'ina na sashen Maanal. Dai-dai nan mota ta iso daga Kaduna ta kayan gara daga Daddy sai kuma kayan rabo da zasuyi na buɗar kai. Dan zuwa ƙarfe ɗaya na rana an gama shirya Manaal cikin wani arnen lafaya da yay mata ƙyau. Ana idar da sallar azhar sama-sama sukaci abincin da aka kawo musu na lunch, sannan sukai zaman sake yima amarya Maanal daketa hawaye nasiha. Bayan sun kammala sashen Oum suka nufa da Maanal dan acan za'ai buɗar kai. Dole suma dangin Mamy nan suka zo aka haɗu gaba ɗaya. Anyi buɗar kai, tare da damƙama su Oum kayan rabo na al'ada daya bada mamaki, dan su Shahidah sunyi matuƙar ƙoƙarin nuna bajintarsu suma. Saboda tunda akace za'aima Maanal biki kafin tarewa suma suka shiga yin wannan tanadi su da Ammie babu wanda yaji ko ya gani sai Nene. Sai yau da ake fiddo kayan arziƙi ƴaƴan su Hajiya Yaya da na Hajiya Basariyya sukai tsuru-tsuru jikinsu na ƙarasa yin sanyi. Dan da gasken gaske an goge musu kaf haddarsu a wannan biki. Hatta su dangin Mamyn abin ya basu mamaki, dan su dai Mamy ta gama sanar musu Maanal ƴar matsiyata ce. Sai gashi a wajen baye hatta su Naufal dake matsayin ƴaƴa sai da aka basu rabo. Haka kaf manyan family na Darma kowa da nashi har su RK dake ƙananun uncle's kuma ta ɓangaren mace ma. Ga kayan gara mota guda, kaf kuma a sashen Oum aka ajiyesu ba'a ajiyewa Maanal komai a cikinsu ba dan sun ɗan saka mata wasu abubuwan a store da su Shahidah sukai dabarar saya suma ta ɓangaren kayan abincin. Bayan gama rabo aka zagaya da Maanal gaban iyaye. Anan fa suma Darma Family suka sake zuba tasu bajintar. Dan sun sakama amarya kuɗin al'ada sosai, saboda ba kunya Oum ta bada babban basket na kaba tace sotake ta gansa cike da kuɗi iyayen ango da ƙannensa da auntys. Cikin dai raha akai wasa akai dariya. Tuni dangin Mamy suka tsure, dan da alama dai zasu sha kunya a wajen. Saboda su wai a gadarance suka taho da kuɗi mai dubu ɗari mai hamsin Maman Saheeba ma ɗari biyu wai za'a nunama Oum ita ba komai bace koda basa son amarya sai sun bada mamaki sai suka ga yara ƙanana na ajiye 1m da 500k kamar kuɗin banza. (To banda abin talaka ana faɗa da mai kuɗi ko gasa ne akan kuɗi😆😜🥱). Tuni su Mamman Saheeba suka fara ɓoye ƴan dubu ɗari biyu dana hamsin ɗin su, daga baya dai Saheeba data fahimci kunya fa dangin nasu zasu sha tace su haɗe kuɗin waje guda su bata. Haka sukayi, ita kuma ta fita ta ƙundumo 1m a cikin kuɗin sana'arta ta haɗa ta ajiye matsayin na dangin Mamy gaba ɗaya. Tsabar muguntar Hajiya Majdiya sai tace to matan yayyan ango Saheeba da Nibras kenan dole suma su sanya, hatta kuma Najma bata ɗagama ƙafa ba. Wannan abu ya girgiza Saheeba. Nibras da duk ta fige ta rame a kwanakin bikin nan uwarta tazo ta ajiye 1m dan itama bata son harkar zubda girma🤣. Ganin haka fa Saheeba aka sake zuwa aka ɗakko 1m aka ajiye itama. Aunty Rufaidah na ganin haka tazo ta ajiye 3m matsayin na Najma tace ta fanshi ɗiyarta itama. Zokaga ihu da ihu na shaƙiyancin yaran family ɗin darma. (NIKO NACE SHEGIYA NERA, ALLAH KA BAMU NERA MAI ALBARKA😆🙏). Wanna abu ya tsayama Saheeba da uwar Nibras a ƙahon zuciya, dan ita Nibras ma hankalinta ba awajen yake ba. Uwarta kuwa tayata kishi take da ƴan uwanta akan Najma. Dan ko bikin nan sun halarci shi ne kawai dan kar ace gashi-gashi. Amma Maman Nibras ta gama shirya bala'in da zasuyi da Mamy jira take kawai biki ya watse taji dalilin yima ƴarta kishiya batare da an sanar dasu ba..........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖6️⃣9️⃣ ______________ https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Shin kuna Neman in da zamu samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa?kayan yara masu kyau unique na yan gayu ? To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo! Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi tanayi🥳🥳 ___________ ..........To su dai su Shahidah sunyi godiya sannan aka kai Maanal sashen Mamy, Mamy na bedroom, su Shahidah suka zauna a falo. Kasancewar tare suke da Aunty Suhaima, da Aunty Zainab, sai Aunty Kursiyya matan Uncle Hassan da Hussaini da Uncle Mahmoud kenan suka shiga har cikin suka mata magana kasancewarsu matan ƙannen miji. Dole Mamy ta danne ta fito sanye da hijjab, dan kwance take ciwon kai ya addaba mata. Ganinsu warr a falon suka cika mata ido, dole ta aro murmushin yaƙe ta yafama fuskarta. A gabanta aka zaunar da Maanal dake lulluɓe. Da ƙyar ta iya daurewa tace ALLAH ya sanya albarka kawai. Wai ai tasan duk wanda ya isa ya mata nasiha ita basai tace komai ba. Shahidah da a yanzu Maanal ta gama nuna mata wani abu kaɗan daga Mamyn sai tai murmushi kawai, tare da fassara zancen nata da ƙyau a zuciya. Ita kanta Nene yau dai kam tasha jinin jikinta akan Mamyn, amma batace komai ba suka fito da Maaanal. Sashenta suka maidata, aka ƙara mata nasiha sukai sallar la'asar suka firfito dan tafiya. Kuka sosai Maanal keyi abin tausayi, dan ma Amaal na nan tare da ita sai Aunty Sakina. Sai zuwa magrib su zasu koma gidan Shahidah su sake kwana gobe su wuce kd. Sashen Oum suka koma yimata sallama. Sosai Oum tai mamaki ganin wannan tafiya tasu ta yamma haka. Ta shiga lallashinsu akan su bari sai gobe da safe Nene tace ina ai in sha ALLAHU yau a Kaduna zasu kwana, abin ai sai ya koma rashin kangado kuma. Anyi komai an gama ai suma sai a barsu su huta haka nan abi yara da addu'ar zama lafiya.. Badan Oum taso ba ta haƙura, nan fa aka shiga shirya musu kayan biki da aka tanada domin su, dan hatta Ammie sai da Oum ta haɗa mata nata. Sashen Maanal ɗin suka sake dawowa tare da ita, acewarta ya kamata suyi sallama da AA dan ta kaisu sunyi da Abah yanata musu godiya, a can kuma suka sami Mamy itama. Kiran wayar AA datai a kashe kuma Fawzan ya tabbatar mata yana gidan sanda suke buɗar kai ya shigo ya sata biyosu. Rungume Maanal dake zaune a bakin gado ta takure waje guda tana sharar hawaye har yanzu tayi, cike da tausasawa ta shiga lallashinta. Kafin ta bata umarnin hawa sama ta kira musu AA ɗin. Mayafin lafayarta ta gyara da ƙyau, tayi ƙyau sosai, duk wanda ya ganta kuma yaga amarya, dan ƙamshinta daban ne, ga ƙunshinta raɗam yanata ɗaukar ido daga baƙin har jan, fatar jikinta kam da tasha gyara ba'a magana, sai wani irin glowing take a idanun mai kallo kamar ka lasheta. Ita kanta Oum kallonta kawai take tana murmushi, ta jima bataga ma'auratan da suka dace da juna ba irin Maanal da Autan ta, sai dai ai musu fatan zama lafiya mai ɗorewa kuma. Tare da Oum suka baro bedroom ɗin nata suka haura sama. Zuciyar Maanal bata ƙarasa fashewa ba sai da ta hawo upstairs ɗin, ya subahannallah komai yaji, ga wani mayataccen ƙamshi mai ratsa zuciya. Zama Oum tayi a ɗaya daga kujerun, Maanal ɗin zata zauna itama ta katseta tana nuna mata kofar bedroom ɗin AA. Jikinta cike da sanyi ta nufa ƙofar, tana gab da isa sai gashi an buɗe. Cak ta tsaya tana kallonsa. Kamar yanda shima yake kallonta irin na mamakin nan dan ko motsinsu bai jiba. Yama fito ne zai fita dan dama wanka ya shigo yayi rabonsa da wanka tunna safe manyan kayan jikinsa sun takurasa shiyyasa yazo yay wankan ya canja da ƙananu. Juyawa kawai Maanal tai tabar wajen, shima sai bai ce komai ba ya biyota saboda hango Oum zane a falon. Bata zauna ba, sai tai kamar ana kiranta a waya ta gudu ta barsu dan ta basu damarsu. Murmushi kawai Oum tayi danta fahimci wayo Maanal tayi ya gudu babu wani kiranta da akayi. Bedroom ɗinta ta wuce inda su Nene suke. Bata wani jima ba Oum ta shigo da sallama itama. Ta sanarma Nene ga AA zai shigo suyi sallama. Gyagygyarawa suka shiga yi kafin ya shigo bakinsa da sallama. Duk suka amsa banda Maanal datake kallon hotunansu a wayar Aunty Sakina. Cike da girmamawa ya rissina ya gaida Nene, hakama Aunty Sakina duk da ba girmarsa tayi ba, amma tunda akace matsayin ƙanwa take a wajen Ammie yake girmamata. Shahidah ta ce, “Oh mu baza'a gaishemu ba Ajwaad”. Hararrata yay ya ɗauke kai. Su Nene suka sanya dariya. Oum da itama ke dariya tace, “Gaskiya fa Shahidah ta faɗa Auta, dan yanzu babu batun ƴar gaddamar cewa bata girmeka ba matsayin yaya take dai”. “Ni banzanyi Auntys da su ba Oum, Aunty Sakina ta isheni”. Yay maganar ƙasa-ƙasa yana hararar Amaal itama. Dariya kowa keyi, Amal ta ce, “Ni dai na haƙura ma Yaya Ajwaad basai kace min Aunty ba, dan nasan bama cewar zakai ba. Kuma nima bazan so kace ba dan kai Yayana ne”. Oum ta ce, “Amaal yada saurin sallamawa haka”. “Oum gara na sallama wlhy, dan kozan mutu na dawo Yaya Ajwaad bazai ce min Aunty ba kema kin sani”. Nan ma sosai suke dariya. Shi ko ya fuske abinsa. Sai ma satar kallon Maanal yake ta ƙasan ido. Itako tayi kamar bata san ma da shigowar tashi ba, rabin fiskarta ma gyalen ya ɗan rufe. Godiya sosai AA yayma Nene, tare da alƙawarin zuwa gaisheta nan kusa in sha ALLAHU ita da su Ammie. Sosai Nene taji daɗin hakan ta kuma sake yaba AA ɗin dan tarbiyyar sa ta birgeta sosai. Leda dake a hannunsa ya miƙama Oum, yace ta basu, bai jira cewar kowa ba ya miƙe bayan Oum ta amsa ledan ta miƙama Nene tana murmushi. Amasar ledar Nene tayi tana faɗin, “Tofa mi muka samu kai ɗan nan.....” Ta kasa ƙarasa maganar sakamakon tozali da tai da kuɗaɗe ƴan dubu bugun Abuja sabbi fil. Da wani irin sauri ta kalla Oum, sai kuma ta girgiza kai tana miƙa mata ledar. “Bazamu amsa ba ɗiyata. Ai abun ma sai ya zama rashin hankali”. Roƙonta Oum ta shiga yi itama, amma Nene ta dage akan bazasufa amsa ba. Sai ma ta miƙe tana ficewa tunda su Amaal da Aunty Sakina anan za'a barsu su ƙarasa gyara mata gidan sai zuwa anjima kafin anguna su shigo dan ba'a barta ita kaɗai ba. Shahidah dai zata bisu saboda sai sun koma ta gidanta. Suma su Maanal ɗin fitowa sukai yi musu rakkiya, tuni AA ya haɗa motocin da zasu kaisu can gidan Shahidah su ɗauka sauran kayansu sai su kaisu train station. Haɗa ido yay da Maanal dake sharar hawaye Aunty Sakina riƙe da hannunta. Su su Aneesa nata tsokanarta wai sai sun dawo Abuja suna bata kulasu ba. Suna ma haɗa ido da AA ɗin ta risinar da idannunta ƙasa. Haka suka shishshiga mota Oum ta danƙa ledar a hannun Shahidah, zatai magana ta harareta da mata alamar tai shiru. Dole tai shirun kuwa suka wuce. Ciki su Amaal suka koma da Maanal dake kuka sosai, AA ya girgiza kai kawai ya shiga mota ya fice a gidan dan zaije wajen abokansa dake shirye-shirye tafiya suma. Wasu dama tun safe duk sun wuce sai wanda suka rage da zasubi flight ɗin yamma.... _________★ Mamy dai ciwon kai ya hanata sukuni, gashi tasha magani babu wani canji, dole Hajiya Turai ta ƙara turo musu Nurse ɗin nan ta dubata. Cikin damuwa ta ce, “Hajiya akwai matsala fa gaskiya, in dai bazaki rage wannan damuwar ba bp ɗinki fa bazai taɓa ya sauka ba. Gashi zuwa yanzu hatta bugun zuciyarki ya canja. Jininki kuwa ba'a magana wlhy, shiyyasa ma kike ganin dishi-dishi ciwon kan kuma yaƙi sauka. Dole zan sake miki allurar barci mai ƙarfi sosai dan ki samu barci, amma ki sani allurarnan barci kawai zata sanya ki, kwanciyar hankalinki shine maganin matsalar ”. Ita dai Mamy komai tama kasa cewa, dan abun duniya ne ya taru yama zuciyarta rubdugu. Haka Nurse ta mata allurar barci. Tun tana kallonsu da saurarensu har barci yay awon gaba da ita..... Oum bata san wainar ba ake toyawa ba, tana a tsakkiyar ƴan uwanta dan duk dai zuwa gobe in sha ALLAHU zasu wuce su kuma. Itama Oum ɗin bata kawo komai a ranta ba tunda taga Mamyn na zagaye da nata ƴan uwan ne. Duk da dai duk yau bazatace tama ga giccin Mamy ba, koda yake ko Abah ba bi take takansa ba tanata hidimarta. ★ Bayan sallar isha'i su RK da ire-irensa dake sa'oin su AA a family ɗin na Darma suka iso gidan domin masa rakkiya. A dai-dai lokacin ne su Amaal ke fitowa cikin shirin tafiya ita da aunty Sakina. Sun sake gyara ko'ina na sashen sun baza uban ƙamshin da har a compound ana jinsa masha ALLAH. Sai da suka shirya Maanal ɗin itama da taimakon Hajiya Shuwa. An mata wanka da turare iya wanka fiye da yanda ake mata shi tun fara gyaran jikin nan. Kafin Hajiya Shuwa ta naɗeta a cikin sabuwar wata lafayar ƴar ubansu mai shegen ƙyau kalar peach da ɗan fari-fari, sai uban stones saketa walƙiya a jiki, an mata kwalliya ƴar dai-dai a fuska aka sake mata turaren turare. Sai ɗauri daya zauna mata akai sannan aka rufeta da lafaya ɗin. Suka saka mata ac dai-dai misali aka zaunar da ita a tsakkiyar kadon ɗakin nan ƙasa ɗin, Hajiya Shuwa tace su barta anan idan AA ɗin yazo da kansa sai ya mata jagora Upstairs ɗin idan ƴar rakiyar tasa sun tafi. Suna jin shigowar motocin su AA suka fito dan dama su suke jira. Suka ma Maanal wayon cewa bara suje wajen Oum kafin su AA ɗin su gama. Dan tun ɗazun take roƙonsu su kwana anan, ganin zata botsare musu da kuka sukace sunji zasu kwana. Shine suka mata wannan wayon suka gudu. Dan ko sashen su Oum ɗin basu koma ba ganin can su AA suka shiga.... ★Su AA sun shiga falon Oum a dai-dai lokacin da dukkan mayan matan family ɗin ke zaune zaman jiran su, dan dama ƙa'ida kenan ga duk wani angon family ɗin a lokacin masa rakkiya ɗakin amarya. Kuma abinda zai birgeka isu-isu sukema juna rakkiya ba abokai ba. Su duka su a ƙasan carpet suka zauna dan duk iyayene. Yayinda AA yaje gaban Oum ya zauna, cike da sanyi ya ɗaura kansa a saman gwiwoyinta ya wani lumshe idanu. Abin mamaki sai ga hawaye. Murmushi sosai Oum tai saboda jin saukar hawayen nasa a saman ƙafarta, cike da kulawa da tsantsar so irin na uwa ga ɗa ta duƙo ta leƙa fuskar tasa. Kukan kuwa yake yi da gaske, itama sai taji hawaye sun cika mata ido. Ta dai daure tasa bakin mayafinta ta share masa su. Kafin a hankali cike da kulawa ta ce, “Haba Auta na yau ai ba ranar kuka bace, ranar farin ciki ce mun mallaki Maanal na har abada in sha ALLAHU. Dan haka bana son ganin hawayen nan kaji Babyna, addu'a zamuyi mu godema UBANGIJI daya nuna mana wannan rana bayan jarabawoyin da muka tsallake Abaya. Harma mu haɗa da sadaka domin nuna farin cikin mu ga ALLAH okay”. Kansa ya jinjina mata, sai kuma ya buɗe idonsa yana kallonta, tare da kamo hannunta ya sumbata...........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖7️⃣0️⃣ ______________ ........Cike da tsokana RK ya ce, “Ikon ALLAH, amarya na kuka idan za'a kaita gidan miji yau ga ango nama mamarsa kuka za'a kaisa wajen matarsa”. Aiko sosai falon ya kacame da dariya, AA ya ɗauka fillo ya jefa masa. Cafewa RK ɗin yay yana masa gwalo. Aiko sai suma su Mama da Umma da Mamma da Gwaggo Khadijah suka shiga masa tsokana irin ta kakkanni, nan fa su Oum suka shiga karesa suma. Anyi wasa anyi raha kafin a koma nasiha da gaba ɗaya ta ta'allaƙa ne ga AA ɗin, ta yanda zai zama mai haƙuri akan mace, ta yanda zai ƙyautata mata, ta yanda zai shagwaɓata ya riritata, ya sauke haƙƙokinta da ƙyautatata mata. Ya tattala soyayyarsu kullum taita ƙara danƙo a maimakon rauni da maza da yawa ke saka soyayyarsu yi saboda sakacin sauke haƙƙoƙin da suka dace akan iyalansu. Sun nuna masa muhimmancin sauƙaƙama mace saboda kasancewarmu masu rauni. Suka kuma tunasar da shi zaman aure zaman ibada ne ba zama irin na saurayi da budurwa ba, yanzu maganar ƴakin soyayya da farautarta ya ƙare. Lokacine na tabbatar da ita ta jaddadata domin ta ƙara nauyi a sikeli da danƙo fiye da sufagilu. Haƙuri da kura-kuran mata dan mu a karkace muke, wanda ya dage ko fariyyyar son ganin ya lanƙwasamu mun miƙe to ya tabbata sai dai mu karye ɓas. Dan haka ya kula yasan miya dace ga zaman auren, ya zama mai tausasawa sai yaci ribar zaman har yay nisan zangon kaiwa wasu shekarun da za'a ringa lissafi shekarun aurensu suma. Daga ƙarshe aka rufe da addu'a mai tsaho da ratsa jiki, sannan aka sallame su dan zasuje sashen Abah su masa sallama da su Babban Yaya. Kasa tashi AA yayi, har sai da Oum ta miƙe tana murmushi ta kamasa ta miƙar. Sai kawai ya rungumeta. Harga ALLAH zuciyarsa tai rauni, wai shima yau yayi aure za'a danƙashi ga matarsa ya bar Oum ɗinsa da yake manne da ita akoda yaushe, shike nan zai tashi daga saurayi ya koma magidanci. Da ƙyar su RK da jikinsu yay sanyi suma suka janyesa. Dan soyayyar Oum da yaran nan uku musamman Ajwaad na taɓa zukatan wannan Family ɗin matuƙa. Ɗagosa Oum tayi ta share masa guntun hawayen sannan ta kamo hannun Modibbo ta damƙa na AA a ciki, sai ta koma ta zauna tana riƙe hawayenta itama. Yau finally ta aurar da autanta yaranta sun gama auren fari sai kuma ga masu burin ƙarawa kamar yanda Fawzan yayi. Da ƙyar su RK suka ja AA dake ta kallon Oum suka fita da shi. Sun wuce sashen Mamy, sai suka samu tana barci, anan ko maimakon AA ya samu faɗa da nasiha kamar a sashen Mamy sai su Maman Saheeba suka ɓige da habaice-habaice. RK ne kawai ya fahimci inda suka dosa, sauran ko basu kawo komai a ransu ba sai shi AA ɗin kansa. Dan haka baici komai ba ya miƙe yay musu sai da safe ya barsu da baƙin cikin sharesun da yay. Haka sukaita zage-zage da aibanta Oum da Maanal dama Darma Family gaba ɗaya har Maanal da danginta basu tsira ba. Sashen Abah shine na uku, daga shi sai Uncle Mahmud da Uncle Hussain da Hassan ɗinsa, anan ma nasiha mai ratsa jiki iyayen sukai masa. Tare da jadadada masa haƙƙoƙinsa na miji akan matarsa. Sai dabaru na kula da mace ta yanda aure ke ƙarko da ikon ALLAH. Daga ƙarshe akai addu'a sannan suka taso, sai sashen Babban Yaya. Sun sameshi shi kaɗai a falo zaune yana shan shayi yana kallon labarai. Kama AA yay ya rungume tsam-tsam a jikinsa. Kafin ya ɗagosa yana murmushi ya riƙe masa fuska da hannaye biyu. Cike da raɗa Babban Yaya ya ce, “Finally yau Autan Oum ya mallaki Lilly na, zata maidashi babban mutum, nan da wata tara su haifa min ƙyawawan yara masu kama da su”. Kunya sosai ta kama AA. Sai kawai ya sake rungume Babban Yaya hawaye na cika masa ido. Dariya babban yaya ya sake yi sauran na tayashi sannan ya zaunar da shi kusa da shi. Shima dai yayma AA nasiha da jadadda masa zama miji na gari a wajen Lilly. Ya rufe da addu'a mai ƙarfi. Daga nan sashen Fawzan suka nufa, shi kam sai Nibras kawai suka samu a falo. Duk tayi wani wujiga-wujiga da alama kuma leƙensu take ta window kafin su shigo. Bayan ta gaishesu cikin son danne kanta da ƙyar RK yace ta kira musu Fawzan. Tana miƙewa ma sai gashi yana sakkowa daga sama. Yana zuwa ya rungume AA, cike da raɗa yanda kowa baya ji ya ce, “Oh oh yau fa Autan Oum zai shiga daga ciki. Babu dokar Aba a kansa Lilly zata dinga masa TAWAI”. Mintsininsa AA yayi, Yaya Fawzan ya ce, “Ouch wane muguntane wanan haka Auta?”. Cike da shaƙiyanci AA yace, “Ƙanwarka ta koya min”. Yanda yay maganar a fili ya sanya kowa dariya. Dan saika rantse bama shi yay zancen ba, babu wani fara'a a tare da shi. Yaya Fawzan yakai zaune yana faɗin, “Shike nan na yafe maka kaci albarkacin Lilly, zauna na maka nasiha dan bazan yarda da rashin mutuncin mijin ƙanwa ba lallasaka zanyi idan kai mata ko kallon banza eh”. Babu wanda bai dara ba yanzu ma. Kafin Fawzan yaci serious kamar ba shi ba ya fara ma AA nasiha shima, daga ƙarshe suka rufe da addu'a sannan ya sallamesu. Koda AA yace shi bazai masa rakkiyar ba? Sai Fawzan yay shiru, sai da yaga kamar AA ya ƙwaɓe fuska sannan ya miƙe yace “Muje taɓararre kawai. Yanzu dai zamu huta muma Lilly ta kwasa”. Lokacin da suke ficewa idon Fawzan ya sauka akan Nibras dake ɓoye ƙarƙashin bene tana kuka sosai. Kansa kawai ya girgiza yay gaba hannunsa riƙe dana AA. Shima AA ɗin sarai yaga Nibras ɗin, amma ya basar kamar bai ganta ba. Sauran ko babu wanda ya lura sam.. Wani irin daddaɗan ƙamshi mai sanyaya zuciya da sauke gajiya ne ya fara musu sallama a falon, musamman ga AA daya fara shiga. Gaba ɗaya falon ya ɗauki wani irin ƙyau mai ƙayatarwa daka kallesa ka san a lallai gidan amarya kazo. Duk zama su RK sukai kowa na sauke numfashi, dan ba ƙaramin daɗi ƙamshin gidan yay musu ba. AA zai zauna Yaya Fawzan ya ce, “A'a ango tashi kaje kazo mana da amarya muna nan”. Ɗan jimmm AA yayi, sai kuma ya miƙe dan harga ALLAH soyay daga iya nan suyi sallama su koma shi kaɗai yaje ga matarsa. Amma bazai iya ba yana jin nauyin Yaya Fawzan ɗinsa. Tsayawa yay a ƙofar ɗakin ya zubama handle ɗin ido na sakanni, dan Amaal ta tura masa text cewar Maanal ɗin na nan ƙasa. Sai kuma ya sauke numfashi a hankali sannan ya murɗa handle ɗin kamar baya so ya tura kai ciki da sallama ƙasa-ƙasa. Zuwa yanzu Maanal na kwance ne dan ta gaji da zaman, ga tsoro na shigarta haka kawai, ta kira Didi Amaal tace su dawo dan ALLAH tsoro take ji, shine tace mata ta daure na ɗan lokaci ne gasu AA ɗin nan shigowa. Tun tana kallon ƙofa harta zame ta kwanta idanunta a lumshe ta faɗa tunanin duniya da nazarce-nazarcen ruguntsumin cikinta. A wannan yanayin taji an buɗe ƙofa, kafin ma ta nema ba'asin wanene sassanyan ƙamshin turarensa ya shigo mata hanci duk da yanda nata ke tashi da wanda aka sanya ma ɗakin ma. Luff tayi kamar mai barci tana ƙoƙarin saisaita numfashinta har ta fahimci isowarsa inda take ya tsaya cak. Shiru bata buɗe idanun ba, yana daga tsaye shi kuma ya zubama ƙyaƙyƙyawar fuskarta da yake gani kaɗan raunanan idanunsa. Kallon fin minti guda sannan ya wani fusrzar da iska mai nauyi sakamakon saukar idanunsa akan ƙugunta daya wani bada shep ta hanyar fidda lafaffen cikinta zuwa cikar ƙirji dana ƙugun dan lafayar mai kwantawa ce a jiki. Sannu a hankali kamar wanda baya so ya duƙo yana kai hannu ya yaye fuskarta da ƙyau, cike da raɗa ganin taƙi buɗe idanun ya furta, “Amincin ALLAH ya tabbata a gareki Madam pretender”. Baki Manaal ta ɗan cuna a karo na farko, amma still taƙi buɗe idannunta. A karo na farko yay murmushi kaɗan, sai kuma tunawa da ana jiransu yasa shi sake furzar da numfashin ya ce, “I'm sorry drama queen. Ajiye shagwaɓan muje wajen su Yaya Fawzan mu dawo duk sai ki tattaro kiyi min harta shekara 8 da suka wuce da nayi missing duk zan ɗauka a yau ɗin nan koda ina faɗuwa ina tashi ne”. Shiru nan ma tayi, sai dai ta buɗe idannunta a hankali ta sauke a kansa, suka ɗan zubama juna ido, sai kuma ta janye nata tana tashi zaunen a nutse. Taimaka mata yay batare daya janye nasa idanun ba ya miƙar da ita, sai kawai ya sanyata a jikinsa ya rungume. “Alhamdullahi! Alhamdullahi! Alhamdullahi!” ya jera har suka uku a jere yana sauke ajiyar zuciya. Cikin raɗa ya sake faɗin, “Ya rabba nagode maka daka nuna min wannan rana, kai ne ka bani ita tun tana ƙarama, ka jarabceni da kuɓucewarta a gaɓar dana gama sakankancewa, ka dawo min da ita a lokacin dana gama sallamawa na rasata, ka bani ita a randa na gama yarda tawa rayuwar ta ƙare kenan gaba ɗaya. Yau gashi ka shigo da ita a cikin gaba ɗaya duniyata a gaɓar da nake cikin matsanancin zumuɗi, ƙagare, farin cikin kasancewar tamu. ALLAH kai mata albarka, ya rabbi ka tausasa min ita ta zame min mar'atussaliha. Ya rabbi ka ƙarfafa min ita ta zama uwar ƴaƴana jajurtacciya, ya rabbi kai mata rahama mara yanke wa, ka tsare min ita daga kowanne irin sharri na fili dana ɓoye, ka baibaiyeta da alkairinka da rahamarka, ƙasa ta zama mai koyi da Nana Khadijah, kasa ta zama mai koyi da Nana Ai'sha. Ƙasa ta zama mai koyi da Nana Hafsah. Ƙasa ta zama mai koyi da Nana Saudah, ƙasa ta zama mai koyi da Nana Zainab. Ƙasa ta zama kai koyi da Nana Faɗima. Ƙasa ta zama kai koyi da Nana Asiya, ƙasa ta zama mai koyi da ɗabi'un salihan mata bayin ALLAH duka da sauran matan MANZON ALLAH daban ambato ba da jaruman mata da sukai ma addini hidima tako wace fuskar alkairi. Ya rabbi kasa tai koyi da ƙyawawan halaye, haƙuri, juriya, jarumtar Oumna. Ya rabbi ka zama shaida, ita ɗin ta musamman ce a gareni, irin musamman ɗin da baki bazai iya ma furta wa ba.....” Tsam-tsam Maanal ta sake rungumeshi hawaye na sauka mata. Fin minti uku suna faman sauke ajiyar zuciya sannan ya janyeta da ƙyar ya share mata hawayen ya gyara mata lulluɓin lifaya ɗin ya kama hannunta a jikin nashi yaja suka fice. A haka suka fito daga bedroom ɗin kamar makaho da ɗan jagora har cikin falon. Sai a lokacin Maanal ta fahimci basu kaɗai bane ba. Zaunar da ita yay sannan shima ya zauna kusa da ita. Cike da girmamawa yace ma Yaya Fawzan “Gata”. Murmushi yaya Fawzan yayi mai faɗi, sai kuma ya kalla Maanal ɗin yace, “Lilly!”. Jin muryar Yaya Fawzan yasa Maanal amsa masa da “Na'am Yaya F”. “ALLAH yay miki albarka. ALLAH yay miki albarka! ALLAH yay miki albarka!. Nagode ma UBANGIJI daya kaimu wannan rana cike da lafiya da tsohon rai. Dan gaskiya dana mutu banga wannan ranar ba dole ne ma na dinga muku fatalwa banga ƙarshen movie ɗin ba”. Murmushi su RK suka shiga yi, Yaya Fawzan ya cigaba da yiwa Maanal da AA nasiha da addu'a yanda ya kamata. Kafin su RK su amsa kowa yay tashi a taƙaice. Daga haka suka miƙe bayan RK yazo gaban AA ɗin ya ajiye wani haɗaɗɗen basket da akai ma wani irin ado da flowers a sama aka kuma rufesa da net. Shine da Nuwaira suka haɗashi, Sai kuɗi da suma akai ma wani irin nannaɗar ado a wata flower ɗin daban, daloli su kuma wai na sayen baki. Daga haka sukai sallama suka fice. AA ya ɗan rakosu wajen sashen. Sai Yaya Fawzan ya maidashi ciki yana faɗin, “Koma ciki mun yafe bama son rakiyar, dan nasan ma badan ALLAH zakayi ba Auta, maybe ma jikake kamar ka koromu waje kawai. Dariya sauran suka sanya sosai. RK ya matso saitin kunnen AA ya raɗa masa, “Adai bi min daughter a hankali yarinya ce dan ALLAH. Dan wannan fitinar dake cikin idanunka ma ta isa firgitata”. Harararsa AA yayi, RK ya bar wajen yana dariya. Sai kawai yaji an riƙo masa hannu. Dariyar ya tsayar tare da juyowa. Ganin AA ne ya riƙosan ga wani irin kallo da yake masa sai shima ya zuba masa nasa idanun. Tsohon mintuna biyu suna kallon junan, su sauran da basu san mike faruwa ba sunyi gaba abinsu dan komawa sashen baƙi su samu su kwanta suma su huta, gobe kuma in sha ALLAHU Kano tai ɗiba. Da wani irin hankali AA ya shiga jawo RK baya sannu-sannu harya dawo gabansa gab, cak ya tsayar da shi akan ƙafafunsa suna kallon juna cikin ido. Sai kuma kawai AA ya wani kalar jawo RK ya rungume. A tare suka sauke ajiyar zuciya mai nauyi, RK yay murmushi yana ɗagowa bayan ya ɗan bubbuga bayan sa. Magana AA ya buɗe baki zai yi, amma RK ya hana hakan ta hanyar yimasa zipping a baki yace, “Shiiii karkace komai, oya good night my son. Dan ALLAH karka ɓaro min aiki da safe kaga dai na gaji nima mamanka zan ɗauka mubar gidan nan ta ɗan min tausa”. Daga haka ya barsa anan tsaye. AA ya bisa da kallo harya ɓacema ganinsa, a hankali ya furta, “I love you Uncle. Kai ɗin na daban ne a gareni ƙololuwa”. Sai kuma ya ɗan murmusa tare da lumshe idanu ya buɗe a lokaci guda sannan ya murɗa ƙofar ya koma ciki, key ya sake murzawa daga cikin ya kulle........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖7️⃣1️⃣ ______________ .........A inda suka barta anan ya sameta. Ya ɗan bi falon da kallo kafin ya cigaba da takawa a hankali inda take. Komai baice ba ya kama lafayan ya yaye, kaɗan ta ɗago ta kallesa ta maida idanun ta rissinar, ya ɗan zubama hannayenta data matse cikin juna ido, sai ya saki guntun murmushi. Duƙowa yay ya kama hannun nata ya miƙar da ita tsaye, ita dai taƙi yarda ta kallesa. Da wata irin murya mai laushi da komawa can cikin maƙoshi ya ce, “Bestie ki kalleni mana”. Kanta ta girgiza masa alamar a'a. Cikin sake sauke muryar ƙasa sosai ya ce, “Why?”. Da ƙyar ta iya motsa lips ɗinta, batare da sautin muryarta ya fita ba ta ce, “Ba komai”. Kaɗan ya wani ɗan laɓe baki da jinjina kansa still yana kallonta. Sai kuma ya furta, “Okay, to ko zaki koma sashen Oum ne?”. Ai baima gama rufe baki ba ta wani ɗago tana kallonsa. Da ƙyar ya iya gimtse dariyar data taho masa, dan tsoro sosai ya karanto a cikin idanunta. Duk ta koma sanyi-sanyi kamar ba ita ba, “Zaki je kenan?”. Ya faɗa yana riƙo haɓarta dan ƙoƙarin duƙar da kan take. A mamakinsa sai ta girgiza masa kai, idannunta a lumshe. Kafin yay magana ta cigaba da faɗin, “Akwai baƙi sashen Oum. Su Didi Amaal dai sun ce zasu zo su kwana nan suna sashen Oum”. Nan ma dai sai da abun yaso bashi dariya. A zuciyarsa yace (Childish) a fili kam sai yace, “Okay! Ni kuma fa ina zan kwana?”. Idannunta ta buɗe ta nuna masa stairs. Kallon wajen yay shima a ransa yace (Da sauki ma tunda za'a bani wajen kwana baza'a korani ba). A fili kam yace, “To ina godiya, yanzu dai kafin dawowar nasu muje ki tayani yin salla, kafin sannan suma sun shigo sai na rakoki ki dawo”. Kallonsa ta ɗanyi, ganin yana son maidata wata ƙaramar yarinya. Wai ya manta ne takai 20+, tana da ilimin addini dana zamani, tama karance-karance. Tunda aka tsira bikin nan komai buɗe mata shi ake da sunan nasiha. Musamman Hajiya Shuwa sai abinda ta manta ne kawai bata faɗa mata ba a rayuwar aure... “Miye kuma na tunanin?”. AA ya faɗa cikin kunnenta. Ajiyar zuciya ta saki a hankali. Batare da ya sake cewa komai ba ya kama hannunta. Sai ta ƙi motsawa. Dawowa yay ya tsaya a gabanta, “Goyo kika so?”. Kai ta girgiza. “Ɗauka?”. Shiru tai dan saƙe-saƙen ta yanda zata zille masa kawai take a cikin zuciya. Shi ko sai ya ce, “Uhhmyimm”. Babbar rigarsa yasa hannu ya zare tare da hular damar duk sun gallebesa, ya dawo ta gabanta kawai, cak ya ɗagata daga ƙasa riƙe a hannunsa. Sai tai saurin kallonsa dan abun yazo mata a bazata. Ido ɗaya ya kashe mata, babu shiri ta kife fuskarta a ƙirjinsa tare da saka hannunta a kafaɗarsa ta dafe. Murmushi yayi kawai ya fara takawa a nutse kai kace ba mutum ya ɗauka ba. Haka ya dinga taka steps ɗin cike da ƙasaita har upstairs. Kai tsaye ɗakin dake matsayin nata ya kaita, duk da shi a ransa ya gama sakawa babu batun raba ɗaki, adai yi a gama kawai zai canja tsarin komai na gidansa. Sosai ɗakin yayi ƙyau, ga wani irin ƙamshin mai saka kasala na tashi a kowacce kusurwa. Wani irin shegen mayataccen royal bed ne aka saka, gashi an bisa da wata irin rumfa mai shegen ƙyau da idan ana sanyi ka shige ciki sai ka manta anayi. Shi kansa ɗakin yay masa ƙyau sosai. Saman gadon yaje ya ajiyeta, batare da yace komai ba ya juya ya fita. Ba'a wani rufa mintuna bakwai cikakku ba sai gashi ya dawo. Basket ɗin nan ne da kuɗin sayen baki a hannunsa. Ajiyesu yay a gabanta saman lallausan carpet ɗin gaban gadon mai kamar gashin mage gashi milk color sai ɗaukar ido yake. Idan ka taka kuwa ƙafarka nitsewa take a ciki. Kusa da ita ya zauna, ya kamo hannayenta cikin nashi ya rumtse. “Barka da zuwa duniyata a karo na biyu Besty. Gidanki na miki marhababika da shigowarki bayan tsohon shekaru daya ɗauka yana jiranki, da kuma baki zo ɗin ba zai cigaba da jiranki na har abada dan bazai taɓa amsar kowacce mace ba sai ke kaɗai da aka gina domin ke. Yanda UBANGIJI ya nuna mana wannan rana, ina roƙonsa ya sa mu gammu a aljanna tare kamar haka. Maanal kece Ajwaad, idan babu ke shima babu shi har abada......” Hawayen da take yi ne suka sauka akan hannunsa, ya ɗan zuba ma ruwan hawayen ido sai kuma yay ɗan murmushi tare da matsota jikinsa ya rungume. Bayanta ya shiga shafawa alamar lallashi. Kafin ya ɗagota ya share mata hawayen tas da faɗin, “Tom kuka ya ƙare haka, muje muyi alwala domin godiya ga ALLAH. Dare na ƙara yi kizo ki kwanta ki huta gajiyar biki okay”. Kanta kawai ta jinjina masa tana sauke ajiyar zuciya. Shine ya miƙar da ita, ya kama hannunta, closet ɗin ɗakin babba shima suka fara shiga kafin toilet. Komai an tsara mata na kayanta abin dole ya birgeka, su Amaal sunyi ƙoƙari. Bayin ma ƙaton gaske ne, sannan ya haɗu da komai na bayi irin na zamani. Sai wani ƙanshi yake dan shima yaji turaren wuta. Da taimakonsa tai alwala, dan tace tana da tsarki, shima dai yana da shi ɗin, dan haka bayan ta kammala shima yayo suka fito. Anan closet ɗin ya ɗauka sallaya da hijjab da yaga an tsarasu suma a nasu ɓangaren sannan suka fito. Shi ya shimfiɗa musu sannan yazo ya gyara mata mayafin lafayar da ƙyau. Sun gabatar da salla cikin nutsuwa, ya rufe musu da shafa'i da wutri. Sannan ya juyo ya dafa kanta yay addu'a da ya dace ango yayi, ya kuma sake cigaba da wasu addu'oin masu ratsa jiki da zuciya tsawon lokaci. Daga haka ya mata tambayoyi duk da yasan baida haufi a kanta tanan ɓangaren sam. Amma dai yayi ɗin dan yana son yasan a zuwa yanzu wane mataki take a neman ilimin. Yaji daɗi sosai jin bata zauna ba bayan rabuwarsu ma ta cigaba da neman ilimi. Dan haka ya tabbatar mata zasu cigaba da karatu a gida, zai kuma sakata wasu online class na addini suma dan ta ƙara samun sani da ɗammarar bautama UBANGIJI. Kanta a ƙasa tai masa godiya. Hancinta ya ɗan ja kaɗan, ya ce, “Nima kike ma godiyar?”. Murmushi tayi kaɗan, sai kuma a hankali ta ce, “Ka cancanci fiye da haka ma a gareni kai dukkan ahalinka. Tun ban san kaina ba kuke nuna min ƙauna. Ni da nawa a halin, kuna mana soyayya irin ta ƴan uwa na jini batare da kallon kun fimu da wani abun duniya ba tun ma a wancan lokaci. Abah ya zame ma iyayena Yaya, Oum ta zame musu aunty. Ku kuka zame mana yayu. Koda hararrarmu akai baƙwa ƙyalewa balle duka. Ku ɗin a garemu babban alkairi ne da baki yayi kaɗan ya furta. Bamu......” “Shiiiiii!!!” AA ya faɗa a hankali yana ɗaura yatsarsa akan lips ɗinta. Idannunta ta ɗago a hankali ta kallesa, shima kallon nata yake cikin wani irin kasalllalen yanayi. Yanda suke kallon junan a tare tsigar jikinsu ke wani tashi, zukatansu na narkewa a ƙirazansu. AA ne ya fara janye nasa a hankali, batare da yace komai ba ya yunƙura ya miƙe. Sallayar ya ninke, ya ajiye. Saman carpet ɗin nan ya koma ya zauna a ƙasa, a nutse a kwance ɗaurin net ɗin nan da akama basket ɗin. Ya kwashe ledar da aka zuba flowers ɗin saman gaba ɗaya ya ajiye gefe. Kyakkyawar kwali ne ya bayyana, sai milk na kwali guda biyu, sai wani ɗan basket ƙarami da kayan fruits an naɗe samansu da leda suma. da aka zuba a sama gefe. Sai kwalin pizza da shawarma da sandwich suma kowanne an naɗesa daban. Sai wani kwali ɗan babba da bai san miye a ciki ba, da wata leda itama a gefe ƙarama. Juyawa yay ya ɗan kalla Maanal, ganin tana wajen zaune har yanzu ya ce, “Bestie zo kiga”. Kallonsa ta ɗan yi, sai kuma yanda yay magana babu wasa yasa ta miƙe kamar wadda ƙwai ya fashema a ciki ta naɗe sallayar ta ajiye inda ya ajiye waccan sannan ta nufesa. Hannunta ya kama ya zaunar da ita kusa da shi. Kwalin farko ya fara buɗewa, kaza ce da akaima gashin ƴan gayu na musamman a ciki, sai gasashen naman rago a gefenta shima masha ALLAH. Ɗayan kwalin dabai buɗe ba ya buɗe, a mamakinsa sai yaga kaya ne a ciki na barci, nata da nashi duk da a naɗe suke, maidasu yay ya rufe kawai. Ya maida hankalinsa ga abinci yace wanne take so. Kanta a ƙasa tace ita ta ƙoshi. Taci abinci ɗazun. Bai takura mata ba dan yaga yau an koma salihai, tashi yay ya fita, babu jimawa ya dawo da kofuna sai ƙaramin plate. Milk ɗin ya zuba a kofi ya miƙa mata. Kanta ta girgiza sai ya ɗan harareta. “Baki so nayi koyi da MANZON ALLAH ne.?”. A hankali ta ce, “Ina so mana”. “To bismillah”. Ya faɗa bayan yasha madaran itama ya saka mata kofin a baki. Hannunta ta ɗaura akan nashi tasha a haka. Bai kuma barta ba sai da ta shanye tass. Shi ko ya ɗan ci sandwich ɗin dan yana sonshi sosai, ya ƙara shan madarar ya haɗe komai waje guda ya fita dasu. Babu wani jimawa ya dawo ɗakin. Ganin tana lullumshe idanu ya ce, “Barci?”. Kanta ta jinjina masa. Ya ce, “Okay buɗe kwalin nan muga.” Kwalin ta buɗe, ganin kaya a ciki sai ta kallesa. Kai ya jinjina mata alamar ta fiddo. Itama sai ta jinjina nata kan, a bisa tsautsayi tana ɗago na saman dake matsayin nata kawai rigar ta warware kanta. Ya subahannallah, ai Maanal bama tasan ta saki rigar ba, sai kuma ta juya da sauri ta kalla inda yake. Ganin yanda tai tsuru-tsuru yasa AA kauda kansa ya fuske kamar bai gani ba kafin ma ta juyo. Aiko sai ta wani sauke ajiyar zuciya, da sauri ta cikuykuye rigar da p ɗinta daya faɗo shima ta maida a kwalin. Miƙewa yay abinsa batare da yace mata komai ba ya nufi closet ɗin ɗakin, bai wani jima ba ya dawo hannunsa da wasu kayan barcin. A saman gadon ya ajiye mata, sannan yazo inda take ya ɗauke kwalin wancan kayan da ledan nan daya buɗe yaga magunguna ne a ciki.........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖7️⃣2️⃣ ______________ .......Haɓarta ya kamo ya sumbaci lips ɗinya. “Ga wasu kayan nan ki tashi ki canja ki kwanta ki huta goodnight”. Ya sakimmata fuska ya wuce yana ɗan murmushi. Sai da taji ya fice gaba ɗaya ya rufe mata ƙofar sannan ta wani sauke ajiyar zuciya mai nauyin gaske kai kace irin wadda ta kuɓuta daga hannun dodon nan. Kayan daya ajiye ɗin ta juya ta kalla a karo na farko, nan ma sai ta sake sauke ajiyar zuciya ganin su kam na mutunci ne. Amma waccan gantalalliyar riga ai ba'a magana, duk wanda ya saye ta ma ba ƙaramin ƙwallon ɗan is... Bane. Ta jima tana saƙe-saƙen ta kafin ta miƙe ta kwashi kayan ta nufi bayi. Ƙara gyara jikinta tai sosai kamar yanda Hajiya Shuwa ta ɗorata a layi, sannan ta saka riga da wandon na barci masu taushi sosai gasu basu wani kamata ba, duk da dai wandon iyakarsa gwiwar ƙafarta yafi dama-dama akan waccan rigar.. sosai ta sakama jikin wasu turarurruka masu sirrin ƙamshi da Amaal ta sanar mata sun ajiye mata su anan cikin bayin, tana ko buɗe haɗaɗɗen drawer ɗin glass dake bayin da aka cika da kayan gyaran jikin Hajiya Shuwa da turarurruka na wanka da sabulai sai ta gansu. Suma ɗin dai kala-kala ne dama Hajiya Shuwa tace mata sai tana gida kawai ko zata kwanta sannan zata sakasu, haka ma sai in tana sashenta kawai. In har zata fita koda sashen Oum ne kada ta shafa. Ita bata fahimci ma'anarsu ba, ta ɗauka kawai tsarin sakasu kenan shiyyasa ta bajesu a jikinta yanda ya kamata, tsabar rawan kai irin na amare ma kowanne saida ta ɗan taɓa kuma kala-kala ne fin goma sha. Aiko ya arrahaman, bayin kansa yasan amarya tayi shirin barci.... 😂To Manaluwa ALLAH ya rabamu da tsautsayi da aikin danganci🥱🤫🤭🤣🤣 _______★ A dai-dai lokacin da AA ke fita a ɗakin Maanal da wancan kaya dai-dai nan Mamy ta farka a barcin da allura ta sanyata. Maman Saheeba kawai ta gani a gefenta tana latse-latsen waya. Cikin sanyin murya irin na mai tashi a barci ta kira sunanta. Maman Saheeba ta juya da sauri ta kalleta, sai kuma ta saki murmushi da faɗin, “Lah Aunty kin tashi? Bara na kira Aunty Babba ALLAH yasa basuyi barci ba”. Riƙo hannunta Mamy tayi a hankali tana girgiza mata kai, sai kuma ta buɗe baki da ƙyar ta ce, “Ajwaad fa?”. Ɗan zuba mata ido Maman Saheeba tayi, sai kuma ta taɓe baki da faɗin, “Yana sashensa mana Aunty, yazo miki sallama kina barci ai”. Zaramm kuwa Mamy ta tashi zaune jikinta na rawa. Sai kuma jiri ya kwasheta luuuuu ta tafi zata faɗi dole ta koma ta kwanta tana dafe kai. Muryarta na fita da ƙyar ta ce, “Shine kuka barshi Nana? Shine baku tasheni ba”. “Aunty kenan, wa kike ganin ya isa a cikinmu ya hana Ajwaad zuwa ga matarsa ne? Sannan ke kuma taya zamu tasheki baki da lafiya....” “Bani wayata”. Mamyn ta faɗa da ƙyar. Miƙewa Maman Saheeba tai ta ɗauka mata wayar, haka Mamy ta amsa duk da daƙyar ma take iya kallon screen ɗin wayar saboda ciwon kai da idanunta dake gani bishi-bishi ta shiga lalubo sunansa. Dialing no ɗin tayi, cikin sa'a kuwa ta shiga, dan haka takai kunne tana jiran a ɗaga. Sai dai me harta tsinke ba'a ɗaga ɗin ba. Sake kira tayi, amma nan ma tsitt kake ji. Haka ta dinga jera masa kira a dukkan layukansa ma amma anƙi ai picking. Sosai ranta ya ɓaci, hankalinta ya tashi. Gefe ga Maman Saheeba na faɗin, “Aunty kema kin san bazai ɗauka ba shi da ke da amarya duk da dai ba sabon waje bane, amma ai bazasu barsa haka ba sai da sabon shiri...” “Nana rakani sashen nasa”. Jimmm Maman Saheeba tayi, sai kuma ta ce, “Okay muje”. Ta ajiye wayar tana miƙewa. Itama Mamy ɗin ta taƙarƙara ta miƙe sai juwa kuma ta ɗebeta ta maida akan gadon. Kan ta dafe sosai, dan ya wani sara mata na bala'i. Muryarta can ciki ta ce, “Bari juwar nan ta sakeni Nana ban ruwa”.... Mamy dai juwa ta hanata motsin kirki, dole Maman Saheeba ta bata shawarar yin wanka ko hakan zai taimaka mata, batai musu ba tace ta haɗa mata ruwan. Aiko haka ta miƙe taje ta haɗa mata sannan ta dawo ta taimaka mata ta kamata har cikin bayin. Dama ta ajiye mata komai da zata buƙata ta fito ta barta. Wayar sahiba ta kira sukai ƴar magana ƙasa-ƙasa ta kashe. Sama-sama Mamy tai wankan nan, dan hankalinta gaba ɗaya yana wajen AA ne, ta riga tama kanta alƙawarin bai isa ya kwana da Maanal ɗin ba yau, wanda yay a baya har ta samu ciki yayi na ƙarshe. Kai itafa a wannan daren take son Ajwaad ya saki Maanal saki uku duk ma wacce za'ai sai ayi, shima kuma Fawzan sai ta tabbatar masa itace ta haifi abinta shi da duk masu ɗaure masa ƙugun yin auren. Haka ta lallaɓa tai wankan sama-sama, tai kiran Maman Saheeba dake ƙofa tana jiranta. Shigowa tai ta taimaka mata suka fito, da taimakonta ta ɗan shafa mai kaɗan saboda bushewar jiki, ta bata doguwar riga ta saka, ta kuma haɗa mata tea tace tasha ko zata ɗan samu ƙarfin jikinta. Batayi musu ba kuwa ta amsa tasha dan itama ƙarfin take nema ruwa a jallo. Bayan ta gama sha magani ta bata shima ta sha, tace mata taɗan kwanta yabi jikinta sai su tafi..... Hummmmmmm!!!!! Ashe anan ma ya kamata muyi addu'ar ALLAH ya kiyaye tsautsayi da gangancin ba wajen manalu kawai ba🥱🤣 _______★ Lokacin da kiran Mamy ke shigoma AA a waya duka wayoyinsa suna anan ɗakin Maanal kuma a silent suke. Dan yau ko a vibration bai saka su ba. Shi kuma yana can a nasa ɗakin bayan ya ajiye kayan barcin nan da ledar magunguna a zuciyarsa yana saƙa yanda zai sille RK da safe dan ya tabbatar iskancinsa ne saka kayan barcin nan da maganin ya faɗa bayi yay sabon wanka da shirin barci shima. Ya baɗe jikinsa da turarurruka masu shegen ƙamshi da saka zuciya nutsuwa daya tanada domin wannan rana kawai. Ya gyara sumar kansa da kwantaccen sajensa, sai lokacin ma ya ɗan shiga neman wayoyin sai ya tuna ya barsu ɗakin Maanal. Baiyi niyyar koma mata yanzu ba, yaso sai tayi barci dan yanda take a firgicen nan baiso hanata samun nutsuwa a barcinta kasancewar yana son bata damar sakin jikinta yanda ya kamata. Fitowa yay domin ɗaukar wayoyin sai ya dawo ya ɗan kwanta anan har sai yai barci ya koma. A dai-dai lokacin da yake tura kai cikin ɗakin bakinsa da sallama ciki-ciki ita kuma Maanal ta fito a bayin bayan ta gama leƙenta ta tabbatar bai dawo ba. Sai dai me tana gama rufe ƙofar ta juyo kawai ta ganshi tsaye a ƙofar shigowa ya wani zuba mata ido. Cak ta tsaya kamar yanda yake shima cak a tsaye. Sai kuma ta duƙar da kanta tare da runtse ido tana jin kamar ta zura da gudu ta koma wani sashe na zuciyarta na kwaɓarta da tuna mata AA ne fa Bestyn ta mijin nan nata da suka kasance tare a Chaina, a ɗaki ɗaya, gado ɗaya ba wani sabo daban ba. Shi ko mayataccen ƙamshin turarenta ne ya wani irin dokar masa brain gaba ɗaya kasalar jiki data zuciya ta dabaibaiyesa cikin. Ga ƙyawun da kayan barcin sukai mata tamkar an zanata a cikinsu. Wani irin sulululu... Jinin jikinsa ke sulalewa a cikin jijiyiyinsa. Cikin sakanni komai na jikinsa ya canja. Wanda suke a sume domin gajiya duk suka farfaɗo. Idanunsa kam sun kasa barin kanta, sai ma takawa daya shiga yi a hankali har inda take. Yana gab da isowa ta juya da sauri da nufin komawa cikin bayin. A wani irin hankali ya kama hannunta, muryarsa na shaƙewa ya furta, “Ina zaki je?”. Yay maganar yana juyo da ita gaba ɗayanta ya tsayar a gabansa cak. Maimakon bashi amsa sai ta ɗago idanunta da suka tara ƙwalla ciki ta kallesa. Kauda nasa yayi, sai dai ina zuciyarsa tabbatar masa take bazata bashi haɗin kai ba. Hakama gangar jikinsa gaba ɗaya. Kuma harga ALLAH bai niyyar taɓata a yau ba dan shi kansa a gajiye yake barci kawai yake son yi. Amma a yanzu daya kasance a cikin yanayin ƙaulani bashi da tabbacin hakan sai abinda ALLAH yay kawai. Jawota yay jikinsa ya rungume ko zai ɗan samu sassauci, amma ina komai ma sake yin tashin gauron zabi yayi cikin ƴan sakkani, farashin ya sauya daga ainahin farashinsa. Tuni yama manta da wani batun ɗaukar wayoyi da komawa can ɗakin. Cirota yay da ƙyar a jikin nasa ya kaita bakin gado ya zaunar, sai kuma yay mata nunin ta kwanta. Kamar mai shirin yin kuka ta ce, “Bana jin barci”. Murmushin gefen baki ya ɗan saki, sai kuma ya girgiza kansa kaɗan. Sake matsowa yay kusa da ita sosai, ya matsota ya saka a cikin jikinsa. A tare suka sauke ajiyar zuciya, hannunsa na shafa gadon bayanta ya furta, “Yau gadin gida zamuyi ke nan?”. Ƙasa-ƙasa ta ce, “A'a kai ka kwanta kayi barci”. “Ke kuma fa?”. Shiru tayi taƙi yin magana. AA da dariya ke cinsa sosai yana dannewa dan wannan asanyayen data koma abin dole ya baka dariya, “Anya wannan amaryan rowanta baiyi yawa ba?”. Baki ta ɗan tura kaɗan, sai kuma ta ɗan ɗaga ido ta kallesa, shima kallon nata yayi, amma tai ƙoƙarin janye nata dan bazata iya kallon juyayyun idanunsa ba. Ƙin bata damar cire idanun nata yayi, ya sarƙesu da nata dake cike da rauni da fargaba. Rau-rau suka cika da hawaye, maimakon ya tausaya mata ya barta sai ma ya sake narke nashi dake cike da salon shauƙi da buƙata. “Miyasa bazaki iya cigaba da kallon idona ba Besty? Babu abin da zai same ki a cikin su sai natsuwa.” Cikin raɗa, da muryarta mai rawa ta ce, “Ina jin tsoro”. “Why? Zaki ji tsoro Maanal, Ajwaad ne fa, Bestyn ki. Ni ba ƙarfe bane mai dukan farin ciki ko ruguzashi. Ni ruwa ne, mai goge tsoro, in shayar da kwanciyar hankali musamman a duniyarki”. A hankali hawayen da suka cika mata ido suka gangaro, sai kawai ta samu damar lumshe idanun tare da kife fuskarta a ƙirjinsa. “Kalamanka nasa zuciyata tana bugawa da sauri, kamar tana son faɗin wani muhimmin abu a kanka, amma bana jin kalmanta sam.” Murmushi ya saki mai taushi, tare da motsawa ya ɗagata cak ya maida saman gadon ya shimfiɗar, kanta na a saman damtsen hannunsa, sai ya ɗan rufu a kanta hannunsa kwance a saman ƙirjinta ya kai yatsun yana wasa da gashin kanta mai laushi da santsi........