So da Buri Free Book 36 Kamar yadda Arshaad ya fad’a, mintuna ashirin d’in bama su cika ba! Ya gama abunda zai yi… Ya sa komai a sai ti sannan ya kira Granpa da landline d’in wajen ya sanar dashi ya gama, komai yayi normal. Daga nan ya nufi hanyar office d’inshi cikin d’an sauri saboda very important magana suke yi shi da Aslam kafin Granpa ya kirashi ya sakashi aikin. Tun kafin ya k’arasa ya hango k’ofar office d’in nashi kamar a bud’e! Yana suwa kuwa ya gasgata hakan sakamokon ganinta da yayi a wangale sosai.. Da mamaki ya kutsa kai ya shige ciki… Tun bai gama shiga ba ya fahimci babu Aslam babu alamar shi a cikin office d’in. A hankali ya sanya hannu ya rufe k’ofar office d’in yana mamakin abubuwa guda biyu ‘Tafiyar da Aslam yayi bayan ya san maganar da suke yi mai mahimmanci ce!’ Da kuma ‘yadda yazo ya samu k’ofar office d’in nashi a wangale’ Could it be Aslam d’in ne ya fita a rikice? Ko kuma dai bayan ya fitan ne wani ya shigo mishi office May be Auwal? No it can’t be!!….. Duk shi kad’ai yake ta sak’e sak’en shi a cikin ranshi. Ganin babu inda waennan tunane tunanen zasu kaishi ne ya sanya kawai ya yanke shawarar ‘gara ya kira Aslam d’in! Ya ji ko lafiya’. Shafa aljihun shi yayi da niyyar d’aukar wayarshi yaji wayam Yasan daman da guda d’aya ya fito d’ayar kuma tana gida bai ma fito da ita ba! To ko dai ya jefar ne a inda ya baro… Har zai juya ya fita dan yaje ya dubo wayar sai ya hangota a kan table d’inshi a ajjiye. Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya k’arasa yasa hannu ya d’auka da niyyar kiran Aslam.. Sai dai kuma bai kai ga bud’e wayar ba idanunsa suka ci karo da notification Barr dinsa wanda yake nan cike da tarin misscalls d’in Huda! A firgice yad’an zaro ido yana kallon wayar.. Whatever it is da ya sanyata ta jero mishi wanann tarin misscalls haka ya san its very serious and important!! Idanuwansa ne suka sauk’a akan message d’inta…dan haka cikin k’aguwa ya hau karantawa......... Tsayawa yayi cak!!! Kamar wanda aka dannawa pause. Dan ko numfashi kasa ja yayi.. A hankali ya lunmshe idanuwanshi… Da kyar ya samu yace “Ya subahanallah!!” Sannan ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya ya bud’e idanuwanshi da har sun kad’a sunyi jaaaa!. Wani abu ne yaji ya toshe mishi mak’oshi! Da kyar ya samu ya had’iye ya ja numfashi ya fesar da mugun k’arfi!. Yana nan tsaye rik’e da wayar a setin fuskarshi har yanzun ya kasa gota ta…. A hankali kamar mai jin tsoro ya shiga Call log ya danna kiran Aslam… Ya kirashi yafi sau biyar amman bai d’auka ba saboda a lokacin ba abunda yake da buri kamar ya gansu a asibiti! Ko ya samu ya daina jin kukan Huda wadda ta kasa yin shiru, sannan a samu a duba Anty Maryam a ga lafiyar ta! Shiyasa in banda gudu ba abunda yake tsulawa kamar shi kad’ai ne a akan titin Tunda ya samu suka yi waya da Abba yace mishi ‘gashi nan zuwa’. A hankali Arshaad ya zare wayar daga kunnenshi ya yi scrolling zuwa sunan Huda ya danna ya kara a kunnenshi… Sai da ta kusan katsewa tukunna ta iya d’auka tace “Hello Ya Arshaad” Kana ji ka san kuka take yi. A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya yace “Kina ina?” Cikin kukan tace “Ga Ya Aslam d’innan ya zo, muna hanya zamu kaita akth yanzu. Na gode sosai.” Ta fad’i hakan, ita duk a tunaninta shine ya turo Aslam saboda maybe ko shi d’in yana wani abun important ne. A hankali yace “Umm! Mu had’u a chan.” Daga nan ya yanke kiran. Mukullin motarshi kawai ya d’auka ya fice a office d’in! Yana zuwa ya shiga ya kunnata ya bata wuta ya fice ya nufi asibitin..... A mota Aslam yace “ta jira” Shi ya shiga, ya fito, da nurse guda biyu da gado aka d’aura Maman a kai suka shige ciki. Sai da ya tsaya aka yi komai tukunna ya cewa “Huda tazo taje ta zauna” Sai da ya tabbatar ta zauna sannan a hankali ya d’an durk’usa ya shiga lallashinta! Da kyar ta samu ta d’an yi shiru….Yana matsawa a wajen taci gaba da kukanta a hankali tana share hawaye…. Bayan rashin lafiyar Mama har da abunda Hajiya Shuwa tayi d’azu ya daki zuciyarta ya b’ata mata rai kwarai!! Bata tab’a jin zafin kalar abubuwan da Hajiya Shuwa take yi musu kamar irin na yau ba! A hankali Aslam wanda yake ta faman k’ok’arin ganin bai sake kallon direction d’inta ba Ya d’aura idanuwanshi a kanta yana kallonta… Ji yake kamar ya sake komawa yaje ya lallasheta tayi shiru! Har ga Allah kuka yana d’aga mishi hankali. Nurse d’in data taimaka aka shigo da Maman ce tazo zata wuce ta kusa dashi Har ta d’anyi gaba sai kuma ta dawo tace masa “Kaje ka zauna ka lallashi matar taka mana! Ka barta ita kad’ai chan gefe sai faman kuka take yi. Kaje wajenta mana.” Tana gama fad’in haka ta juya ta wuce a bunta. A hankali ya lumshe idanuwanshi a ranshi yace “Why am i too nice to her, yau?” Wata zuciyar ce tace mishi “Saboda Mamanta bata da lafiya mana.” A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya yana mai raya wa a ranshi ‘yadda yayi da yadda ya nuna tsananin damuwarshi! Tabbas kowa ya gani zai yi tunanin ita d’in matarsa ce’ A hankali ya sake lumshe idanuwanshi yace “damn it!” A chan k’asan mak’oshi!. Cikin k’ok’arin son kawar da wani tunanin na daban ya fara k’are mata kallo yana mamakin kamannin ta da Abba! Gata kuma y’ar gidan Anty Maryam! Ko shekaran jiya ma sai da ya ga hoton Anty Maryam wanda suka d’auka ita da shi da Abba da Dad da Mommy lokacin a Saudiyya! Ko da ace ma bashi da hoton ta tabbas fuskar Anty Maryam ba zata tab’a b’ace mishi ba… Sauk’e Ajiyar zuciya yayi, a k’asan ranshi yana zullumin k’arasowar Abba! Tabbas lissafinshi dai dai yake bashi! Bashi da tantama.......... Sai da ya sha d’an k’aramin yak’i! Da security d’in bakin k’ofar shiga emergency d’in tukunna da kyar!! Ya barshi ya shiga. Yana shiga hankalinshi da idanuwanshi suka kai kan Aslam wanda yake a tsaye ya k’urawa Huda wadda take zaune tanata faman kuka, ido! Da sauri ya k’arasa inda yake.. Sam Aslam bai lura da shi ba har sai da ya dafa shi, tukunnan yayi firgigit ya juyo yana kallonshi.. Maimakon yace wani abun kawai sai Arshaad yaga ya k’ura mishi ido kamar wanda yake son hango wani abu, har sai da ya d’an tsargu! Kusan 2 minutes Aslam ya d’auka yana kallon Arshaad Wanda hakan ya sanya duk wani rikicin da yake ciki hauhawa jikinshi kuma yayi sanyi lokaci guda dan bai san me ya sanya Aslam d’in yi mishi irin wannan kallon k’urillar ba!. Kamar daga sama yaji muryarshi yana cewa “Ka tab’a ganin Mahaifiyar Huda??” Da mamaki Arshaad d’in yake kallonsa kafin yace “Ba sau d’aya ba!.” Shiruu, Aslam d’in yayi sai kuma ya runtse idanunsa da k’arfi kafin ya bud’e yace “How old is she? Hudan?” “Close to 18” ya bashi amsa ba tare da ya fahimci inda tambayoyinshi suka dosa ba. “Kwanaki kace min a gidan Mijin Mamanta take, and ba suyi maka maganar Dad d’inta ba ko?” Cewar Aslam. “Aslam what are u getting out of this ne wai??” Arshaad yayi mishi tambayar. Da d’an fad’a yace mishi “Just answer me!!” Shiruuu, yad’an yi sai kuma yace “Tun farko…da na fara zuwa gidansu ta ce mini ‘Basu ma da number d’insa’ (her Dad) Uncle d’inta kuma yace “families d’inne suka samu matsala shiyasa but ana hoping resolving in shaa Allah.” Aslam, Tafin hannayensa duka biyun aslam ya saka yayi cupping iya daidai hancinshi da bakinshi ya fitar da wani Hucin da sai da na kusa dashi ya juyo yana kallonshi! Tukunna ya cire hannun ya dafa Arshaad kanshi tsaye yace “Hudan is our sister!! Daughter d’in Abba ce, bani da tantanma.” Da kyar Arshaad ya daidaita kanshi daga shock d’in daya shiga, kafin yace “How???” Aslam ya bud’e baki da niyyar bashi amsa kenan! Ya hango shigowar Abba!. Kusan a tare suka ga juna don shima Abban yana shigowa idanunsa suka sauk’a akan Aslam d’in. Da sauri ya k’araso yana cewa “Aslam mai ya faru? kace In baro komai in zo asibiti emergency, duk na rikice, waye ba lafiy........” Maganarshice ta mak’ale sakamokon idanuwanshi da suka sauk’a akan Hudan wadda taketa faman kuka har yanzu….. Shi dai Abba bai san ya akayi ba dan kawai tsintar kanshi yayi a gabanta a tsaye! Ana cewa yana kama da su Aslam da Yaya amman tunda yake bai tab’a ganin kamanninshi da wani mahaluk’i kamar na wannan matashiyar budurwar ba! Dukda fuskarta a yanayin kuka take hakan bai b’oye tsananin kamannin da suke yi da juna ba! Ita kam Huda yanayin tashin hankalin da take ciki ne bai bata daman fahimtar kallon fuskar mutumin ba, amman tabbas tun lokacin da yazo gabanta ya tsaya taji wani bak’on al’amari ya shige ta! Tsintar kanta tayi da mik’ewa tana goge hawayen ta sannan ta shiga gaidashi……. Aslam bai bashi damar amsawa ba yace “ya biyo shi, yana so zai nuna mishi Mahaifiyar Yarinyar daga nan sai ya yanke hukunci da kanshi.” Haka nan kawai Abba ya bi bayan Aslam kamar rak’umi da akala! Bayan aslam d’in ya cewa Huda itama ta biyosu! Arshadd ka bashi da wani zab’in da ya wuce ya bisu. A haka suka d’unguma Inda aka kwantar da Mama ake duba ta…suka tsaya suna jiran fitowar Doctor! Kusan wajen 29 minutes ba wanda yace komai kowa ka gani da abunda yake yawo a kanshi… Suna a haka Doctor ya fito! Kallonsu yayi one by one kafin ya k’arasa inda Aslam yake tukunna ya fara magana “Alhamdulillah An ci sa a ta farfad’o! Za ku iya shiga ku ganta amman dan Allah kar kuyi hayaniya kuma kuyi k’ok’arin kwantar mata da hankali saboda jininta ba k’aramin hawa yayi ba!.” Yana gama fad’an haka ya mik’awa Hudan takardun hannunshi ya wuce. Abba bai san daliliba bai kuma san wacece a kwance a d’akin ba, amman yadda zuciyarshi take bugawa da kuma kalar karkarwa da jikinshi ya d’auka lokaci guda ne ya sake d’aure mishi kai! Dan tabbas ya san in da ace za a auna jininshi a yanzu To da za aga yafi na mara lafiyar da ake cewa su taru sun kwantarwa da hankali hawa… Muryar Aslam ce ta katse mishi tunani jin yana cewa “Muje Abba. Bismillah.” D’aga kai kawai yayi alamar ‘to’ sannan ya nufi inda yaga su Hudan da Arshaad sun shiga, Aslam ya mara mishi baya…. ...Shekaru goma sha takwas rabon shi da ita, amman ba a yanayin rashin lafiya ba ko a garin makafi idan ya had’u da Maryam ya shafa yaji to sai ya gane ta! Lokaci guda yayi baya luu!! Ba daban Aslam yayi saurin taro shi ba tabbas da sai ya zube a k’asa! A b’angaren Mama kuwa! Da farko da ya shigo ta ganshi ta d’auka gizo yake yi mata, sai da taga har Aslam ya taro shi yana cewa “Be careful” tukunna ta tabbatar da cewa shi d’in ne! “Mai ya kawo shi? Me yake nema? Me zai ce mata?” Sune tambayoyin da suka taru suka had’e da al’ajabi suka fara k’ok’arin tarwatsa mata zuciya! Da kyar ta k’ok’arta ta tashi ta zauna sai kuma ta fara k’ok’arin tsayuwa. Da kyar ya iya dedeta kanshi sannan ya sake sauk’e idanuwanshi a kanta… Babu abunda ta k’ara ko ta rage, tananan kamar yadda ya santa 18 years ago! fatarta ce kawai ta d’anyi duhu amma kyawunta da yanayin jikinta ba abunda ya ragu ko ya k’aru! “Astaghfirullah!!” Yayi saurin furta hakan, sakamokon tunawa da yayi ita d’in a yanzu mallakin wani ce! Sai kuma lokaci guda ya fara ganin duhu duhu sakamokon kishin da ya turnuk’e sa! Bai tashi dawowa dai dai ba sai da yaji Hudan da Arshaad suna tambayar ta “Ina zata je?” Ba tare da ta kalle su ba tace “Gida!!” Sannan ta sa hannu d’ayan hannunta ta cisge cannular k’arin ruwan da aka d’aura mata a d’ayan hannu nata, tayi hanyar fita (inda su Abba suke tsaye!). Da sauri ya tsaya a gabanta ya fara magana “M mm Maryam Doc ya c ce jji kin kk ki ba kwari kark.......” Mahaukacin Marin data d’auke sa da shi ne ya sanya hatta su Aslam sai da suka d’auke wuta na y’an sakanni! Cikin b’acin rai tace “That’s for Huda!! Na duk wani kuka da bak’in cikin da ta fuskanta ata dalilin hukunci daka yanke tun kafin rayuwarta ta soma!” Bana so ta san ka! Bana so taji komai!! Bana so ta san komai!!! Ba ma buk’atar ka!!!! na rok’eka da girman Allah ka bar nan tun kafin raina ya k’arasa baci!” Ta k’arashe maganar cikin b’acin rai da k’unar zuciya, wasu zafafan hawaye suna zubo mata. Idan lissafinshi ya bashi dai dai to maganganun Maryam suna nuni ne da irin kalaman da ya kamata a yiwa uban da ya gudu ya bar y’arsa…… Bai damu ba sam! Dan bata k’umbiya k’umbiyar magana yake ba a halin yanzu…shi daman ko da ace ya tambaya ance mishi Yarinyar ba y’arsa bace ba to fa ba zai tab’a yarda ba!! Ballantana kuma yanzu da maganganun Maryam suka sake tabbatar mishi da ‘y’ar’ tasu ce!. Hakan yasa ba tare da yabi takan Mama wadda Aslam yake ta rok’o ta koma a saka mata cannula tak’i ba! (Ta nace akan sai dai Abba ya fita ko kuma ita a tafi) Ya nufi inda y’arsa take tsaye! Yana zuwa bai yi wata wata ba kawai ya rungume ta sai kuma ya fashe da wani irin kuka kamar k’aramin Yaro. Ita dai Hudan zuwa yanzu ta koma mutum mutumi! Dan kwakwalwarta ta kasa aminta da amsar da kalaman Mama da kuma reaction d’in wannan bawan Allah suke bata. Shigowar Likita ce ya juyo da hankalin su gaba d’aya, dan hayaniyar su ta fara damun ragowan patients d’in da suke gefen su… Dukda inda suke an yankashi da girma sosai dan yayi biyun ragowar inda patients d’in suke amman dole in sunyi magana za a jisu kasancewar labulaye ne kawai ake sakawa a tsakani. Da mamaki yake kallon Mama a kan k’afafuwanta, sai kuma ya juya kan Aslam ya rufe shi da fad’a! Da kyar ya lallab’a Mama bayan tace “ba zata koma ta kwanta ba sai Abba ya fita” Shi kuma yace wa Abban “yayi excusing d’insu” Bayan ya fita, aka samu ta tsaya ya maida mata cannularta. Har zai fita yace musu “banda hayaniya!” sannan ya juya ya fita. Yana fita kuwa Abba ya dawo! Dan haka Mama ta sake mik’ewa.. This time around Aslam ne ya k’arasa inda take ya rik’e mayafin da take k’ok’arin yafawa ya fara magana “Mama dan Allah ki tsaya ki sauraremu, bafa ke kad’ai ya kamata ace ranki ya b’aci a lamarin nan ba, shi kanshi Abba yana da ikon yin fushi kawai dai daurewa yake yi dan yaga an zauna lafiya!! Amman na tabbatar ko kotu aka je to kinada laifin b’oye masa y’arsa da kika yi tsawon shekaru ba tare da ya ma san Akwai ta a duniyar ba! So i think its about time da ta kamata ki nutsu! Whatever it is that happen between you and Abba destiny d’inku ne, so don’t mix it up da issue na laifin ‘b’oye mishi y’a da kika yi’ kiyi putting blame d’in ankanshi, wannan laifin ki ne ba nashi ba! And if kika ci gaba da acting stubborn muma zamu biyo miki ta hanyar da baki tab’a tunani ba!” Da sauri Arshaad yace “haba Aslam wanne irin magana ne kake yi haka?? At least ai she is an elder watch your tongue mana!!!” Tabbas daman ko Arshaad bai fad’a ba Mama ta gane wannan Aslam ne, dan kamanninshi basu chanja ba kwata kwata, kenan Arshaad d’in shima realative d’insu ne maybe ma brother d’inshi ne dan gashi suna kama sosai!! Ta yiu Abba ne ya turo shi ko kuma me kenan hakan yake nufi? idonshi yana kansu all this time amman sai yanzu yaga ya dace ya nuna kanshi ko ya ne abun yake???? Gaba daya kan Mama ya d’aure tamau!!!......... Maganar da Aslam ya fara yi a fusace ne ya dawo da hankalinta wajen “Elders! elders!! elders!!! Shin duk meye ne farkon issue d’in nasu?” Bai jira jin amsar da Arshaad zai bashi ba yace “Biyewa son zuciyan elders d’in da akayi ne ai duk ya jawo haka!! Itanma kuma I’m pretty sure idan aka yi musu laga laga problems d’in da zata kawo ba kad’an baneba! Tun ranar da Granpa ya nunawa Abba video d’in d’aurin aurenta Abba yake fama da ciwon zuciya har yau d’innan!! Kuma all those years bai samu sauk’i a wajen kowa ba! Fama yake yi da rashin lafiyanshi ba wanda ya damu!! Sannan yanzu kuma itama zata b’ullo da nata issue d’in? Da wanne akeso Abban yaji da?” Ya yiwa Arshaad tambayar yana kallonshi.. Bai damu da jin amsa daga gareshiba dan daman ya san ba lalle ya samu ba, ya juya ya kalli Mama sannan yace “Ba zan d’agawa kowa k’afa ba! daga yau, ke ko Ummi, hatta Granpa!! Therefore I’m advising you to drop this attitude and stubbornness da kuma haushin Abba da kike ji, ki tsaya ku dedeta akan issue d’in Huda If not, wallahi kinji na rantse miki da kaina zan kaiki kotu!! Kuma sai inda k’arfina ya k’are!!! Dani za kiyi ba da Abba ba...” “Huda mik’o mini purse d’ina” Shine kawai abinda Mama tace ba tare da ta zare kwayar idanunta a cikin na Aslam wanda tunda ya fara magana suke kallon juna ba!. A hankali Hudan ta zare hannunta daga cikin na Abba sannan ta d’auko jakarta ta zaro y’ar k’aramar purse d’in Maman a ciki ta mik’a mata tace “Gashi” Hannu Mama wadda har yanzu take kallon Aslam ta mik’a ta amsa sannan ta d’auke idanunta daga kanshi ta sauk’e akan purse d’in ta zuge ta! Bayan wayarta ba komai a ciki sai chanjin naira talatin ashirin da biyar biyu. Zip d’in dake a gefe acikin purse d’in ta zuge sannan ta zira y’an yatsunta ta fara lalubawa.. Wasu takardu an ninkesu ninkin k’anana guda biyu ta zaro ba tare da ta rufe ba ta mik’awa Hudan purse d’in.. Ta farkon ta fara bud’ewa ganin ba ita take nema ba yasa ta mik’awa Hudan tace “ta ninke ta mayar mata ciki” Sannan ta fara k’ok’arin bud’e ta biyun… Hawayen da suka zubo mata ta sa hannu ta share bayan ta gama karantawa sannan ta cillawa Aslam a dede setin fuskar shi. Da sauri jin takardar tana shirin sauk’a k’asa yasa hannu ya cafe ta sannan ya d’ago ta ya fara karantawa… Mama bata jira ya k’arasa karantawan ba ta fara magana “Aslam za ka iya kaini kotu! amman ka sani ni ba zan biyeka inyi shariah da kai ba, nasan kun fi k’arfi na ta ko wacce siga, sai dai kuma ni kotun Allah zan kaiku! Nan ce k’arshe kuma shine zai bi mini hakkina! Dan ba zan yarda ku dake ni kuma ku hanani kuka ba!” Tana gama fad’in haka kuka ya kufce mata ba tare da ta shirya ba. Da mamaki Abba wanda ya k’araso ya karb’i takardar ya hau karantawa yake sake maimaitawa…. Shiruuuu, ya d’an yi sai kuma kawai ya ninke takardar ya sa a aljihun gaban rigarshi! Dan tabbas yau za a yita ta k’are a estate d’insu!! Ba zai yiu ace yana rubuta takardun da bai san lokacin da ya rubuta su ba! A daa yana kokwanto yanzu kam ya samu clue. Ajiyar zuciya ya sauk’e sannan ya k’araso gaban Mama yace “Maryam! na rantse da girman Allah ba nine na rubuta wannan takardar ba! Ban san da zamanta ba kuma ban san dalilinta da ranar data iso gareki ba!” Cikin kuka Mama tace “naji Abba baka san da takardar nan ba ita kuma Hudan laifin me tayi maka!? Ko sau d’aya fa baka tab’a lek’ota ba! Cinta shanta suturarta duk baka sansu ba! Idan ni nayi maka laifi ka datse igiyoyin aurenka a kaina ita kuma laifin me tayi maka daka kasa koda lek’o ta ne????” Kamar Abba zai yi kuka da ihu yace “Maryam, zabi aka bani ko in fita harkar ki for ever ko kuma ku k’are rayuwanku a jail ke da family d’inki har abada!!!Daman kuma an riga anyi agreement dani ke kin sani an yi agreement akan ‘duk ranar da wani naki ko ke kukaje inda yake dole akwai consequences !’ Duk da haka ban hak’ura ba Inata k’ok’ari da adduar in samu a gyara abun sai kawai naji d’aurin aurenki bagatatan!! Ya kikeso in yi??” “Nifa duk ba wannan nake son ji ba, tsakani na da kai it’s over! Ko ma menene ya faru ya riga ya wuce! Laifi yanzu da nake magana a kai ba ni ka yiwa ba! Y’ar ka ka yiwa, kuma ko ita ta yafe maka ni ba zan yafe in yarda ba!! Dan haka kawai ka juya ka tafi dan ban san me ka zo yi anan ba!.” Aslam wanda yake ji kamar zuciyarshi zata tarwatse ne yace “Wai sau nawa zai yi miki bayanin ‘bai san kin haihu ba’ Hatta shi kanshi Granpa d’in bai san kin haihu ba!! Kuma da kike ta cewa bai zo inda kike ba, was ita not you da kika yi ta aika mishi da threats kala kala ba?” Shigowar Doc ce ta katsewa Arshaad maganar da yake shirin yiwa Aslam akan attitude d’inshi towards Mama!! He’s is not like this kwata kwata, he wonders why yake yiwa Maman haka. Ba tare da Likitan yace “k’ala ba ya juya ya fita, ko minti d’aya bai yi ba ya dawo da takardar sallama ya bawa Aslam sannan yace “Kuje gida kuyi solving issue d’inku, dan har ga Allah kun hana marasa lafiya sukuni!! Ba sai kun rufe file ba, zaku iya tafiya kawai…” Yana gama fad’an haka ya kama hannun Mama ya cire mata cannular yana cewa “kuna gama cases d’inku ki tafi asibiti, dan ina jin tsoron jikin nan naki a haka!.” Yana fita Mama wadda daman abunda takeso kenan, ta yafa mayafinta, sannan ta cewa Huda “wuce mu tafi!” ………. Kasa sauk’e kafarta data d’aga da niyyar tafiya tayi jin Abba yana cewa “Babu inda Huda zata bii ki!!” Da mamaki ta juyo tana kallon Abba kafin tace “Ban gane ba!” “Babu inda zata je, tare da ke!!” Abban ya fad’a yana mai k’arasowa inda take sannan ya zuba mata idanuwanshi da ta kasa jurewa kalla tayi saurin yin k’asa da kanta. Cikin tattaro dukkan ragowar k’arfin jiki kuzari da jarumtar ta, ta zagayeshi taje inda Hudan take ta fara k’ok’arin kama hannunta amman kafin tayi hakan tuni Aslam ya juyo da sauri ya rigata, sannan ya tura Hudan bayansa, shi ya zamana yana a gaban Maman!! Da kyar ya iya bud’e idanuwanshi da ya runtse!! Tun lokacin da ya rik’e hannun Hudan ya zubasu a kan Mama! Cikin wata iriyar kasala data dirar masa lokaci guda yace “You have to pass through me first!” Arshaad kam zuwa yanzu ya zo wuya!!! Dan haka cikin fushi ya kalli Aslam d’in yace mishi “Let her go!!” “No” Yace ba tare da ya kalleshi ba! Sannan ya dakawa Hudan wadda take ta k’ok’arin kwace hannunta tana kuka tsawa “Ki nutsu!!”. Wani irin irin kuka Mama ta fashe da shi a take ta durk’ushe a wajen abin tausayi. Abba ne ya umarci Aslam da “Ya kai Hudan mota dan in dai yaci gaba da ganin Maryam a haka tou za a samu matsala!” Da sauri Arshaad yace “babu fa inda zata je ba tare da Mahaifiyarta ba!!! Haba Abba! Ka san kuwa shak’uwar dake a tsakanin y’a da uwa?? Ka san abubuwan da suka yi going through tare, lokaci d’aya kawai kazo kace zaka d’auketa haka nan? Why are you trying to be selfish???” Kallonshi Abban yayi da idanunsa da suka fara rinewa…. He‘s tired so tired of everything!! A yanzu yadda yake jin zuciyar shi tabbas idan ya tsaya kula Arshaad to zai iya yi mishi illa!! So yake yi kawai ya isa gida tare da Huda ya fuskanci kowa da komai! Masu laifi kuma ya hukuntasu dan bashi da tantamar cewa akwai waenda suka san da zaman Huda a dunyia a cikin estate d’in su… Apart from that ma inda ace ya san yanada y’a tun farko to da ko kwana d’aya ba zai barta tayi a gidan Usman ba which definitely ya san anan take da zama… Tabbas ya san bai kyautawa Maryam ba, but she’s not ready to listen!! Baya jin kuma zata yarda ta bashi Huda a cikin sauk’i! Shi kuma a halin yanzu ya kai peak!! Edge!!Limit!! Na tolerance… So yake kawai ya isa gida. Shiyasa cikin k’ok’arin danne zuciyar shi da yake ji tazo masa iya wuya!!! Ya cewa Aslam “Kai ta mota!! Idan tayi tirjiya ka d’auketa!” Yayi maganar ba tare da ya d’auke idanunsa da suka koma tamkar garwashin wuta daga kan Arshaad ba! Yace masa “Do your best ka lallashi Maryam sannan ka maidata gida.” Yana gama fad’an haka ya juya ya bi bayan su Aslam da Huda wadda ta bisa salin alin dan , gani tayi ana cewa ‘ya d’auketa’ ya durk’usa ya fara k’ok’arin ciccib’arta…. Amman fa kukan da take yi still tana k’ok’arin zame hannunta ana Aslam ya sanya gaba d’aya hankalin duk mutanen da suka wuce ta gabansu ya dawo kansu, da yawa tunanin su rasuwa aka yi mata, shiyasa ba wanda yayi k’ok’arin tsaidasu! Sai dai ‘Allah ya ji k’an rai’ kawai da wasu mutanen suka dinga cewa Wasu kuma kallon tausayi suka bisu dashi. Aslam yana isa bakin motar yaiyi mata key ya bud’e ya dannata a ciki ya rufe sannan ya zagaya mazaunin driver ya shiga ya bata wuta, ba tare da ya jira Abba ko Arshaad ba ya d’auki hanyar MT estate da ita........ Arshaad gaba d’aya ya tsorata da ganin yanayin Abba Dan tabbas bai tab’a ganinshi a irin wannan yanayin ba! Duk inda bacin rai ya kai b’acin rai to yau ya hango shi a kwayar idanun Abba! Shiyasa ya kasa tsaidashi. A hankali bayan fitar shi yaje inda Mama ke durk’ushe tanata faman kuka shima ya durk’usa gaba d’aya ranshi ba dad’i! A hankali yace “Mama dan Allah k.....” Kallon da ta d’ago tana yi mishi ne ya sa ya had’iye ragowar maganar sa! A hankali ta mik’e ta gyara mayafin jikinta sannan tace “Arshaad mai yasa kayi mana haka?” Da mamaki yake kallon ta kafin yace “Mama ni kuma mai nayi?” So da Buri Free Book 39 Da sauri Sakina tace “Mamaa” sai kuma ta k’arasa wajen da sauri ta hau tattab’a ta, ganin bata motsi yasa ta sa hannu ta juyo da ita! “Innalillahi wa innailaihirrajiun” Shine abinda Sakina Ummu da matar dake gefen Mama suka fad’a a tare, dan a yadda Sakina ta juyo da ita haka ta biyo hannun Sakinan ta taho yuuu ta zube wanwar kwanciyar rigingine. Ummu mutuwar tsaye tayi a wajen, so take ta k’arasa inda suke amman ta gagara sakamokon ganin y’ar uwartata da tayi kwance tamkar gawa! Ta kasa tab’uka komai banda hawaye ba abunda take yi. Sakina wadda ta rikice tanata tattab’a Maman ne ta juyo tace “Ummu ki zo ki kamata mu mik’ata emergency.. Mama ce amman bata numfashi.” Jin hakan ba k’aramin sake rikita Ummu yayi ba, ita dai kawai ta ganta a gabansu a tsaye amman bata san ya aka yi ta isa wajen ba. Matar nan ce ta matso itama ta hau jijjiga Mama tana cewa “kumafa yanzun nan muka gama magana da ita, tun jiya muke nan tare da ita. In banda kuka ba abunda take yi, nayi tambayar duniyar nan tak’i kulani… Sai dai kawai taje tayo alwala tazo tayi ta sallah. Sai d’azu ne da naga kamar batta lafiya nace ‘tazo muje in rakata taga Likita’, shine na samu ta d’an kulani ta inda take ce min ‘bara ta d’an yi bacci, idan ta farka sai muje’.” Ita dai Sakina cicib’arta ta fara k’ok’arin yi hakan yasa suma suka sa hannu suka taimaka mata suka yi waje da ita..... Su Madu suna tsaye a k’ofar shiga emergency.. Kana ganinsu ka san hankalinsu ba a jikinshi yake ba! Ga tsananin gajiyar da suke tare da ita Dan ma Allah ya taimaka Abokin Junaidu ne ya biya musu kud’in jirgi su kuma suka biyawa Baba Saboda yaga yanayin tsufansu gashi da ya kira Baban ma a hanya ya jisu suna dawowa daga wata tafiyar…. Ba dan haka ba da gajiyar ba zata yi musu da sauk’i ba. Suna tsaye suna tunanin abunyi next suka hango su Ummu d’auke da mata suna nufusu, sai da suka matso su sosai sannan suka gane Mama ce. Basu samu damar tambayar su ba dan da sauri mai gadin k’ofar ya wangale suka shige kawai dukkansu… Ana ganin su aka karb’esu bayan an kawo gado an d’aurata, aka tura ta ciki don yin bincike.. Ba a jima ba sosai, Dr ya fito! Likitan dai da ya karb’eta jiya shine, magana d’aya ce ya maimaita musu “hawa da jininta yayi over ne ya janyo komai..amman this time around har eco za suyi” Nan yake ce musu “ba yadda bai yi da ita jiya akan ta zauna ta shanye drip d’inta ba amma tak’i, ta biyewa wasu suka dinga hayaniya suna fad’a! Yayi yayi akan suyi shiru suka k’i, shiyasa shi kuma ya sallameta, so suma in sun san hayaniyar za suyi gara karma su shiga inda take, dan zai sake korar su ne!”. Yana gama fad’in haka ya nuna musu inda take sannan ya wuce........ Bayan kamar awa d’aya, Kaka da su Baba suka wuce aka bar Sakina da Ummu. Su Kaka na fita Hudan wadda take kiran Sakina a kai a kai ta kira, nan Sakina ta gaya mata “sun ganta suna tare ma yanzu haka” Sai a lokacin hankalinta yad’an kwanta. Nan itama Sakinan take tambayarta “tana Ina?” Hudan tace mata “tana wajen Gwaggon su Aslam, amman still Abba bai san tana gidan ba, dan a b’oye ma Arshaad ya kawo mata wayarta data bari a gidan Gramma, so in shaa Allah gobe da sassafe za ta san dabarar da zata yi ta gudo.” shiruu, Sakina tayi chan tace “ki bari mu yi magana da Ummu tukunna, kar ki yi komai, kinji?” Ummun ce tasa hannu ta karb’i wayar suka yi magana da Hudan ta d’an kwantar mata da hankali, kafin suka yi sallama. Da kyar suka samu bacci ya kwashesu wajen k’arfe 3 na dare. Da sassafe su Madu da Baaba Talatu suka zo kawo musu breakfast, har lokacin Mama bata farfad’o ba. Sama sama take jin hayaniyar su dan haka ta fara k’ok’arin bud’e idanunta. Sakina wadda take a kusa da ita ce ta lura dan haka ta maida gaba d’ayan hankalinta gareta, ganin Sakina ta k’ura mata ido ne ya sanya suma duk suka taso suka zagaye gadon suna tambayar “mai ya faru?” Basu ida tambaya ba Mama ta k’arasa bud’e idanunta… Tsantsar farin ciki ne ya baiyyana a fuskokinsu gaba d’ayansu, cikin murna suka hau furta “Alhamdulillah” suna tambayarta “ya jiki?”. Da kyar Baaba Talatu ta taimaka mata ta mik’e ta zauna.. Tana zama suka had’a ido da Ummu! Kawai sai ta fashe da kuka abun tausayi…… Duk shiru suka yi. Da kyar Madu ya samu ya k’araso inda take ya dafa ta sannan ya d’an fara bubbuga bayanta alamun lallashi. Farin ciki ne ya mamaye zuciyoyinsu gaba d’aya, duk sai suka hau murmushi Kaka har da y’a kwallarshi, ya sa hannu share ba tare daya bari kowa ya lura ba. Ita kanta Mama duk da yanayin da take ciki hakan sai da ya sanyata zubar da kwallar farin ciki, dan rabonta da Madu ya nuna kulawarshi a kanta kaman haka, yau yau shekaru ashirin da bakwai kenan!. Share hawayenta tayi sannan ta d’ago ta kalleshi, shima itan yake kallo, ba abinda ta hango a idanuwanshi sai tsantsar tausayinta, bakinta na rawa cikin kuka tace “Abba, ya raba ni da Huda! Dan Allah ku karb’o min ita, wallahi mutuwa zan yi in ba y’ata, na shak’u da ita sosai, ba zan iya yarda in bar mishi ita ba.” Da sauri Ummu ta k’araso ta rungumeta, sannan cikin tsananin tausayinta tace “Ki yi hak’uri ki huta, munji komai, in kika warke sai a san abun yi, ki kwantar da hankalin ki dan Allah.” Cikin jujjuya kai Mama ta zare Ummu a jikinta kafin tace “Bilkisu ba zan iya yin hak’urin nan ba!! Abba ya zama wani irin mutum! Mugun mutun.. Shi ne fa ya turo Arshaad wajen Huda, Arshaad cousin d’inta ne! Suka dinga yaudarar mu, idanunsa akan mu yake all this time amman bai baiyyana kanshi ba sai yanzu? Saboda ko nace ba zata koma wajenshi ba ya san ai Arshaad zata aura, kenan ko? Wanne irin ubane zai yiwa y’arsa haka? Bilkisu gaba d’aya kaina ya kulle, a baya yace ‘baya buk’atar ta’, yanzu kuma yazo ya raba ni da ita a lokacin da nafi buk’atar ta, mai yasa zai yi haka? Laifin me na yiwa Abba da zafi haka??”. Ta k’arashe maganar tana mai fashewa da kuka. Lallashinta Kaka Baaba Talatu da Ummu suka hau yi, amman furr!! Tace “ba zata hak’ura ba! Ba zata iya yin hak’urin da suke so tayi ba, yanzu zata je ta taho da y’arta, barinta a hannun Abba danger ne! Tunda har ya iya turo wani wajenta saboda son zuciyarshi bai damu da yana sonta tsakani da Allah ba ko akasin hakan ba Tou tabbas zai iya yin komai. Ko bayaga haka ma idan duk duniya zata taru a kanta tofa ba zata d’auki y’arta wadda Abban yace ‘bayaso ta fad’a mata ko da sunan shi ne’ ba, ta bayar a shi yanzu! Sai dai duk abinda zai faru ya faru. Suyi mata kwatancen gidan ko kar suyi mata zata tafi ta nema, tunda Allah yasa taji kwarin jikinta yanzu, daman jiya ma jiri ne ya hanata motsawa daga inda take.” Gaba d’aya Mama ta hargitse musu, data ga ma ba zasu bata goyon baya ba, Sai ta fara k’ok’arin sauk’a daga kan gadon sannan tasa hannu zata cisge cannular hannunta. Madu ne ya rik’e hannun nata, kafin cikin lallashi yace “Maryam koma ki zauna muyi magana.” Cikin sheshshek’ar kuka ta koma ta zauna tana share hawayenta. Sai da yaga ta d’an sassauta kukan nata, sannan ya fara magana “Ki kwanta ki huta, baki da lafiya. Koda kin fita za ki sake fad’uwa ne, saboda baki gama dawowa normal ba! Ki zauna ki shanye allurai da magungunan ki, da ni da Babanku Bashir za muje mu samu Abba, in shaa Allah, kinji ko??” Da sauri Kaka yace “Za muje a yau! Ki kwantar da hankalin ki kinji?” A hankali taji kad’an daga cikin nauyin da zuciyarta tayi ya d’an sauk’a, dan haka ta d’aga musu kai alamar ‘to’ kawai, tana sharar hawaye. Ajiyar zuciya Baaba Talatu ta sauk’e, sannan ta nufi wajen kulolin da suka kawo ta zubowa Mama abinci ta kawo mata. Sakina ce ta karb’a ta fara k’ok’arin bata, amma sai ta kauda kai gefe tace “ta k’oshi” Cikin turo baki Sakina tace “haba Mama ki ce mana, kin ganki kuwa yadda kika koma? Gashi duk kin yi wata zuru zuru kamar…” Dukan da Maman ta kawo mata tayi saurin kaucewa, duk kuwa sai suka hau murmushi…. Da naci da komai hakanan sai da Sakina ta d’urawa Mama abincin nan, ta kuwa ci sosai, dan sai da su Madu suka sa baki tukun Sakina ta hak’ura. Sai wajen 11 na safe su Sakina suka fara shirin tafiya don suke suyi wanka suyi girki, ita da Ummu. Baban su Sakina ne yazo d’aukar su! Ya d’auka Mama ko wani zai yi mishi maganan Arshaad amman yaji shiru shiyasa shima yana yiwa Maman ‘ya jiki’ ya fita, dan baya so suyi mishi d’in, but ya tsara a ranshi zai gayawa matarshi, duk abinda ya sani, da kuma dalilin yin shirun da yai, saboda kar ayi mishi kallon munafuki. Sai da suka biya duk wani bill sannan suka tafi a lokacin an tafi da mama yi mata eco. Su Kaka ma shirin tafiya gidan su Abba suka yi, aka bar Baaba Talatu. Sai a sannan ne Baba yazo, ganin Maman bata nan yasa suka gaisa da Baaba Talatu ya wuce kasuwa akan zai dawo da azahar in shaa Allah. Su Kaka basu samu damar zuwa gidan su Abba ba, sai la’asar, a sakamokon kiran da aka yi musu akan results d’in da ya fito, dangane da case d’in Junaidu......... Yadda Hudan taga rana haka taga dare, Gwaggo Asabe har mamakinta take yi dan duk juyi in tayi sai taga idonta biyu! Gaba d’aya ta kasa bacci ta k’agu Safiya tayi taje taga jikin Maama, da taga safiya ta k’i yi k’arshe kawai mik’ewa tayi taje ta d’auro alwalla, tazo ta fara jero nafilfili. Tana idar da sallar asuba kuwa bayan ta gama Azkar ta d’anyi karatu, ta shiga tayi wanka. Tana fitowa ta tarar Gwaggo Asabe bata d’akin, hatta sallayar data barta akai ta nad’e. Doguwar rigar da Gwaggo Asaben ta bata jiya had’e da Maclean da brush sabbi ta d’auka ta sanya, luckily ta samu comb a d’akin cikin drawer, dan haka ta goge shi da tissue sannan ta sa hannu ta zare ribbom d’inta ta hau ware tufkar da ta yiwa dogon gashinta wanda yanzu har ya kai tsakiyar bayanta….ita kanta tana mamakin yadda ya tofo a cikin shekara uku! Bayan askin dolen da Ya Jalila tayi mata… Tunawa tayi da Jalila wadda Sakina tayi mata k’us k’us d’in Khadija tace mata ‘kamar ciki ne da ita( Jalilan)’ amman Umma tayi k’arya tace ‘ta tafi jinyar Hansai’. A hankali ta sauk’e ajiyar zuciya a ranta tana adduar ‘Allah yasa ba cikin ne da ita da gaske ba’ ….abunka da zuciya mai kyau! gaba d’aya duk sai taji tausayin Yayar tata ya lullub’eta, don haka ta hau yi mata addua da fatan alkhairi, tanayi tana taje kanta. Sai da ta gama tsaf, ta d’auko ribbon d’in ta tufke gashin a d’an k’asan tsakiyar kanta kad’an! Ganin yadda jelar take reto ne ya sanya ta kanannad’e gashin waje guda ta tura ta had’e da ribbon d’in, d’ankwalin doguwar rigar ta d’auko tayi style d’in V da d’aurin very simple amman ba karamin kyau tayi ba, ga gashin data duk’unk’une ana iya hango santsi da kyallin shi da uban yawa dan d’ankwalin k’aramine sosai so bai gama rufewa ba. Ta d’auko wayarta kenan zata kira su Mama ta ganta a kashe, ba chargi. Ajiyar zuciya ta sauk’e, daman ta san za ai haka, dan tun jiya chrgin ta yayi low sosai. Zama tayintana jiran Gwaggwo Asabe ta dawo ta ari wayarta ta kira su Mama don duk ta haddace nambobin su. Kusan minti arbain taji shiru.. ga anxiety yana neman kashe ta! Shiyasa ta yanke shawarar mik’ewa, ta hau nemanta. Bata wani sha wahalan neman nata ba, dan tana fitowa daga d’akin taji k’amshi ya cika ko Ina a gidan wanda hakan ne ya tabbatar mata da inda take(Gwaggwo Asaben), dan haka ta nufi k’asa. A k’ofar kitchen d’in suka had’u da Gwaggon, da tray a hannun ta, da kuma tea flask da ta rik’e da kyar. Sai da Hudan da d’an rissinar da kai tukunna ta gaisheta. Da kulawa Gwaggo Asabe ta amsa… Har ga Allah ta dad’e bata had’u da Yarinya mai hankali da nutsuwa irin Huda ba, ga kyau tubarkallah…shiyasa lokaci guda suka saba, taji ta shiga ranta sosai! Har k’asan zuciyarta take yiwa Aslam d’insu kwad’ayin auren Yarinyar saboda ta had’a komai ga kyau ga hankali ga nutsuwa gata y’ar uwarshi! Sai dai kuma yadda taga Arshaad yana shige mata sosai, watak’il shi ne zai fara cewa yana sonta, dan jiya ta lura har wata y’ar hira suka tsaya yi a parlour, sai wani nan nan yake yi da ita….. Hannu Huda ta saka tana k’ok’arin karb’ar tea flask d’in dake hannunta wanda hakan ne ya katse mata tunanin ta! Ba musu ta sakar mata , dan itama tana jin yadda ya kusan fad’uwa. A tare suka nufi hanyar sama, tana gaba Hudan na biye mata baya, wata hanya suka kuma d’auka bayan sun shanye stairs d’in, nan ta sake hango wani bene, benen suka bi suka hau, suna kaiwa k’arshe suka tarar ta wata y’ar k’ofa A bud’e k’ofar take hakan yasa suka shige, dogon corridor ne sosai, sai k’ofofi biyu, d’aya a farko farko hanyar dama, d’ayar kuma a kusan k’arshen dogon corridor d’in ta hannun hagu, Wadda itan taga Gwaggwon ta nufa, sai da suka iso bakin k’ofar, tukun suka tsaya! Rik’on tray d’in Gwaggwo Asabe ta gyara sosai a hannu d’aya sanna tasa hannu tayi knocking, tukun taja ta tsaya, ta gyara ruk’on tray d’in. Kusan minti biyu tukunna suka ji ance “come in” Hudan ta kalla tace “tayi amfani da empty hand d’inta ta bud’e musu.” Hakan tayi, bayan ta murd’a handle d’in a hankali ta d’an tura sai kuma ta matsawa Gwaggo Asabe don ta fara shiga.. Murmushi Gwaggon Asabe tayi sannan ta shige Itama Hudan ta bita a baya. Sai da ta rufe k’ofar tukun ta juyo ta fara kallon d’akin…. “Ma shaa Allah” tace, a ranta. Ba zaka kirashi d’aki ba kuma ba zaka kirashi da parlour ba, ga set d’in kujeru har da k’aramin dining, da makekiyar tv d’in da bata tab’a ganin irin ta ba, ga kuma set d’in gado shima komai akwai, royal, light blue da fari haka colour d’in kujeru da gadon suke, hatta pentin d’akin haka yake. Ga kuma wani glass door, wanda kana iya hango swimming pool da shuke shuke da kujerun shak’atawa. K’auyanci ta fara, don a ranta ta hau rayawa “daman ana pool a sama? saman ma ta biyu! Ita tunda take bata tab’a ganin d’aki mai girma sosai da kyau irin wannan ba!”…… Tunanin ta ne ya katse jin Dad yana cewa “Hudan k’araso mana ya kika tsaya a k’ofa?”. Sai a lokacin hankalin ta ya kai kan Dad, da wata mata a zaune a gefen shi yana rik’e da hannunta. Ji tayi kamar ta rusa kuka!! Da ta san gurinshi Gwaggo Asabe zata zo da bata biyo ta ba, kenan ita duk b’uyab da takeyi ma a banza, tunda gashi a gidanshi ma ta kwana ba tare data sani ba, kuma yadda ya nuna it’s like ya san tana nan d’in, shikenan ta san yanzu zai kira Abba shi kuma ya hanata zuwa taga Mama. Gwaggo Asabe ce ta katsemata tunani jin ta sake cewa “Huda k’araso mana.” A hankali take takawa izuwa bakin gadon inda suke… Taji Dad yana cewa “Ashe da gaskiyar Abba, daman ya ce tana wajensu Aslam ni ban yarda ba, sune suka kawota jiyan ko?” D’an murmushi Gwaggo Asabe tayi kafin tace “Eh jiya lokacin da ka kira ni, Arshaad bai dad’e da kawota ba, shi ya rakota.” Hudan dake jin su duk sai taji jikinta yayi sanyi, ashe ita kad’ai take ta shirmen ta. A hankali ta k’arasa wajen, kanta a k’asa. Har k’asa ta durk’usa ta gaida Dad, wanda cikin tsananin son yake yiwa y’ar d’anuwan nasa yayi saurin kamo ta ya zaunar da ita a kan d’an stool d’in da yake facing d’inshi, cikin kulawa ya amsa kafin ya hau tambayarta “ya kwanan bak’unta?” “Alhamdulillah” kawai ta iya cewa kafin ta juya ta hau gaida matar gefen shi har sau biyu amman ba alamun zata amsa kuma ta kafeta da idanuwa! Tana shirin sake gaidata a karo na uku ne Dad ya sauk’e ajiyar zuciya ya d’an dafa Huda tukun yace “Karki damu ba zata iya amsawa bane, amman ta fahimceki, tunda gashi tanata kallonki.” Yana gama fad’in haka ya juya ga Gwaggo Asabe jin tana cewa “ga breakfast, watak’il taci tunda naga yanzu jikin da d’an sauk’i, ko?” Shiru ya d’anyi kafin ya sauk’e wata ajiyar zuciya tukunna yace “Sai addua fa, amman Alhamdulillah, ni fa da Granpa zai yarda wallahi da an hak’ura da wannan theraphy d’in, saboda duk lokacin da akaje aka yi aka dawo ni sai inga kamar abun k’aruwa ma yake yi, kwanaki fa har hira tana yi, amman yanzu kiga gaba d’aya sai a hankali, danfa baki ganta last two weeks ba (Tym d’in da suka dawo. A Abuja), shiyasa ai na hanata dawowa nan, da kyar fa da addu’o’i tukunna abun yayi sauk’i ta dawo hakan.” Ajiyar zuciya Gwaggo ta sauk’e kafin tace “nima dai gaskiya na dad’e da lura, magana ce kawai banaso.” Cikin d’an fad’a Dad yace “Ai kuwa ta gama theraphy! Dan a gaskiya, ko ance za aje, sai dai In kaita Abuja kawai muyi sati mu dawo, abu ba fad’ar Allah ba amman an maidashi kamar dole!?” Kwalla Gwaggo Asabe ta share sannan tace “Ai shima Granpa d’in naji yana cewa ‘daga wannan an gama’.”Cikin katseta Dad yace “ai tun last year yake cewa ‘daga wannan an gama daga wannan an gama’! Amman an kasa gamawa da gasken.” Ajiyar zuciya Gwaggo ta sauk’e ranta duk ba dad’i da yanayin y’ar uwarta ta…. A hankali ta durk’usa ta fara serving abincin cikin mutuwar jiki. Hudan itama duk jikinta yayi sanyi dan haka tace “Allah ya bata lafiya”. A hankali Dad ya d’an juya ya kalle ta sai kuma yace “Ameen” cike da jin dad’in adduar tata. Juyawa yayi ya kalli Mommy, gani yayi har yanzu Hudan take kallo, kamar tanaso ta tuna wani abun.. Bai gama fahimtar yanayin ta ba yaga ta d’aga hannunta sannan tayi amfani da yatsar ta manuniya wajen sai da Huda! Gaba d’aya hankulansu kanta ya koma, cikin rawar murya kamar ta mai koyan magana sukaji tace “Aaa-sllam, ttanna kama ddda Aasllm d’Ina” Ba Dad ba hatta Gwaggo Asabe sai da gabanta yayi wani irin mahaukacin fad’uwa!!! Rabon da Mommy ta kira sunan Aslam, tun kafin ta fad’o daga bene! Gaba d’aya rawa jikin Dad ya d’auka, a hankali ya sa hannu ya juyo da fuskarta, ya kalli cikin idanunta sannan yace “Kina so kiga Aslam d’in naki?” Da sauri ta hau d’aga mishi kai, sai kuma hawaye, shaaarrrr suka zubo mata. “Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!” Shine abunda Dad ya dinga maimaitawa, cikin kid’ima ya mik’e ya fita yana cewa “su Gwaggwon su tsaya gashi nan zuwa, kar kowa yaje koina.” Ba ayi minti goma ba sai gashi ya turo k’ofa, rik’e da hannun Aslam Abba yana binsu a baya! Cikin zumud’i yace “Ga Aslam d’in naki” ya fad’a yana tunkarar ta, yana cewa su Abba “komai yazo k’arshe in shaa Allah, Aslam yau da kanta ta kira sunank.........” Razananniyar k’arar da ta fasa ce ta hanashi k’arasa maganar tashi, ta kuma rud’a duk wani wanda ke a cikin d’akin!! Basu ida dawowa haiyyacinsu ba ta kuma sakin wata k’arar! Wadda kusan rabin estate d’in sai da aka ji!. Cikin tsananin tashin hankali firgici kid’ima da tsoron da ya baiyyana k’arara a kwayar idanunta take nuna Aslam d’in tana kururuwa! A kid’ime Dad wanda duk ya rud’e ya sake nufota still yana rik’e da hannun Aslam wanda ya sake shiga tsananin tashin hankali da rud’ani don shi Dad ce mishi yayi “yazo Mahaifiyarsa tana nemanshi yau da kanta!” Gashi yanzu kuma ya tarar da haka!…. K’arar da ta sake saki ne ya kid’ima su dan tafi ta ko yaushe! Sai kuma ta saki jiki rigif ta fad’i sumammiya akan gadon….. Da sauri Aslam wanda idanuwanshi suka kad’a sukai jaa over, ya k’arasa inda take ya hau jijjigata yana kiranta amman bata motsi…….d’ago jajayen idanuwanshi yayi yana kallon Dad. Gaba d’aya sai Dad d’in yaji tausayin su, su duka ukun ya lullub’e shi.. Abba ne yayi k’arfin halin zuwa inda suke, yad’an kura mata ido kafin ya cewa Gwaggo Asabe “ta mik’o mishi ruwa!” A hankali yake yayyafa mata ruwan, har sun cire ran zata farka sai kuma sukaga tana motsi da idanunta alamun zata farfad’o…. A hankali Abba yad’an kalli Aslam wanda ke zaune a gefenta ya rankwafa kanta sannan ya kama hannunta gam!! Yana kallon idon da take k’ok’arin bud’ewa, alamun a kag’e yake yaga ta bud’e idanun nata! Da kyar Abba ya tattaro courage d’in da ya iya cewa Aslam “Aslam, ko zaka d’an je waje ko? Kar ta farka kuma ya zamana kai d’in zata fara gani.” Da sauri yace “No Abba, I think bata gane ni bane ba.” Sai kuma ya kalli Dad yace “Dad da kanta ai kace ta kirani ko?” Ganin da Dad yayi Aslam d’in na neman koma musu wani firgitachche ne ya sanya shi kawai cewa “Kaje wajen tukunna mu gani.” Jikinshi har wani karkarwa yake yi, sai da Dad ya sake cewa “I’m so sorry Aslam, ita tace a kiraka but ban san me ya sake faruwa ba kuma, for now just, ka d’an jira a waje ko?” A hankali ya cika hannun ya mik’e ba tare da ya yarda ya had’a ido da kowa ba ya fice, Dede nan Dad ya fashe da kuka, gaba d’aya sai hankalin su Abba ya sake tashi, saboda abune wanda basu saba gani ba! Don haka duk sai suka hau bashi hak’uri suna tausar shi, tare da adduar in shaa Allah Allah zai bata lafiya soon… A b’angaren Dad shi kuma Aslam yake ji, da ya sani da bai yi saurin kiranshiba, gaba d’aya duk sai yaji ya tsani kanshi….. Da kyar suka samu ya tsaida kukan ya k’arasa gurin Mommy wadda ta farka yanzun tanata faman dube dube a mugun tsorace alamun neman tsari take daga sake ganin Aslam d’in. Sai da komai ya lafa sannan Gwaggo Asabe suka fito ita da Hudan daga d’akin…. Ita dai Huda gaba d’aya kanta ya kulle, hakan yasa ta kasa hak’uri ta hau tambayar Gwaggo “meke faruwa? Mai ya sameta take haka? Tun yaushe? An yi mata sauka?” Dan ita Huda har ga Allah kawai ta fi jirkita akan lamarin na iska ne, tunda gashi dai ita da kanta ta tambayeshi but yana shigowa gaba d’aya ta firgice! Tayaya uwa zata dinga gudun d’anta haka?? Don ko ba a gaya mata ba ta gane itace Mahaifiyar Aslam ko dan yanayin kamar da suke yi da juna! But why him? Him alone?” Ajiyar zuciya Gwaggo Asabe ta sauk’e sannan tace “bani minti talatin, inje inyi wanka, Ina dawowa za kiji komai in shaa Allah.” Kamar yadda Gwaggo Asabe tace Sai da tayi wanka ta dawo ta zauna sannan ta fara bata labari………… Asalin sunan Mommy, Aisha ana kiranta da Humaira, k’anwarta d’ayar duniya Khadijah wadda ake kira da Asabe. Aisha da Asabe sun taso cikin yanayin k’unci na rayuwa ata dalilin babu.. Yahaya ya had’u da Aisha ne lokacin da ya kai ziyara Taraba, jalingo a wani d’an k’aramin k’auye. Ata dalilin, masallaci da makarantun addinin daya d’auki nauyin ginawa. A rafii yana zagaye ita kuma taje d’ebo ruwa suka had’u. Tunda ya kyalla ido ya ganta ya rikice, a lokacin Mahaifiyarsu ta rasu Mahaifinta kawai ya rage musu. Tun Aisha tana kauce mishi har itama ta fara kulashi sama sama. Tashi d’aya ba kwana kwana ya nuna mata yana k’aunarta kuma yana son aurenta, Bata bashi amsa ba tace “yaje ya samu Mahaifinta”. Yahaya bai yi wani jinkiriba yaje ya samu Mahaifinta da maganar sannan yayi mishi alk’awarin ‘bayan auren zai barta tayi karatu har sai tace bataso’, dan ya lura burin Mahaifin nasu kenan. D’an guntun bincike akayi akan Yahaya, a lokacin, daga nan Mahaifinta ya bashi aurenta yace masa “duk lokacin daya shirya yazo da iyayenshi a d’aura” To fa!! anan ake yinta, dan k’iri k’iri Granpa ya nuna k’iyayyar shi muraran akan Aisha da inda ta fito, acewarshi “sam ba a jin auren d’ansa bace ita d’in!!!”. Buwayar Ubangiji, rabon Aslam, da soyayyar Granpa a matarshi ne suka tabbatar da auren Yahaya da Aisha wanda aka d’aura a k’auyen Jalingo ba tare da halartar Granpa ba. Tabbas anyi rigima ba k’arama ba, kafin, da kuma bayan auren!. Zan iya cewa ban taba ganin macen da ta sha wahala a hannun suruki kamar Aisha ba! Sauk’in ta d’aya Gramma tana mugun sonta ba kad’an ba, dan tun lokacin da Yahaya yaje mata da labarin Aisha farat d’aya taji Yarinyar ta kwanta mata, ita ta dinga lallab’a Granpa har aka yi auren. To bayan auren ma haka tayi ta fama, in tak’aice miki labari hankalin Granpa bai kwanta da Aisha ba har sai da ya aurawa Yahaya ajin nashi da yake ik’irari! Wanda ranar d’aurin auren ana d’aurawa Yahaya yana hawaye kamar k’aramin Yaro, dan zan iya cewa ban tab’a ganin Mijin da yake matuk’ar so da gudun b’acin ran matarshiba kamar Yahaya ba. Sauk’i d’aya da Aisha ta samu a gurin Granpa shine haihuwar Aslam da tayi, zan iya ce miki ko y’ay’an da Granpa ya haifa a cikinshi bayayi musu kalar son da yake yiwa Aslam, ko dan ya kasance jikansa na farko ne? Allah kad’ai ya sani. Tun ranar da aka haifeshi da ya d’auke shi aka tabbatar da hakan, domin kuwa kalar farin cikin da yayi kowa sai da ya gani ya tabbatar da ‘Granpa na cikin farin ciki’!. Zakkah da sadakar da ya bayar kuwa bana jin har yau a tarihin kaf garin Kano an tab’a bada irinta. Aslam ya taso cikin gata, duk wani abu da kika sani Granpa ne yake yi mishi… A tunanin kowa, Granpa zai kasance irin kakannin nan masu shagwab’a jikokinsa ne, sai dai kuma shekarar Aslam biyar a duniya aka haifi Arshaad amman kwata kwata Granpa bai yi wani murna sosai ba ma balle aje ga maganar shagali da jan shi a jiki kamar yadda kowa ya d’auka… Tun ranar da aka haifeshi da ya d’auke shi bai k’ara d’aukar sa ba, Aslam kuwa kullum suna tare, hatta abinci tare suke ci, takanas ya nemo wani bature yake yi mishi lesson a gida, da yamma kuma wani balarabe ne yake koyar da shi addini! Sai da Granpa ya fahimci loneliness da rashin wasa da Yara agemate d’in Aslam d’in kan iya jawo mishi wani ci baya a rayuwarshi tukunna ya nemi makarantar da tafi ko wacce tsada a kaf Nigeria ya turashi a Abuja wajen mahaifinshi, tare da kwakkwaran warning a me makarantar na “kar a tab’a mishi jika ko me kuwa zaiyi! Kuma kar a bari aci zalinshi.” Duk da yana da wayo sosai dan, a lokacin shekararshi tara Arshaad hud’u Auwal kuma uku wanda shima Granpa bai wani nuna farinciki ko tunanin janshi a jiki ba tun sanda aka haifeshi. A lokacin ne kuma Yahaya ya sake tadawa Granpa maganar yana so ya tafi da Aisha Abuja , daman ya tab’a nunawa Granpa son yin hakan amman fur k’iri k’iri Granpa ya nuna mishi sai dai ya tafi da Mammy saboda itace tayi karatu bayan k’iri k’iri babu irin artabun da baayi da shi ba amman fur haka ya hana Aishan yin karatu acewarsa ‘irin su In suka yi karatu gagarar mutum suke yi!’. A lokacin ya nace akan sai dai ya tafi da Mammy ita zata iya zaman Abuja wata k’ilan ma ta d’an dinga taimaka mishi ta fannin aiki, shi kuma Yahaya yace ‘ba zai tafi da ita ba! Ko da ace Aisha bata kasance uwargidanshi ba tou tabbas da ita zai tafi’….. Mistake d’aya wanda Yahaya yayi kuma yake kan yi har yanzu shine ‘k’iri k’iri yake nuna fifici a tsakanin matanshi’ (k’iri k’iri yake nunawa kowa ba tare da shakkar wani abu ba ‘ya fi son Aisha a kan Mammy’. Da kyar a wannan lokacin dan sai dai Gramma ta shiga tsakani tukunna case ya mutu, dan daa Granpa cewa yayi sai ya tafi da Mammy dole! Shi kuma yak’i. Tou kuma da Aslam ya koma chan ma da ya sake yin maganar Aisha ta bishi, still magana d’aya irinta farko shima Granpa ya maimaita mishi ‘sai dai ya tafi da Mammy’ shi kuma yak’i, Shiyasa har yau shi kad’ai yake zaune a Abuja, yanzu haka shi da Aaima ne kawai a gidan. K’in tafiya da Mammy da Yahaya yayi ata dalilin Aisha yasa Granpa ya rufe ido ya dinga keta mata ruwan rashin mutunci kala kala, ga Adama da Ummi suma basu barta ba, Mammyn ce ma ita bata shiri da ita kuma bata fad’a da ita. A lokacin ne kuma Mahaifinta ya rasu, Allah yaso ni nayi aure don da ban san ya zan yi ba saboda shi kanshi Mahaifin namu su uku aka haifa biyun duk sun rasu, Mahaifiyar mu kuma daga gidan marayu ma aka aurota, balle inyi tunanin zuwa gidan y’an uwa! Dan a lokacin halin da Aisha take ciki a gidannan, ko mage bata isa ta d’auko tace zata rik’e ba. Aslam shekara biyu kawai ya iya yi a Abuja ya d’agawa kowa hankali Akan shi fa ‘Mahaifiyarshi yake buk’ata’ Dan ba kad’an ba suna mugun k’aunar juna, kuma yana da k’ulafucin uwa ba kad’an ba, itama kuma haka, komai Aslam, shima komai Mommy. Saboda tsabar tsananin shak’uwar dake a tsakaninsu yasa har kusan zarewa tayi lokacin da aka kaishi Abuja, Idan nace zan tsaya fasalta miki kalar soyayyar da sukewa junansu sai mu kai jibi anan.......... Ba yadda Granpa ya iya haka ya tarkatoshi ya dawo dashi kano gurin Mahaifiyarshi, akan dai ya bari a tafi da ita d’in. Sai dai kuma daya dawo d’in abun bai yi dad’i ba sam! Dan k’iri k’iri Granpa ya dinga nuna banbanci k’arara ba tare da shakkar komai ba! Abun mamaki hatta driver d’in da zai kai Aslam makaranta daban ne da nasu Arshaad. Tun abun baya damun mutane har aka fara k’us k’us, su kansu Yaran suma suka fara fahimtar waensu abubuwan….dan shi Arshaad ma a tunaninshi Aslam d’in d’an Granpa ne shiyasa a lokacin yake kiranshi da ‘Uncle Aslam’ a lokacin. Ranar 12th birthday d’in Aslam ne Granpa yayi wani abun da ya girgiza mutane! Gida guda ya d’auka ya bawa Aslam as birthday gift, a Dubai! Wanda su kansu y’ay’ansa basu ma san yana da shi ba, kar ki ce k’aramin gida fa mansion ne mai zaman kanshi! Dan ko a jikin takardar wajen d’akuna ashirin ne suka fito a cikin gidan, iya d’akuna kawai!. Mutane basu dawo daga shock ba ya cewa Yahaya “ya yiwa lawyer d’inshi magana a fara had’a takardun MT! yana so zai mallakawa Aslam su tun yanzu, in yaso shi (Yahayan)sai ya rik’e mishi idan ya kai 18 years ya bashi abunshi.” Cikin nuna k’in amincewa Dad ya d’an fara k’ok’arin fahimtar da shi akan shekarun Aslam d’in da kuma gudun abunda hakan ka iya janyowa K’asa k’asa ba tare da ya bari kowa yaji ba. Amman Granpa maimakon ya fahimceshi sai ya birkice mishi, ya fara magana yana fad’a kowa yana ji! Ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba! Fad’a a ranar ba kalar wanda bai yi mishi ba a gaban taron y’an birthday… Sai da Aslam d’in yayi kamar zai yi kuka yana bashi hak’uri tukunna aka samu ya hak’ura. Jiki a mace haka Dad ya fita ya kira lawyer ya hau kora mishi bayani…… Kusan minti talatin tukunna ya dawo ya sanar mishi lawyer d’in yace zuwa nan da jibi in shaa Allah komai zai kammala. Kaf a wajen! Y’an tsirarrun mutane da Granpa ne kawai suke farin ciki amman kowa a family d’in in ka kalli fuskarshi ba zaka iya tantance me ke wakana a cikin zuciyarshi ba, sai dai tabbas tashi d’aya zaka hango damuwa binne a k’ark’ashin komai. Ana i gobe takardun zasu iso, wato washegarin birthday! Wani mummunan al’amari ya afku.” Ajiyar zuciya Gwoggwo Asabe ta sauk’e kafin ta kalli sama hanyar staircase ( parlourn k’asan da yake da matattakalr staircase d’in biyu anyi tsarin wajen ne irin me high ceiling dinnan, mutumin da yake falon sama wanda ya had’a staircase d’in dama da hagu yana iya hango komai na k’asa, shima na k’asan haka, sai kuma hanyoyin dogon corridor biyu da suke kallon juna, d’aya yana a right staircase d’ayan yana kusa da left one. Sai d’akin special guest guda biyu da yake a main parlourn sama da kuma hanyar da zata had’a ka da benen da zai kaika chan sama). Sannan ta cewa Huda “kinga chan wajen?” Tayi maganar tana kallon falon saman, kafin taci gaba da cewa “Mommy tana tsaye tana waya a jikin k’arafunanan taba d’ab lek’o k’asa…… Ganin shigowar Dad Aslam da Arshaad a tare yasa gaba d’aya hankalinta ya dawo kansu tana yi musu murmushi, Arshaad ne ya hau kawo mata k’arar Auwal tun daga k’asan yana yi yana hawa benen, dan haka ta mayar da hankalinta a kanshi tana ce masa ‘ya taho a hankali kar ya fad’i..’ bata ida rufe bakinta ba dai dai Arshaad ya kusan k’arasawa inda take kawai kamar wadda aka turo sai k’ara akaji timm!!!A take kuma ihun Aslam ya karad’e gidan gaba d’aya… Da gudu ya k’arasa inda take kwance dukda cewa ta fad’o ne bisa wasu tumtum da suke kan kafet d’in k’asan, hakan bai hana kanta zubar da jini ba! Saboda ba duk jikinta ne yayi nasarar sauk’a a kan cuision d’inba!. Da kyar Dad ya iya k’arasawa wajen ganin yadda take kallon sama tana karkarwa yasa kawai ya yanke jiki a take ya fad’i sumamme dan shi a tunaninshi ma mutuwace zata yi. Banda ihun kiran Mommy ba abunda Aslam yake yi, wanda hakan ne ya jawo hankalin mai gadi ya iso.. Ya dad’e ya na knocking yaji shiru ga Aslam yanata rad’a ihu dan ita Mommy a lokacin mai aikin ta zuwa takeyi tana tafiya, kuma lokacin har ta tafi , so ita kad’ai ce sai su Dad da suka shigo wanda yake a sume! Kuma akai rashin sa a suka tura k’ofar bayan sun shigo ta shiga lock!. Arshaad kuwa, mutuwar tsaye yayi, ya k’ame k’am! In banda kallon wajen da take a tsaye kafin ta fad’o d’in ba abunda yake yi, dan har lokacin da mai gadi ya nemo mutane aka b’alla k’ofar aka shigo, Arshaad yana nan a yanda yake, dakyar aka iya janyeshi a wajen aka kaishi wajen Mammy, dan kurma ya koma musu, sai da yayi kwana biyu baya magana….. A asibiti kuwa da kyar aka dedeta numfashin Dad, bayan awa biyar Allah ya bashi ikon farfad’owa, garau ya tashi dan haka hankalin mutane ya d’an kwanta, saboda a yanda jinin shi yayi mugun hawa ba wanda bai yi mishi zaton stroke ba. Mommy kuwa da kyar aka tsaida jinin aka kuma samu ta farfad’o bayan kwana biyu sai dai kuma scan d’in da aka yi mata na kwakwalwa ya tabbatar da cewa jini ya shiga kwakwalwarta, wanda sai anyi aiki an kwashe an kuma d’inke inda ya samu rauni. Dad bai yadda anyi aikin anan ba, waje ya fita da ita aka yi komai, sai dai kuma tun kafin ayi aikin dama sun tabbatar da cewa ba lalle inta farfad’o ta dawo kamar daa ba sai dai a hankali, wasu kan iya d’aukar 1 year wasu 10 wasu 20 wasu kuma 4eva ma basu dawo normal d’in ba! But ita case d’inta minor ne so ana saka ran ma ba lalle ta d’auki 1 year d’inba in shaa Allah komai zai dawo normal. Granpa yayi mugun sauk’owa, ko dan ganin yadda hankalin Aslam ya tashi yasa shima nashi hankalin tashi, Allah kad’ai ya sani, dan tare ma suka tafi har shi da Mammy wadda itama ta d’aga hankalinta da ganin halinda Abokiyar zaman nata take ciki, dan da Dad yak’i biya mata kud’in jirgi ma da kanta ta biya ta bisu daga baya. Tunda aka yi aikin kuwa ita take kula da Mammy sai Dad yayi da gaske take yarda taje hotel ta d’an huta, tayi bacci. Aslam, tunda aka yi wa Mommy aiki, yake azumi kulli yaumin, har ranar data farfad’o. Da farko b’oyewa yayi dan ya san za a hanashi, dan har yi yakeyi kamar yaci abincin sai daga baya aka fahimta, ba yadda ba ai ba amman yak’i ajjiyewa, ganin haka yasa Granpa yace a barshi, sanadiyyar azumin da yayi tayi a jejjere gashi da k’arancin shekaru ya sanyashi kamuwa da cutar ulcer. Kamar yadda Likitocin suka fad’a, haka Mommy ta farfad’o amman a iya rayuwarta Aslam kawai ta iya ganewa, bata magana sannan komai sai an nuna mata sai an koya mata! Abu d’aya ta sani ta gane take iya fad’i, shine ‘ASLAM’. Anji ciwon hakan sosai, amman kwarin guiwar da ake ta samu a wajen manyan Likitoci ne yad’an kwantar da hankalin Jama’a, dan suna ta bada assurance d’in ‘zata dawo normal!’ Sai dai kuma ana yin wata d’aya komai ya burkice!!! Dan Aslam d’in da ta fara fahimta sai ya dawo ya zame mata dodo!!! Da farko yana shigowa zata fara kuka!! Sai kuma ta dawo ihu!!! Daga k’arshe dai ko asibitin in Aslam ya shigo tun kafin ya k’araso inda take zata hau kururuwa tana kuka kowa ta nan ne yake gane Aslam ya iso! Wani abun mamaki shine ta warke garau ta fara magana ta gane kowa amman fa ko a labari idan aka sako Aslam tou yanzu hankalin kowa zai tashi!! Ba k’aramin kid’ima Likitocin suka yi ba dan su kansu sun zama confuse..A iyaka sanin su masu irin wannan matsalar basa haka amman duba da suka yi da shi ta fara ganewa a lokacin data farfad’o ya sanya suka yi y’an bincikensu, iya abunda tunanin su ya basu ne ya sanya su dangantata da psychiatric. Allah sarki Aslam, a lokacin sai da ta kai ga shima aka bashi gado a asibitin tsabar tashin hankalin daya shiga. Yaro ne shi a lokacin amman kasancewarshi mai kaifin basira yasa ya fahimci komai. Dan zan iya ce miki har yau ban tab’a ganin Yaro mai wayo tarin ilimi da kaifin basira irin Aslam ba, har gobe in da wani d’an ajinsu da suka yi makaranta zai zo gidannan to ba zaki tab’a ji ya kirashi da aslam ba , sai dai suce mishi ‘gifted’ Dan wani abun time d’in a makaranta ba sai an koya mishi bama yake iyawa, in kuma ya iya to ya zauna kenan! Ga wayo kamar wani d’an shekaru dayawa.” Ajiyar zuciya Gwaggo Asabe ta sauk’e sannan ta ci gaba “A lokacin hankalin kowa a tashe yake, ni kaina da nake nan da ban ganta ido da ido tana haukan ba sai da naji a jikina, abu yak’i ci yak’i cinyewa har aka shafe wata biyu a haka, ga Aslam a kwance… Tausayin shi da ya lullub’e Granpa gashi yana ganin yana neman mutuwa ne yasashi fara nemawa Aisha magani gadan gadan ba kama hannun Yaro, duk inda yaji labarin Likitan kwakwalwa nan zai tarkata su su nufi k’asar! Cikin shekara biyu zan iya ce miki sun kusa zagaye duniya dan ba k’asar da ba a je ba, in dai kinajin ta kuma sananniyace. Amman dukda haka Allah bai kawo sauk’in ba, saboda lokacin samun sauk’in bai yi ba. Daga karshe dai hak’ura suka yi suka dawo gida Nigeria. Ai ana dawowa abun yafi na daa, ba k’aramin tsorata muka yi ba dan nima nazo a lokacin…Idan Aslam baya gidan nan to k’alau amman ko bakin MT yazo yanzu zata birkice, abun tausayi In kana nan dole kayi kuka, don Aisha mahaukaciya tuburan ta koma. Shawara d’aya Granpa ya yanke shine na ‘kai Aslam boarding school’ don samun sauk’in kowa and ya kamata yaci gaba da karatu kuma ya maida hankali saboda an barshi a baya sosai… A lokacin shekarunshi sun haura 14. Da kyar Aslam d’in ya yarda, ya tafi bayan Granpa yayi mishi alkawarin ‘duk inda magani yake a duniyar nan in dai akwaishi to zai nemawa Mommy d’insa, ko nawa ne kud’in ba zai gaji da biya ba, koda kuwa zai k’arar da duk abunda ya tara ne!!!’. Haka nan aka tarkata Aslam aka kaishi boarding cikin tsananin k’unci, yana kuka muna kuka ba dan munso ba. Wani abun takaicin ko hutu Aslam bai isa ya zo ba, sai dai In kana buk’atar ganinshi kai kaje ka ganshi a inda yake, k’iri k’iri zaman estate d’innan ya gagareshi… Ganin abun na Aisha bana k’are bane yasa suka kira wani babban Likita daga k’asar waje har gida Nigeria ya dinga kula da ita, shi ne ya bada shawarar a kulle su ita da Aslam a d’aki d’aya su kad’ai, for 24 hours, to kuma abun bai yi dad’iba don shi yayi sanadiyyar da Aslam ya bar k’asar nan wanda sai yanzu ne Allah ya dawo mana da shi! Da farko an tsara akan zai d’an dinga lek’owa Hutu sai yake sauk’a gidan Abba, yadda ba zasu had’u da ita ba, har zuwa lokacin da Allah zai kawo sauk’i Amman abunda ya faru a wannan rana ya sanya Aslam yin yaji mai mugun tsayi ya tarkata komai nashi ya tafi sai dai waya, shima wani lokacin sai yake gudun d’auka!. Arshaad da su Abba suna yawan zuwa duboshi, Auwal ne ma yaje sau d’aya, amman Arshaad a shekara ma yakan je sau biyu shi da Abba..saboda shi Aslam ko hutu idan anyi na makaranta baya iya dawowa sai dai yayi achan Oxford Uni inda yayi karatunshi. Aslam a Oxford yayi karatu, Arshaad kuma Dubai aka kaishi Auwal kuma Cairo. Da yake Granpa ne duk ya kaisu..duk da halin da Aslam yake ciki sai da aka fara k’ananan maganganu, Adama da Ummi, wai ‘har yanzu Granpa bai daina nuna bambanci ba’ Sosai Granpa da maganar ta koma mishi yayi musu tataas!!!Kuma ya taso da maganar mallakawa Aslam MT gaba d’aya inyaso sai yaga me za suyi!. Da kyar da sid’in goshi Gramma ta tausheshi, sannan ta lallabashi, sannan tai k’ok’arin fahimtar dashi abubuwan da hakan ka iya janyowa…. Awannan lokacin kuwa anci sa’a ya fahimceta sosai, don da kanshi kuma ya dawo yace ‘a tsakanin Auwal Arshaad da Aslam, duk wanda yaga he’s capable to shi zai mallakawa MT’. Dad yayi mugun mugun yin farin ciki daga jin wannan decision na Granpa, bawai yana zargin wani ba, kawai dai yaji releaf, kuma shima baya son bambancin da Granpa d’in ya dad’e yana nunawa especially tsakanin Arshaad da Aslam, don duk abun nan da ake yi ko sau d’aya Arshaad bai tab’a nuna b’acin ranshi ba, dukda kuwa uba d’aya ne ya haifesu shi da Aslam d’in, Idan akwai fitinanne tou Auwal ne! Amman Arshaad shi ba ruwanshi yana da kauda kai kunyarshi ce ma ta sanya Dad yake yiwa Mahaifiyarshi wani abun dan kar yaga ga kamar bai damu da ita sosai ba. Kowa idan zaki tambaya a estate d’innan ya baki sheda akan Arshaad to zai ce miki ‘yanada hak’uri da kauda kai da kuma saurin yafiya’. Aslam yana kammala degree na farko aka d’aura shi a matsayin MD na MT branch d’in dake achan k’asar da yake, wanda ada Abba ne a wajen. Ayyuka Aslam yake yi bashi da lokacin kanshima, kuma daman hakan yake so dan hakan ya tsarawa kanshi tun farkon komawarshi UK d’in, yana k’ok’arin kullum yaga ya zama busy dan kar ma ya bawa kanshi daman yin tunani.. Aikin kuwa ya taimakeshi ta b’angarori da dama dan Yana da nashi campny d’in a chan, na sarrafa takalma wanda k’wazonshi guminshi da kuma taimakon Granpa wanda yake aika mishi kud’i kamar hauka suka taimaka masa ya had’a ya bud’e wanda yanzu naji suna cewa yanaso ya bud’e wani branch d’in anan ko kuma ya dawo nan ma, gaba d’aya. Kuma akwai wani daban da zasu bud’e na zanen gidaje shi da Abba! Ga mt ga kuma karatu wanda a yanzu ya kammala PHD d’inshi… A b’angaren nasarori Aslam ya samu kam ba a magana sai dai kuma shi duk basa gabanshi, inda za ace ya tatttara ya bada abashi lafiyan Mahaifiyarshi na tabbatar kafin k’iftawar ido zai iya sallama komai! Ba shi kad’ai ba hatta mu duk tsawon wannan lokacin buri daya muke da shi shine ‘Aisha ta warke hankalin kowa ya kwanta’ Dan shi kanshi Aslam d’in abun a jiye mishi ne, saboda gaba d’aya rayuwarshi ya yita ne cikin fargaba, k’unci da damuwa. Yanzu haka ko Abokanai baya iya tarawa shi kad’ai d’insa yake komai sai dai a d’an dinga zumunci sama sama, Abokin shi na k’ut da k’ut guda d’aya tak a duniya wato Arshaad, da Arshaad ne kawai za kiji suna waya suna d’an raha amma ko mu y’an gida wani lokacin idan ka kirashi sai yak’i d’auka. Tsoronma shiga mutane yake yi balle yayi huld’a dasu.. Naji su Abba suna cewa ‘Kana ganinshi in dai ka fahimci yanayin shi tou tashi d’aya zaka fahimci he’s depressed! Kuma hakan ba a so a mutum especially mai k’arancin shekaru kamar nashi, zai hanashi yin farin ciki a rayuwa ne kwata kwata, har abada!.” Ahankali tace “To amman ya za ayi? Magani in dai sunanshi magani tou ba kalar wanda ba ayi ba amman har yanzu shiru............” Ta k’arshe maganar tana share d’an hawayen daya biyo idanunta a karo na ba adadi. Hudan, itama hawayenta ta goge, a ranta tace “Allah sarki bawan Allah, ashe shiyasa kullum yake cikin fushi, da har nake jin haushinshi.. In shaa Allah daga yau na daina jin haushinshi, Allah ya bawa Mahaifiyarta lafiya.” Maganar Gwaggo Asabe ce ta katseta jin tana cewa “Kema dan Allah idan kin yi sallah ki dinga sakamu a addua Allah ya kawo k’arshen wannan abu.” A hankali Hudan ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace “In shaa Allah” Sai kuma ta gyara zamanta ta ci gaba “Amman Gwaggo a duk cikin bayaninki banji inda aka yi mata Sauk’ar Alqur’ani ba!” Cikin katseta Gwaggo Asabe tace “anyi sauk’a Huda, Granpa da Dad da kansu suka je suka raba kud’i lokacin da suka dawo farko farko a islamiyoyi da tsangayar almajurai aka yi ta sauk’a!.” Murmushi Hudan tayi sannan tace “Gwaggo Asabe, idan zan bada shawara a d’auka inaga daa mu da kanmu ya kamata muyi mata sauk’ar bayan an raba a islamiyoyin, kuma in na fahimceki kamar sau d’aya aka tab’a yin sauk’ar ko?” Bata jira jin mai Gwaggo Asaben zata ce ba ta ci gaba “Ni a lokutan baya, idan bamu da lafiya ko wani alamari mara dad’i ya afku Tou bayan Mama ta bamu magani sai ta kammala mana sauk’a, ko lokacin da nake k’arama akwai Yayanmu da yake shaye shaye sai da Mama tayi mishi sauk’ar AlQur’ani sau bakwai!! Ta fara tayi sau hud’u ya warke ya daina amman dake tayi niyyar bakwai d’in zata yi sai da ta k’arasa. Da kuma muka yi wayo haka zata rarraba mana muna tayata da ni dasu Ya Jalila koda izu d’ai d’ai ne mu kan taimaka. Ko yanzu haka In wani abun ya faru rabawa muke yi ni da ita da Sakina wani lokacin da Sumayya, bama wata d’aya muke k’arasawa, in kuma mun kwallafa to a sati muke idawa. Balle nan gidan munada d’an yawa.. Yanzu for example ace mutum shidda kowa ya d’auki izu goma, duk bayan sallar Farilla kayi izu d’aya a kwana biyu fa za mu dinga kammalawa, In kuma izu biyu za ana yi a cikin kwana 1 mun kammala, inda hali kowa in ya kammala sai yayi mata addua dafatan waraka bayan an tofa aruwa a bata tana sha, Daganan ayita yi, kuma akai akai. In Allah ya yarda sai kiga an dace. Dan dai gaskiya kamar yadda kika fad’a abun sam kamar bana asibiti bane ba! Koda ace ma na asibitin ne Sauk’ar Alqur’ani fa shine k’arshen waraka Especially idan mune muka yi da kanmu, saboda waennan na islamiyya ba mu da tabbas, yanzu duniya ta chanja ba lalle In sun karb’i kud’in suna sakawa anayi ba…..” Maganarta ce ta katse jin mutum a tsaye a bayanta ya dafa kanta, tana juyowa sukai ido hud’u da Dad da Abba a bayanshi suna murmushi, waenda shigowarsu kenan suna d’an tatauna wata magani suka ji bayanin Hudan. Dad ne yace “y’ar albarka, naji dad’in wannan shawarar taki sosai. Kuma daga yanzu in shaa Allah zata fara aiki. Kafin masu kwashe kaya su gama na san mun kammala in shaa Allah, na yau.” Yana gama fad’in haka ya d’au waya ya kira Arshaad da Aslam yace “su sameshi.” Sai da ya gama wayar, Hudan ta d’an zame daga kan kujera inda take ta shiga gaida Abba. Shima Dad d’in ta sake gaidashi. Cikin kulawa suka amsa mata sannan suka cigaba ta tattaunawarsu da alamun magana mai muhummanci suke yi. Hudan sai d’ar d’ar takeyi a tunaninta kar Abba yai mata fad’an abunda tayi mishi jiya, shima ya lura da yanayin ta shiyasama ya fasa zuwa inda take, amman da yayi niyyar jin yadda ta kwana da kuma jin ko akwai abunda takeso dan harga Allah shikam yana so ya zama tare da y’arsa ya jaa ta a jiki ko sa samu su saba da juna sosai. Arshaad ne ya fara shigowa… Tsayawa Hudan tayi tana kallonshi dan ta manta rabon da ta ganshi da k’ananan kaya, yafi ta’ammali da shaddodi da yadi, sab’anin yau da yake sanye da wata shirt army green dark an rubuta ‘KING’ a jikin gaban rigar da zanen crown d’in king d’in ata k’asa. Rigar irin mai d’an kama jiki ce, hakan ya taimaka wajen fito da ainahin surar jikinshi dan kana iya hango packs d’inshi na sama sama ta cikin rigar da yadda dantsen hannunshi yake a mummurd’e! Wandon nashi shima ba jeans bane yana yin rigar ne black in colour bai kamashi ba kwata kwata ta sama amman roba ne, kasancewar ya d’an matse daga guiwar wandon zuwa k’asa yasa ya zama kamar pencil trouser ta k’asan… Kayan yayi matuk’ar fito da asalin surarshi ta giant! Ga wani fitinannen k’amshi mai tsayawa a rai da yake zubawa dan tunda ya shigo parlourn ya karad’e da k’amshin shi, tun bai iso inda suke ba…. Hudan bata gama k’are mishi kallo ba suka had’a ido da shi, gira d’aya ya d’aga mata yana d’an murmushin gefen baki, da sauri ta sunkuyar da kanta k’asa kunya duk ta lullub’eta ganin ya kamata tana kallonshi . Ganin yadda tayi ne ya sanyashi sakin wani lallausan murmushi, kafin ya k’arasa inda su Dad suke ya shiga gaidasu cikin girmamawa. Ya so ya k’arasa wajen Hudan dan shima ba k’aramin kyau tayi mishi cikin rigar abaya blueblack mai stones, d’aurin da ta yiwa kanta da d’ankwalin abayan ya yi matuk’ar burgeshi! Amman sai Dad ya tsareshi ta hanyar fara yi mishi bayani abunda za suyi ba tare da b’ata lokaci ba, 100%ya amince da kuma jinjina ga wanda ya kawo shawarar dan abunda ya kamata ayi kenan, cikin jin dad’i Dad yace “ai Hudan ce” da d’an murmushi ya juyo yana kallonta, yanzun ma sauri tayi tai k’asa da kanta, don still satar kallonshi take yi, harga Allah Ya Arshaad yayi kyau yau sosai…… Tana wannan tunanin hancinta ya fara jiyo mata wani k’amshi na daban, wanda a take ya cika mata hanci, kuma ta fahimci wanene Kasancewar a kan kujerar dake gaban side d’inshi take ne yasanya ta fara jin k’amshin kafin kowa, bata san daliliba ba kuma tasan mai ya faru ba, amman ko lokacin idan anyi laifi a islamiyyarsu za a dakesu tabbas zuciyarta bata yin kalar bugun da take yi a yanzu…. A hankali ta runtse idanunta ta sake yin k’asa da kanta jin takunshi a daf bayanta!Sannan bugun zuciya da k’amshin da yake shak’a na k’ara yawa…. Kamar yadda Arshaad yayi shima hakan ya gaida su Dad waenda suke ata gefe kad’an kusan hanyar shigowa sai dai shi bai k’arasa inda suke ba, hasalima zagayowa yayi ya zo kan kujerar da Gwaggo Asabe take ya zauna.. Kasancewar Gwaggo Asabe a 3 seater take zaune Hudan kuma a 1, sai ya zamana kamar suna facing juna shi da Hudan! A hankali ya d’ago idanuwanshi ya sauk’e su a kanta, da tayi k’asa da kai wanda ita kanta ta kasa tantance dalilinta na yin hakan Magana Gwaggo Asabe take yi mishi amman kamar ma baya jin ta, ganin hakan yasa ta d’an tab’a shi kad’an.. Lumshe idanunsa kawai yayi kafin ya bud’e su ya sauk’e a kan Gwaggo Asabe, d’an murmushi kad’an yayi mata kafin yace “barka da gida”. Cike da tausayawa Gwaggo Asaben take kallonshi, ko ba a fad’a mata ba ta san tun d’azu da ya fito daga d’akin Mommy yake cikin tashin hankali!! Dan gashi idanuwanshi sunyi jaaa sosai bakinshi yayi pink shima hatta kan hancinshi yayi jaaa Amman kuma ko ba a fad’a mata ba ta san ba kuka yayi ba wanda wani lokacin har addua take yi Allah ya bawa hawaye ikon fitowa daga idanun Aslam ko ya samu ya rage rad’ad’in da zuciyarshi take ciki. Hannunta ta d’aura akan lallausan gashin kanshi ta d’an shafa… Hakan ya sanya shi sake maida hankalinshi a kanta! Tana shirin yin magana Dad ya fara yiwa Aslam bayanin abunda ya tarasu anan bayan ya zagayo ya zauna, Abba ma ya zauna. Ajiyar zuciya Aslam ya sauk’e bayan ya gama sauraron Dad wanda ya k’arashe maganar shi da cewa “Zamu fara yanzu saboda mu samu mu gama akan lokaci kafin a gama Parking su Abba su tafi” A hankali ya juya ya kalli Abba kafin yace “Abba ka bari I’ll speak with Granpa, dan Allah don’t leave.” Murmushi Abba yayi ya mik’e daga kan kujerar da ya zauna ya k’araso inda yake kafin ya dafa kanshi tukun yace “Karka damu Aslam, ai bamu da nisa anytime kakeso zaka iya visiting, ni kaina i need some time with my daughter, wanda in muna nan na san Granpa ba zai barni ba, and ya dinga k’untata mata kenan, ni kuma from this time forward inaso In bata cikakken kulawa da happiness d’in da ban bata ba a baya, so we need some space from him, Daddy kuma he wants to leave ne saboda yaci ace Granpa ya fara rage abubuwan da yake yi. In bamu tashi mun tsaya munyi mishi haka ba, al amarin family d’innan ba zai tab’a daidaituwa ba! I hope u understand” Yayi maganan yana shafa kanshi, a hankali Aslam ya sauk’e ajiyar zuciya a karo na ba adadi sannan ya d’auke idanuwanshi daga kan Abba wanda tunda ya fara magana ya kafe shi dasu, a hankali yace “shikenan” sannan ya mik’e ya wuce zuwa inda ya fito yana cewa “zan fara daga Fatiha zuwa Nisa’i ayat 147! Someone should continue from were i stop.” Yana gama fad’in haka ya shige ya jawo k’ofar shi ya zuge. Dad ne yace “Abba ko zaku tafi tare, kasan yadda kuka saba da shi, and ga incidence d’in daya faru d’azu kar abun yai mishi yawa” “Ba zai yarda ba but let me try” Inji Abba, ya mik’e yana k’ok’arin shiga side d’in Aslam d’in. Dad ne yace mishi ya tsaya tukunna… Sai da suka tsara yadda za suyi, su mazan za suyi arba’in d’in sama, Huda kuma da Gwaggo Asabe za suyi ashirin d’in k’asa, kowa ya d’auka izu goma goma… Tukunna Abba ya nufi side d’in Aslam. Kamar yadda yace d’in kuwa sam Aslam k’in yarda yayi ya bishi hakan yasa ya hak’ura, ya zauna a d’akin yana d’an kwantar mishi da hankali, daga nan suka hau karatu a tare suka kammala nasu, dede ana kiran sallar azahar… A chan parlour ma Huda da Gwoggwo Asabe kusan tare suka kammala, Dad ne ma da Arshaad suka d’anyi delay don suna hawa sama Mommy taci gaba da kuka da kyar suka lallab’ata tukunna suka samu suka yi nasu. Sunyi addua sosai, kafin su samu ruwan zamzam aka tofa mata aka bata tasha aka shafa mata…. K’arfe hud’u dai dai komai ya kammala, duk sun shirya kaya kuma an gama jidesu, sai y’an tsirrai da za suna kwasa a hankali a hankali, waenda ba wani important bane!. Abba Dad da Daddy ne suka nufi wajen Granpa don yi mishi sallama.. Har sun kama hanya Daddy ya juyo ya cewa Arshaad “yaje ya samu Auwal yace masa ya kawo wannan Yarinyar nan sannan ya tabbatar komai d’inshi ya zama ready dan suna fitowa za a tafi” Da to ya amsa har ya juya ya nufi k’ofa ya jiyo wadda ta biyo shi da d’an sauri tana ki ranshi a hankali ya juyo yana kallonta Sai da ta k’araso ta d’anyi k’asa da kanta tana wasa da y’an yatsun ta tukun tace “Ina wuni.. Dan Allah ka ara mini wayarka zan kira Mama”. B’ata rai yayi kafin yace “Nima ba zan kulaki yanzu ba” Yana d’an turo baki kamar wani k’aramin Yaro. Dariya ma ya bata dan haka ta d’ab yi y’ar dariya mai k’aramin sauti kafin tace “To kayi hak’uri naga su Abba ne shiyasa kuma ka d’an yi nisa ne, da kana kusa da sai mu gaisa” Murmushi kawai yayi ya mik’a mata wayar sannan yace “bara yaje ya duba Auwal kar suyi ta jiranshi…” Huda ba k’aramin tashin hankali ta shiga ba dajin Mama na asibiti an sake admitting d’inta har yanzu, Sakina sai k’ok’arin kwantar mata da hankali take amman taki hak’ura, barema da taji wai an mata har eco, gashi ance Maman tana bacci ba zai yiu suyi waya ba!! Kwata kwata sai ta gaza kwantar da hankalinta, dan haka kawai tabi Ummu da ‘to’ bayan tace mata tayi hak’uri ta d’an Kara jira Amman tasa a ranta yanzu zata samu ya Arshaad ya kaita emergency d’in… Tana cikin wannan tunanin bayan sun gama wayar, wayar Arshaad ta hau k’ara! Kiranshi akeyi akai akai, gashi ya fita. Ganin an jera mishi sama da 20 misscalls ne ya sanya ta yanke shawarar kai mishi wayar. A bakin gate d’in gidan ta tambayi mai gadin ko “Ina Arshaad d’in yayi?” Opposite gidan da yake kallo wanda take ya nuna mata, dan haka ta nufi gidan....... Tun lokacin da Auwal ya dawo daga wajen Mom ake kai ruwa rana da Jalila har yau da suke shirin barin gidan! Dan tace “wallahi ba zata je wajen wata Gwaggo Asabe ba, kuma ba zata koma gidansu ba! Ta gano wayo yake so yayi mata ya yakiceta, ai tunda babanshi yace baya sonta ta san in dai ta yarda suka bar gidan babu ita tou shikenan magana ta k’are” Bikin ma cewa tayi “ta fasa zuwa” gashi ta amshe kud’i, tace “sai anje sabon gida an nuna mata d’akinta ta zuba kayanta tayi settling tukunna maybe taje” Tace kuma “In ya tilasta mata a yau sai ta tona mishi asiri, wallahi.” Auwal kamar yayi hauka, gashi an gama kwashe kaya ya san shi kawai Daddy yake jira ya kai Jalila sannan yazo su tafi, ga kuma batun ta na zata tona mishi asiri, kar fa Yarinyar nan ta jik’a mishi aiki!! A daa yana underestimating d’inta yanzu kam ta fara bashi tsoro gaskiya, he has to do something, duk da cewa Mom tace mishi ‘ya jira ta tana dawowa zata yi maganinta’ amman gaskiya he cant wait!! Yana tsoro kar kwab’arsa tayi ruwa, gara kawai ya k’are komai dan shi gani yake ma it’s like sun rabu da Arshaad d’in tunda ta sameshi dan haka tayaya zai iya breaking d’inshi!!! Takaici ya taru ya yiwa Auwal yawa, ga Jalila sai maganganu take yab’a masa… Da kyar ya iya controlling kanshi dan ji yake yi kamar yaje ya rufeta da duka ko ya samu sauk’i! A hankali very calm ya k’arasa inda take ya kamo hannunta Da sauri ta fisge hannun kafin tace “Ai wallahi anyi an gama babu k’ari!! Mayaudari kawai, haka kurum ka cuceni! Ga wasu zantukanka waenda har yau na kasa fahimtar alk’iblarka a kaina..” Cikin tsananin fushin da ya kasa dannewa yace “na cuceki ko kin cuce ni?? Ke kin San ko waye ni kuwa? Wallahi ba dan abunda na shirya akan ki ba ko a y’ar aiki ba zan tab’a yarda ki zo mini ba! Kina magana kamar irin dole d’innan nayi miki, Ina ce da yardarki kika bini har gidan? Zaki wani rainawa mutane hankali, wallahi ki bini a hankali tun ban fito miki a asalin Auwal d’ina ba!! Magana kad’an In anyi kice wani ‘za kije ki tona min asiri’ To bari kiji, tsaf! Zan iya cewa Daddy na maidake gida! In kulle ki anan yunwa ta kasheki daga baya in zo in fitar da gawar ki babu wanda zai ji labari, tunda itama uwarki kwad’ayi ya rufe mata ido ai bata cewa kowa kina nan ba! Stupid useless girl kawai! Banza wadda bata da daraja kwata kwata, Akuya ma ta fiki daraja tunda ita wani lokacin tana guduwa tana jan aji, ke kuwa ana ce miki kule za ki ce cass!.” Takaici da tsoro ne suka sanya Jalila fashewa da kuka, wani irin takaicin Umma take ji yana taso mata.. Shiyasa fa ita tayi ta dodging, har ga Allah irin rayuwar nan da yadda ta yarda dashi nan da nan ba hakan ta tsarawa kanta ba! Ita dai ta san tanada burin son auren mai kud’i, amma kalli yanzu yadda ta koma, duk ata dalilin biyewa son zuciyar Umma, gashi ta hanata zubar da cikin, kamar ba ita ta tsugunna ta haifeta ba! Tunda take ba a tab’a yi mata zagin daya girgiza taji haushinshi ba kamar kalar zagin da Auwal yake yi mata especially na yau dan ko ranar daya maidata gida bata ji ciwon zagin kamar na yau ba, kuma gaskiya ya fad’a!. Gashi yanda taga ya birkice tabbas zai iya aikata abunda ya fad’a d’in… Kuka take yi bil hakk’i da gaskiya. A take ta gama tsarawa kanta zata ce a zubar da cikin kawai ta koma wajen Umma, kowa ya huta. Ganin yadda tayi ladab ne ya k’ara bawa bawa Auwal kwarin guiwar aiwatar da abunda kwakwalwarshi ta shirya mishi yanzun nan, dan haka ya k’arasa inda take tsugunne shima ya tsugunna, fuskarshi ba alamun wasa yace “Look Jalila, let’s just get this done over with… Zan baki 5 million” Da sauri ta d’ago manyan idanuwanta tana kallonshi. D’aga kanshi yayi alamun ‘yes’ sannan yace “Miliyan biyar!” All I want you to do is ‘Kice cikinnan na Arshaad ne, kuma in sama da k’asa zasu had’e kar ki chanja maganan ki, ko a gaban waye, ke hatta uwar data haifeki inaso ki birkice mata kice na Arshaad ne kawai!’ Gaskiyar Maganar ya tsaya daga ni sai ke. Kar ki damu In komai yazo gangara ni zan san yadda zan yi, komai zai fita normal, ba zaki samu wata matsala ba, understood???”. Rarraba ido ta fara yi tana k’ok’arin yin magana, suka jiyo sallamar Arshaad. D’agowa sukayi dukkansu suna kallon hanyar shigowa. Cikin takunshi ya k’araso cikin parlour… Wani killer smile Auwal yayi kafin ya mik’e tsaye yace “D’an halak! Maganar ka muke yi” Cikin nutsuwa Arshaad d’in ya k’araso inda suke, kallon Jalila yayi yaga yanda take kuka, a ranshi yana mamakin ina Auwal ya samota haka, gashi sai kuka take yi… Ganin ba wannan ne ya kawo shi ba yasa ya d’auke idonshi a kanta ya maida kan Auwal d’in sannan yace “Daddy is waiting, infact everyone, for you, kayi sauri dan yace karka bari yazo ya sameka a nan!” Yana gama fad’in haka ya juya ya fara k’ok’arin fita. Da mamaki Auwal yake kallonshi da Jalilan wadda tunda Arshaad d’in ya fara magana take kallonshi, Ganin arshaad d’in na shirin fita ba tare da ya ma sake kallon Jalilan ba yasa Auwal yin ta maza ya zagaya ya tsaya a gaban shi sannan yace “Saurin me kake yi? I’m just trying to clean up your mess here fa, amman kayi kamar ma baka santa ba, ko In barta ta tafi wajen su Abba ne?” D’an dakatawa Arshaad yayi sai kuma ya juya yana kallon Jalilan.. Da ido Auwal yayi mata signal d’in da ta kasa ganewa, ita dai kawai sai ta mik’e, kamar an tsoma ta a ruwa jikinta na d’an rawa. Murmushi Auwal d’in yayi sannan ya zagayo yace “Talk mana Jalila, ko tsoronshi kike ji yau kuma?” Kame kame Jalila ta fara yi, ta rasa ta Ina zata fara dan Bata san me zata ce ba, gashi duk da halin da take ciki tunda taji Auwal ya ambaci miliyan biyar ta rikice, hali zanen dutse!. Don haka tace “Daman nazo ne akan maganar mu” Tayi maganar jikina na d’an karkarwa dan har yanxu k’irjinta bugawa yake yi… yau ce rana ta farko data tsaya ta k’arewa Arshaad kallo!! Ita dai tun lokacin da yake zuwa wajen Hudan ta san yana burgeta kuma yanayin shi, maganarsa, tsayi da k’amshin turarenshi suna mugun k’ara kid’imata! Kawai dai ita ta san tana so Arshaad har cikin zuciyarta, amman yau data tsaya ta k’are mishi kallo ta sake rikicewa kuma ta tabbatar idan har bata sameshiba to ko dai ta mutu ko kuma ta shiga hauka… K’irjinta in banda bugawa babu abinda yake yi, gashi ya tsareta da dogayen shanyayyun idanuwanshi, cikin tsare gida yace “Wacce magana kenan?? Do i know you?” Wata dariya Auwal ya saka kafin ya k’araso yana cewa “Okayy!! Bari in yi maka dalla dalla.. Maganar cikinka wanda ke a jikinta! Shi ta biyo ka ku k’arasa.” Arshaad zuwa yanzu yazo wuya! Don haka ya yanke shawarar cin uban Auwal dan ya lura bayan rainin hankalin da yake yi mishi, harda hauka ma ya fara damunshi kwana biyu, gara a yita ta k’are ko zai dawo hankalin shi, in hauka ya za ayi ya d’auko Yarinyar da bai tab’a ganiba a rayuwarshi ya hau yi mishi wani maganan banza da wofi??! A fusace ya juyo yana shirin yin kan Auwal, sukaji k’arar fad’uwar abu, da sauri duk suka juya suna kallon k’ofa.. Arshaad, ya san yana da gaskiya amman kalar kallon tuhumar da Hudan take yi mishi da kuma yanayin fuskantar, ne ya sanya gabanshi yayi mugun fad’uwa sannan wata zazzafar zufa ta hau keto mishi, tabbas ya san taji shirmen da Auwal ya gama fad’a yanzu. Auwal kam tsayawa yayi yana kallonta yana mamakin tsananin kamanninta da Abba da Aslam! “Who’s she!?” Ya fad’a a hankali ba tare da kowa ya jishi ba. Chan kuma sai ya tuno da case din y’ar gidan Abba da har ta kaiga kulle su Mom d’inshi a cell! Antake kwakwalwarshi ta d’au chaji, don haka a zafafe ya nufeta, daman neman ta yake yi ya kora mata warning!! Jalila kuwa tsorone ya rufeta ganin Huda, a tunanin ta Umma ce ta fad’i inda take, su kuma suka zo har da su Kaka tafiya da ita, dan haka karkarwar jikinta ya tsananta ba abunda take tunawa irin auren ta da Mati mai wanki ta san yanzu kam babu fashi!. Cikin zafin nama Auwal yana karasawa inda Huda take tsaye yace “Hey! Couz… You must be Huda right? Inaso kije ki samu uban ki kice mishi......” Cikin katseshi Arshaad wanda shima ya k’araso inda take yanzun yace “Huda lets go don’t mind him, he’s crazy!! Muje kawai za mu yi magana a waje.” Ya k’arashe maganar yana durk’usawa don k’ok’arin d’aukar wayarshi data jifar a k’asa. Hudan ita kanta bata san tana da kishi irin haka ba, sai yau. Wato ba zai ma iya fuskantanta a gaban Jalilan ba?! Gashi yadda duk ya rikice jikinshi yana d’an karkarwa yasa ta d’aura ayar tambaya akanshi… Ita Arshaad zai yiwa haka? Why? Of all people kuma yayarta!!! Bata san lokacin da ta fashe da wani irin kuka ba!. Ai kuwa a rikice, Arshaad yace “Oh nooo, Huda dan Allah kar muyi haka dake mana, na rantse miki da girman Allah ban san wacece waccar ba! Ban tab’a ganinta ba a rayuwata, wallahi! Muje waje we ‘ll talk outside.” Yai maganan yana k’ok’arin kama hannunta.. Da sauri ta fisge cikin kuka tace “Don’t touch me! Ai dole kace baka santa ba mana, Ya Jalilan ce baka sani ba? Daman Mama tace min rannan kaje kana nemanta, kuma nima naji Umma ma rannan suna wani magana da Anty Zainab dana kasa fahimta a kanka kaida Ya Jalila. And if baka santa ba mai take yi a nan ya akayi ta san gidanku da ni kaina ban saniba? Ana tunanin tana gidan Anty d’inta a gida ashe tana wajen ka! I trusted you,I tot.....” Arshaad kam zuwa yanzu ranshi yayi mugun b’aci dan a tunaninshi ko Sakina ce zata fad’awa Hudan wannan maganar a kanshi bai ci ache ta yarda ba, balle a bakin mutumin da bata tab’a gani ba sai yau! Dan haka cikin katseta yace “Ba kiyi trusting d’ina ba Huda! Tunda gashi har kin d’auki maganan da aka fad’a miki a kaina… Rantsuwa ta k’arshe da zan yi miki shine ‘wallahi ban san Yarinyar nan ba!’ Mutum d’aya na sani a gidanku age mate d’inki itace Sakina. Kuma ban san wanne Arshaad d’inne yaje nemanta gida ba rannan d’in da kikace, amman bani bane ba!. Maganar su Umman shima i don’t know anything about it, wallahi!. Anyways Na gode da irin shaidar da kika yi mini.. Hudan aure za muyi ya kamata ace kinyi trusting d’ina tunda as far as i know inda ace ni d’an iskane da tuni ke zaki fara fad’a ba wai ita ko shi ba.” Yana gama fad’in haka ya juya ya fita dan in ya ci gaba da tsayawa a wajen zai iya yin abunda zai yi ending up yana regretting… A hankali Hudan ta k’arasa ciki wajen Jalila ta kama hannun ta kafin tace “Ya Jalila” Cikin kukan makirci Jalila ta fashe da kuka ta rungune Hudan kafin tace “Hudan Allah da gaske ne abunda Auwal ya fad’a yanzu, gashi na kasa fad’awa kowa, ban san ya zanyi ba! Arshaad ya cuceni.” Ta k’arashe maganar da wani mugun kuka, don ta lura Hudan ta yarda da ita,,dukda kuwa har yanzu tana cikin rud’u akan ‘’me Hudan take yi a gidan’ Dan kalaman Auwal da yadda yace mata cousin ya sake dilmiyar da tunanin ta… Amman yanzu ba wannan ne a gabantaba, raba Hudan da Arshaad shine first! Ga kuma zancen miliyan biyar! Don haka dole ta ajjiye komai a gefe ta duk’ufa ta cimma burinta. Da kyar Hudan ta lallasheta, ta samu tayi shiru.. Rasa abunyi yasa Huda tace mata “bara taje ta dawo” da taso ta tafi da ita, amman tak’i, dan haka ta mik’e tace “tana zuwa, tukunna sai su san me za suyi” Cikin share ragowan hawayenta ta d’agawa Hudan kai, Hudan kuma ta fita a zuciyarta tana rayawa yanzu zata kira su Ummu dan ba zata iya wannan abun ita kad’ai ba! dole a kwatarma Jalila hakk’inta, tana tafe zuciyarta na tafarfasa, ita kawai idonta ya rufe da kishi har ya kaita ga kasa yin lisaafi mai kyau a kwakwalwarta. Jalila na ganin fitar Huda ta share hawayenta ranta fess! Sannan ta mik’e ta k’arasa inda Auwal ya daskare yake k’ok’arin hada 1+1 akan alamarin da ya gudana yanzun nan dan in dai shi ba dak’ik’i bane ba tou abu na farko daya fara fahimta shine ‘Arshaad Huda yake dating!’ And tabbas bai san Jalila ba, to who….. Muryar Jalila wadda ta k’araso yanzu ne ta katseshi jin tana cewa “Nayi duk abunda kace, yanzu abunda nakeso da kai shine ka kawo miliyan d’aya, ragowar kuma in aiki ya kusan kammaluwa, dan..” Shak’ar!! Da yayi mata ce ta katse mata maganar tata, cikin d’acin zuciya da k’arfi yace “Who are you?”. BULAMA ✍️ Cikin fushi tace “kafi kowa sanin me kayi! Kuma ina so ka sani Allah sai ya bi ma Hudan hakkinta dan wallahi kaji na rantse ita d’in son gaskiya da tsakani da Allah take yi maka! Amman duk da hakan zan yi k’ok’ari inga na cire mata kai a ranta!. Sannan ga sak’o ka gayawa Abba! ‘ in duk duniya ce zata taru a kaina to ba zan yarda ba!! Nima ina nan zuwa karb’arta, daganan in Mahaifinsa yaga dama ya kulle kaf jinsina ba wai iya danginaba!!”. Tana gama fad’in haka ta wuce ta barshi nan, a daskare!! Da kyar ya iya tattaro ragowar kuzarinsa ya fice shima a d’akin, saboda iya yadda yaga ta fita tana layi ya tabbatar mishi ba zata iya kai kanta ko da nan da gate ba! Sai dai kuma, ko da ya fita d’in sai bai ganta ba bai ga alamartaba kamar wadda tayi layar zana ta b’ace! Duddubawa ya hau yi har buildings d’in gefen emergency amman babu ita babu alamar ta! Abun ba k’aramin sake d’aga mishi hankali yayi ba dan babu inda bai duba Mama ba amman bai ganta ba har unguwar su yaje a tunanin shi ko ta koma amma tun kafin ya k’arasa gidan ya hango ana (Baba) datsa datsa kwad’o a gidan, ya fitar da machine da alamun fita zai yi. Sanin da yayi in dai napep ta hau to ba lalle ta rigashi isowa gidan ba ne, ya sanyashi zaman jiranta, anan cikin mota! Sai dai almost 2 hours amman bata dawoba. Zuwa yanzu kam hankalinshi ya kai k’ololuwar tashi!….. …….Tun farkon had’uwar shi da Hudan yake k’ok’arin toshe duk wata hanyar da zata kawo musu matsala, yanzu haka ya ware millions zai siya musu gida, ta yadda In su Mammy sun zo ba zasu samu abun kushewa ba balle har Granpa yaji ya hana, su Abba kuwa ya san su zasu zo nema mishi aure, so gidan uncle Muhammad ba zai zama matsala ba! Dan anan aka shirya za a had’u dan ba daban jiran Dad d’in da suka tsaya yi ba ma to da tuni sun zo an gama magana. Har ga Allah ba zai tab’a iya rayuwa babu Hudan ba, kwata kwata, shi baya jin ma a tarihi akwai wani mahaluk’in da ya tab’a yiwa wata kalar son da yake yiwa Huda since day 1, gashi kuma yau Mahaifiyarta da kanta ta kalle shi tace ‘zata rabashi da ita!’ Bai ankaraba kawai yaji hawaye yana wanke mishi fuska! Sunayen Allah ya fara ambata yanayi yana kuka, kamar k’aramin Yaro. Da kyar ya samu zuciyar data yunk’ura mishi ta d’an lafa. Ganin babu Mama ba labarin ta, ya sanya kawai ya yanke shawarar komawa gida yayi wanka daga nan ya kira Ummu a san abunyi! Dan in ba ruwa ya samu ya sakarwa kanshi ba baya jin kalmar ‘A’ zata iya futowa daga bakinshi a halin da yake ciki........... BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 37 Kamar yadda Arshaad ya tsara, sai da ya lallab’a yayi wanka da kyar tare da hutun awa d’aya! Tukunna yaji d’an dama dama, cikin tsantsar mutuwar jiki ya lalubo wayarshi ya danna kiran Ummu. Sai da ta kusan katsewa tukunna aka d’auka, a tunanin shi ko hayaniyar biki ne yasa ta jinkirin amsawa sai dai kuma tana d’auka yaji hayaniya da koke koke! Cike da fargaba ya hau tambayarta, nan take gayamishi..... ....”Suna shirin shigowa Kano, wani Abokin Junaidu ya kira Baba! Bayan sun gaisa ne yake ce mishi ‘dama ya kira ne a kan maganar Junaidu! Wai an sake shi tun satin baya da ya wuce sai dai kuma babu irin kalar binciken da basu yi ba amman an rasa shi! Wajen kwana uku kenan yau. Lokacin da aka sallameshi yayi mishi waya yace ‘zai zo gidanshi, ya d’an kimtsa tukunna ya wuce Kano, bayaso ya sanar da kowa dan surprise zai yi musu’. Yayi ta zaman jiran nashi amma shiru! Sau daga baya yaji labarin accident da aka samu a garin guda uku ata wajajen k’iri k’iri d’in! mota biyu ta y’an kasuwa ce, d’ayar kuwa ta prisoners d’in ne waenda aka saki sai dai kuma duk sun k’one k’urmus! Dan ko iya tantancesu ba a yi! Yayi shiru ya tsaya bai fad’a musu ba domin yanaso yayi bincike sosai tukunna dan shi tunanin shi yana bashi ba lalle har da Junaidun ba amman duk wani investigation yana tabbatar da akwai gawar Junaidun a ciki! Shiyasa kawai ya yanke shawarar kira ya fad’a musu..’ Gashinan yanzu haka a mutuary in babu damuwa wasu a cikinsu suzo dan ana da buk’atar su wajen tantance gawar da kuma ragowar abubuwan da ya kamata!!’.” (Da kyar Baba ya iya k’arasawa gida ya d’auki kud’ad’e da atms da abun buk’ata ya mik’a Ja’afar wajen K’asimu suka kama hanyar Lagos! Suma su Abba Madu suna ajjiyesu a gidan Baaba Talatu ya juya shi da su Ya Jamilu. Yanzu haka sun kama hanyar Lagos d’in.) “Innalillahi wa inna ilaihirrajiun” Shine abunda Arshaad yayi ta maimaitawa, yana jiwo Sadiya tana ihu tana wallahi “sai tayi sharia da y’an sanda da sojojin da suka rik’e mata Yaro bayan sun gano bashi da laifin komai! Inda ace sun bari ranar su Madu sun dawo da shi ai da duk haka ba ta faru ba! Allah ya isanta” Baba Talatu ce ta hau yi mata fad’a, tana cewa “Bata da tawakkali ne? In Allah ya riga ya tsara abu dole sai ya faru! Ta daina yi mishi kururuwa da ihu…” Amman inaaa, bata ji bata gani sai rafka kuka da kururuwar kawai take yi. Jin yadda gidan ya hautsine ne ya sanya kawai yanke shawarar zai nemo Mama da kanshi in shaa Allah, dan haka yayiwa Ummu gaisuwa, kafin ya kashe wayar. .............. Kusan a tare motar Abba da ta Aslam suka k’araso cikin estate d’in! Basu shiga ko wanne gida ba suka yi parking a babban parking lot d’in estate d’in kamar had’in baki. Abba ne ya fara fitowa kafin Aslam, yana k’arasowa inda yake yace “Ka kaita wajen Gwaggo Asabe. Zan nemaku zuwa anjima.” “Ok” Shine abinda Aslam d’in yace sannan ya juya ya fara k’ok’arin bud’e inda Huda take zaune tana kuka har yanzun, shi kuma Abba ya juya ya nufi gidan Ummi. Hannunta ya sake fincika bayan ya bud’e motar ya fito da ita!! Sannan ya zaro wayarshi ya danna kiran Gwaggo Asabe ya kara wayar a kunnenshi… Fisge hannunta tayi da duk k’arfin ta! Sannan ta juya ta bud’e motar ta d’au wayarta tana dubawa dan ita a nata tunanin ma ta fashe ne saboda yadda Aslam d’in ya had’a wayar da hannunta ya runtse a nasa hannunt tun lokacin da yace ‘Mama ba zata tafi da ita ba’ har sanda ya kaita mota…. Rad’ad’i da zugin da hannunta yake mata da kuma tsananin tashin hankalin da take a ciki ne suka hanata d’aukar wayar data fad’i daga hannunta tun shigar ta motar, sai yanzu Ajiyar zuciya ta sauk’e ganin bata yi komai ba hakan yasa ta rufe motar ta d’an juyo da niyyar kiran Mama. D’an satar kallonshi tayi, ganin ya tsareta da dara daran idanuwanshi ne ya sanya ta yin k’asa da kanta sannan tace “Ko baka ja ni ba zan bika! Wayata kawai na d’auka” Tayi maganar cikin muryar kuka. Murmushin rainin wayo yayi mata, kafin yace “Better!” Sannan ya juya ya fara tafiya yana cewa “Gwaggon ta fito, yanada bak’uwar da zai bata, ta same shi a gate!” Hudan kuwa wata zuciyar ce take ce mata ‘ta d’iba a guje ta fice a estate din!’ Amman kuma ta na juyawa tayi ido hud’u da sojoji har hud’u a wajen gate d’in suna zazzaune. Wani sabon kuka ta fashe da shi kafin ta durk’ushe a wajen abun tausayi… A hankali kuma sai ta d’ago wayar tata ta fara k’ok’arin kiran Mama tana adduar Allah yasa taga purse d’inta ta d’auka a cikin d’akin, dan lokacin da Aslam ya jawota purse d’in ta fad’i a k’asa. Aslam kuwa jin da yayi kamar ba mutun a bayan shi ne ya sanya ya juyo dai dai ita kuma da d’ago kanta sukai ido biyu! A zuciye ya taho gadan gadan yana nad’e hannun rigar shi, Ta san me yake shirin yi hakan yasa ta mik’e da sauri, kafin ya k’araso ita tayi hanyar da taga yayi….. Rashin kwarin jiki da kukan da taci ne yasa har yazo ya gota ta ya zamana ita take binshi a baya. Kamar yadda suka yi a bakin Gate d’in ya tarar da Gwaggo Asabe tana jira, nuna mata Hudan kawai yayi sannan yace “Zuwa anjima zan kiraki!” Da mamaki tab fuskarta take kallon Hudan ganin yadda yake kallonta ne ya sata kawai jan hannunta suka shige ciki shi kuma ya nufi gidan Mammy a falon ta na sama ya samu doguwar kujera ya kwanta, zuciyarshi fal da tunani barkatai. ....... A parlourn k’asa Abba ya samu Ummi tana shafa wa jan lallen da aka gama cire mata yanzu mahallabiya. Sallamarshi ce ta katse musu k’us k’us d’in da suke yi ita da Mom wadda ake k’arasa saka mata nata lallen yanzu. Da sauri ta d’ago jin muryar shi, su na had’a ido ta sakar mishi murmushi sannan ta mik’e ta nufe shi…. Bata damu da Mom da mai lallen da suke parlourn ba! Tana isa gareshi tayi hugging d’inshi tana mai yi masa sannu da zuwa…… Binta kawai yake yi da ido, tanata karairaya… A hankali yasa hannu ya zarota daga jikinshi kafin yace “Ki kawo mini abincina sama, kaina yana d’an yi min ciwo.” Murmushi ta kuma saki kafin tace “ok dear” Ta juya, shi kuma ya kama hanyar b’angaren shi. Sai da taga hayewarshi sannan taje wajen Mom ta rad’a mata wata magana, a take suka kwashe da dariya kafin Mom d’in tace “ki tabbatar kin yi amfani da abunda na baki.” Dariya tayi sannan tace “da gudu ma kuwa” kafin ta nufi hanyar kitchen tanata rawar kai! A nutse ta sake gyara kulolin har da ruwan tea tayi mishi warming da duk wani abunda ta san zai buk’ata. Haka nan ta had’o abincin a k’aton baske tayi saman itama. Abba yana shiga d’aki ya kira Dad…bayan sun gaisa ya zayyanewa Dad d’in komai bai b’oye mishi ba! Dad was very shocked daga jin Abba yana da y’a da Maryam!! Tabbas shima ya na zargin waenda Abban yake zargi… Maganar Abban ce ta katse mishi tunani jin yana cewa “Yaya kayi hak’uri da abunda zan aikata, dan Wallahi ko waye yake da hannu, a cikin lamarin nan zan hukuntashi!!Ba zan duba relationship d’in ka da shi ba, gaskiya.” Ajiyar zuciya Dad ya sauk’e sannan yace “Kayi kwakkwaran bincike, kafin In k’araso, in shaa Allah ni da kaina zan tayaka hukunta masu laifi….. Daman jikin Mommy ne ya d’an tsaidamu amma da tuni mun iso ma.” A haka Ummi ta shigo ta sameshi, yana ganinta ya yiwa Yaya sallama ya katse wayar. A hankali ta k’araso ta ajjiye kafin cikin nutsuwa da karairaya ta hau serving nashi. Sai da ta gama ta ajjiye mishi a kan kafet sannan ta d’ago hannuwanta tace “Kaga k’unshi da nayi saboda na san kanaso, in je a zana min bak’in flower ko ka fi son shi ahaka??” Fararaen hannun nata ya kalla da jan lallen ya yiwa matuk’ar kyau amma sai dai shi memokon yaga kyan shi ma, gaba d’aya sai yaji ya tsani jan lalle a take a lokacin!. “Ki barshi haka.” Shine kawai abinda ya iya fitowa daga bakinshi. Mamakin yadda idanunsa suka kad’a suka jazirr!! take Chan kuma sai tayi murmushi..yanayin yadda ya shigo jikinshi a sanyaye, da kuma yadda yanzu taga yanayinshi tabbas ta gane mai yake buk’ata! Hakan yasa ta fara k’ok’arin mik’ewa dan ta samu taje ta yi amfani da abunda Mom ta bata. “Na had’u da Maryam yau...” Wata mahaukaciyar razana tayi kafin ta koma ta zauna kamar wadda aka jawo da k’arfi!!!. Kafeta yayi da idanuwanshi… Yana ganin yadda gaba d’aya ilahirin jikinta yake karkarwa ga wata uwar zufa da take keto mata dukda kuwa sanyin ACn da ya ratsa ko wacece kusurwa ta d’akin. Ya akai suka had’u? A ina suka had’u? Sun yu magana kenan? Ta fad’a mishi komai?… Sune tambayoyin da suka taru suka sake gigitata! D’agowa tayi za tayi magana, sai kuma taga yadda ya zuba mata lulu eyes d’inshi da sukai jaa, wanda sai yanzu ne ta gane b’acin raine, ashe. Tattaro duk wata basira da wayon da Allah ya bata tayi kana ta had’a da y’ar ragowar jarumta da kwarin jikinta, kafin tace “Wannan kuma matsalarkace! Tunda har ka bijirewa Mahaifinki wanda yayi ik’irarin tsine maka a kanta, to me yasa ni zan tsaya damuwa da kishi?” Tana gama fad’in haka ta fara k’ok’arin mik’ewa, dan tabbas In taci gaba da zama to nan da nan zai b’aro jirginta. Dukda cewa bata da tabbacin Maryam d’in ta gaya mishi sunada baby tare, amman hatta muryarta rawa take yi, sannan idanuwanta duk sun kawo ruwa! Ga shi kuma Abban ya tsare ta da ido, it’s like akwai abinda yake son fahimta… Dan haka ta mik’e tayi hanyar k’ofar fita da sassarfa. Abinda bata saniba shine tun a reaction d’inta na farko Abba ya riga ya b’aro jirginta, gashi kuma yanzu rashin wayonta na son barin d’akin ya sake tabbatar mishi! Dan haka yayi hanzarin mik’ewa shima, ya rigata isa ga k’ofar ya shiga gabanta ya tsaya!. Kasa d’agowa tayi ta kalleshi.. He can feel yadda numfashinta suke korar juna daga inda yake tsaye!. Juyawa kawai yai ya murza key d’in ya zare shi, sannan ya cilla cikin aljihun wandon shi. A take razana da firgicin da take ciki suka sake hauhawa! Tun ba ma daya juyo taga yadda ya tamke fuska kamar bai tab’a dariya ba, zata iya rantsuwa tunda aka haifota duniya bata tab’a ganin Abba a irin wannan yanayin ba. Cikin dakakkiyar muryar da bata da alamun wasa a cikinta yace “Ummi!! A cikin biyun nan, inaso ki zab’i d’aya.” Yayi maganar yana mata alamu da y’an yatsun hannunshi na dama daya d’aga mata su daidai setin fuskarta. Na farko Ko ki gaya min gaskiya tun farko abunda ya faru…yadda kuka yi kuka rufe ba tare da kowa ya ji ba, da yadda aka y munanan kalaman da ban san na rubuta suba suka isa ga Maryam, Inason jin komai da komai karki b’oye min ko, alif. Ko kuma (na biyu) In yi miki dukan mutuwar da ko Mahaifiyar ki in da ace zata dawo duniya ba lalle ta shaidakiba, sannan in k’ara miki da saki, kuma in kulle ki dake da duk wanda ya taimaka miki.! Sannan inaso ki sani sharia zan yi ta gaskiya yadda ko Granpa bai isa ya kwatoki ba wallahi, idan kuma ya tilastamin to tabbas zamu iya samun matsala da shi dan ba zan iya yi mishi biyayya wajen wofantar da hukunta waenda suka raba ni da y’ata ba!.” Wani irin mahaukacin bugawa k’irjin Ummi ya hau yi, especially ma da taji zancenshi na k’arshe. Amma Maryam an yi shegiyar mata!! Wato fad’a mishi tayi kenan! Yanzu Ina mafita?? K’aryatawa za tayi ko kuma ya zata yi? Itakam yau ta shiga tara ma ba uku ba! Ga shi ba Mom a kusa. “Innalillahi wa inna ilaihirrajiun” Ta fara maimaitawa tana neman taimakon Ubangiji, dan tabbas shi kad’ai ne zai iya cetonta a hannun Abba a yau. Tsawar da ya daka mata ne, ya katse mata tunanin, a take ta durk’ushe a wajen ta fara kuka. “Ba kya ji na ne!!!!” Ya fad’a cikin hargowa har wata kwalla tana zuba daga idonshi tsabar b’acin rai. Shiru tayi in banda kuka ba abunda take yi. Dukan mace kwata kwata baya cikin tsarin Abba But Ummi left him with no other choice, bai san lokacin da ya fincikota ya mik’ar da ita tsaye ba! Bata gama sosa, gefen wuyanta da takeji kamar ta yanke sakamokon janyotan da yayi da hannun rigarta ba, taji sauk’ar wani irin gigitaccen Marin da ya kusan d’auke mata nunfashi, bata gama dawowa dede ba ya sake d’auke ta da wani! Cikin tsananin b’acin rai yace “na fahimci option 1 kika d’auka!” Sannan ya juya ya nufi wardrobe da sassarfa. Da sauri Ummi wadda take ji kamar an yi mata b’arin wuta a kumatunta duka biyu ta k’arasa jikin k’ofar tana bubbugawa tana neman taimako, dan ta lura Abba baya a haiyyacinshi… Babu wanda ya jiyota, dan k’ofofin gidan gaba d’aya sound proof ne, ko bayaga haka ma yanayin girman gidan ba lalle a iya jiyota ba! Bata ankara ba taji ya janyota da dukkan k’arfin shi ya zuga mata belt…wani mahaukacin ihu tayi ta fad’a kan gado ta rarumo blanket da quilt d’in kai ta k’udundunu a ciki. Cikin zafin nama ya fincike bargunan yayi cilli da su sannan ya shak’o ta, kafin yasa dukkanin k’arfin da Allah yayi mishi ya fincikota daga kan gadon ya tsayar, still yana rik’e da wuyanta da ya yiwa muguwar shak’a! Ita ya shak’e amman yadda idonshi yayi jaaa zaka d’auka shi aka shak’e!. Cikin d’acin zuciya yace “na fasa sakinki da kaiki kotu Ummi kashe ki zan yi kowa ya huta!!” Ummi kuwa ganin Abba yana shirin kaita lahira ne ya sanya ta fara dukan hannunshi, tana tarin wahala, da y’ar ragowar muryar data ragemata tayi amfani wajen cewa “Za.z.Zan fa ff fad’a” Tana kallon kwayar idanunsa waenda take hango tsananin tashin hankali a cikinsu. Jifa yayi da ita sannan cikin b’acin rai ya juya mata baya kafin yace “Ina jinki, kuma kar kiyi kuskuren b’ata mini lokaci, dan ba zan baki wani chance d’in a karo na biyu ba.” Ajiyar zuciya kawai take ta faman sauk’ewa mai had’e da tarin wahala… Jin shiru ya sanya shi juyowa yana mata wani irin kallo. Ganin haka yasata fara magana “Ranar bayan mun ji labarin sakin da kayi mata…. Muna zaune da ni da Mom, kawai sai ga Daniel ya zo a rikice….dama duk wani abu idan ya faru ya kan fara fad’a mana kafin Granpa, in na dannewa ne mu danne ko kuma mu sakashi ya juya zancen sai mu bashi kud’i. To kamar kullum haka ranar ma yazo mana da takardar sak’on Maryam, yake cewa ‘k’anwarta ce ta kawo kuma tace dan Allah a baka tana waje tana jira’ Ba komai ne a cikin takardar ba fa ce ‘Baka hak’uri da take yi akan duk laifin da tayi maka har ya kaika ga d’auke k’afa wanda ita bata san laifin ba! Sannan tana buk’atar ka a asibiti zata haihu.’ A lokacin kusan sumewa nayi, dan ni ko had’a shimfid’a baka yi da ni amman ita Maryam gata harda ciki zata haihu! Kuma na tabbatar muddin kaji labarin cikin nan to baza ka tab’a yarda mu koma ba, sannan definitely zaka mayar da ita tunda saki d’aya ne a tsakanin ku. Rasa yadda za muyi mukai. Murnar mu gaba d’aya sai ta koma ciki...... Tun muna Yara Allah ya yiwa Adama baiwar kwafar duk wani zane da rubutu duk kuwa wahalarshi tsaf zata kwafe tayi irinshi exactly.. Ganin yadda duk na rikice ne yasa ta ce mini ‘inje In d’auko littafin ka’ Na fahimci me take shirin yi shiyasa da gudu, na fita naje d’akinka na kuwa ci sa’a baka nan hakan ya bani damar d’auko diary d’inka. Da farko da muka zo, mun tsara ne akan zamu rubuta mata ‘ta jiraka nan da 2 weeks in shaa Allah in ka gama settling da Granpa, zaka je ka sameta’ Kaga kafin nan tunda haihuwa zata yi already ta fita iddarka, ni kuma sai in san yadda zan yi in ja hankalinka mu koma, kuma mun tsara zamu tura wani yaje ya aure Maryam d’in kafin mu dawo tukunna mu saka ka fahimci kana da y’a ba tare da sunan mu ko laifin mu ya fito ba! Amman karanta diary d’inka da muka yi ne ya sake hautsina komai! Domin kuwa Abba kwata kwata baka da plan d’in yin rayuwa da ni, you promised maryam (a diary d’in) cewa nan da 1week zaka je ka maida ita, kuma ko parents d’inta sun yarda ko basu yarda ba zaka d’auketa ku sake barin k’asar! Har sai lokacin da Allah yayi Tou were willing to leave and risk everything for her, a plan na future Dinka kwata kwata babu ni a ciki!! And you wrote it ‘a dalilina ne yasa ka tafi ka bar Nigeria, har iyayenta suka kasa hak’ura, suka biyoka, shi kuma Granpa ya yanke wannan hukunci, so I have to pay the price!’ Although ban san menene price d’inba tunda baka rubutaba, but na fahimci saki ne, tunda yadda kake tsarawa..y’ay’an da zaku haifa da sunayen da zaku saka musu, da irin tarin addu’o’in ka na burin samun babys daga gareta, na fahimci baka da tsarin zama da ni! Kuma hankalina yayi matuk’ar tashi da naga kwad’ayi tare da kalar son da kake yiwa y’ay’an da zaku haifa( kai da ita), shiyasa kawai muka yanke hukuncin rubuta mata takardar da muka aika Daniel ya kaiwa k’anwarta!. A baya tunani na son Maryam kakeyi, amman karanta diary Dinka da nayi tun daga farkon had’uwar ku har k’arshe bayan tafiyar Daniel, shi ya tabbatar min da cewa haukan somta kake yi Dan haka with her in your life, Abba banida chance kwata kwata.” Matsowa tayi kusa dashi ta kama hannunshi kafin tace “Abba put yourself in my shoes, yadda kakeji akan Maryam wallahi nima haka nake ji a kanka! Shiyasa da naji plans d’inka hankalina bai ida kwanciya ba har sai da muka had’u da mammy ta rakamu aka rufe maka baki akan batun mayar da ita d’in da kace zaka yi sannan aka cire ta a ranka gaba d’aya! Sai dai kuma shekara d’aya kawai Allah ya bawa addu’o’i n namu ikon yin tasiri a kanka domin har yau zancenta kakeyi ba dare ba rana kuma na tabbatar ba dan ta yi aureba da tuni tana a gidan nan ni kuma na san karshenta zuciyata bugawa zata yi!”