So da Buri Free Book 55 A hankali yake bud’e idanuwansa.. Hasken da ya gani tarr!! A kansa ne ya sanyashi maida idanun nasa ya rufesu dan lokaci guda yaji kanshi yayi wani mugun sarawa. Da sauri Mommy ta matso ta kama hannunshi tana murmushi tana goge hawaye tace “Dad, kaga ya farka, yanzunnan naga ya bud’e idanunsa.” Da sauri Dad ya matso ya d’an shafa fuskarshi sannan ya juya da sauri yana cewa “bara in kira Likitan, Alhamdulillah.” A hankali yad’an damk’i hannun Mommy da yake a cikin nashi, da sauri itama ta d’aura d’ayan hannunta a kai tace “Aslam, sannu mai kake so? Ya jikin?.” Sai da ya sauk’e ajiyar zuciya sannan yace “Hasken yayi min yawa” Da sauri ta mik’e ta rage hasken d’akin sosai sannan tace “Na rage” A hankali yake bud’e idanuwanshi da sukayi mishi nauyi sosai. Fuskar Mommy ya gani tana kallon shi tana murmushi. Murmushin shima ya sakar mata sannan ya fara k’ok’arin tashi. Da sauri tasa hannu ta taimaka mishi, sannan ta saka mishi pillow a bayanshi ya d’an jingina. Yana gama gyara zaman shi tayi huggin nashi sannan tace “Congratulations Son” Shiruuu, yayi chan kuma yasa hannu ya zarota daga jikinshi kafin yace “Mommy dama ba mafarki na yi ba?” Murmushi tayi ta kama kumatunshi ta d’an ja sannan tace “Ba mafarki bane! Angon Huda.” Dai dai nan Dad ya dawo da Likita yana binshi a baya. Y’an gwaje gwaje Likitan yayi sannan ya tambayeshi “ina ke yi mishi ciwo? Ya yake ji a jikinshi?” A hankali yace “Nothing much.. Kawai kainane yake d’an sarawa kad’an kad’an” Y’an rubuce rubuce Likitan yayi daga nan ya basu discharge yace “su yi signing daga nan suna iya wucewa bayan an siya mishi waennan drugs d’in. Ba wani abun bane yake damunshi Like he said before Kawai shock ya shiga, shiyasa ya suma! But he’s okay now. Allah ya kare gaba” Daga haka ya juya ya fita. A hankali Dad ya nemi guri ya zauna a kan kujerar daf da gadon sannan yace “Aslam I’m sorry! So sorry. Ban yi tunanin abun zai b’ata maka rai har ya kaika ga haka ba! Shiyasa kawai da Abba ya zo mana da wannan shawarar muka amince daga mu har iyayen Mahaifiyarta. Aure an riga an d’aura! Ina rok’on k’a da kayi hak’uri ka danne zuciyarka kar kayi wani abun da zai musguna mata kaga itama Yarinyar ba so take yi ba! Wannan zab’in mu ne. Ku zauna lafiya, in sha Allah wata rana za ku so junanku. Kar kayi anything da zai saka mu a kunya ko dan y’an tsofaffin nan Mahaifin Mahaifiyarta wallahi har ga Allah nayi tunanin idan aka gaya musu sauyin da aka samu da matsalar data taso ta wajen Arshaad ba za su yi farin ciki da kai ba amman sam ko a fuskarsu bamu ga komaiba a take suka goya mana baya d’ari bisa d’ari. Sannan, na san Abba kamar uba yake a wajen ka kaima amman dan Allah Aslam ka daure kaga dai yanda ya daure dukda k’iri k’iri ya kusan jin kunya saboda d’a na amman bai damuba haka ya sake yunk’urin ya k’ulla aure tsakanin y’arsa da kai! Kar ka bani kunya Aslam dan Allah”. Dad ya k’arashe maganar yana mai had’e hannuwanshi biyu yana kallon Aslam d’in alamun, roko. Da sauri Aslam d’in ya matso ya kama hannun Dad d’in ya sauk’ar k’asa: Shiruuu, d’akin yayi kowa ya kasa cewa komai. A hankali Dad ya mik’e yace “Mu je. Idan mun fita sai Ado ya tsaya a karb’a maganin a pharmacy” Yana gama fad’in haka ya juya ya fice. Gaba d’aya hankalin Aslam baya cikin d’akin har sai da Mommy ta d’an tab’a fuskar shi tukunna ya juyo yana kallon ta. Tana shirin yin magana ya riga ta ta hanyar cewa “Ina Arshaad?” Ita kanta Mommy sai da gabanta ya fad’i! Sam murna da farin cikin da take ciki sun hanata tuna Arshaad d’in ita kam tun d’azu da sukazo asibitin In ba yanzu da Aslam yayi mata maganar sa ba! A hankali ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace “He’ll be okay. Ka ji? Kar ka damu.” A hankali ya lumshe idanuwansa yana shirin yin magana kiran Dad wanda ya shigo wayar Mommy ya katse su. Tana d’auka yace “Akwai damuwa ne? Naga baku fitoba har yanzu” Da sauri Mommy ta mik’e tsaye sannan tace “Babu, muna tahowa” Sannan ta ajjiye wayar ta kama hannun Aslam wanda yake jin gaba d’aya jikinshi yayi sanyi. A hankali ya mik’e ya bi bayanta suka fita tare. A hanya aka tsaya drivern ya siya drugs d’in daganan suka wuce… Har suka isa gida kowa da abunda yake tunani! Suna shiga ya nufi side d’inshi yana mai cewa Mommy “yana d’an buk’atar ya huta” “To” kawai tace suka wuce ita da Dad sama. Yana shiga d’akin shi ya fad’a toilet yayi alwala ya fito ya hau jero nafilfili…….. Su mommy suna hawa, Dad ya kira Daddy yace mishi ya cewa Auwal Mom da Ummi su taho da drivers da motocin mansion d’in duka a had’u a bakin estate za aje a d’auko Amaryar Aslam. Ya yiwa Granpa bayani ta watasapp, Granpa d’in ya ce masa ‘okay he’ll get back to him later’ So kawai a kawota estate d’in idan an tashi.” Cikin mintunan da basu gaza ashirin ba Mommy da Gwaggo Asabe suka shirya tsaf suka fito. Suna fita a estate d’in suka had’u da su Mom da tawager su don haka suka yi convoy suka nufi gandun albasa….. 12:00pm(earlier) Tun lokacin da su Dad suka fita Arshaad ya kasa zaune ya kasa tsaye! Gashi wani abun takaicin still Mammy ta hanashi fita. Yana ganin kiran Auwal yak’i d’agawa dan kwata kwata baya buk’atar wata hayaniya.. Tunani kawai yake yi akan me zai yiwa Mammy ta barshi ya fita sannan a tunaninshi ya san Auwal d’in ce mishi zai yi yayi sauri ya san yadda zai yi ya fito kawai.. Duk da dai ya san cewa su Dad ba za su tab’a fasa d’aura auren saboda Mammy ba amma yana buk’atar zuwa He needs to be there dan bai kamata ace ya zama absent a rana mafi soyuwa a rayuwarshi ba. Suna a haka yaji wayoyinshi gaba d’aya ukun sun haukace da k’ara!!! Anfi minti goma amman duk ciki babu wadda ta huta, kiran yana katsewa wani yake kuma shigowa. A hankali ya k’arasa kan gadon nashi inda ragowar biyun suke zube ya fara dubawa... Jamil ne da ragowar Abokanayensa suke ta antaya mishi kira Haka kurum yaji jikinshi ya d’au rawa sannan zuciyarshi ta fara wani kalan mahaukacin gudu! Da kyar ya iya amsa kiran Jamil, tun kafin ya kaita ga kunnuwanshi ya juyo muryar Jamil d’in yana cewa “Garin ya haka ta faru Arshaad???” Da sauri ya kai kunnenshi kafin yace “Sorry Jamiel, wani abu important ne ya taso ya hanani zuwa” “Kamar ya Wani abu important shi ya hanaka aurenta?” Cikin rashin fahimta yace “ban gane ba! Ba a d’aura auren namu ba har yanzu?” Fahimtar da Jamil yayi Arshaad d’in bai san halin da ake ciki bane yasa yace “Haba! Biri yayi kama da mutum.. Ni daman na san kamar da wuya ace wai ka hak’ura da Huda! Anyways aikin gama ya riga ya gama yanzu kam… An d’aura wa Huda aure yanzunnan nima shaida ne Amman ba da kai ba da Yayanka Aslam...” Diff!!! Haka Arshaad ya d’auke wuta! “Hello helloo helloo” Haka Jamil yake ta maimaitawa amman shiruu! Yadda ya k’ame ya k’i motsi sai da hakan ya d’an tsorota Mammy dan haka ta taso ta matso kusa da shi ta tsaya tace “Kaii lafiyar ka k’alau kuwa??” Sai a lokacin ya samu damar jan numfashi lokaci d’aya kuma ya saki wayar hannunshi ta fad’i k’asa ta tawarwatse! Da sauri Mammy ta shiga gabanshi da kyau tayi cupping fuskarshi tace “Kaii, ba dai hatsari suka yi ba ko? Ka yi min magana ni duk kabi ka d’aga min hankali” Wani irin jan numfashi yake yi wanda yayi mugun tsorata ta! Cikin tsananin b’acin ran da bata tab’a ganin shi a ciki ba yace “Abunda kike so ai kenan! Kowa ya mutu kowa ya lalace kowa ya shiga tashin hankali! Ko ba shine abunda kike so ba? Ya k’arashe maganar cikin tsawa! Cikin b’acin rai Mammy tace Kai! Dan ubanka ni uwarka ce! Kar In sake ji ka d’aga mun murya idan ba haka b......” Kafad’unta da ya kama duka biyu da mugun k’arfi ne ya sanyata tayi shiru Girgiza ta yayi da k’arfin gaske sannan yace “Uwa! uwa!! uwaaa!!! Shine kalmar da kika yi amfani da ita kika tarwatsa mini rayuwa Tarwatsawa ta har abada! Ki kasheni kawai Mammy na rok’eki da girman Allah ki kasheni in hutu! Kin riga kin kasheni a bad’ini saura na zahiri.” Yana gama fad’in haka ya cika mata kafad’un nata da k’arfi wanda har sai da tayi baya kamar zata fad’i, ji yake yi kamar ya d’agata sama ya kauce! Da k’arfi ya fincike hular kanshi sannan ya cire babbar rigar ya jefar! Yana juyawa yayi facin mirrow d’in jikin wardrobe d’inshi wanda gaba d’aya k’ofar wardrobe d’in mirron ne da mugun k’arfi ya dunk’ule hannunshi ya daki mirrow d’in rabi ya tarwatse! Hakan bai yi mishi ba ya sake rarumo stool ya buga mirror d’in ya k’arasa tarwatsewa! Da sauri Mammy wadda abun ya fara bata tsoro ta k’araso ta rike shi ta baya tayi hugging d’inshi.., Gaba d’aya d’akin ya b’aci da jini kacha kacha dan ba k’aramin rauni ya yiwa kanshi ba daya daki mirrow d’in da hannu ba. Fincikewa yayi ya fasa mirrow d’in d’akin sannan ya d’aga centre table shima ya fasa shi! Zuwa yanzu Mammy tayi mugun tsorata da lamarin Arshaad dan haka ta ware murya ta fara kwala kiran Dad da Aaima tana k’ok’arin rik’e shi tana cewa “Ka nutsu mana Arshaad, ka fara bani tsoro fa! Akan mace kake wannan haukar?” Zare ta yayi daga jikin shi cikin tsananin b’acin rai idanuwanshi sun yi mugun jaa suna zubar da hawaye yace “Mammy kin cuceni! Ban tab’a tunanin haka daga gareki ba! Me nayi miki a rayuwa da nayi deserving haka daga gareki??? A iyaka sanina ban tab’a cusguna miki ba! A kullum k’ok’ari nake yi inga na faranta miki na baki duk wata kariya ta ko wanne fanni…” Matsowa yayi daff da ita yana kallonta kafin yaci gaba “Bari kiji in tuna miki.. A ranar da kika jefo Mommy daga sama, na ganki! Ina ga kina tunanin na manta ko? Ko kuma ban gane ki ba? Sarai na ganeki i was young Mammy very young at that time amma nayi zurfin tunani da hankalin In rufawa Mahaifiyata asiri dan a samu ta zauna lafiya cikin farin ciki da nishad’i!. A lokacin da na had’u da Hudan Ina ganin Mahaifiyarta na gane ita wacece dan dama tun farko Ina mamakin kamaninnta da Aslam da Abba da shigen kama da take yi da ni kaina! A lokacin daman kamar na sani na yanke shawarar neman ki mu fara tattaunawa amman kamar had’in baki Ina zuwa k’ofar d’akinki aka yi rashin sa a Mom ta zo wajenki babu abunda banji ba a ranar game da yanda kuka yi kuka rabata da gidannan! Everything Ba ma iya kar case d’in Huda ba har da na Mommy a ranar duk na sake jin wasu sabbbin abubuwan da kuka aikata! Har abunda ban tab’a expecting za ku iya aikatawa ba duk sai da na ji! But do you wat i did??” Bai jira ta bashi amsa ba yace “I kept quite! Na yi shiru ban fad’awa kowa ba kuma ban nuna miki ba ke kanki, ko a fuska! Ki duba kiga yanda muke ni da Aslam amman i choose to support you Mammy! Ki dubafa irin halin da yake ciki amman nayi ignoring komai saboda rufin asiri da farin cikinki! Because I love you! Bani da kamarki a duk duniyarnan! Zan iya yin komai dan kawai inga you stay safe and happy!. Ko kin san yaya mutum yake ji idan ya kulle maganganu a cikinshi shi kad’ai ba tare da ya amayar wa kowa ba? To, haka nake ta fama da nauyin issues d’inki da guilt for almost 20 years......” Durk’ushewa Mammy tayi a wajen ta fashe da wani irin kuka! Suna a haka nan Aaima ta shigo, da gudu ta k’arasa inda suke a rikice ta hau tambayar “mai ya faru??” Sai a lokacin Mammy ta mik’e ta kama hannuwanta sannnan tace “Aaima na yi laifi! Babban kuskure Idanuwana sun kulle na kasa gane gaskiya, dan Allah dan annabi ki tayani bawa d’an uwanki hak’uri” Da k’arfi Arshaad ya runtse idanuwanshi yana jin yadda zuciyarshi take tafarfasa…. “Ya arshaad mai y....” Da sauri ya juyo gareta ya d’aga mata hannu! Shiru tayi maganar ta mak’ale dan tunda Mammy ta kawota duniya bata tab’a ganin Ya Arshaad d’in nasu a haka ba. Ba tare da yace uffan ba ya isa jikin wardrobe d’in ya hau had’a takardu da kaya!… Wani wawan kuka Mammy ta fashe da shi sannan tace “Arshaad kar kayi mini haka dan Allah kayi hak’uri. Wallahi na amince kaje ka auri Hudan Ai na gaya maka na tuba Idanunane suka rufe amman yanzu sun bud’e! Son, dan Allah ka tsaya ka saurareni, ka yi hak’uri ka yiwa mamanka afuwar laifin da na kusan tafkawa da kaina nayi maka alk’awarin da kaina zan je har wajen Maryam In bata hak’uri sannan In bawa kakannin ta da su Abba hak’uri A d’aura muku aure! Na san za su yarda. Beside ai har yanzu a matsayin fiancé d’inka take so kar ka damu ko Abba muka je muka samu ni da kai a yau d’innan za a iya gyara komai!” Magana take yi tana binshi duk inda yayi tana k’ok’arin rikeshi yayinda shi kuma ko alamar sauraronta ma bashi da niyya, ta had’a kayanshi kawai yake yi!…. Sai da ya had’a akwati da briefcase sannan ya d’au wayoyin shi ya zura a aljihu ya d’auki makullin motarsa ya nufi k’ofa. Da sauri Mammy ta shiga gabanshi ta tsaya sannan tace “Arshaad na baka hak’uri kuma nace na yarda yanzu ka aureta. Wallahi tallahi nima sai yanzu nake dana sani. Ban san me ya shiga kaina ba, na kasa duba ka da halin da zaka shiga amman yanzu idanuna sun bud’e. Ka tsaya ka jirani anan wallahi ko k’iyayyar Huda zata kasheni wallahi zan hak’ura inje in bawa iyayenta hak’uri. I’ll not rest har sai naga ka aureta” Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauk’e! Da kyar yana mai jin numfashinsa yana d’aukewa ya iya fisgo magana yace mata “Mammy an riga an d’aura auren Huda da Aslam! So dan Allah dan Annabi ki bani hanya in wuce kafin in yi abunda zan janyowa kaina bala’i! Dan na rantse miki da girman Allah ko muryar ki bana k’aunar ji! Ahalin yanzu ba abunda na fi buk’ata irin in yi nesa da ke, mugun mugun nesa ma kuwa!!!” Fashewa tayi da wani sabon kukan ta durk’usa a wajen. Da sauri ya ja akwatin shi ya fita rik’e da suitcase d’inshi ganin tana shirin ruk’o shi. Yana jin Aaima ta biyoshi amman yak’i tsayawa sai ma k’ara saurin shi da yayi yana d’an had’awa da d’an gudu gudu…Itama Mammyn yanajin muryarta da alamun biyoshi tayi hakan yasa yayi sauri ya danna key ya bud’e ya zuba kayanshi a baya ya shige ya tada motar ya nufi gate da mugun gudu! Allah yaso mai gadin yana nan dan haka ya na hangoshi ya wangale gate d’in, shi kuma ya fice. Dai dai nan su kuma suka fito compound d’in! Basu tarar da shi ba sai iskar motarshi...... GANSUN ALBASA Yinin biki Shuwa ta had’a mai rai da lafiya. Tun safe mai makeup tazo ta tsantarawa Amarya kwalliyarta amman kafin ma lokacin d’aurin auren kwalliyar ta goge tas! Saboda tsabar hawayen da take yi tana sharewa. Zuwa yanzu kam Huda ta cire rai da Arshaad! Ba abunda yafi d’aure mata kai irin yadda ya yaudareta for almost 4 years bayan ya san ba sonta yake yi ba! “Don kawai ya ga wannan ranar?” Ta yiwa kanta tambayar Wata zuciyar ce tace mata “Ai daman Mama ta fad’a, Abba ne ya turo shi” Da sauri tace “Astaghfirullah! Inaaaa, Abba ba zai tab’a had’a baki a yi mini haka ba. Sai dai in Arshaad d’in ne ya nuna mishi yana sona bayan ya san baya sona shi kuma Abban ya yarda da shi. Amma ai Abba ba zai tab’a turo shi ba No matter what......” Kanta gaba d’aya ya d’aure ta rasa yadda zata yi. Tana zaune daga ita sai Khadija a d’akin dan kwata kwata Sakina kwana biyun nan bata yarda su zauna waje d’aya ko had’a ido Hudan ta lura Sakinar bata so su yi. Ita kuwa Sakina ta san muddin ta zauna tare da Huda sai tayi kuka itama shiyasa taga gara tayi nesa da ita kar taje instead of ta dinga k’ara mata kwarin guiwa taje ta b’ige da karyar mata guiwa. Suna zaune Khadija tanata lallashin ta su Madu suka shigo! Tunda suka shigo dama ta san ba lafiya ba dan bata tab’a ganin Madu ya shigo d’akin Shuwa direct haka ba, dan haka kawai ta lumshe idanuwanta tana jira taji yace ‘Arshaad ya fasa aurenta’ Murmushi yayi kafin taji yace “Amarya! Bud’e idon mana.” Dumm!! Haka gabanta ya bada, da sauri ta bud’e idon taga yana kallonta shi da Baba bashir murmushi shimfid’e akan fuskokinsu. Da kyar ta iya gaishesu daga nan taga Shuwa da Ummu da Mama suka shigo. Mik’ewa Khadija tayi ta fita bayan ta gaidasu. Sai da kowa ya zazzauna tukunna Baba Bashir yayi gyaran murya yace “D’azu mun tafi da niyyar d’aura auren Hudan da Muhammad Arshaad Sai aka samu matsala Ita Mahaifiyar Arshaad d’in ashe tunda ta dawo ta d’aga musu hankali akan muddin aka yi gangancin d’aura auren d’anta da Huda tou tabbas sai ta tsine mishi! Ashe shiyasa ma bai samu zuwa jiya ba instead sai Yayanshi ya wakilceshi. To su a tunanin su Yahayan za su iya shawo kan matsalar shiyasa basu wani damu ba muma basu gaya mana ba. To dai yau Mahaifiyar tasa ta tabbatar ta sake tabbatarwa akan ita fa tana nan akan bakarta ba kuma wanda zai iya sakata ta sauk’a. Su kuma su Abba suka ga bai dace ace Mahaifiyar shi tana ta ik’irarin tsinuwa a kansa haka ba, kuma kinga tabbas dole suna buk’atar albarkar ta! Shiyasa Abba da yayyunshi maza suka yanke shawarar fasa d’aura auren da Arshaad Instead sai aka d’aura da Yayansa Aslam mai sunan Mahaifinta wanda ya wakilci d’an uwan nashi jiya............... “Innalillahi wa innailaihirrajiun” Shine abunda Huda take ta faman maimaitawa tana hawaye. Madu ne yace “Aslam bashi da wata makusa. Abunda yayi Arshaad shi yayi Aslam, sannan an an riga an tara mutane. Kuma tunda Mahaifiyar Arshaad ta furta bata k’aunar Huda to ko an dawo ance ta hak’ura aka d’aura tabbas Huda ba zata zauna lafiya da ita ba! Sannan Mahaifin Huda shi ne ya kawo wannan shawarar ya zab’a mata Aslam It’s like kamar ma yafi farin ciki sannan hankalin shi yafi kwanciya da Aslam d’in dan bakiga irin farin cikin da yake yi ba a lokacin da aka goya mishi baya aka kuma d’aura auren. To who are we to reject? Besides Ni a ganina ma it’s for the best In sha Allah Tunda kullum zab’in Ubangiji muke nema shi ya shirya hakan. Dan haka sai mu runguma mu kuma gode mishi mu bita da fatan alkhairi. Banaso inji wata magana ta taso! Ku saka a ranku kawai Arshaad ba shine Allah ya tsara zai zama Mijin Huda ba Aslam ne!. Sai kuyi mata nasiha ku shiryata, Yahaya yace min k’arfe biyar na yamma za su zo su tafi da ita in sha Allah.. Allah yayi muku albarka gaba d’ayanku.” Yana gama fad’in haka ya mike suka fita shi da Baba Bashir. A hankali sautin kukan Mama ya fara tsananta a cikin d’akin.... Ganin Huda ta mik’e ta nufo inda take tana kuka ne ya sanya Maman ta mik’e da sauri ta fice daga d’akin tana kuka. A tsakar d’akin Huda ta zame ta zauna ta fashe da wani kuka mai ban tausayi Shuwa ce ta umarci Ummu da “ta je ta d’auko mata laffayar da za a nad’a mata Sannan ta taho da turarukan wuta da kasko” Ummu na fita Shuwan ta k’arasa inda Huda take zaune itama ta zauna sannan ta kamo hannunta duka biyu…. Nasiha mai ratsa jiki tayi mata wanda ko Maman iyakar abunda zata gaya mata kenan! Duk wani abunda ya dace sai da Shuwa ta fahimtar da ita dalla dalla. A haka Ummu ta shigo ta samesu dan haka itama ta nemi waje ta zauna ta d’ora mata da nata darussan…, Ita dai Huda zuwa yanzu muryarta ta disashe, hawayene kawai yake fita daga idanuwanta, sai faman sauk’e ajiyar zuciya take yi, a ranta tana tunanin ‘Tayaya zata fara zama da mutumin da ba ya sonta bata sonshi? Mutumin da ta lura ko inda take baya son zama...’ Umartarta suka yi da ‘ta mik’e’ Tana mik’ewa suka hau shiryata.. Suna mata ruwan turarurruka Khumra da na wuta............... A gigice Anty Zainab ta k’arasa gidan Baba. Tana shiga ko sallama bata yi ba ta fad’a d’akin Umma. A kan gado ta sameta ta bararraje tana shan lemo da bredi da gyada Ya Ja’afar kuma yana gefe a kwance yana bacci. D’auke bredin tayi ta jefar Umma na shirin yin magana Anty Zainab ta katseta ta hanyar cewa “Jiya! Sai da nace miki kar ki k’arawa mutumin nan kud’i yaudarar mu zai kuma yi amma da yake kunnen k’ashi gareki kika d’auki mak’udan kud’ad’e kika bashi saboda kinji Jalila duk ta rikice tana kuka ko? To albishirinki kice mini goro! Ga Huda chan ana shirya ta In sha Allah nan da k’arfe biyar za azo a tafi da ita gidan Arshaad! Aure kam ya d’auru, ba d’an borin da yayi nasarar lalatawa.” Kwarewa Umma tayi da d’an ragowar bredin bakinta wanda bata gama had’iyewa ba. Da kyar ta dawo dai dai Cikin tsananin tashin hankali tace “Innalillahi wa innailaihirrajiun! Wacce iriyar masiface ni kam ta fad’amin? Ni sadiya ina zan saka kaina? Yanzu mutumin nan ya kyauta min kenan? Tsofai tsofai da shi amman ya karkace yayi ta faman gilla mini k’arya? Kin san tun yaushe muka sanshi kuwa? An dad’efa ana tare. Haba dan Allah Allah ya isa kud’ina da lafiyata. Kiga fa jiya cikin dare muna barin asibiti haka muka je wajen shi. Har da cewa ko dan halin da nake ciki zai yi mini aiki mai zafi! Shege ashe yaudarata ya kuma yi ya saka min rai Allah sai ya saka min wallahi” Ta k’arashe maganar tana fashewa da kuka.. Duk sai tausayinta ya lullub’e Anty Zainab, a hankali tazo ta zauna a gefenta kafin tace “Yanzu menene abun yi? Kuka ba zai kawo mana solution ba.” Hawayenta ta goge sannan ta mik’e tace “komawa za muyi! Ai ta inda aka bi aka hau tanan ake sauk’a. Wallah ko dai ya lalata auren kafin ta tare ko kuma ya biya ni kud’ina” Ta fad’a haka tana mai yafa mayafinta wanda ta d’auka yanzun. Da sauri Anty Zainab ta mik’e ta tsaya a gabanta sannan tace “Sadiya ki nutsu dan Allah. Na tabbata kafin mu k’arasa wajen nan mai uban nisa Huda ta riga ta shak’i iskar gidan Arshaad. Yanzu ni dai indai zan baki shawara ki d’auka to ki hak’ura da raba auren nan! Kinga fa yadda muka yi ta k’ok’arin rabawarnan yak’i rabuwa to maybe wani babban rabo ne a tsakaninsu Allah ne ma yake son mu shiyasa ya barmu da ranmu, kar muje mu sake yin wani yunk’urin, muje garin neman gira mu rasa idanuwanu.” Cikin tsananin b’acin rai Umma tace “To matsoraciya! Kin san Allah wallahi sai dai duk abinda zai faru ya faru amman aure kam na raba shi na gama billahilazim! Ai In na barsu ma To Maryam taci riba kenan! Idan zaki ci gaba da taimaka min to na gode, idan kuma ba za ki ci gaba ba to kina iya yin tafiyarki dan ni nan kin ganni wallahi sai inda k’arfina ya k’are! Na tabbatar inda ace Khadija ce take cikin halin da Jalila take ciki da kema sai inda k’arfin ki ya k’are!”. Anty Zainab taji zafin maganar amman kawai sai ta basar duba da halin da Umman take ciki kwana biyu..Jafar a haukace! Junaidu ya b’ata!! Baba ya gudu!!! Jalila kuma gata chan itama sai a hankali, sannan duk fad’in duniyar nan ita kad’ai Umman ta gayawa Jalilan cikine da ita amman har Laraba bata sani ba Umman tace ‘In ta fad’a mata tana iya gayawa su Hansai, daga nan su kuma su yayata ayi ta munafurci a cikin unguwa da dangi’ Waennan dalilan su suka sanya itama Anty Zainab d’in tayi sticking by her side take taimaka mata sannan tana tsananin jin tausayin k’awartata, shiyasa yanzu ma Mta kaawar da haushin da taji tace “Sadiya yadda na d’auki Jalila haka na d’auki su Khadija. Ki kwantar da hankalinki ki nutsu kar muje muyi ba daidaiba cikin rashin sani.” Da sauri Umma tace “Hankali na ba zai tab’a kwanciya ba Zainab! Ina cikin tsananin tashin hankali.. Jiya da Jalila ta kira ni gaya miki ne ban yi ba dan kaina ya d’au chaji ba kad’an ba! Cikin jikinta ya zube, garin haukarta taje ta fad’o daga matattakala. Kinga yanzu shi Yaron Auwal babu maganar karb’ar kud’i a hannunshi kuma na tabbatar nan da kwana kad’an uwar nan tashi mara mutunci itama tsayayyiyar kanta zata auno Jalila gidan nan! Ni na ma yi mamakin da ta barta har yanzu dan kwata kwata ba shiri suke yi ba! Gashi ke kin san yadda Jalila take matuk’ar k’aunar Arshaad sannan a haka kike tunanin zan bar Huda taje ta zauna tare da Arshaad a gaban idon Jalila? Tana ji tana gani? Da wanne Yarinyar nan za taji saboda Allah? Sannan ni kaina me nayi ne haka a rayuwa da mugayen abubuwa suketa fad’o mini haka?” Ta k’arashe tana mai fashewa da mugun kuka. Rungumeta Anty Zainab tayi ta shiga lallashinta Sai da taji tayi shiru tukunna tace “Sadiya ki nutsu ki bani hankalinki dan Allah mu yi magana” Kamar wata k’aramar Yarinya haka Umma ta hau share hawayenta tana d’aga kai duk ta rikice, ta manta rabon da ta shiga kwatankwacin tashin hankali irin wannan. Sai da ta nutsu sannan Anty Zainab tace “Anjima idan na dawo daga raka Huda zan zo mu koma wajen mutumin nan, akwai wani ma shima za muje wajenshi. I’m sorry to say amma raba auren Huda da Arshaad ba zai yiu ba Sadiya tunda an riga an d’aura. Yanzu mu bar Huda mu ji da Jalila duk bala’i idan za muyi yawo tsirara mu san yanda za ayi a sati mai kamawa a aurawa Arshaad Jalila. Ke kin san wacece Jalila da kuma yadda take son Arshaad da taimakonta da taimakonmu na tabbatar Huda ba zata yi wata biyu a gidan Arshaad ba. Na tabbatar hakan sai yafi yiwa Maryam zafi akan yanzu a fasa kai Huda gidanta kai tsaye!. Yanzu ki cewa Jalila ta daure ta jure ta kauda kanta, za mu yi nasara in shaa Allah.” BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 56 Sakina ce ta yi knocking aka bata izinin shiga, tana shiga tace musu “Masu d’aukar Amarya sun zo, suna k’asa.” Dumm!! Haka k’irjinsa ya buga hatta Shuwa. Cikin dauriya Ummu ta cewa Sakinan “ta je, ga su nan zuwa” Kallon ta Hudan tayi da idanuwanta da suka k’ank’ance suna zubar hawaye, da sauri ta juya ta fita tana share tata kwallar.. Shuwa na hannun damanta Ummu kuma ta ruk’ota ta gefen hannun hagu, a haka suka sakata a tsakiya suka sauk’o parlourn da ita fuskarta a lullub’e. Kauda kai Mommy ta yi ta share kwallar farin cikin data zubo mata! A hankali ta mik’e ta k’arasa wajensu ta kamo hannun Huda ta kawota kan kujerar da take akai gefenta ta zaunar da ita sannan itama ta samu waje ta zauna kusa da ita. Ummi ce ta mik’e itama ta isa 3 seater da suke zaune su biyu ta zauna a kusa da Huda ta kamo hannunta tana murmushi (ya zamana sun sakata a tsakiya ita da Mommy ) Tsakin da Mom ta yi sai da ya d’an fito fili ba tare da ita kanta ta san zai fito d’inba! Da sauri ta wayance ta sake yin wani sound kamar wadda abu ya mak’alewa a hak’ori sannan ta shiga gaida su Shuwa tana mai k’arewa gidan kallo! Dukda cewa gidan yana da girma gashi mai bene amman hakan bai hana Mom yiwa gidan kallon k’ask’anci ba. Gaggaisawa aka shiga yi cikin barkwanci da mutunta juna, daga nan aka damk’awa su Mommy amanar Huda suka amsa hannu bibbiyu suna masu farin ciki… Mik’ewa aka fara yi da niyyar tafiya amman Amarya furr! Ta k’i mik’ewa.. Da kyar Ummi tasa hannu ta d’agota sannan ta jawo ta jikinta ta rungume ta shiga lallashinta tana cewa “muje mana dota. Yi hak’uri kinji, kowa da haka ya fara.” Cikin kuka, da muryarta wadda ta dad’e da dishashewa ta cewa Ummin “Ban yi sallama da Mama ba. Dan Allah ku kaini wajenta. Zan biku amman sai na fara yiwa Mama sallama.” Lumshe ido Ummi tayi tana jin yadda k’irjinta ya fara bugawa da sauri da sauri… A hankali ta juya ta sanarwa su Mommy abunda Hudan tace Murmushi Shuwa tayi kafin ta cewa Ummu “ta tashi ta kamata su kaita mota. Za suyi sallamar a waya.” Sai da suka yi da gaske kuwa tukunna suka iya janyeta. Tana kuka tana komai haka suka fitar da ita aka sanyata a mota Ummu da Ummi suka sakata a tsakiya Ummi sai faman lallashinta take yi..... Inda Mama take Mommy ta tambaya bayan fitar su. Sakina ce ta kaita har d’akin sannan ta juya ta fita dan itama tana so ta raka Amarya. Mota guda suka yi ita da k’awayensu su hud’u waenda suka zo rakiyar Amarya. A zaune Mommy ta sami Mama a bakin gado tana ta sharar hawaye.. Sai da ta k’arasa inda take ta dafa kafad’arta tukunna ma Maman ta san mutum ya shigo! Murmushi Mommyn tayi ta zauna a gefenta sannan tace “Ai gara da Hajiya tace a tafi da ita ba sai kun yi sallama ba dan na san daa ta shigo ta ganki a haka to da sake tab’arb’arewa al’amarin zai yi” Kukan Mama ne ya tsananta a hankali ta juyo ta kama hannunta tana sheshshek’a tace “Mommy, ga amanar Huda! Dan Allah ki kular min da ita. Ina tausayawa Huda dan ban san ya zaman nasu zai kasance ba saboda na san duk su biyun basa k’aunar juna amman kuma idan na tuna ke ce surukar ta sai hankalina ya d’an kwanta na san at least ko da ace bata samu soyayyar Miji ba na san zata samu ta Mahaifiyarshi Hakan zai d’an rage mata rad’ad’i da damuwa. Naso ace Huda ta auri mai k’aunarta amman kuma k’addara ta riga fata.” Ta k’arashe maganar tana mai fashewa da kuka. Murmushi Mommy tayi kafin tace “Share hawayenki, ki d’ago ki bani hankalinki.” Da kyar Mama ta iya tsayar da kukan nata sannan ta d’ago tana mai kallon Mommy da idanuwanta da suka k’ank’ance sukai jaa. Ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e kafin tace “Ki daina cewa Aslam ba ya k’aunar Huda! Dan zan iya rantse miki ko shi kanshi Arshaad d’in ba ya yi mata kwatankwacin son da Aslam yake mata.” D’an zaro ido Mama tayi tana kallonta da alamun mamaki. “Kwarai kuwa” Shine abunda Mommy tace sannan ta d’aura da cewa “Tunda na warke, although ban zauna da Aslam ba ban kuma san yanayin shi sosai ba amman tashi d’aya na fahimci yana cikin matsananciyar damuwa! Kullum yana fama da zazzab’i da hawan jini, anyi anyi da shi akan ya fad’i damuwar shi amma yak’i fad’awa kowa. Sai da yaga yana shirin mutuwa tukunna ya zo ya samemu ni da Dad yace mana ‘yana neman alfarmar mu barshi ya tafi uk ya d’an yi y’an kwanaki’ Mu kuma ganin rashin dacewar hakan ne ya sanya muka hanashi tafiya. Bayan Dad ya fita ne na lallab’ashi akan ya fad’amin damuwarshi.. Da kyar ya iya gaya min dan shi har ga Allah kunya yake ji… ‘He knows he’s selfish ta ko wanne b’angare amma ya rasa yadda zai yi ya yakice soyayyar Huda a cikin zuciyarshi.’ Yace min ‘tun ranar da ya fara ganinta tun ba yanzu ba Allah ya d’aura masa matsannciyar soyayyarta! Kuma dede da rana d’aya k’aunarta bata tab’a raguwa a zuciyarsa ba instead k’aruwa ma take yi. Baya iya bacci baya iya yin komai cikin nutsuwa idan ba hotonta ya saka a gaba ba yayi ta kalla.’ A ranar yace min ‘Muddin muka barshi aka d’aura auren Huda da Arshaad a gabanshi tou tabbas zai iya rasa ranshi! Dan haka shiyasa yana ganin gara yayi nesa sosai kuma yana rok’ona ko da an d’aura auren to kar In fad’a mishi, ko ya tambayeni kawai ince mishi nima ban sani ba’. Naji matuk’ar tausayin Aslam a wannan lokacin tabbas, ba na so ya zama coward shiyasa na hana shi tafiya na rok’esa Allah da Annabi ya zauna..idan yayi facing ya tabbatar da ta sub’uce mishi forever hakan will make him stronger and zai cire hope yayi moving on. Ya yarda zai zauna bayan ya tabbatar min idan bai mutu a ranar ba to zai iya samun heart attack! Ni kuma na duk’ufa gayawa Ubangiji Ya saka mishi sassauci da dangana sanann ya zab’awa Hudan Arshaad da Aslam dukkan nin abunda yake alkhairi ne a rayuwarsu. Tun jiya na hango silver lining. Shiyasa yau na tilasta mishi yaje d’aurin auren! Idan an d’aura auren Huda da Arshaad a gabanshi na san hakan zai taimaka mishi akan ace ya gudu daga reality da nauyin hope! Idan kuma an d’aura da shi to falillahil hamdu.” Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin ta ci gaba “Tunda har Aslam ya iya kawar da komai ya cire kunya ya furta mini cewa yana son Huda to tabbas na san ba k’aramin so yake yi mata ba! Ki duba kiga yadda suke shi da Arshaad da kuma kawaici irin nashi amman ya kasa hak’ura! Na san Aslam tun yana Yaro k’arya ba abunda ya iya baneba besides why will he even lie? All that I’m trying to point out miki anan shine Hudan ta tafi gidan wanda yake k’aunarta matuk’a! Ki kwantar da hankalinki ki bisu da fatan alkhairi.........” Direct MT estate aka wuce da ita... Already Mommy ta saka masu aiki sun share sun goge side d’in Aslam sai tashin k’amshin turaren wuta yake yi. Ba abunda babu na fannin furnitures, duk ragowar d’akuna ukun akwai gadaje masu kyau! Parlourn ma yana d’auke da duk wani abun buk’ata. Motocin suna gama yin parking aka fara firfitowa. Tun a gate na estate d’in Anty Zainab taji inama bata zo ba! Gashi mata y’an Maiduguri da suka shigo mota d’aya tare da su sai faman zuzutawa suke yi suna “Ma shaa Allah! Huda kam Allah ya bata duniya” ita kuma tanajin kamar ranta zai fita! Sannan kanta ya d’an juye dan cewa aka yi gidanta ita kad’ai ce yanzu kuma taga an kawota nan!. A haka dai tana ji kamar zuciyarta zata fashe ta biyewa jamaa akai ta washe baki da ita, ta bari akan In sun koma zata bugi cikin Khadija ta ji komai dan ta san idan ba bugar cikin nata tayi ba to ba zata tab’a gaya mata ba! Sun sha yin fad’a da ita Khadijar ba sau d’aya ba akan su Hudan. Ummi da Ummu ne suka ruk’ota, suna zuwa main door na shiga gidan suka umarceta da ta shiga da bismillah da k’afar dama, haka ma k’ofar side d’in Aslam da tazo shiga! Yadda suka ce hakan take yi da fuskarta a rufe cikin laffaya tanata kuka. Sai da suka kaita bakin gadonta sannan suka ajjiye ta da bismillah. Bayan an d’an ragu a d’akin Ummu ta k’ara mata da nitsatsiyar nasiha! Basu wani dad’e ba suka fara shirin tafiya hatta gifts da abincin da Dad ya shirya musu ma mota kawai aka kai dan suna idar da sallar Magrib suka fara zuwa suna yi mata sallama suna ficewa…… Jama’a da friends d’insu in banda santin estate d’in da side d’inta ba abunda suke yi, a haka kowa ya watse. Aka barta ita da su Sakina da Khadija da friends d’insu guda biyu da suka zauna dan ragowar cewa suka yi ‘za su wuce saboda basa so su yi dare’….. Da kyar da sid’in goshi Huda ta d’an tsayar da kukan nata, bayan dogon lallashi daga su Sakina ta yi shiru ta bud’e fuskarta. Tana jinsu suna ta hira ana shewa amman ta kasa tanka musu Istigfari kawai take tayi saboda sam! Tunanin Arshaad yak’i fita daga ranta. Daga masallaci direct gida Aslam da Dad suka wuce side d’in Mommy. Suna zaune ita da Gwaggo Asabe da alamun magana suke mai muhimmanci su Dad d’in suka shigo. Mik’ewa Gwaggo Asabe tayi zata fita Dad yayi saurin cewa “ta dawo ta zauna Nasiha za su yiwa Ango!”…. Sun kusan 1 hour suna yi masa Nasihar daga nan Dad ya mik’e yayi musu sai da safe. Kana ganin Mommy da Gwaggo Asabe ka san suna cikin farin ciki. Mommy ce tace “To ka tashi ka je kuyi siyan bakin mana. K’awayenta fa kai suke jira su tafi” Kamar zai yi kuka yace “Mommy siyan baki kuma? Kin san fa a yanda auren nan yazo. Ki barshi kawai su yi tafiyarsu, Ina son ganin Arshaad first.” Ya fad’a yana mai mik’ewa zai fita. “Baya nan” Yaji muryar Mommy. Da mamaki ya juyo kafin yace “Ina ya je?” “No body knows” Mommy ta fad’a tana mai mik’ewa ta k’araso inda yake. “Baka farin cikine? Yau?” D’an Satar kallon Gwaggo Asabe yayi yaga hankalinta sam baya kansu…. A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace “Mommy ba wanda ya kaini farin ciki a kaff fad’in duniyar nan a yau! Amman no matter how i tried sam! Na kasa ignoring some facts ne, If I were in Arshaad shoes I would have die by now. Gara ka san abu ba naka bane ba tun farko akan ka saka rai kuma azo baka samuba daga k’arshe.” Ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e kafin ta shafa fuskarshi ta d’anyi murmushi a ranta ta raya ‘Inama ace kowa irin zuciyar Aslam d’inta gareshi, da duniya ta zauna lafiya’…. Muryarsa ce ta katseta jin yana cewa “Bara inje In fara nemansa” “Ka fara zuwa ko kai da Auwal ne ya rakaka ko? Karka janyo mata abun magana mana a wajen k’awayenta” Sunkuyar da kai yayi chaan! Ya d’ago yace “okay” Sarai Mommy ta san ba iya kiran Auwal d’in zai yi ba shiyasa ta yanke shawarar ta kirashi da kanta. Yana d’aki. Shi kad’ai… Ya gwada kiran Arshaad yafi sau nawa amma baya d’auka! K’arshema kashe wayoyinshi yayi dan in ya kira sai dai yaji ance switchoff! Babban abubda yafi damunshi shine rashin sanin inda Arshaad d’in yake… Suna dawowa gidansu ya nufa Aaima ce take fad’a mishi yadda suka yi d’azun dan haka hankalinshi a tashe ya fita nemanshi amman ba inda bai dubaba ya nemeshi ya rasa! Yana a haka kiran Mommy ya shigo wayarsa. Bayan sun gaisa ne tace “Yazo ya raka Aslam wajen Amarya, k’awayenta suna jiransu ba su tafi ba sannan ya d’an taho da snacks da kaji” Da “to” ya amsa ta daga nan suka yi sallama. Ko da suka gama wayar sai da ya kusan minti biyar yana tunani tukunna ya mik’e ya fita…. Kamar Mommy ta sani Aslam yana fita d’akin shi ya nufa ya zauna shi kad’ai yanata tunani.. Chan kuma ya zaro waya ya fara gwada kiran Arshaad amman sai yaji a kashe! Har ga Allah yana son Huda fiye da tunani dan inda ace bai sameta ba to da bai san ya zata kasance da shi ba amman kuma yana matuk’ar jin tausayin Arshaad! Bai san me yake going through ba! A fili yace “Wannan wacce irin k’addara ce? Ya Allah Astaghfirullah.” Ya jima tukun yaji knocking. Izinin shigowa ya bada ba tare da ya san wanene ba. Kallon kallo suka tsaya yi wa juna shi da Auwal bayan ya shigo, chaan kuma Auwal d’in ya k’araso yazo ya zauna kusa da shi. Ko gaisawa ba suyi ba ya fara magana “Yanzu ya za mu yi? Su Abba sun k’ulla abunda zai iya janyo babbar matsala su Mommy su kuma naga kamar they are okay with it! Ko ka san yanzun nan ta kirani wai In taho da kajin Amarya muje in rakaka a yi siyan baki As if ba abunda ya faru. Aslam na san kaima baka son auren nan amma idan kace za kayi shiru ko kuma kace bara ka yiwa su Abba biyayya dan kar su ji ba dad’i to akwai matsala fa! I can’t even begin to tell you yadda Arshaad yake son Huda. You have to speak tun kafin a lalata muku future ku duka ukun. Dubafa yadda kayi fainting amman bayin Allah n nan ba wanda a cikinsu yayi yunk’urin yace a raba auren! Duba kaga Arshaad is no where to be found amma ba wanda ya damu! Ita kanta Huda na san ba zata ganu ba yanzu, Iya event d’insu da bai je ba jiya sai da ta shiga tashin hankali! Ku yi ending abun nan tun kafin ya janyo matsala Aslam kar ka yi shiru ka cuci kanka.” Tun da Auwal ya fara magana Aslam ya kafeshi da idanuwa, sai da ya kai aya sannan ya d’auke idanunsa daga kansa ya mik’e tsaye kafin yace “Like Mommy said! Mu je ayi siyan bakin, a samu a mayar da friends d’inta gida.” Yana gama fad’in haka ya wuce yayi gaba. Jiki a sanyaye haka Auwal ya mik’e ya d’auki ledar da ya shigo da ita ya bi bayanshi yana mamakin firgici, b’acin rai da tsananin tashin hankalin da ya hango a kwayar idanun Aslam d’in. Auwal ne ya kira Sakina… Kamar ba zata d’auka ba sai kuma ta d’aga. Tana d’auka bai jira jin tsiwarta ba yace “Muna parlour, ku fito” Tana ajjiye wayar, ta fad’a musu dan haka suka mik’e suka fita. Yadda al’ada take ake siyan baki haka aka yi.. 500 thousand suka yi demanding Auwal kuma ya basu 1M! Kud’in k’in shiga account d’aya yayi tashi d’aya sai da suka bada account wajen uku tukunna ya juye musu..... K’awayensu kasa hak’uri suka yi sai da d’ayar ta d’an matso k’asa k’asa ta tambayi Sakina “ya akai aka samu chanjen Ango ne?” “Haka al’adar mu take! Muna yin Angon bogi a wasu events d’in” Haka kawai tace musu daga nan ta kauda kai. Tabbas bata gamsu da ita ba amman ganin yadda ta turb’une fuska kuma ta san halinta hakan ya sa kawai ta hak’ura ta koma gefe ta ja bakinta ta yi shiru. Ita kuwa Sakina ba wani abun bane ya sake tunzurata sai d’ayar k’awar tasu wadda ta lura da ita tun da aka fara siyan bakin! In banda rawar kai da shishshigewa Auwal ba abunda ta saka a gaba. Duk da ta lura da yadda yake d’an basar da ita..... Har aka yi siyan bakin aka gama in banda gaisuwa ba abunda ya shiga tsakanin su da Aslam. Ana gamawa ba tare da b’ata lokaci ba dan dare yayi Auwal yace “su taso a maidasu gida” Dan dauriya kawai yake yi amman baya jin dad’i, kamar shi ne Arshaad haka yake jinshi gaba d’aya jikinshi yayi sanyi, kana ganinshi ka san baya jin dad’i duk yayi wani iri gashi kanshi sai faman ciwo yake yi. Ganin ba zai iya kaisu shi kad’ai ba yasa bayan sun fita ya nemi layin drivers d’in estate d’in mutum biyu yace “su zo akwai ragowar mutane su taya shi maida su” Cikin minti k’alilan suka shigo da motocin compound d’in gidan su Aslam su biyu. Tun kafin su gama parking ya bud’e gaban motar shi ya juyo yana kallon Sakina, suna had’a ido yace mata “bismillah” D’auke kai tayi ta kama hannnun Khadija ta fara ja tana cewa “Zo mu je mu shiga wachchar..” Da sauri wannan k’awar tasu tazo ta wuce ta gaban Sakina ta shige gaban motar Auwal d’in inda ya bud’ewa Sakina ta zauna kafin ta juyo tana wani shu’umin murmushi tace mishi “thankyou” Sakina bata san ya aka yi ba kawai ganinta tayi a bakin motar a tsaye! Batare da ta kalleshiba ta bud’e baya ta shiga ta zauna Khadijah ma ganin ta cikata ta nufi motar ya sanya ta biyota itama ta shiga ta zauna ta rufe matar dan tafiyarsu d’aya. Ragowar y’an mata biyun kuma suka shiga motocin drivers d’in. K’amewa Auwal yayi a wajen ya kasa motsi, mamaki fal a ranshi, da kyar bayan ragowar motocin sun fita ya samu ya ja k’afafuwansa ya shiga ya tada motar…… Da gangan ya saita madubin gaban motar daidai fuskarta aikuwa ya ga ta had’e rai kamar an aiko mata da sak’on mutuwa! A take ya ji dariya ta taso masa, anya kuwa abunda yake tunani shi d’in ne? Sakina fa!? Kenan daman ta san tana sonshi amma take ta faman wahalar da shi haka? Woow!! Allah yasa to hakan ne dan in dai kuwa hakan ne da gaske to tabbas sai ya fi ko wanne d’an Adam farin ciki a fad’in duniya….. Haka nan shi kad’ai yana ta sak’e sak’e a ransa sai faman murmushi yake yi shi kad’ai yana driving wanda hakan kuma ba k’aramin tafiya da imanin k’awar tasu wadda ta shigo ta zauna a gaba gefen shi yayi ba. Sakina tana ganinta har wani juyawa tayi tana facing Auwal d’in tana murmushi itama, ji tayi kamar ta shak’o ta! In banda tafarfasa babu abunda zuciyarta take yi tun lokacin da k’awar tasu ta shige motar ta zauna har kawo yanzu.. Numfashinta har wani d’ad’d’aukewa yake yi! Itafa daman tun a school ta tsani Yarinyar nan dan ko ishashshen shiri ma basa yi gata da k’aryar kud’i tun suna school dan duk waya idan ta fito a hannunta ake fara gani (ta yi sneaking ta shigo da ita) Gata da shegen rawar kai da son a sani shiyasa kwata kwata ita Yarinyar bata yi mata ba! Ko inviting d’inta basu yi ba daga ita har Huda amma ba event d’in da bata zo ba! Kalleta ba dangin Iya bare na Baba amman itace har kusan 11 a waje! Ta taho kawo Amaryar da ba wani shiri suke yi ba... Kamar idanuwanta za su fad’o haka ta tak’ark’are take zabgawa Yarinyar harara…. Sarai Auwal yana sane da ita don yana kallonta! Wani farin ciki yake ji kamar ya zuba ruwa a k’asa ya sha. Wai da gaske Sakina kishinsa take yi har haka? Tayay to zai tabbatar? Ya yiwa kansa tanbayar. Wani malalacin murmushi ya saki ta gefen bakinshi… A hankali ya juyo ya kalli k’awar tasu wadda ita ma shi d’in take kallo, tun ranar cocktail ya tafi da imaninta, jiya har mafarkinshi ta yi! Yau kuwa ba zata bari ya sub’uce mata ba in sha Allah… Murmushi ya sakar mata ganin itama shi d’in take kallo, a hankali but yadda ya san Sakina za ta ji yace “Hey dear beautiful, where to?” Da sauri ta koma baya ta jingina da jikin kujera jin zuciyarta zata faso waje. Wani sanyi Auwal yake ji yana ratsa shi dan yana kallonta duk ta cikin glass, he won’t lie this is the best day of his life!. Sai da budurwar gefen nashi ta sake cewa “Lamido crescent” Cikin rangwad’a da kashe murya tukunna ya jiyo ta dan gaba d’aya hankalinshi yana kan Sakina. “Okay” Kawai yace yana mai karya kan motar dan har sun fara gocewa daga hanyar da za ta kaisu Lamido Crescent d’in. Da mamaki Sakina ta mik’e ta zauna da kyau tana kallon yadda ya juya akalar motar ya d’au hanyar Lamido Crescent. Bata gama shan mamaki ba sai da taji budurwa tana cewa “Ko za ka saka min digits d’inka! Sai mu dinga gaisawa” Murmushi mai had’e da dariya yayi yana mai kallon fuskar Sakina wadda tashi d’aya idanuwanta suka cicciko da hawaye kamar zata fashe da kuka! Har ga Allah yad’an ji tausayinta amma yana so yayi comfirming a yau d’innan sannan idan ma bata saniba to yana so yau ta san tana son shi. Dan haka ya juya yana kallon Yarinyar gefen nashi cikin wani kalar voice yace “Yes sure, kamar kin shiga zuciyata dan nima i was just about to ask for your number” Tana shirin yin magana suka ji Sakina tace “Um, idan ka sha kwana za mu sauk’a” Da saura Khadija ta juyo tace mata “Ke da wa??” Cikin fushi Sakina tace “Ni da ke! Idan kuma ba zaki sauk’a ba to ni zan sauka! Kina gani fa sai ya kaita tukunna zai dawo ya kaimu saboda ga gantalallu.” Ya so dannewa amman sai da dariya tayi nasarar sub’uce mishi, hakan kuwa ba k’aramin sake tunzura Sakina yayi ba dan haka a zuciye ta sa hannu zata bud’e k’ofar motar a hakan ta tana tafiya ba tare da ta jira an tsaya d’in ba. Shi kuma Auwal yayi maza ya danna lock! Murmushi Yarinyar gaban motar tayi kafin tace “Kaga dear mu je ka fara ajjiye su, in yaso sai ka dawo ka kaini daga baya” “Alright” Auwal d’in yace daga nan taga ya saka signal yana shirin juya kan motar, a cikin ranta sai kuma ta raya ‘Kuma fa idan ya sauk’e su tare daga shi sai ita zasu dawo a motar, a hanya su yi ta hira!’ Dan haka da sauri sai tace “Da yake ke gantalalliyarce ba? Kin gwammaci a kaimu sannan a dawo da ke?” Yarinyar taji zafin maganar ba kad’an ba amman gudun kar ta zubar da girmanta a gaban sabon saurayinta yasa taja bakinta tayi shiru ta kawar da kai!. Rai a d’an b’ace Auwal d’in ya juyo yace “Sakina saboda ku fa tazo bikin nan! Wanne irin attitude ne haka?” Cikin fushi da bala’i tace “Ban sani ba!” Tana mai kauda kai. Gani tayi ya juya kawai yana shirin d’aukar hanyar gandun albasa dan haka tace “Wallahi baku isa ba! Ka fara kaita ka ajjiye ta tukunna ka kaimu.” Shiru ne ya biyo baya a motar kafin Auwal ya juya ya nufi hanyar Lamido Cresent zuciyarshi fess… Ganin yadda suka bawa iska ajiyarta suka shiga hirarasu kamar irin sun shekara da sanin juna d’innan ne ya sake tunzura Sakina tun ba ma da Yarinyar tazo sauk’a ba Auwal d’in har da wani ce mata “yana isa gida zai kirata in sha Allah” Ita dai Sakina da kyar take iya jan numfashi, wani irin tuk’uk’i take ji zuciyarta tana yi mata, bata tab’a jin b’acin rai da haushin mutun irin na yau ba! Ji take kamar ta rufesu da duka daga shi har ita..... Da k’arfi taji gabanta yayi wani mummunan fad’uwa..tabbas abunda take ji kishi ne! Kishin Auwal take yi, kenan sonshi take yi? Innalillahi wa innailaihirrajiun How? Taya ta bari haka ta faru da ita? A take sai kuma ta fara jin haushin kanta…tayaya ma zata nuna ta ji haushi k’iri k’iri har haka Allah dai yasa shima Auwal d’in bai fahimci abunda ta fahimta ba…. Ba tare da yace wata ta dawo gaba ba Ya ja motarshi yayi gaba yana waving wannan Yarinyar da suka sauk’e.. Yana d’aukar hanya yayi deleting number d’in nata da ya karb’a sannan ya danna mata block! Sai da suka yi tafiya mai d’an nisa sannan ya d’an juyo kad’an ya kalli Khadija yace “Y’ar uwar, dan Allah ki zama alk’alin mu” Ya fad’i hakan yana maida hankalin shi akan driving d’in da yake yi. Murmushi Khadija tayi kafin tace “ok Ina jin ka” Sai da yad’an juya ya kalli Sakina yaga yanda ta kumbura kafin yayi dariya yace “2 months kenan yanzu, Ina bin Sakina da proposal amman tak’i accepting. Inaso ki gaya min me kika fahimta a attitude d’inta na yanzu a game da ni? Please.” Murmushi Khadija tayi zuciyarta d’aya, a abinda ta fahimta tace “Kishi!” Dai dai nan yayi parking a k’ofar gidan Madu. Da sauri ta bud’e ta fito! Shima shi da Khadija suka fito suna yi mata dariya. Ganin tana k’ok’arin wucewa ne yasa yayi saurin rik’o vail d’inta Khadija kuma tayi masa ‘sai da safe’ ta wuce Ya amsa yana dariya dan still dariyar bata gama sakinsa ba saboda ba k’aramin nishad’i yake ji ba…. Cikin tsananin farin ciki ya dawo ta gabanta ya tsaya yace “Okay, no more pretends, kawai ki yarda.....” Maganarsace ta mak’ale sakamokon had’a ido da suka yi, da sauri ya matso kusa da ita yana cewa “Subahanallah Sakina daga wasa? Yi hak’uri, goge hawayen dan Allah na daina” Ya fada yana shirin sa hannu ya share mata hawayen nata duk ya rud’e. Da sauri ta buge mishi hannun sai kuma wani sabon kukan ya taho mata wannan karon har da sauti! Cikin kukan tace “Cika mini mayafi” Da sauri ya cika yana “Sorry Sakina, wasa ne fa. Naji to ba kya kishina…” Wucewa kawai yaga tayi ba tare da ta waiwayeshi ba ta fad’a cikin gidan ta rufo k’ofar gate d’in da sauri.... A hanyar shiga parlourn taga Khadija tana jiranta su shiga tare amman kawai ta wuceta ta shige, ko kallon inda take bata sake yi ba. Bata yarda sun had’a ido da su Ummu da ragowar mutanen parlourn da suke zaune suna hira kamar rana ba! Haka nan ta wuce su da sauri bayan tace musu “Ina wuni” Bata damu da jiran amsar su ba, ta haye sama abunta. D’akin da suke kwana ita da Khadija da Hudan ta shiga, tana shiga ta ajjiye vail da jakarta ta fad’a toilet da sauri ta saka sakata Sai a lokacin ta samu damar sakin kukan da ya mak’ale mata….. Kuka take tun k’arfinta kamar ranta zai fita, tabbas son auwal take yi wanda ita kanta bata san ya akayi soyayarshi tayi mata mugun kamu har haka ba! Gashi bata tashi farga ba sai yau kuma babban abun takaicin shine shima ya fahimta, Infact ko waye ma yaga yadda ta dinga acting ai dole ya fahimta tunda gashi ita kanta ta dalilin hakan ne ma yasa ta gane tana k’aunarsa. Ba abunda yafi k’ular da ita irin yadda ta zubar da girmanta ta fito k’arara ba tare da ta sakaya ba, kuma wani abun mamakin shine har yanzu zuciyarta tak’i yin sanyi haushi da zafin budurwar nan k’awar su take ji..ji take yi kamar ta hau watsapp yanzunnan ta gaggaya mata magana.. “Damn it! Tabbas Ina son Auwal” Ta furta a fili tana mai fashewa da kuka. Ko Auwal ne kad’ai d’a Namiji a duniyar nan ta riga ta yiwa kanta alk’awarin ba zata tab’a auren sa ba! Tun ranar farko da ya furta mata yana sonta Infact ta san ma ba aurene ya kawoshi wajenta ba, idan ma aurenne ita kam ba zata tab’a iyawa ba! Tayaya zata yarda ta zama surukar Granpa da wannan Mom d’in tasa da suka b’oye Huda! Har gobe tana tuno wasu abubuwan da taji a bakin su Baaba Talatu waenda Granpa d’in ya yiwa Mama tun farkon auren su da Abba besides ita tun kafin ta kai haka take adduar Ubangiji ya tsareta daga auren womanizer! Auwal kuwa ta san yaci uwar womanizer ma tunda gashi har d’a Jalila take shirin ajjiye mishi…. Tana kuka ta yanke shawarar abunda zata yi, duk da kuwa ta san zata sha wahala amman its the right thing to do. Da kyar ta iya cire kayanta ta yi wanka, ta na fitowa ko goge jikinta bata yi ba ta d’au waya ta kira Ashraff…. Tun lokacin da suka fara dating yake cewa yana so ya turo bare ma da yaji zancen bikin Huda, ya so ace an had’a da nasu Ita tak’i yarda.. Bayan sun gaisa ba tare da b’ata lokaci ba tace masa “Anytime from now yana iya yiwa Mahaifinsa magana sai a fara maganar auren nasu” Ba k’aramin murna Ashraff yayi ba, tana jin yadda yake ta faman zumud’i da rawar kai a cikin wayar Ita dai sai murmushi kawai take yi, k’arshema kasa hak’ura yayi yace mata “Bara yaje ya duba idan Daddyn nasu bai kwantaba sai yayi mishi maganar yanzun” Da kyar da sid’in goshi ta lallab’ashi dan 12 ma ta kusa tace yayi hak’uri ya bari gobe ya sameshi da safe ayi maganar. Ba dan yaso ba ya hak’ura… Ya yi ta janta da hira, ganin kamar a gajiye take dan daga ‘um’ sai ‘um’um’ take iya amsashi da su ya sanya kawai yace mata “ta huta” dan shi tunaninshi bashi yayi gajiyar biki ce take d’awainiya da ita. Tana ajjiye wayar Khadija na shigowa, nan ta tusa ta gaba da zancen Auwal… “Ta soshi mana, yana da hankali daga gani, ga kyau, gashi zata zauna kusa da Huda… Waye waye” Ita dai Sakina k’arshe juya mata baya tayi, tayi mata banza kamar tayi bacci, ganin haka yasa Khadijah kashe fitila, abunku da mai k’aramin ciki tuni tana kwanciya bacci yayi awon gaba da ita! Sakina kuwa yadda taga rana haka taga dare Wani abun mamakin shine duk wani labari da plans da Ashraff ya gama gaya mata na bayan aurensu yanzun she can’t help it but to picture it ita da Auwal! K’ok’ari take yi ta danna k’iyayyar shi a cikin zuciyarta sai dai abunda bata saniba ta riga ta makara dan already zazzafar soyayyarshi ta riga ta rinjayi y’ar guntuwar k’iyayyar da take k’ok’arin dannawa zuciyarta ta k’arfi da yaji..... BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 57 Da kyar Aslam ya iya mik’ewa bayan fitar su Auwal. A hankali yana jin yadda zuciyarshi take bugawa da mugun k’arfi ya isa bakin k’ofar d’akin da ya ga su Sakina sun fito daga ciki. Da kyar ya iya d’aga hannunshi ya fara knocking…. A hankali kamar mai kuka yaji tace “Sakina shigo mana” Dan ita har ga Allah ta yarda da Sakina wadda tace mata ‘bara su je su yi siyan baki ta dawo Ai ita a nan ma zata kwana yau’. A hankali ya lumshe idanuwasa ya bud’e kafin ya murza handle d’in ya tura k’ofar ya shiga da sallama. Da sauri ta d’ago jin muryar Namiji!… Duk da su Sakina sun ja mata mayafinta kafin su fita amman tana iya hangoshi! Har yanzun shadda ce a jikinshi abunda bata tab’a ganiba kenan. Sai taga yayi mata mugun kyau! Tsayi kamala surar jikinshi ta cikakkaen lafiyayyen Namiji ta fito sosai… A take zuciyarta ta hau bugawa da sauri da sauri..... Takowa yake yi izuwa bakin gadon wanda hakan da yake yi ji take kamar a kan zuciyarta yake yin tafiyar.. Duk taku d’aya sai taji tamkar numfashinta zai d’auke ne! Hakan yasa ta fara ja da baya.. Yana matsowa ita kuma tana ja baya. Aslam shi bai ma lura da yadda take ja da bayan ba har sai da yaga sun kai edge d’in gado tana neman mik’ewa, dan shi har ga Allah ba abunda idanuwanshi suke gane mishi sai ita, ruhinta! shiyasa sam bai lura da movement d’inta ba… Yana isowa dab da ita, ya jaa ya tsaya a bakin gadon. Ita kuma sai k’ok’ari take ta mik’e amman k’afarsa da side drawer sun tokare ta gashi har ta kai jikin fuskar gadon so ba daman ci gaba da matsawa… A hankali taga yana d’an sukuyowa….ji take yi kamar ta bud’e murya ta kurma ihu! Ko kuma ta tashi ta yi tsalle ta fad’a tsakiyar gadon daga nan ta samu ta sauk’a ta d’ayan side d’in… Ita har ga Allah tun farkon had’uwar ta da shi, sam! Bata k’aunar zama a kusa da shi (Aslam) Saboda muddin suna tare no matter how she tries kwata kwata zuciyarta bata barin wannan mahaukacin gudun data rasa dalilinsa! Gashi bata san dalilin da ya sa yaketa matsowa kusa da ita ba.. Ita fa yanzu abunda ya kamace su shine su nutsu su yi tunanin ya za suyi da rayuwarsu da wannan auren da aka k’ulla musu shiyasa duk a rud’e sannan a rikice take kuma gashi yanzu ya zo ya sake rikitata…… Tana cikin wannan tunanin ta ji fuskarsa daff da tata! A hankali taji yasa hannu ya yaye lullub’in laffayar fuskarta.. Had’a idanu suka yi! Da k’arfi zuciyoyinmu suka buga a tare! Sai da ya lumshe idanunsa ya bud’e kafin ya sak’ale kwayar idanuwanshi da tata sannan yace “Assalam alaiki, Maryama.” Da mugun k’arfi ta runtse idanuwanta sannan dai dai nan hawayen da bata san dalilinsu ba suka b’alle mata a take. A hankali ya hau yi mata kallon k’urilla…. Cikakkiyar minti d’aya ya d’auka yana kallon fuskarta kafin da kyar ya samu ya iya kokawa da zuciyarshi ya d’auke idanunsa yana mai lumshe su.. Wata zazzafar ajiyar zuciya ya sauk’e wadda itama bata san lokacin da ta sauk’e tata siririyar ajiyar zuciyar ba sakamokon numfashinsa mai d’umi da dad’in shak’a da ya ziyarci hancinta wanda har zuciyarta sai da ta amsa! Hakan ne kuma ya haifar mata da sauk’e ajiyar zuciyar da bata shirya wa ba… A hankali ta ji sauk’ar wani lallausar tafin hannu kamar na jarirai mai mugun taushi a kan kumatunta! A mugun zabure ta bud’e idanuwanta da suka k’ank’ance suka yi jaa ta zuba masa su.. Bai damu da kallon da take yi masa ba! Kallonta kawai yake yi yana goge mata hawayen nata… Idanuwansa da ya zuba mata ya kafeta da su ne ya sanya ta runtse nata idanuwan jikinta na wani mugun rawa!. Wata ajiyar zuciyar kawai ya sake sauk’ewa...yana gama goge hawayen ya mik’e da sauri dan ba k’aramin kokawa yake yi da zuciyarsa ba tun lokacin da ya shigo! Sai da ya lumshe ido na some seconds tukunna ya bud’e yace “Ki taso mu je kici abinci” Kafin ya rufe bakinsa tace “N na na k’oshi” Tana mai jan numfashi har yanzu jikinta bai daina rawa ba. Be ce mata komai ba, ya sa kai ya fice a d’akin. Minti kad’an ya dawo da ledojin da Auwal ya shigo da su.. Gefenta ya nema waje ya zauna a bakin gadon! A hankali ya bud’e ledojin ya d’aura akan stool kafin yace “Oya, gashi ki ci. Akwai wani abun da kike buk’ata?” Da sauri ta girgiza kai alamar ‘a’a’. A hankali ya mik’e yace “Sai da safe” Tun kafin ya rufe bakinshi tace “Allah ya kaimu” Don so take ya fita. Shima lura da hakan da yayi ne dama ya sanya kawai ya mik’e d’in. Ajiyar zuciya ya sauk’e kamar zai ce wani abun sai kuma kawai yace “Allah ya tashe mu lafiya” Yana mai juyawa ya fita daga d’akin gaba d’aya” Yana fita ta sauk’e wata wawiyar ajiyar zuciya… Har ta d’an zauna sai kuma ta mik’e da sauri ta isa bakin k’ofar ta murza key ta zare ta taho da shi ta ajjiye a kan side drawer tana ta tunani…. Ta dad’e bata sha mamaki irin na yau ba! Yadda yake yin abu kan sa tsaye sannan kamar bashi da wata damuwa abun yayi mugun d’aure mata kai! Dubafa yadda ya wani zauna a kusa da ita sannan har da wani share mata hawaye.. Ita tana tunanin sai ta yi kusan kwanaki ma bata ganshiba daga nan ya bata takarda yace taje ta auri Arshaad d’inta Amman kalli abunda yayi tun yau.. Ba abunda yafi d’aure mata kai irin siyan bakin da aka yi sai kace waenda suka yi auren soyayya… Harga Allah yunwa take ji sosai ma kuwa amman d’aurewar da kanta yayi ne ya sanya ta mayar da kajin cikin ledarsu ta had’a da ledar drinks d’in ta saka a d’an k’aramin fridge d’in data gani a d’akin. Da kyar ta lallab’a ta yaye laffayar jikin ta ta ninke, ta shiga toilet ta d’auro alwala tazo ta nemi waje ta zauna dan already sun yi sallolinsu Magrib da Isha ita da su Sakina. A ranta ta gama ayyanawa tabbas idan aka yi d’an kwana biyu taji Aslam bai yi mata wata magana ba to ita kam zata tareshi da zancen ya saketa! Idan ma Mahaifiyar Ya Arshaad ta hana aurensu to zata hak’ura ta rungumi k’addara tayi facing karatunta idan Allah ya fito mata da wani ta yi aurenta amman ita kam ba zata iya zama da wannan murd’ad’d’en mutumin da bashi da alk’ibla ba! Infact tayaya ma zata zauna da mutumin da kullum in dai suna tare sai taji zuciyarta tana barazanar fashewa haka kurum salon yaje ya fasa mata zuciya a banza ya yiwa Mama da Abba da su Sakina asara, Inaa ba zai yiu ba! Da wannan tunanin ta kwanta akan lallausan gadon tana mai lumshe ido… Nan kuma ta fad’a tunanin Arshaad! Tana yi tana istighfari amma sam ta kasa dainawa. Tabbas sai ka rasa abu kake gane yawan son da kake yi mishi! A lokacin da take tare da Arshaad bata san tana sonshi haka ba sai yanxu da ta san In ba da kyar ba to ta rasa shi kenan har abada! Dan muddin Mahaifiyarsa bata basu go ahead ba to ita kuma tayi alk’awarin ko sonshi zai kasheta ba zata tab’a aurensa ba tare da albarkar ta ba! Besides sai ma ta fara nemo mafita akan wannan auren! She has to do something fast saboda taga take taken Aslam kamar shi zai iya hak’ura ya zauna da ita don ya faranta ran su Abba Kuma ta tabbata idan hakan ta faru to haka za su k’are rayuwarsu ba soyayya tunda ita dai zuciya d’aya Allah ya bata kuma ta riga ta damk’awa Ya Arshaad shima kuma Aslam d’in ta tabbata bai ya k’aunarta sai dai ya kawai ya zauna da ita saboda ba yadda ya iya To Ina riba? Garama shi Namiji ne anytime idan ya had’u da wadda yake so zai aura Ita fa? An cuceta an cuci Ya Arshaad d’inta..how she wish she can see him now..tana so taga halin da yake a ciki, bawan Allah d’azu ba kalar zargin da batayi mishi ba ashe fin k’arfinsa aka yi…. Bata san lokacin da wani mugun kuka ya kufce mata da k’arfi ba.…… Tunani da kuka basu barta ta rintsaba sai around 2:00am tukunna bacci ya kwasheta wanda bata yishi cikin dad’in rai ba. Kafin asuba ta farka sakamokon mugun ciwon kan da ya rufar mata, da zazzafan zazzab’i ko idanuwanta bata iya bud’ewa sosai in banda rawar sanyi ba abunda take yi..... Tanaji ana kiran sallah k’ok’ari take yi ta samu ta tashi amma sam ta gagara.... A b’angaren Aslam shima bai samu yayi ishashshen bacci ba kusan kwana yayi yana nafila.. A nan kan daddumar ya samu bacci ya saceshi. Kiran sallar farko da aka maka a masallacin cikin estate d’in ne ya farkar da shi, dan haka ya mik’e ya shige bathroom… Sai da yayi wanka ya d’auro alwala sannan ya fito ya d’an kimtsa ya zura jallabiya ya gabatar da fajr nafl, ya zauna karatu. Yana idarwa ana tada sallah dan haka a gurguje ya fice ya nufi mosque.. Ya so ya duba Huda amman gudun kar ya makara yasa ya fita da niyyar ana idarwa zai dawo ya duba ta. Azkar kawai yayi daga nan ya fito daga masallacin. A k’ofa suka had’u da Dad dan haka suka jera yana d’an yi mishi nasiha har suka iso gidan.. Jan hankalinshi yake sake yi akan ya rik’e amana dan Allah kar ya wulak’anta matar da suka zab’a masa, ya taushi zuciyarshi ya bata dukkan hakkin ta da kulawa wata rana zai k’aunaceta in sha Alla… Shi dai Aslam da ‘to’ ‘in sha Allah’ kawai yake ta binshi dan ya rasa dalilin da yasa zuciyarshi taketa faman azalzalarshi akan yaje ya dubata.. Sam ya kasa sukuni ballantana ya samu ya bawa Dad d’in hankalinshi.. Da kyar ya samu Dad ya barshi ya wuce side d’inshi, bayan yace mishi “ya tabbatar sun je sun samu Granpa”… ..saboda ta watsapp yaji yace mishi zai nemeshi tun jiya amman har yau shiru, kar aje ko fushi yayi shi kuma har ga Allah baya so ya je ya sameshi gudun rigimarshi yake kuma bai san a wanna mataki ya saka maganar auren Aslam d’in ba gara idan Aslam d’in yaje da kanshi maybe abun yazo da sauk’i… Da ‘to’ Aslam ya amsashi sannan suka yi sallama ya wuce side d’inshi yana dariya da mamakin Dad d’in k’iri k’iri ya hango tsoro a tartare da shi..wato sun yi abu amman kuma suna tsoro shine bara su tura shi.. Da wanna tunanin ya Isa bakin k’ofar d’akin da Huda take ciki ya d’anyi knocking sannan ya murza handle d’in da niyyar turawa amman k’ofar sai ta k’i motsi, a hankali yad’an sake yin knocking amman still yaji shiru… Yayi mata knocking yafi sau biyar amma yaji shiru dan haka ya d’an sassauta murya ya matsar da fuskarshi jikin k’ofar ya fara kiran sunanta… A take gabanshi ya yanke ya fad’i! Dan in dai kunnuwanshi sun ji mishi dede to kamar sheshshek’a da jan numfashi yake jiyowa yana tashi daga d’akin! Da mugun sauri ya koma d’akinsa ya d’auko spare key sannan yazo ya zura ya murza ya tura da sauri ya shiga A k’udundune ya hangota a kwance tana rawar sanyi Da sauri ya k’arasa ya d’agota ya zaunar sannan ya fara shafa goshinta wanda ya ji ya d’auki zafi ba na wasa ba. A firgice yake kallonta, gaba d’aya ta jik’e da gumi kamar an watsa mata ruwa, pillow ya jawo ya kwantar da ita sannan ya mik’e ya nufi toilet ya jik’o towel ya fito.. Hannuwanta da tafin k’afarta sai saman goshinta ya shiga shafawa towel d’in amman kamar k’ara mata zazzab’in ma yake yi dan haka kawai ya mik’e ya je d’akinsa ya d’au waya ya kira Doctor tukunna ya dawo ya ci gaba da goga mata… ji yake kamar yayi kuka gani yake yi duk laifinshine dan inda a d’aki d’aya suke da tun farkon zazzab’in nata zai yi noticing ya san abun yi….. A hankali ya ga tana bud’e idonta, da sauri ya matso yace “sannu ya jikin?” A hankali ta shiga motsa bakinta a lamun magana take son yi.. Hannunshi yasa a a gefen kumatunta yana kallonta kafin yace “me kikeso? Tell me. Yanzu Doctor zai zoo kin ji, sannu” ya k’arashe maganar a hankali yana kallon bakinta da take k’ok’arin yin magana.. Murmushi ya ga ta fara kafin yaji tace “Ya Arshaad! yaushe ka zo? Ina ka tafi ka bar ni?” Tana mai kallon cikin idanunsa. Da sauri sannan da mugun k’arfi Aslam ya runtse idanuwanshi..... Magana take yi amman ba ya fahimta, babu abunda yake iya ji sai ‘Ya Arshaad’ d’in da take ta ambata a duk k’arshe ko farkon maganarta!….. Ya so ya zauna ya cigaba da shafa mata jik’akk’en towel d’in a samu fever d’inta ya sauk’a amman sai ya kasa! A hankali ya mik’e tsaye daga kan gadon yana ganin dishi dishi…, Ji yayi kawai ta fashe da kuka sannan ta fara k’ok’arin ruk’o hannunshi, cikin kukan tace “Dan Allah kar ka tafi, mu zauna a cikin mafarkin nan da nake yi ni da kai har abada, kar ka tafi ka barni bana so in farka idan kuma zan farka to sai ka yi min alk’awarin zaka dawo gar....” Wucewa yayi da sauri ya fice a d’akin ya barta nan tana ta faman surutai.. Da kyar ya iya kai kanshi d’aki yana zuwa ya dafa bango da d’ayan hannunsa d’ayan kuma ya dafa goshinsa yana jin yadda zuciyarshi take harbawa da tafarfasa tamkar zata fashe! Sunayen Allah ya hau karantowa sannan ya fara k’ok’arin controlling kanshi… Tabbas ya san zafin zazzab’i ne ya sanya ta take hallucinating amman hakan bai hanashi jin kamar zai mutu ba! Da kyar ya samu ya zaro waya ya kira Mommy yace mata “ta zo Hudan bata da lafiya” Daga nan ya lallab’a ya koma bakin gado ya zauna ya jingina bayanshi a fuskar gadon ya lumshe idanuwanshi..... Kamar yadda su Umma suka tsara! Yau da sassafe k’arfe 7:00 na safe Anty Zainab ta biyo mata suka kama hanya… Tafiyar awa uku ce ta kaisu d’an k’aramin k’auyen da za su je wanda tsaf In ka tsaya zaka iya k’irga gidajen wajen kaff d’insu. Wani gida isolated a chan nesa suka nufa, a dai dai hanyar gidan akwai wata y’ar majalisar wasu matasa a k’asan wata k’atotuwar bishiyar mangoro dai dai suna zuwa za su wuce wani a cikinsu yace “Ga wasu b’atattun yau ma sun zo” Sarai sun ji sa ba wannan ne a gabansu ba dan haka suka wuce suka yi cikin gidan…. Sai da suka d’an jirashi ya karya sannan ya samu damar ganinsu. Suna shiga suka nemi waje suka zauna. Da kyar Umma ta iya ce mishi “Ina kwana” Bata jira amsawar shi ba ta hau zuba… Har da cewa da ya san ba zai yi aikin ba tun jiya da bai ce ta k’ara mishi kud’i ba! Sai da Anty Zainab ta d’an zungureta tukunna aka samu ta yi shiru. Gyaran murya Anty Zainab d’in tayi sannan tace “Ni a ganina yanzu aikin gama ya riga ya gama, tunda har ta tare. Yanzu abunda muke so shine a tabbatar da auren Jalila da shi Arshaad d’in sannan a san yadda za a yi a taimakawa Jalila ta fitar da Huda daga gidan!” Shiruuu, mutumin ya d’ab yi ya lumshe idanuwanshi.. Chaan! Ya bud’e, ya kalleta yace “Na riga fa na yi abunda zan yi! Kun tabbatar anyi auren ita Huda da shi Arshaad d’in kuwa? Dan ni gaskiya bincikena bai nuna min an yi ba.” Da sauri Umma tace “Shirme kenan! To bari kaji.. Jiya ma a gidanshi ta kwana k’arshen magana kenan. Kuma na tabbatar idan aka bincika ma yanzu haka ciki gareta! In dai binciken tsakani da Allah za a yi”. Murmushi kawai yayi kafin yace “shikenan. Ku d’an jira ni” Daga nan ya mik’e ya fita. Kamar minti biyar haka ya dawo… Wata bak’ar laya kawai ya mik’o musu bayan ya zauna Anty Zainab ce tasa hannu ta karb’a dan ita Umma in banda tura baki da kumbure kumbure ba abunda take yi. Sai da ta karb’a sannan yace “Ku nutsu! Ku bani dukkan hankalinku! Dan kunga wannan abun da na baku shine kankat! Amman muddin kuka yi ganganci aka samu matsala to abun zai dawo kanku ne! Kun amince?” “Eh” Suka had’a baki duk su biyun. Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya sake cewa “Shawara itace.. Ku sake bincikawa ku tabbatar an yi auren dan in dai basa tare kuma akayi wannan aikin mai zafi to idan ya tafi bai samesu ba kan ku zai dawo! Bi ma’ana Auren d’aya daga cikinku ne zai mutu.” Murmushin takaici Umma tayi kafin tace “Mallan” Yace “Na’am” tace “fad’a mana yadda za ayi amfani da ita kawai! Maganar tare kam Huda da arshaad suna tare.” “To shikenan. Aikin ba mai wani wahala bane ba, ita wannan abar dana baku cikin dare za a tashi a k’ona ta k’urmus! Shikenan Ko wanne irin kalar aure aka k’ulla musu sai sun rabu! Rabuwa ta har abada, idan har kinga sun dawo sun zauna to sai dai in za a iya maida layarnan ta koma dede yadda take kafin a k’onata!. Sannan shi kuma wannan” yayi maganar yana basu wani turare kafin yace “Ita Jalilar za ki bawa ta shafa a jikinta, ta tabbatar shi Yaron ya shak’a da Mahaifiyarsa da Mahaifinsa da duk wani wanda zai iya shige mishi gaba wajen auren, in sha Allah ba za ayi awa 24 ba za a d’aura musu aure.” Sai a sannan Umma tayi murmushi tace “sun gode” Daga nan suka d’anyi wasu maganganun ragowar matsalolinsu…. Sun d’an jima tukun suka mik’e suka fara shirin tafiya.. Har suka fita Malamin nan yana ta nanata musu “su tabbatar sun yi conforming auren Huda da Arshaad kafin su yi amfani da layar na”. Zuciyoyinmu fess haka suka fito Umma ta karb’a kayan ta danna a jaka suka wuce..... A gigice Mommy ta shiga d’akin Huda! Hakan yayi dai dai da k’arasowar Doc shima. Aslam bai bari Mommy ta gansa ba, suna zuwa k’ofar d’akin shi da Doc d’in ya fara jiyo muryarta a rikice tana yiwa Huda magana dan haka yana nunawa Doc d’akin ya juya ya koma d’akinsa. Sai da ta sha allurai sannan aka jona mata drip tukunna ta fara gane waye a kanta. Mommy kuwa da ta samu Huda ta d’an farfad’o sai ta hau fushi da Aslam. Bawan Allah shi kam bai ma san tana yi ba yana d’aki yana fama. Ita da Gwaggo Asabe ne suka yi jinya, kafin dare ta d’an warware amman ba sosai ba Sai a sannan ta samu ta kira su Mama….Lokacin ita d’aya ce a d’akin Gwaggo Asabe ta tafi kitchen Ita kuma Mommy taje shiryawa Dad table…. Ba yadda bata yi dasu ba akan su turo mata Sakina bata jin dad’in zaman ita d’aya amman sam suka k’i suka ce “in ita bata da hankali to su suna da shi” K’arshema fad’a suka rufeta da shi Mama tayi ta gama ta bawa Ummu itama ta yi nata ta mik’awa Shuwa! Haka nan ta hak’ura ba yadda ta iya. Bata ce musu bata da lafiya ba dan karsu d’aga hankalinsu. Mommy a d’akin suka kwana tare da Ita da Gwaggo Asabe. Ita Huda har mamakin tattali da k’aunar da Mommy da Gwaggo Asabe suke nuna mata take yi, ko tari tayi nan da nan hankalinsu zai tashi, ba abunda yafi d’aure mata kai irin yadda Mommy take cika bathtub da ruwan d’umi tace ta shiga, a ranar sai da tayi mata sitbath yafi sau biyar!. Ita dai abun mamaki yake bata har ga Allah, gashi duk da ba wai son Aslam take yi ba amma sai ta tsinci kanta da mugun kunyar Mommy da Gwaggo Asaben, sam ta kasa sakewa a d’akin. Da kyar ta d’an samu bacci kad’an, daga nan ta farka idonta ya bushe, sam ta kasa komawa dan haka ta mik’e tayi alwallah ta fito ta d’au hijabi a cikin akwatin kayanta da tazo dashi ta tada sallah. Shima Aslam bai samu wani isheshshen bacci ba, so yake yaje yaga jikin nata amma d’azu k’iri k’iri Mommy ta hanashi shiga d’akin da suka had’u a k’ofa! Kuma tak’i kulashi. Kafin ya kwanta ya kirata yafi sau nawa amman tak’i d’auka, dan haka shima da yaga ya kasa baccin sai ya mik’e ya fara jero nafilfili….. A Daren ranar ne kuma Umma ta k’ona layarta! Bayan ta yiwa Jalila waya tayi mata kwatancen mansion d’in da suke ita kuma tayi mata alk’awarin ‘gobe da safe zata zo mata ta sak’on da zai saka ta auri Arshaad’ Sannan tace mata “ta kwantar da hankalinta zata fitar da Huda a gidan in shaa Allah” Sai a sannan Jalila ta d’an nutsu dan tun jiya da taji a wajen Umman an kai Huda gidan Arshaad shikenan ta birkice ta susuce ko bacci bata yi ba sai kuka take ta yi duk ta fita hayyacinta. Ba k’aramin dad’i taji a rantaba kuwa. Haka ta kwanta zuciyarta fess tana kwanciya bacci mai mugun dad’i yayi awon gaba da ita! Wanda ta dad’e bata yi ba. Washegari da sassafe y’ay’an Gwaggwo Asabe su biyu suka iso, da y’an yaransu k’anana. Yadda Gwaggo Asabe take da kirki haka suna y’ay’anta. Sai a sannan Huda ta d’an sake ta d’anji sauk’i dan a cikin wuni d’aya suka saba ta sake sosai da su, hakan kuwa ba k’aramin dad’i ya yiwa su Mommy ba. Da yamma jikin nata da d’an kwari dan haka Mommy tace “ta shirya ta fito main parlour kar zaman d’akin ya gundureta. Suna zaune da yamman Huda na gefen Mommy akan kujera 3 seater a zaune ana hira a main parlour Aslam ya fito! Mommy tana ganinshi ta kauda kai gefe ta had’e rai. Dariya Gwaggo Asabe tayi tana tuna yadda d’azu ma yazo tayi hakan, ba yadda basu yi da ita ba amman tak’i kulashi k’arshe sai hak’ura yayi ya tafi kamar zai yi kuka.. Ita kam Huda rabon ta da shi tun ranar da aka kawota shekaran jiya da yayi mata sai da safe ya fita bayan ya kawo mata kaji. Gefen Mommy yazo ya zauna ya kamo hannunta ya b’ata rai kamar zai yi kuka. Bata kula shi ba bata kuma kwace hannunta ba amman ko kallon inda yake bata yi ba. Yaran Gwaggo Asabe Karima da Laurat ne Suka hau tsokanarshi dama sun saba. Daganan kuma aka hau gaggaisawa Karimar Yaranta uku maza itace Babba sai Laurat tana da twins y’an biyu mace da Namiji.. Aslam yana mugun son Yara dan haka ya sake yayi ta wasa da Yaran sunata yi mishi surutunsu na shirme. Da ido Gwaggo Asabe tayiwa Huda sign bayan sun had’a ido. Duk sai taji kunya ta rufeta, ita tama manta ashe basu gaisa ba! A hankali ta d’an kalleshi kafin tace “Ina wuni” Sai da ya ajjiye k’aramin Yaron Karima akan kafet sannan ya juyo yana kallonta yace “Alhamdulillah, ya jikin?” Sunkuyar da kanta tayi kafin tace “Alhamdulillah” Hannun Mommy da yake a cikin nashi yad’an damk’e kafin yace “Mommy bara mujewa Granpa” Bata kula shi ba. Hakan yasa ya mik’e tsaye yana mai sakin hannun nata yana murmushi kafin ya cewa Huda “D’auko hijabin ki mu je” Juyawa tayi ta d’an kalli Mommy. Muryar Gwaggo Asabe ce ta katseta jin tana cewa “ku je mana. Yi maza ki d’auko hijabin.” Ko da ta fito parlourn bata same shi ba, Gwaggo Asabe ce tace mata “yana compound” “To” tace sannan tacewa Mommy “yace za mu fita” Sai a sannann Mommyn tace “A dawo lafiya” Tanaji gabanta yana fad’uwa! Dan bata san ya had’uwar Huda da Granpa zata kasance ba. Su Karima ta juya ta cewa “sai ta dawo” da Gwaggo Asabe sannan ta sa kai ta fita. A tsaye ta hango shi chan bakin gate dan haka ta k’arasa.. Tunda ta taho ta lura da irin kallon da yake yi mata har ta k’araso inda yake ta tsaya. Sai da suka yi kusan 1 minute ba wanda ya motsa a cikin su kafin yace “Jikin da sauk’i sosai ko?” “Um” Kawai tace mishi dan ita haushima ya bata meye nashi na wani nanata tambayar! Bayan already ya riga ya tambayeta tun a ciki. Yanaso ya tambayeta ko akwai abun da take buk’ata amman ya lura kamar bata son yawan maganr tasu dan haka ya rabu da ita kawai, yace “muje” yana mai juyawa. A jere suke tafiya gwanin burgewa… Har suka k’arasa gate d’in gidan Granpa. Cikin girmamawa mai gadin ya bud’e musu gate d’in suka wuce bayan ya gaidasu. A k’asa Aslam suka tsaya ya kira Granpa ya bashi izinin hawa tukunna suka hau! Gaban Huda na dukan uku uku.. A chan sama suka sameshi, Parlournsa! Yana zaune a kan kujera ya baza takardu yana dubawa… Tunda suka shigo ya d’ago ya kafe Huda da ido! Hudan kasa k’arasowa tayi sakamokon yadda fad’uwar gabanta ya tsananta saboda yadda taga Granpa ya kafeta da ido… Har Aslam ya kusan k’arasawa inda yake sai kuma yaji kamar bata tare da shi dan haka ya juya. A chan farkon parlourn ya ganta tsaye ta sunkuyar da kanta. Granpa ya kalla sanan ya juya ya kalleta, d’an lumshe idanunsa yayi ya bud’e tukunna ya koma ya je inda take a tsaye, bata yi auni ba kawai taji ya kamo hannunta! Da sauri ta d’ago zata yi magana taga ya tsareta da kyawawan idanuwanshi, a hankali taji yace “Muje mana” still yana kallonta sannan da kyar ya samu ya iya zare idanuwanshi a nata ya juya ya fara tafiya… Tsintar k’afafuwanta kawai tayi suna takawa suna binshi. Sai da suka k’arasa gaban Granpa sannan yace mata “ta zauna” Shima ya ja ya zauna a kan kafet. A hankali yace “Granpa Good afternoon.” Ajiyar zuciya Granpa ya sauk’e kafin yace “Ya aiki? Ya sabon company?” A hankali Aslam d’in yace mishi “Alhamdulillah, komai Alhamdulillah.” Juyawa Granpa yayi ya kalli Huda kafin yace mata “You can leave now! Na riga na san an yi aurenku da Aslam ba tare da consent d’ina ba! So kije kawai ki jira sakamokon ki.” Da sauri Aslam ya d’ago idanuwanshi ya zuba mishi, zai yi magana Granpa ya d’aga mishi hannu, cikin d’an karaji ya cewa Huda “Leave! Kar In sake ganin ki a nan.” Jikinta na wani irin mahaukacin rawa ta mik’e, da sauri Aslam shima ya mik’e ya kamo hannunta sannan ya juyo yace “Granpa matata fa na kawo maka..” Cikin katseshi yace “Aslam ba zan tab’a yarda da wannan auren ba! Tun jiya nake expecting d’inka, i have a lot to discuss with you. Despite da fact that an yi auren ba tare da consent d’ina ba I can’t believe Yahaya da Aisha suna da guts d’in kwasota ita da y’an kawota su kawo mini cikin estate! Ranar inaji har wajen 12am ana yi min shige da fice a estate. You are very naive Aslam baka san halin mata ba… Ni na san Maryam itace zata k’ullawa Yakubu shi kuma yayi taking advantage d’in innocence d’inka ya mak’ala maka useless daughter d’insa….” Da k’arfi Aslam yace “Grandpa!!!!” K’ura masa ido Granpa yayi na kusan 1 minute haka shima Aslam d’in! Shi kanshi Granpa yayi mugun mamakin b’acin ran da ya hango a cikin idanuwan Aslam d’in… Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya janyo sandarshi ya dogara ya mik’e tsaye ya tako gaban Aslam wanda yake rik’e da hannun Huda yace “Allah ya isa tsakanina da Maryam!” Wani mugun kuka Huda ta fashe dashi ta fara k’ok’arin zare hannunta a cikin na Aslam amman gam! Ya rik’eta as if his life depends on her hands… Sam Granpa bai damuda kukan nata ba yaci gaba da magana “I loose Yakubu because of her and now I think I’m going to loose you duk a ta dalilinta! In banda tsabar rainin hankali tayaya za a d’aura maka aure da y’arta tashi d’aya babu shirin babu sanarwa a cikin rana d’aya? Ya akai aka fasa d’aurawa da Muhammad? Anyways bani da intrest d’in sauraron bayanin kowa, zab’i ne kaima zan baka kamar yadda na bawa Yakubu… Mun riga mun gama magana ni da Maryam 30 years ago akan babu ita babu family d’ina! So ba zan tab’a chanja decision d’ina ba ni matter who gets in the way Idan zan zama ni kad’ai a duniyar nan to zan rayu muddin kuka ce bayan maryam za ku bi ba zan damu ba I can survive alone. Yusuf da Yakubu sun zab’a abunda suke so, yanzu kai ya rage! Duk da kuwa Ina matuk’ar jin ciwo da zafi saboda Aslam kaine backbone d’in family d’ina kai ne na fi ji da a kaf cikin zuri’ata! Na san ka san da hakan amman hakan ba zai hanani ce maka ‘Ba zan tab’a accepting matarka a estate d’innan ba! Sannan within 4 hours ka fitar min da ita tun kafiin bad luck d’in Maryam ya shafi zuriata’ ba.” Nannauyar ajiyar zuciya Aslam ya sauk’e kafin yace “Granpa! Gaskiya d’aci ne da ita.. Abunda kake yi is not right. No matter how yo try fa wallahi ko ta ina aka bi aka zagayo sai an samu jininka a jikin Huda! Da ita kanta Anty maryam d’in you can never change that.” Da k’arfi Granpa yace “Shut up!!” Bai yi shiru ba yaci gaba “Idan kace babu ruwan ka da Anty Maryam ba zaka tab’a cewa ba ruwan ka da Huda ba tunda jikar ka ce y’ar gidan Abba! Ba yadda zaka yi dole fa tana cikin zuriarka itama.” Cikin b’acin rai yace “Aslam I’m warning you, keep quite!!!” Still bai yi shirun ba ya ci gaba “You need to wake up! Ka cire hatred a cikin ranka, Anty Maryam ta rigada ta shigo cikin rayuwarka cikin zuriarka cikin family d’inka ta yi dumu dumu babu yadda za kayi idan har kuwa kace zaka tsameta to tabbas zaka yiwa wannan family d’in babban gi’bi! The sooner you accept that the bett..….” Tassss!!!!! K’arar marin da Granpa ya d’auke Aslam da shi ya karad’e ilahirin makeken parlourn…. Tsit!! Haka parlourn yayi shiruuu, hatta kukan Huda d’aukewa yayi. Shafa wajen da aka mareshi yayi kafin ya d’ago da jajayen idanuwanshi yace “kar ka damu Nan da 4 hour zan fitar da matata daga eatate d’inka in sha Allah Granpa.” Yana gama fad’in haka ya juya ya ja hannun Huda suka nufi k’ofa….. A bakin k’ofar suka ci karo da Gramma da wasu books a hannunta.. Kallon ta kawai Aslam yayi, ba tare da yace komai ba ya kauce ya ja Hudan wadda take ta faman kuka suka fice dan sam ya kasa ma yin magana kuma ga dukkan alamu Gramma ta ji komai. Basu tarar da kowa a main parlour ba dan Magariba har tayi, sai da ya kaita d’akin da aka ajjiye ta tukunna ya cika mata hannu yace “D’auki abunda kike buk’ata mu tafi” Cikin kuka tace “Ina?” Kallonta yayi ya d’auke kai yace “Ki d’au abunda kike buk’ata nace!” Still tana kuka tace “Ya Aslam ba inda zan bika fa! Infact kawai ni ka maidani wajen Mama! Kar kaje kaima ka samu matsala da Granpa.” Ba tare da ya kalleta ba yace “Hudan for the last time! Ki d’au abunda kike da buk’ata If not zan jaki mu tafi empty handed.” Ya k’arashe maganar yana mai juyowa ya kalleta.. Kallon shi tayi still shima itan yake kallon cikin muryar kuka tace “Babufa inda zan je da kai! Ka maidani gidan Mama in yi rayuwata a chan” Cikin b’acin rai ya k’araso inda take kamar zai maketa yace “Baki da hankaline? Da auren nawa akan ki zan maidake gidan Maman da suka kawoki nan shekaran jiya jiya?!” Cikin kuka tace “Ai ba auren gaskiya bane ba! Besides daman ni inaso ince maka ka sakeni! Ya Aslam baka sona nima bana sonka! Ba zan iya wannan zaman ba. Su kansu su Abba a wannan karon basu k’ulla abunda zai yiu ba! So kawai mu nemawa kanmu mafita kayi hanyar ka in yi tawa, ka samu ka zauna lafiya da Granpa.” Aslam bai san lokacin da ya kamo kafad’unta ya manna ta da bango ba cikin tsananin b’acin rai yace “Ni kike cewa in sakeki! Eh?” Ya k’arashe tambayar cikin tsawa. Dai dai nan Mommy da Dad suka shigo. Da sauri Mommy ta k’arasa ta kwace Hudan wadda ta fara galabaita daga ruk’on da yayi mata tana jera mata sannu. Cikin tsananin b’acin rai ta d’ago bata yi wata wata ba ta d’auke shi da wani gigitaccen mari. Dai dai nan Abba da Daddy suma suka k’araso, har da Auwal wanda ya tuk’o su. Da sauri Abba ya k’araso yana cewa “Haba Mommy, me yayi haka?” Daddy ma k’arasowa yayi yana tambayar “me yake faruwa?” Bata amsa kowa daga cikin su ba ta wuce ta fita daga d’akin. Ganin Aslam d’in yak’i kulasu ya sa Abba ya k’arasa wajen Huda da take ta faman kuka ya janyota ya rungume ya shiga lallashinta… Da kyar aka samu tayi shiru. Tukunna Dad yace “Gramma ce ta kira ku kuma?” “Eh” kawai Abba yace still yana rik’e da Huda. Daddy ne ya dubi Dad kafin yace “Bara mu tafi da su kawai Za mu san abun yi daga nan” Da sauri Aslam yace “A’a Dad. Ina da gida a nan. Za mu tafi kawai kar ku damu.” Dafa shi Abba yayi, sai da ya juyo ya kalleshi tukunna yace mishi “Muje ko Aslam, kar ka yi gardama.........” BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 58 Lumshe idanuwansa yayi kawai ya bud’e daganan ya juya ya fita ba tare da yace musu komai ba. Direct sama d’akin Mommy ya wuce.. A tsaye ya sameta tana ta faman safa da marwa. Tana juyowa suka had’a ido, ckin b’acin rai tace “Juya ka fita Aslam, ba na son ganinka! Juya ka fita na ce. Anya Aslam kana son Yarinyar nan kamar yadda ka fad’a kuwa?” Bai fitan ba, ya k’araso inda take kawai yayi hugging d’inta. Sai da ta tsorata da jin yadda jikinsa yake rawa… Da sauri ta sa hannu ta d’ago sa, suna had’a ido yace “Mommy cewa fa tayi in saketa!!” Kallonsa tayi na some minutes kafin tace “Shiyasa kake neman illatata? Are you okay kuwa?. Na san Huda matarka ce but dukda haka duba da abunda ka yi mata shekaran jiya ana kawota sannan kasa kai ka fita ba tare da ka bata kulawar da ta kamata ba! Sannan d’azu kalli fa yadda ka buga ta da bango kuma kana ganin yadda ruk’on da kayi mata yake neman cutar da ita but baka damu ba! A gaskiya Aslam hakan ya sanya na fara kokwanto fa, dan inda ace son gaskiya kake yi mata ai at least ka iya jira ku d’an saba tukunna kafin komai amman ga wahalar biki da ta zuciya sannan kai kum...” Da sauri yace “Haba Mommy” Sai kuma ya sunkuyar da kanshi k’asa yana ji kamar k’asa ta tsage ya shiga.. Kamar zai yi kuka yace “Wallahi ba abunda nayi mata. Bama a d’akin na kwana ba ranar..” Kasa ci gaba da tsayawa a gabanta yayi dan haka kawai ya juya yace “Mun tafi” daga nan yayi sauri ya fita. A hankali Mommy ta fara smiling..a take ta ji zuciyarta ta yi sanyi. Tabbas soyayyar shi ga Huda da ta dasawa aya gaskiya ce! Dan haka ta bisu da fatan alkhairi, amma duk da haka zata kora mishi warning akan kar ya sake attempting abunda ta ga yayi mata d’azun…. A mota ya tarar da su Dad dan haka shima ya wuce tasa ya shiga suka nufi gate Gwaggo Asabe da su Karima suna d’aga musu hannu har suka fice… Kamar su jawo Huda su hanata tafiya haka suke ji amma duba da yadda su Dad d’in suke kamar a d’an firgice yasa suka bari akan za su tambayi Mommy idan ta sauk’o. Ba yadda Aslam bai yi ba akan su bari Huda ta zauna a side d’in Daddy ba amman furr suka k’i amincewa… Gashi daga k’arshema Dad d’in cewa yayi shima sai dai ya koma gidan da zama dan ba zai barta ita kad’ai ba.. Kamar yayi kuka, saboda duk sun bi sun d’aureshi da jijiyoyin jikinshi ta ko’ina, haka nan ya hak’ura kawai akan zai zauna a nan d’in ba dan yana so ba sai dan babu yadda ya iya. Jalila, tana garden lokacin da suka shigo. Ganin motoci ya sanya tayi sauri ta shige kitchen ta lab’e a jikin window tana hangen su tana jin su… Allah kuwa ya taimake ta suka yi parking a kusan windown side d’in kitchen d’in Daddy, dan yana kusa da main k’ofar shiga side d’in Abba. Tabbas! Idan har kunnuwanta sun jiye mata dede tou kuwa Huda da Aslam mata da miji ne! To amma tayaya hakan ta faru? How??… Gaba d’aya kanta ya kulle. Tana cikin wannan taradd’ad’in ta ji Auwal ya shigo suna magana shi da Mom, da sauri ta koma jikin k’ofar ta lab’e………. “Wai nan suka dawo?” Taji muryar Mom. “Yeah, Granpa ya sake yin what he is really good at!” Taji Auwal d’in ya bata amsa. Da sauri Mom tace “To kuma ai Daddy ya ce min shekaran jiya da safe sai da suka tura mishi sak’o bayan d’aurin auren Huda da Aslam d’in, ya ce musu ‘okay’ Mai ya faru yanzu kuma?” Ajiyar zuciya Auwal ya sauk’e kafin yace Mom ce musu fa kawai yayi ‘okay’ Dama ni na san akwai case a k’asa!. Mammy ita ta lalata komai wallahi, da ace ta bar Arshaad ya auri Hudan cikin sauk’i da duk haka bata faru ba. An yi miki magana kema akan ki ganar da ita amman da yake ba k’aunar Huda kike yi ba shiyasa kik’ak’i ki ce komai! Kuma still gashi dai Hudan surukarku ce kuma y’arku! Dan abunda yayi Abba shi yayi su Dad Kuma abunda yayi Arshaad shi yayi Aslam dan haka kinga babu riba kenan sai dai sake tarwatsa family ma da kuka yi dan yadda Granpa ya rufe ido ya gurzawa Aslam to wallahi kowa ya kuka da kanshi.” Yana gama fad’in haka ya wuce ya nufi side d’insa…. Tunda Mom take a estate d’in nan bata tab’a jin farin ciki irin na wannan ranar ba! Dan har goshinta ta saka a k’asa tayi sujjada bayan wucewar Auwal… Arshaad ya gudu Aslam kuma sun yi fad’a shi da Granpa in sha Allah she‘ll make sure it stays like this har izuwa lokacin da za a mallakawa Auwal d’inta MT!.. A b’angaren Jalila kuwa ba k’aramin k’ok’ari tayi ba wajen hana kanta kurma Ihun murna! Bayan ta doka wani uban tsalle, sannan ta fara juyi tana tik’ar rawa. Sai da ta lek’a taga Mom bata parlourn tukunna ta fito tab wuce d’akinta a ranta tana “Wato idan kana da uwa a duniyar nan ba wanda ya kaika gata!”. Tana shiga d’akin bata yi wata wata ba ta d’auki wayarta ta fara kiran Umma…… Tana d’aki a zaune tana goge wa Ya Ja’afar jiki kiran Jalila ya shigo… D’auka tayi ta saka a speaker ta ajjiye a gefe, za ta cigaba da abunda take yi. Ko gaisuwa babu Jalila tace “Ummana albishirinki” Da sauri ta ajjiye towel d’in hannunta ta d’au wayar jiki na rawa tace “Goro” …Nan Jalila ta shiga zayyano mata kaff abunda taji ta gani yanzunnan….. Shiruuu, Umma tayi, tana shirin yin magana ta yi an shigo ana kuka. Kamar an hankad’o Anty Zainab haka ta shiga d’akin a hargitse kamar mahaukaciya! A gigice Umma take kallon ta, sai da ta bari ta nemi waje ta zauna tukunna tace “Zainab lafiya kuwa??” Cikin kuka tace “Ba lafiya ba! Sadiya na shiga uku!!” Da sauri Umman tace “subahanallah mai ya faru?” Ta yi mata tambayar tana me d’aukar wayar ta kashe ta ajjiye a gefe. Da kyar Anty Zainab ta d’an tsayar da kukanta tace “saboda Allah tsofai tsofai da ni amman wai ni Baban Khadija ya rufe ido ya dank’ara wa saki har uku! Saboda tsabar idonshi sun rufe ya ma manta da biyun da ya tab’a yi mini”. Da mugun k’arfi gaban Umma ya yanke ya fad’i! Saboda lokaci d’aya kwakwalwarta ta d’auki chaji Tabbas ita ce ta tafka kuskure abun kuma ya koma kan Anty Zainab! Wadda daga rakiya gashi yanzu ta janyo mata….. Tana cikin wannan tunanin Anty Zainab d’in ta sauk’o ta matso kusa da ita kafin tace “Yi maza Sadiya d’au waya ki kirawo Jalila mu ji…Anya kuwa an yi auren nan? Ko dai zurma mu su Maryam suka yi? Dan wallahi masifarnan tana fad’omin maganar Malamin nan na jiya na tuna. Yi sauri Sadiya ki kirata mu ji, ta bincika mana sosai.. In dai maganarshi gaskiya ce to mu samu mu koma mishi a san abun yi tun da wuri! Kin ji Sadiya! Dan Allah kirawo ta mu ji……” Cikin In Ina Umma tace “Tt ta tam! Amman d’azun nan ma mun yi waya da ita kuma ta tabbatar min da cewa an yi auren.” Hannu biyu Anty Zainab ta d’aura a kai kafin tace “Innalillahi wa innailaihirrajiun Me ya faru da ni tou???” Ajiyar zuciya Umma ta sauk’e jikinta na rawa tace “To wai ke me ya had’a ku ne?” Cikin kuka Anty Zainab tace “Aure wai mutumin nan zai yi! Yarinya k’arama dan tsabar cin fuska shine bai gaya min ba, sai d’azu tukunna Baaba Talatu ta kirani take gaya min, ashe wai ita sun sani ita da Shuwa shine suka b’oye min wai dan kar in d’aga hankalina inzo inyi wani shirmen.. Sadiya abunda zai baki mamaki wallahi tallahi kawai zuwa nayi nace mishi ‘Ya zai yi min haka? Me yasa ya b’oye min? Ai da ya gaya min tun da wuri’ Kar ki k’ara kar ki rage daga haka kawai sai ya hau masifa, k’arshe yace In tattara in tafi ya sauk’e igiyoyinsa na aure kaff ukun da suke a kaina! Wai ya san in dai amaryar tasa tazo ba zan barta ta zauna ba. Ko kayana bai barni na kwasa ba da magariba dan bala’i ko kwana bai bari nayi ba ya kad’oni har da rufe gidansa. Ita kuma Baaba da na je mata daga jin magana bata tsaya taji ba’asi ba kawai ta hau fad’a! Wai ai laifi na ne, daman shiyasa suka k’i gaya min, ai ba a kaina Miji ya fara k’are aure ba, ai yanzu gashi na janyowa su Sadik haka yanzu zai dawo daga boarding ya tarar ba Maman shi a gidan K’iri k’iri Yaro ko secondary school bai gamaba amma ina k’ok’arin maidashi maraya, har su Khadija ma da suke gidan Miji sai ta shafesu… Ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, k’arshe ma ko zama bata barni nayi ba itama ta koreni!” Da sauri Umma tace “Yanzu kenan a nan za ki zauna?” Cikin share hawaye Anty Zainab tace “To ya zan yi? Ina zan je? Port harcourt ko Ina?” Ajiyar zuciya Umma ta sauk’e kafin tace “Ki kwantar da hankalinki, zai mayar da ke, kin ji ko, In sha Allah.” Cikin kuka Anty Zainab tace “Baban Khadija fa babban d’an ka’ida ne ke kin sani ba zai tab’a bari mu zauna da saki ukun nan ba” Cikin yin k’asa da murya Umma tace “Ki kwantar da hankalinki, za mu nemi mafita In sha Allah. Sannan ko hauka muke ba zamu bar auren nan ba yasin sai dai in me taurin ruhi ce kamar Maryam wadda ta nace sai da kyar! Tukunna aka samu ta bar gidan nan, to kinga idan irinta ce ba yanda muka iya dole mu barta amman shima sai mun ci ubanta wallahi. Maza basa kyautawa wallahi sam! Saboda Allah Ina ma lefin ya d’auko miki mai d’an shekaru. Fisabilillahi Ina Baban Khadija Ina sa’ar su Khadija?Tsofai tsofai da shi.” Da sauri Anty Zainab tace “Kuma budurwa!” Cikin karb’e zancen Umma tace “Ba zai ma yiu ba fa Wallahi! Dole mu san abun yi. Ki kwantar da hankalin kar ki saka damuwa a ranki, zamu nemi mafita. Bai isa ba wallahi, kin ji. Su Shuwan nan suna bani mamaki, daga an yi magana suce wani wai kar mutum yayi shirme in za ai mishi kishiya waye waye… Bayan su basu san zafinta ba! Tunda duk cikinsu babu wadda Mijinta ya tab’a yin koda budurwa ne a waje, sun kafa sun tsare nasu mazajen amman sun iya tak’ark’arewa suna yiwa mutum nasiha akan kishiya tsabar renin wayo! Su bar waenda suka san zafin kishiya su yi magana mana ba wai su tsayayyun matan da suka kafe mazajensu ba…” Ita dai Anty Zainab mik’ewa tayi ta isa kan gado ta kwanta ta juyawa Umma baya, dan taga abun nata kamar ya fara zama cin fuska kuma. Tana jinta tana ta bambami daga k’arshe ta yi shiru ta gyarawa Ya Ja’afar wanda yayi bacci kwanciyar sa ta lullub’e sa tazo ta nemi waje gefen Anty Zainab itama ta kwanta….. Ta gama rayawa a ranta gobe zata koma wajen mutumin nan tayi masa maganar Anty Zainab asan abun yi dan gaskiya tayi mugun tausaya mata. Amman kuma abunda yasa tayi shiru bata gaya mata gaskiyar lamarin yanzu ba shine ta lura aikin mutumin kamar yakan iya juyewa kuma waiwaye! Tunda gashi na Huda ya koma kan Anty Zainab d’in , dukda ya fad’a musu dama amma still kamata yayi ace aurenta da Aslam ne ya mutu ba wai na Anty Zainab ba tunda de Hudan aka yiwa abun so it doesn’t matter ko waye Mijin nata ita ya kamata a sako…. Kanta ya kulle dole ta koma wajenshi amman ba zata bari suje da Anty Zainab ba dan yadda take a rikicen nan haka kurum taje ta tunzura mutumin yayi mata nata aikin aje garin gyara nata a tab’o na Jalila da bai gama had’uwa ba. Ko da ace zata gaya mata Hudan ba Arshaad ta auraba to sai ta tabbatar Mutumin ya gama yi musu aiki mai kyau! An d’aura auren Jalila da Arshaad ta kamashi sosai ta samu fada a wajenshi tukunna, saboda kar aje aiki ya had’a masa biyu yak’i concentrating akan na Jalila sosai, ko kuma kuma yaje ya gyara na Anty Zainab wani abun ya samu na Jalila…. A ranar dai haka suka yi bacci duk su biyun rabi da rabi. Su Hudan suna shiga a parlourn suka tarar da Ummi da su Shuraim sunata shirya dining tare da masu aiki. Ummi tana ganinsu ta k’arasa inda suke tayi hugging Hudan tana mata sannu da zuwa. Cikin girmamawa suka gaisheta ita da Aslam, ta amsa musu da kulawa, daga nan suka gaisa da su Sudais, murna kuwa a wajen su kamar suyi me tunba ma da suka ganta har da akwati ba’ Su suka ja mata suka kai mata har d’aki Abba yaso su zauna a sama amman Aslam yace “a barsu a d’akin bak’i” shi da cewa ma yayi ita akai mata nata kayan sama shi a barshi zai zauna a d’akin bak’i, shiyasa kawai Abban yace “a kai mata akwatin ta nan d’akin bak’in”. Ita dai Huda so take tace ‘a barta ta tafi d’akinta’ amman bata san ta ina zata fara ba! Ta san a idon duniya da su Abba Aslam mijinta ne amman taya ake expecting tayi sharing d’aki da shi bayan ga d’akuna birjik kala kala a gidan. Su kuwa su Daddy dama tun kafin su fita daga gidan bayan Gramma ta kirasu suka gama deciding akan zasu san yadda za suyi su taho nan gidan ita da Aslam d’in daga nan kuma su ajjiyesu shi da Hudan a waje d’aya, dan sun lura tabbas sai sun d’an taka rawa a relationship d’in nasu tukunna za a samu su ma fara magana mai tsayi da hira a tsakaninsu. Abba ne ya umarcesu da su je su yi alwala ayi sallah kafin ayi dinner. Hudan so take su had’a ido da shi amman bata samu wannan damar ba. Abba kuwa sarai ya ganta shiyasa ya maida hankalinshi gaba d’aya kan Dad suka shiga hira…. Ganin ta a tsaya ne ya sanya Ummi ta k’araso inda take ta rik’e mata hannu tana murmushi kafin tace “Muje to nan d’inma in rakaki. Naga kin tsaya. Aslam muje In taka ma Amaryar taka, kunyar mu take ji naga alama” Juyawa kawai yayi ya fara tafiya. Ita kuma Ummi ta ja hannun Huda suka nufi d’akin.. A bakin k’ofar bayan taga shigewar Aslam ta ja ta tirje sannan ta kalli Ummi kamar za tayi kuka tace “Ummi wai nima a nan d’akin zamu zauna kuma ni da shi?” Dariya sosai ta bawa Ummin amman sai ta dake ta d’an b’ata rai kafin tace “Eh mana! So kike ya zauna shi kad’ai? Wa zai dinga gyara d’akin yana wanke band’aki? Ko so kike a dinga tura mishi su Linder suna shigar masa anyhow?” Da sauri tace “Ummi zan dinga zuwa kullum da safe ina mishi Allah” B’ata rai sosai Ummin tayi this time around kafin tace “Zamu b’ata da ke fa! Dole anan zaki zauna Huda. So kike idan yana buk’atar wani abu urgent sai ya nemoki kenan? Kinga, gara ki shirya fa dan hatta girki ma sai kin dinga yi masa nashi special ko da kala d’aya ne Breakfast Lunch da Dinner Kullum! Ko kin d’auka auren wasa ne?” Tabbas ta san da waennan abubuwan dan sai da Shuwa ta tsara mata komai amman ita dai a tunanin ta su Ummi da Abba zasu d’aga mata k’afa tunda ai ba shi takeso ba kuma sun sani…… Wani k’ululun takaicine ya tokare mata mak’oshi! Tayaya ma za ace saboda zata dinga yi mishi aikace aikace da abubuwa har wani kuma sai ta zauna da shi a d’aki d’aya dole! Sai kace wani baby.. Ji tayi Ummi ta ja hannunta sun shige d’akin sannann ta mayar a k’ofar ta rufe. Sai da ta kaita kan gado tukunna tace “Ki yi sallah ku fito dinner” Tana gama fad’in haka ta juya ta fice daga d’akin........ BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 59 Sai da Ummi ta fita tukunna Huda ta fahimci Aslam baya d’akin…har ta fara murna sai kuma ta ji k’arar ruwa a toilet. Kamar mara gaskiya haka ta zauna ta k’ame a guri d’aya har ya fito. Kallonta kawai yayi ya d’auke kai, ya fita. Sai a sannan ta sauk’e k’akk’arfar ajiyar zuciya sannan ta zabgawa k’ofar da ya bi ya fice harara kafin itama ta mik’e ta shiga toilet d’in tayi alwallah ta fito ta tayar da sallah.. Ta jima tana adduar Allah ya dawo da Ya Arshaad, watak’il idan su Abba suka ga idonshi su raba wannan auren, ta samu ta auri wanda take so itama yake sonta. Bayan ta shafa ta mik’e ta fita zuwa dining. Ummi da su Shuraim ne kawai akai, da alamun su Abba basu dawo daga mosque ba, Ummi tana ganinta tace “Ai yanzu nake shirin mik’ewa in lek’o ki, na ji shiru” Murmushi tayi ta k’arasa wajen, har ga Allah Ummi tana burge ta Ubangiji yana son bayin sa masu tuba bayan sun fahimci sun yi kuskure. Tana zuwa ta ja kujerar gefenta ta zauna suka fara hira ita da su Shuraim waenda suke a opposite d’insu ita da Ummi. Ko 5 minutes bata yi da zama ba su Abba suka shigo.. Opposite d’insu Abba ya zauna , ga mamakin Huda sai taga Aslam ya ja kujerar gefenta shima ya zauna! Hakan kuwa ba k’aramin dad’i ya yiwa Abba ba dan har kasa b’oye farin cikin sa yayi ya fara zuba murmushi… Ummi itama murmushin tayi kafin ta mik’e ta zagayo inda suke ta fara serving nasu.. Har ta gama Hudan tana zaune kyam! Sai da Ummin ta dawo tukunna k’asa k’asa tace mata “Ta tashi ta zubawa Aslam mana” A hankali ta mik’e dan ita har ga Allah wani abun ma kunyar Abba take ji.. Jiki ba kwari ta hau serving nashi, tana gamawa ta tura masa komai gabansa itama ta zubawa kanta abinci kala d’aya kawai d’an kad’an. Baka jin k’arar komai sai cokula.. Although ba Hudan bace ta dafa abincin amma yadda tayi serving nashi da yanda take zaune kusa da shi tabbas zai iya cewa this is the best dinner da ya tab’a having a rayuwarsa! Lokaci lokaci yake lumshe ido yana sauk’e ajiyar zuciya ba tare da kowa ya lura da shi ba. Abba ne ya fara jan tissue ya goge bakinsa ya sha ruwa yace “Alhamdulillah” daga nan ya mik’e ya juya ya nufi hanyar fita. Yadda ta san zai ji xeji, Ummi tace “Abba fita zaka yi ne?”. Bai juyo ba, be kuma kalleta ba kawai yasa kai ya fice. Ajjiye spoon d’insa Shuraim yayi ya mik’e ya bar wajen gaba d’aya ba tare da ya k’arasa cin abincin nasa ba. Jikin Ummi ba k’aramin sanyi yayi ba, ta san cewa tunda ta dawo Abba baya kulata amma tayi tunanin tunda a gaban su hudan ne zai kulata yau, ta samu ta d’an ji sanyi a ranta. A b’angaren Huda kuwa, ba k’aramin kunya taji ba shiyasa itama kwata kwata ta kasa ci gaba da zama a wajen dan bata so su had’a ido da Ummin, ta lura da yadda Shuraim ya had’a rai ya mik’e ya bar wajen, dan haka tana mik’ewa ta nufi sama side d’insu.. Tana shiga ta tarar da shi yana kuka! Da sauri ta k’arasa inda yake zaune akan gadon ta zauna ta kamo hannunsa, k’ok’arin mik’ewa ya fara yi dan haka da sauri tace “Shuraim wait, let’s talk mana. Ka daina kuka ka fad’amin me yake damunka, ka ji?” Ajiyar zuciya ya sauk’e ya share hawayenshi kafin yace mata “ba komai” kawai. B’ata rai tayi sanann tace “To shikenan! Bara kaga in tashi in tafi kuma ina sauk’a zan d’auki akwatina in bar gidan nan gaba d’aya in dai baka gaya min ba. Sannan sai na gayawa Abba da Ummi kana d’aki kanata kuka” Sai da ya gyara zamanshi ya fuskanceta sannan yace “Abba ne! Ya tsani Ummi. Tun lokacin data dawo daga tafiya baya kulata baya yi mata magana kwata kwata. Idan ita ta kula shima sai dai yayi mata banza ya wuce kamar yadda yayi yanzun. Kullum sai naga Ummi tana kuka not once sometimes a rana sai tayi kuka sau wajen biyar shi kuma he don’t care! Ban san meyasa Abba ya tsani Ummi ba, dama chan baya sonta yanzu kuma ya sake tsanarta!” Da sauri Huda tasa hannunta ta toshe masa baki, sannan tace “kar ka ce haka Shuraim, kar in sake jin irin haka a bakinka. Abba bai tsani Ummi ba, ka ji ko? Kawai maybe su d’anyi fad’a ne kad’an amman na san za su shirya soon, ka ji? Ka daina sakawa a ranka zasu shirya ya zama kamar basu tab’a yin fad’aba in sha Allah soon kuma, ka ji ko?” Still kuka yake yi, dan haka Huda tayi ta lallashinshi har sai da ta samu yayi shiru ta tilasta masa ya k’ara cin cookie a d’akin dan bai wani ci abinci sosai a k’asan ba tukunna ta mik’e ta d’auko mishi tooth brush d’inshi da bathrobe ta bashi tace yaje yayi wanka yazo ya kwanta idan ma game yake son yi sai su yi tare. Shuraim a zuciyarshi ya ji ya sake jin k’aunar Hudan, yadda ta tsaya take k’ok’arin taga yayi farin ciki hakan ba k’aramin dad’i yayi masa ba. Karb’a yayi ya fad’a toilet d’in ita kuma ta jona ps ta fara yi musu settings… Sai a lokacin Ummi ta bar bakin d’akin tana rik’e kukan da ya taho mata... Tana shiga d’akinta ta saki kukan, tabbas tayi kuskuren da ita kanta ba zata tab’a yafewa kanta ba! Kalla fa yadda Hudan take da hankali take k’aunar jininta amman haka nan tayi depriving d’inta childhood mai dad’i! Ta rabata da Mahaifinta! Ta sanyata ita da uwarta a k’unci basu ji ba basu gani ba duk saboda So da Burin mallakar Mijin da a yanzu ta riga ta hak’ura dan ta san ba zai tab’a accepting d’inta ba…. Ummi ta yi kuka ranar kamar ranta zai fita, tabbas zata samu lokaci ta ware ta rok’i Abba ya barta ta je taga Mama ta nemi yafiyarta sannan zata ta nemi yafiyar Hudan itama dan kwata kwata ta kasa sukuni tana jin zafi da dana sanin abunda ta aikata a baya Inama ana dawo da hannun agogo baya....... Abba Yana fita direct side d’in Daddy ya nufa, yana shiga ya tarar da su suma suna dinner su uku abunsu. ………Yanzu Mom ta samu sauk’in Jalila biyayya take yi mata kamar zatai mata sujjada! Duk abinda tace shi take yi sannan ta maida kanta k’asa kamar wata y’ar aiki, yau ma ana gama abinci ta d’iba ta wuce d’akinta har da cewa Mom d’in ‘ko akwai aikin da take so ayi mata?’ Murmushi kawai Mom d’in tayi mata sannan tace ‘ba komai’ already a ranta ta riga ta gama shiryawa akan gobe gobe za tayi mata korar kare! In sha Allah……. Kujera Abba ya ja ya zauna kusa da Daddy. Duk da ya k’oshi amma sai da Daddy ya saka shi yad’an tab’a wani abun. Auwal ne ya fara mik’ewa saboda yana da tulin aikin da yake son yi and yanaso yau ma ya sake gwada sa’ar shi ko Allah zai sa Sakina ta amsa wayarshi. Dan haka yayi musu ‘sai da safe’ ya wuce sama. Daga nan itama Mom ta mik’e suka fara tattare dining d’in ita da mai aikinta.. Tana shigewa Abba ya dubi Daddy yace “Daddy magana na zo mu yi akan Maryam!” Juyowa Daddy yayi ya bashi dukkannin attention d’insa kafin yace “Ina sauraronka, what about her?” Soundin so worried and disturbed Abba yace “Har yanzu bata d’aukar waya ta! Bata replying messages d’ina.. I think kawai mu je mu samu su Abba Madun maybe shi zai iya bata shawara ta d’auka” Ajiyar zuciya Daddy ya sauk’e kafin yace “Abba, I know what you are going through amma sai nake ganin kamar Maryam tana buk’atar more time kafin komai. Ka duba kaga irin abunda Mijinta yayi mata sannan na san ta san Granpa ya sallame mu daga estate saboda Huda kuma na san yanzun ma Huda zata iya gaya mata ya sake korarta! Gaskiya bana jin su kansu su Abba Madun za su goya mana baya ko da ace mun je mun same su da wannan maganar. Let’s assume ma sun goya mana bayan ni na san Maryam ba zata tab’a yarda ba a yanzu, kuma kaga idan suka bata shawara itama ta basu nata uzuri dole fa in aka auna aka duba za a ga ta fimu gaskiya ne. Sannan Granpa! Allah kad’ai ya san irin yawan y’an kallon da zamu kwasa da shi idan Maryam ta dawo gidan nan a yanzu!. Bawai zan yi backing out bane in daina goya maka baya ba not at all Abba, all I’m saying shine Ka kwantar da hankalinka mu d’an jira kad’an tukunna, na san dole Granpa zai sauk’o kwanan nan tunda yanzu case d’in ya shafi har Aslam, kaga daga nan sai mu san abun yi”. Ajiyar zuciya Abba ya sauk’e kafin yace “Na ji kuma na fahimceka. Amman nima inaso ka fahimceni… Daddy, Idan akwai abinda na sani wanda yake dahir! To shine ko da ace Granpa ya huce mun koma yayi accepting d’inmu da Huda to fa ba zai tab’a accepting Maryam ba kuma idan aka taso da zancen wani sabon case d’inne zai kuma b’ullowa, kaga kenan an koma square 1! So ni a gani na this is the right time da ya kamata muje ayi magana a gyara komai, In yaso idan ma ya hak’ura kaga already Maryam tana nan so babu yadda zai yi. And another thing is wannan Usman d’in! Na san yanzu baya nan saboda iyayensa sun ce ko k’afar gidan da Maryam take kar ya taka amma fa su suka haife shi, shekarun baya Maryam d’in ta tab’a bani labarin yadda Mahaifiyarsa ta murzawa idanuwanta toka ta fifita farin cikin d’anta akan na kowa, so yanzu idan ya dawo ya nuna musu bai hak’ura ba na tabbata hak’uri kawai za a bayar kuma na san Maryam ba zata iya ce musu a’a ba.. Waennan dalilai Daddy su saka sanya kaga hankalina duk ya tashi! I don’t want to loose her again.” Ya k’arashe maganar kamar zai yi kuka. Gaba d’aya sai tausayinsa ya rufe Daddy dan haka yace “Ba komai, In sha Allah ba zaka rasata ba. Za muje d’in, in Allah ya kaimu ko gobe da yamma ne idan na tashi a aiki zan biyo company d’in naku sai mu wuce.” Sai a sannan Abba yayi murmushi yace “Thank you Daddy” Murmushi shima Daddy yayi daga nan suka shiga tattaunawa……. Tunda suka fara magana Mom ta lab’e a kitchen, babu abunda bata ji ba, gaba d’aya ta hada gumi kamar ita akace za a k’arowa kishiya. Sai da su Daddy suka bar dining d’in tukunna ta samu ta fito ta haye sama da niyyar d’aukar mayafinta ta nufi wajen Ummi amma sai aka yi rashin sa’a Daddy ya rik’e ta, ta so ya d’an fita ko ita ya barta taje ko parlour ne tayi waya amman k’iri k’iri ya kafa ya tsare yayi kane kane! Ba yadda ta iya haka ta hak’ura ta bari akan gobe suna fita office zata je ta samu Ummin…. Sai da Sudais yayi bacci tukunna suka yi sallama da Shuraim wanda zuwa yanzun ya ware kamar ba shi ne yake ta kuka d’azu ba! Haka nan ta fito ta barshi yana game d’in. Ta so ta wuce d’akinta kawai amman sai akai rashin sa’a suka had’u da Abba tana fitowa daga parlourn nasu. Ajiyar zuciya ta sauk’e dan daman tana son ganinshi, duk da bata san ta Ina zata fara ba but they need to talk. Kallonta yayi ya kalla inda yaga ta nufa, da sauri ta fara kame kame “Um daman zz n” Cikin katseta yace “It’s late, bara in je In kwanta. Good night.” Har ya wuce yaji tace “Abba” Juyowa yayi yana kallonta fuskarsa ba yabo ba fallasa. K’arasawa tayi inda yake a tsaye tana wasa da fingers d’inta. Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace “Talk mana, Um?” Yana mai bata full attention d’insa. Da kyar ta iya ce masa “Abba daman it’s about Ummi” B’ata rai yayi sosai kamar bai tab’a dariya ba! Kamar ta sani dama tak’i yarda ta kalleshi taci gaba da magana “Abba dan Allah ka daina yi mata abunda kake yi, ka dinga kulata please Abba kar..” Cikin katseta yace “Ita Ummin tace miki bana kula ta?” Da sauri ta d’ago ta hau girgiza kai kafin kanta tsaye tace “Shuraim ne, d’azu ko abinci bai k’arasa ci ba ya bar dining d’in. Ina hawowa na ganshi yana ta kuka, da kyar na lallab’ashi.. Abba if this continues zamu iya samun matsala da brothers d’ina a gaba musamman ma idan suka k’ara wayo suka fahimci duk ata dalilina ne kake yi mata hakan. Dan Allah Abba ka daina Ubangiji ma ana yi mishi laifi ya yafe Ummi ta gane kuskurenta..kalla yadda take yi min, Abba please ko dan neman zaman lafiyarmu ni da su Shuraim ka dai na yi mata haka, no matter yanda muke ni da su uwa uwa ce! Ko ni idan naga ana yiwa Mama haka akansu ba zan ji dad’i ba. Please Abba dan Allah” Ta fad’i hakan tana me matsowa ta kama hannunshi a nata ta rik’e. Ajiyar zuciya kawai ya sauk’e ...Tabbas abunda Huda ta fad’a gaskiya ne, shi kansa saboda su Shuraim d’inne ma yasa yake sassauta mata abubuwan da ya shirya zai yi mata tunda ta nace sai ta zauna da shi! Ummi tayi masa abubuwan da baya jin zai iya yafe mata, yana so ya yafe amman ya kasa, but kamar yadda Hudan ta fad’a kar aje a samu matsala ya raba kan y’any’ansa da kanshi dan haka dole zai dinga danne zuciyarsa…… A hankali yaji Hudan ta sake cewa “please Abba” Kamar zata yi kuka. Murmushi yayi ya zare hannunsa a nata ya shafa kumatunta kafin ya sauk’e ajiyar zuciya.. Baya jin akwai uban da yake yi wa y’arsa irin son da yake yiwa Huda, she’s just like her Mom everything hatta halayyersu iri d’aya ce! Kalla yadda take yiwa kishiyar Mamanta campaign dan kawai kar ayi hurting kowa. A hankali yana kallonta yace “Naji na daina I promise” Murmushi ta fara mai had’a da dariya kafin tace “Thank you Abba” Jingina kai yayi shima yana murmushin yace “Ai kin iya campaign dole in hak’ura, amma inaso nima kiyi min campaign a wajen Mamanki!” Da sauri ta sunkuyar da kanta dan ita kunya ya bata. Dariya yayi kafin yayi kalar tausayi yace “Please princess Tak’i d’aukar wayana. Ko bakya so ta dawo nan ku zauna tare? Kin fi so koma gidan Usman?”. Da sauri ta girgiza kai. A hankali yace “Then you have to do something Huda ina buk’atar taimakonki, kin san Mamanki da kafiya dan haka dole sai mun taru akan ta tukunna za muyi nasara saboda ba zan iya shawo kanta ni kad’ai ba. I need your help”. A hankali ta d’aga kai, ckin tsananin jin tausayin Mahaifin nata tace “In sha Allah Abba, I’ll try my best” Murmushi yayi yace “to shikenan, na gode.” Ajiyar zuciya ta sauk’e a ranta tana tunanin ‘tabbas idan fa akai sake Mama fa zata iya komawa gidan Baba anytime from now, dan tana da labarin yadda Shuwa tayi kawaici a farko ta bi bayan Baba akan Abba. Sannan itama Mama a yadda suke yanzu da Baaba Talatu tsaf zata iya yin kawaici ta koma masa, ko lokacin bikinta sai da taji Baaba Talatu suna magana da Anty Zainab wai tunda Baba ya tafi port harcourt bashi da lafiya! Bara a gama biki zata samu Kaka da Abba Madu da maganar! Kar fa ace tayi hak’uri ta koma zai shiryu tunda gashi har rashin lafiya yake yi which definately ta san akan Maman ne! Komai yana kanta daram! Na yadda Mama ta sha azaba a gidan nan, ba zata tsaya ta zuba ido a sake maida Mahaifiyarta cikin uk’uba ba besides ita dama ta dad’e tana da burin taga an maida auren iyayenta! Tana son ganinsu tare……’ “Good night, ko?” Muryar Abba ta dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi. D’agowa tayi tace “Good night Abba” So take ya wuce tayi d’akinta amman sai taga ya tsaya.. Dakewa kawai tayi ta juya ta nufi side d’inta. Murmushi ya yi mai had’e da y’ar dariya kafin yace “A fatherly advice…kema ki daina gudun Aslam!” Runtse idamuwanta tayi da mugun k’arfi! Wata kunya ta lullub’eta…sai da tayi dana sanin nufar d’akin nata da tayi. Tafi minti biyar a tsaye, k’arshe tayi kalmar shahada ta juyo! Kamar yadda tayi zato bata ga Abba a wajen ba. Kamar wadda akace mata zai fito haka ta zo ta wuce da sauri ta nufi hanyar k’asa ko globes d’in bata tsaya kashewa ba.... BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 60 Tana sauk’a k’asan ta ga shiru ba kowa. Da alama ma har masu aikin sun tafi side d’insu dan har an rufe main door sannan an kashe globes. Hasken fitilun barander waje da suka ratso ta windunan parlourn ne suka taimaka mata ta k’arasa bakin k’ofar d’akin nasu. A hankali ta d’anyi knocking, ita bama ta yi tunanin za aji ba amma sai taji yace “Come in” Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauk’e sannan ta sa kai ta shiga… A zaune kan sofa ta sameshi, da alamun wanka yayi dan ya chanja kaya zuwa wata jallabiya ruwan zuma mai dogon hannu da hula, bai sanya hular ba ya barta ta fad’a baya…ba k’aramin kyau yayi ba. Yana a zaune yana latsa computer ga tea a gefe kan d’an stoll d’in da ya d’aura computer. Gaba daya hankalinsa yana kan aikin da yake yi shiyasa ta yi mamakin ta yadda ya ji d’an mitsitsin knocking d’in da tayi, kuma kamar ma ba shi ya amsa ta ba dan tunda ta shigo be ko kalli inda take ba! Haushi abun ya bata yadda ko d’agowa bai yi ya kalletaba kamar ba d’an Adam ne ya shigo d’akin ba dan haka itama ta d’auke kai bayan ta d’an hararesa ta shige tayi wucewarta…. Inda ta ajjiye akwatinta ta nufa cikin closet, ga mamakinta sai taga wani akwatin wanda ta tabbatar nasa ne! B’ata rai tayi kawai ta hau zabgawa akwatin harara wanda ita kanta bata san dalili ba.. Sai da tayi me isarta tukunna ta d’auki inner wears, toothbrush, tooth paste, hijab da sleeping dress ta shiga toilet d’in… Wanka tayi ta d’auro alwallah, a nan cikin toilet d’in ta chanja kayanta..sai kuma ta fara tunanin a ina zata shanya bra da pant d’inta (waenda ta wanke yanzun) inda ba zai gani ba. Babu inda bata duba ba amman ta rasa mab’oya, k’arshe dai shanyawa kawai tayi a wajen shanya sannan ta d’aura hijabinta akan rigar barcin jikinta ta fito. Still yana zaune a yadda yake har yanzun.. Tsayawa tayi dan so take ya tashi ta kwanta! Tafi minti biyar a tsaye chaan! Ta tsinkayo muryarsa “Kina buk’atar wani abun ne?” Yayi mata tambayar ba tare da ya kalleta ba… ‘Itafa gaskiya ya fara k’ular da ita! Ta tsani ayi mata magana ba tare da an kalleta ba, wato ba ma ta kai ya kalletan ba kenan ko me?’ Huda ta aiyyana hakan a ranta. Gani tayi kawai ya d’ago kyawawan idanuwansa ya zuba mata su! Da sauri ta sunkuyar da kanta a ranta tace “Ko dai a fili na yi maganar??” Shi kuma Aslam shirun da tayi ne yasa ya d’ago ya kalleta, ganin ta sunkuyar da kanta ne still bata ce komai ba ya sanya shi kiran sunanta, a hankali taji yace “Huda” Da mugun k’arfi k’irjinta ya buga! Saboda yanayin da ya kira sunan nata da muryarsa mai mugun dad’in sauraro sannan very calm kamar baya son maganar ta fito. ‘Ita kam, tunda take anya akwai wanda ya tab’a kiran sunanta da dad’i kamar haka kuwa?’ Ta aiyyana hakan a ranta. Ajiyar zuciya Aslam ya sauk’e kafin ya rufe computer ya mik’e ya nufi inda take tsaye…. Tunda ya mik’e ta d’ago ta fara kallonsa, ganin ya nufota gadan gadan yasa ta rikice tashi d’aya, da sauri tace “sofa, sofa! Sofar nake buk’ata zan yi bacci” Kafin ta rufe bakinta ma already ya riga ya k’araso inda take! Da kyar ya iya danne dariyarsa, yana kallonta yana mamakin yadda duk ta duburce kamar ba ita ta gama zuba masa harara yanzunnan ba. Hannunsa yasa ya kamo nata! Da sauri ta d’ago ta na kallonsa, shima itan yake kallo ido cikin ido! K’asa tayi da kanta tana jin yadda zuciyarta take bugawa! Haka kurum taji hawaye sun tarun mata a ido….Tunda take da Ya Arshaad ko da wasa bai tab’a kama mata hannu ba 4 years! Amman shi wannan she just knew him amma bashi da aikin da ya wuce ya shafa mata kumatu ko kuma ya kama mata hannu.. Tabbas! Ta san akwai difference tunda shi wannan Mijinta ne amman kuma duba da yanda basu wani saba ba sannan kuma basa k’aunar juna ai bai kamata ace yana saurin tab’ata haka ba! Ko da yake ai ance daman a uk ya girma…ta tabbata inda Ya Arshaad ne aka yi musu irin wannan auren had’in da shi da ba zai tab’a yunk’urin rik’e mata hannu ba har sai ya bari sun d’an saba tukunna….. A take case d’in Jalila ya fad’o kanta, ta tuna yadda ta d’aura masa laifin da ba nasa ba bawan Allah har da AlQurani ya zo zai rantse mata gaskiya Ya Arshaad yana sonta ba kadan ba!…… Tana cikin wannan tunanin bata yi auni ba kawai taji kuka ya kufce mata!. Ajiyar zuciya taji Aslam yana ta faman sauk’ewa akai akai kamar shine yake kukan! Be hanata yin kukan ta ba, sai da ta gaji dan kanta tayi shiru…. K’afafuwanta har sun fara zafi saboda tsayuwa. Har tayi shiru bata ji ya daina sauk’e ajiyar zuciyar ba, chaan, taji yace “Ki tabbatar duk lokacin da tunanin Arshaad yazo miki, kika yi, kin yi istighfari!” Yana gama fad’in haka ya ja hannunta ya kaita har kan gadon sannan ya ajjiye ta yace “sleep” daga nan ya juya. Huda gaba d’aya tsoron sa ne ya rufeta! A ranta tace “Anya wannan ba alhaji bane ba kuwa?” Har ya d’anyi gaba sai kuma ya juyo, ganinta yayi still a zaune bata da niyyar kwanciyar.. Yunk’urowa yayi zai yi mata magana kawai yaga da mugun sauri ta juya ta d’aura k’afafuwanta akan gadon ta kwanta ta lumshe ido… Tabbas ya san me ta tuna dan haka kawai ya girgiza kai ya juya ya koma yaci gaba da aikin shi… Itama Hudan a tunaninta kwantar da ita zai yi k’arfi da yaji kamar yadda ya durk’usa zai kinkimeta ranar a asibiti shiyasa ta shafawa kanta ruwa ta kwanta tun kafin ya sake matsowa kusa da ita zuciyarta ta tarwatse! Dan har yanzu bata bar uban bugun da takeyi ba. Bata san lokacin da yayi bacci ba dan ita kam tana kwanciya bacci ya kwasheta. Ta riga sa tashi dan tun kafin assalatu ta farka ita… D’akin da duhu ba kamar yadda tayi bacci ta bari da haske ba. Jinta ta yi a lullub’e cikin lallausan bargon da ta gani a gefe kan gadon. A hankali ta karanto addua kafin ta mik’e ta zauna sakamokon kiran sallar farko data fara ji, dan ita da a tunaninta ma farkawar tsakar dare ta yi. Sai da baccin yad’an ragu a idonta sannan ta yaye bargon ta mik’e bayan ta d’auki wayarta. Flash ta kunna sannna ta nufi hanyar bathroom..idanuwanta ne suka sauk’a kan Aslam wanda yake kwance akan sofa! Dogo ne shi d’in sosai shiyasa sofar tayi masa kad’an, saboda kujerar ba wata mai girma bace ba dan da kyar In tafi 3 seater. Ya tankwashe k’afafuwansa akan sofar duk dan ta ishesa amman duk da haka a takure yake da alama kuma sanyi yake ji, gashi taga kamar blanket d’aya ne a d’akin kuma ya rufa mata Pillow kawai ya d’auka ya kwanta a kai ya turo k’ananan throw pillows d’in sofar k’asa……. Hasken fitilar ta ne ya farkar da shi….ya farka amman bai bud’e ido ba. Tsintar kanta tayi da komawa gadon, a nan ta ajjiye wayarta still bata kashe flash d’inba (dan ta ga haske) ta d’auko blanket d’in ta dawo wajen da yake kwance. A hankali gudun kar ya farka ta d’an sunkuyo ta lullub’a masa blanket d’in tun daga k’afafuwansa har zuwa wajen wuyansa… Ajiyar zuciya taji ya sauk’e dan haka ta yi saurin kallon fuskarsa a tunaninta ko ya farka ne amma sai taga baccinsa yake yi peacefully.. Gaba d’aya sai taji tausayinshi ya rufe ta…ta tabbata d’umin ne ya sanya shi jin dad’i har cikin baccinsa yana sauk’e ajiyar zuciya…ya san yana jin sanyi amman ya hak’ura ya lullub’a mata shi ya kwanta a haka… A hankali take nazarin tana kallon kyakkyawar fuskarsa. Durk’usawa tayi sosai a gabansa kamar mai zaman tahiyya. A hankali ta shiga kallon fuskar tasa tun daga kan sumar kanshi zuwa straight girarsa..duk da idanunsa a rufe suke amman hakan bai hana ta ganin kyawun da idanun suka k’arawa fuskar tasa ba, ga wasu kyawawan zara zaran lashes, dogon hancinsa ta kalla tana mamaki da girmama kyawun halittar Ubangiji………. Ta dad’e tana kwad’ayin son ta yiwa fuskarshi nutsatstsan kallo saboda ita har ga Allah tunda take a rayuwarta bata tab’a ganin kyakkyawan Namiji kamar Ya Aslam ba! Komai nasa mai kyau ne, ga muryarshi idan yana magana kamar kar ya daina………. Kallonsa kawai take yi sosai tana nazarin, dan har d’an matsawa ta yi kusa da shi sosai ba tare da ita kanta ta sani ba! So take ta gane me yafi kyau a fuskarsa! Hancinsa ne ko kuma idon ko cikakkaiyar straight brows d’insa, amma ta kasa, taso ace idanunsa biyu ta samu ta yiwa idanuwan nutsatstsen kallo kamar haka. So take ta d’auke kai ammman kwata kwata ta kasa… A hankali take bin skin d’insa da kallo, fuskarsa tass babu alamar k’urji ko zanzana ko wani tabo! K’ayataccen sajensa ne kawai ya bambanta fuskartasa da ta babies. Ahankali idanuwanta suka kai kan d’an mitsitsin pink lips d’insa wanda yake a zagaye da lallausan siririn saje! Ta jima tana kallo chan ya ji tace “Astaghfirullah!!” kafin tayi saurin runtse idanunta sai kuma ta mik’e da sauri ta juya ta fad’a toilet ko wayar tata bata d’auka ba! Tana shiga ta banko k’ofar!. Sai a lokacin Aslam ya bud’e idanunsa, yana wani sassanyan murmushi mai had’e da dariya… Ta jima a toilet d’in kafin ta fito. A zaune ta sameshi this time around da waya a hannunsa, a ranta tace “sai kaje garin daddanna na’ura ka lalata idon” Wucewa tayi ta d’au hijabinta ta zura ta fara k’ok’arin gabatar da nafila shi kuma ya mik’e ya nufi band’akin da gudu ta k’arasa ta shige toilet d’in kafin shi ya shiga ta rufo k’ofar! Chaan, ta bud’e ta fito ta wuce ba tare da ta kallesa ba.. Bayanta ya bi da kallo kafin ya girgiza kai kawai yana murmushi ya shige toilet d’in, kamar ance ya d’aga kai, yana kallon wajen dariya ta kufce masa, abunda bata sani ba shine jiya already ya rigada ya gani dan kafin ya kwanta sai da ya shigo yayi alwala.. Yana dariya yana murmushi shi kad’ai haka yayi wanka cikin farin ciki da annashuwa dan shi kam Hudan already made his day yau before it even begins. Da towel ya fito d’aure a k’ugunsa lokacin ita kuma juya baya tana sallah. Cikin nutsuwa ya hau shiryawa, tana cikin sallar hancinta ya fara jiyo mata wannan azababben k’amshin turaren nasa yana k’aruwa akan wanda already ya riga kama d’akin. Tana idarwa tayi addua ta shafa, ta gyara zamanta a nan gaban gadon kan kafet ta na jira a kira sallah. Takun sa ta ji a hankali yana k’arasowa inda take.. Lumshe idanuwanta kawai tayi tana shak’ar k’amshinsa tana kuma sauraron yadda bugun zuciyarta yake k’aruwa dede da takun nasa. A hankali taji yace “Gyara in yi nafila”. D’agowa tayi suka had’a ido.. Sanye yake cikin jallabiya bak’a mai shek’i amman ta k’asan jallabiyar tana iya hango dogon wando bak’i kamar na suite saboda jallabiyar bata ida rufe duk k’aurinsa ba. Da sauri ta mayar da kanta k’asa ta mik’e ta koma kan gado. Yana idar da nafila ana tadaa iqama a masallaci dan haka ya mik’e ya nufi k’ofa.. Har ya kama handle zai murd’a sai kuma ya juyo ya kalleta, yace “Zan fita yau da wuri. Ina da bak’i tun jiya cikin dare suka zo kuma yau da safe suke son komawa.. Get me something simple to eat, please. Kafin in dawo a masallaci.” Bai jira jin me zata ce ba ya murza handle d’in ya fice. Shiruu, tayi na y’an mintuna chan kuma ta mik’e ta tada sallah. A nutse ta gabatar da sallarta. Sai da ta idar ta yi azkar tukunna ta mik’e ta d’au wayarta ta fita a d’akin. Tana shiga kitchen d’in ta nemi globe ta kunna, ta fara k’arewa kitchen d’in kallo dan ita bama ta san ta ina za ta fara ba. Ganin babu lokaci yasa kawai ta soya omelet ta had’a salad ta d’auko bread da kifin gwangwani ta had’a masa sandwich da tea. Tray ta d’auko ta jera akai ta d’aura cup da tea flask d’in da su madara da sugar da teaspoon ta ajjiye dik a kai sannan ta d’au tray d’in ta fita. Tana fita ta gansu akan dining shi da Abba duk sun shirya, da wasu takardu suna dubawa. A hankali ta k’araso ta ajjiye tray d’in sannan ta d’an rissina tukun tace “Abba Ina kwana” Tunda ta fito Abban yake kallonta yana murmushi, ba k’aramin dad’i yaji ba “Lafiya Alhamdulillah” Yace da ita yana murmushi yana kallonta. A hankali ta d’an kalli Aslam tace “Ina kwana”. Sai da ya d’ago ya d’an kalleta tukunna yace “Lafiya” Sai kuma ya mayar da kanshi kan tray d’in yace “Thank you” Daga nan ya maida kallonshi ga takardun…. Abba ne yace “Princess yau abun son kai ne? Ina nawa cup d’in? Da alama ma breakfast d’in baku yi da ni ba” Gaba d’aya kunya sai ta rufeta cikin shagwab’e fuska tace “Abba ai ban san kaima zaka fita da wuri ba” Tana gama fad’in haka ta koma kitchen ta d’auko cup ta kawo da tea spoon. Har zata sake komawa sai yayi sauri yace “No wannan zai ishemu, wasa nake miki” Murmushi tayi daga nan ta juya ta wuce d’akin nasu. Tana cikin karatu taji fitarsu, sai da ta ida tukunna ta tashi dukda cewar d’akin bai yi wani datti ba amman sai da ta goge ta share ta wanke toilet, ita kad’ai tana ta mitar Aslam bashi da kunya wai k’ato da shi amman ya wani shanye mata boxes tazo ta gani ma shi bai damu ba kenan!………. Sai wajen 9:00am sannan ta fito, lokacin gidan ba kowa daga ita sai Ummi. A cikin parlourn ta hango ta amman da alama ma bata san ta fito ba! Ta rafka tagumi tana kallon gefen tv d’in da take ta faman aiki ita kad’ai… Sai da Hudan ta zo inda take ta ce “Ummi ina kwana” Tukunna tayi firgigit ta juyo, suna had’a ido ta fara murmushi, kafin tace “Lafiya, Alhamdulillah daughter. Ya kika kwana?” “Alhamdulillah” itama Hudan tace tana me zama a kujerar gefenta 1 seater. “Ki yi breakfast mana” Cewar Ummi. “Ok” kawai Huda tace sannan ta mik’e taje tayi, har ta gama ta dawo ta zauna Ummin tana wajen bata ko chanja yana yin zama ba. A hankali ta zauna kafin tace “Ummi tunanin me kike yi?” Kallonta Ummin tayi kafin ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya tace “Huda, gaba d’aya har yanzu na kasa yafe wa kaina. Sannan guilt yak’i barina In samu peace of mind! Ki taimaka ki yafe min sannan inaso ki rakani wajen Mamanki In nemi yafiyar ta na san na zalunceku” Da sauri Huda tace “Ummi dan Allah ki daina. Ni kam wallahi na yafe miki duniya da lahira Mama itama na san ta yafe miki. Ki kwantar da hankalinki ki daina yawan tunani, please.” Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin tace “Huda dukda cewa na san kina da kyakkyawar zuciya ba lalle ki aikata irin abunda na aikata ba, amman still ina me baki shawarar ki rok’i Ubangiji ya tsareki daga aikata aikin dana sani’ Guilt d’in bashi da dad’i kwata kwata na rasa sukuni, nan san tayaya zan yafewa kaina ba.” Ajiyar zuciya Hudan ta sauk’e kafin tace “Ummi, ki saka a ranki da ni da Mama mun yafe miki har abada! Sannan bamu rik’e ki a zuciyoyinmu ba ko kad’an! Mun yafe miki har gaban abada kuma ganin ki ne kamar komai bai tab’a faruwa ba! Ta hakan ne zaki iya yafewa kanki. Wallahi Ummi kinji dai na rantse miki har k’asan zuciyata na yafe miki kuma ban rik’e ki a zuciyata ba kwata kwata”. D’an guntun murmushi Ummi tayi tana jin k’aunar Hudan na sake shigarta, a hankali tace “Na gode Huda but some facts will never change, Ina jin kunyar Abba sosai Ina jin kunyar sa…” Hudan ta bud’e baki zata yi magana kenan! Suka fara jiyo kuka a waje… Da sauri suka kalli juna sai kuma suka mik’e suka yi wajen…. Kaya suka gani a zuzzube gefe guda kuma ga Jalila tanata kurma kuka tana tattare kayan nata. Tana ganin Hudan tayi saurin k’arasawa inda take ta rik’e mata hannu tana cewa “Huda dan Allah ku taya ni bata hak’uri, ni gani nake ma kamar ba ita bace ba ko kuma aljanuntane suka tashi! Lokaci d’aya kawai tace wai In fitar mata a gida! Dan Allah Huda kar ku bari ta kore ni…” Dede nan Mom ta fito ba tare da ta kalle su ba ta k’arasa ta finciko hannun Jalila ta wulla ta gefe sannan tace “oya! Tattare ki fice kafin In kwace kud’in motar da na baki” Da sauri ta mik’e tsaye ta share hawayenta ta k’araso inda Mom d’in take tsaye tace “Mom dan Allah kiyi hak’uri, wallahi ko wanke wanke da shara kika ce zan yi please Mom, dan Allah ki ara min kwana 7 Na yi miki alk’awarin nan da sati d’aya zan tafi wallahi.” Cikin b’acin rai Mom tace “Nan da kwana bakwai na san me zaki yi??? Na san kalar asirin da zaki k’ulla? Na san akircin da zaki shirya? Eh Jalila?” Ta yi mata tambayar tana kallonta. Bata jira jin amsarta ba taci gaba “Kinga, wallahi tallahi tun muna sheda juna ni da ke! Ki fice mini a gida” Da sauri Jalila ta rik’o hannunta tace “Momina dan Allah dan annabi...” Tass!! Mom ta d’auke ta da wani gigitaccen mari, cikin fushi tace “idan kika sake ce min Momin ki sai na datse miki harshe billahillazi. Ki kwashe tsummokaranki ki kama gabanki tun kafin raina ya ida b’aci!” Mom d’in ta k’arashe maganr cikin fushi da tsawa. Tun da ta kifa mata mari ta dafe wajen tana kallon k’asa, bata motsa ba! Sai da ta bari ta kai aya tukunna ta d’ago manyan idanuwanta da suka yi jaaa tana kallon ta! Cikin dakiya ta b’acin rai tace “Babu inda zan fita inje Adama.” Dariya Mom ta kwashe ta ita kafin tace “Perfect!” tana me gwadawa da hannunta sannan ta ci gaba “Wannan Jalilar dama nake so ta fito ba wachchar ba!. Yanzu zaki ga yadda ake hauka da rashin mutunci a cikin gidan nan!” Tana gama fad’in haka ta nufi gate…. Wani christian mai gyaran fulawa ta nemo da wani soja ta had’o su su biyu ta dawo. Tana zuwa ta kalli Jalila tace “Jalila ba da ni za kiyi wanann rashin kunyar taki ba da waennan za kiyi” Tayi mata nuni da k’artin bayanta, sannan cikin bada order ta juya ta kallesu tace “Mai aikinta ce tayi mata sata, so ta sallameta ta koreta amman tak’i tafiya dan haka su fitar mata da ita idan tayi turjiya su yi mata dukan mutuwa!” Jalila ba wani turancin kirki ta iya ba amma ta fahimci me Mom d’in tace. Ganin sojan ya tunkarota ba alamun annuri a fuskarsa yasa ta durk’usa da sauri ta fashe da kuka, tace “Wallahi tallahi kika saka aka fitar dani sai naje na tona muku asiri ke da d’anki a wajen Granpa.” Dakatar da sojan Mom tayi kafin a hankali ta k’arasa inda take durk’ushe. Durk’usawa itama tayi sannan ta saka yatsa ta d’ago fuskar Jalilan.. B’ata rai tayi ta yamushe fuska kalar tausayi kamar wadda zata fashe da kuka kafin a hankali yadda ta tabbatar babu mai ji tace “Ayyah Jalila! Wajen Granpa zaki je? Bismillah to ki je. Amman inaso ki san ko da ace kin je wajensa baki da wata shedar da zaki iya nunawa against ni ko Auwal! Mai yasa kike tunanin na barki kwana uku?” Bata jira jin me Jalilan zata ce ta bata amsar tambayar da tayi mata da kanta tace “To get rid of all the evidence! Sannan ta ci gaba da cewa “Sannan tun farkon zuwanki ranar cewa nayi Inna tayi min message tace min wata zata zo ta tayani y’an aikace aikace saboda an saka ranarta so tana buk’atar kud’in kayan d’aki, kinga yanzu In aka kira Inna tunda ba ita ta turo ki ba zata ce bata sanki ba ba kuma ta san da zancen ba! Nima kuma daman kinga Innar nace ta had’ani da ke… Questions d’in da zasu fad’owa y’an estate d’innan a karon farko shine “Wacece ke? Mai yasa kikayi outsmarting d’inmu? Tayaya kika iya hacking wayar Innaa? Sannan me kikeso me ya kawoki? Waye kuma ya turoki gidan nan?. Jalila bincike In yayi bincike believe you me har sharrin y’ar boko haram sai na d’aura miki wallahi! Family d’innan is a well known family so dole muna da mahassada da masu son cutar da mu so kinga kema a wannan sahun za a jefaki ta yiu ke kika zo da kan ki ko kuma wanine ya saka ki kizo gidan nan kiyi aiki ko bincike ko wani abun wanda Allah kad’ai ya san na menene! Granpa kuwa kinga dole ya tashi tsaye yayi bincike in ta kama a hukuntaki hukunci mai mugun tsanani Idan anyi miki mai sauk’i shine a kaiki cell ayi ta laftarki ace sai kin fad’i waye ya turoki... Shawara ta gareki shine Ki guji mutumin da kika ga Auwal yana mugun jin tsoronsa! Ki duba kiga fa surukan gidan nan ne mu amman da muka yi laifi ya aka yi da mu?. Sanann maganar ciki Already tun a ranar na biyasu y’an asibitin sun goge history d’inki! So kinga ko kince aje chan kina da evidence to nan d’in ma sai dai ki sake k’ulle kanki infact duk inda kikaje ma Jalila kud’i kawai zan bayar amaida lefin kanki. Sannan hatta chat da number Auwal duk na goge wani evidence a wayarki d’azu d’azun nan da nace miki ki ara min wayarki already kuma na san pin d’inki ba tare da kin farga ba shiyasa komai ya zo mini da sauk’i…baki da wayo Jalila sannan baki iya takun ki ba dan haka baki ta evidence ko wani abu da zaki nuna against me… So be a good girl! Ki kwashe tsummokaranki ki yi gaba tun kafin waennan k’artin su miki illar da na san ko kud’in magani ma ba lalle ki samu ba!” Tana gama fad’in haka ta cika mata hab’arta ta mik’e ta bar gurin tana karkad’e hannunta. Still sojan ne ya sake nufarta yace “Stand up and leave!” Banza tayi da shi tana wani kalar kuka mai cin rai. K’afarsa ya d’aga yayi wani mahaukacin ball da ita wanda sai da ta hantsila sau biyu! Da gudu Ummi da Huda suka k’arasa wurin suka dakatar da shi dan har ya sake nufar ta. Ummi tana duba ta taga gefen kanta ya fashe saboda yadda ta kifa a kan interlock d’in. Cikin tsananin b’acin rai ta d’ago ta cewa Mom “Haba Adama! Meye haka? Kin san fa ba ita kad’ai bace ba. Yanzu na tabbatar ko mik’ewa ma bazata iya yi ba balle ta fitar miki a gidan da kike ta faman ik’irari!” Tab’e baki Mom tayi sannan ta kalleshi cikin harshen turanci tace “Jata ka fitar idan ba zata iya tashi ba.” Ummi tana rik’e da hannunta amman mutumin nan bai damu ba haka ya kamo d’ayan hannunta ya fara janta kamar ba mutumba…. Sai da suka yi kusan rabin gidan tukunna Ummi ta hak’ura ta daina binsu rik’e da hannun Jalilan tana masa magana dan har ta fara haki. Haka nan ya jaata ya fitar da ita kamar kayan wanki ya jefar a bakin gate! Mai gyaran flowers kuma ya watso mata kayanta waje suka ja k’aramar k’ofar gate d’in suka rufe gidan...... BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 61 Mikiya Writers Association. Rai a b’ace Ummi ta koma inda Mom take ta rufeta da fad’a. Ita babu abunda ya fi d’aga mata hankali irin yadda aka jaa Jalila a k’asa despite the fact that she’s pregnant, ai ko ba komai de d’an Auwal ne k’unshe a cikinta!. Mom bata ce wa Ummi k’ala ba har tayi ta gama ta wuce ciki. Tana wucewa ta bi bayanta suka bar Hudan a nan tsaye tana mamakin rashin mutunci da rashin tausayin irin na Mom tabbas a wajenta Auwal ya kwaso duk wasu bad habits nasa daga gani kuma ita ta b’ata shi tun farko dan wannan uwar ba zata tab’a iya yin tarbiyyar da ta kamata a Yaro ba. Kamar ta bi bayan Jalila haka taji, to kuma kar Jalilan ta ganta tace zata zauna a wajenta taje sabon case ya b’ullo tsakaninta da Mom sannan Mama ta ja mata kunne akan ta fita harkar case d’in Jalila da cikin jikinta da duk wani abun daya shafeta.. Shiyasa kawai ta share hawayenta ta wuce ciki tausayi da k’aunar Arshaad suna sake shigar mata zuciya dan maganganun Jalila Mom da Ummi sun sake tabbatar da ciki dai na Auwal ne. Sai da Ummi ta kusan kaiwa d’akinta tukunna ta lura da Mom na bayanta. Juyowa tayi tana kallonta kafin tace “Adama baki da bakin yi min magana yanzu, ba zan saurareki ba dan haka kawai ki juya ki tafi. In wulak’anci abun yi ne ki je kiyi. Kuma kin san Allah ki guji had’uwar ki da Auwal saboda duk tsiya dai cikinsa ne a jikinta kika yi mata wannan rashin mutuncin….” Matsowa Mom tayi tana mai sauk’e ajiyar zuciya tukunna tace “FYI Cikin ya zube. Ta fad’o daga bene ya zube 3 days ago” Shiruu Ummi tayi tana kallonta ta jima tana kallon kwayar idanun ta itama Mon d’in haka, chaan ta lumshe idanuwanta ta bud’e ta furzar da iska tana mai girgiza kai duk a lokaci d’aya kafin tace “Adama ki ji tsoron Allah, ki bar ganin cikin shege ne kika zubar wallahi kina da hukuncin kisa a hannunki” Murmushi Mom tayi kafin tace “Gaskiya ya kamata magidanta suzo su d’auki course a wajen Abba! Duk wadda matarsa ta botsare kawai ya mik’ata cell zata dawo dai dai” Cikin b’acin rai Ummi ta juya kawai da niyyar shiga d’akinta, da sauri Mom ta sha gabanta tana cewa “O’o’o’o’! Tsaya mana, ai akwai abunda ya kawoni wajen ki dear new Ummi, may be na san maganar da zan gaya miki yanzun zata dawo dake hankalinki ki koma Ummin da na sani ba wannan ba..” ..Dalla dalla! Haka Mom ta zayyano mata duk wani abunda taji jiya Abba da Daddy suna tattaunawa sannan ta k’ara da cewa “Zab’i ya rage naki.. Kina gani dai abunda yake yi miki tun kafin ta dawo d’in, wallahi na tabbatar idan Maryam ta dawo gidan nan wallahi Ummi kin ji na rantse miki sai masu gadi da drebobin gidan nan sun fiki daraja a idanun Abba! Ballantana yanzu ga y’ar ta dan ni ban san ranar barinsu gidan nan ba tunda kikaga sun zaunar da su anan to ba yanzu za su sallamesu su ba! Tunda dai na san Aslam yanada gidaje balle ace wajen zama suka rasa… Kinaji kina gani haka zaku zama y’an kallo ke da y’ay’anki bar ganin kin haifi maza..ki dai duba ki gani yanzu haka yaya Abba yake gwada so tsakanin Hudan da su Shuraim?” A hankali Ummi ta runtsei danuwanta da suka kad’a suka yi jaaa! Kafin ta bud’e su ta zubasu a kan Mom. Tausayinta ne ya shigi Mom a take dan haka ta matso kusa da ita ta dafa ta kafin tace “Ki yi tunani ki yi shawara da zuciyarki. Inada plan d’in da na shirya wannan karon kwab d’aya kawai za muyi mata. Ummi ke y’ar uwata ce bani da kamarki duk duniyar nan daga Inna sai ke nake gani a matsayin nawa inji dad’i, ba zan tab’a bari a cutar da ke ba! Ki nutsu, zuwa anjima ko gobe ki zo ki sameni ni na san me zamu yi mata.” A hankali Ummi ta sauk’e ajiyar zuciya sannan tace “Nagode Adama. Bara in shiga in kwanta kaina yana min ciwo” “Okay sai anjima, bara in wuce.” Mom d’in tace daga nan ta juya direct ta sauk’a ta fice daga gidan ta nufi side d’insu ranta fess!. Sai yamma chan daff da Magrib Aslam ya dawo Abba kuwa da Daddy basu dawo ba sai bayan sallar isha. Sarai Ummi ta san inda suka je shiyasa tunda taga Aslam ya dawo shi kad’ai hankalinta yayi mugun tashi! Ta dinga ji kamar zuciyarta zata fashe. Da kyar! Da mugun kyar ta iya danne zuciyarta ta dinga karanto adduoi tana tasbihi tukunna ta samu ta d’an dawo hankalinta.... EARLIER… Da kyar Jalila ta iya taimakawa kanta ta mik’e a hankali ta zauna Wani sabon kuka ne ya kufce mata, tana yi ta shiga tattare kayayyakinta ta na d’urasu a cikin ghana most go d’in da Mom ta had’o da kayanta ta dinga watsowa…. Ganin bakkon duk biyun sun cika ya sanya ta ware d’ankwalinta ta d’aure ragowar kayan a ciki bayan ta nemi mayafi ta rufawa jikinta. Cikin ikon Allah tana cikin rufa mayafinta ta hango mai napep ya taho. Goge hawayenta tayi ta samu ta mik’e tsaye da kyar Ta taka da d’an sauri ta isa kusan titin ta tsaidashi dan kar ya sub’uce mata. Har bakin gate d’in gidan ya k’araso ya tayata saka kayanta a napep d’in. Ko ciniki bata tsaya yi ba tace masa “gandun albasa!”. A k’ofar gidan Baba ya direta ta shiga sauk’e kayanta tana jin yadda jikinta ke yi mata masifar ciwo, kallon unguwar da layin da gidan take yi…. A hankali ta lumshe idanuwanta wasu zafafan hawaye suka shiga tsilalo mata.. Ganin kamar mutane sunata kallonta ya sanya ta jaa kayanta one by one ta kai soro ta dawo ta sallami me napep d’in tayi cikin gida. A nan soron ta bar kayan dan bata jin tanad da energy d’in d’aukar kaya. Su Umma suna zaune ita da Anty Zainab Ya Ja’afar yana gefe kamar kullum su kuma suna tattauna ta yanda za su magance matsalolin da suka sakosu gaba a yanzu Jalila ta shigo. A mugun zabure suka mik’e tsaye duk su biyun suna kallonta dagaje dagaje! Kamar jira take yi a take ta fashe da kukan da take ta k’ok’arin dannewa. A rikice suka k’arasa suka rufar mata da tambayoyi…. Bata b’oye musu komai ba ta zayyano musu abunda ya faru tsakaninta da Mom. A zuciye Umma ta rarumi mayafinta ta rufa ta fara k’ok’arin fita tana cewa “Wallahi yau ko ni ko wannan Adamar! Sai dai mu tashi da juna ni da ita.” Da sauri Anty Zainab ta sha gabanta ta tsaya ta rik’eta tace “Sadiya nutsu!!” Da d’an k’arfi sannan ta d’ora da cewa “B’ata lokacinki kawai za kiyi, dan na tabbatar ko ganinta ba zaki samu damar yi ba. Kinaji dai ance miki masu gadi har da sojoji ake gadin gidan In ba so kike ta saka ayi miki shegen duka a kulleki ba to ki koma ki zauna mu nemi mafita dan fad’a da hayaniya da ita bata taso ba saboda ba iyawa za muyi ba! Ki bari mubi ta ruwan sanyi sai mu nemo mafita…” Da kyar ta jaa Umma ta zaunar da ita a bakin gado tanata huci. A hankali Jalila ta share hawayenta tace “Bara in yi wanka da ruwan zafi tukunna. Jikina duk ciwo yake yi.” Cike da tausayin ta Anty Zainab tace “Maza je ki yi, akwai ruwan da na d’aura za muyi d’an wake cike da tukunya, idan kin juye sai ki mayar da wani” Purse d’in wayarta kawai ta ajjiye ta fice ta nufi hanyar band’akin… Da ikon Allah kawai sai ta tsinci kanta da shiga tsananin tashin hankali sakamokon kyankyamin bakin rijiyar ta su da k’ofar band’akin da ya shigeta lokaci d’aya! Tabbas daman ta san ba zata iya rayuwa a gidan nan ba yanzu! Amman ita a nata tunanin abinci ne da wajen kwana zai fi damunta. Da kyar! Tsigar jikinta tana tashi ta samu ta d’auki bokitin da ta gani ta wuce cikin kithchen d’in ta juye ruwan. Hankalinta bai gama tashi ba sai da ta shiga cikin band’akin! Yayi mugun yin datti yayi dama dama gashi dama yana fama da nashi yanayin na tsufa da rashin had’uwa, yanzu kuma yazo ya had’a da rashin kula.. Har wani gansa kuka yake yi ga wani ruwa bak’i k’irin a kwance mai uban yawa da wari da alamar makwarar rufewa tayi! A ranta tace “tabbas Mama bata gidan nan.” A hankali ta shiga ta ajjiye bokitin ta hau zame kayan jikinta… Ta sak’ale a jikin k’aure. Kasa wanka da soson wanka nasu tayi dan shi kanshi abun kyankyami ne! Sabulun kawai ta iya d’auka shima saida ta wanke shi sau uku tukunna ta iya murzawa a jikinta… Sai da tazo kwara ruwa tukunna taji inama batayi wankan ba! Dan duk zubawa idan tayi sai na k’asan nan mai uban wari wanda ta tarar ya taru ya fallatso mata jiki… Kamar ta fashe da kuka haka take ji….a hankali ta hau zuba ruwan a hanakali.. Ta ci sa a kuwa ya daina fallatso mata d’in amman yadda ruwan kumfan jikinta yaje ya had’e da ruwan dattin nan ba k’aramin kyankyami ya k’ara mata ba! Ganin ba zata iya jurar gani ba ya sanya ta runtse idanuwanta ta fara laluben kayanta Cikin rashin sa’a ta bi takan d’an guntun sabulun da ya b’antare ya fad’i wanda ta gama wanka da shi yanzun! Aikuwa santsi ya d’ebeta… Sai da k’afafuwanta gaba d’aya suka bar k’asa tukunna ta dawo ta fad’o gaba d’ayanta a cikin ruwan da take jin kyankyamin kalla!. Wata razananniyar k’ara ta saka!!! Da gudu Umma da Anty Zainab waenda suka juyo ta suka fito suka nufi band’akin. A cikin ruwan suka tarar da ita ta runtse idanuwanta da k’arfi ta k’ame waje d’aya tanata kurma uban ihu! Su kansu sai da suka ji kyankyami da suka d’agata. Da kyar suka iya kamata suka mik’ar tanata faman ihu mai had’e da kuka sannan tak’i ta bud’e idanunta… Anty Zainab ce ta d’au botikin ta fice taje ta janyo ruwa a rijiya sannan ta koma ta d’auko silifas d’inta ta dawo band’akin suka shiga shek’a mata ruwa! Sai da suka juye mata ruwan botikin sannan suka rufa mata zani suka fito da ita tana wani irin kukan tashin hankali. Da kyar aka samu ta bud’e idanuwanta, nan da nan zazzab’i ya rufar mata dan haka ta k’udundune cikin bargon da shi kanshi kyamarshi take yi ta hau rawar sanyi............ NASARAWA gra. Tunda ya dawo bai ganta a d’akin ba. Tana d’akin su Shuraim dan ita ba gwanar yin chatting ko danna waya bace ba shiyasa in dai su Shuraim d’in sunanan take zuwa wajensu..ko suyi ta hira ko kuma su yi game. Yauma suna lunch ita da Ummi suka shigo, shiyasa suna gamawa suka d’unguma suka yi d’akinsu. Har ya fito zai je sallar isha bai ganta ba, sai Ummi kad’ai ya gani tana shirya dining dan haka kawai yace “Ummi ina Huda?” Kamar an fisgi maganar a bakinsa. Ita kanta Ummi sai a lokacin taga rashin kyautawar ta dan ya kamata ace ta tura ta wajensa, amman ya dawo wajen awa nawa har yanzu bai sanyata a idanunsa ba!. Gaba d’aya abubuwa ne suka yi mata yawa shiyasa hankalinta bai je nanba. Sai da ta d’anyi murmushi sannan tace “Sorry Aslam. Tana kitchen. Wani abun ne ya shamin kai shiyasa kaga ban turo maka ita ba.” Murmushi kawai yayi yana kallonta, kamar zai ce mata wani abun sai kuma kawai ya sa kai ya fita.... BAYAN KWANA BIYU. Kamar kullum yau ma bayan isha suka gabatar da dinner d’insu, cikin nutsuwa da farin ciki. Daga haka aka fara watsewa Dining d’in ya rage daga Abba sai Huda da Ummi. Huda tana mik’ewa shima ya fara k’ok’arin tashi, da sauri Ummi tace “Am, Abba dan Allah ina son zan je wajen Mama gobe Huda ta rakani” Bata yi tunanin zai kula ta ba, ga mamakinta sai taji yace “Yin me?” A hankali tace “Akwai wata y’ar magana da nake so mu yi. Ni da ita”. “Wa ta shafa?” Kame kame ta fara chan tace “Dan Allah Abba. Hak’uri nake so in bata akan abunda na yi mata”. Tab’e baki yayi sannan kawai yasa kai ya wuce ba tare da yace komai ba. Huda na shiga d’aki ta tarar da shi as usual yana aiki. Waje ta samu ta zauna a gefen gadon ta d’auko waya suka hau chatting ita da Sakina. “Baki iya gaisuwa ba” Taji muryarsa. Turo baki tayi kafin tace “Ina wuni” Dan Sakina labari take bata za a kawo kud’in aurenta so bataso ya katseta. Be ce mata komai ba, ya kyaleta. Sai da ya kai inda yake son zuwa sannan ya kashe computer yace mata “Zo” D’agowa tayi tana kallon shi irin ‘ni?’. Gira d’aya ya d’aga mata alamun ‘eh’. A hankali ta mik’e ta ajjiye wayar sannan ta k’arasa inda yake. Gefensa ta kalla kan kujerar sai kuma ta kalla k’asa kan kafet d’in gaban kujerar ta fara k’ok’arin zama.. Ji tayi kawai ya kamo hannunta ya jaata ya ajjiye ta a gefen sa.. B’ata rai tayi sosai..ita kam wallahi zata maka masa warning! Dan me yasa ba zai mata ta zauna a gefenshi ba instead zai wani janyota? Hala bakinsa yana ciwo ne.. Muryarshice ta katseta jin yana cewa “D’azu Ummi tace za ki rakata wajen Mama” Da sauri ta d’ago ta kalle shi sai kuma ta fara murmushi…bata san zancen ba amman kawai sai ta hau d’aga masa kai. Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya juyo ya bata dukkannin attention d’insa sannan yace “Ina jinki” Cikin rashin fahimta tace mishi “Me?” “Okay, baki san me ya kamata ki yi ba?” Yayi mata tambayar still yana kafeta da idanuwanshi. Shiruuu tayi ita harga Allah bata san me yake so ta yin ba! A hankali tace “Me zan yi ni?” Kallonta yayi na some seconds sannan yace “Tashi ki je, goben kawai kya bata sak’on gaisuwa ta kaiwa Maman besides saboda Ummi ne ma shiyasa zan barki daman kije dan ai bai kamata ace kinje gida tun yanzu ba.” Sarai zuwa yanzu ta gano so yake yi ta tambayesa, a ranta tace “Wannan wanne irin mutum ne mai son jan magana? Ba Ummi ta tambayar min ba!” Ganin da tayi tambayr da yake son tayi shine mafi sauk’inta ya sanya kawai ta kauda kai tace “Ya Aslam zan raka Ummi wajen Mama gobe” Kafin ta rufe bakinta taji yace “Order kike bani? Ko kuma gaya min kike yi? Ko kuma tambayata da neman izinina kike yi?” Ya mata tambayar a hankali cikin class da nutsuwarshi. B’ata rai tayi sosai kamar zata fashe da kuka. A ranta ta aiyyana ‘Ga zuwa wajen Mama ga kuma wasu shegun renin hankali da Aslam yake yi mata, wanne zata d’auka?’ A ranta tace ‘Ya na iya? Haka zan hak’ura in yi tolerating d’insa.” Muryarsa taji yana cewa “had’o min coffee. Shikenan tunda ba kya son zuwa” Yana fad’in haka shima ya juya yana kallon wani wajen kamar yadda tayi mishi. A hankali yaji tace “Ya Aslam nafa tambayeka. Me zan ce?” Juyowa yayi yana kallonta itan ma shi take kallo Sai dai suna had’a ido tayi saurin d’auke kai. A hankali ya lumshe idanuwansa kamar mai yin bacci….. Sun fi minti biyar kafin yaji tace “Dan Allah Ya Aslam zan raka Ummi wajen Mama gobe” Wayarsa kawai taga ya mik’o mata yace “ki hau ki yi searching ya ake tambayar Miji fita! Ko kuma ki d’auko wayarki and ask Sakina, na san maybe ita zata iya sanin me ya kamata ki ce”. Wani takaici ne yazo mata bata san lokacin da ta fara hawaye ba. Karb’ar wayar kuwa tayi ta hau google ta typer, wasu abubuwa daban aka sako mata… Shiruu, tayi tana share hawayen da suka k’i tsayamata, a ranta tace “Wanne irin mutum ne wannan wai shi? Kalla yadda kanshi tsaye yake wani cewa Mijinta!”. Sun d’an jima a haka chan! Kamar wadda ta tuna wani abun yaji tace “Dan Allah Ya Aslam Ina neman izinin ka zan raka Ummi wajen Mama” Wani sassanyan murmushi yayi kafin a hankali ya fara bud’e idanuwanshi yace “That’s more like it ....” Muryarshi ce ta sark’e sakamokon ganin fuskarta dagaje dagaje da hawaye. A hankali ya matso kusa da ita yace “Mai ya faru?” Kamar jira take yi kuwa ta saki kukan nata dan ji tayi ya taho mata da mugun k’arfi…. Kuka take yi tun k’arfin ta tak’i ma ta saurareshi, sai faman tambayarta yake yi amman tayi mishi banza! Bata yi auni ba taji ya janyota jikinsa bai yi wata wata ba ya rungume ta gabad’ayanta! Ba ita kad’ai ba hatta shi sai da ya tsorata da yadda zuciyarshi take bugawa! A lokaci guda kuma wata nutsuwa ta lullub’esa…jin shi kawai yake yi a saman gajimare. A b’angaren Huda itama kusan hakan ne dan d’iff haka kukan nata ya d’auke lokaci guda in banda ajiyar zuciya babu abunda take ta faman sauk’ewa…. Ita dai ba zata ce ga yanayin da take ciki ba saboda lokaci guda firgici mamaki nutsawa da fargaba suka rufar mata. Da kyar ya iya d’aga hannunsa ya d’aura a kan gadon bayanta ya fara shafawa a hankali, dede setin kunnenta yace “Shii, yi hak’uri. Wasa nake miki fa. Naga d’akin kullum boring ne shiyasa nake d’an jan magana da ke amma sorry tunda bakya so ba zan k’ara ba.” Zuwa yanzu ita kam ba ma jin sa take yi sosai ba! Mamakin kanta kawai take yi yadda ta kasa turesa daga jikinta Infact ita ji tayi ma bataso ya barta! Abu d’aya ne bataso shine bugun zuciyarta da yake yi da k’arfi! Amma apart from that bata k’aunar duk wani abunda zai rabata da duk wani part of yanayin da taje ciki a yanzu. A hankali take shak’ar k’amshin jikinsa da na turarensa tana jin wata nutsuwa da nishad’i suna sauk’ar mata… Bata san lokacin da ta fara lumshe ido tana bud’ewa ba. Wata kasala ce ta rufar mata dan haka ta d’an fara sakin jikinta tana lumshe ido tana sauraron bugun zuciyarshi da yake yi da k’arfi da sauri har ma yafi nata.... A hankali yake jin nauyin jikinta yana k’aruwa a nashi… Sun fi 10 minutes a haka, chaan! Ya ji ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya sai kuma ya fara jin sauk’ar numfashinta a kan k’irjinsa a hankali a hankali… Ajiyar zuciyar shima ya sauk’e kafin yace “Huda” a hankali. Shirun da yaji tayi ne yasa ya fahimci ta yi barci. A hankali kamar wanda rayuwarshi yayi depending akan barcin nata ya janyo trow pillow ya fara k’ok’arin kwanciya da ita a jikinshi. Mik’ewa yayi sosai akan kujerar kwanciyar rigingine. Kusan dukkan nin sangalalin k’afafuwansa sun kere kujerar gashi kuma akan d’an tudun edge d’in kujerar ya d’aura su, tabbas ya san k’afar zata yi mishi tsami amman he can’t even think of ruining wannan best moment d’in, ba. A hankali ya kwantar da ita akan hak’ark’arinsa.. Daga shi d’in har ita ba wani k’iba garesu ba shiyasa faffad’ar kujerar ta ishesu ciff ciff. Mayafin kanta yayi dabara ya ware ya lullab’a mata… Yau ma yana jin sanyin amman yana gudun kar ya motsa ta farka dan haka kawai sai ya hak’ura ya bar bargon… Bai yi cikakken minti biyar ba wani bacci mai mugun dad’in da ya manta rabon da yayi kwatan kwacin irinsa, ya kwashesa... Yau ma, kamar yadda ta farka jiya haka ta rigashi tashi. K’amshin turarensa ta shak’a! A hankali ta fara k’ok’arin motsawa amman sai ta jita ta kasa. Addua tayi ta bud’e idanunta sosai tana kallon d’akin…… A chaan ta hango gadon a gefe ba kowa a kai! A d’an zabure ta sake yunk’urin tashi had’e da kallon kusa da ita…. Tsayawa tayi kawai tana kallonshi yana baccinsa peacefull, sannan ya zura hannunsa d’aya ta k’asan ta gefen cikinta, ya kuma d’aura d’ayan a gefen cikinta ta sama ya had’a hannayen nasa guri guda. Gabantane taji ya yanke ya fad’i! Sai kuma ta tuna yadda suka yi jiya! ‘Kenan bacci tayi ta kwana a jikinshi?’ Ta aiyyana tambayar a cikin ranta. Wani takaici da haushin kanta ne suka rufeta a take. Hannunta ta saka ta fara k’ok’arin raba hannayen nasa da suka kanainayeta. Sai a lokacin ya bud’e idanunsa ya zuba mata. Itan ma shi take kallo dan haka idanuwansu suka sark’e ana juna…… Tun tana k’ok’arin kwance hannuwan nasa a jikinta da sauri har tazo ta fara yi a hankali daga baya ma sai ya zamana hannuwantane kawai akan nasa ko motsasu bata yi….. A hankali take jin fad’uwar gaba da kuma wani sanyi da nutsuwa a yayin da take kallon cikin idanunsa…ta fad’a a yau kuma ta sake tabbatar wa ‘babu wanda ta tab’a gani mai kyawun idanuwa kwatan kwacin na Ya Aslam’ A ranta tace “tubarkallah ma sha Allah” Cikin muryar bacci taji yace “Good morning wifey!” A hankali ta lumshe idanuwanta a ranta take tunanin ‘Anya wannan ba aljani bane ba kuwa? Kallafa yanzunnan ya tashi a barci amman idanuwansa basu yi ja ba sai ma wani kyalli da taga sunayi sannan bakinsa kamar ma sweet ya sha dan in dai taji da kyau tou k’amshin mint taji……….’ D’umin numfashinsa ne taji yana k’ara bak’untar fuskarta! A hankali take sauk’e ajiyar zuciya tana sake rik’e hannunwansa….. Chan! Kamar wadda ta tuna wani abun, tayi saurin bud’e idanuwanta tarr!! A d’an zabure….dai dai shi kuma ya samu nasarar d’aura lips d’insa a kan nata........ A mugun firgice ta sanya dukkannin k’arfinta ta turesa amman ko gezau! Bai yi ba. Wani rikitaccen kuka ta saka masa! Dan haka yayi saurin sakinta ya d’an jaa baya yana kallonta. Tana jin ya saketa, ya bata iska ta bi ta kansa da wani irin sauri ta sauk’a daga kan kujerar! Mayafinta da yake lullub’e a jikinta wanda ya fad’i yanzun kawai ta samu damar d’auka daga nan ta nufi k’ofa……… Tana jinsa yana kiran sunanta amman tayi banza da shi ta fice da mugun sauri.... BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 62 Mikiya Writers Association. Chan sama ta nufa. tana tafe tana adduar ‘Allah yasa side d’inta a bud’e yake’. Tana isa ta tura, cikin sa a ta tarar a bud’e dan haka ta shige ta saka key! Tana zuwa ta zauna a kan kujerar parlourn tana haki kamar wadda tayi gudun famfalak’i… Ta dad’e a nan zaune, jin an shiga masallaci ya sanya ta mik’e tana tunanin komawa d’akin dan ta samu ta d’au hijabi ta yi sallah. Kamar aslam d’in ya biyota haka ta d’an bud’e k’ofar kad’an ta lek’a! Ganin babu kowa a dogon corridorn ya sanya ta sauk’e ajiyar zuciya ta fito tana sand’a….. Sai da ta kai tsakiyar parlourn taji muryar Ummi a bayanta “Hudan” Runtse idanunta tayi a hankali kafin ta bud’e sannan ta juyo, ta shiga k’ok’arin k’ak’alo murmushi… Kallonta Ummin tayi from head to toe sannan ta nufota, tana zuwa “me ya kawoki nan?” Kame kame ta fara…chan! Da kyar tace “Daman zuwa nayi In karb’i Qur’ani a wajen Shuraim kuma d’akin nasu ma a kulle ne “ Had’e fuska Ummi tayi kafin tace “Yaushe kika koyi k’arya? Ina d’aki fa Ina karatu naji an hawo Ina lek’owa naga wucewarki d’akinki tun d’azu! Mai ya faru??” Tayi maganar tana tsareta da idanuwa. A hankali ta sunkuyar da kanta batai auni ba kawai taji hawaye sun zubo mata. Sarai daman Ummi ta so ta fahimci wani abun…murmushi kawai tayi a ranta tana mamakin Aslam! Kafin ta jawo Hudan zuwa jikinta cin son sake fahimtar lamarin tace “Yi shiru, shikenan. Bara in d’auko miki Qur’anin a d’akina sai ki wuce kije ko? Kar Aslam d’in yaga kin dad’e, yau ma na san da wurwuri za su fita. Kiyi sauri kije ki tayashi shiryawa, ko?” Kuka kawai taji Hudan ta kece dashi kamar wadda akace za a yankata! Cikin kukan tace “Ummi dan Allah karki bari in koma, Allah ba zan iya had’a ido da shi ba, baki san meh....” Kamar kuma wadda aka datse harshenta sai ta tsaya da maganar chak! Tana mai ci gaba da kukanta. Murmushi Ummin tayi ranta fess. Tace mata “to shikenan jeki ki yi alwala ki yi sallah ki daina kuka haka. Anjima sai muyi magana ko? Muje d’akina. Tayi maganar tana jan hannunta..... Bayan, Ummi ta gabatar da sallar Asubah, ta yi azkar, ta zauna ta hau nazari… Wani sanyi da dad’i take ji a ranta..ta san Huda Arshaad take so amman tabbas kamar yanda su Dad sukace ‘Ko bayan auren Mammy bazata barta ta zauna lafiya ba’ Aslam shine wanda take gani zai bata cikakkaiyar kula da soyayyar da take buk’ata, bayan haka sun yi mugun dacewa sannan ita daman ta d’an fahimci kamar Aslam d’in yanas son Huda! In dai kuwa hakanne Allah Ubangiji ya barsu tare ya k’ara musu k’aunar juna ya sanyasu farin cikin da basu yi tun tasowarsu ba…… A zaune taga Huda ta fara gyangyad’i dan haka tace mata “ta tashi ta kwanta a kan gado” Da sauri kuwa Hudan ta mik’e saboda daman addua take tayi kar Ummi tace mata taje ta had’awa Aslam breakfast. Tana kwanciya bata dad’e ba bacci ya kwasheta Ummi kuma ta mik’e ta fita dan had’a musu breakfast d’in.. Tana cikin bacci taji muryar Abba yana kiran sunanta, a hankali ta bud’e idanuwanta. Zaune ta ganshi a gefenta yana mata murmushi dan haka itama ta d’anyi murmushin sannnan ta mik’e ta zauna tace “Abba Ina kwana” “Lafiya, Alhamdulillah. Kin tashi lafiya?” “Alhamdulillah” Tace Mik’ewa taga yayi tsaye kafin yace “Zamu wuce UK ni da Daddy. Urgent tafiya ya taso, akwai abunda kike buk’ata?” Murmushi kawai tayi tace “Ba komai. Allah ya kiyaye ya tsare hanya ya dawo daku lafiya” A hankali ya d’an matso ya shafa kanta yace “Ameen princess, take care. Sai mun dawo ko” Yana gama fad’in haka ya juya ya nufi hanyar fita, har ya kama handle d’in sai kuma yaga rashin kyautawarshi dan haka ya juyo ya kalli Ummi dake gefe a tsaye yace “Na tafi. Zan saka miki kud’i ta account ko akwai abun buk’ata. In akwai wani abun you can call me” Wani kalan murmushin farin ciki ne ya baiyyana a kan fuskarta, tana murmushin tace “Nagode. Sai kun dawo” Murmushin daya mayar mata ne ya bata kwarin guiwar binsa a baya domin tayi mishi rakiya. Hudan ma taso ta rakasa amman ganin sun fita da Ummin ya sanya ta bari kawai, dan ta barsu su samu alone time su biyu. Kallon agogo tayi taga har 10 ya d’an gota. Ta san by now Aslam ya fita dan haka ta sauk’e ajiyar zuciya ta zuro k’afafunta k’asa tana tunani da mamakin guts! Kalar na Ya Aslam….mai yasa yayi mata hakan? Ya san ba sonta yake yi ba mai yasa zai dinga yi mata wasu abubuwan kamar waenda sukayi auren soyayya!? She definitely has to stay very far away from him har sai ta gano inda relationship d’insu ya dosa da ita kanta dan gaba d’aya Aslam ya juya mata lissafi kwana biyun nan kanta duk ya d’aure It’s like bama ta san me take so ba! Tabbas ta san tana son Ya Arshaad sannan tana son rabuwa da Ya Aslam Amman kuma when ever she’s with him she feels complete and safe! Da farko bata fahimci hakan ba sai a jiya da yayi hugging d’inta ta kasa kwace kanta daga k’arshema bacci ya kwasheta………..’ Ajiyar zuciya ta sauk’e, a chan k’asan ranta tace “A complicated marriage is enough! I can’t deal with complicated and confused relationship.” Tun d’azu idan ta tuna da moments d’insu na tsakanin jiya da yau da safe sai taji tana feeling somehow…bata k’aunar wannan feeling d’in at all bata son abunda zai na janta garesa shiyasa gara tun kafin ta gama zama confuse tabbas ya kamata ta d’au mataki…. A haka Ummi ta shigo ta sameta. “Tunanin me kike yi?” Taji muryar Ummin. A hankali ta d’ago ta kalleta sai kuma ta maida kanta k’asa tace “Ina kwana” Murmushi kawai Ummin tayi tace “Lafiya” sannan tace “Oya tashi ki shirya mu yi sauri mu tafi ko?” Ai tun kafin Ummi ta ida rufe bakinta Hudan ta sauk’a ta fita daga d’akin cike da d’oki. Murmushi kawai Ummin tayi itama ta hau nata shirin… Sai pass 11 sannan suka shirya suka fito Hudan bata wani yi kwalliya sosai ba, Abaya ce a jikinta nude colour mai kyau sosai, tayi rolling ta d’an saka lipstick, sai zobe da bracelet a hannunta. Ummi kuma lace ne mai kyau da tsada a jikinta peach da farin mayafi da jaka da takalmi. Suna baya suna d’an tab’a hira driver yana jansu, haka suka kama hanya… A wani babban mall Ummi ta cewa drivern “yad’an tsaya” Dai da suka fita tukunna ta bawa Hudan kud’i, tace “D’azu Aslam yace abata ta yi siyayyan tsaraba ta kai gida” “Angode” kawai ta iya cewa daga nan suka shiga sukayi y’ar siyayayr tsarabar suka fito Ummi tana lura da yadda mood d’in Hudan ya chanza tun daga lokacin data ambato sunan ‘Aslam’ So take ta fassara yanayin nata amman ta kasa a haka driver yayi parking a kofar gidan Madu.... Fita suka yi, Driver ya tayasu kai kayan har bakin k’ofar parlour daga nan suka sallameshi bayan sun yi da shi akan 3:00pm zai dawo ya d’auke su. A parlourn k’asa suka tarar da Mama tana zaune tana kallo. Sallamar su ce ta sanya ta maida hankalinta bakin k’ofar, kamar a mafarkin haka taji nan take wani farin ciki ya lullub’eta. Cikin farin ciki Huda ta ajjiye ledojin hannunta a farkon parlourn ta k’arasa da gudu ta fad’a jikinta ta yi hugging d’inta. Tabbas Mama tayi farin cikin ganin d’iyar tata amman sai ta maze ta zarota daga jikinta ta fara yi mata fad’an ‘mai yasa ta fito? Dududu yaushe ma aka kaita?” Ummi ce ta k’araso inda suke tace “Ayi hak’uri Mama ni nace sai ta rakoni” Murmushi Maman tayi dan ita ta ma manta Hudan tare take da bak’uwa hakan yasa ta d’anji kunyar barinta da sukayi a tsaye ita kad’ai. Cikin fara a tace “Bismillah ki zauna. Yi hak’uri wannan ta gudo ta barki bama ta tsaya kun k’araso tare ba” Murmushi Ummi tayi sanann ta k’arasa ta ajjiye ledar hannunta a gefe tukun ta zauna a kan d’aya daga cikin setin kujerun da Maman tayi mata nuni da. Tana zama Mama tayi kitchen.. Sai da ta cika mata gabanta da kayan kwalama da su lemuka tukunna ta nemi waje ta zauna tana raba d’ayan biyu ‘Ko dai babar Auwal ko kuma matar Abba! Amman anya kuwa matar Abba zata yarda tazo kuma tana mata fara’a haka sosai?’ “Ina su Hajiya? Na ji gidan shiru” Muryar Huda ta katse mata tunani. Sai da ta d’anyi jimm! Tukunna tace “Tana gidan Baaba Talatu, Baba ne aka dawo da shi wai bashi da lafiya sosai” “Allah ya bashi lafiya” Shine abunda Huda tace kawai dan jiya ma sai da suka yi maganar ita da Sakina A yanayin take taken Baaba Talatu so take ta fake da rashin lafiyar Baba a maida Mama gidanshi..... “Kafin ku tafi ya kamata ki shiga ki dubo shi” Hudan taji muryar Mama. “Tam” Kawai tace kafin tace mata “Sakina fa? Jiya tace min tana nan” Cikin sigar zolaya Maman tace “Amarya dai zaki ce! Ta tafi. Gobe suka ce za suje gidan dangin Babanta da shi da Yayansa Babansu yayi tafiya. Nan da sati biyu kuma in sha Allah za su koma har da su kawunnansa da Mahaifin nasa a saka rana” Murmushi suka yi daga Huda har Ummi, a tare suka ce “Allah ya tabbatar mana da alkhairi” Kafin Ummi ta d’an nisa tace “Dota d’an bamu guri, ko?” A hankali Hudan ta mik’e ta wuce sama ta bar su su kad’ai a zaune. Gyaran murya Ummi tayi suka d’an sake gaisawa kafin tace “Maryam ni ban ma san ta Ina zan fara ba! Abu biyu ne yake tafe dani wanda duk biyun alfarma ce nazo nema daga gareki amman inaga gara in fara dana farkon dan shi yafi hanani sukuni a rayuwata.” Tabbas tun lokacin da taji ta kira ‘Huda’ da ‘dota’ ta fahimci Zainab ce! A hankali Mama ta gyara zama ta fuskanceta da kyau kafin tace “Ina saurarenki, Allah yasa zan iya taimokonki” “Za ki iya In sha Allah” Shine abunda Ummi tace kafin ta cigaba da cewa “Sunana Zainab, na san kin sanni a bad’ini a zahiri kuma yau gani a gabanki. Da farko ina mai neman alfarmarki Maryam dan dan Annabi ki samu ki yi creating space a zuciyarki ki yafe min laifin da nayi miki shekarun baya sannan ki yafe min laifin da nayi ta maimaitawa Ina nanatawa duk akan Abba kar ya dawo gareki! Ba dan ni ba, tare da taimokon su Adama to da tuni tun a karon farko lokacin da kika tura mishi da sak’o na san da kun koma kun ci gaba da zaman ku cikin kwanciyar hankali da k’aunar juna, amma biyewa zuciya da son kai suka kaini ga aikata makircin da wallahi ni kaina idan na tuna kunyar kaina nake ji!…, Na san I’m asking for a lot, na san da wuya ki yafe min, na san ko da ace kin yafe min to ba lalle ki daina ganina da abun ba….” A hankali Ummi ta share hawayen da suka zubo mata sannan ta d’an zamo daga kan kujerar ta durk’usa…. Da sauri Mama itama ta sauk’a akan kujerar tace “Dan Allah kar ki yi haka! Already ni kam na dad’e da yafe miki besides ba kece kika saka Abba ya sakeni a wannan ranar ba kawai dai kun had’amu fad’a ne wanda yanzu ya riga da ya wuce, komai ya wuce! Dan haka na yafe miki Ubangiji ma ake masa lefi anemi gafara kuma ya yafe mana ballantana ni? Ki manta da komai ki saki ranki In dai dan ta ni ne inaso kisa a ranki kamar komai bai faru ba! Dan Allah. Sannan ki daina d’aura laifin da ba naki ba a kan ki ke kad’ai dan Allah.” Ummi bata san lokacin da ta fashe da kuka ba! A hankali Mama ta rungumeta Itama tana nata hawayen da bata san dalilin sa ba. A hankali ta share hawayen nata sannan ta cika Ummi ta gyara zaman ta ta hau lallashinta….. Da kyar Mama ta iya lallashinta aka samu ta yi shiru. A hankali Ummin ta kamo hannuwanta duka biyu a cikin nata tace “Na gode kwarai! Sai alfarma ta biyu…. Ina rok’on ki ki daure! Na ji kuma na san yadda Abba yake ta faman biko amman kin k’i amincewa! Na san kina da gaskiya ta wani b’angaren amman kuma duk inda akaje aka dawo Abba ya fiki gaskiya. Ki yi hak’uri ki daure ki koma gidanki na farko na tabbatar har yanzu kina son Abba kuma a cikin shekaru goma sha taran nan da nayi da shi a matsayin Miji na fahimci zuciyarsa ba tawa bace ba taki ce! Ba zan tab’a mallakar abunda ba nawa ba kuma indai bakya tare da shi to ba zai samu nutsuwar da ni kaina zan samu koda ace 1/10 d’in kulawar da ya kamata ya bani ba. Ki daure, kar ki cuci kanki ki cuce ku. Ki dawo kusa da y’arki kusa da masoyinki ku k’arashe rayuwar ku just like it was soppose to be… Kar ki damu da kowa ke dai kawai ki yi abunda zai sanyaki farin ciki, dan Allah.” Da sauri Mama tace “A’a zainab gaskiya wann.....” Cikin katseta Ummi tace “Na san alfarma nace Ina nema a wajen ki amman In kikai duba zakiga kamar a cakud’e take da shawara! Shawarar da duk wani masoyinki na gaskiya zai baki. Sanann idan kikai haka za ki sanya mutane da yawa farin ciki.. Kinga na farko ‘Abba’ Ta biyu ‘Huda’ Sannan ta uku ‘Ni’.” Da mamaki Mama take kallonta. Murmushi Ummi tayi sannan tace “tabbas! Dan ni gani nake yi ma ko Abba ba zai kaini farin ciki ba saboda kinga na farko Zan ganshi cikin farin ciki Sannan zai daina blaming d’ina akan na rabaku sannan idan ba gani nayi na gyara abunda na b’ata ba to wallahi har abada har In koma ga mahaliccina ba zan iya samun nutsuwa ba! Ganin ku tare a yanzu living together happily zan iya ce miki shine abunda nake da kwad’ayin gani a yanzu fiye da komai a rayuwata” Zuwa yanzu Mama kam tama rasa bakin magana… A hankali Ummin tace “Ki yi tunani mai kyau. Dan Allah Maryam” A hankali Mama ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya tana kallonta kawai.. Sai a lokacin Shuwa wadda shigo tun d’azu tayi musu sallama. D’agowa sukai suna kallonta, itanma su take kallo har ta k’araso tsakiyar parlourn inda suke, jikinta duk a sanyaye. Cikin mutuntawa Ummi ta shiga gaisheta, Itama ta amsa mata cikin karramawa da kulawa kafin ta k’araso ta nemi waje ta zauna tana tambayarta “ya mutan gidan?” Sun d’an jima kafin Huda ta sauk’o. Shuwa na setin staircase dan haka da ita ta fara tozali! Salatin da ta rafka sai da ya firgita su Mama dan haka suka juya suna kallon inda sukaga tana kallo Ita kanta Huda sai da ta tsorata. Tun kafin ta k’araso ta rufeta da fad’a! “Dan mai yasa za ta fito? Aslam d’in ne ya bata izini saboda shima sakare ne irinta! Ko dai satar hanya tayi ta fito?” Da kyar ta iya tsayawa ta amsa gaisuwarta daga nan tace “su kama hanya maza maza su koma gida! Wannan shirmen ba da itaba.. Ita tunda uwarta ta kawota duniya bata tab’a ganin amaryar da ta fito bata yi sati biyu ba!” Da kyar ta yarda suka d’an jira driver bayan sun kirashi amman da cewa tayi ‘bara ta yiwa Abban Ya Jamilu magana ya maidasu Ai bai dad’e ta kawo Baba ba akwai mota shima a hannunshi.’ Ba a wani dad’e ba Drivern nasu ya k’araso: Ba yadda Hudan ta iya ta fara k’ok’arin tafiya ba dan taso ba haka nan ta yi wa Shuwa sallama ta basu tsarabar da Aslam ya bata kud’i suka tsaya suka siya daga nan ta cewa Mama za suyi waya anjima dan da akwai maganar da itama ta shirya za suyi da Maman. Har mota Maman ta rakasu, haka nan ta tafi tanata kumbure kumbure.. Sai da Shuwa taga fitarsu tukunna hankalinta ya kwanta, yadda tabi ta d’aga hankalinta zaka ce Huda wani gagarimin laifi tayi… Mama tana dawowa daga rakasu ta zo ta nemi waje ta zauna a gefenta kan 3 seater tace “Kiyi hak’uri Hajiya nima sai da nayi mata fad’a wallahi. Wai Ummi ta rako ne shiya sanya. Kin san su family d’in nasu boko ta ratsa su da yawa basu wani damu da al’ada ba amman duk da haka na san inda ace a waje d’aya suke da Mommy da ba zata barta ta fito ba.” Ta k’arashe maganar tana d’agowa ta kalli Hajiya Shuwa wadda tunda ta fara magana ta tsareta da idanu. A hankali taji ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace “Maryam” “Naam” Maman ta amsa a hankali. Wata ajiyar zuciyar Hajiyan ta sake sauk’ewa sannnan tace “Naji duk abunda Ummin tace miki yanzu shigowa ta” Wani yawu Mama ta had’iye kafin tace “Hajiya na gama deciding tun tuni Ba zan koma wa Abba ba! Ba kuma zan komawa Baba ba! A barni kawai, itama Ummin dan tak’i yarda ta saurareni ne da abunda na shirya gaya mata kenan tun da hakan ne ra’ayi na, bana jin kuma zai chanja ko da nan da shekaru nawa ne” A hankali Shuwa tace “Mai yasa?” Da tsananin mamaki Mama ta d’ago tana kallonta kafin ta sake yin k’asa da kanta tace “Hajiya dan girman Allah kar ki biyewa Baaba Talatu wannan karon…har yanzu wasu lokutan ina jin rad’ad’i a k’afata idan abun ya motsa, bayan k’afata har a cikin zuciyata ina jin tsananin rad’ad’in azabar da na sha a hannun Ya Usman. Dan Allah Hajiya kar kice In koma gidansa” Ta k’arashe maganar tana me d’ago kanta ta kalli Shuwan da idanuwanta da suka fara zubar da hawaye. Ahankali Shuwa tayi wani sassanyan murmushi sannan ta kamo hannunta duka biyu a cikin nata ta bata dukkannin attention d’inta tukunna tace “Gidan Abba fa?” A zabure Mama take kallonta saboda bata tab’a yin tunanin jin wannan maganar daga gareta ba. Kasa magana tayi bakinta ya hau rawa da alamun akwai abunda take son cewa amman ta kasa. A hankali Shuwa tace “Maryam, ko ni na kawo taurin zuciya duniya ba zan tab’a bari ki koma gidan Usman ba indai inada rai a doron k’asa” Wani kuka ne ya tahowa Mama lokaci d’aya ta sakeshi! Tana sauraron Shuwa tana cigaba da magana “A baya na yi kuskure, idanuwana sun rufe da takaici da kuma bak’in cikin ganin kina y’ata amman kin kasa yi mini biyayya! Wanda hakan ya kaini ga jefa rayuwarki cikin taskun da na kasa taimokonki kuma na kasa ganin hakan har sai ranar da aka kawo min ke a karye. Ban san da wannne baki zan baki hak’uri ba Maryam ban san ta yaya sannan ta ina zan fara baki hak’uri ba dan laifukan da nayi miki sunada yawa… Ina jin takaicin yadda na kasa fahimta da ganin laifi da badaidan da na ke ta faman aikatawa da wuri ba. Ki yi hak’uri ki yafewa mahaifiyarki Maryam dan Allah” Da sauri Mama ta d’ago tasa hannu ta toshewa Shuwa baki tana kuka bilhakk’i da gaskiya. Cikin kukan ta hau girgiza mata kai alamun ta daina rok’on ta. Da kyar ta iya cewa “Hajiya dan Allah ki daina rok’ona, ke fa Mahaifiyata ce, tayaya za kiyi ta rok’ona haka. Laifin in dai kece kikayi min to na riga na saka a raina na yafe miki tun kafin ma ki aikata laifin.” Kuka itama Shuwa ta fashe da shi, a hankali tasa hannu ta janyo Mama ta rungume ta suna kuka duk su biyun gwanin burgewa gwanin ban tausayi. Muryar Abba Madu wanda basu san da shigowarsa ba suka ji yace “Ni fa? Za a iya yafe min nima?” D’agowa suka yi duk su biyun suna kallonsa. Murmushi yayi ya k’araso inda suke zaune ya zauna akan kujerar shima A gefen Mama (ya zamana sun sakata a tsakiya shi da Shuwa) A hankali yasa hannu ya dafa kafad’arta yace “Za a iya yafewa Abba Madu shima?” Da sauri ta fad’a jikinsa tana kuka at the same time tana d’aga masa kai alamun ‘eh’. A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya, wani hawaye mai cike da tarin k’aunar y’arsa da dana sani ya samu nasarar zubo masa ta ido d’aya! Hannu yasa ya janyo Shuwa wadda itama take nata kukan ya had’asu guri d’aya da Maryam d’in ya rungume……. Mama, ta manta rabon da taji kwatankwacin wannan farin cikin a rayuwarta a ranta ta shiga aiyyana.. ‘ashe zata ga wannan rana? Ashe zata sake samun wannan opportunity d’in a rayuwarta? Allahu akbar! Ubangiji mai zamani duniya juyi juyi mahak’urci mawadaci Tabbas komai in yayi zafi maganinsa Allah sannan duk nisa jifa k’asa zai dawo!……’ Kuka take yi tana godewa Ubangiji tana sake godiya….. A hankali Madu ya shiga lallashinsu yana cewa “Su yi shiru” Da kyar ya samu Shuwa tayi shiru saannan ta tayashi lallashin Mama tukunna itama aka samu tayi shirun. A hankali tasa hannayenta ta kamo nasu sanann tace “Abba Hajiya Dan Allah nima kuyi hak’uri akan yadda na gudu na bi Abba, ku yafe min dan...” Da sauri Abba Madu ya d’aura yatsanshi akan bakinta yace “Ba komai Maryam, komai ya wuce, Allah yayi miki albarka.” Juyawa tayi ta kalli Shuwa, a hankali tana murmushi Itama ta d’aga mata kai tace “ya wuce! Allah yayi miki albarka. Sannan ina neman alfarma nima a wajen ki, kamar yadda Ummi ta fad’a nima In ba gani nayi kin koma gidan Abba ba to ba zan samu peace of mind ba, Ina so in gyara abunda muka taru ni da dangisa da su Usman muka lalata. In dai kin yafe min da gaske to inaso ki yi hak’uri ki koma gidan Abba, hakan shine abunda zai sanyani farin ciki shine abunda nake so da burin gani a rayuwata” Cikin sheshshek’ar sabon kukan da ya tahowa Maman tace “Amman Hajiya..” Da sauri Hajiya Shuwa tace “Ba zan miki dole ba, ba zan tilastaki ba amman inaso ki sani Hakan shine zai sanyani farin ciki hakan shine abunda nake so hakanne zai tabbatar min na gyara abunda na b’ata ya kuma taimakamin wajen sanyani in yafewa kaina. Ki daure, ni Shuwa Ina rok’on ki ki koma gidan Abba, na san har yanzu kina k’aunar sa.” Sunkuyar da kai Mama tayi tana wani gunjin kuka mai d’aci... A hankali Shuwa ta share hawayenta sannan ta sa hannu ta shafa kumatun Mama kafin ta mik’e ta bar wajen da sauri. Muryar Madu Maman taji yana cewa “Kiyi hak’uri ki bi shawarar da duk wani masoyinki yake baki Abba har yanzu yana k’aunarki kema kuma na san kina sonshi. Ki duba kiga ko kwana biyun nan da suka wuce sai da suka zo nan shi da d’an uwansa akan maganarki Maryama a zamanin nan ba lalle a samu mutumin da zai yiwa wata kwatan kwacin k’aunar da Abba yake yi miki ba. Kamar yadda Mahaifiyarki tace to haka nima ba zan yi miki dole ba amman zan baki shawarar ki bari ki yarda ki amince a maida aurenku da Abba, hakan zai bashi nutsuwa da farin ciki na har abada dan a yadda na ganshi ranar da suka zo na san ba abunda yake so da buri sama da a maida aurenku, nima kuma hakan nake so Mahaifiyarki itama hakan takeso Y’arki ma hakan take so above all na san kema hakan kikeso achan k’asan ranki kawai dai obstacles ne suke son tsaidake ga isa inda zuciyarki take so.” A hankali ya shafa kanta yace “Ki yi tunani mai kyau amman ina so decision d’inki ya kasance abunda kike so ne kuma ki tabbatar zai sanyaki farin ciki har k’arshen rayuwarki.” Yana gama fad’in haka ya mik’e ya fice dan lokacin sallah ya gabato…. A hankali Mama take sauk’e ajiyar zuciya, ta dad’e a zaune sai da ta fara jin kiran sallah tukunna ta mik’e ta wuce d’akinta zuciyarta fal sak’e sak’e….. Ta san cewa yanzu Abba baya tare da Granpa amman fa duk inda aka je aka dawo uba uba ne, ba a chanjawa tuwo suna kamar yadda take da tabbacin k’iyayyarta a zuciyar Granpa ba zata tab’a chanjuwa ba..... Haka nan, har dare Mama jikinta duk yayi sanyi kamar wata mara lafiya Shuwa da Abba Madu basu sake yi mata maganarba dan basa so suyi ta pressurizing d’inta.. haka nan suka yi dinner atare cike da da so da k’aunar juna suna hira gwanin ban sha’awa Wani kalar farin ciki kawai Maama take ji wanda ta dad’e bata yi ba, yana ratsa zuciyarta. A hankali from time to time take d’an fakar idonsu ta juya ta d’auke kwallar farin cikin da ta k’i daina taruwa a idanunta. Da daddare tana shirin kwanciya Huda ta kirata, kamar had’in baki itama maganar Abba ce take so suyi, bayan sun gaisa ta gama y’an kame kamen ta kafin ta rok’eta Allah da Annabi ta dawo gidan Mahaifinta. Cikin son kawar da zancen Mama ta sako wata hirar ganin da Hudan tayi kamar bata son zancen ne ya sanya bata sake mata maganar ba har sai da suka zo sallama, nan d’in ma d’an shiru Mama kawai tayi, chan kuka tace mata “ta gaida Ummi da Aslam tayi mishi godiya” sannan ta katse kiran. A hankali Hudan ta gyara kwanciyar ta akan gadonta ta kwanta rigingine tana mai kallon sama ........... AFTER TWO WEEKS. A zaune Ummi ta shigo ta tarar da Hudan ta rafka uban tagumi. Murmushi tayi ta k’araso inda take ta zauna kafin ta dafa ta. A hankali Huda ta d’ago tana kallonta wanda hakan ya sanya Ummin ta fahimci kuka tayi. Karkatar da kai Ummin tayi kafin tace “Huda ko nice Aslam fa ba kawo kud’i ba ko bikin Sakina za ayi ba zan barki ki je ba, wallahi. Ke kika jawowa kanki dan haka kar ki zauna kina wani kuka, ai baki ma yi kuka ba ki jira sai Abban ku ya dawo gobe, na tabbatar in dai yaji labari wallahi da ni da ke kashinmu ya bushe! Bar ganin yana lallab’a ki in dai yaji wannan zance to fa ba zaku kwasheta da kyau ke da shi ba. Kuma yana zuwa zan gaya masa tunda ni kin raina ni Da sauri Huda tace “wallahi Ummi ba rainaki nayi ba.” Cikin katseta Ummi tace “Raini ne mana Huda! K’iri k’iri fa kika hanani number Mama saboda kin san in na kirata na fad’a mata zata yi miki fada kuma dole ki yi abunda bakya so d’in so bama kya so taji ballantana har a kai ga tayi miki magana amma ni Ina kallon ki kina kallona a cikin gidannan yau sati biyu kina wasar y’ar b’uya da Mijinki kuma ban isa in hana ki ki hanu ba tunda ban Isa da ke ba” Cikin kuka Huda tace “Allah Ummi kin isa” Mik’ewa tsaye Ummin tayi kafin tace “Idan har na isa to ki tattara kayan ki da kika kwaso da hannunki ki maida ki gyara d’akin ki wanke toilet kafin ya dawo. Wallahi na manta yaushe zan ce na tab’a ganin Aslam yana gyaran d’aki amman jiya dakanshi har mopping naga yanayi kuma ba yadda ban yi da shi akan ya bari a gyara ba amma ya k’i yarda saboda ya san nan d’in turakarku ce bai kamata a shiga ba. Dan maiyasa shi yana mutuntaki amma ke ba zaki kwatanta ba?. Ki tashi kije ki koma sannan idan ya dawo ki bashi hak’uri tare da alk’awarin ba zaki sake ba… In dai har na isa da ke kenan, kamar yadda kika fad’a.” Tana gama fad’in haka ta juya ta fice daga d’akin. Sai da Hudan taci kukan ta ta godewa Allah tukunna ta tashi ta sauk’a k’asan… Ta yarda zata zauna a d’akin amman tabbas zata cire tsoro kunya da kawaici su yi agreement ita da Aslam! Auren su ba na soyayya bane ba Infact k’ok’arin kawo karshenshi ma ya kamata suyi a yanzu so ba zai yiu ya hautsina mata kwakwalwa da zuciya ba bayan ba son juna suke yi ba so gara su san inda suka dosa kowa ya tsaya a iya limit d’insa……. Tana shiga d’akin k’amshin turarensa ya mata sallama, a hankali ta shak’a ta lumshe idanunta! A take wata nutsuwa da kasala suka dirar mata sannan taji zuciyarta tana yin sanyi b’acin ran da take ciki kuma yana d’an raguwa. Bud’e idanuwanta tayi ta shiga k’arewa d’akin kallo tana ganin fuskarsa a idonta, murmushi ne ya sub’uce mata da ta tuna irin uwar hararar da ya zabga mata sannan yace “Ba zaki je ba!” ya juya ya fice. A hankali tace “Dama maza ma sun iya harara?” Tana murmushin tana tunani ta shiga gyara d’akin cikin nutsawa kwarewa da iyawa. Tana gamawa ta shige toilet ta wankeshi tsaf tsaf. A wajen Ummi taje ta karb’o kasko da turaren wuta ta saka a d’akin sannan ta shiga kitchen ta had’a masa spring rolls da tea, duk dan a barta ta fita. Tana gamawa ta fito ta kai dining ta jera a inda taga yana yawan zama. Tana cikin jerawa Ummi ta sauk’o, dariya tayi kafin tace “Fad’a na ne? Ko kuma biyayyar aure? Ko dai bribe d’in a barki ki fita gobe??” Turo baki Hudan tayi sannan ta d’anyi murmushi. A hankali Ummi ta k’araso inda take ta dafa kafad’arta sannan tace “Na gode Huda. Kin nunamin nima na isa da ke” Ta yi maganar tana murmushi. Murmushi mai had’e da dariya tayi sannan ta fad’a jikinta tayi hugging nata tace “Ummina kin isa mana” A haka su Shuraim suka shigo suka samesu, hakan ba k’aramin burgesu yayi ba kuwa, dan haka Shuraim ya k’araso ya yi joining hug d’in Sudais kuma ya tsaya ya fara bubbuga k’afa shi ala dole sai dai a cika su a yi mishi nashi special… Cika su Ummi tayi yana ganin haka ya k’araso yayi hugging d’inta. Ahankali ta zaroshi daga jikinta ta kama hannun Shuraim ta rik’e da nashi a waje guda sannan ta kamo hannun Huda ta saka mata hannayensu a cikin nata kafin ta fara magana “Na san ba wani girman su Shuraim kika yi sosai ba amman dan Allah Huda ko bayan raina ki zame musu uwa ki yi musu dukkkannin abunda zan yi, ba su da kamarki a duk fad’in duniyar nan.” Da sauri Huda ta toshe mata baki da hannunta Idonta ya cicciko da kwalla tace “Ummi ki daina dan Allah kar ki d’agamin hankali da yammar nan! Bana son irin wannan maganar in sha Allah babu inda zaki je ki barmu muna tare...” Kukan da ya kufce mata ne ya hanata kasa k’arasa maganar tata. A hankali Shuraim ya yi hugging d’inta sannan ya d’ago idanuwanshi da suka taru da kwalla ya kalli Ummi yace “Ummi Ki daina irin wannan maganar please, muna tare happy family together forever in sha Allah” Ya fad’i hakan yana murmushi. Murmushi Sudais yayi sannan yace “Group hug!” Ya had’asu duka yayi hugging yana dariyar son ganin ya kawar da sad moment d’in. Suma duk dariyar suka saka suna sharar kwalla. Sun d’an jima a haka tukunna Shuraim ya jaa kujerar ya zauna yana cewa “Let me eat small.. Yau haddar pages biyu nayi, tunda muka tashi a English section nake abu d’aya amman dukda haka sai da Mu’allim ya rankwasheni, duk cikina ya zuge….” Tray d’in Aslam ya shiga k’ok’arin janyowa, nan Ummi ta hanashi ta hanyar buge masa hannu. Hudan na dariya ta shiga ta d’auko musu nasu wanda ta saka a cooler. Nan kuwa suka hau ci suna santi dan ana bud’e cooler Sudais ma ya dawo yace “ya fasa tafiya saman” Dariya kawai suka yi musu daga nan Ummi ta d’an jaa ta gefe tace “One last thing Taje ta yi wanka ta shirya.. Yana zuwa idan ya ga ta yi miishi kwalliya nan da nan zai barta maybe ma ya barta ta kwana, haka ake yiwa maza….tayi sauri maza maza taje ta shirya yana..” Tun kafin Ummi ta gama magana Huda ta wuce sama d’auko kayanta…kunya da kuma son aikata abunda Ummin tace ne ya sanya ta kasa tsayawa taji k’arshen maganar. Kamar yadda ta had’a akwatinta ta hau da shi saman hakanan ta had’oshi harda kayayyakinta waenda ta d’an d’auraye ta shanya, ta kwaso ta sauk’o da su. Ba iya d’akin ba Hatta parlourn zuwa yanzu ya d’auki k’amshin turaren wuta. Tana shiga ta ajjiye akwatin ta fad’a tayi wanka tayi brush ta d’auro alwallar Magrib dan ta gabato, ta fito d’aure da d’an guntun towel saboda bathrobe d’in da ya had’a ya wanke a washinne machine ya shanya tare da inner wears d’insa har yanzu bata gama bushewa ba. Wani had’add’en d’inkin doguwar riga A shape ta fitar, kalar atamfar royal blue an yi mata d’inki irin mai stones d’innan… A hankali ta ware bra da pant sannan ta kinkimi akwatin nata ta nufi wardrobe Bud’ewa tayi ta sa akwatin nata a chan k’asa sakamokon kayansa da ta gani a jere a side har biyu! A ranta tace “Wato har wasu kayanma ya sake kwasowa Ummi tana chan tanata cewa In dawo d’akin bayan shi gashi partyn shi ma yake yi ya samu freedom” Kamar tana ganinshi haka ta ke kallon kayan tana zabga musu harara… Idanunta ne suka sauk’a abkan wata takarda kamar poster haka a ta chan k’asan takardar taga an rubuta ‘2021 tournament mathematics competition Winner NTIC’ Da k’arfi taji gabanta ya buga! Da sauri tasa hannu ta zaro sticker……..tun bata kai ga k’arasa zarowa ba ta fahimci ita d’in ce da gaske! A hankali ta cirota daga k’asan kayan nasa tana kallo tana sake kallon hotonta da sunanta b’aro b’aro a sama ‘Maryam Huda Muhammad’ Ga award d’inta a hannunta da medal d’inta tana murmushi… Kanta ne ya d’aure ta fara k’ok’arin juya takardar dan kamar da tana zarowa taga rubutu a bayan da biro. “Bincike fa babu kyau” Taji muryarsa a bayanta daff da ita!. Bata san lokacin da ya shigo ba amman ta d’anji k’amshin turaren da yake tashi ata jikin kayanshi ya k’aru a d’akin. Kwakwalwar ta already a cunkushe take ga tarin mamaki gashi dama duhu ya d’an farayi bata kunna globe ba tana d’anjin tsoro hakan ya sanya da taji mutum da murya a bayanta ta kwala ihun da ita kanta sai da ta d’an tsorota…. Da sauri ya juyo da ita ya sa tafin hannunshi akan bakinta yace “Shiiii.” Da sauri itama ta sanya dukkanin k’arfinta ta b’intike hannunshi daga bakinta kafin tace “Ya Aslam banaso Allah ka daina” Ta fad’i hakan tana k’ok’arin kare jikinta a rikice dan ba k’aramin kunyar towel d’in take yi ba. Dariya ma shi ta basa Yarinyar da ya gama k’arewa kallo ba tare da ta san ya shigo ba itace take wani kakkare jikinta… Wani d’an guntun murmushin gefen baki yayi sannan ya kama towel d’in ta sama yace “Idan ban daina ba fa? What will you do? Yaji za ki sake yi min ki gudu sama , ko me?” Ya fad’i hakan yana d’an jan towel d’in kad’an kamar zai fisge. Cikin tsananin tashin hankali ta sake kurma wani ihun a karo na biyu…. Ido cikin cikin suke kallon juna, so take ta d’auke idanunta a cikin nashi amman ta kasa sakamokon sak’onnin da yake aika mata daga kwayar idanuwan nasa. A hankali ya bud’e baki zai yi magana yaji an turo k’ofar d’akin da d’an k’arfi an shigo..................... 5 MINUTES BEFORE NOW. Ummi, sauk’owarta kenan daga sama zata d’auki abu a kitchen, sam bata san Aslam ya dawo ba. Tana shiga kitchen d’in taji kamar an shigo dan haka ta d’au abunda take buk’ata ta fito tana kallon k’ofa… Sakin lemon hannun nata tayi ya fad’i k’asa cike da mamaki da murna tace “Arshaad!! Sai kuma ta k’arasa da sauri bakin k’ofar inda yake tsaye ta hau dudduba shi tana murmushi fuskarta cike da murna da farin ciki. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 63 Mikiya Writers Association. Murmushi Arshaad ya yi kafin a hankali yace “Ummi, na same ku lafiya?” Sai a lokacin Ummin ta yi laakari da yadda bashi da lakka a jikinsa da kuma tsananin ramar da yayi. “Alhamdulillah” tace, sannan ta d’aura da cewa “where have you been?”. Still yanzun ma murmushi ya sake yi, a hankali yace “Bara in d’an huta” Ya fad’i hakan yana mai wucewa ya shige cikin parlourn, wanda sai da ya zo wucewar ne tukunna Ummi ta lura da akwatin da yake tafe da shi! Gabanta ne taji yad’an buga! Gashi babu damar ta tsayar da shi ko ta hanashi wucewa, a k’asan ranta tace “Anya kuwa zaman su Aslam da Arshaad zai yiu a waje d’aya?…” Tana cikin wannan tunanin ta jiyo ihun Hudan! Dakatawa Arshaad yayi ya juyo ya kalleta kafin yace “Kamar muryar Huda..” Shiruuu, Ummi ta d’anyi, chaan kuma ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya tace “Eh, suna nan, Granpa refuse to accept them” Ya bud’e baki kenan zai yi magana suka sake jiyo ihunta a karo na biyu.. Ita Ummi har ga Allah tayi tunanin wani abun ne ya sameta dan batayi zaton Aslam d’in ya dawo ba! Shiyasa tayi saurin nufar d’akin, ba tare da b’ata lokaci ba shima Arshaad ya bi bayanta da sauri…. NOW. Wardrobe d’in a setin k’ofar yake a ta tsaye! Shiyasa suna shiga suka gansu…. Da mugun sauri Arshaad ya juya Ummi kuwa da kyar kunya ta barta ta iya jan y’an k’afafunta ta bar wajen. Ko kyallin Arshaad bata gani ba, ga de akwatinsa nan a tsakar parlourn inda ya barshi… Wucewa tayi sama da sauri dan ji tayi kamar za a bud’e k’ofar d’akin su Hudan a fito. Achan d’akin kuwa su Ummi suna fita Huda tasa kuka! Ba abunda yafi d’aga mata hankali irin Ya Arshaad wanda suka had’a ido dashi! Shikenan ta san yanzu zai ce taci amanar sa ta gama! Bayan ko sati uku ba ayi da yin bikin ba…… Shiruu, Aslam ya d’anyi yana kallonta ta rufe idonta tana kuka ta duk’unk’une a tsaye waje d’aya, ajiyar zuciya ya sauk’e…..a hankali taji kamar ya bar wajen. Addua take yi Allah yasa fita zai yi, ai kuwa a hankali taji ya bud’e k’ofar ya fita. Tana bud’e ido taga ita kad’ai, ajiyar zuciya ta hau sauk’ewa a jejjere, da kyar ta samu ta d’an nutsu tukunna ta soma k’ok’arin barin wajen.. Poster da ta sub’uce a hannunta d’azu ta taka! Kalla tayi ta sake kallo kamar tanason yin nazarin wani abun chan kuma sai ta lumshe idonta ta bud’e kawai ta d’auka ta mayar inda ta ganta. Jikinta duk a sanyaye hakan nan ta samu ta shirya da kyar ta nemi waje ta zauna. Aslam yana fita ya fara k’arewa falon kallo kamar akwai abunda yake nema. Yana cikin kallon parlourn Idanuwanshi suka sauk’a akan trolley madaidaici. Wani yawu ya had’iye mai d’an d’aci tukunna ya furzar da iska ya nufi d’akin da yake da tabbacin Arshaad d’in yana a ciki. Knocking ya tsaya ya d’anyi, jin shiru yasa ya tura k’ofar ya shiga… Ganin ba kowa ya sanya yayi tunanin to ko dai ba nan d’in ya shigo ba, har zai juya sai ya jiyo motsin ruwa a toilet. A hankali ya sauk’e wata siririyar ajiyar zuciya kafin ya koma ya nemi waje ya zauna a bakin gadon. Morethan 10 minutes Arshaad ya d’auka a band’akin bayan shigowar Aslam. Har Aslam d’in ya fara tunanin lek’awa a ransa yana tunanin ‘maybe ko baya ciki an yi mistake d’in barin fanfo a kunne ne’ sai kuma yaji an kashe tap d’in! Still sai da ya k’ara 2 minute tukunna ya fito ya na tsane fuskarsa da towel…. A tunanin Aslam wanka Arshaad d’in yayi amman fitowar da yayi sanye da kayan jikinshi ne ya sa ya fahimci ba wanka yayi ba sai dai ko alwallah dan gashi ya nad’e dogon hannun white shirt d’in jikinsa gashin hannunsa a kwakkwance sajensa da sumarsa suka duk a jik’e. Murmushin da Arshaad d’in yayi masa ne ya katseshi daga nazarin da ya fad’a. A hankali ya mik’e tsaye yana kallonshi har ya k’araso inda yake tsaye. Aslam yana shirin yi masa magana yaji yace “Sorry.. Ban san kuna tare ba Ummi and I tot wani abun ne ya sameta shiyasa mu....” “Where have you been??” Muryar Aslam d’in ta katseshi. “Maldives” Ya bashi amsa a tak’aice sanann ya d’an wuce sa yayi hanyar fita yana ci gaba da cewa “Already na riga na yi arranging komai for honeymoon” Ajiyar zuciya Aslam ya sauk’e kafin yace “Arshaad, i.......” Da sauri Arshaad yace “Let’s pray! Naji har an kusan shiga masallaci.” Yana gama fad’in haka ya bud’e k’ofar ya fice. Aslam ya dad’e a tsaye kafin ya samu ya iya motsawa daga inda yake shima ya fice. Bai sameshi a wajen ba sai a masallacin, a gefensa ya tsaya suka yi sallar, sai da sukazo fita tukunna suka had’u da su Shuraim.. Suna ganin Arshaad d’in suka nufeshi suka yi hugging nashi cikin tsananin farin ciki..Sudais yana dariya yace “Ashe baka manta ba” Murmushi yayi kafin yace mishi “Ai na gaya maka last year daman ko Ina inane zan dawo ayi celebrating this year da ni” Murmushi dukkansu suka yi suka nufi gida. Suna shiga su Shuraim suka yi sama shi kuma Arshaad ya jaa akwatin shi ya nufi d’akin da ya zab’awa kanshi. Bai san Aslam yana tare da shi ba sai da ya shiga d’akin ya juyo zai rufe k’ofar! tukunna suka yi ido biyu. A bud’e kawai ya bar mishi k’ofar daga nan ya juya ya jaa trolley d’insa ya kai ya ajjiye. Yana juyowa ya ga Aslam d’in still a tsaye, murmushi yayi kafin yace “Ka k’araso ka zauna mana” “Arshaad listen, we have...” Cikin katseshi Arshaad d’in yace “We have to talk ko? About Huda! Aure! And everything right?” Numfashi ya fesar kafin ya cigaba “Akan me to za muyi maganan abunda ya riga ya faru ya wuce?” Ajiyar zuciya Aslam ya sauk’e kafin yace “Ba abun magana kam gaskiya, i ust want to know how you feel about us, together, and everything sannan kai! Are you ok??” Murmushi Arshaad yayi mai had’e da dariya kafin yace “Aslam i feel fine! Sannan I’m Ok. Tunda har ka ga na dawo Nigeria Kano to I’m Ok Aslam. So kawai abunda zan gaya maka shine kar ka dubani kace zaka yi affecting relationship d’inku negatively, ni ban ma san kuna gidan nan ba da a hotel zan zauna zuwa jibi inzo a yi birthday da ni daga nan in nemi inda zan je saboda I still can’t face Mammy! Sannan ba zan iya zama a tsakiyarsu ita da Dad suna fad’a kamar Annabi da kafiri ba. But still zuwa jibi zan san yadda zan yi in sha Allah….” Da sauri Aslam ya matso inda yake yace “No, you don’t have to. Kar ka je ko ina…” Cikin katseshi Arshaad yace “I’m sorry to say this amman after yadda kake feeling guilty right now akan halalin ka saboda ka san na ganku i definitely need to go! Kuna buk’atar air, in fact your relationship is somehow complicated dan haka kuna buk’atar time da space In other for you two to build a healthy and happy marriage.. If I can’t help banga dalilin da zai sa in zauna a tsakiyarku ba ina sakaku kuna feeling somehow. Zan iya rantse maka akan cewa I have moved on! And na manta da komai na cire Hudan a raina completely but na san ba lalle ka yarda ba, itama ba lalle ta yarda ba, za ku dinga gani kamar ko in kun yi abu zai sa inji ba dad’i ko wani abu makamancin haka wanda hakan zai sa ku kasa sabawa da kuma sakewa da juna, ni kuma har ga Allah ba zan so hakan ba, therefore i think i need to stay away for some months ko a year haka.. Maybe nima idan na tashi dawowa In dawo da tawa bride d’in” Ya k’arashe maganar da d’an murmushi a kan fuskarsa. A hankali Aslam ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya kafin yasa hannu ya janyoshi jikinshi yayi huggin nashi..... K’arar wayarsa ce ta sanya shi cika Arshaad d’in yad’an matsa sannan ya zaro wayar ya d’auka yasa a kunnenshi yace “Auwal” D’an jimm! Yayi, chan kuma yace “what for?” A hankali kuma sai yayi murmushi yace “Bara mu fito, Arshaad is home ma.” Bai jira jin me Auwal d’in zai ce ba ya katse kiran ya d’ago yana kallon Arshaad kafin yace “Mu je, Auwal ne” Bai musa shi ba ya bi bayanshi suka fita…… A babban parlourn suka sameshi, zaune cikin d’aya daga cikin set d’in kujerun dake a parlourn. Yana hango su ya taso, duk da halinda yake ciki hakan bai hanashi k’arasawa yayi welcoming Arshaad warmly ba. Aslam ne ya katse su ta hanyar cewa “Mai ya faru ne? You sound worried! Yanzun ma kuma you look worried” Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace “Tana Ina please? Bani da energy…..” Gaba kawai Aslam d’in yayi shi kuma ya bishi a baya. Suna zuwa k’ofar d’akin nasu ya murza ya shiga Auwal d’in kuma ya tsaya a waje. A zaune ya sameta, ta rafka uban tagumi…sanye cikin doguwar rigar da ta fitar d’azun zata saka. A rayuwarshi blue is one of his favorite colours, gashi blue d’in mai d’an duhu wanda ya taimaka wajen fito da ainahin kyawun farar fatarta..Yanayin dim light d’in dake kunne a d’akin ne ya taimakawa stones d’in jikin rigar tata wajen yin kyalkyali na musamman mai d’aukar ido da hankali… Normal d’aurin d’ankwali tayi irin na ture ka ga tsiya wanda ya fitar da uban tulin gashinta da ta tufke ta nannad’eshi a k’eyarta. Ba komai a fuskarta ko mai bata shafa ba amman kalar kyan da tayi masa yau dole ya bada tukuici!. A hankali k’asa k’asa yadda ta tabbatar ba zai ji ba tace “Ni fa bana son kallo” Tana mai d’auke kanta daga gareshi had’i da d’an turo baki. Murmushi kawai yayi sannan ya tako gabanta ya tsaya yace “Saboda me yasa bakya son kallon?” Runtse idanuwanta tayi, a ranta tace “Wannan ko maciji albarka” Batai auni ba taji yasa hannunshi a nata ya mik’ar da ita tsaye yana kallon rigar jikinta kafin ya maida idanunsa a kan d’ankwalin, murmushi yayi yace “D’aurin masifaffu dama yafi yiwa masu tsiwa kyau.” Haka kawai sai ta tsinci kanta da kasa d’agowa da kuma kasa cewa komai, still bata san daliliba amman maganar tasa ba k’aramin dad’i tayi mata ba! A take taji haushin shi da fushin da take yi da shi suna d’an raguwa… Ya jima yana kallonta kafin ya sauk’e ajiyar zuciya yace “Ki je Auwal yana parlour yana jiranki, muryarsa har rawa take yi, da alama emergency ne.” Ahankali ta sauk’e ajiyar zuciya dan ta san me ya kawo shi. Sai da ya sake cewa “Ki je” Tukunna ta iya jan k’afafuwanta ta d’anyi baya kad’an ta yadda ta tabbatar ba zata gogeshi in ta zo wucewa ba sannan ta wuce. Har ta kusan k’ofa taji yace “ungo” Tana juyowa ta ganshi a kusa da ita yana bata hijab d’inta. Tsayawa tayi bata matso ba balle yayi tunanin zata saka… A hankali ya matsa inda take yana kallonta itan ma shi take kallokafin ta yi k’asa da kanta kamar d’azu. Yanayin yadda ta yi d’aurin tabbas in ya saka mata a haka zai iya shak’eta shiyasa yasa hannu ya zare d’ankwalin ya rik’e a hannunsa So yake ya saka mata hijabin amman kyau da shek’in da gashin yayi da kuma yanayin parking d’in da tayi ne ya yi mugun tafiya da imaninshi dan haka ya tsaya ya shagalta da kallo…. A hankali yaji tace “Bara in je, ka ce ce emergency ne” Ba tare da ta d’ago kanta ba. Wata nannauyar ajiyar zuciya taji ya sauk’e kafin a hankali ya ware hijabin kamar baya so..sai da ya nemo fuskar hijab d’in tukunna ya ajjiye d’an kwalin nata a gefe ya sa hannuwanshi duka biyu ya bud’a ya kawo dede setin fuskarta yace “Raise your face” Tana d’agowa suka had’a ido yana kallonta itan ma shi take kallo ta cikin hijabin. A hankali ya matsar da hijabin yasa mata a fuska sannan ya d’an jashi ya zauna dede kafin ya ida warewa ya sakar mata shi ya rufe ilahirin jikinta. Tana shirin wucewa taji yayi cupping fuskarta yad’an matso kusa da ita. A zabure ta d’ago tana kallonshi shima ita d’in yake kallo kafin ya lumshe idanunsa a hankali ya kai lips d’insa dede goshinta ya sakar mata light peck d’in da ya sanya ilahirin jikinta d’aukar rawa! A hankali ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya sannan ya matsar da bakinsa a dede setin kunnenta yace “You look beautiful tonight” Yana gama fad’in haka ya cikata ya wuce toilet dan yana buk’atar yad’an watsa ruwa kafin lokacin dinner, garin yau akwai zafi sannan shi kanshi kwana biyun nan yana saurin jin zafin yanayin dauriyace kawai yake yi. Da kyar ta samu k’irjinta ya d’an ragu da bugawa sannan ta d’an dedeta kanta ta fita wajen Auwal. Tare ta tadda su a parlourn shi da Arshaad. Gaba d’aya sai ta tsinci kanta da diriricewa kamar mara gaskiya, ta tsaya. Tun sanda ta fito Arshaad ya ganta, ganin duk ta rikice ta kasa k’arasowa ne yasa yace “ko In baku guri ne?” Ya fad’i hakan da d’an k’arfi ta yadda ya san za ta jiyo sa. Da sauri ta d’ago ta kalli inda suke, suna had’a ido ya sakar mata lallausan murmushi sannan ya sake maimaita tambayar tasa. A hankali ta sauk’e ajiyar zuciya sannan ta fara takawa ta isa inda suke ba tare da ta sake yarda sun had’a ido da Arshaad d’in ba. Murmushi kawai yayi ya zaro wayarsa a aljihu ya shiga daddanawa…., Tana zama Auwal ya juyo gaba d’ayanshi gareta ko gaisawa bai iya tsayawa sun yi ba yace “Dan Allah da gaske gobe za a kawo kud’in auren Sakina?” Ba k’aramin tausayi ya bata ba dan har wata kwalla taga ta taru a idanuwanshi.. A hankali tace “Ya Auwal duk abunda kaga Allah bai yi ba muddin ka yi addu’a to ba alkhairi bane, ka kwantar da hankalinka zaka samu wadda ta fita in sha Allah.” Cikin katseta yace “Da gaske ne kenan” A hankali muryarshi na d’an rawa. D’agowa tayi da niyyar sake bashi hak’urin ya rungumi k’addara kawai taga hawaye bibbiyu suna zubo masa! Da sauri ta runtse idonta tace “Ya Auwal dan Allah ka daina mana, ka rungumi k’addara kayi adduar Allah yasa hakan shine mafi alkhairi” Bud’e baki yayi da niyyar yin magana sai kuma ya kasa, da sauri ya tashi ya fita a side d’in gaba d’aya ba tare da ya sake waiwayon su ba. Ajiyar zuciya ta sauk’e a hankali tana jin tsananin tausayin Auwal a ranta. Kamar ance ta d’ago, tana d’agowa suka had’a ido da Arshaad, murmushi ya sake sakar mata kafin yace “Abun tausayi, ko?” Sunkuyar da kanta tayi a hankali ta d’aga kan alamar “Eh” Yana shirin yin magana Ummi ta sauk’o! Har ga Allah haka kurum sai ta tsinci kanta da rashin jin dad’in ganinsu a zaune su biyu. Tana zuwa ta nemi guri ta zauna kusada Huda ta kamo hannunta k’asa k’asa tace “Huda tunda ba ku kad’ai bane a gidan, ku dinga saka key a k’ofar ku mana. Wallahi ban san ta ina zan fara kallon Aslam ba” Da sauri Huda ta sunkuyar da kanta k’asa sosai wanda hakan har sai da ya sanya Ummi ta d’anyi murmushi. Sarai Arshaad ya ji abunda suka ce amman bai nuna musu ba! Hasalima chatting d’insa kawai yake yi yana murmushi. Ganin hirar tata ba zata yiu da Hudan ba yasa ta juyo ga Arshaad tace “Ka je wajen Mammy?” Sai da yad’an k’ura mata ido, kamar ma bai ji abinda tace ba tukunna yad’an gyara zaman shi ya maida wayar aljihu kafin yace “A’a, direct daga airport nan nayo” A hankali tace “Bata da lafiya” Bata ida rufe bakinta ba yace “I know!” Ta lura da yadda yanayinsa ya chanja amman hakan ba zai hanata yi masa nuni da gaskiya ba dan haka tace “Arshaad no matter what, ko me tayi maka Mahaifiyarta ce! She’s sick! Very sick! She needs you! Aiima bata nan ita kad’aice. Ajiyar zuciya ya sauk’e yana kallon Ummin ido cikin ido yace “Abba baya nan ne?” “Eh, yayi tafiya shi da Daddy business trip sannan za su bud’e branch d’in construction company d’insu shi da Aslam a UK sun ma bud’e It was successful sannan trip din nasu was also successful shiyasa jibi za mu yi double celebration in sha Allah.” Ummin ta zayyano mishi dan so take su yi magana kar ya samu question d’in da zai sake jifanta da shi as an excuse. “Ma sha Allah Allah ya k’ara d’aukaka” Yace, daga nan ya mik’e. Itan ma mik’ewa tayi tace “We are not done” Sai da ya lumshe idanuwansa ya bud’e kafin ya kalleta yace “Ummi ko In koma inda na fito ne? Although i came for Shuraim and Sudais but it’s like bakya murna da ganina!” Da sauri tace “Arshaad ba haka ba...” Cikin katseta da d’an b’acin rai yace “To na rok’eki da girman Allah ki daina yi min maganar Mammy Ummi kina so inje In zauna Ina ganin suna fad’a kullum ita da Dad ko yaya?” Tausayin sa ne ya fara rufeta dan haka ta k’arasa inda yake ta kamo hannunshi ta rik’e a nata tace “Ba haka bane son, ka fahimceni” Kamar zai yi kuka yace “Me kike so inyi yanzu?” Har ta bud’e baki za tayi magana sai kuma tace “Ba komai, nothing” A hankali ya zame hannunsa a cikin nata ya juya ya shige dakinsa. Ta d’an jima a tsaye kafin ta sauk’e ajiyar zuciya ta juya ta nufi kitchen ta fara setting dining table. A hankali itama Huda ta mik’e ta k’arasa ta shiga tayata. Sai da suka gama tukunna Huda ta wuce d’aki, ita kuma Ummi ta zauna anan kan dining d’in ta rafka tagumi. A gaban dressing mirrow ta sameshi yana taje gashinsa.. Sanye cikin pyjams dark ash da suka yi mishi kyau matuk’a!. A hankali ta k’arasa bakin gado ta zauna ta d’auki wayarta da ta mak’ala a charge ta danna kiran Sakina Bayan ta zare wayar a charging. Tana d’auka tace “Yanzu Ya Auwal ya tafi” “Um” Kawai Sakinar tace, a hankali. Ajiyar zuciya Huda ta sauk’e kafin tace “Yayi matuk’ar bani tausayi, har da kuka fa yayi. Da kin sani baki gaya mishi yanzu ba” Shiruu, ta ji Sakinar tayi kafin chan tace “Ya dameni da kira da massages! At least yanzu zan huta sannan i don’t want him to have any false hope.” Cikin son kawo k’arshen maganar Auwal d’in tace “Za ki zo goben?” Sai da ta kalli Aslam wanda yanzun yake zaune akan sofa yana k’ok’arin kunna computer tukunna tace “Ya hanani” Da d’an k’arfi ta yadda ta san zai ji. “Ki lallab’ashi” Shine kawai abunda Sakinar tace. Har zata kashe wayar sai kuma tace “Jiya su Shuraim ma sun biyo nan daga school, sun kawo mana invitation d’in birthday d’insu Su Mama dai ba zasu zo ba amman ni da Sumayya za mu zo goben In sha Allah.” Cike da murna Huda tace “Allah ya kaimu da rai da lafiya. Ku zo da sassafe dan Allah ayi shirye shiryen komai da ku” Murmushi kawai Sakina tayi tace “Ai inaga 3 hours ma kawai za mu yi, za mu zo 2 mu tafi 5 haka, ba lalle ma mu samu event d’inba kawai dai za mu zo ne dan naga sai wajen 10 ma tukunna za a fara, so kawai za mu d’an lek’o.” Da sauri Huda tace “To ku kwana mana” Dariya Sakina tayi tace “Bara in yi sallah. Sai anjima” Dan so take ta kashe wayar sakamokon kanta da yake mata tsananin ciwo da kuma rud’anin da zuciyarta take ciki! Dauriya ce kawai take yi da har aka samu take iya yin magana. “Okay, ki gaida Ummu da Sumayya” Hudan tace daga nan suka katse kiran. Ita bata ma san Aslam ya fita ba sai da ta d’ago tukun taga ba ya nan “Hmm, mutum sai basirar iya san’da kamar munafuki” Ta fad’a a ranta. Tana mik’ewa tayi haramar kimtsawa domin ta gabatar da tata sallar dan taji an shiga masallaci. Tana idarwa ta fita da sauri ta d’ebo abinci a plate ta d’auko ruwa ta shigo har da d’an gudu dan taji kamar mutum zai fito a kitchen. Da wuri tayi ta cinye ta sha ruwa ta yi brush, ko plate d’in bata d’auke ba ta kwanta ta k’udundune a cikin bargo! Ala dole Ita tayi barci kenan saboda gudun kar ma wani ya shigo yace ‘taje tayi dinner’ Saboda ita har ga Allah kunyar had’uwa da Arshaad take yi after what he saw daga zuwanshi gidan bata jin zata iya sakewar had’a ido dashi balle zama waje d’aya. Kusan kamar 40 minutes wayarta ta fara k’ara! Dan haka ta tashi ta d’auka, tana ganin sunan Abba ta d’auka da wuri cike da zumud’i tace “Abba, Ina wuni, kun taho ko?” Murmushi yayi yace “A’a tukunna, yanzu dai muke shirin isa airport. Gobe around 7:00am in sha Allah za mu k’araso saboda muna da transit” “Okay, Allah ya kawoku lafiya” Murmushi yayi yace “Ameen princess, Ina Aslam?” Sai da ta d’anyi shiruu, tukunna tace “Yana waje, suna dinner” Da sauri yace “ke fa?” A hankali tace “yanzu na gama a d’aki” Zai yi magana ya ji tace “Ya Arshaad ma ya dawo.” Shiruuuu, taji Abban yayi kafin yace “Okay, sai mun k’araso goben in sha Allah” A hankali tace “Safe fligh Abba” Murmushi yayi yace “Thank you princess” Daga nan suka katse wayar, tana shirin ajjiyewa Aslam ya shigo! Hannunsa rik’e da plate a da ruwa. Ta ji shigowar tasa amman bata d’ago ba, har ya tako ya zo inda take ya zauna a gefen gadon kusa da ita. Sai a sannan ta d’ago tana kallonsa da plate dinsa.. a ranta tace “shima a nan zai ci abincin yau ko me?” A hankali taji yace “Kin ci abinci kena?” D’agowa tayi tana kallonshi taga yana kallon plate d’in gefenta wanda ta ajjiye akan side drawer. A hankali ta d’aga masa kai alamar ‘eh’. Shiruuu, suka yi chan taji yace “Ya za muyi da wannan??” D’agowa tayi taga shima itan yake kallo! Da sauri ta sunkuyar da kai dan yau wani kalar kallo taga yana yi mata wanda ya sanya kwata kwata bata son had’a ido da shi. Shirun ne ya sake biyowa baya kafin ta ji ya bud’e plate d’in da ya rufa a kan na abincin ya fara tab’a spoon d’in…. Bata gama tunanin me yake yi ba taji yace “Haa” Tana juyowa taga ya d’ebo fride rice d’in wadda taji hanta ya kawo kusa da fuskarta. Sai da ta sauk’e ajiyar zuciya sannan ta kawar da kai tace “Na k’oshi” Ji tayi kawai ya kamo hannunta ya d’an matse a cikin nasa a hankali ya sake cewa “Haa” Yana sake matso da cokalin. “Ya subahanallah! Wannan wanne irin mutum ne?” Ta yiwa kanta tambayar a cikin ranta. Ji tayi ya murza tafin hannunta da nashi hannun still a hankali taji ya sake cewa “Haa” Da sauri ta juyo ta bud’e bakin ta lumshe idanunta numfashinta na fita da sauri sauri. Murmushi yayi ya saka mata cokalin a baki ita kuma ta karb’a ya juye mata tukunna ya zare. A hankali ta shiga taunawa, har yanzu idanuwanta a lumshe suke. Kamar wanda ya samu tv haka ya nutsa ya maida hankalinsa wajen k’arewa kyakkyawar fuskarta kallo. Sai da ya ga ta had’iye tukunna ya mayar da cokalin ya fara k’ok’arin d’ebo wani, da sauri ta d’aura hannunta a kan nasa ba tare da tayi laakari ba, tace “Nafa ci abinci Mai yawa. Please Ya Aslam kar in yi amai” Sannan ta fara k’ok’arin bud’e kyawawan idanuwanta da suka taru da kwallah. Tana gama bud’ewa taga ya ajjiye spoon d’in ya na k’ok’arin bud’e robar ruwa… Ba yadda ta iya haka ta yarda ya bata a baki ta sha tukunna ya mik’e ya d’auke plate d’in da ta ajjiye a kan side drawer ya had’a da wanda ya shigo da su ya fitar. A yadda ya fita ya barta a haka ya dawo ya sameta, bai kalletaba bai ce mata komai ba ya nemi waje ya zauna ya ci gaba da aikin da yake yi d’azun kafin ya fita sallah. Ya d’an jima yana aikin, kafin yaga ta taso ta k’araso ta zo inda yake. A hankali ta zauna a gefensa tace “Ya Aslam” “Um, Anty Huda” Ya ce ba tare da ya kalleta ba, yana mai ci gaba da typing d’in da yake yi. Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin tace “zan je dan Allah, goben.” “No” Yace, still bai kalleta. Turo baki tayi kafin tace “Na dawo fa d’akin” This time around dariya yayi kafin ya rufe computer gaba d’aya sannan ya juyo gareta yace “Ki yi hak’uri, baza ki je ba.” Kamar da wasa kawai sai yaga ta fashe ta kuka! Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya matso ya kama hannunta yace “Mama ce tace kar a barki ki sake fita sai nan da wata d’aya. Idan kina son fita ki kira Hajiya Shuwa idan ta barki sai ki je.” Da mamamki take kallonsa tana rage sauti da yawan kukan nata. Jinjina mata kai yayi alamar tabbatarwa. A hankali ta shiga share hawayenta tana sauk’e ajiyar zuciya a hankali. “Yanzu zaki kuma yin wani yajin kenan? Tunda dai kinga ba damar fita gobe Ba ni zan barki ba Hajiya da Mama ne” A hankali ta girgiza kanta tace “Ka yi hak’uri, a kan abinda nayi” Murmushi yayi yace “Ai kuwa na hak’ura! Tunda har kwalliya da turaren wuta aka saka duk dan saboda ni. Ko ba dan ni akayi ba??” Murmushi kawai tayi ta sake sunkuyar da kanta k’asa. A hankali yana kallonta kafin yace “Je ki kwanta. Gobe tashin asuba ne, ko?” Ba tare da ta d’ago ba tace “Kaje ka kwanta kai, ni a nan zan kwana. Da bananan ai a gadon kake kwana.” Sai da yad’an k’ura mata ido tukunna yace “A nan d’in nake kwana.. Har gyara miki gadon nake yi kullum thinking you will come back A haka bacci yake d’ibana kullum.” Shiruuu suka yi duk su biyun kafin yaji tace “Ka fini tsayi, ina gani kullum kujerar bata isar ka, ka je ka kwanta don’t be stubborn” Dariya taji yayi kafin yace “In da acting stubborn nake miki yanzu ai da na san tuni kin fita a d’akin nan da gudu” Bata fahimci kan zancen nashi ba dan haka kawai ta basar da zance ta sake cewa “Ya Aslam barci nake ji, ka je ka kwanta.” A hankali yan kallonta yace “Are you sure? In je in kwanta ba damuwa?” Da sauri ta d’ago ta d’aga mishi kai sannan tace “Sai ka fi sakewa achan da kyau” Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace “Thank you Hudatie” Haka kurum ta tsinci kanta da murmushi dan ba kad’an ba sunan ya yi mata dad’i matuk’a. Murmushi shima yayi kafin ya mik’e ya fara d’ibar throw pillows d’in kan sofar.. Iya yadda hannunshi zai iya d’iba ya kwasa ya nufi gadon. A ranta tace “Ikon Allah! Neman magana yake yi wannan ko mee? Bayan pillows d’in da suke kan gadon wajen guda 4 masu laushi mai kuma zai yi da throw pillows??” Tunaninta ne ya katse ganin yana jera throw pillows d’in yana raba gadon gida biyu da su. Tuni! Kwakwalwarta ta bata me yake shirin yi dan haka tana gani ya gama ya tunkaro ta ta mik’e ta fara magana ba tare da ta kallesa ba “Ai ni nace maka anan zan kwanta Allah kar ma kayi tunanin haka! Idan kuma neman maganata za ka yi to wallahi zance na fasa sai da ka dawo ka cigaba da kwana a sofa kuma ko zanga k’afafuwanka suna lankwashewa kana tafiya da kyar ba zan sake y......” Dip! Maganarta ta d’auke sakamokon d’aukarta da yayi tashi d’aya in a bridal style…… Ba tare da ya kalletaba ya fara tafiya da ita towards the bed. Tsoro da mamaki da kuma yanayin da ta tsinci kanta a ciki ne suka sanya ta kasa magana ko yunk’urin zamewa.. In banda kallon gefen fuskarsa ba abunda take yi har ya isa bakin gadon ya sunkuya ya kwantar da ita rigingine a kan gadon ya d’aura mata kanta a kan pillow ya zame hannuwansa. Ba tare da ya d’ago daga sunkuyon da yayi a kanta ba fuskarsa dan da tata ya d’ago da idanuwanshi ya sanya su cikin nata a hankali yace “Sleep here. Dan Allah” Sannan ya mik’e tsaye ya zagaya d’ayan side d’in ya kwanta. Sai a lokacin ta samu ta sauk’e wata siririyar ajiyar zuciya mai vibration kamar mai jin sanyi. A hankali taji yace “Ki yi addua, good night”............ Ita dai Hudan a yadda ya barta nan rigingine tana kallon sama a haka ta farka ta ganta lullub’e da bargo, daga cikinta zuwa k’asa..ba ta san lokacin da barci ya kwasheta ba. Ko ba a fad’a mata ba ta san Aslam d’in ne ya lullub’eta. Kiran sallar da ta ji ne ya sanya ta fahimci tabbas yau ta d’an makara dan kamar ma har an shiga masallaci, ta ji. Addua ta yi tukunnan ta d’an juya ta kalli side d’in da ya kwanta. Ga mamakinta sai ta gansa kwance a kan gefen damanshi yana facing d’inta.. Bacci yake yi peacefully kamar kuma da murmushi a kan fuskarsa. Kamar yadda ya rufe mata rabin jikinta haka nan shima ya rufu da bargon. Jin an tada ik’ama yasa ta d’an matsa kusa da shi ta fara kiran sunanshi… A hankali yake bud’e idanuwansa, kafin ya k’arasa bud’e su tarr a kan fuskarta! Murmushi ya sakar mata a hankali taji yace “Lucky Morning” Shiru tayi taana kallonshi shima itan yake kallo chan ta d’auke idonta da sauri tace “Zaka makara fa, har an shiga sallah.” Da sauri ya mik’e ya d’an dafe kansa yana mutstsika idonshi kafin ya sauk’a akan gadon ya fad’a toilet. Ko da yaje har an tafi ruku’u dan haka raka‘a d’aya ya samu. Haka nan suka dawo tare da su Shuraim da Arshaad Sudais yana cewa Arshaad “Ya kamata ya yiwa Ya Aslam bulalar makara sallar asuba yau” Murmushi kawai Arshaad d’in yayi ba tare da yace musu komai ba ya wuce d’akinsa. A shirye ya tarar da Huda, suna gaisawa ta fice zuwa kitchen don had’awa Abba abunda ta san yafi so. A kitchen d’in ta tarar da Ummi don haka suka taru suka had’a masa lafiyayeyyen breakfast.. 6:30am, Aslam ya fice tare da Sudais suka tafi d’auko su bayan shi da Hudan sun yi wishing d’insu ‘Happy birthday’ sun basu gifts d’insu shi da Shuraim. Kafin 8:00am suka dawo, Daddy direct side d’insa ya wuce Abba ma suka nufi side d’inshi shi da su Aslam. Da gudu Hudan taje ta yi hugging d’inshi tana murna haka ma Shuraim, daga nan aka shiga gaggaisawa. Ummi, ba kad’an ba tayi matuk’ar jin dad’in yadda Abba ya yi mata faram faram! Dan haka ta samu kwarin guiwa ta hau gabatar masa da abinci kala kala ita da Hudan. Cike da farin ciki yake karb’a yana ci dan Huda da Shuraim da Sudais ke bashi a baki one by one duk da Sudais yana ta yi musu kwange….. A haka suka ciyar da Mahaifin nasu cike da tsananin so da k’aunar juna. Sai da ya k’oshi aka tattare wajen ya fara shirin mik’ewa tukunna Arshaad ya fito. Cike da kulawa Abba yayi welcoming d’insa daga nan ya wuce sama bayan ya bawa Ummi briefcase d’insa yace ta kai masa dakinsa Shuraim kuma ya ja masa trolley d’inshi. Bai tarar da Shuraim a d’akin ba, sai Ummi ita kad’ai ya tarar ta juya baya tana k’ara turaren wutan da ta saka tana d’an fifitawa… D’akin ya sha gyara ba kad’an ba gwanin sha’awa. A hankali ya k’arasa inda take tsaye yayi hugging d’inta ta baya. A mugun zabure ta juyo dan sam! Ko da wasa bata yi expecting haka daga Abban ba. D’an guntun murmushi ta gani kwance a kan fuskarsa, a hankali yace “Ko ba a shirya yi min wannan tarbar ba?” Ummi bata san lokacin da ta fashe da wani kuka ba, ta fad’a jikinsa cikin kukan tace “Abba ka yafe min dan Allah kayi hak’uri ka yafe min” Hugging d’inta yayi a hankali dede setin kunnenta yace “Shiii, komai ya wuce. Ki manta da komai! Just think about me”. ....…….. Ana cewa mutum yana kasa dai na murmushi bata tab’a yarda ba sai yau da ta faru a kanta. Shi kanshi Abban ya lura da tsananin farin cikin da take ciki! Yaso ya gaya mata cewa Maryam ce ta rok’esa akan ‘ya yafe mata ya zauna cikin kulawa da ita’ dan shi bai iya kwana kwana ko b’oye b’oye ba amman yadda ya ganta cikin tsananin farin ciki ne ya sa ya fasa gaya mata ya kuma yi alk’awarin rufe maganar tsakaninshi daga shi sai Maryam d’in. Tabbas shima yana cikin farin ciki ba kad’an ba dan yanzu Maryam ta kan kulashi, jiya har Friday massage ta mayar masa bayan tayi mishi replying nashi message d’in da ‘Ameen, jazakallahu khairan’…… A hankali ya lumshe idanuwansa yana adduar ‘Ubangiji ya sake mallaka masa ita a karo na biyu’. Har Ummi ta gama drying gashinta ta fita dan ana buk’atar ta urgent a k’asa bai saniba Sai da ya tashi shiga toilet tukunna ya lura bata nan.... Shirye shiryen birthday ake yi na y’an gata! Gaba d’aya compund na mansion d’in ake decorating, an kwashe motocin duk an fitar wasu kuma an kaisu baya. Hudan bata tashi sanin abun na gaske bane sai da taga ana rubuta ‘Happy birthday Sudais&Shuraim’ da grass carpet tun daga farkon mansion d’in har wajen k’ofofin shiga mansion d’in sannan ta sama ma fitilun da ake decorating da su sunan su ne aka rubuta ‘Happy birthday Shuraim and Sudais’ Gurin zaman su ma ya sha decoration ba a magana ga cake d’insu anata jerawa guda biyu iri d’aya each one ya kai kusan hawa biyar. Compound d’in kuma inda guests za su zauna kujeru ne guda biyu da table a tsakiya shima ya sha decoration Irin haka wajen guda 70 a daban daban. Abinci kuwa sai shigowa ake yi da su kula kula drinks da ruwa ma ba a magana cupcakes desert soaked cakes abun dai sai wanda ya gani. Tun 3:00pm Aka fara kawo Yara, friends d’insu maza da mata y’ay’an masu kud’i masu fad’a a ji, daga yanayin motocin da drebobin da suke kawo Yaran za ka gane abun na manya ne. K’awar Ummi d’aya ce tak! Ta zo. Dan mutum d’aya kawai ta yi inviting saboda yawancin k’awayenta ta lura a yanzu halayyarsu ba d’aya ba so ta san tasu ba zata ci gaba da zuwa d’aya ba. Mammy kam kaff sister’s d’inta sai da suka zo tare da y’ay’ansu, Mom itama tayi gayyata sosai amman kuma tunda suka zo ko Ummin ba su lek’awaba sun mak’ale a side d’in Mom wadda suka ja gefe Ita da Mammy sunata k’usk’us! Daga ganin fuskar Mammy ka san ba alkhairi dan ko kallon mutum ma da kyar take iya yi In banda cika da batsewa ba abunda take yi........... Har aka kira isha su Sakina basu zo ba gashi sai kiran su take yi basa d’auka! Haka nan ta mik’e tanata k’unci ta gabatar da sallar isha ta mik’e ta fad’a toilet. Fitowarta a toilet kenan sanye cikin bathrobe gashin kanta wanda ta wanke kuma ta nad’e da towel.. Kusan tare suka bud’e k’ofa suka shigo cikin d’akin ita da Aslam wanda ya shigo rik’e da wani k’aton box! Had’a ido suka yi dan haka ta sunkuyar da kanta k’asa tana gyara zaman bathrobe d’in jikinta. A hankali ya tako yazo inda take nan tsaye tak’i gaba tak’i baya, yace “Mu je ki shirya” Da sauri ta d’ago tana kallonshi kafin tayi k’asa da kanta tace “To ka fita mana” Dariya yayi ya juya ya ajjiye kwalin a kan dressing mirrow ya kwashi kayanshi da zai saka yace “Ki jirani i have a gift for you, kar ki fita please” Ajiyar zuciya ta sauk’e a hankali tana kallonshi ya zo ya wuce ya shige toilet d’in. A hankali ta sunkuya ta bud’e wardrobe ta jawo akwatinta ta d’auki mai ta shafa ta mayar ta day inner wears d’inta ta saka ta maida bathrobe d’in sannan ta d’au turaren jiki da misk ta shafa. Powder eye liner da mascara ta fitar ta ajjiye a gefe sannan ta fidda wata doguwar riga b’aka da mayafinta. Sai a lokacin ta lura bata da takalmin da zata saka sai dai tayi using wanda take yawo da shi a cikin gida saboda duk takalmanta na lefe da wanda take da su gaba d’aya suna gidan Ya Arshaad. Shiruu, ta yi ta shiga tunani….. A hankali taji ya bud’e k’ofa ya fito dan haka ta d’aga kai tana kallonsa… Ba yau ta fara ganinshi da suite ba amman ta yau special ce dukda bai d’aura suite d’inba amman kyawunshi ba k’aramin fitowa ya sake yi ba! Wandon dogo ne Baki kamar pencil wanda ya yiwa dogayen k’afafuwansa tsananin kyau! Rigar kuwa longsleeve ce itama baka yayi tucking cikin wandon. “Na yi kyau har haka ne?” Taji muryarsa ba tare da ya kalletaba. Da sauri ta sauk’e idanunta k’asa, ta shiga kiciniyar mik’ewa sai dai kuma har ya k’araso yazo ya tsaya a wajen bata mik’e d’inba! Murmushi kawai yayi ya bud’e wardrobe wajen kayansa ya d’auki agogo da belt sannan ya zaro suite d’in da zai d’aura akai da necktie ya wuce gaban mudubi. Sai a lokacin ta samu damar d’aukar y’ar mitsitsiyar hair dryer d’in da take buk’ata ta mik’e ta nufi bakin gado da kayan da ta ware… Tsaff ya shirya ya shafa mai kad’an ya fesa turarurruka ya gyara gashinsa, sannan ya d’auki kwalin ya nufi inda take zaune har yanzu ko kwance kan bata yi ba ballantana ta busar Ita ala dole jira take sai ya fita tukunna. Yana zuwa ya d’aura mata akan cinyarta ya nemi waje ya zauna a gefenta. D’agowa tayi ta kallesa, da gira yayi mata alamun ta bud’e! A hankali ta shiga warware bow d’in da yake nan a saman kwalin wanda an yi amfani da igiyar ne wajen d’aure kwalin, tana kwancewa ta d’an d’aga ta zareshi gaba d’aya a jikin kwalin ta ajjiye kafin ta kama gefe da gefen ta d’aga shima ta ajjiye murfin a gefe. Bata san lokacin da tace “woow!” Ba. Wata had’add’iyar riga ce a ciki, duk da a nunke take ta fahimci princess gown ce dan gata a jikin wata a gefe an manna da alamun anaso masu siya su san yanda take ba tare da sun bud’e ledar sun warwaretaba. Gefe guda kuma y’an kunne ne masu kyau da bracelet da anklet, sai takalmi shima an yi mishi gurin ajiyar sa daban mai matuk’ar kyau kalar y’an kunnen da kayan RED!. Chan k’asa kuma wani d’an k’aramin lipstic ne an yi rapping d’inshi da leda garai garai da alamun gift ne shi aka bayar. Banda murmushi tana kallo tana sake kallon katon kwalin, ba abunda take yi. A hankali ta ji yace “Do you like it?” Murmushi tayi mai d’an had’e da dariya kafin ta juyo ta d’aga masa kai tace “Yes, na gode sosai” Kallon idanunta yake yana hango farin cikin da take ciki a hankali ya jinjina kai ya d’an motsa bakinsa yace “Welcome” Sannan ya mik’e ya karb’a dryer d’in hannunta ya bud’e ya mak’ala comb d’in ya jona a socket. Har zai kunna sai kuma ya koma gaban dressing mirrow ya d’auko hair cream ya dawo. Takalmansa sau ciki ya cire ya bar iya safar ya hau kan gadon ya tsugunna ata bayanta sannan yace “ta mik’o mishi dryer” Juyowa tayi da d’an mamaki a fuskarta kafin tace “Me zaka yi?” Tana d’an zaro ido. “Bani sai ki gani, ko?” Ya fad’i hakan yana k’ok’arin b’alle murfin hair cream d’in da ke hannunsa. “Ko kina buk’atar cuddling ne sannan ki mik’o?” Ya fad’i haka yana zare towel d’in da ta nad’e gashin da shi. Tun kafin ya ida rufe bakinsa tayi sauri ta mik’a masa dryer. Karb’a yayi yana dariya k’asa k’asa sannan ya d’an d’ebo man ya mulke mata jik’ak’k’en gashin nata da shi ya fara busarwa yana tajewa. Hudan, ba k’aramin mamaki ta sha ba game da yadda akai ya iya gyaran gashi dan har wani massage yake mata da taji tana shirin fara barci. Gyaran gashin yake yi amman cikin nutsuwa da aji. Kasa hak’ura tayi tace “A ina ka koyi gyaran gashi?” Sai da yayi murmushi tukunna yace “Internet. I always dreamt of making my wife’s hair..gashi is one of the things da nayi ta adduar Allah ya sa matata ta kasance tana da shi, I love it! Sai gashi Allah ya amsa adduar tawa.” Ya fad’i haka yana me kashe dryer dan har ya gama. Dariya Huda ta fara ganin yadda ya dawo gaban gadon yana haki kamar wanda yayi race. Hararar ta yayi ya b’ata rai tukunnan yace “ba thank you sai dariya ko?” A hankali tace “thank you” Sai da ya gama hutawa tukunna ya tashi ya d’auko rigar ya cire a leda ya ware ta ya kama hannunta ya mik’ar…. Da sauri tace “Ya Aslam kai fa kai kad’ai ka shirya” “Bari tou In cire nima sai ki tayani, ko?” Yayi mata tambayar yana k’ok’arin kwance belt d’in wandon jikinsa. Da sauri ta rik’e hannunsa tana turo baki sannan ta sunkuyar da kanta k’asa….. Zip d’in rigar har kusan chan k’asa ne dan haka ya zuge shi duka tukunna ya kawo ta wajen kanta ya zura mata sannan ya saki rigar. Ganin yana k’ok’arin sa hannu ya kwance mata bathrobe d’in ta ciki yasa tayi sauri ta matsa ta kwance ta zame hannuwan kafin tayi k’asa da ita duka sannan ta jaa hannun rigar ta saka threequater hannun ta fara k’ok’arin zuge zip d’in…. Ganin bazata iya ba ya sa duk turjewarta haka ta tsaya ya ja mata….. Kwalliyarma da kyar ya barta ta shafa powder ta saka mascara da eye liner amman y’ankunne bracelet anklet takalmi da red lipstic duk shine ya saka mata! Tayi kyau kuwa sosai…, A hankali ya ajjiye lipstic d’in yana kallonta…. Ganin kallon yayi yawa ya sa ta wuce taje ta d’au ribbom d’inta ta yi parkin, ta d’auko wani tauban cap na chantily mai stones red ta saka ta d’auko vail black medium ta rufa a kafad’a……. Aslam, gaba d’aya jikinsa yayi sanyi dan Huda ba k’aramin tafiya tayi da imaninsa ba..duk inda tayi kawai binta yake yi da idanu. A hankali ya d’au wayarsa ya k’arasa inda take ya jaa hannunta suka nufi gaban dressing mirrow suka tsaya… Ta tsaya a gabanshi shi kuma a baya ya rik’e waist d’inta yayi musu hoto. Sun yi kyau kuwa ba kad’an ba kuma sun fito sosai. A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya ya gyara mata mayafin nata ta hanyar maidashi saman kanta kafin yace “Can we talk?” ya fad’a hakan yana me juyo da ita suka yi facing juna kafin ya d’aura hannayensa a kan kafad’unta ya fara magana “Next week, in shaa Allah inaso mu wuce UK! Mun riga mun gama magana da su Abba tun last 2 weeks jiya kuma har su Ummi na gayawa a wajen dinner, yanzu ke kad’ai ya rage baki sani ba. Za ki bini?” Ya k’arashe maganar a hankali. “Um um” Tace tana mai ja da baya ta d’an sunkuyar da kanta kafin tace “Mai yasa za mu tafi? Me su Ummin suka ce?” Sai da ya lumshe idanuwanshi ya bud’e kafin yace “Arshaad is morethan comfortable! Infact da farko shi ne ma daa zai tafi saboda yace zaman mu under same roof ba zai yiu ba, sai da na yi masa bayani d’azu akan already daman akwai plan d’in tafiyar ta mu tukunna shi ya yarda zai zauna a nan.” Sai da ta gama jin bayanin nasa tukunna tace “Nifa ba saboda Ya Arshaad bane nace A’a ba.” A hankali yace “mai yasa to ba zaki bini ba?” Cikin tarar numfashinsa tace “Ya Aslam kamata fa yayi mu yi focusing akan yadda zamu warware wannan auren! Kar mu bawa su Abba false hope d’in wata rana za mu so juna..” Ta k’arashe maganar tana jin wani nauyi yana sauk’a daga zuciyarta. Janyo ta kawai taji yayi yai huggging d’inta… Sun d’an jima a haka kafin a hankali yace “Za mu tafi UK next week It’s an order” Shiruu, tayi tana mamakin yadda k’irjinsa yake bugawa da kuma yadda gaba d’aya jikinsa yake karkarwa, gashin sai sake rik’eta yake yi da kyau kamar wanda akace za’a kwace ta. So take ta motsa ta gaya mishi itafa ba inda zata je amman kuma kamar wadda aka rufe waa baki, kwata kwata sai ta kasa. Sun jima a haka suka ji ana knocking...... Mommy, tunda tazo take baza ido, so take kawai taga ta Ina za su fito.. Duk da Aslam yana zuwa kullum wajen ta idan ya tashi a office wani lokacin ma kafin ya fita sai ya je amman so take yi kawai ta gansu especially Hudan… Hak’urinta ne ya k’are dan haka ta cewa Ummi “ta je ta kira mata su, da wurwuri take son tafiya su fito su gaisa kafin ta tafi.” Dariya Daddy yayi yace “A’a Mommy ki dai fad’i gaskiya…y’ay’anki kawai kike son gani. Tun d’azu fa nake ganin ki kinata zullo kina lek’en ta Ina za su fito” Ai kuwa gaba d’aya aka saka dariya banda Mammy da Mom Arshaad kam murmushi kawai yayi. Mik’ewa Ummi tayi zata wuce dai dai nan su Shuraim suka sauk’o… Suite d’insu milk masu asalin tsada sai belt da takalmi brown. Ba k’aramin kyau suka yi ba. Wajenta suka fara zuwa suka yi hugging d’inta! Bata san daliliba kawai sai taji hawaye ya zubo mata. A hankali ta dafa kawunan su ta ce “Allah ya yi muku albarka” Daga nan tayi saurin wucewa dan bataso tayi kuka. Nan suka k’arasa inda Dad Mommy Abba Arshaad Mammy Mom da Daddy suke.. Aka fara hotuna bayan an yi wishing d’insu Happy Birthday kowa ya basu gifts d’in da ya shirya musu. Knocking kawai Ummi tayi ta juya dan ta raba kanta da shiga d’akinsu Aslam ita kam...... Bata yi minti d’aya da zama ba suka fito.. Kowa a parlourn zuba musu ido kawai yayi, ba k’aramin kyau da dacewa da juna suka yi ba. Kallo d’aya Arshaad yayi musu ya d’auke kai da sauri Mammy kam tana ganin fitowarsu ta juya kan ma gaba d’aya ta sake tamke fuska. Ba yadda Hudan bata yi da shi akan ya saki mata hannu ba amman fur!! Ya k’i. Haka nan duk sai taji kunya ta lullub’eta especially da suka had’a ido da Mommy wadda take ta zuba murmushi kamar an mata albishir da gidan aljannah… Suna k’arasowa ta mik’e ta kamo hannun Hudan ta fara k’ok’arin janta dan ta zaunar da ita a gefenta. D’agowa tayi suka had’a ido da Aslam! Sai da ta d’anyi dariya tukunna tace “Cikata mana, ko?” Shima kuma sai yaji kunyar Abba da su Dad ta rufeshi dan haka a hankali ya cikata ta zaunar da ita itama ta zauna Aslam ya zauna a gefnta Tun kafin ta fad’a Shuraim ya shiga yi musu hotuna… Abba da Dadddy da Dad ma suka shiga, haka ma Ummi. Ranar dai anshan hotuna kala kala bibbiyu uku uku, daga nan su Shuraim suka fita saboda friends d’insu duk suna waje. Sai wajen 9 su Sakina suka zo, murna a wajen Hudan ba a magana. Suna gama gaisawa da su Abba suka fita compound suka nemi waje suka zauna. Basu dad’e da zama ba aka fara gudanar da program of event. Suna cikin hira su biyu dan Sumayya har ta yi k’awa wata Khairat sun ja gefe anata iyayi da manyance, suka ji an jawo kujera an jona da table d’insu an zauna a gefen su. Tana d’agowa suka had’a ido a take gabanta yayi wani irin mahaukacin fad’uwa! So take ta cire idanunta a nashi amman ta kasa….. “You came.” Yace yana mai kallon cikin idonta. A hankali tace “Yes” Sai kuma ta mik’e da sauri tace “Hudan muje ki rakani bathroom” Tana mik’ewa ta yi gaba….. Da sauri ya kalli Hudan yace mata “A minute please” Sannan ya mik’e ya bi bayan Sakina wadda tayi hanyar falon su Hudan da sauri. Kwarewa Mammy ta yi, da sauri ta kamo hannun Mom! Tana juyowa ta nuna mata su, tace “Kinga Auwal da Cousin d’in Huda wadda suka zo d’azu Hudan take ta murna d’innan.” Babu abunda yafi d’aga musu hankali irin yadda Auwal yake kiranta yana d’an gudu amman ko alamun zata juyo ma bata yi ba... Tana shiga shima yana shiga! Sai a lokacin ta lura da Huda bata biyo su ba. Da sauri ta had’e hannuwanta biyu waje guda alamun rok’o, tace “Dan girman Allah Ya Auwal ka rabu da ni! Ka fita a harka ta. Me kake so in yi maka? An saka ranar aurena! Nan da 5 month in sha Allah Ina gidan wani me kuma zaka ce min yanzun me kake buk’ata a....” Maganarta ce ta katse sakamokon hawayen da ta ga sun tsinke masa lokaci guda kamar fanfo sai kace wani k’aramin Yaro. A hankali ya durk’usa a gabanta ya had’e hannuwanshi duka biyu shima, yace “Sakina dan girman Allah ki san yadda za kiyi da ni! Wallahi ban san halinda nake ciki ba, ba laifina bane ba, na san na takura ki da yawa amman ba laifina bane ya kamata ki gane. Ya kike so in yi? Wallahi na yi na yi In cire ki a raina amman kullum sonki da k’aunarki k’aruwa kawai suke yi! Ki taimaka kar ki auri wani wallahi zan iya mutuwa. Na ji zan baki time zan baki space amman kar ki auri wani na dan girman Allah. Sannan ki san yadda za kiyi da ni, ki yi min abunda zan ji kin fita a raina. In kikayi min haka kin gama min komai. Na san ba a neman aure cikin aure amman na kasa hak’ura da ke! Ba zan iya ba ki san yadda za ki yi dani dan Allah. I know I’m not making any sense here I can’t loose you kuma tunda kince bakya so na i can’t force you to love me so I can’t love you saboda ni happiness d’inki shine abunda nake so amman fa kar ki ce za ki auri wani. Wallahi rabona da bacci tun shekaran jiya! Inaga haukacewa zan yi, bana gane komai bana gane kowa sai ke! Ki fita a raina sai in barki Ki fita a zuciyata sai in...........” Kukan da ya taho mishi fiye da na farkon da yake yi ne ya sanya ya kasa ci gaba da magana. Ita kanta Sakina kukan da take ta k’ok’arin rik’ewa ne ya samu nasarar kufce mata. “Innalillahi wa innailaihirrajiun!!” Suka ji muryar Mom da Mammy a bayansu har da wata k’awar su, suna salati suna tafi. Da sauri Sakina ta share hawayenta ta d’an matsa saboda Auwal d’in ya tashi ya basu damar shigowa amman ko gezau bai yi ba. Wani kallon tsana Mom take watsa mata, kafin cikin tsananin b’acin rai tace “Yanzu ku jinin Madu ashe ba zaku tab’a jin tsoron Allah ba? A haka za ku k’are? Wato Maryam ta yi shine kema zaki biyo ki haukatamin d’a?? To billahilazim na fi k’arfinki! Duk surk’ullen da kika je kika yi ki koma ki je ki wargaza tun kafin In tashi biyowa ta kanki!. Saboda Allah Mammy ku kalli yadda Yarinyar nan ta maida Auwal! Auwal fa!!! Wai yau shine a gaban mace yake kuka haka wiwi da hawaye kamar wani sakare? Wallahi Allah sai yayi mana hisabi da mu da family d’in Madu ranar gobe k’iyama. Wanne irin jarababben abu ne yake yawo a jininku sai kace mayu?” Tayi maganar tana kallon Sakina cikeda tsana wadda itanma ta zuba mata nata dara daran idanuwan da suka rine sukai jaa. Za tayi magana kenan Auwal ya mik’e da kyar ya juya gareta yace “Haba Mom, abubuwan da suke kai na already sun yi yawa Dan Allah kar ki zo kiyi haka kar ki saka ta k’ini completely! Ki koma waje dan girman Allah Magana muke yi, maganar da ta shafemu iya mu biyu tak! Ba wanda ya gayyotoki ke da k’awayen ki nan” Ya k’arashe maganar tari yana kufce masa…” A rikice tace “Auwal na rantse da Allah zan yi maka abunda baka tab’a zato ba! Karankatakaf fad’in duniya ace ka rasa macen da za ka so sai jinin Maryam Jikar Madu da Shuwa? Kasan su waye su kuwa?” Kuka kawai Sakina ta saka ta fara ja da baya… Da sauri Auwal ya juya ya fara binta yana magana yana tari “Ki tsaya.. Don’t mind her.. let’s talk.. Dan Allah.. Sai a sannan Mom ta samu damar shigowa ita da su Mammy. Kamar ma tangad’i Auwal d’in yake yi dan haka suka samu suka wuceshi suka yi kan Sakina! Mom tana zuwa, ta shak’ota tace “You must mind me! In dai kina da hankali kuma kin san darajar uwa a wajen d’anta to ki sani ba zan tab’a barin Auwal ya aurenki ba wallahi! Dan haka ki hak’ura. Ina fatan Huda ta zame miki lesson a rayuwa…..amma idan mahaukaciya ce ke to ki so Auwal ki aureshi dan Allah, wallahi nayi miki alk’awarin sai na lahira ya fiki kwanciyar hankali” Tana gama fad’in haka tayi cilli da ita wanda har ya kaita ga kaiwa k’asa. Kasa motsi Auwal yayi dan zuwa yanzu ya fara ganin dishi dishi, tabbas ya san halaiyyarsa da kuma Granpa su suka hana Sakina yarda ta auresa amma ya san tana sonshi wanda hakan ne ma yasa ta sanya aka kawo kud’in aurenta da wuri! Duk ya fahimci hakan. Yanzu kuma ga Mom! Ya tabbatar ta gama wargaza masa d’an guntun chance d’in da yake hangowa…. Duk da baya ganinta amman yana iya jiyo setin inda take kuka, dan haka ya fara yunk’urin d’aga k’afarsa domin ya k’arasa wajenta. Yana motsawa kuwa kamar jira ake jiri yace bismillah! Gaba d’aya ganinshi ya d’auke in banda duhu babu abunda yake gani, ga wani mahaukacin juyawa da kanshi yake yi…… Da sauri yasa hannu ya dafe kan nashi yace “wash!!” Da d’an k’arfi. Sai a lokacin hankalin Mom da Mammy da k’awar tasu waenda suka k’arasa suka cigaba da tsigale Sakina suna kiranta da ‘talaka, kwadayayyiya’ Ya koma kan Auwal. Da sauri Mom ta nufesa ganin yana shirin zubewa k’asa amman kafin ta k’arasa har ya fad’i k’asa sumamme.. Dede nan su Daddy Abba da Ummi suka shigo dan dama Ummi kamar ta d’an jiyo hayaniya sama sama… Ba karamin tsorata Mom tayi ba ganin Auwal a k’asa kamar matacce. A haukace ta juya ta koma kan Sakina da take nan durk’ushe tana kuka, ta sake shak’ota ta mik’ar tsaye ta hau magana kamar tab’b’abb’iya “Waenna irin mutane ne ku? Baku da tausayi ne? Dolene sai an so ku? Wallahi na rantse da Allah ko a Birnin sin kika yi mishi asiri yau sai mun je yanzu ba sai gobe ba kin warware shi.” Ta fad’i haka tana k’ok’arin fara janta. Sakina kam banda tari ba abunda take yi gaba d’aya ta fice a haiyyacinta dan ba k’aramar shak’a Mom tayi mata ba. “Adama!!!!” Suka ji muryar Dad cikin tsawa a bayansu. Juyawa Mammy da k’awar tasu suka yi ita kuma Mom ta cika wuyan Sakina ta durk’ushe a wajen ta fashe da kuka. Dede nan Aslam da Huda suka shigo! Da gudu Hudan ta k’arasa inda Sakina take… Cikin tsananin b’acin rai Daddy ya k’arasa inda suke ya d’agota ya fara magana “Baki da hankali ne? Me yake damunki? Wachche irin kwakwalwa ce da ku ne wai? She’s our guest for crying out loud!! Ga babanta chan a waje ya dawo d’aukar su a haka kikeso a fitar mishi da ita ko yaya?” Cikin kuka Mom tace Kallafa Auwal” Ta nuna masa Auwal wanda Abba da Aslam suka ciccib’a za su fitar, cikin kukan taci gaba da magana “Asiri tayi mishi Irin wanda Maryam ta yiwa Abba bani da tantama! Daddy a k’asa fa nazo na tarar da Auwal durk’ushe gaban wannan k’ask’antacciyar yana rok’onta ta soshi ta aureshi yana kuka kamar k’aramin Yaro In ba aikin asiri ba tayaya zaka yi tunanin Auwal zai so wannan k’ask’antacciyar?” Tayi maganar tana nuna Sakina a wulak’ance. “Tayaya aka yi na so ki har na aureki?” Muryar Daddy ta katse mata maganar da ta yunk’uro za ta ci gaba. Da sauri ta juyo tana kallonshi cike da shock! Cikin tsanannin b’acin rai yace “Adama na gaji na gaji da rashin tunanin ki da shirmen ki da son zuciyarki! Na gaji wallahi.. Tsabar idonki ya rufe daga ganin gaskiya you don’t even realize the fact that Auwal ya nutsu tunda ya had’u da Yarinyar nan. Kar ki bari In chanza miki wallahi ba zaki ji dad’ina ba dan kin kaini bango!.” Ya k’arashe maganar cikin tsananin fushi. Dede nan Aslam wanda ya dawo daga kai Auwal ya dafa Daddy yace “Daddy dan Allah ka yi hak’uri.” A hankali Arshaad wanda ya shigo yanzun shima ya k’araso inda suke yace “Akwai mutane a gidan Daddy, Abba kai yake jira ku kai Auwal asibiti suna mota.” Kallon Mom yayi wadda ta k’ame tun lokacin da ya fara magana.. Kamar zai ce mata wani abun sai kuma kawai yayi tsaki ya juya ya fita ranshi a mugun b’ace. Yana fita Mammy ta k’araso ta dafa ta tace “Zo mu je” Daga nan ta ja hannunta suka nufi wani d’akin a nan k’asan ita da k’awarta.. Suna shiga kamar jira Mom take ta fashe da kuka tace “Akan Yarinyar chan Daddy ya gaya min wannan maganar?? Waenna irin mutanene su Maryam wai ni Adama…” Cikin katseta Mammy tace “Saboda haka baki ga ta zama ba! Ko kuma ince ba muga ta zama ba har sai mun cire ta a zuciyar auwal!. Sannan akwai wani abunda ya faru na tashin hankali d’azun nan nima na gani amman kar ki damu dama na gama tsara mana mafita tun kafin in zo Sannan itama wannan sai mun yi da gaske tukunna zamu cireta a rayuwar Auwal. Da sauri Mom tace “Kina ganin ciretan zai yiu? Kina gani fa Arshaad bake kad’ai ba har ni d’innan gaba yake yi da ni. In ba asirin aka karya ba ba zamu samu sukuni ba.” Ajiyar zuciya Mammy ta sauk’e kafin tace “Adama Allah ya jefomu cikin wasu kalar family masu zuciya mai naci dan haka sai mun yi da gaske saboda su na fahimci weakness d’insu mace ce! Ki duba kiga har shi kanshi Granpa d’in duk abun shi kina ga yana yiwa matarsa?” Cikin kuka Mom tace “Kullum addua ta d’aya kar Auwal ya fad’a kaidin mace kamar iyayensa sai gashi rana d’aya ya fad’a, ni Adama ya zan yi? Shi kad’ai gareni! Ita kad’ai fa yake gani ko maida hankali kwana biyun nan na lura ba yayi akan aiki ashe ita ce sila! Kiji Daddy tsabar rashin sanin ciwon kai wai har da ik’irarin Auwal ya nutsu! Shi a ganinshi nutsuwa ce wannan an haukatamin kwakwalwar d’a amma shi yana ik’irarin ya nutsu…” Ta k’arashe maganar tana durk’ushewa a wajen. A hankali Mammy ta k’arasa ta hau lalalshinta, sai da taga tayi shiru tukunna ta matsar da bakinta dede kunnenta ta shiga rad’a mata waensu maganganu. Aslam da Hudan ne suka raka su Sakina har bakin mota bayan sun lallasheta ta yi shiru da kyar! Har da Arshaad. Sanann suka tsaya suka kira Sumayya a wajen k’awarta suka wuce tare. Hudan maganganu ne fal a ranta take so tayi da Sakina amman ganin halin da take ciki kawai yasa suka yi musu godiya ta bari akan In komai ya lafa za suyi chatting. A parlourn suka tarar da Mom Mommy da Mammy da Ummi Dad ya had’asu gaba d’aya da alamun fad’a yake yi musu. Suna shiga Aslam ya cewa Hudan “taje ta had’o masa Coffee mai zafi please” Daga nan ya wuce ciki bayan ta amsa masa da “to” ita kuma ta nufi kitchen d’in direct. Arshaad ma ya wuce d’akinsa. Arshaad yana shiga d’akinsa Mammy ta mik’e ta nufi d’akin dan they have to talk, ta lura in ta biye shi gaba zai yi da ita. D’azu sau biyu tana zuwa d’akin nasa bata sameshi ba. Tana shiga su Dad suka gama zaman nasu suma aka mik’e kowa ya kama gabansa. Ta gama had’awa kenan ta d’auko flask za ta juye wayarta ta fara k’ara! Tana dubawa taga sunan Sakina dan haka tayi saurin amsawa ta kara a kunnenta. Ko sallamarta Sakinar bata amsa ba tace “Hudan d’anyi sauri ki fito kinga akwai sak’on da zan baki ashe na manta.” “Ok” Hudan tace sannan ta kashe wayar ta ajjiye flask d’in ta rufe had’in nata ta fita. Tana fita wani mutum ko wata mata ta/ya shigo ta k’ofar baya sanye cikin bak’ak’en kaya kamar irin na leda d’innan na tare ruwa an rufa har hular saman fuska. Ta chan ciki a fuskar da mask bak’ik’irin, baka ganin komai hatta idanuwan a rufe suke da bak’in glass. Tafin hannu da k’afa kuma duk da bak’ak’en socks….. Wani ruwa aka zaro a cikin syring aka bud’e had’in coffe d’in da Hudan ta gama had’awa aka b’alle kan syringing kamar za a matsa sai kuma aka tsaya aka yi shiruuu! Da alama mutumin ko matar is having second thoughts. Ahankali aka ja wani d’an siririn tsaki aka mayar da murfin aka rufe aka ajjiye syringing a gefe kamar ana tunani… Motsin mutum ya ji ko ta ji dan haka aka yi saurin d’agowa ana kallon k’ofar bayan ta inda aka shigo ai kuwa aka ci sa’ar ganin giftawar inuwar mutum! Lalle kuwa ko waye ya gifta to ta/ya san ya ganshi ko ya ganta! Dan haka da sauri aka bud’e k’ofar bayan aka bi Inuwar da aka gani amman ko da wasa babu alamar mutum a wajen… Har bayan compound sai da ya/ta zazzagaya amman ba kowa. Ya/ta dad’e a tsaye tana/yana tunani kafin chan ya/ta nufi hanyar kitchen d’in da niyyyar d’auke syringing da ta/ya manta akan kanter kitchen d’in kusa da tray da coffe d’in da ya/ta had’a. Tana/yana zuwa tayi/yayi saurin ja da baya sakamokon hango Huda da Ummi a cikin kitchen d’in! Hudan tana juye coffe d’in a cikin flask Ummi kuma ga wani abu a hannunta tana sha suna d’an hira.......... BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 64 Mikiya Writers Association. Da d’an saurinta ta fita ta nufi gate saboda ta ji Sakina tace mata ‘ta yi sauri’ Kuma ta ji muryarta dishi dishi sannan kamar maa fa ba muryar Sakinar ta ji ba! Gidan ba kowa shiruu, bak’in duk an watse kasancewar kowa da motarsa yazo wasu kuma drivers ne suka kawosu suka tsaya suka jira su shiyasa ana gamawa kowa ya kama gabanshi. Sai da ta kusan kaiwa gate tukunna ta danna kiran Sakina. Bugu uku ana hud’un ta d’auka, tana d’auka Hudan tace “In fito ko za ki shigo?” Da mamaki Sakina ta zare wayar daga kunnenta ta kalli sunan sanann ta mayar tace “Ki fito Ina? Ina zan shigo?” Turuss! Haka Hudan taja ta tsaya itama ta zaro wayar ta kalli sunan kafin ta mayar tace “Sak’on fa da kika ce za ki bani?” Cikin rashin fahimta Sakina tace “Wanne sak’o?” Ahankali Hudan ta sauk’e ajiyara zuciya tace “Dan Allah Sakina bar wasa, yanzun nan ki ka kirani kika ce in fito kin manta sak’o in zo in karb’a da sauri…” Cikin katseta a d’an firgice Sakina tace “Hudan yi sauri ki koma gida maza maza yanzun nan! Inaga kidnappers ne suka yi hacking wayata sun ga yau kuna taro. Yi maza ki koma ciki da sauri kar ki sake fitowa.” Da sauri kuwa Hudan ta juya k’irjinta yana dukan uku uku! Har da d’an gudu ta shiga had’awa da shi. Parlourn ba kowa shiruu, nan ma duk an watse…. Haka nan ta wuce kitchen d’in jikinta yana karkarwa tana salati. Tana shiga taga kamar an fita ta k’ofar baya! Dan haka tsoronta ya sake nunkuwa. A hankali ta shiga takawa tana kallon k’ofar da aka bi aka fitan dan gani take yi kamar har yanzu ana tsaye jikin k’ofar ba a matsa ba! “Huda” Ummi wadda ta shigo yanzu taga tana sand’a ta kira sunanta. A mugun tsorace tace “wayyo Allah!!” Sai kuma ta juyo jikinta yana karkarwa. Dariya Ummi tayi kafin tace “Matsoraciya!!! Ai kuwa gara tun wuri ki yakice wannan tsoron saboda gidan da za ku zauna a UK inaga ya kusa rabin wannan… D’azun Dad yake gaya mana Granpa although yana fushi da Aslam akan ki amman ya kasa jurar fushin da yaji labarin zaku koma UK ya bashi kyautar gida da mota a chan. A hankali ta kalleta kamar za tayi magani sai kuma ta sunkuyar da kai kawai kafin ta juya ta nufi inda ta ajjiye had’in coffee d’in Aslam. Murmushi Ummi tayi, ganin kamar Hudan bata son maganar yasa itama ta kawar da zancen ta hanyar cewa “Yauwa coffe d’innan na biyo! Gaba d’aya drinks d’in nasu na yau zak’iii sosai kaina har sarawa yake yi idan nayi sipping. Allah yasa baki saka sugar da yawa a wannan ba, bana son sake saka wani abu mai sugar sosai a baki na.” A hankali Hudan wadda duk jikinta yayi sanyi daga fitarta zuwa yanzu tace “Eh. Naga kamar shima baya so sosai shiyasa dama zan ajjiye mishi a gefen tray d’in in yana so sai ya k’ara. Murmushi Ummi tayi sannan tace “To za a zuba min inshaa ne ko sai na jira an fara kai mishi ya d’iba?” Ta k’arashe tambayar cikin sigar tsokana. Murmushi mai had’e da y’ar dariya Hudan tayi kafin tace “Haba Ummi” Tana mai juyawa ta d’auko cup mai d’an girma, ta dawo ta hau tsiyaya mata. Sai da ta kusan cika kofin tukunna Ummin tace “Okay tam ya isa haka na gode dota, Amaryar Aslam.” Sunkuyar da kai Hudan tayi…Ta lura Ummi so take sai taga ta saka ta tayi walwala shiyasa kawai ta d’an sake suka hau hirar yadda birthday d’in ya kasance, suna hirar tana juye coffe d’in a cikin flask…….. Ummin kuwa daman hakan take so dan ita kunyar Hudan ma take ji akan abunda aka yiwa Sakina yau gashi saboda su Shuraim takanas ta zo shiyasa ta dinga janta da wasa har sai da taga ta d’an sake tukunna ta shirya bata hak’uri akan abunda ya farun! A lokacin Huda har ta juye ta had’a tray ta d’aura cup da spoon da sugar tana shirin d’auka Ummi tace “Amm Huda iwant to apol....” Kamar an mak’ale ta haka maganar tata ta tsaya cak! Da sauri Hudan ta ajjiye tray d’in ta nufeta saboda yadda tana juyawa taga Ummin ta damk’i wuyanta kamar zata shak’e kanta sannan ta runtse idanuwanta. Da kyar Ummi ta iya cewa “ya subahanallah!” Sai kuma ta zube a wajen ta fara tari….. “Innalillahi wa innailaihirrajiun” Hudan ta ambata a firgice da k’arfi! Sakamokon ganin jini yana fitowa daga bakin Ummi wadda take nan k’asan tiles d’in kitchen d’in kwance tanata tari. Da sauri ta durk’usa ta hau jijjigata tana “Ummi! Ummi!! Ummiii!!! Abbaaa! ya Aslam! Ya Arshaad! Ummi ki tashi..” Kuka take tana ihu tun k’arfin ta dan tun lokacin da ta durk’usa akan Ummin ta ga ta daina motsi sannan jikinta ya sake. Da gudu ta mik’e ta nufi k’ofa da niyyar fita ta kira jama’a azo a kai Ummi asibiti… Tana gudu tana juyowa tana kallon Ummi bata yi auni ba taji ta fad’a jikin mutum! Da sauri ta d’ago tana kallon Arshaad wanda shima ita d’in yake kallo bakinsa yana d’an rawa da alamun magana yake son yi amman ya kasa. Cikin kuka ta hau juyawa tana nuna mishi Ummi wadda ke nan kwance a k’asa kan tiles! Sannan ta juya da gudu ta nufi Ummin tana cewa “Harda jini! Tama daina motsi” tana mugun kuka. Da kyar Arshaad wanda gaba d’aya ilahirin jikinsa ya d’au karkarwa tun lokacin da ya ga Ummin nan kwance, ya taka ya k’arasa inda Hudan da Ummin suke. Da sauri ya durk’usa a wajen a mugun rikice yace “Innalillahi wa innailaihirrajiun” Kawai kuma sai hawaye ya biyo ta idanunsa. Da sauri Hudan tace “Ya Arshaad dan Allah kar ka ce ta mutu! Wallahi bata mutu ba! Bata mutu ba!! Ka kaita asibiti zata farfad’o. Dan Allah ka kaita asibiti.. Ummi ki tashi! Abbbbbaaaa!!!” Ta sake kwala kiran Abba dan taga Arshaad d’in yak’i motsi kwata kwata so ba lalle ya iya tab’uka komai ba, da alamun ya yi mugun firgita da ganin Ummin. A rikice Aslam ya afko cikin kitchen d’in sanye da bathrobe a jikinsa da alamun ma bai gama wankan ba dan har da y’ar kumfa a gefen kumatunsa. Ganin Ummi yasa shima ya k’araso ciki da mugun gudu ya durk’usa a inda suke dai dai nan su Shuraim suma suka k’araso cikin kitchen d’in. Sai ga Mom itama ta shigo tana cewa “Ife ifen me nake ta ji ne wai hak……?” Muryarta ce ta katse sakamokon kitchen d’in da taga cike da jama a a nata ihu ana kuka! Dan su Shuraim suma suna shiga suka yi kanta sukai joining Hudan a kukan. Da sauri ta k’arasa tana cewa “waye ba lafiya ne mai ya far..” Maganarta ce ta katse sakamokon had’a ido da tayi da Aslam! Sanye cikin bathrobe… Da mamaki take kallonsa har da y’ar kunfar sa a gefen fuska, har zata yi masa maganar fitowar dayayi half naked dan bathrobe d’in bata da wani tsayi sosai sai kuma kawai ta shareshi dan jin dalilin kukan da take ji ne priority yanzun. D’auke kanta tayi ta maida inda su Hudan suke durk’ushe…. Dishi dishi ta fara gani sakamokon Ummi da ta gani kwance bakinta duk jini! A hankali jikinta na mugun karkarwa tace “Innalillahi wa innailaihirrajiun” Sai kuma ta tafi luuuuuuu ta sume a wajen… Sudais da Shuraim ne suka fara k’ok’arin ciccib’ar Ummi dan haka Hudan ma ta sa hannu suka d’auketa. Aslam yana ganin haka ya bisu a baya duk ya rikice… Da gudu ya wuce su ya shiga d’aki ya d’auko mukullin motarsa ya mik’awa Huda yace “su jira sa” Sannan ya koma ya zura jallabiya mai kauri daman already ya saka boxes a k’asan bathrobe d’in! Ya fito ya bi bayansu. Yana zuwa ya kunna motar already sun gama shiga suka yi gaba kowa hankalinsa a tashe sai kuka su Hudan suke yi. Da kyar Arshaad ya iya mik’ewa ya d’auko ruwa a fridge ya shiga yayyafawa Mom…… Har ya d’an fara tsorata dan da farko k’in farkawa ta yi, kafin daga baya kuma ta farka a firgice tana salati sai kuma ta tashi ta zauna ta fashe da kuka! Kallon inda taga Ummi d’azun tayi ganin ba kowa sai d’an ragowar jini jinin da aya zuba a k’asa ne yasa a rikice ta juyo tana kallon Arshaad kafin tace “Tana Ina?” Bai ce mata k’ala ba! Dan kanshi a mugun d’aure yake ‘jini, Ummi, how?’ Sune abubuwan da suka taru suka hautsina mishi kwakwalwa. Mik’ewa kawai yayi ya wuce d’akinsa ya d’auko key ya cire rigar suite d’in jikinsa ya rage daga long sleeve sai dogon wando da belt, ya fito ko cover shoe d’in k’afarsa bai tsaya chanjawa ba. A parlourn ya tarar da Mom tanata faman safa da marwa Yanzun ma bai kulata ba ya wuce ita kuma ta bi bayanshi da sauri suka fice. Sai da suka shiga motar ya kunna tukunna ya kira Aslam. Shuraim ne ya d’auka, nan yake tambayarsu “suna Ina?” Cikin kuka yace “Basu riga sun k’arasa asibiti ba amman duk wanda suka samu mai kyau nearby nan za su je” Ajiyar zuciya Arshaad ya sauk’e daga nan ya katse kiran ya tada motar ya fice daga gidan. Driving kawai ya hau yi towards asibitin da ya san yana a kusa dasu mai kyau…. Kamar had’in baki kuwa yana shiga ya hango motar Aslam nurses suna d’aura Ummi a akan gado. Yana k’arasawa yayi parking suma suka fito suka d’unguma gaba d’ayansu suka rufa musu baya. Da kyar aka iya tsayar da su Shuraim da Hudan daga shiga investigation room d’in…haka nan suka dawo in banda kuka ba abunda suke yi. Da sauri Mom ta k’arasa ta jawo Sudais da Shuraim ta rungumesu itama tana kuka. A hankali Aslam ya k’arasa inda Hudan take tsaye tana kuka, ya juyo da ita ya rungumeta a hankali ya shiga bubbuga bayanta. Da sauri Arshaad ya tashi ya fita a wajen waya kare a kunnensa. Dad, yana amsa wayar ya fad’a masa halin da ake ciki daga nan ya nemi waje ya zauna a harabar asibitin.. BAYAN MINTUNA TALATIN. Cirko cirko haka kowa yake tsaye sun cika wajen Dad Daddy Aslam Abba Mom Mammy Gramma Mommy Arshaad Sudais Shuraim da Hudan! Kowa ka ganshi ka san hankalinsa a tashe yake dan ko zama ba wanda ya iya yi. K’arar bud’e k’ofar inda aka shiga da ita suka ji, dan haka duk suka juya suka zubawa Likitan da ya fito ido. Yana kallonsu ya yi saurin sunkuyar da kanshi kafin ya zare glasses d’insa yad’an murza idanunsa sannan ya mayar ya d’ago ya kalli Aslam yace masa “follow me” A hankali ya zame hannunsa a cikin na Hudan ya bi bayan Likitan.. BAYAN MINTUNA BIYAR. A hankali Aslam ya bud’e k’ofar office d’in ya fito, kamar wanda aka zarewa laakka a jiki haka yake taku, sai da ya kusan k’arasawa corner da in ya shiga zai gansu tukunna ya zaro wayarsa ya danna kiran Granpa! Yana karyo kwana suka yo kanshi gaba d’ayansu suka hau tambayarsa…. Kallonsu kawai yake yi da waya kare a kunnensa, sai ya bud’e baki kamar zai yi magana sai kuma ya kasa. Jijiyoyin kansa sun yi rud’u rud’u! Gashi idanuwansa sun kad’a sun yi jaaa! Wanda hakan ba k’aramin sake gigita ahalin yayi ba. Sai da wayar ta kusan katsewa tukunna Granpa ya d’auka! Jin shiru yasa yace “Talk to me Aslam” A hankali bakinsa na rawa yace “Granpa, its Ummi! Incase you have something to say to her… Likita yace she has less than 1 hour.” “Innalillahi wa innailaihirrajiun” Shine abunda kowa ya hau maimaiitawa a zuciyarsa dan k’amewa k’am! Gaba d’ayansu suka yi kamar an d’auke musu numfashi haka wajen yayi tsit!. A hankali kukan Gramma ya fara tashi followed by na Mom da Mommy sai su Sudais da Huda… Tashi d’aya kuma sai wajen ya hautsine! Masu hawaye nayi masu kururuwar kuka ma suna yi. Da kyar Abba ya iya k’arasawa ya dafa Aslam yace “What happened to her?” Jikinsa yana mugun karkarwa. A hankali da kyar ya iya cewa “poision ta sha! Ya tsinkamata gaba d’aya hanjinta The Soctors where even shocked! Ta yadda take numfashi har yanzu.” A rikice Abba yace “Poison kuma? How? A ina? Wa ya bata poision?” D’agowa yayi ya na kallon Hudan yana son tambayar ta ‘ya aka yi?’ Ganin yadda gaba d’aya hankalin jama’ar wajen ya koma kanta ne ya sa kawai ya d’auke kai. A hankali yace “Ihun Hudan kawai na ji, ina zuwa na ganta tana tarin jini. Ba mu san a ina ta sha ba.” Da sauri Mammy ta matso tana matsar hawaye tace “Ta ya zaka ce baka san a ina ta sha ba!? Ga wadda za ku tambaya nan?” Tayi maganar tana nuna Hudan. Cikin karkarwar jiki Hudan tace “Ban san a ina ta sha ba” Dasauri cikin katseta tace “Ai tare kuke! Dan haka dole kinga ta sha wani abun.” Cikin rashin fahimta Hudan tace “Ina cikin had’awa Ya Aslam coffe ta zo tace zata sha, sai na zuba mata a cup That was the only thing da naga ta sha daganan ta fara tar..........” Shiruuu, tayi ta kasa k’arasawa sai kuma a rikice ta d’ago tana kallon Mammy wadda ita ma itan take kallo kafin ta matso kusa da ita tace “Hudan we all know ba kya k’aunar Aslam!!! Da kika zo kashe shi kika san kin yi poisioning coffe d’insa! Me ye laifin Ummi da zaki had’a har da ita ki bari ta sha?” Cikin tsananin tashin hankali Hudan take kallonta zata yi magana Mammyn ta katse ta ta hanyar sake cewa “Ko jifan tsuntsu biyu kike son yi da dutse d’aya? Because it’s obvious yanzu babu abunda zai sake shiga tsakanin Maryam da Abba!” Wani kalar kuka da Hudan take yi sai da ta kusan shid’ewa! Zata yi magana Mammy ta sake cewa “Wachche irin zuciya ce da ke Hudan? Na tabbatar idan kika rok’i Aslam kika ce ya sakeki tsaf z........” Da mugun k’arfi Aslam wanda ya zo iya wuya yace “Mammy!!!” Wanda gaba d’ayansu sai da suka razana! Kowa ya d’auke wuta…….. A hankali Abba wanda tun lokacin da Mammy ta fara magana ya runtse idanuwan ya bud’e ya kamo hannun Aslam yace “Za a iya ganinta ko?” Sai da ya d’an dedeta kansa tukunna yace “Eh” ba tare da ya kalleshi ba dan wani kalar kallon kallo suke yiwa juna shi da Mammy wanda da ace Mammyn ta san kallon da Aslam d’in yake yi mata to daa ba zata yarda ta bar kwayar idanunta a cikin nasa ba. D’akin da aka shiga da ita sanda aka kawota nan Abba ya shiga dan basu ga lokacin da aka fito da ita ba. Sai a sannan Mommy ta matso ta jaa hannun Aslam suka fice daga wajen gaba d’aya. Suna fita Mammy ta sake juyowa kan Hudan a karo na biyu tace “Yau wallahi mai kwatar ki a hannuna sai Allah, kin san ya Ummi take a wajena kuwa......” Banda kallon Mammy ba abunda Mom take yi tana wani irin kuka, so take tayi magana amman ta ma kasa. Cikin fushi Mammy ta yi kan Huda kamar zata shak’ota. Damk’ar hannunta d’in da Dad yayi ne ya sa ta juyo tana kallonsa! Ba tare da ya kalleta ba ya jaa hannunta da mugun k’arfi ya fita da ita…… Sai da ya sakata a mota ya cewa driver ya maida ta gida tukunna ya juya ya koma ciki ba tare da ya bi takan bak’ak’en maganganun da take jefa mishi ba. Mammy kamar zata mutu haka ta ji, wato bashi da time d’in da zai yi mata magana sai in zai wulak’antata sannan a gaban mutane ko kuma in ba su kad’ai bane to ya kan kulata. Gashi yanzu Arshaad shima ya fara, tsabar wulak’anci ga ta ga shi amman iya gaisuwace kawai take shiga tsakaninsu, d’azu taje d’akinsa har sau biyu baya nan a na ukun kuwa da tayi sa a yana nan tana shiga ya mik’e ya fita ya barta kamar ba uwar da ta tsugunna ta haifesa ba, bama fa ta san ya dawo ba sai a gidan kawai ta ganshi! Takaici da b’acin rai kamar ta d’aura hannu aka tayi ta kurma ihu........ A kwance ya ganta da oxygen da wasu na’urori tana janyo numfashi da kyar! A hankali ya k’arasa wajen ya tsaya a dede kanta yace “Ummi” Sai kuma wasu zafafan hawaye suka shiga sintiri a kan kyakkyawar fuskarshi. A hankali ta shiga bud’e idanunta… Tun tana ganinsa dishi dishi har ta d’an fara ganinsa sosai dan haka ta fara k’ok’arin mik’ewa. Da sauri yace “Nooo.. Stay still” Sai kuma ya juya ya janyo wani stool ya zauna a kai ya kama hannunta ya rik’e. A hankali ta d’an jaa oxygen d’in k’asa, tace “Naji Likitan yana cewa poision na sha ko? Wai hanjina sun tsitstsinke.” A hankali Abba ya kawar da kansa yayi amfani da free hand d’insa ya share hawayen fuskarsa kafin ya juyo yace “You are going to be okay” Murmushi ta yi a hankali tace “K’arya fa ba halin ka bane Abba” This time around kuka ne ya kufce masa… A hankali ya kamo hannunta ya d’ago ya kai setin bakinsa yayi kissing hannun cikin kuka yace “Ki yi hak’uri Ummi. Dan Allah ki yi hak’uri. Na nuna miki k’iyayya, ni kaina naji ina jin haushin kaina ballantana ke.” Murmushi tayi a hankali tace “Ko sau d’aya ban tab’a jin haushin abunda kake min ba Abba remember tun muna Yara na sha gaya maka ‘ko menene idan kayi burgeni yake yi’ dan haka kar kayi tunanin na rik’e ka a zuciyata! Zuciyata iya kar k’aunarka da tsananin son ka ta sani bata san wani abu akasa sin haka ba” Ta k’arashe maganar tana d’an murmushi. Kuka ne sosai ya kufcewa Abba. A hankali take d’an matsar hannunsa wanda yake rik’e da nata tace “Good bye Abba, ka kulamin da su Shuraim dan Allah, har da Hudata itama ka cigaba da kula min da y’ay’ana.” Cikin tsananin kuka yace “Ummi ki yi shiru.. Fad’ar Likita ba fad’ar Ubangiji bace ba. Ki yi shiru da waennan maganganun dan Allah.” A hankali tace “Lokacina yayi! Tun ba yau ba na fara jin hakan a jikina.” Shiruu ta d’anyi kafin ta lumshe idanunta ta bud’e a hankali tana ganin dishi dishi tace “Ina takaicin Ba zaka dinga tunani a matsayin masoyiyarka ba bayan raina! Sai dai a matsayin wadda ta sanya rayuwarka a k’unci ta saka ka tunani da bak’in ciki. Da ace za a bani chance d’in da zan iya komawa farko to da na fita a rayuwarka kayi farin ciki daga farkonta har k’arshe.” Cikin katseta yace “Ummi mun wuce wannan wajen, na fad’a miki na riga na yafe miki na manta da komai. Ba zan tab’a tunoki a matsayin wadda ta sanya rayuwata k’unci ba sai a matsayin ki na matata! Amaryata! Uwar y’ay’ana! K’anwata sannan masoyiyata wadda take tsananin so na.” A hankali ya matso da bakinsa ya d’aura a kan goshinta yayi kissing yana kuka ya d’an d’ago yana kallon idonta yace “I love you, Zainab” Wasu zafafan hawayene suka shiga zubo mata, a hankali tace “Now I’ll have a nice nap! In sha Allah. Thank you.” Kasa ci gaba da zaman yayi dan haka ya mik’e da sauri ya fita a d’akin yana kuka sosai. Yana fita Hudan Shuraim da Sudais suka shigo. Tana jin kukan su ta fahimci sune suka shigo dan zuwa yanzu ba sosai take gani ba. A hankali ta bud’e musu hannuwanta alamun su je gareta. Da sauri kuwa suka nufeta suna zuwa tayi hugging d’insu gaba d’aya…. A hankali suka cikata suka matsa gefe suna kuka. Cikin kuka Huda tace “Ummi wallahi ban san poison bane ba” A hankali Ummin ta katseta ta hanyar cewa “Shhh”. Sai da ta ga ta d’anyi shiru sannan tace “Magana d’aya zuwa biyu nake so in gaya muku… Ku had’a kanku ku so junanku ku rik’e zumunci a duk inda kuke ku rik’e amana dan Allah sannan kar ku cuci wani..” A hankali Granpa ya turo k’ofar ya shigo Idanuwanshi sun yi jajawur! Tun lokacin da Gramma ta fad’a mishi ta fito sam sai ya gagara sukuni shiyasa shima kawai ya yanke shawarar zuwa asibitin. Yana hanya ma lokacin da Aslam ya kira shi ya fad’a mishi abunda Likita yace. Da kyar ya taka da y’ar sandarshi ya k’arasa bakin gadon. Inda Abba ya tashi nan ya zauna tukun a hankali yace “Ummi” Juyowa ta yi sanann ta d’an d’ago hannunta tana k’ok’arin kama nasa. A hankali ya kamo hannun nata da nashi hannayen duka biyu ya rik’e. Inda su Shuraim suke a tsaye yanzu tun shigowar Granpa ta d’an kalla kafin tace “ku bamu guri”. Har sun juya za su fita suka ji tace “Allah yayi muku albarka” Sai da suka juyo gaba d’ayansu tukunna suka ce “Ameen Ummi” Sannan suka juya suka fita suna wani irin kuka. A hankali ta maida idonta inda take Jin Granpa tace “Daddie, dama inada niyyar bada sak’o a baka koda ace baka zo ba. Na gode kuma naji dad’in zuwanka. Maganata ta farko Itace Godiya! Kasancewar ka Uncle kuma Uba a gareni Is one of the luckiest thing da kuma nake alfahari da a rayuwata. Tun tasowata har kawo yanzu bana jin akwai abunda na tab’a nema na rasa shi, baka rage ni da komai ba akoda yaushe k’ok’ari kawai kake yi kaga nayi dariya na samu abunda nake so! Na gode kwarai Daddie bana jin aduniyar nan a kwai d’iyar da tayi sa’ar samun uba mai tsananin kaunarta kamar ni.” Runtse hannunta da yake a cikin nashi hannayen yayi hawaye ya fara sintiri akan tsohuwar fuskarshi. A hankali dan muryarta tayi low zuwa yanzu ta ci gaba da magana “Sai magana ta biyu Shawara ce zan baka! Iyaye da manya suna ganin kamr duk abunda babba yayi shine dai dai alhalin wasu lokutan wani babban yana yin abunda ko d’an shekara tara ba zai aikata ba saboda ya san ba dede bane ba amman tsoro da fargabar gayawa wannan babban gaskiya sai a sanya ido ayi shiru a nad’e hannu a koma gefe a taru ayita tafka b’arna!” Shiruu, ta d’anyi tana k’ok’arin jawo numfashi kafin tace “Same thing da yake going a estate d’inmu kenan… Ka yi hak’uri da abunda zan fad’a yanzu Kai da kanka da hannunka ka hargitsa estate d’innan wanda yanzu abunda ya faru yau yasa na tabbatar da hakan kuma inajin takaicin rashin sanin k’arshen wannan bala’i da musiba da ta shigo mana ko kuma ince muke ciki tsundum ba tare da mun sani ba. Granpa dan Allah dan Annabi the first thing da zan rok’eka shine ka daina nuna bambanci! Yanzu ni ba a maganata amman in baka tashi ka tsaya ka gyara tsagwaran bambancin da kake nunawa a tsakanin Aslam Auwal da Arshaad ba to akwai matsala babba!. Bani da tantama bani da shakku akan Aslam akaso ayi poisioning yau ni kuma na sha ba tare da na sani ba! Ban ce Arshaad ko Auwal bane ba amman dai na san dole a cikin estate d’in mu ne wanda na tabbatar ata dalilin kyautar gidan da kayi mishi ne da kuma ragowar abubuwan da kake tayi tun haihuwarshi har kawo yanzu, sannan ina so ka san wallahi tallahi ba Huda bace ba”. Numfashinta da ya fara sark’e wa ne yasa ta yi shiru ta hau kokawar janyowa…. Da sauri Granpa ya mik’e ya fara kiran “Doctor!!” Ruk’o hannunshi tayi tace “One last thing abunda nake so abunda idan kayi min zan ji dad’i shine Granpa dan girman Allah da manzonsa ka yi hak’uri ka daure ka yarda sannan ka taimaka wa Abba ya maida Maryam! Ka yi accepting d’inta ita da Huda Dan Allah Granpa sannan ka tayani neman yafiyar mutum uku Maryam Aisha da Huda! Although na san su Maryam sun yafe min amman Ina buk’atar ka sake nema min yafiyarsu” Tana gama fad’in haka numfashinta ya fara sama maganar ma da take son sake yi ta sark’e harshenta ya fara fidda maganar da ba ita ba! Da sauri Granpa ya sake cewa “Doctor!!” Da k’arfi yana zubarda hawaye da k’ok’arin barin wajen amman sai yaji still ta sake rik’e hannunshi tak’i saki. Juyowa yayi suka had’a ido yaga yadda idanuwanta suke shirin k’afewa tana ta faman kokawa da numfashinta! Da sauri ya k’arasa yayi cupping fuskarta yana kallon idonta yace “Ashhadu allailaha illallah” A hankali tace “Ashhadu allailaha illallah” Wani kuka ne ya taho mishi yanayi yace “Wa ashhadu anna muhammadrasulullah” Cikin jan numfashi da kyar tace “Wa ashhadu anna muhammadrasulullah” Dai dai nan Doctor nurse da ragowar ahalin MT gaba d’aya suka shigo d’akin ata dalilin kiran Doctor d’in da Granpa yayi…. Cikin tsananin kuka dan har idanuwanta sun k’afe yace “Salllallahu alaihi wa sallam” A hankali yaji ta maimaita daga nan dip! Komai nata ya tsaya ta chak! Ta daina k’ok’arin janyo numfashin da take ta faman yi yana wahalar da ita K’arar naurar da aka jojjona mata shima ya chanja……. Kifawa Granpa yayi abkanta yana tsananin kukan da rabonshi da yi tun ranar da Yaya da Doctor suka rasu.......... A hankali Likitan ya k’araso ya hau dudduba ta, chaan! Ya d’ago agogon hannunsa ya duba kafin ya juya ya kalla nurse d’in da suka shigo tare yace mata “Time of death! 1:30am”. Kuka gaba d’ayansu suka saka lokaci guda, babu mai lallashin wani. A hankali nurse d’in tace “su d’an bata guri zata gyarata ta saka mata auduga kar iska ya shiga kafin zuwa gobe tunda ta san dole zatayi kwanan keso” …………….. A waje suka samu Arshaad da Aslam suna zaune kowa yayi jugum. Daman tunda suka ji Granpa ya kwala kiran Doctor sun san menene shiyasa ma suka k’i shiga yanzu kuma fitowar su kowa yana kuka ya sake tabbatar musu. Da sauri Aslam ya mik’e ya fice a wajen haka shima Arshaad d’in dan basu san wa za su fara lallashi ba! Kowa ka ganshi kuka yake yi masu hawaye nayi hatta Granpa ya kasa tsaida hawayensa. Cikin mintuna 15 nurse d’in ta fito ta mik’a musu kayanta da ta saka a box tace “An gama. Saura rufe bill, daga nan su wuce da ita” A take Dad ya bita ya gama komai har file sanann ya dawo suka turata kanainaye cikin farin bedsheet har mota shi da Daddy, su Mommy da Mom suka shigar da ita suna kuka. Mom ce ta zauna a baya ta d’aura kan ta a kan cinyarta tana wani irin kuka kamar ranta zai fita. Mommy kuma a gaba Dad yana tuk’i, a haa suka kama hanyar MT.. Aslam shi ya ja su Huda da Shuraim da Abba Arshaad kuma suka tafi tare da Daddy Granpa kuma driver d’in da ya kawoshi ya maida shi tare da Gramma. A hanya Granpa bai bari sun k’arasa ba ya kira Abba yace mishi “dan Allah a wuce da ita estate idan ba damuwa” BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 65 Mikiya Writers Association. Direct side d’in Granpa aka nufa da gawar Ummi. Kafin zuwa asuba Mommy da Gramma suka yi mata wanka suka shiryata. Haka nan suka sakata a gaba suka dinga yi mata karatu da tofi tun jiyan dama suke yi su biyar har Huda Shuraim da Sudais, suna yi suna kuka. Ana idar da sallah aka sanar jana’iza k’arfe 9:00am a masallacin estate, daga nan gaba d’ayan su kowa ya nufi side d’in Granpa. Shiruu! Haka b’angaren ya kasance amman kowa da Al’quraninsa, masu hawaye suna yi suna karatun….. Har zuwa lokacin da gari ya waye jama’a suka fara taruwa, mak’ofta da suka ji ana ta lek’awa estate d’in ana gaisuwa, sai k’awayensu da family friends da suka ji ta wayoyi….. K’arfe tara tana yi mazan suka shigo domin fita da gawar sai a sannan abun ya dawo sabo! Abun tausayi especially yadda Huda Shuraim da Sudais suka k’amk’ame gawar suna kuka kamar ransu zai fita! Da kyar Arshaad ya janye Sudais Auwal kuma wanda Daddy yaje ya d’auko ba da jimawa ba ya janye Shuraim Aslam kuma yaja Huda! Tukunna su Daddy suka saka gawar a makara aka fita da ita waje domin a sallaceta…… K’arfe tara aka gabatar da jana’iza aka mik’a Ummi gidanta na gaskiya. Ta samu halarta d’umbin jama’a maza da mata dan kamar yadda mak’abarta ta cika haka ma cikin estate d’in. Suna dawowa Granpa ya cewa Abba “Su zauna anan (estate d’in) ayi zaman makoki ba sai sun koma chan gidansu ba...... Washegari, Sumayya Ummu da Baban su Sakina suka zo suka yi ma Huda da Abba gaisuwa. Ranar sadakar uku, Huda tana d’akin Gramma dan a nan take ita da su Shuraim ta ji wayarta tana k’ara! Tana d’auka Auwal yace “Ta yi bak’o yana waje a bakin estate, wai ya zo mata gaisuwa, yace ‘sunan shi Junaidu’ Ta sanshi a barshi ya shigo?”. Bata san lokacin da ta diro daga kan gadon ba tace “Eh Ya Auwal na sanshi sosai yayana ne! A barshi ya shigo.” Daga nan ta zari hijabinta ta yi waje tana adduar Allah yasa Ya Junaidun ne da gaske. Bata samesu a compound d’in Granpa ba daman bata yi expecting hakan ba! Dan haka ta fice daga gidan ta nufi tsakiyar main compound na estate d’in. A inda ake parking motoci ta hango Auwal sanye cikin bak’ar jallabiya fuskarsa tayi fayau! Idanuwansa da suka ci kuka sun yi jaa sun k’ank’ance yayi tsananin rama sannan kana ganinshi ka san bashi da lafiya…. A tsaye tare da wani ya juya baya sanye cikin shadda fara d’inkin boda da bak’ar hula ya jingina a jikin booth d’in wata bak’ar mota Jeep! Yanayin takalmi da shadda da kuma hular kansa kad’ai sun isa su sa ka san cewa kud’i sun zauna… Da Auwal suka fara had’a ido yana shirin yin magana a hankali yaji tace “Ya Junaidu” Shiruu yayi da maganar da yake yi kafin ya gyara tsayuwarshi daga nan kuma ya juyo gaba d’ayanshi yana murmushi….. Kusan daskarewa Huda tayi, a hankali hawaye na gangarowa akan kumatunta ta ce “Ya junaidu” Murmushi yayi yace “Na’am Huda” Cikin share hawayenta tace “Where have you been? Yaushe ka dawo? Me ya faru? How have you been..” Murmushi ya saki mai d’an had’a da dariya kafin ya shafa k’asumbar da ya tara tayi mishi tsananin kyau yace “Ya muka ji da hak’uri?” A hankali ta sunkuyar da kanta tace “Alhamdulillah” Cikin sanyin murya. Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace “Allah ya ji k’anta yasa chan tafi nan” A hankali ita da Auwal suka ce “Ameen” Kafin Auwal d’in ya juya ya yi mishi sallama ya wuce. Gyara tsayuwarshi yayi yana kallonta kafin yace “How are you?.” Congratulations you have finally found your Dad” Jijjiga kai tayi sanann tace “Thank you” Tana mai d’ago da kanta sannan ta sake jeho mishi tambayar “Where have you been?” Dede nan Arshaad wanda dawowar sa kenan daga airport d’auko Aaima suka k’araso wajen shi da Aaima. Murmushi Junaidu yayi kafin yace “Arshaad!” Da sauri Huda ta juya dan ita bama taga tahowarsu ba. A hankali ta k’arasa inda Aaima take ta rik’e mata hannu tana kallonta kafin ta yi hugging d’inta. Bata iya ce mata komaiba Har ta cika ta ta d’ago. Ahankali Aaima da muryarta ta d’an dishe tsabar kuka tace “Ya hak’urin mu?” “Alhamdulillah” Huda tace Daga nan Aaima ta d’an d’ago ta kalli Junaidu wanda ya kafe Arshaad da ido tace “Ina wuni” Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya juyo ya kalleta a hankali yace “Alhamdulillah. Ya hak’uri?” “Alhamdulillah” tace, daga nan tace “Ya arshaad bara in wuce ciki, thank you.” Tana gama fad’in haka ta juya ta wuce ciki. A hankali Huda ta d’an juya ta maida hankalinta akan Arshaad kafin tace “Ina wuni” Ba tare da ya kalletaba ya ce “lafiya” Junaidu Hudan ta kalla wanda tun wucewar Aaima ya maida idanuwanshi a kan Arshaad tace “Ya Junaidu baka bani amsa ba” Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace “Actually.. Ni kaina ba zan iya ce miki ga a inda nake ba. Forget all that bana so ma In dinga tunowa…” Sai kuma yayi murmushi yace “Congratulations Na ji kin yi aure!” Ya fad’i hakan yana kallon Arshaad kafin ya ce “And kamar ba Arshaad kika aura ba ko? Mai yasa?” Da sauri Huda ta d’ago ta kalleshi, ganin ba ita yake kallo ba gaba d’aya hankalinshi yana akan Arshaad d’inne yasa tace “Ya Junaidu” Juyowa yayi ya kalleta, a hankali ta jujjuya mishi kai alamun ya bar maganar. Murmushi kawai yayi yana maida idanunsa akan Arshaad still kafin yace “No i was just curious ne He has done so much and a lot for and because of you! I wonder why bai samu aurenki at the end of the day ba…” A hankali Arshaad ya d’ago jajayen idanuwanshi wanda har sai da suka so firgita Huda ya watsa su akan Junaidu kafin yace “Did you come here to mock me?” Da sauri Huda ganin Junaidun yana sake shiri yin magana tace “Ya junaidu ka daina mana. Gaisuwa ka zo ko? To kayi iya gaisuwar please.” Shiruu yayi ya d’an sunkuyawar da kanshi yana kallon k’asa kafin ya d’ago yace “Forgive my manners” Yana kallon Arshaad sannan ya juya ya kalli Huda yace “Allah ya ji k’an Ummi. Bara in wuce, su Umma ma basu ganni ba dan ban je ko gida ba I came here straight.” Hudan gaba d’aya lamarin Junaidu ya d’aure mata kai! Bai je gida ba? Tou a Ina ya san Ummi ta rasu? Sannan waya gaya mishi ta yi aure?…. “Sai anjima” Ya ce yana d’an murmushi yana kallonta. A hankali tace “Na gode ka gaida su Umma” daga nan ta juya ta wuce. Wani abun mamamkin.. har ta kai gate Arshaad da Junaidu suna tsaye suna magana kuma da ga yanayin yadda suke demonstrating har da hannayensu zai sa ka fahimci serious magana suke yi. Har ta hau sama d’akin Gramma ta lek’o ta window sai da ta gansu kafin chaan Junaidu ya bud’e motarsa ya shige ransa a mugun b’ace ya ja yayi gaba ya bar Arshaad nan tsaye a wajen…. Tana shirin juyawa sakamokon k’amshin da k’ofofin hancinta suka jiyo mata, ta ji anyi huggin d’inta ta baya. Runtse idanunta tayi da k’arfi! A hankali dede setin kunnenta ta ji ya ce “Haramun kike kalla fa” Muryarshi na d’an rawa. Da sauri ta d’an ture shi kafin ta juyo tana kallonsa sai kuma tayi saurin yin k’asa da kanta dan gaba d’aya sa taji ba dad’i especially ma yadda taga kamar ranshi bai so ba! Sannan ba lalle ya fahimci kallon me take yi wa Arshaad d’in ba. Tana shirin yin magana ya katseta ta hanyar cewa “Who is the other guy?” A hankali ta d’an sunkuyar da kanta kafin tace “Ya Junaidu. Tare muka taso.” Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya matso kusa da ita sosai kamar zai shige jikinta yayi cupping fuskarta a hankali ya d’ago da fuskarta yadda za su kalli juna sosai yana kallon cikin idonta yace “Kar ki sake abunda kika yi yanzu, please.” Yadda yayi mata magana da yadda taga idanuwanshi sun yi da yanayin voice d’inshi ya sanya ta kasa cewa komai ta lumshe idonta kawai tana jin yadda jikinshi yake karkarwa a hankali… Ya dad’e yana kallon fuskarta kafin ya cikata a hankali ya juya ya fita. Tana jin fitarshi ta bud’e idanuwanta tana sauk’e ajiyar zuciya a jejjere…. Bayan rasuwar Ummi Idan akwai abunda yafi damunta ya fi rikitata tou Ya Aslam ne! Kwata kwata ta kasa gane gabanshi ta kasa gane bayanshi ta rasa me yake nufi da ita, sannan ita kanta yanzu ba zata ce ga tak’ameme abunda take ji a kansa ba! Adduar ta d’aya ‘Allah yasa ba ta yi masa ko da d’an mitsitsin so ne’ Dan in dai haka ta kasance to tabbas ta zama butulu! She is trying very hard ta ga ta yi nesa da shi amman idan yaso ganinta duk inda take sai ya shigo ya ganta ya fita. A ranar sadakar bakwai suka tashi jikin Auwal ba dad’i sosai. Daman tun lokacin da aka yi rasuwar dauriya ce kawai yake yi amman sam ba lafiya gareshi ba… Tun yana yi a b’oye dan baya so a fahimta har Mom ta gano dan haka suka dangatashi da asibiti… Ba k’aramin tashi hankalin ahalin gidan yayi ba da ga jin Auwal ya kamu da ciwon zuciya! Da farko Daddy Huda ya fara kira yayi mata maganar Sakina dan tashi d’aya ana tambayarshi mene damuwarshi ya ce “Sakina” Tun kafin aje ko’ina jikin Daddy ya sake yin sanyi jin ‘an bada ita bikinta bai ma kai wata biyar ya rage ba’. Jiki a mace haka Daddy ya sallameta ya shiga nemawa tilo d’an nasa wata mafitar.. Kafin 5 days hankalin kowa ya sake tashi saboda idan ka ga Auwal dole sai ka tausayi masa.. A take mazan suka yanke shawarar tura shi wani waje treatment sannan ya d’an huta. A cikin kwana biyu aka gama shirye shiryen komai… A ranar da za su tafi har an sakashi a ambulance dan zuwa yanzu ko zaman kirki baya iyayi! Auwal d’in ya nemi alfarmar ganawa da Granpa da Arshaad..... Granpa ne ya fara shigowa tukunna Arshaad.. Duk wani abu da Auwal ya san ya tab’a yi mara kyau sai da ya zaiyyanewa Granpa sannan ya fad’i yadda yayi framing Arshaad har Granpa yaso yin shariah da shi! Duk wasu kud’ad’e da ya tab’a d’iba sai da ya maida mishi, a take ya yayi signing ma company account. Daga nan ya ruk’o hannuwansu yana hawaye ya nemi yafiyar Granpa da Arshaad. A hankali Arshaad ya matsa yayi hugging d’inshi, yace “ba komai komai ya wuce ka kwantar da hankalinka”. Cikin sauk’e ajiyar zuciya Granpa shima yace “Komai ya wuce Auwal, kar ka damu na yafe maka. Allah ya baka lafiya Allah yayi maka albarka. Ka kula da health d’inka please ka kwantar da hankalinka Allah ya baka lafiya”. A hankali yace “Na gode Granpa but please inaso in bawa Arshaad shares d’ina, to makeup for all the things da nayi ta masa” Murmushi Granpa kawai yayi ya shafa fuskarshi kafin yace “Allah ya baka lafiya” Daga nan ya mik’e ya fita daga cikin ambulance d’in. Bayan fitar Granpa da kyar Arshaad ya lallab’a Auwal ya hak’ura amman still yace “idan Allah yasa yayi rai ya warke to ya na dawowa ya shirya karb’ar shares d’inshi Idan kuma ya mutu bai dawoba tou ya bashi halak malak!” Auwal was very emotional gashi sai hawaye yake yi hakan yasa Arshaad kasa ci gaba da zama da shi dan haka ya mik’e ya fice bayan Auwal d’in ya ce masa “ya turo mishi Aaima please” Da “to” kawai ya amsa shi ya fita. Har airport Aaima ta rakasu shi da Mom. Mom driver ya jata shi da Aiima kuma a ambulance. Itama Aaiiman hak’uri da neman yafiyarta yake ta faman yi…… A hankali tana hawaye tace “ta yafe mishi” Ya ji dad’i sosai dan haka ya d’an gyara kwanciyarshi ya fuskanceta sosai sannan yace “I saw your message tun kafin rasuwar Ummi. Aaima inaso ki fahimci wani abu guda d’aya.. Right now you are confused! Ta yiu burgeki nake yi ko kuma tausayina like ji amman one thing is for sure ba sona kike yi ba! Nasan tun kina k’arama da tunanin hakan kika taso amman tabbas ba kya so na Za kuma ki ce na gaya miki..zaki fahimci hakan a ranar da kika had’u da matching pair d’inki… Ki nutsu, you deserve better dan ko da ace na aureki wahala kawai zaki sha saboda zuciyata already ta Sakina ce ba zaki tab’a samu ba! Rasa zuciyar Miji a rayuwar aure kuwa is the worst thing da mata zata fuskanta a zaman aure. I don’t want that for you, Ina miki kwad’ayin ki auri wanda kike so yake sonki. Tabbas na san zan yi aure wata rana idan na samu na tashi daga wannan ciwon wanda In ba da kyar ba shine ajalina.. A ko da yashe In na tuno zan yi aure wallah in banda tausayin matar ba abunda nake ji saboda na san gangar jikina kawai zata aura! Bana so ki kasance wannan matar besides ba zama ki iya jira na ba dan tunda na rasa Sakina I don’t think zan yi tunanin yin aure in the next 10 years ma.” ……………….. Sun tattauna sosai Ya ji dad’in yadda Aaima ta fahimci shi. Har akazo za sakashi a jirgi tana yi masa alk’awarin she’ll speak with Sakina for him. Murmushi kawai yayi dan shi kam zuwa yanzu ya hak’ura dan ya san su Daddy ba za su tab’a nema masa aure cikin aure ba! Sannan after abunda ya faru a birthday d’in su Shuraim tsakanin Sakina da su Mom Ya san ba zata tab’a yarda da shi ba!. A yanda yake jin zuciyarsa kuwa ya riga ya sadak’ar…idan bai mutu ba tou tabbas tashinsa ba kwana kusa ba. Gaba d’ayan su sun kasa kunne sun zuba ido suna jira suji daga bakin Granpa! Dan ya cewa Gramma ta gaya musu su zauna a nan ayi zaman makoki for sometime amman har aka shafe kwana ashirin shiru, bai sallamesu ba kuma bai ce su zauna ba. Sai dai In za su yi wanka suka je su yi achan mansion d’in, su kwaso kaya set biyu ko set d’aya su dawo wanda a haka haka har sun kusan had’a wardrobe amman Granpa bai ce komai ba. Daman ita Hudan bata ma tab’a zuwa ba dan tun washegarin rasuwar Aslam ya kawo mata akwatin ta, kamar ya sani. A kwana na ashirin da biyar ne Mommy ta nemi Huda ta dawo wajensu side d’in Aslam inda aka kaita tun farko. Gramma ba k’aramin dad’i ta ji ba amman k’iri k’iri Hudan ta rufe ido a gaban Aslam d’in da Mommyn tace “Ita a wajen Gramma zata zauna” Mommy tana shirin fara lallashinta ta fashe musu da kuka! A hankali jiki ba kwari Aslam d’in ya tashi ya fita haka itama mommy.. Bayan fitar su Gramma lallashi da tambayar duniyar nan amman Huda ta kafe tace “dan Allah ta bar ta ta zauna a wajenta” Haka nan ta hak’ura ta kyaleta bayan Mommy ta kira Gramma d’in tace mata “Kawai ta bar Hudan a wajenta tunda bata so. Aslam d’in ma tafiya zai yi akwai wani abu da ya taso a company d’insa na sarrafa takalma da yake a chan UK so yana so zai je”. Sam Gramma bata ji dad’in abunda Huda tayi ba amman rashin lafiya da rashin kuzarin da yake damunta kwana biyun nan yasa kawai tayi mata shiru ta rabu da ita.. Tun ranar da Ummi ta rasu take rashin lafiya a tsai tsaye ba tare da ta bari an fahimta ba, ba abunda yafi d’aga mata hankali irin yadda family d’inta ya koma ‘Poison!!’ A cikin ahalinta aka samu wani yayi poisoning wani!