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖7️⃣3️⃣ ______________ ........Gefen fuskarta ya sumbata kaɗan, cike da raɗa ya furta, “Kar kiji komai, zan saurari bugun zuciyarki har sai ta tsaya cikin nutsuwa. Zan jira fitar sautin kalmanta har su bayyana a cikin kunnuwana. Kin manta na faɗa miki zan iya jira na har abada ba a matsayin mijin da ke da HAƘƘI ba, domin ke nake kallo a matsayin ke ba surar jiki ko manufar sauke buƙata ba”. Numfashi ta sauke mai ɗan nauyi, sai kuma ta buɗe idanunta kaɗan tana kallonsa yanzu, cikin ido. Idonta yana ɗauke da yanayin nuna tausayawa a gareshi da kuma ɓoyayyar fargaba. Shi ko kallonta yake kamar yana karanta rubutu a cikin idanun nata. Murmushi ya mata mai nauyi da isar da saƙo kakkaifa, ita ma sai ta maida masa murtani a karo na farko. Ya lumshe idanu ya sake buɗewa saboda murmushin nata ya shigesa, cike da iya sarrafa harshe da wayo cikin siririyar murya ya furta, “Na fahimci idanunki suna cike da tambayoyi. Bari na amsa su da yanayin da kika fi buƙata a maimakon magana. Ki ce da ni kawai (Kana tare da ni Besty?). Niko nayi alƙawarin zance da ke, (Har abada)”. Murmushi ta sake sakar masa a hankali, zuciyarta na ɗan sakewa, gangar jikinta na rage tsoron, haka ma bugun zuciyarta na saisaita a cikin ƙirjinta. Kanta ta kauda gefe a cike da kunya, ciki-ciki ta furta, “Kana da wayo sosai”. Murmushin yayi shima, sai kuma ya rungumeta a hankali. Babu matsawa. Babu gaggawa. Sai nutsuwa da shauƙi mai sanyi, a cikin kunnenta ya ce, “Duk wayona na kaiki ne, keda kika ɗauka buhunnan alƙawurra gashi kina neman ɓigewa da zame-zame.” Ƙoƙarin janye jikinta tayi, sai ya hanata yin hakan ta hanyar sake rungumeta da ƙyau. “Ina kike ƙoƙarin guduwa? Bayan naji wani abu mai sanyi yana ratsani, kamar numfashinki. Rungumarki ce kuma tamkar addu’ar da ta yi karo da cikar amsar da nake nema. Ina so ki cigaba da zama a haka a kirjina, ba dan yau kawai ba, sai dan in cigaba da tuna cewa kece sassanyan lambun da zuciyata take so ta huta daga yau har zuwa ƘARSHEN RAYUWA. Na miki alƙawarin in sha ALLAHU zaki cigaba da kasancewa anan. A duk lokacin da duniya ta rikice, zan ajiyeki a wannan mafakar ta jikina babu mai damunki koda da harara”. Hawaye ne suka gangaro mata a hankali, tsigar jikinta na ƙara tashi saboda salon da yake mata a cikin gashi mai nauyi ne. Muryarta a ƙurya sosai ta ce, “Kafin wata rana ina kallonka ne a matsayin garkuwa ta, amma a yanzu sai na ji kamar zuciyata na rawa da zama cikin ƙaulanin ƙila wa ƙala musamman a gaɓar tuna rana mai girma da tarihi ya ajiye mana”. Fuskarsa ya cusa cikin wuyanta, cikin dunƙullen amo ya furta, “Ki bar ni na lallaɓa maki tunanin da ke yawo cikin gangar jikinki, na shafe miki wancan tarihin dake a zuciyarki, na ajiye miki sabon tarihin da zan tabbatarma duniya ke ɗin SARAUNIYAR mata ce. Tanadina mai girma ne a kanki, mai kuma muhimmancin da zai fitar da saƙon daya daɗe AJIYE A DUHU ne Maanal. Ki yarda da ni, duk wata fargaba da ta zo da tsoro ko rashin tabbas, zan shafe ta a yau cikin wannan daren. Ina taɓa gangar jikinki ne tamkar yadda ake taɓa ZINARE a tsakiyar talalaɓuwar ƙasa. Saboda a cikinki akwai daraja da tsarki da bai kamata a yi gaggawa da shi ba.” Ajiyar zuciya ta sake saukewa, fargabarta da tsoro na sake daidaituwa a cikin gangar jikinta. Ɗagowa tai a hankali ta zuba masa ido, shima kallon nata yake a cikin ɗan hasken ɗakin mara ƙarfi. Lips ta motsa a hankali zatai magana ya ɗaura yatsarsa a kansu yana wani lumshe mata idanun da buɗewa. “Ba sai kince komai ba. Idanunki suna gaya min abubuwan da baki ba zai iya furtawa ba ma. Na ga fargaba, tsoro, juyayi, tausayi, rauni, karaya, amma na fi ganin ƙauna da sha’awa mai tsarki.” Idanu ta zaro sosai. Ya kashe mata ido ɗaya. “Yes! Na ga wata murya a cikinsu da ke cewa, (KA KULA DA NI! KA BANI GARKUWA!) kuma na rantse, zan kula Besty, zan baki garkuwa daga ɓangaren kowanne abun hari kina barci ko ido biyu..” Sosai ta wani kalar lumshe idanu tana ɗan murmushi, dan yanda bakinsa ya buɗe yake zuba zance sai take jin shauƙin hakan. Shima murmushin yake, sai kuma ya kai yatsarsa a saman idanunta yay kamar yana sosawa, hakan ya sata ta ɗan lumshe ta sake buɗewa a cikin nashi. Shima lumshe nasan yayi ya sake buɗewa a cikin nata. “Idanunki sunyi shiru, amma tawa zuciyar nata amsa dukkan abinda suke son isarwa. Bari mu kalli juna har duniya ta manta da lokaci. Saboda ni da ke mun ishi juna a wannan ƙyaƙyƙyawan dare har zuwa sassanyar safiya. Kice kin amince ni kuma zan baki tabbaci”. Cikin wani irin tausayinsa da kasalliyar murya ta ce, “Na amince” ta faɗa tana ɗan sumbatar lips ɗinsa, sai kuma tai yunƙurin ƙwace jikinta zata juya dan kunya. Sai kawai ya wani riƙota da saura ya ɗaura tausasan lips ɗinsa akan nata. Alhmdllh kamar yanda yay fata batayi musu ba, sai ma ajiyar zuciya da take saukewa a jajjere. Sannu a hankali ta miƙa wuya tare da sake shigewa jikinsa harma da maida murtani, hakan sai ya ƙara masa ƙaimi da armashi, gaba ɗaya yaji duniyar tai wani irin zama shirun da su kaɗai yake zaton sun rage a raye a cikinta..... (Ikon ALLAH AA mu duk mun mutu kenan, kai dai AA ka dinga tsoron ALLAH ☹️🥱😏)... _____★ A lokacin da can AA kema tunanin duk mun mutu sai shi da Manaluwa gyatumarsa ta haihuwa Mamy ce a yanayi irin na matattu, dan duk yanda taso zuwa sashen nasa da alama jiri bazai barta ba. Cike da zuga Maman Saheeba ta ce, “Yaya kiyi kwanciyarki kawai bara ni naje na kira miki shi kawai. Dan wannan juwar zata iya kadaki a hanya”. Cike da gamsuwa Mamy ta amince, Maman Saheeba ta miƙe ta ɗauka hijjab ta zura ta ɗauka wayarta, “Ki ajiye wayarki a kusa idan yay gaddama zan kiraki”. Kai Mamy ta jinjina mata kawai. fitowa daga sashen Maman Saheeba tai, ta nufi sashen AA. Tana zuwa kofar kitchen ɗin sashen ta baya Saheeba da Nuratu da'a daren nan tazo gidan duk ta rame tai duhu na tsaye na jiranta. Murmushi suka sakarma juna, ƙasa-ƙasa tace ku muje. Sai da suka gama bin gidan da kallo suka tabbatar ko'ina tsitt hatta masu gadi sun kwanta sannan sukai wuff ta suka shige ciki. Cikin sa'a kuwa ƙofar a buɗe take. Cak Mamman Saheeba ta tsaya tana bin kitchen ɗin da kallo saboda ta cikinsa suka shigo, itam Nuratu sai ta tsaya tana kallon komai, dan kuwa dai komai yaji, daka gani kuma kasa na ƴar gata ne. Maimakon su wuce abinsu sai Saheeba catai, “Eh lallai wannan daka gani kasan kuɗin Ajwaad ne da aka wawura bara muga store ɗin shi kuma uwar mi suka ajiye mata tunda anje an tile kayan gara sashen haɗamatu (Wai Oum). Nuratu batai niyyar shiga ba, sai ta ja kujerar work table ta zauna, ga ƙasan zuciyarta na cigaba da bata shawarar ta koma karta biye ma su Mamanata. Amma gefen sheɗaniyar na angizata akan bawani nan taje taga ƙwal uwar daka... A haka Saheeba da mamansu suka fito suka sameta, sai faman taɓe baki suke dan sun rasa abin kushewa acan ɗin ma. Miƙewa kawai Nuratu tai suka shige ciki, Mammansu na ayyana a ranta ai wlhy ko tsinke bazasu sayama Nuratu ba suma shine zai yi komai kamar wannan dan sun san shine yayi. Sun sami falon komai a kashe, Mamman Saheeba ta haska fitilar wayarta ta kunna ta falon. Sai ta shiga leƙe-leƙen bedrooms ɗin ƙasan tana faɗin, “Kuyi maza ku sassaka mu haura saman kafin suji motsin mu”. Da to Nuratu da Saheeba suka amsa suna buɗe wasu ƙullikan tsuma suka shiga cusawa a cikin kujeru, sai rubutu a gora shima suka yayyarfa, sai da suka gama komai tsaf suka haura sama harda maman tasu...... ALLAH ka rabamu da mugun ji da mugun gani dai to🥱😜😂🏃. _______★ Sannu a hankali salon wasan ya fara canjawa, jikin Maanal ya fara rawa, tsoronta na dawowa fresh a zuciya. Ƙoƙarin janye jikinta take amma babu dama, ga baki ma ya rufe mata ruf da nashi ba damar magana. Dai-dai yana gama ɓalle illahirin botiran rigarta ya finciketa yay wurgi da ita Maanal data fara shiga gigita dan Alaramma AA ya fara zuwa inda ake masa rowa ta sake ƙoƙarin fincike jikinta ya sake nuna mata ina ai ta riga ta shiga tarko kuma, ba kuma yaji baya gani sam. Siffofin komawarsa kurma, kuma makaho suka fara tattara kansu. A dai-dai gaɓar ya gama rabasu da garkuwarsu daga ita har shi, ALLAH ya bama Maanal sa'ar fincike lips ɗinta da jikinta tana ƙoƙarin matsawa ya riƙota, ta fashe masa da kuka. Cikin matuƙar gigitar roƙo da magiya ta ce, “Wlhy bazan iya ba! Ka tausaya min na tuba Yaya Ajwaad na tuba.” Ƙasa-ƙasa muryarsa a dasushe kamar tata shima a raɗa ya ce, “Idan na barki mutuwa zanyi Maanal”. “Wlhy nima mutuwa zanyi Ajwaad”. “I'm sorry”. “Ka riƙe Sorryn ni ka bani salama”. “Idan na baki ni taya zan samu tawa salamar. Ki zama mai adalci da tausayi”. “Na shiga uku, da gaske ka zama kurma da makahon da kai alƙawarin komawa? Kafa min alƙawarin barina na har abada”. “Maybe a lokacin dana faɗa aljanuna ne, amma Maanal wake alƙawari zana rubutu akan ruwa mai gudana! Bayan yasan in ma yayi kamar abu ne bamai yiwuwa ba”. “Ka tuna kai fa Bestyna ne”. “Hakan ne zai sake bamu damar zama AMINAI na musamman na kuma har abada”. “Bazaka haƙura ba kenan”. “Idan na haƙura ni wazai bani haƙurin”. “Besty!”. “Na'ama Bestyn Bestynsa”. Baki ta sake buɗewa zatai magana ƙarfin kukanta na ƙaruwa ya ce, “Shiiiii!!!” ya sake maida lips ɗinsa akan nata. Yayinda yake wani kalar bata saƙonsa mai nauyi da karya garkuwar jiki, cikin gushewar tunani ya sake himmatuwar isa inda ya daɗe a cikin mafarki da hasashen zuciya kawai.. A dai-dai lokacin su Maman Saheeba ke ƙarasa hawawo upstairs ɗin, a kuma dai-dai nan Maanal ta fisge lips ɗinta a karo na biyu ta fashe da kuka mai ƙarfi na azaba da ƙwala kiran sunan Oum da Ammie a tare cikin matsamnaciyar gigita.........✍️ Subahannallah, Jamila tayi ɓari, aranar jajibiri😆😛. A ririya-ririya Kamila💃 ƴar sarƙar wuya... Iya nan na iya🤣😜🏃 *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖7️⃣4️⃣ ______________ .........Ai wani irin cak Maman Saheeba da Saheeba da Nuratu suka tsaya kamar waɗan da aka dakama tsawa, sai kuma suka kalla juna, mizai faru sautin disa-sashshiyar muryar AA ce ta daki cikin kunnuwansu. Tare da fitar kukan Maanal dake magiya da roƙo da neman ɗauki harda sunan Mamy kanta amma tabbas AA ya zama kurma, kuma makawo dan yau dai sai addu'a kawai..... Rikica, Mama da Saheeba sukaji a ƙasa, da sauri suka kalli wajen suma nasu jikunan na rawa. Al'amari mai matuƙar nauyi da girma na cigaba da shiga cikin kunnuwansu. “Na shiga uku! Nuratu! Nuratu!”. Suka shiga faɗa suna kamo Nuratu datai wanwanr a ƙasa, cike suke da tashin hankali da ƙunci da baƙin ciki ƙololuwa dan duk wani mai shekarun girma irin Maman Saheeba dama Saheeba ɗin yaji wannan kukan da Maanal keyi har tana yin kamar zata shiɗe yasan ina..... Sosai jikin Maman Saheeba ke sake rawar mazari, wlhy da tasa abin kunnayensu zasu zo suji musu kenan da bata yarda sunzo ɗin ba. Gashi nan basu gama saka maganin ba sunji abinda zai yi maganinsu. Amma shegen bokan nan fa ya tabbatar mata da yayi aiki babu abinda Ajwaad zai ma yarinyar nan a wannan daren, acewarsu ma barci zai sakar musu har suzo suyi abinda zasu yi su fita wani bai sani ba, dan ita kanta Mamyn abu ta zuba mata a shayin data sha kuma bokan ne ya bata. ______★ Duk rakin Maanal a zuwan farko tamkar wasa farin girki ne ga Ajwaad, dan ta riga ta firgita matuƙa taƙi bashi damar samunta yanda yake so. A nashi ɓangaren shima yanayin halin daya daɗe a ciki ya sashi samun nutsuwa bada wani nisa ba. Koda ya matsa daga jikinta yanda ta cigaba da masa kuka kansa kawai ya girgiza, dan shi yasan ba'ai komai ba. Kai bama a fara wasan ba na gaskiya dan sharar hanya kawai akayi. Komai baice da ita ba, sai ma miƙewa da yay yana tafiya a dudduƙe saboda cikinsa dake wani irin sabon ƙullewa. Bayi ya shiga ya haɗa ruwa masu zafi, koda ya dawo cike da dauriya ya ɗagata cak. Kuka ta sake sakar masa, cike da tsiwa tana faɗin ita ya sauketa ya daina taɓata zata iya. Bata so ya barta. Bai kulata ba, sai da ya direba a jacuzzi ɗin tana ƙoƙarin miƙewa tare da sakin kuka ya riƙeta da ƙyau. Kuka ta sakar masa sosai wai zafi. Cikin shaƙaƙƙiyar muryarsa ya raɗa mata, “Faɗan da ba'a fara ba har kike tunanin maida duka, dama kin hutar da kanki dan komai ba'a fara ba yarinya. Yaushe ma aka kai maƙura balle kiji zafin, daga tonon farko kawai” Da sauri Maanal ta kallesa hawaye shaɓe-shaɓe a fuska duk da ba komai ta fahimta ba a kalaman nasa ta gane wasu sarsi. Gira ya ɗage mata yana sake ƙanƙance rinannun idanunsa dake cike da fitina. Sai kuma ya ɗan cije baki saboda cikinsa sake ƙullewa yake yi. Ita kanta ta fahimci akwai abinda ke damunsa. Amma haushin abinda yay mata da ƙin saurarenta da yayi da rashin tausayi yasa taƙi magana. A ƙasan zuciyarta kuwa mamaki take ashe ma ba wata wahala sosai da ake wani sha, dan zafin da take ji ba wani ƙololuwa bane matuƙa kamar yanda take ji ana faɗa, amma dai tana jin zafin tabbas. Haka ya gama kimtsata cikin dauriya ya sata tai wanka shima yayi sannan ya sake ɗakkota suka fito. Saman kujera ya ajiyeta ya kwashe zanin gadon, duk da yasan bazai kasance da damuwa sosai a tare da shi ba amma dai zasu fi samun nutsuwa idan ya canja ɗin. Sai da ya maida mata kayanta tana faman masa ciccika bai kulata ba ya maidata a gadon ya rufa mata duvet. Sai faman sauke ajiyar zuciya take na uban kukan da taci wanda raki yafi yawa. Shi dai yama kasa kwanciyar saboda cikinsa da yay masifar ɗaurewa. Takai yama kasa zaman kujerar ya koma ƙasan lallausan carpet ɗin gaban gadon kawai. Tun yana ɗaukar al'amarin zai iya lafawa harya fara fin ƙarfinsa. Dan wani sabon yanayi jikinsa ke ƙara ɗauka tamkar ma baiyi komai ba. Ga wani irin rawa da jikin nasa ke ƙoƙarin fara yi. Numfashinsa kansa wani irin fisga yake fita a cikin ƙirjinsa, amma kasancewarsa jarumi gwanin dakewa a nutsensa yake a zahirance. Jin abin na neman fin ƙarfinsa dole ya juya ya ɗauka wayarsa daya aje saman side drawer, ko a lokacin bai wani lura da tarin miss call ɗin Mamy ba ya shiga ƙoƙarin fara bincike akan minene ya kawo masa hakan, ko dan ya samu ya rage damuwarsa ne yake jin ciwon?. Da ƙyar ma yake iya gane bayanin saboda ciwo dake cigaba da cin ƙarfinsa. Sakamakon da binciken ya bashi ne ya sashi ji a ransa akwai matsala. Saboda ya tabbatar Maanal ta riga ta firgita, idan yace zai sake zuwa mata to wlhy zata iya sume masa ma shi kuma yayi imanin a karo na biyu bazai iya mata sassaunci ba mai gaba ɗaya zai yi ba kamar a farko ba, mai gaba ɗayan ma irin na babu ragi babu ragowar nan. Wayar ya ajiye ya sake kifewa na tsawon lokaci, wlhy ji yake kamar bazai ga wayewar garin gobe ba idan bai samu mafita ba. Dole ya sake ɗaukar wayar saboda shawarar da zuciyarsa ke basa akan kiran RK ko zai bashi wata mafitar bayan wannan. Sai da wayar ta kusa tsinkewa RK ya ɗauka, cikin yanayin barci ya ce, “Waye?”. Ɗan jimmm AA yayi, kafin acan cikin maƙoshi a kuma dakensa ya furta, “Ajwaad”. Tsai RK yayi shima, sai kuma a hankali ya janye Nuwaira dake jikinsa dan wayo ya mata suka tafi masaukinsa bayan sun ma AA rakkiya. A nutse shima ya furta, “Are you okay?”. Da ƙyar AA ya ce, “No!”. Gaban RK ya ɗan faɗi, Daga gadon ya sauka gaba ɗaya ya nufi ƙofar fita, sai da ya buɗe ya juya ya ɗan kalla Nuwaira, ganin barci take sosai ya fice. Sai da ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun falon ya kunna lamp dake gefen kujerar sannan yay ɗan gyaran murya, dan yana jiyo saukar numfashin AA a wahale duk da yana ƙoƙarin dakewa. Cikin serious sosai RK ya ce, “Ajwaad akwai matsala ne?”. Shiru AA ya masa na tsawon sakanni kamar bazai ce komai ba sai zuwa can ya ce, “Cikina ke ciwo, ina jin kamar zan mutu. Ka faɗa min me zanyi da zan samu sassauci?”. Zama RK ya gyara, babu wasa a tare da shi sam ya ce, “Ajwaad! Ga matarka a kusa da kai mi kake jira? Kaima kasan minene ma'anar wannan ciwon cikin, dan duk da baka kasance likita ba kanada ƙoƙarin bincike akan abubuwa”. “Rafeeq a tsorace take matuƙa, kuma na samu nutsuwa, sai dai ban kai gareta gaba ɗaya ba saboda ruɗanin data shiga har tana yi kamar ma numfashinta zai bar gangar jikinta. Domin wancan tsoron har yanzu yana a tare da ita.” Cike da nazari RK yace, “Ajwaad karka damu da tsoronta, ka samawa kanka nutsuwa kawai, idan ba hakaba akwai matsala. Dan wannan halin da kake gani kana ciki komai zai iya faruwa da kai. Ba kamar na baya bane da kake shiga ka fita. Nutsuwar farko daka samu saboda tsahon shekarun daka ɗauka a ciki ne dole dama hakan zai kasance maka. Amma a zuwa na biyun jikinka da zuciyarka dama ƙwaƙwalwarka zasu samu dukkan dai-daiton daya dace. Kai a yanzu ka fita kasancewa a haɗari saboda ba shine na farko a gareta ba....” Sai da AA ya runtse idon azaba da cije lips kafin cikin ƙarfafa kai ya furta, Rafeeq! Manaal is actually a virgin!”. Babu abinda ya faru a waccan ra...nar”. ya ƙarasa da ƙyar saboda wani irin ƙullewa da cikinsa yayi. A hankali RK ya wani irin lumshe idanunsa yana sakin murmushi mai sanyi da sauke ajiyar zuciya mai nauyin gaske, a da hasashe kawai yake yi amma yanzu yaji tabbaci, tabbas wannan shine plan c, dole ne kuma yayi duk yanda zai yi AA ya yajema Maanal gaba ɗaya a wannan daren kodan ahalinsu dana Mamy dake a gidan su san hakan suma. Dan abu ne dai na sirri ko, amma ALLAH sai ya fasa ƙwai anyi shagalin jinsa gobe a gidan Darma. Dan hakan zai wanke AA da Maanal ɗin kanta ya cirema kowa shakku, masu aibantata suji kunya. Cikin ture tunaninsa ya ce, “Ajwaad maza ka tashi kaje ga iyalinka, ka ajiye wani tausayi gefe dan hakanne kawai zai baka damar tabbatar ma Maanal kai ba mai laifi bane a gareta, a binda take tunanin ka ƙwata da ƙarfi ita kuma ta rasa yana a tare da ita. Abinda take tunawa taji tsoro yana nan dai. Karka damu babu abinda zai sameta yanzu kaine a gaɓar haɗari. In sha ALLAHU da asuba zanzo da Nurse ta duba ta. Maza ka tashi baka da isasshen lokaci dan yanayi ka ya tabbatar min ka fara zuwa matakin ƙarshe”. AA yasan gaskiya RK ya faɗa masa, dan numfashinsa har ya fara fisga kamar mai shirin suma. Anan ya jefar da wayar, ya juya da ƙyar yana kallon Maanal da barcin wahala ya kwashe. Da yake kuma wayar da yake yi magana yake a hankali bata ko motsa ba. Ji yay wani karfi yazo masa, ya kalla agogon dake a side drawer ƙarfe uku da mintuna biyar, gaba ɗayansa ya yunƙura, ya saluɓe bathrobe ɗin jikinsa ya yar anan, ya yaye duvet ɗin da take ciki ya kwanta kusa da ita. Hargitsatsun idanunsa ya ƙura mata, zuciyarsa na bugawa da ƙarfin da bai taɓa ji ba. Hannunsa ya dafa gefen fuskarta a hankali kamar yana lallabar zuciyarta. A firgice ta farka sakamakon saukar hannunsa akan fuskarta dan dama barci bamai nisa bane, jikinta na ɗan rawa ta juyo tana kallonsa da hargitsatsun idanunta da suka sha kuka ga barci data fara. Baki ta buɗe da nufin yin magana a firgice ganin ya sake kwanto jikinsa a nata. Bakinta ta motsa kamar za ta yi kuka, sai ya ɗan matsa baya kaɗan, yana fitar da numfashi mai ɗumi akan fuskarta, da matuƙar zurfin murya mai taushi da santsi kamar ba tashi ba ya ce, “Shhhiii!!... kada ki ce komai, Manaal... ki barni na karantar dake cikakken karatuna daga kundin littafina dana daɗe da tanada domin ke kawai...” Sai ya runtse ido, ya sake matsawa a hankali ya sumbaci laɓɓanta da tausayi, kamar yana tambaya ne ba tilastawa ba ya cigaba da faɗin, “Ki bar zuciyarki ta saurari tawa. Kada ki ce komai, bari zuciyata ta gaya miki babban ajiyayyen saƙon da take ya faman ajiyar. Domin dai-dai wannan shiru tafi buƙata...” Kai ta shiga girgiza masa, hawaye kuwa tuni sun ɓalle, ta sake yunƙurowa zatai magana ya ce, “Shhhiiii!!! ki bar ni in koya miki KARATUN da ya fi kowace magana Please My half...” Kafin ta sake yunƙurowa ya rufe mata baki ruff da nashi, ya riƙe mata hannun da take ƙoƙarin kai masa duka da tureshi, zuciyarta ko wani irin mugun bugawa take har yana ji, jikinta ya fara rawa sosai sai ga hawaye na shararowa har akan tashi fuskar. Eh lallai ashe Maanal bataga komai ba ɗazun, dan tamkar wasan yara akayi a yanzu ne AA ɗin ke tabbatar mata da kansa a Ajwaad Aliyu Abubakar Darma. A yanzu ne ya zama kurma na gaskiya kuma makaho. A yanzu ne ya tabbatar mata da dukkan abinda yake faɗa mata na zuwan wannan ranar. A yanzu ne yake tabbatar mata dole ta cika alƙawari. A ɗazun da sauranta tunda bakinta a buɗe yake har tana iya kiran sunaye da neman ɗauki.. Ya rabba, Maanal bata taɓa sanin akwai wata azaba da jiki zai iya fuskanta ba sai a yau, a yau ɗin ma a yanzu. Tun tana some-somen shiɗewa harta sume masa gaba ɗaya batare daya sani ba. Dan shi ɗin kansa baima san mi yake yi ba. Baya gane komai, baya fahimtar komai, baya ji baya gani. Baya ma tuna kansa a matsayin kansa...........✍️ 💃“Ragargaza! Rigirgiza! Dagargaza! Wuta direba aljanna tamai rabo ce....”. Wannan waƙarfa da akeyi idan za'a kai amarya wani gari a mota ko🥱🥱. Saura wani ya fassara min waƙa ƴan sanda ne zasu rabamu😏😏🥱🏃 *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖7️⃣5️⃣ ______________ .......Mamy na zaune a inda Maman Saheeba ta barta idanunta a lumshe, tun ɗazun so take ta motsa tama ɗauka wayarta ta kirata saboda jinta shiru amma ta kasa. Knocking ƙofar da akai ya sata kallon wajen. Aka ƙara na biyu sai ta bada izinin shigowa. A mamakinta Babban Yaya ne ya shigo bakinsa da sallama. Taɗan zuba masa ido, sai kuma cikin ƙarfin hali ta ce, “Kai kuma lafiya a daren nan?”. “Lafiya Lau Mamy, Saheeba ce tace kin kirata a waya, na ji shiru kuma shiyasa nai tunanin ko babu lafiya”. A zuciya Mamy tace (Saheeba kuma...?) a zahiri kam rasa ma abin cewa tayi, sai kuma ganin yanda ya zuba mata ido ta ce, “Yanzu Fadeel dan na kira matarka shine ka taso ka biyo ta?”. “Lah Mamy ki fahimta mana, nace najita shiru shiyasa nai tunanin koba lafiya ba. Yanzu fa magana ake ta sha biyu ta wuce. Kinga dole nai tunanin akwai damuwa. Amma tunda lafiya ai Alhamdullah sai da safe”. Daga haka ya juya ya fice abinsa. Da kallo ta bisa kawai abu uku na mata kai-kawo a zuciya masu ɗaci. Na farko miyyasa Saheeban zatai ƙarya cewa itace ta kirata? Sannan ina taje a daren nan to?. Na biyu yanda sam su Fadeel basu damu da ita ba, yanzu ace a yanayin nan daya ganta bazaiyi tunanin bata da lafiya ba, ta inda Ajwaad ya ɗarasu kenan, ko yaya yaga canji daga gareta sai ya gane. Hawaye suka ziraro mata. Tamkar wadda aka bama ƙarfi sai gashi ta yunƙura ta tashi. Dolene taje ta duba Saheeban da Nana ma da taji shiru babu ita babu Ajwaad ɗin. Da ƙyar take tafiya saboda ƙafafunta da suka kumbura suntum, ga ciwon kai gana ƙirji da yake mata kaɗan-kaɗan shima. Shiru tsakar gidan babu kowa, haka ta dinga tafiya cike da ƙarfin hali tana haɗa hanya, tama rasa ina zata dosa, shawarar da zuciyarta ta bata na zuwa sashen Ajwaad tabi, dan gwara ta fara duba Nana tasan halin yaron nan ba ragama ƙanwar tata zaiyi ba. Ta ƙofar kitchen tabi itama, tunda dama tannan ta bama Maman Saheeba shawarar bi. Itama sai da tabi komai na kitchen ɗin da kallo tana taɓe baki, kafin ta shige sai dai falon ƙasan shiru ne babu kowa. Amma fitula a kunne. Kuka-kuka da kiran sunan kamar Nuratu da taji anayi yasata nufar upstairs ɗin da ƙyar dan ƙafafunta sun mata nauyi sosai. Ai kamar jira ake ta gama hawowar kunnuwanta suka jiye mata abinda ya sakata tsayawa cak a firgice. Dai-dai nan kuma su Maman Saheeba suma suka ganta duk sai suka ƙara firgicewa. Jikin Mamy rawa yake sosai, takai hannu ta toshe kunnenta amma abinda take gudun jin tamkar a ƙwaƙwalwarta ake zayyanawa. Idanu a rufe tai wani irin juyawa gaba ɗaya domin komawa a bisa tsautsayi tai tsallaken taka step ɗaya, sai kawai ji kake rikicaaaa manyan mata sun kife. A wani irin mugun tashin hankali Saheeba da Mamanta suka bar Nuratu suka kai kan Mamy da har ta fara mulmulawa tana yin ƙasa. Da shegen gudu suka shiga binta, tana gab da ƙarasa direwa ƙasa gaba ɗaya suka samu nasarar riƙota. Sai dai ina aikin gama ya riga ya gama dan gaba ɗaya jini ya wanke mata fuska, kuma sam bata numfashi. Anya Saheeba da uwarta sun taɓa shiga irin wannan tashin hankalin kuwa a rayuwarsu. Dan Maman Saheeba bama tasan ta fashe da kuka ba tana kirama kanta ta shiga uku. Saheeba da itama jikinta ke rawa kaf-kaf ta ce, “Mama mun mutu, yanzu yaya zamuyi, wlhy idan bamu fitar da su a sashen nan ba akwai matsala. Kada fa ki manta duk ƴan kano suna a gidan nan. Sannan wlhy Ajwaad baida mutunci komai zai iya yi idan yazo ya gammu da uwarsa kwance a wannan halin, zai ma iya cewa mune muka turota. Mama aurena, dan ALLAH ki taimaka ni bari na tafi wlhy suka ganni anan zasu saka Fadeel ya sakeni, kuma shima nace masa Mamyn ce ta kirani.....” Itama Maman kukan ta fashe da shi, “Yanzu Saheeba sai ki tafi ki barni cikin wannan bala'in? A tunaninki idan ni sun zo sun sameni auren naki zai tsira ne. Ki kamata mu kaita sai mu dawo mu ɗauki Nuratu itama”. “Mama tayaya zamu iya? Ta yaya bayan kin san dai matar nan itama ba laifi ƙatuwa ce. Gwara-gwara ma Nuratun. Mafita ɗaya garemu kawai ki kira Aunty”. “Baki da hankali Aunty kuma?”. “To wlhy itace kaɗai mafitarmu, idan ba haka ba ni dai zan tafi gaskiya. Dan wlhy ina son mijina da ƴaƴana. Bazan so barin gidan nan ba, yo ko kishiya bana fata balle barin gidan kina dai ganin sun haɗa kai an aurama Fawzan ƴarsu shima Fadeel ɗin zasu iya yin haka”. Ran Mama ya ɓaci amma sai ta danne. Da ƙyar ta iya lalubo number Auntyn su, cikin barci ta ɗaga wayar, roƙonta kawai Maman Saheeba ta shiga yi akan tazo sashen Ajwaad ta biyo ta kitchen akwai matsala. “Sashen Ajwaad kuma? Ke kuwa miya kaiki sashen Ajwaad a wannan daren Nana?”. “Bani kaɗai bace ba fa harda Aunty Kamila”. Kamar dai Aunty bazata tanka ba sai kuma ta yanke wayar, ita kanta lokacin da take isowa falon saman abinda ya fara shiga kunnenta duk sai taji ta gigice. Ta ƙoƙarin juyawa Maman Saheeba daketa sheƙama Mamy ruwa taƙi ta farfaɗo ta riƙota. Cikin ɓacin rai Aunty ta zubama Maman Saheeba mari. “Ku daƙiƙan inane zakuzo ma yara sashe a irin wannan lokacin, ƙarfe biyu saura fa. Mike damunku ne? Kun haukace daga ke har Kamila ne”. Duk da Maman Saheeba taji zafin marin nan matuƙa ta ce, “Ni dai dan ALLAH Aunty kiyi haƙuri, ko kamata mu fita da ita karma yaron nan ya fito ya gammu, ko wani a gidan nan ya fahimci muna nan. Nuratu ma tana a sama a sume” Rasama abin cewa Aunty tayi, dan sai lokacin ta iya hango Saheeba dake wajen Nuratu ɗin a yanzu. A fusace ta ce, “Ai gara ma asan kuna nan ɗin, wannan ai jahilci ne da rashin sanin mutuncin kai, ya ALLAH na shiga uku na, wai mi kuke son ku zama ni kam Nana?”. Aunty ta faɗa tana nufar hanya, cike da magiya da roƙo Maman Saheeba ta kamota, Aunty ta watsa mata wani mugun kallo. Da ƙyar dai ta yarda suka kamata suka fita su ukun. Aunty taja ƙofar kitchen ɗin ta rufe. Sun zo kusan tsakkiyar gidan kawai sai sukai ido biyu da Abah. Gaba ɗaya rikicewa sukai, suka saki Mamy a ƙasa babu shiri. Aiko sai gashi ta farfaɗo, taja wani wahalallen numfashi, sai kuma ta fashe da kuka tana kiran, ta shiga uku. “Shiga uku? Ai da sauran lokaci”. Abah ya faɗa yana sakarma Maman Saheeba da Aunty wani murmushi ya juya zai bar wajen. Sarai kuma abinda ya faɗa a kunnen Mamy. Ai ko sai ƙirjinta ya shiga dukan dubu-dubu jikinta na rawa sosai gashi bata gani da ƙyau saboda jini daya ɓata mata fuska. Aunty kuwa cikin sauri ta ce, “Aban Fadeel wlhy ban san komai ba, yanzu suka kirani a waya ina barci ma”. Juyowa Abah yay ya kalleta, sai kuma yayi murmushi kawai ya cigaba da tafiyarsa. Mamy da ke jin kamar zata sake suma muryarta na karkarwa ta ce, “Na shiga uku da gaske shine?”. Banza Auntyn tai mata, dan harga ALLAH murmushin Abah ya matuƙar dakarta. Ita kanta Maman Nana jitai murmushi na girgiza mata zuciya, balle Saheeba da tun cin karo da Aban tai saurin juya baya dan ita ta fara sakin Mamy a ƙasa ma. A karo na biyu Mamy da jini ke rinjaya ta sake sume musu. Aunty da bata fatan bayan Abah wani ya sake zuwa ya gansu kuma, dan gara shi idan tai masa bayani maybe ya fahimceta a zafafe ta ce, “Sai ku kamata muje, kuma wlhy sai dai ku dawo ku ɗauki Nuratu”. A wahale suka kaita sashenta, Haule da motsinsu ya sakata leƙowa ta bisu da kallon mamaki, ganin fa abun mai girma ne zaram ta fito. Gaba ɗaya sunma manta wacece ita sukace ta taimaka musu dan Mamyn ta musu nauyi sosai. Haka ta kama suka haura da ita sama. Suka shimfiɗeta a ƙasa, Aunty sai zagin Maman Saheeba take, ita kuma tanata rantse-rantse Mamy tace ta rakata zatama Ajwaad magana. “Ai kin rakata, kunje kuma kun jiyo abinda kuke buƙatar ji, kun kuma samo sakamakon daya dace daku. Yanzu sai ku jira shima randa yaron zai san su wanene ku marasa hankali kawai tunda ubansa yau ya sani. Kuma sai dai ku koma ku ɗakko Nuratu wlhy bazan koma ba”. Daga haka ta jawo kwalin tissue dake a table ta fara goge ma Mamy jinin daya wanke mata fuska har ya fara jiƙa gaban rigarta. Ashe rauni taji a goshi da haɓarta sai gefen idon dama. Haule ta aika ta kawo mata first ald box tai mata ɗan abinda zata iya ta saka mata audiga da bandage dan a samu jinin ya tsaya kafin dai safiya... Dai-dai nan su Saheeba suka dawo ɗauke da Nuratu, a falo suka ci karo da wata cousin sister ɗinsu Mamy. Motse-motse ya sata fitowa. Da mamaki take duban Maman Saheeba da Saheebar sai Haule data fito da kayan da aka gama gogema Mamy jini. Sai kuma ta kalla wanda suka ɗako da alamu suka nuna kamar bata numfashi. “Subahanallahi. Nuratu kuma? Nana daga ina haka?”. Hawaye Maman Saheeba ta share, tana kaiwa zaune kusa da Nuratu da suka shinfiɗar anan falon, zatai magana caraf Saheeba ta karɓe. “Aunty Mariya yanzu drivern gidansu ya kawota, wai ta matsa ya kawota nan shine ta suma a hanya. To ya kirani a waya da wayarta na fito sai ga Mama itama shine muka shigo da ita”. Matar da yake akwai kwakwazo ta ce, “Innalillahi... Amma miyasa Hajiya Turai zata barta ta fito a wannan tsohon daren? Koda motar gida ce ai akwai haɗari. Haule kawo ruwa”. Da sauri Haule ta wuce kitchen, babu jimawa ta dawo da gorar ruwa masu sanyi a hannu. Saheeba ce ta amsa ta shafama Nuratu. Amma ko gezau, sai da Aunty Mariya nan ta bata shawarar a watsa mata da ƙarfi sannan Saheeba ta zuba da yawa a hannun ta ta watsa mata. Aiko wani irin nannauyan numfashi ta ja mai ƙarfi sai kuma ta sake komawa lagaf. Hankalinsu ne ya ƙara tashi. Saheeba ta ce, “Kodai za'a duba Rafeeq ne”. Da sauri Mamansu dake sharar hawaye ta ce, “ALLAH ya kiyaye, jini Fateema bazai taɓa min yarinya ba wlhy”. Rasama abin faɗa kowa yayi suka sake watsa mata ruwan mai yawa sai gashi ta sake farfaɗowa. Kuka ta fashe da shi tana wani irin zaburowa zata tashi Maman ta maidata, zatai magana nan ma ta rufe mata baki. “Basai kince komai ba dan ALLAH Nuratu, kiyi shiru baki da lafiya”. Kuka ta sake fashe wa da shi mai ƙarfi, wannan kuka ne ya farkar da mutane da yawa duk suka shiga fitowa suma. Nan fa aka zagaye Nuratu. Caraf wata dattijuwar mata ta ce, “Kai yarinyar nan ba lafiya ba tanada iska.” ai jin wannan batu sai su Maman Saheeba suka laƙe, nan fa kowa ya shiga mata tofi, wani ma babu abinda yake karantawa motsa bakin kawai yake yi ya tofa yawu hankalinsa kwance🤣.........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖7️⃣6️⃣ ______________ .........Ganin hankalinsu ya raja'a akan Nuratu Haule ta zame jikinta ta fita. Ƙasan bene ta maƙale tai kiran Sille. Bugu biyu ya ɗauka, yanda taji muryarsa kuma ya tabbatar mata da wata macen yake tare. Kishi ne ya turnuƙeta, amma tasan ko giyar wake tasha bata isa yin magana ba, kaɗan daga aikinsa yasa taje har gida yay mata dukan tsiya. Sai kawai ta fara masa bayani cikin rawar murya.. “Dear ya kamata ka baro Lagos ɗin nan tunda ka gama aikin daya kaika ka dawo Abuja, dan abubuwa nata faruwa. Kaga dai anci biki an gama yau ango ya shiga ɗaki ga Nuratu can taje ta jiyoma kanta abinda ya dame ta. Hakama Hajiya Kamila kaca-kaca suka shigo da ita cikin jini, ban sani ba ko itama daga sashen AA ɗin ne oho. Dan Mamar Saheeba da Saheebar sun kima ƙarya. “Naji”. Ya faɗa a taƙaice yana wani shiii da baki na iskanci ya yanke wayar. Duƙewa Haule tai a wajan ta sanya kuka...... __________★ Iskar sanyin asuba ce ta farfaɗo da AA, dan yana kaiwa border shima ya sume. A hankali ya shiga buɗe idanunsa da suka masa wani irin nauyi na masifa. Bishi-bishi ya ke kallon Maanal, sai kuma a hankali ta fito masa a cikin ido. Gabansa ne ya faɗi, ya zabura duk da bashi da wani ƙarfi ya matsa daga jikinta. Hannu ya kai ya kunna lamp ɗin dake side drawer, kafin ya kai yatsarsa sai tin hancinta amma babu numfashi, zuciyarsa ta shiga tsitstsinkewa da rarrabewa, gefen wuyanta ya maida ya taɓa jijiyar wajan, nan ma babu motsi. Ji yay kamar shima zai ƙara sumewa. Sai ya ɗora kunensa a saitin zuciyarta... Bugun da tashi zuciyar take ai tamkar zata faso ƙirjinta ta fito a yanzu. A karo na farko ya yunƙura zai tashi, amma hakan ya gagara saboda wani irin ɗaurewa tamau da cikinsa yay masa. Ga jiri yana ji ga ciwon kai mai tsannanin gaske da bai taɓa fuskanta a rayuwarsa ba. Kan ya dafe da hannu ɗaya, ɗayan na riƙe da cikinsa. Ba irin ciwon cikin jiya bane ba, yanzu ji yake tamkar an ajiye masa dutse ne. Sai da yaja fin minti biyu kafin ya sake yinƙurawa cike da ƙarfin hali da jarumta. Aiko ji yay kamar ya fasa ihu dan azaba, amma ina bazai iya zama yana kallon Maanal a haka ba. Da ƙyar ya miƙe a galabaice ya nufi bayi, ruwa masu zafi ya daidaita ya sakarma kansa na shower. Yafi mintuna biyar a haka sannan yay wanka yay na tsarki cikin ƙarfin hali ya fito yana dafe da cikin nasa, dan ko iya miƙewa da ƙyau baya yi ma. Ga idanunsa kamar zasu faɗo idan ya buɗe saboda ciwon kai. Bashi da kaya a ɗakin, sai dai in wanda ya cire zai maida. Ba kuma zai iya haka ba. Haka ya daure ya fita cikin haɗa hanya ya koma ɗakinsa, jallabiya kawai ya ɗakko ya dawo. Yana ƙoƙarin zama dan ya ɗago Maanal duk da shi yasan da wahala ya iya hakan saboda cikinsa yaga wayarsa na haske. Kamar zai share sai kuma ya tuna Rafeeq yace zai kirashi da asuba. Da ƙyar ya iya kai hannu ya ɗauka, Rafeeq ɗin ne kuwa. Ɗagawa yay batare da yay magana ba, daga can RK ya ce, “Ajwaad!”. Ƙasa magana AA yayi, sai da ƙyar ya ce, “Uhmm”. “Babu dai wata matsala ko?”. Nan ma ya daɗe kafin ya iya furta, “Akwai, bata numfashi sam. Nima kaina da cikina na ciw....” Ya kasa ƙarasawa saboda kansa dake kamar ana bugawa da wani ƙarfe. “Wannan sakamakon dama shi nake tsoratar maka tun jiya. Yanzu dai bara muyi salla gani nan zuwa gidan”. “Uhmm”. Kawai yace ya kife wayar batare daya yanke kiran ba, sai RK ɗinne ya yanke daga can. Duk yanda yake tunanin taimakawa Maanal bazai iya ba, ga salla ana ƙoƙarin shiga. Kuma har cikin ransa bazai iya kiran kowa ba. Dama ace cikin ƴan uwanta akwai wani ko Amaal zai iya sawa tazo ta taimaka mata. Baya son wasa da salla, dan haka ya tashi ya gabatar da ita a zaune. Yana zaune ya jingina da gadon idanunsa a lumshe sai dai bai rufesu ba duka yana ɗan kallon Maanal kiran RK ya sake shigowa wayar. Hannu kawai ya kai ya ɗauka, yana ɗagawa RK ya ce, “Zaka iya buɗe ƙofar?”. “Ko sakkowa bazan iya ba”. “Okay ina zuwa, bari na samo keys wajen Aunty. Ka ɗan daure kaɗan saka mata kaya masu kauri, dan zamu shigo ne koda Aunty haka”. “No! Rafeeq kar kai min haka Please ”. “Dole ne ayi hakan Ajwaad, dole ne laifin da kowa ke kallonka da shi na tsawon shekaru ya shafe a yau....” Kafin AA ɗin ya sake magana ma RK ya yanke wayar. Idanunsa ya lumshe tare da cije lips da ƙarfi. Fahimtar babu wani isasshen lokaci ya sashi mikewa cike da ƙarfin hali, closet ɗinta ya nufa, ya samo riga mai kauri sai dai ba wadda zata dameta ba ya fito. Sai da ya ɗan zauna kansa ya lafa kafin ya iya saka mata rigar da ƙyar, ya tattare gashinta dake a baje ya tufke waje guda. Bargon ya sake ja ya rufa mata ya maida hannunsa a goshinsa ya dafe kansa yana kallonta da idanunsa da suka canja launi gaba ɗaya.... ★Kai tsaye RK sashen Oum ya nufa. Ƙofar a buɗe take, dan haka ya shiga kawai. Babu kowa a falon ƙasan amma yana jiyo motsin su Mah-mah dake a bedrooms ɗin. Ɗan jimmm yay na tunanin wazai samu, sai Umma ta faɗo masa, tunda koba komai a yanzu tamkar itace uwa a family ɗin kasancewarta matar Baba Sardauna dake matsayin uba. Wayarsa ya ciro a aljihu yay kiran layinta. Sai da ta kusa tsinkewa ta ɗauka, gaisheta yay, a ɗan rikice ta amsa tana tambayarsa lafiya dai ko kira da asuba yace ba komai gashi a falo ne... Baima gama sauke wayar ba ƙofar bedroom ɗin tsakkiya ta buɗe. Umma ta fito sanye da zabgegen hijjabi idonta akan RK. Yanda take sauri kamar hijjabin zai taɗeta ta faɗi ya sashi saurin tararta yana faɗin, “Umma relax ba wani abu bane ba fa”. “Ka tayar min da hankali Rafeeq mike faruwa?”. Hannunta ya riƙo ya ce, “Kwantar da hankalinki. Nace babu komai fa. Dama su Ajwaad ne ke buƙatar taimako, dan akwai matsala. Yanzu haka ma nace ya buɗan ƙofa ga doctor nan zata zo amma bazai iya sakkowa daga sama ba dan shima bashi da lafiya. Ita kuma ta suma”. Yanda RK yay maganar kansa a ƙasa yasa Umma tsohuwar arziƙi ta fahimci komai, sai dai kuma zuciyarta ta shiga wasiwasi. Amma batace komai ba tace kawai “Muje”. Kansa ya jinjina mata, sai kuma yace, “Bara na amsa key wajen Aunty ya kulle ne”. Zama Umma tayi, shi kuma ya haura sama. Kai tsaye bedroom ɗin Oum yay knocking, Hajiya Basariyya tazo ta buɗe. Ganin shine sai tai wani shock. “Rafeeq lafiya kuwa?”. “Lafiya lau Aunty, zan amsa key ɗin sashen Ajwaad ne”. “Key! Wani abu ya faru ne?”. Kafin ya bata amsa Oum tazo wajen jin an ambaci sunan AA. Ganin Rafeeq kuma sai ya sake rikita ta. Ta ce, “Majdiya bashi hanya ya shigo”. Shiga RK yayi, Oum da duk take a rikice tace, “Rafeeq miya faru da su Ajwaad ɗin ake neman key?”. “Babu abinda ya faru Aunty ku kwantar da hankalinku. Ya kulle ƙofar ne kuma bazai iya sakkowa ya buɗe ba. Shi da Maanal ɗin kuma duk suna buƙatar taimako”. Daga Hajiya Majdiya har Oum shiru sukai suna kallon RK cike da nazari, sai kuma suka kalla juna. Oum ce tai ƙarfin halin faɗin, “Bara na ɗauka maka”. Hajiya Majdiya kuwa sai ta jeho masa tambaya. “Rafeeq mike damun su?”. Kafin ya bata amsa nan ma Oum ta dawo, key ɗin ta miƙa masa. Sai kawai ya juya ya fice dan ana kiran wayarsa ya kuma san doctor ce. Yana gama sakkowa Umma dake falo na jiransa ta miƙe, a tare suka fito, Umma ta nufi sashen AA shi kuma ya nufi motar Doctor dan ya faɗama maigadi daman ya buɗe mata. Tana hangosa itama ta fito. Mace ce babba dan zata iya kaiwa ma sa'ar su Oum, ya gaidata da girmamawa sannan suma suka nufi sashen AA ɗin da har Umma ta buɗe ta shige. A falo suka samu Umma tsaye, Doctor Ruƙayya ta gaida Umma cike da girmamawa, itama ta amsa da kulawa tana mata godiyar tasota da akai da sassafe haka. Dan gari ya fara haske zuwa yanzu. Wayar AA RK ya sake kira, yana ɗagawa ya ce, “Gani tare da Umma da Doctor. Ka koma wani ɗakin zan sameka su sai su dubata”. “Uhmm”. AA ya faɗa a ƙasan maƙoshi. Har ya yunƙura zai miƙe sai kuma ya ɗan matsa ya sumbaci goshin Maanal da lips ɗinta. Murya a shaƙe ya furta, “I'm sorry Bestie. Please for give me. You bloomed in my childhood, and you rule in my forever, my sweet Everbloom. ALLAH yay miki albarka. Yay miki sakamako da mukullin aljanna, ya shayar dake farin ciki na har abada fiye da wanda kika shayar da ni a daren jiya. ALLAH ya hanani ikon munana miki har abada”. Ya sake sumbatar lips nata a hankali sannan ya miƙe da ƙyar. Fita yay yana waiwayenta, shi kaɗai yasan irin nauyin da yake ji zuciyarsa ta masa. Sosai yake jin haushin kansa. Ɗakinsa ya buɗe ya shiga, dai-dai nan su RK ke haurowa, sun kuma ji ƙarar rufe ƙofar da yayi. Sai duk suka fahimci shine, dan haka RK ya nufi can yana nuna musu ɗakin kusa dana AA ɗin. “Inaga tana nan Umma ku shiga. Bara na ganshi shima”. Can ɗin suka shiga, shi kuma yay knocking ɗakin AA, fin sakan biyar kafin ya tura ya shiga. Wutar ɗakin da AA bai kunna ba ya kunna. Can ya hangosa a saman gado ya dunƙule waje ɗaya. Can ɗin ya ƙarasa, batare da yay magana ba ya zauna a kusa da shi. Hannunsa ya ɗauke a hankali daga saman cikinsa daya riƙe, ya maye gurbinsa da nashi ya ɗan danna wajen. Ai da ƙarfi AA ya wani cije lips yana sake matse idanunsa dan azaba. “I'm sorry”. RK ya faɗa a hankali. Kansa ya jinjina masa kawai, sai da yaƙi buɗe ido ya kallesa. RK ya ɗan girgiza kai da sake faɗin, “Kanka na ciwo. Kuma da alama akwai zazzaɓi tare da kai”. Shi dai AA bai ce komai ba, shima RK bai damu ba. Sai ma wayarsa daya zaro a aljihu ya shiga kiran wayar Oum. Bugu biyu kuwa ta ɗaga. A taƙaice ya ce, “Please Aunty zamu samu ruwan lemon tsami da lipton?”. Cikin sanyin murya mai nuna damuwa Oum ta ce, “Za'a samu Rafeeq yaya jikin nasu?”. “Alhamdullah da sauƙi karfa ki damu. A ɗan haɗa da shayi mai kauri sosai cikin yaran nan wani ya kawo min”.........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖7️⃣7️⃣ ______________ .........Yana ajiye wayar ya tashi ya fara buɗe kit ɗin daya shigo da shi, wanda Doctor ce tazo masa da shi dan daya kirata ya sanar mata dukkan abinda yake buƙata. Drip ya fito da shi da allurai kusan kala uku, sai syringe guda biyu da kan allura. Allurai yayi a cikin ruwan AA na kallonsa ta ƙasan ido, sai dai zaka iya ɗauka barci ma yake. Amma azaba ce keta nuƙurƙusarsa. Ga sanyi yana ji har cikin cikinsa. Ga ciwon kai da zazzaɓi. Tsaf RK ya gama haɗa komai, ya miƙe yana hanging ruwan a jikin hanger daya ɗakko a closet ɗin AA ɗin akai knocking. Sai da ya ƙarasa sannan ya nufi ƙofar ya buɗe. A mamakinsa sai yaga Oum ce da kanta. Sai kawai ya matsa mata ta shiga, cikin sauri AA yaja filo ya saka a wajen tare duvet ya rufe jikinsa da bai gama dai-daita ba. Dan a kallo ɗaya zaka fahimci hakan kodan jallabiyar jikinsa mai ɗan santsi ce. Dariya RK ya danne kawai ya kauda kansa, wato shi aka raina sai ba'a rufe ba. Kayan hannun Oum daya amsa ya ajiye, ita kuma ta zauna kusa da AA tana kai hannunta saman kansa da duk jijiyiyin sukai raɗa-raɗa. Muryarta a sanyaye sosai ta ce, “Sannu kaji Auta?”. Tab ɗin, ai ji AA yay kamar ya nutse dan kunya. A karo na farko na rayuwarsa ya kasa buɗe idanu ya kalli Oum. Itama ta fahimci yanayin nasa amma sai ta shareshi. Hannunta ya riƙe cikin nashi, idanun nasa still a rufe murya can ciki ya ce, “Oum ina kwana”. “Lafiya lau! Ya jikin naka?”. Kasa amsawa yayi, RK dai yay murmushi. Ruwan lemon tsami da lipton ɗin ya zuba masa a kofi yana faɗin, “Tashi kasha wannan sai ka sha tea ɗin musa drip ɗin”. Ƙasa motsawa AA yay sai da RK ya taimaka masa, da jikin gadon ya jingina shi, sai lokacin ya ɗan buɗe idonsa dake jajur ya ɗan kallesa, RK ya ɗage masa gira ɗaya. Harararsa AA yay ya amshi kofin kawai. RK yay dariya da faɗin, “Ka dai ji da shi, kana halin ciwo kana masifa da idanu”. Murmushi Oum tai da faɗin, “ALLAH Rafeeq kai ke ja Auta na ƙin yin uba dakai, dan uban banza ne anan”. “Aunty dama ai baƙya ƙi goya masa baya ba, amma wannan yaron da kike gani baida kunya, ba komai zan daina masa dariya”. Harararsa AA ya sake yi. RK ya kwashe da dariya ya ce, “Ka cigaba da hararata zan barka da ciwonka ne”. Shi dai bai sake kulashi ba. Ya gama shan ruwan lemon tsamin ya miƙa masa kofin, tea ya sake miƙo masa. Amma sai ya girgiza kansa alamar bazai sha ba. “Aiko dole kasha wlhy, kuma yanzu nan dan so nake ya saka ka amai. Hakan ne kawai zai bamu abinda muke so a tare da kai”. Lallashin AA Oum ta shiga yi, saboda ita ya daure ya sha fin rabi, aiko kamar yanda RK ya faɗa sai amai ya fara taso masa, da sauri ya kamashi suka wuce bayi. Sosai yayi sa har kamar zai amayar da Kayan cikinsa. RK ya taimaka masa ya wanke fuskarsa da bakinsa suka fito. Sannu Oum keta jera masa cikin damuwa. Shi ko ya wani riƙe mata hannu kamar yaron da bai son gusawa daga jikin mamansa. A haka aka ɗaura ruwan bayan ya masa allurai biyu a hannun ya kumayi biyu a cikin ruwan... Kamar jira barci yay awan gaba da shi cikin sakanni...... ★A ɓangaren su Umma suna shiga suma kan Maanal sukayi, hankalin Umma ya tashi sosai ganin yarinyar mutane a sume. Sai da doctor tace ta kwantar da hankalinta zata farfaɗo sannan. Amma a hakan ma sai faɗa take akan wautar yaran zamani. Wane irin abu ne ka kama yarinya har sai ta suma kamar abin cin rabo. Haba ai rashin tausayin yayi yawa. Yarinyar ma da ba budurwa ba ai mata irin wannan wahalarwar haka, to da virgin ɗin take kuma sai yaya. Doctor dai dake shafama Maanal ruwa a fuska ta kuma warware gashinta tana zuba mata a cikin kan ta ce, “Ai sai dai haƙuri Mama, yaran yanzu sam basa saurare. Kawai su a rana ɗaya suke buƙatar yin komai, haka muke ta fama da cases ɗin nan na amare a daren farko. Amma ta taɓa aure ne naji kina faɗin ba budurwa ba”. “Bata taɓa aure ba, ƙaddara ce ta gitta tsakaninta da shi tun suna yara dai”. Doctor ta fahimci mi Umma ke nufi, amma sai tai mamaki a ranta. Kafin kuma tayi magana Maanal tai wata irin zabura alamar farfaɗowa. Da sauri Doctor ta riƙeta, sai kuma ta sake watsa mata ruwa a fuska. A firgice ta saki ƙara, muryarta a matuƙar dusashe dan ko fita batayi ta shiga roƙo da magiyar AA ya barta, Oum da Ammie suzo su taimaketa, saboda ta suma ne a wannan yanayin na kuka da kiran sunayen dangi🤭 shiyyasa ta farka da abin. Da ƙyar Doctor ta iya rungumeta cike da lallashi da kulawa ta ce, “Relax my baby, ba Ajwaad bane nice. Kwantar da hankalinki ai ya barki, babu kuma abinda zai sake miki okay”. A cikin kunne take mata maganar, dan haka ta shiga sauke ajiyar zuciya masu ƙarfi ga hawaye na zuba kamar an buɗe fanfo (Su Hajiya Maanal ke da kikace babu ma wani wuya🤣). Shafa bayanta Doctor ta cigaba da yi a hankali a hankali har sai da ta nutsu sannan. Gaba ɗaya tausayin Maanal ya rufe Umma, ta gama ɗaukar alwashin sai taci mutuncin Ajwaad yau ɗin nan basai gobe ba. Kwantar da ita doctor tayi ta nufi bayi ta haɗa ruwa mai zafi ta sake dawowa. Dole ita da Umma suka kama Maanal ɗin, ai ko ta sakar musu kuka jikinta na rawa alamar bazata iya zama ba. Cikin lallashi Umma ke faɗin, “Daure kinji ƴar albarka, ALLAH yay miki albarka kinji. Sannu komai zai zama labari kowa da haka ta fara”. Ita dai Maanal hawaye kawai take, da suka miƙar da ita kasa tsayawa tai a kan ƙafafunta, dole suka rungumeta har bayin. Basu cire mata rigar jikinta ba, a haka suka sakata cikin ruwan zafin dake fin rabin jacuzzi. Ƙarar data fasa musu na azaba jikinta na sake ɗaukar rawa sai da suka ji kamar su fashe da kuka. Da ƙyar suka iya danneta a ciki su biyun, bama ita ba su kansu sunyi zufa sharkaf. Yanda jini ya ɗan ɓata ruwan Umma ta kasa haƙuri ta ce, “Wannan jini da alama yaji mata ciwo sosai kenan?”. Doctor ta jinjina kanta, “Eh dama da alamun akwai ciwo gaskiya da taji kodan yanda ta kasa zama ma. Amma kuma fa ina ganin yarinyar nan is a virgin gaskiya”. “Virgin?”. Umma ta maimaita da mamaki. Itama Maanal duk da halin da take a ciki sai da kalmar ta daki kanta Sosai. Cike da tabbatarwa Doctor ta ce, “Tabbas Mama”. Rasama abin cewa Umma tayi, suka sake canjama Maanal ruwa abu na mata kai-kawo a cikin rai. Anan ma tasha kuka. Sai da sukai mata ruwa uku sannan suka barta a cikin ruwan suka fito dan jikinta ma ciwo yake shiyasa duk ta inda aka taɓata take raki. Umma data kasa haƙuri ta ce, “Ƴar nan kin tabbatar da abinda kike faɗa gaskiya ne?”. “Tabbas kuwa Mama, yarinyar nan budurwa ce cikakkiya. Amma bari ta fito zan sake bincikawa”. Ta yaye duvet ɗin dake saman bedsheet ɗin. Ganin yanda duk ya ɓaci da jini ya saka doctor sakin murmushi da sake faɗin, “Mama kinga wani tabbacin ko. Duk da bakowace mace bace ake ganin jini a daren ta na farko wannan ya wuce jinin jin ciwo kawai. Amma dai kamar yanda na sanar miki bara mu sake tabbatar wa”. Kai kawai Umma ke jinjina wa, dan ko ita daba likita ba shekarun girma sun saka kai tsaye ta fahimci duk abinda doctor ke son ta fahimta. Gaba ɗaya sai taji ta sake shiga ruɗani, ta zauna shiru tana kallon Doctor dake cire bedsheet ɗin zata canja da wanda ta ɗakko a closet ɗin Maanal. Tashi tai ta koma wajen Maanal dake bayi, wata irin ƙaunar yarinyar ce mai nauyi ke sake mata tasiri a cikin zuciya. Alhamdullahi tayi wankan da sukace tayi, harma ta daddafa ta saka bathroom tana jingine da bango. Kamota Umma tai suka fito tana tafiya da ƙyar, hawaye kam sun gagara tsayawa gaba ɗaya. Sai sauke ajiyar zuciya take a jajjere. Towel ɗin Umma ta naɗe mata a kai dan ya tsane ruwan, ta amshi riga mai kauri da Doctor ta ɗakko ta sanya mata dan rawar sanyi Maanal ɗin keyi, ga zazzaɓi jikinta zafi zau abin tausayi. Kwantar da ita sukai Umma ta fito dan bama doctor damar yin aikinta. Aiko sai da suka sha dagama da Maanal sannan ta yarda ta duba jikinta, sosai doctor ta runtse idonta tana cije bakin tausayin yarinyar dan da gaske ango yayi ɓarna sosai..... _______★ A ɓangaren dangin su Mamy basu san wainar da ake toyawa a sashen AA ba, dan suma a nasu sashen sun kwana sun tashi ne da tashin hankalin halin da Mamy da Nuratu suke. Sai yanzu da safen nan ne Hajiya Turai tazo tare da Doctor ɗin dake duba Mamy dan tun daren Maman Saheeba ta kirata. Lokacin shigowar tasu ne taga Oum ta nufi sashen AA da kaya a hannu, shine take tambaya taga matar can na nufa sashen Ajwaad da sassafen nan. Kai tsaye Maman Saheeba da Saheeba suka fahimci abinda ke faruwa, aunty Babba kuwa naji bata tanka musu ba. Su kuma sauran da basu san abinda ke faruwar ba suka shiga tambaya. Bayanin kuwa Hajiya Turai tai musu. Mariya ce ta miƙe tana faɗin, “Bara naje naji mike faruwa, dan inba wani abu ba itako mizai kaita sashen yara da safen nan dan masifa”. Bata jira cewar kowa ba ta fice. Koda ta shigo falon ƙasa babu kowa sai tai tsaye, zuwa can kuma ta ɗan zauna tana jiran taga ko Oum zata sakko amma shiru kake ji. Fin mintuna biyar ta fara ɗan jiyo magana sama-sama daga upstairs. Miƙewa tai kawai ta shiga haurowa saman itama. A dai-dai nan Doctor ke fitowa daga ɗakin Maanal. Dan da Umma ce da Oum ke magana bayan Oum ta shiga duba Manaal amma ta ɓoye fuska a barko taƙi yarda ta kalla Oum, shine ta fito ta barsu ta dawo wajen Umma. Sai kuma ga RK shima ya fito daga ɗakin AA. Duk kallon Mariya dake gaishe da Umma sukai. Batare da damuwa ba RK daya gaisheta fisha shima ya kalla Doctor ya ce, “Ya ake ciki Aunty?”