. Cikin kuka tayi k’asa ta durk’usa a gaban shi still tana rik’e da hannuwanshi kafin tace “Duk wani abunda kake buk’atar ji, gashi na fad’a maka, har wanda bai kamata kaji ba duk na fad’a maka Abba Amman inaso ka cire son rai ka duba lamari na, wallahi duk kai ka janyo komai! Komai kuma da nayi, na yishi ne saboda kai, saboda son da nake yi maka da kuma burin inga mun kasance tare har abada!. Dan haka, dan Allah ka dube ni da idon rahama ka yafe min, ni kuma na yi maka alk’awarin ba zan sake wani attempt d’in tab’a rayuwar Maryam ko y’ar ta ba! Tun farko ma da ace baka yi abinda kayi ba, da ba azo nan ba.. Inda ace ka bani time d’inka tun lokacin farkon aurenmu da ba zan yi attempting aika mata da sak’o ba wanda har yayi sanadiyyar da ya sanya ni karanta diary d’inka. A yadda nake sonka inda zaka dinga kula da ni, sannan ka min alk’awarin adalci da zama dani har abada, wallahi Abba da zan rufe idona In danne duk wani kishi, in barka da Maryam Amman yadda ka nuna gaba d’aya baka da plan na rayuwa dani shi......” Hannun shi da ya warce a cikin nata ne ya sa ta had’iye ragowar maganganun data d’ebo! Cikin b’acin rai yace “Ummi! ban tab’a ganin selfish being irin ki ba!. And FYI ba saboda son da kike yi mini bane ya sa kika aikata waennan abubuwan wake up!! Saboda tsananin son da kike yiwa kanki ne ya saki aikata hakan! Kinga dai Ina son Maryam fiye da raina ko?? Amman wallahi inda ace tun farko ta nunamin bata sona kuma akwai wanda take tsananin so, kamar yadda na nuna miki, tou da tabbas zan iya hak’ura da ita, saboda farincikin ta!! That is love, ba wannan shirmen naki ba.” Yana gama fad’in haka ya warce k’asan rigarshi da ta kamo ya wuce ya bud’e k’ofar ya fice a d’akin ya barta nan durk’ushe tana kuka tana kiran sunanshi….. Mom tana zaune a falon da k’unshinta, taga sauk’k’owar Abba… Da k’arfi k’irjinta ya buga! Yadda taga ya sauk’o ya wuce fuuu ranshi a mugun b’ace ko adawo lafiyanta bai amsa ba. Gaba d’aya sai ta kasa nutsuwa… kusan minti biyar ta bayar amman shiru ba Ummi ba labarin ta, dan haka ta yanke shawarar cire lallen! Ko bi takan mai k’unshi da take ta ce mata “bai kamaba” Bata yi ba ta bata kud’inta ta kira mai aiki tace “ta tattare wajen”dan gaba d’aya k’irjinta bugawa yake yi ta rasa dalili. Kaf falon sama da d’akunan ta duba bata nan, har d’ayan side d’in ta sauko ta hau ta sake dubawa nan ma bata nan. Tunawa da tayi Abba yace ta kai mishi abinci bedroom d’inshi ne, yasa da sauri ta nufi stairs d’in da zai kaita side d’in nasa. Tun kafin ta k’arasa d’akin ta fara jiyo sheshshek’ar kuka..dan haka ko sallama bata yi ba ta k’arasa ciki da mugun sauri. A yadda Abba ya fita ya barta a haka ta tarar da ita, da sauri ta k’arasa ta d’ago ta kafin a rikice ta hau tambayarta “mai ya faru?” Kukanta ne ya k’aru, wanda hakan ya sake rikita Mom! Ta d’ago hannu kenan zata tab’ata taga shatin yatsu kwance akan farar fuskarta.. Cikin gigita ta cigaba ta tambayarta tana faman jijjigata Da kyar Ummi wada tun shigowar Mom kukanta ya tsananta ta iya sassauta kukan nata da kyar ta hau gayawa Mom dukkanin abunda ya faru, tana sheshshek’a…. Tunda ta fara magana Mom tayi mutuwar tsaye! Har ta kai aya ta d’ago tana kallonta amma ko gezau bata yi ba. Sai da Ummin ta d’an tab’ata tukunna ta juyo da hankalinta gareta kafin cikin b’acin rai ta fara magana “Ban tab’a ganin dak’ik’iya Irin ki ba! A tunanina rashin wayon ki bai kai haka ba! Amman yau kam na gasgata ya kai har ma ya wuce zatona. In banda rashin hankali, ba duka ba ko kanki Abba zai saka a gabas da wak’a a hannunshi, ya kamata ki fad’a mishi wannan maganganun da muka yi alk’awarin rufawa juna asiri akai har abada??? Barazana ce fa yayi miki!! Tayay ma za kiyi tunanin Abba zai iya yi miki illa?? Na tabbatar ko suman k’arya kika yi tuni zai dawo dai dai hankalinshi kuma ya tashi!! Amman da yake ke d’in dabba ce!! Shine kika tonawa kanki asiri da mu da muka taimakeki, gaba d’aya!! Yanzu ya kike so muy.....”. Cikin katseta Ummi, tace “Adama wallahi ke kike ganin kamar barazana ce amman ba haka baneba, da gaske na hango tashin hankalin da ban tab’a gani ba a cikin kwayar idanunsa, kuma na tabbatar zai iya aikata dukkanin abunda ya fad’a din. Ba abinda yafi d’aga mini hankali irin kalmar ‘saki’ da ya ambata! Shiyasa kika ga nayi haka, kin sanni zan iya yin komai domin inga na kare aurena! Kuma baya ga haka a tunanina idan na fad’a mishi gaskiya to zai yarda da ni kuma ya fara trusting d’ina daganan ya so ni! Shi da bakinshi yace ‘In na fad’a mishi gaskiya komai zai wuce, in kuma ban fad’a ba har saki sai ya had’a mini dashi km....” Marin da Mom ta d’auketa da shi ne ya katse mata ragowan maganartata… Cike da mamaki ta d’ago tana kallon Mom….za ta yi magana Mom d’in tayi saurin d’aga mata hannu sannan tace “Lalle Ummi, wato kin yi komai saboda kare aurenki da jawo hankalin mijinki gareki ko? Mu kuma fa? Da kika zubar mana da k’ima, kika sakamu a matsala? Ke a ganinki kin yi mana adalci kenan?. Ko dan kinga ke baki da wani ishashshen laifi a cikin lamarin shiyasa? To bari kiji in gaya miki kinga wannan abunda kika yi?” Bata jira jin amsartaba tace “ba zai jawo yarda tsakaninki ke da Abba ba ballantana a tafi kan maganar so, in banda bak’in jini da tsana ba abunda rashin tunaninki ya jawo miki!!!. Kuma inaso ki sani, ni da sake shiga harkarki har gaban abada!! Saboda na lura kowa kanshi ya sani dan haka kowa yayi ta kansa.” Tana gama fad’an haka ta juya tayi hanyar fita, sai kuma ta sake juyowa kana tace mata “In zan baki shawara ki d’auka, gara ki hak’ura, saboda inda ace Abba zai so ki to da tuni an wuce wajen!! Amman har yanzu shiru.. Ga kuma sababbin obstacles a gabanki Kin tonawa kanki asiri kuma ga Maryam ta dawo rayuwar shi sannan ga y’arsa da mukeda tabbacin ita zata had’a su!! So kawai gara….” K’arar jiniyar y’an sandan da ta jiyo ne ya sakata yin shiru!! Take gabanta ya yanke ya fad’i, kallon Ummi take yi wadda itama jin jiniyar y’an sanda ya sakata sake rud’ewa! Cikin karkarwar jiki tace “Kamar jiniyar y’an sanda nake ji.” Tun kafin ta rufe bakinta, Mom tace “Ba ‘kamar’ baneba tabbas jini y’ar y’an sanda ne. Tuni ilahirin jikin Ummi ya sake rikicewa da karkarwa, ga uban gumi sai sake keto mata yake yi ta ko wacce k’ofar gashin jikinta, kana ganin ta ka san bata da gaskiya, fuskarta tayi jajir. Da sauri ta k’araso kusa da Mom kafin tace “Adama me kenan hakan yake nufi? Kina tunanin Abb....” “Tabbas Zainab mijinki ya cika tantirin d’an iska kuma mara mutunci! Da y’an sanda zai had’a mu kenan ko me??” Cewar Mom. Ummi bata san lokacin da ta fashe da wani irin mahaukacin kuka ba! Tsoronta d’aya a yanzu kar Granpa yaji zancen nan. “Innalillahi wa innailaihirraji un” Ta shiga maimaitawa, sannan ta fara kallon d’akin tana neman hanyar guduwa, da sauri ta juya ta nufi k’ofar closet, da mugun gudu. Daidai nan Abba ya shigo da y’an sanda mata guda biyu! Mom ya nuna musu yace “suyi arresting d’inta” A take kuwa suka yo kanta.. Babu abinda yafi d’agawa Mom hankali kamar ankwar da suka saka mata, bata san lokacin da idanunta suka kawo ruwa ba. Waige waige Abba ya hau yi…Chan ya hango k’ofar closet a d’an bud’e kad’an hakan yasa ya isa wajen gadan gadan ya bud’e k’ofar ya shiga, ya fara dube dube! Idanuwanshine suka sauk’a a ,wajen jallabiyoyin da aka rar rataye…gani yai wajen yana d’an motsi, hakan yasa ya k’urawa wajen ido, cikin sa’a kuwa ya hango k’afafun Ummi da suka sha jan lalle ta chan k’asa Ai kuwa ya janyo gaba d’aya kayan wajen da sun kusan 30 ya zubar dasu a k’asa! Tarr!! Ummi ta baiyyana a gabanshi sai uban gumi take yi, ga fuskar nan tayi jazir. Dukkan k’arfin shi yasa ya fincikota ya fara janta, sai da ya kaita gaban y’an sandan tukunna ya dank’a musu ita, itama aka sa mata tata ankwar. Bai bi takan magiya da ban hak’urin da take yi masa ba, haka nan ya basu umarnin tafiya da su. Mom kwata kwata bata yi gardama ba, amman Ummi sai da aka nuna mata bindiga tukunna ta nutsu. Suna fita shima ya mara musu baya. A k’asa cikin motar suka samu Mammy itama da ankwar ta . Gidan gaba d’aya ya cika da jiniyar y’an sanda, kowa ya rud’e, duk an firfito, Sudais da Shuraim in banda kuka ba abunda suke yi! Dai dai y’an sandan suna shirin tada motar Granpa ya fito Gramma na biye da shi a baya. Daddy shima wanda shigowar shi yanzun kenan Yayi saurin k’arasowa wajen, yana hango su kuwa da sauri ya k’arasa inda suke yafara kokarin fito da Matarsa, yana yiwa y’an sanda masifa! Granpa wanda yanzu ya k’araso wajen ne ya dakatar da shi sannan ya kira babban d’an sandan… Ko gaisuwar shi bai bari ya k’arasa ba ya d’auke shi da Mari, kafin ya fara magana cikin b’acin rai “Ka san a ina kake!? Ka san ko su waye waennan d’in) Laifin me sukayi? Who the hell ask you to arrest them?”. “I did” Yaji muryan Abba a bayanshi. Da mamaki Granpa ya d’an juyo yana kallonshi.. Ba tare da Abb yace komai ba ya k’arasa cikin motar ya fito da Ummi ya kawota gaban Granpa sannan yace “ta fad’i abunda suka yi”. Rarraba ido ta fara yi. Cikin b’acin rai Granpa yace “a cire musu ankwar a fito dasu gaba d’aya.” Bayan anyi hakan ne ya kalle ta sannan yace “Mai ya faru?” Da kyar ta iya d’agowa ta d’an saci kallon Mom, a take kuwa daman Mom d’in jira take, ta hau girgiza mata kai alamun kar ta fad’a. Nan kuwa ta samu kwarin guiwa, cikin sheshshek’ar kuka tace “Nima ban san abunda ya faru ba Granpa, kawai d’azu yana dawowa yace wai sun had’u da Maryam, in fad’a mishi me nayi ko kuma ya d’au mataki ban san me tace mishi ba amman kawai da nace ban san me nayi ba ya rufeni da dukaa.” Tana kaiwa nan ta fashe da kuka sannan ta durk’usa a gaban Granpa. Da k’arfi Abba ya runtse idanuwanshi… Sai da yad’an seseta zuciyarshi da take ingiza shi a kan yaje ya rufe Ummu da duka, tukunna ya bud’e idanunshi ya sauk’e su akan Granpa… Shima kuwa shi d’in ya zubawa ido. Ganin kallon da Granpa yake yi mishi ne yasa kawai ya juya ya nufi side d’insu Aslam. Ko minti uku ba a yi ba ya fito rik’e da hannun Huda. Tunda suka tunkarosu Granpa ya kafe Yarinyar da ido! Sai da yazo gabanshi sannan ya tsayar da Huda, da gaba d’aya kallo ya koma kanta. Ummi ya kalla wadda ta rikice da ganin Yarinyar had’i da sake rud’ewa, sannan yace “Baki santa ba ko?” Yayi maganar yana nuna Huda, kafin cikin d’acin zuciya yace “Zaki fad’i gaskiya ko sai na yanke hukuncin da nayi miki alk’awarin d’auka???” Gaba d’aya ilahirin jikinta karkarwa yake yi, tun ba ma da taga Gramma ta jawo Hudan kusa da ita tana d’an shafa fuskarta sannan ta k’ura mata ido ba! Tabbas wannan itace y’ar Maryam da Abba, dan ga tsananin kamanni nan suna yi da Mijinta(Abba) ba kad’an ba, yanzu ya za tai mai zata ce?? Karaf!! suka kuma had’a ido da Mom, a take ta sake girgiza mata kai, wanda hakan ya sake rud’a ta dan bata san kuma abun yi ko cewa ba, ba daman tayi k’arya dan ga evidence, kuma ba daman fad’an gaskiya tunda bata san dalilin Mom na hanata fad’a ba. Yanke shawarar sumewa tayi, dan haka ta fara k’ok’arin lumllumshe ido amma sai maganar da Abba ya fara tayi saurin watstsakar da ita daga suman k’aryar da tayi shirin yi jin yana cewa “Granpa wannan y’a ta ce!” Yai maganar yana nuna Huda Sannan ya k’ara da cewa “Those 3” ya nunata da Mom da Mammy, kafin ya cigaba “Knew about everything all this while!!… Ranar da Maryam zata haihu ta turo sister d’inta ta fad’a min, bayan sistern nata ta bawa Daniel sak’on, shi kuma munafuki sai ya fara zuwa wajen su da takardar saboda bakinsu d’aya tuntuni! Bayan sun karance sak’on nata shine suka yi mata wannan reply d’in.” Ya k’arashe maganar tare da zaro takardar gaban rigarshi ya mik’awa Granpa. Hannu Granpa ya saka ya karb’a, sannan ya fara karantawa….. Baya Daniel ya fara ja dan daman, tun lokacin da aka fara zancen ya sha jikin jikinshi… Karaf! idon Granpa ya sauk’a a kanshi, dan haka yace mishi “idan ya isa gate d’in daga nan yayi gaba kar ya sake ganinshi near his estate!!” Ummi dajin haka ta san kashin ta ya gama bushewa don daga gani Granpa ya gama gasgata maganar Abba! Don haka ta fara jiran jin sauk’ar mari ko duka, amman sai taji kawai ya dafa ta. Tana d’agowa gabanta ya fad’i don gani tayi ya mugun had’e rai babu alamun wasa ko sassauchi akan fuskar shi. Suna had’a ido ba tare da b’ata lokaci ba yace “1 word from you! Akwai gyara a cikin maganarshi? Yes or no?” Gabanta yana fad’uwa tana kuka tace “No” Da sauri Mom ta runtse idanuwanta gam!!!. A hankali Granpa ya sauk’e ajiyar zuciya sannan ya zare hannunshi daga kanta, kafin ya kira d’an sandan daya mara d’azu! Yana karasowa gareshi yace “Arrest them!” Da sauri Mom ta bud’e idanunta a firgice tana kallonshi, Daddy ma k’arasowa yayi wajen ya hau rok’on shi yana cewa “Wannan family matter ne, a bari kawai za suyi settling a tsakaninsu dan Allah yayi hak’uri”. Hatta Gramma sai da ta sa baki amman fur!!! Granpa yayi kunnen uwar shegu… Banda kuka ba abunda Mammy da Ummi suke yi…. Sassauchi d’aya Granpa yayi musu shine Bai bari an tafi dasu a motar y’an sanda ba kuma ba a saka musu handcuff ba. Ya bada motar gida yasa drivernshi ya kaisu har cell, bayan ya tabbatar wa da y’an sandan “kar a bawa kowa bellin su sai nan da 2 months............” Duk wannan bidirin da ake yi Aslam yana sama bolcony d’in parlourn Mammy yana kallon komai! Motocin suna ficewa Gramma ta sake ruk’o Hudan da kyau sannan ta rungume ta, kafin tace “Welcome to MT my granddaughter” har da d’an hawayenta. Sannan tace mata “Zo muje ki huta ko?” Ita dai Huda kawai binta take yi a haka ta jata tayi side d’insu da ita. Har bedroom d’inta ta kaita, har ga Allah lokaci d’aya taji Hudan ta shiga ranta matuk’a! Sai nan nan take yi da ita, cikin mintuna k’alilan aka cike gabanta da abinci kala kala. Sai janta take yi da hira… Da kyar Hudan ta samu ta d’an sake da ita, ganin da tayi matar tanada sauk’in kai ya sanya ta cewa “dan Allah tana so taje taga Mamanta! Sun barta a asibiti tanata kuka, kuma bata da lafiya, gashi tanata kiranta amman bata d’auka.” Gramma ta bud’e baki zata yi magana kenan Granpa ya shigo, kallonsu yayi kafin yace “ku biyo ni” sannan ya juya ya fita. A zaune suka sameshi a parlourn da wani da suke da tabbacin Likita ne saboda ga lap coat a jikinshi. A k’asa Hudan ta nemi waje ta zauna kan kafet, gramma kuma ta zauna a kan d’aya daga cikin kujerun parlourn. Nuna mishi ita kawai taga Granpa yayi, daganan taga mutumin ya nufuto…..setin ta ya zauna sannan ya bud’e d’an k’aramin akwatin da ya shigo da shi. Sirinji ya d’auko da wani abu kamar cutting bud sai reza guda d’aya! Sai da aka sha fama sannan aka d’auki jikin, daganan ya bata rezar yace “ta yanko farcenta” cuttonbud d’in kuma a bakinta kawai ta saka ta cire ta bashi, daganan ya d’an sa hannu ya ciri gashinta dake kwance akan goshinta wanda har sai da tasa k’ara dan ba kad’an ba taji zafi! Daga nan ya mik’e ya cewa Granpa “nanda 24 hours in shaa Allah zai dawo” Sannan yasa kai ya fice. Gramma taso tayi mishi magana amman ganin yadda ya had’e rai ne yasa kawai ta kyaleshi suka koma d’aki ita da Hudan bayan ya sallamesu. Iya gata Huda taga gata a wajen Gramma, amman dukda hakka Hudan zancenta d’aya ne “zata je wajen Mama” Da kyar ta samu ta lallab’ata akan zuwa gobe za suje su duba Maman nata, sannan ta yarda tayi bacci mai cike da mafarkin Mama kala kala..... Sai bayan isha tukunna Auwal ya dawo, daman saboda aikin da ya d’orawa kanshi kwana biyun nan sometimes har kusan kwana yake yi a office. Aikin da ba nashi ba da wanda yake nashi duk yi yake…ya kuwa ci sa’a dan Granpa har ya d’an fara sauk’owa da kuma tunanin maidashi kujerarshi. Bai tashi fahimtar babu Mom a gidan ba sai da safe da ya fito zai tafi office!! Cikin nutsuwa yake break fast d’inshi, tun sauk’owarshi Jalila dake kitchen ta had’a uban milo da mdara tana sha ta jiyoshi, tana lek’awa kuwa ta ganshi.. Don haka da sauri ta koma ta hau danna kwab’etar a bakinta har tana kwarewa, cikin minti kad’an ta shanye sannan ta goge bakinta ta nufi k’ofa dan bata so ya fita ba tare data karbi uban kud’ad’en data k’udira a ranta zata amsa ba! Dan bazata iya jira sati biyu ya cika ba kamar yadda Umma ta fad’a ba.. Sannan inta karb’i kud’in ma ba bata zata ke yi ba Dan ita ba sakarya bace ba tana gani sati hudu da suka wuce Kaff kud’in hannunsu sai da suka Kare aka dinga cewa ‘Auwal zai dawo gareta a rikice kuma da maganar auren ganga ganga!’ Ga shi har ita tazo gidan shi bai je ba k’arshentama da tazo d’in da mari yayi mata sannu da zuwa… Sannan bataga alamar rabuwa tsakanin Huda da Arshaad ba dan haka kud’inta kawai zata amsa taje ta yi fafa na kwana biyu ta sayi kayan kwalliya da turarurruka tazo ta yak’i Arshaad tunda gasu a gida d’aya!….. Da wannan tunanin ta fice daga kitchen d’in Ya gama breakfast ya mik’e kenan ita kuma tana fitowa. Sarai ya ganta amman sai ya basar kawai, ya juya ya d’auka jakar shi kafin ya fara k’ok’arin barin wajen, dasauri ta shiga gabanshi ta tsaya sannan tasa hannu ta rik’e jakar, bata damu ta gaisheshi ko ta tambayi ya yake ba tace “Muna biki, inaso zan je, kuma ni wannan mai girkin gaskiya bana iya cin abincin ta tayar min da zuciya yake yi, tun jiya da Adama ta tafi nake fama da yunwa, so anjima ka taho da wata sabuwar mai abincin ta gwada inga ko zan iya ci!” Yayi mamaki da yaji tace ‘Mom bata nan’, a ransa yace “to Ina ta tafi kenan??” Sai kuma ya raya “anyways zai kira ta yana fita yaji mai ya faru! Dan kwata kwata he can’t stand Jalila, shiyasa cikin k’aguwa da son ta rabu da shi yace mata “tou” kawai, sannan ya fara k’ok’arin barin wajen. Da mamaki yake kallon ta ganin tak’i sakin mishi jaka, da d’an fad’a yace “dalla Malama cikani kar In yin latti!” Itama cikin tsantsar rashin kunya tace “sai aikin zuwa office kullum amman kwakwalwa kamar ta kifi, simple abu idan an fad’a maka ba zaka d’auka ba ni ina mamakin ma ta yadda kake yin aikin wallahi!! Da kaji nace maka za muyi biki Ina so zan je kenan! sannan ina nufin yau nake son zuwa maybe kuma kwana zan yi maybe ko kwana biyu dan an riga an fara bikin! Dan haka ka saka driver ya kaini idan na gama kuma yaje ya d’auko ni, in kuma ka bari na dawo da kaina to ka san mai zai faru ba sai na tsaya yi maka bayani ba!. Sannan kuma inaso a cika min jaka ta!” Ta k’arashe maganar tana hard’e hannayenta a kan k’irji, sannan ta fara jijjiga irin ina sauraronka d’innan. Shiru Auwal yayi, ji yake kamar ya shak’eta ta mutu kowa ma ya huta! Cike da gajiya da ita yace “Nawa kike buk’ata??” Ba tare da b’ata lokaci ba tace “Dubu d’ari shidda!!”. kallon tsana ya fara jifanta da shi, chaan! Kuma sai ya d’an yi murmushi kana ya matso kusa da ita ya mik’o mata hannunshi kamar wanda zai karb’i wani abun, cikin yin k’asa da murya ahankali yace “Ban gishiri in baki manda!” Yana murmushi tare da d’age mata girarshi d’aya. Tsaki Jalila taja, Dan sarai ta fahimci me yake nufi hakan yasa ta fara k’ok’arin barin wajen…. Zagayeshi tayi da sauri ganin yana shirin ruk’ota, amman bata tsira ba dan tana wuce shi shima ya juyo kafin ta ankara taji ya ruk’o hannunta sannan cikin sanyin jiki yace “Ko har kin hak’ura da kud’in yanzu kuma bakya so? Na San fa kema kinyi missin….” Maganarshi ce ta mak’ale sakamokon idanuwanshi da suka sauk’a a kan Daddy wanda ya hard’e hannuwanshi kawai ya zuba musu ido, kana ganin fuskarshi ka san yana cikin tsananin b’acin rai!. Da sauri Auwal ya cika hannun Jalila sannan yayi saurin yin k’asa da kanshi.. Daddy yana k’arasowa ya jaa hannunshi kawai ba tare da ya ce mishi k’ala ba suka fice. Mukullin mota ya bashi sannan ya fad’a mishi inda zai kai su. Auwal yana son tambayarshi ‘me zai kai su police station’ amman sai kawai yaja bakinshi yayi shiru sakamokon ganin yadda Daddyn ya had’e fuskarsa tamau!! Suna shiga ciki Auwal ya fara yatsina yana toshe hanci sannan a hankali ya cewa Daddyn “pls, zan jira ka a waje.” Banza Daddy yayi da shi bai ce mishi komai ba.. Suna a haka dpo d’in ya fito, yana ganin Daddy ya ganeshi dan haka ya shiga gaidashi cikin girmamawa.. Amsawa Daddy yayi sannan yace mishi “yana son ganin su Mom” Sai a lokacin Auwal ya d’ago a razane yana kallonshi fuskarsa na nuna buk’atar son jin k’arin bayani. Babu wanda yace mishi komai, dpo d’inne yace “To dan Allah yaje office d’inshi zai kawo mishi su” Daddy bai so hakan ba amman yadda dpo d’in ya nace ne yasa kawai suka nufi office d’in nashi shi da Auwal. Ko minti biyar ba a yi ba aka shigo da su! Dakyar Auwal da Daddy suka iya gane Ummi, Mom itama ta wujigatu ba k’arya! Duk cikin su Mammy ce mai d’an kyan gani. Mom tanaganinsu ta fashe da kuka, da sauri Daddy yaje ya rumgume yayi ta lallashinta tukunna ta zauna. Ummi ma kukan take yi, Mammy kuwa suna gaisawa ta nemi waje ta zauna, dama tsaftataccen wuri take ta adduar samu don ta samu damar baje hanci ta shak’i tsaftatacciyar iska. Auwal gaba d’aya kanshi ya d’aure, dan haka yaje wajen Mammy ya hau tambayarta ba’asi, dan ya lura ita kad’ai ce ke a cikin hankalinta. Tiryan tiryan haka Mamyn ta zaiyyano mishi komai, tana gamawa ta fashe da kuka kafin tace “Na san mun yi laifi, amman wallahi hukuncin nan yayi mana tsauri! Ka ga inda aka ajjiye mu kuwa! Wallahi ko wajen tumaki ya fishi daraja,tsafta da kyan gani A wajen fa ake kashi ake fitsari, gashi ka san Adama da Zainab suna da allergy..kalli jikinsu kaga gaba d’aya borin jini ne,jiya ba wanda ya runtsa a cikinmu!! Ban san tayaya za muyi wata biyu a irin wajen nan ba, dan wallahi Auwal na tabbatar muna yin sati a nan to sai dai a kwashi gawarwakinmu.......” Tana gama fad’an haka ta sake rushewa da wani irin kuka mai cin rai. A fusace Auwal ya mik’e a wajen yayi hanyar fita, Daddy yana ganin yanayin mik’ewar tashi shima yayi saurin mik’ewa ya sha gabanshi yana cewa “ina zaka je?” Cikin d’acin zuciya yace “ba ruwan ka Daddy, this is between me and Abba!!” Yana gama fad’an haka ya sake yunk’urin fita, da sauri Mom wadda itama ta k’araso wajen tayi hanzarin rik’o hannunshi, yana juyowa yace “Mom dan Allah ki barni kawai, i need to teach him a lesson!! In banda tsabar rainin wayo a kan y’arsa zai yi muku haka? Y’ar gwal ce ita?” Cikin fad’a Daddy yace “Tou sannu sarkin marasa kunya!! Uncle d’in naka zaka koyawa hankali? Haukan naka ya tashi daga tsakaninku yana shirin haurawa kan y’an uwana kenan?? To wallahi a kul d’inka Auwal!! Raina a b’ace yake da kai tun d’azu shiru kawai nayi maka, kar ka yarda ka kaini mak’ura!!” Yana gama fad’an hakan ya koma wajen dpo ranshi a mugun b’ace… Da sauri Mom ta sake rik’o hannunshi duka biyun ta matse gagam sannan ta fara magana “Kayi hak’uri ka sauk’a daga kan wannan dokin zuciyar Auwal, dan babu inda zai kaimu, idan ma za a hukuntasu to bata haka za a yi ba, kaji?? Yanzu na tabbatar kana yin wani abun laifin ka za a gani, kuma nima kaga dai gani da nawa issue d’in, sannan ga matsalar ka da Granpa abun zai yi mana yawa.” Cikin yin k’asa da murya tace “Kana gani ai Arshaad da ya fika wayo tun jiya bai zo ba, kuma na tabbatar yana cikin gidan, shi kuma Aslam dayake babu uwar shi a ciki ta sama ya mak’ale yanata kallonmu bai ce ko yayi komaiba, bai san ba ganshiba. Don haka inaso kayi hak’uri ka danne zuciyar ka, tukunna sai mu san abun yi, kaji ko?”. Da k’arfi ya sauk’e ajiyar zuciya yana bin hannun Mahaifiyar tashi da yayi jajur ya kumbura ga borin jini kala kala, da ido. A haka har gara ita nata da d’an sauk’i akan Ummi, dan ita nata har fuska… “Kaji ko?” d’in da tace mishi ne ya sanya yayi mata nodding kai kawai sannan ya koma ya zauna, itama ta dawo ta zauna. A Chan teburin dpo kuwa Babu yadda Daddy bai yi da shi ba akan “zai biya ko nawa ne a ware musu office d’in wani d’an sandan a gyara musu toilet su dinga amfani da shi su uku kawai zuwa nan da 2 months d’in”! Amman furr!! Dpo d’in yak’i, yace “Jiya bayan na dawo sojoji Mahaifinta ya aiko suka kaini har gabanshi da daddare ya ja mini warning akan in tabbatar na basu horo mai tsanani, kuma ya shaidamin yana da cid’s da yawa, muddin na k’etare umarnin shi to a bakin aikina. Tsabar yanaso ya tabbatar min idanunsa suna kaina, yau da safe ya kirani, duk wani abinda ya faru a nan daga dawowata zuwa tafiya ta gida da zuwana nan yau da safen kaff! Babu abinda bai gayamin ba, har na cikin dare wanda bananan a bakin shi na ji. Hatta abinci yace sau biyu kawai za a dinga basu… So, dan haka dan Allah ka rufamin asiri ina son taimakonku tabbas amman ina jin tsoron rasa aiki na. Da kuma hukunci da yayi alk’awarin yanke min, wanda ban san meneneba.” Ajiyar zuciya Daddy ya sauk’e, sannan ya juyo ga su Ummi…. Idanuwa yaga sun zuba mishi alamun suna sauraron komaai. Tausayin su ne ya kamashi, hakan yaasa yayi saurin d’auke kanshi yana shirin yiwa dpo d’in magana Mom ta matso ta katsesu ta hanyar cewa “Tou dan Allah idan ba zaka iya komaiba, ka raba mana d’aki da matan nan, basu da mutunci kwata kwata, gara a kwashesu a zuba mana wasu” Jijjiga kai dpo d’in yayi sannan yace “zan gwada in gani.” Abinci Daddy ya bayar aka je aka siyo musu da alk’awarin zai dinga zuwa dubasu kullum sannan ya yiwa Mammy da Ummi sallama yace “Mom ta tsaya yana da magana da ita.” Suna fita ya cewa Auwal “ya matso”, ba tare da b’ata lokaci ba ya zayyano mata abinda ido da kunnuwanshi suka jiwo mishi daga Auwal d’in da Jalila yau da safen nan, kafin ya k’ara da cewa “Kina tausayin Yarinya kin d’auko ta zaki bata kud’in kayan d’aki! To ga d’anki nan zai lalata mata rayuwa gaba d’aya tun kafin ta samu kud’in da zata yi auren da shi. Ko kuma ma ince ya gama lalata mata rayuwar dan na kasa fahimtar inda zancen nasu ya dosa! Saboda haka it’s either kice mata ta koma wajen Inna ko kuma shi Auwal ya bar gidan, tunda na lura kamar ba kya son sallamar Jalilan. Duk lokacin data tafi shi sai ya dawo.” Hak’uri Mom tayi ta bashi da alk’awarin zata kira Innar taji, idan komawarta ba zai yiu ba, zata rok’i Gwaggo Asabe ta rik’eta a wajenta kafin ta dawo. Da kyar ta lallab’ashi ya hak’ura, akan sai zuwa wani d’an lokaci In ta tuntub‘I Innaa da Gwaggo Asabe amman da cewa yayi a yau zata bar gidan dan shima jibi tafiya zai yi, so ba za’a bar daga ita sai Auwal ba. Taso su d’an keb’e da Auwal d’in amman hakan bata faru ba, dan Daddy bai basu dama ba. A haka suka yi mata sallama suka tafi, zuciyarta a cunshewa gashi babu daman yin waya don an karb’e tun jiya, gaba d’aya hnkalinta kuma sai ya koma kan yadda zata ci uban Jalila! Dan ta kaita mak’ura, so itace target d’inta in the next two months tana fita a cell zata yi maganin shegiya, tukunna Abba sai Aslam sai Maryam sannan Huda da Ummi…. Kmr yadda wannan Likita ya fad’a, da yamma sai gashi e da results ya bawa Granpa da duk wasu bayanai tukunna ya tafi. Sai bayan sallar isha, tukunna Granpa ya nemi ganin Huda Abba Gramma Daddy da Dad wanda dawowarshi kenan ya tarar ana sallah dan haka ya kira Gwaggwo Asabe suka k’arasa cika ita da Mommy shi kuma ya shiga masallacin ana idarwa Granpa yace “su wuce side d’inshi, ko gidanshi bai bari ya lek’a ba................ BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 38 Sai da Arshaad ya dawo daga masallaci ‘sallar isha’ tukunna ya lura babu Mammy a gidan. A bakin cook d’insu ya ji komai bayan ya tambayeta. Da kyar ya iya controlling kanshi dan ya san idan yace zai samu Abba ko Daddy a wannan lokacin a yanayin da yake ciki to tabbas za a samu matsala…. Dafe kanshi kawai yayi ya sallami cook d’in. Ya dad’e a tsaye! Bai ma san ta ina zai fara ba! Dan haka kawai ya sake komawa d’aki ya kwanta…. Da kyar kuwa ya samu ya iya rintsawa a daren ranar. WASHEGARI. Sai bayan sallar isha, tukunna Granpa ya nemi ganin Huda Abba Gramma Daddy da Dad, wanda dawowarshi kenan ya tarar ana sallah dan haka ya kira Gwaggo suka k’arasa cika ita da Mommy shi kuma ya shiga masallacin.. ana idarwa Granpa yace “su wuce side d’inshi”, ko gidanshi be bari ya lek’a ba............. A tare su duka hud’un suka iso parlourn Granpa. Ba tare da b’ata lokaci ba ya d’au waya yayi kiran Gramma yace “su zo ita da Huda!” Hijabin Gramma na salla mai hannu Hudan ta zumbula a kan abayar jikinta. Bayan sun fito Hudan ta bisu duk ta gaidasu..cike da kulawa duk suka amsa mata apart from Granpa wanda ya kauda kai gefe! Tana k’ok’arin zama a k’asa Abba yayi saurin jawota ya zaunar da ita a kan kujera kusa da shi sannan ya hau tamabayarta “how is she?” Tana shirin yin magana Granpa yayi gyaran murya! Sai da ya lura hankalin kowa ya dawo kanshi, sannan cikin serious voice d’inshi na tsoffi ya fara magana “Na san kowa a nan ya san abunda ya faru! Da kuma wannan Yarinya da Abba ya kawo yace ‘y’arsa ce’! Although ga kamanni nan na gani kuma su Ummi suma sun tabbatar da hakan, but dukda haka i need proof! Saboda ko dan abinda akace su Ummi sun yi jiya ya sa na saka jin ba zan iya trusting family members d’ina ba ma akan komai talkless of Maryam! Na lura ba zata iya hak’ura da Abba ba so she can do anything, zata iya tricking su kansu su Ummi d’in ta jira for years tukunna ta aiwatar da plan d’inta. Wannan dalili yasa jiya aka d’au sample d’inta da kuma na Abban wanda ya nemi yayi mini rashin kunya bayan na kirashi za a d’auki jinin nashi! He looked at me yana cemin ‘ko da ace The girl is not his, shi already ya riga yayi accepting nata, so tests d’ina babu abunda zasu saka ko su chanja!’.” Shiru Granpa yayi ya d’an sauk’e ajiyan zuciya sannan yaci gaba “Idan nace muku na tsani Maryam!!! Sai ku dinga ganin laifina….. jiya kawai ya ganta suka had’u amman har ya zama mara kunya mara mutunci!!! I’m pretty sure inda ace bai ganta ba to da ba zai iya gayamin maganar da ya gaya mini ba!! He even hit his wife! Saboda kawai giyar ganin wannan matar yana yawo a jikinshi…. Anyways duk ba wannan ne ya zaunar da mu anan ba!. Abba, inaso ka sani ko da ace zan yi disowing d’inka kamar farko, i’ll make sure Maryam bata lik’a maka y’ar da ba taka ba! Shiyasa na saka aka yi DNA and results d’in sun fito positive, so she’s your daughter, although na san you don’t need it!. Magana ta anan itace …. 29 years ago!!! Na fad’a maka na fad’awa Maryam cewa ‘I’ll never accept her and her children!!’ Dan haka wannan Yarinyar”yayi maganan yana nuna Huda, sannan yace “Kasancewarta y’a ga Maryam hakan ya sa she cannot live with us in this estate!!!!. Kana da two options Either ka mayar da ita wajen Maryam Or You are free to leave this estate and family, with her Forever!!!.” Yana gama fad’in haka ya koma yayi lamooo, a kan luntsumemiyar sofar da yake kai. Shiruuuu, parlourn ya d’auka, baka jin komai sai sheshshekar kukan Huda. A hankali Abba ya mik’e rik’e da hannunta har yanzun.. Gaban Granpa suka je suka durk’usa sannan ya fara magana “Granpa bani da bakin da zan yi maka godiya akan irin abubuwan da kayi mini tun haihuwata har kawo yanzu, ba zan tab’a iya biyanka ba sai dai In kamanta! Ko da ace kai ka cire Ni a cikin y’ay’anka Ni ba zan tab’a iya chanja uba ba! You’ll forever remain my Dad that same Dad that loves me so much! Wanda son zuciyata ya sanya a yanzu bana jin akwai 10% out of 100 na son da yake yi mini. Na san ba lalle ka iya finding place a heart naka kayi forgiven d’ina ba, but i’ll keep on apologizing till the end of time, I’m sorry, so sorry, very sorry! Dan Allah kayi hak’uri ka yafe min.” Yana gama fad’in haka ya mik’e ya mik’ar da Huda itama sannan yace “Hudan and I are leaving!! Good bye.” Da sauri Huda tace “Dan Allah kayi hak’uri, ka zauna da su, ni zan koma wajen Mamana, na ma fi son wajen ta akan nan, kar kuyi fad’a saboda ni dan Allah!”. Abba bai saurareta ba sai ma k’ok’arin janta da yake yi, dan so yake yayi sauri ya bar parlourn baya so su had’a ido da Gramma. Ya juya kenan yaga Daddy a tsaye! Bai gama tunanin me ya mik’ar da shi ba yaga ya k’araso inda yake ya rik’e free hand d’inshi! D’agowa yayi yana kallonshi da jajayen idanuwanshi, ganin Daddyn shima shi yake kallo ya sanya shi cewa “Don Allah kar ka ce komai, ka san ba zai tab’a chanja decision d’inshi ba, ni kuma ba zan iya barin y’ata taci gaba da zama a gidan wani ba! Please don’t stop me.” Ajiyar zuciya Daddy ya sauk’e, kafin yace “I’m not trying to stop you Abba. I’m coming wit you!!.” Da sauri ya kalleshi sannan ya juya ya kalli Granpa wanda ya lumshe idanunsa yana nan kishingid’e kamar mai bacci. Shima Daddy juyawa yayi still rik’e da hannun Abba yana kallon setin Granpa sannan ya fara magana “Granpa! Laifin Maryam da Abba bai kamata ace ya shafi Yarinyar nan ba! Bafa mu ma santa ba, bamu san ma tana existing ba, ta taso ba tare da kulawar d’aya daga ciki mu ba. I think yanzu lokacine da ya kamata ace mun yi welcoming d’inta warmly + mu nuna mata gatan da bamu nuna mata ba a baya! Bawai a hukuntata a kan laifin da iyayenta suka aikata ba wanda yaci ace yanzu ka yafe tunda Abban da Maryam d’in sun dad’e da rabuwa!!. To be honest Granpa What you have been doing is not right!! Kawai muna yi maka biyayya ne because we respect and love you as a father! But it’s like abun yana neman yin yawa! Tunda gashi kana k’ok’arin kai Abba wuta! Ko baka tunanin Allah zai tambayeshi hakkin y’arsa akanshi ranar gobe k’iyama?? What you are about to do is wrong! Very wrong!! Dan haka i think it’s about time da ya kamata mu fara fad’a maka gaskiya! But na san ba lalle ka yarda ba, kamar yadda Abba ya fad’a nima na san ba lalle ka chanja decision d’inka ba So idan ka kori Abba, nima zan bishi, that’s it!!!”. Ajiyar zuciya Granpa ya sauk’e kafin ya bud’e idanuwanshi, bai kalli ko inda suke ba, ya sauk’e idanunsa a kan Dad, a hankali yace masa “What about you Yahaya?? Wat’s your decision?” Ahankali cikin mutuwar jiki Dad ya mik’e, muryarshi na d’an rawa dan shi kwata kwata abun nan da ake bai yi mishi dad’i ba! Bayason tension kwata kwata..a halin yanzu shi ko da matsalar matarshi aka barshi ta isheshi, but he has to do whats right, dan haka yace “Na zab’i side d’in brothers d’ina Granpa. I’m sorry, but whatever Yusuf just said is the truth.” “Ok “ kawai Granpa yace, kafin ya juya wajen Gramma ya kalle ta itama yace “Ke fa??” Hawayenta ta sa hannu ta share, sannan tace “Sun fika gaskiya!! Na rok’eka da girman Allah for once a rayuwanka kayi hak’uri kayi abunda suke so dan Allah” D’an murmushi Granpa yayi kafin yace “If not kema baki da choice d’in da ya wuce ki bisu ko???” Shiruuuu, tayi bata ce komai ba, har sai da ya sake cewa “ke muke jira, your decision is important.” Tukunna,a hankali cikin kuka Gramma ta hau d’aga kai alamar ‘eh’. Da sauri Abba ya durk’usa ya fara yi mishi magiya “Dan Allah kayi hak’uri ka barni In zauna da ku! Ka yi accepting Huda plss karka....” Hannu Granpa ya d’aga mishi kafin ya mik’e tsaye! Yaje inda yake shima ya mik’ar dashi tsaye sannan ya fara magana “Already na riga na gama magana Abba, kai ka sani. And please stop pretending dan na san this is wat you want! Kana so inyi regretting akan abunda na yiwa Maryam Tunda inda ina shiri da ita tun farko ai da duk haka bata faru ba, right? But inaso kan san 1 thing Ko d’aya, hakan bai sa naji ba dad’i ba, infact I’m happy because i’ve and i’m punishing the devil!!! Ka duba fa kaga yadda Ummi ta koma, abunda suka yi ita da su Adama, duk saboda matar nan( Maryam), which I’m pretty sure ba halinsu baneba! Laifinta ne she push and made them act that way!! And now look! Abunda dukkan ku ku kayi mini, all because of her!! Abba How? Tayaya kake tunanin zan yi accepting y’ar matar nan? Matar da ta mayar mini da family haka? Tunda nake da mahaifiyarku gata nan ku tambayeta bata tab’a yi min koda yaji ba nima ban tab’a tunanin tura ta gidansu saboda wata matsala ba amma yanzu kalli, she’s ready to leave.. Because of Maryam! Maryam bad luck ce! Amman ka kasa fahimta kwata kwata. Ka duba kaga fa, tun lokacin da ka had’u da ita baka samu peace of mind ba har yau d’innan! Iya jiya( just yesterday) da kayi spending time da ita kalli abunda ya janyo, bu.....” Mahaukacin kukan da Hudan ta fashe da shine yasa su kallonta gaba d’aya, dukkanin k’arfin da Allah ya bata tayi amfani da shi wajen fincike hannunta a cikin na Abba, sannan ta d’iba a guje tayi waje……a ranta tana ayyanawa “wallahi ba sojoji ba ko barrack ne a bakin gate d’in estate d’in yau sai ta fita, yadda ta kwasa a gujen nan ba zata tsaya ba sai ta ganta a titi sai dai ayi mata kallon mahaukaciya. Shiyasa ashe Baabaa Talatu take rok’on ta akan karta kuskura ta yiwa Mama maganar Mahaifinta (Abba) ashe wannan ne dalilin kenan…Tunda take bata tab’a ganin hatred irin wannan ba, dan ko k’iyayyar Shuwa garesu bata kai ta wannan tsohon da ake kira da Granpa ba, gashi har yana k’ok’arin danna musu tambarin ‘bad luck’, kuma duk wanda yaji labarinsu tabbas zai yi musu kallon hakan, tunda gashi ita kanta iya kwana d’aya kawai tayi a estate d’in but familyn yana neman hargitsewa! What type of daughter will she be idan ta yiwa Mahaifin da yake k’ok’arin making up to her sanadin tarwatsewar family d’inshi? Besides tanaso taje taga halin da Mama take ciki, so she has to leave, ta ko wanne hali a yau sai ta gudu daga estate d’innan!” Da wannan tunanin ta dinga zabga gudu. Cikin ikon Allah ta hango k’ofar gefen gate d’in gidan a d’an bud’e kad’an dan haka ta k’ara gudu ta bi ta k’ofar ta fice… Tun tana jin muryar Abba wanda ya biyota yana kwala mata kira har ta daina. Fitulu ta ko ina tarr!! Kamar rana, shiyasa ta samu damar ganin gabanta cikin sauk’i!. Gudu kawai take tun iyakar k’arfinta… Tana gudu tana kallon baya taga fitowar Abba daga gidan Granpa inda ta fito. Mai gadin ya tsaya yana tambaya taga yana nuno masa direction d’inta, hakan yasa tayi saurin b’uya a bayan motar data gani a gefenta jikin wani gida, tana d’an lek’owa kad’an ta jikin glasses d’in, gadan gadan taga yayo inda take dai dai aka bud’e k’aramar k’ofar shiga gidan dake jikin gate d’in da alamun fitowa za ayi, Allah ya taimaketa Daddy ya biyo Abba yana mishi magana dan haka ya juya gareshi… Wani wawan tsalle tayi da mugun sauri ta afka gidan. Da sauri yasa hannunshi ya dafe bango d’ayan kuma ya dafe bayanta, wanda hakan da yayi ne ya taimaka musu basu zube a k’asa ba! K’amshin turaren shi da tun ranar da suka fara had’uwa ta sanshi da shi ne ya tabbatar mata da waye!! K’ok’arin barin jikinsa take yi amman bata san dalilinshi na rik’e mata baya ba!.. Dukkanin k’arfinta tayi amfani da shi wajen ganin ta raba kusancin nasu amman hakan sai ya gagara! Don ruk’on da yayi mata bana wasa bane, as if his life depends on it. Gaba d’aya sai ta sake firgicewa, kukanta ya k’aru barema yadda taji zuciyar shi na wani kalar mahaukacin bugawa.... So yake ya cire ta a jikinshi amman ya kasa, idan ana maganar over racing to shine abinda zuciyar Aslam ke ciki a halin yanzu, tun daga lokacin da yaga tayo tsalle ta shigo da gudu tana kallon baya, har kawo yanzu da take a jikinshi.... Tun lokacin da Arshaad ya fara kiran sunanta taji, dan haka har d’an dukan Aslam take tana kuka akan ya barta! Amman kwata kwata babu chanji a yanayinshi sam, it’s like yama k’ame a hakan ne ko yaya ne ita dai ta kasa ganewa. Sai da Arshaad ya k’araso ya kama hannunshi wanda ya rik’eta gagam, da kyar ya iya b’amb’areta daga jikinshi.. tukunna hankalinshi ya fara dawowa jikinshi a hankali abhankali… Sannan da kyar ya cika bangon ya d’an seseta tsayuwarshi kafin ya kalli Arshaad wanda kafeshi da manyan dogayen idanuwansa. He looks calm ammanfa idanunsa sun mugun chanja kala. Gaba d’aya kuma sai abunda ya faru ya dawo mishi, take yaji wata kalar kunya ta lullub’e shi, da kyar ya Iya tattaro y’ar ragowar jarumtarshi, yana shirin yin magana suka jiyo muryar Abba da Daddy suna dumfaro su, Daddy yana cewa “ga k’ofar a bud’e maybe nan ta shiga, dan na san ba lalle an barta ta fita ba lets check.” Da sauri Hudan wadda har yanzun gaba d’aya ilahirin jikinta ke rawa ta juya tana kallon Arshaad kafin a hankali tace “Ya Arshaad dan Allah ka b’oye ni dan Allah.” Tayi maganar tana had’e hannuwanta waje d’aya alamun rok’o, tana kuka. Ganin sun kusan isowa ne yasa Arshaad d’in da sauri ya jata yasa a d’akin mai gadi sannan yace mata “ta shige toilet d’inshi(mai gadin) tayi shiru.” Tana rufe k’ofar toilet d’in su kuma su Abba suna shigowa gidan, dai dai Arshaad yana shirin fita shi kuma, suka yi kicib’is!. Kallon kallo aka tsaya yi, kafin Daddy yace “kunga Hudan?” Aslam yana shirin yin magana Arshaad yace “No” da sauri sannan ya d’ora da “Neman ta ake? ina tayi? Mai ya faru?” Aslam kawai Abba ya k’urawa ido..ganin yak’i had’a ido da shi yasa ya cewa Daddy wanda yake shirin yiwa Arshaad bayani “Mu koma kawai, inaga wajen Gwaggo Asabe tayi. Ma duba ta anjima, lets take care of Granpa, na tabbatr biyotan da muka yi yanzu ma case ne.” 100% Daddy ya yarda da hakan dan haka ya cewa Aslam “ya ci gaba da duba musu Hudan za suyi musu bayani anjima, shi kuma Arshaad yaje Gate yayi confirming in bata fita ba daganan ya sa curfew a estate d’in har su samu su gama meeting da Granpa su fito.” Da “to” suka amsa musu daganan su Abba suka wuce. Suna fita shima Arshaad ya fara k’ok’arin fita a gidan “Kace mata zata iya fitowa.” Shine kawai abinda ya iya cewa Aslam ba tare da ya yarda sun had’a ido ba. Har ya juya yaji Aslam d’in ya ruk’o hannunshi… Da sauri ya runtse idanunsa da k’arfi, sai da ya d’an dedeta fushinsa kafin ya juyo yana kallonshi. Aslam tunda yake bai tab’a jin nervousness irin na yau ba, dan haka ya fara kame kame “Um, I’m sooo sorry a b bout” Da sauri Arshaad ya katseshi ta hanyar cewa “It wasn’t your fault, tayi laifi, so ko baka yi abunda kayi ba dole na san wata rana gaskiya zata fito, kuma za ayi punishing nata. Kawai dai i was disappointed in you ne that’s all” Sai da ya d’anyi shiru yaji hucin da yake yi ya d’an ragu tukunna ya ci gaba da magana “Ko sabon mai aiki aka chanja a gidan nan baka nan Aslam kana Uk but sai na kiraka na fad’a maka! Ya kamata ace lissafinka ya baka ‘if Abba yana da y’a and bai san da ita ba, to dole akwai wani abu a k’asa’!. Da kayi finding out about Huda you should have talk to me first mu samu mu fara bincike first! Because that is wat i’ll definitely have done if i were in your shoes. But you just went ahead and ruin everything. Yanzu because of you Mahaifiyata is there a cell da anty Adama su da basu da laifin komai, they just help a friend.” A hankali yace “i tot we were brothers, best friends.” Cikin katseshi Aslam yace “and yes we still are, yana matsowa kusa dashi da rik’eshi”. Murmushi kawai Arshaad yayi ya zare hannunshi sannan ya zagayeshi ya fara k’ok’arin shiga d’akin mai gadi. Ajiyar zuciya Aslam ya sauk’e kafin yace “Ok, I’m sorry” yana mai sake ruk’o hannunshi. Sai da Aslam d’in ya maimaita sannan Arshaad ya juyo ya kalleshi na y’an seconds kafin yace “Apology accepted.” “Thankyou “ shine abinda Aslam d’in yace kafin ya d’aura da “And about what you just saw, i’m..” Cikin katseshi Arshaad yace “Aslam we’re good fa, komai ya wuce, let me check on her, ta shiga toilet d’in mutumin nan barefoot kuma i don’t even know ko yana ciki dan ban ganshi a d’akin ba.” Yana gama fad’in haka ya zare hannunshi sannan yayi cikin d’akin ya isa bak’in k’ofar toilet d’in yana cewa “Hudan open the door, it’s me, su Abba sun tafi.” A hankali take bud’e k’ofar tana d’an lek’owa.. Sai da ta tabbatar da shi d’inne tukunna ta k’arasa bud’ewa. Murmushi ya d’anyi mata.. Gaba d’aya ta had’a gumi tayi zuru zuru! A hankali yace “matsoraciya kawai” A hankali tayi k’asa da kanta sannan ta fito, Allah ya taimaketa ba kowa a toilet d’in kuma mutumin yanada tsafta dan band’akin tass yake gashi tiles ko ina kuma a bushe. Amman dukda haka sai da Arshaad yayi amfani da ruwan butan da ya gani bayan sun fito ya zuba mata akan k’afafunta. Suna fitowa ya cire takalminshi ya bata ta saka sannan yace “ta zo ta rakashi ya saka takalmi.” A hankali ta fara kuka kafin tace masa “Ita wajen Mama zata je” Gaba d’aya sai yaji wani matsanancin tausayinta ya kama shi. Shiruuu, yai yana tunanin ta yadda zai fita da ita bayan shi aka d’orawa alhakin curfew. Dole ya lallab’ata ta d’an hak’ura ko zuwa gobe ne sai su je. Matsowa yayi yana shirin lallashinta wayarshi ta hau k’ara, ganin sunan Sakina ya sanaya shi ce mata su k’arasa ciki akwai maganar da yake ai suyi da ita, dama. Tukunna sai ya kaita gurin Maman. Ba tare da musu ba ta bishi suka yi hanyar shiga parlourn gidan, Aslam har zai bisu dan still ya lura Arshaad d’in is still mad, saboda da suka fito ko inda yake bai yarda ya kalla ba.. Sai kuma kawai ya chanja shawara ya juya kawai, duba da yayi ba shi kad’ai bane kuma ya lura soyayyar Mahaifiya ta rufe mishi ido, if not tayaya zai ce “ita da Mom basu da laifil!” ko kuma may be bai san story d’in gaba d’aya ba, dai. Da wannan tunanin ya fita a gidan bayan ya yanke shawarar sai nan da 4 to 5 days haka zai nemeshi ya sake bashi hak’uri, by then ya san ya sak’k’o..... Suna shiga parlour ya umarceta da “ta zauna akan kujera” Bayan ta zauna shi kuma ya nufi fridge ya d’auko mata ruwa da glass cup a kan dining ya kawo. Dama kuwa tana buk’ata hakan yasa yana zuba mata ta k’arb’a ta hau sha. Sai da ta shanye tass sannan ta ajjiye tana sauk’e ajjiyar zuciya a jejjere. Kallonta yayi da idanuwanshi da har yanzun basu gama dawowa dede ba sannan a hankali yace “In kara?” Girgiza mishi kai tayi tana y’ar mitsitsiyar gyatsa kafin tace “Alhamdulillah” Sai kuma anhankali ta mik’e tace “Bara inje wajen Aaima” Mik’ewa shima yayi yace “bata nan, bata dawo daga school ba tukun! Mammy kuma tana cell! It’s just me.” Ya fad’i hakan yana tsareta da ido. Saurin yin k’asa tayi da kanta, kafin a hankali tace “Kayi hak’uri dan Allah.” Murmushi ya d’an yi yana kallonta kawai ba tare da yace komai ba. A hankali tace “bara in tafi, nayi tunanin Aaima tana nan ma.” Bata jira jin me zai ce ba ta fara k’ok’arin fita tana cewa “ka d’auko takalmin naka muje mu duba Mama da wuri, ko?”. Dede nan wayarshi ta sake ringing, ganin me kiran ne yasa shi kai mata wayar har bakin k’ofa sannan yace “Na so muyi magana but it’s like kamar tsorona ma kikeji! Gashi ungo, Sakina ta gaya miki, bara in d’auko takalmin nawa” Yana gama fad’an haka ya kara mata a kunne bayan ya amsa kiran daga nan yayi hanyar part d’in nashi. Da sallama ta amsa wayar.. Ajiyar zuciya Sakina ta sauk’e jin muryar Huda sannan tace “Alhamdulillah” Jin yanayin muryar Sakina yasa ta fahimci akwai matsala. Cikin sanyin muryar da bata santa da shi ba taji tace “Huda kuna Ina? bakya hawa watsapp, ba kwa amsa waya tun jiya, gamu kuma mun dawo gida bakwa nan. Ina kukaje gaba d’aya hankalin mu ya sake tashi.” Da sauri Huda tace “Sakina Mama bata gida? Ya naji muryar ki wani iri duk ya dishe?” Ajiyar zuciya Sakina ta sauk’e, har zata fad’a mata kuma sai tayi shiru (saboda su Madu sun ce a bari a fara yin test na gawarwakin da ake expecting akwai Junaidun a ciki da jinin Baba, before ayi confirming nashi as dead ) Hakan yasa tace mata “Ban gane ‘Mama bata gida ba’ bakwa tare? Ke kina ina?”. Gefe guda Hudan ta koma kan kujerar dining ta zauna sannan ta fara bawa Sakina labarin tun daga sumewar da Mama tayi jiya da safe, har kawo yanzu da take son gudowa…. To fa!! Ana wata ga wata. Numfashi Sakina ta fesar kafin tace “With all that is goin on Hudan, congratulations! Kin had’u da Mahaifinki finally, and baya gudunki, kamar yadda mutane suke fad’a. But first Maama, so yanzu ki bani kamar 20 minutes haka za sake kira in shaa Allah.” ......Su Abba kafin su koma ciki suka tsaya shi da Daddy suka yanke shawara…suna zuwa suka sanar musu cewa “Shi da Daddy za su bar gidan, Dad da Gramma kuma za su zauna. Addua suka dinga yi akan Allah yasa kowa ya yarda. Ba dan su Gramma sun so ba haka nan suna ji suna gani suka amince da tafiyar su su kad’ai, Dad yaso ace shi ne yabi Abba tunda shine Babba Amman bayan sun keb’e sai suka yi mishi bayani akan kasancewar shi babban ne yasa suka ce ya zauna a estate d’in, sannan ya taimaka ya dedeta Gramma da Granpa, kafin ya koma Abuja, dan tun a wajen meeting d’in suka fahimci iyayen nasu suna fushi da juna wanda hakan it’s not usual. Ahaka ba dan rai yaso ba aka tsara akan gobe zasu bar estate d’in kafin a samu komai ya dedeta In Granpa ya sauk’o su dawo, Dad ne ya basu mukullin makeken mansion d’inshi wanda ke anan bayan su kad’an yace “su zauna su biyu a tare ba sai sun raba gidaje ba.” Dan ana hoping d’in daidaituwar komai soon in shaa Allah. Daddy yayita jiran Granpa ya kirashi yace “yayi resigning, ya kawo takardun companies d’in da yake rik’e dasu sannan ya sauk’a a md d’in MT UK branch Amman ga mamakin shi sai yaji shiru, bai ce masa komai ba......... Sakina tana katse kiran ta mik’e ta isa inda Ummu take ta jaa hannunta suka koma gefe, ganin haka yasa Shuwa itama ta iso inda suke, nan Sakina ta zayyane musu komai. Kafin awa d’aya gaba d’aya su Kaka kowa ya hargitse a neman Mama har da Madu wanda ba kad’an ba kowa yaji dad’in yadda ya shiga cikin lamarin. Babu inda ba a duba ba har wajen 10 amman shiru. Ummu ce ta bada shawarar “aje asibitin malan d’in a sake bincika ta!.” Nan d’inma ba Inda basu duba ba dan rarrabuwa ma suka yi amman shiru… Tunda suka fito Baba yake ta maimaita magana d’aya “Aje gidansu Abba! Shi ya tabbatar idan aka yi kwakkwaran bincike a gidan za a ganta. Ya san tabbas Abba ne ya d’auke Maryam ya b’oyeta bashi da tantama! A kira y’an sanda a kama Abba…waye waye.” Su Ummu tun suna k’ok’arin fahimtar da shi har suka hak’ura suka kyaleshi kawai dan sun lura abun nashi ba na k’are bane. Ganin dare ya lula yasa Ummu tace bara kafin su koma gida ta shiga masallacin can tayi sallar isha dan gaba d’aya ta sha’afa bata yi ba gashi lokaci ya tafi sosai, sai a lokacin Sakina itama ta tuna bata yi ba hakan yasa suka nufi famfo suka yi alwalla tare daga nan suka shiga masallacin domin gabatar da sallah… Babu kowa a ciki sai wasu mata guda biyu a chaan k’uryar masallacin, d’ayar a zaune da Yaro a hannunta d’ayar kuma ta juya baya tana kallon bango alamun bacci ma take yi. Cikin nutsuwa suka gabataar da sallar su suka d’ora da doguwar Adduar Allah ya baiyyana musu Mama. Daga nan suka mik’e suka fara k’ok’arin fita. Ummi ji tayi kawai gabanta ya yanke ya fad’i, kamar kuma ance ta juya…bata san daliliba amman taji tana buk’atar juyawan… Matan nan na d’azu ta sake kallo still suna a yadda suke, har tana shirin juyawa idanunta suka kai kan atamfar jikin matar kwance da mayafinta, sai a yanzu ma ta lura da kayan dan sanda suka shigo kwata kwata hankalinsu baya tare dasu, gasu a gajiye. Kusan a tare zuciyoyinsu suka buga ita da Sakina wadda itama taga atamfa da mayafin jikin Mama Tabbas mayafin Mama ne wannan Atamfar kuma ankon wunin kai amarya Khadijah ne. Da sauri Sakina tace “Maamaa!” Sai kuma ta k’arasa wajen da sauri ta hau tab’ata ganin bata motsi yasa ta sa hannu ta juyo da ita. “Innalillahi wa innailaihirrajiun” Shine abinda Sakina Ummu da matar dake gefen Mama suka fad’a a tare. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 39 Da sauri Sakina tace “Mamaa” sai kuma ta k’arasa wajen da sauri ta hau tattab’a ta, ganin bata motsi yasa ta sa hannu ta juyo da ita! “Innalillahi wa innailaihirrajiun” Shine abinda Sakina Ummu da matar dake gefen Mama suka fad’a a tare, dan a yadda Sakina ta juyo da ita haka ta biyo hannun Sakinan ta taho yuuu ta zube wanwar kwanciyar rigingine. Ummu mutuwar tsaye tayi a wajen, so take ta k’arasa inda suke amman ta gagara sakamokon ganin y’ar uwartata da tayi kwance tamkar gawa! Ta kasa tab’uka komai banda hawaye ba abunda take yi. Sakina wadda ta rikice tanata tattab’a Maman ne ta juyo tace “Ummu ki zo ki kamata mu mik’ata emergency.. Mama ce amman bata numfashi.” Jin hakan ba k’aramin sake rikita Ummu yayi ba, ita dai kawai ta ganta a gabansu a tsaye amman bata san ya aka yi ta isa wajen ba. Matar nan ce ta matso itama ta hau jijjiga Mama tana cewa “kumafa yanzun nan muka gama magana da ita, tun jiya muke nan tare da ita. In banda kuka ba abunda take yi, nayi tambayar duniyar nan tak’i kulani… Sai dai kawai taje tayo alwala tazo tayi ta sallah. Sai d’azu ne da naga kamar batta lafiya nace ‘tazo muje in rakata taga Likita’, shine na samu ta d’an kulani ta inda take ce min ‘bara ta d’an yi bacci, idan ta farka sai muje’.” Ita dai Sakina cicib’arta ta fara k’ok’arin yi hakan yasa suma suka sa hannu suka taimaka mata suka yi waje da ita..... Su Madu suna tsaye a k’ofar shiga emergency.. Kana ganinsu ka san hankalinsu ba a jikinshi yake ba! Ga tsananin gajiyar da suke tare da ita Dan ma Allah ya taimaka Abokin Junaidu ne ya biya musu kud’in jirgi su kuma suka biyawa Baba Saboda yaga yanayin tsufansu gashi da ya kira Baban ma a hanya ya jisu suna dawowa daga wata tafiyar…. Ba dan haka ba da gajiyar ba zata yi musu da sauk’i ba. Suna tsaye suna tunanin abunyi next suka hango su Ummu d’auke da mata suna nufusu, sai da suka matso su sosai sannan suka gane Mama ce. Basu samu damar tambayar su ba dan da sauri mai gadin k’ofar ya wangale suka shige kawai dukkansu… Ana ganin su aka karb’esu bayan an kawo gado an d’aurata, aka tura ta ciki don yin bincike.. Ba a jima ba sosai, Dr ya fito! Likitan dai da ya karb’eta jiya shine, magana d’aya ce ya maimaita musu “hawa da jininta yayi over ne ya janyo komai..amman this time around har eco za suyi” Nan yake ce musu “ba yadda bai yi da ita jiya akan ta zauna ta shanye drip d’inta ba amma tak’i, ta biyewa wasu suka dinga hayaniya suna fad’a! Yayi yayi akan suyi shiru suka k’i, shiyasa shi kuma ya sallameta, so suma in sun san hayaniyar za suyi gara karma su shiga inda take, dan zai sake korar su ne!”. Yana gama fad’in haka ya nuna musu inda take sannan ya wuce........ Bayan kamar awa d’aya, Kaka da su Baba suka wuce aka bar Sakina da Ummu. Su Kaka na fita Hudan wadda take kiran Sakina a kai a kai ta kira, nan Sakina ta gaya mata “sun ganta suna tare ma yanzu haka” Sai a lokacin hankalinta yad’an kwanta. Nan itama Sakinan take tambayarta “tana Ina?” Hudan tace mata “tana wajen Gwaggon su Aslam, amman still Abba bai san tana gidan ba, dan a b’oye ma Arshaad ya kawo mata wayarta data bari a gidan Gramma, so in shaa Allah gobe da sassafe za ta san dabarar da zata yi ta gudo.” shiruu, Sakina tayi chan tace “ki bari mu yi magana da Ummu tukunna, kar ki yi komai, kinji?” Ummun ce tasa hannu ta karb’i wayar suka yi magana da Hudan ta d’an kwantar mata da hankali, kafin suka yi sallama. Da kyar suka samu bacci ya kwashesu wajen k’arfe 3 na dare. Da sassafe su Madu da Baaba Talatu suka zo kawo musu breakfast, har lokacin Mama bata farfad’o ba. Sama sama take jin hayaniyar su dan haka ta fara k’ok’arin bud’e idanunta. Sakina wadda take a kusa da ita ce ta lura dan haka ta maida gaba d’ayan hankalinta gareta, ganin Sakina ta k’ura mata ido ne ya sanya suma duk suka taso suka zagaye gadon suna tambayar “mai ya faru?” Basu ida tambaya ba Mama ta k’arasa bud’e idanunta… Tsantsar farin ciki ne ya baiyyana a fuskokinsu gaba d’ayansu, cikin murna suka hau furta “Alhamdulillah” suna tambayarta “ya jiki?”. Da kyar Baaba Talatu ta taimaka mata ta mik’e ta zauna.. Tana zama suka had’a ido da Ummu! Kawai sai ta fashe da kuka abun tausayi…… Duk shiru suka yi. Da kyar Madu ya samu ya k’araso inda take ya dafa ta sannan ya d’an fara bubbuga bayanta alamun lallashi. Farin ciki ne ya mamaye zuciyoyinsu gaba d’aya, duk sai suka hau murmushi Kaka har da y’a kwallarshi, ya sa hannu share ba tare daya bari kowa ya lura ba. Ita kanta Mama duk da yanayin da take ciki hakan sai da ya sanyata zubar da kwallar farin ciki, dan rabonta da Madu ya nuna kulawarshi a kanta kaman haka, yau yau shekaru ashirin da bakwai kenan!. Share hawayenta tayi sannan ta d’ago ta kalleshi, shima itan yake kallo, ba abinda ta hango a idanuwanshi sai tsantsar tausayinta, bakinta na rawa cikin kuka tace “Abba, ya raba ni da Huda! Dan Allah ku karb’o min ita, wallahi mutuwa zan yi in ba y’ata, na shak’u da ita sosai, ba zan iya yarda in bar mishi ita ba.” Da sauri Ummu ta k’araso ta rungumeta, sannan cikin tsananin tausayinta tace “Ki yi hak’uri ki huta, munji komai, in kika warke sai a san abun yi, ki kwantar da hankalin ki dan Allah.” Cikin jujjuya kai Mama ta zare Ummu a jikinta kafin tace “Bilkisu ba zan iya yin hak’urin nan ba!! Abba ya zama wani irin mutum! Mugun mutun.. Shi ne fa ya turo Arshaad wajen Huda, Arshaad cousin d’inta ne! Suka dinga yaudarar mu, idanunsa akan mu yake all this time amman bai baiyyana kanshi ba sai yanzu? Saboda ko nace ba zata koma wajenshi ba ya san ai Arshaad zata aura, kenan ko? Wanne irin ubane zai yiwa y’arsa haka? Bilkisu gaba d’aya kaina ya kulle, a baya yace ‘baya buk’atar ta’, yanzu kuma yazo ya raba ni da ita a lokacin da nafi buk’atar ta, mai yasa zai yi haka? Laifin me na yiwa Abba da zafi haka??”