…. Wannan tunanin shi ya haifar mata da high Bp ba tare da ita kanta ta san ya hau d’inba. A ranar da zai tafi tana d’akin Gramma, ta Idar da sallah kenan ta jiyoshi a parlour suna gaisawa da Gramma! Da gudu ta mik’e ta fad’a band’aki ta rufo k’ofar, dai dai yana shigowa ita kuma tana rufewa, dan haka ya k’arasa k’ofar band’akin ya tsaya. Ya dad’e a tsaye kafin ya lumshe ido ya fara magana Na san saboda ni kika b’uya, kuma na san kina jina… I just come to say good bye! Tun da yanzu naga kamar na zame miki dodo. Naso ache tare muka tafi but iya yadda kika nuna ranar da Mommy tace ki dawo wajena ya isa ya fahimtar dani idan ma nace ki bini kunya kawai zaki sake bani. Idan wani abun na yi miki wanda ban san da shi ba ki yi hak’uri ki yafe min.. If by any chance kinji ra’ayinki ya d’an sauyu akan fushi da wasar b’uyan da kika d’auka da ni to ki yi min magana in sha Allah zan sa a shirya miki komai sai ki zo ki sameni achan d’in. Ga numberki na karb’a a wajen Gramma, zan yi miki message da tawa ta chan once i settled. Kar ki damu ba zan dameki da messages ko calls ba! Na fahimci you need some space so think and decide wisely. Hudan i can’t stay under one roof with you kina guduna kina b’oye min ba ba zan iya ba..Ni kad’ai na san what I’m going through. Ina fata kafin in dawo kin yi figuring out whats going on with you.” A hankali yace “I’m going to miss you” Yana gama fad’in haka ya juya kamar mara lakka a jiki ya fice. Ta dad’e a cikin toilet d’in kafin da kyar ta bud’e k’ofar ta fito.... Kamar yadda ya fad’a yana isa ya turo mata “Arrived safe, Aslam.” Da numbersa ta chan. Tun daga ranar bai sake nemanta ba, itama kuma bata nemeshiba. Bayan kwana goma sha uku, yau Ummi ta cika kwana arba’in da rasuwa. Ahalin gidan kowa ya ji rasuwar Ummi sosai sun girgiza matuk’a! Hakan kuma ya zamo izina ga wasu, wasu kuwa da zuciyoyinmu suka ruga suka daskare ba abunda ya chanja a lamari da tsaurin su. Sai a ranar sadakar arba’in d’in tukunna Aslam ya dawo da safe, dan haka bai samu damar shiga cikin gidan ba ya tsaya a wajen da ake addua. Bayan an ida an kammala sauk’a aka raba sadaka aka fara watsewa… Sai a sannan Granpa ya yafito shi da hannu. Cikin nutsuwarshi da class ya mik’e ya k’arasa inda yake ya durk’usa ya gaidashi ya sake yi mishi gaisuwa. A hankali yasa hannu ya shafa kanshi, kafin ya amsa. A hankali Aslam d’in yace “Allah ya jaddada rahama a gareta” “Ameen” Granpa yace yana mai sauk’e ajiyar zuciya sannan ya zare hannunshi daga kanshi yace “Taso muje akwai inda nake so ka rakani.” Driver d’inshi yana ganin sun nufi wajen parking motoci ya mik’e da d’an sassarfa ya k’arasa inda suke. Hannu kawai Granpa ya mik’a masa! Ya gane me yake nufi dan haka ya zaro key d’in Gwagon d’in da suke tsaye a gabanta ya bashi. Ya na karb’a ya mik’awa Aslam ya ce “mu je!” Daga nan suka k’arasa duk su biyun suka shiga Aslam ya kunna ya ja suka fice daga estate d’in….. “Gidan Madu Mahaifin Maryam za mu je!” Granpa ya fad’a yana mai gyara zamanshi ba tare da ya kalli Aslam d’in ba. Wata nannauyar ajiyar zuciya Aslam ya sauk’e wanda har sai da Granpa ya jiyo shi kafin ya lumshe idanuwanshi ya bud’e ya gyara zama suka d’auki hanyar gandun albasa. A dede k’ofar gidan ya yi parking ya kashe motar ya juyo yana kallon Granpa wanda yake kallon gidan yana sake kalla, a hankali Aslam d’in yace “Mun iso Granpa” Lumshe idanuwanshi Granpa ya yi, kafin ya bud’e ya sauk’e ajiyar zuciya yace “mu je” Yana mai sa hannu ya bud’e k’ofar motar. A hankali Aslam wanda tsananin farinciki da fargaba suka lullub’e a lokaci guda yasa hannu ya bud’e k’ofar side d’inshi ya fito zuciyarshi cike da fargabar abunda ya kawo Granpa nan sannan kuma yana addua da tsananin farin ciki In Allah yasa alkhairin da yake tunani ne ya kawo su.. Kame kame Aslam ya fara yi da dibi dibi dan shi dai ya san bai kamata su shiga kai tsaye ba! Rashin sanin kan al’ada da lamarin garin Hausawa kuma yasa ya rasa abun yi. Suna tsaye Junaidu ya bud’e k’ofa ya fito.. Kallon kallo aka tsaya kafin Junaidun ya k’arasa ya mik’awa Aslam hannu. Bayan sun yi musabaha yace mishi “Dan Allah suna son ganin Abba Madu idan yana nan.” Da mamaki Junaidun ya kalleshi kafin yace “Wa za a ce mishi?” Sai da yad’an kalli Granpa wanda still har yanzu gidan yake ta kalla tukunna ya d’an sunkuyar da kanshi kafin ya d’ago yace “Kace mishi Mijin Maryam ne, Huda.” Murmushi Junaidun yayi ya sake bashi hannu suka gaisa sannan yace “Ashe k’anin namu ne” Ya fad’a cikin raha da barkwanci sannan cikin ladabi ya juya ya gaida Granpa! Ba yabo ba fallasa ya amsa shi daga nan Junaidun ya juya da d’an sassarfa yace “Minti biyu dan Allah” ya shiga cikin gidan. Bai rufe second talatin ba suka ga ya bud’e wata k’ofa ta waje ta cikin gidan sannan ya fito ta k’ofar yace musu “Ku shigo, bismillah” Sai da suka zauna ya d’auko ruwa da lemo a cikin babban fridge d’in da yake a parlourn bak’in ya jere musu tukunna ya juya ya fita ya ce “bara yaje ya kira musu Abba Madun, yana gidan Kaka.” Ba ayi minti biyar ba Madu da Kaka suka shigo da sallama. Cike da kamala suka k’arasa cikin parlourn suka nemi waje suka zauna a kan 3 seater d’in su biyun wadda take facing 1 1 seaters d’in da Aslam yake zaune a k’asan d’aya Granpa kuma ke a kan d’aya. A hankali cikin girmamawa Aslam yad’an sunkuyar da kanshi ya shiga gaidasu…. Da kulawa suka amsa shi kafin su maida hankalinsu a Granpa suka soma gaidashi cikin girmamawa zuciyoyinsu fal mamaki da tunanin abunda ya kawo shi garesu. Ba yabo ba fallasa ya amsa su kafin yayi gyaran murya ya gyara zama sannan ya kalli Madu yace “Ina son ganin ku ne amman first Ina buk’atar Maryama a nan” Ajiyar zuciya Madu ya sauk’e kafin yace “Ok ba damuwa” daga nan ya mik’e ya fita. A parlourn k’asa ya sameta ita da Shuwa suna tattaunawa a kan al’amarin Junaidu! Bai bi ta kansu ba yace mata “ta taso ta d’auki hijabinta ta zo” Ganin yanayin shi ta san koma menene it’s serious dan haka ta mik’e ta nufi sama, bata wani dad’e ba ta sauk’o daga nan suka fice a tare. Suna fita ya kalleta ya ce “Kun yi magana da Abba ne? Akan aure ko wani abun? Kuna magana da shi sosai yanzu?” Da mamaki ta d’an kalleshi kafin ta sunkuyar da kanta tace “A’a! Na dai kirashi washegarin ranar da Ummi ta rasu nayi mishi gaisuwa” A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace “Tou Allah yasa lafiya” Dede nan suka k’arasa bakin parlourn dan haka bata samu damar tambayar shi komai ba suka kutsa kai suka shiga yana gaba tana biye da shi… Da Granpa suka fara had’a idanu tana shiga dan an ci sa a k’ofar yake kallo. A take gabanta ya yanke ya fad’i! sannan ta fara tariyo had’uwarsu da irin kalar warning d’in da yayi mata! Sai yanzu ta gane dalilin tambayoyin Abba Madun da kuma dalilin damuwar da ta hango shimfid’e akan fuskarsa. “Shigo mana Mama” Muryar Kaka ta katse mata tunani… A hankali ta taka ta k’arasa cikin parlourn k’irjinta na dukan uku uku!!! A k’asa kan kafet ta zauna gefen kafar Madu, muryarta na d’an rawa tace “Ina wuni Daddie” Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauk’e, kafin ya ja wani yawu ya had’iye sanann ya d’ago ya zuba mata idanuwanshi yace “Alhamdulillah, Maryama” A hankali ta sake cewa “Ya hak’uri” Bata jira jin amsarshi ba dan bataso maganar tasu tayi tsayi kar ya ga zak’ewarta kuma bataso ya kasance batayi mishi gaisuwa ba dan ta san yanda yake da Ummi d’in, dan haka tace “Allah ya gafarta mata yasa Aljannah ce makoma” “Ameen” ya ce. A hankali Aslam ya gaidata cikin girmamawa, da kulawa ta amsa kafin Granpa yace “Marigayiya ta bani sak’o wajenki” Da sauri Mama ta d’ago kai tana kallon shi.. Shima itan yake kallo kafin yace “A ranar da zata rasu tace ‘In sake nema mata yafiyarki’.” Da sauri Mama tace “Na riga na yafe mata tun ba yau ba mun gama wannan maganar da ita. Mun yafe mata daga ni har Huda fatan mu Allah ya ji k’anta da rahama” A hankali Granpa yace “Ameen” Sannan yad’an sake muskutawa ya gyara zamanshi kafin yace “A ganina ya dace ace nima na zo na nema yafiyarki tun kafin azo a nema min” Ba Mama ba hatta su Kaka da Aslam Granpa suka kalla fuskokinsu d’auke da tsananin mamaki! Bai damu da yadda suke kallonshi ba yace “Shekaru 29 ko ace 30 baya! Na san na baku wahala ke da Abba… Ban san halinda za ku shiga ba na biyewa b’acin rai da zuciya na turaku chan wata k’asa sannna bayan shekaru goma duk irin shak’uwar da kuka yi ban duba ta ba na sa Abba ya sake ki! Ki yi hak’uri….” A hankali ya kalli su Madu yace “Kuma ku yi hak’yri ku yafe min abubuwan da na aikata muku” Da kyar Madu wanda ya shiga shock yace “Ba komai ya wuce Allah ya yafe mana gaba d’aya.” “Na gode” Granpa yace, sannan ya maida idanuwansa kan Mama wadda ta kasa cewa komai. Ganin ta yi shiru yasa ya sake cewa “Ki yi hak’uri Maryama ki yafe min dan Allah....” Da sauri Mama wadda sai yanzu ta dawo haiyyacinta tace “Daddie dan Allah ka daina bani hak’uri.. Gaba d’aya am not comfortable with you apologizing. Ka yi hak’uri dan Allah ka daina bani hak’uri. Na hak’ura na yafe na manta komai, mu yafewa juna muma mun yi laifi ni da Abba dan kamata yayi ace dole muma mun tsaya mun bi zab’in iyayenmu… Ku yi hak’uri ku yafe mana” Ta yi maganar tana kallonshi sanann ta juya ta kalli su Madu. Ajiyar zuciya Granpa ya sauk’e kafin yace Na gode Maryam amman in dai da gaske kin yafe min ke da iyayenki To a yanzu Ina so mu d’aura aurenki da Abba!” This time around k’amewa Mama tayi k’am! Hatta numfashinta sai da ya kusan d’aukewa…. Ganin ya sake yunk’urowa zai yi magana yasa kawai ta fashe da kuka sai kuma ta tashi da sauri ta fita a parlourn tana kuka sosai. Da sauri modu ya mik’e zai bita Granpa ya hanashi ta hanyar cewa “Barta, kyaleta. Dawo ka zauna mu k’arasa magana.” Ahankali ya koma ya zauna jikinsa duk ba laka. Ajiyar zuciya Granpa ya sauk’e kafin yace “Ka lallab’ata. Na san dama dole ba lalle ta amince lokaci guda ba. Amman yau! Ni, a matsayina na Mahaifin Yakubu na zo nema mishi auren Maryam. Ina fata za a bamu.” Tun kafin ya rufe bakinsa Kaka yace “na baku, za ku jimu nan ba da jimawa ba in sha Allah.” A firgice Abba Madu ya juya yana kallonshi yana shirin yin magana Kaka ya mik’e tsaye yace “Mun gode kwarai Granpa. Ba ka san yadda maganganun ka na yau suka sanyani cikin tsananin farin ciki ba! Allah yasa ka gama da duniya lafiya In sha Allah ni da kaina zan samu Maryam mu yi magana da ita, daga nan zan tsayar da rana kawai a d’aura aure” A hankali ya kalli Aslam yace “Ina so ka yiwa Abba albishir d’in Baba Bashir ya sake bashi Maryam a karo na biyu! Sannan ba zai yi k’asa a guiwa ba wajen ganin ya mallaka mishi ita cikin sauk’i.” Daga haka ya kallesu yace “Bara in je gida na barku lafiya” Yana gama fad’in haka ya juya ya fita yana share wasu hawaye da shi kanshi bai san dalilinsu ba. Kana ganin Madu ka san yana cikin tsananin rud’ani! A hankali ya koma ya gyara zamanshi da kyau ya hau kame kame kafin ya daure yace “Mun gode Granpa.. Kwarai za ku jimu in sha Allah” Ya fad’i haka wani gumi yana keto masa. Tashi d’aya Granpa ya fahimci akwai wani abun a k’asa haka ma Aslam, amman ganin da suka yi tunda har suka b’oye kuma ga abunda suka gaya musu sai kawai suka bari akan bara kawai suma su bisu a hakan. Dan haka Granpa ya dogara sandarshi ya mik’e tsaye sannan yace “Na barku lafiya” Daga nan ya juya ya kama hanyar fita. A hankali Aslam ma ya mik’e ya yi wa Madu sallama ya fice. Har ya isa mota ya bud’ewa Granpa ya shiga ya rufe mishi sannan shima ya zagayo ya shiga ya tada motar kansa a d’aure yake! Ga dai abun farin ciki, abunda yana d’aya daga cikin abubuwan da yake mafarkin son ganin sun tabbata amman kuma Allah yasa babu wata matsalar da zata kunno kai ta b’angaren su Madu dan nan kam a b’angaren su Granpa ya gama gyara komai............. Mama tana shiga ta tarar da Shuwa a yadda ta barta, suna had’a ido ta sake fashewa da kuka ta k’arasa inda take ta tsugunna a gaban kujerar da take ta d’aura kanta akan cinyarta. Shafa kanta Shuwa tayi kafin tace “Lafiya Maryam, mai ya faru? Nifa daman yadda naga Abban ku ya shigo na san akwai matsala. Mai ya faru?” Tayi mata tambayar cike da fargaba. A hankali Mama ta share hawayenta ta d’ago tace “Hajiya matsalar ba daga kowa bane ba, daga mu ne! Matsalar daga ni da Abba ne! Faith d’inmu a baibai yake duk lokacin da muke so ko ya dace mu kasancewa da juna sai a samu matsala ta yadda indai muka zamo tare wani sai ya k’untata… Mai yasa farin cikin mu yake tahowa a tare da bak’in cikin wasu?” BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 66 Mikiya Writers Association. 39 DAYS AGO! Gandun Albasa. Gidan shiruuu, gaba d’ayansu suna zaune kowa yayi jugum! Kamar anan ake zaman makokin. A hankali Shuwa ta juya ta kalli Ummu kafin tace “Gaskiya fa Mama ta fad’a Ummu, ku je kawai ke da Sakina.. Ai ta ce ta kirashi ko?”. A hankali Mama ta d’aga kai alamun ‘eh’. Ajiyar zuciya Ummu ta sauk’e kafin tace “To shikenan Hajiya. Sakina taso mu je, Babanku yana waje.” A hankali Sakina ta d’an kalleta sai kuma ta d’auke kai tace “Ummu, dan Allah ki je kawai ko da Sumayya ne bana son zuwa gidan wallahi”. D’an k’ura mata ido Ummu tayi kafin tace “Taso mu je! Ba na son shirme.. Ba zaki yiwa su Abba da Aslam gaisuwa ba ko me??”. A hankali Mama tace “Ummu barta kawai ku je ke da Sumayya.” Shiruu Ummun tayi kamar za tayi magana sai kuma tace “Sumayya mu je” Ta fad’i hakan tana mik’ewa ta d’au mayafinta ta nufi k’ofa da alamun ranta ya b’aci. Suna fita ita da Sumayya Hajiya Shuwa ta mik’e ta fita tsakar gidan don yin zagaye saboda kumburin da k’afafuwanta suke yi idan ta zauna shiru. A hankali Mama ta mik’e ta koma kan kujerar da Sakina take zaune 2 seater.. Tana ganin ta dawo kusa da ita ta tashi ta zauna da kyau sannan ta d’an sunkuyar da kanta a hankali tace “Bara inje d’aki in kwanta” Tana shirin mik’ewa Mama ta kamo hannunta ta rik’e. Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin ta sunkuyar da kanta k’asa. Sai da Mama ta gama k’are mata kallo ta gama nazartar ta tukunna tace “Nima b’oye min za ki yi?” Da sauri Sakina ta d’ago tana kallonta kafin ta juyar da kanta tace “Me ne zan b’oye miki Mama?” Tana k’ok’arin danne kukan da taji ya taho mata. A hankali Maman ta sa hannunta ta juyo da fuskarta sannan ta ce “Tun ranar da kikace kin bawa Ashraff go ahead ya turo Sakina har yau ban ga walwala a kan fuskarki ba! In akwai wani abun ki yi magana a samu a gyara Idan mai gyaruwa ne.. B’oye b’oye ba abunda yake janyowa sai dana sani a rayuwa. D’azu Ina jinki a band’aki ke kad’ai kinata kuka! Meye ne yake damunki? Ko na tashi daga Mama na koma wata daban wadda ba zaki iya gayawa damuwarki ba?” Duk k’ok’arin Sakina na ganin ta tsayar da kukanta kasawa tayi, tashi d’aya ta hau ambaliyar hawaye ta shiga kuka tsakaninta da Allah.. Janyota Mama tayi zuwa jikinta ta rungumeta. Sai da tayi me isarta tukunna ta yi shiru da taimakon lallashin Mama kafin a hankali ta fara magana “Daman akan Ya Auwal ne cousin d’in su Hudan............” Tun ranar da suka fara ganin juna har kawo yanzu ba abunda Sakina ta b’oyewa Mama… Kallon ta Maman take yi tana sake wa kafin a hankali ta ce “Sakina wa ya gaya miki ana aure saboda a yakice soyayyar wani daga cikin zuciya?” Bata jira jin me zata ce ba tace “to bari kiji in gaya miki.. Shekarata goma sha takwas tare da Ya Usman matsayin mata da miji amman har yau ba abunda ya shiga zuciyata game da shi ta fannin soyayya sannan ba abunda ya ragu a cikin soyayyar Abba a zuciyata.” Da sauri Sakina ta d’ago tana kallon ta sai kuma ta fashe da kuka ta ce “Mama dan Allah kar ki yi min fatan in yi dakon soyayyar Ya Auwal haka har k’arshen rayuwata! Wallahi tallahi In dai yadda nake ji akanshi haka zan ci gaba da ji har abada bayan bana tare da shi tabbas mutuwa zan yi” Ta k’arashe maganar tana kifewa akan cinyar Mama tana sakin wani sabon kukan. A hankali Mama take shafa kanta…. Sai da taji ta d’anyi shiru tukun tace “Sakina ba zan b’oye miki ba, kin yi mistake!” A hankali ta d’ago tana kallon Mama da dara daran idanuwanta da suka rine sukayi jazir. Jinjina kai Maman tayi alamun tabbatarwa. Cikin share hawaye Sakina ta ce “Mama kin ji fa abunda Mom da Mammy suka yi min still in aureshi? Daman ni saboda family d’insa shiyasa na k’i tun farko bana san issues sannan…” Sai da ta d’anyi k’asa da kanta kafin tace “Sannan womanizer ne shi ne ya yiwa Jalila ciki fa” Ajiyar zuciya Maman ta sauk’e kafin tace “Sakina Ubangiji ya halicci bayinshi kowa da irin yananyin tashi k’addarar! Idan Allah yayi wannan ce k’addararki kina ganin kina da wayon da za ki kufce?. In dai Auwal yana sonki tsakani da Allah to zai daina abubuwan da yake yi, za ki iya gyarashi besides ai Auwal d’in ya shiryu ke kanki kin ce Arshaad tun ba yau ba ya cewa Hudan ya ga changes a tare da shi sannan kin ce Mahaifinsa shima yace ya shiryu! Ni a ganina zaki iya sake gyarashi tunda yana son ki wanda Allah kad’ai ya san d’umbin ladan da za ki samu. Tabbas ban so ki aura irin Miji mai halinshi ba ko da ace ya shiryu amman in dai haka Allah ya tsara yana sonki kema kuma kina son abunki to ya za ai?. Kuma Mahaifinsa ma baya k’in ki yana son ki wanda shi ne yake da say a gidan! Tabbas Mom matsala ce amman ni a ganina zugar Mammy ce…yadda kika ce tanata kuka ta rikice a lokacin da ya suma na tabbatar inda ba a kawo kud’in auren ki ba to da tuni yanzu tazo nan gidan saboda farin cikin d’anta dan tana tsananin sonshi wanda hakan shi zai sakata ta sauk’o ta so ki In sha Allah. Yanzu kam ba abun yi sai dai hak’uri… But by any chance kar ki sake yunk’urin toshe hanyar da za ku bi ku mallaki juna ke da Auwal! Ko da wasa, tunda kuna son juna.” Kukan da Sakina take ne yasa Mama ta janyo ta jikinta, a hankali ta shiga lallashinta kafin tace “Ki yi hak’uri Allah ya zab’a miki mafi alkhairi. Ku yi ta addua Allah ya zab’a mafi alkhairi.” Da kyar Mama ta samu ta lallab’ata ta yi shiru dann ita kam ta san inba wani tsananin rabo ba to Auwal yayi mata nisa! Ta riga ta datse duk wata igiyar da zata k’ullasu su kasance tare k’ark’ashin inuwa d’aya da hannunta…. A Cikin kwanakin da ba su kai wata d’aya ba da Anty Zainab ta yi da Sadiya tabbas ta fahimci ba zaman amana take yi da ita ba! Mamaki k’arara take yi game da yadda Abotar tasu take k’ok’arin juyewa ta koma wani abun na daban. Haka nan ita za ta yi musu girki da kud’inta saboda duk wani ragowar gari ko abun dafawa da suke da shi Umma ta tattare tace “babu ya k’are!” Sai ta fita aiki ita da Jalila su dafa su ci. Tun bata gane ba har tazo ta fara fahimta.. Ga shegiyar k’azanta daga Umma har Jalilan sannan wani lokacin Jalila har yada mata da magana take yi wai ‘anzo an zaune musu a gida!’ Sannan Ya Ja’afar kwata kwata basa kula da shi dan wani lokacin wandonshi har tsutsa ne suke binshi gashi kullum cikin datti kacha kacha especially gashin kansa sak mahaukacinsa! Haka nan zata tartare kitchen da band’aki dan idan zai yi tsutsu ba za su gyara ba! Sannan ta gyara Ya Ja’afar ta fita aiki ta je ta dawo ta dafa kuma su ci tare. Ana cikin haka Junaidu ya dawo… Ranar suna zaune a d’aki suna d’an tab’a hira kawai suka ganshi ya shigo! Da farko Umma tsorata ta yi dan ihu ma ta yi, fahimtar da tayi ba ita kad’ai ce take ganinshi ba yasa ta tashi ta k’arasa ita da Jalila inda yake. Sai da suka d’an tab’a fuskarshi da jikinshi suka tabbatar da shi d’inne tukunna suka rungume shi a tare suka fashe da kuka… Tabbas shima yayi matuk’ar kewar gida shiyasa bai san lokacin da hawaye suka wanke mishi fuska ba. Da taimakon Aanty Zainab aka samu suka yi shiru ita ma ta rungume shi tana d’an nata hawayen sannan suka nema waje suka zazzauna......... Tun daga lokacin duniya ta dawowa Umma da Jalila sabuwa!…. Hankalin Junaidu ba k’aramin tashi yayi ba ganin halin da Ya Ja’afar ya ke ciki. Bai yi k’asa a guiwa ba haka suka kinkimeshi shi da Jalila suka sa a mota suka nufi asibiti… Bayan y’an dube dube Likita ya basu sunan asibitin da ya kamata a kaishi. Ba abunda ya fi bawa Jalila mamaki irin kyan asibitin da mak’udan kud’ad’en da Ya Junaidun ya bayar daga nan suka amshi Ya Ja’afar d’in. Kusan kamar gidan mahaukata haka wajen yake amman ana basu kulawa da treatment mai ma’ana. Suna dawowa washegari ya fara da case d’in Baba shima wanda tun ranar da ya dawo yaje ya ganshi a gidan Kaka don tun dawowarshi a wajen Baba talatu yake. To anan ma an kashe kud’i wajen bincike da ragowar abubuwa, duk kuma tare ake zuwa da Jalila wadda babu abunda tafi sakawa ido irin aljihun Junaidun dan haka tana dawowa gida take sayarwa da Umma Jarida! Nan kuwa suka maidashi atm…. Tun abun yana burge Anty Zainab har yazo ya fara bata tsoro saboda yadda Junaidu yake wasa da kud’i ya kamata a bincikesa. Ita kuwa Umma ba abunda ya dameta, da Anty Zainab tayi mata maganar ma cewa tayi “Kar su yi mishi magana yayi tunanin zarginshi suke yi ya rage basu kud’in” Tun daga nan Anty Zainab taja bakinta tayi shiru bata k’ara magana ba. Su Umma duniya ta dawo sabuwa! Hatta shinkafa basmati ake ci a gidan Kaji kuwa ba a magana.. Wani zubin ma da daddare sai dai a siyo tsire ko pizza da fresh milk aci a kwanta. Har gidan su Kaka da Abba Madu junaidu bai bari ba alkhairi na yau daban na gobe daban… Tabbas zama da Sadiya sai mutum mai d’ankaren hak’uri! Dan wannan duniya da jin dad’in da ta samu sai ta mayar da Anty Zainab kamar wata bola! Idan an kawo kaji sam ba zata bari ta tab’a ba ma, ita da kanta za ta gyara ta soya su d’ibar mata dan wulak’anci a nata kason kai da k’afa suke fitowa, sam basa la’akari da ‘shi Junaidun nephew d’inta ne itama’ Idan ya zo fita suka ce suna buk’atar kud’i har da na Anty Zainab yake ajjiyewa amman sai su hanata! Abubuwa kala kala haka ta dinga fuskanta wanda daman ance ba a gane asalin halin mutum sai an zauna tare ko an yi yunwa… Gashi wani abun mamaki sam Umma tak’i yarda su koma wajen malaminsu tare! Kullum sai sun bari ta fita aiki sai su je ita da Jalila, idan ta dawo sai ta tarar sun je sun karb’o mata sak’o. Gashi kullum ita ke bada kud’i su basa bada ko sisi wannan watan tun kafin wata ya zo k’arshe an bita bashi ba dan Khadija da Yayarta sun aiko mata kud’i ba to da bata san ta ya zata dinga zuwa aikin ba ma. Haka kurum yau taji bata yarda da bayanin su Umma ba dan agaskiya so take a san yanda za ai ta koma gidanta! Shiyasa tana tashi a aiki ta wuce wajen mutumin da kanta. Hankalinta ba k’aramin tashi yayi ba da taji bayanin mutumin….tabbas ashe shiyasa ko waya idan tace su kira a gabanta sai suce an sace wayar mutumin bashi da waya yanzu. Jiki ba kwari haka ta yi mishi sallama dan ita kasa ma yi mishi bayanin komai tayi ta mik’e kawai ta tafi...... A tsakar gida ta samesu Suna gashin zabi akan abun gashi, gaba d’aya gidan ya d’au k’amshi. A hankali ta k’arasa ta zauna a kan tabarmar da suka shimfid’e a tsakar gidan ta kalli Jalila ta ce “Auta dan Allah d’an kawo min ruwan sanyi a fridge d’in Junaidu in akwai” Ba tare da ta kalletaba tana chattn a wayarta tana nan kwance akan tabarmar bata motsa ba tace “Babu!” Ajiyar zuciya Anty Zainab ta sauk’e kafin tace “Je ki duba” Ta yi maganar cikin d’an tsare gida. Banza Jalilan tayi da ita. “Hmmm” Umma wadda take zaune akan kujerar tsugunno a gabn abun gashin tace sannan ta juya ta kalli Jalilan tace “Auta dan Allah je ki duba mata mana.” Tsaki tayi ta ajjiye wayar sannan ta mik’e ta wuce d’akin. Tana wucewa Umman ta juya ta ci gaba da abunda take yi, ba tare da ta kalli Anty Zainab d’inba tace “Zainab y’ay’an yanzu fa sai hak’uri, in ba da Allah ka had’a su ba ba zuwar maka aike suke yi ba.” Murmushin takaici Anty Zainab tayi kafin tace “Y’ay’an da aka b’ata dai! Y’ay’an da son zuciyar iyayensu take kaisu ga halaka” A zabure da mamaki Umma ta juyo tana kallonta sai kuma ta kwashe da dariya ta rangad’a gud’a! Kafin ta ajjiye brush da man hannunta ta juyo gaba d’ayanta ta gyara zamanta ido cikin ido ta kalli Anty Zainab d’in kafin tace “Kin san Allah! Bar ganin wai kin san cikina na san naki Bar ganin mun yi Abotar sama da shekaru talatin da ke! Billahil Azim kin ji rantsuwar y’ar musulmi ko? Yanzun nan zan murzawa idanuna toka in gurza miki rashin mutunci, har makofta sai an jiyomu.” Ta k’arashe maganar tana d’aga murya. Cikin tsananin b’acin rai Anty Zainab tace “Murzawa ido toka kuma na nawa Sadiya? Banda tsantsar son zuciya da son kai da rashin sanin ya kamata mai kuka sani?” This time around mik’ewa tsaye Umma tayi cikin kad’a hannuwa tana gyara d’aurin zaninta tace “Oya oya Zainba shiga d’aki yanzun nan ki d’auko kayanki ki yi waje! Tun kafin mu kasa sheda juna ni da ke.” Dai dai nan Jalila ta k’araso wajen da gorar ruwan sanyi a hannunta, ba tare da ta san dalilin hayaniyar da ta tarar ta d’an fara tasowa ba tace “Ko baki ji abunda aka ce miki ba ne? ‘Out’ ta ce!!!!” Anty Zainab d’in bata kulata ba dan ba saar yin ta bace ba, ta kalli Umman tace “Ko baki koreni ba Sadiya na gama zama da ke, dan ba zan tab’a zama kina yi min zagon k’asa ba, amman kafin In tafi ina so ki san na san abunda kukayi ke da y’arki.. Yau naje wajen Malan yanzu haka ma daga chan na ke” Bata damu da yadda maganar tata ta girgiza su ba taci gaba da magana “Sadiya da kika san ba zaki bari ayi min abunda nace ba ai da kin fito kin fad’amin na chanza shek’a, tunda na san dalilinki na hana ayi aiki na saboda kina gani ata dalilin aikin Jalila ne na samu matsala so kar azo a gyara nawa azo ita kuma Jalila ta rasa Arshaad ko? Haka ne ko ba haka ba? Haba Sadiya!! Wacce irin zuciya ce da ce? Wacece Ummul aba’isin fad’awata wannan matsalar tsofai tsofai da ni? Ko kina tunanin ban san abunda nake yi ba? Sarai fa na fahimci komai kuma duk dan kar ku ji ba dad’i shiyasa na ja bakina na yi shiru. Abun naki ma ni sai na ga kamar har da mugunta saboda a ganina Idan kin ce nace na hak’ura da Baban su Khadija bana son komawa gidansa a bar aikin mene kuma zaki d’aura da cewa ayi abunda ba zan koma ba? Haka muka yi da ke? Haka alk’awari ya ce Sadiya saboda Allah?” Anty Zainab ta k’arashe maganar tata tana fashewa da kuka saboda wani takaici da dana sanin biyewa Sadiya da ta dinga yi tun Yarinta da ya lullub’eta lokaci d’aya….. Da kyar ta samu ta lallashi kanta ta share hawayenta sannan ta d’ago ta kallesu! Su na nan a tsaye sun yi cirko cirko tace “Bari ku ji in gaya muku.. Wutsiyar rak’umi ta yi nesa da k’asa! Ba na duba bana buga k’asa dan bin malaman ma ke kika saka ni amman wallahi tallahi ku rubuta ku ajjiye in dai Arshaad kuke jira ya dawo ya auri Jalila to kuwa zata k’are ne a haka har abada babu Miji! Ku d’auki maganata as curse a matsayina na k’anwar Mahaifinta, bi’ma’ana baki ne na yi mata….” Wani wawan tsalle Umma tayi ta dira kan Anty Zainab ta shak’o wuyanta wanda sai da ta kaita k’asa Ba su yi wata wata ba suka rufeta da duka ita da Jalila…. Tun Anty Zainab tun tana daurewa har ta ware murya ta hau zunduma ihun neman agaji…. Da kyar mak’ofta suka kwaceta a hannunsu bayan sun shishshigo.. Still inbanda zage zage da tujara ba abunda Umma da Jalila suke zubawa. Wata mata ce tace mata “Ta zo su wuce ta kaita wajen Talatu ta d’an kimtsa daga nan sai ta wuce gidanta saboda gaba d’aya jikinta sun yi mata jjina jina.” Ba wanda ya iya tanka musu dan an san halinsu, haka nan matar ta kama Anty Zainab wadda take tafiya da kyar ta jata sukai waje Mutane ma aka fara watsewa. Wani tsohone ya kasa hak’ura ya juyo ya kalli Umma yace “K’anwar Mijinki ce fa! Kuma k’awarki tun kuna Yara saboda Allah idan ke kin daketa ai bai kamata ki bar y’arki ta d’aura ko da yatsa a jikinta ba. Wannan rashin sanin ya kamata har Ina? Ki bi duniya a sannu fa, Sadiya.” Yunk’urowa ta yi zata yiwa tsohon rashin mutunci wasu samari biyu da suma basu kai ga fitaba suka yo kansu d’ayan ya ce “Kun san Allah In rashin d’a’a ne mu har certificate muke bayarwa! In kuma kanku na hayak’i to ku tanka mu gani” Shiruuu, suka yi ba wadda tace uffan. Girgiza kai kawai tsohon yayi ya juya ya fita. “K’ananan marasa kunya kawai” Samarin suka ce kafin su juya su fita, daga nan aka watse aka barsu su biyu suna huci. Su Baaba Talatu suna tsakar gidansu na ciki wajen d’akinta a kan darduma gaba d’ayansu hankalinsu a mugun tashe dan yanzun nan aka shigo da results d’in tests d’in da aka yi wa Baba! Suna a haka aka shigo da Anty Zainab. Da sauri Ya Jamilu ya mik’e ya k’arasa kusa da matar yana tanbayarta “lafiya?” Dan su da farko ma basu gane Anty Zainba d’in ba saboda gaba d’aya fuskarta jini ne. Tiryan tiryan matar ta koro musu bayani tun daga kan ihunta da ta jiyo da yanda idanuwanta suka gane mata Sadiya da Jalila a kanta suna jibgar ta. A hankali Shuwa ta mik’e ta k’arasa ta kamo hannun Anty Zainab ta cewa matar “an gode” Matar tana fita Baaba Talatu ta rarumi mayafinta! Da sauri Kaka ya mik’e yace “ina za ki je” Fashewa ta yi da kuka cikin kukan tace “Kar ka hanani. Na rok’eka da girman Allah kar ka hanani ci ma Sadiya yau! Duk abubuwan da take yi bana magana yau kam ta kaini bango wallahi.” Kallonta kawai Kaka yake yi kafin cikin b’acin rai yace “Laifin waye Zainab taje gidanta ta zauna?” Ta bud’e baki kenan zata yi magana ya d’aga mata hannu yace “Dan Allah ki barmu mu ji da Usman yanzu! Shuwa ku wuce ciki ki taimaka mata ta gyara jikinta ku kyale Sadiya kawai! Kuna ganin halin da Mijinta yake ciki ai amman wani lokacin sai ta yi kwana biyu ma bata lek’o shi ba! Ku zuba mata ido ita da y’arta zan samu lokacinsu kwanan nan.” A hankali Shuwa ta jaa Anty Zainab suka shiga ciki Baaba Talatu ma tabi bayansu tana sharar kwalla. Kaka kuma da Ya Jamilu suka koma inda Baba yake zaune yanata faman zubar da hawaye. Sai da aka had’a da allurai da magungunan bacci tukunna Anty Zainab ta samu ta iya runtsawa a ranar. Washegari kuwa sai da Shuwa ta yiwa su Khadija da gaske tukunna suka hak’ura amman da cewa suka yi sai sun je sun samu Sadiya da Jalila sai dai a tashi gidan wallahi! Daman chan ita Khadija basa shiri da Jalila kwata kwata. Da yamma bayan su Khadija sun wuce, Mama da Shuwa suna zaune suna kallo Baaba Talatu ta shigo. Yanayin ta kad’ai yasa Shuwa ta fahimci abunda ya kawota a hankali ta lumshe idanuwanta ta bud’e sai kuma kawai ta mik’e ta bar wajen. A hankali Baaba Talatu ta k’arasa inda Mama take ta zauna sannan ta amsa gaisuwar da Maman take yi mata da fara’a, sai da suka gama gaisawa tukunna ta mik’a mata takardun hannunta da ta shigo da su. Kallonta Maman tayi kafin ta kalli takardun sai kuma tasa hannu ta karb’a ta fara karantawa..... Tabbas ta sha wahala a hannun Baba amman ba k’aramin tausayinsa ta ji ba. A hankali tace “Allah sarki Ya Usman” wasu hawaye suna zubo mata. Hannayen ta duka biyu Baaba Talatu ta kamo kafin tace “Dan Allah dan Annabi Maryam Ina neman alfarma a wajenki… Usman bashi da lafiya dududu sauran mishi bai kai shekara ba! Ya nemi a maida aurenku dan yanaso ya mace a matsayin Mijinki.. Na san Usman bai kyauta miki ba! Na’am ya yi laifi amman a halin yanzu bashi da maraba da babu. D’an lokacine wanda ba zai ma kai shekara ba kawai za ku yi tare. Dan Allah Maryam.” Kasa magana Mama tayi Sai da Baaba Talatu ta sake cewa “Maryam” Tukunna ta juyo a hankali tace “Baaba dan Allah dan Annabi kar ki rok’eki abunda ba zan iya ba! Ki yi hak’uri amman a gaskiya wannan alfarmar taki ta yi tsauri da yawa.” Bayan kwana biyu, Baaba Talatu ta sake dawowa. Sun dad’e suna magana da Mama… Haka kurum kamar almara Mama ta samu su Madu tace “ta amince da auren Baba! Tunda ya rok’i yana neman alfarmar ya mace a matsayin Mijinta to zata yi mishi hakan a matsayinshi na wanda take kallo kamar d’an uwa” Ba yadda ba su yi da ita ba amman fur!! Tace “Ya Usman kamar d’an uwa yake a wajenta dan haka zaata zauna da shi na shekara d’ayan ba komai.” Ba dan sunso ba suka amince saboda sun riga sun yi alk’awarin ba za su sake tilastamata ko su sakata tayi abunda bata so ba. Sai dare Shuwa taje ta sameta, cikin son fahimtar da ita ta shiga yi mata nuni da yadda Abba yake ta faman zirya…. A hankali Mama ta yi murmushi kafin tace “Hajiya ni fa dama na gama yanke shawarar ba zan koma gidan Abba ba” Da mamamki Shuwa take kallonta. A hankali ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace “Jin ku kawai nake yi Hajiya, amman yanzu tashi d’aya in na koma cewa za ai kamar Ina jira matarshi ta mutu ne. Sanann ko bayaga hakama na riga na gama deciding in dai ba Mahaifinsa bane ya amince da ni to ba zan tab’a komawa ba, ina so Mahaifinsa ya nema mishi aurena kamar yadda ko wanne uba yake yi wa d’ansa sannan ya yi welcoming d’ina cikin zuri’arshi, ya karb’eni a matsayin surukarshi kamar yadda ko wanne uban Miji yake yi wa matar d’ansa... ....na san hakan ba zata tab’a kasancewaba ni kuma In ba hakan yayi ba to ba zan koma ba! Kinga kuwa babu batun maida auren mu ni da Abba dan na san Mahaifinsa ba zai tab’a amincewa ba sannan ba zai yi waennan abubuwan da nake kwad’ayin inga yayi min ba. Shuwa za tayi magana Mama tayi saurin d’aura hannunta a kan bakinta ta ce ‘dan Allah ta yi shiru, a bar maganar’ Saboda ita kanta daurewa kawai take yi. CONTINUATION!. Driving Aslam yake yi cikin nutsuwa, har suka isa MT estate ba wanda yace k’ala! Dan kowa akwai abunda yake tunani… A cikin gidan Granpa ya yi parking, da sauri driver d’inshi ya k’araso ya bud’e mishi motar ya fito cikin kamala suka nufi cikin gidan direct. Ba kowa as usual, har chan sama suka wuce tare.. A hankali Granpa ya d’an kalleshi ya ce “ka fad’awa su Yusuf Ina buk’atar ganin kowa da kowa anan after isha” “Okay Granpa” Aslam d’in yace daga nan Granpa ya nufi personal parlourn shi wanda zai sadashi da bedroom d’insa. Da mugun sauri Aslam wanda yake ta faman kame kame ya na rarraba ido ya fad’a d’akin Gramma..... A zaune ya tadda su suna hira su biyu. Da sauri duk suka d’ago suna kallon k’ofar ganin yadda ya afko. Dariya Gramma ta yi kafin tace “K’araso mana” Sannan ta mik’e tace “Granpa ya dawo ko? Arshaad yace tare kuka fita” “Eh yana d’akinsa” ya bata amsa sannan yad’an russuna ya gaida ta cike da ladabi. Sai da ta k’arasa bakin k’ofar tukunna ta d’ago kansa ta amsa sannan tace “Sannu da zuwa, ya hanya?” A hankali yace “Alhamdulillah” Yana d’an satar kallon inda Huda take zaune ta sunkuyar da kanta. Murmushi Gramma tayi sannan ta sa kai ta fice ta ja musu k’ofar dan ta lura idan ta ci gaba da zama a d’akin Aslam na iya zuwa ya rungumo matarshi a gabanta. A hankali ya ke takawa har ya k’arasa inda take ya tsugunna a gabanta. Da sauri ta lumshe idanunta ta fara k’ok’arin nemo nutsuwa da lakkar jikinta dan ta gaza samunsu. A hankali ya kamo hab’arta ya d’ago da fuskarta yana kallon yadda ta runtse idon da k’arfi!. Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace “I miss you.. Sosai!!!” Bata bud’e ba kuma bata yi magana ba, tana nan a yadda take. A hankali ya fesar da numfashi yace “Ko you still need more time?” Sai a lokacin ta bud’e idanunta da suka d’an tara hawaye tace “Moree time for?” Ba tare da ya bari ta jaa numfashi ba yace “Us! More time for us.. ranakun da na baki sun yi miki kad’an ko?. I was so eager to see you amman ke naga ko murna ma ba ki yi da ganina ba” A hankali yana kallonta yace “ko arzik’in sannu da zuwa ma ban samu ba. Ya fad’i hakan yana d’an cika hab’arta sannan ya gyara zaman shi yana fuskantar ta. Da sauri ta yi k’asa da kanta tana jin yadda k’irjinta yake dukan uku uku. A hankali ta ji ya ce “Umm??” Cikin wani kalar yanayi da siga. Sai da ta sake yin k’asa da kanta tukunna tace “Ina wuni, ya hanya? Ya aiki?” Ajiyar zuciya ya fesar kafin yace “Lafiya, hanya Alhamdulillah Aiki kuma, was terrible! Na d’an samu matsala har ya kai ga an rufe company d’ina na chan.” Da sauri ta d’ago ta kalleshi kafin tace “Subhanallah. Garin yaya?” Ya ji dad’in yadda ta damu da alamarin ba kad’an ba. A hankali ya d’anyi murmushi cikin son kawar da zancen company d’in yace “Don’t worry, ba komai. Ai inada wani ni da Abba.. Daman bawa ya kan samu abu at any time kuma ya kan rasa, wannan yana daga cikin k’addarar bawa, fata kawai shine ya zamo mai yarda da k’addara mai kyau ko marar kyau” A hankali ya sa hannu ya kamo nata yace “wata biyu baya!, Ubangiji yayi mini kyautar da sai da na suma tsabar farin ciki! Ya bani abunda na riga na fidda rai da samu, Amma yanzu ace dan na rasa company sai in damu?” Yayi mata tambayar yana wani sassanyan murmushi. A hankali k’irjinta yana wani mahaukacin racing tun da ta fara jin bayaninsa, ta d’ago tana kallonshi. Har yanzu murmushi yake mata. Wasu hawaye ne suka zubo mata dan ta so ta fahimci inda ya dosa! Cikin son fahimtar da shi da kuma kawo k’arshen bagwaren relationship d’in nasu a hankali tace “Ya Aslam shike nan yanzu Granpa zai sake cewa ni bad luck ce kenan” Sai kuma ta sunkuyar da kanta da sauri ta fara share hawayenta. Shi da farko ma bai fahimceta ba saboda yadda ya shagala da kallon lips d’inta, sai da yaga ta fara kuka tukunna yad’an dawo dede sannan ya fahimceta! Dariya ma shi ta basa dan haka a hankali yayi y’ar dariya kafin yad’an matse hannunta wanda yake a cikin nashi yace “In ya fad’i hakan, sai yaya?” Da sauri ta d’ago tana kallon yadda yake mata wani murmushi mai tsada! Cikin zubar hawaye tace “Masoya ma wasu in sun lura zaman su tare zai na causing problem hak’ura suke yi da juna, ballantana kuma mu. Tun kafin abu yayi nisa azo tun Granpa yana magana shi kad’ai har kowa ya fara gara kawai mu rabu da juna Ya Aslam ka samu wadda kake so ka aura nima in........” Da sauri ya d’aura d’ayan hannunshi akan lips d’inta yace “shhh…” Bai jira jan lokaci ba yace “Ni already na samu wadda nake so Hudatie bana jin kuma zan sake son wata a gaba sai dai wani ikon Allahn. Tunda Allah ya bani ke ya gama mini komai.” A hankali ya cire hannunsa a lips d’inta ya yi cupping fuskarta a cikin palms d’insa biyu ya d’ago da kan da take ta k’ok’arin b’oyewa yace “open your eyes”. Gam!! Haka ta sake runtse idanuwan nata k’irjinta na dukan uku uku da wani kalar mahaukacin sauri. Cikin matso da fuskarsa daff da tata ta ji yace “Open your eyes before i kiss you!” Da sauri ta ware idanuwan nata tarr! Ta zuba su a cikin nasa….. Kallonta yake yi itanma shi take kallo ta ji yace “I love you” Da sauri ta runtse idanunta sai kuma hawaye sharr! Kamar an bud’e fanfo.. A hankali cikin kuka still yana rik’e da face d’inta tace “Ya Aslam dan Allah kar ka yi haka. Za aga kamar daman chan muna son juna. Za a ganmu kamar butulu. Ba sona kake yi ba, idan muka rabu ka had’u da true love d’inka zaka fahimci hakan. For now dan Allah let’s just end this relationship............” Muryartace ta mak’ale sakamokon had’e bakinsu da yayi waje d’aya!…. Wani Irin salo ya shiga aika mata da shi wanda ya kusan tarwatse kwakwalwarta. Sai da ya ji tana shirin sume masa tukunna ya janye a hankali ya bud’e rinannun idanuwanshi, yana maida numfashi, a hankali yace “Those this feel fake?” Fashewa tayi da kuka ta fara k’ok’arin kwace fuskarta amman yak’i bata dama Instead ma kawai sai ya janyo ta izuwa jikinshi yayi hugging d’inta ya shiga shafa bayanta alamun rarrashi yayinda zuciyoyinsu suke bugawa a tare da mugun k’arfi...... Jin yanda take kuka sannan ta ma k’i ta saurareshi yasa ya cikata a hankali yace “ki gayawa su Shuraim Granpa yana son ganin kowa after sallar isha.” Yana gama fad’in haka ya mik’e ya fice dan yaga kamar tana buk’atar fitar tasa...... BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 67 Mikiya Writers Association. Tunda Baba Bashir ya shiga gida yake ta faman kai kawo, ba wai tunani yake akan wa Mama zata aura tsakanin Baba da Abba ba a’a tunani yake yi ta yadda zai fahimtar da Baaba Talatu dan already ya gama deciding tunda dama Mama tace ‘saboda Granpa yasa ba zata koma ba’ Gashi kuma yanzu Granpa d’in ya zo da kansa to kuwa in sha Allah ba zai yi k’asa a guiwa ba sai yaga an d’aura auren Mama da Abba. Kawai shi yanzu damuwar shi Baaba Talatu ce dan ko jiya da kyar tayi bacci! Halin da Baba yake ciki ya tada mata hankali ba kad’an ba so take kawai taga farin cikin shi ta ko wacce hanya tsananin tausayinsa take yi. Ya dad’e yana nazari kafin ya d’au hanyar d’akin da Baba yake jinya dan yana ganin gara su fara maganar da shi tukunna. Yana zuwa ya d’aga hannu kenan zai tura k’ofar ya ji suna magana shi da Ya Jamilu.......... MT ESTATE. Kamar yadda Granpa ya buk’ata, ana fitowa a masallaci su Abba suka bi bayanshi zuwa gidansa.. A nan parlourn suka tarar da Mommy Mammy Gramma Huda da Aaima. Ko ciki bai shiga ba ya nemi waje ya zauna a kan cousion ya fara bin ahalin nashi da kallo one by one waenda suke nan jere a gabanshi wasu a kan kujera wasu a kan kafet. Ajiyar zuciya ya sauk’e sannan ya kalla Aslam yace ‘ya bud’e taro da addua’. Cikin nutsuwa ya jagoranci adduar suka yi suka shafa tukunna Granpa ya gyara zama yace “Abubuwa uku! Zuwa hud’u ne suka sanya na taraku a nan. Na farko Aisha, Kafin Zainab ta cika ta rok’eni akan in tayata neman yafiya da gafarar ki! Sannan nima in nema yafiyarki dan tabbas an zalinceki a baya, da fatan za ki yafe mana.” Ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e a hankali tace “Komai ya wuce. Na yafe na manta da komai Allah Ubangiji ya ji k’an Zainab ya sa tana aljanna Firdausi. Ahankali duk suka ce “Ameen”. Sai da Granpa yad’an lumshe idonshi ya bud’e tukunna ya kalla setin da Abba da Daddy suke yace “Yusuf, Yakubu, kuna iya dawowa estate anytime from now. Komai ya wuce.” A hankali Dad wanda tunda suka zauna yake ta k’ok’arin ganin bai bari kwallarshi ta zubo ba ya sa hannu ya goge hawayen da suka samu nasarar zubo masa. Ahankali kamar had’in baki su duka ukun suka ce “Alhamdulillah” A fili, kafin Daddy ya ce “mun gode Granpa Ka yi hak’uri ka yafe mana.” D’an guntun murmushi yayi kafin yace “Ni za ku yafewa Ina neman.....” Da sauri Abba ya katseshi ta hanyar cewa “Dan Allah kar ka rok’emu yafiyar komai, kai Mahaifinmu ne kuma d’an Adam ajizi ne, kasancewarka Mahaifin mu ya sanya tun kafin ka yi mana wani abun ma mun riga da mun yafe maka! A Yanzu ba abunda muka fi buk’ata kamar yafiya da albarkar ka saboda tabbas na san mun kwashi zunubi ata dalilin k’ok’arin mu na ganin mun nuna maka daidai. Ka yi hak’uri Daddie a ko da yaushe zan baka hak’uri ne in yi ta baka hak’uri har k’arshen rayuwata” Ya k’arashe maganar hawaye suna tsilalo masa. Mik’ewa Granpa yayi ya k’arasa inda yake ya kamo hannunshi ya mik’ar da shi tsaye sanann yace “Magana ta uku, na amince maka ka auri Maryam! Na yi accepting d’inta sannan ina yi maka albishir d’in d’azu mun je ni da Aslam na nema maka aurenta da kaina kuma an baka! Ka zab’i gida d’aya a cikin gidajen estate d’innan ko wanne yayi maka ka gyara mata dan iyayenta sun ce anytime from now za su nemeni akan batun d’aurin auren. Sannan Aslam shima ya zab’i d’aya su zauna shi da matarsa Huda! Allah yayi muku albarka.” K’ok’ari Abba yake ya rik’e kukan da ya taho mishi amman sam ya gagara! Dan haka kawai ya rungume Granpa a jikinshi ya sa kuka kamar wani Yaro. A hankali Granpa yake murmushi mai had’e da dariya kafin yace “So kake ka k’arasa ni ne, Abbana.” Wannan karon hatta Gramma sai da ta sa kuka….. A tsakaninsu Abba Dad Mommy Daddy Gramma sam aka kasa samun wanda zai lallashi wani. A hankali Daddy shima ya taso yazo ya rungume su su biyun duka, haka shima Dad yana hawaye yace “ba za ayi babu ni ba” Ya k’araso shima yayi joining hug d’in yana dariya. Gramma ce ta ce “Kar fa ku kadashi k’asa” Tukunna suka cikashi suna murmushi, Dad ya ja mishi k’aramar kujera mara nauyi ta study ya zauna akai, tukunna suma suka zauna. Sai da parlourn yad’an yi shiru tukunna Granpa ya ci gaba da magana “I was wrong! Duk tsahon wannan lokacin ina kan ba dai dai ba Allah ya ji k’an Zainab Ita ta fara nasarar nuna min gaskiya sanann bayan dogon nazarin da nayi na fahimceta.” Shiruu, ya d’anyi kafin ya cigaba da magana “Na san dukkan nin ku anan kun san yadda nake jin Zainab a raina, ba abunda yake d’aga min hankali irin in na tuna she was killed! Sanann by an insider.” Tsit!! Parlourn ya d’auka ko k’arar numfashi bakaji. Kafin Granpa ya ci gaba da magana “Tun ranar da ta rasu nayi alk’awarin sai na yi punishing killer d’in no mattaer how smart he or she thinks they are! Dole zan yi bincike in nemo su kuma zan hukuntasu dan ba zan yarda jinin Ummi ya tafi a banza ba. 30 days guda aka yi ana binciken caterers da waiters d’in da suka yi serving da girkin abincin birthday and an gano basu da hannu a ciki, sannan an binciki masu gadi kuma an bincika akan ko sun ga wani abun shima bamu samu komai ba shiyasa nace muku its an incider! Therefore bincike zai fara daga yau yanzun nan! Ku yi hak’uri amman dole kowa ya amsa tambaya sannan ayi investigating d’inshi including me. Daga nan banaso inga k’afar kowa a mansion d’in chan inda incidence d’in ya afku har sai an gama komai.. Menwhile, Aslam” Granpa ya kira sunan Aslam yana kallon sa. A hankali ya d’ago idanuwanshi ya kalle shi sannan yace “Naaam Granpa” Sai da ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace “Ka je first building by your left akwai bak’i a parlourn k’asa, ka taho da su nan.” A hankali cikin girmamawa Aslam d’in ya mik’e ya fice… Ba a yi 20 minutes ba suka shigo shi da wasu maza su biyar!! ……..Da kyar suka had’iye yawun da ya tokare musu mak’oshi, In banda “innalillahi wa innailaihirrajiun” ba abunda suke maimaitawa a tare!……. Gaisawa bak’in suka yi da Granpa kafin yace “Bismillah, you can start.” Ta kan Granpa suka fara… Tambayoyine suka yi masa akan relationship d’inshi da marigayiya sannan when last ya ganta? Akwai misunderstanding d’in da ya tab’a had’asu? Akwai wani secret ko magana da ta tab’a gaya masa? Ta tab’a gaya mishi sun yi fad’a da wani ko wata a cikin estate d’in? d.d.s………. Daga nan suka d’auko wani abu kamar na tomb print amman babba suka ce “ya d’aura hannusa akai duka gaba d’aya biyun” Hakan yayi, sai da hoton palm da yatsunsa suka fito a kan fuskar computer da suka jona a jiki tukunna sukayi gaba. Gramma ce next suna gamawa da ita sai Daddy sai Dad sai Aslam, Sudais Shuraim Arshaad Aaima tukunna Mammy sai ta kusan kuka dan yana yin yadda suke tambayar tasu ko kana da gaskiya sai ka rikice kafin wani ya rufe baki wani ya jeho maka wata… Da akazo kan tambayar ‘ta tab’a fad’a mata sun yi fad’a da wani?’ A take ta hau zuba tana bada labarin yadda Abba baya sonta sannan ta tab’a ce mata sun yi fad’a da huda! Yana yin maganar tata yasa kawai d’ayan ya tsayar da ita ya d’anyi y’an rubuce rubuce akan takardar ta yace “shikenan. Ta d’aura hannayenta”. Successful suka yi suka gama da Abba da Huda sannan d’ayan ya kunna computer ya ajjiye a gabansu, ga mamakinsu sukaga Mom da Auwal suma ana yi musu nasu binciken exactly kamar yadda akayi musu. Ana gamawa suka yiwa Granpa sallama suka fice. Suna fita tun kafin Granpa ya fara magana Arshaad ya kalli Granpa d’in yace ‘Please idan an gama yana so zai wuce, Yanada aiyyyuka da ya tara da yawa.’ Sai da Granpa yad’an yi shiru tukunna yace “Ok, you can go.” Yana fita aka yi addua aka watse kowa ya kama gabanshi….. A hankali Granpa ya tura k’ofar d’akin Gramma ya shiga, yana lura da ita tun d’azu kamar jikin ya motsa dan bata da lafiya dama gashi ta hanashi ya fad’awa kowa. Yana shiga da Hudan ya fara tozali tana daddanawa Gramma d’in k’afa dan zuwa yanzu kam ta gagara b’oye mata ciwon nata. Hudan tana ganinshi ta sauk’e k’afar Gramma dake a kan cinyarta sannan ta mik’e ta d’an russunar da kanta ta wuce ta fita. Sai da ya ga fitarta tukunna ya juyo ya fara takawa inda Gramma take nan kwance akan gadon ya zauna a inda Hudan ta tashi ya d’auki k’afafun nata ya d’aura akan cinyarsa! Tana k’ok’arin mik’ewa ya ce mata “Stay still”. A hankali ya shiga matsa mata kamar yadda yaga Hudan tanayi…… Sun d’an jima a haka kafin chan yace “K’afar dai? Ba kya feeling kwata kwata?” A hankali tace “Ina ji, ba kamar d’azu ba. Da k’afafuna na fita meeting na shigo nan fa d’azu” Ta fad’a tana d’an murmushi alamun so take ya bar maganar. Sai da ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace “Maijidda, ko wanne family fa suna da nasu issues d’in! Ba a kan mu farau ba, dan Allah ki kwantar da hankalinki. Kin dai ga yadda d’azu jinin ki ya hau da muka gwada a d’akina, gashi har ba kya feeling side d’in jikinki! Kar kije ki samu stroke fa, ki yi hkr ki rungumi k’addara komai zai dawo normal.” A hankali ta mik’e ta zauna sannan ta sauk’e k’afafuwan nata k’asa kafin tace “Daddie dole in damu. Ace wai a cikin zuriata an samu killer! Taya kake so in kwantar da hankalina? Bayan ban san k’arshen wannan musibar ba… Suma fa y’ay’a za su haifa kuma mugun hali da bak’ar zuciya jini yake bi, sannan Ina tsoron idan zance ya fito kar zuriar Ummi suma su zuciya su yi tunanin d’aukar fansa bayan sun girma duk da kuwa ba Mahaifiyar tasu aka so a kashe ba.” Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin ta cigaba da cewa “Daddie dan Allah idan result ya fito, aka kawo muka ga wanda muke zxargi d’inne Dan Allah karka baiyyana sunanshi a gaban kowa dan Allah.” Ajiyar zuciya Granpa ya sauk’e kafin yace “That! I cant promise you Maijidda. Saboda dole In cire rotten seed a cikin family d’ina… An yi masa laifi tabbas amman hakan ba zai sa In hak’ura in bar killer d’in Ummi ya tafi free ba! I’m sorry amman inaso kar ma ki sake yi min maganar nan dan Allah, saboda itace alfarmar ta biyu da na ce miki daman ba zan iya yi miki ba bayan mallakawa mutum d’aya a cikin su MT.” A hankali Gramma ta sa hannu ta share hawayenta… Ajiyar zuciya ya sauk’e sanann ya d’an matsa ya rungumota izuwa jikinsa ya shiga lallashinta da kwantar mata da hankali. Sai da yaga ta d’an dawo dede tukunna yace “Yarinyar nan har yau tana nan? It’s like a nan take dan tare nake ganinku” Murmushi Gramma ta d’an yi kafin tace “Ai har nan surukarta ta zo sata tafi da ita amma tayi ta kuka. Ranar ina jinta tana waya kamar da y’ar uwarta ne na wajen Maman ta wai ‘In ta biyewa Aslam suka shantake da juna mutane za su ga kamar daman chan tana sonshi!’ Wai ‘za ayi mata kallon butulu’. Murmushi Gramma ta sake yi kafin taci gaba “Ni wallahi dariya ma ta bani”. Girgiza kai Granpa yayi kafin yace “Dariya ko abun haushi? Wanann ai shirme ne! Ita zata ke maida hannun agogo baya.” Yana gama fad’in haka ya mik’e yace “Zan yiwa Aslam magana ya zab’i gida zuwa gobe ya zo ya d’au keys, da sassafe ki shiryata ki kaita gidanta in yaso aa gyara a yi mata jeren suna ciki.” Yana gama fad’in haka ya juya ya fita, da alamun ransa shima duk a dagule yake.” Ajiyar zuciya Gramma ta sauk’e kafin ta mik’e ta d’auki wayarta ta danna kiran Mommy... Washegari da safe, kamar yadda Granpa ya buk’aci Aslam yazo ya karb’a keys haka aka yi… Yana zuwa bayan sun gaisa ya cewa Granpa d’in ‘kawai ya zab’a mishi duk wanda yake ganin yayi Ya gode Allah ya k’ara arzik’i.’ Murmushi Granpa yayi yace “okay” Sannan ya mik’e ya shiga ciki. Makullin d’aya daga cikin gidanjen da ba’a tab’a bud’ewa ba ma ya d’auka ya fito. Ya na fitowa ya gaya mishi gidan da number ya mik’a mishi. Karb’a Aslam d’in yayi ya sake yin godiya, yana shirin mik’ewa Granpa d’in yace “Ku yi sauk’a. Gidan sabo ne, ba a tab’a shiga ba. Sannan yanzun nan Gramma za ta kawo maka matarka In yaso sai a gyara gidan tana ciki kawai ayi furnishing.” A hankali Aslam yad’an russunar da kai yace “na gode”Sannan ya mik’e ya fita. Da murmushi Granpa yake kallonshi har ya b’acewa ganinsa. Ya so bashi dariya yadda yaga kamar ma yau d’in kunyar sa yake ji, zai so ya ganshi tare da Abba yau d’in yaga ya zai yi…. K’arar wayarsa ce ta katse masa tunani. Ganin number yasa ya d’aga ya kara a kunnenshi ya yi shiru. “Assalama alaikom” Baba Bashir yace. Ba tare da ya fahimci waye ba yace “Ameen Wa alaikummussalam” Ajiyar zuciya Baba Bashir ya sauk’e kafin yace “Kaka ne. Daga b’angaren Maryam Madu, yanzu Arshaad yayi min texting numberka” “Okay, okay” Granpa yace yana gyara zama kafin yace “Ya iyali?” “Alhamdulillah” Kaka yace sannan ba tare da b’ata lokaci ba yace “Na kira ka ne domin in sanar da kai cewa a duk lokacin da kuka shirya kuna iya zuwa a d’aura aure.” Sai da Granpa ya lumshe idanuwanshi ya bud’e tukunna yace “Weekend Saturday! Rana ita yau, in sha Allah za mu shirya komai…mu zo.“ “Okay Na gode” Baba Bashir yace. Murmushi Granpa yayi yace “Mune da godiya, sai mun had’u” Daga nan suka yi sallama suka tsinke kiran. Ajiyar zuciya Baba Bashir ya sauk’e. Yana ajjiye wayar ya juya da niyyar fita su ka yi kicib’is da Baaba Talatu! A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya kafin ya fara k’ok’arin wuceta domin ya fita. Da sauri ta tareshi ta hanyar shiga gabanshi, ta fara hawaye sannan tace “Mai yasa za ka yi haka? D’an shekara d’ayan da zai yi da mu shi kake neman maidawa sati d’aya? Dan na tabbatar muddin aka d’aura auren Maryam a gaban idonshi to tabbas a ranar zai cika!. Ka barsu mana, ita kanta Maryam d’in ta amince ta tausayi masa.. Nan da shekara d’aya ma fa ba zaka sake ganin Usman a doran k’asa ba.” Sai da Kaka ya runtse idanuwanshi tukunna ya bud’e yace “Ke mahaifiyarsa ce, ki daina yi masa baki haka Usman ba inda zai je in sha Allah.. Bari kiji in gaya miki d’azu na je akan In fahimtar da shi ya hak’ura kawai tunda har ga Granpa ya zo da kanshi, ina zuwa k’ofar d’akin nasa kin san me na ji suna tattaunawa?” Cikin share hawaye Baaba Talatu tace “Amman dai ko meye ne ka ji ai a ganina bai shafi..” Cikin d’an fad’a fad’a yace “Ki amsani kawai! Kin san me na ji suna tattaunawa?” A hankali ta girgiza kanta alamun ‘A’a’ Sai da Kaka ya had’iye wani k’ululun takaici kafin yace “Akan maganar k’aryar takardun da suka yi na ji suna magana! For your information Usman garr!! Ya ke babu mutuwar da zai yi in sha Allah. So yake kawai Maryam ta koma gidansa ya cigaba da azabar da ita. Wallahi Talatu kunyar Yarinyar nan nake ji. Ban tab’a b’oyewa Madu wani abu ba amman tabbas zan b’oye masa wannan maganar idan shekara ta zagayo aka ga Usman bai mutuba mu ce Ikon Allah ne! Dan ban san ta ina zan fara ce masa Usman da Jamilu sun yi k’aryar ciwo da mutuwa a Usman d’in dan kawai su yaudaremu ya aure masa y’a ya ci gaba da azabtar da ita, ba. Ki dubafa ki gani tsabar ya san bai kyauta ba ya ma kasa fitowa a mutum yayi bikon ta dan bai san ta Ina zai fara ba! Sai da ya had’a da k’aryar ciwon mutuwa.. Wanne irin deceiver ne wannan Yaron???? Kiga fa duk abunda ya yiwa Maryam amma tashi d’aya ta hak’ura ta ji tausayinshi zata koma ta yi jinyar sa har ya koma ga mahalliccinsa alhalin shi yana nan yanata yaudarar ta da mu kanmu..” Cikin katseshi Baaba Talatu tace “Ai dan ba ka san ya muka yi da Maryam d’in bane, ba ka san ya akai ta yarda ba! Ba ka san me na ce mata tukunna ta yarda ba.....” Cikin tsananin b’acin rai ya d’aga mata hannu ya ce “Talatu!!!!” Jin yadda ya daka mata tsawa ya sanya ta nutsu ta sha jinin jikinta. A fusace ya fara magana “Ban damu da in san me kika ce mata tukunna ta yarda ba, tunda dai har ta yardan to ta yi proving kanta ba as selfish kamar ke da d’anki ba! Abu d’aya nake so in yi miki gargad’i akai ko kuma ince In umarceki ki yi… Ina so ki tsame hannuwanki a lamarin nan…ko da wasa idan kika sake yunk’urin had’a Maryam da Usman su koma su yi zaman aure wallahi!! Kin ji dai na rantse sai na datse igiyoyin aurena kaff! Da su ke a kanki!” A zabure ta ware idanuwanta tana kallonshi. “Tabbas!” Kaka yace cikin gasgasta maganar tasa sannan ya ci gaba “Tunda na lura son kan naki ya yi yawa.. Tun farko kike gwada son kai har yau kin k’i ki saduda Talatu Usman d’a ne haka itama Maryam y’a ce! Amman wani abun takaici tunda kike Talatu not once kika tab’a duba farin cikin Maryam kullum kawai ke Usman! Baki damu da kowa ba sai d’anki. Kamata yayi ace yanzu kin nuna masa tsananin b’acin ranki kallafa k’aryar mutuwa yayi amman kina k’ok’arin yin burus da al’amarin saboda..........” Shiru yayi sakamokon ido biyu da suka yi da Baba. A hankali cikin mutuwar jiki ya k’araso cikin d’akin ya durk’usa a gaban Kaka da Baaba Talatu ya fara hawaye a hankali ya ce “ku yi hak’uri, na san na yi laifi amman ku yafe min dan Allah kar ka bari su Abba su ji wannan maganar, tunda har ita Maryam d’in ta yarda zata koma kawai ku kyaleta, daga baya duk abunda.........” Marin da Kaka ya d’auke sa da shi ne ya sa ya yi shiru! Cikin tsananin b’acin rai ya ce “Usman inaso ka tattara kayan ka ka koma inda ka fito! Kuma kar ka kuskura ka dawo har a gama d’aurin auren Maryam a kaita gidan Abba! Dan na lura imaninka ya fara rawa so zaka iya yin komai. Ka tattara ku koma kai da Jamilu har a k’are tukunna ka dawo. And one more thing.. Ko ka san cewa y’arka ciki ta yi? Kuma Sadiya ta tura ta gidan su shi Yaron ta zauna ta yiwa kowa k’aryar tana gidan Hansai?? Baka sani ba ko? Badaban cikin ya zube ba na tabbatar da sai ta haifi shege a cikin zuriata!. Saboda kawai Yaron ya kasance mai kud’i shiyasa tsananin buri irin na Sadiya ta gwammaci jikata ta je ta haifa shege dan kawai ta dinga turo mata da kud’i! Kana nan sake da baki kana k’ulla ta yadda zaka dawo da Maryam instead of ka tsaya ka kula da iyalinka Usman!! Kaf y’ay’anka da matarka babu wanda za a kalla a nuna a yi alfahari da shi! Dan shi kansa Junaidu abun a bincika ne! Amman daga kai har Jamilu da ya kamata ace kun tashi kun tsaya akanshi kun yi bincike, kun zauna kuna k’ulla makirci da k’arya kamar mata! Kun zuba mana ido ni da Madu tsofai tsofai da mu mu za mu yi komai.. To Ina so ka sani nima yanzu ta kaina nake yi, abunda kawai zan yi focusing akai bayan d’aurin auren Maryam shine ibada! In samu in gyara tsakanina da Ubangijina kafin In koma gareshi.. Duk wanda yaga zai gyara iyalinshi to ya gyara wanda kuma ya ga ba zai gyara ba shi ya sani kar ya gyara ya zauna ya ci gaba da shirme yana biyewa so da buri. Abu d’aya zan yi maka na taimako da ga shi ba k’ari! Kasancewar Jalila y’a mace kuma yanzu na san tunda zance ya fara fitowa in an kwana biyu ba lalle ta auruba, dan haka zan rufa mata asiri In nema mata miji kamar yadda na yi da farko. A yanzu Mati ya riga ya cike ta hud’u if not wallahi da tun a jiya da Zainab ta bani labarin ta da tuni na aura masa ita. Dan haka yanzu zan bada sanarwa this time around ba a fili ba a b’oye saboda kar Sadiya tace na yi talla da y’arta kamar farko.. Duk wanda ya zo ya ce yana so daga nan zuwa ranar asabar rana ita yau to za a had’a a d’aura aurenta tare da na Maryam da Abba, in sha Allah.” Yana gama fad’in haka ya juya ya fita dan yana so ya sanar da Madu an saka rana. A ranshi ya gama rayawa ‘Ko Madun bai yarda ba wallahi sai dai kawai ya ga ana d’aura aure ranar Asabar! Ai Maryam bazawara ce yanzu sannan ba Yarinya bace ba, kowa ya san Abba take so ba Usman ba dan haka Madu bashi da hurumin yi mata dole’. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 68 Mikiya Writers Association. Tabbas Mommy taso ace ta gyara Huda kafin ta tare amman jin bayanin gramma yasa kawai ta hak’ura ta k’udurta a ranta zata had’ata da Gwaggo Asabe na kwana biyu. Allah yaso ta taho da wayarta dan haka ta d’auka ta danna kiran Ummu. Da sallama Ummu ta amsa kafin ta ce “Ina wuni Mommy ya gida” “Alhamdulillah Ummu ya Yaran” Mommy ta amsa ta. Sai da taji amsarta tukunna tace “To fa aikin gaggawa ya samemu.....” ………… Lokacin da ta shigo d’akin Huda na toilet tana wanka Gramma bata gaya mata komai ba daman ta fi so sai Mommy ta zo su yi mata bayani tare. D’aure da d’an guntun towel ta fito gashinta a jik’e gaba d’aya wani ya zubo ta gaba wani kuma yayi baya Yana reto yana d’igar ruwa. Sam bata ma lura da su waye a d’akin ba saboda duniyar tunanin da ta lula ‘Tabbas ko ta halin yaya ne yau dole ta je ta samu Mama! They definitely need to talk.. She can’t believe abunda Maman ta gaya mata jiya sannan Sakina ta tabbatar mata wai gidan Baba za ta koma! Mai ya faru? Ko dai gaba d’ayansu sun samu shigar aljanu ne! Dan in ba haka ba tayaya za ai ga Abbanta amma azo ace wai gidan wani Baba za ta koma! Granpa fa dakanshi ya je ya samesu…. Wanne irin abune wannan? Tun jiya ta kasa gane kanta har kawo yanzun nan…..’ “Dota” Mommy ta kirata tana d’an kallonta ganin gaba d’aya hankalinta baya a kansu. Firgigit! Ta yi ta d’ago, suna had’a ido kuma sai ta tuna da towel kad’ai ne fa a jikinta shima kuma guntu dan haka da sauri ta juya ta koma toilet d’in tana cewa “Mommy Ina kwana” Bata jira jin me za ta ce baa ta rufoo k’ofar ta shiga neman bathrub. Tana shigewa Mommy ta sauk’e ajiyar zuciya kafin a fili tace “Ko sai yaushe Hudan zata saba da ni kamar Maryam? Sai Allah.” Tana gama fad’in haka ta kalla Gramma tace “Bara in je In fara shiri kafin su Ummun su zo. Dan na san ba lalle ta iya sake fitowa ba balle ta sake mu yi maganar. “Ok” Kawai Gramma ta ce mata daga haka Mommy ta juya ta fita. Tana fita dede Hudan tana fitowa itama sanye da bathrub. Ba k’aramin dad’i ta ji ba ganin bata d’akin, dan har ga Allah tayi mugun jin kunya. Tana shirin nufar gaban madubi Gramma tace “Zo nan Huda” A hankali ta k’arasa ta zauna a gefen ta tace “Gani Gramma” Sai da ta sauk’e ajiyar zuciya tukunna tace “Shawara nake so in baki… Ki daina nunawa Mommy kamar suruka take a wajenki Instead ki d’auketa kamar Mama ki sake da ita. Tana matuk’ar k’aunarki, ki saki jinkinki ku saba sosai, za ki ji dad’in hakan. Magana ta biyu… Ki shafa mai ki jirani zan kawo miki kayan da zaki saka yanzu! Granpa ya ce akaiki gidan ki za a gyara kina ciki.” Da sauri ta d’ago ta kalli Gramma. D’aga mata kai tayi alamar gasgatawa sannan tace “In kuma kinada ja to mu je in raka ki wajensa” Ta fad’i haka tana d’an b’ata rai saboda ta lura In ba hakan tayi mata ba to fa sai an sha drama da ita dan gashi idanunta har sun ciko da hawaye. A hankali ta girgiza kanta alamun ‘a’a’ Sai kuma ta mik’e ta nufi gaban mudubi hawaye na bin fuskarta. Tana gama shafa man Gramma ta shigo da wasu had’add’un kaya riga da zani da alkyabbarsu sai kyalli suke yi sannan kamar wanda aka yi design d’in edges d’in da gwal! Tana ajjiyewa ta juya ta fita. Bata dad’e ba ta dawo da kasko da wata robar Kaplas, sannan ta sake komawa ta d’auko kujerar tsugunno. Ita dai Hudan tana zaune kawai tanata binta da kallo dan tunda ta gama shafa man ta dawo kan gadon ta zauna ta yi shiruu tanata tunani. Gramma na gama shigowa da kayayyakinta ta sa kwaskon garwashin a k’asan kujerar sanann ta bud’e kaplas d’in… Wasu y’an k’ananan robobine masu murfi a ciki! Sai da ta bud’e kusan duka ta d’eba wannan ta d’eba wannan tukunna ta tara akan murfin roba d’aya, ta kalla Hudan tace mata “tashi” Sai da ta tashi tukunna ta k’arasa ta d’auko k’atoton bargon kan gadonta sannan ta dawo ta wareshi ta ajjiye a gefe kafin ta d’auki had’in da tayi na kan murfin robar ta zuba a cikin kaskon wutar ta saman kujerar tukunna ta umarceta da ta zauna da wuri. Sai da ta rufa mata k’aton bargon tukunna ta ce ‘ta kwance bathrobe d’in jikinta ta bata’ A hankali ta warware ta mik’a mata sai kuma ta fara k’ok’arin tashi dan wani zafi ne ta fara ji yana ratsa ta saboda hayak’in ya fara turnuk’e koina a cikin bargon. Sai da Gramma ta yi da gaske tukunna aka samu Huda ta zauna, har da hawayenta kuwa fuskarnan ta yi jajawur. Tana nan zaune suka ji ana knocking! Sai da Gramma ta kora mata warning d’in karta motsa tukunna taje ta bud’e k’ofar. Murmushi tayi sanann tace “Ashe ma kishiyar tawa raguwa ce nake ta jin tsoro? Shigo ki ga kuka wiwi a iya tsugunno kawai.” Tana jin murmushin Ummu ta fahimci itace, ai kuwa ta fara zillo tana lek’awa nan suka had’a ido. Tana shirin tashi Ummu tace “dalla zauna” Cikin sigar tsokana. Wani sabon farin cikin ta sake ji ya lullub’e ta sakamokon ganin Sakina sun shigo ita da mommy suna yi mata dariya suma. Cikin mutunta juna aka shiga gaggaisawa daga nan Gramma ta fita tace musu “Ku k’arasa shiryata dan ni kam ragwanta da shagwab’a take ta yi min”. Ummu ma da nata ta zo, dan haka bayan ta tashi a na Gramma sai da ta kuma wani zaman sannan kafin awa biyu suka sakata ta shanye tsumi wajen roba uku! Ita kam gaba d’aya ma fitsari take ta ji sai faman zaryar toilet take yi, da tayi magana kuma Ummu ta rufeta da fad’a! Dan ma Mommy tana d’an kareta. Sakina kam tana gefe kawai a zaune ta yi shiruu sai da murmushi kawai kamar ba Sakina ba. Aaima na zaune a parlour ita kad’ai tana karatun Alqur’ani Aslam ya shigo. Dama itan yake nema kuma yaci sa a ya sameta ita kad’ai dan haka ya k’arasa ya zauna a kusa a ita. Sai da ta kai aya tukunna ta d’ago tana kallonshi tana murmushi. Murmushi ya mayar mata kafin yace “Can we talk?” A hankali ta jinjina kai alamun ‘yes’. Sai da ya sauk’e ajiyar zuciya tukunna ya ce “Huda zata tare yau” Shiruu ta d’anyi ta sunkuyar da kanta. A hankali yana nazartarta yace “You are my only sister Aaima.. Relationship d’in dangin Miji da Matar wa yana lalacewa ne idan akai rashin sa’ar samun rashin jituwa tsakanin Sister’s d’inshi da Matar tasa! Ko da ace uwar Miji bata son surukar indai Sister’s d’in suna k’aunarta to su kan iya bata shawara a zauna lafiya kuma itama uwar Mijin in dai taga surukar tana jan y’ay’anta a jiki tou za a zauna lafiya. Ke ce mace a tsakanin mu duk kan mu har Auwal da da su Shuraim, although Huda is also our sister amman kasancewarta wife d’ina ya sa dole ta amsa sunan suruka a tsakaninmu Ni Ke Arshaad Mammy da Mommy… Mommy is morethan good with Huda being my wife amman ban san ke ko Mammy ba! Ke, za ki iya gyara tsakaninta da Mammy sannan za ki iya b’atawa but first Aaiima please Inaso ki goge haushinta da kike ji na zuwan Mammy cell tunda ba ita ta kaita da kanta ba, ina so ku koma kamar daa, Arshaad yace min kuna shiri sosai da farko ku zauna lafiya please hankalina zai fi kwanciya daga nan kuma sai ki yi aikin gyara tsakaninta da Mammy dan na san za ki iya.” Tunda ya fara magana Aaima ta yi shiru tana sauroronshi, sai da ya dire aya tukunna ta d’ago ta kalleshi tace “Ya Aslam, komai ya wuce. A b’angarena komai ya wuce, na yi maka alk’awari za mu koma kamar da ni da Hudan in sha Allah after all she’s my only sister sannan sister in-law.. Gaskiya Ya Auwal ya fad’a a ranar da zai wuce shi da Mom, kafin ya tafi, ya ce min ‘I really need to relax In daina biyewa duk abunda zuciyata ta yi karo da shi a karon farko na b’acin rai ko akasin haka! In bud’e idanuna da kyau! There is more to life than holding onto the past’ Agaskiya nima sai yanzu na fahimci ba laifin ta bane” Sai da ta d’anyi murmushi sannan tace “I owe her an apology, In sha Allah zan bata hak’uri wannan duk ba wata matsala bace In sha Allah. Ka kwantar da hankalinka Hudan and I will be good.” Ta fad’i hakan tana murmushi. Kamar kuma wadda ta tuna wani abun sai tayi shiruuu ta shiga tunanin, chaan! Ta sauk’e wata k’akk’arfar ajiyar zuciya kafin tace “Matsalar a nan shine Ya Arshaad! Ba zan b’oye maka ba Ina jin tsoron wani abu… Not that wai Ina tunanin Ya Arshaad bai hak’ura ba or something like that amman so makaho ne kuma inaso ka san cewa har gobe Ya Arshaad yana son Huda so mai tsanani!! Ban san abun yi ba ban san abun cewa ba saboda gaskiya ni kaina I’m confused and broken akan lamarin nan Ina tausaya masa… Jiya kusan a parlourn nan na kwana ba wanda ya sani saboda Ina so in kammalawa Ummi sauk’ar da nake yi mata a yau shiyasa jiya around 12 na sauk’o na fara karatu dan ina buk’atar chanjin waje… Da farko magana sama sama na fara ji, sanin da na yi cewa shi kad’ai ne yasa na k’arasa dan inji ko lafiya, sai da na je bakin glass door d’in naji ashe waya yake yi… A hankali na d’an tura na ganshi a tsaye a parlourn yana waya yana safa da marwa gaba d’ayan shi a rikice!. Yana gama wayar ya kama hanyar d’akinsa ya shige ni kuma na zuge na bishi a hankali na tsaya a bakin k’ofar d’akin! Wallahi Ya Aslam kukan da na ji yana yi sai da na tsorata!” Da sauri Aslam cikin katseta ya ce “Ki je side d’in Gramma Ku shirya ki raka Huda Ta shi ki je yanzu na san sun kusan kammalawa” Za ta yi magana ya ce “Aaima please, je ki! Ki mata rakiya Mommy ne kawai achan ata wajena”. A hankali ganin yadda idanuwanshi suka kad’a suka yi jaaa, ta mik’e ta ajjiye Alqur’anin akan side table ta nufi sama domin chanjawa. Tana shiga ta cire hijabi da y’ar kantin doguwar rigar da suke jikinta ta saka atamfa ta fesa turare ta d’au mayafinta ta fita. Har ta zo ta wuce bai ma sani ba! Ya rufe fuskarshi da tafukan hannunshi banda “innalillahi wa inna ilaihirrajiun” ba abunda yake maimaitawa cikin tsananin tashin hankali. Ya dad’e kafin ya samu kwakwalwar shi ta gama lissafi, a hankali ya mik’e ya nufi side d’in Arshaad, sai dai yana zuwa ya bincika koina amman babu shi ba alamunshi kamar ma babu abubuwan amfaninshi… Haka ya fito kanshi a hargitse ya nufi gidanshi dan yana so ya sallami cleaners d’in da suka gyara suka goge su tafi kuma yana so ya duba waenda suke sauk’a tare da shi ko sun gama nasu suma a samu su wuce kafin su Gramma su k’araso. Yana shiga ya tarar da su Dad da Daddy tare da masu gadaje anata faman jere… Cikin girmamawa ya shiga gaidasu yana mamakin su dan kusan komai an kawo. Daman kuma shima ya siya wasu kayan a nan Kano d’in saboda ba lokaci d’azu! Dan haka nashin ma suna isowa aka hau kafi..... Hudan na gama shiryawa Gramma tace “su tafi a kaita” Dede nan Aaima ta shigo. Cikin fara a suka gaisa da Sakina bayan ta gama gaisawa da su Ummu daga nan suka fito gaba d’ayansu…. A k’ofar gidan suka samu Junaidu a cikin mota a zaune, gefe guda kuma motar drivern da Mommy tace ya zo ya jira su, dan haka suka shishiga. Har cikin gidan Junaidu da drivern suka kaisu tukunna suka fito. Ummu ce rik’e da ita suna zuwa bakin k’ofar shiga tace “ta shiga da k’afar dama da bismillah” Anan suka tarar da su Dad da masu d’aura kaya.. Royal chairs har set biyu ta samu a parlourn k’asa da dining da tv stand da centers show glass duk komai na royal d’in. Dad ne ya ce ‘su kaita main bedroom na chan sama an gama shiryawa’ da “to” suka amsa daga nan suka nufi saman… Duk d’akuna biyun an gama kafa gadajen dan haka suka nufi nata d’akin. D’akin da gani Aslam ne ya sa furnitures d’in saboda favorite color d’inshi ne. Tsayawa fad’an had’uwar d’akin ma b’ata baki ne. A bakin gadon suka ajjiyeta suka yi mata Nasiha mai ratsa jiki daga nan Gramma da Mommy suka wuce Ummu ma ta mik’e ta tafi tace “Junaidu anjima zai dawo ya d’auki Sakina. Saboda kar taji shirun yayi yawa kafin a gama jeran Aslam ya shigo.” Da kyar kuwa Huda ta barta ta tafi itama Ummun har da y’ar kwallarta. Daga nan d’akin ya rage saura su uku Ita Aaima da Sakina. Suna gama fita Aaima ta mik’e ta k’arasa inda Huda take ta yaye mata hular alkyabbar jikinta tana murmushi tace “Amaryar Ya Aslam” K’asa Hudan ta yi da kanta tana goge hawayenta. A hankali Aaima ta sa hannu ta shiga goge mata hawayen sanann tace “Amaren yanzu fa basa kuka, haba mana kar ki bada girlss” Dariya suka saka gaba d’ayan su har ita Hudan tana d’an share hawaye tana dariya. A gefenta ta zauna suka sakata a tsakiya kafin tace “Kwanakin baya mun d’an samu misunderstanding… Uwa daban ce Huda, therefore i hope za ki fahimceni Sannan ku yi hak’uri daga ke har Sakina” Sannan ta d’an lek’a Sakinar ta ce “I know i was rude that day da kika kirani a waya, i shouldn’t have talk to yo.....” Cikin katseta Sakina ta ce “Haba Aaima, dan Allah ki manta da komai ya wuce, mun fahimci situation d’inki. You will lways be our big sis sanann kuma friend at the same time”. D’agowa Hudan ta yi itama ta d’an kalleta sannan ta ce “Ba komai Aaima ya wuce.” Ta yi maganar tana kamo hannunta. A hankali Aaima ta ce “thank you”. Murmushi suka yi dukkan su kafin Aaima ta ce “Sakina daman ina son ganinki. Na ma shirya zuwa inje In sameki sai kuma gaki yau Allah ya had’a mu.” Da mamaki Sakina take kallonta kafin ta gyara zamanta ta bata dukkannin attention d’inta” Sai da Aaima ta sauk’e ajiyar zuciya kafin ta ce “A kan Ya Auwal ne” Da sauri Sakina ta lumshe idanuwanta ta yi k’asa da kanta… Tun ranar da Huda ta ce mata ciwon zuciya gareshi shikenan ta rasa nutsuwarta Ta tabbata itama yanzu haka maybe ta kamu da nata ciwon zuciyar.. Aaima ba ta tsaya jira ba ta ci gaba da magana “Tun ranar da za su tafi mun yi magana da shi a kan ki! Sanann jiya ma sai da muka yi chattinga da Mom! Shi kam yama daina chat zuwa yanzu tun shekaran jiya da oxygen yake iya numfashi! Bar ganin muna raha a cikin gidan nan wallahi kowa kawai k’ok’artawa yake yi amman dukkanmu hankalinmu a tashe yake. Sakina na san Ya Auwal farin sani! Ba zan b’oye miki ba har dating d’inshi nayi… Tunda nake a rayuwata ban tab’a ganin Ya Auwal yana soyayya bilhakk‘I da gaskiya ba sai a kan ki! Kinga na farko Saboda ke ya shiryu, duk wani bad habit da yake yi yanzu ya daina. Sannan ranar da zai tafi duk wani abun da ya tab’a yi a company da sharrin da ya yiwa mutane duk sai da ya fad’awa Granpa! Ya nemi yafiya. Na uku, ki duba kiga mawuyacin halin da yake ciki! Duk fa a kanki ne fa Sakina. Wallahi na manta rabon da inga mutum yana tsananin rashin lafiya akan soyayya sai a lamarin ku! Dan Allah ki duba halinda yake ciki ki san abun yi tun kafin mu rasa shi. Jiya Mom cemin ta yi ciwon ya motsa jininsa ya hau ga ulcer! Sakina ki taimaka…. Ni ko number Ashraff d’inne ki ba ni, ni na san me zan gaya mishi.. Please Sakina.” Ta k’arashe maganar cikin karyewar zuciya. Da gudu Sakina ta tashi ta shige toilet ta rufo k’ofar… Tana shiga ta fashe da wani irin gigiceccen kuka. Ahankali Huda ta sauk’e ajiyar zuciya kafin ta ce “Me za ki cewa Ashraff d’in in kin samu numbershi?” Kawai zan rok’esa ne akan ya je ya ga halinda Ya Auwal yake ciki. Zan iya biya mishi kud’in jirgi ma kawai ya je yaga halinda ya ke ciki! Daga nan ya san abun yi. Wallahi Huda zan iya dafa alqurani akan Ashraff baya yiwa Sakina kwatankwacin son da Ya Auwal yake yi mata.” Ajiyar zuciya Huda ta sauk’e kafin tace “Kuma itama Ya Auwal d’in take so” Da sauri Aaima ta juyo tana kallonta sosai. Jinjina kai Huda tayi kafin tace “Ni dama na dad’e da fahimtar hakan. Tou kuma jiya Ashraff d’in ya sake tabbatar min… Ya min complain akan Ko kiranta idan yayi bata iya d’auka wani lokacin sannan In zata kira sunanshi sometimes sai ta ce masa Ya Auwal! Wani lokacin in ta fahimta ta yi saurin gyarawa. Kwata kwata bata bashi time.. Shine ya kirani akan wai In na samu time yana son mu yi magana face to face sannan kuma wai waye Ya Auwal?!”