. Kai Doctor ta jinjina, sai kuma ta kalla Mariya. RK ya fahimta, dan haka ya ce, “Karki damu kiyi bayani nan duk ƴan gida ne kuma iyaye”. Kanta ta jinjina masa. Ta cigaba da faɗin, “Dole za'ai mata ɗinki gaskiya dan taji ciwo sosai. Gashi har yanzu a firgice take.” Caraf Mariya ta ce,.........✍️ Na kula Mariyar nan ƴar ɓare-ɓare ce fa😂 *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖7️⃣8️⃣ ______________ ........“Ciwo kuma, yarinyar daba budurwa ba miyya haɗata da ciwo? Ko ɗinkin nan na zamani taje akai mata?”. Babu wanda maganarta bata zafeshi ba a cikin su Oum, amma sai babu wanda ya tanka sai doctor da tai murmushi da faɗin, “Wlhy ko ɗaya Hajiya babu wani ɗinki. Hasalima yarinyar nan cikakkiyar budurwa ce yau aka fara taɓata.” “Budurwa? Kai likita sake dubawa dai da ƙyau. Ko ana rasa budurci ne ya kuma sake dawowa a karo na biyu? Yarinyar nan fa shekara takwas data wuce an mata fyaɗe”. Kallonta Oum tai zatai magana rai a ɓace yanzu kam Umma ta riƙe mata hannu ta girgiza mata kai alamar kar tace komai. Doctor ta ce, “Tabbas Hajiya budurci sau ɗaya yake ga kowacce mace, kuma baya maimaita kansa, duk ma wadda tace zata iya dawo da shi da wani magani ko ɗinki ƙarya take, sai dai tayi abinda za'a mace amma ba dawo da budurci ba. Dan sau ɗaya tak ake yaye wannan tantanin. Dan haka zan sake jaddadawa yarinyar nan cikakkiyar budurwa ce yau ne karo na farko data fara sanin namiji. Idan kuna kokwanto kuma za'a iya sake kaita asibiti ma ko a kira wasu doctors ɗin su dubata banda haufi akan hakan. Fyaɗen da kuke tunanin kuma an mata gaskiya ku ƙara bincike akwai abinda ya kamata Ku sani”. Daga haka ta juya tana kallon RK. “Doctor zanje na dawo yanzun nan. Amma zaka iya samo ma su Hajiya wasu likitocin su duba yarinyar nan kafin na dawo dan su sami nutsuwa.” Murmushi RK yay da faɗin, “Karki damu Aunty ni dai na gamsu, iyayena ma nasan sun gamsu in sha ALLAHU. Wanda bai yarda ba sai ya kawo nashi likitan. Amma ko shi ma Ajwaad ɗin a yanayin da yake ciki yau ne karonsa na farko da hakan ta kasance. Sannan da bakinsa ya sanar min Maanal budurwa ce babu abinda ya faru a waccan ranar”. Wasu irin hawayen farin ciki ne suka silalo a idanun Oum. Ta shiga tuno kalaman AA a randa ta turkeshi akan batun fyaɗen. (Oum dan ALLAH ki bar zancen kawai. Amma ki yafe min. Ki kumayi haƙuri komai daren daɗewa UBANGIJI zai warware komai cikin sauƙi da rahamarsa. Amma a yanzu babu wani bayani da zan yi a fahimta ko a yarda. Abinda kawai na sani shi ALLAH baya barci. Ki tayani da addu'a kawai ALLAH yasa na gano inda su Maanal suke. Wannan shi nafi buƙata a yanzu) Hawaye suka sake ziraro mata. Ita kanta Umma tuna ranar da suka tirke Ajwaad ɗin take. Marukan daya sha wajen Abah da Uncle Mahmoud har sai da fuskar yaron nan ta kumbura da shatin yatsunsu. Amma akai juyin duniya yaƙi cewa komai. Daga ƙarshe ma ya yanke jiki ya faɗi, faɗuwar data zame masa sanadin ciwo na shekara kusan biyu da rabi. To mike faruwa? Ko tace ma miya faru a waccan ranar? Ranar da ranar farin ciki ce da suka taru domin yin shagalin bikin yaran su shida reras. Amma komai ya hargitse ya lalace a sanadin wannan maganar fyaɗe. Mi hakan ke nufi? Miya kamata su sani? Miyasa Ajwaad ya zaɓa yin shiru akan faɗin gaskiya?... Mariya kam tuni ta fice a sashen jikinta na rawar mazari na gulma. Tamkar wadda aka jeho haka ta faɗo ma su Mamy dan ɗakinta duk suke a yanzu ana dubata. Fuskarta ta kumbura suntum idanun sun shige ciki, hakama ƙafarta ta dama da hannun haggu sun kumbura da alama dai taji ciwo koma karaya kamar yanda doctor ta faɗa, har ma tama wani abokin aikinta daya san harkar ƙashi magana zai zo ya duba Mamyn yanzu. Shayin da likita tace a kawo Mamyn ta sha Haule ta haɗo mata da zafinsa. An bata kenan zata fara sha da hannunta mai lafiya Mariya ta afko, duk kallonta suka juya sunayi harda Haule dake duƙe tana haɗama Mamy ƙwai a cikin bread wai ko zata iya ci dan bakin ma a kumbure yake saboda raunin haɓarta. Hakama goshinta yay wani irin tulluwa. Kai fuskar dai babu ƙyan gani kamar wadda tai haɗarin mota. Cikin matuƙar fargaba da ƙaulani da su Maman Saheeba ke ciki na jiran sakamako dama ta ce, “Mariya lafiya kuwa?”. “Uhhhmm!! Lafiya Lau, wani abin mamaki ne ko al'ajabi zan kira shi oho. Wai yarinyar nan matar Ajwaad budurwa ce, babu wani fyaɗe da aka taɓa mata yanzu likita ke faɗa, wannan yaron kuma ƙanin Hajiya Fateema shima yace Ajwaad yace masa babu abinda ya faru a waccan ranar wai.” “What!!”. Maman Saheeba, Hajiya Turai, da Saheeba suka faɗa a lokaci guda suna miƙewa tsaye zambar. Yayinda kofin shayin hannun Mamy ya suɓuce shayin ya ƙyalaye mata a jiki gaba ɗaya kuma akwai azabar zafi. Aiko babu shiri ta fasa ƙarar da ta sakaku juyawa kanta gaba ɗaya. Cikin sauri Doctor ta ɗauka gorar ruwan sanyi data gani kusa da Mamy ɗin ta juye mata a jiki. Sai dai ina azabar ta riga ta gama ratsata har wajen fitsarinta saboda a yanda take zaune ƙafa a bubbuɗe... Haule ma jikinta har rawa yake ta fice. Gaba ɗaya tabar sashen ta nufi can wajen garden ta kira sille a waya. Harta tsinke bai ɗaga ba, ta sake kira. Tana gab da tsinkewa ya ɗaga yanzu. A fusace ya ce, “Bana faɗa miki zan dawo yau ba. K nifa bana son jaraba dan nasan abinda ya dame ki kenan kiketa son damuna”. Cikin raunin murya ta ce, “Wlhy ba haka bane Dear, Update ne da ɗumi-ɗuminsa. Wai matar Ajwaad budurwa ce ba'a taɓa mata fyaɗe ba. Yanzu wata ƴar uwarsu ta shigo tana faɗa da'alama daga sashen Ajwaad ɗin take”. Wata irin mahaukaciyar dariya Sille ya kwashe da ita daga can irin ta ƙeta. Kafin ya ce, “Ajwaad! Ajwaad!! Shegen yaro. Tabbas na yarda ya cini wannan wasan, amma kuma ya jira sabon wasa dan yanzu ne za'a fara tsakanin ni da su. Ƙarfe biyar na yamma kizo gida ki saman zan bada saƙo a isar min da shi cikin gidan..” daga haka ya yanke wayarsa. Kasare Haule tai tana kallon wayar dan babu abinda ta fahimta a zancen nasa. Hasali ma ita har yanzu bata san ainahin abinda ya haɗa AA ɗin da Sillen ba. Kawai dai ya sata ta dinga ɗauka masa rahoton kowa na gidan da motsinsa. Amma har ga ALLAH tana son sanin minene tushe sanadin wannan BASHIN GABAR..... ________★ A ɓanagaren su RK ma tuni Oum ta fito ta nufi sashen Abah duk da tasan akwai su Uncle Mahmud dan anan suke kwana kasancewar akwai ɗakuna wadatattu. A falo ta samesu zaune zasu sha coffee. A yanda Oum ɗin ta shigo duk suka bita da kallo, ita ko babu wani damuwar ganin ƙannen nata a tare da Abah ɗin taje ta rungume Abah ta sakar masa kuka. Sosai hankalin Abah ya tashi, suma su Uncle Mahmud duk suka miƙe nasu hankalin a tashe. Cikin ƙarfin hali Abah daya rungumeta shima ya ce, “Lafiya kuwa Fateema? Ko wani ne ya rasu?”. Kai ta girgiza masa. Ya ce, “Rashin lafiya ne?”. Dan yayi zaton zuwa yanzu tasan halin da Mamy ke a ciki. Amma a nan ma sai ta girgiza kanta. “Gobara ce?”. Cikin kuka Oum ta ce, “Ajwaad bai yi ma Maanal fyaɗe ba Gadanga, babu abinda ya faru a waccan ranar ashe. Shiyyasa ya ƙi magana akan dukkan tuhumar da kukai masa”. Shi kansa Abah sai da yaji abu ya tsarga masa. Su Uncle Hussain ma suka shiga kallon kallo. Cikin ƴar rawar Murya Abah yace, “Ban gane komai ba Fateema. Yimin bayani, Please yimin bayani yanda zan fahimta. Taya akai kika gane Ajwaad bai aikata ba?”. Ɗagowa Oum tai tana share hawayen da ke cigaba da ziraro mata. Babu wani ɓoye-ɓoye ta shiga yi musu bayanin komai daya faru a sashen AA. Aiko Abah sai da yaji shima hawaye sun cika masa nasa idon. Ya tuna yanda ya ringa zubama fuskar AA maruka a waccan ranar masu gigitarwa. Da yanda ya fara jifansa da munanan kalamai sai da Baba Sardauna ya kwaɓesa, ya tuna yanda AA yaƙi magana, ya ƙi musu bayanin komai. Ya tuna wahalar ciwo daya sha na tsawon shekaru har biyu. Ya tuna yanda ya daina shiga sabgar yaron gaba ɗaya duk da yana cikin halin rashin lafiya. Har depression ɗin daya shiga a lokacin da akace a dinga zama da shi shi yace babu mai zaunawa yama haukace sun sallama shi. Haka zaije asibiti ya duba Oum amma ko kallon gadon AA bayayi duk da matsanancin halin da yaron ke a ciki. Jagwab ya kai zaune abubuwa masu yawa na dawo masa ta yanda ya hora Ajwaad babu tausayawa babu rangwame dan harga ALLAH yaji zafin abin nan ne matuƙa. Ya ji zafin yanda Ajwaad ya lallata Maanal ƴar su ta amana. Su kansu su Uncle Mahmud komai ji sukai ya tsaya musu cak, dan suma dai gwargwadon iko sun taka rawar gani a hora Ajwaad..... ________★ A lokacin da ɓangaririn biyu ke a wancan yanayin anan sashen su AA doctor ce ta dawo tare da wata Nurse. Sun sami Umma nata lallaɓa Maanal tasha tea da RK ya haɗo ya kawo. Sai dai yanda bakinta babu daɗi ta kasa sha. Ga zazzaɓi sai uban rawar sanyi take yi. Ga azaba dan ko zama ta kasa yi sai da aka saka mata fillo ta karkace a kishingiɗe tunda ba damar tasha tea ɗin a kwance. Da ƙyar tasha rabin kofi Umma ta fita doctor ta fara aikinta. Bayan tama Maanal allurar kashe zafi. Ji Maanal take a ranta yau mai rabata da AA sai ALLAH a gidan nan, dole ma ayi walle-walle kowa ya kama tsaginsa dan sashen Oum zata koma. Ita zai ma wannan baƙin muguntar ya gudu ya barta ko sannu baizo ya mata ba... Tuni ta saki wannan saƙe-saƙen nata saboda azabar zafin ɗinkin duk da anyi allurar kashe zafi. Tako sha kuka sosai da jerama AA ALLAH ya isa a zuciya tafi cikin kwando. Doctor data bama tausayi tana gamawa ta rungumeta tana lallashi da share mata hawaye. Ta ɗora da mata nasiha mai ratsa jiki, da yanda zata kula da kanta dan wajen ya warke da wuri. Kafin ta sake mata allura ta shiga ɗaura mata drip kuma. A haka Oum ta shigo ta samesu. Kan Maanal data fara lullumshe ido ta shafa cike da so da ƙauna da tausayawa. Fuskarta ko murmushi ya kasa ɓacewa. Yanzu ta shiga ta dake shiga sukaga Ajwaad ita da Umma shima dake barci mai nauyi saboda alluran da RK ya masa ga ruwa da ya sanya masa. Shima yasha albarka da tarin addu'oi a wajen Umma dan yau ji take kamar ta ɗaukesa shi da Manaal ɗin ta goye tai ta zagaya Abuja da su.........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖7️⃣9️⃣ ______________ .........Har sashen su Abah suka shiga suka duba AA da Maanal, duk da dai basu shiga ɗakin da Maanal ɗin take ba. Sai dai na AA kuma yanata barcinsa. Hakama matan sun cika sashen anata taya juna murna. Suma sun shiga sun duba Maanal. Su Baba Sardauna kansu da ke Kano tuni labari yake kunnuwansu, haka ma sauran ƴaƴa da suka wuce dan dama a maza Uncle mahmud, Hussain, Hassan ne kawai suka rage sai yau suma zasu wuce da matan dan su gaba ɗayansu suna nan Abuja ƴaƴa da iyaye. Kowa dake ta ɓangaren Darma yau ka kalla fuskarsa kasan yana acikin farin ciki sosai, dan abinda ya faru a tsakanin Maanal da AA na shekarun baya zasu iya cewa shine tarihi mafi muni da girma dake jingine da wani ɗansu na cikin zuri'ar. Dan haka yau jin wannan mummunan tarihin ya goge babu shi yay matuƙar motsa musu zukata. Su Abah kansu sun ƙagara AA ya farka suji ta bakinsa. Farin ciki yay farin ciki babu wanda ya lura da rashin ahalin Mamy ko ɗaya a masu shiga sashen AA ɗin sai Abah, amma uffan bai ce ba. Sai daga baya ne Hajiya Majdiya da itama take lure da komai tai magana. “Wai nikam halan su Aunty Kamila basu san halin da muke ciki ba yau a gidan nan? Naga banga kowa ba daga sashen. Haka ma Fawzan shi da matarsa ban gansu ba”. Rashin sanin halin Mamy yasa da yawansu sukace, gaskiya maybe basu sani bane. Aiko sai Hajiya Majdiya ta fice zuwa sashen Mamy tana faɗin, “Aiko nice zan kai albishir ɗin nan”. Aunty Rufaidah ta miƙe itama ta ce, “Aiko Aunty harda ni. Sai itama matar Uncle Hassan tace itama da ita”. Murmushi RK yayi, shima ya zaro waya yana neman Fawzan. Dan ya kira shi ɗazun ba'a ɗauka ba. Shiyasa ya ƙyalesa, yasan shi da barcin tsiya. Balle su duka suna hutu yau sunce bazasu koma aiki ba sai sun huce gajiyar biki... A lokacin da kiran RK ke shiga wayar Yaya Fawzan yana barci ne sun gama tafka bala'i ne da Nibras, dan tun daren jiya suke yinsa, bayan ta gama haukar kukanta koma ace tana tsaka da yi shi kuma yazo mata da buƙata tace bai isa ba kamar yanda take masa. Shima ko yace bata isa ba ya biya sadaki bamai hanashi biyan buƙatarsa. Kamar yanda ya saba ya saka mata ƙarfi. Tunda fa ya samu natsuwa bata barsu sun huta ba take ta gaya masa maganganu masu zafi ta kuma dage akan sai ya saketa. Shi ko ya banza da ita, haka ta kwana tana azabarta, sai da safen abin nata ya fara hawa masa kai ya shashsheƙama fuskarta maruka. Aiki shine wutar ta ƙara tashi a tsakaninsu. Ta rantse yau sai ta bar gidan kuma da saki. Ta kira mamanta kuma tana kuka ta faɗa mata ƙauli da ba'adi shine tace ta jirata gata nan zuwa gidan. Shi ko Fawzan yana jinsu sarai, sai ma ya buɗe wani ɗakin ya shiga ya kwanta abinsa dan jiya ta hanasu barci. Vibration ɗin wayarsa na kiran da RK ke masa ne ya farkar da shi. Da ƙyar ya iya ɗaga wayar cikin muryar barci ya ce, “Assalamu alaikum”. RK ya kwashe da dariya kuwa, cike da tsokana ya ce, “Sai da kai kasa uwar barci. Ana nan anata hayya-hayya kana can kai barci ma kake abunka. To maza ka fito mutuminka baiji gargaɗinka ba yama ƙanwarka biji-biji gata can rai a hannun ALLAH”. Tsabar gulma tarwai Yaya Fawzan ya buɗe idanu, sai kuma ya tashi zaune wani kalar shegen murmushi na mamaye fuskarsa. Ya ce, “Uncle karka ce min Auta?”. “Yo inba shi ba sai wa. Yaro yaji wuta ya tona ma kansa asiri yau ƙanwarka dai fil take a leda babu abinda ya faru a waccan ranar”. “What! Are you serious dan ALLAH?. Kai ni wlhy kama rikitani, ina dai zuwa”. Ya faɗa yana yanke wayar ya afka bayi, brush yayi sharp-sharp ya fito. A dai-dai lokacin motar Momyn Nibras ke shigowa gidan. Ko kallonta baiyi ba ya wuce sashen AA da aketa shigi da fici....... _________★ A bangaren su Mamy kuwa abu kamar wasa ta samu ƙuna sosai. Tsabar azabar dake ratsata tama kasa hawaye sai idannunta ne sukai wani masifar kaɗewa kamar an kunna harwashin wuta a cikinsu. Ga azabar ƙafa da hannunta da keta sake kumburi raunuka na ƙara tsami. Su Maman Saheeba kam sunyi jigun-jigun abin duniya ya ishesu babu bakin magana tunda basu kaɗai bane. Ga Nuratu an danna mata allurar barci ita dai sun ɗan huta da ita. A haka doctor da zai duba ciwukan jikin Mamy ya iso. Auntynsu tace ai dolene a gayawa Abah kafin likitan ya shigo tunda ba kamar mace ba dai. Dan haka tace Mamy tai kiransa a wata da kanta. Cikin tsanin azaba Mamy tace wlhy bazata iya ba, tsoro take ji, dan shirun Aban ba ƙaramin girgiza mata zuciya yayi ba. Jiba fa a yanda ya ganta jiya, amma bai nuna damuwar komai ba, ga shi yau har ƙarfe kusan sha biyu koma tace ana neman ɗaya amma bai leƙo ba, kai wani a cikin ma ahalinsu bai leƙo sashenta ba. Sai da Mariya ta fita tana naɗo musu gulma ta shigo tana ƙara sanar musu halin da gidan yake a ciki na farin ciki a yau. Sai ta fahimci hankalin kowa yana a can kenan. Dai-dai sanda ake jajen kiran likita su Hajiya Majdiya ke shigowa sashen kuwa. Sosai ganin su Hajiya Majdiya ya saka su Maman Saheeba a shock, sai dai sun san kuma dai babu damar hanasu shiga ɗakin Mamyn. Haka dai suma daure aka gaisa sukace Mamyn na ciki. Da yake daga ita sai doctor da Aunty kawai a ɗakin su duk suna a falo ne, wasu a falon ƙasa wasu a falon sama. Turus su Hajiya Majdiya suka ja suka tsaya ganin fuskar Mamy tamkar wadda tai accident, accident ɗin ma bana wasa ba, dan fuska a kumbure komai ya ninka kansa sau uku, ga hannu da ƙafa ɗai-ɗai suma a kumbure. Cikin tashin hankali sosai suke tambayar miya faru haka? Miyasa ba'a sanar Mamyn babu lafiya ba? Ai ko Abah basa jin ya sani farin ciki ya ɗauke hankalinsu a sashen Ajwaad. Cikin ƙarfin hali Aunty ta ce, “Faɗuwa tayi jiya da dare a stearcase, ruɗanin da suka kwana suka tashi a ciki yasa basu sanar ma kowa ba. Yanzu haka ma doctor yazo zai duba mata ƙafarta da hannun dan suna tunanin akwai rauni a ciki”. Ba dai ta faɗi na shayi ba daya sale Mamyn a majalissa. ALLAH yayi ma ahalin Darma tausayi da ɗaukar nasu a nasun, tuni Hajiya Majdiya ta manta da iya shegen data zo da niyyar yima Mamyn ta juya ta fita tana faɗin, “Ai dole a sanar kuwa, bari taje a shigo da likitan”.... Lokacin da Hajiya Majdiya ke fitowa domin sanar ma su Oum halin da Mamy ke ciki Momyn Nibras kuma ke ƙoƙarin shiga ita da ƙawayenta su uku. A kallo ɗaya zaka fahimci a matuƙar fusace suke. Dan har ɗan bangaje ta sukai. Mamaki sosai abin ya bata dan haka ta bisu da kallo, dan da farko ma ita bata gane Momyn Nibras ɗin ba sam saboda abinda ta shafa a fuska. Ashe wai duk a cikin shirin bala'i ne. Sashen Abah ta nufa da sauri, suna tare da Umma da Mah-mah sai Gwaggo Khadijah da Mammah suna tattaunawa ne akan batun Ajwaad a tsakaninsu manyan sai su Uncle Mahmud dake tare da su an kira Baba Sardauna, da Baba, da Abbah video call. Shigowar Hajiya Majdiya yasa duk suka kalleta. Kafin ma wani ya iya yin magana a cikinsu ta ce, “Kuyi haƙuri gidan nan fa babu lafiya. Ga Aunty Kamila can cikin mummunan yanayi daren jiya ta faɗo daga saman stearcase, taji ciwo kuma sosai. Yanzu kuma zan fito ga wasu riɗa-riɗan mata can fitsararru sun shiga sashen daga ganinsu kasan basa tare da alkairi.” A tare su Uncle Hussain suka miƙe, hakama su Umma. Amma Abah bashi da niyyar yin hakan. Baba Sardauna da suke jin komai duk da ba ganin Hajiya Majdiya suke da ƙyau ba ya ce, “Kutashi kuje ku duba mike faruwa. Kuma ku dama duk bidirin da kuke baku sanar musu ba ne?”. Da mamaki Umma tace, “Sun sani fa gaskiya, sai dai in ƴar uwarsu bata sanar musu ba. Dan tun ma ana duba yaran nan kamar cousin sister ɗinsu ce yarinyar nan Mariya tazo sashen Ajwaad ɗin. Tare da ita ma likita ta sanar mana komai ai. Amma dai bara muga mike faruwa to”. Dama su Uncle Mahmud har sun fice, dole shima dai Abah ya tashi yabi bayansu...... _______★ Su RK basu san mike faruwa ba, suna can sashen AA jira kawai suke ya farka musamman Yaya Fawzan da aka ƙara bama labari kaf. Shi kansa dai Babban Yaya yau bakinsa akwai magana. Dan a hakan ma sai jehota yake ɗai-ɗai su RK na dariya. A haka su Maimoon da aka saka gyaran sama suka sakko, sun share ko'ina tas sun saka ƙamshi mai daɗi, dai-dai nan Oum itama ke fitowa a ɗakin Maanal tare da Hajiya Shuwa data shigo gidan yanzu babu daɗewa saboda kiran da Oum tai mata ta mata bayani. Ba ƙaramin shock kuwa itama Hajiya Shuwa ta shiga ba. Matuƙar tausayin Maanal ya kamata, dan harga ALLAH data san yarinyar nan virgin ce da batai mata kalar gyaran can ba, dan ko'a hakan dama tana tausayama yarinyar saboda gyaran datai mata ko mace mai haihuwa uku iyaka kenan. Amma ita tayi ne dan samar da nutsuwa a zamantakewar auren. Shi rashin samun mace a cikakkiyar budurwa a daren farko nada wata illa ne koda ace mijin ne ya santa a mace kafin aure. Sai ya dinga sakama namiji zargi da wasu-wasin bayan shi akwai wani ƙila a gefe. To wannan ƙofar ce suka shirya toshewa gaba ɗaya a zamantakewar Ajwaad ɗin da Maanal. Ta tabbatar ma Oum da kafin ma ayi ɗinkin ne ta sanar mata da bazata bari ayi ba. Akwai magungunan da zata haɗa mata da ganyayyaki ta dinga sit bath cikin ƴan kwanaki zata warke komai ya koma normal, amma ko yanzun ma bata ɓaci ba in sha ALLAHU zata tsaya akan Maanal ɗin. Da wannan zancen suka fito zataje gida ta haɗa kayayyakin ita kuma Oum tace zata kira Ammie itama a sanar mata wannan daddaɗan labari har ma da su Shahidah. Sai dai me suna sakkowa hayaniyar da gidan ta ɗauka ya shiga rige-rigen shigewa cikin kunnuwansu. Da sauri suka ƙarasa sakkowa dai-dai suma su Babban Yaya na fita dan ganin mike faruwa...........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖8️⃣0️⃣ ______________ ........Tofa babbar magana. Dambe ne fa ya harƙume tsakanin Mariya da ƙawayen Momyn Nibras. Dan suna shiga sashen basu kula kowa ba suka haye sama Momyn Nibras ɗin na ƙwalama Mamy kira. Mamaki yasa duk ƴan uwan nata ƙoƙarin tsaida su amma basu saurarensu ba sai ma hankaɗe duk wadda ta nema taresu suke cike da bala'i suna faɗin ba dasu zasuyi ba Mamy ce daidai da su. A haka suka ƙarasa hawowa falon saman. Sai kuma duk suka ja tunga ganin su Aunty Rufaidah dake jiran dawowar Hajiya Majdiya, suna a ɗakin Mamyn ne kwakwazon su Momyn Nibras ya fito da su. Jinin Darma manyansu da yaransu jinin girma ne da kamun kai, ALLAH kuma ya musu kwarjini wannan tamkar a jininsu ne. Aunty Siyama ce ta ce, “Lafiya kuwa haka Hajiya su wanene ku?”. Ji sukai sun kasa mata da hargagin da suka shigo. Momyn Nibras ta ce, “Wajen Kamila muka zo”. “Amma ko wajenta kuka zo bayin ALLAH ya ƙyautu ku shigo mata gida a haka kenan? Kar ku manta nan fa sirrinta ne, inama laifi ku jira a down stairs amma har upstairs babu wani excuse. Wannan take hakkin ɗan adam ne, sannan babu girma sam”. Mariya dake hawowa ta ce, “To dama wannan suna da girma ne in ba na jikinsu ba. Wai baku ganeta bane, uwar waccan yarinyar ce fa matar Fawzan da akama kishiya”. Da mamaki kowa ke kallon Momyn Nibras a karo na farko. A fusace Momyn Nibras ɗin ta ce, “Ke kuma a suwa ana magana da manyan gida kina saka baki ƴar a jira aci a wanke kwanika. To ahir ɗinki da saka baki anan. Dan ke baki isa ba ita Kamilar ce dai-dai dani. Idan kuma ba tsoro ba ta fito nan muyita naji dalilin yima gudan jini na kishiya bada saninta ba, dan an ga munyi kawaici mun kauda kai kuma yau ƙaton banza ya ɗaga hannu ya mata har mari uku dan ta nema sakinta. To ina son naji ita ta saka shi yay marin ko kuwa raɗin kansa ne?”. “Ikon ALLAH yau naga masifa. Yo ita ƴar taki har wacece da baza'a mata kishiya ba. Juyar da bata haihuwa sai dai taci takai masai kullum. To mu ƴan duguy-duguy muke son gani dan gidan Darma gidan ƴaƴane kema kin sani.” Mariya ce da wannan murtani a jarabe. Aiko kalmar juya da aka kira Nibras da tafi komai yima Momyn Nibras ciwo yasa Mariya na rufe baki ta sauke mata mari. Tace manyan matan da tazo dasu wai ƙawayenta wai suma Mariya dukan tsiya su saita mata bakinta, dan duk duniya babu mai kira mata ɗiya da juya ya kwana lafiya wanan gangan ne. Yo ALLAH na tuba Mariya dama ƴar daru ce. Aiko kafin kace mi ta fara musu dukan kan uwa da wabi. Tuni ta kaɗosu ƙasa dan tace suje filin tsakar gida wasan zai fi musu dai-dai ita nan ya mata kaɗan. Shine fa suka fito har compound ana dambe. Duk kuma abinda ya faru a kunen Mamy ne dake fama da kanta. Ga azabar ƙunar cikin zani ko ƙafa bata iya haɗewa da ƙyau ga kuma ta ƙafar da hannu ga raunikan fuska. So take kuma tai kuka amma sam yau hawaye sun ma ƙi su zubo mata sam. Ji take a ranta ashe kuka rahama ne ga bawa. Ita fa duk wannan ba shine damuwarta ba ma, hankalinta na'akan Abah ne, so take ya shigo sashen ko zazaginta yayi zataji sanyi a ranta. Dan Wlhy UBANGIJINTA ne kawai yasan iyakar soyayyar da zuciyarta kema Abah. Zata iya ɗaukar komai amma banda fushinsa ya mata girma. Musamman a mihalin shiru, dan tasan wanene Abah kai masa laifi ya maka shiru, sai ka gwammace ya maka duka ma an wuce wajen.... Da ƙyar da ƙyar aka raba Mariya da ƙawayen Momyn Nibras. Zuwa sannan itama Nibras ɗin ta fito. Ƴar zubama juna ashariya manya-manyan aka koma yi, yayinda Momyn Nibras ke faɗin, “In har Fawzan ya cika ɗan halak ya sakar mata yarinyarta, tace bata auren ko dolene. Yanda ta birkice sai kuma ya tada hankalin Nibras, dan ita ba haka take so Mom ɗinta tayi ba. Idan kuma ta ɓata da ƴan family ɗin taya in Fawzan ya saketa zata dawo ta auri AA ne. Ƙoƙarin riƙeta take tana faɗin, “Mom Please kiyi shiru mana. Bafa sai kin zagi kowa ba kibi komai a hankali”. Ina sam bata jinta. Fawzan da ransa ya ɓaci ya daka wata mummunar tsawa yana isowa tsakkiyar faɗan. Cikin wani irin fushin da kowa zai iya rantsuwar bai taɓa ganinsa a ciki ba ya ce, “Badai saki take buƙata ba, to kije da ƴar taki ni Fawzan Aliyu Abubakar Darma na......” Tsawa shima Abah ya daka masa. Tare da faɗin, “Kull ka furta Fawzan, kai da nake kallonka ne haƙuri a gidan nan. To ban yarda ka saki matarka ba, suyi duk abinda sukaga zasuyi mugani. Babu abinda ya dameka da rikicinsu can suje su ƙarata tunda babu wanda yasan lokacin da suka ƙulla. Ko ka sani?”. Kai Fawzan ya girgiza. Sai kuma cike da girmamawa ya ce, “Kayi haƙuri Abah, raina ne ya ɓaci, kaga fa irin zagin da sukema mutane na rashin mutunci”. “Zagi suyi tayi ai baya tsiro a jiki. Kuma ba ƙurji bane bare idan yayi ruwa ya fashe warinsa ya addabi kowa. Tunda da suka zo bakai suka nema ba ka barsu da wadda suka nema ɗin ita ta sakar musu ƴar”. Babu wanda kalaman Abah basu girgiza ba. RK ya saki wani makirin ɓoyayyen murmushi, zuciyarsa na faɗin anya Abah kuwa bai san halin Mamy ba pretending kawai yake. Kai wannan al'amari da mamaki yake. Ƙoƙarin barin wajen kowa ya fara musamman su ahalin Darma ɗin ma saboda suna respecting maganar na sama dasu matuƙa sai Hajiya Majdiya ta dakatar da su. Cikin damuwa ta tuna musu halin da Mamy take ciki. Wani irin zabura Oum tayi tana faɗin, “Suhanallahi shine kuma duk bamu sani ba. Wane kuma jiran umarni ake likitan ya shigo kawai ciki.” baiwar ALLAH jikinta har rawa yake ta nufi sashen Mamy. Sai suma su Babban Yaya da su Umma suka rufa musu baya. Suma dai su Momyn Nibras ɗin jin batun rashin lafiya yasa ta shanye komai. Dan ita wlhy wannan bala'in yanzu ne aka farashi su da Mamy har sai an sakar mata ƴarta. Ai sanda Mamyn taje tana roƙarta a aurama Fawzan Nibras ta tabbatar mata sufa ahalinsu ba'a musu kishiya. Mamyn kuma ta tabbatar mata suma haka suke, itace kawai tsautsayi da soyayya ya sata shiga gidan mai mata. Dan haka Fawzan da Nibras kishiya ko'a mafarki babu ita, shine dan rainin hankali kuma za'ai mata yanzu. To wlhy sai inda ƙarfinta ya ƙare kuwa..... ★Babu wanda halin da Mamy ke ciki bai girgiza ba a cikin su Oum. Ransu kuma ya ɓaci da rashin sanar da su da akayi. Aiko Umma ta fara faɗa sosai musamman akan ajiye Mamy gida da sukai maimakon su wuce da ita asibiti tun dare. Sannan ko babu komai sun san ai Rafeeq likitane, koda ba likitan fannin halin da Mamyn ke ciki bane ai zai kira wani ko. To dama suka ajiyeta a gida su basu sanar musu ba basu kaita asibiti ba mi suke nufi da hakan ne?. Aiko nan fa hankalinsu ya tashi, suka shiga rantse-rantsen son kare kansu suna kallon Abah ko zai yi magana dan wlhy tsoronsa da ganin da yay musu ya hana su sanar da mutanen gidan ya kuma hana su kaita asibitin. Amma abin mamaki bawan ALLAHn nan tamkar ma bai san mi ake tattaunawa ba. Zaki rantse bai san komai ba. Haƙurin dai da dattijan ciki suka babbada da amsar laifinsu yasa Umma tai shiru. Duk fitowa sukai a ɗakin aka bar doctor da RK sai Babban Yaya da Fawzan a ciki. Shi dai RK yana ganin ƙafar yasan dole akwai karaya, amma bai ce komai ba yabar likitan da suka kawo ya dubata. Likitan nan na gama dubata sai cayay ba sai anje asibiti ba gocewar kashi ce kawai da ɗan targaɗe zai dubata kawai a gida. Haka suka bashi dama ya fara aikinsa. Hannun ya fara taɓawa, aiko hajiya Mamy ta tsandara ihu sai da su Babban Yaya suka riƙeta, ashe wasa farin girki. Sai da akazo kan ƙafa harda fitsarinta, gashi shima fitsarin wata azaba ce idan yana fita dan waje dai ya ƙone kuma taƙi magana. Sosai ta wajigu, ba ita ba hatta su Fawzan suma sunyi sharkaf da zufa. Harda sumanta kafin a gama. Ana gamawa dole akai mata allurar barci.... Lokacin salla yayi, dan haka kowa ya nufi yin tashi, dangin Mamy suka fara shirin wucewa kamar yanda Maman Saheeba ta nuna musu dama Saheebar. Dan sun samesu sukace ya kamata su tafi haka nan tunda anci biki an cinye, kar suga waɗan can basu tafi ba sufa dangin maigidan ne. Bayin ALLAH badan sun so ba sukace to. Aiko suka fito suna murmushin samun nasara, dan sunyi haka ne saboda Mariya, sun kula in dai tana a gidan bazasu sami yin rawar gaban hantsi ba yanda suke so. Cike da taƙama Saheeba ta nufi sashenta dan tun jiya har yanzu bata samu komawa ba saboda yanayin da suka kwana suka tashi, mizai faru ta samu ƙofa a rufe. Ta koma ta hanyar kitchen nan ma a rufe. Mamaki ne ya kamata, dan ko fita zasuyi basu taɓa kulle ƙofa ba koda duka gidan ne kuwa. Sai zuciyarta ta bata kodan Babban Yayan yaga da baƙine shiyyasa. Sashen Mamyn ta sake komawa wai har ya dawo massalacin.... _________★ Bayan dawowar su salla kaɗan AA ya farka. Lokacin RK na tare da shi dan yana saka ran farkawar tasu dama kusan a yanzu. Babu kowa a sashen sai yara ma da aka saka sukazo suka sake gyara ko'ina tsaff. Sai Hajiya Shuwa da Oum dake ɗakin Maanal suma yanzu suka shigo babu jimawa. Dan Oum nacan ta saka ama su AA ɗin abinci mai rai da lafiya. Da kanta taso tayi ma sai ga Hajiya Shuwa. Sai tace Hajiya Majdiya tayi. To tana fitowa Mah-mah tace Hajiya Majdiya ɗin ta barshi itama bari ta musu ita. Dan abu na musamman take son shiryama ƴan jikokin nata. Ai ko sai Gwaggo Khadijah ta shigo suka jone. Abinka da tsoffi an san takan sirrikan abubuwa, nan fa suka shiga haɗama Maanal haɗin nama da wasu abubuwa na musamman, sai abincin shima irin na tsoffin hannu ya subahannallah..... Da taimakon RK AA ya tashi, Alhamdullah zazzaɓi ya sauka. Hakama cikinsa da kansa duk komai sai godiyar UBANGIJI. Sai ma wani irin fresh yake jinsa tamkar sabon mutum. Tambayoyi RK ya ɗan masa ya sake tabbatar da komai normal sannan ya taimaka masa zuwa bayi dan yayi wanka. Da kansa ya gyara masa ɗakin, fitowa yay dan bincika ko itama Maanal ta farka...........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖8️⃣1️⃣ ______________ .........Alhamdullah itama Maanal ɗin ta farka. Dan RK na fitowa sai ga Oum ta fito domin kiransa tace masa Maanal ɗin ta farka yazo ya cire mata ruwan da ya ƙare har jini ya ɗan fara komawa ciki. Hajiya Shuwa na zaune kusa da Maanal data ƙi buɗe ido ta kallesu tunda ta farka wai ita kunya. Jin RK kuma ya shigo sai taji kamar ta nutse ma a cikin gadon ta huta. Shi dai ya cire mata ruwan, sai Hajiya Shuwa ke tambayar basu shigar musu aiki ba idan sukama Maanal amfani da magungunan gargajiya wajen sit bath ko. RK ya tabbatar mata in dai an yarda da ingancin su babu wani abu. Fita yay ya barsu dan ya fahimci halin da Maanal ke a ciki. Aiko yana fita Hajiya Shuwa ta tashi ta fita kitchen da kayayyakin tana faɗin Maanal ɗin taje tai wanka tai salla kafin su dahu. Da ƙyar Maanal ta yarda Oum ta tadata zaune. Sai kuma azaba ta sakata shiga jikin Oum dan bazata iya zama ba. Murmushi Oum tayi, cike da tsokana ta ce, “Babyna raguwa”. Sake ɓoye fuska Maanal tai a jikin Oum. Hakan ya sake bama Oum dariya. Ta ce, “Oh ni Fateema yau ke da mijinki duk kun maida ni surukar ku dai a gidan nan. Haba Babyna, Oum ce fa. Ai ni yau babu abinda zance da UBANGIJI sai godiya, ALLAH yay muku albarka, ya zagaye rayuwarku da farin ciki, ya baku zuri'a masu albarka. Yanda ALLAH ya bayyana gaskiya yau abinda muka daɗe cikin ɓacin ransa ya kasance ba haka bane ALLAH ya shafe mana dukkan zunubanmu. Na kira ƙanwata na sanar mata komai harda kukanta. Na rasa ma miya shiga kammu a lokacin muka gagara fahimtar babu abinda ya faru dake? Koda yake muna cikin ruɗani sosai, kuma ya riga shima ya amsa yayi ashe yaron nan baiyi ba.....” Karan farko dai Maanal ta ɗago ta kalla Oum, cikin kasa daurewa a wannan gaɓar ta ce, “Oum wai da gaske ne abinda doctor ta faɗa ɗazun kenan?”. “Da gaske ne Baby na, babu abinda ya faru tsakanin ki da Auta a waccan ranar. Bamu san dalilinsa na amsawa da yayi ba. Mukuma firgici yasa bamu nutsu mumma dubaki ba da kammu a lokacin, kawai jinin dake zuba a jikinki da wanda ke a jikinsa yasa muka aminta yayi. Shi kuma doctor ɗin daya dubaki ban san dalilinsa na yi mana ƙarya ba. Amma yanzu dai kowa Auta yake jira ya tashi muji yaya aka faɗi a ragaya. Aban ku kuma har yasa a bincika masa likitan daya dubaki a waccan ranar muji shi kuma dalilinsa na mana ƙarya.” Hawaye ne sosai suka ziraro a fuskar Maanal, komai daya faru a waccan ranar ya shiga maimaita kansa a ƙwaƙwalwarta. Muryar Ajwaad da ƙamshinsa da taji, faɗa mata jiki da akayi, fara kissing nata daga haka bata sake fahimtar komai ba, kawai ta farfaɗo akace ai ya mata fyaɗe ne. Abubuwa suka rikice saboda mutuwar baba Haruna suka wuce Giro. Ciwo ya kwantar da Ammie mutanen gida da su Gwaggo suka cigaba da wulaƙantasu harda Babu, hatta mutanen gari ma basu barsu ba aka koma aibantasu ana cewa tayi cikin shege, kai su bama ƴaƴan Babu bane daga waje Ammie ta rorosu. A lokacin bazata iya ƙarar da cewar fyaɗen ne ya sata a halin ciwo ba. Amma tana jin ciwo a zuciyarta idan ta tuna an mata fyaɗe kuma Ajwaad ne. Bestyn ta fa. Bata san ainahin minene fyaɗe ba kai tsaye ko a aikace. Amma yanda al'ummar duniya ke ƙyamatarsa harda ma saɓanin musulmai yasa itama taji ƙyamatar abun a ranta a lokacin ƙwarai da gaske. Amma shigarta cikin matsanancin halin ciwo shine, ƙuncin rayuwa fa suka tsinta kansu, zafin rabuwa da Ajwaad dake cinta a ƙansan zuciya. Abinda ya aikata mata da rashin biyo sahunsu da basuyi ba. Sai firgicin tsorata da tayi a lokacin da take da tabbacin Ajwaad ɗin ne yake ƙoƙarin keta mata mutumcin, tunda a lokacin ne ta suma shiyyasa abin ya zauna daram a brain nata. Koda ta girma ta ƙara hankali ta sake tantance mi ake nufi da tabon fyaɗe ga ɗiya mace sai al'amarin ya ƙara zafafa ta, musamman da shekaru suka cigaba da ja babu Ajwaad babu labarinsa......” Oum ce ta katse mata tunani ta hanyar share mata hawaye. Cike da lallashi ta ce, “Kuka ya ƙare ai Baby in sha ALLAHU, tashi muje kiyi wanka kiyi salla kema Rafeeq yace shima Auta ya farka”. Kai Maanal ta jinjina mata, sai kuma kanta a ƙasa ta ce, “Oum shima baida lafiya?”. Kai Oum ta jinjina mata tana murmushi, ta ce, “Yana taya Bestyn sa jiyya mana”. Siririyar dariya Maanal tayi saboda yanda Oum tai maganar tana lakace mata kumatu cike da tsokana. Itama Oum ɗin dariyar tayi. Tare da miƙar da ita suka nufi bayi tana takawa a hankali. Dan har yanzu tana jin zafi sosai a wajen, labarin farin cikin nan ne kawai ya sata dannewa. Sai da Oum ta haɗa mata ruwan wanka masu ɗumi sannan ta fito ta barta, haka Maanal ta fara wanka tana sake nazartar abubuwa. Kamar zararriya tana hawaye tana murmushi. Ƙasan zuciyarta kuma na mamakin dalilin Ajwaad na amsa laifin da bai aikata ba. Ashe shiyyasa bai taɓa bata haƙuri ba, kai tunda suka sake haɗuwa bai taɓa tada mata zancen ba. Lallai yanzu ta sake yarda RK ya fahimci Ajwaad matuƙa, dan shine ya ɗan fara mata shaguɓe akan hakan. Amma ita koda ta karanta abinda AA ɗin ya rubuta fassarar data basu daban ce. Jitai ma ta ƙagara ya shigo suga juna. Haka dai ta kammala wankan tai alwala. Cike da dauriya ta fito ita kaɗai, ashe ma Oum na kusa tana jiranta. Itace ta taimaka mata suka ƙarasa, har an gyara ɗakin tsaff an saka kamshi. Oum ta bata doguwar riga tace saka tai salla yanzu Hajiya Shuwa zata dawo, ita kuma ta fita tana cigaba da faɗin “Bara na duba ko Majdiya ta kammala muku abincin”. Kai Maanal ta jinjina mata, ta ɗauka Abayar ta saka da hijjab, cike da dauriya tai sallar azhar ko zama bata iyayi da ƙyau. A haka Hajiya Shuwa ta shigo da botiki babba yana ta tururin ruwan zafin dake a ciki. Maanal ɗin na idar da salla ta kamata suka nufi bayi..... _________★ Yaya Fawzan dake fitowa a wanka ya nufi wayarsa dake haske alamar kira ya tsinke ko shigowar saƙo. Wayar nada alaƙa da komai nasa mai muhimmanci ne shiyyasa baya wasa da ita. Ilai kuwa Najma ce ta turo masa message. Zama yay a bakin gado kafin ya buɗe, abinda ta tura masa ya saka shi sakin murmushi, tun shekaran jiya ita ta wuce gida da yamma tare da ƙannenta dan jiya ta fara jarabawa. Idanunsa ya lumshe ya buɗe dan kowannensu ya iya wannan ɗabi'ar AA ne kawai ya ɗara kowa dan shi komai nasa irin na Aba ne sosai. Hasken fata kawai zai nuna masa dan Abah shima fari ne tas kamar su Fawzan. Ƙoƙarin kiranta yay amma wayar a kashe, ya sake sakin murmushi yana kaiwa kwance. Babu abinda ke dawo masa a zuciya sai washe garin ɗaurin aurensu. Dan ranar da aka daura auren bata yarda sun haɗu ba ko a wajen dinner ɗin su AA tana maƙale da Mah-mah saboda shi. Shi kuma sai yay kamar bai ganta ba duk da yana cike da ɗokin kadaicewarsu sai a washe gari. (To bari mubi tunanin Yaya F muji miya faru shi da ƴar shalelensa a waccan ranar da bamu sani ba😂🙏). A ranar walimar su Maanal data kasance washe garin ɗaurin auren sa da Najma bayan ya gama wahalar bin duk hanyar da zasu haɗu ta toshe kwatsam sai gata ita da Aunty Rufaidah sun dawo daga gidan Hajiya Shuwa da suka je. Dan aunty Rufaidah na son a mata gyara ita da Nuwaira. To sai Nuwaira ta tashi a safiyar da zazzaɓi abinka da mai laulayi. Shine Oum tace a haƙura da nata gyaran jiki aje ama Najma a maimakonta, ita Nuwaira tunda suna nan a Abuja idan ta samu sauƙi a mata dan RK yace bazata koma Kano ba yanzun. Shine fa sukaje akai musu. Sunyi ƙyau sosai masha ALLAH. Suna shigowar ne shi kuma yana fitowa a sashensu zai shiga mota. Suna haɗa ido da Najma ta wani basar ta ɗauke kai harda ƙara sauri. Aiko sai ya wani dake ya ce, “Najma zonan”. Cak Najma ta tsaya gabanta na faɗuwa, zuciyarta na gudu a ƙirjinta. Basu san raina na gaba da su ba musamman ma yayun nan nasu. Ga Aunty Rufaidah tayi kamar ma bataji mike faruwa ba tayi gaba abinta dan waya take da mijinta. Cike da sanyi jiki kai a ƙasa Najma taje, sai wani sinne kai take gana gaishesa. Ƙin amsawa yay ya buɗe mata mota yace shiga. Idanu ta waro sosai waje, zatai magana yay mata alamar zipping. Dole ta rufe bakin ruf ta shiga ya maida ya rufe ƙofar ya zagaya nasa waje shima ya shiga. Komai baice mata ba ya tada motar ya fice a gidan. Tun tana tunanin zasu tsaya a cikin anguwar ne har taga ya bar ta yankin ma gaba ɗaya, sai da yaje wani waje da babu kowa shiru duk Companys ne ma sannan ya samu ƙasan wata bishiya yay parking. Ita dai kanta a ƙasa tama kasa kallonsa. Shi kuma ya zuba mata ido yana kallon yanda taketa cuɗa hannunta a cikin na juna alamar a tsorace take, nishaɗi sosai abin ya saka shi da dariya amma ya dake. Muryarsa ba wasa ya ce, “Babu gaisuwa”. Muryarta a ƙasa sosai ta ce, “Kayi haƙuri ina yini”.. “Bazan amsa ba sai da na roƙa! Kuma ai bama haka ake gaida miji ba”. Fuskarta tai ƙoƙarin ɓoyewa tana murmushi ya riƙota, a bazata ya wani jawota gaba ɗayanta ta koma jikinsa ya rungume ta tsam-tsam. Uhmm su Hajiya Najma ko musu babu akai luff a jikin Yaya Fawzan. Sai ma sauke ajiyar zuciya suke a tare. Dan shi zuciyarsa har wani gudu take a ƙirji, sakamakon hakan ya jima bai faru a tsakaninsa da Nibras cikin salama ba. A farkon aurensu dai komai normal ne, amma tunda Ajwaad ya dawo gidan nan komai ya canja, bukatarsa ma zai biya sai da ƙarfin tuwo balle runguma. Kiss kam ai tun na farkon amarci bai ƙara samu ba. Dan haka tuni ya shiga laluben bakin Najma a lokacin, sai ko bata hanashi ba ta bashi dama harda taimaka masa duk da dai a kunyace take sosai, aiko sai ya rikice mata, ya shiga sumbatar ta tamkar zai cinye mata lips. Daga ƙarshe ma al'amarin ya shiga canja salo sai da ta shiga roƙonsa. Da ƙyar ya iya barinta, dan harga ALLAH shi kansa bai san fitinanne bane irin haka sai tsakanin daren da aka ɗaura aurensu daya kwana da ita a ransa zuwa ranar.......✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖8️⃣2️⃣ ______________ ........Sun jima shiru fuskarta na ɓoye a jikinsa kafin a hankali ya furta, “Thanks you Love! Na godema UBANGIJI daya bani ke a matsayin mata. Na kuma godema Babban Yaya da Uncle Rafeeq da Ajwaad daya kasance gaba-gaba na ganin kin zama mallakina na har abada. Naso ace an bani ke a yau ɗin nan koma tun jiyan, amma ba komai zanyi haƙuri har ki kammala exam ɗinki maybe dariyan dana dingama Auta ce ta bini nima”. Dariya Najma ta sanya. Fuskarta a ɓoye ta ce, “Ato shiyasa ai tsokana ba ƙyau, gashi shi an bashi tashi kai kuma zaka fara naka zaman jiran”. Dariyar shima yayi da faɗin, “Oh hakama zaki ce. Ba komai zan rama ne yarinya. Shima kuma ba ƙyalesa zanyi ba. Ɗazun Abah yace min yau zaku wuce dan gobe zaki fara exam”. Kanta ta jinjina masa. “Eh zan tafi dasu Nah-nah zamubi train zuwa kaduna, Abba zai ɗauke mu dan yana kadunan yace zai jira mu”. “Amma shine daban ganki ba ma yanzu sai dai naji kin wuce. Gaskiya da sai na hukuntaki kuwa. A kiyaye bana son haka kinji ko. Ina son komi ya shafi matata na fara sani kafin kowa har iyayenmu. Na yafe miki wannan dan na farko ne bakuma ki sani ba.” “Thanks you Yaya, in sha ALLAHU bazan sake ba kuma kayi haƙuri. Ina jin kunya ne kawai dama. Dan komai yazo min ne a bazata. Amma jiya da naji an ɗaura mana aure bamma san yanda zan musalta abinda naji ba gaskiya.” Murmushi sosai yayi yana kallonta, ji yake kamar ya haɗiyeta ya huta. Ga wani irin canjawa da jikinsa ke neman yi. Haka dai ya daure ya amshi wayarta yay abinda zai yi, sannan ya saka mata kuɗi masu yawa a account ɗinta ya sake rungumeta ya sumbaci lips ɗinta. Cike da sanyin yanayi ya ce, “Idan kun shirya ki kirani dan da kaina zan kai amaryana station ɗin”. “Thanks you Yaya”. Ta faɗa a hankali tana sake lafewa a jikinsa..... Bugo ƙofa da shigowar da akai ya yanke tunanin nasa, a hankali ya buɗe idanunsa dake a lumshe ya sauke akan Nibras dake wujiga-wujiga yau ko wanka batai balle ai maganar taci wani abu ma. Sai huci take na bala'i, tsabar son bata haushi sai ya sake maida idanun ya lumshe kamar bai ganta ba..... _________★ Sosai Maanal tasha gashi a wajen Hajiya Shuwa ta kuma sha kuka. Amma harga ALLAH taji daɗin jikinta sosai dan hatta jikin nata Hajiya Shuwa saida ta daddana mata da towel kamar wata mai jego. Baiwar ALLAH sai sauke ajiyar zuciya take. Bayan sun fito ta sata tai tsigunnen turaren wuta na jiki dana ƙasa, harma dana gashi ta kuma busar mata da shi ta gyara mata tsaf duk da tana faman raki. Kafin ta taimaka mata ta shirya cikin abaya mara nauyi ƙirar dubai. Ta ɗan gyara mata fuska aka ƙara gyara ɗakin aka saka masa turare. A lokacin Oum ke dawowa da abincinsu tare da Meeno data ɗakko. Meeno ta gaida Maanal cike da damuwa dan yarinyar nasan Maanal sosai, har catai mata ita bazata koma Kano ba zata zauna a wajenta. Maanal kuma ta mata alƙawarin in sha ALLAHU zata sa a barta dan itama tana son yarinyar, kodan ta ɗanyi duhun fata irin ta AA ne oho, gashi tana kama da shi sosai koda yake kaf family ɗin Darma kama suke da juna na bala'i ma kuwa. Sosai Oum taji daɗin ganin yanda Maanal ɗin tayi ƙyawun gani, sai idanun da har yanzu suke a kumbure dan manyan mata sun sha kuka. Dan ma yanzu Hajiya Shuwa ta saka mata kwalli. Oum bata zauna ba suka fice da Hajiya Shuwa, itama Meeno suka tisa ƙeyarta dan yanzu RK ke sanarma Oum da zata shigo AA fa nason zuwa ya duba matarsa ya damu. Shine Oum tace to bari ta bar musu abincin kawai a tare ba sai an kawo masa ba. Aiko suna fita bai fi da mintuna uku ba Maanal na kwance da wayarta a hannu zata kira su Didi da taga miss call ɗin su harda Ammie aka buɗe ƙofar. Idannunta ta ɗago a hankali ta kalla wajen jin ba'ayi magana ba kuma ba'a ƙarasa shigowa ba. Ido huɗu sukai da AA, a hankali ta lumshe idanunta ta maida kanta ta kwantar. Shima sai ya lumshe nasan ya buɗe a lokaci guda, sai kuma ya maida ƙofar ya rufe sannan ya shiga takowa ciki. Ƙananun kaya ne a jikinsa da suka masa ƙyau sosai. Kai da ka gansa kaga sabon ango fill a kwali dan sai ƙyallin goshi yake. Lips ɗinsa ya wani koma pinkish sosai alamar ansha shagali da shi daren jiya. Idanun kam sunyi tar-tar da su kamar an watsa madara da oil a cikinsu. Sai da ya ɗan tsaya a kanta ya gama ƙare mata kallo sannan gently yakai zaune a kusa da ita. Ƙoƙarin matsawa tai da sauri, shi kuma slowly ya riƙota ya hana ta. Sai ta kauda fuska gefe. Wani lallatacen murmushi ya saki a karo na farko. Sai kuma ya ɗan leƙa fuskar tata, nan ma da sauri ta sake juyawa, ya sake leƙota ta can, sai kawai taja pillow ta ɗaura a fuskar. Yanzu kam dariya yayi mai sanyi. Sai kuma ya ɗan rufu a kanta ya janye pillow ɗin. Veil ɗin abayarta ta sake ja ta rufe fuskar. Nan ma ya sake murmusawa, tare da ɗaga veil ɗin ya shiga da fuskarsa ciki shima. Hancinsu na gogar na juna lumsassun idanunsa na kallon nata dake rufe. Sai kuma ya shiga matsar da bakinsa a hankali zuwa saitin idanunta. Iska ya shiga hura mata akan idanun. Murmushi ke son suɓuce mata amma tana danneshi da tsiya-tsiya. Murya can ciki a yanayin raɗa ya ce, “Bazan tambayeki komai ba sai lafiyar ki Besty. Idan kina dariya, ZUCIYATA tana hutawa, farin cikin ki na mantar dani duk wani tarnaƙi da rikicin dake cikin duniyar nan. Your smile lights up my world, please let me see it again ZUCIYATA”. A hankali Maanal ta saki murmushin da batai niyya ba. Ji AA yay kamar ana narkar masa da zuciya da wannan murmushi, dan haka ya lumshe idanunsa a wani irin hankali ya sake buɗewa a kanta. Cikin sake maida muryarsa ƙurya matuƙa ya ce, “Open your eyes dan naga hasken da nake so, ki kalla mijinki, kiga lallashi da tarin ban haƙuri dake cikin nasa idanun.” Tamkar wadda yake control da remote nan ma ta shiga buɗe idanun sannu a hankali. Zubama juna kallo sukai irin mai ratsa zuciya da ƙashi ɗin nan ya marmasar da ɓargo. Sai idanun Maanal suka shiga tara ƙwalla. “I'm sorry! Na tuba bazan sake ba Besty, na tuba! Na tuba. Please for give me zuciyata cike take da nadama. Ki hukunta ni da kowanne irin hukunci da zai sa ki yarda shine dai-dai da abinda na aikata a daren jiya. Ki.....” “Shhhhhiiii!!!”. Manaal ta faɗa a hankali tana ɗaura yatsarta a saman tausasan lips ɗinsa idanunsu na cikin na juna. Har yanzu fuskokinsu na cikin veil ɗin. Shirun kuwa yay yana kallonta kamar yanda itama take kallonsa da kumburarrun idannunta, sai dai cike suke da laushi da sanyin yanayi, kamar yanda nashi ke cike da lallashi da damuwar halin daya jefata a ciki, dan RK ya masa bayanin komai. Muryarta data sha kuka har yanzu take a dusashe ta sake marairaicewa kamar zata saki kukan yanzu ma ta ce. “Besty! kafin yau ina kallon kai tamkar rubutaccen littafi ne daga kundin rubutacciyar ƙaddarata, amma a yau na fahimci kai ɗin ne da kanka gaba ɗaya kundin ƙaddarar tawa. Kai tamkar wani darene da ake bege da buƙata da fatan gani a shekara ɗaya tak na cikin rayuwa.....” Cikin narkewa AA ya ce, “Wane dare ne haka Besty na?”. “Daren lailatul ƙadri. Shi ya kasance ɗaya tak da kowanne bawa ke fata da zalamar riska, da yin aiki tuƙuru domin samuwar kodan rabauta ne a duniya, balle ma har lahirar muna fata. To kai a tawa duniyar tamkar wannan daren ne. Da ace za'a bama mata damar zaɓen Namiji sau dubu a rayuwarsu lallai kai zan zaɓa sau biliyan cikin biliyan matsayin aboki, yaya, kuma MIJI. Daga daren jiya zuwa yau ka sauya ni gaba ɗayana da martaba da mutuncin dana gama sallamawa da samuwarsa ga irinka namiji. Dan na jima ina tsoron dare irin na jiya dana san dole zan riska in dai ina a raye koda a bigiren tilas ne, na jima ina tunanin yanda ranar farko zata kasance mai ɗaci da zafi da ƙuna a gareni koda banga canji daga mijin aurena ba, amma ka sauya min ita, ka maida min ita inuwa mai ƘAMSHI mai TSARKI. Mai TSARO. Mai DARAJA. Mai RAHAMA. Mai cikakkiyar SALAMA. Nagode Besty! Nagode da wannan ƙyauta, AJIYA A DUHU ta zame min AJIYA MAI HASKE.....” Kuka ya ƙwace mata mai ƙarfi, ta rungumesa gaba ɗaya tanayi kamar zata shiɗe. Dan tamkar tana kukan tsahon shekaru ne dake danƙare a cikin ƙirjinta daskare. Tana a jiye da wannan kukan tamkar dama ƙirjinsa take buƙatar samu ta kwanta domin yinsa. Tana kukan da tuna rayuwar azabar da suka sha a Giro ita da ƴan uwanta da Ammie saboda wannan kalma ta fyaɗe ɗaya tak... Kuce min me AA keyi. Bari na baku amsa, HAWAYE yake yi, KUKA yake yi shima tamkar ita, abinda a rayuwa zaka jima baka gani a cikin idanunsa ba. Duk abinda kaga ya saka Ajwaad Aliyu Abubakar Darma kuka to lallai wannan abu ya kai a kira shi mai daraja da kima. Oum kaɗai AA kema hawaye, ita kaɗai tak. Dan ko ita Maanal ɗin zata iya rantsuwar bata taɓa ganin Ajwaad na kuka ba, tun ma suna yara sai dai kaga idanunsa sun sauya launi amma ba hawaye ba. Hatta uwar data haifesa Mamy tunda yay wayo bata taɓa ganin hawayensa ba. Amma yau kuka yake, hawaye na zuba masa. Kalmomin Maanal na kekketa masa zuciya. Yana jin shine ya cancanta yay mata godiya, ya durƙusa a gabanta ya nema gafararta, ya ɗauketa ya riritata, ya goyata ya zagaya duniya da ita, ya shelantama kowa ita ɗin RAYUWARSA ce. Ta masa hallaci, zuri'arta sun musu hallaci musamman mahaifiyarta da ƴan uwanta guda biyu. Ba Maanal kaɗai yake ƙauna ba, wlhy har Ammie ƙaunarta yake irin kwatankwacin ƙaunar da ɗa kema uwa. Har Shahidah da Amaal ƙaunarsu yake irin kwatankwacin ƙaunar da yake ma Babban Yaya da Fawzan. Jinsu yake a jinin jikinsa saboda bashi da abinda a duniya zai kwatantama wannan zuri'ar da shi. Sun jima a wannan yanayin mai taɓa zuciya. Kafin ya ɗago yana share mata hawaye. Idannunta dake rufe ta buɗe a hankali, ganin hawaye a fuskarsa shima ta wani waro nata tare da ɗaura hannunta a baki. Cikin muryarta ta kuka ta ce, “Lah kuka kake yi?”