. Ta k’arashe maganar tana mai fashewa da kuka. Lallashinta Kaka Baaba Talatu da Ummu suka hau yi, amman furr!! Tace “ba zata hak’ura ba! Ba zata iya yin hak’urin da suke so tayi ba, yanzu zata je ta taho da y’arta, barinta a hannun Abba danger ne! Tunda har ya iya turo wani wajenta saboda son zuciyarshi bai damu da yana sonta tsakani da Allah ba ko akasin hakan ba Tou tabbas zai iya yin komai. Ko bayaga haka ma idan duk duniya zata taru a kanta tofa ba zata d’auki y’arta wadda Abban yace ‘bayaso ta fad’a mata ko da sunan shi ne’ ba, ta bayar a shi yanzu! Sai dai duk abinda zai faru ya faru. Suyi mata kwatancen gidan ko kar suyi mata zata tafi ta nema, tunda Allah yasa taji kwarin jikinta yanzu, daman jiya ma jiri ne ya hanata motsawa daga inda take.” Gaba d’aya Mama ta hargitse musu, data ga ma ba zasu bata goyon baya ba, Sai ta fara k’ok’arin sauk’a daga kan gadon sannan tasa hannu zata cisge cannular hannunta. Madu ne ya rik’e hannun nata, kafin cikin lallashi yace “Maryam koma ki zauna muyi magana.” Cikin sheshshek’ar kuka ta koma ta zauna tana share hawayenta. Sai da yaga ta d’an sassauta kukan nata, sannan ya fara magana “Ki kwanta ki huta, baki da lafiya. Koda kin fita za ki sake fad’uwa ne, saboda baki gama dawowa normal ba! Ki zauna ki shanye allurai da magungunan ki, da ni da Babanku Bashir za muje mu samu Abba, in shaa Allah, kinji ko??” Da sauri Kaka yace “Za muje a yau! Ki kwantar da hankalin ki kinji?” A hankali taji kad’an daga cikin nauyin da zuciyarta tayi ya d’an sauk’a, dan haka ta d’aga musu kai alamar ‘to’ kawai, tana sharar hawaye. Ajiyar zuciya Baaba Talatu ta sauk’e, sannan ta nufi wajen kulolin da suka kawo ta zubowa Mama abinci ta kawo mata. Sakina ce ta karb’a ta fara k’ok’arin bata, amma sai ta kauda kai gefe tace “ta k’oshi” Cikin turo baki Sakina tace “haba Mama ki ce mana, kin ganki kuwa yadda kika koma? Gashi duk kin yi wata zuru zuru kamar…” Dukan da Maman ta kawo mata tayi saurin kaucewa, duk kuwa sai suka hau murmushi…. Da naci da komai hakanan sai da Sakina ta d’urawa Mama abincin nan, ta kuwa ci sosai, dan sai da su Madu suka sa baki tukun Sakina ta hak’ura. Sai wajen 11 na safe su Sakina suka fara shirin tafiya don suke suyi wanka suyi girki, ita da Ummu. Baban su Sakina ne yazo d’aukar su! Ya d’auka Mama ko wani zai yi mishi maganan Arshaad amman yaji shiru shiyasa shima yana yiwa Maman ‘ya jiki’ ya fita, dan baya so suyi mishi d’in, but ya tsara a ranshi zai gayawa matarshi, duk abinda ya sani, da kuma dalilin yin shirun da yai, saboda kar ayi mishi kallon munafuki. Sai da suka biya duk wani bill sannan suka tafi a lokacin an tafi da mama yi mata eco. Su Kaka ma shirin tafiya gidan su Abba suka yi, aka bar Baaba Talatu. Sai a sannan ne Baba yazo, ganin Maman bata nan yasa suka gaisa da Baaba Talatu ya wuce kasuwa akan zai dawo da azahar in shaa Allah. Su Kaka basu samu damar zuwa gidan su Abba ba, sai la’asar, a sakamokon kiran da aka yi musu akan results d’in da ya fito, dangane da case d’in Junaidu......... Yadda Hudan taga rana haka taga dare, Gwaggo Asabe har mamakinta take yi dan duk juyi in tayi sai taga idonta biyu! Gaba d’aya ta kasa bacci ta k’agu Safiya tayi taje taga jikin Maama, da taga safiya ta k’i yi k’arshe kawai mik’ewa tayi taje ta d’auro alwalla, tazo ta fara jero nafilfili. Tana idar da sallar asuba kuwa bayan ta gama Azkar ta d’anyi karatu, ta shiga tayi wanka. Tana fitowa ta tarar Gwaggo Asabe bata d’akin, hatta sallayar data barta akai ta nad’e. Doguwar rigar da Gwaggo Asaben ta bata jiya had’e da Maclean da brush sabbi ta d’auka ta sanya, luckily ta samu comb a d’akin cikin drawer, dan haka ta goge shi da tissue sannan ta sa hannu ta zare ribbom d’inta ta hau ware tufkar da ta yiwa dogon gashinta wanda yanzu har ya kai tsakiyar bayanta….ita kanta tana mamakin yadda ya tofo a cikin shekara uku! Bayan askin dolen da Ya Jalila tayi mata… Tunawa tayi da Jalila wadda Sakina tayi mata k’us k’us d’in Khadija tace mata ‘kamar ciki ne da ita( Jalilan)’ amman Umma tayi k’arya tace ‘ta tafi jinyar Hansai’. A hankali ta sauk’e ajiyar zuciya a ranta tana adduar ‘Allah yasa ba cikin ne da ita da gaske ba’ ….abunka da zuciya mai kyau! gaba d’aya duk sai taji tausayin Yayar tata ya lullub’eta, don haka ta hau yi mata addua da fatan alkhairi, tanayi tana taje kanta. Sai da ta gama tsaf, ta d’auko ribbon d’in ta tufke gashin a d’an k’asan tsakiyar kanta kad’an! Ganin yadda jelar take reto ne ya sanya ta kanannad’e gashin waje guda ta tura ta had’e da ribbon d’in, d’ankwalin doguwar rigar ta d’auko tayi style d’in V da d’aurin very simple amman ba karamin kyau tayi ba, ga gashin data duk’unk’une ana iya hango santsi da kyallin shi da uban yawa dan d’ankwalin k’aramine sosai so bai gama rufewa ba. Ta d’auko wayarta kenan zata kira su Mama ta ganta a kashe, ba chargi. Ajiyar zuciya ta sauk’e, daman ta san za ai haka, dan tun jiya chrgin ta yayi low sosai. Zama tayintana jiran Gwaggwo Asabe ta dawo ta ari wayarta ta kira su Mama don duk ta haddace nambobin su. Kusan minti arbain taji shiru.. ga anxiety yana neman kashe ta! Shiyasa ta yanke shawarar mik’ewa, ta hau nemanta. Bata wani sha wahalan neman nata ba, dan tana fitowa daga d’akin taji k’amshi ya cika ko Ina a gidan wanda hakan ne ya tabbatar mata da inda take(Gwaggwo Asaben), dan haka ta nufi k’asa. A k’ofar kitchen d’in suka had’u da Gwaggon, da tray a hannun ta, da kuma tea flask da ta rik’e da kyar. Sai da Hudan da d’an rissinar da kai tukunna ta gaisheta. Da kulawa Gwaggo Asabe ta amsa… Har ga Allah ta dad’e bata had’u da Yarinya mai hankali da nutsuwa irin Huda ba, ga kyau tubarkallah…shiyasa lokaci guda suka saba, taji ta shiga ranta sosai! Har k’asan zuciyarta take yiwa Aslam d’insu kwad’ayin auren Yarinyar saboda ta had’a komai ga kyau ga hankali ga nutsuwa gata y’ar uwarshi! Sai dai kuma yadda taga Arshaad yana shige mata sosai, watak’il shi ne zai fara cewa yana sonta, dan jiya ta lura har wata y’ar hira suka tsaya yi a parlour, sai wani nan nan yake yi da ita….. Hannu Huda ta saka tana k’ok’arin karb’ar tea flask d’in dake hannunta wanda hakan ne ya katse mata tunanin ta! Ba musu ta sakar mata , dan itama tana jin yadda ya kusan fad’uwa. A tare suka nufi hanyar sama, tana gaba Hudan na biye mata baya, wata hanya suka kuma d’auka bayan sun shanye stairs d’in, nan ta sake hango wani bene, benen suka bi suka hau, suna kaiwa k’arshe suka tarar ta wata y’ar k’ofa A bud’e k’ofar take hakan yasa suka shige, dogon corridor ne sosai, sai k’ofofi biyu, d’aya a farko farko hanyar dama, d’ayar kuma a kusan k’arshen dogon corridor d’in ta hannun hagu, Wadda itan taga Gwaggwon ta nufa, sai da suka iso bakin k’ofar, tukun suka tsaya! Rik’on tray d’in Gwaggwo Asabe ta gyara sosai a hannu d’aya sanna tasa hannu tayi knocking, tukun taja ta tsaya, ta gyara ruk’on tray d’in. Kusan minti biyu tukunna suka ji ance “come in” Hudan ta kalla tace “tayi amfani da empty hand d’inta ta bud’e musu.” Hakan tayi, bayan ta murd’a handle d’in a hankali ta d’an tura sai kuma ta matsawa Gwaggo Asabe don ta fara shiga.. Murmushi Gwaggon Asabe tayi sannan ta shige Itama Hudan ta bita a baya. Sai da ta rufe k’ofar tukun ta juyo ta fara kallon d’akin…. “Ma shaa Allah” tace, a ranta. Ba zaka kirashi d’aki ba kuma ba zaka kirashi da parlour ba, ga set d’in kujeru har da k’aramin dining, da makekiyar tv d’in da bata tab’a ganin irin ta ba, ga kuma set d’in gado shima komai akwai, royal, light blue da fari haka colour d’in kujeru da gadon suke, hatta pentin d’akin haka yake. Ga kuma wani glass door, wanda kana iya hango swimming pool da shuke shuke da kujerun shak’atawa. K’auyanci ta fara, don a ranta ta hau rayawa “daman ana pool a sama? saman ma ta biyu! Ita tunda take bata tab’a ganin d’aki mai girma sosai da kyau irin wannan ba!”…… Tunanin ta ne ya katse jin Dad yana cewa “Hudan k’araso mana ya kika tsaya a k’ofa?”. Sai a lokacin hankalin ta ya kai kan Dad, da wata mata a zaune a gefen shi yana rik’e da hannunta. Ji tayi kamar ta rusa kuka!! Da ta san gurinshi Gwaggo Asabe zata zo da bata biyo ta ba, kenan ita duk b’uyab da takeyi ma a banza, tunda gashi a gidanshi ma ta kwana ba tare data sani ba, kuma yadda ya nuna it’s like ya san tana nan d’in, shikenan ta san yanzu zai kira Abba shi kuma ya hanata zuwa taga Mama. Gwaggo Asabe ce ta katsemata tunani jin ta sake cewa “Huda k’araso mana.” A hankali take takawa izuwa bakin gadon inda suke… Taji Dad yana cewa “Ashe da gaskiyar Abba, daman ya ce tana wajensu Aslam ni ban yarda ba, sune suka kawota jiyan ko?” D’an murmushi Gwaggo Asabe tayi kafin tace “Eh jiya lokacin da ka kira ni, Arshaad bai dad’e da kawota ba, shi ya rakota.” Hudan dake jin su duk sai taji jikinta yayi sanyi, ashe ita kad’ai take ta shirmen ta. A hankali ta k’arasa wajen, kanta a k’asa. Har k’asa ta durk’usa ta gaida Dad, wanda cikin tsananin son yake yiwa y’ar d’anuwan nasa yayi saurin kamo ta ya zaunar da ita a kan d’an stool d’in da yake facing d’inshi, cikin kulawa ya amsa kafin ya hau tambayarta “ya kwanan bak’unta?” “Alhamdulillah” kawai ta iya cewa kafin ta juya ta hau gaida matar gefen shi har sau biyu amman ba alamun zata amsa kuma ta kafeta da idanuwa! Tana shirin sake gaidata a karo na uku ne Dad ya sauk’e ajiyar zuciya ya d’an dafa Huda tukun yace “Karki damu ba zata iya amsawa bane, amman ta fahimceki, tunda gashi tanata kallonki.” Yana gama fad’in haka ya juya ga Gwaggo Asabe jin tana cewa “ga breakfast, watak’il taci tunda naga yanzu jikin da d’an sauk’i, ko?” Shiru ya d’anyi kafin ya sauk’e wata ajiyar zuciya tukunna yace “Sai addua fa, amman Alhamdulillah, ni fa da Granpa zai yarda wallahi da an hak’ura da wannan theraphy d’in, saboda duk lokacin da akaje aka yi aka dawo ni sai inga kamar abun k’aruwa ma yake yi, kwanaki fa har hira tana yi, amman yanzu kiga gaba d’aya sai a hankali, danfa baki ganta last two weeks ba (Tym d’in da suka dawo. A Abuja), shiyasa ai na hanata dawowa nan, da kyar fa da addu’o’i tukunna abun yayi sauk’i ta dawo hakan.” Ajiyar zuciya Gwaggo ta sauk’e kafin tace “nima dai gaskiya na dad’e da lura, magana ce kawai banaso.” Cikin d’an fad’a Dad yace “Ai kuwa ta gama theraphy! Dan a gaskiya, ko ance za aje, sai dai In kaita Abuja kawai muyi sati mu dawo, abu ba fad’ar Allah ba amman an maidashi kamar dole!?” Kwalla Gwaggo Asabe ta share sannan tace “Ai shima Granpa d’in naji yana cewa ‘daga wannan an gama’.”Cikin katseta Dad yace “ai tun last year yake cewa ‘daga wannan an gama daga wannan an gama’! Amman an kasa gamawa da gasken.” Ajiyar zuciya Gwaggo ta sauk’e ranta duk ba dad’i da yanayin y’ar uwarta ta…. A hankali ta durk’usa ta fara serving abincin cikin mutuwar jiki. Hudan itama duk jikinta yayi sanyi dan haka tace “Allah ya bata lafiya”. A hankali Dad ya d’an juya ya kalle ta sai kuma yace “Ameen” cike da jin dad’in adduar tata. Juyawa yayi ya kalli Mommy, gani yayi har yanzu Hudan take kallo, kamar tanaso ta tuna wani abun.. Bai gama fahimtar yanayin ta ba yaga ta d’aga hannunta sannan tayi amfani da yatsar ta manuniya wajen sai da Huda! Gaba d’aya hankulansu kanta ya koma, cikin rawar murya kamar ta mai koyan magana sukaji tace “Aaa-sllam, ttanna kama ddda Aasllm d’Ina” Ba Dad ba hatta Gwaggo Asabe sai da gabanta yayi wani irin mahaukacin fad’uwa!!! Rabon da Mommy ta kira sunan Aslam, tun kafin ta fad’o daga bene! Gaba d’aya rawa jikin Dad ya d’auka, a hankali ya sa hannu ya juyo da fuskarta, ya kalli cikin idanunta sannan yace “Kina so kiga Aslam d’in naki?” Da sauri ta hau d’aga mishi kai, sai kuma hawaye, shaaarrrr suka zubo mata. “Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!” Shine abunda Dad ya dinga maimaitawa, cikin kid’ima ya mik’e ya fita yana cewa “su Gwaggwon su tsaya gashi nan zuwa, kar kowa yaje koina.” Ba ayi minti goma ba sai gashi ya turo k’ofa, rik’e da hannun Aslam Abba yana binsu a baya! Cikin zumud’i yace “Ga Aslam d’in naki” ya fad’a yana tunkarar ta, yana cewa su Abba “komai yazo k’arshe in shaa Allah, Aslam yau da kanta ta kira sunank.........” Razananniyar k’arar da ta fasa ce ta hanashi k’arasa maganar tashi, ta kuma rud’a duk wani wanda ke a cikin d’akin!! Basu ida dawowa haiyyacinsu ba ta kuma sakin wata k’arar! Wadda kusan rabin estate d’in sai da aka ji!. Cikin tsananin tashin hankali firgici kid’ima da tsoron da ya baiyyana k’arara a kwayar idanunta take nuna Aslam d’in tana kururuwa! A kid’ime Dad wanda duk ya rud’e ya sake nufota still yana rik’e da hannun Aslam wanda ya sake shiga tsananin tashin hankali da rud’ani don shi Dad ce mishi yayi “yazo Mahaifiyarsa tana nemanshi yau da kanta!” Gashi yanzu kuma ya tarar da haka!…. K’arar da ta sake saki ne ya kid’ima su dan tafi ta ko yaushe! Sai kuma ta saki jiki rigif ta fad’i sumammiya akan gadon….. Da sauri Aslam wanda idanuwanshi suka kad’a sukai jaa over, ya k’arasa inda take ya hau jijjigata yana kiranta amman bata motsi…….d’ago jajayen idanuwanshi yayi yana kallon Dad. Gaba d’aya sai Dad d’in yaji tausayin su, su duka ukun ya lullub’e shi.. Abba ne yayi k’arfin halin zuwa inda suke, yad’an kura mata ido kafin ya cewa Gwaggo Asabe “ta mik’o mishi ruwa!” A hankali yake yayyafa mata ruwan, har sun cire ran zata farka sai kuma sukaga tana motsi da idanunta alamun zata farfad’o…. A hankali Abba yad’an kalli Aslam wanda ke zaune a gefenta ya rankwafa kanta sannan ya kama hannunta gam!! Yana kallon idon da take k’ok’arin bud’ewa, alamun a kag’e yake yaga ta bud’e idanun nata! Da kyar Abba ya tattaro courage d’in da ya iya cewa Aslam “Aslam, ko zaka d’an je waje ko? Kar ta farka kuma ya zamana kai d’in zata fara gani.” Da sauri yace “No Abba, I think bata gane ni bane ba.” Sai kuma ya kalli Dad yace “Dad da kanta ai kace ta kirani ko?” Ganin da Dad yayi Aslam d’in na neman koma musu wani firgitachche ne ya sanya shi kawai cewa “Kaje wajen tukunna mu gani.” Jikinshi har wani karkarwa yake yi, sai da Dad ya sake cewa “I’m so sorry Aslam, ita tace a kiraka but ban san me ya sake faruwa ba kuma, for now just, ka d’an jira a waje ko?” A hankali ya cika hannun ya mik’e ba tare da ya yarda ya had’a ido da kowa ba ya fice, Dede nan Dad ya fashe da kuka, gaba d’aya sai hankalin su Abba ya sake tashi, saboda abune wanda basu saba gani ba! Don haka duk sai suka hau bashi hak’uri suna tausar shi, tare da adduar in shaa Allah Allah zai bata lafiya soon… A b’angaren Dad shi kuma Aslam yake ji, da ya sani da bai yi saurin kiranshiba, gaba d’aya duk sai yaji ya tsani kanshi….. Da kyar suka samu ya tsaida kukan ya k’arasa gurin Mommy wadda ta farka yanzun tanata faman dube dube a mugun tsorace alamun neman tsari take daga sake ganin Aslam d’in. Sai da komai ya lafa sannan Gwaggo Asabe suka fito ita da Hudan daga d’akin…. Ita dai Huda gaba d’aya kanta ya kulle, hakan yasa ta kasa hak’uri ta hau tambayar Gwaggo “meke faruwa? Mai ya sameta take haka? Tun yaushe? An yi mata sauka?” Dan ita Huda har ga Allah kawai ta fi jirkita akan lamarin na iska ne, tunda gashi dai ita da kanta ta tambayeshi but yana shigowa gaba d’aya ta firgice! Tayaya uwa zata dinga gudun d’anta haka?? Don ko ba a gaya mata ba ta gane itace Mahaifiyar Aslam ko dan yanayin kamar da suke yi da juna! But why him? Him alone?” Ajiyar zuciya Gwaggo Asabe ta sauk’e sannan tace “bani minti talatin, inje inyi wanka, Ina dawowa za kiji komai in shaa Allah.” Kamar yadda Gwaggo Asabe tace Sai da tayi wanka ta dawo ta zauna sannan ta fara bata labari………… Asalin sunan Mommy, Aisha ana kiranta da Humaira, k’anwarta d’ayar duniya Khadijah wadda ake kira da Asabe. Aisha da Asabe sun taso cikin yanayin k’unci na rayuwa ata dalilin babu.. Yahaya ya had’u da Aisha ne lokacin da ya kai ziyara Taraba, jalingo a wani d’an k’aramin k’auye. Ata dalilin, masallaci da makarantun addinin daya d’auki nauyin ginawa. A rafii yana zagaye ita kuma taje d’ebo ruwa suka had’u. Tunda ya kyalla ido ya ganta ya rikice, a lokacin Mahaifiyarsu ta rasu Mahaifinta kawai ya rage musu. Tun Aisha tana kauce mishi har itama ta fara kulashi sama sama. Tashi d’aya ba kwana kwana ya nuna mata yana k’aunarta kuma yana son aurenta, Bata bashi amsa ba tace “yaje ya samu Mahaifinta”. Yahaya bai yi wani jinkiriba yaje ya samu Mahaifinta da maganar sannan yayi mishi alk’awarin ‘bayan auren zai barta tayi karatu har sai tace bataso’, dan ya lura burin Mahaifin nasu kenan. D’an guntun bincike akayi akan Yahaya, a lokacin, daga nan Mahaifinta ya bashi aurenta yace masa “duk lokacin daya shirya yazo da iyayenshi a d’aura” To fa!! anan ake yinta, dan k’iri k’iri Granpa ya nuna k’iyayyar shi muraran akan Aisha da inda ta fito, acewarshi “sam ba a jin auren d’ansa bace ita d’in!!!”. Buwayar Ubangiji, rabon Aslam, da soyayyar Granpa a matarshi ne suka tabbatar da auren Yahaya da Aisha wanda aka d’aura a k’auyen Jalingo ba tare da halartar Granpa ba. Tabbas anyi rigima ba k’arama ba, kafin, da kuma bayan auren!. Zan iya cewa ban taba ganin macen da ta sha wahala a hannun suruki kamar Aisha ba! Sauk’in ta d’aya Gramma tana mugun sonta ba kad’an ba, dan tun lokacin da Yahaya yaje mata da labarin Aisha farat d’aya taji Yarinyar ta kwanta mata, ita ta dinga lallab’a Granpa har aka yi auren. To bayan auren ma haka tayi ta fama, in tak’aice miki labari hankalin Granpa bai kwanta da Aisha ba har sai da ya aurawa Yahaya ajin nashi da yake ik’irari! Wanda ranar d’aurin auren ana d’aurawa Yahaya yana hawaye kamar k’aramin Yaro, dan zan iya cewa ban tab’a ganin Mijin da yake matuk’ar so da gudun b’acin ran matarshiba kamar Yahaya ba. Sauk’i d’aya da Aisha ta samu a gurin Granpa shine haihuwar Aslam da tayi, zan iya ce miki ko y’ay’an da Granpa ya haifa a cikinshi bayayi musu kalar son da yake yiwa Aslam, ko dan ya kasance jikansa na farko ne? Allah kad’ai ya sani. Tun ranar da aka haifeshi da ya d’auke shi aka tabbatar da hakan, domin kuwa kalar farin cikin da yayi kowa sai da ya gani ya tabbatar da ‘Granpa na cikin farin ciki’!. Zakkah da sadakar da ya bayar kuwa bana jin har yau a tarihin kaf garin Kano an tab’a bada irinta. Aslam ya taso cikin gata, duk wani abu da kika sani Granpa ne yake yi mishi… A tunanin kowa, Granpa zai kasance irin kakannin nan masu shagwab’a jikokinsa ne, sai dai kuma shekarar Aslam biyar a duniya aka haifi Arshaad amman kwata kwata Granpa bai yi wani murna sosai ba ma balle aje ga maganar shagali da jan shi a jiki kamar yadda kowa ya d’auka… Tun ranar da aka haifeshi da ya d’auke shi bai k’ara d’aukar sa ba, Aslam kuwa kullum suna tare, hatta abinci tare suke ci, takanas ya nemo wani bature yake yi mishi lesson a gida, da yamma kuma wani balarabe ne yake koyar da shi addini! Sai da Granpa ya fahimci loneliness da rashin wasa da Yara agemate d’in Aslam d’in kan iya jawo mishi wani ci baya a rayuwarshi tukunna ya nemi makarantar da tafi ko wacce tsada a kaf Nigeria ya turashi a Abuja wajen mahaifinshi, tare da kwakkwaran warning a me makarantar na “kar a tab’a mishi jika ko me kuwa zaiyi! Kuma kar a bari aci zalinshi.” Duk da yana da wayo sosai dan, a lokacin shekararshi tara Arshaad hud’u Auwal kuma uku wanda shima Granpa bai wani nuna farinciki ko tunanin janshi a jiki ba tun sanda aka haifeshi. A lokacin ne kuma Yahaya ya sake tadawa Granpa maganar yana so ya tafi da Aisha Abuja , daman ya tab’a nunawa Granpa son yin hakan amman fur k’iri k’iri Granpa ya nuna mishi sai dai ya tafi da Mammy saboda itace tayi karatu bayan k’iri k’iri babu irin artabun da baayi da shi ba amman fur haka ya hana Aishan yin karatu acewarsa ‘irin su In suka yi karatu gagarar mutum suke yi!’. A lokacin ya nace akan sai dai ya tafi da Mammy ita zata iya zaman Abuja wata k’ilan ma ta d’an dinga taimaka mishi ta fannin aiki, shi kuma Yahaya yace ‘ba zai tafi da ita ba! Ko da ace Aisha bata kasance uwargidanshi ba tou tabbas da ita zai tafi’….. Mistake d’aya wanda Yahaya yayi kuma yake kan yi har yanzu shine ‘k’iri k’iri yake nuna fifici a tsakanin matanshi’ (k’iri k’iri yake nunawa kowa ba tare da shakkar wani abu ba ‘ya fi son Aisha a kan Mammy’. Da kyar a wannan lokacin dan sai dai Gramma ta shiga tsakani tukunna case ya mutu, dan daa Granpa cewa yayi sai ya tafi da Mammy dole! Shi kuma yak’i. Tou kuma da Aslam ya koma chan ma da ya sake yin maganar Aisha ta bishi, still magana d’aya irinta farko shima Granpa ya maimaita mishi ‘sai dai ya tafi da Mammy’ shi kuma yak’i, Shiyasa har yau shi kad’ai yake zaune a Abuja, yanzu haka shi da Aaima ne kawai a gidan. K’in tafiya da Mammy da Yahaya yayi ata dalilin Aisha yasa Granpa ya rufe ido ya dinga keta mata ruwan rashin mutunci kala kala, ga Adama da Ummi suma basu barta ba, Mammyn ce ma ita bata shiri da ita kuma bata fad’a da ita. A lokacin ne kuma Mahaifinta ya rasu, Allah yaso ni nayi aure don da ban san ya zan yi ba saboda shi kanshi Mahaifin namu su uku aka haifa biyun duk sun rasu, Mahaifiyar mu kuma daga gidan marayu ma aka aurota, balle inyi tunanin zuwa gidan y’an uwa! Dan a lokacin halin da Aisha take ciki a gidannan, ko mage bata isa ta d’auko tace zata rik’e ba. Aslam shekara biyu kawai ya iya yi a Abuja ya d’agawa kowa hankali Akan shi fa ‘Mahaifiyarshi yake buk’ata’ Dan ba kad’an ba suna mugun k’aunar juna, kuma yana da k’ulafucin uwa ba kad’an ba, itama kuma haka, komai Aslam, shima komai Mommy. Saboda tsabar tsananin shak’uwar dake a tsakaninsu yasa har kusan zarewa tayi lokacin da aka kaishi Abuja, Idan nace zan tsaya fasalta miki kalar soyayyar da sukewa junansu sai mu kai jibi anan.......... Ba yadda Granpa ya iya haka ya tarkatoshi ya dawo dashi kano gurin Mahaifiyarshi, akan dai ya bari a tafi da ita d’in. Sai dai kuma daya dawo d’in abun bai yi dad’i ba sam! Dan k’iri k’iri Granpa ya dinga nuna banbanci k’arara ba tare da shakkar komai ba! Abun mamaki hatta driver d’in da zai kai Aslam makaranta daban ne da nasu Arshaad. Tun abun baya damun mutane har aka fara k’us k’us, su kansu Yaran suma suka fara fahimtar waensu abubuwan….dan shi Arshaad ma a tunaninshi Aslam d’in d’an Granpa ne shiyasa a lokacin yake kiranshi da ‘Uncle Aslam’ a lokacin. Ranar 12th birthday d’in Aslam ne Granpa yayi wani abun da ya girgiza mutane! Gida guda ya d’auka ya bawa Aslam as birthday gift, a Dubai! Wanda su kansu y’ay’ansa basu ma san yana da shi ba, kar ki ce k’aramin gida fa mansion ne mai zaman kanshi! Dan ko a jikin takardar wajen d’akuna ashirin ne suka fito a cikin gidan, iya d’akuna kawai!. Mutane basu dawo daga shock ba ya cewa Yahaya “ya yiwa lawyer d’inshi magana a fara had’a takardun MT! yana so zai mallakawa Aslam su tun yanzu, in yaso shi (Yahayan)sai ya rik’e mishi idan ya kai 18 years ya bashi abunshi.” Cikin nuna k’in amincewa Dad ya d’an fara k’ok’arin fahimtar da shi akan shekarun Aslam d’in da kuma gudun abunda hakan ka iya janyowa K’asa k’asa ba tare da ya bari kowa yaji ba. Amman Granpa maimakon ya fahimceshi sai ya birkice mishi, ya fara magana yana fad’a kowa yana ji! Ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba! Fad’a a ranar ba kalar wanda bai yi mishi ba a gaban taron y’an birthday… Sai da Aslam d’in yayi kamar zai yi kuka yana bashi hak’uri tukunna aka samu ya hak’ura. Jiki a mace haka Dad ya fita ya kira lawyer ya hau kora mishi bayani…… Kusan minti talatin tukunna ya dawo ya sanar mishi lawyer d’in yace zuwa nan da jibi in shaa Allah komai zai kammala. Kaf a wajen! Y’an tsirarrun mutane da Granpa ne kawai suke farin ciki amman kowa a family d’in in ka kalli fuskarshi ba zaka iya tantance me ke wakana a cikin zuciyarshi ba, sai dai tabbas tashi d’aya zaka hango damuwa binne a k’ark’ashin komai. Ana i gobe takardun zasu iso, wato washegarin birthday! Wani mummunan al’amari ya afku.” Ajiyar zuciya Gwoggwo Asabe ta sauk’e kafin ta kalli sama hanyar staircase ( parlourn k’asan da yake da matattakalr staircase d’in biyu anyi tsarin wajen ne irin me high ceiling dinnan, mutumin da yake falon sama wanda ya had’a staircase d’in dama da hagu yana iya hango komai na k’asa, shima na k’asan haka, sai kuma hanyoyin dogon corridor biyu da suke kallon juna, d’aya yana a right staircase d’ayan yana kusa da left one. Sai d’akin special guest guda biyu da yake a main parlourn sama da kuma hanyar da zata had’a ka da benen da zai kaika chan sama). Sannan ta cewa Huda “kinga chan wajen?” Tayi maganar tana kallon falon saman, kafin taci gaba da cewa “Mommy tana tsaye tana waya a jikin k’arafunanan taba d’ab lek’o k’asa…… Ganin shigowar Dad Aslam da Arshaad a tare yasa gaba d’aya hankalinta ya dawo kansu tana yi musu murmushi, Arshaad ne ya hau kawo mata k’arar Auwal tun daga k’asan yana yi yana hawa benen, dan haka ta mayar da hankalinta a kanshi tana ce masa ‘ya taho a hankali kar ya fad’i..’ bata ida rufe bakinta ba dai dai Arshaad ya kusan k’arasawa inda take kawai kamar wadda aka turo sai k’ara akaji timm!!!A take kuma ihun Aslam ya karad’e gidan gaba d’aya… Da gudu ya k’arasa inda take kwance dukda cewa ta fad’o ne bisa wasu tumtum da suke kan kafet d’in k’asan, hakan bai hana kanta zubar da jini ba! Saboda ba duk jikinta ne yayi nasarar sauk’a a kan cuision d’inba!. Da kyar Dad ya iya k’arasawa wajen ganin yadda take kallon sama tana karkarwa yasa kawai ya yanke jiki a take ya fad’i sumamme dan shi a tunaninshi ma mutuwace zata yi. Banda ihun kiran Mommy ba abunda Aslam yake yi, wanda hakan ne ya jawo hankalin mai gadi ya iso.. Ya dad’e ya na knocking yaji shiru ga Aslam yanata rad’a ihu dan ita Mommy a lokacin mai aikin ta zuwa takeyi tana tafiya, kuma lokacin har ta tafi , so ita kad’ai ce sai su Dad da suka shigo wanda yake a sume! Kuma akai rashin sa a suka tura k’ofar bayan sun shigo ta shiga lock!. Arshaad kuwa, mutuwar tsaye yayi, ya k’ame k’am! In banda kallon wajen da take a tsaye kafin ta fad’o d’in ba abunda yake yi, dan har lokacin da mai gadi ya nemo mutane aka b’alla k’ofar aka shigo, Arshaad yana nan a yanda yake, dakyar aka iya janyeshi a wajen aka kaishi wajen Mammy, dan kurma ya koma musu, sai da yayi kwana biyu baya magana….. A asibiti kuwa da kyar aka dedeta numfashin Dad, bayan awa biyar Allah ya bashi ikon farfad’owa, garau ya tashi dan haka hankalin mutane ya d’an kwanta, saboda a yanda jinin shi yayi mugun hawa ba wanda bai yi mishi zaton stroke ba. Mommy kuwa da kyar aka tsaida jinin aka kuma samu ta farfad’o bayan kwana biyu sai dai kuma scan d’in da aka yi mata na kwakwalwa ya tabbatar da cewa jini ya shiga kwakwalwarta, wanda sai anyi aiki an kwashe an kuma d’inke inda ya samu rauni. Dad bai yadda anyi aikin anan ba, waje ya fita da ita aka yi komai, sai dai kuma tun kafin ayi aikin dama sun tabbatar da cewa ba lalle inta farfad’o ta dawo kamar daa ba sai dai a hankali, wasu kan iya d’aukar 1 year wasu 10 wasu 20 wasu kuma 4eva ma basu dawo normal d’in ba! But ita case d’inta minor ne so ana saka ran ma ba lalle ta d’auki 1 year d’inba in shaa Allah komai zai dawo normal. Granpa yayi mugun sauk’owa, ko dan ganin yadda hankalin Aslam ya tashi yasa shima nashi hankalin tashi, Allah kad’ai ya sani, dan tare ma suka tafi har shi da Mammy wadda itama ta d’aga hankalinta da ganin halinda Abokiyar zaman nata take ciki, dan da Dad yak’i biya mata kud’in jirgi ma da kanta ta biya ta bisu daga baya. Tunda aka yi aikin kuwa ita take kula da Mammy sai Dad yayi da gaske take yarda taje hotel ta d’an huta, tayi bacci. Aslam, tunda aka yi wa Mommy aiki, yake azumi kulli yaumin, har ranar data farfad’o. Da farko b’oyewa yayi dan ya san za a hanashi, dan har yi yakeyi kamar yaci abincin sai daga baya aka fahimta, ba yadda ba ai ba amman yak’i ajjiyewa, ganin haka yasa Granpa yace a barshi, sanadiyyar azumin da yayi tayi a jejjere gashi da k’arancin shekaru ya sanyashi kamuwa da cutar ulcer. Kamar yadda Likitocin suka fad’a, haka Mommy ta farfad’o amman a iya rayuwarta Aslam kawai ta iya ganewa, bata magana sannan komai sai an nuna mata sai an koya mata! Abu d’aya ta sani ta gane take iya fad’i, shine ‘ASLAM’. Anji ciwon hakan sosai, amman kwarin guiwar da ake ta samu a wajen manyan Likitoci ne yad’an kwantar da hankalin Jama’a, dan suna ta bada assurance d’in ‘zata dawo normal!’ Sai dai kuma ana yin wata d’aya komai ya burkice!!! Dan Aslam d’in da ta fara fahimta sai ya dawo ya zame mata dodo!!! Da farko yana shigowa zata fara kuka!! Sai kuma ta dawo ihu!!! Daga k’arshe dai ko asibitin in Aslam ya shigo tun kafin ya k’araso inda take zata hau kururuwa tana kuka kowa ta nan ne yake gane Aslam ya iso! Wani abun mamaki shine ta warke garau ta fara magana ta gane kowa amman fa ko a labari idan aka sako Aslam tou yanzu hankalin kowa zai tashi!! Ba k’aramin kid’ima Likitocin suka yi ba dan su kansu sun zama confuse..A iyaka sanin su masu irin wannan matsalar basa haka amman duba da suka yi da shi ta fara ganewa a lokacin data farfad’o ya sanya suka yi y’an bincikensu, iya abunda tunanin su ya basu ne ya sanya su dangantata da psychiatric. Allah sarki Aslam, a lokacin sai da ta kai ga shima aka bashi gado a asibitin tsabar tashin hankalin daya shiga. Yaro ne shi a lokacin amman kasancewarshi mai kaifin basira yasa ya fahimci komai. Dan zan iya ce miki har yau ban tab’a ganin Yaro mai wayo tarin ilimi da kaifin basira irin Aslam ba, har gobe in da wani d’an ajinsu da suka yi makaranta zai zo gidannan to ba zaki tab’a ji ya kirashi da aslam ba , sai dai suce mishi ‘gifted’ Dan wani abun time d’in a makaranta ba sai an koya mishi bama yake iyawa, in kuma ya iya to ya zauna kenan! Ga wayo kamar wani d’an shekaru dayawa.” Ajiyar zuciya Gwaggo Asabe ta sauk’e sannan ta ci gaba “A lokacin hankalin kowa a tashe yake, ni kaina da nake nan da ban ganta ido da ido tana haukan ba sai da naji a jikina, abu yak’i ci yak’i cinyewa har aka shafe wata biyu a haka, ga Aslam a kwance… Tausayin shi da ya lullub’e Granpa gashi yana ganin yana neman mutuwa ne yasashi fara nemawa Aisha magani gadan gadan ba kama hannun Yaro, duk inda yaji labarin Likitan kwakwalwa nan zai tarkata su su nufi k’asar! Cikin shekara biyu zan iya ce miki sun kusa zagaye duniya dan ba k’asar da ba a je ba, in dai kinajin ta kuma sananniyace. Amman dukda haka Allah bai kawo sauk’in ba, saboda lokacin samun sauk’in bai yi ba. Daga karshe dai hak’ura suka yi suka dawo gida Nigeria. Ai ana dawowa abun yafi na daa, ba k’aramin tsorata muka yi ba dan nima nazo a lokacin…Idan Aslam baya gidan nan to k’alau amman ko bakin MT yazo yanzu zata birkice, abun tausayi In kana nan dole kayi kuka, don Aisha mahaukaciya tuburan ta koma. Shawara d’aya Granpa ya yanke shine na ‘kai Aslam boarding school’ don samun sauk’in kowa and ya kamata yaci gaba da karatu kuma ya maida hankali saboda an barshi a baya sosai… A lokacin shekarunshi sun haura 14. Da kyar Aslam d’in ya yarda, ya tafi bayan Granpa yayi mishi alkawarin ‘duk inda magani yake a duniyar nan in dai akwaishi to zai nemawa Mommy d’insa, ko nawa ne kud’in ba zai gaji da biya ba, koda kuwa zai k’arar da duk abunda ya tara ne!!!’. Haka nan aka tarkata Aslam aka kaishi boarding cikin tsananin k’unci, yana kuka muna kuka ba dan munso ba. Wani abun takaicin ko hutu Aslam bai isa ya zo ba, sai dai In kana buk’atar ganinshi kai kaje ka ganshi a inda yake, k’iri k’iri zaman estate d’innan ya gagareshi… Ganin abun na Aisha bana k’are bane yasa suka kira wani babban Likita daga k’asar waje har gida Nigeria ya dinga kula da ita, shi ne ya bada shawarar a kulle su ita da Aslam a d’aki d’aya su kad’ai, for 24 hours, to kuma abun bai yi dad’iba don shi yayi sanadiyyar da Aslam ya bar k’asar nan wanda sai yanzu ne Allah ya dawo mana da shi! Da farko an tsara akan zai d’an dinga lek’owa Hutu sai yake sauk’a gidan Abba, yadda ba zasu had’u da ita ba, har zuwa lokacin da Allah zai kawo sauk’i Amman abunda ya faru a wannan rana ya sanya Aslam yin yaji mai mugun tsayi ya tarkata komai nashi ya tafi sai dai waya, shima wani lokacin sai yake gudun d’auka!. Arshaad da su Abba suna yawan zuwa duboshi, Auwal ne ma yaje sau d’aya, amman Arshaad a shekara ma yakan je sau biyu shi da Abba..saboda shi Aslam ko hutu idan anyi na makaranta baya iya dawowa sai dai yayi achan Oxford Uni inda yayi karatunshi. Aslam a Oxford yayi karatu, Arshaad kuma Dubai aka kaishi Auwal kuma Cairo. Da yake Granpa ne duk ya kaisu..duk da halin da Aslam yake ciki sai da aka fara k’ananan maganganu, Adama da Ummi, wai ‘har yanzu Granpa bai daina nuna bambanci ba’ Sosai Granpa da maganar ta koma mishi yayi musu tataas!!!Kuma ya taso da maganar mallakawa Aslam MT gaba d’aya inyaso sai yaga me za suyi!. Da kyar da sid’in goshi Gramma ta tausheshi, sannan ta lallabashi, sannan tai k’ok’arin fahimtar dashi abubuwan da hakan ka iya janyowa…. Awannan lokacin kuwa anci sa’a ya fahimceta sosai, don da kanshi kuma ya dawo yace ‘a tsakanin Auwal Arshaad da Aslam, duk wanda yaga he’s capable to shi zai mallakawa MT’. Dad yayi mugun mugun yin farin ciki daga jin wannan decision na Granpa, bawai yana zargin wani ba, kawai dai yaji releaf, kuma shima baya son bambancin da Granpa d’in ya dad’e yana nunawa especially tsakanin Arshaad da Aslam, don duk abun nan da ake yi ko sau d’aya Arshaad bai tab’a nuna b’acin ranshi ba, dukda kuwa uba d’aya ne ya haifesu shi da Aslam d’in, Idan akwai fitinanne tou Auwal ne! Amman Arshaad shi ba ruwanshi yana da kauda kai kunyarshi ce ma ta sanya Dad yake yiwa Mahaifiyarshi wani abun dan kar yaga ga kamar bai damu da ita sosai ba. Kowa idan zaki tambaya a estate d’innan ya baki sheda akan Arshaad to zai ce miki ‘yanada hak’uri da kauda kai da kuma saurin yafiya’. Aslam yana kammala degree na farko aka d’aura shi a matsayin MD na MT branch d’in dake achan k’asar da yake, wanda ada Abba ne a wajen. Ayyuka Aslam yake yi bashi da lokacin kanshima, kuma daman hakan yake so dan hakan ya tsarawa kanshi tun farkon komawarshi UK d’in, yana k’ok’arin kullum yaga ya zama busy dan kar ma ya bawa kanshi daman yin tunani.. Aikin kuwa ya taimakeshi ta b’angarori da dama dan Yana da nashi campny d’in a chan, na sarrafa takalma wanda k’wazonshi guminshi da kuma taimakon Granpa wanda yake aika mishi kud’i kamar hauka suka taimaka masa ya had’a ya bud’e wanda yanzu naji suna cewa yanaso ya bud’e wani branch d’in anan ko kuma ya dawo nan ma, gaba d’aya. Kuma akwai wani daban da zasu bud’e na zanen gidaje shi da Abba! Ga mt ga kuma karatu wanda a yanzu ya kammala PHD d’inshi… A b’angaren nasarori Aslam ya samu kam ba a magana sai dai kuma shi duk basa gabanshi, inda za ace ya tatttara ya bada abashi lafiyan Mahaifiyarshi na tabbatar kafin k’iftawar ido zai iya sallama komai! Ba shi kad’ai ba hatta mu duk tsawon wannan lokacin buri daya muke da shi shine ‘Aisha ta warke hankalin kowa ya kwanta’ Dan shi kanshi Aslam d’in abun a jiye mishi ne, saboda gaba d’aya rayuwarshi ya yita ne cikin fargaba, k’unci da damuwa. Yanzu haka ko Abokanai baya iya tarawa shi kad’ai d’insa yake komai sai dai a d’an dinga zumunci sama sama, Abokin shi na k’ut da k’ut guda d’aya tak a duniya wato Arshaad, da Arshaad ne kawai za kiji suna waya suna d’an raha amma ko mu y’an gida wani lokacin idan ka kirashi sai yak’i d’auka. Tsoronma shiga mutane yake yi balle yayi huld’a dasu.. Naji su Abba suna cewa ‘Kana ganinshi in dai ka fahimci yanayin shi tou tashi d’aya zaka fahimci he’s depressed! Kuma hakan ba a so a mutum especially mai k’arancin shekaru kamar nashi, zai hanashi yin farin ciki a rayuwa ne kwata kwata, har abada!.” Ahankali tace “To amman ya za ayi? Magani in dai sunanshi magani tou ba kalar wanda ba ayi ba amman har yanzu shiru............” Ta k’arshe maganar tana share d’an hawayen daya biyo idanunta a karo na ba adadi. Hudan, itama hawayenta ta goge, a ranta tace “Allah sarki bawan Allah, ashe shiyasa kullum yake cikin fushi, da har nake jin haushinshi.. In shaa Allah daga yau na daina jin haushinshi, Allah ya bawa Mahaifiyarta lafiya.” Maganar Gwaggo Asabe ce ta katseta jin tana cewa “Kema dan Allah idan kin yi sallah ki dinga sakamu a addua Allah ya kawo k’arshen wannan abu.” A hankali Hudan ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace “In shaa Allah” Sai kuma ta gyara zamanta ta ci gaba “Amman Gwaggo a duk cikin bayaninki banji inda aka yi mata Sauk’ar Alqur’ani ba!” Cikin katseta Gwaggo Asabe tace “anyi sauk’a Huda, Granpa da Dad da kansu suka je suka raba kud’i lokacin da suka dawo farko farko a islamiyoyi da tsangayar almajurai aka yi ta sauk’a!.” Murmushi Hudan tayi sannan tace “Gwaggo Asabe, idan zan bada shawara a d’auka inaga daa mu da kanmu ya kamata muyi mata sauk’ar bayan an raba a islamiyoyin, kuma in na fahimceki kamar sau d’aya aka tab’a yin sauk’ar ko?” Bata jira jin mai Gwaggo Asaben zata ce ba ta ci gaba “Ni a lokutan baya, idan bamu da lafiya ko wani alamari mara dad’i ya afku Tou bayan Mama ta bamu magani sai ta kammala mana sauk’a, ko lokacin da nake k’arama akwai Yayanmu da yake shaye shaye sai da Mama tayi mishi sauk’ar AlQur’ani sau bakwai!! Ta fara tayi sau hud’u ya warke ya daina amman dake tayi niyyar bakwai d’in zata yi sai da ta k’arasa. Da kuma muka yi wayo haka zata rarraba mana muna tayata da ni dasu Ya Jalila koda izu d’ai d’ai ne mu kan taimaka. Ko yanzu haka In wani abun ya faru rabawa muke yi ni da ita da Sakina wani lokacin da Sumayya, bama wata d’aya muke k’arasawa, in kuma mun kwallafa to a sati muke idawa. Balle nan gidan munada d’an yawa.. Yanzu for example ace mutum shidda kowa ya d’auki izu goma, duk bayan sallar Farilla kayi izu d’aya a kwana biyu fa za mu dinga kammalawa, In kuma izu biyu za ana yi a cikin kwana 1 mun kammala, inda hali kowa in ya kammala sai yayi mata addua dafatan waraka bayan an tofa aruwa a bata tana sha, Daganan ayita yi, kuma akai akai. In Allah ya yarda sai kiga an dace. Dan dai gaskiya kamar yadda kika fad’a abun sam kamar bana asibiti bane ba! Koda ace ma na asibitin ne Sauk’ar Alqur’ani fa shine k’arshen waraka Especially idan mune muka yi da kanmu, saboda waennan na islamiyya ba mu da tabbas, yanzu duniya ta chanja ba lalle In sun karb’i kud’in suna sakawa anayi ba…..” Maganarta ce ta katse jin mutum a tsaye a bayanta ya dafa kanta, tana juyowa sukai ido hud’u da Dad da Abba a bayanshi suna murmushi, waenda shigowarsu kenan suna d’an tatauna wata magani suka ji bayanin Hudan. Dad ne yace “y’ar albarka, naji dad’in wannan shawarar taki sosai. Kuma daga yanzu in shaa Allah zata fara aiki. Kafin masu kwashe kaya su gama na san mun kammala in shaa Allah, na yau.” Yana gama fad’in haka ya d’au waya ya kira Arshaad da Aslam yace “su sameshi.” Sai da ya gama wayar, Hudan ta d’an zame daga kan kujera inda take ta shiga gaida Abba. Shima Dad d’in ta sake gaidashi. Cikin kulawa suka amsa mata sannan suka cigaba ta tattaunawarsu da alamun magana mai muhummanci suke yi. Hudan sai d’ar d’ar takeyi a tunaninta kar Abba yai mata fad’an abunda tayi mishi jiya, shima ya lura da yanayin ta shiyasama ya fasa zuwa inda take, amman da yayi niyyar jin yadda ta kwana da kuma jin ko akwai abunda takeso dan harga Allah shikam yana so ya zama tare da y’arsa ya jaa ta a jiki ko sa samu su saba da juna sosai. Arshaad ne ya fara shigowa… Tsayawa Hudan tayi tana kallonshi dan ta manta rabon da ta ganshi da k’ananan kaya, yafi ta’ammali da shaddodi da yadi, sab’anin yau da yake sanye da wata shirt army green dark an rubuta ‘KING’ a jikin gaban rigar da zanen crown d’in king d’in ata k’asa. Rigar irin mai d’an kama jiki ce, hakan ya taimaka wajen fito da ainahin surar jikinshi dan kana iya hango packs d’inshi na sama sama ta cikin rigar da yadda dantsen hannunshi yake a mummurd’e! Wandon nashi shima ba jeans bane yana yin rigar ne black in colour bai kamashi ba kwata kwata ta sama amman roba ne, kasancewar ya d’an matse daga guiwar wandon zuwa k’asa yasa ya zama kamar pencil trouser ta k’asan… Kayan yayi matuk’ar fito da asalin surarshi ta giant! Ga wani fitinannen k’amshi mai tsayawa a rai da yake zubawa dan tunda ya shigo parlourn ya karad’e da k’amshin shi, tun bai iso inda suke ba…. Hudan bata gama k’are mishi kallo ba suka had’a ido da shi, gira d’aya ya d’aga mata yana d’an murmushin gefen baki, da sauri ta sunkuyar da kanta k’asa kunya duk ta lullub’eta ganin ya kamata tana kallonshi . Ganin yadda tayi ne ya sanyashi sakin wani lallausan murmushi, kafin ya k’arasa inda su Dad suke ya shiga gaidasu cikin girmamawa. Ya so ya k’arasa wajen Hudan dan shima ba k’aramin kyau tayi mishi cikin rigar abaya blueblack mai stones, d’aurin da ta yiwa kanta da d’ankwalin abayan ya yi matuk’ar burgeshi! Amman sai Dad ya tsareshi ta hanyar fara yi mishi bayani abunda za suyi ba tare da b’ata lokaci ba, 100%ya amince da kuma jinjina ga wanda ya kawo shawarar dan abunda ya kamata ayi kenan, cikin jin dad’i Dad yace “ai Hudan ce” da d’an murmushi ya juyo yana kallonta, yanzun ma sauri tayi tai k’asa da kanta, don still satar kallonshi take yi, harga Allah Ya Arshaad yayi kyau yau sosai…… Tana wannan tunanin hancinta ya fara jiyo mata wani k’amshi na daban, wanda a take ya cika mata hanci, kuma ta fahimci wanene Kasancewar a kan kujerar dake gaban side d’inshi take ne yasanya ta fara jin k’amshin kafin kowa, bata san daliliba ba kuma tasan mai ya faru ba, amman ko lokacin idan anyi laifi a islamiyyarsu za a dakesu tabbas zuciyarta bata yin kalar bugun da take yi a yanzu…. A hankali ta runtse idanunta ta sake yin k’asa da kanta jin takunshi a daf bayanta!Sannan bugun zuciya da k’amshin da yake shak’a na k’ara yawa…. Kamar yadda Arshaad yayi shima hakan ya gaida su Dad waenda suke ata gefe kad’an kusan hanyar shigowa sai dai shi bai k’arasa inda suke ba, hasalima zagayowa yayi ya zo kan kujerar da Gwaggo Asabe take ya zauna.. Kasancewar Gwaggo Asabe a 3 seater take zaune Hudan kuma a 1, sai ya zamana kamar suna facing juna shi da Hudan! A hankali ya d’ago idanuwanshi ya sauk’e su a kanta, da tayi k’asa da kai wanda ita kanta ta kasa tantance dalilinta na yin hakan Magana Gwaggo Asabe take yi mishi amman kamar ma baya jin ta, ganin hakan yasa ta d’an tab’a shi kad’an.. Lumshe idanunsa kawai yayi kafin ya bud’e su ya sauk’e a kan Gwaggo Asabe, d’an murmushi kad’an yayi mata kafin yace “barka da gida”. Cike da tausayawa Gwaggo Asaben take kallonshi, ko ba a fad’a mata ba ta san tun d’azu da ya fito daga d’akin Mommy yake cikin tashin hankali!! Dan gashi idanuwanshi sunyi jaaa sosai bakinshi yayi pink shima hatta kan hancinshi yayi jaaa Amman kuma ko ba a fad’a mata ba ta san ba kuka yayi ba wanda wani lokacin har addua take yi Allah ya bawa hawaye ikon fitowa daga idanun Aslam ko ya samu ya rage rad’ad’in da zuciyarshi take ciki. Hannunta ta d’aura akan lallausan gashin kanshi ta d’an shafa… Hakan ya sanya shi sake maida hankalinshi a kanta! Tana shirin yin magana Dad ya fara yiwa Aslam bayanin abunda ya tarasu anan bayan ya zagayo ya zauna, Abba ma ya zauna. Ajiyar zuciya Aslam ya sauk’e bayan ya gama sauraron Dad wanda ya k’arashe maganar shi da cewa “Zamu fara yanzu saboda mu samu mu gama akan lokaci kafin a gama Parking su Abba su tafi” A hankali ya juya ya kalli Abba kafin yace “Abba ka bari I’ll speak with Granpa, dan Allah don’t leave.” Murmushi Abba yayi ya mik’e daga kan kujerar da ya zauna ya k’araso inda yake kafin ya dafa kanshi tukun yace “Karka damu Aslam, ai bamu da nisa anytime kakeso zaka iya visiting, ni kaina i need some time with my daughter, wanda in muna nan na san Granpa ba zai barni ba, and ya dinga k’untata mata kenan, ni kuma from this time forward inaso In bata cikakken kulawa da happiness d’in da ban bata ba a baya, so we need some space from him, Daddy kuma he wants to leave ne saboda yaci ace Granpa ya fara rage abubuwan da yake yi. In bamu tashi mun tsaya munyi mishi haka ba, al amarin family d’innan ba zai tab’a daidaituwa ba! I hope u understand” Yayi maganan yana shafa kanshi, a hankali Aslam ya sauk’e ajiyar zuciya a karo na ba adadi sannan ya d’auke idanuwanshi daga kan Abba wanda tunda ya fara magana ya kafe shi dasu, a hankali yace “shikenan” sannan ya mik’e ya wuce zuwa inda ya fito yana cewa “zan fara daga Fatiha zuwa Nisa’i ayat 147! Someone should continue from were i stop.” Yana gama fad’in haka ya shige ya jawo k’ofar shi ya zuge. Dad ne yace “Abba ko zaku tafi tare, kasan yadda kuka saba da shi, and ga incidence d’in daya faru d’azu kar abun yai mishi yawa” “Ba zai yarda ba but let me try” Inji Abba, ya mik’e yana k’ok’arin shiga side d’in Aslam d’in. Dad ne yace mishi ya tsaya tukunna… Sai da suka tsara yadda za suyi, su mazan za suyi arba’in d’in sama, Huda kuma da Gwaggo Asabe za suyi ashirin d’in k’asa, kowa ya d’auka izu goma goma… Tukunna Abba ya nufi side d’in Aslam. Kamar yadda yace d’in kuwa sam Aslam k’in yarda yayi ya bishi hakan yasa ya hak’ura, ya zauna a d’akin yana d’an kwantar mishi da hankali, daga nan suka hau karatu a tare suka kammala nasu, dede ana kiran sallar azahar… A chan parlour ma Huda da Gwoggwo Asabe kusan tare suka kammala, Dad ne ma da Arshaad suka d’anyi delay don suna hawa sama Mommy taci gaba da kuka da kyar suka lallab’ata tukunna suka samu suka yi nasu. Sunyi addua sosai, kafin su samu ruwan zamzam aka tofa mata aka bata tasha aka shafa mata…. K’arfe hud’u dai dai komai ya kammala, duk sun shirya kaya kuma an gama jidesu, sai y’an tsirrai da za suna kwasa a hankali a hankali, waenda ba wani important bane!. Abba Dad da Daddy ne suka nufi wajen Granpa don yi mishi sallama.. Har sun kama hanya Daddy ya juyo ya cewa Arshaad “yaje ya samu Auwal yace masa ya kawo wannan Yarinyar nan sannan ya tabbatar komai d’inshi ya zama ready dan suna fitowa za a tafi” Da to ya amsa har ya juya ya nufi k’ofa ya jiyo wadda ta biyo shi da d’an sauri tana ki ranshi a hankali ya juyo yana kallonta Sai da ta k’araso ta d’anyi k’asa da kanta tana wasa da y’an yatsun ta tukun tace “Ina wuni.. Dan Allah ka ara mini wayarka zan kira Mama”. B’ata rai yayi kafin yace “Nima ba zan kulaki yanzu ba” Yana d’an turo baki kamar wani k’aramin Yaro. Dariya ma ya bata dan haka ta d’ab yi y’ar dariya mai k’aramin sauti kafin tace “To kayi hak’uri naga su Abba ne shiyasa kuma ka d’an yi nisa ne, da kana kusa da sai mu gaisa” Murmushi kawai yayi ya mik’a mata wayar sannan yace “bara yaje ya duba Auwal kar suyi ta jiranshi…” Huda ba k’aramin tashin hankali ta shiga ba dajin Mama na asibiti an sake admitting d’inta har yanzu, Sakina sai k’ok’arin kwantar mata da hankali take amman taki hak’ura, barema da taji wai an mata har eco, gashi ance Maman tana bacci ba zai yiu suyi waya ba!! Kwata kwata sai ta gaza kwantar da hankalinta, dan haka kawai tabi Ummu da ‘to’ bayan tace mata tayi hak’uri ta d’an Kara jira Amman tasa a ranta yanzu zata samu ya Arshaad ya kaita emergency d’in… Tana cikin wannan tunanin bayan sun gama wayar, wayar Arshaad ta hau k’ara! Kiranshi akeyi akai akai, gashi ya fita. Ganin an jera mishi sama da 20 misscalls ne ya sanya ta yanke shawarar kai mishi wayar. A bakin gate d’in gidan ta tambayi mai gadin ko “Ina Arshaad d’in yayi?” Opposite gidan da yake kallo wanda take ya nuna mata, dan haka ta nufi gidan....... Tun lokacin da Auwal ya dawo daga wajen Mom ake kai ruwa rana da Jalila har yau da suke shirin barin gidan! Dan tace “wallahi ba zata je wajen wata Gwaggo Asabe ba, kuma ba zata koma gidansu ba! Ta gano wayo yake so yayi mata ya yakiceta, ai tunda babanshi yace baya sonta ta san in dai ta yarda suka bar gidan babu ita tou shikenan magana ta k’are” Bikin ma cewa tayi “ta fasa zuwa” gashi ta amshe kud’i, tace “sai anje sabon gida an nuna mata d’akinta ta zuba kayanta tayi settling tukunna maybe taje” Tace kuma “In ya tilasta mata a yau sai ta tona mishi asiri, wallahi.” Auwal kamar yayi hauka, gashi an gama kwashe kaya ya san shi kawai Daddy yake jira ya kai Jalila sannan yazo su tafi, ga kuma batun ta na zata tona mishi asiri, kar fa Yarinyar nan ta jik’a mishi aiki!! A daa yana underestimating d’inta yanzu kam ta fara bashi tsoro gaskiya, he has to do something, duk da cewa Mom tace mishi ‘ya jira ta tana dawowa zata yi maganinta’ amman gaskiya he cant wait!! Yana tsoro kar kwab’arsa tayi ruwa, gara kawai ya k’are komai dan shi gani yake ma it’s like sun rabu da Arshaad d’in tunda ta sameshi dan haka tayaya zai iya breaking d’inshi!!! Takaici ya taru ya yiwa Auwal yawa, ga Jalila sai maganganu take yab’a masa… Da kyar ya iya controlling kanshi dan ji yake yi kamar yaje ya rufeta da duka ko ya samu sauk’i! A hankali very calm ya k’arasa inda take ya kamo hannunta Da sauri ta fisge hannun kafin tace “Ai wallahi anyi an gama babu k’ari!! Mayaudari kawai, haka kurum ka cuceni! Ga wasu zantukanka waenda har yau na kasa fahimtar alk’iblarka a kaina..” Cikin tsananin fushin da ya kasa dannewa yace “na cuceki ko kin cuce ni?? Ke kin San ko waye ni kuwa? Wallahi ba dan abunda na shirya akan ki ba ko a y’ar aiki ba zan tab’a yarda ki zo mini ba! Kina magana kamar irin dole d’innan nayi miki, Ina ce da yardarki kika bini har gidan? Zaki wani rainawa mutane hankali, wallahi ki bini a hankali tun ban fito miki a asalin Auwal d’ina ba!! Magana kad’an In anyi kice wani ‘za kije ki tona min asiri’ To bari kiji, tsaf! Zan iya cewa Daddy na maidake gida! In kulle ki anan yunwa ta kasheki daga baya in zo in fitar da gawar ki babu wanda zai ji labari, tunda itama uwarki kwad’ayi ya rufe mata ido ai bata cewa kowa kina nan ba! Stupid useless girl kawai! Banza wadda bata da daraja kwata kwata, Akuya ma ta fiki daraja tunda ita wani lokacin tana guduwa tana jan aji, ke kuwa ana ce miki kule za ki ce cass!.” Takaici da tsoro ne suka sanya Jalila fashewa da kuka, wani irin takaicin Umma take ji yana taso mata.. Shiyasa fa ita tayi ta dodging, har ga Allah irin rayuwar nan da yadda ta yarda dashi nan da nan ba hakan ta tsarawa kanta ba! Ita dai ta san tanada burin son auren mai kud’i, amma kalli yanzu yadda ta koma, duk ata dalilin biyewa son zuciyar Umma, gashi ta hanata zubar da cikin, kamar ba ita ta tsugunna ta haifeta ba! Tunda take ba a tab’a yi mata zagin daya girgiza taji haushinshi ba kamar kalar zagin da Auwal yake yi mata especially na yau dan ko ranar daya maidata gida bata ji ciwon zagin kamar na yau ba, kuma gaskiya ya fad’a!. Gashi yanda taga ya birkice tabbas zai iya aikata abunda ya fad’a d’in… Kuka take yi bil hakk’i da gaskiya. A take ta gama tsarawa kanta zata ce a zubar da cikin kawai ta koma wajen Umma, kowa ya huta. Ganin yadda tayi ladab ne ya k’ara bawa bawa Auwal kwarin guiwar aiwatar da abunda kwakwalwarshi ta shirya mishi yanzun nan, dan haka ya k’arasa inda take tsugunne shima ya tsugunna, fuskarshi ba alamun wasa yace “Look Jalila, let’s just get this done over with… Zan baki 5 million” Da sauri ta d’ago manyan idanuwanta tana kallonshi. D’aga kanshi yayi alamun ‘yes’ sannan yace “Miliyan biyar!” All I want you to do is ‘Kice cikinnan na Arshaad ne, kuma in sama da k’asa zasu had’e kar ki chanja maganan ki, ko a gaban waye, ke hatta uwar data haifeki inaso ki birkice mata kice na Arshaad ne kawai!’ Gaskiyar Maganar ya tsaya daga ni sai ke. Kar ki damu In komai yazo gangara ni zan san yadda zan yi, komai zai fita normal, ba zaki samu wata matsala ba, understood???”. Rarraba ido ta fara yi tana k’ok’arin yin magana, suka jiyo sallamar Arshaad. D’agowa sukayi dukkansu suna kallon hanyar shigowa. Cikin takunshi ya k’araso cikin parlour… Wani killer smile Auwal yayi kafin ya mik’e tsaye yace “D’an halak! Maganar ka muke yi” Cikin nutsuwa Arshaad d’in ya k’araso inda suke, kallon Jalila yayi yaga yanda take kuka, a ranshi yana mamakin ina Auwal ya samota haka, gashi sai kuka take yi… Ganin ba wannan ne ya kawo shi ba yasa ya d’auke idonshi a kanta ya maida kan Auwal d’in sannan yace “Daddy is waiting, infact everyone, for you, kayi sauri dan yace karka bari yazo ya sameka a nan!” Yana gama fad’in haka ya juya ya fara k’ok’arin fita. Da mamaki Auwal yake kallonshi da Jalilan wadda tunda Arshaad d’in ya fara magana take kallonshi, Ganin arshaad d’in na shirin fita ba tare da ya ma sake kallon Jalilan ba yasa Auwal yin ta maza ya zagaya ya tsaya a gaban shi sannan yace “Saurin me kake yi? I’m just trying to clean up your mess here fa, amman kayi kamar ma baka santa ba, ko In barta ta tafi wajen su Abba ne?” D’an dakatawa Arshaad yayi sai kuma ya juya yana kallon Jalilan.. Da ido Auwal yayi mata signal d’in da ta kasa ganewa, ita dai kawai sai ta mik’e, kamar an tsoma ta a ruwa jikinta na d’an rawa. Murmushi Auwal d’in yayi sannan ya zagayo yace “Talk mana Jalila, ko tsoronshi kike ji yau kuma?” Kame kame Jalila ta fara yi, ta rasa ta Ina zata fara dan Bata san me zata ce ba, gashi duk da halin da take ciki tunda taji Auwal ya ambaci miliyan biyar ta rikice, hali zanen dutse!. Don haka tace “Daman nazo ne akan maganar mu” Tayi maganar jikina na d’an karkarwa dan har yanxu k’irjinta bugawa yake yi… yau ce rana ta farko data tsaya ta k’arewa Arshaad kallo!! Ita dai tun lokacin da yake zuwa wajen Hudan ta san yana burgeta kuma yanayin shi, maganarsa, tsayi da k’amshin turarenshi suna mugun k’ara kid’imata! Kawai dai ita ta san tana so Arshaad har cikin zuciyarta, amman yau data tsaya ta k’are mishi kallo ta sake rikicewa kuma ta tabbatar idan har bata sameshiba to ko dai ta mutu ko kuma ta shiga hauka… K’irjinta in banda bugawa babu abinda yake yi, gashi ya tsareta da dogayen shanyayyun idanuwanshi, cikin tsare gida yace “Wacce magana kenan?? Do i know you?” Wata dariya Auwal ya saka kafin ya k’araso yana cewa “Okayy!! Bari in yi maka dalla dalla.. Maganar cikinka wanda ke a jikinta! Shi ta biyo ka ku k’arasa.” Arshaad zuwa yanzu yazo wuya! Don haka ya yanke shawarar cin uban Auwal dan ya lura bayan rainin hankalin da yake yi mishi, harda hauka ma ya fara damunshi kwana biyu, gara a yita ta k’are ko zai dawo hankalin shi, in hauka ya za ayi ya d’auko Yarinyar da bai tab’a ganiba a rayuwarshi ya hau yi mishi wani maganan banza da wofi??! A fusace ya juyo yana shirin yin kan Auwal, sukaji k’arar fad’uwar abu, da sauri duk suka juya suna kallon k’ofa.. Arshaad, ya san yana da gaskiya amman kalar kallon tuhumar da Hudan take yi mishi da kuma yanayin fuskantar, ne ya sanya gabanshi yayi mugun fad’uwa sannan wata zazzafar zufa ta hau keto mishi, tabbas ya san taji shirmen da Auwal ya gama fad’a yanzu. Auwal kam tsayawa yayi yana kallonta yana mamakin tsananin kamanninta da Abba da Aslam! “Who’s she!?” Ya fad’a a hankali ba tare da kowa ya jishi ba. Chan kuma sai ya tuno da case din y’ar gidan Abba da har ta kaiga kulle su Mom d’inshi a cell! Antake kwakwalwarshi ta d’au chaji, don haka a zafafe ya nufeta, daman neman ta yake yi ya kora mata warning!! Jalila kuwa tsorone ya rufeta ganin Huda, a tunanin ta Umma ce ta fad’i inda take, su kuma suka zo har da su Kaka tafiya da ita, dan haka karkarwar jikinta ya tsananta ba abunda take tunawa irin auren ta da Mati mai wanki ta san yanzu kam babu fashi!. Cikin zafin nama Auwal yana karasawa inda Huda take tsaye yace “Hey! Couz… You must be Huda right? Inaso kije ki samu uban ki kice mishi......” Cikin katseshi Arshaad wanda shima ya k’araso inda take yanzun yace “Huda lets go don’t mind him, he’s crazy!! Muje kawai za mu yi magana a waje.” Ya k’arashe maganar yana durk’usawa don k’ok’arin d’aukar wayarshi data jifar a k’asa. Hudan ita kanta bata san tana da kishi irin haka ba, sai yau. Wato ba zai ma iya fuskantanta a gaban Jalilan ba?! Gashi yadda duk ya rikice jikinshi yana d’an karkarwa yasa ta d’aura ayar tambaya akanshi… Ita Arshaad zai yiwa haka? Why? Of all people kuma yayarta!!! Bata san lokacin da ta fashe da wani irin kuka ba!. Ai kuwa a rikice, Arshaad yace “Oh nooo, Huda dan Allah kar muyi haka dake mana, na rantse miki da girman Allah ban san wacece waccar ba! Ban tab’a ganinta ba a rayuwata, wallahi! Muje waje we ‘ll talk outside.” Yai maganan yana k’ok’arin kama hannunta.. Da sauri ta fisge cikin kuka tace “Don’t touch me! Ai dole kace baka santa ba mana, Ya Jalilan ce baka sani ba? Daman Mama tace min rannan kaje kana nemanta, kuma nima naji Umma ma rannan suna wani magana da Anty Zainab dana kasa fahimta a kanka kaida Ya Jalila. And if baka santa ba mai take yi a nan ya akayi ta san gidanku da ni kaina ban saniba? Ana tunanin tana gidan Anty d’inta a gida ashe tana wajen ka! I trusted you,I tot.....” Arshaad kam zuwa yanzu ranshi yayi mugun b’aci dan a tunaninshi ko Sakina ce zata fad’awa Hudan wannan maganar a kanshi bai ci ache ta yarda ba, balle a bakin mutumin da bata tab’a gani ba sai yau! Dan haka cikin katseta yace “Ba kiyi trusting d’ina ba Huda! Tunda gashi har kin d’auki maganan da aka fad’a miki a kaina… Rantsuwa ta k’arshe da zan yi miki shine ‘wallahi ban san Yarinyar nan ba!’ Mutum d’aya na sani a gidanku age mate d’inki itace Sakina. Kuma ban san wanne Arshaad d’inne yaje nemanta gida ba rannan d’in da kikace, amman bani bane ba!. Maganar su Umman shima i don’t know anything about it, wallahi!. Anyways Na gode da irin shaidar da kika yi mini.. Hudan aure za muyi ya kamata ace kinyi trusting d’ina tunda as far as i know inda ace ni d’an iskane da tuni ke zaki fara fad’a ba wai ita ko shi ba.” Yana gama fad’in haka ya juya ya fita dan in ya ci gaba da tsayawa a wajen zai iya yin abunda zai yi ending up yana regretting… A hankali Hudan ta k’arasa ciki wajen Jalila ta kama hannun ta kafin tace “Ya Jalila” Cikin kukan makirci Jalila ta fashe da kuka ta rungune Hudan kafin tace “Hudan Allah da gaske ne abunda Auwal ya fad’a yanzu, gashi na kasa fad’awa kowa, ban san ya zanyi ba! Arshaad ya cuceni.” Ta k’arashe maganar da wani mugun kuka, don ta lura Hudan ta yarda da ita,,dukda kuwa har yanzu tana cikin rud’u akan ‘’me Hudan take yi a gidan’ Dan kalaman Auwal da yadda yace mata cousin ya sake dilmiyar da tunanin ta… Amman yanzu ba wannan ne a gabantaba, raba Hudan da Arshaad shine first! Ga kuma zancen miliyan biyar! Don haka dole ta ajjiye komai a gefe ta duk’ufa ta cimma burinta. Da kyar Hudan ta lallasheta, ta samu tayi shiru.. Rasa abunyi yasa Huda tace mata “bara taje ta dawo” da taso ta tafi da ita, amman tak’i, dan haka ta mik’e tace “tana zuwa, tukunna sai su san me za suyi” Cikin share ragowan hawayenta ta d’agawa Hudan kai, Hudan kuma ta fita a zuciyarta tana rayawa yanzu zata kira su Ummu dan ba zata iya wannan abun ita kad’ai ba! dole a kwatarma Jalila hakk’inta, tana tafe zuciyarta na tafarfasa, ita kawai idonta ya rufe da kishi har ya kaita ga kasa yin lisaafi mai kyau a kwakwalwarta. Jalila na ganin fitar Huda ta share hawayenta ranta fess! Sannan ta mik’e ta k’arasa inda Auwal ya daskare yake k’ok’arin hada 1+1 akan alamarin da ya gudana yanzun nan dan in dai shi ba dak’ik’i bane ba tou abu na farko daya fara fahimta shine ‘Arshaad Huda yake dating!’ And tabbas bai san Jalila ba, to who….. Muryar Jalila wadda ta k’araso yanzu ne ta katseshi jin tana cewa “Nayi duk abunda kace, yanzu abunda nakeso da kai shine ka kawo miliyan d’aya, ragowar kuma in aiki ya kusan kammaluwa, dan..” Shak’ar!! Da yayi mata ce ta katse mata maganar tata, cikin d’acin zuciya da k’arfi yace “Who are you?”. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 40 Sai da yaga numfashinta yana shirin d’aukewa tukunna yayi wurgi da ita sannan ya sake jeho mata tambayar “who are you??” Yana huci. Cikin tsananin tsoro Jalila take kallonshi kafin ta ankara taga ya sake yiyowa kanta yana shirin damk’ar wuyanta a karo na biyu, yace “Naga take taken baki da shirin fad’amin gaskiya ta cikin sauk’i!” Da sauri cike da tsoro Jalila tace “me kakeso ka sani to?” Tana mai ja da baya. “Wacece ke! Meye alak’ar ki da Arshaad sannan mecece alak’ar shi da wachchar Yarinyar??!” Da sauri tace “wajenta yake zuwa a gidanmu! Ni ban tab’a ganinshi sosai bama sai yau, ban sanshi ba bai sanni ba! Ai kaine kace ince na sanshi, amman ni bamu tab’a magana bama sai yau!!” Takaici ne ya hana Auwal yin magana.. Chaan, kuma cikin tsananin b’acin rai yace “kin san da duk wannan amma shine baki tab’a gayamin ba sai yau?” Ya k’arashe maganar cikin tsawa!. Jalila gaba d’aya duk ta rud’e ta gaza fahimtar inda Auwal ya dosa. Gashi yadda taga ranshi a b’ace tayi mugun tsorata hakan yasa cikin rarrashi tace “To ai naga nayi abunda ka fad’a ko? Gashi har sunyi fad’a! Menene kuma laifina a nan?”. Da k’arfi yake sauk’e ajiyar zuciya! Tabbas Micheal yayi masa shirme to amman kuma ta bakin Jalilan ‘ai gashi sun yi fad’a!’ One of abunda yake so ya faru ai farun ai at last! But still ya zama dole ya koyawa Jalilan itama hankali.. Fuskar nan babu walwala ya kalle ta, kafin yace “Mai yasa da na fara zuwa, baki fad’amin cewa baki da alak’a da shi ba? Eh? Kika barni a duhu?” Cikin rashin fahimta tace “Wallahi ni ban gane komai ba! Dan Allah ka fahimci ni”. Shiruuu, Auwal yayi yana d’an nazartarta yana kallonta.. Chaaan! Kuma yayi tsaki kafin yace “kije ki tattaro kayan ki, ki wuce wajen Gwaggo Asabe, i’ll get back to you, idan kuma zaki zauna anan d’in ne to zan iya barinki but ki tuna abunda na fad’a miki d’azu!”. Da sauri ta nufi d’akin ta na sama, kafin minti goma ta tattaro komai… Auwal ji yake kamar ya shak’e ta yayi ta dukanta! Kawai dai ya barta ne ya samu ta rabu dashi for now dan bayaso Daddy yazo kiranshi da kansa! Amman tabbas sai ya koya mata hankali, dukda ya fahimci kamar jahilcinta da dak’ik’ancinta ne ya janyo komai.................. A gate d’in estate ta had’u da su duk sun fito har Gramma wadda ta kawo su Shuraim don tun jiya da suka k’i bacci da safe kuma suka dinga yiwa Abba kuka akan suna son Ummi ta dawo, ya kaisu wajenta. Da kyar ta lallab’asu bayan tace musu “Ummin tayi y’ar tafiya ne amman soon za su dawo, suyi hak’uri.” Hudan tana k’arasowa Gramma ta kamo ta, tace “Ki kwantar da hankalinki Ki bisu kinji, na san kina kewar Maman ki, amman na san Abba da kansa zai kaiki idan komai ya gama daidaituwa, kinji y’ar albarka?”. Anhankali ta d’aga mata kai tanajin k’aunar matar da girman ta suna ratsa zuciyarta. Dad shima abunda ya fad’a mata kenan sannan yace “duk abinda take buk’ata idan sunje ta rubuta ta bawa Arshaad ya kawo mishi,,already anyi mata d’an siyayyan abubuwan da zata buk’ata for now suna cikin mota.” Da “to” da kuma godiya shima ta amsa mishi. Auwal yana fitowa daga mik’a Jalila wajen Gwaggo Asabe suka fara shirin tafiya… Abba ne ya bud’e mata gaban wata mota yace ta shiga, tana shirin shiga dai dai nan Gwaggo Asabe wadda ta fito yanzu ta k’araso taja Hudan tayi hugging d’inta, ji suke kamar kar su rabu dan har sun saba a cikin y’an wuni biyun da suka yi tare. Auwal yana gefe in banda tab’e baki babu abunda yake yi, ji yake kamar yaje ya shak’e ta! Shi fa ya tsani yaga ana fifita wani, kuma ya lura kamar hakan a jinin y’an gidan yake! k’iri k’iri sun iya nuna banbanci…..gashi yanzu ma akan y’ar k’ank’anuwar Yarinya an kwashe Surukan gida kaf! An kai cell, an bar mahaukaciya!…. Ya ja tsaki yafi a k’irga k’arshema mota ya shige yana ta mita a ranshi yana cewa “Kamar duk ba a tsatso d’aya muka fito ba!” Mu an maida mu kamar wani bole especially ma ni….kowa idan ya tashi k’orafi sai kaji yace ‘Auwal’.” Shi kad’ai haka yayi ta mita yana ta faman kumbure kumbure.. Su kam bama su san yana yi ba. Sallama suka yiwa juna kafin Gramma ta ruk’o hannunta (Hudan) da kanta ta saka ta a mota ta juyo. Daurewa kawai take yi, amman Abba yana zuwa da yayi hugging d’inta sai ta kasa ci gaba da daurewa ta fara hawaye. Da kyar suka lallasheta sannan suka maidata gida, suka fito, suka kama hanya ba dan ransu yanaso ba, suka fice a estate d’in suna masu jin dumbin kewar gida cike a zuk’atansu. Suna fita suka had’u da motar Kaka da Madu, horn suka d’anyi musu don haka suka dakata! Dan shi Abba bai ma gane su ba. A D’an gaba kad’an suka yi parkin, dan haka suma su Kaka suka juyo da akalar motar tasu suka isa inda suke suka yi parking…. Suna fitowa Abba ya ganesu dan haka ya k’arasa ya cewa su Aslam su zauna a motar, shi da Dad kuma suka fita suka samesu. Suna wucewa itama Hudan ta fara k’ok’arin bud’e k’ofar amman sai ta jita a rufe! Cikin d’an tsare gida tace “zan je wajen Kakannina!” A k’ufule yace “Baza ki ba!” Wani takaicine ya rufe ta taji kamar ta rufeshi da duka, taya ga su Kaka tana kallo suna kallonta, amman ace ba zata je wajensu ba? Inaaa, ba zai yiu ba! Dan haka ta fara k’ok’arin bud’e k’ofar ta k’arfi! Tun k’arfinta. Ta gefen ido yake kallonta, tanata dambe da handle d’in motar, tun k’arfin ta. Ta fi minti biyar tana fama ganin ta kasa yasa ta juyo da d’an ladabi tace “Ya Aslam dan Allah ka bud’e inje wajen su mana.” Ta bashi dariya sosai amman ya danne, still amsar d’azu ya sake maimaita mata babu alamun wasa a fuskarshi “Baza ki ba!” Wani k’ululun takaici ne ya tokare mak’ogwaronta, dama ga haushin Arshaad da take ji tun d’azu! (Don Abba har yana shirin shiga motar da take amman ya janyeshi yace “yazo zai tuk’a shi”) Yanzu gashi ya had’ata da wannan boss d’in! Shi bai bari ta tafi da Abba ba kuma shi ma ya kasa shigowa su tafi tare ko dayake ta san saboda yana jin kunyar had’a ido da ita ne shiyasa! Kuma ya san koda ya shigo d’in ma fita zata yi ta bar mishi motar dan haka d’in ta gama shiryawa a ranta. Amman kuma at least ai da ya gwada Insted yana kallonta amman ya shige motar Abba yaja suka tafi da shi da su Shuraim.. .....Abunda Huda bata sani ba shi kuwa Arshaad fushi ya d’auka da ita bana wasa ba ata dalilin zargin da tayi mishi!. Bata iya rashin kunya ba amman bata san lokacin data tak’ark’are ta zabgawa Aslam wata uwar harara sannan ta murguda mishi baki ba! A tunanin ta su Abba yake kallo dan direction d’insu taga yana kalla amma abunda bata sani ba shine duk abunda take yi yana kallonta ta gefen idonshi. Tunda yake a rayuwarshi bai tab’a ganin harara da murgud’a bakin da yayi matuk’ar burgeshi da bashi dariya irin wannan ba, hakan ya sanya wani sassanyan murmushin da ya dad’e bai yi ba wanzuwa akan kyakkyawar fuskarshi, wanda har sai da Hudan taji sautin murmushin tayi saurin juyowa tana kallonshi amman ga mamakinta sai taga still su Abba yaketa kallo waenda suka tsaye a setin su.. Gani tayi kamar Madu yana magana da fad’a fad’a! Cikin takaici ta juyo tana kallon Aslam a ranta tana aiyyana “wato dan yaga ana fad’a shine yake murmushi, lallema wannan mutumin!.” A chan wajen su Madu kuwa abu bai yi dad’i ba! Dan tun farko da Madu ya tambayi Abba “dalilin da yasa ya d’auko Hudan lokaci guda haka?” Abba ya k’ule! A ganinsa dan mai yasa Madu zai yi mishi tambayar ‘dalilin d’aukar y’ar sa da yayi’ bayan shekaru da dama da yayi ba tare da ita ba!. Daga k’arshe dai, Abba tafiya yayi ya bar wajen dan bayason yayi musu rashin kunya. Daddy ne ya tabbatar musu da “sunje har unguwar da Hudan ta taso kuma sunji irin zaman da Huda tayi a gidan Baba, wajen mutane bakwai suka tambaya amman duk maganarsu d’aya ce! Ba abunda basu saniba a halin yanzu na irin zaman da Hudan tayi na azaba a hannun mutumin nan, har k’usar da Ja’afar ya buga mata a ciki suna da labari!” Yace musu “Tun jiya suke ta faman lallab’a Abba, da kyar suka samu ya hak’ura amma daa cewa yayi sai ya kulle Usman kuma yayi shariah da su!” Daga k’arshe yace musu “Dan haka, ko kotun da Madu yake ik’irarin zai je sai dai ya kulle kanshi da kanshi dan wannan dalili kad’ai ya isa a barma Abba custody d’in Huda!.” Yana gama fadin haka shima yayi musu sallama cikin girmamawa ya wuce ya koma mota Auwal ya ja suka yi gaba suka barsu a wajen, daman su su Abba sun dad’e da wucewa. Tunda suka shigo gidan Huda take bin had’add’en mansion d’in mai hawa biyu da kallo! Har Aslam ya gama parking bata sani ba, sai da yace “Na bud’e lock d’in, ki fita sai kin fi jin dad’in kallon!” Tukunna ta dawo hankalinta, gaba d’aya kuma sai kunya ta lullub’eta. A hankali tasa hannu ta bud’e ta fito, still mutane waenda suka kwashe kaya daga chan gidan sunata kai kawo, da alamun basu gama jeran ba, dan gashi har sets d’in kujeru wasu ba a shishshigar ba. K’ofar shiga gidan biyu ne manya manya! Kamar yadda Dad ya fad’a gidan wajen zaman mutum uku ne ma amma k’ofar farko ta gefen dama yafi girma dan wajen d’akuna sha biyar ne da faluka bakwai (shine mutum biyu zasu iya using dan hatta kitchen biyu ne) Sai d’ayar k’ofar gefen hagu ta d’an gefe kad’an na d’auke da 7 bedrooms da 4 parlourns. Mai girman Abba ya d’auka Daddy kuma ya nufi d’ayar k’ofar (side d’in mutum d’aya wanda bai kai na Abba ba). Suna shiga Hudan ta kusan daskarewa… Dukda gidan chan estate d’in shima yana da double height ceiling amman ko rabin wannan bai kai ba, ga wata mahaukaciyar chandelier da tunda take bata tab’a tunanin akwai irinta ba, wasu irin kwayayene da suke k’ok’arin makantar da ita tsabar haske a gidan! Waiting parlour yana a ta gefe a cikin wani d’an glass door kafin ka k’arasa shigowa makeken main parlourn k’asa wanda girman parlourn zai iya cin set d’in manya manyan kujeru 6 ko bakwai! Gefen dining daban, sai wata had’add’iyar matattakalar bene doguwa da zata kaika sama. K’aramin Kitchen d’in na ata gefen waiting parlour kana iya hango cikin shi dan bangon half ne bai kai har chan sama ba Main kitchen d’in kuma yana ta gefen dining Amman shi rufaffiyar k’ofa babba gareshi. Akwai wasu k’ofofin still a cikin parlourn wanda take da tabbacin d’akuna ne. Sama suka yi gaba d’ayan su, Parlour ne nan ma biyu d’aya a gefen dama d’aya a hagu masu masifar kyau, dukda basu kai na k’asan girma ba saboda double height ceiling d’in da aka yanka ya cinye kusan 1/3 d’in saman amman suma sun had’u sosai ba a magana! pop kam kamar ka kirashi ya amsa ta jikin bango ta ceiling hatta k’afar bene shima ba a barshi ya huta ba. Wata matattakalar suka sake bi suka hau chaan sama. Suna hawa suka nufi side d’in su Sudais, d’akunan su da parlourn su yayi matuk’ar burgeta. Sudais yanata murna Shuraim kuwa miskili bai ce komai ba Sudais shi a shirmen shi ya d’auka har da Huda, dan haka ya hau tsarawa ‘Za su d’auki d’aki daya ita kuma ta d’auki d’aya, sannan ya cewa Abba “ai da anyi mata nata gadon pink ba kalar blue ba”…’ Dariya dukkansu suka yiwa shirmen shi, kafin Abba yace “a’a ita nata d’akin daban ne bara in kaita in dawo ko?” Yana shirin fita yaji Shuraim yace “Abba yaushe Ummin zata dawo? Gramma tace za kaje ka d’auko ta” A lokaci d’aya duk suka d’auke wuta.. Gaba d’aya duk sai Hudan taji ba dad’i, yadda taga Abba ya had’e rai ne yasa ta kasa cewa komai “Bana son yawan tambaya!” shine abunda yace daga nan ya fice daga d’akin. Ganin haka yasa itama Hudan tayi musu sai anjima ta fice.. Tanata kallon parlourn nasu har ta fita, ta jaa musu k’ofa ta rufe. Sai a sannan Abba yace “tazo suje ya kaita d’akinta” yana mai kama hannunta. A gefen parlourn da suke a ciki suka shiga wani dogon corridor, k’ofar tana achan k’arshe suna isa ya sa hannu ya zura key ya murza k’ofar ta bud’u! Sanna ya jaa hannunta suka shige ciki. Set d’in kujeru biyu ne Peach da black, sai wani d’an k’aramin dining mai mugun kayau mai d’auke da kujeru biyu a gefe, da wata had’add’iyar tv babba mai curve. Wucewa sukayi suka shiga bedroom a nan ta sake shiga mamaki, gadon nata pink ne mai rumfa da net a jiki (princess tent) ga wasu had’add’un resting da coffee chairs guda bibbbiyu a kusa da tvn bedroom d’in, fad’ar had’uwar d’akin kawai sai wanda ya gani! Kawai. Still toilet d’inta ya nufa da ita don ya nuna mata… Ta closet suka bi kafin su isa cikin toilet d’in A nan kuwa ta saki baki, wajen wanka har uku shower da wani had’add’en jacuzzi, sai kuma wani makeken bathtub da mutum hud’u ma za su iya shiga su kwanta kamar gado da Showers a jikinshi ta ko ina. Ba abunda yafi bata mamaki irin wutan pop da take gani na sama, da taga yana ratsowa ta k’asan toilet d’in toilet d’in ta ko wanne angle. Bata gana dawowa dede ba , taji Abba yana cewa “Duk abunda bai yi miki ba ki fad’a sai a chanja! Munata sauri ba a samu anyi komai a nutse ba, so if you need anything just say it sai a chanja miki ko a siyo, an d’an zab’a miki kad’an jiya kayan suna mota mostly abaya ne da shoes da sauran y’an abubuwa, zan kawo miki tab zuwa anjima, sai kiyi shopping duk abunda kike buk’ata, in kuma a furnishing akwai abunda kikeso ki fad’a shima sai a kawo.” Ita dai mamakine ma ya hanata yin magana, wai A nan d’in amman still ana tambayanta ko akwai wani abun da takeso a kawo! Girgiza kai kawai tayi, kafin tace “Abba na gode komai yayi Allah ya k’ara Arzik’i. “ A hankali ya dafa kanta yana mai jin tsananin kaunar y’ar tashi tana ratsa ko Ina na jikinshi sannan ga tsananin tausayinta da ya hanashi sukuni! Ji yake kamar yaje ya kama Usman yayita dukanshi har sai yaga baya numfashi tukunna ya kyaleshi! Jiya yanda yaga rana haka yaga dare tsabar bak’in ciki… Jin yadda zuciyarshi ta fara tafarfasa ne yasa ya kawar da tunanin yace “Ki huta bara a kawo miki tab d’in da kayan, anyi order abinci shima na san kafin ki gama freshining up ya zama ready sai ki sauk’o muci ko?” D’aga mishi kai kawai tayi ta kasa d’ago kanta, saboda kwallar da ta tarar mata! Dan tana ganin inda aka kawota a matsayin mallakinta Mama ce kawai ta fad’o mata…… A tare suka fito daga toilet d’in suka shigo d’aki. Ganin Abba yana shirin fita yasa tunanin ta ya katse tayi saurin cewa “Abba” Juyowa yayi yana kallon ta. A hankali ta k’arasa wajen da yake sanna tace “Dan Allah Mama, mun yi waya da Sakina tace min Maman tana asibiti tun shekaran jiya”ta k’are maganan hawaye na zubowa daga idanunta. A hankali ya kama hannunta suka k’arasa bakin gadon suka zauna sannan yace “Zan kaiki wajenta anjima da daddare. Ki daina kuka” Da sauri tasa tafin hannunta tana share hawayen duka biyu. Kallonta yayi tukunna yaci gaba “Amman idan kinje, inaso ki yi promising d’ina zaki dawo, 30 minutes kawai za kiyi, zan jiraki a mota! Ku gaisa ki dubata daganan kice musu kina zuwa, in kin fito sai mu dawo. And karkice musu ni na kawoki”. Da sauri ta d’ago ta kalleshi kafin tace “To ai kamar na yaudaresu ne idan nayi hakan, kuma Mama ba zata ji dad’i ba.” Mik’ewa yayi kafin yace “Shine ni kuma zaki yaudareni ki tafi kik’i dawowa ko?” Kuka ta fashe da shi….saboda daman ta san ko da ace ta yarda zata dawo d’in su Mama ba za su barta ba!. A hankali yace “Hudan nima mahaifinkine kamar Maman ki, na san ba lalle ki fahimci komai ba, amman inaso ki san cewa ‘ban tab’a k’in ki ba’ Yadda Mahaifiyarki take sonki nima haka nake sonki, kina gani a gabanki na hukunta waenda sukayi nasarar raba ni dake!. Ba zan tab’a yarda in barki ki koma gidan da kika taso ba, dan duk halin da kike ciki a gidan na sani. Idan kin yarda kullum idan kina so to za kije ki dinga duba Mamaki, amman Hudan ba zan sake bari kiyi nesa dani ba.. I want to take care of you Make it up to you Make you forget all the sufferings that you go through. Amman hakan ba zai tab’a faruwa ba, sai da had’in kanki! Ba zan b’oye miki ba har ga Allah banji dad’in yanda kike yi mini ba kwata kwata Huda, it’s like kamar ma bakya farin ciki da ganina, komai ke kawai Mamanki! Ko maganan 10 minutes ban tab’a yi da ke ba! Yanzu ma kalli yadda kike yi min kukan in maidake wajen ta kamar irin na satoki d’innan?” Ya k’arashe maganar a hankali. Gaba d’aya Hudan sai taji jikinta yayi sanyi, tabbas bata kyauta ba! Ya kamata ta nuna mishi shima Mahaifinta ne tunda gashi ata dalilinta har gidansu ya bari da shi da d’an uwansa don kawai ya zauna a tare da ita…. Tunaninta ne ya katse jin yana cewa “I’m sorry Hudan dan unless you promise me ba zan tab’a barinki ki je ki ganta ba.” Shiruu, d’akin ya d’auka kafin yaji tace “Tam”. Kallonta yake yi, kamar zai ce mata wani abun kuma kawai sai ya juya ya fita. Kamar yadda ya fad’a haka aka kawo mata kayan da ya ambata.. Ita dai Hudan mamaki ta shiga yi dan bata ga kuma abun k’ari ba anan, komai akwai hatta inner wears sai dai kawai kamar ba za suyi mata ba, dan haka ta d’au tab d’in ta hau shopping… Sai da ta hau d’in kuwa tukunna tayita gannin abubuwa dan haka ta zazzab’a, bayan ta gama ta rufe ta ajjiye. Tana idar da sallar Magrib ta sauk’a k’asan kamar yadda Abban yace mata. Bata samu kowa ba, amman dai ga uban abinci nan shak’e a kan dining d’in wajen kala nawa.. Ga kuma wata maid cikin uniform sai kai komo take yi tsakanin kitchen da dining d’in tana jera su plates. Bata yi minti uku a zaune ba, suka shigo daga masallaci… Su Sudais ne suka fara shigowa, Sudais yana ta tsallen tsallenshi, Shuraim kuwa ya mazee, kallonsu take tana mamakin kamanninsu dan ita kam miskilancin Shuraim ne kawai yake sawa take iya gane su.. Tana murmushi tanata kallonsu tana jin tsananin k’aunarsu a ranta su Abba ma suka shigo dukkansu, har a Auwal wanda Daddy ya matsawa akan dole sai yazo sun gaisa da cousin d’inshi! Sai kumbure kumbure yake yi, ba wanda yabi ta kanshi haka nan suka shigo abunsu ana d’an tab’a hira kowa yana fara’a banda shi. Suna shigowa da Daddy suka fara had’a ido dan haka ya yafitota da hannu. A hankali cikin nutsuwarta ta nufi dogon dining d’in mai kujeru kusan ashirin inda taga sun nufa kamar an tsamota a ruwa a haka ta k’arasa wajen, Abba ne da kansa ya jaa mata kujera ta zauna, ita har kunya take ji yadda ake wani lallab’a ta ana janta a jiki musamman ma Abba yadda yi mata kamar ya goya ta yayita zagaye garin da ita. Cikin ladabi ta shiga gaidasu suka amsa, su Aslam kuma tayi musu jimla tace “ina wuninku” Aslam ne kawai ya amsa mata, a hankali ta d’ago ta kalle setin da Arshaad yake taga ya wani had’e rai ya d’auke kai ko inda take bashi da niyyar kalla ma! Nan kuwa ta k’ule, tana mamakin shi, a ranta tace “tabarmar kunya yake son nad’ewa da bori!” A take ta d’auke kanta itama bata sake kallonshi ba, tana jin haushi da wani tuk’uk’in kishin dake sake taso mata. Tana cikin wannan tunanin taji Daddy yace, “Sorry dota mun barki ke kad’ai ko? Za kini shiru kam, gashi Aaima na school, ya kamata a nema miki Abokiyar hira gaskiya!in ba haka ba bazaki ji dad’in zaman ba kwata kwata tunda su Sudais suma islamiyyarsu da boko a had’ene sai pass 5 suke dawowa.” Da sauri cikin tarar numfashinsa Auwal yace “ai daman da ace Ummi tana nan ba a kaita cell ba to da zata ji dad’in zama sosai, gashi Gwoggwo Asaben ma da naga kamar sun d’an saba itama ta saka an baro inda take! Dole ta sha zaman shiru kuwa ai!.” Dakatawa Abba yayi da zuba mata abincin da yake yi ya rik’e serving spoon d’in kawai still yana kallon plate d’in! Yana mamakin Auwal!! Wato rashin kunyar tashi yau ta hauro kanshi kenan, a gabanshi haka yake zuba mishi magana….. Yana shirin yin magana yaga Daddy ya taso ya nufi Auwal d’in a zuciye, da sauri Abba ya mik’e ya rik’e shi haka ma Aslam ya mik’e yana cewa “Daddy dan Allah kayi hak’uri ka kyaleshi.” Arshaad kuwa ko motsi bai yi ba dan shi kam tasa kad’ai ma ta isheshi, ba k’aramin k’ok’ari yake ba wajen share Hudan da yake yi, gashi tunda ya zauna yake d’an satar kallonta amman yaga kamar ma ko inda yake bata son kalla!. Cikin fushi Daddy yace “Dan uban ka iskanci naka yau a kanmu zai k’are? Auwal wallahi zan yi mugun sab’a maka fa!!” Cikin katseshi Abba yace “ya isa haka Daddy ka kyaleshi kawai! Dan Allah” Cikin rashin jin dad’i Aslam ya cewa Auwal d’in “you can leave, tunda ka ganta gashi har kun gaisa ma.” A fusace Auwal ya kalleshi, yana shirin yin magana Daddy ya daka mishi tsawa yace “Get out akace!! Stupid boy kawai!!!” Fuu!! haka ya tashi ya fita kamar zai tashi sama. Daddy da kyar ya koma wajen zaman shi ya zauna gaba d’aya guiwanshi a sace! Ya so ace a kusa da Auwal ya zauna yau da sai ya sauya mishi kamanni ya nuna mishi still da ragowar k’arfinsa shima har yanzun, dan yaga alamun Auwal d’in ya kawo k’arfin da yawa shiyasanya yakejin kanshi a sama kamar yafi kowa!. To dai dinner d’in haka ta wakana babu dad’i,,kowa da abunda yake damun ranshi. Sai wajen 9 Aslam da Arshaad suka yi musu sallama suka tafi, bayan an yanke yin wata sauk’ar gobe amman sai dare za a kammala, kowa zai yi izu biyu bayan sallar farilla sai su tafi da ruwan addu’ar a shafa mata . Suna fita Abba ma yace mata “ta d’auko hijabinta ya kaita ta duba Mama” Murna a wajen Hudan ba a magana dan da gudu ta haye benayen, bata yi minti uku a saman ba ta sauk’o sanye da hijab har k’asa wanda ta gani a cikin kayan da aka bata. Ya lura da yadda jikinta har karkarwa yake yi, shiyasa bai b’ata mata lokaci ba yace “suje”. Da sassarfa ta shige motar. Shi dai Abba kallonta kawai yake yi, tabbas Hudan da shi take kama komai da komai amma idan tana wani abun sai ya dinga ganinta kamar Maryam!!! Wani d’an murmushi ne ya sub’uce mishi, a hankali cikin sanyin jiki ya murza key ya tada motar ya nufi gate. Masu gadin gidanjensu na chan estate su suka d’auko suka taho dasu.. Suna Isa gate d’ayan ya ajjiye rediyonshi a kan dogon bencin da suke zaune su wajen biyar harda driver da mai wankinsu da gyaran fulawar, yaje ya bud’e musu makeken gate d’in, suka fice. Tunda suka fita Huda ta kasa sukuni, tsabar zumud’i, gani takeyi kamar Abba baya gudu, har d’an tasowa take yi ta d’an lek’a gaban titin ta gaban glass d’in motar.. Dariya ta bashi sosai dan haka yace “Gani kike kamar bana gudu ko?” Ya fad’a yana dariya sannan ya k’arawa motar wuta… Itama murmurshin tayi ta koma ta zauna da kyau a mazaunin ta. Tafiyar minti ashirin ce ta kaisu AKTH emergency, dan ma sun d’an tarar da go slow a hanya. Tana shirin fita taji yace “You promised Hudan, right?” A hankali ta d’aga mishi kai, sannan tace “Na gode sosai Abba” sannan ta fita. Da kyar security suka barta ta shiga bayan tayi ta nacin ce mishi Mamanta ne a kwance, Allah ya taimaketa, wanda yake gadi ne a wajen ranar da suka kawota ita da Aslam, kuma d’azu tabbas yaga Maman nata an fito da ita tana d’an zagaye, shiyasa ma ya barta ta shiga, don ya tunata tun ranar da suka zo ita tana kuka shi kuma yanata mamakin had’uwar Yarinyar, hakanan yaketa ganin hoton fuskarta a zuciyarshi amman ya san ko hauka yake ba zai ma yi tunanin tunkarar ta ba. Dube dube ta hau yi bayan ta shiga, da kyar da sid’in goshi ta hango su… Mama da Ummu a kan gadon a zaune suna magana da alamun mai matuk’ar mahimmanci ce sai Sakina ita kuma a gefe kan kujerar mai jinya da waya a hannunta. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 41 Basu ga tahowarta ba, kawai suka ga an afka kan Mama da gudu an rungumeta! Kukan da ta fashe dashi ne yasa suka gane itance, da sauri Sakina ta d’ago ta, ai kuwa tana ganinta tayi hugging d’inta tana dariya. Ummu itama murna kamar tayi me, Mama kuwa ba a magana. Ummu ce ta zare Hudan daga jikin Sakina sannan ta d’an muskuta ta ajjiyeta a tsakiyar su ita da Mama. A hankali Mama tasa hannu ta shafa fuskarta tana hawaye, da sauri itama Hudan ta goge mata hawayen tace “ki bar kuka Mama, i missed you so much, kwana biyun nan ji nayi kamar shekara wallahi” Ta fad’a tana sakin wani kukan, sannan ta kwanta jikin Mama. Sakina ce ta d’aka mata duka a cinya kafin tace “dalla Malama d’agata, kin wani zo sai kuka kike yiwa mutane salon ki karya mana zuciya muma mu biye ki! To Mama dai ance a daina sakata a damuwa dan haka sai kiyi k’ok’arin tashi ki ware garau ki bar wannan tab’arar.” Da sauri ta d’ago tana goge hawayen da suka k’i tsayawa, da kyar kuwa ta tsaidasu, ta d’an harari Sakina tana murmushi sannan juya tace “ina wuni Mama, ya jikin ki?” Da murmushi Maman tace “Alhamdulillah” Sannan Huda ta juya ta gaida Ummu, wadda itama ta amsa mata cikin kulawa sannan tace “ya mutanen gidan naku?” A hankali Huda tayi k’asa da kanta tace “Alhamdulillah” Sakina ce tace “a estate d’in kike? Family house d’in nasu kamar estate ne kowa da kowa ko?” Numfashi Hudan ta fesar tukun tace “Eh, nan aka kaini da farko, amman yanzu dani da Abba da Daddy da Ya Auwal mun tashi mun koma wani gida a baya. Saboda Granpa yace ‘Abba sai dai ya zab’a, ko ni ko su!’.” Cikin mutuwar jiki Sakina tace “Shine ya zab’e ki kuka tashi?” Da “eh” ta amsa, kafin tace “Har da d’an uwanshi ‘Daddy’ shima muka tashi, sun yi fad’a sosai jiya da Granpa d’in.” Tana shirin sake yin magana Mama tace “Kuka tashi as in how?? To ai yayi ta banza ne, dan ke kam kin zo kenan!! Ya aka yi kika fito? D’azu su Kaka suke gaya mana kalar rashin kunyar da yayi musu ai! Yanzu haka takardun shiga kotu ake had’awa!…” Cikin rashin jin dad’i Ummu tace “Mama dan Allah ki daina biyewa su Abba Modu kina k’ara tunzurasu! Kina ji fa bawan Allahn nan har gidansu ya bari, saboda ita!. Ko fa anje kotun nan na fad’a miki bamu da nasara saboda kamar yadda Abba Madun yace d’an uwanshi( Daddy) ya fad’a musu d’azu ‘ko a iya case d’in Baba aka tsaya dole a bashi Hudan!!’ Ballantana kuma idan aka duba yanayin standard of living! Shi (Abba) yana da aikin da zai iya kula da ita ke kuma.....” Shiru Ummu tayi ta kasa k’arasawa ganin yanda Maman ta kafeta da idanuwa. Cikin jan numfashi Maman tace “Ki k’arasa mana! Ni kuma bani da aikin yi, bani da komai ko?.” Sai kuma tace “Bari kiji idan su sun yi amfani da Baba to ni kuma zan yi musu amfani da Granpa! Ai har gara Baba shi bai tab’a korar Huda a gidanshiba, Granpa fa?” Cikin katseta Ummu tace “Amman ai yanzu ko me Granpa yake ji dashi bai isa yayi mata ba! Saboda Abban ma ya d’auketa a kusan shi gaba d’aya! Dan haka Kotu ba zata duba wannan bama a matsayin reliable.” Cikin d’an fad’a Mama tace “Wai Ummu kina nufin in barta kenan a wajenshi ko me kike son gaya min?” Cikin kwantar da murya Ummu tace “ba nufi na kenan ba, ki fahimceni Dan Allah… Maganar shiga kotun ne bana so saboda idan anje mune za muji kunya! Kuma In dai Abba yaga anbashi custody d’inta gaba d’aya to fa ba lalle ya dinga barinta tana zuwa mana ba! Mama, Hudan y’a mace ce! Makaranta ma zata shiga yanzu university wanda idan kika kwantar da hankalinki ma wata rana a wajenki za tayi Hutun ta! A hankali a hanakali zakiga zata iya dawowa wajenki gaba d’aya wata rana. Abunda nake so dake shine yanzu ki barshi (Abba) Zafin zuciya ne kawai yake damunshi.. Ni a nawa ganin banga amfanin a shiga kotu anata kace nace ba k’arshe kuma na san mu ne da kunya!. Kuma Hudan aure zata yi nan ba da dad’ewa ba, daga k’arshe fa dole ta bar gabanku gaba d’aya daga ke har shi. Dan Allah Mama ki fahimceni ki tayani fahimtar da su Kaka.” Cikin tsananin b’acin rai Maman tace “Eh!! Ai shiyasa ya turo mata da Arshaad, kuma abunda basu saniba na riga na gama yanke hukunci ‘In shi kad’ai ne Namiji a duniya to Hudan ba zata auresaba!’ Wai wanne irin rainin wayo ne ma wannan Abba yake yi wanda kika kasa fahimta??? Kina ganifa yadda muka taso muka sha wahalar rayuwa tare, bai tab’a ko da lek’en ta ba, sai yanzu data zama mutum tukunna shine zai nuna ya santa? Inace daa cewa yayi ‘kar ma in fad’a mata sunanshi?’.” Dafe kai Ummu tayi tana shirin yin magana Huda tace “Mama da gaske yake tun ranar anan ya fad’a miki ‘bai san da ni ba!’ Kuma dagaske yake.” Cikin jin haushi Mama tace “k’arya yakeyi!! Na fad’a na sake maimaitawa ‘k’arya yake yi!’ Kinji mai uba! To nuna min shine ya haifeki kinji Huda, hakan yayi kyau! Wato d’an kwana biyun da kika yi tare dasu har an juya miki tunani akaina ko? Bilkisu kinga irinta ko? Ina kuma ga in na barta ta zauna dasu gaba d’aya? Hudan fa ita kad’ai Allah ya bani, amman kalli mugu Abba abinda yayi a cikin kwana biyu kawai!!.” Ta k’arashe maganar tana fashewa da kuka. Da sauri Hudan ta hau lallashinta sannan ta fara basu labarin yadda akayi da Mom da su Ummi da Mammy, har cell d’in da suke ciki a yanzu…. Ummu wani sanyi da proud na Abba take ji, kuma ta sake amincewa zai kula da Huda iya iyawarshi kuma zai yi duk iyakar bakin k’ok’arin shi wajen bata kariya. Amman wani abun mamaki furr!! Mama tak’i amincewa da zancen tace “Makirci ne suka k’ulla da shi da y’an uwan sa, aka yi komai a gaban Huda dan ta yarda dashi asa ta juya mata baya!” Ba Ummu ba hatta Sakina da Huda da basu da shekaru sosai, sai da suka tsorata da lamarin Mama, ga gaskiya nan ana nuna mata amman ta kafe! Tak’i ji taki gani.. Ummu har ce mata tayi “zata je suyi maganar fahimta ita da Abba, ba sai anje kotu ba! Kawai Huda za ta dinga sati sati a hannunsu, har Allah ya kawo mata miji tayi aure Ma’aana taje Gandu tayi sati d’aya sai ta koma Nasarawa tayi sati daganan ta sake dawowa Gandu….haka dai.” Amman nan ma furr!! Mama nace akan ‘attakafur!! Ita sai dai a bata Huda gaba d’aya!’ K’arshema cewa tayi “idan Ummun ba zata tsaya mata ba ta daina yi mata kwana kwana kawai ta fito fili ta fad’a! Ta samu ta fara neman wani lawyer d’in, tun kafin lokaci ya k’ure mata.” Da jin hakan ne yasa Ummu taja bakinta tayi shiru bata sake cewa komai ba! Daganan shiru ya wanzu a wajen…. Hudan ce ta kawo k’arshen shirun ta hanyar cewa “Ya Jalila ma tana gidan” Da sauri duk suka zuba mata idanu… Cikin In Ina tace “Ciki ne ma da ita” A firgice Sakina ta rafka salati haka ma Ummu Mama kuwa daman ta riga ta Sani, amman abunda ya bata mamaki shine ‘me take yi a gidan su Abba’. Ummu ce tace “Me take yi kuma a gidan?” Shiruuu, Hudan tayi, bata san daliliba amman sai ta kasa ce musu cikin na Arshaad ne kawai tace “itama bata sani ba” Tana goge wani hawaye mai zafi daya zubo mata ba tare data bari sun gani ba, kafin ta k’ara da cewa “A gidansu Ya Auwal dai ta ganta, kuma yanzu da suka tashi, Ya Auwal d’in ya kaita wajen Gwaggo Asabe.” Ajiyar zuciya Ummu ta sauk’e kafin tace “Sadiya ta cuci Yarinyar nan har abada wallahi…” Cikin sanyin murya Huda tace “Ummu nace mata ta kwantar da hankalinta zan nema mata mafita, ya za ayi yanzu? Dan wallahi naji tausayinta..” Da sauri Mama tace “Wacce mafitar za ki nema mata?? Meye naki a cikin lamarin ciki, iye?” Ta k’arashe maganar cikin fad’a! Sannan taci gaba “Kin san Allah Huda babu ruwan ki a cikin lamarin nan, mafita Sadiya ta nema mata, wannan maganar tafi k’arfin ki kar inji kar in gani! Ballanta a tsunduma ki a cikin lamarin a yi miki bak’in fenti ke daman mai bak’in jini a idonsu…” Hawayen Hudan ne ya k’aru, ta sa hannu ta shiga gogewa.. Ita kad’ai ta san kalar tuk’uk’in da zuciyarta take yi mata, kawai tunowa da lamarin cikin da tayi And Tana mamakin masifar da Maman nata ta koya.” Ummu ce tace mata “kin dai ji ko Huda? Ki bita da addua kawai, Sadiya ta fiki sanin kalar taimakon da zata yi mata, ba ruwan ki! Dan yanzu za a goga miki fenti taki sai tafi ta kowa tsami!” Cikin katseta Mama tace “Ai gashi irin tarbiyyar Abban da kuke magana akai!! Yanzu kamar Hudan har tana shiga lamarin ciki tana alk’awarin zata nemawa mutum mafita sai kace wata nurse??!” Ajiyar zuciya Ummu ta sauk’e sannan tace “Ki kwantar da hankalinki, ai taji abunda muka ce mata ko Huda? Besides ai basa tare ma yanzu, naji tace tana wajen Gwaggo Asabe ko? Wacece Gwaggo Asaben?” Nan Hudan tace “k’anwar Mommy ce” Sannan ta basu labarin halin da Mommyn take ciki. Kaf a labaran da Huda tazo da su na Mommy ne kawai ya girgiza Mama. Ta ji ba dad’i sosai, gashi ta san matar sun d’an saba dan haka tayi ta jimami…ga shima Aslam wanda dukda kalar rashin kirkin da yayi mata ranar amman har yanzu tana jinsa har cikin ranta….. Kamar ance ta kalli wayar Sakina da message ya shigo yanzu ta d’anyi haske! Wayar na nan akan cinyarta don haka ta samu damar ganin time… Mamakine ya kamata dan har ta shafe wajen awa d’aya da minti ashirin a wajen. Cikin k’arfin hali ta d’an kwanta a jikin Maman, bayan kamar minti uku ta mik’e ta cewa Sakina “tazk ta rakata taje tayi fitsari.” Kamar kuwa Mama ta sani dan tashi d’aya ta fara k’ok’arin mik’ewa tace “bari ta rakata da kanta!” Da kyar Ummu ta lallab’ata, ta hak’ura ta koma ta zauna. Daganan Sakina ta gyara mayafinta suka rik’e hannu suka yi gaba…. Har suka fita daga wajen tana d’an juyowa tana satar kallon inda su Maman suke…..tun kafin suje waje ta fashe da kuka mara sauti suna fita harabar asibitin ta sakeshi mai sauti ya fito, da sauri Sakina wadda tun d’azu taketa ce mata “bafa nan bane hanyar toilet d’in” amman tayi mata shiru sai janta kawai take yi tace “Lafiya Huda mai ya faru kuma?” Waige waige ta hau yi, chaan ta hango motar Abba da suka yi parking d’azu! Daman bata yi tunanin zai tafi ba. Bata b’oyewa Sakina ba, nan ta fad’a mata komai akan yadda suka shirya da Abban nata. D’an k’ura mata ido Sakina tayi….Chaan! Tace “Yanzu sai yaushe kuma? Anyways kinga dai 30 minutes ya baki yanzu kuwa kin kusan awa d’aya ma. Ki kunna wayarki kawai za muyi magana. Mai yasa kika kashe ko kwacewa akayi?” A hankali tace “Charger ne babu. Amman d’azu na siya a online an kawo har na ma jona Ina so ya cika ne kafin In kunna.” “Ok za muyi waya muje in rakaki” Hannun ta Hudan ta ruk’o kafin tace “Sakina kina ganin Mama ba zata ji haushina ba? Me za kice mata idan kin koma ciki?” Ajiyar zuciya Sakina ta sauk’e sannan tace “Haushin ki kam za taji, ba d’aya bama kuwa! Kuma yau Allah yasa ta bar Ummu ta rintsa dan ni ba anan zan kwana ba Baba nake jira yazo ya d’auke ni sai gobe tukun zan dawo. Amman na san yau rikici zata yi tayi, Mama ta zama mai fad’a sosai!. Maganar da zan fad’a mata kuwa, gaskiya ce zan fad’a kawai ba wani abun ba.” Rau rau Huda tayi da idanu. A hankali Sakina tayi murmushi tace “Kije ku tafi, tabbas Mama za taji ba dad’i amman kije kawai kin ji?” A hankali ta share hawayenta ta matso ta rungume Sakina, dai dai nan Baban su Sakina shima ya k’araso wajen. Abba ma haka wanda tun fitowarta ya gansu ganin da yayi kamar bata ganshiba ne yasa ya fito ya k’araso inda suke tsaye. Kusan a tare suka k’araso wajen, Baban su Sakina yana ganinshi ya gane shi ne baban Hudan dan haka yayi saurin mik’a masa hannu (wani aiki ya tab’a had’ashi da Abban kuma ya samu alkhairi sosai! Har gidansa ma sukaje suka yi mishi godiya. Yanata yaba alkhairin mutumin, shiyasa da Arshaad ya rok’esa akan ‘ya rufa mishi asiri kar ya fad’awa kowa daga family d’in daya fito yet saboda gudun matsala’ Shi kuma ya yarda yayi shiru bai fad’a d’in ba Don yaga sun san mutunci kuma shi kanshi yana so Hudan ta had’u da Mahaifinta a samu a dedeta komai! Amma Arshaad yace baya nan yanzu ya tafi wani aiki kuma akwai issue har yanzu a k’asa, but a hankali a hankali za suyi settling in shaa Allah, komai ya dawo normal . Shi kanshi a lokacin ya yarda da hakan saboda ya san wani part na case d’in su Madu da family d’in Abban… To kuma suna k’ok’arin ganin komai ya koma normal d’in tukun a samu a daidai sai shi kuma Aslam yazo yayi musu mai gaba d’aya!).... Shima Abban kallon sani yake yi masa, sai da Baban su Sakinan ya tuna mishi ‘ya tab’a basu wani contract kwanakin baya’ Tukunna Abba ya tuna shi, Hudan kuma ta gabatar masa dashi a matsayin Baban su Sakina mijin anty d’inta. Sake gaisawa suka yi sakina itama ta gaidashi cikin girmamawa… kallon Abban take yi tana sake maimaitawa! Tanaji Ummu tana cewa ‘Baba kishi yake da Abba shiyasa yake yin wasu abubuwan’ tabbas kam dole Baba yayi kishi da wannan mutumin! Dukda cewa shima Baban ba mummuna bane kuma fari ne shima amman ko makaho In ya shafa yaji ya san babu had’i kwata kwata tsakanin Abba da Baba, Abba ya tsere mishi a komai da komai.. Gashi wani abun mamaki ba zaka tab’a cewa ma ya haifi Hudan ba dan kamar wani d’an 33 haka yake, jikinsa san bai nuna tsufa ba kamar dai Mama, Ita kam tunda take a rayuwarta bata tab’a ganin perfect match irin na Abba da Mama ba…… Da kulawa ya amsa gaisuwar tata yana tambayarta “ya school” a hankali tace “muna jiran results ne har yanzu”. Sun d’an tab’a hira da Baban Sakina daga nan sukayi exchanging numbers suka yiwa juna sallama. Abba ya lura da yadda Huda ta shak’u sosai da Sakina dan har suka isa mota tana waigawa tana waving d’inta kamar wata Yarinya itama Sakinan haka dan ita kam har sai da taga fitarsu tukunna suka shige ciki don su d’auko kayanta. Tun kafin Mama ta gama gaisawa da Babansu Sakinan ta san yanda tayi ta zulle ta gudu, daman itama k’arfin haline kawai zata yi wajen yiwa Maman bayani kuma yanzu ga mafita Allah ya kawo mata. Tunda suka kama hanya Hudan take tunanin abunda tayi sam bata kyauta ba! But ya kamata shima Mahaifinta ta d’an kwantar mishi da hankali tunda ga halin da yake ciki da family d’inshi…. Ya lura da ita sosai, don k’arshema har da y’ar kwalla yaga tana gogewa. Shiru yayi mata kawai…..har sun kama hanyar gida sai kuma ya juya yayi hanyar dominos. Suna zuwa yayi parking ya shiga bai dad’e ba ya fito da Ledoji nik’i nik’i dangin su ice cream da milk shake da pizza….. A baya ya saka ya zagayo ya zauna yace “gashi ita da su Shuraim, in kuma sun yi bacci by the time da suka gidan sai ta sa musu nasu a fridge.” Godiya tayi masa, daga nan suka kama hanya, yana ta d’an janta da hira kad’an kad’an, yace if “she’s bored gobe ta shirya Arshaad ya kaisu munjibir park” Kamat zata ce masa a’a sai kuma tace “to” kawai. A haka suka karasa gida. Shi ya taya ta d’aukar kayan sai da suka isa chan sama tukunna ya ajjiye a parlour yayi hanyar d’akin shi bayan ya rarrage fitulu yana ce mata “ta duba su ta shafa musu addua idan sun yi baccin, itama tayi kafin ta kwanta.” Kamar yanda tayi tunani, ko da taje su Shuraim d’in har sun yi bacci dan haka tasa a fridge d’in sama dan ita tsoro take ji ba zata iya sauk’a k’asa ba, a Iyaka saman ma itakam duk a tsorace take!. Tana jera kayan tana mamakin uban yawansu…. Ice cream d’aya ta Iya d’auka, dan gaba d’aya bata da laka a jikinta tunanin Mama take tayi..duk jikinta a sanyaye yake, ta san tayi laifi babba a Mama, bata san ma ta ya zata sake facing d’inta ba! Cokali biyu kawai ta iya yiwa ice cream d’in duk dad’in shi amman sai ta kasa sha, da kyar ma ta iya had’iye biyun a mak’oshinta don haka ta rufe ta saka a d’an mitsitsin fridge d’in gefen gadonta ta mik’e tayi wanka. Tana fitowa ta rarumo waya ta danna kiran Sakina Ita kuwa Sakina tunda suka fita tana zama a mota ta kashe wayarta ma gaba d’aya dan wallahi ta gaji dayawa tana buk’atar isheshen bacci, in yaso duk fad’an da za ayi mata ayishi gobe!. Shiyasa Hudan tayita kiranta amma taji a kashe…. daga k’arshe ta hak’ura tayi cilli da wayar, ta kwanta, gaba d’aya ranta ba dad’i, bata san ya Mama zata kwana ba yau! Kuka ta fara yi, ta dad’e tanayi kuma daga baya ta share hawayenta…. Wayarta taji tana k’ara dan haka ta lallab’a ta d’auka, gabanta ne yayi wani irin mugun fad’uwa ganin sunan Ummu, sai da wayar ta kusan tsinkewa tukunna ta iya d’auka tana karawa a kunnenta Ummu tace “kina gida ne?” “Eh” ta bata amsa. “Waye ya mayar da ke?” “Abba” ta sake bata amsa. “Daman tare kuka zo?” “Eh!” “Tam! Sai da safe.” Hudan tana shirin yin magana taji kit!! A yanke kiran. A daren ta kira layin Ummu yafi sau ashirin amman bata d’aga ba! K’arshema dena shiga tayi. Gaba d’aya hankalinta sai ya sake tashi, sai wajajen 2 tukunna ta samu tayi d’an baccin ta rabi da rabi, kiran sallar farko ta farka. Tashi tayi tayi Nafila ta jira aka kira tayi sallar Asubah… Bata kwantaba sai da tayi azkar d’inta ta fara karatu. Sai bayan gari ya d’anyi haske tukunnna ta d’an iya yin bacci shima nisanshi iya awa d’aya! Wayar Sakina ta sake gwadawa tana tashi but still a kashe. Tana zaune taji kamar ana knocking chan waje k’ofar falo, mik’ewa tayi ta fita taje ta bud’e… Tana bud’ewa taga ashe ragowar kayantane na jiya aka kawo/ Cikin girmamawa maid d’in ta gaidata sanann ta hau shigo mata da kayan leda leda. Godiya Huda tayi mata bayan ta gama, ta juya ta fita. Ita kuma ta tura k’ofar taja kayan zuwa bedroom. Tana gama ajjiyewa a closet ta fito kenan ta zauna akan gado Abba ya shigo cikin jallabiya mai k’aramin hannu rik’e da hannun Sudais wanda shima yake sanye cikin kayan bacci. Da sauri Sudais d’in yazo ya rungumeta sannan yace “Abba just told us that you are our big sister, i’m so glad that we’ve a big sister” Ya k’arashe maganar yana sake hugging d’inta. Murmushi tayi itama tayi hugging nashi back kafin tace “I’m so glad to have cute brothers too.” Da sauri ya d’ago yace “Monday idan anje school zan gayawa Ashraf da Sultan da Kareem nima nayi big sister, dariya suke yi min kullum suna tsokanata! Yanzu kema kice Abba ya kaiki school d’inmu a sakaki a ss2 dan Allah so that i can come and see you during break time just like they do, and also....” Abba ne ya dafa kanshi yana dariya, kafin yace “Sudais wai har yanzu baka san ka girma ba? Ya kamata fa ace ka daina wannan shirmen And Big sis ta gama secondary ai,,kar kayi mata adduar komawa baya mana. School d’in su Aaima zata tafi, ko?” Yayi maganar yana kallonta yana murmushi. D’an zamowa tayi ta gaidashi, a hankali ya amsa yana mai dafa kanta yana kallon idonta da tashi d’aya ya fahimci taci kuka. A kan Kujerar gefen gadon ya zauna yana kallonta kafin yace “Me ya saki kuka? Mama kike son sake gani?”. A hankali ta sunkuyar da kanta k’asa kafin tace “ina jin ba dad’i ne akan abunda nayi mata jiya, Ummu ta kirani nace mata mun dawo, inaga haushi suka ji dan I’ve been calling them since last night amman ba wanda ya amsa.” Ta k’arashe maganar tana sakin kuka. Ajiyar zuciya Abba ya sauk’e kafin yace “A kawo miki Sakina? Ku zauna tare?” Da sauri ta d’ago tana kallonshi, sai kuma ta hau d’aga kai tana share hawayenta. Murmushi yayi kafin yace “Ok, but no more crying, in ba haka ba in fasa.” Da sauri ta cigaba da goge hawayenta, da kyar kuwa ta samu suka tsaya…. Abba bai kira Baban Sakina ba sai da ya sakata tayi murmushi kala uku! Sudais yana tayashi da yi mata cakulkuli. Bayan sun gaisa ya tambayeshi akan “Dan Allah ya bar Sakina ta zo ta d’anyi kwana biyu da su tunda basu fara school ba yanzun, maybe Hudan ta d’an sake in ta ganta.” Nauyi da kunyar Abban ne suka hanashi yi masa musu dan haka yace “yanzu an sallami Mama ne suna kwashe kaya, amma zuwa anjima in shaa Allah zai kawota. Ya tura mishi adress kawai.” Godiya yayi sannan ya kashe wayar, ya tura mishi da adress d’in. Yaji dad’in yadda ta saki ranta sosai. Cikin murna ta tanbayeshi “me zata dafa?” Murmushi kawai yayi yace mata “koma me ne in ta dafa yayi” Kafin ya tambayeta adress d’in su Sakina, tayi mishi kwatance, daga nan suka fita shi da Sudais........ Wanka tayi ta sa wani silk gown, A shape, colour d’in emerald green, an d’anyi kwalliya ta k’asan k’irjin da igiya mai stones ya zagaye, daga gefe ta gaban an tufkeshi yayi kmr ribbon babba. Bai matsetaba kuma bai yi mata ruwa ba dai dai jikinta, tayi masifar yin kyau, ta gyara gashinta ta tufke a k’eyarta sannan ta d’auko d’ankwali kayan ta nad’a wanda kasancewarshi k’arami, yasa ta d’anyi normal d’aurin kai dashi ta kuma bi da edges d’in dankwalin ta kan gashin data tufke ta sake zagayewa da shi d’ankwalin. Sannan ta d’auki turare ta fesa duk a cikin kayan da tayi order jiya. Tayi kyau sosai kuwa abunta. Wayarta ta d’auko ta kira Ummu still bata d’auka ba, Sakina kuma a kashe. Jiki a mace haka ta sauk’a ta shiga kitchen. Ga mamakinta har an gama breakfast, maid d’in jiya da wani shima da uniform a jikinsa irin nata (maid d’in), Sun gama hada komai, kuloli wajen uku, kitchen d’in sai tashin k’amshi yake yi. Sai da ta k’araso tsakiyar kitchen d’in tukunna suka lura da ita, kamar zasu kifa haka suka hau gaidata cikin girmamawa.. Itakam kunya da mamaki ma da kyar suka barta ta amsa. Ta riga tayi niyyar yiwa Abba girki shiyasa ta tambayesu me suka dafa? To dai d’ayan abincin itakam ba ma ta sanshi ba kuma bata tab’a ganinshi ba ma, sai shawarma a d’ayan kulan, farfesun kayan ciki kuma a d’ayan, sai ruwan zafi a flask ga mai buk’ata. A hankali cikin nutsuwarta ta k’arasa ta bud’e inda suka nuna mata a matsayin store d’in ta shiga.. Babu abinda babu a ciki, dan haka ta d’auko, dankali kad’an da kwai da Mayonnais da su albasa sai su green beans da macaroni. Sun so su tayata aikin amman tak’i, da kanta ta had’a mishi potatoe salad mai d’ankaran dad’i da kyau! A dining d’in taje ta ajjiye bayan ta juye a cooler. Tana shirin barin wajen Auwal ya shigo… Suna had’a ido da shi ya b’ata rai! Fuskarnan tamau haka ya nufo dinning d’in. ita dai Huda ta lura kwata kwata wannan baya k’aunarta ya tsaneta! A hankali ta gaidashi amman kamar wanda take magana da dutse ko kallon inda take bai yi ba! Kujera kawai yaja ya zauna ya hau had’a tea. D’aga sagaggun k’afafunta tayi ta fara takawa don barin wajen dai dai Abba yana sauk’owa, bata ma lura dashi ba sai da ta kusan tsakiyan falon suka yi kicib’is! Murmushi yayi ya dafa kanta sannan yace “har an gama girkin?” Itama murmushin ta mayar mishi tace “Eh” “Ok, muje.” Yace sannan ya kama hannunta suka juya. Suna zuwa Auwal ya mik’e ya gaidashi, cikin kulawa Abban ya amsa mishi sannan ya cewa Huda “kun gaisa da yayan naki?” A hankali ta d’aga kai alamar ‘eh’ Harararta yayi sannan yace “Daddy ne yace kuzo muyi breakfast.” “Ok” Abban yace sannan ya cewa Huda taje taga ko su Shuraim sun gama shiryawa. Har ta juya taji yace “Ina abincin da kika dafa?” Da sauri taje ta d’auko kular ta mik’a mishi, karb’a yayi sannan ya mik’awa Auwal yace masa “fara yin gaba da wannan, gamu nan zuwa.” A k’afar bene ta had’u da Yaran dan haka suka juya tare. Suna k’arasowa parlourn suma suka wuce side d’in Daddy. Ita dai tana mamakin tou wanchan uban abincin, da aka dafa musu waye zai ci!? Kasa hak’ura tayi ta cewa Abban “Ko ta koma ta d’auko kulolin chan, masu aikin fa sun yi girki”. Murmushi yayi yace mata “Karta damu anjima da yamma idan anyi na sadaka za a had’a a kai tare da wanchan d’in.” BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 42 Yadda side d’insu yake, haka na Daddy shima yake, komai da komai iri d’aya, kawai de akwai k’ofofi da corridors d’in da suke a nasu wanda babu a na Daddyn. A parlourn suka tarar da Daddy d’in da alamun su yake jira. Abba ne ya fara gaidashi tukun su Huda. Yana jin Yarinyar a jikinshi matuk’a dan haka bayan ya amsa ya hau tambayarta “ya take? Tana jin dad’in zaman? Akwai abunda take buk’ata?” A hankali tace “komai Alhamdulillah. “Ma shaa Allah” yace sannan suka k’arasa….. Nan d’in ma abinci wajen kala hud’u akayi. Cikin nutsuwa da nishad’i sukayi serving kansu suka fara having breakfast d’in. Basu dad’e da fara cin abincin ba, Hudan taji yanayin bugun zuciyarta ya chanza! A hankali ta runtse idanunta tana k’ok’arin saita kanta, da kyar ta samu ta bud’e idanunta tana mai jin wata nutsuwa tana sauk’ar mata sakamokon k’amshin turaren da ya sakarmata da kasala lokaci guda! Basuma lura da shigowar tasa ba, sai da ya matsosu sosai da k’amshin turarenshi ya yi musu sallama, tukunna suka lura da shi. A hankali yace “AsSalama alaikom” “Wa’alaikassalam, d’an albarka!” Daddy yace yana mai ja mishi kujerar kusa dashi. Zama yayi, a lokaci guda kuma yana mai amsa gaisuwar su Shuraim sannan yace Daddy Ina kwana” Da kulawa Daddy ya amsa haka shima Abba bayan ya gaidashi. Sannan ya juya ya mik’awa Auwal hannu, sukayi musabaha. A hankali Hudan ta gaidashi ba tare da ta yarda sun had’a ido ba! Juyowa yayi ya kalli inda take, sai kuma da sauri ya kauda kanshi, a hankali yace “lafiya” Hira suka d’an fara sama sama, kusan rabin hirar akan maganan company d’in da Aslam da Abba za su bud’e ne. Ita dai Hudan kasa ci gaba da cin abincinta tayi, tun lokacin daya shigo! Bata san daliliba amma in dai yana waje to sai ta dinga jin kanta uncomfortable, ga yadda k’irjinta yake yi mata shima, wanda ta rasa dalili. Abba ne ya cewa Aslam “Ina Arshaad ne? Ban ganku tare ba.” “Ya tafi d’aurin auren wani Abokin su, and wai za su kai amarya Kaduna, around 2 haka.” Aslam d’in ya bashi amsa. “Ok” Abba yace kafin ya kalli Huda yace “Ko a bari sai gobe kuje park d’in ko? Tunda yau Arshaad d’in yana busy.” Kafin ya rufe bakin shi Auwal yace “Bani da aiki sosai yau, zan kaisu.” Hudan ta d’anji sauk’i saboda daman ba zata so su fita itada Arshaad ba, kuma ba zata so ace Aslam ya kaita ba! Amman kuma ba ita kad’ai ba hatta su Daddy sai da suka fahimci akwai wani abun da Auwal ya shirya duba da yadda baya son ta yanzu kuma lokaci guda yace ‘Zai kai ta’ Daddy wanda ya san halin kayanshine yace “a’a! Ka barshi goben Arshaad d’in ya kaisu” “Daddy i volunteered fa.” Auwal d’in ya fad’a yana kallonshi. Cikin d’an fad’a Daddyn yace “And i insist akan ka barshi Arshaad ya kaisu.” Murmushi Abba yayi kafin yace “Daddy tunda ya nuna zai kaisun a barshi mana ko? Please.” Baya son jan magana dan haka yace “ok” kawai ….dukda ya san Auwal bai Isa yayi mata komai ba tunda tare za su tafi ita da su Shuraim amma baya so suje Auwal d’in yayi mata wani kalar rashin mutuncin da zai ja yaji kunya ne. Murmushi Auwal d’in yayi ya kalli Hudan kafin yace “Ki shirya around 2:30pm haka” Yana gama fad’an haka ya mik’e yayi hanyar sama, da alama ma ko “to” d’in data ce mishi bai ji ba. Shuraim ne ya mik’e, yace “Abba zanje in yi assignment d’ina kafin mu fita” Da sauri itama ta mik’e daman hanya take nema saboda sam bata k’aunar zamanta waje d’aya da Aslam kwata kwata, gashi ta lura sai faman kallonta yake tayi, sannan anyi rashin sa a ya zauna a kujerar da take opposite d’in tata ne….a hankali cikin nutsuwarta tace “Abba nima bara inje” sannan ta juya ta yiwa Daddy sai anjima. Sudais shima binsu yayi, suka fice a tare…. Da murmushi Abban ya bisu da kallo yana jin wani tsananin farin ciki a ranshi.. Gyaran muryar da Daddy yayi ne ya juyo da hankalin su inda yake. Ganin yanayin shi yasa duk suka maida hankulansu a kanshi. Cikin rauni yace “Abba jiya da daddare naje wajen su Mammy, and thier situation is bad! Very bad!! Na san abunda suka yi was wrong but anyi saurin yanke hukunci cikin fushi gaskiya.. Thou they deserve it, but matsalan shine they can’t survive in there most especially ma Ummi, dan a yanzu inda zaka je ka kalla jikinta to ba zaka so ka k’ara kalloba sakamokon k’uraje da borin jinin da suka fito mata ta koina! Ka san dama ita tanada allergy tun tana y’ar k’arama tanada kyankyami sosai! Ko fa 1 week ba ai ba amman in kaje ba lalle ka iya gane ta ba! I don’t think zata iya kai 2 months a wajen nan gaskiya, jiya da naje ruwa ake k’ara mata, amai da gudawa take yi, gashi ko abinci mai kyau in mutum ya kai musu Granpa sai ya sab’a maka. Kar garin punishing d’insu kuma muje mu shiga hakkinsu, after all they are our wives..” Ajiyar zuciya Abba ya sauk’e kafin yace “Daddy inda case d’innan a hannu na yake, tou da zan iya sassauta musu, not because of wai na yafe musu ko na huce, NO! Only because of maganan da kayi min yanzun… Amman Granpa ke rik’e da case d’in, already ni da kai masu laifine a idanunsa a yanzu, Ina tunanin In muka yi interfering, za a iya samun matsala…” Cikin katseshi Daddy yace “Ba interfering za muyi ba! Gramma za muyi wa magana, na san ya san yanda za tayi ta d’an shawo kanshi, at least a d’an sassauta musu, ya bari a dinga kai mu su abinci daga nan, sannan a ajjiye su a tsaftataccen waje, dan gaskiya jikin Ummi ya bani tsoro jiya.” Numfashi Abba ya fesar, sannan yace “ba komai zan kira Gramma d’in a waya zuwa anjima in shaa Allah.” A hankali Aslam yayi k’asa da kanshi sannan yace. “Zan yiwa Granpa magana, in sha Allah zai sauk’o, zan lallab’ashi.” Shiruu, suka d’an yi, chan kuma Daddy yace “ok, hakan zai fi.” Abba yana shirin mik’ewa, Daddy yace “akwai wata maganar still fa. Jiya bayan mun rabu Arshaad ya kirani, wai yana son yin magana dani, i think kunyar ka yake ji shiyasa ya bari sai da na koma.” Da mamaki Abba yace “Arshaad? Kunya ta kuma? Ikon Allah!” Murmushi Daddy yayi, sannan yace “Bayan yace ‘yana son magana dani’ shine nace masa ‘ya zo tou muyi face to face’ Mun dad’e tare dan tare ma muka je station d’in da shi.” D’an kallonshi Abban yayi sosai ya bashi dukkanin hankalinsa alamun yana buk’atar k’arin bayani… Murmushi Daddy ya sake yi, kana ganinshi ka san yana cikin farin ciki da jin dad’in al’amarin, fuskarsa cike da annashuwa yace “Good news ne, Ashe wai ya san Huda, for the past 3 years, and suna dating ne, ita ce Yarinyar da muke da shirin zuwa nema masa aurenta! So yanzu ya same ni ne akan ko za a fara maganar tasu tund........” Kwarewar da Aslam yayi ne ya hanashi k’arasawa. Da sauri Abba ya mik’a mishi ruwa dan haka ya karb’a ya d’an kurb’a yana tarin kad’an kad’an still, su kuma sunata jera mishi “sannu!” D’aga kanshi kawai ya iya yi Idanunsa sun yi jaaaa! Alamun ba kad’an ba yaji azabar kwarewar… Sai da suka ga ya d’an nutsu tukunna Daddy ya kalli Abba yace “ya ake ciki?” Shiruu, Abba yayi, kamar mai nazari, kafin yace “all those years kuma bai gane ta ba?” “Abun mamaki ko? Suna tare amman basu gane junan su ba!” Daddyn ya fad’a, kafin ya ci gaba da cewa “Ya yiwa Dad ma maganar! Wallahi baka ji yadda lamarinnan yayi mana dad’i ba! Ni kam na riga ma na bashi ita.” Ya k’arashe maganar yana murmushi mai kama da dariya wanda ke baiyyana tsantsar farin cikin da yake ciki. A hankali Abba yayi k’arfin hali ya d’an k’ak’alo guntun murmushi kafin yace “Tou Allah ya zab’a mana mafi alkhairi” Ameen Daddy yace sannan ya juyo ya kalli Aslam wanda ya runtse idanunsa ya kwantar da kansa da bayansa a jikin kujerar! Cikin zolaya Daddyn yace “wannan azumin da kaina zan buga maka wak’ar gauro!! Arshaad yayi maka wayo..” D’an murmushi kawai yayi ba tare da ya bud’e idanunsa ba. Abba baya son maganan shiyasa ya sako wata maganar daban dan haka suka hau tattaunawa…… Shi kam Aslam mik’ewa yayi yayi musu sallama ya kama gabanshi. A b’angaren Hudan kuwa bayan sun gama dabdalar assignment d’insu dasu Sudais ta tafi d’akinta, tana kwanciya bacci mai nauyi yayi gaba da ita. Sai wajen 1:30 ta samu ta farka. Alwalla tayi tayi sallah, sanin da tayi ba a gida za tayi sallar laasar ba ya sa ta karanta izu hud’u, tayi doguwar addua ta tofa, itama ta shafa. Tana idarwa Shuraim yazo ya kirata yace “taje inji Abba, yana parlour” Jikinta ba kwari ta fito, dan still ta sake gwada number Ummu tana shiga amman tak’i d’auka! Gashi har yanzu Sakina itama bata kunna wayarta ba, ba kuma ta k’araso ba, Allah yasa ba hanata aka yi ba!. Tana wannan tunanin tana tafiya domin amsa kiran Abban nata. A parlourn saman inda sides d’insu yake ta sameshi. Tun daga yanayin ta ya fahimci tana cikin damuwa.. Ajiyar zuciya ya sauk’e bayan ya amsa gaisuwar ta kafin yace “Zauna, i want to talk to you” Zama tayi, a one seater d’in parlour da yayi mata nuni da. Ba tare da b’ata lokaci ba , ya fara magana “D’azu Daddy yake cewa wai Arshaad ya sameshi akan maganar ku!” Da sauri ta d’ago ta kalleshi, a zuciyarta ta hau mamakin Arshaad da kalar nerve d’inshi! Despite abunda yayi da kuma fushin da suke yi da juna amman shine yaje ya samesu da maganan! Me kenan yake so? Auren yakeso ayi ko tanaso ko bataso kenan ko me!?