. Cikin rashin jin dad’i Aaima ta ce “To ai za su cuci kansu ne daga ita har Ashraff d’in! Kawai kamata yayi ta fito ta gaya mishi gaskiya shi kuma ya hak’ura.” A hankali Huda ta sauk’e ajiyar zuciya kafin ta ce “Bara in baki number tasa ku yi magana” “Okay ba ni” Aaiman tace tana mik’a mata wayarta. A hankali Huda ta zaro wayarta wadda ke nan rik’e a hannunta daga cikin alkyabbar jikinta ta bud’e ta juye mata nambobin Ashraff a wayar ta mik’a mata. Message ta tura mishi…. ‘yau an kai Huda gidanta so ba zata samu damar sauraronshi ba amman ta fad’a mata komai game da issue d’in da yake facing ta b’angaren Sakina! If he’s free ya zo su tattauna’. A hankali Huda ta mik’e ta k’arasa k’ofar toilet d’in ta fara yi mata knocking.. Ta d’an jima kafin Sakinar ta bud’e k’ofar ta fito a hankali tana tsane ruwan fuskarta da hannunta alamun ta wanke fuskar ne. Bata ce mata komai ba ta rab’a ta gefenta ta wuce.. Inda take zaune a kan gadon ta je ta gyara pillow ta koma chan k’arshe ta jingina da jikin gadon ta lumshe idanuwanta bata ma bi ta kan Aaima da take cewa “Yace gashi nan zuwa har ta bashi adreess” ba. Kamar minti talatin ya kira number Aaima ya ce “yana bakin estate d’in”. …….. Aiima bata yi minti ashirinba ta dawo. Tun da ta shigo suka lura da yadda jikinta ya yi sanyi over. A hankali ta nemi waje ta zauna a gefe ta yi shiruuu, ita kad’ai! Sai ta d’an yunk’uro za tayi magana sai kuma ta koma ta yi shiru, dan ita ba ma ta san ta ina za ta fara ba. Su dai su Hudan ido kawai suka dinga binta da shi kafin Huda ta yi k’arfin halin cewa “Aaima lafiya kuwa?” Dan suma yanayin nata ya saka su a rud’ani. Har ta yunk’uro za ta yi magana kamar farko sai kuma ta sake yin shiru kafin tace “ina zuwa” Ta fad’i hakan tana d’aukar wayarta. Gallery ta shiga ta hau bincike har ta nemo hoton da take nema! Kamar za ta mik’a musu sai kuma ta ce “Bara in baku wani d’an tak’aitaccen labari…… Akwai wata k’awar mu da muke department d’aya level d’aya d’aki d’aya da ita a Nile! Mu hud’u ne a group d’in mu, ni da ita da ragowar friends d’inmu su biyu tun farkon zuwanmu tare muke har yanzu da muka zo k’arshe.” Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin ta ci gaba “Wadda muka fi shirin da ita ita ce ‘Suhailat’ K’ut da k’ut muke ni da ita sosai. Akwai wani saurayinta da suke tare tun farkon zuwanmu Nile ta ce min tun a secondary school ta san Abokinsa tare suka yi makaranta secondary ajinsu d’aya! To irin sun d’an shak’u d’innan kamar besties haka suke. Wata rana Ina tunawa muna level 1 lokacin ya zo kawo mata ziyara (shi bestyn nata) sai suka zo shi da wani Abokinsa mai suna ‘Sageer’ Tun da Sageer ya kyalla ido ya ga Suhailat tashi d’aya ya ji yana sonta! Kasa ma hak’ura yayi mu koma a lokacin dayake ni na rakata, a take yake cewa Abokin nasa shifa ya ga mahad’in shi! Bai bar wajen ba sai da number da address d’in gidansu Suhaila na nan Kano. To ashe itama Suhailan duk kanwar ja ce dan muna komawa d’aki itama ta haukace mun haka nan ta dinga yabon kyawun Sageer d’in da had’uwar shi sanann ta sanar da ni yanda ya samu kyakkyawan gurbi a cikin zuciyarta. Kafin wata d’aya Soyayya da shak’uwa mai zafi ta shiga tsakanin Suhaila da Sageer... A Dawowar da nayi kafin exams lokacin bikinku da Ya Arshaad, kafin In koma wani mumunnan alamari ya afku ata dalilin rashin wayon Suhaila! Ta biyewa soyayya ta mallakawa Sageer kanta gaba d’aya bayan ya d’auketa sun je sun yi court marriage sai kace wasu marasa mafad’i! A cewar sa hakan zai sanya ta yarda da shi ta aminta ita zai rayu da har abada tunda ita a tsarin gidansu Mace sai tayi phd tukunna take yin aure! Haka nan Babansu yake da wannan muguwar ak’idar, shi kuma Sageer ya ce ‘in dai ita kad’ai zai so kuma ita kad’ai zai aura zai kula to ya kamata ta fahimci a yanayin tsarin halittarshi ta d’a Namiji ba zai iya yi mata wanann dogon jiran ba’. In tak’aice muku labari dai ciki yana yin wata d’aya ya baiyyana kanshi a jikin Suhaila! Dan tsananin laulayin da take yi ya sanya hatta matan dake gefen d’akin mu sai da suka soma fahimtar wani abu game da wannan k’addarerren cikin! Dan ta ce babu kalar protection d’in da ba suyi using ba. Ba yadda muka iya haka muka rufa mata asiri mu uku muka nufi asibiti da ita dan tace idan Baban ta ya san labarin wallahi na lahira sai ya fita jin dad’i! Yadda kika ga Granpa to haka itama Babanta yake da mugun tsauri! Kuma ita abun nata ma duka biyu za a iya cewa dan Mahaifiyarta itama hakan take da tsauri. Muna zuwa muka zubewa Likitan kud’i muka gaya mishi flushing muke so a yi mata duk da tanata ce mana ance ‘tana da matsala cikin ba zai fita ba’ Amman still muka zab’i mu gwada sa’ar mu.. Bayan y’an gwaje gwaje unfortunately Likitan ya zaunar da mu yayi mana cikakken bayani akan cikin nan ba zai fita ba! Saboda tanada matsala kuma in dai ance za a cire d’in tou it’s either ta mutu ko kuma ta samu uterus failure. Bamu da wani zab’in da ya wuce mu nemi Sageer duk da kuwa ta ce mana ‘tun last zuwanshi da ta ce mishi tana da ciki ya d’auke ta ya kaita asibiti aka gaya mishi abunda aka gaya mana! Kwana d’aya kawai yayi mata a gidan da suke had’uwa daga nan ya k’ara gaba kuma tun daga ranar ko wayarshi ta kira a kashe take jin ta. Although bai nuna mata komai ba dan faram faram ma suka rabu ko amai idan ta yi shi yake kwashewa ya gyara gurin yanata faman jera mata sannu’. Wani babban tashin hankali da abun al’ajabin da muka fuskanta shine Hatta gidansu Sageer da address d’insu da ya bayar a garin Gombe gaba d’aya fake ne! Hatta sunan Babanshi Alhaji Bashir mai galon da ya fad’a mana gaba d’aya k’arya ne. Har Gombe d’aya a cikinmu ta rok’i saurayinta ya je ya bincika mana amman babu abu d’aya da yake gaskiya a cikin labarin Sageer! Komai fabricating kawai yayi. Da muka fahimci haka sai muka koma wajen Bestien ta, to shima dai ta wajen na sa duk sammakal dan ce mana ya yi shima Iyakar wannan information d’in da muka sani akan Sageer shima shi kad’ai ya sani, ya ce a wajen ball suka had’u suka fara shiri suka d’anyi business tare ranar kuma suna tare ya ce masa zai je wajen k’awar shi shine yace zai rakashi. Shi bestyn nata ma cewa yayi wai ‘mu yi ta addua gaba d’ayan mu maybe aljani ko maye muka had’u da Allah ya tak’aita’.” Ajiyar zuciya Aaima ta sauk’e sannan ta ci gaba da cewa “To yau dai Allah ya had’ani da Sageer!” Bata gama rufe bakinta ba ta mik’a musu hoton data nemo a wayar tata tun d’azu……… Sakina ce ta fara karb’ar wayar tana kallonta kafin ta sauk’e idonta a kan wayar. A hankali Huda ta ce “Innalillahi wa innailaihirrajiun” Bayan itama ta l’eka ta gani. Sakina kuwa lumshe idonta kawai ta yi ta bud’e ta kalli Aaima idonta jazir tap kwalla ta ce “Aaima are you sure??” “Very sure Sakina! Ki yi ta sliding za ki ga pictures da videos d’insu kala kala irin wannnan shi da Suhaila. Daga nan ki gaya min Idan wannan bawan Allahn ba Ashraff bane ba.” BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 69 Mikiya Writers Association. Kai kana ganin fuskokinsu ka san suna cikin tashin hankali ba na wasa ba. Kallo suke suna sake kallan pictures d’in amman ba ta inda za su ce ba Ashraff bane ba. A hankali Sakina ta mik’a mata wayarta sannan ta ce “yana Ina?” Ta yi mata tambayar tana k’ok’arin mik’ewa tsaye. Cikin ruk’o hannunta Aaima ta ce “Ya tafi” Sannan ta d’aura da cewa “Mai aiki nasa taje har chan waje ta shigo da shi parlourn Mammy. Abunda ya bani mamaki ya kuma d’aure min kai shine yadda ya nuna kamar irin kwata kwata babu alamun yama tab’a ganina d’in nan sannan kuma he looks calm and innocent! Kasa hak’ura na yi bayan mun gaisa na ce mishi “Sageer” Amman sai na ga yana kallona da mamaki! Ganin da nayi ban ma san abunyi next ba yasa kawai na ce masa ‘ya tafi, dan Allah yayi hak’uri wani abun ya taso min urgent!’ Cikin fahimta ya nuna min ba damuwa ya mik’e ya tafi. Sakina kaina ya d’aure saboda a ganina inda ace Sageer d’in ne to da ko a idanunsa zan fahimci firgici! Da d’an alamun wani abun dole zai nuna amman kuma ko twins banajin za su iya zama super identical haka kamar shi da sageer.. Hatta fa yanayin magana kallo tafiya komai nasu iri d’aya ne..” Cikin katseta Sakina ta ce “Kar ki damu Aaima, ba wani Sageer sunanshi Ashraff! Shine! Raina miki hankali kawai yayi. Ga Abokin sa nan ma Abbakar a wanann hoton.” Da sauri Aaima ta karb’i wayar ta kalla sai kuma ta ce “Ai shine Saddik d’in” “Hmm” Kawai Sakina ta ce tana mai dialing numbershi a wayarta. Ajiyar zuciya Aaima ta sauk’e kafin tace “Kuma kin san abunda zai sa ma mu sake gasgata shi d’in ne… Ranar farko da suka fara zuwa a ranar da ya had’u da Suhaila da ya ce mata ‘I’m Sageer by name’ Sai da Abokin nashi ya juya a zabure yana kallonshi sai kuma na ga ya fara murmushi yana girgiza kai.” Dede nan Ashraff ya amsa call d’in Sakina… Daman a handsfree ta saka “Hello baby” Suka ji ya fad’a. Sai da Sakina ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya tukunna ta ce “Ashraff ko Sageer?” “My god!! Waye ne Sageer d’innan ne? Kin san i was just about to call you sai kika kira… That cousin of yours she looks confuse! Tana ganina ta ce min Sageer itama. Ask her ta yi miki bayani please dan i d.........” Cikin katseshi ta ce “Dakata Ashraff! Ba ita bace confused, ni ce! Bayani kuma ba ita za ta yi min ba kaine!. So I’m all ears Ina so inji ta yadda ka chanja sunan ka da kuma yanda kake planing zaka yi da mu Ni da Suhaila da kuma d’an cikinta” “Oh Noooo! Innalillahi wa innailaihirrajiun Sakina haba mana. Tana ina ita cousin d’in taku? Bata wayar please… Wallahi daman yadda na ga tayi na san akwai matsala, waye Sageer? Wacece Suhaila? Ciki kuma a Ina?. Sakina na riga na gaya miki y’an mata biyu kawai na yi dating b4 you and duk na nuna miki pictures d’insu, please Sakina kar ki biye mata i think akwai confusion a lamarinta amman wallahi ni ban san wani Sageer ba, bata wayar please”. Fashewa kawai ya ji Sakinar ta yi da kuka, cikin kukan ta ce “Haba Ashraff! Despite abunda ka yi da k’aryar da ka yi still kana so ka ci gaba da b’oye b’oye? Wat have i ever done to you to deserve this?” “Innalillahi wa inna ilaihirrajiun” kawai ta ji yanata maimaitawa kafin ya ce “Shikenan Sakina, na gane! Yanzu na fahimci komai… Kina neman hanyar da za ki zillemun ki auri Auwal d’in da kike ta tunani kullum ko? Ko kina tunanin ban saniba ne? Idan ba kya sona ki fito fili kawai ki gaya min ki daina yi min kwana kwana! Bawai ku had’a baki ba ku k’ulla min sharrin abu mai muni haka ba. Wallahi tallahi kin ji de na rantse miki ni ban san wani Sageer ba ban san wacece Suhaila ba sanann wallahi Sakina da gaske nake sonki ba yaudara a ciki! Ke kad’ai ce a cikin zuciyata” Ya fad’i haka yana me fashewa da kuka kamar k’aramin Yaro sai kuma ta ji ya kashe wayar, kiit!. Ashraff, yana kashe wayar ya kira Saddik yana d’auka bai jira jin me zai ce ba ya ce “Saddik, I’m doomed….” Sanann ya hau koro mishi bayani hankalinshi a mugun tashe. Shiruu Saddik d’in yayi bayan ya gama ji kafin ya ce “Listen closely Ashraff..................” Gaba d’ayansu hankalinsu a tashe yake, bama su san ta Ina za su fara ba. Aaima ce ta yanke shawarar kiran Suhailar dan haka ta d’au waya ta shiga sunanta ta danna call…… An fi thirty minutes tukunna aka samu layinta ya fita daga busy ta amsa kiran Aaiman. Ajiyar zuciya Aaima ta sauk’e kafin ta ce “Da wa kike waya haka?” Sai da ta d’anyi jimm! Tukunna ta ce “Wata friend d’ita ce” Shiruu, Aaiman ta yi tana tunanin wacece k’awar Suhaila haka da bata san ta ba… Sanin ba wannan ne a gabansu ba ya sa kawai ta kawar da zancen ta hanyar bata labarin Sageer Ashraff from A -Z kafin ta ce “Yanzu ko gidan su idan kinaso zamu iya zuwa dan Sakina ta ce ta san gidan kuma zata bamu adress har number Mamansa.” Cikin katseta Suhailan ta ce “Mun gama case d’in Sageer fa! Ki manta kawai please, kar ki sake yi min maganarsa” A rikice Aaiman ta ce “Kin gama case d’insa da cikinsa a jikinki??” “Please Aaima” Shine kawai abunda Suhaila ta ce. Aaima za ta yi magana kawai ta ji ta katse kiran. Kasa cire wayar daga kunnenta Aaiman ta yi, da kyar ta d’ago tana kallonsu still da wayar kare a kunnenta. Kirane ya shigo wayartata dan haka ta d’an zabura saboda a kunnenta wayar take har yanzu… Tana ganin mai kiran nata ta d’auka da sauri ta ce “yauwa Khadija kin san me yake faruwa? Yanzun nan....” Cikin katseta Khadijar ta ce “Sageer, yanzun nan ya kira Suhaila…. Suna fara magana ta tashi ta shiga bathroom, haka kawai na ji inaso in yi mata lab’e saboda na san kusan wata nawa ana neman shi sai yau kawai muga ya kirata. A yadda na fahimta Its like akwai wadda zai aura a yanzu! Wai family d’insu sun zab’a masa shiyasa ma ya d’auke k’afa amman yayi mata alk’awarin aure nan da wata biyar muddin ta yi shiru. Ban gama dawowa daga mamaki ba na ji conversation d’in ku a waya yanzu. Meyene yake faruwa?”. Ajiyar zuciya Aaima ta sauk’e rai a b’ace ta ce “Wato shine Ashraff d’in ta tabbata kenan!…” Nan ta d’an yi briefing Khadija a kan case d’in sannan ta ce “Khadija Suhaila tana son Ashraff ba zata tab’a iya k’etare umarninshi ba! Dan haka yanzu aiki yana a hannunki.. Ki taimaki y’ar uwar ki tunda ni dai kinji yadda muka yi da ita. Zan turo miki number Mamansa yanzu daga nan ki kirata ki yi mata bayanin komai! Lokacin b’oye b’oye ya wuce dole iyaye su shiga case d’innan. Mugun tantiri ne Ashraff d’innan wallahi! Kin san yadda ya nuna kuwa kamar bai sanni ba amman kalli har ya kirawota munafuki d’an iska! Kuma wallahi k’arya yake yi shi ya ga Sakina ya ce yana sonta ba wani had’asu da akayi Infact Families d’insu ma basu san juna ba sai ata dalilin ita Sakinar da shi Ashraff d’in. Wanne irin rashin wayone haka Suhaila take yi! Dan bayan soyayya tabbas akwai dak’ik’anci a cikin lamarinta, saboda Allah ace wai Mutumin da yayi maka wannan abun tashi d’aya ya dawo ya kalallame ka kuma ka yarda? Duk da ban san me ya ce mata ba amman ai ya kamata ta tambayeshi dalilin da ya sa ya bamu fake adress ko?” A hankali Khadija ta ce “Tabbas” Sannan ta ce ‘Ta tura mata number Maman ashraff d’in ta kirata yanzu ba sai anjima ba kafin Suhaila ta dawo d’akin.” Da “to” ta amsa sannan ta katse kiran kafin ta kallesu ta ce “Yayar Suhailan ce, Itama ta san da zancen. Ina number Maman nashi?” Kamar yadda Sakina ta fad’a haka ta bada number Maman Ashraff bayan sun kwantar mata da hankali da kyar! Dan da cewa ta yi sai ta je ta sameshi a duk inda yake! Hudan ma harda y’ar kwallarta ganin yadda Sakinar duk ta firgice ta fita haiyyacinta tana ta kuka wiwi. Gaba d’aya sun gigita da lamarin Ashraff. .......... Suna zaune a d’akin wata maid ta shigo musu da abinci kala kala.. Aaima da Huda ne suka d’an ci Sakina kam har yanzu hankalinta a tashe yake, ashe ita ta yi gudun gara ne ta tadda zago ba tare da ta sani ba… Sai bayan sallar Magrib tukunna Junaidu ya kirata ya ce “taje yana waje, su wuce.” Aaima ce ta rakata har bakin mota bayan sun sha kukan su ita da Huda sannan sun d’an yi mata y’ar guntuwar Nasiha suma, dan itama Aaiman ba komawa za ta yi ba sunyi sallama kenan saboda ta san Huda tsaf sai ta rik’eta kamar yadda ta kanainaye Sakina. Duk da halinda Sakina take ciki sai da ta fahimci kallon da Aaima da Junaidu suke yiwa juna! Tun d’azu dama da za a kawo Huda ta d’an lura yanzu kuma ta sake tabbatarwa dan har tana yiwa Junaidun magana ma bai sani ba. Kasa hak’ura tayi bayan sun d’au hanya ta ce “Ya Junaidu ko dai In had’aku ne?” Wani lallausan murmushi ta ga ya yi kafin ya ce “A’a fa Sakina, tuwon girma ai miyarsa nama! Idan na d’auko wannan ina da wajen ajjiyeta ne?” Da sauri Sakina ta ce “Ya Junaidu ranar nan fa na ji Kaka yana cewa Gidajen ka wajen biyar a Kano kawai ga motoci ga filaye.” Dariya ya yi this time around sanann ya ce “Ki bar maganar nan.. Although har ga Allah i felt something towards her very strong amman tunda na rasa Huda i don’t think zan yi aure idan ma zan yi d’in to gaskiya ba nan kusa ba.” Ajiyar zuciya ta sauk’e tana kallon yadda fuskarsa ta chanja lokaci guda. Daga haka motar ta d’auki shiruuu kowa da abunda yake sak’awa a ranshi, har ya kaita k’ofar gidan nasu ya ajjiyeta. Tana sauk’a yayi reverse ya juya dan akwai ayyuka da dama akanshi. Tana shirin tura gate d’in gidan ta ji ya ce “Sakina” Da sauri ta juyo! Daman taga kamar motarshi a parke d’an gaba kad’an. Ganin sa d’in ne kuwa yasa ta had’e fuska tamau! Kafin ta ce “Naam, Sageer.” A hankali ya k’araso inda take, sai da hasken globe d’in k’ofar gidan nasu ya haska fuskarshi da kyau tukunna ta lura da abun mamaki.. Gani tayi yana kuka wiwi fuskarshi har ta kumbure da alamun ya dad’e yana yi. Tana shirin yin magana shi ya rigata ta hanyar cewa “Sakina komai Aaima ta fad’a muku gaskiyane nine Sageer! Amman asalin sunana Ashraff. Ba zan b’oye miki ba… Har ga Allah tun farkon had’uwata da Yarinyar na ji ina sonta amman ba so na aure ba sha’awace kawai irin wadda shed’an kan saka a zuk’atan waenda ya yi nasara. Na san Abbakar Abokina ne tun Yarinta. Muna barin gurin ya tambayeni ‘dalilin b’oye mata asalin sunana da na yi’ Ban b’oye mishi ba na fad’a mishi k’udurina a kanta! Ya ji ba dad’i kuma yaso nusar da ni amman da yake shed’an ya riga yayi galaba a kaina yasa sam ban ji ba.” Matsowa ya sake yi kusa da ita wanda hakan yasa ta d’an ja baya. Cikin kuka kamar Yaro ya ce “Sakina na yi laifi, na san na yi laifi! Amman dan Allah ki fahimceni ki fahimci k’aunar da nake yi miki ta tsakani da Allah ce. Ki duba kiga yadda ita na fad’a mata fake adress fake suna and everything Ke kuma na fad’a miki komai nawa! Har waya kuke yi da Mamana. Dan Allah kar ki bari a rabamu, ki toshe kunnuwanki, fight for our love! Ko wanne d’an Adam ajizi ne ni ga nawa mistake d’in dan Allah ki fahimceni kin ga gashi na fad’a miki komai ban b’oye miki ba, ki yi min adalci Sakina.” Girgiza kai kawai Sakina ta yi sannan ta share hawayenta ta ce “Meyasa ka zab’i ka gaya min yanzu? Saboda an kira Maman ku ko? Kuma ka san dole case zai taso… Bara ka ji Ashraff magana d’aya kawai zan iya gaya maka saboda at this stage ba zan ma iya tolerating ganinka ba! Saboda abubuwan da ka yi sunada yawa ban san ta Ina zan iya farawaba… Abunda nake so ince kuma nake so ka fahimceni da kyau tunda naga kana da sharp brain shiine Ba zan aureka ba!” A gigice ya d’ago yana kallonta. “Kwarai!! Babu wannan maganar. Ga responsibility d’inka chan ‘Suhailat’ Ka koma gareta ka nemi yafiya ku haifi d’anku ku zauna lafiya ku reneshi a tare!” Tana gama fad’in haka ta juya zata shige gidan ya yi saurin ruk’o hannunta. A mugun fusace ta juyo bata yi wata wata ba ta d’auke shi da wani irin mahaukacin mari jikinta har karkarwa yake yi ta ce “Na rantse maka da Allah idan baka bar nan ba zan iya yi maka illa! Dan duk abunda na raruma sai na maka ma saboda raina ya kai k’ololuwa wajen b’aci! Audacity d’inka shi yafi komai d’aga min hankali Ashraff! Ka ma raina min hankali wallahi! How kake tunanin.....” Shiruu ta yi ta kasa ci gaba da magana chan kuma ta ce “Kaga! Just go, kama gabanka. Like i said Idan na ce zan yi maganar abubuwan da ka yi da renin wayon da ka zo da shi yanzu to ba zan iya jurar ganinka k’alau akan k’afafuwanka ba! So just leave!!!!” Ta k’arashe maganar cikin tsawa sannan ta juya ta tura zata shige cikin gidan ta ji ya ruk’ota! Za ta yi magana ta ji ya toshe mata baki da hanci da wani handkerchief.... Sai dare tukunna Granpa ya tara su Dad da Gramma ya fad’a musu d’aurin auren Maryam da Abba next week in sha Allah. A ranar Abba kasa bacci yayi yadda ya ga rana haka ya ga dare! Daga k’arshema ma ji yayi cheecks d’inshi sun fara ciwo tsabar murmushi. Tun ba ma da ya kira Mama ta kula shi sosai ba. Kaka ma ya samu Madu, babu alamun wasa a fuskarshi yace “In dai har yanzu yana yi mishi kallon Mahaifi a wajen Maryam to ya sani ya saka ranarta! Rana ita yau su Granpa za su zo a d’aura aure. Kuma dan girman Allah kar ya tambayeshi dalili ko ya yi mishi musu indai yana buk’atar Abotar su ta d’aure har k’arshen rayuwarsu.” Murmushi kawai Madu yayi kafin ya ce “Kaka ai Abotar mu har aljannah in sha Allah ba abunda zan bari ya shiga tsakani dan haka duk abunda ka yanke na goyi bayanka blindfolded….duk da ban san dalilinka ba amman i trust you kuma zan yi sopporting d’inka d’ari bisa d’ari! So dan Allah kar ma ka sako maganar lalacewar Abotar mu Allah ya kaimu ranar asabar d’in da rai da lafiya.” Ya k’arashe maganar yana murmushi. Duk fushin da Kaka ya kwaso daga gida sai ya ji gaba d’aya ya kau. Dan haka yad’an sake suka shiga tattauna abunda ya shafi alamuransu mostly a kan Jalila. Kafin daga baya ya nemi ganin Mama itama…. Same yada ya yiwa Madu itama haka yayi mata kafin ya d’aura da cewa “Indai ta d’auke shi a matsayin uba har yanzu tou kar ta yi mishi jayayya kawai yanaso ta amince da abunda ya zo da shi” Daga anan ya d’aura mata da Nasiha akan ‘kar ta rik’e Abba a ranta komai ya wuce su zauna su yi rayuwarsu kamar farko Allah yayi musu albarka.’ A hankali ta ce “ameen” sannnan ta yi mishi godiya daga nan ta mik’e ta fita. Wata nannauyar ajiyar zuciya Kaka ya sauk’e yana jin wani nauyi yana sauk’ar mishi tun kafin ya kai ga sauk’ewa gaba d’aya……. Tana zaune a kan darduma ta idar da sallar isha kenan Gwaggo Asabe ta shigo da akwati sai kuma Mommy da ragowar masu aiki mata duk da akwatuna… Tun tana iya irga su har ta hak’ura ta tsaya kawai a tsaye bayan ta mik’e ta gaidasu cikin girmamawa. Sai da aka jere akwatunan tukunna suka yi mata sai da safe suka juya suka fita suka barta nan a daskare. Ta fi minti uku kafin ta samu ta k’arasa bakin gadon ta zauna still idanunta a kan akwatunan. Da sallama ya turo k’ofar ya shigo! Da leda a hannunshi. Da sauri ta sunkuyar da kanta ta ja hular alkyabbar ta rufe fuskartata. Murmushi yayi kafin ya k’araso inda take nan bakin gadon ya zauna ya kamo hannunta cikin nashi ya rik’e ya d’an murza kafin ya ce “Sai na yi siyan fuska shima?” Dariya Hausar tashi ta bata dan haka ta d’an saki murmushi wanda har sai da ya jiyo sautin shi. A hankali ya ajjiye ledojin dake nan rik’e a hannunshi kafin ya sauk’o gabanta yad’an durk’usa tukunna ya sa hannu ya janye hular alkyabbar. Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace “Ma sha Allah” Sai kuma ya sake cewa “Kukan me kika yi?” A hankali ta girgiza kanta alamun ‘ba komai’ Tana jin bugun zuciyarta yana kara tsananta!. Cikin son ya tashi a gaban ta ta ce “Akwatunan menenen wannan?” Murmushi yayi yad’an sunkuyar da kanshi k’asa ya ciji lips d’inshi kafin ya d’ago da kanshi yana kallonta tukun ya fara magana “Ai dama sai da na cewa Mommy ta yafe min a barni ba sai na yi ba amman ta saka ni kashe uban miliyoyi akan lefe! Yau kusan wata biyu kenan tana ta tatsemin aljihu. Ga shi ke kanki bama ki so ba ko? Mu mayar mu karb’o kud’in mu?” Sai yanzu ta d’ago ta kalleshi “Ma sha Allah” ta fad’a a ranta.. Tunda ya shigo dama ta lura da fararen kaya ne a jikinshi kaftan, sai yanzu taga ashe har hular kansa itama fara ce tas! A ranta ta ce “Manyan kaya sun fi yi maka kyau” Cikin katseta ta ji ya ce “Kwalliya ya biya kud’in sabulu kenan! Tunda gashi har an saki baki ana kallona” Ya fad’a yana murmushi gefen baki da d’age mata gira. Da sauri ta d’auke idonta da kyar. Cikin son kawar da zance ta ce “Ya Aslam wasa wasa fa kanada rowa, tun ba yau ba na fuskanci haka” Dariya sosai yayi kafin ya ce “Ai kin fini rowa! Tunda gashi ana ta yi mini rowar zuciya.” Ya fad’i maganar yana k’ok’arin yin zaman dirshen akan kafet d’in gaban gadon ( a gabanta) Yana zama, bata san lokacin da ta yi sauri itama ta sauk’o ta zauna a gabansa ba har guiwowinsu suna gogar juna. Sai kuma ta fara k’ok’arin janyewa… Hannuwanshi ya saka ya rik’e cinyar tata ta yadda ba zata iya motsawa ba! Yana jin wani yanayi na daban ya na shigar shi… A hankali yana d’an murmushi ya ce “I love this respect da kike min Hudatie, Thank you.” Sunkuyar da kanta ta yi kawai ta kasa cewa komai. A hankali yana kallonta ya ce “Baki ce komai ba. Akan maganar mu da muka fara a d’akin Gramma”. Da sauri ta ce “Ya Aslam dan Allah ka daina bana son maganar. Kuma ni dai ka d’auke hannunka.” Gefe ya kalla yayi wani murmushin gefen baki.. Bata gama fahimtar murmushi da jinjina kan me yake yi ba ta ga ya mik’e tana shirin yin magana ya sunkuya ya d’auketa! Sai da ya k’arasa wajen sofa tukunna ya zauna ya d’aura ta a kan cinyarshi kafin ya ce “Bud’e idon sannan ki ja numfashi Matsoraciya kawai… In kika sake yi min musu ko kika ce kar In tab’aki Allah sai na nuna miki matsayina a wajenki.” A hankali ta bud’e idonta tana kallon k’asa.. Hankalinta In yayi dubu tou ya tashi! Tanajin yadda jikinsa yake d’an rawa kad’an kad’an ga zuciyarshi tana iya feeling bugunta! A hankali ta ji ya ce “Unhm ina jinki. Say something anything… i told you how I feel. Let’s talk about us, Um??” Yayi maganan yana ruk’o hannunta. Zuwa yanzu kam Huda ji ta yi ba zata iya jurar wannan torture d’in ba dan apart from heart d’inta da yake over racing! Ta rasa fahimtar meyene game da hannun Aslam da yake sanya touches d’inshi suke zautar da ita. D’igar hawayenta ya ji dan haka ya sauk’e ajiyar zuciya ya mik’e da ita a jikinshi ya ja hannunta… Sai da suka je inda ya ajjiye ledojin d’azu tukun ya d’auki wata ledar bag y’ar babba mai zip lock mainkyau sosai ya bata ya ce “Gashi ki shirya ki sa wannan kayan ki yi alwalah..please ki saka rigar ciki” Har zai juya sai kuma ya ce “If not” Ya matso da bakinshi kusan kunnenta ya fara magana….. Da mugun sauri ta juya ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta jikinta na karkarwa. “Kisa rigar kin ji, pls” Ya fad’i maganar kamar ba shi ya gama zuba mata maganganu a kunne ba yanzun nan. A hankali ta ce “tou” dan ita Allah Allah take ya fita ya bata guri ta samu ta shak’i isashshiyar iska. Yana fita ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya tana dafe k’irji sanann ta nemi waje ta zauna akan gadon. Ta jima a haka kafin kawai ta mik’e ta fad’a toilet dan daman wanka take son yi tun kafin ya shigo: Ta d’an jima tukun ta fito bayan ta yi wanka da ruwan turarrukan da Ummu ta jere mata a toilet d’in, da brush duk sai da ta yi sannan ta fito. Rigar, dan kyau ta yi kyau sosai sai dai spaghetti hand ke gareta. Ba wani rashin d’a’a a rigar dan doguwar gown ce har k’asa Slim mai bin jiki sai wasu stones masu shek’i na azaba k’anana a saman edge d’in wuyan rigar da kuma dede k’asan boost sai kuma chan k’asan edge d’in rigar shima an zagaye da stones d’in. Ko bra bata saka ba dan rigar irin me bra d’innan ce ta ciki. Sai da ta saka rigar ta zuge zip d’in da kyar tukunna ta ga rashin d’a’ar rigar dan kusan rabin k’irjinta a waje ne sannan bayanma gaba d’aya ashe akwashe yake dan ma Allah ya taimaka gashinta ya rufe kusan rabi. Da sauri ta fara k’ok’arin zuge zip d’in domin ta samu ta chanza rigar kafin ya shigo. Bata kaiga zugewan ba kuwa ya shigo! Sanye cikin jallabiya fara tass! Mai k’aramin hannu. Suna had’a ido da shi bata san daliliba kawai sai ta fashe da kuka. Da sauri ya k’araso gaban madubin dan shi a tunaninshi yadda ya ga ta rik’e wajen zip d’in ta na jaa ya d’auka had’ewa ta yi da fatarta. Sai da ya duba ya ga ba komai tukunna ya sauk’e ajiyar zuciya ya juyo da ita ya fara lallashinta yana dariya k’asa k’asa dan sai yanzu ya fahimci dalilin kukan nata. Da kyar ta yi shiru tana sauk’e wasu tagwayen ajiyar zuciya tana nok’ewa: A hankali yake binta da wani irin kallo kafin ya tattara gaba d’aya gashin nata ya zubo mata shi ta gefen fuskarta suka fad’a a kan k’irjinta gefe d’aya. Tunda ya fara kallonta har ya gyara mata gashin kan nata ta sunkuyar da kanta k’asa. A hankali ya zaro wata red rose ya sak’ala mata a jikin gashinta ta d’an saman kunnenta kafin ya zaro wani tsadadden pendant necklace d’an mitsitsi mai shape d’in heart ya ware shi ya bud’e ya kara mata a wuyanta sannan ya matso sosai ya lek’a ta baya ya manne mata sark’a ya saketa ya gyara mata gashinta. A hankali ya na nan a yanda yake dan baya son motsawa daga position d’insa ya ce “Open it” Da kyar ta iya bud’ewa hannunta na gogar k’irjinsa… Bata san lokacin da murmushi ya sub’uce mata ba Right side d’in an rubuta ‘Y’ Left d’in kuma ‘M’. A hankali ta mayar ta rufe sark’ar tana d’an murmurshi. Jin yayi shiruu yasa ta d’an motsa sai kuma ta tuna ashe a jikin madubi ta ke! Da sauri ta juya ta katseshi daga k’are mata kallon da yake.. Dariya ya yi ya ce “To ai nan d’in ma zan ganki” Da sauri ta koma ta kanannad’e shi ta baya ita ala dole kar ya sake ganinta. Ganin tana shirin kunce mishi lissafi yasa ya ce “Tsaya In d’auko miki hijabi mu je mu yi sallah” Da kyar ya samu ta sakeshi ya k’arasa wajen akwatunan ya bud’e wanda yake kyautata zaton akwai hijabin a ciki.. Cikin sa’a kuwa ya samu ya d’auko harda darduma ya dawo ya mik’a mata hijab d’in ya ce “Ungo, saka” A hankali ta karb’a ta saka tana sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya.. Daga nan ya ja hannunta ya ce “mu je, i have a surprise for you.” Yana rik’e da hannunta suka fito suka nufi d’akinsa… Yana bud’ewa! A hankali ta ce “Woow..” Tana murmushi. Sai da ta k’arasa shiga cikin d’akin tukunna ta fahimci abunda ya rubuta da y’an k’ananan candles d’in da ya kunna a tsakiyar d’akin I Love You Hudan!. Kan gadon ma wanda ke nan shimfid’e da white bedsheets haka ya rubuta da wasu k’ananan red roses. Murmushi kawai take yi tana kallon yadda d’akin ya k’awatu matuk’a! Ya burgeta sosai. A hankali ta ji yayi hugging d’inta ta baya sannan ya ce “Do you like it? Ya yi kyau?”. Murmushi ta yi a hankali ta ce “Ya yi kyau”. Juyo da ita ya yi ya d’an b’ata yayi kalar tausayi fuska abun dariya ya ce “Ya yi kyau but you don’t like it ko? Y?” Sai da ta yi k’asa da kanta tukunna ta ce “Ni Ya Aslam kana confusing d’ina ne idan na ji ka ce you love m me” Ta k’arashe maganar da d’an inda inda. A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya kafin ya ce “Y?” Cikin runtse idanunta ta ce “Ya Arshaad fa k’anin ka ne! Amman kuma how kake sona bayan ka san shi zan aura? Idan kuma ba haka ne ba to tayaya zaaka ce ka fara sona ana d’aura auren mu? Tunda na lura tun lokaci ka fara nuna intrest.” Ta fad’a tana sake sunkuyar da kanta sosai. Ya ji zafin zancen Arshaad da ta kawo amman sai ya basar, ya ce “Dole ki sunkuyar da kai ai” Ya fad’i hakan yana d’an jan hancinta, kafin ya sa hannu ya sake jawota jikinshi tukunna ya fara magana “Hudan! That day da muka fara had’uwa ranar da Arshaad ya ce in zo mu je yayi min introducing d’inki mu ga juna Wasn’t the first time i saw you.” Da sauri ta d’ago tana kallonshi. Lumshe kyawawan idanuwanshi yayi ya bud’e su sannan ya jinjina mata kai alamun tabbatarwa. “Banso gaya miki haka ba na so ace na saka soyayya ta a cikin zuciyarki a hakan in ya so daga baya ki sani amman zancen Arshaad da kika kawo wanda na fahimci it’s like kina tuhuma ta da betraying d’inshi, shi ya sanya zan fad’i miki.. ...Akwai wani competition da kuka yi,Tournament, Mathematics.. I think a time d’in kina ss 2 ne. A cikin makarantun akwai wata makaranta ta y’an labanoon wadda sister d’in wani employee d’ina d’an labanoon ta yi representing. A chan uk yake min aiki a company d’ina, muna shiri sosai da shi. Ke kika zo first ntic Sistern nashi kuma ta zo second Labanoon school. Employee d’in nawa ne ya turomin full video d’in yana me tambaya ta ‘Dama inada sister bayan Aaima?’ Na ga resemblance d’in sosai nima amma ba wannan ne matsala ta ba dan a tashi d’aya kika shiga raina. Sai da ta kai ta kawo bana iya bacci idan har ba hoton ki da wannan video d’in na gani ba. Inada waenda na sani suke koyarwa a school d’inku dan haka na sakasu suka nemo min sport, prep da duk wani pictures d’inki da wasu information a kan ki! Tabbas hankalina ya tashi sosai da na ga a scholarship kika je school d’in dan zuwa wannan lokaci soyayyarki ta riga ta yi min kyakkyawan kamu! Sanin da na yi tabbas za asha gwagwarmaya da Granpa! Ne ya yi matuk’ar d’aga mini hankali, duk da inada tabbacin idan na lallab’ashi na shawo kanshi maybe ya iya yarda. Har ranar graduation d’inku sai da na saka aka yi min video d’inki kina bada speech special aka turomin ke kad’ai. Zuwa wannan lokacin na san in dai ban sameki ba tou tabbas akwai matsala, dan ni kad’ai na san me nake ji…… Na shirya akan zan dawo In karb’i adress d’inki In samu Granpa in yi mishi bayani idan yayi aproving In je in sameki dan no matter how much i love you I don’t think zan iya yarda in jefa ki a irin halin da Anty Maryam da Mommy suka shiga ciki, ba. Ina shirin dawowa Arshaad ya kirani akan wai Auwal yayi framing d’inshi har an kaishi Kotu! Bani da kamar Arshaad shiyasa tun kafin In dawo na maida case d’in shi priority tukunna in samu Granpa tukunna in sameki. Ana cikin case d’in nashi kuma ya ce ‘in zo mu je In ganki’ Ba k’aramin tashin hankali na shiga ba ranar Huda! Don a take Ina ganinki na ganeki sannan kika sake samun guri kika yi bake bake a cikin zuciyata. Shiyasa In zaki tuna da kyar na iya seseta kaina na fito….. Arshaad is my brother and best friend that is why i did what i do to you that very day saboda a ganina ya zame min dole in yakiceki In kuma saka miki k’iyayya ta a rai saboda gudun kar ma zuciya ta rud’eni In so kaina in zo miki da nawa zancen saboda a wannan lokacin ina k’ok’arin tursasawa zuciyata In samu Inga na hak’ura da ke amman kwakwalwata da tunanina suna nusar da ni a kan Ba fa zan iya hak’urin nan in barwa Arshaad ke ba!. And yadda na ga Arshaad yana sonki as his big brother hak’ura da ke is the best thing to do tunda na ga kema shi kike so! Shiyasa na yi k’ok’arin zama bad guy a idon ki har Anty Maryam (and still Ina jiye wa Abba a wannan ranar shiyasa abun ya zama biyu na aikata mata abunda na yi ranar a asibiti.) Amman kuma sai abun ya gagara dan no mattaer how i try tun ranar da na ganki har kawo yanzun nan I don’t think k’aunarki ta ragu dede da kwanyar zarra a cikin zuciyata! A ko da yaushe k’aruwa kawai take yi…. Har d’an k’aramin hauka na yi da aurenku ya matso! Gashi Mommy ta hanani guduwa… Zakkah sadaka da sallar dare su suka taimaka Ubangiji ya ji k’aina ya mallaka mini ke a lokacin da ban tab’a tunani ba. Na tabbatar da ace ban aure ki ba to It’s either in k’are a asylum ko kuma mak’abarta…” Ya k’arashe maganar yana mai cupping face d’inta kafin ya d’ago fuskar tata yana kallonta a hankali ya yi kisssing idanuwanta da ta lumshe sannan ya ce “I love you Hudan! Bawai sai da na aureki na fara showing intrest ba, noo, not at all! Tun kafin in dawo Nigeria nake So da Burin inga na aureki. You are my happiness my everything my whole heart kin shiga kin kanainaye ke kawai nake gani ke nake So da Burin in mallaka in rayu da har k’arshen rayuwata….. Na san ba lalle ki soni ba a yanzu but please dan Allah kar ki k’i ni Hudatie try and find a place for me in your heart i promise you won’t regret it! Just a tiny place, please my love.” Ya k’arashe maganar a hankali. Hawaye ya ga ya fara bin k’uncinta dan haka ya jata ya yi hugging nata ya ce “Sorry.. Amarya bata kuka Shikenan a bar maganar in dai zata saka ki kuka. Let’s pray.......” A hankali ya cikata ya sunkuya ya d’auki sallaya ya wuce ya shimfid’e. Nafila ya ja suka yi. Ya dad’e yana addu’oi kafin ya juyo ya dafa kanta ya yi addua. Sannan ya shiga jero mata tambayoyi game da addini… Ya ji dad’in sanin da ya ji tana da. Daga nan ya ce “itama ta yi masa tata tambayar..” Kasawa tayi dan haka kawai yayi murmushi ya ja hannunta suka mik’e… Shi kansa yunwa yake ji amman a yadda yake jin sa sam! Ba zai iya jira a sha ko da ruwa ba!. Da kyar dan sai da yayi da gaske tukunna ya zare hijabin nata. ..…………….. Tabbas Hudan ta ga ikon Allah! Tsaurin ido! Tsantsar rashin kunya da kuma k’arfin hali a wajen Aslam. Tun tana tirjiya har ta d’an fara sakin jiki dan salon nashi babu sauk’i. Kafin daga baya kuma ta ji an d’auki wata hanya daban mai cike da rad’ad’i wahala da azaba na fitar hankali’ Tun tana kuka a hankali tana d’an dauriya saboda rok’o da magiyar da yake ta yi mata har ta zo ta fara tirjiya sannan ta ware murya ta fara ihu tun k’arfinta dan taga abun nashi ba na wasan Yara bane ba. Babu wanda Huda bata kiraba har K’asimu sai da ta kira! Indai Huda ta sanka to tabbas a wannan dare ta kira ka tana magiyar ka zo ka kawo mata d’auki. Tun tana ganin daidai ta zo ta fara ganin dishi dishi! Tsananin azaba ta sanya daga k’arshema ta shak’i numfashi ta sume ba tare da oga Aslam ya san inda kanshi yake ba ballantana ita........... BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 70 Mikiya Writers Association. Kamar a cikin ruwa take jinta! Sai kuma muryarsa sama sama yana d’an shafa mata ruwan a fuska yana tapping kumatunta a hankali yana kiran sunanta a d’an rikice. Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauk’e kafin ta samu ta bud’e idanuwanta da suka yi mata nauyi. A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya ya ce “Alhamdulillah!! Sannu sannu sorry sannu” Da kyar ta iya had’a idanu da shi, wani haushinsa ta ji a take sannan duk kyawun fuskarshi yau sai ta nema ta rasa! A hankali ta kawar da kanta gefe ta sa kuka…. Cikin rashin jin dad’i yace “Sorry mana, yi hak’uri please, na ce sorry fa” Cikin kukan ta ce “Ka fita.” Zai yi magana ta sake cewa “Allah ka fita!” A hankali ya mik’e ganin kamar ma bata son kallon fuskarshi ya sanya ya ce “Ki kirani kafin ki fito, kar ki fad’i” D’aga masa kai kawai ta yi shi kuma ya sa kai ya fita daga cikin bathroom d’in…. Duk da baya son ganin ta a wannanan halin da mood d’in amman sai ya tsinci kanshi da sakin wani k’ayataccen murmushi…. Yana fita ya ga wayarsa tana haske dan haka ya k’arasa ya d’auka da d’an sauri. Ganin Aaima ya sa ya d’auka cike da ishashshen kuzari ya ce “Auta ya aka yi?” Sai da ta gaidashi tukunna ta ce “Yaya na zo ne” Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya kashe kiran ya k’arasa ya zaro jallabiya ya zura akan gajeran wandon jikinsa ya fita. Da baskets nik’i nik’i ya ganta na break fast. Bayan sun sake gaisawa ta ce “Gashi inji Mommy” Murmushi ya yi ya ce “ki ce mata mun gode. But akwai cook a nan itama ta huta dan na san wannan da kanta ta girka.” “To” ta ce, ga mamakinsa sai ya ga ta wuce shi ta nufi hanyar sama. Da sauri ya ce “Ina za ki je?” Ba tare da ta juyo ba ta ce “Zan d’an je mu gaisa da Anty Huda ne” Gani ta yi ya biyota da sauri sannan ya kamo hannunta ya dawo da ita bakin k’ofa ya ce “Ki bari ba yanzu ba! Bacci take yi.” K’asa k’asa Aaima take danne dariyarta kafin ta ce “Ya Aslam akwai important maganar da nake so mu yi da ita. D’an matsa dan Allah in wuce.” Ganin ya saki baki cike da shock yana kallonta ya sanya ta kasa daurewa ta saki dariyar da take ta k’ok’arin dannewa… Sai yanzu ya gane me take yi mishi dan haka ya yunk’ura Ita kuma ta juya ta wuce da gudu tana dariya. Sai da ta b’acewa ganinsa tukunna ya girgiza kai ya mayar da k’ofar ya rufe. Ya shiga kitchen ya d’auko plate da cups ya had’a da baskets d’in ya nufi sama. Har Aaima ta k’arasa gida tana murmushi da mamakin yadda ta ga Aslam d’in yayi wani irin haske na ban mamaki sannan ga wani nutsatsen kyau da annuri cike da fuskarsa. A hankali ta sauk’e ajiyar zuciya a fili ta ce “Hmm” Kawai, daga nan ta yi gaba. Yana komawa ya tarar da Huda ta fito a wanka tana takawa da kyar za ta isa kan gadon… Ajjiye kayan hannunsa yayi nan bakin k’ofar sannan da sauri ya k’arasa ya d’auketa chak! Yana mai cewa “ba na ce ki jira ni ba? Taurin kai ko?”. Bata kula shi ba, haka ya kaita kan gadon da ya shimfid’awa sabon bedsheet ya kwantar, a hankali ya yi mata light peck a goshinta kafin ya zauna a gefenta ya kamo hannunta yana d’an matsawa a nashi ya ce “Ya Aslam bai kyautaba! He is sorry. Yanzu kam na san kafin a samu a bani amsa ta ta jiya sai na garu. Nima dai inbanda ni da karambani na ta yaya zan yi wannan aikin In sake b’allawo kaina ruwa? Ni da ban gama samun matsugunni ba…” Turo baki tayi ta d’an juyar da fuskarta kad’an. A hankali ya yi murmushi ya kawo hannunta setin bakinshi ya yi kissing kafin ya ce “Thank you Hudatie, thank you so much! Ban san ta yaya zan fara yi miki godiya ba.. I just want you to know that You are everything that I need to be happy and more.. Tnx a lot, I love you.” A hankali ta lumshe idanuwanta… Tabbas maganganun shi sun yi mata dad’i amman yadda take ji a jikinta ji take yi kamar ta yi ta kwarara ihu!. A hankali ya mik’e ya d’auko baskets d’in ya kawo ya zuzzuba abincin. Naciii da threats d’in da ya dinga yi mata ne suka sanya ta ta ci da d’an dama dan ita kam ko a mafarki bata buk’atar wata had’uwar tasu ita da Ya Aslam! Ita ta san waye shi Ita ta san azabar da ta sha..................... A hankali Sakina take bud’e idanuwanta.. Da sauri Ummu ta ce “Alhamdulillah! Ta farka.” Sannan suka yo kanta da sauri ita da Mama suna jera mata “sannu” Daga nan suka kamata suka zaunar da ita.. Wani irin abu take ji yana yi mata yawo a cikin kanta! Daman tun jiya da ya toshe mata hanci da baki da wannan handkerchief d’in a take ta ji kamar an zuba mata tsutsotsi a cikin kanta kafin ta sume to yanzun ma tana farkawa ta cigaba da jin hakan, sosai kuma da k’arfi! Shi ya sanya ta shiga shafa kanta har ta kaiga tuje d’ankwalin ta hau jan gashinta da k’arfi kamar wata shahararriyar mahaukaciya!…. Idanuwa kawai ta ga su Ummu sun zuba mata. Sai a lokacin ta lura da yadda idanuwansu suka yi jaaa duk su biyun da alamun sun ci kuka. Tana shirin yi musu magana idanuwanta suka sauk’a a kan Ashraff! Wanda ya tunkaro gadon shima. Cikin tsanannin tashin hankali da b’acin rai ta ce “Ashraff! Ashraff ne.. Kar ka k’araso, Ummu kidnapping d’ina ya zo zai yi wallahi Ashraff ne” Duk ta rikice ta gigice dan a tsorace take. A hankali taga ya fara zubda hawaye yana sa hannu yana gogewa. Gani ta yi Mama ta juya ta fita Ummu kuma ta sunkuyar da kanta. Bata gama tunanin abunda yake wakana ba Mama ta shigo tare da Doctor. Yana shigowa ya nufeta ya hau dubata kafin ya ce “Me kike ji yanzu?” A tak’aice ta ce masa “Tsana da tsoro! Na wanchan bawan Allahn, ka ce masa ya fita Allah in bai fita ba zan illatashi” Ta k’arashe maganar tana dukan tsakiyar kanta saboda yadda take ji abu na yi mata yawo a ciki. Ajiyar zuciya Likitan ya sauk’e kafin ya juya ga su Mama ya ce “Results d’in sun fito! Gaskiya ta bugu sosai a kan nata shi yasa dole za take misbehaving… Kar ku biyeta kawai ku yi addua nima akwai magungunan da zan d’aurata a kai In sha Allah za a dace.” Cikin tsananin tashin hankali Sakina ta ce “inna lillahi wa inna ilahirrajiun” Tana mai d’aura hannunwanta duk biyu a ka! Za ta yi magana kawai Likitan ya kama hannunta su Ummu suka taimaka masa wajen rik’eta dan har ta fara bubbuge hannunsa tana tirjiya da surutai, bai yi wata wata ba ya danna mata allurar da ko gama shiga cikin jijiyoyin ta basu yi ba Jikinta ya sake gaba d’aya ta tafi luu ta zube a nan kan gadon jinyar..... Kuka kawai Ummu da Mama suka saka hankalinsu a mugun tashe. Da sauri Ashraff d’in ya matso ya fara lallashinsu kafin ya ce “Akwai wani Doctor d’in da na sani a New York! Dan irin haka ta tab’a faruwa da wani cousin d’inmu…. Basket ball ne ma shi wani ya buga masa a ka wanda muna a filin ball d’in fad’a ya had’osu. Mama ni har ga Allah tsakani na da Allah nake son Sakina! Ba hauka ba ko me ne take yi na ji na gani zan aureta in rayu da ita. A yanzu idan kuna so tsaff zan iya booking appointment da Likitan in fitar da ita domin samun lafiyarta.” A hankali Mama ta ce “Haka kurum ta fara?” Cikin share hawayensa ya ce “Suna buga mata dutsen suka gudu. Ni kuma ban samu na bisu ba tunda naga kamar a buge suke sannan ga itama a kwance. Muna zuwa asibitin nan bayan taimokon gaggawa ta farfad’o, abunda ta fara ce min shine ‘Ta bawa Aaima labarin Suhaila! Allah ya isanta, na cuceta ba zata aure ni ba’. Ganin da na yi she s not making any sense ne yasa kawai na yanke shawarar In kiraku.” Ya k’arashe maganar cikin karyewar zuciya da zubar hawaye. A hankali Ummu ta ce “Shikenan Ashraff mun gode. Bara in kira Baban nasu na ji har yanzu shiru.” Tana shirin fara dialing numbersa suka shigo shi da Abba! Sai da suka d’anyi kallon kallo shi da Mama tukunna aka gaisa kafin Ummu ta hau zaiyyano musu bayani dalla dalla…. “Gaba kura baya damusa” Baban Sakina ya fad’a a ranshi dan yanzun nan yana shirin shigowa asibitin Abba ya kirashi ya ce yana buk’atar ganinshi urgent! Shi ya sanya ya jirashi sai da suka gama tattunawa tukun suka shigo duba Sakinar dan shi Abban ma bai san tana kwance ba! Ya zo mishi ne akan maganar Auwal….. Tabbas sun san cewa bai kamata ba amman maybe a san abun yi dan Auwal tun shekaran jiya an kasa gane kanshi kwata kwata! He’s not even responding to treatment, gaba d’aya jikin nashi sai a slow, hankalin Daddy a mugun tashe yake shiyasa suka yanke shawarar zuwa su sameshi ko akwai wani taimakon da za su yi musu, duk da kuwa ba su ga way out ba amman dai gara a gwada…… A hankali Abba ya ce “Bacci take yi ne?” “Eh” Ummu ta bashi amsa. Yana shirin yin magana Ashraff d’in ya ce “Bara in kira Doctor d’in Idan anyi sa a yana nan ma ko a yau za a iya wucewa…” A hankali Ummu ta ce “Sannu Ashraff” Yana fita Baban Sakina ya nema waje ya zauna ya dafe kanshi, bai san abun yi ba! Har ga Allah. Cikin sanyin jiki Ummu ta yi mishi bayanin Likitan New York…. “In dai zata samu sauk’i kuma zamanta a haka zai iya janyo matsala! Tou why not kawai ya d’aura musu aure tunda an riga an gama bincike akan shi Ashraff d’in, in ya so sai ya tafi da matarshi ya yi jinyarta a chan tunda ya nuna zai yi d’in kuma zai biya makudan kud’ad’e a nema mata lafiya da komai” Baban Sakina ya aiyyana hakan a ranshi. Dede nan Ashraff d’in ya dawo ya ce “Yana nan! But zuwa nan da next week zai bar k’asar zuwa wani important aiki and ba lalle ya samu ganin mu ba idan aka kai next week d’in.” A hankali Baban su Sakina ya mik’e ya ce “Ina zuwa bara in yi waya da brother d’ina” Dafa shi Abba yayi ya d’an kalleshi kafin ya juya ya cewa Ashraff d’in “Za ka iya wucewa kawai, za mu san abun yi kar ka damu” Zai yi magana ya ce “ ka je kawai an gode” Sai da Ummu ta ce “Ashraff ka je za mu nemeka, mun gode” Tukunna ya juya ya fita da kyar. Da mamaki Abba yake kallonsu yana ganin yadda duk suka rikice Yaro k’arami ya na raina musu hankali. Cikin son gasgata zarginshi ya nemi Ummu da ta yi mishi ishashshen bayani.... ....Tana dire aya ya zaro waya ya danna kiran Aaima… Da kyar Aaima jikinta na karkarwa jin Abba ya ji abunda k’awarta ta aikata a school ta shiga koro mishi bayanin tiryan tiryan… Har zuwan da Ashraff d’in ya yi estate a jiya. Tana dire aya Abba ya kashe wayar ya kallesu ya ce “Me kuka fahimta a lamarin su su uku?” Bai jira jin me za su ce ba ya ce “Ni na fahimci K’arya Yaudara Da tsoro a lamarin Ashraff. Inaso ka zo mu je mu samu Mahaifinsa a nan na tabbatar in dai mutumin kirki ne to gaskiya za ta fito k’arara! But first sai na fara kulle asibitin nan da mai asibitin tunda karb’ar cin hanci ya maida sana’a” Bai gama rufe bakinshi ba Likitan ya shigo! Sai da ya kallesu one by one tukunna ya k’arasa inda Ummu take ya shiga yi mata bayani akan wasu takardu da ya shigo da su yanzu…. “Case d’in Sakina fa is severe! In ba a fitar da ita a yau ko gobe ba tou tabbas za a samu babbar matsala! Shima sai yanzu ya ke ganin wannan result d’in bayan ya tsananta bincike…..” Kasa magana Abba yayi tsabar mamaki da takaici dan haka kawai ya turawa commisioner of police message tare da adress d’in asibitin daga nan ya cewa Baban Sakina “ya zo su je..” Suna fita ya ce mishi su wuce gidansu Ashraff. A motar Abba ya yiwa Baban Sakina k’arin haske akan abunda ya fahimta game da Ashraff d’in kuma aka ci sa a Baban Sakinan ya fahimceshi. Ba Baban Sakina ba hatta Abba sai da ya cika da mamaki da suka k’arasa k’ofar gidan suka tarar da tafkeken masallacin juma’an dake a jikin gidan cike da jama’a anata shige da fice. A hankali da kamala suka kutsa kai suka shige ciki, sakamokon hango Mahaifin Ashraff ya gilma ciki sanye cikin shiga ta alfarma. Ba su gama tunanain meke faruwa ba suka ji a loudspeaker ana “An d’aura auren Ashraff Muhammad Bashir Da Suhailat Yusuf Tanko a kan sadaki naira dubu d’ari uku lakadan ba ajalan ba.” Kallon kallo suka hau yi kafin su hau kallon jamaar one by one… Chaan! Suka hango Baban Ashraff d’in da suka biyo cikin masalllacin, yana ta fara a yana gaisa wa da wasu Abokanayen sa na jiki jiki waenda suka samu damar halartar d’aurin auren gaggawan da aka gaiyyacesu. Yana ganin Baban Sakina hankalinshi ya d’an tashi! Dan a iya saninshi bai gaiyyaceshi besides auren ma ai secret aka yishi to me kuma ya faru?! Bai gama dawowa dede ba suka k’arasa wajen shi da Abba suka zauna a kusa da shi. Abba ne ya iya bashi hannu suka yi musabaha Baban Sakina kuwa da kyar ya iya ce mishi “Barkanmu.. Dan Allah d’an yi min elaborating abunda na ji an fad’a yanzu.” Sai da Baban Ashraff d’in ya d’an kalli gefe da gefen shi tukunna ya mik’e ya ja su gefe ya fara magana k’asa k’asa “Kasan me ya faru ne? Yaron yanzu sai a hankali wallahi….” Sai kuma ya d’an yi shiru kafin ya fesar da numfashi ya ci gaba da cewa “Shi Ashraff an d’an samu matsala ya je ya yaudari wata Yarinyar oga na wanda shi ya siya min takardar kujerar sanatan da nake mulka a yanzu! Hatta campaign shi yake taimaka min da komai. Kaga ni d’an siyasa ne In na yi mishi butulci ban kyauta ba kuma siyasata za ta samu matsala tunda party d’inmu d’aya. Jiya Yayar Yarinyar ta kira Mahaifiyarshi direct… To kasan mata abun nasu sai a hankali, a take sai ta yi mata fata fata kuma ta ce ‘ba dai Ashraff d’inta ba’. Tofa shine Yaran su kuma suka je suka samu Mahaifinsu da Mahaifiyarsu suka fad’i komai. Adress da sunana kawai ya karb’a ya gano Ashraff d’ana ne! Yau da safe sai ganin shi na yi. Baban sakina ko kaine a situation d’in da nake na san dole ka yi abunda nayi. Amman ka kwantar da hankalinka Aure tsakanin Ashraff da Sakina babu fashi! In sha Allah lokacin da muka d’iba yana cika za a d’aura musu aure. Jiya sai cikin dare Ashraff ya dawo gidan nan a hargitse wallahi ya bani tsoro kuma hakan ya sanya na sake fahimtar yana tsananin k’aunar y’arka dan na san tabbas labarin ta ji suka d’an samu matsala shiyasa ya damu har haka.. Kar ka ce za ka yi interfering dan Allah kar kace za ka yi komai ka barsu, dan Ashraff jiya har d’an k’aramin hauka ya yi! Idan ka ce za ka hanashi Sakina ban san ya za ai ba”. Cikin tsananin b’acin rai Baban Sakina ya ce “A jiyan da ya dawo muku a haukace ka san me ya je ya yi?” Bai jira jin amsarshi ba ya ce “K’wamushe mini y’a ya je ya yi! Ya kaita wani asibiti suka had’a baki da mai asibitin aka manna mata ciwon hauka! Yanzu haka da ka ganmu da farko shirin d’aura musu aure shi da ita muke yi saboda ya ce ya san wani k’warerren Likita A New York Inkuma aka barta ba a kaita wajen Likitan da wuri ba to zata iya mutuwa.” A firgice Baban Ashraff d’in ya ce “Innalillahi wa inna ilaihirrajiun” Sai kuma ya dafe kanshi kafin ya d’ago ya ce “Kayi hak’uri Alhaji Muhammad Ashraff yayi laifi amman wannan yana yi maka nuni da abunda hanashi ita ka iya jawowa! Na tabbatar tsorata yayi shiyasa yayi hakan! Yanzu ka kwantar da hankalinka zan yi mishi magana ba zai k’araba In sha Allah Lokaci yana yi za a d’aura musu aure a samu a zauna lafiya”. Shi kam Abba dariya ma Mutumin ya so ya bashi… Yana shirin yin magana ya ji Baban Sakina ya ce “Unfortunately, Alhaji ka yi hak’uri amman itama Sakina akwai wanda na ga ya fi dacewa ta aura! Za mu dawo muku da duk wasu kud’ad’en ku da kaya dan na janye maganar aurenta da Ashraff gaskiya! Bawai saboda Ashraff ya yi aure ba..not at all. Zan yi hakan ne saboda yadda na ga kana shakkar Mahaifin Yarinyar da ka aurawa d’anka a yau na tabbar idan ya ce kar a yiwa y’arsa kishiya to ba za ka bari ba. Cikin b’acin rai mutumin ya ce “Wai Alhaji Muhammad ya mutum kamar ni da girma na ina yi maka magana har da magiya amma kana yi min musu???” Ciki sauk’e ajiyar zuciya Baban Sakina ya ce “Shiyasa zan barka In bar maka d’anka dan ba zan iya musun rashin gaskiya da kai ba” Yana gama fad’in haka ya wuce inda ya ga limama, ya same shi ya gaya mishi wata magana kafin ya dawo inda Abba yake tsaye shi da Baban Ashraff ya ce masa “Kana da sadakin da zaka bayar na Auwal ko sai ka je banki?” Kallonshi Abba ya yi a d’an rikice sai kuma ya sauk’e ajiyar zuciya yana murmushi kafin ya ce “akwai a mota, bara in je in d’auko”. Ko minti biyar bai yi ba ya dawo…. Alokacin limamin har ya d’an tara jama’a an zazzauna. Yana zuwa bayan an shirya komai ya mik’a sadaki ya yiwa Auwal wakili…a take aka d’aura auren Auwal Yusuf Umar Farouk MT Da Amaryarsa Sakinat Muhammad a kan sadaki naira dubu d’ari biyu lakadan ba ajalan ba. Ana gamawa Baban Ashraff ya juya ya fita fuuuuu! Daman tun d’azu ko zama kasa yi yayi yana mamakin tsaurin ido da taurin kai Irin na wannan talakan mutumin............ Ana shafa Fatiha Abba ya bayar aka siyo alawowi a shagon gefen su aka zo aka rarraba aka watse.. A take ya kira su Dad ya sanar da su good news. Kasa hak’ura suka yi suka ce ya bawa Baban Sakina wayar Shi kam har d’an kunyar irin godiyar da suka dinga yi mishi ya ji, daga nan suka yi sallama suka nufi wajen Granpa domin sanar da shi. Su Abba kuma suka koma asibiti wajen Sakina. Suna shiga dede suka tarar ta farfad’o amman Mama da Ummu sun danneta Likitan yana k’ok’arin sake sank’ama mata wata allurar yana cewa “Ai dama na gaya muku! Ku duba fa kugani irin abubuwan da take yi if possible a wuce da ita kawai Yau! Tunda na ji Yaron ya san garin da Likitan, shi zai yi komai dan haka komai zai zo da sauk’i.” Da sauri Baban Sakina ya je ya kwab’e allurar daga hannunshi! Yana shirin yin magana y’an sanda suka shigo. Babban su ne ya k’araso ya karanto mishi laifinshi.... Tabbas Likitan ya san Ashraff zai fito da shi tunda ba ayau suka fara harka da shi ba! Yasha kawo mishi mata ya cire musu ciki amman duk da haka sai da ya ji gabanshi ya fad’i! Da kyar ya dake ya bi bayansu salin alin bayan ya turawa Ashraff d’in message…. Suna fita Sakina ta ce “wallahi Abba k’alau nake, Ashraff munafuki ne! Shi ne ya shak’a min hanky d’insa wanda Allah kad’ai ya san girman kwayar da ya saka a jiki shiyasa nake jin k’aik’ayi a kaina kuma yanzu na daina. Dan Allah ku fahimceni Munafuki ne! Baba dan Allah kar ku kaini wajen Likitan mahaukata……” Matsawa inda take Baban nata yayi a hankali ya dafa kanta ya ce “ba komai komai ya wuce ki kwantar da hankalinki kin ji? Mun yarda da ke Aaima ta fad’a mana komai ai” Kallonshi kawai Ummu da Mama suke yi….: A hankali cikin nutsuwa ya karanto musu yadda suka je suka tarar ana d’aurawa Ashraff aure da komai da kuma yadda suma suka d’aura auren Sakina da Auwal a yau….. Wani sassanyan murmushi ne ya sub’ucewa Mama a hankali ta ce “Alhamdulillah” Abba da yake kallonta ne ya ce “Ma sha Allah.” Yana sakin nashi murmushin. Sakina kuwa wani irin kuka ta saki....... Direct parlourn Granpa Dad da Daddy suka nufa. a nan suka iskeshi shi da Gramma yana jik’a towel yana d’aura mata a ajiki. Ba yadda suka iya haka suka sanar da y’ay’an nasu rashin lafiyar Gramma d’in wanda hawan jinine yake neman yi mata illa tun rasuwar Ummi…. Ba k’aramin tashin hankali su Dad suka shiga ba kuwa. Da kyar! Granpa da Gramma d’in suka lallab’asu suka d’an nutsu bayan sun gama shiryawa akan za a fitar da Gramma d’in waje ta d’an huta ta samu change of environment ko da na wata d’aya ne ta yarda. Sai da Granpa ya tambayesu tukunna suka tuno da zancen Auwal da Sakina dan haka suka zaiyyano musu labari tiryan tiryan….. Mik’ewa Gramma ta yi ta zauna tana murmushi ta ce “Alhamdulillah na samu another grand in-law Allah ya sanya albarka dama inata addua wallahi saboda Yarinyar ta shiga raina tun a ranar da suka zo za a kai Huda. Barka Alhamdulillah. Auwal sai ya warke ai yanzu Ja’iri mai ciwon so.” Dariya duk suka yi har da Granpa kafin Granpa d’in ya ce “Yanzu abunda zai faru shine.. Ku fara shirye shiryen visar har da na ita matar Auwal d’in, Yahaya ka kirawo Kakan ta ka sanar da shi cewa Duba da yanayin halin da Mijinta yake ciki muna so mu tura mishi ita da wurwuri! At least a samu ya warke da wuri ja’irin.” Dariya duk suka yi nan ma kafin Granpa ya ce “Sai ta wuce as soon as possible mu kuma idan mun yi welcomin Maryam sai mu wuce da washe gari ko?” Ya fad’i maganar yana dafa kafad’un Gramma. Murmushi kawai ta yi ta sunkuyar da kanta dan duk sai ta ji ya bata kunya. Daddy ne ya ce “Inyeee.. Grand honeymoon za.....” Bai k’arasa ba Gramma ta d’auko throw pillow ta buga mishi! Da sauri suka mik’e suka fita shi da Dad suna dariya. A hankali Gramma ta kwanta a jikinsa tana sauk’e ajiyar zuciya kafin ta ce “Thank you Daddie” Murmushi kawai yayi yana me shafa kanta a chan k’asan zuciyarsa kuma yana regretting abubuwan da ya yiyyi.. ashe haka happines d’in frank family life yake amman ya dinga depriving kanshi da zuri’arsa ba tare da ya sani ba? Tabbas miskilanci da mugun hali bashi da rana.................... BULAMA ✍️ Bismillahirrahmanirrahim So da Buri Free Book 71 Barkanmu da sallah Al’ummar Musulmi🥰 Allah ya maimaita mana, Ameen. Abba Madu yana gama waya da Dad Motar su Baban Sakina tana yin parking. Sai da Baban Sakina ya raka su har ciki tukunna ya ce “Bari ya je ya samu d’an uwanshi ya sanar da shi halin da ake ciki.” Yana fita su kuma suka fara korawa Shuwa bayani…. Har ga Allah Shuwa ta ji dad’in hakan..at least su duka ukun za su zauna a family d’aya. Basu damu da gyangyad’i da jirin da take yi ba (dan allurai da abun da Ashraff ya shak’a mata masu k’arfi ne sosai) Haka suka duk’ufa wajen gyarata Ita kam anayi ma tanata baccin ta. Sai dare tukunna Huda ta samu ta kira Mama Gramma Ummu da Abba ta gaidasu. Suna gama waya da Abba ta fara jiyo motsi dan haka tayi sauri ta runtse idanuwanta kamar mai bacci. Dama ya bata dinner ta ci ta yi sallah tukunna ya fita bayan ya ce mata “bara ya je ya d’an yi aiki” Dan in dai yana gabanta to ya san ba abunda zai iya tab’ukawa. Yana ganin yadda ta lumshe idanun nata ya fahimci ba bacci take yi ba! Murmushi kawai ya yi ya k’arasa y’an abubuwan da zai yi ya hayo kan gadon. Tashi d’aya ya lura da yadda jikinta ya hau b’ari dukda kuwa baccin k’aryar da take shararawa amman he cant help it! Ba k’aramin k’ok’ari ma ya yi aka kawo yanzun ba. Addua ya yi ya tofa ya shafa mata shima ya shafa. Jin an shafa mata addua ya sanya hankalinta yad’an kwanta a tunaninta kyaleta za ayi amman inaa nan take ta ji sabon labari… Babu daman kwacewa dan yau ma Aslam d’in da gaskensa ya zo mata kamar jiya. Babu kalar magiyar da bata yi amman yayi mata kunnen uwar shegu!…… Ga rad’ad’i ga azaba ga ciwon kai ga rashin bacci shiyasa kafin asuba zazzab’i ya rufeta, ruf!. Shi ya kira family Doctor ta zo da sassafe ta yi mata allurai harda k’arin ruwa tukunna ta d’an ji dama dama… Ba abunda yafi bata tsoro irin yadda ya sake zuwan mata yauma kamar jiya da shekaran jiya. Ita kam har mamaki da tsoro ya fara bata dan idan yana wani abun kamar wani mai aljanu..yanzun zaka ganshi garau amman yana d’aukar hanya zai birkice sam baya ji baya gani. Bashi da aiki sai dai ya bata abinci ya yi ta lallab’ata yana faman lallashinta yana kula da ita, ya yi ta gaya mata kalaman soyayya yana lallashinta Idan dare yayi kuma a koma ruwa...... Tun a washegarin ranar aka shirya musu komai na tafiya. Basu wani sha wahalar yiwa Sakina komai ba saboda Dad ne akan komai. Auwal, bai san da labarin ba dan ko da aka gayawa Mom da ta ga jikin nasa yad’an nutsu kamar ya sani sannan nan da kwana biyu Sakinar zata zo sai kawai ta barshi akan sai ta zo d’in ya ganta kawai a surprise Another thing kuma tana tunanin in dai Auwal ya ji an aura masa Sakina kuma tana Nigeria tou tabbas zai iya tsige oxygen d’in ya dawo gida ko bai gama warkewa ba..... Tun lokacin da aka ce ‘visar su ta fito gobe zata wuce’ Take kuka! Har yau da safe..Shuwa da su Baaba Talatu da Ummu ne sai kuma matar wan Mijin Ummu sai wata distant cousin d’insa, suka shirya za su kaita MT. Suna cikin shiri Anty Zainab ta shigo ita da su Khadija waenda zuwansu kenan. Da mamaki Mama take kallon Anty Zainab d’in wadda duk ta rame ta lalace jikinta yayi mugun sanyi kamar ba itaba ko dan ta jima bata ganta ba dan ko ranar da Kaka ya kirata ta je bata ganta ba tana d’aki wai tana bacci. Inda Mama take Anty Zainab ta nufa tana zuwa ta rungume ta sai kuma ta fashe da kuka!. Duk tsayawa suka yi suna kallonta da mamaki. A hankali Mama ta zaro ta daga jikinta kafin ta ce “Haba Zainab kuka kuma?” Cikin share hawayenta ta ce “Dole in yi kuka Maryam! Dole in yi takaici da bak’in cikin abubuwan da na aikata.. Na yi miki laifi na yi kuskure wanda a yanzu nake matuk’ar danasani, sam! Na kasa nutsuwa na kasa yafewa kaina.” Sai da ta share hawayenta wasu suna sake zubowa tukunna ta d’aura da cewa “Yanzu haka daga gidan me unguwa nake..na je na fad’a masa gaskiyar laifin da na yi miki sharrin da na yi miki wanda yayi sanadiyyar har aka koroki a makaranta.. Na gayawa Kaka shima gaskiya. Ki tayani neman yafiyar Abba dan Allah Maryam kema ki yafe min na yi kuskure Sadiya ta cuceni! Wallahi duk hud’ubarta ce ta sanya na juyawa aminiyata baya” Ta k’arashe maganar tana fashewa da wani sabon kukan. A hankali Mama ta yi hugging d’inta tana murmushi kafin ta ce “Zainab! Har ga Allah ba zan ce miki zan iya mantawa da abunda kika yi mini ba a lokaci guda ba, dan zan iya cewa ke ce ummulabaisin fad’a na da su Abba. Amman maganar yafiya kam wannan na yafe miki Allah ya yafe mana gaba d’aya. Sanna ki yi k’ok’ari ki yafewa Sadiya itama ko ba komai kar abun ya yi mata yawa saboda ko da bakin y’an layi aka barta ya isheta! Dan kowa idan ya tashi magana ita, kowa matsalarsa Sadiya… Idan mu bamu yafe mata mun yi mata fatan alkhairi ba wa zai yi?”. Wani sabon kukan Anty Zainab ta fashe dashi tana mamakin kyakkyawar zuciya irinta Mama. Da kyar su Shuwa da Ummu har Maman suka samu suka lallasheta ta nemi waje ta zauna tana gunjin kuka. Basu kai ga fara magana ba Madu ya shigo ya ce “Su fito da Sakina ga motocin MT sun k’araso” Sai a lokacin ta saki kukanta mai sauti…. Haka nan tana kuka tana komai Mommy da Mammy suna shigowa aka d’auketa aka fita da ita. Tana shiga motar motocin suka d’auki hanyar MT. A b’angaren Gramma aka ajjiyeta. Hudan, daman ta san da zuwan nasu dan basu ma dad’e da gama waya da Sakinar ba, shiyasa tana jin shigowar motoci ta lek’a ta sama da yake gidantane a farko farko yasa ta hango su. Tama manta da ciwon kafa da na jikin da take yi…Haka nan tana takawa tana d’an d’ingishi ta nufi hanya.. Da kyar ta iya sauk’a daga benen farko kawai sai ta durk’usa a wajen ta saki kuka… A haka Aslam ya shigo ya sameta. A rikice ya k’arasa ya hau tambayar ta ‘me ya sauk’o da ita?’. Ko kallon sa bata yi ba ta mik’e kawai ta fara k’ok’arin wucewa wanda sai a lokacin ne ya gane matsalarta… Dariya da tausayinta ne suka rufeshi amman ya dake ya b’ata rai ya ciccib’eta. Duk kalar rigima da yakushin da take yi mishi da kuka bai diretaba sai da ya kaita kan gadon tukunna. A hankali ya zauna ya kamo hannunta tana shirin mik’ewa ya ce “Ki nutsu. Kin san dai Sakina ba zata tab’a wucewa ba tare da ta zo ta yi miki sallama ba ko? Ki kwantar da hankalinki yanzu ma da na ajjiye su na ji suna cewa duk za su shigo miki kafin su wuce” Shiru ya yi yana kallonta still kafin ya ce “Yanzu ke idan aka barki a haka a wannan yanayin naki za ki je gaban su Ummun?”