. Dariya ta bashi dan yanda tai ɗin sosai cikin nuna shock ne. Murmushi ya saki mai faɗin gaske da har haƙwaransa na bayyana sai kuma ya kauda kansa gefe ya sharesu tas. Kafin ya juyo yana kallonta, ya ja hancinta kaɗan cike da raɗa ya ce, “Bafa kuka nake ba hawayen amarya ne suka shafeni. Kin san ita amarya ita komai nata daban yake”. Dariya sosai ta kuɓucema Maanal. Taja hancinsa itama da faɗin, “Ai shima ango komai nasa daban yake”. Cikin ɗan taɓe baki da waro idanu ya ce, “Uhhhyim!! Kamar mi da mi kenan?”. Itama bakin ta ɗan taɓe kamar yanda yayin ta ce, “Bazan faɗa ba sai ka biya”. Kafin ma ta rufe baki ya sumbaci lips ɗinta, hancinta, da idannunta ya ce, “Wannan yayi?”. “Uhm-uhm yayi kaɗan gaskiya”. Lips ya wani kalar ciza, yana ɗage mata gira, ita kuma ta juyar da kai tana dariya. Fuskar ya taro ya maidota, sai kawai ya manne lips ɗinsu ya fara kissing nata. A mamakinsa itama sai ta shiga bashi haɗin kai harda maida murtani. Ai ko brain ɗin AA neman tarwatsewa yayi, tuni ƴan maza suka fara ƙwacewa daga sunansu na Maza........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖8️⃣3️⃣ ______________ ........Maanal da itama ta lula gaba ɗaya sai da taji salon ya fara canjawa da shiga bubbuga masa baya ta maidosa a hayyacinsa. Yana sakin mata baki ta juya masa baya. Baice komai ba ya rungumeta kawai sukai shiru. Fin mintuna biyar suna a haka shiru kafin ya raɗa mata “I'm sorry” a cikin kunne. Murmushi tayi kaɗan, wani shauƙi na ɗawainiya da ita. Sai ta kawo hannu kawai ta shafi fuskarsa a haka batare data juyo ba. Hannun ya kama ya sumbata. Shima wani iri yake jinsa, Wlh ji yake tamkar zuciyarsa zata fashe, bai taɓa jin abu a ransa irin yarinyar nan ba. Idan yace zai zaman furta abinda yake ji akan Maanal da baki ɗauka za'ai ya haukace ne ma. Kiran sallar la'asar ne ya sashi tashi zaune. Ya kamata dan ta tashi itama ta saki ƴar ƙara saboda zafin da taji. Da sauri ya maidata ya kwantar, zuciyarsa na raunana ya ce, “Miya faru?”. Baki ta ɗan tura masa, cike da shagwaɓa tace, “Zafi fa, wajen na zafi bana iya zama”. Sosai yaji wani irin tausayinta, dan har ƙwayoyin idanunsa sun nuna haka. A tausashe ya ce, “For give me”. Kanta ta jinjina masa kawai, ya ɗan rungumeta a jikinsa, sai kuma ya sake raɗa mata, “In duba in gani?”. Fuskarta ta ɗan ɓoye a ƙirjinsa ta ce, “Ina jin kunyarka fa”. Murmushi ya ɗan yi yana cije gefen lips ɗinsa, yace, “Kunya kuma ta ƙare ai Babyn Oum, Besty Besty kuma Lillyn Yaya F da babban Yaya, sannan shalelen Abanta mai hana mijin ƴarsa matarsa”. Dariya sosai kirarin ya sanya Maanal. Ta ja masa ɗan gashin gemunsa dake dan kaɗan dan baya barin yay tsaho tana faɗin, “Kai dai ka cika wayo ALLAH Besty”. Dariya AA ya sanya tamkar bashi ba. Ya miƙe kawai da ita jin ana ƙoƙarin tada salla suka shige bayi. Alwala sukayo, ya sake ɗakkota ya dawo da ita. Shi da kansa ya saka musu sallaya yay musu jam'i, suna idarwa ta miƙe dan bata iya zama da ƙyau, gashi in tana tafiya ma tana jin zafi dan haka take yi a hankali. Sosai tausayinta ya cika zuciyarsa. Haka dai ya daure sukai zaman cin abinci. Gaba ɗayansu ma akan naman da akama dahuwa ta musamman suka huce haushin yunwarsu. Sai da sukaci suka ƙoshi yana faman tsokanarta tana ɓoye fuska sannan ya bata magani tasha, shima yasha nashi. Yana son zuwa ya gaida mutane yana jin kunya, gefe kuma baya son barinta ita kaɗai. Sai wajen biyar Amaal da Shahidah da Sakina suka zo gidan. Tana cikin jikinsa yana karanta musu novel Oum ta kira shi ta sanar masa ga su Shahidah tun 4 sunzo gidan zasu zo su duba Maanal. Dama ta zata zai sakko sallar la'asar ne shiyyasa. Sosai kunya ta kamashi, dan wlhy yau kunyar Oum yake ji, kai ko Yaya Fawzan saboda shegen tsokanarsa baya fatan su haɗu, dan Rafeeq sai da ya masa tas ɗazun ƙin kulashi dai yayi. To balle kuma ace Babban Yaya da Abah. Dan shi a zatonsa ma duk baƙin sun tafi zuwa yanzu...... _________★ A ɓangaren Aunty hamshaƙiya Shahidah kuwa tanata dakon dawowar Babban Yaya daya garƙame ƙofa. Amma bawan ALLAH bayan sallar azhar bai shigo gidan ba. Sai da aka idar da la'asar harma da kusan rabin awa sai gashi ya shigo da mota ashe ma fita yayi. A dai-dai lokacin kuma Ameerah ke fitowa daga sashen Mamy ita da su Shahidah sunje sun dubata. Dan sun saba da Ameera yanzu suma tunda akai kai-kawo a hidimar bikin nan tare. Tsai babban Yaya ya tsaya yana kallon Shahidah da Ameerah dake a jere tare. Su dukansu fuskokinsu da murmushi da alama magana suke yi, sai Amaal a bayansu ita da Sakina. Iska ya ɗan furzar yana mai kauda kansa daga kan Shahidah gaba ɗaya ya maida ga Ameerah. Wani shegen murmushi data sake saki sai shima ya samu kansa da sakin makamancinsa. Sai kuma ya kai hannu ya ɗan shafi sajensa ya lumshe idanunsa ya buɗe lokaci guda, a fili ya ce, “Fadeel kana lafiya kuwa?”. Dai-dai nan su Amaal suka nufi sashen Oum, ita kuma Ameerah ta nufo hanyar gate alamar gida zata wuce dan har tana magana cikin taushin mutyarta da ɗan ɗaga sauti ta ce, “Didi ina jiranku fa dan ALLAH”. “Shahidah ta ce, “Ke dai jeki shirin tarbarmu kawai”. Dariya Ameera keyi tana tafiya da baya da baya. Sai kawai ya buɗe motar ya fito. Ya ɗan duƙar da kansa yana saka key a aljihu kawai ya jita a jikinsa. Da sauri ta juyo, dai-dai shima ya ɗago idanunsa suka shige cikin na juna. Ido ta ɗan waro waje, sai kuma ta sake matsawa baya kanta a ƙasa ta ce, “I'm sorry Babban Yaya”. Shiru bai amsa mata ba tsawon sakanni, sai kuma ya taka kaɗan ya ƙara matsawa gabanta. Kan Ameera dai a ƙasa zuciyarta na bugawa da sauri-sauri. A bazata matuƙar bazata ya ɗan duƙo saitin kunnenta ya furta, “Ranar kin bigeni kince min sorry, yau ma haka, gobe kuma idan mun haɗu ban san miza'a min ba a ƙare da cemin sorry”. Gaba ɗaya ji Ameerah tai kamar zata narke. Ta wani ɗago da sauri idannunta a ware ta kallesa, cike da suɓutar baki ta ce, “Lah na shiga uku....” “Ko dai na shiga uku ni da ake ta turewa ba”. Ya sake faɗa da wani salo mai taushi dai-dai da yanayinta yana wani ɗage mata gira sama. Ai bama tasan ta kwasa da gudu ba tai hanyar gate. Samun kansa yay da sakin dariya yana binta da kallo harta gama ficewa. Ai a tare maigadi da Bola da drivers dake hira a gate suka saki baki da hanci suna kallon Babban Yaya. Tab ɗin babban Yaya ne da dariya. Babbar magana ɗan sanda yaga gawar soja. Maigadi yace, “Sufa miskilan mutane idan suka faɗa soyayya narkewa suke yi gana ɗaya ba sauƙi”. Da sauri drivern AA ya ce, “Nizan baka labari dan ni nake ganin ainahin narkewa a wajen ogana da tashi tauraruwar. Eh lallai wato gidan nan bana ƴar aure-aure za'ai, sabon zubi aketa mana. Dama mun gaji da mugun halin ruɓaɓɓun nan Hajiya Saheeba da Hajiya Nibras.” “Wlhy munfa gaji, mu ƴan jam'iyyar amare ne ALLAH yasa ayi damu”. Cewar drivern Abah..... Dai-dai nan mai delivery yay knocking gate, tashi mai gadi yay ya leƙa. Mutumin ya gaisheshi da miƙa masa wata ƴar leda yana faɗin, “Saƙone aba Hajiya Kamila”. Sai kuma yaba mai gadi littafin hannunsa alamar ya saka hannu. Amsa yay ya saka hannun ya bashi, ya juya da ledar a hannun yay sashen Mamy yana faɗama su Bola yana zuwa... Babban Yaya kam da bai san sunayi ba tuni ya nufi sashensa fuskarsa da murmushi, sai dai yana isowa yaga Saheeba da yara alamar shi suke jira ya gimtse fuska. A take tasha jinin jikinta. Amma sai ta dake tana masa sannu da zuwa da faɗin, “Tun ɗazun ai muke jiranka nazo naga ƙofar sashen a rufe”. Maimakon bata amsa hannun Naufal da Anum dake masa oyoyo ya kama. Yasa key ya buɗe, yaran ya fara turawa ciki ya shiga. Saheeba zata shigo yay tsaye a ƙofar. Cikin watsa mata mummunan kallo ya ce, “Ina zaki?”. A daburce ta ce, “Ciki mana Daddyn Naufal”. A dake yace, “Sai dai wani cikin amma ba nan ba, ki koma can sashen Mamyn ki ci gaba da zama har sai na nemeki. Kuma ba gidan nan nace ki bari ba can nace ki zauna, dan ko nan da gate kika taka na rantse sai kinsha mamakin abinda zan miki.” Bam ya maida ƙofarsa ya rufe kafin ma tace komai. Ai garrrrr jikin Saheeba ya shiga rawar mazari kamar an kunna vibration. Brain dinta kam neman tarwatsewa take saboda yanda kalamansa ke maimaita kansu a cikin kanta....... ____________★ KADUNA Sosai hawaye suka ciko ma Yazeed idanu ga murmushi shimfiɗe a fuskar tasa duk a lokaci guda. Zuwa yanzu kam ya gama yarda, ya kuma sallama lallai ya rasa, ya rasa Maanal na har abadan. Dan videos na shagalin bikin yake kallo a media. A bazata Nazeefa daketa bayansa batare daya sani ba tai ƴar dariyar data sashi juyowa ya kalleta. Gimtse dariyar tayi tana mai daidaita yanayinta, sai kuma ta zagayo ta zauna a kusa da shi ta ɗora kanta a kan kafaɗarsa kamar bataga yanda ya wani sake haɗe fuska ba. “Yaya! Ya kamata ka bani no ɗin Maanal na kirata na mata ALLAH ya sanya alkairi ko? Tunda ALLAH baiyi za'ai bikin damu ba”. Idanunsa ya rufe zuciyarsa na masa wani irin zafi da rainin hankalinta, amma a zahiri sai baice komai ba ya ture hannunta data ɗora a saman ƙirjinsa ya miƙe gaba ɗaya ya bar mata falon. Kallo ta bishi da shi tana wani murmushi, sai dai kuma yana gama ficewa ta haɗiye murmushin, wayarta ta ɗauka ta shiga media, cikin sa'a da videos ɗin data shiga nema ta fara cin karo. Wani irin bugawa taji zuciyarta na mata da tiririn zafi ganin wanda Maanal ɗin tai ƙyau dan sai yau ne itama take kallon bikin, duk yanda ake zuzuta abin a media ta kasa kalla saboda takaici, a fili ta furta, “AA Darma humm? Wai wanan shegiyar yarinyar taya take kame zukatan maza ne haka?”. Sosai taji hassadar Maanal na sake ƙarfin tasiri a zuciyarta, dan sam ba haka taso ba, da akai haka kuma na nufin ta cita wasan kenan. Idan har zataci nasarar amshe Yaya Yazeed a hannunta ta kuma samu AA Darma lallai anyi ba'ayi ba kenan. Sosai ta cije lips ɗinta tana jin tamkar ta fasa ihu dan takaici da ƙarin tsanar Maanal babu gaira babu sabar.........✍️ _Haka fa wasu suke a rayuwa. Koda baku da alaƙa ta zahirin rayuwa, ko wani ɓangare ya alaƙantaku da alaƙar marar ƙarfi, koda sun ci nasara a kanka a bisa dalilin ƙaddararka, idan ka samu cigaba daga abinda suke ganin sun amsa a hannunka maimakon su haƙura da bibiyar rayuwarka sai su cigaba da girmama hassadarka a ransu, dan su a nasu hauka tunda suka ƙwata a farko, burinsu ka ƙasƙanta a bisa wanda zaka samu a gaba domin su sami damar cigaba da maka dariya. Ya arrahaman duk wanda sharrine a rayuwarmu ka nisantamu da shi, idan mun sanshi ka rabamu, idan bamu san da zamansa ba ka hanamu saninsa na har abada🙏._ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* AJIYA A DUHU 84 .......Saƙo ya isa ga Mamy dai-dai da shigar Saheeba sashen tana kuka. Bata kula su Mamanta dake a falo zaune ba ta danna kai cikin bedroom ɗin Mamy, a lokacin ɗayar mai aikinta tana bata ledar da maigadi ya kawo tace saƙone mai delivery ya kawo. Da ɗan mamaki a fuskar Mamy dake kumbure har yanzu ta amsa ledan, dan tasan ita dai bata da wani order a waje gaskiya. Sannan batai da kowa zai aika mata saƙo ba. Ita duk yau ma bazatace tabi takan waya ba. Zata buɗe ledan kenan Saheeba ta faɗo, su Mamanta da suka biyota biye da ita. Cikin tsawa Aunty ta ce, “K lafiya zaki shigowa mutane kina kuka?”. “Daddyn Naufal ne ya rufe ƙofa wai bazan shiga ba na dawo nan sai ya nemeni”. “To saboda mi?”. Maman Saheeba ta faɗa a harzuƙe. Mamy kam kallon Saheeba kawai take kamar ta samu tv da idonta ɗaya da rabi. Ga ciwon kai da zazzaɓi dan ƙafar nan zugi take mata bana wasa ba, ga inda ta ƙone shima yana damunta. Bata son hayaniyar da suke mata a kai, dan haka ta buɗe baki da ƙyar ta ce, “Kira min shi a waya”. Wayar Mamyn Maman Saheeba ta ɗauka, ta lalubo number Babban Yaya ta kira. Amma mi a kashe ma gaba ɗaya. Wayar ta ajiye ta ce, “Ya kashe wayarsa. Bara na aika a kirashi”. Aunty da abubuwan nasu suka fara daina birgeta kallon Saheeba kawai take. Ita fa gaskiya yau badan kar ace sunbar Mamy cikin wani hali ba da yau zata koma Kano. Wannan abun kunyar ya fara isarta. Ta gode ALLAH da bata da ɗiya mace ƴaƴanta biyu duk maza ne. Kasancewar Mamy ta rigasu aure har AA ma ya girma babban ɗanta sosai. Shiyyasa duk cakwakiyar nan ba sanin ainahinta tai ba..... Dawowar Maman Saheeba a fusace ya katse tunanin Aunty. Cikin hargagi Maman Saheeba ta ce, “To yama bar gidan, ance ya zuba yara a mota sun fice.....” Zata cigaba da magana Aunty ta dakatar da ita. “Nana tunda dai dole zai dawo gidan ba sai ayi haƙuri a jirashi ba. Kunga dai ita ba lafiya ne da ita ba wannan hayaniyar ma ba so take ba muje falo.” Badan Maman Saheeba taso ba suka fice. Mamy ta sauke ajiyar zuciya a hankali. Sai dai taji sun rufe mata ɗakin sannan ta buɗe, wayarta ta ɗauka da hannunta mai lafiya ta gwada kiran Babban Yayan itama. Amma a kashe, sai kawai ta ajiye. Saukar hannunta akan ledar nan ya sata kallon ledar, ita har tama manta da ita. Da hannu ɗayan ta buɗe, ganin an nannaɗe abu kamar box da leda ne yasa ta ajiye ledar ta fara ƙoƙarin warware box ɗin. Kwaline kuwa, koda ta buɗe cikinsa waya ce kawai ƙarama, sai takarda fara. Wayar ta ɗauka ta danna sai taga ta kawo haske. Kamar jira ake ta danna ɗin kira ya shigo. Kasa ɗauka tai har wayar ta tsinke, aka sake kira. Anan dai sai ta daure ta ɗaga, cike da ƙarfin hali tace, “Wanene?”. “Hajjaju! Hajjaju! Kina tsoron ko kidnapper ne shiyyasa kika kasa ɗauka. To kwantar da hankalinki Mrs Aliyu Darma”. Da mamaki Mamy ta ƙara cewa “Waye kai?”. “Ni ba ɓoyayye bane, musamman a gareki, BABBAN ƊANKI ne da kika manta tsohon shekaru. Amma yau ya dawo ya tuna miki da kansa, da hakkinsa na ɗa dake a kanki. Maimakon na baki wahalar tunani ɗan fara duba ɗayan saƙon”. Ajiye wayar Mamy tayi, zuciyarta na ɗan tsinkewa, ta ɗauka takardar da aka naɗe abu a ciki ta shiga kiciniyar buɗewa abinka da mai hannu ɗaya. Da taga zata sha wahala sai ta yage ta kawai da baki. Hotuna ne suka faɗo har guda biyar. Na farko ta ɗauka kamar mai jin tsoro. Hoton Maanal ne, bata wuce 14-years ba a jiki. Gefenta da ɗan sauran jikin mutum kaɗan an yage sa da alama ba ita kaɗai ce a hoton ba. Kai tsaye kuma Mamy ta gane Ajwaad ne a wajan. Ajiyewa tai batare data fahimci komai ba da farko, sai kuma kamar wadda aka haskoma wani abu a brain tai saurin sake ɗaukar hoton ta juya bayansa. Ai wani irin waro idannunta tayi, sai kuma cikin rawar jiki ta ajiye ta ɗauka na biyu, hoton Jariri ne sabuwar haihuwa a cikin zanin atamfa batik ta da, babu kaya a jikin yaron, daga gani kasan sabuwar haihuwa ne da ko awanni bai yi da haihuwa ba aka ɗauki hoto. Yanzu kam zuciyar Mamy ce ta motsa sosai a cikin ƙirjinta. Ta ƙurama zanin ido zuciyarta na tsitstsinkewa, sai kuma ta kai dubanta ga date ɗin da aka ɗaɗara a jikin hoton tamkar da gayya. A wannan gaɓar jitai tamkar zuciyar tata ma ce ta zubo cikin bakinta, jikinta kam rawa yake sosai, wayar ta ɗauka ta danna kiran Number, bugu ɗaya kuwa a ka ɗaga mata. “Wanene kai?”. Ta faɗa cikin hakki da sarƙewar numfashi. Wata shegiyar dariya Sille yayi daga can, cike da iskanci ya ce, “Ya da ruɗewa haka Mrs Darma, ko har kin gama kallon hotunan ne duka? Idan baki gama ba ƙarasa tukunna”. Ƙit ya yanke kiran. Idan Mamy tace bata jin kamar zuciyarta zata fashe a yanzu ƙarya take, cikin rawar hannu dana zuciya ta ɗauki hoto na uku, yaro ɗan shekara bakwai da babban mutum a gefensa da suke matsannciyar kama. A yanzu kam jikin Mamy tari ne ya sarƙe Mamy mai ƙarfi, ta kalla ƙofa da sauri tana danne bakinta domin hana tarin kanta na wani irin bubbugawa kamar ana dukan ƙarfe da ƙarfe. Lips ɗinta na rawa-rawa ga hawaye na gudu ta furta. “Ju..j... Junaid”. Hoton ya suɓuce a hannunta ya faɗi, tamkar mai tsoron taɓa wuta ta ɗauka na ƙarshe. Matashin saurayi ɗan shekaru kusan ashirin da biyar ne a jikin hoton, tabbas ta taɓa sanin fuskar, amma ta manta a ina ne, kuma yaushe ne??... Dai-dai nan kira ya shigo wayar. Jitai tana tsoron ɗaga ma kiran a yanzu harya tsinke aka sake kira na biyu. Zuciyarta dake bata shawarar ta ɗaga taji wanene shi? A ina ya samo wannan hotunan taci ƙarfinta. Ɗaukar tayi sai dai ta kasa magana. Daga can Sille dake jiyo fitar numfashin Mamy a sarƙe cike da shaƙiyanci ya ce, “Nasan kin gama kallon hotunan nan duka zuwa yanzu Mrs Darma? Nasan kuma kin gane wasu a ciki, musamman Surukarki, Tsohon zumanki, da Jaririn nan”. Sosai jikin Mamy ke ƙara ƙarfin rawa, har tana buge ƙafarta mai ciwo, azabar data ratsata ta sata sakin ƴar ƙara saboda ƙafarta. Daga can Sille dake iya jiyota ya ce, “Relax Mrs Darma, karki ruɗar da kanki. Dan ban baki hotunan dan ki ruɗe ɗin ba. Na tabbatar dukansu suna tare da alamar da zaki tunasu. Idan kuma baki tuna ɗin ba zan baki lokaci ki tuna su daga nan har zuwa 1 week sannan ki banbanta su da tunanin miya alaƙantasu a waje guda, bayan kowanne kinyi AJIYA A DUHU ne a mabanbanta GURBI. Na barki lafiya Mrs Darma”. Ƙittt wayar ta yanke. Ba ƙaramar zabura Mamy tai ba domin son dakatar da shi, amma ina ya kashe, hannunta na rawa tai ƙoƙarin sake kiransa wayar amma switch off. Yunƙurawa tai zata tashi ruɗani ya mantar da ita halin da take a ciki azaba ta ratsata. Ai tuni ta saki wayar tana sakin wata azababbiyar ƙara. Wuff Haule ta shigo ɗakin kamar wadda take jiranta dama. Koda yake jiran nata take a ƙofa kam. Itace ta riƙeta dan ƙoƙarin faɗowa a gado take. Cikin dabara kuma tana tattare hotunan nan ta kwashe da hannu ɗaya, sai da ta kwantar da Mamyn sannan ta duƙa ta ɗauka wayar dake a ƙasa dan idon Mamy a rufe suke sai zufa take. Wayar da hotunan Haule ta tura ƙasan gadon Mamy bada nisa ba sannan ta miƙe tana faɗin, “Hajiya bari a kira su Aunty”. Kafin ma Mamy tai magana Haule ta fice da sauri..... Fitar Haule dai-dai da shigowar AA da Fawzan sashen. Dan kiran da Oum tai masa ya sashi dole ya baro sashensu. Su Shahidah na shigowa sashen shi kuma yana sakkowa daga upstairs. Cike da gulma suka zuba masa ido, sai da yay gab da gama sakkowar suka fuske kowanne na mamaki a zuciyarsa, dan kaga AA a fuska zaka rantse bazai iya kallon mace ba saboda jin kai. Amma munafukin yama ƴar ƙanwarsu walmakalifatu yanzu ya fito yana wani basarwa. Aunty Sakina kawai ya gaisar, itama dai Amaal dake gimtse dariya ta gaishesa. Ciki-ciki ya amsa zai wuce dan ya fahimci munafuncin dake a fuskokin su musamman Shahidah da Amaal Shahidah ta ce, “Oh ni bazaka gaisheni ba”. Harara ya zuba mata, cike da baƙar magana ya ce, “Sai kin ƙara girma”. Dariya Aunty Sakina ke musu, hakama Amaal ƙasa-ƙasa take tata. Shahidah tai ƙwafa ta ce, “Haka kace ko, zako kasan na girma yau kuwa, dan da Auta zan wuce har sai kazo ka durƙusa ka gaisheni”. Kallonta yay kamar zai yi magana sai kuma yay shiru, a duniya babu wanda ya saka shi gaba kamar mutane uku, Yaya Fawzan, Shahidah, Rafeeq. Ficewa yay batare da yace mata komai ba, sai kuma ya saki murmushi yana cizar lips dan bai ƙyaleta ba, saboda Aunty Sakina da yake jin nauyi kawai ya zaɓi yin shirun yanzu, amma taci bashi. Sashen Oum ya nufa gaisheta ya samu ƴan kano basu tafi ba suma ya zauna suka gaisa shine Oum ke sanar masa Mamy babu lafiya. Ya fito da nufin zuwa duba Mamyn suka haɗu da Yaya Fawzan. Zai fara aikin tsokanarsa shima yaja hannunsa yana faɗin, “Fara rakani na duba Mamy mu dawo zan iya da kai kaima”. Dariya Fauzan yayi, bai musa ba suka nufi sashen Mamyn. Shine suna shigowa suka samu Haule na sanar ma su Aunty halin da Mamyn ke ciki. Ba ƙaramin tashi hankalin AA ya shiga ba da ganin halin da Mamy ke ciki ba. Nan fa ya shiga tambayar Fawzan accident sukai. Babu wani alamar ruɗewa irin ta AA ɗin a tare da Fawzan ya ce, “Aa sunce ta faɗo ne daga stairscase jiya da dare......” nan dai yay masa bayanin komai.........✍️ AJIYA A DUHU 85 ........Zama AA yay kusa da Mamyn ya share mata hawayen da yaga suna silalo mata, ga jikinta na rawa. A mamakin kowa sai ta buɗe idanunta tana kallonsa, sai kuma ta sake runtse idanun dan abinda ta jiyo jiya ne ke rige-rigen dawo mata a cikin kunne saboda kallon fuskarsa da tayi. Cikin rawar lips muryar na fita da ƙyar zuciyarta na ƙuna ta ce, “Ajwaad ku kaini asibiti ƙirjina”. ALLAH sarki rayuwa, ɗa mai jinƙai daban yake komai wahalar da kake bashi a rayuwa. Mamy bata gama rufe baki ba AA harya miƙe, layin RK ya fara ƙoƙarin nema. Babu jimawa kuwa ya ɗaga, zai fara tsokanarsa shima AA ɗin ya katsesa da faɗin, “Rafeeq kana ina ne?”. Ɗan jim RK yay daga can, sai kuma ya nisa ya ce, “Ina asibiti. Miya faru?”. “Ambulance! Ka turo Ambulance yanzu ta ɗauki Mamy.” Murmushi RK yay mai sanyi, a ransa yay hamdala dan dama abinda yake jira kenan tun ɗazun, daurewa kawai yake yi amma hankalinsa gaba ɗaya nakan halin da Mamy ɗin ke ciki. Sai dai yasan bazai samu abinda yake fata ba sai AA yaje yaga halin da take a ciki saboda wasu dalilansa. Cikin abinda baifi mintinan ashirin ba Ambulance ɗin ta iso, zuwa lokacin harsu Oum na'a sashen dan abun kamar wani magic jikin Mamy ɗin ya rikice alamar jininta ya haura sama ko gani idannunta basa yi. Su Abah sun fita tun ɗazun, hakama Babban Yaya bai dawo ba. AA da Yaya Fawzan da kansu suka sakko da Mamy ƙasa, sannan aka sakata a abin ɗaukar mara lafiya aka fita da ita. ALLAH sarki Oum baiwar ALLAH, itace ta shiga kusa da Mamy ɗin. Su kuma su AA suka shiga motar Fawzan. Saheeba ma ta ɗauka su Mamansu suka bisu.... _________★ Su Maanal basu san mike faruwa ba. Tana can da ƴan uwanta dan ba ƙaramin farin ciki tayi da ganin yayun nata ba, duk da yanda suke tsokanarta musamman Amaal ita dai tanata ɓoye fuska, har suka gaji suka barta, sun baje mata kayan daɗin da suka kawo mata kowa na wani tattalinta. Sai Ammie da suka kira ta video call suka sha hira. Maanal na kuka Ammie nayi saboda farin cikin yanda abubuwa suka canja, baiwar ALLAH ji take kamar tai tsuntsuwa tazo Abujan ma. Albarka da addu'a babu irin wadda bata jerama AA ba yau harma da Maanal. Sunyi hirarsu cike da farin ciki da shaƙuwa. Maanal nata zubama Ammie shagwaɓa wai tana son ta tazo Kaduna idan ta warke sai ta dawo. Ammie dake murmushi ta ce, “A'a Auta kiyi zamanki a ɗakinki kinji, ko sashen Aunty ban yarda ki koma ba balle Kaduna. Kefa yanzu kin girma, kiyi zamanki gidan aurenki kima mijinki hidima. ALLAH yay muku albarka ya baku zuri'a mai albarka kinji. In sha ALLAHU zanzo bikin Fawzan ai nan da sati uku”. Murmushi Manaal tai mai sanyi, cike da shagwaɓa ta ce, “Amma Ammie a wajena zaki kwana ko?”. Dan kawai Ammie ta kwantar mata da hankali sai tace eh. Aiko hakan yama Maanal ɗin daɗi sosai. Bayan sunyi sallama da Ammie suka koma hira a tsakaninsu, hirar da gaba ɗaya ta ta'allaƙa ne akan batun fyaɗen nan, Amaal ta sanya Maanal gaba da sabuwar tsokana. Tun tana ƙyaleta harta fara ramawa, suka fara tsiyar tasu ta sako-da-sako. Daga ƙarshe suka yanke shawarar zuwa Giro da babbar salla. Dan Maanal ta rantse sai taje ta maidama Gwaggo da kaf mutanen gidansu murtani babu fashi. Yanda tayi ɗin ya tabbatar ma su Amaal ƙanwarsu ta dawo ainahin Maanal ta shekarun baya data mutu. Aiko ɗari bisa ɗari suka bata goyon baya akan wannan ƙudirin nata, sun kuma roƙi Aunty Sakina kada ta gayama Ammie dan sai sun dawo zasu sanar mata karma ta hana su. Ta tabbatar musu bazata faɗa ba, kuma tana goyon bayan zuwan nasu itama.... Sai da sukai Magrib sukai ƙoƙarin tafiya, a lokacin ne Hajiya Shuwa ta shigo yima Maanal gashi take sanar musu ai an tafi da Mamy asibiti jikinta ya rikice. Mamaki ya kama Maanal dan sai lokacin ma ita take sanin Mamyn bata da lafiya gaba ɗaya... ★Matuƙar sanyi jikin Auntyn su Mamy yayi da ganin yanda RK ke tsaye akan al'amarin Mamyn tunda suka iso asibitin, dan cikin ƙanƙanin lokaci likitocin da zasu dubata sun rufu a kanta. Sai taita kallon Maman Saheeba da tace bata yarda a kira Rafeeq ya duba Nuratu ba tun a jiyan. Itama kuma Mamyn da akace a kira Rafeeq ya dubata da safe catai bata yarda ba. Ta maida kallonta kan Oum datai shiru damuwa kwance a fuskarta, AA da Fawzan sun sakata a tsakkiya suna lallashi. Sai Auntyn taji kamar ta fara jin kunyar kanta. Anya kuwa babu gyara akan al'amarin su na ƙin baiwar ALLAHn nan Hajiya Fateema. Koba komai fa itace sanadin shigiwar ƴar uwar tasu a wannan daular. To wai miyema aibunta da suke zaginta? Ƴar uwarsu fa ce da kanta ta ɗauka yaran ta bata..... Wannan tunani shine danƙare a zuciyarta har RK ya fito yana sanar musu karaya ce fa a ƙafar Mamy, sannan akwai ƙonewa a jikinta... A tare Oum da Ya Fawzan sukace, “Karaya da ƙonewa kuma?”. Sai suka juya suna kallon su Maman Saheeba alamar tambaya. AA kam yama gagara cewa komai. Cikin ƙarfin hali Oum ta ce, “Aunty amma bakuce mana da ƙuma ba ai, batun karaya nasan maybe wancan likitan ne bai san aikinsa ba”. Cikin ƙarfin hali Aunty ta ce, “Wlhy bamu san da ƙunar ba muma Oum Fawzan (da haka take kiran Oum kafin Mamy ta nuna bata so). Amma tabbas tea ya zuba mata a jiki babu kuma wanda yay tunanin zai ƙonata, ita kuma batayi magana ba”. RK ne ya ce, “Ai shi ruwan zafi ba'a rainashi gaskiya. Yanzu dai an kira wanda zai yi ɗorin karayar kun san mu anan asibitin muna aiki da ɗorin karayar gargajiya ne saboda mai yi mana aiki na wannan fanin yasan aikinsa. Zamu jirashi dan yana a suleja ne. Amma gaskiya likitan can da kuka kira ya dubata bai san komai ba, kuma da ƙafar nan takai wasu kwanaki a haka komai zai iya faruwa. Dan haka ina baku shawara ku kiyaye, kusan da waɗanne irin likitoci zakuyi mu'amula musaman wanda kuke iya kira gida su muku aiki.” Daga haka ya juya ya fita ransa a ɓace. Ita kanta Oum ranta ya ɓaci, dan tun ɗazu dama yanda sukai ɓoye-ɓoyen halin da Mamyn ke a ciki yanata mata kai-kawo a zuciya. A ganinta mizaisa suyi hakan? In dama ƙaramin ciwo ne sai ace. Shi kansa Abah ta fahimci ransa a ɓace yake. Ture tunanin tayi daga ranta gaba ɗaya ta ƙyautata musu zato kawai da yardar ma zuciyarta abinda suka faɗa a ɗazun. (Wannan shine babbar halayyar Oum dake saka mata kwanciyar hankali akan zamanta da kowa, take kuma iya hakuri da dukkan jarabawarta. Tana da ƙoƙarin ƙyautatama mutum zato. Ko abu akai mata a gabanta mara ƙyau kai tsaye bazata saka jin zafin mutum a ranta ba, sai taita kawo uzirin maybe kaza ne, ko kaza yasa yay haka. Sai kaga zuciyarta ta samu salama da kwanciyar hankali. Mu gwada kasancewa haka zamu sha mamaki wlhy koda akan mazajen aurenmu ne ma🙏😀). Waya ta ciro ta kira Abah ta sanar masa komai. Yace mata suna masallaci idan sun idar da salla zasu zo. Daga haka ya yanke kiran. Mamaki ya kamata jin babu wata damuwa a cikin muryarsa. Amma sai ta ture tunanin kawai. Ta kalla su Fawzan tace suje suyi salla suma.... Sai bayan sallar isha'i mai ɗori yazo, lokacin suma su Abah na asibitin harma da Babban Yaya. Su Hajiya Majdiya da su Umma ma sun iso asibitin jin shiru su Oum basu dawo ba. Ƙafar Mamy tayi tsami sosai, ta yanda ana taɓa ƙafar sai da ta saki wani ihun da har reseption sai da aka ji. Ashe ma karaya har biyu ce ba ɗaya ba. Dole sai da su AA suka shiga aka riƙeta, a haka ma RK yaji tausayinta an mata wata allurar kashe zafi. Sumarta biyu dan azaba. Su kansu su AA ƴan riƙeta sunyi sharkaf da zufa duk da acn dake a ɗakin. Shima hannun an gyara mata, shi kam targaɗe ne. Matuƙar tausayi dole ta baka. Allurar barci aika mata bayan sun farfaɗo da ita. Ganin ba wani abu ake buƙata ba RK yace zasu iya tafiya gida tunda anyi gyaran. Dan allurar da sukai mata ta awa goma sha biyar ce, ita da farkawa sai gobe idan ALLAH ya kaimu. Auntyn su Mamy kawai aka baro a asibitin, sanda suka iso gida sha biyu saura. Kowa sashensa ya nufa, Saheeba tabi Babban Yaya, wani kallo daya watsa mata bama tasan ta tsaya cak ba. Dama mamarta ce tace ta bishin. Aiko bataga fuska ba dole ta wuce sashen Mamyn duk da hararar da maman tata ke mata..... _______★ Tun bayan fitar Hajiya Shuwa hankalin Maanal a tashe yake, ta kira wayar Oum ba'a ɗaga ba. Ta kira ta AA shima haka. Ta kira Yaya Fawzan shima bai ɗaga ba sai taji matuƙar damuwa da tunanin ko dai wani abu ne ya samu Mamyn. Dan yanda Hajiya Shuwa da su Didinta suka bata labarin halin da Mamyn ke ciki abin ya tsaya mata a rai. Tun tana kallon agogo da cigaba da kiran AA harta sare, a haka ta lallaɓa ta fito falo, ta window ta leƙa compound babu kowa sai hasken fitulu, motocin gidan ma duk an fita da su sai huɗu kawai dake a lulluɓe, sai maigadi na gyangyaɗi gidan shiru sosai. Har zata saki labulen idonta ya sauka akan Nibras dake tsaye a barandar sashensu ta upstairs. Idanu ta zuba mata sai taga gaba ɗaya hankalinta na'a sashensu ne. Tsaki Maanal taja da faɗin, “Wawuya”. Ta bar wajen. Sai kawai ta sakko ma falon ƙasa cike da dauriya, a hakan ma da sauƙi dan tana jin daɗin gashin nan na Hajiya Shuwa. Anan ta kwanta cikin kujera, tun tana kallon agogo har barci ya saceta... Tunda AA ya shigo idanunsa suka sauka a kanta. Zuba mata su yay shiru yana kallonta na tsawon lokaci. Sai kuma ta bashi tausayi. Ƙarasowa yay inda take. A nutse ya saka hannu ya ɗauketa gaba ɗayanta. Sama ya haura da ita yana tafiya a hankali dan kar ta tashi. Har ko ya kwantar da ita a gadon ɗakinsa bata farka ɗin ba, duvet yaja ya lulluɓa mata tare da duƙowa ya sumbaci lips ɗinta da goshinta sannan ya wuce closet ɗinsa yana cire kaya. Sosai yake jin damuwa akan halin da Mamy ke ciki, haka ya samu yay wanka yayo alwala. Shafa'i da wutri yay ƙoƙarin yi, yana idarwa kiran Oum ke shigo masa. Ɗagawa yay, Oum tace ga abinci nan zata saka a kawo musu hankalin kowa a tashe an manta ko Maanal ba'a kawoma abinci ba........✍️ AJIYAH A DUHU 2 86... ........Maanal ɗin ya kalla, sai kuma cikin taushin muryarsa dake fita ƙasa-ƙasan nan ya ce, “Oum tama yi barci ita, kawai a barshi nima na ƙoshi zan sha shayi dare ya riga yayi”. “Auta kasan bana son zama da yunwa ko, itama zata iya farkawa anjima ta nema abincin”. “Oum ALLAH bana jin yunwa, itama kuma inta farka sai ta sha tea ɗin kiyi haƙuri”. “Shike nan ALLAH ya tashemu lafiya”. Sallamar yay mata shima ya ajiye wayar yana miƙewa. Shima baibi takan tea ɗin ba ya nema wajen kwanciya dan barci ne a idonsa sosai. Sai dai me yana kwanciyar ya saka Maanal a jikinsa sai yaji kuma yanayinsa na sauyawa. Sosai yake jin buƙatarta, amma ya danne da tsiya-tsiya kodan bayanin da RK ya masa akan dole ya kauda idonsa akanta harta warke. Sannan shi a kanran kansa tausayi take bashi sosai. Dan yasan jiyan nan bai mata da wasa ba sam. Da ƙyar ya samu yay barci, gabannin asuba kuma ya sake farkawa a yanayin matsuwa sosai, sai kawai ya shiga bayi ya shashsheƙa ma kansa ruwa yayo alwala yazo ya hau nafilfili da karatun Alkur'ani. Hakanne ya bashi ƴar nutsuwa har lokacin salla yayi. Sai da ya tada Maanal ya taimaka mata tayo alwala sannan ya fita salla..... _________★ 1 WEEK LATER Alhamdullahi satin AA guda ke nan cur da angwancewa. Ba ƙaramin dauriya yay da juriya ba na kauda kai akan Maanal ba. Idan ka cire ɗan sumbatarta iya lips hatta kissing ɗinta dainawa yay, dan tunda yay hakan a washe gari bayan ya dawo sallar asuba ya ƙare da ciwon ciki bai sake kwantatawa ba. Sauƙinsa ma ciwon Mamy da zaryar zuwa dubata asibiti tana cimasa lokaci. Idan kuma ya dawo gida sai ya hau aikin office. Hakan bai damu Maanal ba dan itama harga ALLAH tana son ko zai nema wani abu kuma daga gareta to ya kasance ta warke tas kamar yanda kullum Hajiya Shuwa ke gargaɗinta, dan ta kula shauƙin soyayya na ɗawainiya da yaran. To Alhamdullah gashin da take mata ya taka rawar gani sosai ga kuma jikinta baya riƙe ciwo a cikin kwana huɗu ma zaren ɗinkin ya gama fita tas a jikinta. Sannan bata jin zafin komai sai ma wata nutsuwa ta musamman. Zuwa yau da take cika sati kam ras take jinta, kamar yanda doctor da tazo ta duba ta ma ta tabbatar ta warke sarai, dama tun shekaran jiya Hajiya Shuwa tace ta ga warke ɗin. Amma tai gum da bakinta. Zuwa yanzu kam dai su kaɗai ne a gidan nasu. Sai Auntyn su Mamy dake jiyyarta ita da Maman Saheeba dan an sallamota yau kwana biyu kenan zata ƙarasa jiyya a gida, badan ma jininta da yaƙi sauka ba su RK nata fama da kwana uku zatai su sallameta a asibitin, anyi-anyi ta faɗi mike damunta taƙi. Da ƙyar dai da lallashin da AA ke mata da kulawa aka samu jinin nata ya dai-dai shine aka sallamosu. Fuskarta ta saɓe raunikan sun warke, hakama hannunta har an kwance ƙafarce kawai dai da ɗaurin karaya, itama nan da kwana biyu ake saka ran kwancewa saboda bata da ƙan jiki. Maganar hotunan nan kuwa da sun zo mata a rai sai ta turesu da tsiya-tsiya. Kai da ka ganta kasan abin duniya ya isheta. Amma sai kowa ke ɗauka ciwon ne, itako ita tasan tashin hankalinta. Har ƴan hutun Oum duk sun wuce ba kowa. AA daya fahimci zamansa a gida akwai matsala jiya ya koma aiki. Dan haka yau ma yana fita Maanal ta shirya ta wuce sashen Oum. Jiya ma acan ta yini har sai da ya dawo. Sashen Mamy ta fara zuwa. A falon ƙasa duk ta samesu har Saheeba dan tana sashen Mamyn har yanzu Baban Yaya ya murje idanunsa. Abah kuma yaƙi saka musu baki ya kuma hana Oum yin magana. Har Nuratu tana gidan itama, taji sauƙi sosai sai uban ramar da tayi da duhu. A down stairs ɗin Mamy ke jiyyar, dan tunda suka dawo asibiti aka gyara mata cikin ɗakunan ƙasa taƙi yarda ta hau sama saboda tsoron sake kallon hotunan nan. Tun kafin Maanal ɗin ta shigo ƙamshinta ya iso musu. Duk sai suka zubama ƙofar ido kuwa. Sai ko gata ta bayyana garesu cikin gayunta kamar ka saceta ka gudu. Ga wani irin ƙyau dama da amarcin ya sata ta wani ƙara fresh abinta. Ga uban gyaran jikin Hajiya Shuwa na nan raɗam tamkar yau akai mata sabo. Nuratu ce ta fara kauda idonta tana jan siririn tsaki zuciyarta na raɗaɗi. Sai itama Mamy ta ɗauke nata. Saheeba da Mamansu ma suka taɓe baki suna ɗauke kai. Aunty ce kawai tai murmushi da faɗin, “Ɗiyata kece?”. Murmushi mai ƙayatarwa Maanal ta sakar mata. Cike da girmamawa ta ce, “Eh Mama sannunku”. Sai kuma takai zaune a kujerar dake kusa da ita ta ce, “Mama ina kwana! Ya mai jiki?”. Cike da kulawa Aunty ta amsa mata, dan tama kanta alƙawarin canjawa ita kam, shiyyasa ko jiya da Maanal ɗin ta shigo cike da kulawa ta tarbi yarinyar, hakama idan sukaje asibiti duba Mamyn ita da AA dan ya kaita a da daddare a washe garin da aka kwantar da su, daga nan kullum da dare suke zuwa. Maanal ta juya tana gaida Mamy da tambayarta jiki. Ciki-ciki ta amsa mata. Ko'a jikinta ta juya ta gaida Maman Saheeba. Ƙin amsa mata tai ita kam, nan ma Maanal bata nuna damuwa ba. Ba kuma ta kalli ko inda Nuratu da Saheeba suke ba balle ta gaida Saheeba ɗin. Hakan sai yay ma Saheeba zafi. Itama Mamansu haka, ta kalla Maanal ɗin cike da ɓacin rai zatai magana kira ya shigo wayar Maanal. AA ne, dan haka ta ɗan lumshe ido ta buɗe bata ɗaga ba harta tsinke, kiran ya ƙara shigowa a karo na biyu. Yanzu kam tasan dole ta ɗaga dan maybe wani abun ya manta. Aunty dake murmushi ta ce, “Ɗaga wayar mana Daughter”. Murmushi Maanal tayi tare da ɗagawar takai kunneta.. “ZUCIYAR Ajwaad ina kika shiga haka?”. Abinda AA ya fara faɗa kenan tana kai wayar kunne. Gashi bata san sound ɗin yayi hight ba. Aiko a kunnen kowa wannan furuci nashi, ragewa tai, kafin ƙasa-ƙasa ta ce, “Ina sashen Mamy idan na fita zan kira ka”. Ɗan jimm AA yay daga can, sai kuma ya ce, “Okay 2-minutes kawai na baki fa.” Murmushi tayi kawai ta yanke kiran. Ɗagowar da zatai taga kowa ya cika yay fam banda Aunty dake murmushinta. Sai kawai ta kalla Auntyn da murmushi ta ce, “Aunty bara naje, Mamy ALLAH ya ƙara lafiya”. Aunty ta amsa mata da amin tana sanya mata albarka, Mamy kuwa bata tanka ba. Maanal ɗin na fita Saheeba da Nuratu har haɗa baki suke wajen zaginta. Da mamaki Aunty ta ce, “Datai muku mi zaku zageta? Kunga ku kama kanku, da wannan halin ke kike so ki shigo gidan nan? Ke kuma dake ciki idan baki sani ba raini kike siyama kanki a wajen yarinyar nan, kina matsayin matar yayan mijinta amma baki san yanda zaki riƙe girmanki ba. Ke ko Kamila ina ƙara nuna miki ki rufama kanki asiri ki daina nunama yarinyar nan ƙiyayya ƙuru-ƙuru. Kina dai ganin abinda kikai mata a asibiti ranar sai da Ajwaad yay magana, kawai ya shanye ɓacin ransa ne saboda girma irin na uwa. Sannan ke kanki raini kike jama kanki a wajenta wlhy. Ni banga aibunta ba, yarinya mai natsuwa da hankali. Ai wlhy yaron nan Ajwaad ya more da mata dai-dai da halayensa. Hakama baiwar ALLAHn nan Fateema idan ta shigo kita ɗaure fuska da ɗauke kai, ko ki hau barcin ƙarya, a tunaninki bata san ciwon kanta bane ko bata lura da komai ƙyaleki kawai take yi, ki cigaba, kina dai ganin mijin naku banda ran farko da aka kaiki asibitin yaje kin sake ganin shi inda kike? Ko sannu bata haɗa ku ba har yanzu, yana gidan ma baya nan baki sani ba. Maimakon ki gyara zuciyarki kodan abinda ya faru ɗin nan ƙoƙarin buɗema kanki aiki kike kowama ya fahimci mike ranki, to ALLAH ya baki sa'a kin san dai familyn Darma ba Ƙanwar lasa bane. Ga matar Fawzan nan sanadinki ta shigo gidan amma saboda wannan saɓanin ko sau ɗaya bata zo ta dubaki ba har muka gama zamanmu na asibiti muka dawo gidan nan. Ita ko fa, tana fama da kanta amma kullum sai sunje sun dubaki hakama jiya zuwanta uku sashen nan, harda yo miki abinci. Ga Saheeba nan tare damu take kwana tana tashi ko ruwan shayi ta taɓa dafawa dan ki sha......” “Haba Aunty wannan kuma maganar miya kawota, nifa na fahimci kamar akwai abinda kikeji a kaina da ƴaƴana a zaman nan. Haka fa ranar kika zage Nuratu a asibiti shiru kawai nai na ƙyale dan a zauna lafiya. Yanzu kuma kina nuna wata banza can bare kamar ta fisu...” Kallon Maman Saheeba mai maganar kawai Aunty keyi, sai kuma ta girgiza kai tai murmushi da faɗin, “ALLAH ya ƙyauta. Nana yanzu ƴaƴanki ba nawa bane, dan na tsawata musu su gane abinda ya dace shine kuskure? To ALLAH ya baki haƙuri maida wuƙar an bari in sha ALLAHU”. Daga haka Aunty ta miƙe tama bar musu falon. Babu wanda bai rakata da harara ba cikinsu, Nuratu kam harda ƙunƙunin zagi. Mamy dai batace komai ba, dan ita kam duk sun isheta sotake ma su tafi ta samu filin baje matsalarta da neman hanyar maganceta amma taga basu da niyyar hakan............✍️ Nima fa na ƙagara hankalinki ya dawo kan hotunan nan Mamy😌, kun san mu duk inda gulma take nan muke amma a Nobel😮‍💨😜koya kuka ce🥱 AJIYAH A DUHU 2 87.... ........Maanal kam na fita sashen Oum ta wuce. Kamar ko yaushe ko'ina na zuba ƙamshi ne. Babu kowa a ƙasa sai su Inte dake kitchen suna gyara, da alama yau sun makara aiki. Suna jin motsinta kuwa suka leƙo suna gaisheta. Amsawa tai da kulawa, cike da tsokanarsu tace, “Wane shagali ake haɗamana a kitchen ɗin?”. Dariya sukayi, duk da zasuyi sa'anni da ita Aunty suke kiranta saboda girmamawa. Inte tace, “Aunty wainar fulawa zamuyi kin san Joy tunda ta iya ci kowa ya bani”. Maanal na murmushi ta ce, “Ato ayi dani nima. Bara na duba Oum na dawo”. Da girmamawa sukace mata to, suna son Maanal dan sam bata da damuwa, ba girman kai, ba wulaƙanci, huɗɗa take da su tamkar ƙawaye. Bata samu Oum a falo ba sai ta leƙa bedroom. Wanka take dan haka ta dawo falo ta zauna, sai ga kiran AA ya sake shigo mata. Ɗagawa tai tana murmushi da kaiwa kwance a cikin kujerar ta ce, “Na tuba”. Daga can ya ce, “Oh kina ma sane kenan?”. “Ni na isa. Na bari na zauna ne kasan ita wayar Sarki babu girma a ɗagata ana tafiya ko ana tsaye”. Murmushi yayi har tana jin sautinsa. Sai kuma cikin sake tausasa murya ya ce, “Yanzu kina ina?”. “Falon Oum”. “Ƴar gata mai aure kusa da Mamanta”. Murmushi tayi mai ƙayatarwa, sai kuma tace, “Yanzu ya akai ta samu ne?”. “Zadai ta samu anjima. Yanzu kam kewar ZUCIYATA nake yi shiyyasa nace bari na ji sautinta. Gaskiya inaga gobe zaki dawo aiki”. Cike da shagwaɓa ta ce, “Amma kaifa kace sai Monday”. “Na fasa, idan ba hakaba nima zan zauna gidan sai Monday ɗin mu dawo tare. Dama yanzu ne ya kamata fa na fara nawa angwancin tunda kwanakin duk sun tafi a jiyya”. Ƙasa-ƙasa cikin raɗa Maanal ta ce, “Yanzun ma jiyyar zaka cigaba da yi dan ban warke ba”. “Haba Besty kiji tausayina mana, kullum sai dai aita zuwa min cikin barci ana sani wankan dole haba mar'atussaliha”. Murmushi Maanal tayi, muryarta na fita a maƙoshi ta ce, “To alƙawari banda jin ciwo”. “Nayi da gudu ma kuwa zan bi a hankali My Everbloom”. “To ka dawo da wuri”. Ta faɗa cikin raɗa sosai. Tana gama faɗar kuma ƙitt ta yanke kiran, tama kashe wayar gaba ɗaya tana murmushi. Dan inba haka tai masa ba bazai yi aikin ba. Haka jiya kaɗan-kaɗan ya kirata har Oum ta ganosu ta ce, “Anya yau Auta zai yi aikin arziƙi a office ɗin nan kuwa”. Aiko tunda ta tashi ta gudu bata dake dawowa sashen Oum ɗin ba sai yanzu.... _________★ KADUNA A KD kam dukan labarin shagalin biki yaje kunnen Hajiya Yaya tas. Da yake bata koma ba tun zuwan datai gidan randa Yaya Yazeed ya daki su Nusaiba. Daddy yayi niyyar sake fatattakata Ammie ta dinga roƙonsa harda kukanta. Dole ya ƙyaleta amma fa ko sau ɗaya bai nuna yasan tana gidan ba. Ita kuma girman kai ya hanata zuwa inda yake acewarta ma su zuba. Sai dai maimakon su zuba da Daddyn sai suka zuba da ɗanta Yazeed. Dan kuwa dai da gaske kan Yaya Yazeed ɗin ya juye gaba ɗaya. Babu wanda yake ji da gani sai Nazeerah da iyayenta. Kai tunda ma Hajiya Yaya ta dawo gidan bai leƙa sashen nata ba. Sai dai ta hangesa ya fito zai shiga mota ko ya dawo zai shiga sashensu. Ta aika a kira mata shi Nazeerar ta kore ƴar aiken. Hajiya Yayan taje sashen da kanta bugawar duniya Nazeefa taƙi ta buɗe mata kuma Yazeed ɗin na zaune a falo yana jinsu, aiko ranar harda kukanta, shine taje ta kai ma Babanta ƙara. Babban ya kira Yazeed amma sai cayay masa shi yamayi tafiya baya gari. Hajiya Yaya tace ƙarya yake. Baba yace to shi mizai yi kuma tunda yace baya nan. Haka dole ta dawo gida tana kukan zuci mamakin Sabuwa na girgizata. Dan yanzu kota kirata bata ɗaga mata waya itama, taje gidan ance basa nan ita da mijin. Shima kuma Yazeed ɗin ana saura kwana biyar salla yara sukazo suna sanar mata gashi can shi da Nazeefa sun shiga mota sun bar gidan harda akwati alamar tafiya zasuyi. Daga wannan fita ce har yanzu babu Yazeed ɗin babu matar tasa ga shi har sati uku kenan dayin salla. Ta gwada kiran shi a waya bata shiga alamar ma ƙasar suka bari. Hakan kuwa akai Yazeed da Nazeefa basa Nigeria, sun fita hutawa shida surukansa, hakan kuma duk a cikin shirin mijin Sabuwa ne zai fara aiki akan Daddy. Zancen biki ma Sabuwa ce ta sanarma Nazeefa, sai kuma ranar taga Yazeed ɗin na kallo a waya shine ta kunnashi da cewar tana son ya bata no ɗin Maanal shi kuma ya tashi ya bar mata wajen gaba ɗaya... Itama dai Hajiya Yaya labarin biki kaf yaje kunneta a bakin ƴaƴanta. Duk da cike da hassada yaran ke bata labari basu rage mata komai ba. Aiko ta girgiza, abin kuma ya tsaya mata a zuciya sosai har ya nema gagararta barci. Washe gari ta tashi da wannan ɓacin ran sai kuma ga Hajiya Basariyya an dawo da ita. Kawu Manu da kansa ya maidota, ta rame sosai tayi baƙi kamar ba Hajiya Basariyya ƴar gaye ba. Su kansu yaran tambayarta suka dinga yi tayi rashin lafiya ne. Tunda ta dawo yanda bata kula kowa ba itama Hajiya Yayan bata kulata ba. Ammie kam bata nan ita da su Waleed Daddy ya kwashesu sun ma bar ƙasar kwannansu biyar kenan. Itama dai Hajiya Basariyya ko hutawa bata gama yi ba yaranta suka shiga bata labarin bikin Maanal. Wani irin ƙuna ta dinga ji a zuciyarta, daga ƙarshe ta daka musu tsawa alamar su barta bata buƙatar ji. Dole sukai shiru kuwa. Ranta a ɓace ta korosu daga bedroom ɗin nata dan dama duk suna zagaye da ita ne acan. Wayarta ta cire daga caji data sanya ta shiga kiran layin Huznah. Amma switch off. Shiru kawai tai abin duniya ya isheta. Sai kuma ta tashi ta hau gyaran jikinta dan ita kanta ƙyanƙyamin kanta take balle wani. Sauƙinta ma Daddyn baya gida balle ya ganta ta koma kamar bola, duk da dai taji zafin jin wai basa ƙasar shi da Ammie da ƴaƴanta. Gefe ga yaran sun ƙara mata wani ɓacin ran da labarin bikin Maanal. Aiko sai haɗiyar zuciya take tana fesarwa cikin ƙunar rai..... _________★ KANO A ɓangaren Huznah tunda taga shagalin bikin AA da Maanal a wayar Khadijah jikinta ya sake rikicewa. Da farko bata san abinda ke faruwa ba tunda ba wayace da ita ba. Tsautsayi a washe garin dinner ɗin su AA Sageer ya kaita gidansu dan ta yini, saboda da salla bai barta taje ko ina ba. Ganin kwana biyu laulayin ya ɗaga mata sai ta bashi tausayi da zaman kaɗaicin yace ta shirya ya kaita can ta yini. Ashe rabon ta ganoma kanta abinda zai dameta. Aiko ta tarar Khadijah na kallon shagalin biki a TikTok. Ita Khadijah batare data san akwai wata alaƙa tsakanin Huznah da AA ba ta shiga bata labari. Huznah sai taji kawai tana son ganin bikin tace ta bata ga gani, Khadijah tace ai datan ta ya ƙare. Dubu ɗaya Huznah ta bata tace taje ta sanyo, aiko cike da murna ta amsa taje ta sako ta bama Huznah waya. Ai tunda taci karo da fuskar AA da Maanal shike nan. Bata ƙarasa ma kallon video ɗin ba ta yarda wayar, bayin gidan ta shiga taci kukanta ta fito. Sai tai kamar amai tayo. Haka dai tai wannan yini babu daɗi, ƙagara ma tayi dare yayi yazo su tafi gida. Tun ranar laulayinta ya dawo sabo fil, ƙarshe dai sai da aka kwantar da ita asibiti. Yau kwana biyu kenan da sallamota..... ________★ Kamar jiya yau ma Maanal ta hana Oum yin komai, ita tayi girki tsaf su Inte suka shirya a table. Dan yanzu shima Babban Yaya ya dawo nan cin abinci. Suma su Naufal anan suke gun Oum ɗin. Maanal ɗin ce ma taje ta ɗakkosu a school jiya. Yau ma tana ganin biyar tayi ta ɗauka key ɗin motar Oum dan nata sai an kaisu service. Tare da Inte da tace zata rakata suka tafi. Babu jimawa sai gasu sun dawo. Kusan dai-dai lokacin shima AA ya shigo gidan, amma ya rigasu dan Maanal na shigowa da mota ciki shi kuma yana fitowa. Ganin motar Oum ya sashi dakatawa da mamakin ina Oum ɗin taje haka da yamma. Fitowar Anum da gudu ya sashi gane Maanal ce, kai tsaye wajensa yarinyar tayi cike da farin ciki. Shima sai ya ɗauketa ya ɗaga sama yana murmushi da faɗin, “Oh oh Oumna ta dawo school”. Shima Naufal AA ɗin ya nufa ya rungume, dai-dai nan Maanal ta fito itama idonta a kansu. Gira ya ɗan ɗage mata ita kuma tai murmushi. Koda ta iso inda suke tana masa sannu da zuwa sai yay mata nuni da ido tazo. Bata musa ba ta matsa, ya wani matsota ya haɗa ita da yaran ya rungume. Cikin kunneta ya raɗa mata, “In sha ALLAHU nan da 5years haka zan dinga haɗaku ke da yara ina rungumewa”. Murmushi tayi tare da ɗan mintsininsa zata fita a jikinsa ya hana hakan, sai da ya bata wani ɗan sumba a kan wuya yanda yaran bazasu lura ba, da mata raɗa ya ce, “Ina taya kaina murna yau a angona nake”. Harararsa Maanal ta ɗanyi da matsawa yanzu kam dan karma wani ya fito ya gansu. Sai dai bama ta sani ba komai da suke a idon Nibras ne, hakama ma Saheeba dake dakon jiran dawowar Babban Yaya tana a barandar sashen Mamy ita da Nuratu da itama taga komai. Yana ɗauke da Anum ya riƙo hannunta cikin nashi suka nufi sashen Oum. Naufal kuma na ɗauke da ledan tsarabar da AA ɗin yay musu dan kayan sunma Inte yawa ta kwashi school bags nasu da lunch box. Yanda yake murza mata hannu yasa ta kallesa, shima kallon nata yayi cikin lumshe idanu da buɗewa. A saman lips ya furta, “Hannunki yana da sanyi mai nutsar da raina. Ina jin kariya da salama idan kina kusa da ni. Zan so naita riƙe hannunki a haka har abada Besty”. Abinda ta gani kwance cikin idanun nasa yasa ta kauda kanta kawai tana murmushi. Shi ko ya ɗan cije lips da sake lumshe idanu da buɗewa. Suna shigowa main falo ta hanga Oum ta cire hannunta a cikin nasa, bai hanata ba dan duk rashin ta idonsa baiyi a gaban Oum. Barsu dai suyi ɗan faɗansu da tsokanar juna shi da Maanal ɗin shike nan. Oum kam sarai ta gansu amma ta basar, tama maida hankalinta ama su Naufal oyoyo. Suko sun zagayeta, yaran na matuƙar ƙaunar Oum, ana hanasu zuwa inda take ne kawai dan basu da yanda zasuyi. Dan sam ba ƙaunar zama sashen Mamy suke ba. Amma uwarsu ta kafa musu sharaɗin sai can kawai. Shiyyasa yanzu da suka dawo sashen Oum ɗin wani kalar daɗi suke ji ko neman uwar kuwa basayi ma sam...........