…. A hankali ta sunkuyar da kanta k’asa, jin Abban ya sake cewa “Yace wai you two knew each other for a while ko?” Sai da ta taushi zuciyarta, tukunna ta iya d’agawa Abba kai alamar ‘eh’ sannan ta bashi labarin yadda Arshaad d’in ya kaisu makaranta… Hatta wayoyin daya siya musu sai da ta fad’a mishi bata b’oye komai ba a labari da tarin alkahairan da yayi musu tun daga had’uwar su har kawo yanzu. Dan ita bata kasance mai manta alkhairi ba kwata kwata. Tanaso ta fad’a mishi issue d’inshi da Jalila amman sai ta kasa. Ajiyar zuciya Abba ya sauk’e bayan ya gama jin bayaninta ya na k’ok’arin fassara lamarin Arshaad amman ya kasa! Tabbas akwai abinda Arshaad ya sani tun farko kuma yayi shiru wanda shi kad’ai ya san dalilin yin shirun da yayi! Dan a cikin labarin da Huda ta bashi yanzun yaji inda Arshaad ya had’u da Mama ba so d’aya ba, and in dai Arshaad ne ya tattare mishi d’akinsa kwanakin baya da za suyi parking ya kai personal kayayyakinshi gidanshi na kwandila, tou tabbas ya san wacece Huda! Ahankali yaji tace “Amman Abba yanzu bama tare mun yi fad’a sosai..” Ta k’arashe maganar ta na kuma yin k’asa da kanta. Murmushi Abban yayi kafin yace “Ai kuwa ke kad’ai kike fad’anki! Don shi gashi yazo yana binmu one by one yana expressing how much he loves you.” Da sauri tasa tafukan hannayenta ta rufe fuskarta… Tashi d’aya Maryam ce ta fad’o mishi arai, yanayin kunyarsu iri d’aya ce, kalli fa fad’a tace sunayi amman kuma anyi magana ta hau jin kunya…. Murmushi yayi kafin yace “Kije ki shirya dan na san yanzu Auwal zai zo, Shuraim yace min “zai bada hadda yau a islamiyyarsu da suke zuwa duk asabar da lahadi so nan zai je shi ba zai samu daman binku ba. Sai kuje da ke da Sudais kawai.” “To” tace, sannan ta mik’e, har tayi gaba sai kuma ta juyo Tace “Abba Allah da gaske nake yi munyi fad’a dashi, fad’an gaske!” Dariya ta bashi ganin yanda ta dage akan ita fa sun yi fad’a, amman ko a cikin bayaninta, yadda take yabon Arshaad d’in, ya sanya ya fahimci still tana son abunta. Murmushi kawai ya sake yi yace “Tam na yarda kun yi fad’a, shikenan.” Ahankali ta juya ta wuce don taje ta shirya. Lumshe idanunsa yayi ya kwantar da bayanshi da kanshi jikin kujerar... .....Zai fara yin magana da Arshaad first! He just hope yanada kwakkwaran reason ba munafuntar su yayi ba all this time.. Saboda in dai hakane tou gaskiya zai murzawa idanunsa toka, ya hanashi Huda! Dan ba zai bari y’arsa ta rayu da Namiji mai b’oye b’oye ba. Ya lura da tana sonshi, so yana adduar Allah yasa Arshaad d’in ya zamana yanada reason d’in da zai kare kanshi kwakkwara! Zai yi farin ciki da hakan domin kuwa ya san that’s wat she wants.. Dukda kuwa yana da wani buri da ya d’aura akanta tun lokacin da ya fahimci yanada y’a mace mai shekarunta amman tunda he’s late ta riga ta zab’i Arshaad, shikenan ba komai, yana yi mata fatan alkhairi….. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 43. Cikin nutsuwa ta shirya ta d’auki y’ar k’aramar jaka da wayarta ta fito. Bata samu Abba a wanann parlourn ba! Dan haka ta sauk’a chan k’asa cikin nutsuwarta… Tun kafin ta k’arasa ta hangoshi shi da Sudais wanda shima har ya shirya da alamun ita yake jira. Har ta sauk’o Abba bai lura ba, yana nan ya dulmiya duniyar tunani….surutun Sudais ne ya d’an dawo da hankalinshi parlourn, dai dai nan kamar had’in baki Auwal ya shigo.. Riga da wando ne a jikinshi, rigar maroon mai dogon hannu da black jeans asalin crazy! Ga wani had’add’en takalmi sau ciki mai mugun kyau black! D’azu uban gashi ne a kanshi amman yanzu yayi sabon aski an aske gefe da gefe da k’eyar an bar tsakiyan (saman kan) lallausar sumar ta taru a kanannad’e iya tsakiya sai shek’i take yi, gefe wajen kunnenshi na dama ta sama inda aka aske an sake bi anyi wani style kamar zigzag, asalin farar fatar kan nashi ta baiyyana ta fito da design d’in radau!! Ga wani bracelet kamar sark’a a hannun daman shi, sannan ya maka wani arnen bak’in glass mai shek’i wanda kana gani kasan mai mugun tsada ne…… Yana shigowa k’amshin turarenshi ya gauraye ko ina. Tafe yake yana danna waya, har ya k’araso cikin parlourn bai ma lura da su Abban ba. Da Hudan ya fara lura kasancewar ta a tsaye sai kuma sudais wanda ya k’arasa wajenshi da sauri yace “Ya Auwal har da wannan wajen nan zaka kaimu ko? Wanda ake sa glass ayi game..” Dariya yayi ya d’an sa hannunshi akanshi ya hautsina y’ar sumar data d’an tarar mishi ba sosai ba sannan yace “Ashe yau za asha ihu kenan” Dariya dukkansu suka yi, sannan ya dago ya kalli Huda.. Three quarter riga mai fad’i ce a jikinta wadda ta wuce mata har gaba da guiwowinta peach colour, sai pencil trouser white, ta yi mopling da white vail, sai y’ar k’aramar white bag d’inta. Kwalli kad’ai ne a idonta sai d’an pink d’in jam baki data shafa amman tayi masifar kyau! A ranshi yace “Yarinyar akwai kyau kamar aljana” sai dai shi ko sau d’aya bata tab’a burgeshi ba, asalima shi haushin ta yake ji! Ko dan ita tayi sanadiyyar zuwan su Mom da Mammy cell ne, oho! Duk da ba wani shiri yake yi da Mom d’in tashi ba amman yayi mugun jin zafin abunda aka yi musu ata dalilin y’ar k’aramar Yarinya. Gyaran muryar da Abba yayi ne ya katse mishi tunani.. Bai ma lura da shi ba, sai yanzun. “Abba ashe kana nan.” Ya fad’a yana d’an murmushi. A b’angaren Abba kuwa yanda yaga ya kafe mishi y’a da ido ne ya sanya yaji kamar yace su fasa fitar! Ajiyar zuciya ya sauk’e yayi saurin kawar da tunanin daga zuciyarshi, sannan ya sake kallon Auwal d’in yace “Kallo d’aya tak! Duk wani mai isheshen hankali zai yi maka ya fara yi maka zargin gudowa kayi daga gidan mahaukata!!Kalli wandon ka kamar wanda aka yi maka gorin kaya, kalla nan” Abban ya mik’e yana nuna mishi wandon da hannunsa kafin yace “har cinyarka ana iya hangowa! Wannan d’an iskan askin shi kuma an hanaka amman naga abun naka gaba yake yi dan na yau ma yafi na kullum! Sai kace wani zakara. Harda sark’a a hannu!! Wai ni auwal mai kake son ka zama ne? Eh??” Yayi mishi tambayar cikin b’acin rai, bai jira jin amsar shi ba yace “Wallahi ka tabbar ka seseta wannan d’an iskan askin kafin ku dawo gidannan inba hakaba kowa sai ya ji kanmu!” Yana gama fad’in haka yayi hanyar sama ranshi a b’ace… Gaba d’aya In ka kalli Auwal ba zaka tab’a kiranshi da musulmi ba, ba abunda yafi b’ata mishi rai kamar sark’ar hannunshi ya lura harda wata sark’a a wuyanshi wadda ta b’uya a cikin rigar kawai shiru yayi masa dan in yaci gaba da kulashi zuciya zata jashi ya fella mishi mari!! Anyi maganan anyi har an gaji amman saboda ya raina mutane sam bai fasa ba. Auwal kuwa kamar ya had’iye zuciya… Tunda Abba ya fara fad’a ya had’e rai! Ba abunda yafi b’ata mishi rai irin tijarar da Abban yayi mishi a gaban Yara, don haka ya ja hannun Sudais suka fice ba tare da yabi ta kan Hudan ba. Ganin da tayi ranshine a b’ace yasa kawai ta bishi wajen, bata biye sa ba. Sudais yasa a gaba, amman dake Yaron ya fishi hankali yana ganin Hudan ta taho ya bud’e mata motar shi yayi saurin tsallakawa baya. Kamar zai yi magana sai kuma kawai yayi shiru. Ko ida rufe murfin motar bata yi ba ya fige ta da azabar gudu.. Daman masu gadin tun da suka hangoshi ya tada mota suka wangale gate, gudun kar garin saurin bud’ewa idan ya taho yayi gaba da wani! In kuma kayi jinkiri a balbaleka da zage zage! Komin tsufan mutum. Gudu yake shatatawa kamar zai tashi sama.. Hudan duk ta tsure, ta rik’e kujeran da take kai gam! Ta k’ame, yana lura da ita wanda hakan ne ma ya sa ya sake k’arfin gudun nashi. Ikon Allah ne kawai ya kaisu inda za suje, Ita ba sanin munjibur park d’in tayi ba, shiyasa bata gane inda suke ba! “Fito” Yace, yana k’ok’arin bud’e motar ya fita. Sudais ma ya fito daga baya. Tana fitowa tun kafin ta rufe motar gabanta yayi mugun fad’uwa ganin su a police station. Juyowa tayi tana kallonshi wanda zagayowarshi kenan kafin tayi magana yace “Su Mom zan nuna miki, halinda suke ciki all because of you!” Ganin ya tsareta da ido ne yasa ta wucewa jikinta sai karkarwa yake yi. Direct wajen da suke ya nufa, bayan ya amsa gaisuwar police d’in da suka tarar a reception, sannan ya zaunar da Sudais a kan kujerun wajen yace mishi “kar ya kuskura ya tashi, ya jirasu a nan” Da kyar ta iya k’arasawa wajen! Tun daga lokacin jikinta ya mutu, yayi wani irin sanyi… Da kyar ta iya bud’e baki ta gaishesu amman ba wadda ta amsa mata tsakanin Mammy da Mom, Ummi ce wadda take mugun jin jiki ta d’ago da ta kalle ta a hankali tace “Lafiya Alhamdulillah.” Sannan ta komar da kanta k’asa ta kwantar. Wata jakar leda wadda ya shigo da ita yayi saurin mik’a musu, ganin wani police ya taho yasa Mammy tayi saurin b’oyewa a cikin mayafinta , sannan tace “Ka cewa Arshaad inata jiranshi akan maganar mu naji shiru!! Shekaran jiya dana samu waya nayi mishi more than 20 miss calls amman bai d’auka ba k’arshema kashe wayar yayi! Kace nace Dan ubanshi shi nake jira in kuma ba zai iya ba to ya daina kashe mini waya kawai ya fito fili ya fad’a min!!” Hudan kamar tace mata ‘ba kashe wayar yayi ba’ Don tana gani kamar wannan number da tayita kira ranar nan da wayar tana a hannunta ne Mammy take magana akai! Sanann sub’ucewa wayar tayi a hannunta ta fashe…. Amman kuma kawai sai tayi shiru ganin yanda ko inda take Mammyn bata kalla ba. “Muje” taji muryan Auwal. A hankali tace musu “Sai anjima’ Nan ma ba wanda ya kulata sau Ummi dake kwance taga ta d’an d’aga mata kai alamun ok. Suna fita Mom tacewa Mammy “Nifa gaskiya ko Arshaad ya kawo kud’ad’en nan ba inda zan biki mu fita, maybe ma yaudararki police d’in nan yake shirin yi, dan ba miliyan uku ba gani nake ko miliyan arba’in zaki bashi ba lalle ya iya k’etare umarnin Granpa ba! And in ma ya yarda, bakya tunanin irin mummunan hukuncin da shi Granpa d’in zai yanke mana muddin yaji labari?” Murmushin takaici Mammy tayi kafin tace “Adama na gaji da halin mutanen nan! Na kawo wuya! Ke dai kawai kamar yadda na fad’a miki ‘ki zuba min ido’ wuyarta kawai mu fita daga nan, dakanshi shi Granpa d’in zai kira mu mu koma gidajenmu… Shi kuma Yahaya wallahi kinji rantsuwar d’an musulmi ko? Sai na gasa mishi aya a hannu! Wai ace mutumin nan ya dawo amman ban isa yazo ya ganni ba? Hak’uri na ya k’are Adama!Maganar gaskiya na gaji da cin kashin da ake min na gaji!!!” Ta k’arashe maganar tana share kwallar data zubo mata. Matsowa daff da ita Mom tayi tana magana k’asa k’asa gudun kar Ummi taji, tana cewa “To ki kira maman ki mana, ai kina nan ma ita d’in zata iya yi mana komai” Ajiyar zuciya Mammy ta sauk’e kafin tace “Tace babu ruwan ta, ranar dana ari wayar ai har ita na kira kin tafi fitsari lokacin, tace in yi hak’uri har lokacin daya yanke yayi, ita ba ruwan ta waye waye….. Ni k’arshe ma kashe wayar nayi dan tsabar bak’in ciki. Adama ba abunda yake d’aga min hankali irin maganar nan ta fita wasu suji, dukda shima Granpa d’in na san k’ok’arin b’oyewa yake tayi dan Inajin wanda yake sa mana ido yana gayawa wani Abokin shi wai ‘kar a had’a mu da kowa Granpa d’in yayi waya yace a ware mu.’ Inaga yana gudun kar wani ya gane mu ne. Amman fa kin san zancen duniya ba ya b’uya, wacce irin kunya kike tunanin zamu kwasa idan k’awayenmu sukaji labari?”. Ajiyar zuciya Mom ta sauk’e kafin tace “Shikenan ba damuwa, amman kinada tabbacin ba zata kwab’e mana ba ko?” D’aga mata kai kawai tayi alamar ‘eh’ Shikenan nima zan gwada yiwa Auwal magana, inaga maybe ya taimaka, dan naga kamar abun ya dameshi. In kuma yak’i, to ko sark’ata ce zance ya duba ya d’auki d’aya ya saida sai ya kawo kud’in” Cewar Mom. “Allah ya shige mana gaba”Mammy tace Daganan suka ci gaba da maganganunsu, ita kam Ummi tun d’azu bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita, ata dalilin allurar da akayi mata..... Tabbas su Ummi basu kyautaba amman a nata tunanin bai kamata ayi musu haka ba! Hukuncin yayi yawa kuma abunda akai musu d’in tabbas zai jawo mata bak’in jini a wajen y’ay’ansu ne, besides ita tama yafe musu har k’asan zuciyarta…… Tana waennan tunanin suka isa munjibir park, sun sha doguwar tafiya ba kad’an ba, ita Huda jikinta ma duk ya fara ciwo. Parking yayi duk suka fito, sai da ya gama komai ya siyaawa Sudais ice cream d’inshi, ya d’aura shi a lilo tukunna ya dawo inda take tsaye. Kallonta yayi kafin yace “Ko kema lilon kike son hawa k’atuwa dake??” Kauda kai tayi ta girgiza kai, kawai. Murmushi yayi kafin yace “Ta kwancen, itace wacce aka saki Mamanki a dalilinta! Matar Abbanki har a yanzu.” Taji zafin maganar amman ta shareshi kawai… “Wadda ta bani sak’o kuma, na san daga maganar da tayi mini kin fahimci Mahaifiyar Arshaad da Aaima ce! D’ayar kuma Mom d’ita ce! Ummi, ko dan su Sudais da kike pretending kina so, ya kamata ki tausaya mata. Mammy kuwa ko Arshaad ya kauda kai saboda son da yake yi miki, to ina tausaya miki In Aaima ta dawo dan sam ba za kiji dad’i ba at all. Mom d’ina kuwa, to be sincere ba ma wani shiri da ita, but blood is thick! And you should know me by now I’m capable of anything.. Huda! All you need to do Is talk to your stubborn father ya san abun yi… Idan ba haka ba kuma Wallahi! Ni kaina ina jin tsoron abunda zan yi miki!… A matsayin ki na so called cousin d’ina yasanya nayi deciding in baki warning first akan in aiwatar da abunda nayi niyya akanki kai tsaye. Idan kika yi min abunda nakeso to kin tsira In kuma kika yi taurin kai! To fa gaskiya i can’t save you from me. Lastly, kar ki kuskura kiyi mentioning cell d’in da kika je yau, to anyone.” Ya k’arashe maganar yana kallon cikin idonta. Da sauri tayi k’asa da kanta… Tabbas ta hango b’acin rai a cikin idanuwanshi, gashi har colour d’insu ya soma chanza wa. Bud’e baki yayi zai yi magana yaji an dafa shi ta baya. Kafin ya juya ita ta zxagayo gabanshi ta tsaya tsakaninshi da Huda. Murmushi yayi kafin yace “Har kin iso?” Yayi maganan yana mai rik’o waist d’inta ya d’an jawota jikinshi. Yadda Huda ta zabura zaka d’auka ita aka janyo.. D’an jaa da baya budurwar tayi ta d’an juyo tana kallon Hudan kafin tace “Who’s she??” Tayi masa tambayar ba tare data kalleshi ba, da d’an alamun b’acin rai a fuskarta. Murmushi yayi kafin yace “Relax! She’s just a cousin, daga k’auye tazo shine Daddy yace In kawota ta ga gari.” Ture hannunshi da yake rik’e da waist d’inta tayi, har yanzu idonta nakan Hudan wadda ita ma ta kasa d’auke idanunta akan su tana kallon ikon Allah, budurwar tace “Cousin and more, ha?” Dariya sosai yayi this time around kafin ya matso da fuskarshi dede tata tukun yace “If she’s cousin and more would I do dis in front of her?” Ya k’arashe maganan da kissing lips d’inta lightly….. Da sauri Hudan ta bar wajen tana had’a hanya. Kujerun data gani a gefe chan taje ta zauna tana haki tana istighfari. A chaan wajen su Auwal kuwa murmushin jin dad’i budurwar tayi sannan suka shiga sabgogin gabansu.......... A tap d’in wajen tayi alwala, wasu mata manya ta gani da darduma sun shinfida k’atuwa suna zazzaune ga kuloli alamun picnic suka fito, dan haka ta k’arasa tayi musu sallama tace “Dan Allah tanaso za tayi sallah” Da fara’a suka tarbeta suka matsa mata d’ayar ta fiddo hijabi a jakanta ta bata.. Bayan ta idar suka yi mata tayin abinci, gorar ruwa kawai ta d’auka ta sha tayi musu godiya a wajen ta ci gaba da zamanta a wajen, tana hango Sudais yanata wasanshi, chan gefe kuma Auwal da budurwarshi an cika musu gaba da kayan kwalama kala kala amman ita ko ruwan sha ya kasa bata… Ganin bata da abunyi yasa ta bud’e wayarta ta hau karatunta ragowar ruwan da ta sha d’an mitsitsi ta rage ta tofa a ciki.. Sai da aka fara kiraye kirayen sallar Magrib tukunna taga ya taso… Yana tasowa ta mik’e ta hau sallarta dan ta lura In suka kama hanya yanzu sai sun kusan 40min suna tafiya. Takaici, kamar ya kifa mata mari haka yaji, ba yadda ya iya shima yaje yayi alwalla yayi iya magribar d’in daya tarar maza sunyi jam’i suna yi. Tare suka jero da budurwar da Sudais da yaje ya d’auko, suka nufota. Sallama da godiya ta yiwa matan da suma suketa shirin tashi, ta rik’e hannun Sudais wanda ya iso gareta da sauri suka nufi inda suka yi parking. Sai da ya k’araso ya bud’e motar tukunna suka shiga Ita da Sudais suka zauna a baya shi da budurwar suka zauna a gaba. Sai da suka biya wani gida a lamido crescent flat mai kyau suka ajjiyeta tukunna suka wuce…Abunda ya d’aurewa Hudan kai shine shi Auwal d’inne ya bawa budurwar makullan gidan! Ita dai batayi magana ba, ta yi shiru kawai tana mamakin shi.. Ko da yace wani ya koma gaba, Sudais ta matsawa ya tsallaka. A gajiye suka isa gida yana ajjiye su yayi reverse ya sake fita. A parlourn ta tarar da Arshaad wanda suna dawowa daga kai Amarya ya had’u da Aslam cikin hira yake gaya mishi ‘Hudan sun fita munjibir da Auwal!’ Ko wanka kasa yi yayi ya taho gidan… Yana tunanin bin bayan su kenan suka shigo. Ajiyar zuciyar daya sauk’e lokacin da suka shigo sai da taji, sarai ta lura dashi amman ta d’auke kai tayi wucewarta….ganin yadda ta bawa iska ajiyarshi kuwa hakan yayi mugun bak’anta mishi rai! At least in tana jin haushinshi ai ko darajar kallo yaci ace ya samu. Sai da ta raka Sudais d’akin shi tukunna ta nufi side d’inta. Tana shiga parlourn ta saki jakarta ta tafi da gudu tana ihun murna. Rungume juna sukayi suna dariya kafin tace “tun yaushe kika zo?” Dariya itama Sakina tayi tace “D’azu Abbas yaje da kanshi ya d’auko ni hala ke kikayi mishi kwatance ko?” “Eh” tace tana sake hugging d’inta, sannan ta jata suka nufi bedroom. “Ma shaa Allah, Ubangiji mai zamani” Sakina tace. Sannan tace “gaskiya wajen nan ya burgeni Huda, over!! Ina tunanin had’uwar parlourn ashe bedroom d’in har ya fishi? “ Murmushi Hudan tayi tace “Ni kuma duk toilet d’in yafi burgeni” da sauri Sakina tace “muje In gani” ta fad’a tana cire hijab d’in jikinta dake nan har k’asa. Suna shiga nan itama tace “gaskiya kam toilet d’in duk yafi had’uwa” Haka nan suka taru suka dinga hauka, daga su kunna wannan sai su kashe wannan, wani abun ma ba iyawa suka yi ba da karambani suka koya. Babu abunda yafi burge Sakina irin closet dan haka ta fito wajen tana kuma setawa Hudan zaman kayanta kafin ta fito a wanka. Bata wani dad’e ba ta fito a wankan tana fitowa tace “itama ta shiga tayi wanka sai ta chanja kayan jikinta, lace d’in zai yi mata nauyi dan garin ana zafi sosai” Murmushi Sakina tayi kafin tace “Ni fa daga ni sai hand bag d’ina nazo, Ummu daa hanani zuwa tayi fa, sai da Baba ya bud’e mata wuta!Amman tace wai gobe da safe in dawo, har na d’auko kaya set uku tace wai In na tafi da kaya ba zan dawo da wuri ba! Shi kuma Baba yace tunda Abba ne da kansa ya rok’esa to sai lokacin da kika saba da nan d’in tukunna zan koma!. Wallahi tun d’azu jikina a sanyaye yake, Mama ma bata san na taho ba, dan Ummu tace bata san da wanne ido zata kalle ta ta fad’a mata ba! Shinema dalilinta na hanani zuwa tun farko daman.” Ajiyar zuciya Hudan ta sauk’e kafin tace “Ranar dana tafi ya aka yi? Ina ta kiran Ummu bata d’auka.” “Hmm.. Mama ce ta rikita kowa wai Abba ya aiko an sace ki! Amman har yanzu a haka su Ummu suka barta basu gaya mata ke kika tafi da kannki ba saboda kar taji haushinmu, kawai dai ance mata kina nan d’in so ta kwantar da hankalinta tunda kina wajen Mahaifinki ne ba wani mugun hannu ba.” Hawaye Hudan ta goge kafin tace “Sakina wallahi ni ban san ya zan yi ba” ta fad’a tana fashewa da kuka, rungumeta Sakina tayi kafin tace “wallahi Huda ni kaina abun nan yana daure min kai, sai ka rasa ina zaka tsaya, gaba d’aya ni kaina i’m confused, ballantana kuma ke. Muyi ta addua kawai ki kwantar da hankalinki, kinji?Please”. Hawayenta ta goge jikinta duk yayi sanyi, sannan ta d’an d’aga kanta a hankali kafin ta cewa Sakinan “kije kiyi wanka sai ki sa kayana Inner wears kuma ina da sababbi suma, muyi sauri dan na san yanzu Abba zai fara kira, lokacin dinner yayi.” Hijab d’inta wanda ta ajjiye a bedroom Hudan ta fita ta d’auko ta wuce ta sa a washing machine ta fito ta bata towel, Ita ta tayata wankin dan sai da ta tayata ma shanya kayan data cire suka wanke d’in tukun ta fito ta barta dan tayi wankan. Sallah ta tarar Hudan tanayi lokacin da ta fito dan haka itama ta nemi hijab ta tayar da sallar. Sauranta izu d’aya a izu goman daya kamata tayi, dan haka ta hau karatu bayan ta idar…. Tana idarwa tayi addua ta tofa ta had’e ruwan d’azu data shigo dashi dana d’akin waje d’aya!. Da mamaki Sakina ta kalle ta kafin ta tambayeta Bayani ta hau yi mata a kan ‘na maman Aslam ne wanda ta basu labarinta….’ “Allah sarki Allah ya bata lafiya, abun tausayi wallahi” Sakinan tace. Kayan bacci dukkansu suka sanya, sai suka d’aura hijabai a sama, sannan suka sauk’a dan Abba har ya kirata kamar yanda tayi tsammani. Sai da ta lek’a d’akin su Sudais, ganin basa nan yasa suka nufi k’asan. Har Aslam suka tarar a dining d’in da Arshaad amman yanzu ya chanja kaya wanda hakan ke nuni da wanka yaje yayo. Yaji tahowa amman bai d’ago ba, dan babu abunda yake sosa mishi zuciya irin yadda ko kallon inda yake bata yi. Sai da suka k’araso tukun Abba yace “a’a inyee! Yau ga annuri a fuskar princess, duk a dalilin Sakina, irin wannan murmushi haka?!” Ya fad’a yana murmushi kafin yace “bismillah ku zauna mana” A hankali suka fara k’ok’arin jan kujera… Yana shirin d’agowa ya ga da gaske Sakinan ce jin abunda Abba yace, yaji tace “Ya Arshaad Ina wuni.” Da sauri ya d’ago, ya d’an zaro ido alamun mamaki, sai kuma ya fara murmushi yace “Lafiya, Alhamdulillah. Ashe kece da kanki! Welcome, ya gida?” “Alhamdulillah” tace kafin ta d’an turo baki tace “Ai gani nayi da farko ka wani had’e rai ko kallon inda muke ma bakayi ba” Dariya yayi kafin yace “Hankalina baya wajen ne, sorry” Itama murmushi tayi ta sake gaida Abba da Aslam wanda ya amsa ko kallonta bai yi ba! Tunda suka sauk’o ma ta lura bai ko kallesu ba… Tana ganinshi tashi d’aya ta fahimci shine Aslam. Lokacin da Hudan take zuzuta mata kyawun Aslam d’in bata yarda ba, dan har ta fara tunanin wani abun a tare da Hudan na daban, but yanzu kam tagani itama! “Tubarakallah!” Ta fad’a a k’asan ranta. Cikin nutsuwa taji Hudan suna gaisawa da Abba wanda yake zaune a opposite d’insu shi da Aslam. Da kulawa yake tambayanta hope taji dad’in ganin Sakina? Is she happy now? Taji dad’in zuwa munjibir park d’in? Ba wata damuwa ko?…… Murmushi Hudan tayi duk tana ta binshi da “Alhamdulillah komai Alhamdulillah..” Abun yayi matuk’ar burge Sakina a ranta tace “yau ina Baba da Umma suzo suga gatan da akewa Huda, suga yanda Abbanta yake janta a jiki yana lallab’a ta” Wani farin ciki ne taji ya lullub’eta, tabbas tana yiwa Hudan murna da baiyyanar Mahaifinta! Itafa sometimes ji take a ranta kamar ma tafi Hudan farin ciki. A hankali taji sun gaisa da Aslam, taga ita Hudan ta d’an samu darajar kallo a wajenshi tukunna yace “lafiya” da d’an mitsitsin bakinshi. Har an fara serving ta mintsili Huda da k’arfi ta k’asa k’asa inda ba za a gani ba. “Ouch” tace, a hankali sannan ta juyo tana kallon ta, harara Sakina ta zabga mata k’asa k’asa tace “shi ba zaki gaidashi ba???” Itama Hudan hararar ta maida mata ta cigaba da zuba abincinta! Mintsilinta Sakina ta sake yi, kafin tace “Wallahi ko ki gaisheshi ko kiyi ta karb’ar ruwan mintsili kala kala!” Dai dai nan wayar Abba tayi k’ara … Excusing kanshi yayi ya mik’e ya d’an koma gefe yana amsa wayar dan it’s a very important call ba zai yiu yayi ignoring ba. Kamar jira Sakina take, nan ta sake sakar mata wani sabon mintsinin da sai da tayi k’ara mai sauti sosai this time around har su Aslam sai da sukaji suka juyo suna kallonsu… Sudais kuma ya fara kyalkyala dariya dan shine a kusa da Sakina yana kallonta tun d’azu! Ganin da Huda tayi Sakina ba zata hak’ura ba yasa ta juya, kujera biyu ne tsakaninta da Arshaad d’in dan haka ta d’an kalleshi tace “ina wuni” Sai da ya sake tamke fuska tukun yace “Lafiya” Yanajin haushi a ranshi, wato gaisuwar ma sai ta ga dama zata yi, kuma shine na k’arshe! Har su Sudais sai da ta gama kulawa tukunna shine last! Tashi Sakina tayi daga kan kujerarta ta dawo ta gefen Hudan side d’in da Arshaad yake ta zauna kafin tace “Am i missing something here???” Tayi musu maganar tana juyowa ta kalli wannan ta kalli wannan. “Eat!” Arshaad yace sannan yaci gaba da cin abincin shi. Dawowar da Abba yayi ne ya katse mata maganganun da suka taso mata don haka tayi shiru… Luckily aka sake kiran Abba a waya dan haka ya mik’e yace “bara ya shiga wajen Daddy” Ba a jima ba Aslam shima ya mik’e, da sauri Hudan ta mik’e ta mik’a mishi Goron ruwan hannunta Opposite yau ma suke dan haka ya kalle ta yace “thankyou!” a hankali yana kallonta. Bata san daliliba! Dan kwata kwata sam sai ta kasa janye idanunta daga nashi. Tunda Mama ta kawota duniya ko a tv bata tab’a ganin kwayar ido mai kyan nashi ba! Shape d’in Idon kansa abun son ka kalla ne! Komai na idanun nasa masu kyau ne Itakam wata rana zata tambayeshi ‘me yake shafawa eyelid d’insa?’ Dan wani haskene yake fitowa daga wajen ..... Dukda yadda zuciyarta ta tsananta bugu hakan bai sanyata ta d’auke idanunta daga kansa ba kuma baisanya ta sakar mishi robar ruwan da ta mik’a masa ba! “GOOD NIGHT Sakina!!” Suka ji Arshaad ya fad’a da d’an k’arfi! Da sauri Aslam yayi firgigit, ya janye robar da mugun k’arfi, sannan ya juya yayi hanyar fita. Har ya fice daga parlourn bai yarda ya sake juyowa ba. Hudan ita kam kunya ce gaba d’aya ta lullub’eta.. Ashe har Arshaad da Sakina sun mik’e su shuraim kuma suna shirin fara hawa bene ita bata ma sani ba!. Yana shirin barin wajen Sakina tace “pls mana” Tana d’an karkartar da wuyanta. Murmushi yayi yace “she’s busy rn, let it go kawai.” A hankali Sakina tace “Plss” Tana had’e hannuwanta biyu waje d’aya alamun rok’o. Ajiyar zuciya ya sauk’e ya d’an ja ya tsaya. Hudan na ganin wucewar su Shuraim sama ta juya itama zata bar wajen. Hannu Sakina tasa ta rik’eta. Ba tare data juyo ta kalleta ba tace “Sakin mani hannu plss, bacci nake ji” Jin abunda tace ya sake tunzurashi don haka kawai ya fice fuuu!! Ko sauraron Sakina bai sake yi ba. Haushi Sakina taji ta saki mata hannu suka haura sama… Har suka shafa addua suka kwanta suka ja bargo ba wanda ya yiwa d’an uwanshi magana........... BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 44 Tun Asuba Hudan ta sauk’o ta fara kula Sakina, dan ita ta tasheta ma sallar Asuba. Sakina kuwa har suka yi wanka suka shirya, aka je aka yi breakfast aka dawo bata kula Hudan.nKo tayi mata magana ma sai dai tayi mata banza: Hankalin Hudan bai tashi ba, sai da taga Sakina ta saka kayanta waenda tazo dasu chap ta shirya, tace mata “sai sunyi waya”. Da sauri ta shiga gabanta ta tsaya dan har ta kusa k’ofa, kafin tace “Ban gane ‘sai munyi waya’ ba! Me hakan yake nufi?” Ba tare data kalletaba tace “Tafiya zan yi” Cikin rashin jin dad’i Hudan tace “Akan Ya Arshaad kikayi fushi dani haka har kika yanke hukuncin tafiya ki bar ni?? Kin san kuwa me yayi min?” D’ago dara daran idanuwanta Sakina tayi, kafin tace “Nasani Hudan, sanin abunda ya had’akun ne ma har yasa kike fushi dashi hakan ne zai sanya in tafi.. Jiya baki b’ata min rai sosai ba amman dana san dalilin fad’an naku wallahi bakiji yadda raina ya b’aci ba.” Cikin takaici da son fahimtar da ita Huda tace “Sakina Jalila fa yaje........” Cikin katseta Sakinar tace “Na fad’a miki fa, na sani. Jiya mun yi chatting da shi sosai ya fad’amin komai! Haba Huda, kamar baki san wacece Jalila ba? Dan ta fad’a miki magana sai ki hau ki zauna?? Kishi ne ya rufe miki ido ko rashin wayo? A tsakaninki keda Ya Arshaad bai kamata a samu haka ba. Jiya cemin yayi kawai bakya sonshi, maybe akwai wanda kike so yanzu saboda he can recall yadda kikayi calling off engagement d’inku saboda Ya Junaidu kawai don bakya son ki b’ata mishi rai! Amman shi yanzu lokaci d’aya kin murzawa idonki tuka kinata zuba mishi rashin kirki! Ba abunda yafi b’ata mishi rai irin yadda ana fad’a miki kika hau kika zauna, kamar daman tun farko kina zarginshi… Anyways yace yana neman alfarma a wajenki, anjima zai san yadda zai yi ya kawo Jalila nan, akawo AlQurani suyi alwala shi da ita kowa ya rantse akan gaskiya yake fad’a! But yace b4 then dan Allah ki d’au waya ki kira Aaima ki tambayeta waye Auwal ya halinshi yake!” Tunda Sakina ta fara magana jikinta yayi sanyi Sai yanzu take ganin rashin kyautawarta…. Ganin Sakina, tana shirin zagayeta ta fita ne yasa ta kuma tararta ta tare hanyar kafin tace “To kiyi hak’uri ki fasa tafiya, haba Sakina, ko kece kikaji haka fa dole kiji haushi” Da sauri Sakina tace “Hudan zan tafi! Dan ba zan iya tsayawa inga wai Ya Arshaad yana dafa Qur’ani yana rantse miki akan ba shi ne ya yiwa Jalila ciki ba! So that ki yarda kuyi getting back together.. Haba Huda! Ya Arshaad ne fa, wallahi sam bai chanchanci haka daga gareki ba!. But ba zan hanaki ba, ki barshi yayi dan na san tunda kin riga kin saka haka a ranki to in ba rantsuwar yayi miki ba ba zaki tab’a yarda ba!. Amman wallahi kinji dai na rantse miki ba ruwan Ya Arshaad a lamarin nan! Shi wannan Auwal d’in shine yayi aika aikar shi kuma zaki ce na gaya miki, Ya Arshaad ya fad’a min baki tab’a ganinshi ba sai ranar amma yana fad’a miki magana kika hau kika zauna shi kuma da kika sanshi for almost 4 years kika k’i yarda dashi. Hudan Ya Junaidu, kwatar ki yake yi a hannun su Jalila idan suna kimar ki amman kince ba zaki tab’a manta alkairinshi gareka ba Ya arshaad fa? Zaki iya gaya min irin tarin alkairan da yayi miki? Ba ke ba har ni kaina da nake kusa dake sai da alkairinshi ya shafeni.” Ahankali Hudan ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace “Sakina ranar nan fa a gaban ki Mama tace min taji Yaro yazo yace wai Jalila taje inji Arshaad..” Murmushin takaici Sakina tayi kafin tace “kuma a same day da time ne ke da Ya Arshaad d’in kuka yi dogon video call ba! Ba ma voice call ba video call and a d’aki muka ganshi throughout bai fita ba har kuka gama, ba a mota ba!. Kinsan wani abu Huda? Bata jira jin amsarta ba tace “wallahi duk makirci ne, so sukeyi kawai su shiga tsakaninku! That Auwal shi yayi planning komai, ban san mecece agenda d’inshi ba, but na san shine master mind! Ban ganshi ba amman na tsaneshi!. Ni dai shawarata a gareki itace ki bud’e idonki da kyau, ki fahimci gaskiya tun kafin dare yayi miki! Arshaad ya sanki ya soki tun kina Hudan ki! Idan kikace zaki juya mishi baya yanzu gaskiya baki kyauta ba!. Ban hanya in wuce, dan ba zan iya ganin wannan abun takaicin ba.” Rugumeta Huda tayi kafin tace “Shikenan ya wuce Na hak’ura! Dan Allah karki tafi.” “No, Hudan seriously ki bari yayi miki clearing confusion d’inki, saboda kar ki dinga ganinshi da abun dan na sanki da taurin kai! Kar kije an kashe case but still kina zarginshi so just ki barshi su zo d’in.” A hankali tace “komai ya wuce, ki cire hijabin please haba mana”!Ta k’arashe maganar kamar zatayi kuka. Sai yanzu Sakina tayi murmushi kafin tace “Shikenan na faasa tafiya amman ki barsu kawai suzo d’in ayi a gama” D’aga mata kai Hudan tayi. A hankali Sakina ta koma ta zauna akan gado, bayan ta cire hijabin. Da kad’an kad’an Hudan ta dinga janta da hira har ta samu ta sake ta daina fushin.. Nan take bata labarin Ya Junaidu, amman the good news is that DNA d’in su Baba bai yi matching da gawarwakin ba Both wanda akayi a Lagos da wanda suka taho da sample d’in nan Kano aka yi. Hawaye Hudan ta share kafin tace Yanzu Ya Junaidu ya b’ata kenan?” A hankali Sakina tace “Mu yita addua kawai Allah ya baiyyana shi” “Ameen” tace. Ba abunyi dan haka daga kallo sai chatting da hira.. Yau su biyu tol suka yi lunch, su Shuraim suna school Abba kuma ya d’an fita wasu ayyuka, Arshaad bai lek’o ba Aslam ma haka. Sai bayan Magrib Arshaad ya kira Sakina yace mata “suna k’asa shi da Jalila, su sauk’o!”. Jalila tunda take bata tab’a jin farin ciki irin wannan ba!……. D’azun tana d’aki Gwaggo Asabe tazo tace mata “taje, inji Arshaad, yana kiran ta.” Kasa b’oye farin cikin ta tayi a gaban Gwaggwo Asaben har da su fesa turare da shafa jambaki, daman already idanunta da kwalli fuskarta kuma da powder! Ita dai Gwaggo Asabe tsayawa tayi tana kallon ikon Allah, Allah yasa dai ba wannan Yarinyar Arshaad zai kwaso musu ba, ita tunda tazo gidan gaisuwa bata tab’a had’asu ba, gashi bata son aiki, hatta d’akin da take ciki sai dai tazo ta kira aje a gyara mata. Doguwar riga y’ar kanti mai kyau ce a jikinta, dan haka ta d’auko d’an k’aramin mayafi tayi d’auri sannan ta d’auko wani ta yafa shima d’an mitsitsi daga nan ta d’au wayarta tazo ta wuce ta fita ta bar Gwaggo Asabe da baki a sake. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauk’e, kafin ta lek’a da d’an k’arfi tace mata “yana chaan waje a bakin mota” Don har tayi nisa. “Ok” Kawai Jalila tace tayi gaba abunta. A bakin motarshi ta ganshi a tsaye. Bai yi wani kwalliya ba hasalima Jallabiya ce a jikinshi bak’a amman sai da numfashin Jalila ya kusan d’aukewa dan yayi mugun tafiya da imaninta! A k’asan ranta tace “Ma shaa Allah” Tanajin tsananin tsantsar k’aunarsa tana sake ratsa dukkannin ilahirin jikinta, itafa ko da ace Arshaad zai dinga yi mata dukan tsiya kullum! Muddin zai yarda ya aure ta su zama k’ark’ashin inuwa d’aya, ta na amsa sunan matarshi to wallahi zata iya zama da shi!. Tsabar kallon da take yi mishi har tuntub’e tayi ta kusan fad’uwa wanda hakan ne ya janyo hankalinshi gareta dan shi bai ma san ta fito ba!. Suna had’a ido ya tamke fuskar shi kamar bai tab’a dariya ba. A take taji gabanta ya fad’i amma sai ta dake ta k’arasa inda yake still tanata satan kallonshi…. Sai da ta d’an risssina tukunna tace mishi “Ina wuni” cikin wani kalan yauk’i da kissa. Sake had’e rai yayi, ya bud’e mata murfin motar tukun yace “lafiya, shiga mu je!” A take tsoro ya rufeta, D’an bata san mai ya shirya mata ba Tana shiga, ya rufe ya zagayo ya zauna mazaunin drivern. Sai da taji tashin motar tukun ta bud’e idanunta dan tun lokacin da ya rufe mata motar ta wani lumshe ido tana murmushi saboda ba k’aramin dad’i taji ba. D’an juyowa tayi ta kalleshi fuskar shi yanda kasan wanda bai tab’a dariya ba! A hankali ta zaro wayarta ta turawa Auwal message saboda gaskiya in dai daga ita sai Arshaad ne a waje tou za a iya samun matsala dan tabbas tsaf! Zata Fallasa komai kuma ta san Auwal uban ta zai ci idan tayi hakan. Suna parking a cikin gidan dai dai message d’in Auwal ya shigo wayarta… Sai da su Hudan suka sauk’o tukun ta fahimci inda suka zo dan haka tayi mishi reply ta ajjiye wayar. Tunda ta sauk’o take maka mata harara!! A kujerun tsakiyar parlourn suke dan haka suma suka nufi wajen suka zauna. A hankali suka gaidashi ya amsa Sannan Huda ta kalli Jalilan tace “Ya Jalila ina wuni” Wani uban tsaki Sakina taja ta d’auke kai. “Hmm” Kawai Jalilan tace, wallahi ba don Arshaad yana wajen ba da sai ta tashi ta bugewa Sakina baki, dama a k’ule take dan ita kad’ai ta san tashin hankalin data shiga tun saukowarsu….. Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin ta kalli Hudan tace “lafiya” Kawai! Amman a k’asan zuciyarta ji take yi kamar ta mutu dan tsananin bak’in ciki! Wani irin tuk’uk’i ne yake taso mata saboda abunda idanunta suka yanzu nan ne gidan Mahaifin Huda?? Ba abunda yafi d’aga mata hankali daman tuntuni irin labarin da taji Gwaggo Asabe tanayi da wata mai aiki dattijuwa akan ‘Mahaifin nata ya bar gidan saboda Babansa yace ya zab’a ko shi ko ita!!’ Ita a tunaninta bashi da wani kud’i sosai dan tama d’auka gidan haya suka je suka kama suna zaune Ashe shima mugun mai kud’i ne. Ta tabbata Hudan y’ar masu kud’i ce kenan yanzu? Kuma Babanta yana matuk’ar sonta! Muryan Arshaad ce ta katse mata tunani jin yana cewa “Jalila ga Al Qurani, izu sittin.” yayi maganar yana nuna mata kan center table kafin yaci gaba “Idan baki da alwalla kije kiyi kizo yanzu! Zan rantse akan ‘cikin jikinki ba nawa bane ba! Sharri kika yi mini’ kema kuma zaki rantse akan ‘gaskiya kike fad’a (cikin nawa ne). Tsakanin ni da ke duk wanda yayi karya Al Qur’ani ya ci shi!.” Wata zazzafar zufa ce ta keto mata, tana shirin yin magana taji ance “Sannu Ya Sheik! Akaramakallahu.” Suka ji muryarshi yana takowa cikin parlour… Cikin gadara Auwal ya k’araso wajen, kafin one by one ya kalle su! Da kyar ya iya janye idanuwanshi daga kan Sakina! Sannan ya d’anyi murmushi yace “Ai ya kamata ni ma a gaiyyaceni meeting d’in ko?” Ya fad’i hakan yana mai neman kujera ya zauna kafin yace “Ya sheikh!! You were saying??” Banza Arshaad yayi da shi ya tashi ya matsa yana k’ok’arin d’aukar Qur’ani n Hudan tasa hannu ta d’auka a hankali tayi k’asa da kanta ta fara magana “Ya Arshaad dan Allah kayi hak’uri akan abunda nayi maka, na yarda da kai please ba sai ka rantse ba!” Wani farin ciki ne ya lullub’e Arshaad da Sakina a take. A hankali shima, yace “Thanks for trusting me Hudan, but i’ve to do this, please don’t stop me, okay?” Cikin katseshi tace “Nima please kar kayi haka, wallahi i trust you, in kuma kak’i yarda har kayi, to it means stilll baka hak’ura ba kenan da abunda nayi maka.” This time around murmushi yayi, kafin yace “Tou kawo, bani” Yayi maganan yana mik’a mata hannunshi Tana shirin yin magana, suka ji Auwal ya kwashe da dariya, cikin dariyar yace , “Yayi Romeo and Juliet!! Hey, look here” Yayi maganan referring to Hudan, kafin yace “Ki yarda da shi ko kar ki yarda da shi wannan matsalarku ce!! Ba wai dama na fad’a miki dan wani abun bane, that very day kin shigone a time d’in da case d’in yake goin that’s why har kika san maganar! Anyways Jalila it’s up to you, sai ki san abun yi… Tunda gashi yanzu ya nace akan ba nashi bane! I think su Granpa ne kawai zasu iya kwatar miki hakkinki dan ni kam daga yau na cire hannuna a case d’innan naku, in shaa Allah.” Ya k’arashe maganar yana mai bud’e hannayenshi biyu ya kai bayan k’eyarsa ya sak’ale sannan yayi resting gaba d’ayansa akan kujerar ya d’aura k’afa d’aya kan d’aya. Wani tuk’uk’i ne ya turnuk’e Sakina, bata san lokacin da ta fara magana ba! Kamar yadda ya yiwa Huda itama hakan tayi mishi Hey! You look here, Auwal kake ko wa? Waye ne ya gayyatoka nan? Wa ya kira ka? Waye ya kasa da kai? Wa yace maka ana son jin opinion d’in ka a cikin maganar nan? Hakanan kawai ka kama ka shigo tsulum! Ka tarar da mutane ko sallama baka yi ba ka hau magana kamar wani kwarkwar!. And let me tell you something abunda kayi yanzun, ya tabbatar da you got something to do with her and the baby! Kuma da kake wani cewa ‘zaka kai magana sama’ Ai da kai! Da mu! Da ita munafukar taka duk munsan gaskiya dan haka ina mai shawartarka da ka tabbatar ka d’auko fad’an da ka san zaka iya k’arasawa, in ta kwab’e!! Ke kuma!” Ta juyo kan Jalila, sannan tace “ki karb’a ki rantse a gaban kowa, sannan ki yi Allah ya isa a duk wanda ya cutar dake haka, a tsakanin Ya Arshaad da wannan Auwal d’in. Hudan Dan Allah ki bawa ya Arshaad, yau zan ga k’aryar iskanci.” Tunda Sakina ta fara magana Auwal yake kallonta ya kasa d’auke ido, k’arshe ma murmushi ya fara yana jin inama kar ta daina. Muryar Jalila ce ta katseshi jin tana cewa “Tou uwata! Ke har kin isa ki gaya min abunda zan yi?” Da sauri Arshaad ya juyo yace “in baki da alwala kije kiyi kizo yanzu” Yayi maganar babu alamun wasa a tattare da shi. Gaba d’aya jikin Jalila ya jik’e da gumi, tun lokacin da aka fara maganar, tsabar tsoro! “Ko bakya ji ne?” Arshaad ya fad’a cikin b’acin rai dan takaicin Yarinyar yake ji ba kad’an ba, ji yake yi kamar yaje yayi ball da ita. Auwal ta d’ago ta kalla, taga yayi mata wani kallon data fassarashi da warning!! Ganin kowa ita yake kallo yasa ta cire mayafinta ta ajjiye ta wuce tana cewa “ina ne toilet?” Wata k’ofa kurkusa Arshaad ya nuna mata yace “ta shiga”. Tana shiga ta turo k’ofar ta jingina tana haki, kamar wadda tayi y’ar tsere! Tunda take bata tab’a shiga tashin hankali irin na yau ba…ko hauka take yi ba zata tab’a dafa Qur’ani akan k’arya ba, akan gaskiyar ka ma ba a cika son kana dafawa ba, balle k’arya! Da albarkar ka ma ya ka k’are ballantana babu! Kuma ita a halin yanzu tana buk’atar albarkarta fiye da ko yaushe, da kusanci da Ubangijin ta! Tana so ta rok’esa arzik’i da soyayyar Arshaad dan muddin taci gaba da ganin Huda a cikin wannan daular alhalin ita bata da shi, to wallahi ta san zuciyarta sai tayi ajalinta…. Ta dad’e a cikin band’akin sosai, har sai da Sakina taje tayi mata knocking tukunna ta bud’e, tana bud’ewa ta zabga mata harara kafin tace “Banza y’ar karere kawai, sarkin zak’ewa!” Dariya Sakina tayi kafin tace “Ai gara ni y’ar karere ce Kuma kirana aka yi takanas! Nazo ba abun kunya ne ya zaunar dani a gidan ba.” Jalila bata ita take ba, dan haka tayi shiru kawai ta fito suka k’arasa parlourn tana tunanin next stage! Gabanta in banda fad’uwa ba abunda yake yi.. Ana tsayawa Sakina ta amshi Al Qur’ani n ta ajjiye akan centre inda yake tun farko, kafin ta kamo hannun Jalila ta kaita wajen tace “Bismillah!” Fusge hannunta Jalila tayi tana hararar ta Kallonta Sakina take sosai da mamaki akan fuskarta kafin tace “Da alama dai taimama kika yi ko? Dan banji alamun danshin ruwa a hannunki ba, ga d’aurin vail d’inki shima rad’au!! Powder ki kuwa kamar ma k’arawa kikayi.” ….Gaskiya In Sakina bata daina shiga huruminta ba wallahi zata illatata a wajen nan!! Wanne irin iskancine wannan??… Jalilan ta aiyyana hakan a ranta. Muryar Hudan taji tana cewa “Ya Jalila idan kin san baki yi alwala ba karki tab’a Qur’anin nan fa, Dan Allah.” Takaici kamar ta shak’eta haka Jalila taji, a ranta tace “Y’ar ‘Yaa Jalilan’ uwa!”. Muryar Arshaad taji yace “Ba kiyi alwalar ba?” Cikin rawar murya tace “Eeh bbb ban dd’akin babu ruwa” Da sauri Hudan tace “Zo muje d’akina, kiyi a chan” Sakina ta yunk’uro za tayi magana taji Arshaad yace “Muje in kunna miki famfon, yana da wuyar sha’ani dama.” Ya fad’i haka yana wucewa gaba. Jikinta har karkarwa yake yi haka ta wuce, ta bishi…. Suna shiga ya kunna mata shower ya kunna famfon sink, da wani famfo a gefe ya nuna mata yanda zata matsa abun tsarkin jikin toilet sannan ya fito ya bata waje ya bar ruwan yanata zuba bai kashe ko d’aya ba. Alwalar tayi ba yadda ta iya, ta kashe famfunan, ta tsaya tana kallon fuskarta a mudubi. Jin yayi knocking yasa gabanta mugun fad’uwa! Ita kam yau ta ga talatar kanta, gashi ba daman tace tana fashin sallah! Da kyar ta iya daurewa ta fice, k’irjinta na dukan uku uku. Suna k’arasowa, Sakina ta mik’a mata vail d’in da ta cire a jikinta d’azu ta ajjiye tace “Bismillah” Fisgewa tayi tana hararar ta. Murmushi Sakina tayi kafin tace “Yarinya yau ko idanunki zasu fad’o k’asa sai kin rantse!”…. ……A nan fa ake yinta, ga Jalila ga Al Qur’ani a gabanta ga jama’a kowa ya zuba mata ido… Parlourn yayi shiruuuu. Ba abunda yafi bawa Arshaad mamaki irin yanda Auwal ya d’auke wuta diff!!! Don gaba d’aya kamar babu shi a wajen.. Shi kam Auwal yana chaan ya sha’afa da kallon Sakina kamar ya samu tv, sam! Bai damu da kalar harar da take zabga masa a duk sanda suka hada ido ba! Babu abunda yafi tafiya da imaninshi kamar idanuwanta waenda idan ta kalleshi dasu yake ji gaba d’aya kamar an zare mishi lakka bayan fad’uwar gaban da yake tsintar kanshi a ciki..duk wata hayaniyar shi yau ya ji babu ita, yanaso yasa baki a lamarin su Jalilan amman ya kasa, don bashi da wani sauran energy, gaba d’aya jikin shi yayi lakwass!!!. Sakina kuwa so take ta gama da Jalila ta koma kanshi idan bai daina yi mata wannan kallon k’urillar ba!. Hudan tana lura dasu, dan haka ta gama aiyyanawa a ranta suna komawa d’aki zata zaiyyanewa Sakinan waye shi!! Kar ma ta soma bashi fuska dan ita tun zuwan su Munjibir park ta gama aminta da Auwal ba mutumin kirki bane ba!. ...duk sunyi shiruuu, kowa da abunda yake tunani a ranshi. Nishi suka fara ji sama sama, da sauri duk suka juya kanta.. Wani lumlumshe ido take yi tana layi, kafin ta tafi luuuu ta fad’i akan kafet d’in! Da mugun sauri Sakina ta d’auki robar ruwan dake gefenta ta nufeta, ta na zxuwa ta bud’e murfin ta kelaya mata ruwan mai mugun sanyi dan har da k’ank’ara k’ank’ara ma a ciki!! Ai kuwa a firgice Jalila ta bud’e idonta tana wani mugun tari dan ruwan har cikin hancinta ya shige sosai…. Da kyar ta samu ta seseta kanta ta fara k’ok’arin mik’ewa, tana mikewa kuwa ta d’aga hannunta zata zabgawa Sakina mari shi kuma Arshaad a take ya rik’e hannun da sauri. Wani kalan shock taji a jikinta da wani sanyi a zuciyarta wanda ya sanyata kasa yin motsi! A hankali ta lumshe idanunta tanajin yanda laushin hannun nashi yake ratsa jini tsoka da b’argonta. Muryarsa ce ta dawo da ita duniyar su, jin cikin fad’a fad’a yana cewa “Jalila kin fara isata wallahi ranki zai yi mugun b’aci! Inada abun yi amman kin tsaya sai b’ata mana lokaci kike yi!! Sannan meye na yunk’urin marin nata da kika yi? Ina taimakarki tayi? Kar ki kaini bango, ranki zai b’aci wallahi kinji dai na rantse!!.” Ya fad’i hakan cikin tsananin b’acin rai sannan yayi wurgi da hannun nata, ya wuce ya k’arasa ya durk’usa a wajen, ya fara kokarin dafawa…. Kuka kawai yaji Huda ta saka dan haka da sauri ya sago ya kalle ta. Cikin kukan tace “Ya Arshaad da Allah fa na had’a ka, nace maka komai ya wuce amman still kak’i ka yarda ka hak’ura, itama Ya Jalilan ku barta kawai, ni na fahimci gaskiya, dan Allah ku daina , Al Qur’ani fa ba abun wasa bane ba..” Tana gama fad’an haka ta juya ta haye sama da gudu,,tana kuka. Mik’ewa Arshaad yayi ya dafa kanshi, ya kusan one minute a haka kafin ya juya yana kallon Sakina yace “Kice mata nace idan cikin ya kai 5 ko 7 months in shaa Allah za aje ayi dna test, plss kar tace a’a,,for me.” Yana gama fad’in haka bai jira amsar Sakina ba ya juya ya fice. Haushin su ne ya hana Sakina ci gaba da zama a inuwa d’aya dasu, dan haka ta juya ta haye sama itama. Da k’arfi Jalila ta sauk’e ajjiyar zuciya, bata gama dawowa dede ba taji Auwal ya fincikota da mugun k’arfi, cikin b’acin rai yace “Wanne shirme da iskancine ya sa kika biyo shi in the first place??? Mahaukaciya mara kamun kai kawai!! Daga ji ance tazo a tafi ta shige mota ta biyo mutum zungui zungui. Wallahi yau da wani abun ya fito, toda da hannun nan nawa zan illataki, mahaukaciya kawai.” Ya k’arashe maganar yana sakin ta sannan ya juya yayi hanyar waje. Da sauri ta mik’e ta bishi….. Ba k’aramin artabu suka sha ba a wajen ma, daga k’arshe dai ya hak’ura ya mik’ata gida, yanata faman zazzaga mata ruwan bala’i! Daga nan yace “yayi grounding d’inta! Ko wajen umma kar ta yi gangancin tambayarshi Daga yau babu inda zata sake fita har sai yayi sorting out ma kanshi solution!” sannan yace “ko hanya tabi in dai ta hango Arshaad to ta chanja! Don ya lura sam Arshaad d’in bai hak’ura ba, ita kuma wawuya ce, so kasancewar su tare is very dangerous for him.” Ita dai Jalila da “to” kawai ta bishi amman a yanda take jin Arshaad a ranta ai ko labari taji ance zai bi ta waje to fa ita mai iya zuwa ta tsayane ta jira wucewarshi. A gate d’in estate d’in ya tsaya yace “ta fita!” Allah ya so ta mai gadin yaga motarshi kuma ya ganeta dan haka aka barta ta shige. Ko da Aslam yazo, Hudan Sakina ta bawa ta kai masa ruwan karatun… Dinner kam dama a k’oshe suke, gaba d’aya kunyar Arshaad take ji bataso su had’u, iyakar yadda Ya Jalila tayi ta acting ya ishi yasa ta gane gaskiya….ita sai yanzu ma take ganin shiriritarta da ta yarda da su! A gefe guda kuma na zuciyar ta tausayin Jalilan take ji. Yayinda gaba d’aya hankalinta kuma yau ya d’unguma ga son ganin Mama dan har yau Ummu tak’i d’aukar wayarta, wayar Sakina ma ta daina amsawa! Tanaso ta tambaya amman kuma bata son zuwa k’asan dan haka ta yiwa Abban message. Ba a fi mintuna uku ba, taga reply dinshi kamar haka “Ok, no problem, but let it be tomorrow.” Taso zuwa yau d’in, amman ta tura “Thanks Abba ❤️” Kawai, ta mik’e tayi sallah.. Yau basu wani zauna hira sosai ba,,ta dai fad’awa Sakina halin Auwal tace “Don taga yanata kallonta kar yazo mata da shirme” Dariyan takaici Sakinan tayi kafin tace , “First, kin dai san akwai wanda naki dating, right? Second, ga abunda ya yiwa Jalila sannan ya k’ulla makirci wai Ya Arshaad ne. And third, wallahi ni bana son irin waennann mazan kwata kwata yana yinsa bai yi min ba at first sight!”