. Sai a lokacin kanta ya d’an d’au chaji. A hankali ta sunkuyar da kanta kafin ta ce “Ya Aslam tou dan Allah ka je ka taho da su, kar su k’i zuwa.” Sai da ya d’an yi shiruu tukunna ya kamo hannunta ya rik’e ya d’anyi kisssing sannan ya ce “Okay love, amman ki nutsu kin ji” D’an d’aga masa kai ta yi alamun ‘okay’. Ya d’an jima yana kallonta yana murmushi kafin ya sauk’e ajiyar zuciya a hankali ya ce “Alhamdulillah”tukunna ya mik’e ya fice a ranshi yana tunanin ta yadda Hudan take so ya je ya sake fuskantar su Ummu! Shi fa da kyar ma ya iya tsayawa suka gaisa especially ma Mama lokacin da ta rako Sakina har k’ofa, wata irriyar kunyarsu yake ji gaba d’ayansu. Shi kam gaskiya idan Mama ta k’araso estate d’inma bai san taya za su kaya ba. Cikin ikon Allah yana sauk’a parlourn chan k’asa Khadija da Yayarta suka shigo tare da Gramma da Sakina, dan Sakinar tunda taga su Ummu za su tafi ta sake d’aga hankalinta shine Gramma ta ce ‘bara ta yi bribing d’inta ta kaita wajen y’ar uwarta’. A parlourn sama Gramma ta ajjiyeta bata k’arasa chan sama ba ta juya ta fice dan tashi d’aya ta fahimci Aslam d’in baya so ta had’u da Hudan. Ba kunya haka ya kinkimeta bayan ya koma sama wajenta wai zai kaita wajensu. Da kyar sai da ta saka mishi kuka tukunna ya sauk’e ta ta yi practicing tafiyar da zata yi a gabanshi ta d’an dedeta yanayinta dan duk tayi kalar da duk mai hankalin da ya ganta sai ta tona masa asiri ne, ga kuma ciwon k’afa da na jikin da suka taru suka sauk’ar mata da d’ingishi. Sannan ya kama mata hannu ya d’an karata a jikinsa suka sauk’a tare. Suna tahowa Khadija ta fara yi mata dariyar tsokana k’asa k’asa Sarai Hudan ta fahimceta amman ta basar dan bata shirya biye mata ba Ita a ganinta wannan lamarin da take ciki jaje ya kamata ayi mata ba tsokana ba dan ita komai ya wuce tunaninta. A kusa da Sakina ya ajjiyeta kafin ya ce “Su zama ready nan da 2 hours su Sakinar za su wuce In sha Allah” Yana gama fad’in haka ya juya ya fita. Yana fita Huda ta fad’a jikin Sakina ta yi hugging d’inta. A hankali ta ji Sakinar ta sa kuka, d’agowa ta yi ta d’an b’ata rai itama idonta yana kawo kwalla ta ce “Haba mana dan Allah ki daina kar ki saka ni kuka nima” Ta fad’i haka ragowar hawayenta yana zubowa. Murmushi su Khadija ita da yayarta suka yi kafin Yayartata ta ce “to yanzu wa zai lallashi wani?” A hankali Huda wadda taga d’an rashin kyautawarta ta juya ta yi hugging Khadijar sannan ta kamo hannun Yayar khadijah daga inda take zaune ta ce “ina wuni” A hankali tana murmushi dan itama yanzu duk ta sauk’o ta ce “Alhamdulillah, gida yayi kyau Huda Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya” A hankali ta juya cikin d’an tsokana da dauriya ta yayewa Sakina fuskarta, dan har yanzu fuskar tata a rufe take cikin mayafin laffayar da aka nad’a mata. Da kyar ta iya daurewa batayi kuka ba, fuskar nan tayi dagaje dagaje ta yi jajawur kana gani ka san ta ci uban kuka bana wasa ba, daman tun shekaran jiya da suke waya take jin yanayin muryarta a dashe. Cikin son sakata nishad’i ta ce “Haba mana Sakina, ki daina kuka, kinga fuskarki kuwa? Gashi duk kin yi wani laushi kamar ba ke ba. Ai ba wai zama za ku yi achan d’in ba har abada, yana warkewa fa za ku dawo in sha Allah…Ni kumafaa daa? da zan tafi chan wani gari ba ke kika yi ta bani kwarin guiwa ba?” Ta k’arashe a hankali daga nan ta yi shiru ta kasa ci gaba da magana. Su Khadija ne suka saka baki, suka taru suka yi ta lallab’ata har sai da ta d’an sake ta bar hawayen ta d’an kwantar da hankalinta tukunna suka d’an shiga hira a hankali. Khadijah ce ta ce “Gaskiya Huda gidan ki ya had’u over! Kalla kuma kaya koina duk girman gidan. Bara mu lek’a mu kashe kwarkwatar idonmu” Ta fad’i haka tana ajjiye mayafinta ta mik’e. Itama yayartata mik’ewa ta yi. Hudan har ta mik’e ta d’an fara takawa za ta bisu Khadija ta kamo hannunta ta zaunar da ita ta ce “zauna mai tafiyar ta’ta’taaa mun san hanya” Duka Huda ta kai mata ta yi saurin gocewa tana dariya suka nufi k’asa ita da yayar tata. Banda dukan uku uku ba abunda k’irjin Sakina yake yi daman tun d’azu ta d’an tsorata da yanayin tafiyar tata da ta gani. Maganar da Huda ta fara yi mata ne ya dawo da ita daga duniyar tunani da tsoron data tafi. A hankali ta juyo tana kallonta jin tana cewa “Ya Arshaad ya sake guduwa.. Ba a san inda yake ba! D’azu inaji Ya Aslam suna maganar shi da Dad a waya da na tambayeshi kuma sai ya k’i gaya min komi, kamar ma haushi ya ji.” Ta k’arashe maganar cikin karyewar zuciya. A hankali Sakina ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya kafin ta ce “Hudan I can’t even begin to imagine what Ya Arshaad is goin through! Dauriya ce kawai yake yi dan haka idan ya ga ba zai iya zama ba ya nuna yanaso zai tafi ya kamata ku bashi space ku barshi ya tafin. Kuma dan Allah ki daina nuna damuwarki over a kan Ya Arshaad a gaban Ya Aslam…Yes! Na san dole abun is somehow amman ki d’an dunga daurewa har Allah ya yaye miki son shi a zuciyarki ki manta da shi ki rungumi Mijin da Allah ya zab’a miki ku zauna lafiya dan na san Ya Aslam yana sonki wallahi tun a mansion d’in chan naso In fahimci wani abun shiru kawai na yi miki.” Shiruuu, Hudan ta yi kamar tana tunanin wani abu kafin chan ta ce “Yauwa Sakina, kin san wani abun mamaki? Ashe Ya Aslam ya sanni tun kafin yazo gidanmu shi da Ya Arshaad............” Nan ta zaiyyane mata labarin da ya bata da kuma yadda yake nanata mata yana ‘tsananin k’aunarta’ yake kuma gwada mata. Da zaman da suka yi a chan gidan da komai…… Murmushi kawai Sakina ta yi kafin ta ce “Hudan you are lucky, Very lucky! Ban yiwa Ya Arshaad adalci ba amman inaso ki rubuta ki ajjiye ni Sakina na ce ‘Ya Aslam ya fi k’aunarki Akan Ya Arshaad’ Sannan Huda dan Allah ki daina pushing d’insa away ki janyo abunki ku rungumi juna, Allah ya bawa Ya Arshaad shima tashi wadda zai so. Ki nutsu, ki fahimci karatun soyayyarsu su biyun duk true love suke yi miki that I’m sure of amman ko waye yaji labarinku ya san Ya Aslam ya fi k’aunarki although Ya Arshaad shima has sacrificed a lot for you sannan shine ya reneki kika zama mutum therefore na san ba lalle ki iya mantawa da halaccinsa ba wanda ni kaina ba zan tab’a mantawa ba amman Huda soyayyarki da Ya Aslam daban take a cikin labarin soyayya! Ki nutsu kar ki cuci kanki dan kema kina son abunki fahimta ne kawai baki yi ba.” Hudan na shirin yin magana Aaima ta hawo. A kan 3 seater da suke zaune ta zauna kafin ta ce “Anty Huda da Anty Sakina, kinga na kasa hak’ura sai da na sake biyoki ko?” Ta fad’i maganar tana kallon Sakina. Murmushi kawai Sakina ta yi ta kamo hannunta. “Crying bride” Aaiman ta ce tana d’an lakatar hancinta, sannan ta d’aura da cewa “Amarefa sun daina kuka yanzu” A hankali Sakina ta d’an kwanta a jikinta ta ce “Thank you Aaima. A lot!” Murmushi Aaiman ta yi kafin ta ce “Ba komai Sakina, Allah yasa mu dace. Ni dai yanzu matsalata shine wannan kukan da kike yi, ki daina pls, ko kun zo tafiya kar ki sake yin wani kuka Ya Auwal raina ki zai yi! Bar ganin bashi da lafiya Allah idan ya tusoki gaba ko hmm.. Gara ki nuna mishi kema Amaryar zamani ce” Duk murmushi suka yi kafin Huda ta ce “Aaima Allah duk ranar da za a kaiiki gidanki idan kika yi kuka ni kad’ai na san me zan yi miki” Murmushi ta yi ta sauk’e ajiyar zuciya kafin ta ce “Speaking of which..Ina son tambayarku wani abu amman kunyar ku nake ji” Ta fad’i hakan tana rufe fuskarta da tafukan hannunta. Dariya duk sukayi dan yadda ta yi d’in dole ka yi dariya. Cikin dariyar Hudan ta ce “Mene pls?” Sai da ta d’an dara itama kafin ta ce “Sakina wanda ya maidaki gida shekaran jiya wachchar Brothern ku ne?” “Woow!!” Sakina ta ce da d’an k’arfi tana d’an zaro idanu waje kafin ta ce “An gama! Ai harma na hango ranar d’aurin auren ku. Kin san shima sai da ya ce min he felt something..” Wani ihu Aaima ta yi a hankali sosai irin na jin dad’in nan kafin ta ce “Shikenan…” sai kuma ta sunkuyar da kanta ita ala dole ta ji kunya, k’arshe ma tashi ta yi ta tafi bayan ta yi hugging Sakina ta ce mata “A kula da Ya Auwal plss Allah ya bar k’auna sai kun dawo” Tana fita Sakina ta zaro waya zata kira Junaidu Hudan ta rik’e mata hannu. Da d’an mamaki ta juya tana kallonta kafin ta ce “mai ya faru?” A hankali Huda ta ce “Sakina Aaima bata yi deserving suruka da k’anwar Miji irin Umma da Jalila ba. Shiruuu Sakina ta yi itama duk sai jikinta ya yi sanyi, a hankali ta ce “Tabbas” Dede nan su Khadija suka hawo suna haki Yayar Khadijan ce ta ce “Hudan wannan tour a gidanki ai aiki ne!” Sai kuma ta ce “Na ga d’akin da zan zauna idan na zo yi miki wankan jego a chan ma muka shantake Gadon laushi Allah yasa dai idan nazo kar in yi ta bacci dan gadon nan duniya ne.” Dariya Khadija ta yi kafin ta ce “Ai kuwa ki shirya dan alamu sun nuna nan da wata tara cif za ki dawo zaman jegon. Duk dariya suka yi banda Huda wadda hankalinta ya fara tashi dan ta ga yamma ta fara yi. Sai da suka huta tukunna suka mik’e suka dudduba saman chan sama kuwa suka ce basu isa su shiga turakar sabbin maaurata ba haka kurum su ganewa kansu. Haka nan Khadijah ta tisa Hudan a gaba sai shak’iyanci take yi mata Hudan kuwa kamar ta yi kuka dan ita kad’ai ta san halin da take ciki. Suna a haka Gwaggo Asabe ta shigo, abun dariya suna had’a ido da Sakina kawai sa Sakinar ta saka kuka…. Dakyar aka lallab’ata aka rarrasheta suka yi sallama da Huda tana kuka itama tana kuka Gwaggo Asabe da su Khadija suka yi mata rakiya har bakin mota su kuma su Khadijan aka saka driver ya maidasu gida daman sun yiwa Huda sallama, ta so ta basu ko d’an inner wears ne na sa rana da ake rabawa, ganin a yanda suka tafi yasa ta yanke shawarar kai musu har gida in shaa Allah. Aslam, ne ya kai su Sakina har airport, ita da Daddy za su yi tafiyar wanda yaketa janta da hira da barkwanci ba ruwanshi da wani batun surukantaka, sai da ya ga ta d’an sake tukunna ya ji dad’i… Haka har jirginsu yayi taking off. Duk dauriyar Sakina sai da idonta ya cicciko sanann ta k’ank’ame kujerar da take kai, sai da jirginsu ya dedeta ya lula sararin samaniya tukunna ta samu nutsuwa Daddy yana ta tsokanarta. Washegari da daddare Granpa ya nemi ganin kowa! A lokacn jikin Huda ya d’an yi sauk’i tafiyar ma ba laifi dan k’afar tata ma da sauk’i dan haka suka tafi tare ita da Aslam. A chan suka tarar da kowa. Suna zuwa Huda jikin Mommy wadda ta fara mik’o mata hannu taje ta fad’a. Sai da suka gaisa cikin so da tattali tukunna ta mik’e ta nufi inda Aslam yake a gaban Granpa. “Hmm” kawai Mammmy ta ce ta yi d’an mitsitsin tsaki sannan ta kauda kai. Cikin kulawa Granpa ya amsa gaisuwar tata ya na mai tambayarta “ya sabon guri?” “Alhamdulillah” ta ce ba tare da ta iya d’agowa ba dan gaba d’ayansu kunyarsu take ji. Sai da kowa ya zauna tukunna Granpa ya kalli Dad ya ce masa “Ina Muhammad?” Cikin tsananin tashin hankali da rashin jin dad’i dan su already sun san case d’in tun 3 days ago shi da su A hankali Dad d’in ya ce “Bamu gansa ba since” Ajiyar zuciya Granpa ya sauk’e, shi kansa bai san ta Ina ma zai fara ba. A hankali ya ce “Yi musu waya su shigo za a nemoshi.........” Mutanen nan da suka zo suka d’auki sample na tomb print d’insu sukayi musu tambayoyi sune suka shigo. Dukkan su waje suka nema suka zazzauna bayan sun kai wani file gaban Granpa sun ajjiye. A hankali Granpa ya kalli Dad ya ce “Kirawo Yusuf! Duk da ya san komai ya kamata a yi komai da su har Auwal da Adama” Computer d’in parlourn ya yi using ya kira Daddy..,, Mom na gefensa a lokacin suna cin abinci, yana ganin kiran ya ji gabnsa ya yanke ya fad’i! Dan haka ya ture abincin ya d’auka ya ajjiye wayar a gabansu shi da mom. Bayan y’an gaishe gaishe Granpa ya ce “Ina Auwal?” Suka ce “su suna hotel su Auwal kuma suna asibiti” Kamar zai ce ‘a kirashi shima’ sai kuma kawai ya ce ‘a barsu kawai’ Daga nan ya yi gyaran murya ya fara magana….. “Last week waennan mutane sunzo sun karb’a tombprint d’in kowa! Na san ba lalle kun san dalilin d’aukar tombprint d’inba dan haka bara in yi muku bayani.” A hankali Aslam ya mik’e ya ce “Granpa, please excuse me” Kana ganin fuskarsa ka san yana cikin tsananin tashin hankali. Cikin no nonsense face Granpa ya yi amfani da kakkausar muryar wajen ce masa “Koma ka zauna!” Babu alamun wasa a tattare da shi. A hankali Aslam ya koma ya zauna yana sauk’e ajiyar zuciya a jejjere jijiyoyin kansa duk sun baiyyana…Ya rasa wanne irin taurin kai ne Granpa yake da shi! Shi sam bai yi tunanin wannan maganar za ayi ba da wallahi ba zai zo ba! Shi a tunanin sa sun riga sun gama kashe case shi da su granpa d’in da su Abba har abada……. Muryar Granpa d’in ce ta katseshi jin ya ci gaba da magana yana cewa “Dalilin da ya sanya aka d’auki tombprint d’inku ba komai bane ba illa… A lokacin da ake bincike an yi nasarar samun yatsun mutum biyu da palm a jikin tukunyar da Huda ta dafa coffee wanda kamata yayi a samu tombprint d’inta ita kad’ai tunda hatta Ummi ta ce bata tab’a tukunyar ba ma Ita ta zuba mata da kanta.” Kwarewa Mammy ta yi da k’arfi wanda duk ya janyo hankalin jama’a kanta. Da sauri Aaima ta je ta matso ruwa a dispenser ta kai mata suka shiga shafa mata baya ita da Mommy tana sha tukunna ta d’an dawo dede. Ajiyar zuciya Granpa ya sauk’e kafin ya ci gaba da cewa “Bincike yana tafiya bayan an yi testing tukunyar an tabbatar da poison mai k’arfi ne a ciki sannan har da shinkafar b’era. Sai kuma still aka samu gidan allura a cikin dustbin d’in kitchen d’in wanda ba komai ne a cikin wannan allura ba face poison d’in da aka yi amfani da shi aka zuba a cikin coffe d’in. Tou a jikin syringe d’inma kuma sai aka sake samun wani sabon tombprint d’in wan..........” Shigowar Arshaad ce ta katse Granpa da kowa na wajen gaba d’aya sai kallo ya koma kansa. Shiruu parlourn ya d’auka na y’an mintuna kafin ya ce “Assalam alaikom, sorry I’m late” Bai jira jin me za su ce ba ya k’arasa gaban officer d’in kawai ya mik’a mishi hannayensa duka biyu. Kuka Dad ya saka kawai ya mik’e ya fita. A hankali Granpa ya sunkuyar da kanshi k’asa wasu zafafan hawaye suka zubo masa. Da mamaki Mommy ta mik’e ta k’arasa wajen ta kamo hannun Arshaad cikin zaro ido ta ce “Arshaad me ye haka ?” Da kyar ya samu hawaye ya zubo masa a ido d’aya! A hankali yana kallonta ya ce “Mommy ni ne! Duk wannan bayanin da Granpa yake yi muku a k’arshe suna na za ku ji a matsayin mai laifi! Ni na yi poisoning Ummi wanda Aslam naso kashewa tashi d’aya abun ya fad’a kan Ummi dan haka dan Allah taron nan ya watse haka, ku daina kwana kwana kowa ya tafi officer please arrest me” Ya k’arashe maganar yana sake juyawa ya mik’awa officern hannuwanshi duka biyu kamar farko. Mik’ewa kawai officer d’in ya yi ya zaro ankwa. Ba k’aramin tashin hankali Mommy ta shiga ba bata san lokacin da ta shiga tsakaninshi da officer d’inba cikin fushi ta cewa officer “meyene haka yake faruwa?” Kafin ta juya ga Arshaad ta ce “Arshaad ba zan bari ka tafi gidan yari ba!” Ta fad’i haka tana nunashi da yatsanta dede fuskarshi alamun warning tana hawaye sannan ta ci gaba da cewa “Ko meye ka aikata ba zan bari ka tafi gidan yari ba wallahi! Na san ba halin ka baneba pushing d’inka aka yi kayi hak’uri ka dawo Arshaad d’in da muka sani” Cikin kukan ta k’arasa gaban Granpa ta ce “Granpa Ummi kanta na san ba zata so haka ba! Dan Allah in domin ita kake yi to ka yafewa Arshaad ransa ne ya b’aci zuciya ce ta kaishi ba laifinsa bane ba.” Gani tayi kawai mutumin yana k’ok’arin sakawa Arshaad wanda ya tsaya kawai yana hawaye ankwar, da sauri ta mik’e ta koma wajen ta fincike ankwar ta yar sannan cikin fad’a ta cewa mutumin “Wallahi bar ganin aikinka kake yi, na rantse da Allah idan ka saka mishi ankwa sai na tsinka maka mari!” Runtse ido Arshaad ya yi da k’arfi kafin ya samu ya bud’e ya juyo da Mommy ya ya kama kafad’unta duka biyu ya fara magana cikin d’aci Idanuwanshi jajawur “Mommy ba laifi d’aya bane a kaina okay?! Ko kin kawar da wannan dole zan tafi jail saboda Junaidu ya yi filing complaint a kaina and all evidences are against me so just let it go this is wat i deserve. Dan Allah.” K’amewa kawai ta yi tana kallonshi. A hankali Aslam ya k’araso wajen ya dafa shi ya ce Arshaad! Ka juya ka fita a parlourn nan zan san abun yi please. Dan Allah ka tafi kawai! Meye ma ya kawo ka nan in the first place?!” Ya fad’i hakan cikin d’an d’aga murya. A hankali Huda wadda ta k’araso wajen yanzu itama tare da Aaima ta ce “Ya Arshaad me ya had’aka da Ya Junaidu?” Lumshe idanuwansa ya yi a hankali ya juyo yana kallonta ya ce “Kin tuna sharrin da aka yi masa akan case d’in Chief Justice!? Sannan akaso a sake d’auke shi bayan an sakeshi? Those that ring a bell??” A firgice wani kalan kuka yana taho mata ta ce “Ya Arshaad dan Allah kar ka ce min kaiine! Dan Allah Ya Arshaad” Sai da ya matsa dede setin fuskarta tukunna yana kallon cikin idonta ya ce “It was all me!” Wani irin kuka ta fashe da shi ta durk’ushe a wajen cikin kukan ta ce “How?? Why???” Ranshi a tsananin b’ace ya ce Why? Tambayata ma kike yi ‘why’!? Bara ki ji dalili ‘It was all because of you’ And bari ki ji abunda ya faru… Naga take taken Junaidu At that very day kuma kema naga kamar kina k’aunar sa, nuna miki ne ban yi ba amman hankalina a matuk’ar tashe na bar wajen ki. Na biya ta wajen friend d’ina Jamil! Sai na samu suna tattaunawa akan wata magana…Yanayi na yasa ya tambayeni dan haka ban b’oye mishi komai ba na fad’a mishi damuwa ta. Ya san ki ya san yadda nake sonki shiyasa ya ce ‘in bashi number da information d’in Junaidun kawai’. Abun ya zo mana da sauk’i saboda already best friend d’in Junaidun Yaron Abokin nawa ne Jamil. A time d’in ban san me za su yi ba kawai ni dai nace ‘a san yadda za a yi min da Junaidu’ Sai da aka kashe mutumin tukunna na fahimci me sukayi.” Cikin d’aci ya ce “Kinsan wani abu?” Be jira jin me zata ce ba ya ce “Ban damu ba! Kwata kwata ban damu da kisan kan da aka yi ba saboda Idanuwana sun rufe I was just selfish and bad! And happy tunda Junaidu ya b’ace kenan babu abunda zai sake shiga tsakaninmu ko ya yi yunk’urin raba mu. Ban damu da yadda ya sha wahala a Prision ba bayan an sake shi na sa a d’auko mini shi.” Yana kallonta ya sake cewa “Kinsan wani abu?” Nan ma be jira amsa ba ya d’aura da cewa “Ko da aka ce motar su ta kama da wuta Hudan ban ji haushi ba ban ji babu dad’i ba ban kuma fad’awa kowa na san wani abu ba! Na take komai na rufe idona duk dan inga na mallakeki! I was bad! Ban yi deserving freedom ba so pls dan Allah ku bari kawai su tafi da ni.” Cikin fushi Aslam ya ce “Ba za a bari ba! Da kasa aka kama Junaidun ai kuma still kai kasa aka dinga bashi shelter da abinci mai kyau Kaga hakan yana nuni da still akwai good in you Arshaad you felt guilty which is good.” A hankali ya juyo ya kalleshi kafin ya ce “For your information nine na janyo aka rufe maka company d’in takalman ka! Is there any good in me left?” Ya fad’i hakan yana kafeshi da dogayen idanuwanshi. A hankali ya ji Aslam d’in ya ce “I know Arshaad na san komai! Tun kafin In tafi a time d’in da aka kirani na fahimci kai ne So dan Allah maganar nan ya wuce please”. Cikin katseshi ya ce “Na so In kashe ka! Ka bar duniya gaba d’aya In auri matarka! Is there any good in me? Still kana da hope a kaina ........” “Ina za ki je?” D’in da Granpa ya ce ne yasa gaba d’ayansu suka juya suna kallon k’ofar da Mammy ta nufa sad’af sad’af zata fice. A hankali Mom wadda tun d’azu take magana ba a jinta tace “I have something to say” Da d’an k’arfi. Duk juyawa akayi aka zubawa screen d’in ido, suna kallonta Idonta sharkaf da hawaye ta ce “Arshaad baka so kashe Aslam ba! Ka dai yi yunk’urin yin hakan amman kuma baka aikata ba saboda baka so ba....…… A ranar birthday d’in su Shuraim! Bayan Dad ya gama yi mana fad’a akan Sakina da abubuwan da muke yi..I was furious! Sannan burin da na d’aura akan Auwal ya mallaki MT duk sai naga yana shirin tab’arb’arewa tunda na lura shi soyayya ce a gabanshi a yanzu! Hankalina bai sake tashi ba sai da Mammy ta sanar min da cewar ta ga copies d’in takardun MT da Granpa ya mallakawa Aslam a d’akin ka a ranar Lokacin da ta shiga kai kuma ka fita ka barta a d’akin, wanda bamu san ma an mallakawa Aslam d’inba kuma bamu san ya aka yi kai ka sani ba. A take take ce min ‘Komai ya zo mana k’arshe ni da ita! Amman ta samo mana solution dan daman tun da taji labarin kyautar gidan da Granpa ya yiwa Aslam ta gama cire hope akan MT a Yaranmu muddin Aslam yana raye!.. Dan haka yanzu it’s either I’m with her ko kuma I’m doomed’. Sai da muka keb’e mu biyu tukun ta yi min bayanin abunda za a yi shine… ‘Ga shinkafar b’era nan daman ita da shirin ta ta zo gara kawai a yita ta k’are!’. Dukda a lokacin i was furious amman ban yi amanna da shirin nata ba, sai da ta yi mini cikakken bayani kuma na lura komai ya kusan zuwa mana k’arshe tukunna na yarda but still sai na ce mata ‘Gara mu zuba iyaka wadda zata la’antashi ko ta sakashi doguwar jinya dan ni gaskiya ba zan iya kashe Aslam ba’. D’ari bisa d’ari ta nuna min ta yarda, ban tashi sanin Mammy yaudarata ta yi ba sai da na ga gawar Ummi a kan cinyata”. Ta fad’i hakan tana fashewa da kuka. Da sauri Mammy ta k’araso wajen ta ce “bana son munafurci! Munafuka ai da ke aka yi....” Wata mahaukaciyar tsawa Dad ya daka mata ya ce “wallahi idan kika sake yin magana sai na kasheki da hannuna kafin a tafi da ke gidan yari!” In a serious tone Granpa shima ya ce mata “Ki nutsu! Ko In saka a fasa miki kai da bindiga” Sannan ya juya ya cewa Mom “Continue” Cikin kuka Mom ta ci gaba da magana “Muna tunanin ta yadda za mu shiga d’akin su Aslam mu zuba a lemon cikin fridge d’in da yake a d’akin nasu ko mu zuba a ruwa ya sha sai Allah ya kawo sauk’i muka ji ya cewa Huda “ta had’a mishi coffe” Hudan na shigewa kitchen aka fara watsewa, muma muka fita Mammy ta cewa Dad ‘zata tafi tare da k’awarta ta ajjiyeta a bakin gate yanzu’. A gaban sa ta shiga motar kawar tata, motarsu shi da Aisha tana fita ta fito ta yiwa k’awartata sallama muka zagaya baya ta ce min ‘in tsaya a nan baya in tabbatar babu wanda ya ganta In yi keeping mata watch daga nan ita kuma zata shiga ta aiki Huda ko kuma dai ta d’an ja hankalinta ta watsa gudun kar idan zance ya fito Huda ta ce ita ce ta aiketa’. Har zata juya na rik’o hannunta na ce mata ‘ta zuba d’an mitsitsi kawai dan Allah’ A gabana ta nuna min d’an k’aramin da zata zuba wanda na tabbar ko b’era ba lallae ya iya kashewa ba! Na so ta bani ragowar amman sai ta ce ‘ko dai ban yarda da ita bane ba?’ Shiyasa kawai na yi trusting d’inta na barta ta wuce. Kafin Mammy ta zagaya ina zuwa bakin k’ofar kitchen d’in ta baya sai na ga Hudan ta fita! Ina shirin kiran Mammy a waya naga an shigo.. Wallahi Arshaad fuskarka da jikin ka a rufe suke ko’ina amman tashi d’aya na gane ka. A tunanina bakin ku d’aya kaida Mammmy sai da na ga ka zaro allurar da bata cikin tsarin mu tukunna gabana ya fara fad’uwa. Ba k’aramin sanyi na ji ba da naga har ka bud’e allurar zaka zuba kuma sai naga ka yi tsaki ka rufe ka mayar ka ajjiye alamun ka fasa”. A take gaba d’aya kowa a falon aka ce “Alhamdulillah” Cikin kuka ta ce “Garin lek’en ka da nake ta yi yasa har ka gannni ka fito ba tare da ka d’auke allurar ba. A cikin filawowi na b’uya kana wucewa na zagaya ta k’ofar parlour zan shiga kitchen d’in tun a bakin main door na parlourn na hango Huda tana shirin shiga kithchen d’in amman ban hango Mammy a kitchen d’inba wadda na tabbatar ita ce ta had’a da allurar da ba lalle ta gama sanin ta mecece ba ma da shinkafar b’erar ta matse gaba d’aya a cikin coffee d’in wanda sanadiyyar hakan ne na rasa y’ar uwa ta d’aya tilo a duniya. Da sauri na fita na zagaya baya. Ina zuwa bayan kitchen d’in na ga Mammy a wajen tanata gumi, ta ce min ‘ta zuba amma fa saura kad’an Huda ta kamata’. Jin kamar tahowar mutum ta bayan mu ne ya sanya kawai muka yi sauri muka bi ta gaba muka bar wajen. Na saka driver ya mik’a Mammy estate ni kuma na koma part d’ina.” Cikin kuka ta ce “Arshaad ba kai za a kama ba Mu za a kama…baka da laifin komai”. Da sauri Mammy ta ce “Ke dai za a kama munafuka!! K’arya take yi min, duk abunda ta fad’a k’arya ne wallahi.” A hankali Arshaad ya lumshe idanuwanshi wasu zafafan hawaye suna zubo masa. Mom bata damu ba ta ce “Another things… Although ban san waye ya turo Mommy daga bene ba but Mammy nake zargi dan na ji tana waya rannan kamar da malaminta ne tana cewa ‘a sake toshe mata baki a goge mata tunani kar ta tona mata asiri kafin ta san abun yi next da ita’ da kuma na tambayeta sai ta k’i gaya min komai dan haka bani da tabbas amman tabbas na san wanenen musabbabin ciwon nata tun farko Mammmy ce ta yi mata asiri! Har wajen bokan da yayi aikin idan kuna so zan kaiku. Shiyasa tun a cell Mommy tana warkewa mu bama ma saniba Ita kuma Mammy ta fara mugayen mafarkai Inaga sauk’ar da akeyi a gidan nan kullum ne ya sanya abun bai koma kanta ba ta samu mafarkan suka barta.” A hankali Aslam ya ce “Ita ta turo ta daga bene” Kafin ya kalli Mommy ya ce “Mommy ranar da naje zan ce miki Ina son tafiya Uk ana i jibi auren su Arshaad… Pretending kawai na yi dan ban san ta Ina zan fara ba sannan naji kin ce peace da kwanciyar hankali kawai kike buk’ata a yanzu Amman tabbas na ji conversation d’inku ke da Dad.” Mom ce ta sake cewa “Sannan mammy.....” Da sauri Mommy ta k’arasa gaban screen d’in ta had’e hannuwanta biyu ta ce “Dan Allah dan Annabi Adama ki yi shiru” Sai kuma ta fashe da wani sabon kuka. A hankali Granpa ya ce “kowa ya zauna” Ba ayi minti uku ba duk suka zazzauna har Arshaad da Granpa ya sake ce mishi “Muhammad zauna kaima” Da kyar Granpa ya samu ya ci gaba da magana…. “daZa mu yi amfani da tombprint mu hukunta mai laifi… Second hannun da ya fito a jikin tukunya apart from na Huda hannun Rukayya ne! Sannan ya sake fitowa a jikin syrinji tare da na Arshaad wanda na tabbatar kafin ya saka safar da Adama ta fad’a ne ya yi mistake ya rik’e dan bai fito a jikin tukunya ko murfin ta ba. Ya fahimci hakan inaga tun a ranar da aka d’auka samples d’in shiyasa ya yanke shawarar ya gudu! Ban kuma san me ya dawo da shi ba dan haka yanzu inaso ka fad’i gaskiya da gaskiya tun da an san komai kuma muma mun fahimci komai. Kaga waennan manyan y’an sanda da ss ne kar ka cuci kanka ka yi bayanin da zasu d’auki rahoto dan na yi alk’awari sai na hukunta duk wani mai hannu a kisan Ummi!. Shin maganar da Adama ta fad’a gaskiya ce?” A hankali Arshaad ya girgiza kanshi kafin ya ce “Ba haka bane ba! Ni ne na zuba! Ni na yi hacking wayar Sakina na kira Huda waje tana fita ni kuma na je na zuba! Dama inada wannan plan d’in a raina tun dawowata saboda na fahimci Aslam yana son auren shima. Granpa na rok’eka da girman Allah ka barsu su tafi da ni.” Tsabar takaici Aslam bai san lokacin da ya shak’o sa ba ya ce “Meyene ribar ka Idan an tafi da kai? Me za ka ji a jail!? Arshaad ka san inane jail kuwa?” Sai yanzu Gramma wadda tunda aka fara case d’in ta sunkuyar da kanta tana salati ta samu ta fashe da kuka… A hankali ta d’ago kanta ta taso ta iso inda suke ta kama Arshaad ta mik’ar da shi tana kuka ta ce “Aslam ka manta waye Arshaad ne? Tun kuna Yara Idan ya yiwa mutum laifi b’uya fa yake yi ko da ace mutumin ya yafe masa sai yayi kusan wata yana wasan y’ar b’uya da shi. Ka san Arshaad yana da kunya yana da kawaici kuma yana k’aunarka! Na tabbatar laifin da ya aikata ne ya saka shi yake jin ba lalle a yafe mishi ba sanann shi kanshi ba zai iya fuskantar kowa ba shiyasa ya gwammaci zaman jail a kan zama da mu sannan kuma ka tuna Arshaad yana iya sacrificing komai saboda Mahaifiyarsa unlike her! I’m pretty sure ita yake ta k’ok’arin rufawaa asiri wanda hakan ya had’u da Guilt shiyasa yake k’ok’arin tura kanshi jail! Haka ne ko ba haka ba! Arshaad?” Gramma ta k’arashe maganar tana sake fashewa da wani sabon kukan. Gaba d’aya kuka suka saka Aiima Huda Dad Sudais Shuraim Mammy Daddy Mommy hatta Granpa da Abba wanda yake chan a zaune ya kasa motsi kowa kawai hawaye yake yi. Hannuwan Gramma ya rik’e gamm! A cikin nasa ya ce “Gramma dole Ina da laifi one way or the other.. Ga Junaidu sannan ga successful company d’in da na tarwatsa na lalatawa Aslam… Na biyewa son zuciya Gramma! Na biyewa So da buri, ki kyaleni dan Allah ki rabu da ni I need time alone away from all of you! Besides Ina jin tsoron kaina a duk lokacin da na ga Huda da Aslam na kan ji tsananin kishi! Ba zan iya ba! This is torture! Ni kad’ai na san abunda nake going through” Ya k’arashe maganar yana fashewa da kuka. Wanann karon hatta Abba kuka ya saka. Da sauri Huda ta mik’e ta fita da sauri Aaima kuma ta bi bayanta. Bata tashi sanin Aaiima na bayan nata ba sai da suka shiga cikin parlourn gidanta. Jin mutum a bayanta yasa ta juyo suna had’a ido kawai sai suka fashe da kuka a tare gaba d’ayansu…. Da kyar Huda ta iya d’akko wayarta ta kira Junaidu yana d’auka ta ce “Dan girman Allah ya zo tana son ganinshi a kan case d’in Ya Arshaad! Ya dubi girman Allah ya taimaketa idan wannan ce alfarma d’aya tak da zai yi mata a duniya ya zo ya yi withdrawing complaints d’inshi dan ya rasulillahi...........” “Za mu yi arresting Rukayya Yusuf za mu tafi da ita! Za a sake bincikar ta sannan a kotu za ta ji hukuncinta” Daya a cikin y’an sandan ya fad’a……..... Anfi 20 minutes ana fama da Mammy dan hauka tayi musu tuburan da kyar sai da aka nuna mata bindiga tukunna ta tsaya aka datsa mata ankwa. Kukan da Arshaad yake yi sai da ya saka kowa kuka. A hankali ya durk’ushe a wajen. Mommy ma ta so hanawa amman Dad ya rik’eta haka aka fita da Mammmy tanata kuka tana tonawa kanta asiri dan sai faman jerowa Dad Granpa da Mommy Allah ya isa take yi a cewarta su ne suka tunzurata ta yi komai sannan in da Granpa bai bawa Aslam gida sannan ya bashi Mt a b’oye a munafurceba to da bata yi abunda ta yi ranar birthday d’in su Shuraim ba. Ana fita da Mammy bayan d’akin ya d’auki shiru na kusan 7 minutes. Babban y’an sandan ya yi gyaran murya ya sake cewa “Unfortunately za mu tafi da Arshaad shima.. Bashi da laifi a case d’in Ummi amman yana a case d’in Junaidu! Kuma Junaidu a sama shima ya kai k’arar shi dan direct case d’in daman hannuna ya fad’o. Sannan Aslam ma idan yanaso zai iya filing complaint ya yi shara’a da shi akan tarwatsa mishi company da ya yi.” Cikin tsananin b’acin rai Asalm ya k’arasa inda mutumin yake tsaye ya ce “Who the hell do you think you are? Ni zaka gayawa abunda zan yi da brother d’ina!? Idan na sake ji kace zan yi shari’a da shi I ‘ll make sure ka yi regretting kasancewarka d’an sanda! Off you go.. Just leave! Za mu k’arasa issue d’in mu mun gode.” A hankali cikin d’an b’acin rai mutumin ya ce “Mr Aslam watch you words! Kuma let me assure you Idan ba Junaidu ne yazo nan ya ce ya yi withdrawing complaints d’inshi a Arshaad ba to dole za mu tafi da shi! And idan ka yi interfering to za mu had’a da kai” A hankali Arshaad ya mik’e ya k’arasa ya dafa kafad’un Aslam ya ce “Let it go.. It’s fine i’m fine.” Yana shirin yin magana Junaidu ya shigo shi da Aaima………………… Tabbas! Ya so ya hukunta Arshaad, yaso ya hukuntashi akan irin abunda ya yi masa amma ta dalilin Hudan sannan tsakanin shi da Aaima tabbas ya san watak’il wani abun ya k’ullu dan tunda ya ganta ya rasa sukuni sam! Waennan dalilai biyu suka sanya kawai ya k’arasa inda mutumin yake tsaye ya ce “Na yi withdrawing complaint d’ina! Arshaad can go free. Allah ya sa mu fi k’arfin zuciyoyinmu.” Wata nannauyar ajiyar zuciya Aslam ya sauk’e kafin ya juya inda Junaidun ya ke ya yi hugging d’inshi sannan ya d’ago yad’an yi tapping shoulder d’inshi ya ce “Thank you Junaidu, thank you so much.” Murmushi kawai ya yi Arshaad yana shirin yi mishi magana ya juya ya fita. Da sauri Aaima ta bi bayansa dan yi mishi godiya. Bata samu ta cimmasa ba sai a compound d’in Granpa dan sauri yake yi sosai. Da d’an k’arfi ta ce “Hey” Ajiyar zuciya ya sauk’e ya lumshe manyan idanuwanshi tukunna ya juyo. Gaba d’aya jikinta a sanyaye yake a haka ma bata ga sanda aka tafi da Mammy ba. Tana zuwa ta ce “Thank you. Mun gode kwarai! Allah Ubangiji ya taimakeka kaima a lokacin da kake buk’atar taimakon gaggawa” A hankali ya d’an sunkuyar da kanshi, har ya d’ago zai yi magana sai kuma ya lura da yanayinta.. Ganin da yayi bai kamata su yi wannan maganar yanzu ba yasa ya ce “Ba komai. Amman akwai alfarmar da nake nema a wajenki! Naga yanzu you are not in a good shape idan ba damuwa zan iya zuwa nan da 1 week da laasar around 5 haka! I need to talk to you.” A hankali ta ce “Allah ya kaimu” Daga nan suka yi sallama ta sake yi mishi godiya ta koma ciki. Tana tafe tana matsar hawaye. Abakin kofar shiga taga mutumin ya fito da ragowar mutane biyu Haka kawai jikinta ya bata an tafi da Mammy dan daman bata ganta ba d’azu da ta dawo parlourn... Anan wajen kawai ta durk’ushe ta sa kuka. Aslam yana ganin mutumin ya fita ya sauk’e ajiyar zuciya ya kalli Gramma ya ce “Gramma Ina takardun dana baki d’azu da safe?” A hankali Gramma tana matsar hawaye ta juya ta nufi hanyar d’akinta. Bata yi 4 minutes ba ta fito rik’e da wasu takardu masu yawa file file wajen uku. Bai bari ta k’araso ba ya k’arasa ya karb’a sannan ya zaunar da ita a kan kujera ya ce “thank you” A hankali ya k’arasa ya d’an rissina ya mik’awa Granpa ya ce ‘ya duba, yana zuwa bara ya d’anyi magana da Arshaad.’ A hankali ya k’arasa inda Arshaad yake ya ce “Arshaad you are my brother and best friend. Bani da d’an uwa kuma Aboki kamar ka amman ka yi hak’uri ba laifina bane Allah ne ya d’aura mana son mace d’aya! Ba zan iya b’oye maka ba I loved Huda tun kafin ka kaini wajen ta mu gaisa i knew her tun ina Uk....” Nan ya bashi brief labarin da ya gayawa Huda. A hankali ya ce “Da na dawo naga yadda kake k’aunarta shiyasa kawai na yi deciding In bar maka ita! Which almost kill me shiyasa yanzu nake mai baka hak’uri.. Da ace inada iko da zuciyata to da na hak’ura na bar maka ita amman ba zan iya ba! I’m sorry to say this to your face wallahi ban san irin k’aunar da nake yi mata ba ban san ma kalar wannan son nake yi mata ba sai da na mallaketa a matsayin matata! Dan Allah ka yi hak’uri ka fahimceni......” Hugging d’inshi kawai Arshaad ya yi yana hawaye. Dakyar suka cika juna Arshaad d’in ya ce “You have sacrificed a lot for me ka gaya min dalilin da zai sa ba zan hak’ura In cire matarka a raina ba? Kar ka damu you have tried Aslam for my happines kanaji kana gani ka danne farin cikin ka saboda ni in yi farin ciki. You are the best brother and the best friend in the world.. Komai ya wuce Ina so ka saka a ranka kamar ban tab’a had’uwa da Huda ba amma dan Allah please inaso zan bar k’asar nan! For some years Ina son in yi healing daga Mammy da kuma everythin.. Don’t stop me please......” Murmushi Aslam ya yi kafin ya ce “ba zan barka ka tafi haka ba” Ya fad’i haka yana mai juyawa ya isa inda Granpa ya ke yad’an rusuna tukunna ya karb’a takardun da Granpa ya gama dubawa ya fara magana.. “Granpa ya mallaka min Mt duk da na san kowa ya sani a nan a yanzu, wanda maganar ta fito ne ta wajen Mammy da ta ga copies d’in takardun a d’akin Arshaad, shi kuma na san a mota ta ya ga takardun ranar da ya d’auka ya fita ya ce tasa ta lalace. A ranar da ya bani gida a UK a ranar ya bani had’e da MT. Ba yadda ban yi da shi ba amman ya ce ‘yana so yayi komai ya gama ya gaji da cases kuma daman shi ni ya shirya bawa.’ Na yi godiya tabbas na kuma yi farin ciki amma a ranar na fara working akan nima nawa decision d’in……… Arshaad, mun yi magana da kai a kan kana so ka bar k’asar nan shiyasa na baka na Uk! Hope you are happy.” Da sauri kowa ya zuba mishi ido. Murmushi ya yi ya d’aga musu kai alamun tabbatarwa Sanann ya ci gaba da magana “Auwal kuma na bashi na Abuja, ni kuma na d’auki na Kano” A hankali ya juya inda Granpa yake ya ce “Granpa ba wa ban ji dad’i akan kyautar da ka yi mini ba No I really appreciate it but this has been my wish since.. It was your wish ka mallaka min MT ni kuma wish d’ina shine mu rabashi a tsakaninmu brothers uku. I hope ban b’ata maka rai ba sannan kayi farin ciki da decision d’ina. Ban yi tempering da wish d’inka na passing MT from generation to generation ba Instead na sake fad’ad’a wish d’in naka ne Na tabbatar duk mu uku zamu zage kwazo wajen kular maka da MT in sha Allah kowa zai kula da nashi sannan za mu yi passing d’in shi each to our capable child just like you wanted sannan zamu rubuta mu ajjiye y’ay’an mu suma su bawa capable jikan mu each suma kuma jikokin namu su bawa capable d’ansu… A haka dai har illa masha Allah. I hope ban sab’a maka ba.” Ya k’arashe maganar yana sunkuyar da kanshi ganin yadda Granpa ya kafeshi da idanuwa. A hankali Granpa ya mik’e ya sauk’o daga kan kujerar tashi ya dogara sandarshi ya k’arasa inda Aslam yake tsaye ya shafa fuskarshi a hankali yana jin tsantsar k’aunar jikan nashi tana sake shiga cikin zuciyarshi, a hankali ya ce “I wonder why mutane suke jin haushi Idan nace kaine favorite jikana.” Yana gama fad’in haka ya ce “Allah ya yi muku albarka I’m very happy with your decision, thank you.” Daganan yasa kai ya wuce side d’inshi yana dogara y’ar sandarshi Gramma itama ta mik’e ta mara mishi baya. A hankali Dad ya k’arasa ya yi hugging Aslam sai kuma ya jawo Arshaad shima ya had’asu duk su biyun ya rungume. Murmushi Abba yayi shinda su Shuraim waenda suka koma kusa dashi tun d’azu da za a tafi da Mammy suka mak’ale masa. Haka shima Daddy yana d’an murmushi idanunshi tap kwallah ya ce “Inama ace inada super powern da zan yi using in ganni a tsakiyanku” Dariya duk suka yi har Mommy. A hankali ya ke kallonsu kafin ya ce “Sai mun dawo in shaa Allah.. May this smile never fade away a fuskokinmu” Duk had’a baki suka yi wajen cewa “Ameen” Daga nan su Daddy suka yanke kiran. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 72. A parlourn k’asa Aslam ya tadda Huda tanata faman safa da marwa… Duk yadda taso kasa rik’e kukanta tayi dan haka kawai sai ta sakeshi ta taho tana zuwa ta fad’a jikinsa. A hankali yana sauk’e ajiyar zuciya ya shiga lallashin ta yana rad’a mata wasu maganganu a kunne. Cikin d’an murmushi da kuka at the same time ta kai mishi duka a k’irji. A hankali ya ce “auch!!” Yana shafa kanta....... Washe gari da sassafe Arshaad ya zo. Aslam bai tashi ma akan sallayar da ya gama karatu ba ya ga call d’insa..tunaninsa kuwa yake yi dama yana rayawa a ranshi dalilin da ya sanya bai ganshi a masallaci ba. Yana d’auka ya ji ya ce masa ‘yana k’asa gidansa, ya zo ya bud’e masa.’ “To” kawai ya ce daga nan ya mik’e ya cewa Hudan “Ina zuwa” ya fita. A hankali ta bishi da kallo har ya wuce ya fice tana jin yanayin da takan tsinci kanta a gameda shi yana sake nunkuwa. Masu aikin su duk ba anan suke kwana ba shiyasa sai da Arshaad ya jira Aslam ya bud’e mishi tukunna ya shigo. Da murmushi suka yiwa juna sallama kafin Arshaad d’in ya ce “sorry, na tada ku da sassafen nan ko?” Ajiyar zuciya kawai Aslam ya sauk’e sanann ya ce “Bismillah” Yana me bashi hanya. Suna zama ba tare da b’ata lokaci ba Arshaad ya ce “Sallama na zo yi muku” Yana d’an murmushi. Da mamaki Aslam d’in yake kallonshi kafin ya ce “Tun yanzu?” Sai da ya sauk’e ajiyar zuciya tukunna ya ce “I have to, sanann inaso in fara aiki da wuri..you promised Granpa ba za mu yi letting nashi down ba so bana son in baku kunya da kai da shi. Sannan tun a jiya bayan mun rabu da na kira Daddy yake cemin akwai aiki gaskiya a company d’in.” A hankali Aslam ya ce “So this is it?” “It’s just a good bye na d’an wani lokaci, zan dinga zuwa in sha Allah kar ka damu.” Arshaad d’in ya fad’i hakan cikin tarar numfashin shi. Ajiyar zuciya Aslam ya sauk’e ya sunkuyar da kanshi yana kallon k’asa sai kuma ya fara wani kalar murmushi tukunna ya fara magana “This Life is very funny! Difficult! Harsh! And way too upside down A ko da yaushe it’s very hard ka ga mutum ya samu all that he ever wished for ko da ace kuma zai samu d’in to sai kaga ya samu late ko kuma ya samu opposite ko dai ma ya rasa gaba d’aya…. Tun tasowarmu ba ni da burin da ya wuce Inga mun rayu cikin farin ciki gaba d’ayanmu a inuwa d’aya Ni Kai Aaima Dad Mommy Mammy har da su Auwal this has been my wish since childhood amma It turns out ba wai ga ni kad’ai ba ga yawancin mutane za ka ga dukkannin abunda kake so shi yake zame maka jarrabawa. Hak’ik’a Ubangiji yana jarabtarmu ne domin ya gwada imaninmu, yana jarabtar mafi soyuwa a cikin bayinsa da abunda ya san sun fi tsananin so da kwad’ayin samu….i have accept my destiny, i have accepted the fact that rayuwar da na so in yi da ku baki d’aya a inuwa d’aya ba zata tab’a yiwuwa ba. Although i was and I’m broken amma I’ll heal and embrace it with time.” Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya d’ago ya kalli Arshaad wanda tunda ya fara magana ya kafeshi da idanuwa, a hankali ya ce “Ina yi maka fatan alkhairi Allah ya sanya albarka a cikin dukkannin alamuranka Allah ya baka sa’a ya kare ka a duk inda kake. Arshaad inaso ka sani you will forever be my best friend, bani da da d’an uwa who stood by me through my worst times irinka shiyasa nake ji a raina inama ace Ina da dama to da ba zamu so mace d’aya ba.” Murmushi Arshaad ya yi ya had’iye wani yawu mai tauri kafin ya ce “Na gode Aslam, Allah ya k’addara saduwarmu. Kar ka damu ko da ace bama kusa I’ll make sure ban baka chance d’in da za ka yi missing d’ina ba daga kai har su Mommy zamu dinga waya video call sannan zan dinga zuwa time to time In sha Allah” Cikin sanyin murya ya ce “Ubangiji ya azurta ni da family masu matuk’ar sona dole in dinga lek’o su” A hankali yana murmushi yana kallonsa ya ce “Especially ma you Aslam.. Ina takaicin yadda na bari soyayya da takaicin ganin an mallaka maka MT suka kaini na kusa in halaka ka! A tunani na ina ganin maybe if I have the company zan iya mallakarta ta hanyar power! Hak’ik’a So da Buri ya kusan kaini ga matakin da za a iya saka ni a mazaunin the most ungrateful and selfish being a duniya!” Numfashi mai matuk’ar zafi ya fesar sannan ya ce “Babban darasin da na fahimta na d’auka shine ‘Wayo! Dabara da kuma k’arfin iko ba su Isa su baka abunda Allah ya riga ya k’addara ba naka bane ba! Shi ne kad’ai mai bayarwa kuma mai hanawa a duk lokacin da ya so ya kuma ga dama, bawa bai Isa ya kwatar wa kanshi abu ba Allah kad’ai ne yake wannan, shine kad’ai yake kwata ya bawa wanda ya so ya ga dama a duk lokacin da ya so ya kuma ga dama’.” Shiruu ya yi kafin ya sauk’e numfashi yana mai kallon k’asa a hankali ya ce “Na yi wayo, na so kaina, na kawar da duk wani negative Abu da nake gani a kan hanyata da ka iya kawo min tangard’a wajen mallakarta, na take gaskiya, na cutar da Junaidu kaima na so in kawar da kai amma duk da haka….” Shiruu yayi ya kasa ci gaba da magana sai kuma ya d’ago ya kallesa sosai ya ce “Aslam dan Allah please forgive m…” Da sauri Aslam ya ce “Arshaad mun wuce wannan wajen.. Idan akwai abunda zan rok’eka ka yi min a zaman ka na Uk shine ka goge komai.. Duk abunda ka ga yafaru it was already written tun kafin a haife mu dan haka ya faru ya wuce na manta kaima ka manta kar ka bari ya dameka… Bana duba abunda ka yi min dan bana ganinshi ma Iyaka abunda na sani nake gani shine ‘You are my best Man Arshaad’ Shine kuma abunda zan rik’e har abada. Ina rok’on Allah ya bar mana zumunci mu.” A hankali Arshaad ya ce “Ameen” Sannan ya mik’e ya ce “bisssalam” “Bara in kirata ku yi sallama” Aslam ya ce yana k’ok’arin juyawa. Da sauri Arshaad ya ce “A’a barta. Kawai ka ce mata na wuce” Da “to” Aslam ya bishi, daga nan ya yi mishi rakiya har bakin mota. Already sun yi sallama da su Dad da Granpa da kowa dan haka ya shiga.. Driver na k’ok’arin ja a hankali Arshaad d’in ya kalleshi ya ce masa “Ka kula mana da Aaima, tana wajen Mommy.” A hankali Aslam ya ce “I’ll.” Sai kuma kamar wanda baya son yin maganar ya ce “G’bye Arshaad”. Yana kallo driver ya yi reverse daga nan ya ja suka fice…. Yafi minti biyar a tsaye ya zubawa inda motar ta bi ta fice ido kafin a hankali ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya ya juya ya shige ciki idanuwansa jazur!. .................. ….24 HOURS AGO!…. Jirginsu yana Landing Daddy ya na shirin d’aukar drop ya ji Mom ta dafa shi ta ce “Daddy”. A hankali ya juyo suna had’a ido ya d’an b’ata fuska ya ce “Ke da ba y’ar gari ba Adama Ina ke ina zuwa d’aukar mu??” Murmushi kawai ta yi ta ce “Sorry” sannan ta wuce ta isa inda Sakina take tsaye tanata kame kame dan tun tasowarsu take fargabar ya zata kasance mata ita da Mom d’in. Ga mamakin Sakina Mom tana zuwa kawai sai taga ta yi hugging d’inta a hankali ta ce “Welcome dota” Sannan ta ja hannunta da d’an k’aramin trolley d’inta suka yi gaba. Murmushi Daddy ya yi dan ba k’aramin dad’i ya ji ba. Cikin sigar zolaya shima ya nufi motar da suka nufa yana jan nashi trolley d’in yana cewa “Wato ni ko In taho ko In zauna a nan ba damuwarki bane ba ko? Tunda kin samu y’arki”. Murmushi kawai Mom d’in ta yi a haka suka isa bakin motar. Suna zuwa drivern ya fito ya karb’i akwatunan ya saka a booth, suka shiga driver ya jasu suka wuce. Ga mamakin Sakina sai ta ga an kaisu hotel! So take tayi tambayar ‘Ina Auwal d’in’ dan in akwai wanda tafi buk’atar gani ta ga lafiyar shi a halin yanzu tou Auwal ne..so take ta yi magana amman kuma kunyar su sai ta hanata dan haka kawai ta bi bayan Mom wadda take ta wani lallab’ata har suka isa k’ofar wani d’aki. Wanda ya d’aukar mata akwati yana ajjiyewa Mom ta bud’e d’akin ta ja suka shige bayan ta mik’awa Daddy makulli. Suna shiga Mom ta rufe k’ofar kafin ta kamo hannun Sakina duk biyun ta rik’e, a hankali ta ce “Dota ki huta ki ci abinci daga nan sai ki je asibiti wajen Auwal ko?” Sai kuma ta d’an yi shiru chan ta ce “Ki yi hak’uri akan abunda na yi miki ranar birthday d’in su Shuraim, ki yafe min”. A hankali Sakina ta ce “Ba komai Mom ya wuce, ki daina bani hak’uri dan Allah” A hankali Mom ta saka hannu ta yi hugging d’inta. Sun d’an jima a haka kafin ta cikata ta juya ta fita tana cewa “Yanzu za a kawo miki abinci, ki ci ki yi wanka sai mu zo mu wuce gaba d’ayanmu.” Da “to” kawai ta iya binta dan ita har ga Allah so take kawai ta ji ance ta zo su wuce wajensa. Ba yadda ta iya haka ta daddannna abincin ta yi wanka duk ranta a jagule. Allah yaso su Mom basu wani d’auki time ba ta ji ana knocking.. Ta san sune dan ta gansu ta jikin d’an TVn dake jone da cctv camera d’in gaban k’ofar, dan haka gudun ma kar a sake yin wani jinkirin ta d’auko har handbag d’inta ta sak’ala akan bak’ar abayar da ta chanja dama ta yi rolling ta nufi k’ofar ta bud’e ta fita. Suna ganin ta a shirye chap suka ce “su wuce kawai” Mom na y’ar dariya k’asa k’asa tana yaba tsantsar k’aunar da Sakina take yiwa d’anta tana jin k’aunarta na shiga zuciyarta. Tun d’azu ta lura da yadda Sakinar take ta rawar k’afar son zuwa ta ga Auwal d’in…… Da wannan tunanin suka k’arasa mota Drivern jiya shi ya ja su ya kaisu har cikin tafkeken asibitin. Tunda suka fara takawa cikin asibitin gabanta yake mugun fad’uwa! Had’e da wani sanyin farin ciki da ya lullub’eta. Suna shiga dakin ta fashe da kuka, duk da kuwa Aaima dama ta gaya mata halin da yake ciki amman bata yi tunannin samun shi da oxygen har yanzu ba. Ajiyar zuciya Daddy ya sauk’e kafin ya k’arasa wajen ya tsaya a dede kanshi yana kallon shi.. Ya rame ba kad’an ba ya yi haske sosai. A hankali ya shafa kanshi ya ce “Son” Tun lokacin da suka shigo yake d’an jinsu sama sama. So yake ya bud’e idanuwan nashi amman ya kasa dan haka kurum suna shigowa gabansa ya yanke ya fad’i. A hankali ya samu ya bud’e idanuwan nashi da suka k’ank’ance.. Suna had’a idanu da Daddy ya sakar masa d’an murmushi. Murmushi Daddyn shima ya yi masa kafin ya ce “I’ve a surprise for you” Ya yi maganan yana mai juyawa ya yafito Sakina. A hankali ta k’arasa inda suke. Tunda ta taho jikinshi ya bashi, yana cikin tunani kawai ya ganta a tsaye a kanshi! Mutumin da ko iya motsin kirki baya yi kawai su Daddy suka ga ya yunk’ura da sauri zai tashi sai kuma ya ce “auch!!” Yana dogarar da guiwar hannunsa a kan gadon for sopport dan da mugun ciwo k’irjinsa wuyansa kafad’unsa da kansa suka sara! Sai kuma ya fara juwwa. Da sauri Daddy ya tareshi yana mai zama a bakin gadon ya maida shi kwance ya ce “careful mana” Sai kuma yasa dariya ya ce “har ka warke kenan?” Sai a lokacin kunya ta rufe Auwal….A hankali ya d’auke idanuwansa a kan fuskar Sakina ya mayar ya lumshe….. Tsananin farin ciki ya ji da ya ganta by surprise dan ji yayi kamar an tsundumashi a aljannah! Sai kuma a take batun Aurenta da Ashraff ya fad’o masa dan haka take lokaci guda ya ji wani tsananin tashin hankali sanann k’irjinsa ya hau zafi. Muryar Daddy ce ta katseshi jin yana cewa “Auwal ba komai mutum yake sa rai kuma ya samu ba! Kar ka ga ka mallaki Sakina ka yi tunanin duk wani abu idan ka sa rai nan gaba zaka samu. Ubangiji shi ya baka ita ba wai saboda nacin ka da rashin lafiyarkaba. An d’aura muku aure jiya kai da ita sakamokon matsalar da ta b’ullo a alamarin Aurenta da Ashraff. Amana ce Yarinyar nan Mahaifinta yayi mana kawaici da mutunci Dan Allah kar ka bamu kunya.” Tunda ya fara magana Auwal ya k’ame! Ya kasa motsi sam! Ji yake yi ma kamar iskar oxygen d’in bata isarsa……… A hankali Daddy ya yi wani sassanyan murmushi ya ce “Dota idan kuna buk’atar wani abun ga waya chan….idan Likita kuke so za ki ga digits d’in a gefe idan kuma abinci ne shima digits d’in suna gefe. Mu bara mu wuce ko? Yana da number mu duk abunda kuke buk’ata ku kira. Allah ya yi muku albarka.” A hankali Sakina ta ce “ameen” tana mai sunkuyar da kai. Da kyar ya iya bud’e idanuwanshi ya ce “Thankyou Daddy” A hankali dan shi kad’ai ya san luguden da zuciyarsa take yi masa. Murmushi ya yi daga haka suka juya shi da Mom suka fice tare da alk’awarin ‘zuwa anjima za su dawo’ Bayan Itama Mom d’in ta yi musu addua sun amsa...... A hankali ta ga ya mik’o mata hannunsa yana kallonta. Cikin nutsuwa ta k’arasa ta sa hannunta a cikin nashi. Still yana kallon fuskarta ya zaunar da ita a gefenshi. Da kulawa ta ce “Ina wuni” Tana kallon bakinshi ya amsa da “Alhamdulillah” a hankali. Daga nan ya ja hannun nata ya d’aura a gefen fuskarsa saman kumatunshi ya had’a da nashi hannun ya runtse kafin ya maida idanunsa ya rufe… Ko minti uku ba a yi ba ta ji yanayin rik’o da ya yiwa hannun nata ya sauya alamun ya yi bacci, bata san lokacin da murmushi ya sub’uce mata ba.. Kallon shi kawai take yi tana sakewa..ya d’an tara k’asumba har da gemu, tabbas ta so ta tarwatsa rayuwarta da hannunta dan bata jin akwai wanda zata iya so ta zauna ta rayu ta yi farinciki da shi idan ba Ya Auwal ba. Bata tashi sanin zazzafar soyayyar da take yi mishi ba sai da ya kwanta ciwo…. Sun fi 40 minutes a haka gaba d’aya hannunta ya k’age amman bata so ta motsa gudun kar ya farka dan ta lura baccin nashi mai dad’i ne yake yi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali kamar ma murmushi taga yana yi. Sai da ya yi 1 hour yana baccin tukunna ya farka. Yana bud’e ido da fuskarta ya fara tozali Itanma shi take kallo dan haka ya sakar mata wani tsadadden murmushi. Sai kuma ya d’an gyara ganin kamar a takure take kafin ya ce mata “call the Doctor” a hankali. Ta fahimci me ya ce shiyasa ta mik’e ta je ta danna kiran Doctor d’in. Bayan sun gama magana ta koma ta zauna. Tana zama ya sake kamo hannunta yana kallonta sam murmushi ya ki barin fuskarsa. Ba ta jima da zama ba Likitan ta shigo. Yanayin yadda ta ganshi kwance yana kallon kowa tar hakan ba k’aramin dad’i ya yi mata ba. Jininsa ta fara aunawa cike da mamaki ta shiga dudduba shi… Ganin no nid of oxygen d’in ne ya sa ta cire ta yi mishi y’an allurai daga nan ta cewa Sakina “ta k’ok’arta a samu ya ci abinci jikinshi is weak kuma ta cire mishi drip d’in da yake d’an rik’e shi tunda ba abincin yake iya ci ba.....” Tana gama fad’in haka ta juya ta fita tana murmushi…Irin wannan soyayyar haka tabbas saboda wannan Yarinyar ne zuciyarshi ta d’an tab’u dan gashi daga zuwanta komai ya fara yin normal a hankali..Ashe dama Nigerians ma suna irin wannan zazzafar soyayya haka? Dukda ba bak’ak’en fata bane amman ta fahimci Hausa suke yi.......... Sakina na shirin mik’ewa ya sa dukkannin d’an ragowar k’arfinsa ya jawota, bata ankara ba shiyasa yayi nasarar janyotan, ta tafi ta fad’a jikinshi. A zabure ta yunk’ura zata tashi ya ce “Don’t move please” A hankali dede kunnenta. Shiruu ta yi kawai tana jin yanda bugun zuciyarshi yake yi da k’arfin gaske.... Ganin lamarin na shirin sauya masa ya sanya ya d’an cikata. Da sauri ta tashi ta koma gefe ta zauna dan tabbas ba zata iya had’a ido da shiba kuma. Ya fahimci ta gano shi shiyasa kawai ya yi murmushi ya girgiza kai kafin cikin kasala da rashin k’arfin jiki ya ce “D’an duba chan locker ki fitar min brush da maclean da body lotion sai jallabiya da k’aramin wando. Please.” Ya fad’i hakan a hankali. Jinjina kai kawai ta yi ta mik’e ta isa inda locker take, ta d’auko duk abubuwan da ya lissaafa mata ta dawo ta ajjiye a gefen gadon kafin ta ce “Gashi” tana kauda kanta sannan ta d’an turo baki..kallon nashi ya fara isarta kwatakwata ko kifta idon ma fa baya son yi! Aranta ta ce “Har sai ya hango muni na” “Um” Ta ji ya ce wanda hakan yasa ta juya ta kalleshi. Gani tayi ya d’an d’aga hannuwanshi biyu irin yanda Yara suke yi idan suna so a d’auke su. Bata san lokacin da dariya ta sub’uce mata ba, da sauri ta sa hannu ta toshe bakinta sannan cikin dariyar k’asa k’asa ta ce “In d’auke ka?” Ta yi maganar tana nuna kanta. D’aga mata kai yayi kawai Idanuwanshi a kanta kafin a hankali ya ce “Allah na kasa tashi! Jikina ba kwari ko mostin kirki fa ba iyawa nake yi ba so kike in mik’e in zube?” Cikin yin kalar tausayi ta ce “Ya Auwal dan Allah ta yaya zan iya d’aukar ka?” Tana maganar tana kawar da kai dan bataso su had’a ido. Murmushi ya yi yad’an ciji lower lip d’inshi kafin ya ce “To shikenan naji ba zaki iyaba Zo to ki taimaka min In tashi.” Da sauri cikin tarar numfashinsa ta ce “A’a gaskiya” This time around sai da ya d’anyi dariya wadda ta taho mishi da d’an tari, sai da tarin ya tsagaita tukunna ya ce “Mai yasa ba za ki rik’e ni in tashi ba? Ko bakya so in sake.....” Da mugun sauri ta k’arasa ta sa hannunta ta toshe mishi baki, cikin muryar kamar wadda zata fashe da kuka ta ce “Wallahi idan ka k’arasa sai na tafi yanzunnan zan koma wajen su Mom” Da kyar dan jikinshi sam ba k’arfi ya iya zare hannun nata ya ce “Ni kuma wallahi idan baki taimakamin na tashi ba sai na k’arasa kuma In rufe k’ofar in hanaki fita sannan In yi ta maimaitawa.” Kamar zata yi kuka haka ta sunkuya kansa yadda za ta iya taimaka masa. Sai da ya gama d’aga mata gira yana kashe mata ido tukunna ya sak’ala hunnunshi a kafad’arta yana dariyar yadda ta chuno baki ta kauda kai gefe. Sai da ta yi bismillah tukunna ta d’an motsa da niyyar taimaka mishi, d’an yunk’urawa shi kuma ya yi hakan ya bashi damar mik’ewa ya zauna, da taimkon Ubangiji da na Sakina da kyar ya samu ya mik’e! K’afafuwansa har d’an karkarwa suke yi…… Ita ta d’an fara motsawa yana rik’e da ita ya ce “ta d’auka kayan da ta d’auko mishi” Hannu kawai tasa ta d’auka daga nan suka d’an fara takawa…….. Har Cikin bathroom d’in ta kaishi. A bakin tangamemen bathtub d’in ya zauna, sai da jirin yad’an sakeshi tukunna ya cikata ta had’a mishi ruwan wankan tab bathtub d’in sanann ta matsa mishi Maclean ta mik’a masa.. Sai da ta taimaka masa ya isa wajen sink d’in yayi tukunna ta fara k’ok’arin fita domin ya samu ya yi wanka. Cikin ruk’o hannunta ya ce “Saurin me kike yi? Jikina fa babu kwari! Idan kika fita na fad’i baya fa za ki dawo damu.” A hankali ta d’an matso suka nufi bathtub d’in tare………. Sanabe! Kala Kala awajen Auwal dan hatta shirt d’in ma ita ta b’alle mishi mab’allin ta cire, da kyar ya yarda ya sa hannu ya cire singlet d’in! Tun daga nan ta sunkuyar da kanta sosai ta fara k’ok’arin tafiya amman ya rik’e mata hannu…. Drama sosai suka yi dan ya kafe akan wandon ma ita zata cire masa gashi ya tare hanya ya rik’eta for support ya hanata tafiya. Ganin da ya yi ta tubure sannan tama k’i kallonshi tana shirin fashewa da kuka yasa kawai ya kama wandon ya fara ja yana dariya k’asa k’asa a hankali ta ji ya ce “FYI! Babu boxers a ciki.” Ta mugun k’arfi ta saka kuka ta durk’usa a wajen dede nan kuwa ta ga ya saki wando ya fad’o k’asa dan haka ta ci gaba da kuka ta k’i dagowa sam! Ta runtse idonta. Kukan da take yi ne yasa ya cika mata hannu, ai kuwa bata yarda ta kalli direction d’insa ba ta juya ta mik’e ta fice da mugun gudu. Banda dariya ba abunda yake yi… A hankali ya zare boxers d’in jikinsa ya shiga cikin ruwan da kyar. Ya kwanta a ciki ya lumshe idanuwanshi yana jero wa Ubangiji kirari da godiya…. Ya dad’e a haka tukun ya ja sponge da soap ya fara wankan.... Banda dukan uku uku ba abunda k’irjinta yake yi! Da kyar ta samu ta tsaida kukan nata… Kana ganinta ka san a mugun tsorace take ba abunda yafi d’aga mata hankali irin kar ya zo fitowa ya fito mata a haka! Tunda ta lura sam babu d’igon kunya a tattare da shi….. Da wannan tunanin ta juya gaba d’ayanta tana me kallon bango. Ta jima a haka ta ji k’arar bud’e k’ofar, sake matsawa jikin bangon ta yi wanda hakan ba k’aramin dariya ya bashi ba. Tana jinshi yana yi mata dariya ta yi banza da shi. A hankali ta ji ya ce “Relax! Har da jallabiyata da towel a kaina na fito, Okay?!” Bata yarda ba sai da ya matso kusa da ita ya kamo hannunta ya d’aura akan jallabiyar jikinshi tukunna t sauk’e ajiyar zuciya ta juyo amman still dukda haka bata kallonsa. A gefen ta ya zauna da kyar yana jin tsananin jiri da rashin kuzari ya ce “Anya ba a sauya mini ke ba kuwa? Ina tawan ta tafi ne?” B’ata rai ta yi ta turo baki. A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya ya d’an matsa ya yi peckn kumatunta ya ce “Matata!” Yana kallonta yana murmushi. Bata san lokacin da murmushi ya sub’uce mata ba Itama. A hanakali ta mik’e ta yo musu order abinci sannann ta dawo ta zauna a kusa da shi. Yana nan rik’e da hannunta tana bashi labarin Ashraff aka kawo abincin.... Auwal, ya ma manta rabon da ya ci abinci irin wannan sai dai drip most a times, da kanta take bashi! Wani nishad’i farinciki da jin dad’i yake ji wanda ba zai misaltu ba. Haka nan ta ciyar da shi suka yi baccin su tare suka farka suka yi sallah tare! Kafin washe gari kam Auwal ya warke ba laifi sai dai yawan baccin da yake yi da kuma rashin k’arfin jiki da y’an abubuwan da ba za a rasa ba.. Dan ko da Daddy ma ya je da daddare yana bacci. Ba k’aramin dad’i Daddy ya ji ba da ganin shi har yayi wanka kuma babu oxygen. Bai wani jima ba gudun kar motsin shi ya tada shi yasa ya yiwa Sakina sallama bayan ya bata abubuwan da ya tsaya ya siya musu. .....…………….. Suna gama video call d’in Daddy ya mik’e idanunshi sharkaf da hawaye zai wuce! Da sauri Mom ta ruk’o hannunsa ta durk’usa a gabansa. Ta lura tun d’azu da ta fara bada labarin ta’asarsu ita da Mammy Daddyn yak’i kallon direction d’inta, yanzu ma haka. Tana kuka ta ce “Dan Allah Daddy kar ka yi min wannan shirun naka……Ka hukuntani! Ka yi min duk hukuncin da kaga ya dace dani amman dan Allah kar ka rik’eni a zuciya ka banxatar da ni.” A hankali cikin share hawaye Daddy ya ce “Adama I love you morethan you can ever imagine! Amman ba zan iya zama ince wai na yafe miki duk abubuwan da kikayi min lokaci guda kuma naci gaba da sonki ba! Tbh, wallahi k’aunarki da k’imarki tayi mugun raguwa a zuciyata… How could you?! Haba Adama! Saboda son zuciya? Adama Mommy fa kusan a kwance ta yi rayuwarta kin sani kin san matsalar amman kika yi shiru!. Sannan kika taimakawa Mammy dan ku kwantar da Aslam yayi jinya shima? Doguwar jinya!!! saboda kawai kwad’ayin MT??”. Cikin kuka ta ce “I was wrong! I have been wrong for so long Daddy dan Allah ka yafe min. Ban san ta Ina zan fara baka hak’uri ba, ka yi hak’uri tabbas na yi kuskure kuma kuskuren ya dawo mini tunda gashi na rasa y’ar uwa ta d’aya tilo a duniya.” Numfashi Daddy ya furzar kafin ya ce “Duk son da nake yi miki dole ne in kin tab’a min family zan ji haushi Adama! Ba zan iya kallon ki ban tuna abubuwan da kika yi ba. Ki je wajen Inna! Ni ban ce na sakeki ba amman kawai ki tafi wajenta zan nemeki idan na huce.” A hankali ya zaro atm ya bata ya ce “Akwai driver da Aslam ya turo ya taho wai Auwal ya ce a kawo mishi wasu abubuwa.. Idan ya zo zan turo miki shi ku je ke da shi ku yi visa da komai Direct ki wuce wajen Innaa. Dan Allah ko kira na kar ki yi. Idan na neme ki to..Idan kuma ban neme ki ba shikenan, zan aika miki da takardarki! Allah ya raya mana Auwal.....” Yana gama fad’in haka ya juya ya fita da sauri. A wajen ta durk’ushe tana wani irin mugun kuka....... ..BAYAN KWANA BIYU.. Haka kurum tunda Mama ta tashi yau jikinta a mace Ummu na lura da ita dan tun jiya a wajen saloon taga kamar ma kuka take yi. A hankali ta matso kusanta tace “Maama” A karo na biyu. D’agowa ta yi ta kalle ta. A hankali ta ce “Ki tashi ki cire lallen nan mana a yi miki black mai k’unshi ke take jira”. Ajiyar zuciya Mama ta sauk’e kafin a hankali ta janyo abun sakace Ummu ta hau b’alle ledar… Atake suka cire ita da Ummu ta shafa mata Mahallabiya. Mik’ewa Ummu tayi da zummar zuwa ta kira me lallen tayi mata bakin ta ji Mama ta rik’eta a hankali ta ce “Abba ya fi son jan lalle” Murmushi Ummu tayi ta koma ta zauna ta kamo hannuwanta biyu kafin ta ce “Kina tunawa kenan har yanzu alamun yana nan rad’au a zuciyarki har abada amman kuma kiketa faman k’unci tun jiya Me yasa baki da walwala? Ko kema kukan za ki yi mana kamar y’ay’anki Huda da Sakina?” Ajiyar zuciya Mama ta sauk’e kafin ta ce “Bawai walwala ne bani da shi ba, dana sani nake yi.” Da sauri Ummu ta gyara zama kafin ta ce “Dana sani kuma? Name?” Wani d’an guntun murmushi Mama ta yi kafin ta ce “Dana sanin kuka da sab’on dana dinga yi ina cewa ‘mai yasa rayuwarmu ni da y’ata ta zo a haka?!’. Ummu na cire rai da Abba na cire rai da soyayya amma gashi yanzu Ubangijin da nake ganin ya d’aura mana kaddara mai tauri zai sake mallakamin Abba sannan Huda ma ta auri wanda yake tsananin k’aunarta shi da iyayensa What more could I ever ask for?. Godiya da tasbihi nake ga Ubangijin talikai amman gani nake yi kamar is not enough! Bansan ta yaya zan fara yiwa Ubangijina godiya ba. Ki duba fa kiga yadda rayuwa ta chanja mana daga k’unci tashin hankali da bak’in ciki zuwa Farin ciki cikar buri a lokaci daya!. Ba abunda yake bani mamaki nake kuma gasgata Ubangiji mai kun fayakun ne Irin yadda komai yake tafiya smooth.. Hatta Granpa ya sauk’o sosai jiya fa kira na yayi a waya wai ya kira mu gaisa sannan ya sake bani hak’uri!… Ashe dama za mu ji dad’i ni da Huda? Ashe za mu yi farin ciki? Ashe zan sake d’and’anar soyayya?”. Ajiyar zuciya Ummu ta sauk’e a hankali ta matsa kusa da ita tasa hannu ta rungumeta, a take kuka ya taho musu a tare su biyun. Suna a haka Shuwa ta shigo. Murmushi kawai ta yi cikin dakiya ta k’arasa inda suke ta d’an b’ata rai kafin ta ce “Yanzu dan Allah Maryam kema sai kin saka mu kuka? Su Huda sunayi kema kina yi?” Sannan cikin d’an fad’a ta cewa Ummu “tashi ki fita, yi maza ki fita kije kin bar Zainab da had’a abinci ke kin zo nan. Oya Maryam kema tashi ki shirya yanzunnan za ki ga an fara zuwa”. Bata Ida rufe bakinta ba Hudan ta shigo ita da Mommy. Da d’an sauri ta k’arasa ta fad’a kansu Ummu tana murna. Jujjuya kai kawai Shuwa tayi ta ce “Nikam wannan alada taku ta turai ban santa ba! Dan tsabar rashin man kai Huda yanzu keda za akai miki Maman naki inda kike shine kika fito? Kalleki ko nuna baki gama yi daga jinin amarcinba amman dan fitina har kin fito?” Murmushi Mommy ta yi suka gaisa ita da Shuwa kafin ta ce “Hajiya ayi mana uzuri, nima naso in hana amman ita da Mijin suka kafe! Wai zata yi mishi kuka idan na tafi.” Cikin d’an fad’a Shuwan ta k’arasa ta sakar mata rankwashi a kai tace “ja’ira!! Sannnan kin zo kin wani wuce ni kin fad’a jikin iyayenki..” Murmushi Huda ta yi ta mik’e ta yi hugging Shuwa kafin cikin dariya da zolaya ta ce “Hajiya kawai ki fito ki ce daman kishi kike yi ban kula ki ba ba wai kiyi ta kame kame ba .” Dariya duk akayi. A hankali Shuwa itama tana d’an murmushi tasa hannu ta yi hugging Huda tukunna ta cika ta ta juya ta fita da sauri tana cewa “su tabbata sun sa Mama ta shirya yanzu”. Already Maman ta yi wanka tun sassafe dan haka kayanta kawai ta shiga bathroom ta saka Sky blue lace da white jaka takalmi da jewelry’s Ummu ce tayi mata d’auri nan take ta fito rass Amarya… Anyi hotuna sosai Allah sarki sakina a video call Huda ta kirata ta saka fuskarta akan screen din full aka d’auki hoton da ita su Ummu suna ta yiwa shirmen nasu dariya gashi Sakina ta dage sai an yi da ita. A masallacin unguwar kusa da gidan Madu anan za a d’aura aure dan tun kafin lokaci ya cika manyan motoci suka cika layin tap! Har layin baya saboda Abba gayya yayi kamar wannan ne na farko. Lokaci yana cika dubban mutane suka shaida D’aurin Auren Yakubu Umar Farouk Mt (Abba) Da Amaryarsa Maryam Muhammad Madu (Mama) Akan sadaki naira dubu d’ari uku. Ana shirin watsewa Kaka ya cewa Limamin ya sanar za a sake wani d’aurin auren …..……Tun lokacin da Kaka ya bada sanarwar Jalila wani mai d’an kantin ana ce mishi Abdullahi ya ce yaji ya gani! Shi da Mahaifiyarshi basu wani dad’e sosai da tarewa a anguwar ba kasancewar Mahaifinsa ya rasu kuma anata rigima tsakaninsu da dangi da iyayen uban a kan gado yasa suka baro Katsina suka dawo Kano da shi da Mahaifiyarshi da k’anwarsa Aminatu tsarar Jalila. Da farko Hudan ya so sai da mazan layin suka zaunar da shi suka yi mishi lecture a kan ‘indai ba gudumar late comer da heartbreak yake son yasha ba tou ya hak’ura’ Tukunna ya hak’ura ya koma kan Jalila wadda sai da ya fara sonta ne ma ya lura yama fi k’aunarta akan Hudan, dan haka ya je ya sameta ya gaya mata.. K’iri k’iri ta fito mishi ta k’i amincewa da shi sannan ta wankeshi tass!! Ta yi gaba abunta. Babu yanda bai yi ba amman ya kasa cire ta aranshi har rashin lafiya yake yi saboda Jalila tun ba ma lokacin da Auwal ya fara kwasarta ba sai da ya yi k’aramin hauka. Har gida Mahaifiyarsa ta je ta samu Sadiya amman tijarar da Sadiya ta yi mata har yamafi wadda Jalilan ta yiwa Abdullahin kumafa idan ka ga Abdullahi bashi da laifi sam! Bak’in saurayi dogon gaske mai fad’in k’ashi bashi da wani muni a fuska sam ya kammala degree d’inshi bai samu aiki ba shiyasa ya bud’e shago saboda d’awainiyar Mahaifiyarsa da k’anwarsa dole shi ne zai yi. Yana jin labari ya tafi wajen Kaka.. Ba abunda Kaka ya b’oye masa gameda cikin da Jalila tayi amman wannan Yaro ya ce yaji ya gani. Kaka ba k’aramin farin ciki yayi ba dan bai tab’a tunanin Jalila zata samu Miji saurayi kamar Abdullahin ba amman still sai da ya sake tura Baaba Talatu wajen Mahaifiyarsa da bayani Itama ta amince Dan haka aka bashi Jalila ba tare da an gayawa ita kanta Jalilan ko Sadiya ba Baba ne kawai ya sani…… Su Sadiya suna gidan Baaba Laraba sai uban hayak’i suke yi dan Malamin nasu yace in dai sun yi wannan hayak’in a anguwar in da Maryam (Mama) take tou ba za a d’aura auren Maryam da Yakubu ba. Suna hayakin suna ta uban tari kawunan su na ciwo suka jiyo an d’aura auren Maryam da Yakubu!…… Fatali Umma ta yi da kaskon kafin ta fashe da wani matsanancin kuka!. Jalila kanta sai da ta yi kwallar tashin hankali. Ba a yi minti talatin ba suna cikin jimami da tashin hankali suka ji ana sanarwa “An D’aura Auren Abdullahi Muhammad Da Amaryarsa Jalila Usman Bashir”. BULAMA ✍️ So da Buri Free book 73 Mikiya Writers Association. A hankali Mama ta lumshe idanuwanta wasu hawaye suna zuba. Dai dai nan Ummu ta shigo, ta na Isa gareta ta sa hannu ta yi hugging d’inta ta ce “congratulations”. Ajiyar zuciya kawai Mama ta sauk’e daga nan d’akin ya fara cika da jamaa.. Banda hayaniyar mata babu abunda ke tashi. Suna cikin hira suka ji d’aurin auren Jalila itama, nan take kowa ta hau tofa albarkacin bakinta wasu su ce “Allah shi k’ara” wasu kuma su ce “Ai ta ma yi sa a data auri Abdullahin, Mutum mai kirki da hankali da zuciyar nema wallahi ta tsinci dami a kala...”. Kowa idan ya ga Abba a wajen d’aurin auren nan tashi d’aya zai san yau d’in fa yana cikin farin ciki. Ba shi kad’ai ba hatta su Granpa idan ka gansu fuskokinsu tap! Cike da annuri. Ba a jima ba suka shiga parlourn Madu aka yi musu hotuna suka wuce bayan sun ce “nan da anjima in an d’an watse Abba zai dawo ya d’auki Amaryar shi da kanshi.” Madu ya ji dad’in hakan dan dama shima ya gama deciding akan ‘ba sai an yi wani reton kai Amarya kamar wata Yarinya ba’. Hakan kuwa aka yi, Hudan ta so tsayawa amman awa uku kawai Aslam ya bata daga nann ya dawo ya d’auketa a cewarshi ‘gidan yayi mishi girma ya kasa shan ko ruwa tunda ya koma’… Tunda ta ji haka dama ta b’aro jirginsa! Dan haka ta yi murmushi kawai ta girgiza kai tana mamakinsa. Tunda aka idar da sallar Magrib Abba ya shirya tsaf! Ana idar da sallar isha ya kama hanyar gandun albasa bayan ya samu Dad ya cika shi dakyar dan da farko rik’esa ya yi ya ce “akwai wani important aiki da zai tayashi dan Allah” Kamar Abba zai yi kuka haka ya yi mishi sai kuma ya ga Dad d’in yana dariya k’asa k’asa dan haka ya gano tsokanace! Amman dukda haka sai da ya yi da gaske tukunna Dad d’in ya cika mishi riga ya wuce mota Dad d’in kuma ya nufi gidanshi yana dariya………. Yana zuwa ya tadda Madu zai shiga gida ya fito kenan daga masallaci dan haka suka shiga tare har parlourn Shuwa. Nan Madu ya d’au waya ya kira Kaka da Baaba Talatu suka zo suka had’u suka yi musu Nasiha! Daganan suka sanya musu albarka…. Sai da suka zo tafiya ne Mama ta ji kuka ya taho mata. Murmushi kawai Baaba Talatu da Shuwa suka yi daga nan Baaba Talatu ta mik’e ta k’arasa ta mik’ar da ita suka yi gaba Abba shima ya yi musu godiya da fatan alkhairi ya bi bayansu….. Da shi da mai aikin ne suka ja akwatunan Mama guda biyu da ta had kayanta a ciki suka kai mota suka sanya mata a booth... Har k’ofar mota Baaba Talatu ta raka Mama ta bud’e ta saka ta a ciiki tukunna ta ce “Allah ya miki albarka” Tana mai rufe mata motar ta koma ciki. Dede nan Abba ya shigo ya rufe motar ya kunna ta, a hankali ya sauk’e ajiyar zuciya sannan ya juyo ya sa hannu ya jawota ya yi hugging d’inta wasu hawaye suna zubowa daga idanunshi.. Da sauri ta ce “Abba mutane fa suna wucewa” Tana mai d’an k’ok’arin janyewa. Bai cikata ba sai da ya yi niyya tukunna ya matsa amman still yana rik’e da hannunta yana kallonta ta cikin mayafin da ta d’an ja. Murmushi kawai ya yi yana sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya kafin ya koma ya zauna rik’e da hannunta ya tada motar suka wuce. Sai a sannan tukunna Baba ya share hawayenshi ya juya ya nufi cikin gidan Kaka yana ganin uku uku...... Tunda suka isa bakin estate d’in ta lumshe idanuwanta. A hankali ya yi horn aka zuge makeken gate d’in suka shige ciki. Direct gidan Granpa Abba ya nufa da ita. Yana kashe motar ya d’an murza hannunta wanda tun d’azun da ya rik’e bai cika ba ya ce “Maryama” Sai a sannan ta bud’e idon ta d’an juyo ta kalleshi. Murmushi ya yi ya ce “mu je ko?” Jinjina kai kawai ta yi daga nan ta fara k’ok’arin fita sai kuma ta juya ta ce “hannuna” Sai a sannan ya d’anyi murmushi ya sakin mata hannun da kyar ta fita da k’ofar dama shima ya fito… Suna d’an yin gaba ta ga yana shirin kama mata hannu! Bama ta san wajen su Granpa za su je ba amman kawai ta yi gaba da sauri! Murmushi kawai ya yi ya girgiza kai ya bi bayanta, daga nan suka jera suka shiga a tare. A parlourn su Granpa na biyu suka samesu suna jiransu gaba d’ayansu har Mommy da Dad. Tana shiga Mommy ta mik’e ta je ta yi hugging d’inta tana farin ciki… A gaban Granpa ta fara durk’usawa suka gaisa ya yi welcoming d’inta sannan ta k’arasa wajen Gramma itama ta yi welcoming d’inta ta saka mata albarka tukunna Dad shima ya yi welcoming d’inta ya sanya mata albarka. Daganan Granpa da Gramma suka bata gifts d’insu Granpa ya bata fili a asokoro Grandma kuma ta bata sark’ar gold babba mai kyau da bangles d’inta da zobe. Godiya sosai su Mama da Abba suka yi daga nan Dad shima ya bata nashi gift d’in kyautar mota har da Mommy aka hau godiya.. Sannan suka sake yiwa su Gramma godiya daga nan suka yi musu sallama da Allah ya kiyaye hanya dan sun ce jirginsu 3:00am zai tashi...... A ranar dattijawan unguwa suka zo suka zo suka bawa Madu hak’uri sannan da maganar ‘ya koma matsayinshi na mai unguwa’! Da kyar kuwa da mugun kyar aka samu ya yarda ya karb’a saboda shi a ganinshi komai ya wuce sannan yanzu tsufa ya kamashi amman sam suka k’i amincewa suka ce “Ai su basu da wani mai unguwa wanda ya chanchanta sama da shi”…. Tunda Abba yake bai tab’a ganin nisan dake a tsakanin gidan Granpa da Gidan da zai zauna ba sai yau! Allah Allah kawai yake su k’arasa. Suna shiga Mama taga abun mamaki..har da wata k’atuwar heart a tsakiyar falon an yi decoration, ita kam abunma ma sai ya bata kunya..kar wani ya shigo ya gani.. Ruwan furniture da electronics kuwa kamar ba a san zafin kud’in ba. A chan sama ma d’akinsu Abba ya yi decorating sosai da red hearts Ita dai Mama in banda murmushi ba abunda take yi dan har ga Allah abun ya burgeta. Idanuwanta suna kaiwa kan akwatuna dozen a take ta b’ata rai! Da sauri ya kauda kai yana d’an murmushi. Cikin rashin jin dad’i ta ce “Abba cewa fa na yi ka barshi. Ka san za ka yi shine mu kuma ka hana mu yin kayan d’aki?”