✍️ Wa yaga tufƙa da warwara Mamy. Kina ƙoƙarin janye wasu, wasu na karuwa, shifa kyakkyawan hali zanen dutse🥰🥰🥰❤️ *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖8️⃣8️⃣ ______________ .........Kusa da Oum AA ya zauna, ya saka kansa a kafarta yana faɗin, “Haba Oum ki ƙyale jikokin nan naki kiyi ta ɗanki”. Cike da tsokana Maanal dake wucewa kitchen ɗauka masa ruwa ta ce, “Jealousy”. Harrarta yay yana ɗaukar pillow kamar zai wulla mata ta masa gwalo ta shige kitchen da sauri”. Pillow ɗin ya ajiye yana cije lips alamar zan kamaki, Oum dake murmushi ta shafa kansa. Hannun data shafa masa kan ya kama ya sumbata. Sai kuma cikin ɗan damuwa ya ce, “Oum wai yaushe Abah zai dawo ne? Nifa idan ina gida nafi son naita ganin duk kowa na nan”. Oum da itama take cikin damuwar tafiyar Aban dan cikin fushi suka rabu akan ƙin zuwa duba Mamy asibiti da yay, tambayar duniya kuma yaƙi gaya mata mike faruwa. Amma bata bar su AA ɗin sun san hakan ba, cike da kulawa ta ce, “Maybe cikin satin nan dai, baƙwa waya ne?”. “Munayi, kawai dai na tambaya ne. Dan dana tambayesa jiya cayay min yana da uziri sosai”. Murmushi Oum tayi, kafin tace wani abu Maanal ta ƙaraso da ruwa a tray, a gaban AA ta ajiye, dan haka ya tashi daga kwantar da kansan da yay a kafaɗar Oum ya zauna sosai. Ruwan data zuba masan ya amsa yasha ya miƙa mata kofin yana wani binta da kallon ƙasan ido. Maanal dake basarwa saboda idon Oum ta ce, “Abinci fa?”. Mikewa yay yana faɗin, “No zan fara wanka, sai ma anyi magrib cin abincin gaba ɗaya yafi daɗi. Oum bari naje sai na dawo”. “To Auta a dawo lafiya”. Sai da ya fita da fin mintuna biyar sannan Maanal ta tashi itama. Ruwan da ya sha ta ɗauke ta maida kitchen, ta can tabi ta ƙofar baya ta gudu. Dama jiya haka tayi, aiko mi Oum zatai ba dariya ba. Dan ma ta tabbatar Inte ta kira, koda ta fito cemata tai, “Ina Baby?”. Inte dake ƴar dariya ta ce, “Oum ta fita ta back door”. Itama Oum dariyar tayi, tace “Ja'ira”. Inte dai ta koma ciki tana cigaba da dariyarta. Yanda Maanal ɗin keyi daɗi yakema Oum, dan ta fahimci Autanta zai samu irin kulawar da magidanci ya kamata ya samu ga iyalansa ba irin matan su Fawzan ba. Wannan shine babban dalilinta na ɗora Hajiya Shuwa akan gyara Maanal ɗin dama. Dan bata son Babynta tai rayuwa irin tasu Saheeba sam..... ★Tuni Maanal ta shiga sashensu dan tasan AA na sashen Mamy dubata. Bedroom ta wuce dan haɗa masa ruwan wanka. Ta shagala a haɗa masa turarurrukan ƙamshi a ruwan ya shigo batare da taji motsi ba ma. Sai da ta fito ta ganshi tsaye a closet yana zare jacket ɗin suit ɗinsa. Kallonsa tai ta ɗauke kanta, zata wucesa ya riƙo mata hannu. A slowly ya maidota baya ya jingina da glass ɗin closet ɗin. Shima ya matsa jikinta sosai ya dafa glass ɗin da hannunsa ɗaya. Fuskarsa ya sauke a hankali a gefen wuyanta, yanda yake busa mata numfashi da manna ma wuyan tagwayen kisses ya saka tsigar jikinta tashi, cikin wata irin kasalliyar murya a cikin raɗa ya ce, “I miss you my heart”. Motsawa tai ta shige jikinsa, tare da zagaye duka hannayenta a bayansa kanta na kwance a ƙirjinsa. Shima sai kawai ya rungumetan yana sauke ajiyar zuciya. “Rungumarki tafi laushin katifa, laushin jikinki ni'ima ce mai sauke gajiya da nauyin jikina. Hakan tamkar kwantar da tarnaƙin dake zagaye da ni ne, dan kin saka jikina na min magana fiye da kalmomina. Zan so kiyita kasancewa a cikinsa na har abada, hakan a gare ni gata ne da riritawa”. Itama cikin raɗa ta ce, “I miss You you too My Root-Soul! Nima idan har nayi ko awa ɗaya batare da kai ba duniyata bata da tushe ko kwanciyar hankali. Dauriya kawai nake yi saboda Ina ganinka a kowanne murmushi na, domin kaine ka shuka shi.” A hankali ya wani busa mata iska cikin kunne, tare da raɗa mata, “Zan cigaba da ajiye wannan murmushin kuwa na har abada in sha ALLAHU akan ƙyaƙyawar fuskar nan taki”. Ƙanƙamesa ta sakeyi sosai tana jin kamar ta tsagashi biyu ta shige cikin jikinsa kawai. Shima dai hakan yake ji a ransa. Sun fi minti uku a haka kafin ya cirota daga jikin nasa ya riƙe fuskarta a cikin tafukan hannunsa suna kallon juna. Sosai take karantar ruɗaɗɗen al'amarin dake a cikin ƙwayoyin idanunsa, kamar yanda shi kuma yake karanto tsoro da fargaba mai haɗe da sallamawa a garesa. Lallausan murmushin kwantar da hankali ya sakar mata. Muryarsa na sake komawa cikin maƙoshi ya ce, “Mizan samu?”. Akan lips ta bashi amsa da, “Komai ma”. Ya ɗage gira sama tare da taɓe baki a yanayin murmushi yana jinjina mata kai irin na (kin tabbatar?). Ido ɗaya ta kashe masa alamar (Yes) sai kuma tai ɗiɗɗishe da ƙafafunta kasancewar ya fita tsaho sosai ta zare gilashin idanunsa, hannayenta gaba ɗaya ta zagayo akan wuyansa ta matsar da fuskarta gab da tashi har suna zuƙar numfashin juna. Sai kuma ta lumshe idanunta cike da jin nauyi da kunya. Shi dai kallonta kawai yake kamar ya samu television. Idanun nata a lumshe ta ɗaura lips ɗinta akan nashi ta sumbata. Tana ƙoƙarin janyewa ya hana hakan ta hanyar riƙo kanta kawai ya kamo lips ɗin nata da ƙyau ya tura cikin bakinsa. Da jikin closet ɗin ya mannata, sai kuma ya kamata ya ɗaga cak a jikinsa, tako harɗe ƙafafunta a bayansa kamar yanda ta harɗe hannayenta... A haka ya dinga tafiya da ita har cikin bayin, bai kuma tsaya ba har sai da ya tsaya dasu ƙasan shower, kawai ya sakar musu ruwa mai ɗumi a jiki. A tare suka sauke ajiyar zuciya, ya kuma cigaba da yin yanda yaso da lips ɗinta. Kafin ya saki da ƙyar ya shiga rabasu da kayansu. Daga haka ya sake ɗaukarta ya fito a wajen wankan suka shige jacuzzi. Anan ne fa ya fara tabbatar mata ta tsokalo ƴan samari, dan sai da idannunta suka fara raina fata ganin zai ɗauki wani sabon layin. Ta fara roƙo da magiya da son kuɓutar da kanta. Shi ko ya nuna mata a wannan fannin bai san wasa ba, bai san ɗanɗani haukaci ba. ALLAH dai ya taimaketa akai kiran sallar magrib, amma data gayawa mutanen Giro kam. A gurguje suka ƙarasa wankan suka fito, ta taimaka masa da shafa mai da saka kaya kamar yanda ya buƙata, da ɗan hanzari ya sumbaci goshinta ya fice dan sallar ake ƙoƙarin tayarwa. Yana gama fita ta sauke ajiyar zuciya, sai kuma tai murmushi, dan ita da kanta bama kanta dariya take. Itafa komai ayi tana so, amma tsakani ga ALLAH banda sha ƙundum, dan a tsorace take. Itama kimtsawa tai tayi sallar, tai zaman yin azkar. Tana a wajen har akai sallar isha'i sannan ta miƙe. A gurguje ta gyara jikinta ta canja kaya wanda suka dace dan sashen Oum zasu koma cin abinci. ★Maanal na kammala shiryawa sashen Oum ta wuce. Dan tasan shima ya wuce can tare da su Yaya Fawzan. Ta samesu su duka ukun kuwa a can, Anum na jikin AA yana mata homework. Tana yin sallama da shi suka fara haɗa ido, yanda yake kallonta babu ko kunyar yayunsa yasa ta ɗauke kanta. Cikin girmamawa ta gaida Babban yaya da Yaya Fawzan. Yaya Fawzan sarkin tsokana ya fara tsokanar tata kuwa. Cike da jin kunya tasa hannu ta rufe fuskar tata tana dariya. Dai-dai nan Nuratu da Oum suka shigo, Nuratun najan akwati. Su duka kallonsu suke, banda AA da yay musu kallo ɗaya ta ƙasan ido ya ɗauke idonsa. Yaya Fawzan ne daya kasa haƙuri ya ce, “Lafiya kuwa Oum?”. Sai da Oum ta nunama Nuratu hanyar upstairs tana faɗin, “Jeki kai kayan sama sai kizo kici abinci”. Sannan ta zauna tana bama Fawzan ɗin amsa. “Faɗa suke da Saheeba acan shiyyasa nace ta dawo nan.” Cikin ɗan ɓacin rai Babban Yaya yace, “To ta wuce gida mana dole ne sai ta zauna anan Oum?”. Fuskar Oum da murmushi ta ce, “A'a Fadeel ba ayi haka ba, tunda tana son zama nan ɗin a barta. Kasan Hajiya Turai ba wani zama waje ɗaya take ba. Ga Nuratun ba isashen lafiya ba wazai kula da ita. Su Nana kuma suna nan suma balle ace taje Kano. Kuma muna nan ma ai ba'ace taje Kanon ba koda suna can”. Babban Yaya dai da alama ba son zaman Nuratun yake ba, haka shima Fawzan sai da ya nuna hakan a fuska. Gwaska AA kuwa ma bai nuna yama san mi sukeyi ba balle ya tanka. Maanal kuwa murmushi tayi babu wani damuwa a fuskarta, amma acan ƙasan ranta ita tasan saboda AA Nuratun tace zata dawo nan ɗin da zama ko kuma akwai dai wata a ƙasa. Shekararsu nawa da Saheeba ɗin faɗan baisa tazo nan ɗin ta zauna ba sai yanzu. Amma babu komai zata iya da su, dan a yanzu kam a shirye take tsaf zata buga da kowa akan mijinta, kuma zata basu mamaki. Dan haka ta turama RK saƙo. Ganin duk yanayinsu ya canja Oum tai murmushi, cike da kulawa ta ce, “Bana son ku koyi halin daba naku ba, ku manya ne, sai kun gyara na ƙasa zasuyi koyi. Ko'a fuska bana son wani cikinku ya nunama yarinyar nan wani abu mara daɗi. Fawzan bara na kira matarka a waya, itama kwana biyu naga duk ta tsangwami kanta.” Kafin ma wani yay magana Oum ta fara kiran Nibras a waya. Tana ɗagawa kafin ma tace komai Oum ta ce, “Zo ina nemanki yanzun nan”. Tamkar dama kiran Oum ɗin take jira zambar ta miƙe, cikin ƙanƙanin lokaci sai gata a sashen. Shi Fawzan ma sai abin ya bashi dariya. Amma bai ce komai ba, baima kalla inda take ba tunda ta shigo. Sai ga Nuratu itama ta sakko, wani kallon harara sukaima juna ita da Nibras ɗin kowa ya ɗauke kansa........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖8️⃣9️⃣ ______________ ........Koda Nibras ta gaida AA kansa kawai ya jinjina mata amma ko kallon inda take baiyi ba itama. Saima ya miƙe ɗauke da Anum datai barci ya haura sama. Ɗakin Oum ya kaita ya kwantar, Naufal dama yay barci shi tun a massallaci, suna shigowa Fawzan ya wuce da shi saman. Koda ya dawo kai tsaye dining ya nufa yana faɗin, “Besty zoki bani abinci barci nake ji”. Amsawa tai tana miƙewa, sai da taje dining ɗin ganin babu plates sai ta wuce kitchen ɗakkowa. Fawzan da Babban yaya ma sai suka miƙe. Sai da suka zauna kamar abin arziƙi Fawzan ya ce, “Babban yaya ina da tambaya”. Babban Yaya da bai san mi za'a tambayesa ba ya ce, “Uhum ina jinka”. Sai da Fawzan ya ɗan kalla AA sannan ya ce, “Dama ango na barci a farkon dare dan ALLAH?”. Kallon AA dake hararar Fawzan Babban Yaya yayi, cikin son riƙe murmushin dake neman kufce masa ya ce, “Nikam ka tambayeni, tambayi Auta maybe shi yana da amsar baka”. Dariya Fawzan ya tuntsure da ita ganin shima dai yau Babban Yaya ya ɗana. Cike da neman son ƙure AA ɗin Fawzan ya ce, “Auta ance na tambaye ka, dama ango na barci a farkon dare?”. Waya AA ya ɗauka yana dannawa batare da ya bashi amsa ba, minti ɗaya ya ajiye wayar yana wani makirin murmushi da kallon Fawzan, sai kuma ya ɗage gira sama ya ce, “Ka duba na tura maka amsar”. Wayar Yaya Fawzan ya ɗauka. Idanu sosai ya waro akan AA, sai kuma yace, “A lallai Auta kaci wake, ni ka turama wannan abun?”. “Naga amsar da kake nema kenan?”. AA ya faɗa ciki-ciki. Babban Yaya dake murmushi Yaya Fawzan ya kalla baki buɗe. Sai kuma ya miƙa masa wayar yana faɗin, “Kalla fa abinda ya rubutan Yaya”. Fitt AA ya ɗauke wayar yana harararsa. “Oh ashe ma kai ƙaramin mara kunya ne, ka bari Babban Yayan ya gani mana”. Fawzan ya faɗa yana dariya. Isowar Oum dining ɗin ya samawa AA lafiya a wajen Yaya Fawzan. Sai ga Maanal ma ta dawo. Suma su Nuratu duk suka zauna. Daga nan tsokana ta ƙare akai zaman cin abinci. Bayan sun kammala sun koma falo su Inte suka gyara wajan. AA dama shi bai zauna ba, sallama yay ma Oum da babban Yaya, ganin Maanal bata da niyyar tashi ya zuba mata ido. Itako ta fiske. Oum na lure da su, sai kawai tai murmushi ta kalla Maanal, babu wasa tace, “Oya Baby tashi kuje sai da safe”. A kunyace Manaal ta miƙe. Fawzan ya ce, “Auwwwwwn! Lillyn Babban Yaya ƴammata”. Ai da sauri ta fice tana murmushi. Oum da Babban Yaya sukai murmushi suma. AA kam hararar Fawzan yayi da faɗin, “Girma dai ya faɗi”. Yaya Fawzan dake dariya ya ce, “Naga kai a jaka ka zuba naka ka ɓoye”. Sarai AA ya fahimci abinda Yaya Fawzan ya ke nufi, sai ma ya rasa abin cewa ya murmusa kawai yana ma Babban Yaya da Oum sai da safe yabi bayanta. Sai da suka fara zuwa sukama su Mamy sallama. Har sun miƙe Mamy tace ya zauna zatai magana da shi. Jin hakan yasa Maanal fitowarta a ɗakin, AA ya bita da kallon ƙasan ido. Mamy dake lure da shi ta sake ɗaure fuska zuciyarta na zafi. Cikin dakewa ta ce, “Gobe ka sayama Aunty ticket zata tafi”. Da mamaki ya kalleta, sai kuma ya daure yace, “Baki gama warkewa ba fa Mamy miyasa zata tafi bayan itace mai ƙoƙarin kula da ke?”. “Ni nace da kai ban gama warkewa ba? Baga Nana nan da Saheeba ba kuma”. Ɗan jimmm yay na sakkani, sai kuma ya ce, “Shike nan ALLAH ya kaimu goben.” A daƙile ta ce, “Ina maganar mu ta tsaya ta documents ɗinka?”. Yanzu kam kasa jurewa yay sai da ya ɗago ya kalleta da ƙyau. Ganin yanda ta zuba masa ido sai ya ɗauke nashi. Baya buƙatar wani abu da zai ɓata masa wannan daren, dan haka ya miƙe yana faɗin, “In sha ALLAHU zan kawo miki ina kan tattarawa.” “Hummm! Ka cigaba da raina min hankali zan baka mamaki. Kuma yarinyar nan bana buƙatar sake ganinta ta shigo dubani”. Murmushi yayi mai ƙuna, cike da girmamawa yace, “In sha ALLAHU bazata sake zuwa ba kiyi haƙuri”. Ya nufi ƙofa abinsa ya fice. Ya yi tunanin Maanal ta wuce, sai ya sameta suna hira da Aunty a falo sunata dariyarsu hankali kwance. Su dukansu basu da wata shaƙuwa da dangin Mamy saboda ba wani shiga sabgarsu suke ba, badan suna talakawa ba ne, kawai dai tun farko Mamyn ba zuwa take dasu sabgohinsu ba, koda yake itama bason shiga take ba sai ta zaɓa, a karo na farko yaji Auntyn ta shiga ransa yau, dan duk wanda yaso Maanal da Oum to shima zai so shi kuwa. Sai da ya gama kallesu sannan ya ƙarasa in da suke. Miƙewa tai sukaima Auntyn sallama suka wuce, ta bisu da kallon sha'awa, a karo na farko taji haɗin nasu ya mata dai-dai kuma ya birgeta.... Ta riga shi haurawa sama, ya tsaya kashe wuta da rufe ƙofa, lokacin da yake iskota ɗakin hatta shiga bayi tana yin brush. A haka ya shigo ya sameta. Tsayawa yay ya harɗe hannayensa a ƙirjinsa yana kallon ta kawai. Ta cikin mirror ɗin ta zuba masa ido itama. Sai kuma ta ɗage masa gira alamar (kallon fa). Idanunsa ya ɗan lumshe ya buɗe a kanta, ya cigaba da kallonta kawai. Bayan ta kammala ta saka masa makilin ɗin a jikin nasa brush ɗin, ta matso gabansa, hannunsa ta kama ta saka masa brush ɗin sannan tai ɗiɗɗishe ta hure idanun, “Kallon ya isa haka”. Ta faɗa tana zagayesa ta fice. Da kallo ya bita, sai kuma ya saki ɗan murmushi mai sanyi. Ya matsa jikin mirror ɗin kawai ya fara brush ɗin shima. Kafin ya fito harta shirya cikin kayan barci ta ƙarama jikinta turaren Hajiya Shuwa. Sai dai yau kala uku kawai ta sanya dan Hajiya ta gargaɗeta sosai. Sai dai duk da haka bata gane ma'anar turaren ba. Ta gama shiryawa tana gaban mirror tana warware gashinta ya fito. Gaban mirror ɗin yazo shima ya tsaya a gefenta, kamar yanda yay a bayi yanzu ma hannaye ya harɗe ya wani ɗan jingina da katakon mirror ɗin yana kallon yanda take yamutsa fuska, dan a duniya Maanal fa ta tsani abinda zai taɓa mata kan nan koda itace da kanta. Jin idanun nasa sun mata yawa a jiki ta juyo tana kallonsa itama. Sai kuma ta tura baki cike da shagwaɓa da jin zafin taɓa kan da take ta ce, “Wai mi kake kallo?”. Cikin ɗan motsa lips kaɗan ya ce, “Matata mana”. “Tana ina?”. Ta faɗa tana waigawa gefe-da-gefe like tana neman matar tasa. Wani miskilin murmushi ya saki yana kauda kansa gefe da cije lips kaɗan, sai kuma ya sake maido dubansa kanta ya wani bita da kallo tun daga ƙafafunta har zuwa saman fuskarta. Sake ɓata fuska tai tana harararsa, yay murmushi, cike da son sake kunnata ya kai hannu ya shafa gashin nata da faɗin, “Ya kamata ama gashin nan kitso, dan yafi ƙyau”. Rau-rau ta kallesa idanunta cike da hawaye ta ce, “Ni ALLAH bana so. Kai ka cika tada zaune tsaye”. Cikin ɗan waro idanu ya ce, “Yanzu Besty kitson ne tada zaune tsaye? K dan baki san kitso na miki ƙyau bane ba....” “Ni dai bana so”. Shiru bai sake cewa komai ba ya zuba mata ido kawai. Sai kuma taga kamar yay fushi. Juyowa tai riƙe da cumb ɗin tana kallonsa. Sai ya ɗauke kansa gefe. Yatsa tasa tana ɗan takalar hannunsa dake harɗe a ƙirjinsa har yanzu. Irin ɗan gocewar nan yayi kamar yara na fushi ana son lallashinsu, ta ƙara takalarsa, ya sake gocewa. Sai itama ta haɗe fuskan ta kauda kanta. Fuuu ta yunƙura zata bar wajen ya riƙota da sauri. Fisgewa take ƙoƙarin yi yaƙi barinta. Cikin ƴar shagwaɓa ta ce, “Ni ka sakan, ina maka magana ma kana min wulaƙanci danma kaga ina kulaka zaka wani mun fushi”. Tsayar da ita yay a gabansa yana wani binta da kallon ƙurulla, cikin muryarsa data fara canjawa saboda yanayin daya fara shiga ya ce, “Ni nace ina fushi ne, kawai na tafi wani tunani ne daban.” Yanzu kam nutsuwa ta ɗan yi tana kallonsa ta ce, “Nami to?”. Sai da ya ɗan ja mata hanci sannan ya ce, Naki mana”. Ya ƙare maganar yana binta da ɗan iskan kallon daya bata kunya. Matsawa tai daga kusa da shi tare da faɗin, “Haramm irin wannan kallon baida ƙyau ALLAH”. Haka kawai ya tuna randa ta masa bore a asibiti, murmushi mai haɗe da ƴar dariya ta kufce masa. Sai ta tsaya tana kallonsa tare da sake ɓata fuska. “To miye na min dariyar?”. Cikin son danne dariyar da tsiya-tsiya yay zipping bakinsa da faɗin, “Na bari na bari. Kawai na tuna randa kika min rashin m ne a asibiti. Kai yarinyar nan idan kika birkice kina da wahalar sha'ani dan darunki bala'i ne, ranar kinfa kunna ni fiye da yanda kike zato, tsabar ɓacin rai kwana nai ban barci ba. Rafeeq kuma ya sake tunzurani a washe gari, ai ko kaɗan ya rage na fasa masa baki”. Dariya Maanal ta shigayi, ta ce, “Kai jama'a ban taɓa ganin ɗan daya raina kawunsa ba irin ka, nima ɗin ka kunna nin ai, dan ji na dingayi kamar na faffaleka da maruka, dama ina ciki dakai sosai ta yanda ka ke wani basar da ni like bama ka taɓa sani na ba. Sai kuma kazo ranar kana wani min gadara kai miye-miye, harda wani cewa ba mai shiga gonar da ka shiga, idan na auri wani zaka min fatalwa ne ma ko mi kace... Hummm da gaske fa baka da kirki Besty”. Hannunsa ɗaya ya cire yakai shi saman fuska ya shafo gemunsa. Yana binta da wani kallo mai ƙarfi da laushi, sai kuma ya saki murmushin “Humm bazaki gane ba ne.....” “To ganar da ni”. Tai maganar tana ɗan hararsa. Matsowa yay jikinta sosai ya mannata da mirror ɗin, ya kamo hannunta ya zare cumb ɗin. Sai kuma ya ɗagata cak ya ajiye saman katakon mirrorn ya cigaba da taje mata gashin a hankali. Amma duk da hakan sai da ta riƙe hannunsa tana yamutse fuska kamar zata saki kuka. Daina tazan yay ya tsaya yana kallonta, ta sake cuna masa baki gaba da faɗin, “Besty! Wai mata basa aski?”. Dariya sosai ta bashi amma baiyi ba. Sai ya sumbaci bakin kaɗan yana kallonta gira a ɗan ɗage.........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖9️⃣0️⃣ ______________ .........“Ke yanzu idan akace kiyi aski sai kiyi?”. “ALLAH da gudu ma”. “Ai da yake baki da man kai”. “Eh naji ɗin banda shi, kai baka san zafin kitso bane”. Cikin wani shegen salon iskanci da iya shege ya sake narke idanunsa cikin nata. A yanyin raɗa ya furta, “Duk zafinsa ya kai DAREN AIKAIRI ne”. Wani kunya ne na bala'i ya lulluɓe Maanal. Da sauri tasa tafukan hannunta ta rufe fuskarta. “ALLAH baka da kunya. Nifa ƙanwarka ce”. “Da an shigo cikin ɗaki nake tashi daga Yaya ai, dan haka ni ba yayanki bane yanzu.” Ƙoƙarin tureshi tai zata sauka ya riƙeta yana dariya. Sai kawai ta kife kanta a ƙirjinsa. Murmushi yake mai ƙayatarwa, sai kuma ya samu damar tufke mata gashin nata a hakan. Yana gamawa ya kamata cak ya sauke a ƙasa. Aiko fitt tabar masa wajen. Bai dakatar da ita ba ya fara ƙoƙarin cire kayansa kawai domin canjawa zuwa na barci.. Maanal kam data gudu haye gadon tai ta kwanta, sai kuma ta ɗauka wayarta. WhatsApp ta shiga tana ɗan duba sakwannin, dan shi kaɗai take yi, bayan anan bata da account a kowanne shafi na media sai dai ta shiga ta ɗan yi kallon abu buwa a TikTok da Instagram tunda bata saye bata sayarwa, har YouTube ma takan je. A WhatsApp ɗin ma yawancin groups ne na makaranta, sai sakwanin taya murnar aure da suka tura mata pc, da masu ƙorafin rashin gayyatarsu da batai ba, sai na addini haka da class na abubuwa data ɗan shiga ta koya, mafi yawama girke-girke ne sai harkar zane dan tana son girki, bayan zane-zane. “Yanzu lokacin miji ne”. AA dake hawowa gadon ya faɗa yana zare wayar daga hannunta. Kallonsa tayi a marairaice ta ce, “Hiran group fa kawai nake gani sai sakwannin taya murna”. “Karki damu zan miki hirar ni, na kuma tayaki murnar auren”. Baki ta ɗan tura kaɗan, zatai magana ya hanata. Hasken ɗakin ya kashe gaba ɗaya ya bar musu ta barci datai dummm sosai. Sai kuma ya sake matsota sosai a jikinsa ya rungume. Ajiyar zuciya suka sauke a tare, a cikin kunenta yay mata raɗar data sakata kife fuskarta a ƙirjinsa tana ƴar dariya. Ta ce, “Nidai ba ruwana kai da Abah”. “Shima ya haƙura ya sallama. Alamar jikoki yake so da wuri”. Ƙaramin dundu ta masa a baya. Tare da kai bakinta kan kunensa ta raɗa masa, “ALLAH ka canja hali”. Shima sai ya raɗa mata. “Mudai canja, dan da an ganki da cikin ansan tare mukayi”. Tureshi ta shiga yi tana tirza ƙafa. Wata ƴar ƙanƙanuwar dariya mai tada tsigar jiki ya shiga yi mata yana sake matseta a jikinsa. Yayinda shima kukan shagwaɓar nata ke yamutsa masa garkuwar jikin nasa. Sai kawai ya shiga laluben lips ɗin nata, cike da nutsuwa da tarin ƙauna da shauƙi ya rufesa ruf da nashi. Tun tana ƙoƙarin son ƙwacewa harta nutsu ta sallama tana sake ƙanƙamesa. Ita in dai iya haka ne normal ne zata bada haɗin kai. A zarce nan ɗin ne hankalinta ke tashi. Sai ko daya bari ya shagaltar da ita da salonsa ta miƙa wuya gaba ɗaya sannan ya ɗauki layin da take tsoron. Ai ko a take ta firgice masa. Tana ƙoƙarin masa magiya ya rufe kowacce ƙofar yin hakan. Ta riga ta tsorata da al'amarin tun farko, dan haka yake tayar mata da hankali. A haka yau ma ya bita a sannu saboda ba kamar waccan ranar da shima yake a wani yanayi ba. Amma duk da yanda ya lallaɓata, ya riritata sai da tasha azaba, ta kuma dinga masa kuka hawaye share-share. Addu'a ta dinga yi a ranta ALLAH yasa ma ta suma kamar ranar, amma addu'ar nan bata karɓu ba kuwa, dan sai da ya samu yanda yake so ya barta. Ganin yanda ta galabaita ya sashi jin tausayinta sosai, dan shi da kansa yasan bana wasan yara bane tako wane fanni. Ita kuma dama can yasan tana da tsoro, duk tsiwar Maanal da iya takalar faɗa akwai tsoro, bata ƙaunar abinda zai taɓa jikin nan nata sam-sam. A wajen sit bath ma yasha shagwaɓa da kuka, shi har ma yayi tunanin koya sake ji mata ciwo ne. Bai samu natsuwa ba sai da ya dubata yaga lafiya lau sannan ya sauke ajiyar zuciya. A ransa kuwa yana tunanin lallai akwai daru kenan in dai haka za'a cigaba da kasancewa. Dan Maanal akwai shegen raki. Dama duk mutum mai baki ai sai a hankali ne, zaka samesu akwai ɗan karen rakin tsiya da tsoro. Sai da ya bata magani tasha sannan ta fara sauke ajiyar zuciya. Shima ajiyar zuciyar ya sauke ya rungumeta yay musu addu'a sai barci. Gabanin asuba kuwa ya farka cikin wani matsanancin yanayi, jinta a jikinsa kam ya sake tunzura. Cikin barci ta farka a firgice. Kuka ta sanya masa. Bai kuwa ƙyaletan ba dan ya fahimci sai ya mata da gaske zasu dai-daita, saboda ya daɗe da fahimtar yanayinsa. Kuma bashi da sha'awar ajiye mace fiye da ɗaya, kenan dole ya cire tausayi ya horar da ita a irin layin da zata iya ɗaukar lalurar tasa tako wane irin yanayi. Aiko rikicin datai masa yanzu sai da yafi na daren sosai. Sai da ya tabbatar ya samu yanda yake so nan ma sannan ya koma lallashinta. Yanzun ma shine ya gyara mata jiki, ya ɗakkota ya ajiye har kan abin salla dan langyare masa tai bazata iya ba. Shi ko yace yaji ya gani duk zai iya. Yana fita salla ta sama ƙofar key, salla tayi a gurguje tai azkar ta miƙe bama ta ƙarasaba ta haye gado ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya, anan ta ƙarasa azkar ɗin. Koda ya dawo ya ji ƙofar a rufe dariya ta bashi, amma koba komai ta tsira, dan da ace bata rufe ɗin ba babu abinda zai hanashi sake ziyartarta a safiyar nan. Fuskarsa da murmushi ya koma ɗayan ɗakin dake matsayin nata ya kwanta. Duk da dai yanzu sun raba kayansu biyu kowanne ɗaki akwai na kowa, dan yace babu batun raba ɗaki bai yarda ba. Sai dai duk inda suka so kawai suyi zamansu. Itama tafi gamsuwa da hakan, dan ko shi ya zaɓi su raba ɗin bazata yarda ba.... _________★ GIRO A guje Sule ya shigo gida. Gwaggo na ƙofar ɗakinta zaune tana gyara ganyen kuka ya tsallaketa ya shige ɗakinta. Tana ƙoƙarin yin magana kawai ƴan sanda suka afko musu. Sosai gidan ya kacame matan dake a tsakar gida suna harkokinsu duk sun tarwatse sun afka ɗakuna sun banko ƙofa. Jikin Gwaggo ya fara rawa, ko ada sanda Babu ke zuwa da kaki ma tsoro take ji ta dinga masa masifa kenan har sai ya ciresu balle yanzu da tsufa ya sake razanata. Cikin tsawa ɗan sanda yace mata ina Sule. Fitsari na zuba mata zuuuu a zane ta nuna ƙofar ɗakinta. Ga hawaye share-share ta shiga rantsuwa da faɗin ita wlhy koma mi Sule yay babu hannunta a ciki. Su nemi uwarsa bata da alaƙa da Sulen. Ko takanta basu biba suka afka ɗakin, babu wani jimawa suka fito da Sulen, handcuffs suka sanya masa. Aiko ya tsaya yayma Gwaggo wani shegen kallo, cike da taurin kai da rashin ji ya ce, “Ke kuma zamu haɗe ne, ki jirayi dawowata na kwanaki ne. Kin san ALLAH garama kikai kanki maƙabarta kafin na fito. Ba dai ni kika tonama asiri ba, kika ce kuma baki da alaƙa da ni ko? Hummmm!!”. Ya cije baki. Tisa ƙeyarsa sudai ƴan sandan sukayi. Aiko matan gida sai leƙe ta windows, ga mazan duk basa nan suna daji ana gyaran gonaki saboda ruwa dake ta haramar sauka. Haka aka tisa ƙeyar Sule aka wuce da shi. Sai da suka tabbatar sun bar kusa da gidana gaba ɗaya sannan aka shiga fitowa kowa baki cike da gulma. Akan daɗe ba'a kama Sule ba saboda yana da shegen wayo, dan ko kame ƴan sanda suka shigo ƙauyen yasan yanda zai gudu. Yau ma dai da alama mamayarsa sukayi gaskiya. Dan in ba haka ba kama Sule ga ƴan sanda ai jidali ne babba. Amma koba komai ai suma sa ɗan huta. Ga Sailu bata gidan tana can yawan biɗiɗinta na tsiya. Hakama Haƙila tun safe ta fita da cin-cin da fara har yanzu ba'a dawo ba, dama tace Suru zataje. Rashin jin motsin Gwaggo yasa aka leƙata, sai gata zube a ƙasa firgici ya sakata sumar wucin gadi. Ruwa aka shafa mata ya farfaɗo, sai kuka wiwiwi tana jama Sule ALLAH ya isa. Kowa dai yasan dan taga baya nan ne ta samu baki. Su dai suka kamata suka shiga da ita ɗaki suka koma cikin gida gutsiri tsoma. A gigice Sailu ta dawo gidan, dan kuwa tun a hanya aka tareta aka sanar mata ƴan sanda sun kama Sule kuma Gwaggo ce ta tona. Tab ɗin, ai tana shigowa gidan Gwaggo ta taƙarƙara ta fito yin alwalar azhar kawai Sailu ta wanke fuskar tsohuwar nan da mari sai da Gwaggo ta zube ƙasa. Jikin Gwaggo na rawa kar-kar ga hawaye ta kalla Sailu ta ce, “Ni kika mara Sailu? Ni dana haifa miki Habibu kika daka?”. “An dake kin munafukan tsohuwa annamimiya, idan kika ƙara magana ma sai na sake wanka miki wanda haƙwaranki zasu zuba a ƙasa. Kuma wlhy ki sani in har wani abu ya sanar min yaro kema ki jira sakamako”. Tana gama faɗa ta fice a gidan. Shiru Gwaggo tai a zaune tama kasa kuka. Babu abinda ke dawo mata a rai sai fuskar Ammie. Ta tuno randa ta hana Babu zuwa inda Asiya take, sai cikin dare ya lallaɓo ya shiga, kawai gabannin asuba ta fito fitsari suka haɗe da Babu ɗin da Ammie sun fito daga bayi alamar wanka sukai tare. A fusace ta wani ɗauke fuskar Ammie da mari, ta sake ɗauketa da na biyu. Amma baiwar ALLAHr nan ƙasa kawai tai da kanta har ta wuce su ta shige bayin. Sai da ta shiga sannan Ammie ta wuce ɗakinta yana sharar hawaye, Babu kuwa tsoron Gwaggon bai barshi ya koma ba haka ya fice... Sharrr hawaye suka sake gangaroma Gwaggo, tabbas ta cuci kanta, ta tsige Asiya jinin Lubabatu da Umar daga jikinta, ta aurowa Habibu wadda ranta ke so, ga shi nan itama tana mata yanda take so ita da ɗan nata. Jikokin kuma da take ƙauna take ganin sunfi ƴaƴan Asiya suma suna tisa karatun uwarsu a a garesu........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖9️⃣1️⃣ ______________ ........Duk yanda AA yaso Maanal ta fita aiki yau dole ya haƙura. Dan da gaske fa ya jigatata. Haka dole bayan ya tashi ya haɗa mata break fast mai sauƙi da kansa, da ƙyar ya lallasheta tazo ta buɗe masa ƙofar data rufe. Duk da yana ganin zai makara haka ya haƙura ya taimaka mata ya gasa mata jikinta taci abincin ya bata magani sannan yay nasa shirin ya fita. Aiko ko Oum ta waya yay mata sallama. Hakama Mamy ta waya ya kirata yace tai haƙuri ya makara ya wuce. ALLAH sarki Oum ita sai ta fahimta tai murmushi kawai da binsu da addu'a. Mamy kuwa sai ta shaƙa. Amma batai magana ba saboda Aunty dake wajen. Dan yanzu sun haɗema Auntyn kai ita da Maman Saheeba da Saheebar basa zancen komai a gabanta. Shiyyasa ma tace zata wuce yau dan tana son ta tsira da mutuncinta.... Koda AA ya isa company yau a makare staff ɗinsa sun sha gulma. Dama kwanakin nan haka suketa gulmarsa wai ya ƙara ƙyau yay fresh na angwanci, sun ƙagara Maanal ta dawo aiki kullum cikin fata suke. Amma sunji tsitt. Babu kuma mai ido da kwallin iya tunkararsa da tambaya. AS kansa yau sai da yay gulmar makarar boss ɗin a zuciyarsa, dan hakan abune mai matuƙar wahala da zakaga AA yayi. Oga AA da bai san sunayi ba kam akan aiki kawai ya dira, sai dai kaɗan-kaɗan ya saki murmushi. Dama kuma fuskar tasa yau da sauƙin ɗaurewa. A haka AS yay masa knocking. Izinin shiga ya bashi, koda ya shigo yaga yanda boss keta murmushi sai yay ta satar kallonsa. Har sai da AA ɗin ya tsargu ya ɗago a bazata ya kamashi, sai AS ya wayance. Komai AA baice masa ba ya duba file ɗin daya kawo masan ya saka masa hannu. Ganin AS ɗin yaƙi tafiya ya ɗago ya kallesa. Ƙasa AS yay da idanunsa. A dake AA ya ce, “Akwai wani abu ne kuma?”. AS ya girgiza kansa. Sai kuma cike da girmamawa ya ce, “Boss dama zan sanar maka za'a kai kuɗin aurena weekend ɗin nan, shine Abbana yace na sanar maka idan baka da uziri sai kuje”. A mamakin AS sai ji yay AA ya ce, “Humm munafuki wato kaima aure kake so, no wander naga ka fara ajiye gemu kwanan nan kana kuma saka manyan kaya”. File AS ya saka ya rufe fuskarsa yana dariya, ransa fal mamakin yau Boss na masa wasa tab ɗin. Lallai Amarya Manaal ta shayar da boss zumar soyayya original mara gauraye. Shima AA dake murmushi sai ya ɗan taɓe baki yana maida hankalinsa ga computer ya ce, “Okay ALLAH ya kaimu tunda naga nine ma surukin naka, fita min a office”. Fitar kuwa AS yay batare da ya yarda ya buɗe fuskarsa ba. AA dake binsa da kallo ƙasa-ƙasa a fili ya ce, “Yaro kayi ƙyan kai, dan koni da nasan haka aure yake aljannar duniya da ban yarda na cika ashirin a tuzuru ba. Amma ba damuwa, ko yanzu ma zamu fanshe shekarun mu tsaff in sha ALLAHU”. Ya wani lumshe idanun ya buɗe yana jin nutsuwa da wani sabon feeling na farin ciki. Waya ya ɗauka ya turama Maanal guntun message ya cigaba da aikinsa... Wajen ƙarfe sha biyu AS ya shigo office ɗin, batare da AA da aiki yayma yawa ba ya ɗago ya kallesa ya ce, “Badai lokacin meeting ɗin yayi ba?”. Cike da girmamawa AS ya ce, “Aa Sir, baƙo gareka. Na nuna masa aiki ne da kai sosai, kuma yau babu ma ganin kowane baƙo a tsarinka, amma yaronsa na neman yin hayaniya”. A karo na farko AA ya ɗan ɗago ya kallesa, sai kuma ya maida kansa, da ƙyar ya iya motsa lips ya ce, “Waye?”. “Senetor Bukar Kaugama”. Karo na biyu AA ya sake ɗagowa ya kallesa. Sai kuma cikin cije lips ya ce, “Barshi ya shigo”. Sosai AS yay mamaki, amma sai baice komai ba ya amsa da girmamawa ya fita. Aikinsa ya cigaba da yi hankali kwance, tsahon mintuna goma akai knocking ƙofar. Sai da ya mula dan kansa sannan ya bada izinin a shigo. AS ne ya fara shigowa, sai Sen.. Bukar da matashin ɗansa da bai wuce 26years ba, dan zai yi sa'a da AS. Tsabar wulaƙanci AA baima nuna yasan da shigiwarsu ba har Sen.. ya zauna shi da ɗansa da kusan minti ɗaya sannan ya ɗago oily fararen idanunsa ya kallesa, fuskarsa da wani ɗan munafukin murmushi, da maganar nan tasa mai fita ciki-ciki da ƙasaita tamkar baya so ya ɗan lumshe idanun da ɗan rissinar da kai sannan ya buɗesu slowly ya ce, “Barka ranka ya daɗe”. Sai kuma ya ɗan kalla hannun yaron Sen... Bukar ɗin daya miƙo masa wai su gaisa amma AA ɗin ya watsar bai bashi nashi ba. Wata irin fusata ce ta zoma Sen.. a maƙoshi, ji yake tamkar ya shaƙo AA ya kashe ya huta. Tunda yaga video ɗin bikin aurensa da ƴar shilarsa yake jin irin wannan fusatar, da ƙyar ya yarda da shawarar abokansa akan ya biyoma AA ɗin ta ƙasa. Su kuma zasu dafa masa baya su ƙulla masa. Shima yaron yaji zafin abinda AA ɗin yay masa naƙin bashi hannu, amma ya basar yace masa “Barka da safiya”. A dake AA ya amsa ciki-ciki ya ɗauke kansa. Sen.. Bukar ma ya dai-dai ta kansa shima yana sakimma AA ɗin murmushi da faɗin, “Fatan kana lafiya. Kayi haƙuri na maka zuwan bazata harda baƙo”. Murmushi AA ya saki shima, ya ce, “No babu damuwa ranka ya daɗe, ai mu ƴan kasuwa ne munfi son ma bazata”. “Hakane kam, dan kuwa nima bussines ɗin ne ya kawoni yanzu. Kaya nake so, masu nauyi kuma. Dan yarona ke son fara irin business ɗinku. Sunansa Afeef. Muna son fitaccen design”. AA dake masa wani irin kallon ƙasan ido yay murmushin gefen baki tamkar baiji sunan yaron ba ma ya ce. “Okay baka da damuwa ranka ya daɗe. Idan kuna da sample zaku iya bamu, idan kuma mune zamu baku zaku bamu kwanaki. Sai dai zaku bamu bayanan dukkan abinda kuke buƙata kayanku suzo da shi.” “Bamu da wani sample mu a hannu gaskiya, sai dai abinda muke buƙata kayan yazo da shi wannan zamu baku.” Kai kawai AA ya jinjina, ya ɗauka kan waya yay kiran AS. Babu jimawa kuwa ya shigo. AA daya maida hankalinsa kan screen na computer ɗinsa ya ce, “Kaje da shi ku ƙarasa duk abinda ya dace”. “Okay boss”. Cewar AS cike da girmamawa. Dan kallon Sen... AA yay fisha cikin girmamawa ya ce, “Mungode ranka ya daɗe”. Murmushin yaƙe Sen... Yay zuciyarsa na ƙuna. A ransa faɗi kaye (zanyi maganinka dan ubaka. Sai na ruguza wannan izzar taka ta inda bakai zato ko tsammani ba. Sai na talautaka har ubanka ma ta yanda zaku dawo bara akan titi). Sen.. Bukar da AS na fita a office ɗin AA ya dakata da aikin da yake yi, shiru yay cikin nazari, yasan yaron Sen... Bukar sosai, dan a yanzu sune matasan ƴan iskan yara dake tashe a birnin Abuja. Dama tunda ya baro gida yau yake jin girarsa ta haggu na rawa, sannan jikinsa na bashi akwai wani abu mai girma kamar na tunkaroshi. Wannan tamkar baiwa ce da ALLAH yay masa, yanada tsarta sosai, shiyyasa ko akan harkar kasuwancin nan bada kowa yake yarda yay huɗɗa ta manyan kuɗi ba. Ama cire duk wancan batun, Sen.. Bukar dama tun asali abokin dabi ne. Daga shi har abokansa sun jima suna masa zagon ƙasa tunda shugaban ƙasa ya bashi mukamin nan. Duk da shi yaƙi shiga sabgarsu su kowane motsinsa na akan idonsu ne. Ga lamarin Maanal daya gitta, dan tsaff sai da yay binciken kaikawon Sen... Ɗin akan Maanal hatta zuwa Giro da hidimomin daya dinga musu. Duk da yana ganin tunda yaji tayi aure zai iya haƙura amma sai bai yarda da wannan zuwan na Sen... Ba. Dole akwai dalilinsa, dole akwai manufa a wannan harƙallar. Shima kuma dole ya bincika kafin lokaci ya ƙure masa... ________★ Sosai Maanal tasha barci, dan bata farka ba sai ɗaya saura. Tafi mintuna goma shiru tana tuna abinda ya faru a daren jiya. Sai faman ɓata fuska take, ranta fal mamakin ƴan iska musamman wasu da zaka gansu ƴan yara da su ƙanana. Yanzu dan ALLAH da wannan azabar har mutum ya iya zuwa ya kai kansa. Eh dole tace azaba, dan ita dai a nata ganin banbancinsa dana farko kaɗan ne, amma Didi Amal tace mata shike nan bazata sake jin wahala ba shiyyasa ta hakura ta sallama. Haka dai taita saƙawa da kwancewarta har taji ana shirin kiran salla sannan ta yunƙura ta miƙe da ƙyar. Duk da ba ciwo taji ba, ba kuma zafi take ji kamar ranar ba kasa zama tai da ƙyau, dan harga ALLAH tana jin babu daɗi a jikinta, ga gaɓɓanta na mata ciwo sosai duk da taimakon daya bata. Wayarta ta ɗauka ta danna screen ɗin ya kawo haske. Miss calls da yawa. Na Oum, na Didi Shahidah, sai na AA da sukafi na kowa yawa. Shi harda ma message. Saƙon ta buɗe, tai shiru tana karantawa fuskarta na canja yanayi zuwa murmushi. _“Barka da tashi My Ever-Bloom. Samun ki a rayuwata yana faranta mini zuciya kullum. Na gode kalma ce ta fatar baki, sannan kuma gama gari a cikin al'umma. Amma nauyinta da kimarta mai daraja ne a garemu Musulmai. Domin idan UBANGIJI ya mana rahama kafin komai godiya muke fara masa, ya kuma horemu da mu godema juna a yayin ƙyautatawa. Nagode Maanal, irin godiyar da bata da adadin kintace, kin canja ni, kin maidani babban mutum a zahiri da baɗinin rayuwa. ALLAH yay miki albarka, ya dawwamar da farin ciki a zuciyarki na har abada. Koda duniya tayi nauyi kasancewar ki a cikin ƙirjina nasa nutsuwata ta tabbata❤️.”_ Wayar ta kife a hankali, sai kuma takai hannu ta share guntun hawayen da suka cika mata idanu. Gaba ɗaya ma sai taji ciwon jikin ya ragu mata. Bata cutama kanta ba ta fita kitchen ta ɗaura magungunan sit bath da Hajiya Shuwa ta bar mata, ta kuma ce ta dinga yi a duk lokacin da haka ta faru har lokacin da komai zai zama jiki. Taji kunya sanda take faɗa matan, amma Hajiya Shuwa ta fuske abunta. Sama ta dawo tai sallar azhar sannan ta koma ta juyi maganin. Sosai tai sit bath sannan tai wanka ta fito ta gyara jikinta da gidan gaba ɗaya tasa ƙamshi ko'ina. Fes da ita sai dai idanun da suka sha kuka na nan da ɗan fushi. Kwalli ta saka sai ya taimaka ya ɓoye kaso mafi yawa. Yau jitai bata jin zuwa gaida Mamy, sai kawai ta wuce sashen Oum. A falon ƙasa ta sameta ita da Nuratu, Oum na duba wani littafin addini Nuratu na kallo. Ko kallon inda Nuratun take batai ba, taje jikin Oum ta kwanta, tare da faɗin, “Oumna ina kwana”. Fuskar Oum da murmushi taja hancinta kaɗan ta ce, “Ina yini dai Baby. Ko duk daɗin barcin ne”. Dariya Maanal tai tana ɓoye kanta a jikin Oum ɗin, dai-dai nan RK ke sallama shi da Nuwaira. Zaune Maanal ta tashi tana musu sannu da zuwa, Nuwaira tazo ta ɗan bata runguma sannan ta zauna suna gaisawa da Oum dake tsokanarta. Maanal kuma RK take gaidawa. Shi ko dake dariya a da gulmar AA a zuciyarsa ya amsa mata da kulawa. A ransa ko faɗi yake, (Wato fitinannen yaron nan bazai bar yarinyar nan ta huta ba) dan kallo ɗaya yayma Maanal ya fahimci taji a jikinta dan idonta ma bai ɓoye kukan data sha ba. Dan ma ta saka kwalli. Da ƙyar Nuratu ta gaishesu, shi kaɗai ya amsa a ransa yana mamakin uwar mi take anan ɗin, Nuwaira kam bama ta nuna tasan da Nuratun ba. Hirarsu suke da Maanal da Oum. Daga baya Maanal da Nuwaira suka tashi suka shiga kitchen, RK Kuma ya fice akan zaije damai kwancema Mamy ɗori ya iso. Binsa Oum tai suka fita tare, aka bar Nuratu ita kaɗai a falon. Aiko sai taji wani irin takaici. Itafa shiyyasa tun farko bata so zaman nan sashen Oum ba, amma mamanta tace dole ta zauna dan su samu damar aiwatar da aikinsu da malam ya basu akan Oum da Maanal har ma da AA da shi kansa Aban. Dole su kame zukatan kowa su samu auren nan nata ayi-ayi sauran rikicin ya biyo baya. Ita ma kuma wani fannin nata son taita ganin AA duk da yanzu yana zarya a sashen Mamyn ma saboda dubata..........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖9️⃣2️⃣ ______________ .......AA daya kasa haƙuri Maanal bata kirashi ba, kuma taƙi ɗaga masa kiransa ƙarfe huɗu ya dawo gidan. Lokacin sun kammala komai suna ƙoƙarin zubawa a kuloli. Nuratu na kwance har yanzu tana kallo. Kawai a bazata AA ɗin ya shigo, sai taji duk ta rikice, ALLAH da tasan zai dawo gida yanzu wanka zataje tayi taci kwalliya abinta. Shi ko kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa. Jin muryar Maanal a kitchen ya sashi sakin murmushi, yana jin daɗin yanda ta ɗaukema Oum kai-kawon girkin nan da take kullum dama abin na damunsa, yayi-yayi kuma ta daina taƙi, sai tace basa son abincin masu aiki, itama bata so ya za'ai ta zauna, dole ta shiga ta girka ai da kanta. Sauran ƴan uwansaa yasha ji suna nuna damuwa akan aikin nan na Oum. Kamar an faɗama Maanal ɗin sai gata ta fito daga kitchen ɗin tana ƴar dariyar maganar Aunty Nuwaira hannunta ɗauke da jug zata kai dining. Turus ta ɗan tsaya tana kallon AA ɗin, kamar yanda shima yake kallonta da sassanyan kallo. Janyewa tai ta kalla agogo, sannan ta sake juyowa ta kallesa tare da faɗin, “Hu'um tseren office ka fara Besty! Ƙarfe huɗu fa”. Shi dariya ma ta bashi wlhy, wai tsere kamar wani ɗan yaro ya gudo daga makaranta. A mamakin Nuratu data kume a wajen sai taga AA ɗin ya saki murmushi mai ƙayatarwa yana nufar Maanal. Babu ko tunawa da tana a wajen, ko wani zai iya ganinsu kawai ya rungumeta ta baya, tare da sauke fuskarsa a kafaɗarta ya sumbaci wuyanta. Ya kai bakinsa kan kunnenta ya gwargwaɗa mata maganar da ita bata ji. Dariya taga sunyi a tare, mamakin ALLAH ya cika mata zuciya, wai AA ne ke dariya haka har haƙoransa a waje. Shin wai mi tsinanniyar yarinyar nan tai masa ne haka, su sunata wahala kullum da zubema malamai kuɗi amma babu wani ci gaba. Jiba abinda suka saka a sashenta daren ranar amma a banza babu abinda aka fasa, sai taji ma hawaye ya cika mata ido. Manaal da idanunta suka hango mata yanda Nuratu ta zuba musu ido cike da gayya bayan sun ajiye Jug ɗin tare da AA ta juyo suna fuskantar juna. Ɗan ɗiɗɗishe tai ta sumbaci haɓarsa, sai kuma ta kashe masa ido ɗaya ta sumbaci lips ɗinsa. Tana ƙoƙarin juyawa da sauri ya riƙota. Ciki-ciki ya ce, “Kinma isa kimin ɗan kaɗan ki gudu”. Dariya Maanal ta sanya tana ƙoƙarin ƙwacewa shiko ya mannata da table ɗin dining ɗin yana ƙoƙarin kai lips ɗinsa kan nata, itako tasa hannu tana karewa tana cigaba da yin dariyar ƙular da Nuratu.... Gyaran murya RK da basu san da shigowarsa ba yayi. Dakatawa AA yay yana wani yin luuu da idanunsa irin na (ɗan yawar nan ya katse min jin daɗi) sai kuma ya ɓata fuska kamar ba shi ba ya juyo yana kallon RK ɗin da harara. Ita dai Maanal samu tai ta zille ta gudu. Shima RK ɗin kallon AA yake cikin ɗage gira da shaƙiyanci. Cikin ƙara balla masa harara AA ya ce, “Kai dai wlhy anyi kawun banza”. “Oh koba Kawun banza ba. Idan ni Kawun banza ne kai miye naka sunan. Ɗan iskan yaro kazo ka matse yarinya a sashen mamanta ko kunya baka ji jarababbe kawai”. Cokali AA ya zara dake dining ɗin ya wulla masa. RK ya kauce yana dariya. Murmusawa shima AA ɗin yay, batare da ya sake cemasa komai ba ya nufi ƙofa. Binsa RK yay suka fice tare... Wani irin takaici, baƙin cikin da ƙunar zuciya Nuratu take ji, a ranta ko ayyanawa take bazata iya cigaba da zaman sashen nan ba. In ba hakaba wataran sai ta bubburmawa Maanal wuƙa wlhy, sai dai itama a kasheta..... _________★ Alhamdullahi Mamy dai an kwance karaya, dan haka Aunty Babba ta wuce. Maman Saheeba kuwa tace sai nan da kwana biyu. Amma a washe gari itama zata bar gidan gidan Hajiya Turai zatai kwana biyun. Auntyn tace ita ta sani kuma wannan ita dai tai wucewarta dan AA da kansa ya saya mata ticket, ya kuma yimata tsaraba mai yawa batare da sanin ko Mamyn ba. Itama sai da aka kaita airport ɗin ne driver ya bata yace inji AA, ya kuma bata wata leda yace inji Maanal. Jitai gaba ɗaya kunya ta ƙara kamata, dama gashi Oum ta cikata da nata abin arziƙin, ta kuma saka Fawzan da Babban Yaya sukai mata. Itako wadda tai wahalar jiyyar ma da faɗa suka rabu wato Mamy, saboda ta sake mata nasiha akan al'amarin Oum dana Maanal Mamyn ta birkice mata, sai kawai ta ƙyaleta ta bita da addu'ar ALLAH ya ganar da ita gaskiya kafin lokaci ya ƙure mata..... A ranar Maman Saheeba bata wuce gidan Hajiya Turai ba sai washe gari. Sai dai kafin ta wuce ɗinne saƙon Sille ya sake iske Mamy a karo na biyu tunda farar safiya. Saƙo ne daya ƙara birkitata fiye ma da wancan karon. Dan ya ce mata yana son su haɗu, sannan kuma yana son kuɗi miliyan goma, idan zata taho address ɗin daya rubuta mata tazo masa da su. Idan ba hakaba kuma shi zaizo gidan Darman da kansa ya amsa, kuma sai ya naƙasta rayuwar AA ta wani ɓangare dan ta tabbatar bada wasa yazo ba. Zufa sosai Mamy keyi a zaune jikinta na rawa. A cikin wannan yanayin Maman Saheeba da taje suka gama ƙulle-ƙullensu da ƴaƴanta dan har Saheeba an bar mata abinda zata dinga sakama babban Yaya a abinci, dan haka itama zata maida hankalinta a sashen Oum tunda taga yanzu a can yake cin abincin ta shigo ta samu Mamy. Sosai ta tsaya tana mata kallon mamaki. Sai kuma ta ce, “Aunty wai lafiyarki kuwa? Sai zufa kike fa ga jikinki na rawa”. Miƙewa Mamy tai, da ƙyar ta iya faɗin, “Ba komai” ta wuce bedroom ɗinta fuuuuu. Maman Saheeba da mamaki ya cikata tai sagade tana kallon ƙofar, sai kuma ta taɓe baki ta gyara zama ta hau cin naman da Mamyn ta saka akan gasa mata zataci. Itafa wlhy irin wannan cin daɗin yasa idan tazo gidan nan bata son tafiya... Kai-kawo Mamy ta shiga yi a cikin bedroom, karo na farko ta bama brain nata damar yin nazari akan wannan mai turo saƙon. Dan ya kamata tasan ma wanene shi? Saboda idan zata auna da hankalinta abinda ya turo matan, ko yake mata barazana da shi ta AJIYE SHI NE A CIKIN DUHUN da babu wani mahaluki a duniya daya taɓa sanin koda labarinsa. Hatta kuwa da kakarta da babanta da suke kwana suke tashi a gida ɗaya lokacin. Kai hatta da Junaid kansa. Sai dai me, kalaman Junaid ɗin ne suka shiga maimaita mata kansu a ƙwaƙwalwa tamkar yanzu ne yake faɗa mata su. _(Lallai kinyi kuskure Kamila, babban kuskure ma kuwa na cin amanata. Amma ki sani kuma ki shirya ɓadda Junaid a wannan duniyar tamkar kin KASHE MACIJI NE BAKI SARE KANSA BA. Domin akwai AJIYA A DUHUn ki a hannuna dake a karan kanki bazaki taɓa iya hasaso minene ba har sai a lokacin dake zaki koma cikin duhun. Maza jeki, jeki da iya gudun da zaki iya ki taka irin taki rawar yanda kike so, ni kuma ZAN DAWO a gaɓar da ƙafafunki da gangar jikinki har ma da zuciyarki da ƙwaƙwalwa suka gaji. Dan kinfi kowa sanin JUNAID baya barin BASHIN GABA)_. Dummm kanta ya yi, zuciyarta na rawa da bugawa. Dan a wancan lokacin sam bata ɗauki kalamansa da wani muhimmanci ba face cika baki da kirarin banza irin na wanda akaci wasa. Amma sai gashi a yau fa kamar kalamansa na neman kama hanyar tabbata ne. Kai ina hakan bazai yiwu ba. Bama zai taɓa yiwuwar ba sai dai idan a cikin yaran Junaid ɗin ne wani ke son mata barazana da son tatsarta kuɗi tunda gashi ya ambata a yanzu. To aiko zata nunama ko wanene ita ɗin ba ƙaramar ƴar wasa bace. To amma kuma minene ya alaƙanta yarinyar nan Maanal da wancan AJIYA A DUHUN nata na tsawon shekaru da babu mahalukin daya sani. Hoton nan dai na Maanal tabbas itace ta bada shi da Maman Saheeba da Hajiya Turai a lokacin da suke son ai musu aiki. Kuma idan bata manta ba a lokacin Hajiya Turai ce ta haɗasu da yaron da zai yi aikin, dan lokacin suna zaune ne a Lagos, sun zo ganin gida ita da mijinta da Nuratu da zata girmi Maanal kaɗan, kasancewar basu san wazasu samu ya musu yanda suke so ba saboda gudun mizai je ya dawo sai Nana tace ta bari ta shawarci Hajiya Turai ɗin dan tasanta itama ƴar ƙunar baƙin wake ce. To bayan sun tattauna da Hajiya Turai ɗin shine tazo wajen bikin da saurayin da zaiyi kusan sa'a da AA a lokacin tace ɗan ƙanin mijinta ne, tace ya zauna wajen su Fawzan har a gama biki dan sun san AA bazai shiga harkar shi ba dan shi babu ruwansa da kowa sai Maanal. Fuskar yaron ce ke son dawo mata, amma ta kasa tunashi da ƙyau. Sai tai tunanin duba hotunan ranar. Closet ɗinta ta nufa, ta buɗe wani box dan tun suna asibiti tai kiran Haule tace ta kulle mata ɗakinta saboda hotunan, Haule najin haka ta gane, sai ta kwaso hotunan daga inda ta ɓoye ta ajiye mata su saman gado sannan ta kulle ɗakin. Koda aka sallamosu suka dawo gidan bata yarda an buɗe ɗakin ba shiyyasa ma ta zaɓi yin jiyyar a nan ƙasa sai jiya ta shigo da kanta da za'ai shata ya kwaso su taɓoye sannan. Shine yanzu ɗin ta ɗakkosu a inda ta ɓoye. Hoton matashin yaron nan ta ciro, ta maida sauran ta ajiye. Bakin gado ta dawo ta zauna ta zuba masa ido, tsahon lokaci zuciyarta na tabbatar mata shine wani sashe na cewa a'a. Da taga dai tana neman rikicewa sai tai kiran Maman Saheeba a waya tace ta shigo ta sameta..........