. Ajiyar zuciya Hudan tayi kafin tace “Duk cikin su Ya Arshaad shi ya fita daban i don’t know why.” Murmushi Sakina tayi kafin tace “d’an halak, gashi yana kiranki.” Tayi maganan tana mik’a mata wayar ta dake a hannunta. Karb’a tayi ta amsa bayan sun gaisa ta fara son sake bashi hak’uri amman sam yak’i yarda, a cewarshi bata laifi a gurinshi…….. Tun Sakina najin hiran su sama sama har bacci ya kwasheta bata san lokacin da suka gamaba. Ranar ansha soyayya abun ba a magana dan sai wajen 2 tukunna suka yi hanging up, suka kwanta. Bata samu magana da Sakina ba, kamar yadda ta yanke zata nemi shawarar ta jiya, sai da suka sauk’o yin breakfast… Suna zuwa suka tarar ba kowa dan haka suna zama Huda tace “Daman akwai maganan da nake ta so muyi in mun gama shiryawa” “Ok, akan me?” Sakina ta fad’a tana mai d’an juyowa ta bata dukkannin attention d’inta.” A hankali Hudan tace “Ya arshaad ne, daman already ya yiwa su Abba maganan! So yanzu jiya yace, wai ya nake gani,,jiya sun yi magana da Dad wai sun tsaida in anzo saka rannan za asa two months ne ba wani lokaci za a dauka mai tsawo ba!” “Woow” Sakina tace tana d’an zaro idanuwanta, kafin tace “Amma hakan bai yi wuri ba kuwa?” Da sauri Huda tace “nima dai abunda na gani kenan! Amman dana nuna mishi tun kafin ma In furta sai naga kamar bai ji dad’i ba. Wai shima yana so ya tafi wani course, so kafin a juya sabon session yake son samamun admission sai muje chan ni Ina degree shi kuma yana course din, nashi.” Dai dai nan suka ji sauk’owar Abba, dan haka a hankali Sakina wadda duk jikinta yayi sanyi jin za a rabata da best frnd d’inta tace “Anjima ma ji me su Mama za suce, in munje.” Cikin girmamawa suka gaisheshi ya amsa da kulawa yana ce musu “ai da sun fara kawai” Sai da suka kammala ya kalli Hudan yace “ki cewa Arshaad idan ya dawo a office ya zo, ku zo tare Ina son ganin ku!” Da “to” ta amsa, shi kuma ya tambaya ko “akwai abinda suke buk’ata zai fita shima” a hankali tace “a’a” sukai yi mishi a dawo lafiya, ya wuce. Gidan shiru, daga su sai masu aiki… Tun lokacin da Abba ya fita take nazari a kanshi, kamar akwai abunda yake damunshi, dan har sai da ta yiwa Sakina maganar… Murmushi Sakina tayi kafin tace “Hudan he just knew you fa, kuma yanzu ana shirin aurar da ke, dole yaji ba dad’i mana.” Jikinta itama duk sai yayi sanyi, ba abunda yafi d’aga mata hankali, irin barin k’asar da Ya Arshaad yace za suyi, ta san aure dolene dama wata rana za tayi shi, but bata tab’a kawowa nan kusa ba, kuma ba a k’asar ta ba. Haka dai ta wuni ranar sukuku kana ganinta tashi d’aya zaka fahimci akwai abinda yake damunta! Ko da Sudais ya shigo musu shi da Sakina suka yi ta shirmen su tana jin su k’arshema kwanciya tayi ta lumshe idanunta kamar mai bacci Sakina kanta k’arfin hali kawai take yi tana daurewa, dan bataso itama ta zama moody kamar Hudan ta sake d’aga mata hankali. Kafin Magriba Arshaad d’in yace mata zai dawo, so tana gani 6 yayi ta mik’e ta isa parlourn Abba. Knocking tayi aka bata izinin shiga, a hankali da sallama ta tura k’ofar ta shige ciki. Aiki ta sameshi yanayi tuk’uru ga takardu da computer a gabanshi takardun duk a zuzzube. Suna had’a ido yayi murmushi ya ture kayan aikin gefe ya bata dukkannin attention d’inshi bayan ya nuna mata gefen shi inda yake zaune a 2 sitter yace “ta zauna.” Bayan sun gaisa ba tare da b’ata lokaci ba yace mata “Dad d’in Arshaad jiya ya kirashi akan maganarsu ..... Yayi mata bayani dai dalla dalla kamar yadda Arshaad yayi mata jiya” Kafin ya k’ara da cewa “Kina son shi! In ba kya sonshi ki fad’amin, ba zan bari ki auri wanda ba kya so ba!” Just say watever it is that you feel towards him ko friendship ko love ko ma meye just feel free to tell me” Ya k’arashe maganan yana kallonta da dukkan hankalinshi. Shiruuu, tayi tana d’an jin kunyar cewa Abban tana son shi k’iri k’iri, dan haka tace “Abba mun ma shirya mun daina fad’an, duk abunda kuka yanke dai dai ne.” Ya fahimceta sarai amman yace “Kina sonshi kenan? Za ki aureshi?” A hankali ta d’aga kanta, sannan tayi saurin rufe idonta da tafun hannunta. Murmushi yayi, bai ce komai ba, daga nan d’akin ya d’au shiru. A hankali Hudan ta aro jarumta kafin tace “Daman Abba akwai wata magana danake ta so in rok’e ka” Kallonta yayi kafin yace “Un hm, Ina jinki” A hankali tace “akan su Ummi ne Abba dan Allah ka..” Tun kafin ta k’arasa yace “Maganan ya fita a hannuna tun tuni, so karki sake min maganan bana son ji.” Ganin da tayi kamar ranshi ya b’aci ne yasa tace “Sorry Abba” A hankali ya sauk’e ajjiyar a zuciya kana yace “It’s okay” Dai dai nan suka ji ana knocking! Izinin shigowa ya bada, hakan ya sa ya turo k’ofar a hankali ya shigo… K’amshin turarenshi ne yasa ta ganeshi! Me kuma ya zo yi? Ta yiwa kanta tambayar a cikin ranta. Bata gama wannan tunanin ba, ta ji muryar Arshaad yana sallama alamun tare suka shigo. Rashin nutsuwar da takan tsinci kanta a ciki ne ya ziyarceta a take, lokaci guda!. Akan kujerun suka nemi wajaje suka zazzauna. Sai da suka gama gaisawa da Abban tukun ta juya ta gaidasu A hankali Aslam yace “Lafiya Alhamdulillah” Arshaad kuma yana d’an murmushi ya d’aga mata gira d’aya yace “fine” a hankali. Murmushi tayi itama ta maida kanta k’asa. A hankali Aslam ya lumshe idanuwanshi kafin ya bud’e yace “Abba, Arshaad yace wai akwai meeting inzo kana son ganinmu” Murmushi Abba wanda ya fahimci Arshaad d’in yayi kafin yace “Ni shi kad’ai na kira, sai dai kuma na lura har kunyar surukai ta fara shiga tsakaninmu tunda gashi sai da ya nemo d’an rakiya.” Murmushi Arshaad d’in yayi ya sunkuyar da kanshi k’asa yana danna wayarshi dan gaskiya Abban ya fad’a sam bai san daliliba amman wata kunyarshi yake ji kwana biyun nan. D’an murmushi kad’an Aslam d’in yayi yana mai sauk’e ajiyar zuciya. A hankali Abba ya sauk’e ajiyar zuciya shima kafin yace “Mun gama magana da Huda saura kai” Har zai fara magana sai kuma ya juyo yace “Daughter akwai wani abun da kike son sanar dani ko shikenan?” A hankali tace “ba komai Abba duk na fad’a kawai dai maganar zuwa wajen Mama ne, k’arfe nawa?” Murmushi yayi yace “bayan isha zan kaiki ku shirya ko?” Da “to” ta amsa tana murmushi kafin ya sallameta tayi musu sallama, ta wuce. D’an gyaran murya Abba yayi kafin yace “Arshaad!” Jin yanda Abban ya kirasa yasa Arshaad d’in d’agowa yana kallonshi with full attention. “No need na In tsaya tamabayar ka ko kana son Hudan tunda gashi duk ka fad’a mana ko? But inaso In sake tabbatarwa tunda kaga shi aure ba abun wasa bane, sannan kuma inaso ka tsayar da kanka da hankalinka waje guda kafin a gama magana, dan naji Dad yana cewa 2 months kawai za a saka bikin saboda tafiyarka! So kaga kar aje abu ya taho kuma kuzo ku fara inda inda, bayan ba wannan lokacin.” D’an tari kad’an Aslam yayi, kafin ya mik’e tsaye yace “Abba Ina zuwa, i’m thirsty” Bai jira jin me zasu ce ba ya fice daga parlourn ya sauk’a chaan k’asa. Yana fita Abba ya ci gaba da cewa “Sannan magana ta biyu! Why do you hide Hudan away from me?? Meye shirinka? Bana so ka b’oye min komai” A hankali Arshaad ya lumshe shanyayyun Idanunshi, kafin ya bud’e su ya d’aura akan Abban sannan ya fara magana “Abba ba 2 months ba, ko nan da 2 days ne aka yanke ranar aurenmu, I’m ready in auri Hudan dan ita nake so, so na tsakani da Allah, Ita nake son aura in rayu da ita har abada, na yanke wa kaina wannan decision d’in 3 years ago and I don’t think akwai rana d’aya dana tab’a jin tunanin sauya decision d’ina. Magana ta biyu kuma Tabbas na fahimci wacece Huda, tun ranar da muka had’u da Mama a graduation d’inta saboda naga pictures d’inta (Mama) da yawa a locker d’inka da sunan ta and everything a time d’in da kace in tayaka, parking. But I’m really sorry Abba i was selfish back then, shiyasa na k’i fad’awa kowa har ita (Hudan) dan na san no mattarr how much I love her itama take sona muddin iyayenta (b’angaren uwa) suka fahimci waye ni to ba zasu tab’a yarda da auren mu ba duba da issues d’in da suke tsakanin families d’in kuma kaima it can cause problems for you daga Granpa dan na lura maganar kad’ai idan akayi ran kowa sai ya b’aci a estate d’in. Shiyasa na rok’i Baban Sakina akan ya b’oye identity d’ina har iya lokacin da za a d’aura mana aure, daga nan zan san yanda zan yi In shirya ku kaida su Madu, tunda kuma ga auratayya a tsakani, dole a na san za a hak’ura a sauk’o a yafewa juna… Na san nan ne side d’in Mahaifinta mun fisu k’arfin da iko da ita amma da nayi lissafi tabbas naga akwai possibility d’in suci galaba a kanmu, ni kuma issue ko case ne kwata kwata bana so har in samu cikar buri na shiyasa nayi k’ok’ari wajen ganin na danne duk wani abu da ka iya zama mini matsala wajen ganin na mallaki Huda a matsayin matata. I know I was wrong! Ban san taya zan fara baka hak’uri ba, but I did everything out of love! Dan to be honest a yanda nake jin k’aunar Huda a raina Abba wallahi I don’t think I can go on living idan aka yi tunanin raba ni da ita! Please try to understand and forgive me.” Ya k’arashe maganar cikin tsananin kalar tausayi kamar wanda zai fashe da kuka. Shiruuu, Abba yayi yana nazari kafin yace “Arshaad na san menene so, tbh a lokacin da nake tare da Maryam, ake k’ok’arin rabamu! Hakan nima nayi na zama selfish har naga mun mallaki juna… Amman abunda kai kayi is morethan selfish, Arshaad banji dad’i ba, ka k’i ka baiyanar mini da y’a ta.” Shiruu, Abba ya d’anyi kafin ya sauk’e ajiyar zuciya yaci gaba da magana “But, zan iya yafemaka! Zan yi k’ok’ari In manta da abunda kayi after all everyone deserves a second chance sannan naji reason d’inka and its not all bad. But Arshaad don’t ever try something like this again saboda i as selfish back then just like you and abun bai yi ending well ba! Although I was happy for good 10 years, but har yau Maryam is not in good shape with her parents because of my decision.” A hankali Abba ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace “And another thing thankyou so much! Hudan ta fad’amin yadda ka dinga d’awainiya da su har makaranta, Allah ya saka maka da alkhairi.” A hankali Arshaad yayi murmushi kafin yace “Ba komai Abba, thankyou” Murmushi Abban yayi kafin yace “A matsayina na Mahaifin Hudan! Na baka ita Halak Malak! Allah ya nunamin ranar da zan aura maka ita. Dan Allah Arshaad ka kula min da ita.” Ya k’arashe maganar, cikin nauyi da karyewar zuciya. Zamowa Arshaad yayi daga kan kujerar da yake kai kawai ya hau godiya, yana yi masa alk’awarin in shaa Allah zai bata dukkanin kulawar data kamata….. Sai godiya yake yi, har sai da Abban ya sallameshi tukun ya mik’e ya fita still yana godiya. Murmushi Abba yayi bayan fitar Arshaad d’in, ba abunda ya zo kanshi sai lokacin dasu Kaka suka bashi Maryam! Yanda Arshaad yayi exactly shima hakan yayi….. A hankali yayi murmushin da har sai da y’ar kwalla ta zubo daga idanunshi! Yana tuno ta (Maryam) da moments d’insu…. Chaan, ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya, a hankali yasa hannu ya sharce kwallar shi, sannan yace “Astaghfirullah”. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 45 Kiran sallah aka fara, dan haka ya mik’e ya wuce toilet ya d’auro alwalla ya sauk’a don zuwa masallaci. Arshaad yana zuwa k’asan, ya tarar da Aslam a tsaye jikin dispenser yana shan ruwa.. wanda jin sauk’k’owar tasa ne yasanya shi ya juyo. Fara’ar da ya ga yana yi ne ya sanya Aslam d’in fahimtar wani abu dan haka yad’an matsoshi yana shirin yin magana yaga yayi hugging d’inshi yana wani murmushin da yake baiyyana tsantsar farin cikin da yake a ciki! Cikin farinciki ya cika shi still yana murmushi ya d’ago ya kalleshi sannan yace “Call me Ango! An bani mata”. Ya fad’i hakan yana dariya. Ajiyar zuciya Aslam ya sauk’e, sannan yace “Congrats bro, i’m very happy for you.” Cikin zolaya Arshaad yace “na yi maka wayo! Kai ma kayi sauri ka nemo..” Murmushi Aslam d’in yayi kafin yace “ka yi mini wayo kam!” Shigowar da Auwal yayi cikin parlourn ne ya katse su. Bai kalli kowa ba ya wuce yaje ya zauna akan d’aya daga cikin kujeraun parlourn… Aslam ne yace masa “Auwal ya gida” D’an d’agowa Auwal d’in yayi ya kalleshi, har zai ce wani abu kuma sai ya d’auke kai kawai yace “Fine” yana mai kallon hanyar staircase…. Bayan kamar 2 minutes Abba ya sauk’o. Cikin girmamawa ya gaida Abban har da d’an rissinawa! Da d’an mamaki Abba ya kalleshi ya amsa sannan ya wuce, su Aslam suma suka nufi hanyar wajen ganin zasu fita yasa shima ya mik’e suka nufi mosque gaba d’ayansu....... A dining d’in suka tarar da Hudan, Sakina Sudais da Shuraim don haka suka yi joinin d’insu su uku, banda Aslam wanda ya wuce gida daga mosque d’in don kanshi yana d’an ciwo! Shiyasa kawai ya wuce bayan ya cewa Arshaad “ya karb’a tofin ya taho dashi in sun gama”. Babu kunya haka nan Auwal ya samu guri ya zauna dai dai gefen Sakina! Da mugun sauri tayi zumbur! Zata mik’e Hudan tayi saurin rik’ota tana nuna mata Abba da ido. Suna shirin farawa Daddy ya shigo, yana ganinsu gaba d’aya ya cewa Abba “Wato ka had’a kan y’ay’anka ni kuma ka manta da ni, ko?” Dukkansu dariya suka yi kafin su shiga gaidashi one by one.. Cikin kulawa ya amsa musu yana mai cewa “Na gaji da cin abinci ni kad’ai daga yanzu kawai a dunga yin dinner a chan side d’ina, breakfast da lunch ku dinga yin abunku a nan, in ba haka ba shirun ai sai yayi min yawa, daga ni fa sai Auwal shima kuma in yaga dama ma sai ya kwana biyu bai yi dinner d’inba, yau kuma kalleshi ja’iri ya gudo ya barni!”. Duk dariya aka sa sannan suka fara cin abincin cikin nishad’i….. A zaman su Auwal ya cewa Sakina ‘Hi’ Yafi sau ashirin amman har aka tashi bata amsashi ko d’aya ba! Ko arzik’in kallo ma bai samu daga gareta ba k’arshema juyar da kujerar tata ta yi kad’an ta karkatar da hankalinta a Huda gaba d’aya! Wanda hakan ya sanya duk jikinshi yin sanyi dan tunda yake a rayuwarshi tun yana secondary school mace bata tab’a yi mishi haka ba, wasu ma sune suke cewa suna sanshi, dan ko a yanzu haka kafin yace yana so sau d’aya sai ance ana sonshi sau goma!!. Daddy ne ya fara mik’ewa sai Abba…. Auwal yana shirin yi mata (Sakina) magana tayi sauri ta mik’e ta haye sama Hudan kuma ita da Arshaad suka koma cikin parlourn suka zauna, su Sudais ma suka yi mishi sai da safe suka tafi. Kasa mik’ewa Auwal yayi a wajen, dan haka har Abba ya dawo ya taddashi yana nan bai tafi ba!. Hudan daman a shirye take dan haka ta kira Sakina a waya tace “tazo su je” Arshaad yaso yace zai je amman kunyar Abba sai ta hanashi yin maganar, dan haka ya yi musu sai da safe ya tafi bayan ya karb’i ruwan Addu’an Mommy. Auwal ma ganin yanata zama shi d’aya yasa ya yiwa Abban sai da safe ya tafi, bayan yaga sauk’owar Sakina. A tare suka fito shi( Auwal ) yayi part d’insu su kuma suka wuce mota Sakina na baya Hudan na gaba a haka har suka isa bakin k’ofar gidan Baba. Ba Hudan ba hatta Sakina zumud’i take yi.. Cikin rawar k’afa suka fita a tare suka shige gidan. Basu tarar da mashin d’in Baba a soro ba, da alamun bai kai ga dawowa ba. Gidan shiruuuu, sai d’an hasken fitulu da suke hangowa ta d’akin Umma da Mama. A hankali Huda tasa hannu ta d’an tura k’ofar kafin su shiga a tare da sallama… Kendir d’in dake kan dressing mirrow ne ya taimaka wajen haskaka d’akin! Tana zaune a k’asa gaban gado kan sallayarta, da charbi a hannunta, da alama bata tashi daga wuridin bayan Isha ba dan ga hijabinta ma a jikinta, a gefe guda kuma ta kunna maganin sauro yana d’an tashi da kad’an da kad’an. D’ago fuskarta tayi ta kallesu, kafin ta maida idonta k’asa kamar bata ga kowa ba!. Gaba d’aya jikinsu sai yayi sanyi, amman suka aro jarumta suka k’arasa inda take! Sakina ce tayi k’arfin halin hugging d’inta kafin tace “Mama Ina wuni ya jiki?” “Alhamdulillah” kawai tace Maman tace mata. Itama Hudan ta gaisheta ta bita da “Alhamdulillah” Sannan ta mik’e ta cire hijabin jikinta ta ninke da sallayar, ta mik’e ta haye gado ta kwanta abunta. Duk kasa cewa komai suka yi, d’akin ya d’auki shiruuuu. Wajen minti goma ta tashi taje ta kashe kendir d’in ta dawo ta tofa addua ta kwanta, harda d’an jan abun rufuwa. Sheshshek’ar kukan Huda ne ya sa Sakina kunna flash d’in wayarta! Itama Mama jin kuka yasa ta mik’e ta zauna daga kan gadon tana kallonsu a inda suke. A hankali Sakina ta cewa Mama “Mama dan Allah ki yi hak’uri mana.” Cikin katseta Maman tace “Hak’urin me?” Dibi dibi Sakina ta hau yi kafin ta samu damar cewa “Naga kamar kina fushi da mu ne” Murmushi Maman tayi kafin tace “ba fushi nake yi ba Sakina, ko kad’an bana fushi daku Kawai kun zab’i abunda kuka ga ya dace ne Nima kuma na zab’i wanda naga ya dace!” Ajiyar zuciya ta (Mama) sauk’e kafin ta juya kan Huda tace “Na san abunda kika yi ranar da kika zo duba ni a asibiti! Dukda Ummu taso b’oyewa amman naji kuma na fahimta! Na gode Hudan, Mahaifin ki ya fini ko? Ba komai.. Amman abunda nake so ki fahimta shine Tunda shi kika zab’a, to ki zauna a iya shi kad’ai kar in sake ganin k’afar ki a inda nake! In ba hakaba wallahi sai ranki ya b’aci! Na bar masa ke! Tunda naga a ganin ki yanzu ban dace ki zauna da ni ba, kin girma ko? Kin mallaki hankalin kanki, so bani da wani amfani a wajen ki, tunda ba abunda zan iya miki ko zan iya baki..” Wani irin kuka Hudan ta rushe da shi, tana shirin yin magana Mama ta katseta ta hanyar cewa “Haka ne mana, kar ki min kuka gaskiya na fad’a! Kinyi girma ai yanzu tunda har kika iya yankewa kanki decision..” Sakina ce tace “Mama dan girman Allah kiyi hak’uri, wallahi kin yi misunderstanding d’in mu ne Please Mama ki tsaya ki fahimcemu” “Hmmmm” Maman tace, kafin tace “Nima kun kasa fahimta ta Sakina ba wai haushi naji ba fa, kawai ina baku space d’in da kuke buk’ata ne, tunda gashi ta nuna min k’iri k’iri abubda ranta yake so ai kinga sai in barta in daina kutsa kaina cikin rayuwarta ko?? Ku tashi kuje dare yayi, na san yau ma yana waje yana jiranki! And maganar zuwa kotu itama na daina yi! Tunda gashi k’iri k’iri kin riga kin zab’i abunda kikeso, so ba amfanin zuwa kotun tunda babu amfanin inje inata yak’i ni kad’ai. Sai kuje ku yi ta rayuwarku mai dad’i cikin daula ke da Mahaifinki.” Tana gama fad’in haka ta koma ta kwanta abunta. Kusan 20 minutes suna bata hak’uri, amman tak’i kulasu Sai da suka kaita bango ta tashi ta balbalesu da fad’a tace “wallahi In basu fita ba zata dake su! Su bar ganin wai sun girma.” Mik’ewa Hudan tayi kamar zata fita, sai kuma ta koma da gudu ta je ta kanainaye Maman tace “Ni ba inda zan je, dan Allah ki daina fushi dani haka, ba zan sake komawa ba, anan zan zauna.” Kasa cewa komai Mama tayi.. Suna a haka wayar Hudan ta fara ringing, har ta tsinke ba wanda yayi yunk’urin d’aukar wayar… Sai da aka sake kira, tukunna Sakina tayi k’arfin halin d’auka ta d’an fita waje, ta fad’awa Abban halin da ake ciki “Sai da safe” kawai yace mata, daga nan ya kashe wayar! A chan d’aki kuwa, da kyar Mama ta d’an kulasu.. Sai da Hudan tayi mata alk’awarin ta bar zuwa gidan Abba har abada sannan ta d’an sauk’o…. Daga Hudan har Sakina, gabansu fad’uwa yake yi dan basu san ta inda zasu fara yi mata bayanin baikon Hudan da sa ranar da aka yi ba! Chaan dare! Kowa ya kasa bacci sai juyi suke yi, Mama ta hango kendir d’in d’akin Umma a kunne, ita tama yi tunanin ko tana d’akin Baba ne tunda ita ke da girki, gudun kar ya k’are ya kama wani abun yasa ta cewa Sakina “taje ta kashe mata kendir d’in, in k’ofar a bud’e take.” Tun daga bakin k’ofar d’akin Sakina fara jiyo gwarti! Tsaki tayi ta d’anyi sallama kusan sau uku, jin shiru yasa ta d’an tura k’ofar ta shiga… Kendir d’in saura kad’an ya k’are, dan ba don ta je ba ma to da babu abunda zai hanashi kama kan mudubin katakon d’akin, dan Umman bata d’aurashi akan komai ba kamar yadda taga Mama tayi ba. Kallonta tayi dariya taso kufce mata, da sauri ta hure kendir d’in ta fito ta maida k’ofar ta rufe ta wuce a ranta tana mamakin rashin hankali jahilci da rashin sanin ciwon kai irin na Umma! Ace y’arki tana nan da ciki a chan wani gidan da baki san ko su waye ba! Amman kalli yanda ta barrarraje tana shek’a uban bacci kamar wata jaka! Da wannan tunanin Sakina ta k’arasa d’aki ta tarar bacci yayi nasarar d’auke Hudan, daman ita bata da wuyar bacci. Itama Sakinan bata wani dad’e ba baccin ya d’auketa cike da tunanin rashin man kai irin na Umma…inda ace su Ummu ne akace d’aya a cikin ita ko Huda bata gida ta tabbatar ko gigin yin bacci ba zasu yi ba!….. Abunda Sakina bata sani ba shine Umma magani mai k’arfin tsiya ta sha, dan yau kusan kwananta uku bata iya bacci tun lokacin da Jalila ta gaya mata Huda cousin d’in Arshaad ce! Ga kuma Mahaifinta yana son ta harma sun bar gidan kakan da shi da yayanshi duk akan Huda! Yau kuwa da Jalila ta kirata take shaida mata irin daular da Hudan take ciki sai da ta kusa hauka! K’arshema dishi dishi ta fara gani! Ga zuciyarta tana ta bugawa da mugun k’arfi ga zazzab’i. Don haka ta lallab’a taje wani Chemist a chan bakin titi babba da aka bud’e sabo! Matar(mai chemist d’in yare mai mutunci) Anan ne bayan an gwadata matar ta tabbatar mata da jininta ne yayi mugun hawa…dan haka ta samu ta sha magani ta rage damuwa tayi bacci.. Tun achan chemist d’in ta nemi matar ta bata maganin da zai sakata baccin dan itama tana buk’ata, saboda ta san in ta samu baccin at least zata huta da tashin hankalin da take ciki na y’an awanni, kafin kuma ta farka. Mai chemist d’in taso ta hanata, but ganin halin da take ciki yasa kawai ta siyar mata saboda tayi mugun tausaya mata dan a yanda jininta ya hau ita kam tama yi mamaki da ta ganta tsaye akan k’afafunta. Hakanan ta bata ta sallameta sai faman sannu take jera mata zuciyarta cike da tausayinta, har ta tafi a ranta tace “Maybe halin mazan zamanin nan ne yake neman hallakata, Allah sarki mata! Allah ya baku ladan hak’uri da maza........” Washegari da safe Umma bata samu tashi da wuri ba, har sai da Baba ya lek’a d’akinta ya tasheta tukunna saboda shima yaji shirun nata yayi yawa dan jiya yayi ta jiran ta amma yaga shiru bai ganta ba, yauma kuma gashi har ya shirya amma babu abun kari ba k’amshin shi babu alamun shi! Ba yadda bata yi da shi ba akan ya tsaya ta d’an dafa mishi abu mai sauk’i amman ya k’i yarda a cewarshi ya makara! Don haka tayi mishi a dawo lafiya ya amsa ya juya ya fita. A bakin rijiya ya hango Huda tana jan ruwa zata yi wanka saboda jiya cikin dare period d’inta yazo, gaba d’aya ya b’ata mata jikinta… Suna had’a ido dashi gabanta ya fad’i! Dan wani irin kallon mamaki taga yana yi mata. A hankali ta sunkuyar da kanta kafin tace “Baba ina kwana” Bai amsa mata ba, yace “Me kike yi a nan?” Tambayar tayi matuk’ar bata mamaki, dan duk tsawon zamanta da shi bai tab’a yi mata haka ba! Sai dai ya nuna tsana da kyamar ta k’iri k’iri, ko lokacin da take boarding ma sai dai ya cewa Mama ta hanata zuwa nasa gida in an yi hutu, ita kuma Maman ta gaya musu… Tambayar ya sake maimaitawa a d’an hassale!Don ya k’agu yaji dalilin zuwan nata sannan kuma yaji waye ya kawota. Cikin d’an rawar jiki da murya tace “Jiya da daddare nazo, ni da Sakina” “Da wa kuma? Waye ya kawoku?” Yai mata tambayar ba alamun rahama a fuskarshi. A hankali tace “Abba” “Ma shaa Allah” Baba yace Har yayi hanyar d’akin Mama a zuciye sai kuma taga ya juya ya fice fuuuu, ko mashin d’insa bai tsaya d’auka ba. Har tayi wankan ta fito duk ranta ba dad’i, dan a yanda taga Baba yau ta san ba za a kwasheta lafiya da shi ba! Su mama da Sakina sarai sun ji duk abunda ya faru, dan haka da ta shigo suka tambayeta “Ina yayi?” tace musu “Waje, ba mashin” kawai, ta fara shiri. Mik’ewa sakina itama tayi ta je tayi wanka.. Basu samu breakfast daga Sadiya ba, itama k’osai ta siya ta ci, tunda mijinta ya riga ya fita. Wankan itama Mama tayo ta d’an shirya, sannan ta basu kud’i dan suje su siyo musu abunda za suyi kari da shi Y’ar tsala suka siyo ta d’ari biyu, suka tafasa ruwan Lipton suka soma karyawa….. Hudan tana jan Mama tana ta shige mata a hankali a hankali dai tana d’an kulata. Suna cikin karyawa wayar Mama ta hau ringing Ganin number Kaka, yasa ta d’auka da sauri! ko gaisawa bai bari sun yi ba yace “ki zo yanzu nan ke da su Sakina! Muna gidan Abban ku.” Gabanta ne ya fad’i ras! Tana shirin yin magana ya kashe wayar… Mik’ewa tayi ta d’au hijabinta sannan ta rarumi purse d’inta kafin tace “Ku taso muje, Kaka yana kira.” Hijabansu suma suka sanya, suka fito, gaba d’ayansu. A tsakar gidan suka tarar da Umma tana bawa Ya Ja’afar koka a baki! Ya dalalar da wani ya zxubar da wani…. Da tsoro Hudan ta kallesu, sai kuma ta k’arasa! Sai da ta d’an rissina tukun ta gaida Umma. Da kyar Umman ta iya amsawa Ya jafar d’in kuwa da ta gaidashi, kallonta kawai yake tayi bakinshi na zubar da yawu da d’an ragowa ragowar kunun, ya kasa cewa komai. Daga d’an nesa Sakina tace “ina kwana” bata jira jin amsawar su ba ta wuce tayi waje abunta. Itama Mama d’an matsawa kad’an tayi suka gaisa sama sama kafin tace “Ya jikin nashi?” “Da sauk’i” Umma tace, tana wani b’ata rai irin ita an dameta d’innan… Ajiyar zuciya Maman ta sauk’e kafin tace “Bara muje Kaka yana kiranmu.” Wannan karon banza Umman tayi da it. Guiwa a sace suka fice daga gidan ita da Huda Umma tana jin kamar ta bisu ta shak’e su! K’arshe dai haushin akan Ya Ja’afar aka sauk’e, dan kokon da bai sha ba kenan tace wai “yana ta b’ata mata lokaci”. Jikinshi ta bashi tsumma ya goge, da kyar! Daganan ta mik’e ta fice ko wanka bata yi ba. Su Mama kuma bayan sun fita ne, Hudan take tambayar “mai ya samu Ya Ja’afar?” Sakina ce ta iya amsa mata da “Fad’a suka yi! Nasu na y’an shaye shaye Wani ya d’au makeken dutse ya buga mishi a kai. A haka ma ya d’anji sauk’i….” A babban parlourn Madu suka same su dukkansu, Shuwa Baaba Talatu Madu da Kaka! Kana ganin fuskokinsu ka san ba lafiya ba! Dan haka su Mama suka sha jinin jikinsu suka gaidasu suka nema waje suka zazzauna. Baaba Talatu ce tace “Maryam yaushe Yaran nan suka zo?” A hankali Mama tace “Jiya da daddare” Jingina kai tayi tukunna tace , “Shi Abban ne yace su kwana?” A hankali ta girgiza kai. D’an shiruu ne ya biyo baya kafin Kaka yace “Maryam mun yi miki magana akan ‘ki d’in jira tukunna’ amma ko? Mai yasa kike da taurin kai ne? Kinsan me taurin kan naki ya haifar yanzu?” Bai jira amsar taba ya d’aura da cewa “Kinga na farko yanzu haka Usman yana hannun hukuma! Yanzun nan aka kamashi bayan ya wanke k’afa yaje ya kwashi y’an sanda ya kaisu wai su d’aure Abba saboda yana bin matar aure!! Ban san dai ya aka yi ba amman reshe ya juye da mujiya, yanzu haka yana d’aure a station! Sannan kema Abban yace ya baki minti 40 ki maida masa Yarinyar shi da hannun ki, in ba hakaba kuma to duk abunda ya biyo baya ke kika ja! Kuma yace gaishe kin ma ta daina zuwa yi daga yau!. Cikin kuka Mama tace “Kaka dan Allah kar ku ce in yi abunda yake so.. Wannan wanne irin son kai ne Abba yake gwadawa? Na ji na yarda da maganar ku da kuka ce bai san da itaba tun farko na yafe mishi wannan amman dan Allah kar ku bari ya raba mu! Kawai ni ya fita a harkar mu gaba d’aya, bama buk’atar shi.” Murmushi Madu yayi kafin yace “Hudan kema ba kya buk’atar Mahaifinki??” Sai da ya sake maimaita tambayar tukunna ta d’aga kanta alamar ‘eh’ sannan tace “Zan zauna a wajen Mama” A hankali, Madu yazo ya zauna a gefen su da kyau kafin ya fara magana “Shikenan zamu gwada mu gani, amman idan mun yi nasara kin dawo wajen Maman naki to inaso kisan cewa Ba a inda take zaki zauna ba sai dai ki zauna a gidana! Saboda Usman ba zai tab’a bari ki ci gaba da zama nasa a gida ba sannan na san ba zai dinga barin itama Maman naki tana zuwa inda kike ba kwata kwata kinga kenan baki zauna da Abba ba kuma baki zauna da Mama ba!” Cikin kuka Mama tace “Abba dan Allah ka dai na, za ka karya mata guiwa” Murmushi ya sake yi kafin yace “Maryam hakan shine gaskiya! Kuyi hak’uri, for the first time nayi miki alk’awari ban cika ba! In dai zan fad’a miki ki ji, tou inaso dan Allah ki bar Yarinyar nan ta koma wajen Mahaifinta kamar yadda ya buk’ata, ko munje kotu ya fimu gaskiya, kuma rashin hankalin da Usman ya sake yi yau d’innan ma wata shaida da point ne Abba ya sake samu. Ki barta ta tafi, za ku dinga waya sannan yace anytime kike son ganinta kije ki ganta, idan ma bakya son zuwa gidan nasa to zai saka ko driver ne ya kaita ko wani park ko restaurant, ku had’u achan amman yace ba zai sake barinta tazo inda kike ba! Har ga Allah Maryam, Abba is trying to be just here.” Da sauri ta d’ago tana kallonshi da jajayen idanunta. D’aga mata kai yayi alamar gasgata mganar shi, kafin Baba Bashir ya d’aura da cewa “Maryam har yanzu zuciyar ki a k’ulle take da zafin abunda Abbas ya aikata miki, shiyasa ba za kiga abinda mu muka ganiba, wanda muma a da bamu ganshiba sai bayan da muka yi k’ok’ari muka goge takaicin shi daga idanuwanmu.” “Mune muka haifeki, baki da masu fad’a miki gaskiya sama da mu, ki tashi ku tafi suyi miki kwatance ki kaisu ki dawo, dama haka rayuwar take, ba komai kake kwallafawa rai kuma ka samu ba, ki bari ko nan da wata biyu ne haka, sai a san abun yi kinji? Yanzu kuje kawai.” Hudan ke kuma idan kin koma, ki san yanda za kiyi mishi magana a samu ya saki Babanku Usman kinji?” Cewar Shuwa. A hankali Mama ta rintse idanuwanta wasu zafafan hawaye suna zubo mata! Ta manta rabon da Shuwa tayi mata magana mai tsayi haka. Bata dawo daga duniyar tunanin da ta tafi ba, taji Sakina ta furta wasu maganganu da suka girgizata matuk’a! Wai “An saka ranar Huda nan da wata biyu da Arshaad!!” Ba Mama kad’ai ba, gaba d’aya parlourn shiru ya d’auka! Chaaan! Shuwa tace “Allah ya sanya albarka” Da sauri Mama ta kalle ta da idanunta hawaye shab’e shab’e! Kasa jurewa Shuwan tayi kawai ta mik’e ta kama hanya ta fice… Baba Bashir ne yace “ku tashi kuje Maryam, za muyi wannan maganar wata rana!” Cikin kuka Mama tace “Kaka, Abba Naji zan barta ta koma amman dan Allah kar ku saka na maida ita, ba zan...” Kukan da ya kufce mata ne yasa ta kasa ci gaba da magana ta mik’e ta fice tayi cikin gidan… Baaba Talatu ce ta bita domin lallashin ta. Wannan shi ake kira isa da mallaka!!! Tayaya zaka sa ranar Yarinya ba tare da tuntub’ar Mahaifiyarta ba? Saboda Allah fa!. Shiruuu, parlourn ya d’auka, chaan Kaka yace “su mik’e su kai su” Ita Sakina tausayi ma y’an tsofaffin suke bata, sun tsufa amman har yau basu huta ba, bayan jigilar case d’in y’an unguwa ga na family…ta tabbatar yanzu suna maida su, police station zasu wuce, akan case d’in Baba……….. A k’ofar tafkeken mansion d’in da suka isa da taimakon kwatancen Sakina suka yi parking, daganan suka yi musu sallama, da d’an Guntun maganganu tukunna suka wuce, su kuma suka shige ciki. A parlourn suka tarar da Abba, Daddy har Dad da Arshaad! Da alamun maganganu suke yi masu mahimmanci. Yadda Hudan ta baro Mama tana kuka yasa ta d’an ji zafin Abba! A hankali suka gaidasu, bayan sun amsa bata tsaya ba kawai ta haye sama! Har sai da Sakina ta d’an yi mata magana bayan sun hau, dan taga kamar basu ji dad’in yadda tayi musu d’in ba. Ko lunch k’in sauk’a tayi, ba yanda Sakina batayi da ita ba amman tak’i sauk’a, gashi Abba sai kira yake a waya tana amsawa tana cewa “Huda sallah take” Kamar minti ashirin haka, suka ji knocking. Sakina ce tace “Come in” A tunanin ta ko maid aka turo ta kawo musu abincin. Turo k’ofar yayi ya shigo, Sakina bata san lokacin da ta fara dariya ba ganin Abba ya shigo har da hular kuku a kanshi da basket d’in abinci a hannunshi. Harararta yayi, ya d’aura yatsanshi akan lips d’inshi alamun tayi shiru! D’aga hannuwanta sama tayi tana gimtse dariyar tata, sannan ta mik’e ta fice da sauri. Sai da ya ajjiye kular, sannan yace “princess” Shiru tayi still tana kwance ta bawa k’ofar baya. Chan taji yace “Hudan” A hankali ta mik’e ta zauna ta juyo tana goge hawayenta, fuskarta tayi jaaa alamun taci kuka, over!! Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya zauna a bakin gadon, yayi hugging d’inta ya fara lallashinta ai kuwa kamar jira take ta saki kukan babu control. Bai hana ta ba, sai da ta gaji dan kanta tayi shiru tukunna a hankali yace “sorry dota, i’m really sorry, ok?” Cikin sheshshek’a tace “Abba Mama na da bp, yanda na baro ta tana kuka, Allah zai iya tashi?” Murmushi yayi yana sakinta kafin ya gyara zamanshi yana kallon k’ofar fita tukun yace “Hudan, na fiki jin zafin kukan da Maman ki take, please don’t question my decision, it’s the right thing.” Ahankali tace “Amman Abba pls...” “Shhhhhhh” Yace ba tare daya kalleta ba, kafin ya juyo ya fara k’ok’arin zuba mata abinci. Omelet d’in da ya soya mata ya saka a gefe, da pizza slice uku da ya d’auko. Da farko k’in ci tayi sai da yayi dagaske, tukun ta d’an karb’a. Bayan ta gama ta sha ruwa, ya d’an dunga janta da magana yana ta faman lallashinta. Hudan bata iya dogon fushi da mutum ba, don haka ta d’an sauk’o, hakan kuwa yayi matuk’ar ragewa Abba kusan 20% na damuwar da yake ciki shiyasa da ta rok’esa akan ya saki Baba ba don halinsa ba sai dam kakanninta da hankalin su yake a tashe! Abban ya amince, a take ma a gabanta yayi waya yace a sake shi. Ta ji dad’i sosai kuwa. Daganan suka d’an ci gaba da maganarsu. Hammar da yaga tanayi ne ya sanya ya fahimci bacci take ji, dan haka yace mata “ta kwanta” Bata yi 10 minutes da kwanciyar ba ta fara bacci…. Ahankali yake kallonta yana tunani kala kala… Sai bayan kusan 1 hour tukun ya rage mata k’arfin ac ya lullub’eta da bargo, sannan ya fita da kayan abincin............... A chan parlourn k’asa kuwa, sam Sakina bata lura da Auwal wanda ya daya dawo break ba, sai da ta kusan k’arasawa dining d’in! Tun kusan sauk’owarta yaji a jikinshi! Addua yake Allah yasa itance, don haka ya k’urawa stairs d’in ido… Ba a hankali take tafiyarta ba ba kuma da sauri ba! Da d’an murmushi a kan fuskarta. Gaba d’aya ya shagala da kallonta, har wani lumshe ido yake yi yana bud’ewa. Jikinta ne ya bata kamar ana kallonta, sai kuma mayen k’amshin turarenshi da ta fara ji a jikin shi tun ranar farko ya daki hancinta! Dan haka da sauri ta d’ago ta kalli dining d’in.. Suna had’a ido yayi saurin rintse idanuwanshi kafin a hankali ya bud’e su a kanta! Doguwar riga ce a jikinta Ashape y’ar kanti bak’a mai ratsi ratsin sky blue sai d’ankwalinta wanda tayi simple d’auri da shi.. Rigar bata wani kamata ba, amman kasancewarta mai garin jiki yasa ta d’an fiddo mata surar jikinta kad’an!. Ranta ne ya b’aci ganin yanda yake wani rufe ido yana sake bud’ewa yana k’are mata kallo! Da sauri ta sa hannu ta warware d’ankwalinta ta yafa a jikinta sannan ta doka wani uban tsaki, wanda yayi sanadiyyar dawo dashi cikin parlourn. Har ga Allah abinda take tunani ma shi Allah bai bashi ikon lura da nan d’in ba, kawai shi dai yasan ya tsinci kanshi cikin tsananin farin ciki da shauk’i na daban, sannan yanda ta yi d’aurin ya sake fito da ainahin kyauwun fuskarta dan yawanci cikin hijabi yake ganinta, ga wani lallausan saje dake shirin had’ewa da gashin girarta, na gefen kunnenta ma ya sauk’a sosai kamar zai had’e da gashin k’eyarta, sannan tunda yake bai tab’a ganinta tana murmushi irin yau ba! Bai ida dawowa dede ba yaga ta juya da sauri zata bar wajen. Da sauri ya mik’e ya k’arasa ya sha gabanta kafin yace “Sakina, please, listen to me dan Allah.” Wani kallon tsana tayi masa kafin tace “mallan dalla matsa In wuce” Tayi maganar babu alamun wasa a tare da ita…. Zagayeshi take k’ok’arin yi amman yak’i ya bata damar yin hakan, da alamun ma in ta biyeshi to a yadda yakesa hannayenshi wajen k’ok’arin kareta daga wucewa tsaf zai tab’ata! Don haka ta tsaya ta fara aika mishi da harara kafin tace “Malan ni ba Jalila bace ba! Ka bar ganin wai a gidanku nake wallahi Idan baka bani hanya na wuce ba, zan zabga maka mari!” Ga mamakinta sai taga yana dariya, sai da yayi mai isarshi sannan yace “Na yarda! But duk mari d’aya zaki bani 10 minutes d’inki, kawai ko d’an hira ne muyi…..tbh i can do anything to get your attention” Ya k’are maganan yana kallonta da murmushi akan fuskanshi sannan ya d’anyi k’asa da kanshi….. Yanayin zanen flower d’in da aka yi na sky blue akan kayan jikinta yayi mishi kyau sosai! Zanen ya bi da kallo, har ya sauk’e idanunsa akan yatsun k’afarta! , Gaba d’aya ya shagala da kallo yaga ta janye da sauri cikin b’acin rai tace “D’an iska kawai!!” k’asa k’asa, ita kanta bata yi tunanin zai ji ba, sannan tayi sauri ta nufi d’akin da ke kusa kusa, tana shiga ta datse k’ofar ganin yana shirin biyo ta. Tunda Auwal yake a rayuwar shi, har snake friends d’insa wani lokacin suke kiranshi da shi, ko master, ko danger sunaye dai na rashin d’a’a kala kala but bai tab’a jin ba dad’i ba! Amman yau da Sakina tayi mishi wannan kallon har ta furta, gaba d’aya duk sai yaji babu dad’i! He hates it. Kasa ci gaba da lunch d’inma yayi don haka ya mi’ke ya fita ya koma office da tunani barkatai a ranshi! He just wants to talk to her, yana so ya sake ganin smile d’in nan nata! D’an 5 minutes d’in da suka yi shi da ita d’azu tare zai iya cewa ‘it one of the best moment of his life.......’ BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 46 BAYAN WASU Y’AN KWANAKI. Tun ranar da su Hudan suka koma Nasarawa gra, malaria da mura suka yi mata ram!Bata iya komai hatta karatunta ma Sakina ce ta karb’a take yi. Gaba d’aya hankalin Abba a tashe yake, kwananta d’aya a asibiti aka sallamosu aka had’o su da nurse wadda zata dinga yi mata allurai da chanjin drip. Shi da kansa (Abba) yake jinyar ta, da kyar yake yarda yaje yayi bacci amman da sassafe shi da Arshaad ne suke tashinsu a bacci. Babu abunda yafi d’aga musu hankali irin yanda bata iya cin abinci dan ta samu lost of appetite! A rana sai a girka abinci kala nawa amman da kyar zata iya tsakular d’aya, gaba daya duk ta zabge ta rame tayi wani irin fariii! Sai dogon hanci wanda ya sake fitowa tubarkalla, idanuwan nan daman ya lafiyar kura sun sake lumshewa kamar na mashaya. A cikin kwana biyun nan ba Hudan ce kad’ai ta rame ba har Auwal!! Dan kwata kwata Sakina ko a waje ta ganshi to ta bar wajen kenan sai in ya tafi tukun zata koma, k’iyayyar k’iri k’iri take nuna masa babu ji babu gani. Ranar da aka kwantar da Hudan a asibiti kuwa, da Auwal d’in yaje dubota akai rashin sa’a Sakinar ce a wajen Abba ya d’an fita ita kuma Huda tana bacci dan haka ya samu chance! Ganin da Sakina tayi abun nashi ba na k’are bane yasa ta fito mishi a Sakinar ta ta wankeshi tass!! Sannan tace “Ta tsaneshi, ba zata tab’a iya yin rayuwa da mazinaci mak’aryaci kuma mayaudari ba! Ya fita a harkar ta tun kafin ta sauya mishi….” To dai tun daga ranar ta samu ya d’an sakar mata mara, dan ita yau kusan sati d’aya ma amman bata saka shi a idontaba. Abunda bata sani ba ashe rashin lafiya shima yayi na kwana biyu..gaba d’aya duk ya rame, office kawai yake iya zuwa, Daddy yayi tambayar duniya har ya gaji ya kyaleshi….. Yau Hudan ta d’an tashi jikin da sauk’i tun safe, dan yau through out batayi amai ba kuma ta d’an ci abinci ba laifi Abba sai murna yake yi, don haka yace “idan zata iya tazo suje k’asa suyi dinner da kowa (cikin mutane)”. Sudais ne ya ruk’o hannunta na dama Abba kuma na hagu, Sakina sai murmushi take yi, dan ba k’aramin burgeta suke yi ba sai wani lallab’a ta ake yi kamar kwai! A haka suka sauk’o gwanin ban sha’awa. Tayi tunanin a nan za suyi dinner d’in amma sai taga sun nufi side d’in Daddy, Sakina ba dan taso ba ta bisu dan kwata kwata bata son abunda zai had’ata da Auwal, sam!. A chan suka tarar da Aslam da Arshaad… Basu samu Daddy a wajen dining d’inba amman an kammala jera komai. Ba suyi 5 minutes da zama ba, su Daddy suka sauk’o shi da Auwal! Bai yi wata wata ba ya nemi kujerar dake gefen Sakina ya zauna Allah ya taimakeshi babu kowa a wajen. A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya yana jin wata nutsuwa ta musamman…. Sakina kuwa kamar ta tashi haka taji, kawai dai ta san su Abba za su d’an iya fahimtar wani abun shiyasa ta zauna saboda itafa ko a labari bata k’aunar a sako sunanta kusa da na Auwal! Cikin kulawa aka shiga exchanging greetings.. Sai da aka gama gaggaisawa tukun Daddy yace “sorry i kept you waiting, Auwal ke hunger strike kamar wani baby abincin ma wai sai naje na lallab’ashi tukunna zai yarda yazo yaci” Murmushi Aslam yayi, Abba kuma yace “gashi kuwa duk ka rame, what’s wrong with you?” Yayi maganar referring to Auwal d’in. “Nothing” kawai ya iya cewa yana sunkuyar da kanshi k’asa. Murmushi Abban yayi, dan kamar yad’an gano Auwal d’in amman sai ya basar kawai aka fara cin abinci. Arshaad ke zaune a kusa da Aslam Abba kuma na ata gefenshi (sun saka shi a tsakiya) Duk su biyun suna lura da yanda yake kallon Hudan wadda ke opposite d’insu akai akai! Gaba d’aya Arshaad sai yaji ya damu sannan bai ji dad’in hakan da Aslam d’in yake yi ba kwata kwata! Amman sai yayi ta k’ok’arin kawar da duk wani negative thinking a kanshi. Ita kanta (Hudan) a takure take, gashi zuciyarta ta hanata sukuni. Loma biyu kawai Sakina ta iya yi cikin kwanciyar hankali dan tunda Auwal ya fara mata ‘Hi’ ‘How are you?’ D’insa taji wani malolo ya tokare mata mak’oshi! Bata san lokacin da ta ajjiye spoon d’inta da k’arfi ba wanda hakan ya janyo hankalin kowa kansu… Dariya Abba yayi dan tun d’azu yanata lura da su, cikin dariyar yace “Ya takura miki ko?” Da sauri tace “Eh wallahi Abbac kace mishi....” Kasa k’arasawa tayi sakamokon zungurinta da Hudan tayi, k’asa k’asa tace “kinga Daddy fa yanda yake kallonki, ki yi shiru” Kallon inda Daddyn yake tayi, karaff! Taga itan yake kallo yana d’an murmushi, gaba d’aya sai kunya ta lullub’eta tayi k’asa da kanta. Y’ar guntuwar dariya Daddyn yayi kafin yace “K’arasa mana Sakina… Ace mishi ya daina takura miki ko?” Cikin dariyan ya kalli Auwal kafin yace “Auwal, Allah har a gama cin abincin nan kar inji ta sake kawomin k’arar ka!” Shi dai Auwal shiru kawai yayi kamar ruwa ya cinye sa.. Arshaad kuwa dariyar mugunta yake yi mishi a ranshi yace “Allah mai had’i!” Don ya tabbata Auwal sai yaci kwal ubanshi a hannun Sakina. Daddy kuwa kallonsu yake ta yi lokaci zuwa lokaci….tabbas daman ya d’an fahimci akwai abunda yake damun Auwal kuma yake kaishi side d’in Abba! Kenan wannan Yarinyar ce, but yaga kwata kwata Yarinyar bata da interest a kansa shi kuma gashi ya fahimci tsakani da Allah Auwal d’in nasa yake son Yarinyar. A zuciyar shi ya hau adduar ‘Allah ya karkato da hankalinta ga Auwal d’in a samu yayi aure ya bar wannan tsalle tsallen, dan tabbas ya hango nutsuwar d’an masa a tareda Yarinyar……. Har aka kammala, Auwal bai sake yi mata magana ba. Sai da aka d’an tab’a hira tukunna aka watse. Arshaad na son ya gana da Hudan amman Abba yayi kane kane! Har d’aki suka rakasu shi da su Sudais kamar d’azu… Sakina ce ta kawo musu tofi suka yi sallama suka tafi shi da Aslam..... Suna shiga d’akin, suka hango wayar Hudan dake kan gado tana kyalli, da sauri Shuraim ya k’arasa yaje ya d’auko dan yanayin tafiyar tata kafin ta isa kiran zai iya tsinkewa, amman dukda hakan kafin ta kai ga amsawa kiran ya tsinke. Gabanta ne ya fad’i ganin 20 missed calls d’in Mama akan screen d’in, tana shirin kira wani kiran ya sake shigowa…. Tana amsawa taji Maman ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace “Duk hankalina ya tashi na d’auka jikin naki ne ya motsa.” Murmushi Hudan tayi tana k’arasa zama a kan gado kafin tace “Da sauki Alhamdulillah, ai na fad’a miki na warke fa Mama ki daina d’aga hankalinki.” Ajiyar zuciya Mama ta sauk’e sannan tace “Gobe zamu zo mu dubaki ni da Ummu in shaa Allah.” Hudan, cikin d’an zaro ido na murna tana murmushi tace “Na gode kuwa sosai Mama zan ji dad’i, sai kin zo.” Murmushi itama Maman tayi kafin tace “take care, kina dai shan maganinki ko? Na sanki da k’in shan magani.” Cikin yin y’ar dariya Hudan tace “Maama kin manta Sakina na tare dani.” Y’ar k’aramar dariya taji itama Maman tayi kafin tace “Hakane fa, sai mun zo goben in shaa Allah, Hajiya ma tace a gaida ke!” A hankali Hudan tace “kiran ki tayi? Kun shirya? Na ga rannan ma tayi miki magana a gida lokacin a gaban kowa.” Ajiyar zuciya Maman ta sauk’e kafin tace “Kirana tayi takanas Hudan dan taji jikinki da kuma yanda nake” ta k’arashe maganar tana share hawayenta. Murmushi Hudan tayi itama kwalla ta zubo mata, kafin tace “Alhamdulillah” Tana share hawaye sannan tace “Sai kun zo Mama” Tana murmushi, itama murmushin tayi sukai sallama ta kashe wayar. Cike da nishad’i Abba dake tsaye a kanta yace “Y’ar gidan Mama” Cikin yanayin zolaya. Cikin d’an murmushi tace “Wai hankalinta ya kasa kwanciya gobe zata zo ta ganni” ta k’arashe maganar cike da zumud’i. Murmushi Abban yayi sannan yace “Allah ya kaimu goben” ya shafa kanta tukun ya juya ya fita. “Sai da safe” Shuraim yayi mata, Sudais ma haka, yayi pecking cheek d’inta sannan ya fita. A hankali ta kwanta ta lumshe idanunta ahaka Sakina ta shigo ta sameta. Nan take fad’a mata good news d’in! Ta kuwa yi murna, sannan tace “Ai daman lokacin dana ce mata har a asibiti kika kwanta baki ji yanda hankalinta ya tashi ba, daman na san ba lalle ta iya hak’ura ba, sai tazo. Allah ya kaimu goben ya kawosu lafiya.” A hankali Hudan tace “ameen” tana hamma...... Tun da suka tashi da safe suke expecting d’in su Mama, har girki suka d’anyi musu dukda rashin k’arfin jikinta sai shirye shirye suke yi. Suna cikin setting dining Abba ya shigo, murmushi yayi a ranshi yana yaba irin k’aunar da y’ar tasa take yi wa Maman ta. Sai da yazo ya dafa kanta tukunna ma ta fahimci ya shigo. Gaishesa suka yi ya amsa musu cikin kulawa kafin yace “Suje da Linda (mai girki) ta bata kayan wankinsu da suka tara, masu wanki zasu fara. Da mamaki yake kallonta, jin tace “Ai su kullum In suka cire kayansu a washing machine suka sakawa su wanke” Sannan ta k’ara da cewa “Akwai fa washing machine a toilet din nawa Abba” Murmushi yayi ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace mata “Na wanke inners ne wannan dota. Next time ku tara akwai masu wanki da guga da suke yi, time to time. Yanzu ku bata kayan ta kai musu sai a goge” Da ‘to’ suka amsa ya wuce Sakina ma ta kira Linda suka wuce domin ta bata kayan, ta bar Huda anan tana ci gaba da setting dining. Sai bayan sallar azahar, Ummu tayi musu waya tace “su fito, suna waje.” Sai da suka gayawa Abbas tukunna suka fita…. Babu yadda basu yi da su ba akan su shigo ciki amman suka k’i shiga gidan. Sun d’an jima a wajen, dan ma unguwar ba mai mutane da yawa bace ba dan babu k’afa a layin, shima titin shiruuuu. Daga baya Mama ta bawa Hudan ledar su tsami gayen da tace ta taho mata dasu. Aikuwa taji dad’i sosai, ta dinga murna, nan Mama ta cewa Sakina “kar su durfafi mand’on suyi ta sha fa dan in suka sha da yawa zai kunche musu ciki.” Mama, tunda sukazo dama taga wata adaidaita sahu tayi parking, sai yanzu taga mai mashin d’in yana juyowa, kamar ance ta kalli cikin napep d’in suka had’a ido da Baba! A take gabanta ya yanke yayi wani irin fad’uwa! Sannan zufa ta hau keto mata ta ko wacce b’ular gashin dake jikinta… Daman tun da safe da tace masa “za su fita ita da Ummu” taga kamar rashin yarda a fuskarshi. Laifinta d’aya da tak’i fad’a masa gaskiya wanda ita kuma dalilinta shine ‘Ta san ba barinta zai yi ba’ ita kuma har ga Allah tana so tazo taga Huda. Dafa ta d’in da Ummu tayi ne yasa ta d’anyi firgigit ta dawo cikin haiyyacinta, tana mai k’ak’alo murmushi. Cikin d’an k’arfin hali ta cewa su Huda “su koma gida, kar a ga sun dad’e.” Sai da suka d’anyi y’ar kwallar su, tukunna suka rabu bayan ta sake tambayar Hudan akan “tana son Arshaad d’in?” Hudan kuma ta amsa mata da ‘eh’ sannan suka wuce… …Tunda Ummu da Madu suka zaunar da ita( Mama) suka fahimtar da ita sosai ta d’an dawo saita, tana k’ok’ari taga ta jaa y’arta itama a jiki su zauna lafiya wata rana sai labari…fushi da turjiya ba inda yake kai mutum sai garin dana sani, In Allah yayi auren yanzu shine mafi alkhairi kuma sai anyi a yanzun to fa idan ta dage tace zata hana tsaf rabo zai iya kasheta! Shiyasa tun ranar farko a waya bayan su Hudan sun dawo da ta tambayeta ita kuma Hudan tace mata ‘eh, tana sonshi’ shikenan Mama ta shafe komai, ta rungumi abunda Allah ya k’addaro da hannu bibbiyu……. Da kyar suka samu adaidaita sahu, Ummu dai ta lura akwai abunda ya firgita Mama amman ganin tayi tanbayar har ta gaji bata bata amsar komai ba ya sanya kawai ta kyaleta, a tunaninta maybe ko Abba ta gani. Mama aka fara ajjiyewa, sannan Ummu suka wuce ita da mai napep d’in ko shiga bata yi ba dan yau week end so tana son yin kwalema, saboda tun da Sakina ta tafi aiyuka duk sun yi mata yawa sun ch’ab’e mata. Tun a soro taga machine d’in Baba kamar yanda ta fita ta bari, amman k’ofar d’akin shi a rufe da kwad’o! Tunani ta fara a ranta tace “kenan bai dawo ya d’auka ba ko dai aiki ya wuce a napep d’in? Mai yasa ma ya bisu a napep in the first place?….” Da wannan tunanin ta k’arasa k’ofar d’akinta ta zaro makulli a y’ar purse d’inta. Gidan shiruuu, ba kowa. Tana d’aura makullin a ramin shi taji k’ofar tayi motsi! A take gabanta ya yanke ya fad’i. A hankali ta d’an tura k’ofar, ga mamakinta sai ta ga ta bud’u! Cikin rawar murya tayi sallama tare da kutsa kai ta shiga ciki. Turus! Haka ta ja ta tsaya sakamokon ido hud’u da suka yi da Baba wand yake a kwance a kan gadon nata yayi pillow da hannuwanshi akan pillows d’in da ya d’aura kanshi, ya d’aura k’afa d’aya kan d’aya yana d’an jijjigawa…. Ba abunda yafi d’agawa Mama hankali sai yanda taga idanun Baba sun sauya kala! Idan aka ce mata tunda ya dawo yake kuka tabbas ba zata musa ba domin kuwa idanunsa sun yi jaaaaa!! Sun k’ank’ance hatta fuskarshi sai da ta d’an kumbura. Bata gama fahimtar yanayin da yake ciki ba taji yace “Ai nayi tunanin ba zaki dawo nan ba!” Yayi maganar yana mik’ewa ya isa k’ofar d’akin, kawai taga ya sa key ya juyo yana kallon ta. A take wani mugun tsoro ya dirar mata, for the first time da taji tsananin tsoron Baba tunda take a rayuwarta dan hatta yanayin maganar shi yau ta sauya, kamar wani wanda yayi shaye shaye. Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauk’e, yana kallonta kafin ya sake cewa “Tun yaushe kuka fara had’uwa?” Yayi mata tambayar yana kallon kwayar idanunta waenda suka rine da b’acin rai da takaici, ga tsoro sannan ga ruwan hawaye da ya cika su taf!! Itan ma shi take kallon, tsaf ta fahimci wa yake nufi amman kawai sai tace mishi “Da wa kenan??” Murmushi yayi, kafin yace “Abba” Kanshi tsaye. Hawayen da take k’ok’arin rik’ewa ne suka yi nasarar zubo mata, cikin karyewar zuciya tace “Zargina kake yi?” Bata jira jin amsarshiba taci gaba da magana “Ka yarda ko kar ka yarda Rabo na da in ga Abba a idona wallahi tun ranar da ya d’auke Huda daga wajena a asibiti! Wanda a ranar kuma rabona da shi shekara goma sha takwas!..” Cikin katseta yace “Mai ya kai ki gidanshi yau?” “Y’ata naje gani, kuma ko gidan ban shiga baduk da na san ka sani kuma ka gani….Indai bibiyar da kayi mini ta biya to ya kamata ace ka fahimci ba wajen Abba naje ba! Tun da muka je ko gate d’in gidan ban tab’a ba, kuma inda wajenshi zan je to da ba zan d’auki Ummu muje tare ba da ni kad’ai zan je.” Ajiyar zuciya ya sauk’e, ransa na k’arasa baci yace “Kinga kin kama kanki!! Abunda nake so inji kenan! Kalmar ki ta k’arshe da kika fad’a yanzun ta bada ma’ana kwarai Maryam! Amman karki damu dan a yau d’innan ba zan barki ba sai na tabbatar da cewa ko a hanya In Abban ya ganki ba lalle ya iya gane ki ba!” Cikin b’acin rai Mama tace “Ko a musulunci ba a aure da zargi! Na gaji da halinka na gaji da abunda kake yi min na gaji da komai na gidan nan! Kuma wallahi tunda zargina kake yi to ba zan sake zaman second d’aya da kai ba!.” Ta k’arashe maganar tana kuka ta zagayeshi… Tana k’ok’arin fita yayi mata wata mahaukaciyar fincika, ya janyo ta da k’arfin tsiya kafin ya cillata ta tafi ta fad’a kan dressing mirrow, ta bugu sosai dan hatta madubin sai da ya fashe, sannan ta buga cikinta a jikin tudun katakon da ake jeran kayan kwalliya…. Farfashewar da gilashin yayi ne ya sanya wasu suka ji mata ciwo a goshi da hannu, take jini ya b’alle ya fara zuba. Bai damu ba! Ya sake juyo da ita ya kifa mata wani marin da sai da ta kai k’asa, tana shirin tashi ya hau dukanta ba ji ba gani yana ball da ita! Cikin tsananin b’acin rai yana cewa “Yanzu kin shirya da su Hajiya ko? Wato kina da wajen zuwa kuma y’arki ta samu matsugunni shine har kike da bakin ce mini za ki bar gidana saboda rashin halacci ko? Ai daman na san using d’ina kawai kike yi tun ba yau ba, burinki a yanzu bai wucce in barki ki je ki auri Abba ba ko? To wallahi bari kiji ko mutuwa zan yi sai dai mu tafi tare ba dai in barki ki koma masa ba!!…” Yana hawaye yana maganganu kamar zararre yana jibgarta….. . Idan ana maganar dakuwa to Mama ta daku a hannunshi, tun tana salati tana neman d’ouki har k’arfinta ya k’are ta kasa furta komai. Ya fad’i gaskiya kam Tabbas! Dan ko ita da kanta a yanzu da ace zata kalli madubi to ba lallai ta iya gane kanta ba, ballantana kuma Abba. Karshema da Baba yaga abun bai yi mishi ba, katakon da take rataye jakankunan ta ya raruma ya maka mata a k’afa! Tun daga nan da tayi wata razananniyar k’ara bata sake motsawa ba! Fahimtar da yayi ta sume ne ya sanya shi sarara mata ya juya nufi gefen gadon yana layi ya zauna dab’ass!!! Ya dafe kanshi sai kuma ya fashe da wani irin kuka.. Ba abunda idanunsa suke hararo masa sai irin yanda yaga Mama tana ta k’arewa gidan Abban kallo! Tayaya? How? A haka shi zatayi appreciating d’inshi!? He has been trying his best ya goge Abba a ranta, amman abun yak’i yuwuwa sam ya kasa cireshi a ranta, in dai abu da Abba a ciki to ba zata iya hak’ura ba Duba fa yanda ta shirya mishi k’arya yau ta tafi gidanshi…… Yana wannan tunanin shed’an kuma yana sake rura mishi wutar zarginsu d’in da yake yi ita da Abban A ranshi yake aiyyana “to in ba hakaba in dai ba suna tare ne ba tayaya za su dinga bawa juna mahimmanci haka?” Ya lura da yanda ran Abba ya b’aci matuk’a ranar da yaje gidanshi da y’an sanda a lokacin da ya aibanta Maryam d’in a gaban kowa, aiban ta tan da yayi ne ma Ummul abaisin dalilin da yasanya Abban ya kulle shi…… Ya jima ya na kuka kamar k’aramin Yaro, zuciyar shi ce ta bashi shawarar gwara ya karyar mata zuciya ta hanyar nuna mata Abba fa yayi mata nisa ba zai tab’a dawowa ba! Amman ta yanda zuciyartata za tafi karyewa ta hak’ura shine idan ta saka rai sannan ta samu full hope akan zata samu Abban for the second time sai hakan yak’i yiwuwa ta sake rasa shi! In ta samu wannan disappointment d’in ya san zata ji zafi zuciyarta zata karye kuma tabbas zata cire rai ta hak’ura da Abba ta rungume shi (Baba) a matsayin Masoyi. Da wannan tunanin ya mik’e ya fara dube dube.. Da kyar ya samo takarda, ya yi rubutu ya d’aura mata akan k’irjinta, ya juya ya bud’e k’ofar ya fice ya barta kwance cikin jini cikin mawuyacin hali. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 47 Tun bayan sallar la’asar su Hudan suka fara neman layukan su Mama domin su ji ya suka isa gida. Ummu dai ta d’auka amma Mama har bayan Maghrib bata d’aga ba. Tun suna ganin abun kamar wasa har bayan sallar Isha shiru dan haka Ummu ta yanke shawarar zuwa domin taga ko lafiya saboda Mama ko 2 misscalls bata bari ayi mata take amsa waya........ A hankali take bud’e idanuwanta….dishi dishi ta fara gani kafin ta samu ta d’an fara gani. Gefen fuskar Hudan wadda ke zaune a gefenta ta fara gani ta sharkaf da hawaye, sai kuma cikin fad’a sosai taji Kaka yana cewa “Wallahi tallahi Talatu zan yi mugun b’ata miki rai! Wannan wanne irin rashin tunani ne da son kai? Mutumin da yayi wannan b’arnar shi kike cewa a saka? Reputation d’in yaci k’aniyar sa! Ai babu wani maganar image da reputation shi da kansa ya riga ya lalata kayanshi…” Tana k’ok’arin yin magana ta fara ganin dishi dishi still.. Har ta koma ta sake sumewa babu wanda ma ya san ta farka! Bata farfad’o ba sai washegari da safe, d’akin daga Ummu sai Hudan, Arshaad da Sakina. Sakina ce ta fara lura da ta farka dan haka ta k’arasa da sauri tana cewa “Ummu kinga ta bud’e ido yanzun nan kuma ta sake rufewa”. “Alhamdulillah” Ummun tace sannan ta fita dan zuwa ta kira Likita saboda yace tana farkawa a kirasa. Bayan y’an dube dube ya k’ara mata wasu allurai ta drip sannan yace “su yi k’ok’ari su bata abinci mai kyau, ta ci.” Yana fita Hudan ta k’araso, duk yadda taso ta rik’e hawayenta kasawa tayi dan haka ta fashe da kuka Sakina ma haka, haka itama Ummu wadda ke tsaye a gefe. Arshaad ne yayi k’arfin halin lallashinsu da kyar suka samu suka yi shiru, sannan suka shiga tambayar ta “ya jiki” Fahimtar da Arshaad d’in yayi suna buk’atar space ne ya sa shi yi musu sallama sannan yace “zuwa anjima zai dawo ya tafi dasu, akwai abunda ake buk’ata?” Da “Babu” suka amsa sannan Ummu ta sake yi mishi godiya, ya fita. Yana fita Ummu ta juyo tana kallonta kafin tace “shi ya kawomu nan shekaran jiya.” Da mamaki Mama tace “Shekaran jiya?” Da kyar. Shiruu, Ummu tayi kafin tace “eh! Kwanan ki biyu a nan. A yanayin dana ganki na yi tunanin na rasa ki ne Mama” Ta k’arashe maganar tana fashewa da kuka sannan cikin kukan tace “Ban yi tunanin kina da ragowar rayuwa a gaba ba, sannan na san muddin Abba ko Hajiya wani ya ganki a yadda na ganki to ba lalle su iya jura ba tsaf za su iya yanke jiki su fad’i dan ni kaina sai da na zube a wajen, da na ganki. Gashi Baban Sakina baya gari, shiyasa na kira Arshaad wanda shi kuma ashe a lokacin ma su Hudan sun d’agawa Abbansu hankali akan suna so su zo su ganki dan sunyi ta kira bakya d’auka, gashi kuma nima a lokacin sunata sake kirana amma ban d’auka ba! Dan haka suka taho. Banyi 20 minutes da kiransu ba, suka k’araso duk su ukun a hargitse dan a yanda sukaji muryata (lokacin da na kira Arshaad) sun san ba lafiya ba. Shigowar da suka yi ya sanya maimakon a d’auki mara lafiya d’aya sai kuka zama ku biyu! Dan itama Hudan suma tayi, Arshaad ya d’auketa a hanyar fitar da ita suka had’u da Baba! Yana ganin fitarshi ya datsa sakata wai Namiji ba zai sake shigar mishi gida ba! Kuma muka ce masa ya taimaka mu fitar dake ya k’i!. Ba yadda na iya sai su Abba Madun muka kira, abunda muke gudun kuwa sai da ya faru don yanzu haka shima yana kwance tunda ya ganki jininshi ya hau sosai! Don shima yayi tunanin mutuwa kika yi. Amman abu d’aya wanda aka yi yayi mini mugun dad’i shine ‘bayan an kawoki an tabbatar da kina da rai da Kaka da Abba Madu suka je dakansu suka yi arresting Baba! Kuma sun ce basu ga ranar fito da shi ba’.” Cikin kuka Mama tace “ki kira min su Kaka, ina da buk’atar magana da su, Bilkisu na gama auren Ya Usman, wallahi.” Ajiyar zuciya Ummu ta sauk’e kafin ta zaro wata takarda a cikin jakarta, ta mik’a mata...... Wani sanyi ne ya lullub’e Mama, atake taji kamar an yi mata bushara da gidan aljannah! Saki d’aya tak! taga yayi mata “Alhamdulillah” ta hau jerowa wasu hawaye suna gangaro mata….. A hankali Ummu ta dawo ta zauna kusa da ita kafin tace “A ta sanadiyyar dukan da yayi miki! Cikin da ke kanki na san baki san kina d’auke da shi ba ya zube jiya, har an yi miki wankan ciki!”