. Da sauri ya sa hannu ya toshe mata baki ya ce “Maryam wallahi bani da energy d’in arguing yanzu, ba ri mu yi sallah ko? Mu ci abinci sai mu yi magana.” Da “to” kawai ta bishi, tana ta faman fushi suka yi sallar suka ci abinci. Za ta ci gaba da mitar ya ce “Bara inyi wanka sai ayi min mitar ko?” Ya fad’i haka yana tattare wajen ya yi waje da sauri yana mamakin Mama da mitar ta har yanzu ashe tana nan. Itama wankan ta yi ta nad’a laffayarta bayan ta chanza kayan da ta zo da su a cikin akwatinta. Tana cikin nad’a laffayar ya shigo, ya tsaya a bayan ta. Ko juyowa bata yi ba ta ce “Yanzu inda nice na nace sai na zo da kayan d’aki nasan ba zaka ji dad’i ba amman ni kalli ka yi lefe bayan an riga an gama magana, sai kace wata Yarinya...” A hankali ya juyo da ita ya ce “Wallahi bana gane abubuwan da kike fad’a! Na gaya miki bani da energy d’in arguing................” EARLIER.. Wata razananniyar k’ara Umma ta saka mai had’e da ashar kamar wata mahaukaciya! Jalila kuwa gefe guda kawai ta koma ta zauna dab’ass!! Ta k’ame a waje guda sai kuma hawaye suka hau zirya wani na korar wani ba k’akk’autawa….. Tabbas ko jiya sai da Abdullahi ya kirata, da ta k’i d’auka ya yi mata message yana cewa “Gobe in shaa Allah zai yi mata kyauta surprise na ban mamaki.” Tsananin tashin hankali da bak’in ciki suka sanya kawai ta tafi ta sulale ta sume a wajen. Da gudu Umma ta k’arasa kanta ta hau jijjigata amman sam bata motsa ba! Sai da Hansai ta d’ebo ruwa aka shek’a mata tukunna ta farfad’o, suna had’a ido da Umma ta fashe da kuka: Kasa cigaba da kallon idon nata Umma ta yi, ta mik’e kawai ta ja hannun Hansai suka shige chan k’uryar d’aki. Jakarta kawai ta d’auka ta cewa Hansai “yi mini kwatancen Dajinma!”. A zabure Hansai ta ce “Ke!!! Sadiya? Dajinma?? Gaskiya ni kam ba da ni ba! Har me ya yi zafi haka?”. Cikin katseta da sauri Umma ta ce “komai ma ya yi zafi!!! Haba Hansai! Sai kace ba kya gani? Ki duba kiga Maryam da Huda sun fini ta ko wacce hanya sannan tsabar Bashir d’an kutumar bura uba ne Kalli a yadda ya aurar da Jalila kuma auren ma da talakan tukuf!! Dan nasan had’in sa ne wanan, shegen tsoho ya tsaneni ya tsane y’aata! Tun da ya kafa mata k’ahon zuk’a sai da ya yi mata auren dolen tukunna hankalinsa ya kwanta! Ai kuwa wallahi ba zata sab’u ba! Ko sadakin ba za mu karb’a ba wallahi sai ya sakar mini y’ata, ban haifeta dan ta je ta auri talaka ba wallahi.. Ki yi min kwatance ko kuma In tafi in nema. In ba haka ba mutuwa zan yi kin san Allah takaice da bak’in ciki sai sun kasheni!!!!…..” Cikin son fahimtar da ita Hansai ta ce “Sadiya wajen nan ban da mayu da aljanu ba abunda suka cikashi! Kumafa sai kin yi tsirara tukunna zasu saurareki! Ke kad’ai a tsakiyar daji.” Da sauri Umma ta ce “zan iya!! Kwatance kawai nake buk’ata ki yi mini idan na je ko me akace min inyi zan iya muddin zan ga Maryam da Huda a k’ark’ashina sannan basu fini da komai ba! Haba mana! sun fi kowa ne? Kalli mazajen fa da suka aura Hansai zuciyata zata buga ki yi min kwatance in wuce da wuri tun kafin Maryam ta tare a lalata auren sannan a sauwwak’ewa y’ata wannan auren talakan tukuf d’in ta auri Arshaad.” Ajiyar zuciya Hansai ta sauk’e kafin ta ce “Sadiya ni a ganina gara dai aje wajen y’an saffa saffa da aka saba susan abun yi, Dajinm......” Wani uban ashar Umma ta k’unduma kafin ta ce “Hansai kar ki kashe ni! Malaman Ina ce sune suka bamu wannan hayak’in muka yi muka turnuk’e ko Ina? Na tabbatar ya shiga gidan Madu ta shak’a kowa ya shak’a ke har kwandila na tabbatar ya zagaya amman kinga an fasa auren Maryam da Abba? Sannan malaman ba su ne suka yi ta amshe kud’ad’en mu akan batun Jalila da Arshaad ba? Kin tab’a ganin Arshaad ya yiwa Jalilan koda message ta waya? Dan haka kawai ni kinga ki rabani da zancen malaman nan ba zan iya ci gaba da kwasar takaicinsu ba duk y’an damfara ne! Gara kawai ki had’ani da Aljani ko Maye wanda na san ba cuta ba cutarwa!!!… Yi min kwatance maza maza inje ayi a gama kafin Maryam ta tare”. Ta k’arashe maganar rai a masifar b’ace a gaggauce tana gyara ruk’on jalarta da mayafinta. Ajiyar zuciya Hansai ta sauk’e sannan ta kalleta ta ce “Zan iya kaiki wajen dan ba lallai ki gane ba, nima k’awarnan tawa na tab’a rakawa kuma zan gane..Ni na yiwa Mijina ita kuma kishiyarta wadda ta b’ace b’at!! Har yau babu ita ba labarinta kamar yadda ta buk’ata.” Wani shu’umin murmushi na tsantsar jin dad’i Umma ta yi. A hankali Hansai ta ce “Muje in rakaki, sai ke ki shiga jejin ni kuma in jiraki a bakin kogin.” “Na gode Hansai” Umman ta ce fuskarta tana baiyyana tsananin farin cikin da take ciki. Laraba da Jalila suna parlourn a yanda suka barsu suka zo suka wuce su. Ce musu kawai sukayi “bara su je su dawo” Ko Laraban basu gayawa inda suka nufa ba suka fice suka kama hanya……… Sai da sukayi mota uku da mashin biyu tukunna suka isa bakin kogin dede ana kiran sallar Magrib. Naira hamsin suka biya mai kwale kwalen ya tura su ya kaisu bakin dajin Umma ta shiga cikin dajin Hansai kuma ta zauna a wajen itada mai kwalekwalen zaman jiran fitowarta da alk’awarin zasu bashi naira d’ari biyu idan ya jira ya fitar dasu. Sauri sauri Umma take tafiya ita kad’ai a cikin dajin dan tana so su yi su gama su koma koda wani d’an k’auye ne su kwana a hanya saboda tasan tabbas komawarsu a yau ba zata yiu ba. Wani kalan murmushi ta yi sakamakon hango dakali a zagaye mai kewaye da ruwa a tsakiyar wasu dogayen bishiyu guda bakwai. Already Hansai ta fad’a mata yadda zata yi dan haka ta kwab’e tik! Hatta zoben hannunta da y’an kunne sai da ta cire ta ajjiye ta cire takalminta ta nufi dakalin tsirara haihuwar Laraba. Tana zuwa ta d’auki itace mai d’an tsini ta chaka a tsakiyar hannunta sannan ta bi ta zagaye wannan ruwan da yake kewaye da dakalin tana mai d’iga jininta a cikin ruwan! Tana gama zagayewa ta tsallake ruwan ta hau ta d’ale kan dakalin ta zauna. Wata firgitatciyar k’ara aka yi da ta sanya jinta ya d’auke d’iff gaba d’aya! Hatta Hansai da mai kwalekwalen sai da suka ji dan haka a firgice mutumin ya ce “Kai! Kai!! Kai!!! Maza mu bar nan basa k’aunar jininta!! Kar mu je abun ya shafemu, bara mu juya da sauri.” Da sauri Hansai wadda itama k’arar ta mugun firgitata ta ce “Ban gane basa k’aunar jininta ba? Kamar ya?” Kallon ta mutumin ya yi kafin cikin b’acin rai ya ce “Au ku baku san sharud’an wajen ba kuka kwaso k’afa kuka taho? To ni kam bada ni ba gaskiya! Ba zaki sa a had’a da ni ba.” Yana gama fad’in haka ya fara k’ok’arin juya kwalekwalensa. Kuka Hansai ta saka kafin ta ce “Malan y’ar uwa ta fa? Ya za ai In tafi In bar y’aruwata??” Tsaki kawai ya yi kafin ya ce “Kin san Allah in kika b’ata min rai kika yi min taurin kai har wani abun ya shafeni sai na kasheki!!! In kuma kina son tsira tou ki ja bakin ki ki yi shiru mubar nan tun kafin a jiyo mu!! Idan Allah ya kaimu gobe da sassafe na san basa nan sai mu zo mu d’auki gawarta!” Hansai na shirin yin magana cikin kuka wata mahaukaciyar iska ta hankad’o su dagasu har kwalekwalen nasu! Da kyar ta tsayar da su a tsakiyar kogin ai kuwa da mugun sauri mutumin ya cika inda suka kakkama saboda kar su zube ya hau tuk’a kwalekwalen ya kaisu bakin rafin… Ko tsayawa k’ullewa bai yi ba ya fita da guda ganin haka yasa itama Hansai ta raka shi da nata gudun dan ba k’aramin tsorata tayi ba. A gidansa inda ya nufa ta kwana bayan sun sha artabu saboda da cewa yayi ba zata bishi ta ja mishi jalala ba dan ya lura dak’ik’iya ce...... Kamar yadda ya yi mata alk’awari washegari da sassafe ya nemo mutane suka nufi wajen! Har ita suka shiga wajen. Anan kan dakalin suka hango Umma kwace k’afafuwanta a cikin ruwan ta gaba Hannayenta ta gefe da gefe duk a cikin ruwan da yake zagaye da d’an dakalin Gashin kanta kuma yana tab’a ruwan ta baya. Da sauri suka k’arasa inda take suna isa Hansai ta fashe da kuka a mugun tsorace ganin an kwakule mata idanuwa. A cikin Mutannen ne wani ya cire y’ar sharar jikinsa suka rufa mata suka yi waje da ita. Har aka isa gidan Mutumin in banda kuka ba abunda Hansai take yi duk a tunanin ta mutu amman ana zuwa gidan da aka kawo ruwa matar mutumin tana wanke mata fuska sai sukaji tana magana k’asa k’asa. Da sauri Hansai ta matsa sosai ta fara yi mata magana tana cewa “Sadiya me kike cewa?? Sannu sannu Sadiya, mai ya faru dake haka?” Sam amsar da take bata babu kai! Ita kuma Hansai ta dage sai magana take yi tana d’an murna ganin y’ar uwar tata nada sauran rai. Matar ce ta ce mata “Bafa zata fahimceki ba. Babban abun mamaki ne ma da aka sameta da rai, sai dai kuma ina yi mata takaicin a haka zata k’are rayuwarta dan sam ba zata tab’a yin hankaliba. Allah kad’ai ya san me da me ta gani sannan kin san suna d’auke hankali da kwakwalwa bayan sun cire ido.” Cikin tsananin fashewa da kuka Hansai ta ce “Na shiga uku!!! Dan Allah idan akwai mai Magani duk inda yake ki yi min kwatance In kaita wallahi k’anwata ce.” Sai da matar ta d’an k’ura mata ido tukunna ta sauk’e ajiyar zuciya kafin ta ce “K’anwar ki ce amman kika kawota ga halaka? Wacce iriyar yaya ce ke? To bari kiji in gaya miki tunda muke a k’auyen nan kafuwar shekaru kusan d’ari! Ba a tab’a yin wanda ya shiga wajen nan basu k’aunaci jininshi ba ya fito da rai! Wasu kuma da aka k’aunaci jinin nasu ma za su je su dawo k’alau daga baya kuma kiga hankalin ya tab‘u! Balle ita da basu k’aunace ta ba tunda gashi har idanuwan sun cire ai kawai ku rungumi k’addara dan ni bansan wani me magani ba gaskiya. Ku samu ta warke daga wannan radd’ad’in kwakulewar idon, ku yi jinyar haukarta Idan iyakar abunda ya sameta kenan.” Tana gama fad’in haka ta mik’e ta yi gaba. Hansai ta yi kuka ta yi kuka kafin daga baya kawai ta sa aka taya ta ta kinkimi Sadiya bayan an sanya mata kayanta ta d’aura akan mashin....... Suna isa wani k’auye ta ci sa’a ta samu motar kano direct! Shata ma tayi ta ce in sukaje gidan zata shiga ta d’auko masa kud’insa saboda Sadiyar ta samu ta mik’e. Har k’ofar gida ya kaisu. Sai da ta rufe mata fuska da d’ankwali tukunna ta shiga ta kira K’asimu da Laraba. Da taimakon drivern aka shigar da ita K’asimu sai faman sababin tambayarta yake yi….. Laraba kuwa tun daga yadda taga fuskar Hansai da kuma Sadiyar gabanta ya fad’i! Shiyasa ta ma kasa maganar ko iya kama Sadiyar ma bata yi ba, yadda take a sandare ne ya sanya ta yi tunanin ko mutuwa ta yi shiyasa ana shiga gidan tun kafin a gama kwantar da ita akan tabarma ta fashe da kuka. Jin kuka yasa Jalila wadda tun jiya Laraban ta b’oye ta a d’aki ta cewa su Baaba Talatu ‘ta gudune itada Sadiya’ ta fito! Tana hango Sadiyar a kwance ta tafi jikinta ta fad’a ta fashe da wani matsanancin kuka. Hansai bata tanka su ba sai sake kiran Junaidu da tayi ta ce masa “sun iso yanzu ya zo” sannan ta je ta duba d’akin Amarya taga da sakata tukunna ta dawo inda suke ta tsugunna. Daga K’asimu har Laraba babu wanda ya iya tab’a Sadiya dan shima K’asimun zuwa yanzu ya fara tsurewa sakamokon ganin da yayi ko motsi Sadiyar bata yi. Tana tsugunnawa taji ana tab’a k’ofa dan haka ta je ta tambaya “waye?” Ajiyar zuciya ta sauk’e jin Junaidu ya ce “ni ne” A hankali ta bud’e mishi. A hankali yad’an gaisheta sannan ya hau tambayarta “mai ya faru? Ina Umman nasu!? Sun tafi tun jiya wayar su bata shiga. Mai ya faru ba dai hatsari suka yi ba ko?….” Maganarsa ce ta katse sakamokon hango Sadiya a kwance a sank’ame!……. Dakyar Junaidu wanda k’irjinsa ya hau dukan uku uku ya samu ya k’arasa wajen ya tsugunna ya yaye mata fuska! Wani wawan tsalle K’asimu yayi had’e da ihu ya fad’a kan Laraba tsabar tsananin tsoro. Da sauri shi kuma Junaidu ya kauda kanshi gefe ya runtse idanuwanshi wasu zafafan hawaye suna zubo mishi dai dai nan Hansai ta k’araso wajen…… Cikin kuka Laraba wadda ta samu ta ture K’asimu daga kanta da kyar ta ce “Hansai garin yaya haka ta faru? Mai ya sameta haka ba ido? Su waye suka kashe min Sadiya?” Ta k’arashe maganar tana sake fashewa da wani matsanancin kuka. Tiryaan tiryaan haka Hansai ta zayyano musu duk abunda ya faru bata b’oye komai ba sannan ta ce “Tana da rai bata mutu ba, inaga yanzun bacci tayi.” Cikin tsanannin b’acin raii Junaidu ya rufe ta da fad’a kamar y’arsa…babu abunda ya fi b’ata mishi rai irin wai ‘wajen mayu da aljanu suka je’! Ya jima yana bala’i yana hawaye kafin ya mik’e a mugun fusace ya fita. Jalila kuwa in banda kiran sunanta tana tattab’ata ba abunda take yi. Junaidu bai yi minti ashirin ba ya dawo gidan da wasu mutane kana gani kasan Likitocine. Su suka d’auketa daga nan ya cewa Hansai ta biyo shi. Bai dawo ba sai washe gari shi kad’ai ba Hansai. Jalila da Laraba ya tarar a parlourn. A hankali ya zauna yana kallonsu Jalila ta rakub’e tanata faman kuka abun tausayi. Da kyar ya kauda idonshi a kanta yana jin tsananin tausayin ta dai dai nan K’asimu ya shigo ya nemi waje ya zauna sannan ya ce “Gani dan albarka ya ake ciki?” Sai da ya sauk’e ajiyar zuciya tukunna ya ce “Umma bata mutu ba! Amman halin da take ciki gara mutuwa….. Ta samu tabun hankali sannan idanuwanta babu kuma k’afafuwanta sun shanye . Yanzu dai na turasu Cairo ita da Hansai, za a yi mata aiki a chan daganan ta d’an dede ta kafin su dawo...” Shiruuu, yayi yana jin zuciyarshi tana tafarfasa kafin ya mik’e ya k’arasa wajen Jalila wadda take kuka wiwi ya zauna sosai a gabanta A hankali ya kamo hannunta ya fara magana “Jalila sai dai hak’uri, kuka ba zai yi maganin komai ba, mu bita da addua kawai da fatan Allah ya bata lafiya. Kuma inaso ki yi hak’uri sannan ki cire taurin kai ki rungumi Mijin da aka zab’a miki! Ki nutsu ki yi hankali Jalila dan girman Allah, Umma kad’ai ta isar miki ishara. Ba komai kake sakawa a gaba ka samu ba. Dan Allah dan Annabi Jalila ki koma kamar Jalilan ki ta daa yadda kike lokacin da muke a hannun Mama kafin dawowar Umma cikin rayuwarmu! Ki duba dai ki gani tsarin da kuke kai ke da Umma ba dai dai baneba sam! Na fad’a muku na yi nasihar har na gaji daga ku har Anty Zainab wadda ita yanzu Allah ya taimaketa ta gane gaskiya. Ki bud’e idonki da kyau ki duba ki gani shin da ku da su Mama waye ya ci riba yanzu? Kinga fa tun a duniya Ubangiji ya nuna muku iyakarku. Ki hak’ura da Arshaad ki hak’ura da So da Buri Jalila ki hau matakin gaskiya za ki ji dad’i a yanzu da gaba. Ki yi hak’uri ki tare a gidan Mijinki Na so in bashi gida babba mai bene da komai amman furr ya k’i, haka dole na hak’ura na bashi k’arami mai d’akuna biyu da toilet d’aya da parlour har da tsakar gida saboda ya ce shi kad’ai zai iya affording dan ya tabbatar min ‘tabbas zai dinga biyana kud’in haya’ Jalila irin wannan Mijin mai wadatachchiyar zuciya shi a ke nema, ki duba fa kiga ya san da zancen ki ke da Auwal ya san komai amman ya ce ‘ya ji ya gani’ Mahaifiyarshi ma ta ce ‘ta ji ta gani’ What more could you ask for daga bawan Allah nan??. Kar ki damu na yi miki kayan d’aki da kayan kitchen na gani na fad’a, ki yi hak’uri ki daure Jalila pls, Mahaifiyarshi tana chan hankalin su duk a tashe! Shiyasa na je na samesu na ce ‘anjima da yamma su zo a mik’a ki gidanki’. Ki fad’amin ko nawa kike so zan baki jari. Duk abunda kikeso don’t ever hesitate to ask me! Dan Allah Jalila amman ki yi k’ok’ari ki gyara halayenki dan zaman gidan aure daban yake da zaman gida Baki da wanda zai gaya miki gaskiya sama da ni.....” Nan ya yi mata Nasiha mai tsananin rashi jiki. Ya k’arashe da “Allah yayi miki albarka. Anjima kafin a kai ki ki je gidan Kaka Baba ya ce ‘ki je ki sameshi suna son ganinki’.” Cikin tsanannin kuka Jalila ta fad’a jikinsa tana cewa “Ka yi hak’uri Ya Junaidu. Ka bawa su Mama hak’uri In sha Allah zan chanja zan yarda…. Dan Allah ku tayani da addua ni kaina bana son in sake komawa waccar Jalilar saboda in banda tsananin k’unci da tashin hankali da wulak’anci ba abunda na tsinta! Hankalina yafi kwanciya a lokacin ina wajen Mama babu kyashi ba hassada ba komai… Dan Allah Ya Junaidu ka tayani bawa su Huda hak’uri wallahi na tuba.” Hannu yasa ya rungume ta shima yana hawaye…. Sun jima a haka tukunna ya mik’e ya mik’ar da ita tsaye ya kama hannunta ya ce mata “Ta shiga d’aki ta huta zuwa lokacin da Anty Zainab zata zo ta tafi da ita gurin su Baba” dan sam baya son barinta da su Laraba gudun kar su sake hargitsa mata lissafi. Da “to” ta amsa sannan ta shiga ciki dan itama tana buk’atar Hutun. Sai da ya ga ta kwanta tukunna ya juya ya fita ya yiwa su K’asimu sallama ya fice...... BULAMA ✍️ So da Buri Free Book Final Episode. Mikiya Writers Association. Sai da aka yi sati d’aya tukunna Aslam ya bar Huda ta je wajen Mama da kyar, dan sai da ta dinga yi masa kuka wiwi tukunna amma ya ce “Daga ranar sai wata wata zata dinga zuwa”. Tanata fushi haka suka nufi gidan da yamma bayan ce mishi ta yi wuni takeso ta yi. Tana zuwa aka yi sa’a su Ummu suma sun zo ita da Sumayya da Khadija dan haka farin cikin ya had’e mata biyu. Gaisawa kawai Aslam ya yi da su da kyar daga haka ya juya ya fita da sauri. Dariya su Ummu suka yi suna mamakin irin tashi kalar kunyar. Cikin tsananin farin ciki suka zauna anata hira har su Shuraim waenda Mama ta damu Abba har sai da ya kwaso mata su yau da safe tukunna hankalinta ya kwanta…tun suna nuk’u nuk’u har suka ware aka shiga tab’a hirar da su abun gwanin ban sha’awa. Hudan ce ta ce “bara ta kira Sakina itama ayi da ita” Dan haka ta kirata video call… Mura take yi sosai dan hatta muryarta ma ta d’an disashe sannan sai goge hanci take yi ya yi jaaa sosai har ma da fuskar tata gaba d’aya. A haka sukai mata sannu sukai mata sallama a cewar su “ta je ta huta” Ba dan taso ba ta ce “tou” ta yi musu sallamar itama ta kashe. …..BAYAN SATI BIYU….. Duk yadda Aslam ya so ya hana ta fita haka yanaji yana gani yau ma ya barta ta fita gidansu Mama bayan doguwar magiyar da su Sudais suka yi ta jera masa. Kasancewar yau birthday d’in Mama yasa suke son had’a mata surprise birthday kafin ta dawo… Tun Safe Abba ya d’auketa suka fita daga gidan, ya kaita spa suka je shopping daga nan suka biya park! Sai da Sudais ya tura mishi ‘we are done’ Tukunna ya ce mata “ta taso su koma gida”. Ba wani hayaniya ballons d’inma ba wasu masu yawa ba ne sai k’atoton cake d’inta mai hotanta a jiki da drinks kala kala.. Haka suka shirya surprise d’in. Tana shiga ta gansu har Mommy da Aaima duk sun zo suma…. Ta yi tsananin farin ciki kuwa harda y’ar kwallar ta…ba abunda yafi mata dad’i irin yadda Shuraim da Sudais suka maida ta uwa suke ji da ita kamar yanda itama take ji da su......... Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, Mama bata bawa Sudais da Shuraim single reason d’in su yi kukan rashin uwa ba! Daman tun ranar farko a bikin su Huda da ta gansu Yaran suka shiga ranta matuk’a. Yadda take yi musu ko Ummin iyakar abunda zata yi musu ne. Tarbiyya kam da gaske take basu ita, idan lokacin raha yazo ayi in sun yi kuskure kuma ta nuna musu kuskurensu ta yi musu gyara..... Suma su Shuraim d’in tun basu sake da ita ba har suka sake, ko shawara suke nema wajenta komai wajenta dan tabbas yadda take jinsu a cikin ranta haka nan suma suke jinta suke kuma tsananin girmamata... Tsakaninta ita da Abba kam tabbas Mama zata iya cewa tana cikin mata first class a sa’ar miji a duniya, ko kuma ma ta ce ita kam ta fi kowa sa’ar Miji a duniya…...Tsantsar zallar k’auna da kulawa had’e da tattali yake bata baya duba shekarunsu sam dan shi idan ya tashi gwada mata soyayya kamar wasu teenagers haka yake ganinsu shi da ita........ A b’angaren Mommy itama bata bawa Aaima reason d’in da zatayi missing Mammy ba, kulawa da shak’uwa ce a tsakaninsu ta musamman dan ita Mommy ce mata ta yi ta d’auketa a matsayin best friend d’inta......... ........ Kamar kullum yadda suka saba yau ma Sakina ta kirata suka shiga hirarsu gwanin ban sha’awa duk da kuwa Sakinar ba wani dad’i take ji ba saboda murar da take ta faman mata on and off! Ta rasa sukuni gaba d’aya sanyin garin ya isheta. Jin yanayinta da muryarta da kuma rashin lafiyar da take ta yi kwana biyu ya sanya Hudan ta ce “Maman baby je ki kwanta ki huta Allah ya sauwake.” Ta k’arashe maganar da d’an dariya k’asa k’asa sannan tana addu’ar Allah yasa harsashenta akan Sakinar ya zamo gaskiya ne. “Ok na gode sai da safe” Sakinan ta ce..Ba ta kashe wayar ba ta d’an yi shiruu kamar mai tunani sai kuma ta kwashe da dariya kafin ta ce “Ai ni sai yanzu ma na fahimceki! Tab! Inaaa ba wannan tukunna wallahi iyaka mura ce kawai take damu na.” Cikin rashin fahimta Huda ta ce “Ba kince an sallameku ba?” Dariya Sakina ta yi ta ce “to kuma daga an sallamemu sai me?” Bata jira amsar ta ba tana dariya ta ce “Eh, an sallamemu dan jikin nashi ya yi kyau amman muna lek’awa, kullum, check up”. Shiruuu, Huda ta yi kafin ta ce “Anya kuwa Sakina?” Sai da Sakina ta yi dariya sosai tukunna ta ce mata “Allah da gaske, babu komai ma fa tsakaninmu har yanzu sai dai hira kawai da tsantsar kulawa da soyayyyar da yake gwada min. Da sauri Hudan ta ce “Kai!” Cikin murmushi Sakina ta ce “Kin san Allah nima kaina ina mamakin shi, ba daban ina fahimtar yanayin sa ba tou da sai in iya cewa ma bashi da lafiya…Ban san dalilinsa ba kinga ni kuwa ai bazan ce gani ba! Besides ni nama fi son haka.” Ajiyar zuciya Hudan ta sauk’e kafin ta ce “Kuma bai chanja miki ba? As in ba ya wani fushi da ke” “Ko d’aya, wallahi kulawar ma da yake bani ni kaina banyi tunanin ta ba kawai dai maybe shi tsarinshine haka ko kuma dai wani abun besides ai bamu fa wani dad’e ba so it’s not an issue.” “Shikenan tou, ki gaidashi” Shine abunda Huda ta ce. Daga nan suka yi sallama suka kashe wayar. Murmushi kawai ta yi tana duba wayar, a hankali ta sauk’e ajiyar zuciya ta shiga tunani ....Kullum tare suke kwana, a jikinsa take yin bacci, tana jin yanayin bugun zuciyarshi da yadda yanayinsa yake alamun lafiyarsa k’alau kuma a k’age yake amman in banda hug ba abunda ya tab’a shiga tsakaninsu…… Sam bata san ya shigo d’akin ba dan yaje siyo musu milkshake a chan k’asan hotel d’in da akeyi wani mai dad’i! Sai da ta ji ya kwanta a bayanta tukunna ta yunk’ura da sauri tana shirin yin magana shi ya rigata ta hanyar cewa “Sakina I love you fisabilillah Ba wai wani abu daban ba! Shiyasa kika ga ban yi yunk’urin komai ba saboda Ina so ne har sai kin fahimci hakan, kin yarda dani, kin saki jiki dani tukunna. Na san zan takura amman yadda nake jin ki a raina tsaf zan iya rayuwa dake a haka muddin baki gama fahimtar kalar k’aunar da nake yi miki ba……..” A hankali ta juyo sosai tana kallonshi suka yi facing juna a kwancen! Kasa cewa komai ta yi kawai sai ta sunkuyar da kanta k’asa kafin chaan! Ta ce “Ya Auwal na yarda da kai na yarda da chanjin da na gani a tattare da kai. Tunda har kaga na aureka tou yarda da k’auna ce ta kawo hakan. Sannan zan rayu da kai a ko wanne hali.…..” Yadda ta ga yana kallonta ne ya sanya ta yi saurin b’oye fuskarta a k’irjin shi dan tashi d’aya sai ta ji duk kunya ta lullub’eta. Murmushi ya yi yad’an shafa kanta, a hankali ya yi kissing kan nata yana mai shak’ar k’amshin da yake fitarwa kafin ya shiga binta da wani mayen kallo k’irjinsa yana bugawa da masifar gudu…. Sannu a hankali yanayinsa yana k’arasa sauyawa ya sa hannu ya janyota ya saka ta a jikinsa sosai!. Sai da numfashinta ya kusan d’aukewa sakamokon wasu sak’onnin da ya shiga aika mata waenda suka girmi hankali da wayonta. Da sauri cike da tsoro da fargaba muryarta na rawa ta ce “Dan Allah!!! Ni fa da nace haka bawai ina nufin yanzu ba.” Ko sauraronta Auwal bashi da niyyar yi, dan tun kafin a je ko’ina notikan kansa suka kwance hankali ya fara barin gangar jikinsa… Tabbas ya yarda kuma ya sake tabbatarwa ‘kamilalliyar mace daban ta ke! Sannan matar sunna sinadarinta na musamman ne’ Gashi kuma abun sai ya taru ya had’e masa da giyar zazzafan feelings da soyayyar da yake yi mata, shi yasa ya manta kowa ya manta komai hatta shi da karankansa ya manta kansa. A ranar Huda ta sha Allah ya isa dan ita ce ta kirata a waya har ta janyo mata wannan jalalar. Sam bata tab’a tunnanin zatayi rai ba dan Mr Auwal sai da ya yi mata dalla dalla…….. Tun daga ranar kuwa ta rasa nutsuwa da sukuni. Daga nan ma Las Vegas suka wuce Honeey moon… Auwal shi kad’ai yake k’ibarsa yana enjoyment d’inshi Ita kam in banda rama ba abunda take yi dan kwata kwata ba enjoying garin take yi ba dan ita gani take ma kamar su suke tunzurashi yin wasu abubuwan......... Da kyar Aaiima ta iya samun Abba ta yi masa maganar Junaidu dan zuwa wannan lokacin kam soyayya mai k’arfin gaske ta k’ullu a tsakaninsu. Abba ne ya samu su Dad ya yi musu bayani su kuma suka ce a tambayi su Mama indai har ba shi da wani mugun hali sai a shirya komai dan kasancewarsa d’a ga Usman hakan ba shi zai sanya su shiga tsakanin Aaima da farin cikin ta ba dan k’iri k’iri ta nuna shi take matuk’ar so!. Sannan su a ganinsu yanzu Aaiman abar tausayi ce duk da kuwa sun san idan suka ce rashin Mammy yana a cikin matsallolin Aaima ba su yiwa Mommy adalci ba duba da yadda take iyakar k’arshen k’ok’arinta wajen ganin Aaiman bata rasa komaiba amman kuma uwa dole daban take. Dan haka za su yi k’ok’ari wajen ganin sun taimaka farin ciki ya wanzu a rayuwarta na dindindin...... Tabbas Mama ta ji dad’in wannan had’in dan haka tashi d’aya ta faiyyacewa Abba halayen Junaidu wanda tun tasowarta dashi bata tab’a ganin shi da wani mummunan hali ba sai dai mai kyau sannan yanada zuciyar nema da amana ga sanin ya kamata….. Abba ma ya ji dad’in jin haka dan haka ya ce “bara ya je kawai ya samu su Dad ayi komai a gama. Kafin Aaiima ta tafi rubuta finals d’inta a saka rana, tana dawowa a d’aura aure in shaa Allah.” A hankali Mama ta ce “Amman fa Abba akwai wani abu guda d’aya! Kasan case d’in Junaidu na zaman jail wanda tunda ya je ya dawo ya kud’ance! Kud’i na ban mamaki…. Last week ma sai da aka sake gano Gidaje da kadarorinsa dan shi b’oyewa yake yi..a iyaka Kano fa Gidajensa masu matuk’ar kyau da tsada sun fi ashirin ga kadarori ga filaye wanda bamu san source of income d’inshi ba! Inda hali gaskiya a d’an yi mishi tambayoyi akan wannan lamari a bincika. Naji dai kwanaki su Abba Madu sun ce sun yi mishi tambaya amman banji sun ce ga amsar da ya bayar ba.” Jinjina kai Abba ya yi daga nan ya ce ‘zai nemi zama da Junaidun ko zuwa gobene in shaa Allah, su tattauna.” .....Har gida kuwa Junaidun ya zo ya sameshi bayan ya ce masa ‘ya zo yana son ganinsa’ Shi da Daddy ya tarar dan haka ya gaidasu cikin girmamawa suka amsa masa da kulawa. Ba tare da b’oye b’oye ba Abba ya ce “sun san bashi da wani mummunan hali amman kuma suna buk’atar sanin kwakkwaran source of income d’inshi” A hankali Junaidu ya sauk’e ajiyar zuciya kafin ya fara basu labari.... “A lokacin da aka sallame ni daga prision………… Mun fito mun kama hanya, bamu kai ga zuwa inda za mu je ba cikina ya b’aci! Dan haka na nemi alfarmar su tsaya in d’an yi uzuri. Suna tsayawa na fita… Ina kutsa kai cikin d’ajin kamar an ce in juyo nan na ga wasu maza da mask su uku sun nufi motar. Duk sai da suka fito da y’an motar suka dubasu amman sam babu abunda suke nema wanda sai daga baya na gane waenda Arshaad ya tura ne kuma ni suke nema. Kamar na sani a lokacin sai na b’oye kaina. Bayan na b’oye kaina su kuma suka gama dube duben su suka tafi. Su kuma Abokanan tafiyar tawa inaga tsorata suka yi dan ina shirin fitowa naga duk sun shige motar suna shirin tafiya. Da sauri na yunk’ura zan tafi na ji an rik’e min k’afa! Sai da gabana ya fad’i da na juya dan ni sam ban lura akwai tsoho ma a wajen ba a durkushe sai da ya rik’o nin. Cikin kuka tsohon ya ce “bawan Allah ko baiwar Allah dan Allah taimakon musulunci zan mutu yunwa nake ji.” Da sauri na ce “Baba dan Allah Abokanan tafiya ta za su tafi ka cikani In wuce.” Cikin kuka tsohon ya ce “yunwa nake ji ka taimakeni dan Allah” Haka nan inaji ina na gani na kama hannunshi ya mik’e su kuma Abokanayen tafiyar tawa suka wuce dan maybe sunga na dad’e su kuwa a tsorace suke. Na ji takaici sosai amman yadda tsohon nan yake karkawa da kuka yasa kawai na yanke shawarar In taimakeshi. Sai da muka fara tafiya na fahimci ashe makaho ne! Haka muka yi ta kutsawa dan hanyar ba jama’a sosai har muka iske wata mai k’osai da kunu na siya da d’an kud’in da aka bani in yi na mota na bashi ya ci ya sha. A hankali muna zaune a wajen ya ce “in bashi labarina” Haka kurum ban sanshi ba amman na tsinci kaina da fad’a mishi komai na rayuwata har kawo yanzu. A hankali ya ce “kuma kana ganin ba kai ake nema ba kuwa!?. Ka zo mu je Gidana ka d’an b’uya kafin kwana biyu sai ka wuce gudun kar ka je suna nan har yanzu ka fita a kamaka.” Tsoro ya sanya ni na amincewa wannan tsohon, dan a yadda naga mutanen nan babu kalar imani a tattare da su. Gidan nasa y’ar bukka ce sai band’aki wanda aka yishi da langa langa a gefe sai wani murhu da rijiya. Sam babu wani katanga ko wani abun da yake nuni da wajen keb’antacce ne. Y’ar bukkartashi muka shiga muka zauna anan yake ce mini “Matarsa ta rasu watan da ya mutu, Allah bai bashi d’a ba! Danginsa kuma duk sun guje shi saboda basa son d’awainiya.” Atake na ji tausayin bawan Allahn nan ya rufe ni, kuma a take muka saba shak’uwa ta shiga tsakaninmu….. Kwana na biyu a wajensa, na siya mishi abinci da d’an abun da ba a rasa ba duk a cikin kud’in da aka bani a lissafina idan na tashi ni sai In d’auki drop har gidan Abokina ya biya. Ban b’oyewa tsohon nan ba na ce masa “muma ba wasu masu arzik’i baneba, ba daban haka ba da na tafi da shi” dan na lura yana cikin kad’aici da buk’atar taimako “kuma akwai abubuwa da dama a kaina amman dai bara mugani in shaa Allah idan na koma gida na yi settling zan dawo in duba shi. Dan nima a yanzu Ina matuk’ar buk’atar kud’i.” Daga nan na nemo wata mata a gefe na rok’eta akan “dan Allah ta d’an dinga lek’ashi” Ita kam Matar mamakima ta dinga yi dan a cewarta “duk zaman ta a k’auyen ita bata san da shi ba”. Bayan Matar wuce ne muka yi sallama muna ji kamar kar mu rabu… A bakin bukkar tashi Ina fitowa na ci karo da wani mutum cikin suite! Da akwati a hannunshi, kamar yana cikin sauri, ya nuna min hotonshi da wannan tsohon kamar lokacin tun suna samari ya ce min “an ce yana nan! Da kyar da wuya ya samu location d’insa, dan Allah na san shi?” Ba tare da b’ata lokaci ba na ce masa “eh” Dan haka mutumin ya ce mini “sun tab’a yin businesses da tsohon ne, tsohon ya aminta da shi amman shi sai ya gudar masa da kud’insa so tun daga lokacin abubuwa basu yi mishi kyau ba! Shiyasa ya yanke shawarar dawo mishi da dukiyarsa.” Ya d’aura da cewa “Dan Allah in bashi in ce masa ya ce sunanshi Kabir, Alhaji Kabir. Ya taimaka ya yafe masa” Yana min maganar ne shi duk a tunaninsa ma ni d’an tsohon ne. Jin muryar tsohon ya fito yasa ya yi sauri ya yi min sallama a cewarsa ‘ba zai iya facing d’insa ba dan kunyarshi yake ji.’ Duk da nace ya d’an tsaya ko ruwa ne ya sha saboda naga inba magana ya yi ba tsohon ba zai gane shi ba dan ba gani yake yi ba, amma sam yak’i yarda, ya damk’a min akwatin yana d’an waiwayowa yana kallon tsohon har ya shige motarshi driver ya ja suka tafi. Akwatin na ja na kai d’aki na fito na kama hannun tsohon muka shiga ciki na zauna. Na zuge akwatin ba tare da na ce komai ba. Sai da gabana ya yanke ya fad’i dan gabaki d’aya akwatin cike yake da mak’udan kud’ad’e dollars! A hankali na ji tsohon ya ce “Kai da waye d’azu a waje?” Cikin In inaa na ce “wani mutum ne ya zo neman ka! Ya ce kun tab’a yin buisiness kai da shi ya gudar maka da kud’i.” Shirruuu tsohon nan ya yi kafin chaan! Ya yi murmushi ya ce “na kasa tunawa” Kafin ya sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya ya ce “Akwai abunda ban gaya maka ba… Inada sabara a kwakwalwata shiyasa ma kaga wasu lokutan Ina zama ina yin kuka ni kad’ai. Wani makwafcina anan ya d’auke ni satin baya ya kaini asibiti aka tabbatar da cewa ‘ba zan k’ara sati uku a duniya ba!’.” A take wani tsananin tausayinshi ya lullub’e ni! Ga dai kud’ad’e nan ya samu bayan ya sha wahalar rayuwa amman a lokacin da kud’ad’en suka riskeshi sai ya zamana ba za su yi mishi amfanin komai ba. Ban san lokacin da kuka ya kufce mini ba!. Jin ina kuka yasa tshon ya hau tambayata “menene? Mai ya faru? Me ye a cikin jakar? Ko wani abun tsoron na gani?” Shiru na d’anyi kafin ince mishi “Kud’i ne a ciki, Dollars.” Shiruuu na ji ya yi… Ya jima tukunna ya ce “Ka taimakeni ko masallatai ne in gina dan Allah. Saboda kaga ni ba ido da lafiya gare ni ba. Bana bukatar ka gina min gida ko wani abu daga kud’in tunda kaga ba lallae inga k’arshen aikin bama kawai dai ka rik’e Allah ka tayani gyara lahirata ta hanyar gina masallatai da islamiyoyi a k’auyukan nan.” A lokacin tabbas ina son komawa gida amman kuma wannan tsohon yana buk’atar taimakona a yanzu sannan inaso a ida auren Huda da Arshaad kafin In koma dan tabbas na kasa cire ta a cikin zuciyata kuma na riga na d’auki alk’awarin ba zan aureta ba! Tunda na lura sam bana cikin zuciyarta tun ranar da ta ce min Arshaad zata aura k’ok’ari kawai nake yi inga na fitar da ita a raina saboda no matter how much I love her ba zan tab’a iya zama da ita idan bata ra’ayi na ba! Amman kuma bana buk’atar a aurar da ita a gaban Idona sannan still ina jin fargabar fitowata duba da sharrin da aka yi min da kuma waenda nake tunanin ni suke nema..A ganina gara In d’an fahimci abubuwa daga b’oye kafin a kaini lahira tun da ban san waye yake farautata ba! Sannan aikin da zan yiwa wannan tsoho tabbas lada zan samu… Shiyasa a take na yanke shawarar jifan tsuntsu biyu da dutse daya.... ...Haka nan na tsaya tsayin daka wajen taimaka masa kamar yadda ya buk’ata aka shiga gina masallatai a duk k’auyukan da makarantun islamiyya gini mai kyau da had’uwa, na ban mamaki. Tabbas Ina da buk’atar kud’i amman ban tab’a yunk’urin d’aukar ko naira biyar ba! Apart from kud’in motar da yace In dinga d’auka a ciki dana abinci da shelter. Akwai kud’i sannan na samu maaikata masu yawa sosai dan ko wanne k’auye masu ginin daban suke shiyasa kafin wata uku aka fara shirin kammalawa. Ba abunda yafi sakani farin ciki irin yadda Allah ya arawa wannan tsohon tsawon rai har na tsawon lokacin da aka zo kammalawa duk da dai jikin nashi sai a hankali. Ranar da na kammala aikin da washegari ya tashi da tsananin ciwo wanda kana gani ka san sai a hankali kawai. A wannan bukkar tashi muke har kawo wannan lokacin amman fa muna cin mai kyau mu sha mai kyau. Ina ganin yana yin jikin nashi na ce “bara inje In nemo mai abun hawa a kaishi asibiti cikin gaggawa” Amman sai ya rik’eni ya rok’eni akan in tsaya akwai maganar da yake so ya yi da ni. Abu na farko da ya fara tambayata shine sunana! Duk tsawon lokutan nan Yaro yake kirana da shi ni kuma in kirashi da Baba. Sai da mutanen last k’auyen da aka yiwa masallaci suka tambayeni ‘suna son rubuta sunanshi’ Tukunna da kyar ya ce min sunanshi ‘Alhaji Kabir mai fetur’ ....Ahankali na ce mishi “sunanan ‘Junaidu’.” Da kyar cikin tsananin ciwon da yake ciki ya iya ce min “in d’auko masa wata y’ar jaka” Ya yi maganar yana mai yi min nuni da wajen da jakar take! Tabbas na shiga rud’ani saboda yadda ya juya ya nuna min jakar yasa na fahimci yana gani..... Ina d’aukowa ya ce “In bud’e” Ko da na bud’e d’in wasu takardu ne a ciki da waya had’ad’d’iya mai kyau da tsada. Wayar ya umarceni da in d’auko, in yi dialing number dana ga an yi saving da ‘barrister’. Haka akayi, tana shiga bugu d’aya ana biyu aka d’aga! Cikin girmamawa na ji ance “sir” Da mamaki na kalli tsohon wanda shi kuma yake mik’a min hannu alamun in bashi wayar… Kaina bai gama d’aurewa ba sai da na ji kalar turancin da tsohon yake yi inda cikin harshen turanci na ji yana cewa wannan wanda suke waya “Suna kusa ko? To su yi sauri suzo yanzu.” Tsoro da firgici suka sanya na mik’e da sauri na fara ja da baya. A hankali tsohon nan ya ce “Dan Allah kada ka ji tsoron komai. Matso kusa in baka wani d’an tak’aitaccen labari.” Da farko k’in yarda na yi in matsa d’in dan ni a tunanina ko d’an shan jini ne ko kuma d’an 419 bare ma da na tuno da mak’udan kud’ad’en da aka kawo mishi gaba d’aya sai na sake duburbucewa. Da kyar da sid’in goshi ya lallab’ani na matsa kusa da shi. Ina zama ya ce min “Kar ka ji tsorona d’ana, Ni ba macuci bane ba” Bai bani damar yin magana ba ya cigaba da cewa “Kamar yadda na fad’a maka da farko Allah bai bani haihu wa ba. Na kasance attajiri na gaske dan a k’asar nan idan akwai waenda suka fini kud’i tou bana jin za su fi mutum biyu! Arzik’i na ya samo asali ne daga sana’ar man fetur, da na samu Ubangiji ya sanya mini albarka harkar tawa ta bud’e sai na fad’a sana’a Business ko wanne iri ne zan yishi kuma da ikon Allah Ina farawa sai ya habb’aka ya yi albarka ta ban mamaki. Ni asalina maraya ne, tun Ina gidan marayu muke soyayya da matata da na ce maka ta rasu watan baya. Ina matuk’ar k’aunarta sai dai kuma kishiyoyinta suka zamo silar da ya sanya bata ji dad’i a rayuwarta ba! Ta rayu cikin tsananin k’unci da azabar rayuwa. Ni mutum ne wanda yake son mutane masu amana, bayan son da nake yi wa uwar gidanaa tsoron Allah da amanarta ne suka k’ara min tsananin k’aunarta. Apart from her bana jin akwai wanda ya tab’a rik’e mun amana yayi mun abu tsakaninshi da Allah sai kai Junaidu. Na sha adopting Yara in rik’esu tsakani da Allah amman kowa idan ya lek’a ya hango tarin dukiyata sai ya nemi cutar da ni! Rabinsu ma buri suke kawai suga sun halaka ni. Da taimakon Allah da taimakon uwar gidana nake tsere wasu tarkunan wanda fahimtar da aka yi tana taimaka min ne yasa aka shiga tsakaninmu na juya mata baya.” Cikin kuka ya ce “Ban tashi gane gaskiya ba sai a ranar da zata bar duniya tukunna aka samu asirce asircen suka bar jikina na ganta a matsayin masoyiyata instead of da da nake ganinta as my enemy. Na yi kuka ma yi takaici! Saboda ita take d’awainiya da ni idan ciwona ya motsa Ina kyararta Ina komai ashe itama bata da lafiya. Duk da na saki ragowar mata na biyun da na fahimci laifin su ne sannan na bata hak’uri ta ce ta yafe min amman na kasa yafewa kaina! A ranar da zata bar duniya maimakon ni in lallasheta A dead bed d’inta sai ya samana ita take lallashina. Na yi rashi tabbas sannan na san na rasa mutum d’aya tak da ya tab’a rik’e mun amana. Ita ce ta ce min ‘In kwantar da hankalina zan samu wanda zai rik’en amana kamar ita I should mark her words.’ Bayan ta rasu da kwana biyu.. daman tun kafin a shiga tsakanin mu na yanke shawarar ‘zan damk’awa mutum mai amana guda d’aya rabin dukiya ta idan na samu kenan, rabi kuma in rarraba a gidan marayu, ba wai kuma masu kula da gidan marayun zan bawa in ce su raba musu ba A’a Yaran gidan marayun zan bud’ewa account each In saka musu kud’insu a ciki saboda yadda duniya ta lalace tsaf mutane za su iya danne kud’in dan na ga yadda mutum yake komawa akan dukiya….. Saboda haka na fara searching….. A yadda na je maka a haka nake zuwama mutane amman har da waenda suka mareni! Mutum d’aya na samu kafin kai ya taimaka min kamar yanda ka yi sai dai shi ana kawo kud’i kamar yanda aka kawo aka baka ya gudu! Ko lek’e na bai sake yi ba.......” ....... Muna cikin wannan zancen Mutannen da ya kira suka k’araso. Manyan lauyoyine da kuma wani babba a efcc. Da mamaki nake kallonsu. Ban san sanda hawaye suka zubo mini ba! Jin yana musu bayani akan yadda ya yi alk’awarin bawa mai kyakkaywar zuciya dukiyarsa. Hope takardun sun zama ready? Saboda gani nan” Ya yi maganar yana nuna ni ya ce “Nine successor d’insa” A take suka ce “eh, komai is ready” Sannan suka mik’o min takardu suka ce “in yi signing.” Da farko kasawa na yi saboda yadda mamaki aljabi da tsoron Allah ya lullubeni, sai da tsohon ya rik’e mun hannu tukunna na dawo dede na shiga signing takardun da kwakwalwa ta ta kasa d’aukar d’umbin kud’ad’en da idanuwa na suke gane min!. Ina gama cike wadannan tsohon ya ce “yaso ya rabawa marayun kud’ad’en da kanshi amman kuma bashi da isheshen lokaci so zai d’aura wannan nauyin a kaina” Nan ma wasu takardun na cike na kud’i shima dede adadin wanda aka gama mallakamin wanda zan rabawa marayun nan. Jakar da d’azu ya ce ‘In d’auko in bashi waya a ciki’ Ita kuma filayene da gidaje da gidajen man fetur d’insa, ya ce min “I should consider it shikuma as thankyou from him, dan bai san ta Ina zai fara yi min godiya ba! Na tabbatar da maganar matarshi sannan na bashi hope na cika mishi burinshi.” Daga nan duk ya saka na yi signing Ina kuka yana kuka. Sannan ya bada will d’in nine d’ansa sannan ya rok’eni ‘ko bayan ranshi in dinga yi mishi addua dan Allah.’ Ganin numfashinshi yana d’aukewa yasa na kinkimeshi muka kai shi motar da mutanen nan suka zo a ciki amman Ina kwantar da shi a seat d’in baya na ji yayi kalmar shahada a hankali sannan jikinshi ya sake...... Na yi kuka matuk’a..... Ban yi k’asa a guiwa ba, tundaga Adamawa har Abuja sai da na je da kaina na fara rarrabawa marayun nan rabin kud’ad’en shi da na yi alk’awari wanda har yau ina kan aikin.” A hankali Junaidu ya sauk’e ajiyar zuciya kafin ya ce “Wannan shine sanadin arzik’i na. Babu k’arya k’ari ko ragi a cikin labarina.” ...... A hankali su Abba suka sauk’e ajiyar zuciya bayan sun gama saurarenshi kafin Abba ya ce “Tabbas Junaidu samun irinka a zamanin yanzu sai an tona. Allah ya yi maka albarka. Ka cigaba da rik’e amana da alk’awari Allah yasa ka gama da duniya lafiya. Idan mun gana magana za ka ji sak’on mu daga wajen Aaima in sha Allah.” Cikin girmamawa ya yi musu godiya daga nan suka yi sallama ya wuce......... Bayan sati d’aya Aaima ta ce masa “su Daddy sun ce yana iya turowa anytime idan sun shirya” Tsakanin Aaima da Junaidu ba zaka iya tantance wanda yafi wani farin ciki ba. Su Kaka da Ya Jamilu ne suka zo suka nemawa Junaidu auren Aaima. A parlourn Daddy aka tarbesu tarba ta mutunci! Cikin mutunta juna suka yad’a manufarsu suka nema aka basu. Wata biyar ciff! Aka saka ranar auren daga nan suka bayar da goronsu da alawa da kud’i nera miliyan d’aya! Aka watse cikin farin ciki barkwanci mutunta juna da nishad’i. …………….. Sai da Sakina ta fara kukan gida tukunna Auwal ya yarda suka dawo a lokacin watansu biyar a k’asashen waje. Ya so ta tsaya su biya Paris dan nan ne kad’ai basu je ba a cikin k’asashen da ake yawan zuwa a d’an shak’ata (Har Hajji da Umaara sun yi) Amman ganin yadda ta d’aga hankalinta sannan ga yanayin condition d’inta yasa kawai ya hak’ura suka dawo. Direct gidansu, Daddy ya ce su wuce dan ta samu ta d’an huta. Tabbas Daddy ya san in ba da kyar ba to kuwa za a yi irinta Granpa da Aslam A shi da d’an cikin jikin Sakina saboda yanda yake jin son jika ko jikar tashi tun kafin su zo duniya a ransa Allah kad’ai ya sani. Ita Sakina har mamaki da kunya ma take yi, haka nan fa takanas! Zai kirata ya yi ta jero mata adduo i ita da babyn sannan ya yi ta turo mata important things akan condition d’inta abunda ya kamata ta ci da wanda bai kamata ta ci ba saboda lafiyarta da babyn… Wasu lokutan ita kam har kukan farin ciki take yi dan gata da soyayyar da Auwal yake nuna mata bata jin she could ever ask for more. Tunda ta lura yana d’an wasa da sallah ta kafa ta tsare sannan ta nuna mishi b’acin ranta! Yanzu sam Auwal ya manta rabon da ya bari lokacin sallah ya wuceshi. Zaman lafiya da k’aunar juna shine definition d’in rayuwar su ga families d’inshi suma hatta Granpa da Mom kiranta suke yi su ji ya lafiyarta da babyn dan Auwal a ranar da ya sani washegari ya kasa rufewa farin ciki yasa sai da ya fad’awa su Mom da Gramma har su Abba tukunna hankalin shi ya kwanta, sai da ya gama sanarwa kuma sai ya d’anji kunya. Idan ka gansu tsaf da su sun yi k’iba sun yi fresh in banda glowing ba abunda suke yi! Gashi sun yi mugun dacewa da juna, kamar ka sace su ka gudu. Gidan da Arshaad ya siya zasu zauna da Huda nan ya mallakawa Auwal, hatta lefe da kayan d’akin suma su Daddy duk suka bashi. Sakina taso biyawa ta ga Huda amman jin yadda Daddy ya damu akan ta huta wai ‘ta hawo jirgi ta yi jigila jigila’ yasa kawai ta hak’ura suka wuce gidan ba dan ranta yaso ba. A hakan ma kuma Daddyn ya ce “zuwa gobe su je asibiti a tabbatar da komai dai lafiya” A chan suka tarar da Gwaggo Asabe tana gyaggyara musu gidan ita da wata mai aiki har girki sai da tayi musu. Suna gama oyoyo d’insu ta sulale ta fice ko sallama bata yi musu ba dan karma su rik’eta saboda ita tun kwanakin baya da Mommy ta tilastamata zama a wajen su Hudan ko kwana d’aya bata iya yi ba ta gudu ta koma gidan Mommy a ranta kuwa ta raya ‘ta gama zama gidan sabbin Amaren nan gaskiya’.......... Aslam, yana tuk’i yana d’an satar kallonta. Ganin tak’i ta yi shiru yasa ya sauk’e ajiyar zuciya ya yi parking a d’an gefen titi kad’an ya kashe motar ya juyo ya kamo hannunta. Kamr za fashe da kuka ya ce “Hudatie, kukan nan ya isa haka dan Allah. Saboda ke fa na je wai dan ki d’an samu ki shiga mutane amman ni kam na jima ma rabona da shi. Da ace na san kuka za ki d’ebo Allah da ba za mu je ba gaskiya. Ki share hawayenki… Come here.” Ya fad’a hakan yana mai janyota izuwa jikinshi. Da kyar ya samu ta d’an yi shiru kafin ya ce “Ya Aslam matar nan ta bani tausayi..wallahi ba ita ta d’auka ba! Sannan Yaron ina ganin lokacin da Maman shi ta bawa wannnan maid d’in shi a wani lungu wajen ba kowa time d’in ni kuma na fita yin waya da Sakina ne.” Da sauri Aslam ya ce “are you sure?” Cikin tabbatarwa ta d’aga mishi kai alamun ‘eh’. A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya kafin ya ce “Tun farko daman maganar sark’ar nan na fahimci makircin mata ne. Wannan maganar Babyn kuma da kika fad’a min yanzu ya sake tabbatar min. Zan je in samu Yash d’in In fad’a masa sannan In tsaya har sai naga an fitar da ita tun kafin a shiga kotu ma. Amman wacce iriyar dak’ik’iyar uwa ce zata yiwa d’an da ta haifa a cikinta haka?” Cikin share hawayenta ta koma gefe ta zauna ta ce “Nima dai abunda na ce kenan, amman wallah yadda naga ta bawa wannan maid d’in Yaron Allah yasa In ga Annabi. Sannan jakar MANNUBIYAn a hannuna take! Ta bani bayan ta d’auki abu a ciki ta ce ‘in rik’e mata bara ta je ta yi chanjin ta dawo’ A gabana ta bud’e ta d’auka abun da zata d’auka, ba komai a cikin jakar sai y’ar k’aramar fasashshiyar wayarta da abunda ta d’auka sai d’ari biyu wallahi. Tana dawowa ko tab’a jakar bata yi ba na ajjiye mata akan cinyarta. Kuma ko da ta dawo d’in babu komai a hannunta haka nan ta nemi waje ta zauna da jakar a gefenta. Tana zama wayarta ta d’au ringin ta bud’e ta d’auka…. Tana gama wayar muka ci gaba da hira take ce min ‘Babanta ne Za’a yi sadakar arbain d’in Mahaifiyarta jibi.’ Daman tun zama na na fahimci tana cikin damuwa, tun farko ita kad’ai a gefe na hango shiyasanya ma na je na zauna kusa da ita Ashe dalilin kenan.......” Cikin jinjina kai Aslam ya ce “shikenan, zan je In samu Yash d’in. I wonder why ya yi believing da sauri haka har ta kai shi ga yi mata wannan wulak’ancin! Yanada zurfin tunani ban san me ya shiga kanshi ba… Anyways zan je in sameshi. Yanzu ki daina kuka share hawayenki kin ji honey…” Cikin share hawaye Hudan ta ce “Ta bani tausayi ne sosai wallah, har da kukanta dama tana bani labarin Mahaifiyarta sai kuma kawai muka ji sanarwa. Ni a ganina lokacin da wajen ya hargitsene aka saka mata sark’ar a cikin jaka saboda tabbas a k’asa muka hango jakar a jefe tana d’auka kuma aka k’araso kanta.” “Hmmm, makircin mata ne kawai.” Cewar Aslam yana mai kunna motar. A hankali Hudan ta ce “D’an Indiya ne? Friend d’in naka, na ji sunansa ‘Yash’.” Murmushi Aslam ya yi kafin ya ce “sunanshi Yashjub, Itama MANNUBIYAn baki ji Manu ake ce mata ba.” Cikin son faranta mata rai da kawar da zancen ya ce “Good news sannan surprise…. Bara dai mu je In munje za ki gani......” Tunda suka shiga gidan suka zauna Aslam ya yi waya ya ce “suna parlour” ta kasa nutsuwa, in banda gyara zama da kalle kalle ba abunda take yi. Ta so ta gane wasu items a cikin gidan kamar waenda suka zab’a ne ita da Sakina lokacin bikinta da Arshaad. Da sauri ta kalli Aslam ta ce “Laaa Ya Aslam Sakina ce ta dawo ko?” Dai dai nan suka k’arasa sauk’owa ita da Auwal. Jikinta ne kawai ya bata tana bayanta ga kuma Aslam yana kallon wajen yana murmushi. Da sauri ta juya sai kuma ta mik’e da gudu ta zagaye kujerar ta tafi zata fad’a jikin Sakinar. Da sauri Auwal ya shiga gaban Sakina tsakaninsu ya tsaya ya ce “a,a,a,a careful!!” Yana d’an zaro ido da d’aga gira da d’an murmushi akan fuskarshi. Da sauri Huda ta ce “Au sorry na manta, Daddy ya Auwal” tana d’an dariya. Dariyar shima ya yi yad’an matsa ai kuwa da sauri Sakina ta rungumeta ta na share hawayen murnar ganin y’ar uwartata. Cikin farin ciki da k’aunar juna suka hau gaggaisawa da tambayar bayan rabuwa. Sun jima suna hira kafin Sakina ta ja Huda suka yi sama. Auwal kuma ya kira Arshaad suka hau video call su uku! Ba k’aramin dad’i suka ji ba da ganin yadda Arshaad d’in ya sake sakewa ya ware sosai kamar komai bai tab’a faruwa ba….. Suna hawa saman Huda ta fara tab’a cikin Sakina tana murna har da kwallarta… Nan suka zauna Huda ta fara zab’an sunayen da zxata sakawa Babyn In sakina ta haihu. Ganin da tayi kamar Sakinar is moody ne yasa ta shiga tambayarta da damuwa akan fuskarta. A hankali Sakina ta ce “Ni inata mita mu ba a cikin estate za mu zauna kusa da ku ba, ashe ba ma a garin zamu zauna ba gaba d’aya.” Ajiyar zuciya Huda ta sauk’e kafin ta ce “Ai kin san Ya Auwal shi ke da MT d’in Abuja, dole kinga a chan za ki zauna kusa da shi mana Sakina. Za mu dinga zuwa ai ku ma kuma na san za ki dinga zuwa sannan na san maybe ma ya dawo dashi Kano gaba d’aya ko?” A hankali Sakina ta ce “Ai cewa yayi wai a chan Cairo zan yi karatu kuma de! Ni duk kaina a d’aure yake ban ma san wajen zama d’aya tak’ameme ba, ya ce min dai wai zan ji dad’in karatun sosai.” Dariya Huda ta yi kafin ta ce “ashe ya yarda kenan.. Ya Aslam ne ya sama mana karatun mu biyu ni da ke, da yayi mishi maganar da farko sai kamar bai yarda ba ya ce ‘shi yana Abuja family suna Kano ke d’in idan kika yi masa nesa aganinshi abun zai d’anyi wuya’ Shiyasa Ya Aslam ma ya ce min kar In gaya miki yet ki d’aga mishi hankali tunda bai riga ya amince ba. Kinga yanzu kuma ashe ya amince…” Da sauri Sakina ta rungume Huda ta ce “Na ji dad’i da za mu yi karatu tare”. …. Sai da dare ya yi sosai tukunna su Huda suka kama hanyar estate. Aslam sarai ya lura da Huda, yadda duk jikinta ya yi sanyi kuma tabbas ya san damuwarta.. A hankali ya ce “Hudatie kowa fa da lokacinshi, sannan ai lokacima bai wani ja ba, Manu fa matar Yash Indai zan iya tuna lokacin da ya turo min iv d’in bikinsa tou ina jin yanzu shekararta uku da aure! Amman har yanzu bata haihu ba kuma kinga kishiyarta ita har ta haihu Ita kuma tace me? Ga Mommy itama sai da ta yi shekara kusan...” Kukan da ta fashe masa da shi ne ya sanya shi sauk’e ajiyar zuciya yad’an kamo hannunta ya ce “Gaskiya Hudatie zan fara miki bulala! Gaba d’aya kin zama shagwab’abb’iya, abu kad’an kuka?” Cikin kukan ta ce “tou Ya Aslam bakaga ita Manu d’in an yi mata kishiya ba?” “Da sauri Aslam ya ce “Woow!! Good idea Huda, kai! Amma Allah ya yi miki albarka, kin kawo shawara kinga nima sai in k’ara auren kenan! Bara muga..daman ina son k’asar Egypt dan haka y’ar egypt zan fara aurowa sai in auri y’ar indiya sai in je garin Taraba In auro saboda Mommy sai kuma In tafi Chad in auro saboda inyiwa Dad shima kara.” Cikin k’ara sautin kuka Huda ta ce “Ya Aslam ka fa lissafa hud’u kenan, ni kuma a ina za ka saka ni?” Tana tambayar tana sake fashewa da kuka. Cikin dariya k’asa k’asa ya ce “Au haba?? Ok tou bara in cire y’ar indiya tunda kema ai kinada gashi sosai Irin nasu” This time around duka ta fara kai masa…… Cikin tsananin dariya da nishad’in da yake ciki ya ce “Haba mana Hudatie Ubangijine fa ya ce mu yi biyu uku har hud’u indai za mu yi adalci.” Ya fad’i haka yana Parker motar a harabar gidansu dan har sun iso. A hankali ya kamo Hannunta cikin kulawa ya ce “Kinga ni kuwa ba zan iya yin adalci tsakaninki da ko wacce mace ba shiyasa na zab’i in zauna da guda d’aya! Dan nasan muddin na k’ara aure to zan kasance cikin mazan da suke tashi da shanyeyyen b’arin jiki ranar gobe k’iyama.” Kamar wata wawuya sai kuma ta fara murmushi kad’an kad’an tana kuka. A hankali ta kwanta a jikinshi yasa hannu ya yi hugging d’inta. Dariya ya yi kafin ya ce “Irin wannan zafin kishi haka? How much do you love me??” Ya yi mata tambayar yana murza tafin hannunta. A hankali ya ji ta ce “Stars da ruwa kansu inda ace za a iya kirga su tou baza su kai adadin yadda nake k’aunarka ba Ya Aslam.. I love you so much!!! Till eternity I’ll always love you...................” ..BAYAN SHEKARU GOMA!.. Abubuwa da dama sun faru.. An samu cigaba k’ari d’aukaka da farin ciki sannan an samu rashi na rasuwar Gramma Kaka da K’asimu. Shekara biyu Mom ta yi a wajen Innaa, da kyar da fad’a da lallashi da shawarwari aka samu Daddy ya amince ta komo amman fa ya k’ara aure! Dan tana tafiya ko shekara ba a yi ba ya auri wata k’anwar Abokinsa y’ar gayuu Budurwa amman zata kai 35 years Ana kiranta da ‘Kaulat’. Tabbas sai da Mom ta yi da gaske tukunna ta yi kokawa da zuciyarta dan Kaulat ta fita ta ko wacce hanya Kyau! Ilimi! Aji! Kud’i! Gata!! Sannan sai take gani kamar ma Daddyn ya fi son Kaulat d’in a kanta. Amman kuma da ta yi hak’uri bata yi komai ba sai abun ya zo mata da sauk’i dan Kaulat sam babu ruwan ta a waye take sosai kowa nata ne shiyasa ana aurota ma ta siye zuciyar kowa a cikin estate d’in. Mammy kuwa hukuncin life inprisonment aka yanke mata na kisan Ummi dan k’iri k’iri Mommy ta kafa ta tsare tak’i yarda a yi shari’ar case d’inta da Mammy. Mammy ta yi nadama a gaske a prison… Sukan je su ganta dan ba a chanjawa tuwo suna she’s still part of the family. Banda sauk’a da haddar Alqurani, nafila da neman yafiyar Ubangiji ba abunda ta saka a gaba..... Yanayin karatun su Huda wanda Aslam ya tsara akan za su yi a Cairo hakan bai faru ba saboda Mama da Daddy cewa suka yi ‘Huda ta yi BUK tunda a kano Aslam yake Sakina kuma ta yi gwagwalada.’ Mazajen nasu sam! Basu so hakan ba amman ba yadda suka iya haka nan suka amince domin sun san duk abunda babba ya hango Yaro ba zai iya hangowa ba. Cikin sa a suka fara karatun nasu Allah ya taimake su ba a samu strike da delay ba ko sau d’aya har suka kammala karatunsu da first class ba tare da sun samu delay ko tangarda ba. Hudan ta zab’i fannin Paediatric Sakina kuma Gynecologists. Suna kammala karatunsu suka tafi course na k’aro Ilimin sani a fannukansu na shekara bibbuyu a UK. A lokacin both Aslam da Auwal kowa ya bud’e sabbin company d’insa a chan uk d’in dan haka kusan tare suka tafi da mazajensu da ‘ya’yan su har suka kammala! Sai a wannan lokacin ne kuma Arshaad ya yanke shawarar dawowa gida tare da Amaryarsa mai suna ‘Jahad’ y’ar k’asar Saudi Arabiya wadda ya aura last year! Kaff familyn MT babu wanda bai je bikin Arshaad ba har su Ummu, tun a lokacin suka so ya koma gida yak’i yanzu kuma shi da kanshi ya yanke shawarar komawa gida dan he’s pretty sure baya yiwa Huda zazzafar soyayyar da yake yi mata a baya. A ranar da suka dawo Huda da Sakina suka tarar da babbar kyauta daga Granpa wanda ya bud’e musu tangamemen asibiti mai hawa wajen biyar! Ya basu ya ce “su zab’i suna su saka” Da farko sunan Madu suka so su saka amman sai Mama da Ummu suka basu shawarar su saka ‘Mai Turare’ A ranar Granpa ya had’a walimar welcoming Arshaad da Amaryarsa Bud’ewar Asibitin su Huda da kuma saka ranar Sumayya da Shuraim wadda Sumayya ta amince da auren da kyar! Bawai don bata son Shuraim ba sai dan ita a ganinta bai kamata ta auri age mate d’in ta ba...... ......Yau da kanta take so ta je ta d’auko Yaran saboda tana son zuwa wajen Jalila da su, duk da cikin wajen wata bakwai d’in dake a jikinta hakan bai hanata driving da kanta ba. Tunda wuri dama ta kira driver ta ce masa ‘kar ya je, da kanta zata je ta kwaso su’. Tana zuwa tun a bakin gate mai gadin da ya bud’e mata ya ce “ta je da wurwuri office d’in principal yana ta fad’a! Tun d’azu ake kiran layin office d’insu ita da Maman Arshaad amma duk su biyun basa d’auka.” Da sauri ta k’arasa office d’in, tana shiga ta sauk’e ajiyar zuciya ta girgiza kanta a ranta ta ce “Dama na sani” Tana k’arasawa ta kamo kunnen Arshaad ta jaaa da k’arfi ta d’aga shi ya mik’e cikin fushi ta ce “yau ma ko? Wai mai yasa baka jin magana ne?” Da sauri principal d’in ya ce “Mrs Aslam This boy must leave this school gaskiya! We can’t tolerate him anymore!! Wallahi saboda share d’in Dad d’insa a makarantar nan ne yasa muka barshi amman yanzu kam mun gama yanke shawarar sallamarshi. Zamu fitar wa da Dad d’in nasa share d’insa idan yak’i amincewa.” Hudan na shirin fara lallab’asa principal d’in ya katseta ta hanyar cewa “Mun rigafa mun gama magana! Saboda Allah ko malamai bama bari su daki Yaro saboda iyaye basa so amman bamu huta da case ba kullum duk akan Arshaad. Fad’a da zuciyar shi yayi yawa gaskiya.” Ajiyar zuciya Hudan ta sauk’e sannan ta cikawa Arshaad wanda yake ta faman kumbure kumbure kunne ta mik’awa Anum key d’in motar ta ce “Na san ya girmeku amman kun fishi hankali! Gashi ke da A’ish Ku ja Yaran ku je ku jirani a mota gani nan zuwa.” Har suka fice yana nan a tsaye bai motsa ba dan haka ta daka mishi tsawa ta ce “Bisu kaima ka je ka jirani! Saura kuma idan na fito in ji sabon labari”. Yana fita ta nemi guri ta zauna.. Da kyar da sid’in goshi ta lallab’a principal d’in, dan zuciyarshi ta zo wuya game da lamarin Muhammad Arshaad.... Wani abun mamakin tana fita ta tarar da wani sabon damben! Ko ba a fad’a mata ba ta san waye.. Tun kafin ta k’arasa ta hangoshi akan ruwan cikin wani almajiri yanata kimarshi d’ayan almajirin kuma yana kanshi yana dukan shi amman ko a jikin sa. Da kyar da taimakon wasu samari aka janyeshi daga kan almajirin da ya danne dan shi d’ayan almajirin yana hangota ya matsa gefe. Sosai kuwa ya yiwa almajirin jina jina dan dama a fusace ya ke su kuma suka tab’osa. Sai da ta d’an duddubashi ta ga ba wata matsala tukunna ta basu kud’i ta had’asu da samarin da suka raba damben ta ce ‘su taimaka su kaisu chemist tana da Yara k’ananu a mota’ daga nan ta basu hak’uri ta ce “su bisu su tafi chemist aje ayi masa dressing.” Daga nan Arshaad ya shiga motar ta ja suka wuce daman su Anum ana fara fad’an suka tura su Abbakar suka hana su fita suka rufe motar ba wanda ya fito a cikin su balle a had’a da shi. Gidan Jalilan da bata je ba kenan, haka ta kama hanyar estate da su tana mamakin Arshaad, chan wani murmushi ya sub’uce mata a hankali ta girgiza kanta a ranta ta ce “Sai dai ba d’an Sakina da Auwal ba”. K’ala! Ba ta ce mishi ba. Driving d’inta kawai take yi dan a mugun takure take jinta. Tun da Yaron ya ga an zo gidansu ta lura da yadda yad’an tsorata, aikuwa tana gama parking a compound jikinshi ya fara karkarwa ya ce “Ummi dan Allah kar ki gayawa Ammi komai.” Ko kallonshi Huda bata yi ba ta ce “Ai naga ni ka rainani! Jiyan nan ka gama yi min alk’awari amman fad’a har biyu yau kad’ai? Haba Arshaad!” Shiruu ta yi kamar mai tunanin wani abu kafin ta ce “Ka san wani abu?” Bata jira ya Bata amsa ba ta ce “Na ma daina kiran ka da ‘Arshaad’ daga yau dan baka yi halin mai sunan ka ba wallahi, dan haka chanja maka suna zan yi In maidaka mai sunan me gadi! za ka sha mamaki.” Takaici da zafin zuciya dan har yanzu fushi yake da waenda sukai fad’a yau bai gama hucewa ba yasa ya fashe da kuka. Dai dai nan Auwal Aslam da Arshaad suka shigo compound d’in suna hira suna raha da dariya… Arshaad, yad’an yi k’iba kad’an Auwal kuma ya tara k’asumba da gemu kamu d’aya Aslam kam ba abunda ya k’ara ba abunda ya rage. Tun kafin su k’araso Yaron ya tafi wajen Arshaad da gudu ya fad’a jikinshi ya ce “Uncle kaga wai Ummi za ta maidani mai sunan me gadi!” Sai da sukayi dariya k’asa k’asa tukunna Arshaad d’in ya d’an b’ata rai ya d’auke shi ya ce “Eh to… Ni na bata shawara saboda naga ka cika fad’a sosai.” Ai kuwa nan ya rikice da kuka. Dariya kawai Aslam da Auwal suka yi sukai gaba suka barsu. Sai da Aslam ya k’arasa wajen Huda ya d’an shafa fuskarta da tirtsetsen cikin ta tukun ya ce “Baki je wajen Jalilan ba kenan” Sai da tad’an kalli Arshaad da takwaranshi tukunna ta ce Abhu, Gaskiya ya kamata yau a saka Yaron nan a gaba a yi mishi fad’a sosai wallahi, saboda shi na dawo, dambe har da almajirai a waje sabida Allah.” A hankali Auwal wanda ya d’auka mai sunan Dad ya ce “Mu je ciki yau inga har duka sai ya sha” Ya fad’i hakan yana mai wucewa ciki. Dariya Aslam ya yi ya ce “Kiga yadda yake wani had’e rai kamar ba a wajen shi ya gado ba” “Um um fa! Yarintar shi kad’ai ka gani baka san na mamansa ba” Hudan ta bashi amsa. Murmushi duk suka yi Huda ta wuce shi kuma ya juya wajen su A’ish waenda suka gama kwasar lunch box da jakankunan su. Murmushi ya yi ya d’aga A’ish sama ya ce “Mamana ya school ke ba kya fad’a ai ko?” Sai kuma da sauri ya sauk’eta ya d’auki Anum yana cewa “sorry kakata yi hak’uri na manta na yi alk’awarin yau ke zan fara kulawa.” Da d’an k’arfi Huda ta ce Kar ki yarda ya yi miki dad’in baki” Tana mai wucewa bayan ta kamo hannun Abbakar k’anin su Arshaad wanda yake a kindergarten suka shige ciki… Sakina taso ta yi mishi shegen duka bayan ta gama jin bayanin abunda ya yi yau dan ta zo wuya da halinshi amman sai Aslam ya jata gefe ya yi mata Nasiha.. Nutsatsen fad’a sosai suka taru suka yi mishi dan har Jihad Arshaad ya kira ta zo itama saboda Yaron yad’an shak’u da ita itama dan tun yana zuwa hutu wajen Arshaad a Uk suke video call da ita, lokacin da su Sakina suka tafi course d’insu kuma a gidansa ma ya zauna gaba d’aya ko da yayi aurenma tare suke har lokacin da suka dawo Nigeria tukun ya gudu gidan su Huda dan sam baya san zama waje d’aya da Ammi saboda ya san zai yi laifi itakuma zata dake shi ta yi fushi da shi duk da yanayin rigimarshi amman yana tsananin k’aunar iyayenshi shiyasa baya son yaga tana fushi da shi. Sannan baya son fad’a da duka. Haka nan suka had’u su shidda! Da turanci da Hausa da larabci duk aka yi mishi fad’an. Kuma da alamu fad’an ya shige shi sosai. Tun daga ranar an d’an samu ya nutsu amman ba a yi cikakken wata d’aya ba ya koma ruwa dan haka kawai suka bishi da addua..... Sai da bikin su Shuraim da Sumayya ya rage saura sati tukunna Aaima suka zo dan a Abuja itama take tun aurenta. Ya’yanta uku biyu maza Farouk da Bashir sai auta Aisha. Tun aurensu har kawo yanzu cikin kwanciyar hankali suke sai dai y’ar rigimar Mata da Miji wanda wannan normal ne a ko wanne aure. .... Sai da Ya Ja’afar ya yi shekara biyar tukunna aka samu ya dawo dai dai, idan ka ganshi yanzu ya nutsu sosai kamar ba shi ba. Yana fitowa Junaidu ya bashi jari aka nema mishi mata ya yi aure shima y’ar bazawarar da Baba ya aura y’ar garin Katsina dutsanma bafulatana. Umma har yau tana nan jiya i yau! A nan gidan Baba da Junaidu ya rushe ya sayi filin bayansu ya had’e ya yi musu ginin zamani take itama amman b’angarenta daban ita da masu aikin da Junaidu ya d’auko suke kula da ita. Wani lokacin Huda idan ta je dubata har kuka take yi saboda Umma ta zama abun tausayi. Duk k’asar da take ji da kwararrun likitoci Junaidu sai da ya kaita…an yi maganin Hausa da turanci amman har yau babu ci gaba sai ma abun da ya k’aru dan wasu lokutan har duka take yi. Anty Zainab itama bata koma gidan Mijinta ba! Ganin tana zaune haka ba wanda ya fito mata yasa itama Junaidun ya bata nata jarin suke zaune ita da Baaba Talatu a gidan Kaka wanda nan ma ya gyara musu sosai. Idan ka ga Jalila ba zaka ce ta tab’a yin rashin ji ba! Ta nutsu sosai. Bayan aurenta sai da ta yi sauk’a yanzu haka a islamiyyar da Mijinta ya bud’e take koyarwa. Ta rungumi Mama a matsayin Uwa Sakina da Huda da Sumayya kuma a matsayin y’an uwa sannan ta rik’e Mijinta wanda ta fahimci shine gatanta kuma shine masoyinta na gaskiya. Tabbas Jalila tana cikin matan da za ace sun yi sa’ar samun Miji mai tsananin k’auna da tausayinsu tsakani da Allah. Wani lokacin har ce mishi take yi ‘ya k’ara aure’ saboda duba da a yanda ya sameta ita! Amman duk sanda ta yi mishi wannan zancen sai taga fushinshi a cewarshi ‘shi ita yake so ba wani abun ba kuma ya tabbatar ba zai tab’a iya had’ata da wata y’a mace a zuciyarshi ba.’ Ibraheem irin mazan nan ne masu zuciya Mahaifiyarsa ta rasu itama two years back k’anwarsa ma ta dad’e da yin aure. Dukda Ubangiji ya rubuta mishi rayuwar middle class zai yi hakan bai hanashi siya mata y’ar k’aramar mota ta mata ba! Sannan ya tashi daga gidan Junaidu ya yi gidansa Ita ma kuma tana business d’in kaya daga India Dubai wanda Junaidu ne yake kawomata duk zuwanshi, itanma kuma ta tab’a zuwa sau d’aya da kanta ta je ta sari kayan ta dawo bayan Hajji da Umara da Junaidun ya biya musu suka je ita da Mijinta tun farko farkon aurensu. Ya’yan ta biyu mace da Namiji, ta farkon sunanta Maryam mai sunan Huda tana ce mata didi na biyun kuma mai sunan Kaka, Bashir. Sai kuma tsohon cikin jikinta maybe su haihu tare da Huda ko kuma Huda ta rigata. Tsakaninta da Aaima akwai zaman lafiya da friendship da mutantanta juna ga zumunci...... Tunda aka fara bikin su Sumayya Hudan take nak’uda sama sama.. Sanin da ta yi lokacin haihuwar ta bai yi ba yasa kawai ta yi shiru a tunaninta juyi ne! Sai dai ranar da za a kawo Amarya jikinta ya motsa sosai! Dama Sakina ta fahimceta tun jiya dan haka ta yi rushing nata zuwa asibiti ba tare da ta gayawa Aslam ba dan ya ce ‘ba a nan yake so ta haihu ba, tunnda haihuwa ta uku tana zuwa da complications gara ya fita da ita waje’. Kuma ta san in dai ya ji Huda tana nak’uda ne amman ta yi shiru to zai ji haushi sosai. Tun kafin su k’arasa asibitin faya ta fashe, ko minti talatin baayi da shigar da itaba ta haifo y’ay’anta biyu kyawawa maza masu kama da Aslam sak..... Sai after one week tukunna Granpa ya had’a walima iya family kawai na welcoming Sumayya da twins waenda suka ci sunan Arshaad da Auwal (Abhi da dada). Takanas Granpa ya aikawa su Shuwa nasu invitation d’in. A compound d’in tsakar gidanshi aka yi decoration manya manyan dining table masu seat 20 guda biyu aka k’awata D’aya na manya d’ayan kuma na Yara jikokin gidan. Wajen 5:00pm kowa ya hallara, tun rasuwar Kaka Granpa ya zama shine Abokin Madu, shiri suke yi sosai….Allah ya arawa Granpa tsahon rai tubarkallah, sai dai fa ya tsufa sosai dan baya ma iya takawa a kan wheelchair yake. Haka aka fara gabatar da walimar bayan Madu ya bud’e taro da addua. In ka gansu kowa cikin farin ciki da walwala da annashuwa Mama na zaune kusa da Abba Mom da Anty Kaulat sun saka Daddy a tsakiya Mommy a kusa da Dad Hudan kusa da Aslam sun d’au twins d’insu a hannu Arshaad da Jihad Sakina da Auwal Aaima da Junaidu sai Jalila da Mijinta. D’ayan dinning d’in kuma Yaran ne tun daga kan Arshaad har kan Abbakar Saddik. Ana gama cin abincin Granpa ya yi gyaran murya ya ce “Hudan Maryam Aisha inaso in sake baku hak’uri” Da sauri Madu ya ce “Dan Allah ka yi shiru. Yanzu haka kana ganin akwai grudges? Komai ya wuce, mu yafi juna Allah ya yafe maana.” A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya yana kallonsu Mama one by one… Cikin had’in baki Mama da Mommy suka ce “Granpa iyaye basa laifi a wajen y’ay’ansu, komai ya wuce.” A hankali Huda itama ta ce “Mune za mu nemi yafiya da albarkar ka. Komai ya wuce ka manta komai kamar bai faru ba! Ka sanya mana albarka dan mu samu haske a rayuwarmu.” Ajiyar zuciya Granpa ya sauk’e sannan ya russunar da kanshi k’arasa yana jin yadda hawaye suka fara taruwa a tsofaffin idanuwanshi da suka ga jiya suka ga yau. Cikin zolaya Madu ya ce “Stop being emotional mana old man!” Da sauri Granpa ya d’ago ya ce “Ai ka fini tsufa!” Dariya aka saka saboda ansan dama sun saba, duk cikin su biyun ba wanda yake so d’an uwanshi ya ce mishi tsoho! Watarana ma Granpa cewa yake yi Madu ya girmeshi kuma ya tubure! Dole a hak’ura a tafi akan an yarda Madun ya girmeshi……. A hankali Huda da Mama suke kallon family d’in nasu.. Tun daga kan tebur d’in su har na su Arshaad kowa kawai dariya da farin ciki yake yi. A tare Mama da Huda suka share kwallar farin cikin da ta zubo musu ba tare da kowa ya gani ba sannan a tare a hankali suka ce “ALHAMDULILLAH!”. Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!… Na godewa Allah da ya bani ikon kammala littafina mai suna ‘So da Buri’. Kuskuren da na yi a ciki Allah Ubangiji ka yafemin, darussan da suke a ciki kuma Ubangiji kasa mu amfana. *Godiya ta musamman tare da fatan alkhairi ga Anty Aisha Gadanya, Ina godiya kwarai Anty, alkhairin Allah ya Isar miki a duk inda kike* *jinjina tare da godiya ta musamman ga y’an group d’in So da Buri da H B’s palace masoyana bani da bakin gode muku sai dai Addu'a wallahi, na gode na gode sosai Allah bar zuminci ya kuma kare min ku kullum da koda yaushe na gode sosai* *Godiya tare da fatan alkahairi ga duk wani member na Mikiya Writers Association, Ina godiya kwarai sisters Allah ya barmu tare ya ci gaba da kare min ku* Taku har kullum Humaira Bulama. ............