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖9️⃣3️⃣ ______________ .........Babu jimawa Maman Saheeba kuwa ya shigo, kusa da Mamyn ta zauna, ita tama yi zaton wani sirrin zasuyi, amma sai taga Mamyn ta miƙa mata hoto. Amsar hoton tayi tana kallo, tsahon mintuna ta ɗago tana kallon Mamyn. “Aunty waye shi?”. Numfashi Mamy ta fusrzar, sannan ta amshi hoton ta ce, “Zaki iya tuna fuskar yaron nan da Hajiya Turai ta kawo yay mana aiki a shekarun baya?”. Jimmm Maman Saheeba tayi, sai kuma ta ce, “Kai ai shekarun da yawa ne Aunty, kuma kinga yana gama aikinsa ai bamu sake ganinsa ba. Amma muga hoton nan ALLAH kamar shi fa a nan”. Ta jima tana kallon hoton, sai kuma ta ɗago da sauri ya kalla Mamy. “Kai wlhy aunty yaron nan shine. Ina kika samo hotonsa?”. “Kin tabbatar shine?”. “ALLAH babu kokwanto shine, kuma a kira Yaya Turai, ai ita dai bazata manta ba tunda ita ta kawo mana shi. Amma tabbas yaron nan shine Ra'iz”. Sosai zuciyar Mamy ta shiga karkaɗawa, amma sai ta ce, “Bari dai a sake turama Hajiya Turai ɗin mu sake tabbatar wa”. Tai maganar tana ɗaukar waya ta ɗauki hoton, ta WhatsApp ta turama Hajiya Turai, kafin tai kiranta a waya. Sai dai harta tsinke bata ɗaga ba. Sake kira tayi, nan ma ba'a ɗaga ba. Sai ta ajiye wayar yana faɗin, “Maybe bata kusa, nasan in ta gani zata kira”. Maman Saheeba ta ce, “Hakane, amma Aunty miya kawo kuma zancen yaron yanzu? Kodan ance yarinyar nan virgin ce? Ke baƙya ganin duk shiri ne kawai dan su wanke yarinyar. Ko bayan wancan maganar kin sake jin sun tada maganar. Washe gari ma dangin nasu ba tafiya sukai ba kuma basu zauna da Ajwaad ɗin ba kamar yanda suka ce zasuyi”. Kai Mamy dake kallonta ta jinina, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya da faɗin, “Hakane dukkan zancenki Nana. Amma akwai abinda na sani game da mutanen wannan family ɗin dake baki sanshi ba. Dama kai tsaye bazasu zaunar da shi su tambayesa ba a lokacin dake kike zato, sai sun gama munafunce-munafuncensu ke kin ma manta da al'amarin sannan su dawo da shi. Haka kawai kuma nake ji a jikina bincike sukeyi, dan haka dole muma mu dawo da tunanin mu baya akan duk wanda keda alaƙa da aikin nan a wancan karon mu binciko shi musan ina yake a yanzu? Mi yake yi? Musamman shi yaron nan da yay aikin da kuma Doctor. Sai maƙwafciyarmu”. Cikin gamsuwa Maman Saheeba ta ce, “Kuma tabbas hakane, ai sai yanzu na dawo hankalina. Wlhy duk zatona sun bar zancen ne. Amma abin na matuƙar damina a zuciya. Taya za'ace ba'ama yarinyar fyaɗe ba bayan shi Ra'iz ya tabbatar yayi, shiyyasa ma shi Ajwaad ɗin ya ari laifin ya ɗaurama kansa dan a barshi ya aureta”. “Nana zuciyata ta fara bani akwai abinda ya kamata mu sani. Ni na haifi Ajwaad na sanshi nasan halin wannan yaron. Wlhy hatsabibi ne na gaske, babu abinda ya baro na ubansu. Shiyyasa kikaga ina kaffa-kaffa da al'amarinsa, na kuma fito na bayyana masa wacece ni kai tsaye bakamar sauran ba. Idan kin san kalmar bahaushe ta KAMAR KAYI KAKI KA AJIYE to haka ne tsakanin Ajwaad da ubansu, tamkar yayi kakin ne ya ajiye. Da da ban bayyana masa wacece ni ba akan waccan banzar matar shi zai fara ganoni, amma yanzu hakan da nayi kamar na kama lagonsa ne. Tsohon shekaru bai iya faɗa ba, duk kuma wata hanyar da wani zai fahimci ni ɗin wacece hatta da sauran ƴan uwansa cikin tosheta yake. Wannan shine dalilina nayin garkuwa da shi.” Sosai Maman Saheeba ta fahimta, ta kuma gamsu da bayanin Mamy ɗin. A ƙasan ranta kuma tana jinjina mata da jin lallai dole itama ta sake shiri kenan. Dan ƴar uwar tata ba kanwar lasa bace ba ashe. Karma ya zamto tana mata kallon kitse ne ita tana mata na rogo. Daga ƙarshe maimakon ita ta ajiyeta a duhu ita sai ta ajiyeta. To itama dai Mamyn kusan kalar tunanin nata kenan. Dan dariya take a cikin ranta da faɗin (Nana kenan, a zatonki ba kallonki nake ba. Duk wani kai-kawonki a tafin hannuna kike wlhy. A tunaninki amfani kike dani wajen cimma burinki akan ƴaƴana da dukiyarsu. Baki san nice nake amfani dake ba wajen cimma nawa burin. Amma muje zuwa dan irin wannan wasan na birgeni, kuma yana min daɗi) 😂Tofa babbar magana, wannan fa shi ake kira da ainahin AJIYA A DUHU. Wayaga kafin biri yaga ayaba, ayaba ta ganshi🤣. Kumuje zuwa mutanena yanzu ne zamu warware ainahin ma'anar AJIYA A DUHU 😄👍. _______★ A nan kuwa Babban Yaya ne ya samu Oum da batun Ameerah dai yau kai tsaye. Matuƙar mamaki ya kama Oum, farin ciki kuma ya mamayeta har idannunta na tara ƙwalla. Ta kamo hannun Babban Yaya cikin nata. “Fadeel da gaske kake wannan maganar?”. Murmushi Babban Yaya yayi, cike da kulawa ya ce, “Oum girmanki da kimarki ya wuce nazo miki da kalmar wasa a wannan bigiren. Nace zan rabu da Saheeba kun hanani ke da Abah, ni kuma na gaji da banzayen halayen yarinyar gaba ɗaya. Shiyyasa naga kawai gara nayi irin na Fawzan na ƙara auren. Ɗari bisa ɗari kuma na gamsu da tarbiyyar Ameerah, na kuma tabbatar zan samu yanda nake so. Hakan kuma dazan ma Saheeba shine zai zama hukuncin laifinta har naji na huce”. “Alhamdullahi, Fadeel ALLAH yay maka albarka. Na kuma baka goyon baya ɗari bisa ɗari.” “Nagode Oum, ALLAH ya ƙara miki lafiya da nisan kwana mai albarka. ALLAH ya cigaba da tsare mana ke, ALLAH ya cigaba da baibayeki da farin ciki da kwanciyar hankali”. “Tare daku baki ɗaya Fadeel. ALLAH yay muku albarka. Yasa kuma ace gwara da aikai. Yanda Auta ya samu farin ciki haka nake fatan kuma na ganku kai da Fawzan”. Ƴar dariya Babban Yaya yayi, ya ce, “A Oum autanki kam sai dai muce Alhamdullah. Kina ganin wata ƙiba ma da yake yi sati uku kacal da tarewa. Idan naga yana murmushi sai naita kallonsa”. Dariya itama Oum ɗin tayi. Ta ce, “Kaima haka nake fatan naita ganin wannan murmushin a fuskarka. Dan haka ma ni bazan iya haƙuri ba yanzu zan je na samu Hajiya Shuwa. Idan zai yiwu ma wlhy a haɗe dana Fawzan nan da sati biyu kenan. Dama itama Hajiya Shuwan ta sameni akan Maimoon, Ameer ya sameta da batun yana son Maimoon kasan abin nasa ya fara sauka kwana biyu jiya ma matar ta tafi gida wai tayi yaji”. “Ikon ALLAH, Oum dama shi komai lokaci ne, musamman irin wannan sihirce-sihircen. Haba shiyasa naga kwana biyu ya koma fita aiki, sannan zai tsaya mu gaisa yana wani duƙe-duƙen kai. Dan jiya da magrib har gidan nan ya shigo neman Fawzan, to kin san ɗan naki akwai sauƙin kai amma idan ya birkice yafi kowa daru. Sai cayayma maigadi yace baya nan”. Dariya Oum tai da faɗin, “Oh ni Faɗima wato Fawzan ko. To ka barni da shi zan zauna da shi, ai tunda ya dawo sai yay haƙuri komai ya wuce tunda mun san bayin kasan bane ba”. “Ato ya dai kamata Oum”.... ★Kamar yanda Oum ta faɗa batai ƙasa a gwiwa ba ta samu Hajiya Shuwa da batun babban Yaya. Ya subahannallah farin cikin da baiwar ALLAHr nan ta nuna har sai da Oum tai mamaki. A take tace wlhy ko yau Fadeel ya shirya ta yarda a aɗaura masa aure da Ameera koda Ameera bata so kuwa. Balle dama taga kwana biyu wani mutunci na yawaita tsakanin Ameera da babban Yayan har tanata mamaki, ashe ashe sun san mi suke ƙullawa... Shima Aba a ranar Oum ta bashi labari a waya. A mamakinta shima farin ciki sosai ya nuna. Harda tabbatar mata washe gari zai dawo gida. Dariya ma abin ya dinga bama Oum, dan ta fahimci Gadanganta ya huce kenan. Yajin da akai musu kuma ya ƙare. Aiko ya ƙare ɗin, dan washe gari sai ga Abah ya dawo. AA ne yaje ya ɗakkosa a airport shi da RK da sassafe. Ita Oum ta zata Abah ya sanarma Mamy, tunda da dare sukai maganar washe gari kuma sai gashi itama bata san da safen zai dawo haka ba sosai. Dan bama tasan AA yaje ɗaukarsa ba shi da RK, tunda RK banan yake kwana ba yana gidansa dake cikin asibitinsa shi da matarsa, sai dai kusan kullum Nuwaira na nan gidan saboda laulayi. AA kuwa yau weekend batai tsammanin ganin idonsa da wuri ba ma sam... A lokacin da su AA ke shigowa da Abah gidan ne kuma su Mamy ke can suna tattaunawa ita da Maman Saheeba akan batun hoton Ra'iz, suna kuma tsumayen kiran Hajiya Turai amma shiru.. sai kawai ga Saheeba kamar an jehota tana sanar musu ga Abah can ya dawo. Mamaki ya kama Mamy da Nana, amma sai Mamyn batace komai ba tunda tasan mike faruwa tsakaninta da Aban. Koda Maman Saheeba ta ɗakko zancen ma sai ta basar ta hanyar ɗaukar waya tana faɗin, “Bara dai na sake kiran Hajiya Turai ko ina ta shiga haka”..... __________★ Duk kiran da Mamy kema Hajiya Turai akan idonta ne. Dan lokacin tana jikin Sille kwance ya gama Sille ta tas. Yau kwanansa biyu a gidan tare da ita, shiyyasa dama take son tura Nuratu gidan su Mamyn dan tafi samun isashen lokaci da Sillen. Cikin ɗan yamutse fuska ta nunama Sille fuskar wayar da faɗin, “Mamarka fa ta daman. Kuma bazan ɗauka ba dan nasan sotake tace Nuratu zata dawo gida. Ni kuma bana buƙatar haka ban gaji da kai ba”. Cike da iskanci Sille yay dariya da faɗin, “Ke dama kina gajiya dani ne. Shekaru sunja amma kina ƙara kangarewa. Ya kamata ki ɗaga kiji minene, kin san daren jiya na tura mata saƙo na san kuma ya risketa zuwa yanzu. A nawa hasashen ta zurfafa tunani akan hotunan dana fara tura mata, tana son sanin miya alaƙanta hoton matar ɗanta da sauran hotunan, anan ne zata fara tuna wanene ɗayan hoton shima”. “Eh kuma fa hakane, ai bari ma na duba WhatsApp dan ɗazu kuwa naga kamar ta tura min hoto kafin kiran nan ma”. WhatsApp ɗin kuwa ta shiga, sai ko ga hoton Ra'iz. Da mamaki ta ce, “Baby na kaga kuwa hasashenka yayi dai-dai. Wai ya akai kasan matar nan haka da yawa ne?”. Mintsini mai zafin gaske ya bata cike da baƙar mugunta har sai da tai ƙara. Kafin cikin raɗa ya ce, “Karki manta ita ɗin UWATA ce, sannan irin tunaninta gareni ki kula ita ɗin SURUKARKI ce”. Hajiya Turai tasan halinsa sarai dan haka tai murmushin yaƙe kawai. Shi kuma ya ɗauka taba yana kunnawa da faɗin, “Kice mata shine wanda take tunanin, idan ta tambayeki yana ina yanzu kice ta tambayi ɗanta Ajwaad”. Cike da mamaki ta ce, “Amma Baby miyasa zanyi hakan?”. “Saboda haka na tsara. Dan komai nawa ni ina binsa daki-daki ne kema kin sani”. Kanta ta jinjina masa da faɗin, “Kayi haƙuri na fahimta”. Banza ya mata, sai kuma ya ɗaura mata tabar a baki, dole ta zuƙa. Aiko tari ya sarƙeta dan bata iya sha ba. Sai idan yaso mata mugunta ne yake sakata sha dole ko ƙwayoyi. Aiko tari take sosai idannunta sunyi jazur. Yako shiga balbala dariya cike da tsantsar mugunta har kifawa yake..........✍️ 😮‍💨Kai jama'a ALLAH ya rabamu da faɗuwar baƙar tasa. Ga kuma wata sabuwa. Shin miya alaƙanta Hajiya Turai da Sille kuma🤣 AJIYA A DUHUn fa kenan kumuje dai zuwa🏃🏃🏃🏃. *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖9️⃣4️⃣ ______________ ........Maanal na kitchen AA ya shigo, dan tunda taji yana waya da RK daya kirashi yazo su ɗaukesa Abah a airport ta martaye daga barcin da take yi tunda taji Oum ma bata sani ba. Sosai AA da ƙamshi ya jawoshi kitchen ɗin mamaki ya kamashi, dan yasan shi dai barci ya barta tanayi. Hankalinta yayi nisa a harhaɗa abincin yay gyaran murya, juyowa tai da sauri, sai kuma ta sauke ajiyar numfashi a shagwaɓe ta ce, “ALLAH ka bani tsoro Besty”. Murmushi yayi, sai kuma ya ƙaraso inda take ya rungumeta ta baya kasancewar ta juya tana kwashe Irish ɗin dake cikin air pryer. Wuyanta ya sumbata tare da raɗa mata, “I'm sorry. Yaushe kika tashi ke da na bari kina barci?”. Ɗayan hannunta takai ta shafo fuskarsa. “Tunda Uncle R ya kiraka na farka, kawai nayi shiru ne harka fita. Yaya Aban?”. “Abanki na lafiya gashi can a sashensa. Yanzu wannan kayan daɗin duk na waye?”. “Na Abah mana”. Ta faɗa tana juyowa bayan ta zuba wani dankalin. “Mu baza'a sammana ba kenan?”. Kaɗan taja hancinsa da faɗin, “Ko ɗan guntu bazaku samu ba”. “Idan an hanamu wannan ai Ni sai a bani nawa abincin”. “Oh kana ma da wani abinci kenan?”. “Eh mana”. Ya faɗa yana kashe mata ido ɗaya. Sam bata wani fahimci ina ya dosa ba, dan haka ta ɗan taɓe baki. “To maza kuwa kaje kaci, dan nan babu kasonka”. Fahimtar bata gane ina ya dosa ba ya sakashi sakin murmushi. Cike da son ƙureta ya duƙo ya gwargwaɗa mata a kunne. Ai babu shiri ta kallesa, sai kuma ta shiga turashi cike da bori tana faɗin, “ALLAH ya shiryeka bar kitchen ɗin nan”. Dariya ya shiga yi, itako ta dage sai turashi take. Gocewa yay kawai ya ɗane kan kitchen cabinets. Ta tsaya tana hararsa hannayenta riƙe da ƙugu. Fuskarsa da murmushi ya haɗe hannayensa waje guda. “Yi haƙuri giwar mata, amaryar AA Darma”. Dariya ya bata sosai, ta murmusa tana juyawa kan aikinta. Sai kuma ta matsa inda coffee maker yake ta haɗa komai a ciki. Ta sake dawowa tana duba abubuwanta dake kan wuta. AA kuma ya zaro wayarsa datai ƙaramin vibration alamar shigowar saƙo yana dubawa. Coffee ɗin da yay ta juye dama kofi ɗaya ta saka ta ɗako tazo gabansa da shi. Miƙa masa tai, ya amsa tare da sumbatar gefen fuskarta ya ce, “Thanks you, ALLAH yay miki albarka”. “Amin ya rabbi tare da kai”. Itama ta faɗa tana komawa kan aikinta. Zuwa can yace. “Besty zo kiga”. Spoon ɗin hannunta ta ajiye ta nufoshi. Kamota yay ya saka a tsakiyar ƙafafunsa kansa na a kafaɗarta ya shiga nuna mata abu a waya. “Woow ammafa sunyi ƙyau, amma da za'a ɗan ƙara wani abu da zasu fi haka ƙyau. Waya zana?”. “Da gaske?”. “ALLAH kuwa. Musamman ma hannun, ni sai yay min girma gaskiya. ” “Prof... Ne ya turosu yanzu ta email. Wai ko zamu iya fitar da su amma fa gaggawa ake so kada su wuce 10 days”. “Da gudu ma za'a iya, musamman idan akwai kayayyakin da agogon ke buƙata a company”. “Eh to sai dai mu bincika. Mizan tayaki da shi? Faka-faka ki duba zanen zuwa gobe dole muje company”. “Amma gobe fa muna da baƙi ka manta”. Gannin yayi jimmm alamar tunani ta ce, “Amma idan dan tattaunawa ne ai nake ga babu damuwa tunda dama wanda ya kamata a tattauna da su ɗin ne sai kawai ayi meeting ɗin anan. Kaga Monday sai kowa ya tashi da shirin aiki”. “Woww kuma haka ne. Thanks you. Mizan taya ki?”. “Yi zamanka nama kammala, kashewane kawai. Sai dai zaka taimaka ka kaima Oum kaga banyi wanka ba”. “Na zama ɗan aike kenan?”. “Eh mana, bakaji wani mawaƙi yace ku bayin mata bane ba”. “Ya muka iya mun amsa da hannu biyu. Dan jin daɗin duniyar sai da ku Besty”. Dariya sosai Maanal ta sanya. Da taimakonsa ta zuba komai a kuloli da bowl masu ƙyau da duk ta fiddo a kwalayensu. Suka jera su a basket har uku sannan. Cike da tsokana tace, “Kafa bi a hankali Besty, dan in ka zubar sai kasha bulala”. Dariya yayi yana fita ta back door, itama tana dariyar ta shiga fita da nasu saman dining, Dan yau anan sashensu zasu yini itama Oum a barta ta huta da Abah. Babu daɗewa AA ya dawo ya ɗauka ɗayan basket ɗin ya sake fita. Ita kuma ta hau gyaran kitchen ɗin. Koda ya dawo ya sanar mata Aban da Oum nata sanya mata albarka murmushi tayi, shima aikin gyaran kitchen ɗin ya fara tayata, suka gama suka dawo falo har can sama da bedroom ɗin da suka kwana duk da ba wani datti bane sai da suka gyara komai tsaff suka saka turaren wuta da air freshener sannan suka shiga wanka a tare. Sun jima a bayin dan sai da ya ɗan mommore sannan suka fito. A tare suka taimakawa juna wajen shiri abin sha'awa. Tsaf suka fito abinsu suna uban ƙamshi. Ƙananun kaya ne a cikinsa da sukai masa ƙyau sosai. Ita kuma sai ta saka Abaya da itama tai mata ƙyan. Fita sukai a sashen gaba ɗaya zuwa sashen Abah. Acan suka samu Oum da babban Yaya, Yaya F dai tasan yana can yana barci yau weekend. Abah ya kasa ɗauke idanunsa a kansu, hakama fuskarta a washe take da murmushi. Cike da girmamawa suka zauna a ƙasa, Manaal kusa da Abah AA kusa da Oum. Babban Yaya da shima ke kallonsu da murmushi ya ce, “Aunta na Auta”. Hannu Maanal tasa ta ɓoye fuskarta. Aba dake ƴar dariya ya ce, “Auta kam na auta.” Shima dai AA murmushin yake yi. Cikin haɗa baki shi da Maanal ɗin suka shiga gaida Abah. Ya amsa musu da kulawa yana sanya ma Maanal albarka da hidima. Hakama Oum ta sanya mata albarka. Shima Babban Yaya albarkar ya saka mata. AA ya ce, “Abah tare fa mukayi, naga sai ita jaɗai ake sakama albarkar”. Cikin waro ido Maanal ta ce, “ALLAH Besty kaji tsoron ALLAH. Kana zaune kana surutu dai nayi”. “Oh rinto ma zaki min kenan?”. “Kai ne dai zaka min rinto”. Dariya sosai Abah da Babban Yaya da Oum ke musu. Babban Yaya yace, “Ni dai na yarda Lilly na kawai tayi, Aunta gaskiya bama son runto”. Maanal ta ce, “Yauwa Yaya ai dama kasan halinsa dai”. Abah ya ce, “Nima ina bayanki Auta. Shi dama girkin ba wani ya iya bane”. Oum dake dariya ta ce, “Ato bara dai na shigarma Auta nima. Idan ta gaskiya za'ai shi fa ma ya koya mata girkin nan”. “To Oum tuna musu dai idan sun manta. Amma ba komai yau an min 1-0 next”.... __________★ Abin duniya ya ishi Mamy ƙwarai da gaske, tana son zuwa wajen Abah tana jin tsoro. Bata son kuma taje taga Oum tare da shi. Gashi ta ƙagu da jiran kiran Hajiya Turai amma shiru kake ji. Maman Saheeba na son wucewa itama tana tsoron ko Hajiya Turai bata gida ne. Amma dai haka ta shirya dan bata kuma ƙaunar su haɗu da Abah. Ta nema Saheeba ta kaita ita ko ta murje ido tace aa wlhy ba inda zata Babban Yaya yace ko nan da gate taje zai bata mamaki. Wannan abu ya matuƙar bama Nana mamaki kuma ya ƙona mata zuciya. Haka ta tattara ta fito, kasa zuwa yima Oum sallama tayi, Nuratu dai ta rakata bakin gate itama ta dawo, dan hakankalinta a tashe yake ita duk yau bata ga AA ba a gidan. Maman Saheeba ta fito daga gidan Darma idanunta suka sauka akan Babban Yaya da Ameerah a mota zasu shiga gidan Hajiya Shuwa da alama daga wani wajen suke. Sai AA da Maanal su kuma zasu fita amma sun tsaya suna magana da su Babban Yayan. Maanal ce ke driving ɗin. Mamaki ne ya kamata, tai tsaye tana kallon ikon ALLAH har Babban Yaya ya gama shigewa da motar. Manaal na ƙoƙarin wucewa itama ta hango Maman Saheeba ɗin. Sai ta ɗan yo reverse kaɗan. AA ya ɗago zai yi magana yaga ta tsaya saitin Maman su Nuratu. Cikin girmamawa Maanal tace, “Aunty zaki fita ne?”. Kamar Maman Saheeba bazata amsa ba sai kuma tace eh. “Bismillah ki shigo sai mu saukeki”. Sosai abin ya bama AA haushi, amma yay banza bai tanka musu ba har Maman Saheeba ɗin ta shiga suka wuce. Sai da suka bar street ɗin sannan Maanal ta tambayeta ina zasu kaita. Cike da isa ta gaya mata. Takaici ya ƙara kama AA, dan sam tafiyar tasu ba ɗaya bace ba. Maanal kuwa ko'a jikinta duk da taga ya canja fuska. Haka ta nufi gidan su Nuratu duk da tana tunanin ba lallai ta gane ba. Amma cikin ikon ALLAH sai gashi ta gane. Abin tsautsayi Maanal na gama tsayawa a gate ɗin dan batai niyyar shiga ba sai ga Sille ta fito a gidan da waya a kunnensa, saƙo wani yaronsa ya kawo masa yake son amsa ya koma. Tsaiii AA yay yana binsa da kallo, hakama Maanal. Itama kanta Mamman Saheeba kallon nasa take tana mamakin ina kuma Hajiya Turai ɗin ta samo wannan da kallo ɗaya zaka fahimci taƙadari ne. Shi ko Sille baiga su AA ba, sakamako bai san motar ba dan ƙaramar motar Maanal ce ta cikin lefe, gata tinted glass, sune kawai suke iya ganinsa. Hankalinsa kwance yay wucewarsa da tunanin tarkacen Nuratu ne tunda ya santa da masifar jaye-jaye. Bai lura da Maman Saheeba ba harta shige, dan bata side ɗin da take yake ba. Motar Maanal tama key ta bar ƙofar gidan, suka sake wuce Sille dake tsaye tare da yaronsa suna magana. Sai AA cayay “Niko kamar nasan fuskar nan fa Besty”. Kallonsa Maanal ta ɗanyi, sai kuma ta maida hankali a titi. “Kai Besty a ina kuma? Kana ganin mutum da zubin ƴan jagaliya. Ni wlhy tsoro ma ya bani jibeshi kamar irin baƙaƙen ƴan iskan amerikawan nan. Jiki duk tatu.” “Oh kallonsa ma kika tsaya yi kenan?”. Yanda yay maganar a tunzure ya saka Maanal yin murmushi. Cikin kwantar da murya ta ce, “Rufa min asiri mizan kalla a wannan ƙazamin, nida nake da namijin gaske gashi kuma a gefena. Kawai dai suffarsa batai kama da mutanen kirki ba, sai nake ta tunanin mima ya kaisa gidan ma”. Baki AA ya ɗan taɓe kamar bazai tanka ba, sai zuwa can yace, “Ai ƴar kasuwa ce matar, duk kuma wani tarkace ƙya sameshi a wajen sayen kayanta tunda tana tare da ƴan siyasa.” “To ALLAH ya ƙyauta. Mu dawo batun su Babban Yaya. Besty anya babu wani abu tsakanin Babban Yaya da Ameerah”. Yanzu kam kallonta AA yay sosai, sai kuma ya murmusa da faɗin, “Da nayi farin ciki ƙwarai da gaske ALLAH Besty.” “To ALLAH ya tabbatar mana da alkairi, dan gaskiya nima zanyi farin ciki. Shike nan kaga gida ya zama kowa da mata biyu”. Dai-dai sun iso inda zasu tana ƙoƙarin parking tai maganar. Murmushi AA yay tare da kwantowa jikin kafaɗarta, sai kuma a hankali ya kamo hannunta cikin nashi. Ƙasa-ƙasa ya ce, “Ni dai na auri Autar mata.” “Uhm daɗin bakin maza”. “Oh mu maza har daɗin baki ne damu?”. “Sosai ma, musamman a wajen ƙara aure baku da gaskiya”. Dariya ta bashi, amma baiyi ba ya murmusa kawai. Daga haka suka fito fuskar Sille na masa kai-kawo cikin idanunsa har yanzu. So yake ya tuna shi amma har yanzu ya kasa haskowa. Abinda kawai ya sani ba'a Abujan nan ya sanshi ba, sanin kuma ba yanzu ne yay masa ba shekarun baya ne..........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖9️⃣5️⃣ ______________ .........Haushi sosai Hajiya Turai taji da ganin Maman Saheeba, amma sai ta dake suka gaisa, koda Maman Saheeba ke sanar mata ai sunata kiranta a waya tun ɗazun sai tace ta fita ne yanzu take dawowa. Akwai kayan ta da suka ɓace a airport shine sukaje ake nema ga mai kayan ma har yazo amsa yanzu. Dan tasha jinin jikinta tabbas sunga Sille. Aiko sai cewa Maman Saheeba tai, “Ko shine ma mukaga yana fita yanzu”. “A eh kwarai shine! Shine!”. “Kai wanan kasuwanci naku kuna ƙoƙarin, ai ni wannan mutumin sai ya firgitani”. Cikin murmushin yaƙe Hajiya Turai tace, “To mu da muka kasa a siya ina ruwanmu da s....” maganar ta maƙale saboda shigowar Sille.. Daburcewa Hajiya Turai tayi, haka shima sai ya tsaya turus yana kallon Maman Saheeba, dan ya santa, kai kaf dangin Mamy ma ya sani saboda a biye yake da komai nata tsahon shekaru, sune dai basu sanshi ba sai ita Hajiya Turan. Cikin in ina Hajiya Turai ta ce, “Yauwa ka dawo? Dama nace ko na ɗakko maka wanda ke hannuna kafin wancan su fito?”. Shiru Sille yay bai tanka ba, sai ma zaune da ya kai a cikin kujerar. Hajiya Turai data fahimci mi yake nufi saita kalla Maman Saheeba. “Nana muje ciki, idan na ƙarasa da shi zan shigo”. Miƙewa kuwa tayi zaram dan dama harga ALLAH a tsorace take ita kam. Yo kallon idanun Sille kawai abin firgitarwa ne. Tana shigewa Hajiya Turai ta tabbatar ta shige ɗin ta dawo kusa da shi cike da tashin hankali da lallashi ta ce, “Dan ALLAH kayi haƙuri Baby, wlhy ban san zata zo ba, nima ganinta kawai nai yanzu”. Batare da ko kallon Hajiya Turai ɗin yayi ba a daƙile ya ce, “Ki sallameta yanzu nan ta koma inda ta fito kota kama gabanta, dan ban gama abinda nake ba bazan tafi saboda wata banza ba matsalarku ce”. Ya miƙe abinsa ya wuce bedroom ɗinta yana wani tafiyar rangajin iskanci. Ji Hajiya Turai tai kamar ta sanya kuka, amma tasan dole ne ta sallami Nana kamar yanda ya faɗa dan bazai bar gidan ba kuwa. Mamman Saheeba na a ɗakin da take sauka idan tazo Hajiya Turai ta sameta. Fuskarta ta ƙawata da murmushi tana kallonta. Sai kuma ta ce, “Kinga ko kinzo a dai-dai, dama akwai ticket dana saya yau zan je Kano sai batun kayan nan ya shigo, dole zan canja na tafi Lagos anjima dan wai kayan nacan. Ga mutumin nan bai da kirki ya bani daga yau ne zuwa gobe kayansa kawai ko kuɗinsa. Ni kuma na cinye kuɗin, tare ma zamuje lagos ɗin da shi”. Cikin rashin damuwa Maman Saheeba tace, “Ai kije Lagos ɗinki kawai ki dawo zan zauna abina. Saina kira Nuratu ta tayani zama”. Hajiya Turai ta danne takaicinta ta ce, “Ai bazai yiwu ba Nana, mutumin nan yaje yay bi baya ko yasa azo a cutar daku, shiyyasa ma naji daɗin da Nuratu bata gidan. Baya ji fa cikin Abujan nan kaf tsoransa ake ji, nima tsautsayi wani ministar ne ya taɓa aikosa amsar kaya a wajena shine sanadin da ya fara sayen kayan shima ga shi nan ya zame min alaƙaƙai. Dan haka faka-faka shirya mu wuce airport nima daga can zan wuce.” Sam ba haka Maman Saheeba taso ba, gashi bata son komawa gidan Darma tana kunyar haɗuwa da Abah. Ga al'amarin nan na babban Yaya da ƴar Hajiya Shuwa ya tsaya mata a rai. Ƙin gaisheta da AA yayi, har ma ta shiga motar ta fita bai nuna ya santa ba nan ma ya zafeta. Haka dai ta shirya badan taso ba Hajiya Turai ta ɗauketa suka tafi airport. Suna isowa sai ga kiran Mamy ya sake shigowa Hajiya Turai, kaɗan ya rage taja tsaki ALLAH dai ya kiyaye. Koda ta ɗaga cike da wayancewa taba Mamy haƙuri da tsarata kamar yanda ta tsara Maman Saheeba. Mamy tace “Ba komai, dama wani hoto na tura miki ta WhatsApp dan ALLAH idan ban takuraki ba ɗan duba ki gani yanzu”. Babu musu Hajiya Turai ta shiga WhatsApp ɗin kuwa tana faɗin, “Haba ba komai ai” dai-dai tana buɗe hoton dan bata yanke kiran ba. Ta ce, “Wannan ai Ra'iz ne. Badai zancen first night ɗin yaran nan bane ke neman tada ƙura?”. Mamy da abin ya daketa cikin dauriya ta ce, “Shine kuwa Hajiya Turai, ina son nasan gaskiya kafin Aban su Ajwaad yace zai yi bincike. Kinga dai ƴan uwansa duk suna a gidan nan maganar nan ta fito, wannan shirun nasu kuma na tabbatar akwai wata a ƙasa. Ina Ra'iz yanzu? Ina son naji shin da gaske baima yarinyar nan komai ba a wacan ranar amma ya amsa mana yayi.” “Tab babbar magana. A yanzu Ban san ina Ra'iz yake ba gaskiya. Dan tun bayan aikin nan wata alaƙa bata sake haɗamu ba”. Ji Mamy tai kamar ta zandara ihu. Amma ta danne da ƙyau zuciyarta sai bugawa take. Cike da damuwa ta ce, “Lallai akwai matsala Momyn Nuratu”. “Amma ni sai nake ganin abun duk mai sauƙi ne. Ki zauna da shi Ajwaad ɗin mana. Nima kuma zan bincika inda Ra'iz ɗin yake” “Zama da Ajwaad ba shine mafita ba shiyyasa ma ban masa ko zancen ba har yanzu. Kin san wannan matsiyacin yaron Rafeeq ne ya baza musu zancen yarinyar virgin ce. Ina da tabbacin koshi Ajwaad ɗin babu wanda yay maganar da shi akan hakan har yanzu, alamun akwai abinda suke shiryawa. Nasan su wanene wannan family ɗin Turai, wlhy akwai damuwa. Gashi na saka a bincika min Dr Tofa ɗin ma har yanzu babu wani bayani. Idan nace kuma zanje Kanon da kaina a yanzu akwai damuwa”. “In dai dan wannan ne ki kwantar da hankalinki, daga yau zuwa gobe zansa a bincika mana Dr Tofa ɗin shima”. Mamy ta ɗan ji sanyi a ranta, amma zuciyarta a birkice take fiye da farko. Tana ajiye wayar zufa na keto mata. Gadai Hajiya Turai ta tabbatar mata yaron da suka saka aiki ne akan Maanal. To miya haɗashi da Junaid kuma? Sannan Junaid bai san da zaman jaririn can ba taya za'ai hotunan su su kasance tare a wajen mutum ɗaya? Yau ta shiga uku mike shirin faruwa da ita? Ga batun Abah na ɗaga mata hankali. Kada dai ace abubuwa ne zasu rikice mata a gaɓar da take ganin nasararta zata fara, ƴaƴanta da komai nasu zai dawo tafin hannunta. Mijinta da take ganin ta gama nasarar wawashe zuciyarsa gaba ɗaya zuwa yanzu amma zai suɓuce mata. Wai wanene wannan mai tura mata saƙon? Wanene shi? Miyyasa zai shigo duniyar ta a gaɓar samun nasararta da ribantuwa da wahalhalunta da haƙuri da juriya da tai na shekaru aru-aru. Mafita ɗaya gareta a yanzu ta sanin wanene shi? T kuma yarda su gana kamar yanda ya buƙata, to amma idan ta amince lokaci guda zai ɗauketa shashasha. Bari ta ɗan latsashi na wani lokaci kamar bata damu ba. Kuɗi kuma bai isa ya ci su ba.... __________★ Gaba ɗaya Yazeed baya gane komai a yanzu sai umarnin mahaifin matarsa. Ji yake ko wuta yace ya faɗa zai faɗa domin faranta masa. Nazeefa kuwa wata irin soyayya yake nuna mata kamar ya cinyeta. Balle da maganar cikin jikinta ta bayyana. Ita kanta sai abinda tace yayi yake yi. Dan haka take mugun tatsarsa kuɗaɗe, tana daga kwance shike mata tausa shine fita sayo mata abinci, shine mata wanki kai komai daya kamata tama kanta, tai masa matsayin matar gida yanzu shine keyi. Ga itama Sabuwa na zuba nata capacity ɗin a gefe. Sai da suka tabbatar sun gama samunsa a yanda suke so, sannan suka dawo gida Nigeria. Dawowar tasu kuma ta kasance rana ɗaya da dawowar su Ammie da Daddy suma. Sosai Daddy ya zubama Yazeed ido, yaron ya rame yayi duhu daka ganshi kasan baya a cikin hayyacinsa. Ji Ammie tai ƙwalla sun cika mata ido, dan a wannan dambarwar dai shi Yazeed shi aka cuta wlhy, tana ƙaunar Yazeed tana tausayinsa, dan yaron ya taka rawar gani a rayuwarsu suma, kuma in sha ALLAHU ta ɗauki aniyar taimaka masa a wannan gaɓar, bazata so cigaba da ganinsa a wannan yanayin ba. Daddy kam bazaka taɓa fuskantar komai a fuskarsa ba. Amma shima al'amarin Yazeed ɗin na matuƙar damunsa a zuciya. Sai dai ya zuba ido ne dan Hajiya Yaya taji a jikinta. Sai dai tabbas bazai yafe mata ba, dan ta cutar masa da yaro. Ɗansa babba abin sonsa, mai hankali da nutsuwa ga jin ƙan iyaye ta zama sanadin da aka maida masa shi ƙarƙashin ikon mace.. Yaya Yazeed kam sai yaji kunyar ganin Daddy da Ammie, dan ko wancan dawowar har suka sake barin ƙasar bai bari sun haɗu ba duk da gida ɗaya suke kwana suke tashi. A mamakin Nazeefa sai taga yaje yana gaida Daddyn da Ammie. Wannan abu ya mata zafi, fuuu ta wuce sashensu batare data gaida Daddyn ba ita balle ma Ammie da bata saka rai ba. Sai ko Yazeed ya zabura ya biyota yana kira kamar zai faɗi dan sauri. Hawaye suka zuboma Ammie. Daddy kam sai ya ma kauda kansa gefe. Ƙannensa da komai ka faruwa akan idonsu cike da baƙin ciki suka nufi sashen su suka sanar ma Hajiya Yaya. Aiko sai gata ta fito kamar zata tashi sama. Kai tsaye sashen Yazeed ɗin ta nufa, tana tura ƙofar kuwa ta buɗe. Ta wani bugata da iya ƙarfinta ta shiga falon. Turus taja ta tsaya hakama ƴaƴanta da suka biyota ganin Yazeed durƙushe a ƙasa yayi kneeling yana bama Nazeefa da tai wani zaman ƙasaita haƙuri. Itako sai danna waya take tana taunar cingum kamar ma bata san da shi ba. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un. Sarai Nazeefa taji shigowarsu amma sai ta watsar da su kamar bataji ba, sai ma cike da rashin mutunci ta dakama Yazeed tsawa. “Dalla malam yimin shiru, shashasha kawai dabai san ciwon kansa ba. Kai ko kunya bakaji ba zagam-zagam ka tafi gaida ubanka sai kace wani uban kirki. To wlhy ka jama kanka yau sai kaji a jikinka a gidan nan. Dalla tashi ka mana shara kana ganin waje duk datti”. Jiki Yazeed har rawa yake ya miƙe kuwa. Ko kallon su Hajiya Yaya baiyi ba ya nufi inda suke ajiye kayan shara ya ɗibo...........✍️ Tofa Hajiya Yaya da alama anzo dai-dai wajen🥱. *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖9️⃣6️⃣ ______________ .......Muryar Hajiya Yaya na rawa ta ce, “Yazeed!”. Yanzun ma baiko kalleta ba sharar sa ya fara ma. Ta ƙara kiranshi cikin tsawa. Ko gezau baiyi ba. Dariya Nazeefa ta shiga tuntsurawa. Sai kuma ta wani miƙe cike da gadara da raini taje gaban Hajiya Yaya ta tsaya, kallon sama da ƙasa tai mata fuskarta da murmushin ƙularwa ta ce,. “Kima daina wahal da kanki, dan in dutsen arfa zaki hau kiyi ihu bazai taɓa ya jiki ba. Dan yanzu shi ɗin ba naki bane, nawa ne nan, dama kin rainar min shine Hajiya Sadiyya”. Ta kira ainahin sunan Hajiya Yaya. Hannu Hajiya Yaya data gama kaiwa wuya ta ɗaga ta ɗauke fuskar Nazeefa da mari. Marin daya farfaɗo da sauran ƴaƴanta da sukai sumar tsaye tunda akace yayansu yay shara. Gigitaccen ihu Nazeefa ta fasa da kiran sunan Yazeed. Bawan ALLAH tamkar ƙyaftawar ido har yazo inda suke. Yay ƙoƙarin kama Nazeefa yana tambayar miya sameta? Hankaɗashi tai baya ya tafi taga-taga zai faɗi saboda a bazata ta turesan. Ta kallesa hannunta riƙe da kuncinta ɗayan ta nuna Hajiya Yaya da yatsarta manuniya. “Wannan jakar ce ta mareni, kuma wlhy idan baka rama min ba sai na tafi gidanmu yau....” Ai baki ma Nazeefa bata gama rufewa ba Yazeed ya zabura tare da ɗaga hannu zai sauke ma Hajiya Yaya a fuska. Ammie da ihun Nazeefa ya sata nufo sashen saboda sashen su Yazeed ɗin shine kusa da nata, duk tana iya jiyo hayaniyar tasu caraf ta riƙe hannun Yazeed ɗin. ALLAH sarki Hajiya Yaya harta rufe idanu tana jiran saukar marin ɗanta a fuskarta😥. Abinda zai baka mamaki suma sauran yaran kowa ya kasa yunƙurin komai sai idanu kawai suka rufe dan suma su Sabuwa ba ƙyalesu sukai ba😂👍. Kai Ammie ta shiga girgiza masa hawaye cike da idannunta. Muryarta na rawa ta ce, “Karka sake ka taɓa wannan gangancin Yazeed. Komu da muke matan uba bama fatan ALLAH ya jarabceka da aikata hakan a kammu balle ita. Yazeed bakai data haifa ba, ko mu da muke ƙarƙashin miji ɗaya bazamu so taɓa kwatanta haka ba gareta kodan shekarun da ALLAH ya bata a kanmu. Haba Yazeed Mamma ce fa...” ALLAH sarki, a mamakin kowa sai Yazeed ya risinar da kansa a hankali. Itama Ammie sai ta sakar masa hannunsa. Sum-sum ya wuce yabar wajen kansa a ƙasa ya koma ya ɗauka tsintsiyar daya yarda ya cigaba da shararsa. Ko kaɗan ba haka Basariyya dake laɓe jikin window tana leƙe taso ba. Sai taji wani irin haushi da takaicin Ammie ya sake kamata. Cikin ƙus-ƙus tace, ‘Munafuka ta hanamu kallon show. Ai mu irin wannan wasan muke so’. Ko kallon Nazeefa dake cika tana batsewa Ammie batai ba. Sai ma hannun Hajiya Yaya ta kama. Cike da lallashi da kwantar da hankali ta ce, “Yaya kiyi haƙuri muje”. ALLAH sarki rayuwa, Hajiya Yaya ko musu bataima Ammie ba. Ta sake kallon inda taga Hajiya Basariyya dake laɓe tun ɗazun ta janye idanun ta dake cike da hawaye. Suma yaran Ammie tace, “Ku wuce muje”. Suma babu wanda yay musu. Har falo Ammie takai Hajiya Yaya, ta taimaka mata ta zauna sannan ta dubi yaran ta ce, “Ku bani ruwa mai sanyi”. Amrah ce dake hawaye taje ta ɗauka mata. Koda ta kawo Ammie ta buɗe ruwan Hajiya Yaya ta ba, nanma bata musa ba ta amsa ta sha, dan ji take tamkar zuciyarta zata fashe mata a cikin ƙirji. Sosai tasha ruwan, dan ɗan kaɗan ta rage. Kamar dama ruwan take jira tasha kawai ta saki kuka. Yaran duk sunyo kanta a zabure zasuyi magana Ammie tai musu alamar suyi shiru. Duk komawa sukai suka zauna, sai da Hajiya Yaya tai kuka sosai sannan Ammie ta ciri tissue ta bata ta kuma sake bata ruwan tasha. Bayan wasu mintuna ta sake natsawa Ammie ta fuskanceta. “Yaya kuka ba shine mafita ba, na barki kiyisa ne dan ki samu nauyin zuciyarki ya ragu. Kiyi haƙuri idan na shiga hurumin daba nawa ba. Amma Yazeed ba kuka ko biyema yarinyar nan ai rikici al'amarinsu ke buƙata ba. Hasalima ɗauke idanu daga garesu shine yafi alkairi, idan ba haka ba komai zai iya faruwa, saboda Yazeed baya a cikin hayyacinsa gaba ɗaya. Yanzu shi yana a wani matsayine da baya banbance fari da baƙi sai wanda yarinyar nan ta nuna masa kawai. To idan muka ce ta ƙarfin tsiya zamu sakashi ya gane akwai babban matsala, dan maimakon ya gane ɗin sai ya sake rikice mana ne kawai, idanunsa su sake makancewa daga ganinmu. Dan haka dole zamuyi haƙuri da kauda kai na wani ɗan lokaci, mu shanye zafi da radaɗin da muke ji akan wannan sabon yanayin nashi tunda mun san bayin kansa bane. Ita kanta yarinyar mu barta ta rinƙa jin tamakar ta gama samun dukkan nasarar da take buƙata sai mu samu damar gayama ALLAH damuwar ya warware mana ita cikin sauƙi kuma. Amma tankawa da nuna damuwar kai tsaye a yanzu tamkar sake zaburar da ita ne ta cigaba da sabon shiri a kansa, shi kuma dama illar sihiri ɗaura wani aikin akan wani, yakan sa asha wahala sosai kafin a raba mutum da shi. Wannan shine mataki na farko da zai taimaka mana. Mataki na biyu addu'a, Yaya Addu'a Yazeed yake buƙata daga garemu baki ɗaya. Kuma taki ita ce mafi ƙololuwar daraja a gareshi, itace kuma tamkar yankan wuƙa. Kasancewar ta a hakan kuma bazai samu ba sai kin daure kin sanyaya zuciyarki, kin yafe ma Yazeed kurakuransa. Ki rage barci, ki tashi cikin dare ki gayama ALLAH damuwar ki masa kuka ki masa bagiya shi mai ji ne mai gani, kuma shine ke raba abinda duk duniya babu mai kwatantawa. Yaya da zakiji wahalhalun da na fuskanta a rayuwata data zuri'ata da kince wannan na Yazeed ba komai bane ba. Amma wlhy ban taɓa zuwa gaban wani na duƙa nace ya taimakeni da garin magani ba. UBANGIJINA na fuskanta, shi kaɗai na amince zai yaye min damuwar da ƙuncin. Na ajiye maganar barci gefe, na sadaukar da rabin nema na a sadaƙa, na maida harshena da laɓɓana a ambaton UBANGIJI ne a koda yaushe. Na rungumi ƙishirwa da yunwa a kowane yini. Na sakama zuciyata jarumta da tunatar da kaina akwai fa wanda suka fini shiga ƙuncin rayuwar, akwai wanda idan zanga halin da suke a ciki nawa ba komai bane ba. Na dinga tuna ANNABAWAN ALLAH ma an jarabcesu. SAHABBAN MANZON ALLAH sun sha gwagwarmaya da jarabawoyi kala-kala. Amma da sukai haƙuri wace irin riba ce basu samu ba. Ƙarshen dai wahala da faɗi tashin bawa shine ya samu makoma mai ƙyau ta aljanna. To su tun ma suna duniya akama mafiya yawansu albishir da aljannar, sakamakon ayyukansu na alkairi da sadaukarwar yaƙi a bayan MANZON ALLAH. Wannan abubuwan sun ƙarfafani matuƙa, na kuma saka yarana suma suka dage, dan nasan yanda tasirin addu'ar uwa take akan ɗa haka addu'ar yara nada tasiri matuƙa. Dan haka Yaya ki jure, ki gwada ki gani in sha ALLAHU zakiyi dariya nan bada jimawa ba, al'amarin Yazeed zai zama tamkar labari ne. Muma kuma ba zama zamuyi ba in sha ALLAHU. ALLAH ya baki haƙuri ya sanyaya ranki.” ta juya ga yaran suma da duk suka nutsu suna saurarenta. “Kuma ina muku nasiha da ku kauda kanku akan al'amarin Yayanku, komi zaku gani tsakaninsa da matarsa dan ALLAH ku daina zuwa kuna faɗawa mahaifiyarku. Ba wannan Yazeed ke buƙata ba, addu'a yake buƙata, idan ba haka ba maimakon mu tsamoshi a wannan masifar sai dai mu sake bada hanyar sakashi a cikin wani. Kunga dai abinda yaso faruwa. Da taci nasara ya mari mahaifiyarku kunga ya sake shiga wata masifar ne ai ko. Ku kwantar da hankalinku mu haɗu mu tayashi da addu'a, sadaka, komai zai wuce”. Daga haka Ammie ta miƙe abinta. Harta kusa kaiwa ƙofa Amrah dake kuka sosai ta ce, “Ammie!”. Tsayawa Ammie tayi, tare da juyowa tana kallon ta, sai kawai Amrah ta taso da gudu ta rungumeta tana sake fashewa da kuka da faɗin, “Mun gode Ammie, mun gode, in sha ALLAHU ke ƴar aljanna ce. Dama nace ke mai ƙaunarmu ce da zuciya ɗaya amma ba'a fahimtata.....” Murmushi Ammie tayi, tare da ɗagota, cikin katseta ta ce, “Amrah ya isa haka kinji, mu dukanmu in sha ALLAHU ƴan aljanna ne. Kuma ba fahimtarki ne ba'ayi ba. Kowace rayuwa da nata ƙalubale ne kinji”. Amrah zata sake magana Ammie ta hanata, sai ma share mata hawaye datai tas sannan ta maidata ta zaunar ta fice... ★Baki Hajiya Basariyya ta ƙyaɓe. Tare da faɗin, “Kai wannan kilakakkiyar mata anyi munafuka. Ita adole gata ALLAH. Yannn! yannnn! yannnn! Tana wani zabga wa'azi. Sai dai kuma a gayama wasu amma wlhy bamu ba. Ubanwa ye zai yarda wani kin tsaya a addu'a ne da azumi da mima tace. Waye wawa an gama tsaface mana miji, da samarin ƴaƴanmu sun aure ƴaƴanki”. Haka dai ta gama surutanta sai kuma ta gyara yanayinta ta nufi cikin falon Hajiya Yayan a ɗan rikice. Har wani neman yin tuntuɓe take zata faɗi. Tadai dafe kujera tana kaiwa zaune kusa da kujerar da Hajiya Yaya ke zaune. Sudai kallonta suke kawai. Cike da makirci ta fara faɗin, “Mun shiga uku, ina wanka yanzu Jannah ke sanar min abinda ke faruwa. Kai wannan yarinya anyi ibilishiya, ita yanzu dan bata da mutunci sai ta saka Yazeed ya mareki, kai ALLAH wadan naka dai ya lalace. Amma gaskiya dai ya kamata a kira Sabuwa a gaya mata wannan ɗanyan aiki tazo tai mata faɗa dan ba halin arziƙi bane ba. Yanzu haka ƙawayen banza ne suka ɗorata a wannan hanyar mara ɓullewa. Yo mara ɓullewa mana kasa ɗa ya mari suruka ina arziƙi. Ita bata tunanin zata haifa tunda ga cikin nan a gabanta itama za'ai mata wataran. Ai ni yaran nan baku ƙyauta min ba da baku haɗu kun lakaɗama shegiya duka ba, har sauran ƴan uwanku duk basai ku kira ba damu mu haɗu mu ci ubanta ai daɗi gidan yawan kenan dama ko”. Amrah da surutun ke ƙonama zuciya ta ce, “Ai hakan baida amfani Ummi. ALLAH kawai ya shiryeta. Jarabawace watarana sai labari.” Kasare Hajiya Basariyya tai tana kallonta, ta zata wani zai sake magana ta samu point, sai taga kowa bai tanka ba. Hajiya Yaya ma miƙewa tai abinta ta nufi bedroom. Sai suma yaran suka fara miƙewa.. ganin fa zataji kunya sai itama ta miƙe tana faɗin, “To ALLAH dai ya ƙyauta. ALLAH kuma ya kiyaye gaba iyakarta kenan”. Daga haka ta fito tana tsine musu a zuciya. Ganin nan babu nasara sai ta nufi sashen Ammie, Sakina da Waleed kawai ta samu, sukace mata Ammie na sashen Daddy. Nan ma ta fito cike da baƙin ciki, amma sai itama ta nufi sashen Daddy ɗin duk da kuwa ɗazun taje ya korota..........✍️ 🤣Itafa Hajiya Basariyya tafi dacewa da haihuwar Saheeba. Kai ALLAH ya rabamu da munafunci gaskiya☹️. *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖9️⃣7️⃣ ______________ .........Maanal na kwance barcin wuya ya ɗauketa dan oga da kansa ne ya gama wajigata. Itako sarkin raki tasha kuka har ta godema ALLAH. Sam ta kasa sabawa, gabanta har faɗuwa yake ya nuna buƙatarsa a gareta. Zata biye masa a shan minti amma da anzo fagen fama ta fara kuka da roƙo. Shi ko ya zama kurma ya zama makaho har sai ya samu yanda yake so dan bai san ɗanɗani haukaci ba bai kuma san haƙuri ba. Kwana biyun nan har ƴar rama ta fara. Ko kuma ta gudu sashen Oum sai yata zarya ko Oum ɗin ta korosu sannan. Gaba ɗaya ta ƙagara weekend ɗin nan ta ƙare, idan aka koma aiki ta samu sauƙinsa ai tunda da rana babu dama. Oum data fahimci matsalar Maanal dan ramar da yarinyar ta fara ta fara tsaya mata a rai sai ta shiga haɗa abubuwa, ta kuma amso wasu hannun Hajiya Shuwa. Itama ta fuskanci irin wannan yanayin a hannun Abah, dan shima akwai fitina kamar AA ɗin, kai bama su kaɗai ba kusan duk mazan family ɗin Darma haka suke sai dai wani yafi wani. Gasu kuma ALLAH ya jarabcesu da son zama da mata ɗai-ɗai, shiyasa matan ke jigatuwa a hannunsu kafin su saba.. Kiran da Oum tama Maanal ɗin a waya ne ya farkar da ita, dan AA ya fita shi da Yaya Fawzan shiyyasa sai ita kaɗai. Muryarta kawai Oum ɗin taji ta fahimci mike faruwa. Dan dama tana anan sashen suna hirarsu AA yay kiranta a waya ta kawo masa wai fruits dan shi yana sashen Abah suna meeting shi da su babban Yaya. To daga kai fruits ɗin ne fa ya samu ya matseta a sashen sai da ya sauke damuwarsa sannan yay shirin fita da zasuyi da Yaya Fawzan ɗin. Ita kuma wahala ta hanata tashi dan barci ne ya ɗauketa sama-sama ma taji fitarsa. Cike da tausayi Oum ta girgiza kai, sai kuma ta ce, “Barcin yamma kike Baby?”. Cikin sanyin murya Maanal ta ce, “Eh Oum, amma na ma tashi gani nan zuwa sashen.” “Okay sai kinzo”. Oum ta faɗa tana yanke kiran. Itama Maanal tashi tai ta shiga bayi ta gyara jikinta yanda ya kamata, koda ta fito gashinta ta busar ta shirya cikin atamfa doguwar riga tai sallar la'asar da ake kira sannan ta gyara gadon da suka yamutsa ta fita. Ta nufi sashen Oum motar Momyn Nibras ke shigowa gidan. Maanal bata tsaya ba tai shigewarta, dan yanzu kusan kullum Momyn Nibras ɗin sai tazo gidan. Jiya da yamma har sabuwar rigima suka tafka da Mamy. Wani haɗaɗɗen gashin nama mai ruwa-ruwa Oum ta bama Manaal taci ta ƙoshi, sannan ta bata abubuwa na musamman data haɗasu da kanta kuma ita tasan sirrinsu dan sune take amfani da su. Har sai da Maanal taji kamar zatai amai sannan ta ƙyaleta. Daga haka suka cigaba da hirarsu. Su AA basu dawo gidan ba sai bayan sallar isha'i. Anan suka yada zango sashen Oum sukai dinner aka ɗora da hira, hirar gaba ɗaya akan yanda bikin Fawzan zata kasance ne dan shi aka fara shirye-shirye, amma suna saka rana a haɗa dana Babban Yaya, sai dai ba'a yanke hukunci ba sai gobe idan ALLAH ya kaimu su Baba Sardauna zasuje Katsina domin ganawa da dangin mahaifin su Ameerah. Koda AA yace Maanal tazo su tafi catai ita anan zata kwana. Shiru kawai yay yana kallon ta, Oum kuma taƙi saka musu baki. Yanda AA ya tsaya yana kallonta mi Yaya Fawzan zai yi inba dariya ba. Harda ƴar waƙarsa ta neman tsokana. Aiko AA ya wuce ya tafi kawai ransa a ɓace. Babban Yaya daya bisa da kallon ƙasan ido ya ɗan murmusa a zuciyarsa. A zahiri kam fuskarsa babu alamar wasa ya kalla Maanal da itama ta kumbura baki ta kwanta a cikin kujera. A dake yace, “Lilly!”. Amsawa tai tare da tashi zaune. “Tashi kibi mijinki kinji, sai da safe”. Ji Maanal tai kamar ta fashe da kuka. Amma bazata iya ma Babban Yaya musu ba. Haka ta miƙe tai musu sallama ta tafi. Babban Yaya ya bita da kallon tausayi. Dan a ransa kawai yaji cewa ga abinda takema gudun. Cike da shaƙiyanci Yaya Fawzan da baya iya shiru shi ya kai bakinsa saitin kunnen Babban Yaya ya ce, “Idan baka saita fitinannen ƙaninka ɗin nan ba watarana ma nan Lilly zata dawo gaba ɗaya dan zugeta sanyi da kaina”. Fillo Babban Yaya ya ɗauka zai buga masa. Da gudu ya tashi ya fice yana dariya da faɗin, “Oum goodnight ”. Oum ta ce, “ALLAH ya tashemu lafiya.” Shima Babban Yaya miƙewa yay ya mata sallama. Oum ta amsa masa da kulawa shima, ta musu addu'a da sanya albarka. Koda ya fito sai yaci karo da Saheeba tsaye a ƙofar sashensu tana jiransa. Tamkar bai ganta ba ya ɗauke kansa. Da sauri tasha gabansa ta durƙusa. Tare da fashewa da kuma tana roƙonsa yayi haƙuri ya yafe mata koma wane laifi ne yake ganin tayi, wlhy bazata sake ba dan ALLAH yayi haƙuri ya barta ta dawo sashenta. A daƙile ya kalleta ya watsar, sai kuma yay wucewarsa batare dako tanka mata yayi ba ya shige ciki ya maida ƙofa ya kulle... Kuka mai tsuma zuciya da ruhi Saheeba ta saki. Wlhy ta gaji da zaman sashen Mamy bazata iya ba. Dan duk daɗin wani waje naka wajen daban ne. Ga Mamy da saka aikin tsiya. Haka zatai zaune saboda ƙafarta ba gama ƙwari tai ba taita sakata Safa da marwa tsakanin upstairs da downstairs. Wai sai tace bata gamsuwa da aikin su Haule ita tai mata da kanta, Nuratu kuwa lafkewa take ita adole bata da lafiya. Gaba ɗaya ta maidata wata ƴar aikinta ma. Ga kewar mijinta da buƙatarsa ya riga ya saba mata da fitinarsa. Ga kewar ƴaƴanta dako kallonta basayi gaba ɗaya sun koma sashen Oum ko tunawa da zamanta a gidan basayi. Ga jiya mamanta tace mata ta sanya ido akan Babban Yaya dan tasan mike faruwa tsakaninsa da ƴar Hajiya Shuwa. Wannan magana ma tafi komai ɗaga mata hankali. Dan a duniyar nan babu abinda ta tsana irin kishiya. Kai itafa ko ƙawarta akama kishiya ta daina ƙawance da ƙawar kenan. Shiyyasa ta shirya zuwa ta bashi haƙuri dan gara ta dawo kusa da mijinta in ma nesa da shi da take ne ya sashi fara kallon wasu matan. Tun ɗazun take dakon fitowarsa daga sashen Oum. Dan ita Nuratu yau taje gida amso musu wasu kayayyaki da mamansu ta aiko da su.. Ta jima a wajen tana kuka. Kafin ta tashi ta koma sashe Mamy. Ta buɗe ɗakin da take zaune ta shiga, waya ta ɗauka tai kiran Mamanta tana mata kuka ta zayyane mata komai daya faru. Ran Maman ya sake ɓaci, amma ta kwantar mata da hankali akan ta ƙyalesa indai sukai amfani da wannan kayan data turo duk wani girman kansa zai saukane. Wannan ya sake Saheeba jin sanyi a ranta, har tai shirin barci ta kwanta.... _______★ A ɓangaren Maanal kuwa koda ta shigo sashen nasu ta samu AA ya haye sama abinsa, har yama kashe wutar ko'ina sai amfani tai da fitilar wayarta. Tana shigowa bedroom ɗin yana fitowa daga bathroom, bathrobe ce a jikinsa alamar wanka yayo. Kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa dan harga ALLAH yaji haushi. Itama sai ta ɗauke nata tare da ɗan murguɗa baki ta wuce closet tana ƙunƙuni. (Haka kawai sai na zauna ka kashe ni. Sam babu tausayi a al'amarin ka. Yo in haka auren yake banga abin cewa akwai daɗi ba. Tsabar jaraba sam bana son naga mun kasance mu biyu kawai a waje tunda nasan ƙarshen zancen. ALLAH in zan dawo sashen nan gabana gabana har faɗuwa yake yi. Abu dare da safiya, yammaci da rana idan kana gida ma ba hutu.....) Haka dai taketa masifarta a rai idonta har yana cika da ƙwalla. Wai a hakan ma maganin nan na sit bath da Hajiya Shuwa ta bata yana matuƙar taimaka mata ne. Koda ta fito har ya gama nashi shirin yana zaune a cikin sofa ya ɗakko laptop yana kunnawa. Gefe ɗaya takardu ne sai kwalin fresh milk da kofi. Ɗauke kanta tai tayi shirinta. Tana gamawa tai shafa'i da wutri ta haye gado ya kwanta. Idanu AA ya ɗan ɗaga ya kalleta, sai kuma ya cije lips ya cigaba da aikinsa. Tun fa yana aikin da marmari har yaji ina bashi yiwuwa. Tattare komai yay ya ajiye, ya tashi ya kashe fitilar ɗakin ma gaba ɗaya dan dama mara haske sosai ce ke a kunne. Maanal datai barci cike da farin cikin fushin nasa dan tasan ko dai yaya ne ta samu sauƙi kawai ta farka a rikice jin ya nutsata cikin jikinsa. Muryarta na rawa ta buɗe baki zatai magana, ai bai bari a ta gama fita ba ya rufe shi ruff da nashi. Bore taso fara masa ya nuna mata ƙarfin ba ɗaya bane, wayon ma kuma ba ɗaya ba, dan sai da yasan duk hanyar da ya bi wajen lankwasar mata da jiki ta fara amsar saƙonsa. Sai da tafiya taje gaɓar tayar mata da hankali ta sanya masa kuka. Baiko saurareta ba sai da ya samu yanda yake so. Daga ƙarshe ya koma lallashinta da mata wayon daya saba. Sai ga hajjajunku an lafe a jikin AA ana sauke ajiyar zuciya..... Na gabannin asuba kam da ya zame masa jiki kuka ta saka masa bana wasa ba, dole ya haƙura ya ƙyaleta. Koda ya fita salla kafin su dawo haka ta daure ta tashi ta hau gyaran gidan, harta sakko kitchen ta fara ƙoƙarin haɗa breakfast sai gashi ya shigo. Ƙin yarda tai ta kallesa, a haka ta gaishesa ita a dole tana fushi. Shi sai ma ta bashi dariya. Ya rungumeta yana murmushi da faɗin, “Haba Besty munyi faɗa ne wai?”. Baki ta tura gaba, idannunta na tara ƙwalla ta ce, “Eh munyi, kuma kada ka sake kulani tunda baka tausayi na. Ni wlhy sashen Oum zan koma kafin ka kasheni.” Sosai dariya tazoma AA wuya. Amma ya danne da ƙyar, a ransa ko ayyanawa yake (Inda ana mutuwa Besty da ba'a haifomu ba ai. Kedai kin cika raki ne kawai da tsoro. Sai kuma yanayin jikinki da sai dai nace Alhmdllh) a fili kam rungumeta yay yana lallashi, sai da tace masa ta haƙura sannan ya fara tayata sukai komai a tare, su Inte ta kira a waya suka kwashi abincin zuwa sashen Oum, dan haka take yi, a sashenta take musu breakfast gaba ɗaya, sai akai can sashen Oum, da rana kuma taje can tayi, hakama na dare. Yau da tasan zata koma aiki saita haɗama Oum harda abincin ranar ta, suma tai musu nasu ta na lunch. Tare sukai wanka suka shirya. Kayan farko data ɗakko zata saka AA yace bai yarda ba. Shi da kansa ya zaɓo mata wanda zata saka. Data saka ɗin kuma nan ma ya haɗe fuska wai suma ɗin dai tayi ƙyau. Gudun kar ya ja musu makara ta shiga lallashinsa, da ƙyar ya haƙura suka fito.........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖9️⃣8️⃣ ______________ .......Sashen Mamy suka fara nufa. Sosai zuciyar Mamy ta wani irin tsargawa. Dan wani irin ƙyau da nutsuwa ta gani a fuskokin yaran. Kodan hankalinta ba a kwance yake ba kwana biyun nan shiyyasa bata luran ba sai yau. Badan kar ace tayi ƙarya ba da tace idannunta kamar suna kallo mata yaron ciki a tare da Maanal. Kai ina abinda ma bazai yiwu ba kenan. Ciki fa, tabbas yarinyar nan akwai ƙaramin ciki a jikinta. Sai maganar wancan cikin ƙaryar ya faɗo mata a rai, a take taga wautarta a wancan lokacin, to yama akai ta zurma da wuri daga ganin yarinyar na amai, yanzu kam gashi babu wani signing na ciwo a tare da ita amma wlhy gaba ɗaya alamomin yarinyar ya mata na mai ciki..... Gaisuwar da suke mata ta katse mata tunaninta. Da ƙyar ta iya amsawa tana tsare AA da shima yay mata wani fresh da shi da ido. Yaron ya ƙara ƙyau da cikar kamala harda ƙiba. Kaida ka ganshi kasan hankalinsa a kwance yake, yana kuma hutawa da kwasar ganima a jikin mace dai-dai gwargwado. A lallai babbar magana. Ina hankalinta ya tafi har haka ita kuwa. Bata da amsar hakan, dan a yanzun ma dai hankalin nata baya a tare da ita har AA da Maanal ɗin suka fice abinsu. Sai Saheeba da itama jikinta ke mazarin abinda ta hango a tattare da Maanal ɗin ta maidota hankalinta ta hanyar faɗin, “Kai amma yarinyar nan fa wlhy kamar mai yaron ciki”. “Taratsatsatsa!!!!!!”. Kake jin sautin tarwatsewar abu a ƙasa. Ba komai bane face kofin shayi da Nuratu ta fito da shi a hannu daga kitchen. Dan ƙamshin turaren AA da tajiyo ne ya sata fitowa da sauri sai furicin Saheeba a kunneta babu kuma AA a falon. Muryarta na rawa ta ce, “Ciki kuma! A jikin wa?”. Saheeba ta ce, “A jikin wa kuwa in ba tsinanniyar yarinyar nan ba Maanal. Wlhy ko rantsuwa nayi babu kaffara wannan yarinyar ciki ne da ita ko Mamy?”. Mamy bata iya ta bama Saheeba amsa ba Nuratu dake hawaye ta ce, “Kenan da gaske wancan cikin bana gaskiya bane yarinyar nan is a virgin?”. Saheeba tace, “Tabbas wancan lokaci mun ruɗa kammu ne kawai yanzu ne yarinyar nan ke ɗauke da ciki na gaske. Maganar budurwa ce kuwa dole shima mu bincika dan akwai ƙamshin gaskiya”. Saheeba ke bayanin amma zuciyar Mamy ce ke duka da ƙarfi, jikin Nuratu kuwa na rawa..... ★★★ Su AA da basu san suna yi ba kuwa tuni sun isa sashen Oum. Itama dai yau kamar hasashen su Saheeban ya buɗe mata idanu akan Manaal ɗin. Dan sai duk kammanin ta suka juye mata na mai yaron ciki. Ko kuwa kwalliyar da tai ne ya canjata zuwa hakan. Duk da bawai Maanal ɗin tayi zane-zane a fuska bane. Hasalima hoda da kwalli sai lips-gloss ne kawai ta saka. Komai dai Oum batace akan hakan ba, sai ma gaisuwa da sukayi, dai-dai kuma nan Babban Yaya da Yaya Fawzan suka shigo suma a tare cikin shirin fita. Manaal ta gaishesu suka gaisa da Oum da AA sannan sukai zaman yin breakfast. Yau dai Fawzan bai tsokani AA ba. Hakan yasa Oum da sauran ƴan uwansa fuskantar ransa a ɓace yake. Sun tabbatar dai bazai wuce shi da Nibras ba, dan haka cikin hikima irin ta iyayen ƙwarai Oum ta shiga yimasa nasiha, ai ko sai gashi kafin su gama su fito harda ɗan murmushinsa. Su dukansu sukan shiga damuwa a duk lokacin da suka ga babu fara'a a fuskar fawzan, ba komai yasa haka ba kuma sai sanin shi mutum ne mai sauƙi da yawan fara'a, akan jima baka ga damuwa a tare da shi ba, dan ko abu ya ɓata masa rai yakan shanye shi ta yanda da wahala a gane masa kai tsaye. AA da kansa ya buɗema Maanal mota ta shiga, sannan ya zagaya ɗayan side ɗin da driver ya buɗe masa shima ya zauna. Yana gama zama ta kwanto jikinsa, kanta a kafaɗarsa ta lumshe idanunsa ɗan barci ne a cikinsu. Kallonta ya ɗanyi, sai kuma a hankali ya kamo hannunta cikin nashi ya riƙe. Ɗayan hannunsa kuma wayarsa yake dannawa yana son yay kiran RK. Tafiyar ƴan mintuna ta kawosu MAWAAD COMPANY. Sai Maanal taji tayi kewar wajen sosai. Yanda take kallon ko'ina yasa AA sakin ɗan murmushi. Ƙasa-ƙasa yace, “Kinyi kewarsa ne?”. “ALLAH sosai ma Besty”. Murmushi ya sake yi, sai kuma ya ɗan taɓe baki ya yunƙura ya fita dan har driver ya buɗe masa. Zagayawa yay ya buɗe ma Maanal, ya duƙo ya riƙo hannunta, ɗayan kuma ya ɗauka handbag ɗinta ya riƙe. Tuni masu shigowa suka tsaya kallon gulma, dan haka kawai suka tsargu da boss ɗin yau tare yake da amarya. Aiko sun gane ma idonsu abinda suke jiran, AA kam da baima san sunayi ba ƙoƙarin gyarama Maanal mayafinta yake yana kallon ta da murmushi, ita kuma tana masa magana a shagwaɓe dan yace mata yau a office ɗinsa zatai aiki ne, ita kuma tana cewa a'a bata yarda ba ita dai nata zata zauna sai tafi yin aiki da ƙyau. Uhhm babbar magana boss na murmushi available. Wannan shine taken gulma yau a Maawad. Lokacin da suke shigowa AS da shima ya iso yanzu suka haɗu a waje na biye dasu sai driver daya kwaso musu kayayyakinsu. Cike da farin ciki da girmamawa kowa kema Maanal barka da dawowa office. Itako tana amsawa kowa da kulawa da fara'a. Hakan kuma sai yayma kowa daɗi dan basuyi zaton haka ba. Jin tarihin alaƙarta da ogansu yasa suka fahimci hotonta ne a ko'ina na companyn, yanda aka ɓoye kamaninta ne yasa basu gane ba. Irinsu Zaharadeen kam kunya ce fal a cikinsu da jin shakkar haɗuwa da Maanal. Yayinda ƴammata masu ɓoyayyar manufa akan boss suke jin kishinta da shakkarta a wani gefen. Dan sun san dai lallai wutsiyar raƙumi tai nesa da ƙasa. Saboda muhimmancita ga boss mai girma ne ƙwarai da gaske da yanzu yake a bayyane gare su. Har cikin elevator hannunta na riƙe cikin nasa, amma kasancewar su AS a tare da su ya kama kansa kamar ba shi ba, itama Maanal ɗin a nutsenta take. Sai da suka fito ne ta saka masa rigimar ita dai office ɗinta zata. Dole ya haƙura ya yarda, amma sai taga ya nufi sama inda nashi yake na ƙarshe shi da AS. Zatai magana ya hanata, sai da suka iso taga AS ya buɗe office ɗin jikin na boss ɗin da ada yake kamar ma'ajiyar wasu muhimman abubuwa yasa Maanal a mamaki. Koda suka shiga sai tai tsaye tana kallon ikon ALLAH, sai kuma ta kalla AA ɗin dake kallonta yana murmushi. “Office ɗin waye?”. “Matar AA Darma mana. Kina tunanin zan barki ki cigaba da zama can ni ina nan? Sannan kema president ce kuma (Chairwoman) a wannan companyn, kina kuma da damar cigaba da kasancewarki a artist dan bazamuyi sakacin rasa gwarzuwarmu ba a wannan fanin. Barka da zuwa sabon office Bestyna”. Rasa ma abin cewa Maanal tayi, sai taji kawai ƙwalla ya cika mata idanu. A hankali ta shige jikin AA ta rungumesa tsama ta wani kalar sakar masa kuka. Shima slowly ya lumshe idanunsa tare da rungumeta yana ɗan murmushi. Saɗaf-saɗaf AS ya lallaɓa ya koma tare da ja musu ƙofar gulma da dariya fal cikinsa. AA cak ya ɗauka Maanal har zuwa office chair ɗinta dake sabuwa fil dan komai na office ɗin sabone irin na office ɗinsa, wancan kuma office ɗin Yaqub aka maida ciki a madadinta. Zama yay a kujerar ya sakata a cinyarsa. Sai da ya ɗiba tissue dake a saman desk ɗin ya share mata hawayen sannan cike da lallashi da soyayya ya ce, “Babyn Oum kwana biyun nan shagwaɓa kike jin yimin da yawa. Komai kuka kina son zama rigimammiya. Minene abin kuka anan, companyn ki ne fa, ko office ɗina kikace na fito na baki ba da gudu zan fito ina faɗin, “An gama Madam ba”. Dariya yanda yay ya bata, sai ta saki murmushi da ɗan ja masa hanci ta ce, “Daka zama mijin tace”.. Murmushi yayi mai ƙyatarwa, tare da sumbatar lips ɗinta ya ce, “Aini mijin kafin tace ne ma. Idan kuma da abinda yafi ma hakan to gaskiya duk ni ne Besty”. Dariya sosai yanzun kam Maanal keyi, shima yana tayata da murmushi. Zata fara masa godiya ya rufe mata baki da nashi. Bata hanashi ba, sai da ta tabbatar ta nuna godiyar tata a haka sannan. Ya rungumeta shima yana sanya mata albarka. Jin yanayinsa na ɗaukar sabon salo cike da wayo ya zame jikinsa ya bar office ɗin zuwa nashi shima. Ita ko ya barta da farin ciki tana faman zagaye office ɗin da kallo komai. Daga ƙarshe tai kiran Ammie a waya tana sanar mata. Ita kanta Ammie sai da taji ƙwalla ya taru mata a ido, dan a rayuwa takan ji matsannacin farin ciki idan taji Maanal a farin ciki. Kodan yarinyar ta wahalu a shekarun baya ne fiye da sauran oho. Bayan ta katse kiran su Didi ta kira suma ta gumtsa musu. Suma suka tayata farin ciki sosai.... Aikin dake a companyn sosai yasa babu zama, kowa aiki yake tuƙuru a tsakanin nan. Ita kanta Maanal yau gaba ɗaya bata huta ba. Sun shiga meeting har sau kusan huɗu kafin break. Sun fito na ƙarshe ne lokacin salla yayi, AA yaja ra'ayinta suka je office ɗinsa sukai alwala. Sannan suka fito zuwa yin salla. Ana idarwa suka dawo, a hanya ne suka haɗu da CFO. Sai tai saurin ɗauke kai kamar bata gansu ba. Murmushi Maanal tayi a ranta tace (ƙyaji da shi dai) a fili kam yitai kamar bata ganta ba. Dan taga dama wani ɗacin rai da take a wajen meeting. Shi kam AA baima ɗauka abinda CFO ɗin keyi a komai ba. Dan yanda ta iya takunta yasa bai wani fahimci take-takenta ba har yanzu. A office ɗinsa sukai zaman cin abincin data shiryo musu sukazo da shi. Suna nishaɗinsu da soyayyarsu. Bayan sun kammala Maanal ɗin ya haɗe komai waje guda ta koma nata office ɗin. Bata wani jima da zama ba suka sake fita yin meeting, sai dai yanzu babu AA yana ganawa da baƙi, AS ne ya zauna a madadinsa. Meeting ɗin ya jasu lokaci mai tsayi kafin su fito. Dan lokacin ma la'asar tayi........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖9️⃣9️⃣ ______________ 🥱🥱 Nace ba, na fara saida GUMAMA ta yara data manya mai so yayi magana kafin ta ƙare. Dan na sakata a farashi mai RAHUSA da ARHA, karku damu tana ƙamshi yanda ya kamata😆🤌. Hhhhh Haba hajjaju ya da fara maida murtanin faɗa bayan WASAN bama a farashi ba. Banning number Bilyn Abdull tamkar an kashe MACIJI ne ba'a sare kansa ba wlhy😂. Dan ko mutuwa Bilyn Abdull tai in sha ALLAHU ina ji a raina zan cigaba da zama a zukatan masoyana zasuna min addu'ar kwanciya lafiya a kabari. Karki kuskura kice zakiyi wannan wasan, dan wlhy mamaki zan baki keda ƴan jagaliyar taki. Ke reporting kika sa akayi a WhatsApp ni kuma dare zan raba ina reporting naki ga babban sarki. Kinga maimakon Banning a WhatsApp ke a media ɗin gaba ɗaya ma UBANGIJINA zai yi banning ɗinki, (Wayaga ruwa zai ƙarema ɗan kada, dama kuma da ruwan muka dogara😜😆🤭). Wannan Bilkisun da kike ganinta ba ƙyalan bace ƙyalle ce, kawai kafin mu sara ne mu sai mun dubi bakin gatari ALLAH wlhy. Ina ƙara baki shawara karki ce zaki saka Game dani akwai damuwa, ubana har ya rasu albarka yake zuba min, uwata kullum sai tace ALLAH yay miki albarka Bilkisu dan dattijuwar ƙwarai ta kullum goshinta na bisa ƙasa tanama UBANGIJI Sujuda. Mijina kam ai duk motsinsa sai ya ce Bilyn Abdull ALLAH yasa ki gama da duniya lafiya, yo an gaya miki a banza nake ɗaɗara shi a littafin🤪, gata yake bani iya gata, tsaro iya tsaro, naci shinkafa na kora da ruwan fanfo ga windows ɗin gidana iska tako ina ko ba'a bamu wutar nepa ba bana damuwa. Idan zai fita yanda nake masa addu'a haka yake min shima kaga shalelen Bilyn sa ALLAH yasa muna jone har a aljanna🤏🥰. To Ladidi banda kankamba😲 ke wacece da kike tunanin zaki nuna min yatsa ban karya shi ba🤣 ina da waɗan nan ƙafofin murhun uku na haye kansu na zauna matsayin tukunya na dafa duk kalar ruwan dana gadama TSAYAWAR ALLAH kenan. To gaskiya ina baki shawara, kawai dai ki daurewa zuciyarki abar kaza cikin gashinta, dan in akace figeta za'ayi wallahi jikinta zai koma ne kamar na BALBELA. Shegen tsuntsu kenan ƙyau iya ƙyau a waje ciki kam ba'a cewa komai. WAJENJI FARI CIKINKI BAƘI KENAN😂. Nifa a duniya cakwakiya na birgeni kwarai-kwarai da gaske kun ganni nan, ALLAH birgeni take😆, idan akai wasa ana gama AJIYA A DUHU zan saki sabon Update na zazzafan littafi mai suna Ladidi a harhaɗa🤣, alƙalami ɗan albarka, kun san yafi takobi kaifi, balle na Bilyn Abdull har ƴan a leƙa katanga zanowa yake, gashi baya yafiya dalla-dalla yake cika aikinsa🤫. Bari dai nayi shiru, tsiyar Mamy ma ta ishi al'ummata, ita kuma Sille ya isheta😂, wayaga AJIYA A DUHU. Kai idan akace ƴar baka za'ai na rantse akku zan koma muku ALLAH dai ya ƙyauta ba shekarar zazzaga bace ta kama😆, dan wata tabarmar idan aka zazzageta babu mai sake ɗora ɗuwawunsa akai saboda ƙazantar da aka zubar a bisanta. Kudai kuyita salati ƴan uwa karna zare a maimakon labarin na koma muku tatsuniyar gizo-gizo. Dan labarin ƙoƙi dai baya wuce na gizon Update iya Update 😎. 🤔To Kuma su Haƙilah a dai kiyaye dan mun jima da sanin suna kuma mun san numbers, yanzu komai mai sauƙi ne a buga maka sallama a ƙofar gida daga ƴar jagaliyar media ki jawa kanki ai miki tonon leƙa katanga a gaban Rijalu da matan anguwa, ya barki a gida da tunanin ya killaceki ƙarƙashin igiya uku a kira shi ace kina ofishin ƴan doka. Banu taci ƴan a ara a yafa kenan, bamu san tushe ba amma muna rawar takaɗiɗi akan nera biyar-biyar😂. Tab ɗin wayaga goge hadda, kajawa kanka daga karanta HIKAYIYIN su Bilyn Abdull a tuɓale ƴar igiyar auren😮‍💨 dama lamarin rijalu yanzu ana basu wuta a sama suna bama Nisa'u a cikin gida, yana ƙaraki gaba wlhy galleliya zai santalo, idan dama kuma kina da abokiyar burmi a cikin gidan shike nan ya samu filin shakatawa, yo kunga laifinsa ne, koni na auri mace ta zama ƴar ARE-ARE (Gayyar SHANU) a media walle na kamata zanen yarbawa zan mata a uwawu😌 kafin na saita miki hanya zuwa gidan tsoho.🥳 To kama kanki wannan kokawar ta GIWAYE ce, ke kunama daga neman suna ko na gwajin harbi karki jama kanki ƙafa ta takeki batare da ansan da ke a cikin ƘURAR YAƘIN ba. Idan kunne yaji jiki ya tsira. 👉🙆👈 Dan ni idan na tashi bada gumamar kaya idan ta kama har ZINARI haɗawa nake a ciki🤪😂, yo miye amfaninsa ALLAH na tuba, ƙaryar banzar da wal-wal a kan wuya baya fansata ga walakirin kabari🥱. Oh oh faɗan matsoraci wai wasan sunƙuru, idan mace takai mace ta fito a bamu fili dan ALLAH, Bilyn ce fa, jinin Kanawan dabo da katsinawan dikko kunya gareku badai TSORO ba. Idan kin yarda mu fara wannan game ɗin dan GIRMAN ALLAH gobe naga raddi😏👈 . Nawa ki ɗaukesa kamar na taba kasa ne na lashi miyau tushen faɗan yara kenan😂, koda yake muma yaran ne bamu wuce ehhhhhhhhh😉 ba, kun dai gane mutane na🤪😂. LADIDI BISMILLAH🙄🤌 zamu iya fara wasan, ni banda matsala ko ina typing ɗin zan iya😂, yo wani abune ina gama muku posting na koma filin yaƙi💪, kafin safiya nasan koda na ciyo wuya da DUKA wajen zai huce🤣 sai a cigaba da gashi zuwa yammar washe gari a koma filin dagar, wayaga faɗan Kurame, ta AA Darma zan koma, KURMA kuma MAKAHO😆😆🤣Ladiyos bismilla👆🏻😒😣☹️😔🥶🥱🥱🥱. Kar wanda yace Bilyn yaya akayi, shi saƙon yasan inda aka aika shi😆, waɗanda zasu ƙarɓi saƙon suma sun san nasu ne🥱. Idan kuna son kallo ku jira a maido min raddi ai kune ƴan rakkiyata faɗan🤣🤣👍. Ina sonki masoyana, ALLAH wlhy sai da ku na Bilyn Abdull, Zafafa family na miƙo muku gaisuwa irin ta girma da mutuntawa❤️❤️❤️❤️🥰🥰🥰🥰😘👏🏻 Bala'i page guda ya tafi a banza Ni balki kumuje jan labari, gulmar ta isa haka dare ya fara yi kuma.😩🏃 ____________ ......Anan Kaduna kam da ƙyar Ammie ta shawo kan Daddy ya yarda da batun sakawa aima Yazeed addu'a a islamiyyu. Amma da farko yace ta barshi uwar tasa ta ƙara ji a jikinta. Ammie taita masa magiya da nuna masa ba Hajiya Yaya za'a duba shi Yazeed ɗin. Dan yaron kirki ne mai hankali da sanin ya kamata. Kodan ibadarsa da ta samu rauni sa tarosa. Sannan halin da yake a cikin ba Hajiya Yayan kawai yake ƙonawa ba har da su suma. Da nasiha da lallashi dai Daddy ya amince. Dan haka Ammie ta fara fitar da kuɗinta batare data nema komai a wajen Daddyn ba taba Nene akan a dinga abinci ana sadaka. Suka kuma saka ana sauka a islamiyyun yara. Ta kuma shirya da kanta taje Kano ta amso masa ruwan addu'a a gidan Babban malamin nan.... A lokacin da nan su Ammie keta ƙoƙarin ganin sun maido Yazeed hayyacinsa da ƙarfin ikon ALLAH a ɓangaren mijin sabuwa shirinsa ne ya gama kammala akan Daddy, aiwatarwa kawai zai saka Yazeed ya fara masa. Dan kuwa tun randa abin can ya faru Nazeefa ta kirasu tana kuka ta faɗa musu ƙarya da gaskiya. Aiko suka ƙullaci Ammie harda alwashin yin maganinta itama. Suka kuma sake ɗammarar yin sabon shiri akan Yazeed ɗin. Washe gari Sabuwa tazo ta kawo mata komai da zatai amfani da shi. Ko kallon sashen Hajiya Yaya batai ba balle ta shiga su gaisa. Sai yara taji suna hirar zuwan Sabuwar gidan batare da sun san ma taji ba. Dan yanzu suna aiki da nasihar Ammie basa gaya mata komai daya shafi Yazeed ɗin ko sun gani... Aiko komai Nazeefa ta aikata, sai dai anyi rashin sa'a Sakina taga lokacin da take ajiye na sashen Ammie. Dan tsabar munafunci sashen tazo wai bama Ammie haƙurin abinda ya faru kuskure ne, miye-miye ita ba laifinta bane kaza-kaza.. Ammie bata nuna mata komai tace ta fahimta, sai ma tai mata nasiha akan hakan. Shine a zama ta saƙaka abu a cikin kujerar ta barbaɗa wani a ƙasa. Tana fita Sakina tace Ammie kada ta tashi ta jirata tana zuwa. Zuwa tai ta ɗakko kayan shara ta kwashe maganin tas, ta ciro wanda Nazeefa ta saka a cikin kujera. Sosai Ammie tai mamaki ta kuma jinjina al'amarin. Ta kuma yarda su Sabuwa da gaske suke babu wasa a shirin nasu. Ko Daddy Ammie bata gayama abinda ya farun ba kuwa, balle Hajiya Yaya. Ta dai sake dagewa da addu'a ta kuma gargaɗi su Waleed suma. Kai daga ƙarshe ma ta saka suka dawo sashen ta da kwana suka baro nasu, dan a wannan halin tako ina Nazeefa zata iya ɓullo musu. Aiko Ammie tayi farar dabara, dan kuwa a randa tasa su Hameed suka dawo sashen nata har su Amaal data zo gidan na dariya a daren suma Baban Nazeefar ya aiko abinda za'a sakama yaran. Dan ya fahimci aikin zaima Yazeed yawa sai ya haɗa da su Waleed ɗin.... Hajiya Basariyya dai banda son ina aka tsaya ina aka kwana babu abinda ta saka a gaba. Ta kowane ɓangare kuma taƙi samun damar shiga jikin Hajiya Yayan ko Ammien balle taji. Abin na ƙona mata rai sai take ganin sun haɗe mata kai ne kawai. Gashi Daddy ma yaƙi bata fuskar yimasa batun Yazeed ɗin nan ma. Dan zuwa yanzu dai bisa dagewar Ammie ya haƙura sun koma raba kwana. Daga ita har Hajiya Yayan suna zuwa turakarsa kuma yana cin abincinsu. Basariyyar ce ma ke zumuɗin hakan, ita ko Hajiya Yaya ta kanta take, al'amarin Yazeed ya maidata shiru-shiru ga wata rama da tayi alamar abin na cimata zuciya bana wasa ba. Dan da gaske kuwa lamarin na girgiza mata zuciya, kuma Sabuwa tafi kowa bata mamaki a cikin al'amarin. Ga iyayensu sunce babu ruwansu, sanda suka ƙulla zancen yaran ai basu sani ba batun aure kawai sukazo musu da shi. Musamman ma babansu yafi ɗaukar zafi, dan har tina mata batun Maanal yayi da yanda ta katsatstsare ta dinga aibanta yarinyar da mahaifiyarta. Sai gashi yanzu Ammien ce dai tsaye a al'amarin ɗan nata da ta hana ya auri ƴarta... Ji Hajiya Yaya tai abubuwan sun mata yawa. Kamar tana jin nauyin Ammie kuma a ƙasan ranta. Amma dai a zahiri bata nuna ba, ba kuma ta furta ba. Sai dai duk shawarar da Ammie ke bata akana al'amarin Yazeed yi take yi. Yayinda Hajiya Basariyya ke bata mamaki.. Duk da kai-kawo gulma da Hajiya Basariyya keyi hankalinta kuma na'a kan Huznah ne, tama Daddy magana akan rashin jin Huznah ɗin ya nuna mata ta shiga hankalinta ta kama kanta, idan ba haka ba kuma zatasha mamaki. Da yake yanzu tana tsoron komawa gidan Kawu Manu sai tai shiru, sai dai abin na damunta a rai matuƙa, musamman daya kasance Maman Yaseerah ta mata bayanin komai har wayar da suka dinga yi da Huznah kwanaki ta kuma daina jinta ma gaba ɗaya...... ___________★ KANO. Anan Kano kuwa abu biyu ne ke shirin faruwa a ɓangare biyu. Bangaren Huznah mahaifin Sageer yace ya barta taje ganin gida dan a tunaninsu Hajiya Basariyya ta risina yanzu zata kama kanta akan al'amarin auren yaran. Yazeed dai zuciyarsa bata so hakan ba. Amma bazai iya jayayya da iyayensa ba ya amince. Amma ya roƙa alfarmar a bari har sai babbar salla dake tunkaro mu. Zuwa lokacin itama ta ƙara jin sauƙi sosai duk da dai Alhmdllh zuwa yanzu ma taji sauƙin. Shi kuma yana samun damar baje hajarsa yanda ya kamata a jikinta, sai dai taci kukanta a ɓoye da jera masa ALLAH ya isa babu damar yi a gabansa dan wani tsoronsa take ji bana wasa ba. A hakan ma sai yaga ta takura kanta da yawa ne yake ɗan sassauta mata. Ko in yaga laulayin ya takura mata, dan wani lokacin takayi lafiya na kwanaki sai kuma jikin ya rikice.. Ga kewar yan uwanta dana mahaifiyarta, dan Alhmdllh a cima babu abinda ta rasa a gidan Sageer. Duk da kasancewarsa talaka yana iyakar ƙoƙarin sa na bata abinda take ci a gidansu. Kuma duk abinda zai sakata a farin ciki yana iyakar ƙoƙarin sa yay mata gwargwadon ikonsa.... _______★ Ɓangare na biyu kuwa su Baba Sardauna da Baba, Abbah, Uncle Mahmud, Hassan, Hussain, Najeeb da wasu aminansu Baba Sardauna uku a yau suka shiga garin Katsina domin ganawa da dangin mahaifan su Ameerah. Kwarjinin Darma a idanun al'umma da yawa daban ne. Ko sunan wannan family kaji alkairansu nasa kaji kimarsu da girmansu a zuciya. Duk irin alwashi da cika bakin da dangin mijin Hajiya Shuwa suka dingayi akan sai sun nuna mata su ɗin sune a bikin Ameerah sai gashi sunyi kurum. Dan kuwa wata gaban ai tafi gaban a taka... Jikunnansu na rawa suka ma su Baba Sardauna tarba ta mutuntawa, ta girma, ta kuma martabawa. Dan kuwa cikin ikon ALLAH a cikin ƙannen baban su Ameeran akwai mai aiki a ƙarkashin asibitin Abbah. Wato KK HOSPITAL dake garin Kano. Babu wani ja'inja ko kai kawo sukace sun bama Babban Yaya Ameerah, kuma sun yarda a haɗe biki dana Fawzan nan da kwanaki goma kenan. Matuƙar jin daɗi su Baba Sardauna sunyi da wannan karramawa. A take Uncle Najeeb ya ajiye sadaki daga aljihunsa. Uncle Hussain ya ajiye kuɗin gaisuwa dana mungani muna so dama duk wani tarkacen tsarabe-tsarabe na aure. Akai huɗɗar arziƙi aka kuma rabu cikin mutunta juna da karramawa. Suma sukace suna nan tafe Kano nemawa Ameer auren Maimoon. Shi halin girma duk mai shi to mai halin girman ne. Sai kawai Baba Sardauna yace in dai haka ne wace wahala kuma. Ai kawai ayi komai anan a gama sun hutar dasu a haɗe ranar ɗaurin aure. Babbar magana. Dangin mahaifin su Ameerah fa mamaki ya sake kamasu da waɗan nan bayin ALLAH. A take sukai kiran Hajiya Shuwa suka sanar mata. Ai sai ta sanya kukan farin ciki, babu wani jeka ka dawo tasa Ameer ya tura ma kawunansa kuɗaɗe. Suma dai a take anan akai hannun karɓa kuma hannun bayarwa. Dan suma dai sun ajiye kuɗin gaisuwar Ameer da sadaki da dukkan abinda ya kamata na aure. Kafin aka sake sabuwar addu'a suka musu rakkiya airport dan dama ta jirgi suka zo. Dan haka komai da komai cikin awanni biyar aka yishi aka kammala tamkar a cikin Kano akayi... ________★ Lokacin da duk su Maanal ke dawowa aiki da wannan farin cikin suka iske Oum a ciki, su Mamy dai basu san anayi ba. Sai da su Oum da ƴayanta da RK da Matarsa dake gidan suka gama farin cikinsu da murna RK da Fawzan harda ma Babban Yaya liƙin kuɗi dan neman tsokana. Abin ya bama Oum da Maanal dariya sosai, AA kam sai murmushi yake, shi kaɗai yasan a irin kalar farin cikin da yake a ciki yau. Yayinda yake sake girmama al'amarin UBANGIJI. Wani gefe na zuciyarsa na addu'a da fatan ALLAH yasa Mamy kada ta ɗaga hankalinta akan wannan al'amari dan itace kawai damuwarsa ba wata Saheebar banza da wofi ba. Sai bayan sallar isha'i a karo na farko tun bayan bikin AA da Maanal Abah yay kiranyen meeting a sashensa. Tsoro fal zuciyar Mamy kamar tace bazata je ba ita dai, sai dai bazata iya ba, dan koba komai tana matuƙar jin kishirwar rashin ganin Abah na tsawon kwanaki. ALLAH ya jarabceta da son bawan ALLAHr nan kwarai da gaske. Zata iya yin komai akan Abah. Jiki a sanyaye ta kimtsa ta amsa kiran ita da Saheeba. Nuratu nason zuwa Mamyn ta hanata. Sanda suke shigowa kowa ya gama hallara. Abah ne kawai da Oum basu fito ba suna bedroom ɗin Abahn. Ganin harda RK da Nuwaira abin ya tsayama Mamy a rai. Amma dai batace komai ba ta zauna. Nuwaira bata taɓa damuwa da zuwa gaida Mamy ba a gidan, dan tunda RK ya bata wasu labarai akan Mamy taji ta tsani matar sosai. Haka family ɗin Darma suke akwai kishin nasu. Akan ɗan uwansu komai zasu iya maka suna son juna. Yanzu ma darajar su Babban Yaya dake a wajen taci Nuwaira ta gaisheta. RK ma dai ya gaisheta dan shi akwai iya taku, yanda Mamy ta iya fuska biyu shima baka isa sanin shike ƙullama Mamyn tsiyataku ta ƙarƙashin ƙasa ba. Suma su Maanal su Yaya Fawzan duk sun mata Barka da fitowa. Tadai danne duk tana amsawa fuska a sauƙaƙe. A haka Abah da Oum suka sakko daga sama suna dariya. Daka gansu kasan baibaye suke da kwanciyar hankali da farin ciki, ga tarin ƙaunar junansu da bata ɓoyuwa a cikin idanunsu kida a gaban ƴayansu ne. Abu mai nauyi ya tsayama Mamy a maƙoshi, haka dai ta danne sa da ƙyar Hari Abah ya zauna Oum kuma ta zauna a kusa da ita tana gaisheta fuskarta da fara'a. Dannewa tai ta amsa, Saheeba ma da tunda ta shigo babu wanda ya kulata ta gaida Oum da Abah........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣0️⃣0️⃣ ______________ .....Sai a lokacin Nibras ta shigo, duk tayi wani wujiga-wujiga itama ta rame. Itama dai ta gaida kowa sannan ta nema waje ta zauna. Aba ya fara da gyaran murya dan haka kowa ya sake nutsuwa ya bashi hankalinsa. Yay musu sallama da addu'a, kafin ya fara da faɗin, “Na tara ku anan ne domin dalilai guda biyu. Na farko nasiha a garemu baki ɗaya. Musamman akan zamantakewar gidan nan da nake ganin tana neman canja salo daga bigiren da muka ginosa na shekaru zuwa yanzu. Hakan baya min daɗi. Muɗin ahali ɗaya ne, da su da aka haifa a gidan, da ku da suka auro a wajena a yanzu duk matsayinku ɗaya ne, domin duk ƴaƴa kuke a wajenmu. Ita rayuwar aure ibada ce, daga ɓangaren mace har na namiji duk wanda ya samu raunin sauke hakkin ɗan uwansa akan ganganci UBANGIJI bazai barshi ba. Sannan kuma masu haihuwa ne, wataran zaku aurar da naku ƴaƴan ko mazan su auro muku. Dan haka ina nasiha a gareku da komai ma a ajiyeshi hakanan ya isa. Mu haɗu mu zauna lafiya da junanmu kamar yanda muka saba. Karna sake jin ko ganin wani yazo daga waje ya tada min tarzoma a gida akan abinda bai shafesa ba. Idan ba hakaba kuma zan ɗauki mataki.” A nutse suka shiga bashi haƙuri, tare da neman afuwa. Aba ya cigaba da faɗin, “Abu na biyu hidimar biki dake tunkaro mu. Kowa dai yasan an ɗaurama Fawzan aure a cikin hidimar bikin nan na Ajwaad, bata tare bane saboda exam da take yi kuma Alhamdullah ta kammala. Dan haka zamu fara shirye-shiryen tarewarta nan da kwana goma. Sai dai ba ita kaɗai bace, dan wani alkairin ya sake shigo mana. Shima Fadeel zai ƙara auren......” Wani irin kallon Abah Mamy da Saheeba sukai. Cikin rawar murya Saheeba ta ce, “Abah! Fadeel kuma?”. Wani banzan kallo Babban Yaya ya jefa mata na ki shiga hankalinki. Abah kuwa sai yay murmushi. A nutsensa ya ce, “Tabbas Fadeel Saheeba, domin ALLAH ya bamu dama mu maza muyi mace daga ɗaya har zuwa huɗu. Sai dai ba hakan na nufin ku da muka fara ajiyewa zamu wulaƙanta ku ba, ko kuma mun ƙara ne dan mu wulaƙantaku. Sam ba haka bane ba, shi ƙarin aure da son mace fiye da ɗaya a jininmu mu maza yake”. Ƙasa-ƙasa Maanal ta kalla AA, sai akai sa'a shima kallonta yake. Ganin yanda idanunta suka cika da ƙwalla sai ya shiga girgiza mata kai, tare da yi mata alamar shi dai banda shi. Ba AA da Maanal kawai ba Nuwaira nacan ta tsare RK da ido itama fuska kicin-kicin. Shima dai lallashi yake da ido dan Abah na neman ɓallo ruwa da wannan jawabi gaskiya. Duk abinda suke Abah na lure da su, dan hankalinsa nakan kowa. Sai abimma ya bashi dariya. Amma dai ya danne baiyi ba. Cigaba yay da faɗin, “Amma hakan ba yana nufin kowane namiji nada wannan ra'ayin ba. Wani ƙaddara ce take sakawa ya ƙara, wani auren dole ma ake masa da tsiya-tsiya....” kallonsa Oum tai dan tasan da ita yake kuma yanzu, aiko shima kallon nata yake, ya saki wani guntun murmushi ya ɗauke kansa. Mamy kam wani irin dukanta kalaman Abah ɗin sukayi, suka kuma shiga yimata kai-kawo a zuciyarta da tai nauyi sakamakon ambata zancen auren Fadeel. Oho Abah ya cigaba da maganarsa. “Wasu kuma sakacin matan dake gidan ne ke sakasu son su ƙara ɗin, wani kuma shi dama ra'ayinsa kenan. Kai wani jin daɗin ƙyautatawar da ake masa ma zata iya sakashi ya ƙaro dan farin cikinsa ya ƙaru. To koma dai miye sai mu zama masu tsarkake zukatanmu a komai na rayuwa. Ku dukanku shaida ne kun taso kunga iyayenku su biyu ne, kuma babu wanda zaice ga wata rana tazo suna sa'insa a tsakaninsu, ko cin mutuncin juna, ko wani abu makamancin hakan. Ina son kuyi koyi da su, domin mu haɗu mu gudu tare mu tsira tare. Hakan zai sakamu a farin ciki baki ɗaya, dan gaskiya bana son halin banza. Nayi tunanin a saka musu gini suma, sai dai guri ya ƙure mana gaskiya, dan haka kuyi haƙuri zaku fara zama a tare waje guda zuwa bayan babbar salla za'a sanya aikin nasu suma tunda muna da filin yin hakan. Akwai auren Maimoon itama da Ameer, dan haka sai mu fara shirye-shiryen dukkan abinda ya dace. Ina sake gargaɗin kowa da bana son kowane irin tashin hankali a gidan nan, mu mutunta kammu ayi taro lafiya a tashi kamar yanda aka saba. Idan ba haka ba, duk ta inda wani abu ya ɓullo to lallai Zan hukunta ko wanene da hukunci mai tsauri. ALLAH yay muku albarka. Ya bamu zaman lafiya baki ɗaya. Kuje abinku. Amma Saheeba da Nibras su zauna zanyi magana da su. Kaima Rafeeq zauna”.... _________★ Nasihar Abah ta saka kowa nutsuwa a zahiri. A bayan fage kam Mamy da Saheeba a birkice suke. Dan tunda ta koma sashenta bedroom ta shige ta kulle kanta. Bala'i ne fal a cikinta, sai dai shakkar sakamakon yinsa ya hanata fitarwa. Fin minti talatin ta gama yanke shawarar zuwa yau dai ga Abah, amma kafin haka zata fara da Fadeel ne. Babban Yaya na tsaye a compound shi da AA da Fawzan suna magana kiran Mamy ya shigo masa. Koda yaga itace bai kawo komai a ransa ba ya ɗaga. Sai dai tunda ya ambaci sunanta AA da Fawzan suka maida hankalinsu kansa sosai. Koda ya sauke wayar daga kunnensa dan umarnin zuwa kawai ta bashi ta yanke baice ma ƙannen nasa komai ba sai “Ina zuwa”. Da kallo duk suka bishi, sai kuma Fawzan ya kalla AA. “Da alama shima Babban Yaya Mamy bata son ƙara auren nan nashi”. Murmushin basarwa AA yayi, tare da faɗin, “Kai ko Yaya taya zata so ama ƴarta kishiya”. “Amma tana son aima ƴar wasu tunda tana son kai ka auri Nuratu. Ni nayi mamaki ma yau da bata kawo batun Nuratun ba”. “Maybe tayi shirun ne dan na Babban Yaya ya bata mamaki, tunda koda alama shi ba taɓa nunawa yay zai ƙara ba. Lokaci guda abin ya taso”. “Hakane kuma”. ★Babban Yaya yakai zaune yana kallon Mamy da mamakin ganin yanda ranta ke a matuƙar ɓace. Cikin kasa iya shanyewa ya ce, “Mamy lafiya kuwa?”. Bata amsa masa ba, sai ma tambaya ta jeho masa a fusace. “Fadeel wace yarinya ce zaka aura?” Kai tsaye babu wani kwana-kwana ya ce, “Ameerah ce”. “Ameerah! Wacece hakan?”. Ɗan jimm yay na mamaki, sai kuma ya ce, “Wai Mamy lafiya kuwa?”. “Tambayarka nai wacce?”. Sai da ya furzar da iska sannan yace, “Ƙanwar Ameer nan makwaftanmu ƴar Momy Shuwa”. “To baka isa ba! Ba kuma zai yiwu ba!”. Murmushi ya saki a karo na farko. Cikin girgiza kai ya ce, “Mamy dan mi bazai yiwu ba? Saboda Saheeba kike tunani ko ƴan uwanki. Mamy bazan ɓoye miki ba na gaji da halin Saheeba. Na miki iya biyya akan zama da yarinyar nan mara tarbiyya, nayi haƙuri nayi kawaici, sai dai anzo gaɓar da komai zai iya faruwa. Dan zaɓi biyu ne. Kodai ta zauna da wadda zan auro, ko kuma na saita mata hanya. Amma bazan iya haƙurin ƙin ƙara aure ba. To mima ya rage iyaye har sun shiga hatta sadaki an bada. Mamy farin cikin Saheeba yafi nawa muhimmanci ne a wajenki? Nayi haƙuri na rasa Shahidah, ALLAH ne shaida kuma har gobe ina son yarinyar nan, na auri Saheeba, tsahon shekaru bana jin daɗin zama da ita, ban taɓa zuwa na miki ƙorafi ba duk wani banzan halinta na shanye ma cikina. Yanzu kuma naga wadda zata bani salama da kwanciyar hankali saboda kar ran wata banza Saheeba ya ɓaci sai na haƙura Mamy. Oum ta bani goyon baya, Abah ya bani goyon baya, miyyasa ke bazaki bani ba? Dan tana ɗiyar ƴar uwarki?. Gaskiya kimin afuwa babu abinda zai hanani auren nan sai dai idan na mutu ne kafin kwanakin”. Daga haka yay shiru ransa a matuƙar ɓace. Ai mutuwar tsaye Mamy tai tana kallonsa. To ashe gwara-gwara Fawzan ma. Tana ganin AA yafi Fawzan, to ashe Fawzan ma mai biyayya ne. Dan gaba ɗaya ma Fadeel yau ya juye mata ne kamar Abah. Wlhy saima taji ta rasa abinda zatace masa. Sai wani irin tsuma da jikinta ke mata. Zuciyarta kam zafi take mata, gashi tai nauyi a cikin ƙirjinta... Dai-dai nan Saheeba ta shigo tana sharar hawaye. Ganin Babban Yaya zaune sai ta tsaya tana kallonsa kukan na sake kufce mata. Ƙasa takai durƙushe, tana ƙara fashewa da kuka ta ce, “Dan ALLAH na tuba Daddyn Naufal, dan ALLAH kada kamin kishiya, wlhy na rantse maka zan canja, duk abinda kake ganin inayi baka so zan daina shi. Dama bayin kaina bane Mamy da Mama ke sakani yinsu. Amma wlhy bazan sake biye musu ba....” Da wani irin sauri Mamy ta kalla Saheeba, har taune harshe take wajen faɗin, “Saheeba! Wace banzar magana ce wannan. Nice ma zan sakaki ki masa halin rashin arziƙi?”. Babu ko ɗar Saheeba ta ce, “Wlhy kece Mamy, ke da Mama kune ke tsara komai kuce nayi saboda na ƙwato muku shi daga hannun O......” Ai wani irin tassss!!! Kake jin Mamy ta saukewa Saheeba mari. Zata ƙara magana ta sake ɗauketa da wani marin na biyu. Sannan ta ce, “Wawuya kawai, kin haukace ne? Kodan mijinki zai aure sai hankalinki yabar jikinki har ki kasa tauna maganar dake fitowa daga bakinki. To idan kin manta bara na tuna miki nice na haifi Fadeel har kika aura shashasha”. Tsam Babban Yaya da mamaki ya kashe ya miƙe. Raɓasu yay ya fice abinsa zuciyarsa na matuƙar jinjina al'amarin Mamyn da Saheeba. Mizai saka Mamyn harzuƙa haka dan Saheeba tace sune suke sakata yin abu. Sannan a ina za'a ƙwatoshi kuma? To shi koma dai minene su suka sani, aure dai kam in sha ALLAHU babu fashi sai yayi. Ita kuma ya rage nata ta gyara ko ta cigaba da yin abinda tai niyya shima zai fara yin wanda yay niyya kuwa. Dan yanzu ya ɗauki ɗammarar saitata a layi. Abinda ya ɗauka a baya ko kwatarsa bazai ɗauka a yanzu ba daga garetan............✍️ 😂😂Hajiya Mamy yada haka kuma. Marin surukai fa baida ƙyau gaskiya🤣. *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣0️⃣1️⃣ ______________ .....A wannan dare dai Mamy bata iya ta tunkari Abah ba, dan Babban Yaya da Saheeba sun fusata ta. Sai washe gari da safe suna shigowa daga massallaci tai dakonsa. Dan suna fita dama ta fito a nata sashen sai ga Oum ta fita daga sashen Abah ɗin dan dama ita haka take yi. Sai kawai tai wuff ta shige ita bayan ta gama zagin Oum da tsine mata a zuciya. Anan falon Aban tai sallar asuba. Ta cigaba da zaman tsammanin dawowarsa har suka shigo. Koda Abah ya shigo ya ganta ɗauke kansa yay tamkar bai gantan ba. Sai taji gaba ɗaya ta sake rikicewa. Amma haka ta daure tace masa ina kwana. Idan bangon ɗakin ta tanka shima ya tanka. Jikinta na ƴar tsuma ta tari gabansa, muryarta na rawa tana kallonsa da idannunta da suka kaɗe ta ce, “Dan ALLAH kayi haƙuri ka saurareni ko sau ɗaya ne. Wlhy-wlhy ba abinda kake tunani bane ranar zan gaya maka gaskiyar komai, Fadeel ne......” “Kinji nace miki ina buƙatar sanin miya faru ne?”. Abah ya katseta babu alamar hayaniya a muryarsa. “Kayi haƙuri dan girman ALLAH. Zan maka bayani koda bakace kana buƙatar ji ba ko hakan zai sa ka sassauta min. Wlhy a duniyar nan fushinka shine mafi ƙololuwar tashin hankalina fiye da komai kaima ka sani”. “Ni a suwa da fushina zai zama ƙololuwar tashin hankalinki Kamila. Idan ma shi ɗinne kwantar da hankalinki baki da matsala dani. Duk abinda kike tunanin dai-dai ne ƙofa a buɗe take kiyi abinki.” ya ƙare maganar da raɓata zai wuce. Da sauri ta riƙo hannunsa tana fashewa da kuka. Fisgewa yay ƙoƙarin yi ta riƙesa da hannu biyu duka da iya ƙarfinta kuma. “Amma kin san zan iya marinki ko?”. “Gara ka marenin, wlhy gara ka mareni da wannan fushin dai da kake yi dani. Ka tausaya min dan ALLAH ka duba min, wlhy ji nake kamar zuciyata zata tarwatse.” kuka mai ƙarfi ya sarƙeta. Shiru kawai Abah yay yana kallonta. Kamar wanda ya fahimceta sai kawai jitai ya zare hannunsa yay gaba. Sai da yaje zai shiga bedroom a kausashe ya ce, “Ki gayama ƴan uwanki akan wannan bikin wlhy-wlhy duk wanda ya nema ɗaga hankalin iyalina nima sai na ɗaga nashi. Ba kuma lallai dole bane sai ƴaƴana sun zauna da ƴaƴansu. Hanawa su ɗauki wani mataki akan yaran adalcina ne, amma a wannan gaɓar duk wadda tace zata kawo musu shirme zan basu damarsu ta ɗaukar matakin da duk sukai niyya dan ina son farin cikinsu. Dan ko kece kika ce zaki ɗaga musu hankali sai dai ki bar musu gidan ubansu. Idan kunne yaji jiki ya tsira”. Yay shigewarsa. (Dan ko kece kika ce zaki ɗaga musu hankali sai dai ki bar musu gidan ubansu) Wannan kalma tai matuƙar dukan zuciyar Mamy da girgiza mata duniyarta. Ta kuma fahimci eh lallai da gasken gaske Abah yake yi. Itako ta shiga uku, shin mike faruwa ne? Anya kuwa? Anya ganin da Abah yay musu sun fito a sashen Ajwaad ne kawai matsalar kuwa? Kai da mamaki gaskiya, akwai lauje cikin naɗi. Dole akwai wani abinda ke a ƙasa. Batun Ajwaad da Maanal ya faɗo mata a rai. To kodai binciken da take tunanin zasu iya yi suka yin ne?. To amma ta ina? Inma zasu bincika ai Doctor ne kwai, jiya jiyan nan kuma Hajiya Turai ke sanar mata a binciken da tai Dr Tofa ma baya Nigeria kusan shekara biyar kenan. To kodai munafukar matar can ce tai mata wani ƙullin?. Zuciyarta tafi tsayawa a hakan, sai dai hujjar ta mata rauni da yawa. Amma ko akan batun auren nan ta tabbata akwai saka hannun Fateema. Kenan dai Fateema ta cita wasa. Ajwaad ya auri ƴar ƙawarta, Fawzan ƴar ƙanwarta, ga Fadeel ma zai auri ƴar ƙawarta. Shike nan yaƙinta na shekaru ya tashi a banza. Tunda ga Saheeba nata auren na rawa, Nibras ma bata sakata a sahun mata ko wanda take amfana. Auren Nuratu na tangal-tangal. Tana a ruwa fa kenan har yana shirin zuwa mata wuya idan bata tashi tsaye ba. Ga wancan batun duk da tana ƙoƙarin hidden ɗinsa yana nan daram a ranta, yana kuma cimata zuciya..... ________★ Anan ɓangaren Oum kam shirye-shiryen biki suke hankali kwance. AA ya riga yay order ɗin kayan lefen Fawzan tuni, yanzu kuma gana babban Yaya. Duk da zai iya yin hakan shima saboda kawai yaje ya ɗan huta da tashi amaryar sai suka tsiri tafiya Dubai wai haɗo lefe shi da RK da Maanal da Nuwaira. Sarai Oum ta fahimcesu, dan haka batace komai ba face binsu da addu'a. Shima Abah koda suka faɗa masa addu'ar yayi. Dan daga shi har Oum ɗin ƴan ba ruwa na ne. Haka kuwa suka shirya suka tafi, suka bar su Oum kuma anan Nigeria suna shirin fara gyara amare ita da Hajiya Shuwa. Sai dai ita Najma ma can wajen Ammie zata zauna nata gyaran. (Kun san dai itama Ammie tsohuwar mai gyaran jiki ce) Dan haka Hajiya Shuwa data haɗa duk abinda ake buƙata aka aikama Ammien, itama kuma daga can Ammien ta aiko musu da tata basirar da za'ama Ameerah da Maimoon da itama ta dawo nan Abujan amma a sashen Oum zata zauna dan ba'ayi abin kunya suruka Hajiya Shuwa tayi gyara ba.. Babban Yaya da Yaya Fawzan kuma sai suka maida hankali a gyaran sassan nasu. Amaren zasu zauna a downstairs kafin a gama musu nasu ginin. Amma duk da haka sai da aka gyara duka sashen biyu. Hakan yasa Nibras komawa sashen Oum da zama. Saheeba dama har yanzu tana a sashen Mamy. Duk da dai sunata zuba rikici ita da Mamyn, dan kota sakata abu yanzu batayi. Mamanta da itama ta tadama Mamy hankali tace Saheeba ta taho gida amma Saheeban tace babu inda zataje, dan Babban Yaya ya rantse mata indai ta fita a gidan ta fita kenan na har abada. Hajiya Turai ce da ƙyar ta sasanta Mamy da Maman Saheeban. Ta kuma nuna musu illar bari kan nasu ya rabu. Acewarta a yanzu ne ma ya kamata kansu ya haɗu suyi yaƙi na gaske dan abaya wasan yara sukayi. Fargarwar tata ta shigesu, dan haka suka sasanta ɗin itama Saheeban mamanta ta ƙwaɓeta. Ita kuma ta bazama gidan bokaye da malamai neman sa'a... _______★ Rayuwa a Dubai ta sati ɗaya kacal rayuwa ce mai tsayawa a zuciya da ɓargon jiki tsakanin Maanal da AA. Hakama Nuwaira da RK ba'a barsu a baya ba. Ƙara'in amarci akai sosai mai kuma ƙayatarwa. Sunyi wani fresh abinsu musamman Maanal data fara shiga wani yanayi na biyema fitinar AA. Shi kanshi har mamaki abin ya fara bashi. Tana shan wahalar amma tana nane da shi yanzu ba kamar da ba. Takai wani lokacin ma ita da kanta take takaloshi koda zatai masa rakin daga baya. Ranar dai suna hira shi da RK Maanal da Nuwaira kuwa sun fita kasuwa dan yau su AA ɗin sunce sun gaji sukam, sai AA ke ɗan yima RK tambaya akan hakan. Murmushi RK yayi dan shikam tun a Nigeria ya fahimci Maanal nada shigar ciki. Amma rashin tabbas ya sashi yin shiru tunda mata nada abubuwan ban mamaki a tattare da su. Cikin nuna rashin tabbas RK ya ce, “Ciki zai iya saka mace hakan, dan wani lokacin idan suna da ƙaramin ciki sukan buƙacemu a kusa da su fiye da ko yaushe. Dan a farkon aure gaskiya mune zaka samu muna zalamarsu amma su ba sa jin daɗin yanayin gaba ɗaya wahala tafi yawa. Shiyyasa sukafi son a tsaya iya romancing kawai. Wata macen zata iya maka haihuwa uku sannan ta fara sanin muhimmancin yanayin. Wata ɗaya, wata biyu wata ma har biyar. Idan kuma ba'a haihu da wuri ba zakaga an ɗauki shekaru, bawai basa so bane gaba ɗaya, a'a badai kamar mu ba, doke zaka ga dai sai sunja shekarun nan sannan komai me daidaita musu. Sai dai idan suna shan ƙwayoyin saka ƙarfin sha'awa ne ko wannan kayan nasu na mata” Cikin gamsuwa AA yake jinjina kansa. A ƙasan zuciyarsa kuwa wani irin farin ciki yake ji da fatan ALLAH ya tabbatar da hasashen RK ɗin na batun cikin ne bawai shan maganin Maanal keyi ba duk da dai bai taɓa gani ba. RK da duk ke lure da shi ya ce, “To amma fa kaima sai ka ɗan sassauta a irin wannan yanayin. Dan in har hasashenmu ya zama gaskiya cikin ne ALLAH zaka iya ɓaro shi. Ka aikata hakan kuma ba yafe maka zamuyi ba”. Harararsa AA yayi, sai kuma ya ɗauke kai gefe da faɗin, “Shiyyasa bazan taɓa Kawu da kai ba dan kawun banza ne anan”. Dariya RK ya shiga yi. Dole AA ɗin ya tayashi da murmushi. ★ Satinsu ɗaya suka dawo Nigeria, a kallo ɗaya kuma Oum ta tabbatar da hasashenta akan Maanal. Dan komai na jikinta ya ƙara canjawa a sati ɗayan nan. Sai wani mahaukacin ƙyau takeyi da haske. Sai murmushi ya kasa barin fuskar Oum, duk motsinta addu'a take na ALLAH ya tabbatar da hakan. Da ƙyar ta iya danne zuciyarta bata gumtsawa Abah ba........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣0️⃣2️⃣ ______________ ....Washe garin da suka dawo wasu cikin ƴan Kano suka iso Abuja. Dan za'a kai lefen Najma Zaria. Koda Maanal ta nuna zataje AA yace bai yarda ba. Dan tunda RK ya masa kanta farga yake wani kaffa-kaffa da al'amarin Maanal ɗin duk da ba tabbas. Koyaya yaga zatai wani aikin da zai jijjiga mata jiki yanzu zai amshe gara shi yayi. Tunma yana yi a su kaɗai harya kasa daurewa bai iya kawaicin hakan ko a gaban Oum. Ita ko Oum babu ruwanta, irin wannan abubuwan kawaicema yaran nata take tayi kamar bata gani ba. Dan farin ciki hakan ke bata akan kulawar da suke bama matan nasu. Kamar wasa rigima ta kacame akan zuwa Zaria. Dan AA ya dage kuma ya ɓata rai a yanda Maanal ɗin bata taɓa gani ba. Ita kuma ta rigime akan sai taje sai masifa take masa kamar dama jiranshi take yi. Kuma tana masifar tana kuka. Takaici ya sashi yinƙurin baro mata sashen gaba ɗaya. Amma sai ta biyoshi yana gab da fita ta riƙeshi wai wlhy bazai fita ba. Tsayawa yay yana kallonta, fuskarsa babu alamar wasa ya ce, “Sakeni”. “Anƙi ɗin”. Ya faɗa a fusace. Sai ma ya rasa mi kuma zai yi. Dan kallon ma abin yake a matsayin rainashi ta farayi ne ko mi bai san yazai fassara ba. A wani kuma gefe na zuciyarsa yana ƙara yarda lallai mata zuma ne ga zaƙi ga harbi. Duk yanda kake da su idan suka kuma maka wani takaicin sai kaga kamar basu taɓa ma saninka ba. Wannan yanayin dakan gitta lokaci zuwa lokaci shine iyaye kullum ke tisa mana kalmar haƙuri a kansa, sai anyi haƙuri da mata sai anyi haƙuri da mata. Idan ka fusata ka zafafa su kuma matan su kalleka a matsayin namiji ba ɗan goyo ba. Jiba fa ƴar ficiciyar yarinyar nan daya raina da hannunsa ce yau take neman birkita masa lissafi gaba ɗaya. Ƙiri da muzu yace baza'ai abu ba tace sai tayi. Yayi yunƙurin bar mata gidan yaje ya ɗan huce ta masa ɗaurin goro tana mazurai wai bazai fita ba kai kace itace Oum. Oh shi ɗan Aliyu da Fateema yau yaga takansa. Kallonta ya sake yi, yanda take hura hanci wlhy saika ɗauka duka zata lakaɗa masa. Anya a duniyar nan akwai wanda yakai mata ƙarfin hali kuwa. Ka gansu abu ba abu ba amma fitinarsu da rikicinsu yafi na yaƙin basasa girma. Nan kuma anjima fa idan ta huce sai ta rungumeshi ta masa kiss ƙauna ruwa-ruwa. Nisa'u na rijalu kenan..... “Ni ka daina kallona”. Maanal ta faɗa tana fashewa da kuka. Ajiyar zuciya ya sauke, cikin daidaita nashi yanayin ya kama hannun nata ya jata suka koma cikin falon, zaunar da ita yay shima ya zauna. Idanunsa na binta da kallo mai tausasawa ya ce, “Na zauna yanzu mi kike so ayi?”. Sai da ta share hawayenta sannan tace, “Ni ka barni naje”. “Besty kima daina ɓatawa kanki rai da batun tafiyar nan dan bayinta za'ai dake ba. In da ace jirgi ne sai na barki, amma tafiyar mota daga nan Abuja har Zaria badani ba wlhy. Ban shirya asara ba gaskiya. Zaɓi dai wani abun”. “Ni ba abinda nake so, Zaria kawai nake son zuwa. Da da nake tafiya a motar miya saman, sai yanzu zakace wani bazanje ba bayan kuma kowa zaije. A can Dubai wane irin yawo ne bamuyi a mota ba sai anan da yake kana jin mugunta..” Wai yana jin mugunta abin dariya. Dannewa yay cikin lallashi ya ce, “Ki gane mana Besty, titin Nigeria dana Dubai ai ba ɗaya bane b.....” Baima gama ba ta sake fashe masa da kuka tana faɗin, “Ni ban yarda ba! Ni ban yarda ba. Kawai sai naje! Sai naje”. Shi kam yau AA yaga bala'i ai ganin idonsa. Wlhy ta birkice masa gaba ɗaya kamar ba Maanal ɗin ba. Sai kawai ya zuba mata ido ma yana kallon ta. To sai kuma sabon masifa, ita dan mi zaiyi banza da ita. Dan mi tana magana zai yi shiru. Ita bazata yarda ba, ita miye-miye.” Da yaga abin bana ƙare bane sai ya fara tunanin hanyar da zai gudu. Can dabara ta faɗo masa. Sai yay ɗan gyaran murya yana miƙewa da faɗin, “Bari na kawo miki ruwa ki sha sai muyi magana naga yanda za'ai tafiyar ta yiwu, in ma ni zan kaiki sai na kaiki da kaina”. Da farko riƙeshi tayi, sai kuma ta sake shi tana share hawaye ta ce, “Kuma mara sanyi nake so, ka haɗo da fresh milk mai sanyi ka saka min inibi da dabino a ciki”. “An gama Aunty”. Ya faɗa yana nufar hanyar kitchen. Haɗa mata duk abinda tace tana so yayi, ya buɗe back door ya gudu. A can compound ya samu su Naufal na ball da yaran maƙwafta, sai ya kirashi yace yabi ta back door ya ɗauka abu nan akan work table ya kaima Auntynsu falo tana jira. Shi kuma ya shige mota yabar gidan. Gara yaje ko zagaye gari yayi idan ta huce ya dawo. 🤣🤣AA bawan ALLAH yau Nisa'u sun nuna maka hali kenan😂? Maanal karfa kisa mu Aurama brozan su o'e Nuratu fa. Koda yake ki kiyayi ranar da suka Rijalu zasu murɗa nasu kambun rigimar tommm😂. ________★ A lokacin da AA ke fita anan ɓangaren Mamy ta fito wanka ne ta samu wayarta na ringing. Koda ta duba taga number ce kawai babu suna ajiyewa tai tana jan ƙaramin tsaki. Sai dai me kiran sai ya cigaba da shigowa babu ƙaƙƙautawa harta ji haushi ta ɗaga a fusace. Tana fara masifa Sille ya wani kwashe da dariya daga can. Sai tai tsai tana saurarensa zuciyarta na bugawa dan ta gane sa. A ranta tace ubanwa kuma ya bama wanan ɗan iskan number ta. A fili kam cikin ƙarfin hali ta ce, “Malam waye kai?”. “Ai kin san waye ni Mrs Darma. Karki wani yi pretending. A tunaninki kin kashe waccan wayar kin tosheni ke nan. To ai abinda baki sani ba ni kamar kurege nake bana hanya ɗaya. Hanyoyine dani kashi-kashi harta inda bakiyi zaton zan fasa ba. Ina muka kwana ina muka tashi? Bake ba kuɗina mike faruwa?”. Tsaki mai kauri Mamy taja. Cikin dakiya ta ce, “Kai bari kaji na fika iskanci wlhy, kai ubanwaye daka isa ka sani yin abinda banyi niyyar yi ba. Anƙi a baka kuɗin, kuma anƙi a yarda a ganka ɗin yi duk abinda kaga zakayi”. Wata irin mahaukaciyar dariya Sille ya sanya daga can. Tare da faɗin, “Oh haka kikace? Shike nan zanko baki mamaki. Amma bisa wasu dalilai zan baki dama ta mintuna talatin yanzun nan kacal. Koki fito yanzu ki sameni a bayan gidanku da kuɗina 10m, ko kuma yanzu na nuna miki ni bana magana biyu, dan zaki ganni har cikin ɗakin barcin ki, sai ki fara ƙirga lokaci.....” Ƙittt ya yake kiran. Ba ƙaramin bugawa zuciyar Mamy tayi ba. Tai shiru kamar mai nazari tsahon sakanni sai kuma ta taɓe baki da faɗin, “Ɗan iskan banza, su masu gadin dake gate ɗin wawayene irinka da zasu barka ka shigo har nan”. Hankali kwance ta shiga shafa manta. Kafin ta miƙe ta nufi closet ɗinta dan saka kaya. Harda su kallon agogo kuwa tana sake jan tsaki. Ta gama shirinta tsaff ta fito dan gidan wata tsohuwar aminiyarta take son zuwa. Da bala'in sauri tai baya zata fasa ihu jikinta na rawa saboda ganin mutum zaune a bakin gadonta. Sille dake kallonta yay wata shegiyar dariya da faɗin, “Haba relax mana Mrs Darma. Sai kace bake ɗin ba.” A rikice matuƙa Mamy ta nufi ƙofa, ta danna mata key sannan ta dawo inda yake. Bakinta har rawa yake ta ce, “Ubanwa ya shigo da kai har nan?”. “A ƙafafuna mana. Ai na faɗa miki ni bana magana biyu kamar ubana nake.” “Waye uban naka? Kai wanene ma kai? Mi kake so a wajena?”. “Tofa irin wannan tambayoyi haka wacce zan amsa a ciki”. Sai kuma ya zame hular rigarsa data rufe masa fuska yana cigaba da faɗin, “Kalla fuskar baƙya buƙatar bayani”. Kaɗan ya rage Mamy kuwa ta zube ƙasa tsabar razana. Junaid fa take gani, Junaid dai Junaid. Amma taya Junaid zai cigaba da zama a iya wannan shekarun har yanzu. Wannan fa bazai wuce talatin da tara ba haka. Dan zai girmi Fadeel gaskiya kamar da shekara biyu ma. Jiri ke neman ɗibarta ga numfashinta sai wani fisga yake da ƙyar. Shi dai Sille kallonta kawai yake. Sai da yaga kamar zata sume sannan ya miƙe zai kamata. Hannunsa ta bige tare da faɗin, “Karka taɓa ni”. Hannayensa ya ɗaga sama tare da ja baya ya koma ya zauna inda ya tashi, itama ta daddafa ta kai zaune cikin sofa, ruwan dake a saman table ta ɗauka tasha tana hakki ga idanunta sunyi jazur. Da ƙyar ta iya sake furta, “Wanene kai? Miya kawoka waje na?”. Murmushi Sille yayi mai haɗe da dariya. Sai kuma ya taɓe baki da faɗin,.....✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣0️⃣3️⃣ ______________ .......“Zuwa yanzu ko baki san wanene ni ba kin san daga ina na fito. Kin kuma fahimci zan iya aikata komai idan baki min yanda nake so ba. Sunana Junaid ibn Junaid, kuma ɗan Kamila”. Da wani irin razani Mamy ta kallesa yanzu ma har yawu na neman sarƙeta ta ce, “Wace Kamilar?”. “Bayan ke akwai wata Kamila anan ne? Ki maida tunaninki baya, 39years da suka wuce, ranar lahadi ƙarfe sha ɗaya da arba'in na daren litinin, cikin kangon jikin makarantar allon Malam Bello ɗan Bichi dake bayan anguwarku. Budurwa ƴar kimanin shekaru goma sha bakwai, ana ruwan sama mai yawan gaske, ita kuma tana durƙushe tana naƙudar haihuwa data fara tun yammaci, fahimtar haihuwa zatai ya sata zuwa wannan kangon ta ɓuya, bata sha wata wahala ba ta haihu, tsabar taurin zuciya ta yanke cibin jinjirin da kanta sannan ta naɗeshi a zani ta koma gefe ta huta batare da ko kallonsa tayi a matsayin sa na wanda ya fito a jikinta ba, kafin ta tashi ta sake ɗaukar jaririn ta fita a cikin dai wannan ruwan ta tafi can bayan layinsu a ƙafa ko tsoro bata ji ta tona bola ta ajiye shi. Babu ko tausayi balle imani a tare da iya ta zuba tarin bolar nan a kansa ta rufe ta juya tabar wajen ranta ko gezau babu na nadama balle jin tausayi ta koma gidansu. A zatonta shike nan shike nan tayi AJIYA A DUHU na har abada, sai dai kuma shi ALLAH babu ruwansa, yayi alƙawarin saina more wannan duniyar, harna taka ƙasa nazo inda take da ƙafafuna a yau a yanzu..” Tunda Sille ya fara wannan bayanin jikin Mamy ke mazari. Zufa kam ba'a magana tai mata sharkaf. So take tai magana amma ta kasa, dan gaba ɗaya lissafinta ya birkice... Sille dake kallonta ya wani kwashe da dariyar ƙeta yana miƙewa. “Bara na barki haka, dan na fahimci ƙwaƙwalwarki na buƙatar yin cikakken tunanin daya fi wannan bayanin nawa. Kuɗina kuma daga yanzu zuwa safiyar gobe ki tabbatar kin haɗa min su. Idan ba haka ba zan sake dawowa na amsa da kaina, idan na dawo kuma zan fara ganawa da Alhaji Aliyu Darma ne kafin ke. Dan ya kamata shima fa ya tuna da abokinsa na yarinta Junaid, ya kuma san alaƙar Kamila da Fateema ta asali. Na barki lafiya mahaifiya”.... Iya kwatanta muku Mamy a cikin tashin hankalin da take ciki abu ne mai wahalar gaske, kawai dai kowa ya ƙiyarsta a ransa, dan kuwa Sille ya tafi ya barta a wani irin mummunan yanayi ne mara kwatankwacin kintace. Binne sirri mai girma irin haka a kai kaɗai batare da kowa ya taɓa sani ba, sai bayan tsahon shekaru kwatsam wani yazo yace maka shine wannan sirrin naka, har ya labarta maka exactly abinda ya faru a shuɗaɗɗen yanayin, bayan kayi imanin babu wani mahaluki daya ganka, tunda gashi har tsawon shekaru babu wani daya taɓa kwatanta maka ya sani ko'a fuska, shi kuma wannan yaron jariri yake sabuwar haihuwa da baya magana baya gane komai ai ruɗanin bashi da kwatankwaci. Yo ko gulma kayi da miji ko ɗa ta fita ya kake shiga ruɗanin mamaki balle irin wannan na Mamy, ai sai ka rasa ina zaka kama ina zaka riƙe ma gaba ɗaya. Ga zancen Sille ya tabbatar mana akwai alaƙa tsakanin Abah da Junaid ubansa, kenan dai akwai AJIYA A DUHU tsakanin amintakar Kamila da Oum ma tun asali tun fari. Babbar magana. Kumuje zuwa kudai, sannu a hankali komai zai warware kansa dai.... ____★ Motar AA dake dawowa gida na shigowa gida Sille na ficewa. Da mamaki yake kallonsa, duk da ba fuskarsa ya gani da ƙyau ba kamar a gidan Hajiya Turai. Amma gaba ɗaya zubin mutumin da wata tafiyar rangajin tantirai da take bata mai ba. Kasa haƙuri yay sai da ya tambayi maigadi wanene?. Kai tsaye maigadi yace, “Ranka ya daɗe mai gyaran ruwa ne. Pipe ne ya fashe a sashen Hajiya ƙarama shine ya gyara.” Jimmm AA yay yana kallon Sille da yay nesa da gidan kaɗan ta cikin mirror ɗin motar, a ransa yana jinjina kalmar mai gyaran ruwan ƙwarai da gaske. Dan zubin mutumin sam bai masa kama dana mai aikin arziƙi irin wannan ba. Amma sai bai takura ba yaja motar ya shige ciki. Tarkacen daya sayoma ƴar rigimarsa ya ɗiba ya wuce sashensu. Samunta yay tana barci anan falon inda ya barta, ya sauke ajiyar zuciya yana girgiza kai. Kitchen ya wuce da kayan ya ajiye komai a inda ta dace, sannan ya dawo ya kwashe abubuwan data baza na ciye-ciyen da tayi suma yakai kitchen ɗin ya ɗauraye na wankewa ya ajiye na ajiyewa. Koda ya dawo ɗaukarta yay gaba ɗaya ya haura sama da ita. Dan yasan wannan kuma barcin in sha ALLAHU ita da farkawa sai kusan sha biyun dare, koda yayi barci shima sai ya tashi saboda wanka kawai take yi da salla tazo ta kanannaɗe jikinsa. Tana samun yanda take so zata sake komawa barci. To daga fa sallar asuba kuma bazata sake kwanciya ba sai wata yammar kamar wannan, idan kuma anyi sa'a ta daure yanayin magrib zata kwantan. Oum ma data fahimci yanayin nata ko nemanta batayi idan yamma tayi taji shiru. Wani lokacin kuma acan sashen take barcin sai sun gama hira da cin abincin dare yake ɗakkota su dawo nan.. ______★ Washe gari tunda wuri ya mata wayo suka bar gidan zuwa MAWAAD. Ta haka ne ƴan kai lefe suka tafi lafiya bada saninta ba. Lokacin da suke dawowa gida bayan la'asar kuma sama-sama ta gaida Oum ma ta shige bedroom ɗinta ta kwanta sai barci. Da daddare sunyi zaman cin abinci Babban Yaya ke tambayar Lilly fa? Dan tun jiya rabonsa da ganinta a gidan, kwana biyun nan kuma ya fahimci Nuwaira da Oum ke girkin dare banda Maanal ɗin. Oum ta ce masa tana barci a ɗakinta tunda suka dawo aiki. Dan ko sashensu ma bataje ba. Mamaki ya kama Babban Yaya, yace, “Bata da lafiya ne? Barcin yamma haka”. Kafin Oum tai magana Yaya Fawzan da bakinsa baya iya shiru ya ce, “Anya Babban Yaya Lilly na lafiyar nan kuwa?. Barci dai barci dai maybe akwai malaria tare da ita”. RK dake danne dariyarsa da ƙyar yay fuska da faɗin, “Sai fa malaria ɗin. Saurayen ne na yanzu ɗika-ɗika, da sun ciji mutum kuma sai ciwo ba sauƙi. ALLAH dai ya ƙaremu da lafiya”. Harga ALLAH Oum bata gane shaƙiyancin RK ba. Kai shi kansa Yaya Fawzan bai hasko komai ba sai da yaga babban Yaya yayi wani miskilin murmushi kawai. AA ma da bai fahimta ba da farko ya ce, “Inaga ya kamata ai feshi a gidan nan gaskiya. Dan ɗan zaman da mukai jiya a waje nima sai da naji kamar zanyi zazzaɓin alamar nasha cizo”. A wani ɗage RK ya ɗan dubeshi ya ce, “Ai tunda baka kwanta ba da alama kai naka cizon na musulmin sauro ne. Wanda ya ciji ƴar gidan Oum dai kamar yafi iya cizo”. Yanzu kam sosai AA ya kallesa, hakama Yaya Fawzan. Ido RK ya kashema Fawzan. Yaya Fawzan ya kwashe da dariya dan ya gano kam yanzu. yace, “Ohhhhh na gane na gane, lallai wanan sauro kam ya iya cizo gallari”. Sai suka sake kwashewa da dariya shi da RK. Ƙasa-ƙasa suke zancen shiyyasa Oum bata jinsu. Shi kuma AA a tsakkiyarsu yake. Babban Yaya na kusa da Oum. AA da sai yanzu ya fahimci inda iskancin nasu ya dosa ya girgiza kai kawai. Bai sake magana ba saboda Oum da babban Yaya dake wajen, amma yayi alƙawarin sai ya rama su duka.. ________★ Washe gari ƴan Kano da suka rabu biyu wasu suka tsaya Zaria gobe idan ALLAH ya kaimu zasu taho da amarya Najma, wasu kuma suka wuto nan abuja dan anan za'a ɗaura auren Ameerah da Maimoon dan sauƙaƙama mutane. Zasuyi tafiyar yamma ne saboda bikin da zasuyi suma can Zariya, anan kuma Abuja gobe za'ai kamu in sha ALLAHU anan gidan Darma. Asabar a ɗaura aure ai dinner, lahadi walima da safe, da yamma ai buɗar kai shike nan amare su shige daga ciki. Ƴan Kano na gama hutawa aka kai lefen Ameerah. Lefen ya ƙayatar da kowa dan su Maanal sunyi ƙoƙarin saka abubuwa na girma. Sosai kuma Hajiya Shuwa da ahalinta da suka iso da ƴan Katsina suma da sukace komai ya wuce suka dai-daita da Hajiya Shuwan tun kai kuɗi da su Baba Sardauna sukai. Tukuyci mai tsoka su Maanal suka samo. Babu dai dangin Mamy ko ɗaya a ƴan kai lefe hakama Nibras ko ƴan Kano bata zo ta gaidar ba. Suna dawowa daga kai lefen Ameerah aka kuma biyosu da lefen Maimoon. Hummm shima dai su Hajiya Shuwa sun rigirgiza kayan arziƙi sai dai ace sambarka kam. Sai kuma abi ma'auratan da addu'ar zaman lafiya da zuri'a masu albarka. A ɓangaren Mamy yaƙe kawai take da dauriyar dole har ta fito ta gaishe da ƴan Kano su Mah-mah, dan su Umma sune a Zaria zasu taho da amarya Najma gobe idan ALLAH ya kaimu........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣0️⃣4️⃣ ______________ .....A yanzu gaba ɗaya hankalin Mamy ba'a kan auren nan yake ba. Dan Sille ya gama rikita mata al'amari gaba ɗaya. Amma dai tana ta ƙoƙarin danne yanayin ta dan bata fatan kowa ya san halin da take ciki a wannan gaɓar. Abinda ya bama Abah mamaki yanda ta sake ba kamar bikin Maanal da AA ba. Amma dai baice komai akan hakan ba. A ɓangaren Sille kam a yanzu itace mai nemansa a waya ruwa a jallo. Amma abin mamaki kaf layukan da yake kiranta da su bata samunsa. Tun a daren ranar ta bashi 10m daya buƙata, dan ta fahimci zai yi dukkan abinda ya ambata. Amma ta saka ana mata bincike a kansa dama Junaid, duk da ita tafi kowa sanin abinda ta aikata ma Junaid ɗin. Amma hankalinta yaƙi kwanciya sam. Tana son fita a gidan tana tsoron idon mutane, wani gefe na zuciyarta kuma na tunatar da ita idan ma ta fita ɗin ina zata samo Sillen. Tunda shi dai ba wani waje da yake zaune ta taɓa sani ba. Haka dai ta daure tana sauraren sakamakon binciken data saka anai mata akan Junaid..... ________★ A washe garin da za'a iso da Najma da ƙyar Oum ta lallaɓa Maanal sukaje saloon. Wankin kai kawai ta yarda akai mata, kitso sai ta sakama Oum kuka. Ƙyaleta tayi suka dawo gida akai zaman mata ƙunshi ja da baƙi. A lokacin su AA da zasu ɗakko Najma nata shirin wucewa. Ya shigo sashen Oum ɗin cikin tsokana yace mata saura kitso ta sanya masa kuka. Ita Oum ma sai abin ya bata dariya, ta dai gimtse batai ba. Sai ma ta harari AA da shima yake danne dariyar da ƙyar. “Yanzu dan ALLAH Auta banda neman faɗa ina ruwanka. Munce maka muna son kitso ne.” AA dai ya sake danne tasa dariyar da ƙyar ya ce, “ALLAH ya baku haƙuri Oum nayi shiru. Bani keys ɗin in dai nine yanzu zan yi gaba”. Oum na bashi maimakon ya tafi da arziƙi sai ya faki idonta ya duƙo ta bayan kujera saitin kunnen Maanal ya raɗa mata magana”. Tare da sumbatar wuyanta. Kafin ta juyo ya fice, cikin ɗaga murya Maanal ta ce, “Sai na rama kuma zaka dawo ai”. Mai ƙunshi dai abin nasu sai ya bata dariya da birgeta. Dan daka gansu kaga ma'auratan dake matuƙar son juna.... _________★ A Zaria su Ammie sune amarori ƙirjin biki. Amarya Najma tasha gyara ɗan gaske ciki da waje sai ɗaukar idanun mai kallo takeyi. Dan Ammie babu wasa sai da ta fidda ƴar tata Masha ALLAH. Ƙamshi kuwa ba'a magana, dan bayan nata gana Hajiya Shuwa. A jiya Ammie ta maidata Zaria. Anyi kamu a jiyan da yamma, yau kuma suke ƙunshi da safe. Da yamma aka fara yinin bikin Hajiya Majdiya. Gaba ɗaya ran kishiyoyinta su Maman Yaseerah a ɓace yake. Suma su Yaseerah dai ƙiri-ƙiri ƴan ubancinsu ya kasa ɓoyuwa akan shagalin bikin Najma ɗin. Dan sun san dai kam ta kere musu fintin kau kamar yanda uwarta ta kerema iyayensu a komai. Balle kuma ita Yaseerah zuwa yanzu tasan minene family ɗin Darma. Randa aka kawo lefen Najma habaice-habaice sukaita saki. Kallon inda suke Hajiya Majdiya batai ba balle kuma su Ammie da ke tsaye akan komai. Hajiya Basariyya kam ai ji take ina bashi yiwuwa, koda tsiya-tsiya sai ta kaso auren Huznah ta shiga wannan family na Darma. Sai kuma tura su Madeena ƙannen Huznah ɗin take cikin yaran family ɗin Darman wai suma ko sa samu mazan aure. Abin ya ba Maman Yaseerah haushi ta hau Hajiya Basariyya da masifa amma saita ƙi kulata. Dan ita lissafinta daban dana Maman Yaseerah a yanzu.... Bayan la'asar kaɗan tawagar su AA da abokan Yaya Fawzan suka isa Zaria. Zuwa lokacin an gama shirya amarya Najma dake ta shan kuka tsaff cikin lafaya. An kaita gaban iyaye an mata nasiha. Lokacin da aka kaita gaban Hajiya Majdiya suyi sallama sai kawai ta rungumeta tana kuka mai ban tausayi, ita ko Hajiya Majdiya ta dake abinta, acewarta ai Najma gida zataje minene na ɗaga hankali. Kuma itama dai gobe nan da safe zata wuce Abujan dan ai bikin su babban Yaya da ita. Da ƙyar Ammie ta cire Najma a jikin Hajiya Majdiya aka fito da ita. AA da RK ne zasu ɗauki amarya, ga Ammie itace riƙe da amarya ita da Aunty Rufaidah. Kunya ta kama AA, dan yanzu wani nauyin Ammie yake ji na musamman. Ko a waya ya kirata yata sum-sum da murya kenan. Itama dai Ammien nauyin nasa take ji. Cike da shaƙiyanci RK ya ce, “Babbar magana, suruki zai ɗauki suruka a mota”. AA dai bai kula shi ba, dan su Ammie sun riga sun kawo gab da su. Itama kuma sai a lokacin ta farga da shi. A zuciyarta tace (Ya subahannallah ya akai haka) a fili kam ta daure ta saka Najma a motar. Har inda yake AA yazo ya rissina yana gaisheta. Ta amsa masa da kulawa da tambayar yaya hanya. Yace Alhmdllh. Haka dole ta shiga motar, ya rufe mata murfin da kansa sannan ya zagaya ya shiga mazaunin driver dan RK ne ya kawosu, yanzu kuma yace bazai maidasu ba ya gaji sai dai AA ɗin ya tuƙa. Haka dole ya amsa dan Ammie da zata kasance a motar, sai kuma alƙawarin da yay ma Yaya Fawzan na shi zai kawo masa Najma har gida. Yana ƙoƙarin yima motar key kiran Maanal ya shigo masa. Sai da ya saci kallon Ammie da hankalinta ke akan lallashi Najma dake a jikinta sannan ya ɗaga kiran. Ƙasa-ƙasa dan AA ya iya munafuncin magana a ƙasan maƙoshi ya ce, “Zuciyar Ajwaad yaya ne?”. Daga can a shagwaɓe Maanal dake hammar barci hayaniya ta hanata zama sashen Oum ta gudo sashensu duk da nan ma cike yake da ƴammata ƙawayen Maimoon da aka taho da su daga Kano, amma da yake a ƙasa suke babu wanda ya hau mata sama sai ta haye saman ita. Tace, “Kun taho?”. “Uhm-uhm! A nan zamu kwana”. Ya faɗa cikin tsokana. Muryar Maanal harta fara rawa ta ce, “Kwana fa?”. Murmushi yayi jin za'a fara masa kukan shagwaɓar. Cike da lallashi ya ce, “Wasa nake, ga amarya nan ma a mota yanzu zamu taho”. Ajiyar zuciya ta sauke, tare da sakin hamma. Ƙasa-ƙasa ya ce, “Barcin ne?”. “Uhmm”. Ta faɗa can ƙasan maƙoshi. Murmushi yayi, zai faɗa mata tare suke da Ammie yaji ta fara sauke numfashi alamar barcin ya fara ɗaukarta. Wayar kawai ya katse ya tada motar. Sai suka haɗa ido da RK. Kallon da yake masa na shaƙiyanci ya sashi hararsa kawai ya ɗauke kansa. Haka suka ɗakko hanyar Abuja da amarya gwanin sha'awa. RK da Aunty Rufaidah ne kawai ke hira a motar. Ammie nauyin kasancewar AA da shi kansa ma RK ɗin ya sata yin shiru. Haka shima AA ɗin tuƙinsa kawai yake. Duk da dama bamai yawan magana bane ba kowa ya sani. Duk da uban gudun da sukai basu shigo cikin Abuja ba sai gab da sallar isha'i. Dan ma sunyi dabarar bi ta jere ne suka fito ta dutse. Maanal nacan na shaƙa barci bata san mi akeyi ba. A ƙofar sashen Oum AA yay parking. Auntyn su Mamy da a yammacin nan. Ta iso, kuma a sashen Oum ta sauka wannan karon ita ce ta fito ta tarbi amarya Najma ta nuna kara ma Oum. Aiko hakan da tai ya saka kowa jin daɗi sosai, hatta AA sai da ya murmusa. Oum kam Ammie ta rungume cike da jin daɗi, AA ya bisu da kallo yana sauke ajiyar zuciya. Ƙaunar dake a tsakanin Ammie da Mamy dabance a rayuwa. ALLAH yayi wannan haɗin kam. Ya matuƙar gajiya, ga Maanal na ransa dan tunda bai ganta a ƴan tarbar Najma ba yasan tana can tana barci. Sashen nasu ya wuce, ƙawayen Maimoon na falo duk da wasu sun fita saboda shigo da Najma sai ɗai-ɗai da akaima ƙunshi bai ƙarasa bushewa ba yana shigowa sukai ɗif. Sai kuma suka shiga gaisheshi da masa sannu da dawowa. Hannu kawai ya ɗaga musu ya haura sama ko kallon basu isheshi ba. Yanda Maanal ta hana kowa hawo musu sama ba ƙarin daɗi yay masa ba, sai ya ƙara fahimtar Bestynsa nada hankali. ACn data ƙure a ɗakin ya kashe gaba ɗaya, yayi yayi ta daina hakan taƙi, sai dai idan ya shigo ya kashe. Ya matsa gaban gadon yana kallonta, tayi luf a cikin duvet tana sauke numfashi a hankali. Gently yakai zaune gefenta, tare da shafa kanta sai kuma ya duƙa ya sumbaci idanunta da lips ɗinta. A hankali ta motsa, sai kuma ta buɗe idanunta dake cike da barci ta zuba masa kamar ƴar maye. Murmushi ya sakar mata mai sanyi, cikin raɗa ya ce, “Wakey wakey, beautiful”. Murmushi ta sakar masa, cike da kasala takai hannu ta shafi fuskarsa. Cikin muryar barci da shagwaɓa tare da tasowa ta dawo jikinsa ta ce, “Not yet, I'm still sleepy. Ƙamshinka ne ya tashe ni”. Murmushi yayi sosai, tare da kaiwa kwance ya sakata a cikin jikinsa sosai ya rungumeta. Sai kawai ta matso da fuskarta gab da tashi, idanunta a lumshe alamar barci sosai ne a cikinsu ta ɗaura lips ɗinta kan nashi. Babu musu ya amshe dan dama yau gaba ɗaya rowa ake masa. Rabonsa ma da ita tun jiya da safe.........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣0️⃣4️⃣ ______________ .....A yanzu gaba ɗaya hankalin Mamy ba'a kan auren nan yake ba. Dan Sille ya gama rikita mata al'amari gaba ɗaya. Amma dai tana ta ƙoƙarin danne yanayin ta dan bata fatan kowa ya san halin da take ciki a wannan gaɓar. Abinda ya bama Abah mamaki yanda ta sake ba kamar bikin Maanal da AA ba. Amma dai baice komai akan hakan ba. A ɓangaren Sille kam a yanzu itace mai nemansa a waya ruwa a jallo. Amma abin mamaki kaf layukan da yake kiranta da su bata samunsa. Tun a daren ranar ta bashi 10m daya buƙata, dan ta fahimci zai yi dukkan abinda ya ambata. Amma ta saka ana mata bincike a kansa dama Junaid, duk da ita tafi kowa sanin abinda ta aikata ma Junaid ɗin. Amma hankalinta yaƙi kwanciya sam. Tana son fita a gidan tana tsoron idon mutane, wani gefe na zuciyarta kuma na tunatar da ita idan ma ta fita ɗin ina zata samo Sillen. Tunda shi dai ba wani waje da yake zaune ta taɓa sani ba. Haka dai ta daure tana sauraren sakamakon binciken data saka anai mata akan Junaid..... ________★ A washe garin da za'a iso da Najma da ƙyar Oum ta lallaɓa Maanal sukaje saloon. Wankin kai kawai ta yarda akai mata, kitso sai ta sakama Oum kuka. Ƙyaleta tayi suka dawo gida akai zaman mata ƙunshi ja da baƙi. A lokacin su AA da zasu ɗakko Najma nata shirin wucewa. Ya shigo sashen Oum ɗin cikin tsokana yace mata saura kitso ta sanya masa kuka. Ita Oum ma sai abin ya bata dariya, ta dai gimtse batai ba. Sai ma ta harari AA da shima yake danne dariyar da ƙyar. “Yanzu dan ALLAH Auta banda neman faɗa ina ruwanka. Munce maka muna son kitso ne.” AA dai ya sake danne tasa dariyar da ƙyar ya ce, “ALLAH ya baku haƙuri Oum nayi shiru. Bani keys ɗin in dai nine yanzu zan yi gaba”. Oum na bashi maimakon ya tafi da arziƙi sai ya faki idonta ya duƙo ta bayan kujera saitin kunnen Maanal ya raɗa mata magana”. Tare da sumbatar wuyanta. Kafin ta juyo ya fice, cikin ɗaga murya Maanal ta ce, “Sai na rama kuma zaka dawo ai”. Mai ƙunshi dai abin nasu sai ya bata dariya da birgeta. Dan daka gansu kaga ma'auratan dake matuƙar son juna.... _________★ A Zaria su Ammie sune amarori ƙirjin biki. Amarya Najma tasha gyara ɗan gaske ciki da waje sai ɗaukar idanun mai kallo takeyi. Dan Ammie babu wasa sai da ta fidda ƴar tata Masha ALLAH. Ƙamshi kuwa ba'a magana, dan bayan nata gana Hajiya Shuwa. A jiya Ammie ta maidata Zaria. Anyi kamu a jiyan da yamma, yau kuma suke ƙunshi da safe. Da yamma aka fara yinin bikin Hajiya Majdiya. Gaba ɗaya ran kishiyoyinta su Maman Yaseerah a ɓace yake. Suma su Yaseerah dai ƙiri-ƙiri ƴan ubancinsu ya kasa ɓoyuwa akan shagalin bikin Najma ɗin. Dan sun san dai kam ta kere musu fintin kau kamar yanda uwarta ta kerema iyayensu a komai. Balle kuma ita Yaseerah zuwa yanzu tasan minene family ɗin Darma. Randa aka kawo lefen Najma habaice-habaice sukaita saki. Kallon inda suke Hajiya Majdiya batai ba balle kuma su Ammie da ke tsaye akan komai. Hajiya Basariyya kam ai ji take ina bashi yiwuwa, koda tsiya-tsiya sai ta kaso auren Huznah ta shiga wannan family na Darma. Sai kuma tura su Madeena ƙannen Huznah ɗin take cikin yaran family ɗin Darman wai suma ko sa samu mazan aure. Abin ya ba Maman Yaseerah haushi ta hau Hajiya Basariyya da masifa amma saita ƙi kulata. Dan ita lissafinta daban dana Maman Yaseerah a yanzu.... Bayan la'asar kaɗan tawagar su AA da abokan Yaya Fawzan suka isa Zaria. Zuwa lokacin an gama shirya amarya Najma dake ta shan kuka tsaff cikin lafaya. An kaita gaban iyaye an mata nasiha. Lokacin da aka kaita gaban Hajiya Majdiya suyi sallama sai kawai ta rungumeta tana kuka mai ban tausayi, ita ko Hajiya Majdiya ta dake abinta, acewarta ai Najma gida zataje minene na ɗaga hankali. Kuma itama dai gobe nan da safe zata wuce Abujan dan ai bikin su babban Yaya da ita. Da ƙyar Ammie ta cire Najma a jikin Hajiya Majdiya aka fito da ita. AA da RK ne zasu ɗauki amarya, ga Ammie itace riƙe da amarya ita da Aunty Rufaidah. Kunya ta kama AA, dan yanzu wani nauyin Ammie yake ji na musamman. Ko a waya ya kirata yata sum-sum da murya kenan. Itama dai Ammien nauyin nasa take ji. Cike da shaƙiyanci RK ya ce, “Babbar magana, suruki zai ɗauki suruka a mota”. AA dai bai kula shi ba, dan su Ammie sun riga sun kawo gab da su. Itama kuma sai a lokacin ta farga da shi. A zuciyarta tace (Ya subahannallah ya akai haka) a fili kam ta daure ta saka Najma a motar. Har inda yake AA yazo ya rissina yana gaisheta. Ta amsa masa da kulawa da tambayar yaya hanya. Yace Alhmdllh. Haka dole ta shiga motar, ya rufe mata murfin da kansa sannan ya zagaya ya shiga mazaunin driver dan RK ne ya kawosu, yanzu kuma yace bazai maidasu ba ya gaji sai dai AA ɗin ya tuƙa. Haka dole ya amsa dan Ammie da zata kasance a motar, sai kuma alƙawarin da yay ma Yaya Fawzan na shi zai kawo masa Najma har gida. Yana ƙoƙarin yima motar key kiran Maanal ya shigo masa. Sai da ya saci kallon Ammie da hankalinta ke akan lallashi Najma dake a jikinta sannan ya ɗaga kiran. Ƙasa-ƙasa dan AA ya iya munafuncin magana a ƙasan maƙoshi ya ce, “Zuciyar Ajwaad yaya ne?”. Daga can a shagwaɓe Maanal dake hammar barci hayaniya ta hanata zama sashen Oum ta gudo sashensu duk da nan ma cike yake da ƴammata ƙawayen Maimoon da aka taho da su daga Kano, amma da yake a ƙasa suke babu wanda ya hau mata sama sai ta haye saman ita. Tace, “Kun taho?”. “Uhm-uhm! A nan zamu kwana”. Ya faɗa cikin tsokana. Muryar Maanal harta fara rawa ta ce, “Kwana fa?”. Murmushi yayi jin za'a fara masa kukan shagwaɓar. Cike da lallashi ya ce, “Wasa nake, ga amarya nan ma a mota yanzu zamu taho”. Ajiyar zuciya ta sauke, tare da sakin hamma. Ƙasa-ƙasa ya ce, “Barcin ne?”. “Uhmm”. Ta faɗa can ƙasan maƙoshi. Murmushi yayi, zai faɗa mata tare suke da Ammie yaji ta fara sauke numfashi alamar barcin ya fara ɗaukarta. Wayar kawai ya katse ya tada motar. Sai suka haɗa ido da RK. Kallon da yake masa na shaƙiyanci ya sashi hararsa kawai ya ɗauke kansa. Haka suka ɗakko hanyar Abuja da amarya gwanin sha'awa. RK da Aunty Rufaidah ne kawai ke hira a motar. Ammie nauyin kasancewar AA da shi kansa ma RK ɗin ya sata yin shiru. Haka shima AA ɗin tuƙinsa kawai yake. Duk da dama bamai yawan magana bane ba kowa ya sani. Duk da uban gudun da sukai basu shigo cikin Abuja ba sai gab da sallar isha'i. Dan ma sunyi dabarar bi ta jere ne suka fito ta dutse. Maanal nacan na shaƙa barci bata san mi akeyi ba. A ƙofar sashen Oum AA yay parking. Auntyn su Mamy da a yammacin nan. Ta iso, kuma a sashen Oum ta sauka wannan karon ita ce ta fito ta tarbi amarya Najma ta nuna kara ma Oum. Aiko hakan da tai ya saka kowa jin daɗi sosai, hatta AA sai da ya murmusa. Oum kam Ammie ta rungume cike da jin daɗi, AA ya bisu da kallo yana sauke ajiyar zuciya. Ƙaunar dake a tsakanin Ammie da Mamy dabance a rayuwa. ALLAH yayi wannan haɗin kam. Ya matuƙar gajiya, ga Maanal na ransa dan tunda bai ganta a ƴan tarbar Najma ba yasan tana can tana barci. Sashen nasu ya wuce, ƙawayen Maimoon na falo duk da wasu sun fita saboda shigo da Najma sai ɗai-ɗai da akaima ƙunshi bai ƙarasa bushewa ba yana shigowa sukai ɗif. Sai kuma suka shiga gaisheshi da masa sannu da dawowa. Hannu kawai ya ɗaga musu ya haura sama ko kallon basu isheshi ba. Yanda Maanal ta hana kowa hawo musu sama ba ƙarin daɗi yay masa ba, sai ya ƙara fahimtar Bestynsa nada hankali. ACn data ƙure a ɗakin ya kashe gaba ɗaya, yayi yayi ta daina hakan taƙi, sai dai idan ya shigo ya kashe. Ya matsa gaban gadon yana kallonta, tayi luf a cikin duvet tana sauke numfashi a hankali. Gently yakai zaune gefenta, tare da shafa kanta sai kuma ya duƙa ya sumbaci idanunta da lips ɗinta. A hankali ta motsa, sai kuma ta buɗe idanunta dake cike da barci ta zuba masa kamar ƴar maye. Murmushi ya sakar mata mai sanyi, cikin raɗa ya ce, “Wakey wakey, beautiful”. Murmushi ta sakar masa, cike da kasala takai hannu ta shafi fuskarsa. Cikin muryar barci da shagwaɓa tare da tasowa ta dawo jikinsa ta ce, “Not yet, I'm still sleepy. Ƙamshinka ne ya tashe ni”. Murmushi yayi sosai, tare da kaiwa kwance ya sakata a cikin jikinsa sosai ya rungumeta. Sai kawai ta matso da fuskarta gab da tashi, idanunta a lumshe alamar barci sosai ne a cikinsu ta ɗaura lips ɗinta kan nashi. Babu musu ya amshe dan dama yau gaba ɗaya rowa ake masa. Rabonsa ma da ita tun jiya da safe.........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣0️⃣6️⃣ ______________ ....Ba ƙaramin narkewa Hajiya Basariyya data biyo ƴan kawo amarya tai ba da ganin gidan Darma. Yo ashe ma yara sun rage mata abubuwa da yawa kenan a labari. Tirƙashi lallai wannan fa shine ake kira da wani baban wani, wani ma kakan wani. Gefe kuwa yanda kowa ke nan nan da Ammie tun a Zaria ke bata mamaki da shakka. A zuciya sai ayyanawa take (wannan shegiyar mata akwai iya asiri, ita ko ina kowa dai sonta yake). Tana zagin Ammien amma tana nane da ita har bedroom ɗin Oum. Oum dai batace komai ba, amma a zuciyarta ta ƙudiri dole ne Hajiya Basariyya ta basu waje dan hirar zuminci zasu sha da ƙanwarta (Ammie). Hajiya Basariyya dai nata baza ido taga Maanal amma shiru. Tadai kasa haƙuri sai da ta tambaya a kaikaice. Murmushi Oum tai da faɗin, “Wannan kam inaga barci take yanzun, dan tun ɗazu da suka gama cin abinci da Mah-mah bayan an gama mata ƙunshi ban sake ganin giccinta ba. Amma bari na taɓa mijin naji”. Ammie na jinsu amma saboda kawaici batace komai ba. Sai ma kiran Shahidah daya shigo mata a lokacin ta ɗaga..... ★ Kiran Oum daya shigo wayar AA ne ya sashi raba lips ɗinsa da na Maanal da ƙyar. Sai da ya ɗan ja sakanni ya dai-daita yanayinsa sannan ya tashi zaune yana ciro wayar a aljihu. Kiran Oum ɗin yay back. Duk da ƙoƙarin kaurara muryarsa da yay sai da Oum tai ɗan jimm da jin yanayinsa. Amma sai ta danne cike da kulawa ta ce, “Halan Baby barci take yi?”. Maanal ɗin dake lumsha idanu ya kalla, sai kuma ya jinjinama Oum kai tamkar yana gabanta, kafin ya ce, “Eh Oum”. “Okay to barta karka tasheta, da safe taga Ammien. Ga abinci nan yaro zai kawo maka dan nasan kaima ɗin dai ba sake fitowar zakai ba. Sai da safe”. Murmushi yayi mai sanyi, ƙaunar Oum na sake ratsa masa zuciya. Sai kuma ya ajiye wayar tare da juyawa yana kallon Maanal. Ai shi ma yasan idan ya faɗa mata Ammie na gidan nan akwai daru, shiyyasa yay gum da bakinsa. Miƙewa yay ya fara zame kayan jikinsa dan ko magrib basuyi ba. Yana ƙoƙarin wucewa bayi kira ya sake shigowa wayarsa. Ganin Babban Yaya ne ya koma ya zauna a bakin gadon yana amsa wayar. Sun ɗan jima kafin su kammala. Cak ya ɗaga Maanal, tana turjewa da kukan shagwaɓar ita ya barta barci take ji bai kulata ba ya wuce da ita bayi. Shi yay mata wankan dan da gaske barci take ji, alwala ma da ƙyar ya samu tayita suka fito. Haka ya taimaka mata ta saka doguwar riga sukai salla. Suna idarwa a nan kan sallayar ta sake kwanciya. Ya girgiza kai kawai yana tashi ya fita. Babu jimawa ya dawo da basket ɗin abincin da Oum ta aiko musu, dan har nan falon sama Salim yazo ya ajiye. Babu lallashin da baima Maanal ba amma abincin nan bai ciyu ba, iyakarta 2spoon ta saka masa kuka dole ya ƙyaleta. A ransa yana mamakin wannan barci. Gashi komai abin kuka ne a wajenta, abu kaɗan zakaga tana hawaye. Shi kam dai abincin yaci sosai dan yunwar yake ji, sannan ya ɗagata ya maida saman gado ya lulluɓeta. Shima ya canja nasa shirin ya zauna, aiki ya ɗan taɓa sannan ya kwanta da gobe yasan basu da wani isasshen hutu kuma... Waya da Oum tayi da AA ya rufe bakin Hajiya Basariyya, amma fa a zuciya sai jinjina lamarin take da faɗin (A lallai yarinya ta samu waje. Dan mulki tun farkon daren nan ki shige da miji wai barci. Asiya duniyar ALLAH, ke dai kin dace da boka kam. Kina baza capacity Yaya na bazawa suma. To bari mu sakawa sarautar ALLAH ido muga da safe kuma karfe nawa za'a fito ni Basariyya.... ______★ A lokacin da ake bidirin isowar amarya Najma acan, anan sashen Mamy Yaya Fawzan ne yasa akai masa kiran Saheeba sashenta bayan ya gama roƙon Babban Yaya da bashi haƙuri. Naufal ya aika yay kiranta. Tunda ta shigo falon Babban Yaya yana zaune shi da Fawzan suna cin abinci da hira. Gaishesu tai a sanyaye dan gaba ɗaya yau jikinta yayi matuƙar sanyi, ta tabbatar dai da gaske wannan aure babu fashi. Asirin babu irin wanda basu zubaba amma shiru kake ji. Yaya Fawzan ne kawai ya amsa mata. Babban Yaya kam sai ma ya ɗauke kansa. Tana nan zaune shiru har suka kammala cin abincin nasu. Kafin Yaya Fawzan ya maida hankali a kanta bayan yaci serious. Nasiha yay mata mai ratsa jiki, tare da nuna mata muhimmancin zamanta lafiya a ɗakinta koda zuri'a data gitta. Ya nuna mata ita fa kishiyar nan ba wani bala'i bace ba, yanda ka ɗauki zamanta a tare dakai haka zaka sameta, sannan koba komai itace babba a gidan, sai ta riƙe girmanta matansu suma zasu girmamata. Sannan dukkan abinda tayi dashi zasuyi koyi. Yay mata misali da Umma a cikin family, matsayin matar Baba Sardauna take, amma a yanzu itace tamkar uwa ga kowa na family ɗin kamar yanda ake ɗaukar Baba Sardauna uba. Sannan Oum, itace matar Abah dake matsayin ɗa na farko a family ɗin, duk da kamar itace mai bi masa ata biyu dama yanda suka riƙe girmansu yasa kowa ke girmamasu. Babu wani ɗa dazaiyi abu a family ɗin sai da say ɗinsu. Kafin a bari wani abu yaje gasu Baba Sardauna sai idan ya gagari Abah da Oum ne sannan. To itama idan ta gyara ta riƙe kanta a matsayin babba dole haka matansu zasu girmamata. Mamy uwa ce a gareta, huruminta daban. Shi kuma babban yaya miji ne nashi hurumin daban. Sai tasan a yanda zata riƙe matsayin kowa a tare da ita. Abu na ƙarshe haɗin kan iyalansu, itace zata zama tushen wannan, basa son wata fitina ta dinga ɓullowa. Idan har tayi hakan suma bazasu taɓa bari sauran su takata ko mata jayayyaba a matsayinta na babbarsu.. Cikin share hawaye Saheeba ta tabbatar masa da cewar zata kamanta. Za kuma ta kiyaye. Tana kuma roƙonsa ya roƙar mata Babban Yaya yayi haƙuri ya yafe mata bazata sake kwatanta abubuwan da suka faru a baya ba. Yaya Fawzan baiyi ƙasa a gwiwa ba ya juya inda Babban Yaya yake. Cike da girmamawa ya ce, “Babban Yaya ayi haƙuri a yafe mata, kai ne second Aban mu, muna yin koyi da komai daga gareka ne muma. Tayi kuskure amma tayi nadama. Gashi kuma tayi alƙawarin bazata ƙara ba. Kaine ke tausarmu akoda yaushe akan al'amarin mata, to dan ALLAH ayi haƙuri kaima yau”. Sai da Babban Yaya yaja fasali cike da takaici, sannan yace, “Fawzan kafa san halin yarinyar nan bata da hankali, cewa ta tuba na tabbatar ba har zuciyarta bane ba akwai dai abinda take ƙullawa”. “Wlhy babu abinda nake ƙullawa Daddyn Naufal, dan ALLAH ka yafe min, ALLAH zan gyara yanzu...” “Karma ki gyara, dan wlhy zaɓi biyu ne dake yanzu a gidan nan. Kodai kibi shawarar Fawzan ki zauna lafiya, ko kuma ƙofa a buɗe take na barin gidan gaba ɗaya. Shawara ta rage ga mai shiga rijiya....” Ya miƙe abinsa yama fice a sashen. Nasiha sosai Yaya Fawzan ya sake mata sannan ya fito shima. Yana fita babu jimawa Mamanta ta shigo. Zama tai kusa da Saheeban. Ta ɗago da sauri tana kallonta da mamaki. Murmushi Nana tai mata da faɗin, “Ai naji duk abinda kuka tattauna ina bayan window ɗinku. Ina son ki bisu a hakan kawai, dan na fahimci dole ne mu sake sabon taku musamman akan uwarsu (Mamy😆). Dole ne mu ajiyeta a gefe muyi abinda ya dace. Na gaji da wannan tafiyar hawainiyar, ki kwantar da hankalinki komai zai zama labari, daga ke har Nuratu sai kunyi dariya. Dan haka ki jawo ƴar uwarki ta dawo nan ta zauna tare dake, tunda aikin maƙaryatan malaman nan yaƙi ci yaƙi cinyewa sai mu koma kissa, dama can Hajiya Turai ta sani wannan biye-biyen banzar da babu riba. Yanzu kam wasan ɗan gaske za'a buga. Fatana dai Nuratu ta shigo gidan ki samu abokiyar gwagwarmaya.” “Mama niko da zaki yarda da an haƙura da abubuwan nan. Wlhy da kike ganin Mamy jarumar kanta ce. Kuma a ɗan zaman nan nawa sashenta fahimci abubuwa da yawa a kanta. Kanta kawai ta sani wlhy, sannan amfani kawai take damu dan ganin ƴayanta sun dawo tafin hannunta. Ki duba fa kiga maganar kishiyar nan ko'a jikinta, sai ma hankalinta data maida akan wani abu daban da ban fahimta ba.” “Na fahimci komai Saheeba, shiyyasa nake son muma mu canja salo, dan munyi sake na jingina da alfarmarta tun farko. Dan ya kamata ace tun bayan shigowarki gidan nan mun raba aiki da ita, amma yanzu ma bamu makara ba. Itama Nuratu zan zauna da ita, ku kwantar da hankaliku ku canja taku. Ku koma musu yanda suke so ta haka ne za'a buga wasa ɗan gaske. Dan a yanzu gaɓar wasan ƙarshe ake mai nasara ya ɗauki kofi. Ina fatan ke da Nuratu kune zaku ɗauki wannan kofin koda tsiya ko da tsiya-tsiya. Ku barta taje can tai nata wasan da kishiyar tata, kai ku koma yima Fateeman hidima a yanzu, ku maida ita uwa kuma a gidan nan, duk wani rashin arziƙi da take sakaku kuna mata a baya yanzu ku daina shi. Zata gane cewa mu gatanta ne, sannan da bazarmu take duk rawa, bamune mukeyi da tata ba. Sai ta biya diyyar marin da tai miki tas”........✍️ Tofa Mamy, kin raini mayakanki zasu dawo yaki dake yanzu 🥺 *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣0️⃣7️⃣ ______________ .....Sosai Saheeba taji daɗin bayanin Mamanta. Ta kuma gamsu. Tana wucewa ta tashi ta hau gyara inda su Babban Yaya sukaci abinci, tana bin sashen da kallo dan yasha gyara sosai kam alamar amarya kawai yake jira. Hawaye ne suka zubo mata masu zafi, haka tasa hannu ta sharesu ta wuce bedroom dan gyara kanta. Dan yau bazatai sakaci ba mijinta take buƙatar kasancewa da shi, wata guda ai ba wasa ba..... ________★ Da safe ainahin rikicewa Maanal tayi da ganin Ammie. Dan AA shiru yay yaƙi gaya mata koda ta dawo daga massallaci ya ganta a kitchen. Sanin yau duk abincin da za'aci a gidan kawoshi za'ai yace mi takeyi a kitchen da sassafen nan. Batare data kallesa ba ta ce, “Abah nake haɗama abinci, nasan yau Oum ko tunawa da shi bazatai ba”. A hankali AA ya lumshe ido ya sake buɗewa a kanta, sai kuma ya saki murmushi mai sanyi da takowa a hankali ya tungumeta. Yanzun kam kallonsa tayi, sai kuma ta saka yatsunta biyu a goshinsa. Ƙasa-ƙasa tace, “Shagwaɓan na miye kuma? Lafiyan ka dai ƙalau Besty. Ko barcin bai isheka ba?”. Murmushi ya sake saki da jinjina lamarin Bestyn tasa, ji yanda take masa abu like wani ɗan yaronta. Hakan na sakashi nishaɗi da jinsa dai-dai da shekarunta, harma ya dinga tuna baya yana jinsu kamar a wancan lokacin. Maanal da taji shiru baice komai ba cikin kunensa tace, “Bestie girki fa nake yi, ba kuma mu kaɗai bane ba a sashen nan wani zai iya shigowa cikin ƴammatan nan”. Ƙin sakin nata yay ya kuma ƙi magana, sai da ya mula dan kansa sannan. Kanta ta ɗan girgiza, tare da juyawa ta cigaba da aikinta. Sake matsowa kusa da ita yay ciki-ciki yace, “Mizan tayaki?”. “Na hutar da kai jeka kwanta, nima saura kaɗan na kammala”. Kansa kawai ya jinjina mata ya juya ya fita dan da gaske barcin yake ji kuwa. Jiya ya gaji da wannan zuwa Zarian, ya dawo kuma ya cinye daren a aiki. Itama bata wani jimaba ta kammala komai, ta shirya na Abah a basket ta shirya na AA a tray ta haura da shi sama. A dining ta shirya masa shi duk da abincin yafi ƙarfin cin mutum ɗaya ma. Koda ta shiga bedroom barci ta samu AA ɗin nayi, sai ta wuce bathroom kawai, dan ita koda kuɗi kuma akace tayi barcin yanzu bazata iya ba. Wanka tai bayan ta gyara bayin, ta fito tai shiri cikin atamfa lass da akaima wani shegen ɗinkin ƴan gayu daya zauna mata ɗas a jiki. Cikin nan a lafe babu alamar akwai wani abu tare da ita. (Koda yake hasashen Mamy ne dama ai🤣🤙) Tai ɗaurinta mara hayaniya tasa turare ta yafa mayafi kamar ka saceta ka gudu. Gaban gadon taje ta shafa kan AA dake barci ta masa kiss sannan ta ɗauka wayarsa tama kanta hoto biyu ta ajiye masa kusa da shi ta fita. Sai yanzu da take fitowa ne take jin motsin su Maimoon na tashi, batabi takansu ba ta ɗauka breakfast ɗin Abah ta fice. Da yaya Fawzan suka haɗu shima zaije sashen Abah ɗin. Cikin tsokanar daya saba mata suka gaisa, ya kalla basket ɗin da faɗin, “Wannan kayan daɗin fa Lilly?”. Ɓoye basket ɗin tai gefe da faɗin, “Yaya F na Abah ne ba cinsa zakai ba kuma”. Dariya yay dai-dai suna shiga, tare da faɗin, “Lilly ki dinga min biyayya nine second Abanki a gidan nan fa ke da Mijinki tam”. “Wa kai ɗin, tab Babban Yaya dai. Kaida kake damumu da tsokala”. Murmushi Abah dake jiyo drama ɗin tasu tun kan su shigo ya saki, a ransa yana ƙara jin ƙaunar yarinyar. Dan sam shi baya ɗaukar Maanal matsayin suruka, ƴa yake kallonta kamar sauran sojojinsa uku. Ansha tambayarsa yaransa nawa yace huɗu.... Shigowarsu ta katse masa tunani, ya ajiye littafin hannunsa yana kallonsu, su duka inda yake suka nufi, Fauzan ya zauna yana gaisheshi, Maanal ta ajiye basket ɗin itama ta zauna ƙasa kusa da ƙafafunsa tana gaishesa. Cike da kulawa ya amsa musu su dukan, kafin ya maida hankalinsa ga Maanal ya ce, “Auta har kin tashi kinyi girki da safen nan?”. Fuskar Maanal da murmushi ta ce, “Abah kasan yau Oum ba tamu take ba, kar'a barka da yunwa shiyyasa”. Murmushi Abah ya saki, Yaya Fawzan kuwa ya ce, “To nima dai ALLAH ya kaimu randa Anum zata girma ta fara min irin wannan tattalin da ƴaƴa kema iyaye.” Abah na dariya yace, “To amin, amma duk jealous ɗinka ni aka fara yimawa Fawzan”. Dariya sosai Fawzan yake yi, Manaal ma na murmushi, suna cikin haka sai ga Babban Yaya da RK sun shigo, gaishesu Maanal tayi suma. Sun zauna ana ɗan taɓa hira ta miƙe domin zuwa gaishe da dasu Oum. Albarka Abah ya saka mata sosai su Babban Yaya na tayashi da Amin. Tana fita suka dasa hirar ƙyawawan halinta. Tare da taya Autansu dacewa da samun mace ta gari. Suma sunama kansu fatan ALLAH yasa amarensu su kasance kamar Maanal ɗin. Manaal kam sashen Oum ta wuce kai tsaye. Sai da ta fara shiga ta gaida su Umma dake bedrooms ɗin ƙasa sunata faman tsokanarta irin na kakanni wanda ke matsayin iyaye na kareta. Suma dai kowa ya kalla Maanal ɗin sai ya ambaci Masha ALLAH. Dan ba ƙaramin ƙyau tayi ba a sati biyar kacal. Masu idon gane ciki da wuri kam irin su Mah-mah tuni sun fahimci Maanal ɗin ta harbu kam. Sai dai ai fatan kuma ALLAH ya inganta. Rashin ganin Oum a ƙasa yasa ta haura sama. Sai da ta fara leƙa ɗakunan da su Aunty Rufaidah suke taga duk barci suke ta rufo musu ƙofar a hankali dan kar ta tashesu, tana shiga ɗakin Oum taci karo da Ammie. Yanda Maanal tai zuru tana kallon Ammie ya bama Oum dariya, dan su biyu ne kawai a ɗakin. Oum ta taɓata da faɗin, “Baby yaya dai?”. Manaal ta ce, “Oum mamakin duniya ne ya isheni, yanzu ni Ammie zatazo gidan nan ta kwana ta tashi bata nuna ta san da zamana ba, dan ALLAH ya za'a kira wanan abun, sallamawa ko mantawa?”. Ba ƙaramar dariya ta bama Ammie da Oum ba, amma sai Ammie ta fiske. Oum dake gimtse dariya ganin Maanal ta fara hawaye tace, “Gaskiya ƙanwata baki kyauta ba, ki kwana ki hantse yarinyata bata san kina gidan nan ba, to faɗa mana, kin sallama mu ne ko kin manta da mu?”. Ammie dake murmushi ta ce, “Aunty ai ni nama manta anan gidan take zaune. Kuma ni ai ba wajenta nazo ba.” Kuka Maanal ta fashe da shi. Zata juya ta fita Oum ta riƙota tana faɗin, “Ƙyaleta kinji Baby, so take dama ta kunnaki. Indai zata manta da ɗiyata nima kuwa zata manta da ni kenan”. Dariya Ammie tayi kawai, dan kallo ɗaya tama Manaal ɗin ta fahimci halin da take ciki. Shagwaɓa, saurin kuka shine salon da take fara fahimtar ta samu ciki. Dan duk rashin mutuncin Babu a farkon samun cikinta kasa gane kanta yake. Birkice masa take sosai, abu kaɗan ta hau taita masa masifa, duk kuma abinda zasuyi faɗa tasan hanyar takaloshi, haka ma cikin su Waleed tayi, dan Daddy lokacin data samu cikin Hameed abinda ta dinga masa sai da yace ko aljanu gareta. Sai daga baya data samu cikin Waleed sai ya fahimta cikine ke sata wannan riginar... Rungumeta da Maanal tayi ya katse mata tunaninta. Ta kalleta tana murmushi, sai kuma ta shafa bayanta cike da lallashi ta ce, “Kefa shagwaɓar ki tayi yawa Auta, yanzu miye abin kuka to anan?”. “Ammie bakin daina soma ba”. Ta ƙara faɗa cikin kuka bil haƙƙi. Abin sai ma ya ƙara bama Ammie dariya ƙwarai da gaske. Amma ta danne dan tasan irin wannan yanayin sarai. Cikin sake kwantar da murya da lallashi ta ce, “Ni na isa na daina son Auta ta, Babyn Oum ɗinta. Yi haƙuri sanda muka iso ance kina barci shiyyasa nace abarki sai kin tashi. Harfa tsaraba nayo miki”. Tashi Maanal tai tana dariya ga hawaye kuma. Ta zauna da ƙyau tana faɗin, “Shike nan na haƙura”. Sai kuma ta sake rungume Ammie ta ce, “I really miss you Ammie.” Cikin kunne Ammie ta raɗa mata, “I miss you too Autar Ammie”. Maanal ta ƙara ƙanƙame Ammie tana dariyar farin ciki. Kafin ta sake tashi da ƙyau ta zauna ta gaisheta da tambayarta su Waleed da Aunty Sakeena da su Nene?. “Kowa yana nan lafiya. Su Hameed anjima zasu zo da Daddynku wajen ɗaurin auren Yayanku. Sakeena ana biki dangin babansu shiyyasa basu zo ba har su Nene.” “ALLAH ya sanya alkairi. Didi Amaal bataje Zaria ba?”. “Bataje ba surukarta jiya aka kai asibiti, amma da sauƙi itama yau zasu taho da mijin, nasan ma yanzu sun taso”. Addu'a Maanal taima mara lafiyar, sai kuma suka fara hirar yaushe gamo. A haka Oum data fita tun ɗazun saboda masu kawo abinci da suka kirata sun iso ta dawo ɗauke da abincin data shiryoma Ammie. Sannu Ammie tai mata. Oum ta zauna tana faɗin,........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*