. Mama bata san lokacin da ta fashe da wani irin kuka ba............. Ta d’an ci abincin kuwa ba laifi. Zazzab’i da zafin ciwukan jikinta especially karayar k’afarta ne suka sanya aka yi mata allurar bacci dan ta samu sa’ida. Sai dare Arshaad yazo, ga mamakin Sakina har da Auwal… Tana d’an murmushi suka shigo amman tunda suka yi ido biyu da Auwal ta had’e rai ta turb’une fuska! Dariya ta bawa Arshaad dan haka suna had’a ido ya hau yi mata dariyar tsokana ai kuwa ta chuno baki gaba ta sake kumbura jira kawai take a tab’ata ta fashe. Ba abunda yafi bawa Arshaad mamaki irin yanda Auwal ya durk’usa har k’asa ya gaida su Mama, shima (Arshaad) d’in d’an rissinawa yayi ya gaidasu, daga nan suka d’an zauna. Kafin daga baya suka mik’e suka ajjiye musu jibga jibgan ledojin da suka shigo musu da su, suka yi musu sai da safe… Ummu ce ta cewa su Sakina “su tashi kar ayi ta jiran su” da kyar suka fita tare da su Arshaad da alk’awarin gobe da sassafe za su dawo!. Sai da suka fita tukun suka ga ashe har da Abba aka zo. Ita da Sakina ne suka shiga motar Abba, Arshaad kuma suka wuce shi da Auwal. Suna yin parking Sakina ta bud’e ta fara fita bayan ta yiwa Abban sai anjima, Hudan na shirin fita Abban yace mata “Ya jikin Maman naki?” A hankali tace “da sauk’i”. Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace “Arshaad yace har da karaya ko?” “Eh” Ta bashi amsa. Cikin d’acin zuciya yace “na yiwa Mamanki laifi! Na saka polisawan wajen da akai kai Mijinta sun yi mishi duka bana wasa ba! Wanda shima hakan da nayi na san maybe idan taji labari zata iya jin haushina! But maza irin Usman irin haka ya kamata a dinga yi musu. Inaso in cire hannuna akan case d’in amman sam na kasa Hudan ban san mai yasa ba. Wallahi da ace ina da hali ko inda Maryam tabi Usman bai isa ya taka ba! Amman k’addara ta riga fata, kuma ance ba a shiga tsakanin Miji da mata, sam.” Shiruuu, Hudan ta d’anyi, tana son gaya mishi amman kuma sai taji ta kasa. Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace mata “Good night, kije ki huta kun sha jigilar asibiti.” A hankali tace “good night Abba” ta fice. Sun dan tab’a hira kad’an a parlour da Arshaad sannan ta sallameshi ta bashi sak’on Mommy, ta nufi d’aki a ranta tana mamakin yajin da Aslam yayi musu, lokaci d’aya kawai ya d’auke k’afa!. Har ta haye bata ga shigowar Abba ba kuma ta san ba fita yayi ba. Ya dad’e a mota, kafin da kyar ya samu ya fito ya shiga ciki yana ganin dishi dishi tsabar tashin hankalin da b’acin ran da yake a ciki, ya rasa me zai yiwa Usman ya huce takaici da bak’in cikin da yake ji….. Sai da su Hudan suka zo kwanciya tukun take gaya mata yanda suka yi da Abba d’azun sannan a hankali ta d’aura da cewa “bana son had’awa Mama case biyu shiyasa na k’i ce masa komai” Murmushi Sakina tayi kafin ta kamo hannuwanta duka biyu tace “Ki yi tunani, duk abinda kika ga ya dace, kiyi musu.” Da sassafe ta tashi ta shirya, tana shirin zuwa side d’in Abba taga call d’in Arshaad, sai da ta d’anyi jimm!! Tukunna ta amsa ta gaidashi. Cikin kulawa da so ya amsata kafin yace “ta sameshi a k’asa” Tare suka sauk’a ita da su Shuraim waenda za su school. A parlourn ta tsaya tayi musu a dawo lafiya, sannan ta k’arasa inda Arshaad d’in yake zaune. “Za ki fita ne? Naga kin shirya da sassafe” Yace yana kallon ta. A hankali tace “eh, amman sai wajen 9 yanzun ina son yin magana da Abba ne” Cikin bata dukkannin attention d’inshi yace “Exactly abunda ya kawo ni kenan. Did you tell him? I’m sorry na san bai kamata in yi miki wannan maganan ba but naga kamar Abban is disturbed, na dad’e ban ganshi a wannan yanayin ba. Me kikayi deciding? Za ki fad’a masa ne?” Ya jero mata tambayoyin yana mai tsareta da ido. Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin tace “jiya dai ban gaya mishi ba, but yau na yi deciding in fad’a mishi d’in, duk da ban san ya zai yi handling abunba, and I’m not even sure they still want each other back.” Murmushi Arshaad yayi kafin yace “Believe me they do! Amma kin tabbatar this is the right time? After all that has happened especially ma a ita Maman” A hankali Hudan ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace “I’m sure. Na riga na gama deciding” Murmushi Arshaad d’in yayi sannan yace “Ok dear. Allah ya taimaka, ya sa a dace.” “Ameen” tace. Yana d’an murmushi ya mik’e yace “Anjima idan na koma gida na d’an shirya zan zo asibitin in shaa Allah.” “Allah ya kai mu” tace. Kafin daga nan suyi sallama ya wuce office ita kuma ta nufi side d’in Abba..... A bakin k’ofar parlournshi ta tsaya ta d’anyi knocking jin shiru yasa ta tura ta shiga. Ba kowa, dan haka ta nufi bedroom. Ta jima tana knocking tukun chaan, taji ance “come in” A hankali ta tura ta shiga, da alamun tun d’azun a balcony yake dan yanzun taga yake shigowa cikin d’akin. Yayi mamakin ganinta da sassafe, dan haka suka fito parlourn suka zauna kafin ya kalle ta yace “Ya aka yi dota?” Kame kame ta fara yi, dan bama ta san ta Ina zata fara ba sai yanzu ta d’anji nauyin shi da nauyin maganar da ke tafe da ita! Chaan! Dai ta dake ta d’an sunkuyar da kanta k’asa tace “Daman, Baban ma na ji Ummu tace ya yiwa Mama saki d’aya shekaran jiya, jiya kuma tayi miscarriage” Tana gama fad’an haka tayi saurin sake sunkuyar da kanta k’asa tana ci gaba da wasa da y’an yatsun ta. Ta kusan minti biyar a haka, jin shirun yayi yawa yasa ta d’ago kanta ta d’an kalleshi, yana a yanda ta barshi idanunsa a kanta amman daga gani hankalinshi baya kanta. Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace “Hudan, are you sure?”. A hankali ta d’aga kanta kafin tace “Very sure”. Ajiyar zuciya ya sake sauk’ewa kafin yace “Thankyou! Za ki iya tafiya” A hankali ta mik’e tayi mishi sai anjima ta fita. Su kad’ai suka yi breakfast d’insu, daman a shirye suke, dan har handbags d’in su sun sauk’o dashi, Hudan ta zaro waya zata kira drivern kenan Abba ya shigo shi da Daddy…. Wani dark ash d’in yard ke jikinshi anyi masa d’inkin kaftan! Kyalli da taushin yadin kad’ai ya isa ya sanya ka gane kud’insa ba na wasa bane sannan daga ganin d’inkin ka san ba a k’asar nan ma aka yishi ba. Ya murza bak’ar hula da bak’in takalmi…. Yayinda Daddy yake sanye cikin suite maybe office yake shirin wucewa. Gaisawa suka yi. Cikin kallon agogon dake d’aure a tsintaiyar hannunshi Daddy yace “dota ku yi sauri mu wuce ko?” Mikewa suka yi Sakina tace “mun ma gama” suka gyara zaman mayafansu. Su Abba ne suka fara fita sai su. A motar Abba suka tafi Daddyn yana binsu a baya. Bayan sun shiga asibitin an yi parking, Hudan tana shirin tamabayar Abba ‘k’arfe nawa za azo a d’auke su’ taga shima ya bud’e motar yana ce mata “ta zagayo tayi leading way d’in” Bayan ta fita sun zagayo, Sakina tayi k’asa da murya tace mata “Ashe yau Abba zance zai zo shiyasa naga ya ci kwalliya” Da sauri Hudan ta mintsineta tana d’an juyawa dan taga ko attention d’in Abban yana a kansu..Magana taga suna yi shi da Daddy wanda ya fito daga mota dan haka ta d’an sauk’e ajiyar zuciya kafin ta jaa hannun Sakina suka yi gaba.. Abba na da ji sosai shiyasa sarai ya ji abunda Sakinan tace, murmushi kawai yayi ya girgiza kai suka bi bayan su… Ba kowa a d’akin sai Mama ita kad’ai tana zaune a kan gadon jinyar tata da littafin addu’o’i rik’e a hannun ta, tana karantawa tana d’an tofawa k’afar da akayiwa d’auri! Tsananin azaba takes sha, shiyasa gaba d’aya jikinta ma rawa yake yi…. Raunukan jikinta sun d’an sab’e, fuskarta ma ta d’an sab’e amman still har yanzu akwai bandej a goshinta wanda aka zagaye kan nata da shi aka d’aure a k’eyarta, ta d’an yafa k’aramin mayafi akan doguwar rigar jikinta saboda masu shige da fice but still kana iya hango dogon gashinta da Ummu ta gama tufke mata shi yanzu ta dunk’ule a k’asan bandej d’in kafin ta fita. Hudan ce ta fara shigowa sai Sakina sai Daddy.. Bata ganeshi sosai ba dan haka ta d’an tsaya tana d’an satar kallonshi A hankali yayi sallama ya shigo, suna had’a ido tayi saurin sunkuyar da kanta sannan ta rintse idanuwanta. Bata gama dawowa dai dai ba taji Daddyn yana yi mata ya jiki, kamar ba zata amsa ba sai kuma ta daure, “Alhamdulillah” kawai ta iya cewa. A hankali su Hudan suka je suka yi hugging d’inta suma suka yi mata ya jiki, da kyar ta iya amsawa. Sannan duk suka nema waje suka zazzauna. Tana jira taga Abba ya fita sai taga shima ya nemi waje ya zauna kafin a hankali muryarshi ta daki dodon kunnenta “Maryam ya jiki?!” Banza tayi da shi! Ya sake maimaitawa Nan ma tayi mishi banza!. Murmushi Daddy yayi kafin yace “Allah yasa kaffara ne, ni bara ni In wuce. Dota sai kun dawo” Allah kiyaye suka yi masa. Sai da yazo fita tukun Mama ta samu k’arfin halin cewa “An gode” Da murmushi yad’an kalleta yace “Allah ya sauwwak’e” daga haka ya fice ya bar Abba a nan zaune wanda bashi da niyya ko ranar tashi dan gyara zama ma suka ga yayi...... Kowa da abunda yake sak’awa a cikin zuciyarshi…..d’akin yayi shiruuu! A haka Ummu ta shigo ta samesu. Da murna suka hau gaisheta bayan sun je sun yi hugging d’inta. Cikin mutantawa suka gaisa ita da Abba Daga nan itama ta nemi waje ta zauna aka ci gaba da zaman kuramen da ita. A haka Baaba Talatu ta shigo ta same su, wadda ta zo tare da jikanta Autan Anty Zainab tsaran Sumayya da Sumayyar. Sumayya tana ganin Sakina taje ta fad’a kanta tana cewa “I miss you” Sai da Hudan ta dungure mata kai tukun ta juyo ta rungume ta tana cewa “Sorry, i miss you more” Dariya duk aka yi, Yaron Anty Zainab kuwa yana gaida Mama da Ummu ya koma gefe ya zauna, daman kaf a y’ay’an nata wadda aka yiwa aure kwanaki (Khadija) ita ce kawai suke shiri amman da babbar da autan duk uwar su sukayo. Tunda Baaba Talatu ta shigo taga Abba ta had’e rai! Hankalinta ba k’aramin tashi yayi ba har sai da su Maman suka lura da hakan. Wani abun mamaki ko gaisuwarshi k’in amsawa ta yi, haka ya yi mata har sau uku a tunaninsa ma shi ko bata ji bane, ganewa da yayi amsawarne ba zata yi ba yasa ya kyaleta. Hudan kuwa abun da taga ana yiwa Abban nata ya k’ular da ita sosai, dan haka ta had’e rai tana gaida Baaba Talatu ta d’auke wuta a d’akin. Su Baaba Talatu basu wani dad’e ba suka tafi. Sai da Abba yayi 3 hours tukunna ya mik’e ya yiwa Mama Allah k’ara sauk’i Ummu ce ta amsa Hudan kuma ta tafi yi mishi rakiya. Har suka je motar ba wanda yace komai. Sai da ya shiga ya zauna, tukun ya d’auko kud’i a cikin motar ya bata yace “ta rik’e, ko suna son siyan wani abun” Godiya tayi ta karb’a. Ganin ta rik’e murfin motar yasa yace “Akwai wani abu ne?”. D’an b’ata fuska tayi kafin tace “Abba In kayi musu magana sau d’aya suka yi shiru kawai ka dinga kyalesu”. Bai san lokacin da murmushi ya sub’uce mishi ba, ya ji matuk’ar dad’i da Hudan ta damu da mutuncinshi haka..dan haka yayi murmushi yace “To shikenan princess, na ji, in shaa Allah. Shikenan? Ko akwai wani abun?” D’an guntun murmushi tayi tace “babu” daganan ta rufe mishi murfin motar, yayi waving d’inta itama haka, ya wuce. Sai da taga fitar motarshi tukun ta koma ciki............ Satin Mama biyu a asibiti aka sallameta. A cikin sati biyun nan ba ranar da zata zo ta wuce Abba bai je ya duba ta ba. Kamar yadda Hudan ta gaya mishi kuwa sau d’aya yake yi mata magana in ta k’i amsawa ya kyaleta Baaba Talatu itama haka! K’arshema idan ya shiga jimla yake yi yace “Ummu sannun ku, ya mai jiki?” Daga nan shikenan… Sau biyu suka had’u da su Madu, dan su Ummu sun rok’esu akan su daina yawan zirga zirga shiyasa ba sosai suke yawan zuwaba! Yayi mamaki dan bai yi tunani idan ya gaishesun za su amsa ba, amman ga mamakinsa sai yaga sun amsa ba yabo ba fallasa! Yadda Baaba Talatu taga sun yi mishi hakan ya sake d’aga mata hankali dan haka suna isa gida ta d’agawa Kaka hankali akan su fito da Usman yazo a maida auren su da Maryam, ko kuma su fad’a mata inda yake taje ta sameshi dan ya kamata ya san halin da ake ciki! Dan ta ga take taken Abba so gara a maida auren su k’arasa rayuwarsu tare tun kafin Abba ya b’ullo da wani abun…. Da farko Kaka a hankali ya fara binta, ganin da yayi ba fahimta za tayi ba sannan kanta ya soma birkicewa ya sanya shima ya birkice mata ya fito mata a mai gidan sa! Yayi mata fata fata!! Tukun ya samu ta sarara mishi dan tayi mugun tsorata da shi. Auwal ma zuwanshi biyar, tun su Ummu basu fahimta ba har Sakina ta tonawa kanta asiri, dan yana shigowa zata had’e rai, ko kulashi ba tayi Hudan kad’ai ke gaidashi. Su su Maman ma dariya take basu, ganin basu ce musu komaiba yasa suka zuba ido kawai dan sun lura Sakinar bata ra’ayin shi kuma sun san da maganar yayan k’awarta Ashraff. Har da Abba aka rakata gida. Tunda aka bud’e gate d’in gidansu gabanta yake fad’uwa, dukda yanzu Shuwa har waya tana yi mata tana jin ya take amman ta san ba lalle ta huce gaba d’aya ba, tunda gashi ko asibiti bata zo ba..tana murnar mutuwar auren Baba a kanta matuk’a amma tana tunanin zaman da za suyi da Shuwa kuma ko ita ta kawo rashin kunya duniya ba zata je tace zata zauna a gidan Kaka ba….. Tana wannan tunanin motocin suka yi parking a harabar gidan, wani sanyi da iska take ji yana shigarta ta koina “gida mai dad’i” Ta fad’i hakan a k’asan ranta wani hawaye yana zubo mata. Abba bai tsaya ba, ana gama kwashe kayan dake motarshi yayi reverse ya fita. Ummu ce ta taimaka mata ta hau kujerar ta, daganan ta tura ta tayi ciki da ita, su kuma su Sakina suka mara musu baya. A parlourn suka tarar da Shuwa, ga mamakin kowa tana gani an shigo da Maryam sai ta fashe da kuka! Bata iya ci gaba da tsayuwa a wajen ba kawai tayi hanyar sama ta kyalesu, ganin haka yasa Baaba Talatu ta bi bayanta. D’akin da aka gyara mata a k’asa mai aikin ta nuna musu dan haka suka nufi d’akin da ita. An gyara d’akin sosai an wanke band’aki, an sa turaren wuta sai tashin k’amshi yake yi. Kuka Mama ta fara yi ana shigar da ita d’akin… Ummi ta san za a rina daman saboda tana tunawa nan ne d’akin Maman a lokacin da take budurwar. Da kyar suka lallasheta tayi shiru, tana tunanin rabonta da d’akin tun ranar da tabi Abba suka gudu! Bayan nan Ko tazo gidan, a tsakar gida ake tarar ta ko alwalla za tayi sai dai ta shiga band’akin tsakar gida, a hakan shima sai in ya zama dole ne kuma in Shuwa taga dama. Ita da Sakina ne suka kamata suka d’aura akan gadon dukda tanata ce musu “zata iya fa”. Favorite food d’inta Shuwa ta sa aka dafa, da mai aikin ta kawo tana bud’ewa suka saki murmushi a tare ita da Ummu. Ummu kalmar “Alhamdulillah” kawai take ta maimaitawa a zuciyarta, ga dukkan alamu Shuwa ta sauk’o! Allah yasa ta yarda ta yafewa Maryam a samu komai ya dawo dai dai kamar daa. Sai dare bayan Ummu ta tafi tukun Shuwa ta shigo. Kwata kwata Maryam ta rasa dalilin da yasa Hajiya Shuwan bata iya had’a ido da ita dan yanzun ma “ya jiki?” tayi mata ta kuma tambayeta “ko akwai abunda take buk’ata” ba tare da ta bari sun had’a ido ba. Da “a’a” ta amsa, dan haka tayi mata “Allah ya k’ara sauk’i” da “sai da safe” ta fice da sauri. Da daddaren ma abincin da Shuwa ta san Maryam d’in tana so tasa aka yi a gidan. A washegarin ranar da aka sallami Maryam aka sako ya Usman! Tunda Baaba Talatu taji labarin za a sake shi yau ta tafi gidanshi ta chake. Suna d’aki ita da Sadiya, suka ji k’arar bud’ewar d’akin shi dan haka suka nufi chan. Baaba Talatu tana ganinshi ta fara kuka haka ita ma Sadiya, sai da su Kaka suka daka musu tsawa tukun suka nutsu. Abinci kawai Baaba Talatu ta bari ya ci, daga nan ta cewa Sadiya “ta d’an basu guri” ko gama fita bata bari Sadiyan ta yi ba ta hau kwararo mishi bayanin halin da ake ciki. Tashin hankalin da ba a saka mishi rana!!! Tsananin tashin hankalin da Baba ya shiga ba zai fad’u ba! Gashi Kaka yace “wallahi ko a k’ofar gidan Madu ya ganshi sai ya tsine mishi!” Madu zai yi magana, Kaka yace masa “Dan Allah yayi shiru, kar yace komai” daga nan ya jaa hannunshi suka fita, suka tafi. Yadda Baba ya hargitse sai da Baaba Talatu ta yi dana sanin fad’a masa… K’arshema kuka ya saka mata, ga tsananin rad’ad’in ciwukan jikinshi ga rad’ad’in zuciya ga tashin hankali!! Kuka wiwi haka ya dinga yi kamar k’aramin Yaro. Shi har ga Allah ya shirya ne akan ….Bayan ya saketa! Ya san zata yi ta Allah Allah ta fita a idda dan ta auri Abba shima kuma Abban haka! Shikuma ana i gobe ko jibi zata fita daga iddar sai ya zo yace ya maida ita! A tunanin shi hakan zai sanya Maryam ta hak’ura gaba d’aya, dan ya san ta tun Yarinta bata son ayi ta ja mata rai akan abu........ BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 48 Da kyar aka samu Baba ya d’an nutsu Tukunna Baaba Talatu ta tafi da alk’awarin gobe da sassafe zata dawo! Washegari, tana zuwa ta tarar da Umma a d’akin tana kuka bata kai ga tambayarta ba Umman ta mik’a mata wata takarda, cikin kuka tace “Yanzu saboda Maryam shine zai tattara kaff ya tafi wajen Ya Jamilu saboda Allah? Ni kuma fa? Ni da y’ay’ana ba damuwarshi bace kenan?. Baaba Talatu rasa bakin magana tayi…..haka suka kasance Sadiya tana kuka ita kuma tayi zurfi a lissafi da tunane tunane ga damuwa kafin da kyar ta shiga bawa Sadiyan hak’uri har ta samu ta d’an nustu. A Washegarin, da safe kafin Ummu ta wuce office ta zo ta dubasu… A d’akin ta tarar da Shuwa itama ta sauk’o duba Maman. Sai da ta tabbatar komai yayi settlling Maman tayi wanka ta ci abinci tukunna ta fara shirin fita dan client d’inta already tana office tana jiranta… Tana mai cewa Huda “akwai bak’uwar da zata yi daga Maiduguri”. Daga haka ta sa kai ta wuce bayan Hudan tace mata “to, Allah ya kaimu.” Tace “Ammen”. K’arfe uku bak’uwar ta iso, mai gyaran jiki. D’aki guda Shuwa tasa aka ware ake gyarata ciki da waje….tun tana nok’ewa har ta sake, Sakina ita ma ba a barta a baya ba, dan duk abinda aka gogama Huda a fatarta itama sai ta goga Kafin sati biyu suka yi wani kyau na ban mamaki, in ka gansu kamar ka sacesu ka gudu. A lokacin bikin Hudan da Arshaad bai kai saura sati uku ba. A lokacin kuma k’afar Mama ta warke ba laifi, kasancewar transverse fracture ta samu shiyasa abun yazo da sauk’i, but still bata gama warkewa ba, so zata ke zuwa follow ups akai akai. Abba baya samun zuwa gidan ganin Mama, sai dai yakan zo ya karb’i ruwan karatu a wajen su Hudan time to time! Wani lokacin kuma yace kawai suyi addu’a daga gidan Arshaad ma daga inda yake , yake yi. Idan Abban yazo Hudan ce ke kai mishi a mota inda yayi parking, yana so ya shiga ya gaida Shuwa yaga jikin Maman amman bai san ta ina zai fara ba! Har yau yana tuno b’acin ran da ya gani a idanun Shuwa ranar daya kawo Maryam Madu kam suna had’uwa su gaisa da shi da Kaka wasu lokutan ma tare suke yin sallar Isha.. Haka nan yanaji yana gani in ya karb’a sak’on zai tafi, ga dai Maryam a kusa amman ba daman ganinta. Yana yawan kiran waya yace Hudan ta bata amma k’iri k’iri zata k’i karb’a, ayi ayi tak’i, k’arshe dai In ya kira sai Sakina ta karb’a ta sa wayar a speaker ta ajjiye akan gado, su fita da sauri… Tun Maman tana yi musu fad’a har ta daina. In suka dawo a inda suka ajjiyar wayar anan suke tarar da ita, Mama tayi ta mata fad’a amman gobe ma sai ta k’ara, in ta cika magana tace “Ai lada take nema, dan ita aure take shirin k’ullawa!” Dan haka kawai Mama sai ta daina fad’an ta daina biyeta, dan ta ga alamun kakarta ma take son mayar da ita, ita kuma bata shirya biyeta akan zancen Abba ba. A Satinsu na biyu ne Abban ya nemi su koma haka, Mama taso yin musu amman Shuwa tasa baki.. Sakina kam ta nace ba zata bi Hudan ba tace “ai yanzu ta saba da kowa” Sai da taga Huda na shirin yi mata kuka tana had’awa da magiya tukunna ta yarda zata bita a ranta tana tuno irin nacin Auwal da bataso! Dan wallahi ita saboda shi ne ma daa d’in tace ba zata bi Hudan ba! Bata san a ina ya samu nunbertaba amman kullum sai ya kirata bata gajiya da rejecting shi kuma baya gajiya da kira! Sai dare Abba ya zo d’aukar su, tun safe daman da ta san zasu tafi taketa nuk’u nuk’u Da suka zo tafiya kuwa sai da tayi kwalla! Ummu ce ta rakasu har mota (Sakina Hudan da mai gyaran jikinsu ) ta dawo. Tana shigowa d’akin ta tarar da shuwa tana lallab’a Mama Abun yayi matuk’ar burgeta dan haka ta zauna a gefe tana jin Shuwan tana cewa “Duk abunda hak’uri bai bada ba fushi da zuciya ba zasu kawo ba! kwanaki da kika d’aga hankalinki akan sai Hudan ta dawo hannunki, waye waye aka yi ta rikice dai kina kukan ya rabaki da y’arki hankalin kowa a tashe!. Yanzu ki gaya min a cikin wata d’aya da sati d’ayan nan da wa Hudan tafi zama tsakanin ke da shi? Ai ita y’a mace da Mahaifiyarta aka santa, ki ci gaba da bin komai a hankali wata rana sai labari! Kuma in dai za kiyi wa Abba adalci shima ya kamata ace ya d’an zauna da y’arsa kafin aurenta, kuma kinaji da kansa yace ‘In bikin ya rage saura kwana biyar nan zai dawo da ita a hannunki za a d’auketa!’ Wanne kalar adalci kuma kike buk’atar yayi miki sama da wannan??”….. Shuwa bata barta ba sai da ta tabbatar ta gwada mata gaskiya sannan ta d’an sauk’o tukunna tayi musu sallama ta tafi d’akinta. Ummu da Sumayya su suka ci gaba da zama da ita saboda Baban Sakina yayi tafiya tun wanchan satin. Arshaad ma yayi tafiya zuwa Uk da kuma garin da za suyi honeymoon d’insu… Yaje domin ya d’an yi settling accomodation da sauran harkar karatun su shi da Amaryarsa kafin su tarkata su yi chan gaba d’aya. Satinshi biyu, sai yau ya dawo shima (Washegarin ranar da su Huda suka koma GRA). Aslam ne yaje ya d’auko shi. Ba yadda Arshaad bai yi da Aslam ba akan ya kaishi ya fara ganin Hudan amman furr!! Aslam d’in ya k’i! Yace “ai shi ce mishi yayi yazo ya d’auko shi ya kaishi gida ba golden G Avenue ba.” B’ata rai Arshaad yayi, yana ji yana gani Aslam ya kaishi MT estate. Ko thankyou bai che mishi ba ya bud’e k’ofar fito ya bud’e baya ya d’au kayanshi yana ta b’ata fuska.. Yana shirin rufe murfin motar Aslam yace masa “Amm, by the way you are welcome” Yana d’an dariya k’asa k’asa. Rufe murfin motar Arshaad yayi ya juya shima yana d’an murmushi sama sama har ya isa gida. Yana shiga ya tarar da jakankuna, bai gama tantance na waye ba! Yaji anyi tsalle anyi hugging d’inshi ta baya. Yadda tayi masa ya riga ya san wacece dan haka ya fad’ad’a fara’ar shi ya sa hannu ya zare ta a jikinshi ya juyo da ita kafin yace “Wai ni sai yaushe za ki girma ne?” Turo baki gaba tayi, kafin tace “Ya Arshaad oyoyo d’in kenan? Da fad’a za a yi min sannu da zuwa?” Ta fad’i maganar tana hard’e hannunta a k’irji, sannan ta juya mishi baya alamun tayi fushi. Dai dai nan Aslam ya shigo, d’an murmushi yayi da ganinsu a hakan kafin yace “Har an fara ko? Oya! In kin gama fushin, wuce kitchen ki had’a min black tea. Yau duk kun gajiyar da ni da zirga zirgar airport wallahi, ga drivers a gida kamar me amman kowa In ya dawo daga yawon sa sai yace Ni!”. Sake turo baki Aaima tayi kafin tace “Ya Arshaad makarantar ne yawo? Shikenan naji ba komai duk na lura bakwa murna da ganina. Ina Mammy ne? Na duba ko ina bata nan! Ka ce mini bata da lafiya shiyasa ta kashe wayoyinta, meyene ya sameta tana ina ? Wallah duk hankalina a tashe yake, bafa ayi hutu ba ma na dawo! Dad shima same yadda kuke yi haka yayi min.” Ganin duk sun yi shiru sun kauda kai yasa ta k’arashe maganar tata a hankali tana mai cewa “kuyi min magana please”. Aslam ne yayi k’arfin halin cewa “Aaima, kawo min tea, ki huta kici abinci daganan sai mu yi magana ko?” Gani suka yi kawai ta fashe da kuka, cikin kukan tace “Ya Aslam dan Allah in mutuwa Mammy tayi ku fad’a min dan Allah.” Da sauri Arshaad ya toshe mata baki da hannunshi kafin yace “Mammy tana nan, kinji!! Babu abunda ya sameta, in fact zuwa anjima ma zan kaiki ki ganta, kin ji? Yanzu ki huta tukunna nima bara inyi freshening up, sai muzo ayi magana ko?” Cikin tashin hankali tace “Ba dai rabuwa sukayi da Dad ba, ko? Ya a....” Cikin tsawa Aslam yace mata “Idan kika bari na k’araso wajen nan sai na tattakaki wallahi!! Ba za ki wuce kiyi abunda akace ba?” Ta tsorata sosai da tsawar shiyasa ta zo ta wuce sum sum ta shige kitchen d’in jikinta na karkarwa, tana matsar hawaye. Sai da ta wuce kuma sai Aslam d’in yaga rashin kyautawarshi “Damn it!” Ya furta hakan chan k’asan mak’oshi, kafin a hankali ya rintse idanunsa… Shi kad’ai ya san me yake going through those days! Abun har tsoro yake bashi, shekaran jiya fa Gwaggo Asabe ya yiwa tsawa! Abunda bai tab’a tunanin zai kwananta yi ba ko da kuwa da wasa ne. Abunda ya kai yaji haushi da wanda bai kai ba gaba d’aya hassalashi suke yi! Haushin kowa yake ji! Ya tsani kowa ya tsani komai! Baya son shiga mutane, shiyasa shi kuma yake tilastawa kanshi ya dinga shiga mutanen saboda yayi fighting abunda ke shirin hargitsa rayuwarshi! But ko hirar minti uku ba a yi dashi ta kirki, zai fara fad’a. A hankali yace “Ya Allah ka yaye mini abunda yake shirin k’arasa tarwatsa rayuwata, Ya Allah ka ji k’aina.” Kallonshi kawai Arshaad yake yi, ya dai san magana yake yi amman baya iya jiyo abinda yake fad’a. Ya kusan minti uku a tsaye yana kallonsa, kamar zai k’arasa wajenshi sai kuma ya sunkuya ya d’auki suite case d’in shi da ta fad’i garin oyoyo d’in Aaima, ya jaa trolley d’inshi ya nufi side d’insa. Yana wucewa Aaima ta fito da tea d’in akan d’an karamin tray, ta ajjiye mishi tace “Gashi” Bata jira jin mai zai ce ba ta wuce sama itama don yin wanka. Ajiyar zuciya Aslam ya sauk’e, kafin yasa hannu ya d’auki cup d’in wanda yake ta uban tururi yayi sipping a hankali.. Da kyar ya iya had’iyewa sakamokon wani tururi da yake ji yana taso mishi daga k’irjinsa yana yowa sama.. He hates this! Yana disturbing peace d’inshi, kamar ya sa hannu ya kwakule heart d’inshi ya jefar haka yake ji… Takaici da ya isheshi ya sanya shi d’aga cup d’in ya kafa a baki ya hau kwankwad’a yana had’iyewa da k’arfi! Ko zafin tea d’in ba ya ji saboda wanda yake ji a k’irjinsa ya ninnika na tea d’in. Sai da yaga bayan tea d’in tukun ya hak’ura ya ajjiye cup d’in yana uban gumi, had’i da sauk’e ajiyar zuciya a jejjere. A hankali ya jinginar da kanshi da bayanshi a jikin kujerar yana sauk’e ajjiyar zuciya still kafin ya lumshe idanuwanshi… Sai bayan kusan minti talatin tukun Arshaad ya fito wanda kana ganin sa ka san zance zai je. Sanye yake cikin wani had’add’en fari k’al d’in yadi d’inkin boda, yayi matuk’ar karb’ar jikinshi, ya murza sky blue d’in hula zanna bukar sai kyalli take yi, sawunshi sanye cikin farin takalmi sau ciki mai mugun kyau, sai silver agogo da ya d’aura a tsintsiyar hannunshi. K’amshin turarenshi ne ya sanar da Aslam fitowarshi! Dan haka ya bud’e idanuwanshi da suka yi jaa ya zuba mishi. Suna had’a ido Arshaad ya d’auke kai ya tamke fuska yayi hanyar fita. Murmushi Aslam d’in yayi kafin yace “Irin wannan tamke fuska haka! So kake idan kaje ka firgitata?” Banza Arshaad yayi da shi ya ci gaba da tafiyar shi. “You promised Aaima akan za kuyi magana kuma zaka kaita wajen Mammy, remember?” Arshaad ya sake jin muryar Aslam d’in. Ajiyar zuciya Arshaad ya sauk’e, bayan ya tsaya cak! Ba tare da ya juyo ba dan har ya kai k’ofa. Yafi 1 minute a hakan, kafin chaan! Ya juyo ya fara takawa zuwa inda Aslam d’in yake zaune. A kan 3 seater yake zaune dan haka shima ya zauna a kai a gefen shi kad’an, cikin nutsuwa yace “Are you ready to talk?” Murmushi Aslam d’in yayi kafin yace “About?” Cikin d’an b’acin rai Arshaad yace “Ok!! Shikenan, kaga tafiya ta.” Ya fad’a yana mik’ewa tsaye. A hankali Aslam yace “Ka san dai akwai abubuwa da yawa a kaina ko? How kake tunanin zan fahimci wanne kake nufi?” Iska Arshaad ya furzar kafin ya komo ya zauna sannan cikin kulawa yace “Akan abunda yake damun ka kwana biyun nan nake so muyi magana! Ka chanja Aslam, Abba ma sai da ya kira ya tambayeni ko akwai abunda na sani yana damunka, dan ya tambayeka kace mishi ba komai!. Na tambayeka tun a waya kace ba komai, yanzu gani nan face to face so talk! Ka gaya min ko menene idan na addua ne in tayaka idan kuma na taimakone in taimaka maka I hate to see you like this! Dan Allah ka gaya mini ko menene i promise to help.” Murmushi Aslam yayi kafin yace “Ba komai fa Arshaad. Kawai matsalan Mommy ne daga shi ba komai. Ko kuna ganin halin da muke ciki ni da ita for years bai kai ya maidani haka ba?” Ya k’arashe maganar yana kafeshi da kyawawan idanuwanshi da har yanzu basu gama dawowa dai dai ba. Ajiyar zuciya Arshaad ya sauk’e dan ya fahimci Aslam bai shirya fad’a mishi matsalarshi ba tunda yayi haka kuma ya san ko ya tilasta ba sani zai yi ba….. Yana cikin wannan tunanin Aaima ta sauk’o, ta shirya tsaf cikin abaya blue black tayi rolling, tayi masifar yin kyau. A hankali ta k’araso inda suke tace “Ya Arshaad muje” Tana gama fad’in haka ta juya zata wuce Aslam ya rik’o hannunta. Sai da ta turo baki tukun ta juyo ta kalleshi. Bata san lokacin da murmushi ya sub’uce mata ba ganin ya kama kunnenshi d’aya da hannu d’aya yayi kalar tausayi. Zare hannun nata tayi da ke a cikin nashi kafin ta zauna tukunna tace “Allah ya Aslam gani nayi gaba d’aya kamar haushina kake ji, tunda fa ka d’auko ni kake ta wani hantara ta, kamar irin ka tsaneni d’innan. Ni Ina chan a skul ba ni da labarin da ya wuce naku amman na dawo duk baku ma yi murna da ganina ba.” Murmushi kawai Aslam d’in yayi kafin yace “Sorry Auta. Mun yi murna sosai. We good?” Murmushi ta d’anyi itama sannan ta d’aga mishi kai alamar ‘eh’. D’an guntun smiling Arshaad yayi tukun yace “Aaima mun samu newest member a family d’innan! Daughter d’in Abba. Na san kin san labarin Anty Maryam ko? To tanada y’a Hudan!” Cikin murmushi ya k’ara da cewa “Hudan dai da kika sani” Cikin zaro ido Aaima tace “Ma shaa Allah! Haba no wonder! Dama ba nayi ta ce maka tana kama da Abba da Ya Aslam ba kwanaki kace min a’a idonane kawai.” Ta fad’a haka da tsantsar farin ciki kwance akan kyakkyawar fuskarta. Kafin ta tashi ta fara juyi da d’n tsalle tana cewa “Alhamdulillah nima nayi y’ar uwa! Yanzu Gramma sai ta daina yi min tsiya ta daina cemin k’anwar maza yayar maza.. Tana Ina (Hudan)?” Sai kuma ta d’anyi jim! Tayi shiru daga baya ta zauna tukunna tace “Mai yasa Abba bai fad’a ba? Tun farko?” Ajiyar zuciya Arshaad ya sauk’e kafin yace “Anan za kiji dalilin da yasa baki ga Mammy a gidan nan ba!” ….Tiryan tiryan haka ya zayyano mata abunda ya faru tun daga farko har k’arshe!… Sharkaf haka fuskar Aaima ta jik’e da hawaye kafin ya k’arasa bata labarin. Yana yin shiru tace “Mammy tana cell? Yaya ka san inane cell kuwa?. Ina Hudan take? Ashe shiyasa na daina ganinta a wasapp rannan har kiran ta nayi tak’i d’auka, munafuka!!!” Cikin b’acin rai Arshaad yace “Watch your words, Aaima! Ni na hanata ta fad’a miki komai, ita kuma tace ba zata iya chattn dake ba tana yi miki b’oye b’oye, shiyasa na d’auki wayoyinsu ita da Sakina nayi blocking d’inki ba tare da su kansu sun sani ba! Na fi so sai mun had’u ido da ido tukunna in yi miki bayanin komai da kaina saboda na san haka ce zata faru! Ku mata k’aramar kwakwalwa gareku ba zaki duba circumstances da situations ba kawai wanda yake naki shi za kiyi sopporting! Yanzu ki nutsu tukun mu yi magana…” Mik’ewa Aaima tayi taje gabanshi ta tsaya idanuwanta na tsiyayar da ruwan hawaye ba k’akk’autawa wani nabin wani tace “Kenan kai supporting Hudan kake ko Yaya? Over Mammy, Yaya Mammy fa!!!” Ta k’arashe maganar cikin tsawa. Mikewa shima Arshaad yayi cikin fad’a yace “Bana sopporting kowa! In fact case d’innan ba a hannuna yake ba kuma ba a hannun Abba ko ita Hudan yake ba! A hannun Granpa yake dan haka in kinga zaki iya kina iya zuwa kiyi mishi wannan haukar..” Yana gama fad’an hakan ya juya ya fice fuuuu kamar zai tashi sama. A hankali ta durk’ushe a wajen ta na wani irin kuka mai chin rai. A hankali Aslam ya mik’e ya k’arasa inda take ya d’ago ta ya zaunar a kan kujera kafin shima ya zauna, ya fara lallashinta… Cikin kuka tace , “Ya aslam Hudan is bad news! Kaga fa daga zuwanta gidannan abunda ya faru.. Na tsaneta wallahi” “Shhhhh” Aslam yace, yana sauk’e ajiyar zuciya kafin yace “She’s his fiance, dole in kin fara jin haushinta tun yanzu zai yi fushi dake And Aaima zai fi miki sauk’i idan kika rungumi Hudan kuka zauna lafiya dan she’s family kuma gashi za ta sake zama family.” Cikin rashin fahimta tace “Noo Ya Aslam, kalla fa ka gani bata riga ta zama fiancé d’intasa ba amma ji yanda yake yi a kanta, what if ta zama?”. Murmushi yayi kafin yace “Saura sati uku bikin.” Da sauri Aaima ta kalle shi sai kuma ta fashe da kuka tana cewa “Kaga irin abunda rashin Mammy a kusa kan jawo ko? Ni Ina ma na san da wani engagement balle maganar aure! Kana gani fa Ya Aslam muna waya muna chattn kusan kullum amman no one even bothers to tell me…da ga zuwan Yarinya ta hargitsa gida yanzu tana shirin hargitsa zumunci sannan a haka kace ba bad luck bace ba?” Lumshe idanunsa kawai Aslam yayi yana nan zaune a yanda ta barshi ya na jin ta. Cinkin kuka tace “Wallahi Ya Aslam kar ma ku bari In had’u da Yarinyar nan! Bana jin akwai wanda yake jin tsanar d’anuwa kamar yanda nake jin tsanar Huda a raina a yanzu atake naji tsanar ta ta dabaibaye ni. Ko da wasa muka had’u Allah sai na illatata! Tayaya ma za a bar Ya Arshaad ya aureta bayan na tabbatar da Mammy ba zata so ba.” Cikin kukan ta sauk’o ta durk’usa a gaban Aslam sannan ta hau jijjigashi tana cewa “Dan Allah in kowa yak’i fad’a mishi gaskiya Ya Aslam kai ka gaya mishi….in dai yana neman albarkar aure tou kar ya kwaso ta! Mammy ba zata saka ba na sani kuma ya kamata ya fahimci bad luck ce ita.” Surutun Aaima ya isheshi har ga Allah, dan tun d’azu daurewa kawai yake yi, hakan yasa ya bud’e idanunsa da niyyar yi mata magana ya ga ta zabura ta jaa baya a firgice. Cikin tsananin mamaki take kallon yadda kwayar idanunsa suka yi wani irin jaaa lokaci guda. A hankali ya mik’e sannan yace mata “Kiyi hak’uri Aaima, na san dole za kiji zafin rashin Mammy a kusa. Bara inje in d’an huta, anjima kad’an zan dawo mu je dake kiga Mammyn.” Yana gama fad’an haka yayi hanyar fita da sauri ya fice dan so yake yayi nesa da Aaima a yanzu saboda gudun aikata aikin da na sani........... BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 49 An gama yi mata gyaran jiki kenan, Arshaad ya zo. Dama tunda ya kira ta yace ‘gashi nan zuwa’, tayi sauri ta tashi akan turaren wutan da take a kai ta fad’a wanka. Tana cikin d’aura d’ankwalinta ta fara jiyo hayaniyar shi da su Sudais! Kasancewar a d’akin k’asa suke yin gyaran jikin. Loose gown ce a jikinta kalar kwanduwar kwai mai haske, dan haka kawai ta d’an d’aura d’ankwalin ta zagayo da edges d’in ta bayan k’eyarta ta sake su suka zubo akan k’irjinta wanda hakan yayi kamar mayafi saboda d’ankwalin yana da d’an girma. Waya ya fara mata dan haka tayi sauri ta fita, ta bar Sakina wadda ake k’arasa mata nata yanzu. Bai ga fitowarta ba, dan haka ya sake d’aga wayar yayi dialing numberta ya kara a kunnenshi… Har ga Allah baya iya b’oye zalamarshi when it comes to Hudan! Y’ar tafiyar nan da yayi ya sanya ya sake fahimtar tsananin mugun k’aunarta da yake yi! Duk da cewa suna waya amman ji yake kamar yayi irin shekarar nan bai ganta ba! Ko dan tak’i yarda su yi video call ne may be shiyasa, he wonders why tak’i yarda suyi video call d’in Sakina dai tace mishi gyara ake mata kuma in ya ganta idan ya zo ba lalle ya biya kud’in gyaran da kyau ba, ba yadda bai yi dasu ba amman fur itama Huda tak’i yadda ta bashi had’in kai ya gantan… Yana cikin wannan tunanin ya fara jiyo wani k’amshi mai mugun fitinannen dad’i, a take yaji jikinshi ya mutu! A hankali yake jin k’amshin na sake shigar mishi hanci yana sake karad’e ko ina yana sake kashe mishi jiki.. Sai da ta kusan k’arasowa inda yake tukunna ya samu k’arfin jikin juyawa sakamokon jin takun tafiyarta wanda flat shoe d’in k’afarta ke badawa… Yana juyowa suka had’a ido! Tsayawa kawai yayi ya kasa ci gaba da motsi, kamar wani statue. “Ya Arshaad wayarka” D’in da Sudais (waenda suke tare dashi a parlourn, d’an gefe kad’an da shi) yace masa ne ya d’an dawo dashi daga duniyar da ya lula. A hankali ya rik’o wayar wadda ta kusan zamewa daga hannunshi kafin ya iya cewa “Lafiya, ya gida?” Still yana kallonta. Hudan ita kuwa kunyar kallon take ji, dan haka ta fara kame kame ta kasa cewa komai bayan gaisuwar da tayi masa. Sun yi kusan minti biyu a haka! Ganin bashi da niyyar d’auke idanunsa daga kanta yasa ta sake cewa ”Ya hanya? Ka dawo lafiya?” “Alhamdulillah” Ya ce kawai ya ci gaba da abinda yasa a gaba… Wani irin kallo yake yi mata, tun daga kan y’an yatsun k’afarta har kan d’ankwalinta idan ya dire sai ya sake komawa daga inda ya faro kamar ya samu tv. Ganin abun nashi ba na k’are bane ba yasa tace “Ya Arshaad dan Allah ka daina kallona” Tana rufe fuskarta da tafin hannunta, a shagwab’a. Hakan da tayi kuwa ba k’aramin kyau ya k’ara mata ba. Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace “Sorry na daina. Ina Sakina? Kice tazo ta karb’i tukuici mai tsoka.” Ya fadi hakan a kasalance still bai daina kallon nata ba sai dai yanzu ya fara motsi ba kamar d’azu da ya k’ame ba. Cikin son kawo k’arshen kallon tace “Ana yi mata gyaran jiki, in ta gama zata fito. Ka je kaci abinci yanzu, da kaina na yi maka girkin.” Ta fad’a tana sunkuyar da kanta k’asa. Wani sassanyan murmushi Arshaad yayi, yana mai jinsa a sama! Farin cikin da yake ciki yau anya zai iya misaltuwa kuwa? Cikin murmushin yace “Anya Huda ranar da aka ce an d’aura mana aure ba zan mutu dan dad’i ba kuwa?”. Da sauri ta d’ago ta kalleshi, sai kuma ta tura baki ta kauda kai ta d’an b’ata rai. Dariya yayi this time around kafin yace “Sorry tou, ba zan suma dan dad’i ba kuwa? Just looking at you fa da kuma jin wai kin yi min girki da waennan kyawawan hannayen naki! Wallahi ji nake kamar in yi ihu dan murna, Ina kuma ga in akace kin zama mallakina gaba d’aya?” Dariya ta d’anyi tana me sunkuyar da kanta k’asa, kafin tace “To muje kaci kar ya huce”. Ya lura ta gaji da kallon shiyasa take ta so su bar wajen ta samu su daina facing d’in juna, dan haka yayi murmushi kawai kafin yace “Mu je tou” A ranshi ya raya ‘I can’t help it, ni kaina inaso In d’an janye idon but na kasa.’ Ita tayi serving nashi bayan sun isa dining d’in, kamar yanda yayi zato kuwa, tana gamawa ta nemi kujera ta hud’un wadda yake kai a side d’inshi ta zauna. Dariya ta bashi dan haka sai da ya d’anyi dariyarshi tukun ya mik’e yaje inda take yace “Tashi ki ga” Rau rau tayi da ido za tayi magana yace “Shiiii, taso” A hankali ta mik’e ta bishi. Sai da ya zagaya d’ayan side d’in tukunna ya zaunar da ita a kujerar da take setin tashi Kamar za tayi kuka tace “Ya Arshaad to kar ka kalleni” Dariya yayi yace “Tou” kawai, ya zagaya ya zauna ya fara cin abincin shi yana santi yana kallon nata da bata so. Ko plate d’in abincin baya kalla, kawai spoon yake sakawa ya d’ebo ya kai baki, dad’i har kwanyarshi. Suna a haka Sakina ta fito, jin an bud’e k’ofa kuma an nufo dining d’in ne ya sanya ya d’an juya. Murmushi yayi kafin yace “Ta hannun dama! Kina da babbar kyauta yau.” Cikin dariya Sakina ta k’araso suka gaisa tayi mishi sannu da zuwa. Fitowar Abba wanda zai fita ne yasa tace musu “tana zuwa” tabi bayan Abban wanda ya nufi waje bayan sun gama gaisawa da su Arshaad d’in. Ganin ta biyo shi ne yasa ya d’an tsaya a y’ar varendar bakin main door d’in, tana k’arasowa Auwal shima yana isowa wajen! Ai kuwa ta had’e rai ta cuno baki ta d’auke kai. Shi kuwa Auwal gaba d’aya numfashinsa sama yaji yayi, da kyar ya samu ya seseta kanshi, ya shiga gaida Abba cikin nutsuwar da Abban bai tab’a saninshi da ita ba. Murmushi Abban yayi bayan sun gaisa yace “wuta da auduga” yana kallon Sakinar da ta d’an kalleshi kad’an, kunya ce ta rufeta dan haka tace “Ya auwal Ina wuni” Murmushi yayi wanda ya baiiyyana dimple da tsantsar kyawun fuskarshi, kafin yace “Lafiya, ya gida? Kwana biyu” Cikin takaici tace “Alhamdulillah” Abba ne ya katsesu ta hanyar cewa “You were saying?” yana kallon Sakina had’e da kallon agogon dake d’aure a tsintsiyar hannunshi. Bataso yin maganar a gaban Auwal ba amman ba yadda ta iya, hakan yasa tace “Um daman Abba, wai pre wedding picture nake so inyi surprising su Hudan da shi, In ba damuwa, please.” Dan k’uraa mata ido yayi, kafin yace “Okay, banda shirme.” Sannan ya juya har zai wuce sai kuma ya juyo yace “Kina buk’atar cash ko?” Yayi maganar yana mai zura hannunshi a aljihu. Dasauri Auwal yace “No. Abba I’ll take care of it.” “Okay” kawai Abban yace, dan sauri yake yi, yayi gaba ya bar su a wajen. Murmushi Auwal yayi kafin ya dawo dai dai setin Sakina inda ta kawar da kai ta mayar da fuskarta ta, yace “For this surprises sake za a d’an kula ni ko? Na wuni d’aya tak dai?” Ya k’arashe maganar yana karyar da wuyanshi sannan ya maida fuskarshi kalar tausayi. Kallonshi tayi, bakinta na d’an motsi, tana son yin magana amman yanda idanuwanshi ya sarke da nata ne, ya sanya ta kasa cewa komai. A hankali ya lumshe idanunsa ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciyar da har sai da ta jiyo hucin numfashinsa mai d’umi wanda ya had’e da wani calm scent da kuma k’amshin turarenshi… tana shirin d’auke idanunta daga kan kyakkyawar fuskarshi, ya bud’e idanunshi cikin hikima ya sake yin nasarar sark’e kwayar idanuwan nasu waje d’aya, a hankali taji yace “I love you!”. Gabanta ne ya bada wani ‘Dumm!! Da masifar k’arfin da bata san dalili ba.... Da kyar ta aro jarumta ta yafa, da mugun k’ok’ari tayi nasarar zare kwayar idanunta a nashi k’irjinta na ci gaba da dukan uku uku. Harara ta zabga masa, ba tare da ta yarda ta sake kallon cikin idanunshiba had’e da yin tsaki sannan ta juya da mugun sauri zata shiga ciki..a ranta tana aiyyana ‘Tabbas Auwal tantirin shed’an ne!’ Dan gashi yana k’ok’arin rusa mata tsari cikin mintunan da basu gaza ashirin ba… Da kyar ya iya had’a kuzarin da ya bashi nasarar shan gabanta, ya tsaya a bakin k’ofar, dan ba k’adan ba jikinshi yayi mugun yin weak! Da sauri ya had’a hannuwanshi biyu waje d’aya kafin yace “I’m sorry? so sorry ba zan k’ara ba. Please lets just.. Bari in kira wanda na san zai yi, a Kano yake yanzu nan zai zo, professional ne, okay?” Ya k’arashe maganar da alamun serious a kan fuskanshi, yana mai d’aga mata gira duka biyu da d’an ware ido. “Unhm” Kawai tace sannan ta koma gefe tayi folding hannayenta tana kallon wani waje. A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya, ya fara k’ok’arin dialing number mai hoton…. A gabanta suka yi waya sukai fixing time @5:00 pm Zai k’araso, nan da 2 hours kenan. Suna gama wayar tace “thankyou” kawai sannan ta fara k’ok’arin wucewa. A hankali yace “Am, Sakina… i”. Da sauri ta d’aga mishi hannu d’aya, alamar (stop) Kafin tace “Ya Auwal please.. Ka kyale ni! Bana so!. I’m in a very serious relationship, besides ko ma bana dating d’in kowa I will never ever choose you! After what you did to Jalila kuma still ka ke dodging.. Kullum ko sunan ka naji an kira abunda nake tunowa kenan!. Ban shirya auren bazawari ba, ko da ace maza sun k’are ina rok’on Allah kar ya d’aura min k’addarar auren bazawari second hand.” Auwal bai san san ya akai ba, amman tabbas kamar hawaye yake ji suna shirin zubo mishi. Ita kanta Sakinar ta lura da yanda idanunshi suke kyallin hawaye. Jikinta ne ya d’anyi sanyi dan haka ta yi k’ok’ari ta danne ragowar maganganun da take ji suna taso mata. A hankali yace “Sakina na rantse miki da Allah a yanda nake jin ki a cikin zuciyata, ba abunda ba zan iya sacrificing akan ki ba, kuma babu abunda ba zan iya yi a kanki ba, zan iya chanja kaina in koma yadda kike so na zama, muddin zaki yarda da ni. I don’t know how why but ni kaina ina jin tsoron kalar k’aunar da nake yi miki! I just knew you but i have fallen head over heels… Na tabbatar ba wanda ya tab’a yiwa wata kalar pure love d’in da nake yi miki.. Ba wai wani abu daban ba kawai k’aunarki, yardarki, soul d’inki shi nake muradi.” Ya k’arashe maganar cikin karyewar zuciya. Shiruu, tayi kawai tayi k’asa da kanta, bata k’aunar abunda zai sa ta sake had’a ido da shi. A hankali tace “Ka rabu da ni! Dan Allah.” Yana shirin yin magana Arshaad ya bud’e k’ofa Hudan na a bayan sa. Juyawa Auwal d’in yayi aka hau kallon kallo..,, Arshaad ne ya katse shirun ta hanyar mik’awa Auwal hannu suka yi musabaha, a hankali Hudan ita kuma ta gaidashi. Yana amsawa ya wuce ya nufi part d’insu yana ji kamar zuciyarshi zata fashe! Tabbas ya san ba komai ke binshi ba sai hakki..Hakkin y’an matan da ya yaudara, da waenda ya wulak’anta, da waenda yayi mocking soyayyar da suke yi mishi! Duk hakkin su ne yake binshi. Yayi mocking soyayya, ya yaudari dayawa ta hanyar kalmar soyayya, ya wulak’anta dayawa dan sun nuna mishi zallar soyayya, shiyasa shi kuma yanzu Allah ya d’aura mishi tsantsar so mai mugun zafi da azabtar da zuciya wanda ya san wadda yake yi wa ba lalle ta soshi ba, gashi yanzu ma direct ta fad’a mishi ‘she’s in a very serious relationship’ wanda hakan sai da ya kusan kasheshi ba tare da ta lura ba. Daman haka so yake? Dama haka mutum yake ji? Tabbas shi kam ya san ajalinshi..dan muddin Sakina bata yarda dashi ba akwai matsala! Ranar kuwa da akace ta auri wanda take ik’irarin suna tare d’in ya san a ranar zai bar duniya…… Yana wannan lissafin da tunanin ya k’arasa b’angarensu, direct side nasa ya nufa, yana zuwa ya rufe ko Ina ya k’ara k’arfin ac ya zxube a kan kujera, ko d’aki kasa k’arasawa yayi.......... Hudan ta bud’e baki kenan zata yi magana Sakina tayi sauri ta wucesu ta shige ciki. Direct sama d’akin Hudan ta nufa, ta dad’e ta kusan awa d’aya tana juyi a kan gado ita kad’ai, daga baya ta hak’ura ta sauk’o. Suna zaune suna hira su Sudais suna gefe suna chess, tun da suka dawo daga karb’o gown d’in ta (Hudan) wadda delivery man ya kawo suke zuba idon ganinta amman bata sauk’o ba, Hudan taso zuwa amman Arshaad ya hanata… .....Sakina bata dace da Auwal ba at all, amman in haka Allah ya tsara basu da damar shiga tsakani, besides yayi mamakin changes d’in da yake gani a Auwal those days, maybe in ya samu wadda yake so ya aura a samu ya nutsu! Ko a office yanzu ya daina biye biyen matan da a daa yake yi kamar bunsuru.... Arshaad, yana wannan tunanin yaji sauk’owarta dan haka ya juyo yana kallon yanda take tafiya a hankali kamar ba Sakina ba. Cikin kulawa yace “Sai yanzu?” Murmushi tayi tace “Bacci ne ya kwashe ni” Shima murmushin kawai yayi Hudan kuwa bata ce mata uffan ba… So take sai sun keb’e tukunna dan tabbas In tunanin ta ya bata dai dai to Sakina tana k’ok’arin rufta kanta inda dai dace ba. Suna zaune Auwal ya shigo, kujerar da Sakina ke kai 2 seater yaje ya zauna ya fara yi mata magana k’asa k’asa.. Ga mamakin Hudan sai taga Sakinar ta biyeshi, suna ta k’us k’us daga baya kuma ta mik’e ta cewa Hudan “ta zo taji”, shi kuma ya mik’e ya juya ya nufi hanyar fita. Binta Hudan tayi, suna kaiwa hanyar bene ta rik’o hannun Sakinar wadda ta fara taka stairs.. Juyowa tayi tana kallon ta, k’asa k’asa Huda tace “Sakina kar fa ki biyewa Ya Auwal! Naga kamar ya fara cin galaba a kanki. Kin san Allah kuwa dan iska ne! Ranar da muka je Munjibir park baki ga y.....” Da sauri Sakina ta matsa kusa da ita ta sa hannuta ta toshe mata baki! Tun lokacin da Hudan ta fara magana taga tahowarshi, tana so ta hanata taga ya sa hannu ya d’aura akan lips d’inshi alamun tayi shiru yana d’an murmushi Bama jin Hudan take yi sosai ba saboda gaba d’aya hankalinta ya tafi wajenshi sai da taji tana neman b’aro musu aiki tukunna... Kallonta Hudan take, tana “hum um hum um” Alamun ta saki mata baki. Ganin tak’i barinta ya sa ta sa hannu ta janye hannun Sakinar akan bakinta kafin tace “Dan na fad’a miki gaskiya shine kike k’ok’arin kasheni? Har da hancina fa kika toshe. Kin san Allah, tou su Ummu zan gayawa dan ba zai yiu inaji ina gani ki kula d’a is....” Da sauri Sakina tace “Shhh, behind u.” Tsit! Hudan tayi kamar ruwa ya cinye ta, a hankali kuma ta juya… Karaff! Suka had’a ido da Auwal, yana d’an murmushi yana kallonsu. Hudan ta san gaskiya ta fad’a, amman sai ta tsinci kanta da jin mugun kunyar shi… Juyawa kawai tayi ta haye sama, Sakina kuma ta tsaya, ta fad’a mishi amsar abinda ya manta bai tambayeta ba, har ta kaishi ga dawowa. Bata dad’e da shiga ba Sakina itama ta shigo. A parlournta ta sameta, dan haka ta zauna akan hannun kujerar da take kai kafin tace “Hudan, dan Allah ki daina had’a ni da wannan mutumin, na fad’a miki ba zan tab’a sauraron sa ba, infact kin san ina da wanda zan aura ko?. Kinaso ki san maganar me muke yi?” Sai da ta d’an k’uraa mata ido, tukun tace “Eh” Murmushi Sakina tayi kafin tace “Zo muje d’aki to ki shirya, in yaso muna sauk’a k’asa zaki gani. Kamar tayi mata musu, sai kuma ta mik’e ta bita. Suna shiga taga Sakina tanata fito da kayan kwalliya, aikuwa tace bata san zance ba! Dan in akwai abinda Hudan ta tsana to a shafa mata foundation da concealer, ji takeyi kamar anyi mata suminti a fuska, sometimes har numfashin ta take ji yana d’an yin sama sama, bata tab’a jin iskar gari sai ta wanke.” Ba kalar rok’on da Sakina bata yi mata ba, amman furr tace “wallahi ba da itaba, ko me za ai sai dai ayi a haka” ita a tunanin ta ma ko wani get together su Sakinar suka had’a, dan tace mata surprise ne suka had’a musu ita da Auwal. Abunda kawai ta tsaya Sakina tai mata shine, eye lining..da kyar ta yadda ta ja mata liner black a saman ido d’an kad’an, sannan tasa mata brown kwalli. Ko dan bata saba yin kwalliyar ba ga kuma gyaran jiki da ta sha! Ya sanya Inka kalleta ba lalle ka iya d’auke idonka lokaci d’aya ba. Ita kanta Sakina ta kasa yin shiru da ce mata ‘kin yi kyau’. Akwai wani sirrin da idanun Hudan yake dashi wanda bata tab’a gani a idon kowa ba, gashi kuma yau yasha liner da brown kwalli. Wata zazzafar gown ta d’auko mata black, da ta ji silver stones, sai kyalli take yi. Tun daga k’irjinta zuwa k’asan mararta a tsuke ne daga nan kuma yayi wani irin bajewa har k’asa. Wani fitinennan tauban Sakina tayi mata wanda ya yi mata mugun kyau, sannan ta sak’ala mata wasu arnen silver sark’a da y’an kunne masu shek’i da abun hannunsu da zoben sai silver takalmi ta bata ta saka. Sannan ta d’auki set d’in kaya kala biyu suma duk English Wears kasancewar bata da wasu native masu kyau. Kafin tace “muje suna jira.” Har ta kai k’ofa taji shiru, juyowa tayi tana kallonta tace “Me ne kuma?” Hararar ta tayi tukun tace “A haka kikeson in fita da wannan matsarsen rigar?” Ajiyar zuciya Sakina ta sauk’e kafin tace “Hudan ana jiranmu, ga vail d’in nan a jakar nan na had’a In muka sauk’a sai in baki” Ba don taso ba tabi bayanta suka wuce, dan ta san tunda ta nace tou ba zata bata ba sai sun sauk’an. Ita kuwa Sakina batayi niyyar batan bane, ta gama rayawa a ranta ‘ko hoto d’aya ne sai anyi musu da wannan shigar’ ita tayi tauban d’in amman ba k’aramin tafiya yayi da imanin ta ba, dan haka bata ga dalilin da zai sa ta bata mayafi ta d’aura akai ba. Suna sauk’a suka tarar da mai hoton har ya k’araso da yaranshi dan haka suka fara…… Da kyar Hudan ta yarda ta tsaya aka yi kala uku da d’aurin daga su ta ware tayi rolling abunta. Styles Sakina ta dinga d’aukowa a insta tana nunawa.. Auwal ne yaje har gida ya d’aukowa Arshaad kaya shima kala biyu! Suite kalar kwanduwar kwai dark da kuma black d’in jamfa na yadi Suite d’in yayi using a last pics d’in da suka yi Ita kuma riga da skirt kalan suite d’in nashi tayi roling da black vail Sunyi masifar yin kyau!. Sai bayan Magrib aka kammala. Sun yi hoton har da su Sudais sannan aka yi da Auwal da su Sudais Abun sai ya zama kamar event a tsakaninsu su shidda dan har drinks da snacks suka d’auko suka d’an cicci suka yi videos a wayoyinsu........... Masu hoto suna tafiya Abba yana dawowa..A parlourn ya samesu har Auwal suna zaune suna kallo. Dai da mazan suka yi isha tukun suka zagaya gidan Daddy dukkansu aka yi dinner daganan kowa ya kama gaban shi bayan Arshaad ya karb’a ruwan adduar su...... Akwai maganar da yake so suyi da Aslam amman takaicinshi yake ji shiyasa kawai ya rabu da shi ya nufi gida.. D’azu babu yadda bai yi da shi akan ya kawo mishi kaya kala biyu ba za ai pre wedding amman k’iri k’iri Aslam d’in ya k’i! K’arshema da yayi ta kiranshi k’in d’aukar wayar yayi. A parlour ya ga Aaima ita kad’ai tana shan tea akan dining, har zai wuce ta kawai, sai kuma duk yaji ba dad’i tausayinta ya lullub’e shi, dan haka ya koma ya ja kujerar kusa da ita ya zauna. Bata ce mishi komai ba ta ci gaba da kurb’an tea d’inta. Sai da ya zauna tukun ya fahimci ashe kuka take yi! Dafe kanshi yayi ya furzar da iska kafin yace “Ok, I’m sorry! Kin b’ata min rain ne d’azu sosai Aaima.. Ba zai yiu ki tsani Hudan haka ba! Za a samu matsala..Hudan ta zame miki dole! Ki ajjiye duk issues d’inku da ita aside, ki manta ki yafe She’s about to become my wife! Kar ki zama silar rusa zumunci da raba kan y’ay’anmu da naki in the future..” Murmushin takaici Aaima tayi ta ajjiye cup d’in hannunta kafin tace “Do you know what the funny thing Is?” Bata jira jin mai zai ce ba, tace “Ya Arshaad ban ma san za ka yi aure ba! So i think ba ni ce zan zama silar raba zumunci ba! Kai ne! Infact ka riga ma ka raba dan wallahi ba k’aramin haushi na ji ba ba zan b’oye maka ba Iya wannan banzatar dani d’in da kayi ya isa zumunci ya samu tangard’a!” Cikin son fahimtar da ita yace “Aaima, an saka date d’in a k’urarren lokaci I have a lot to discuss with you, inaso In ganar dake abubuwa da dama kafin In sanar dake shiyasa kika ga ban fad’a miki ba! Issues d’in are all tied up In na gaya miki zan yi aure dole za ki buk’aci Mammy! anan ne kuma za a samu case, na sani. But I was planning inje in d’auko ki a week b4 daga nan in miki bayani ta yanda zamu fi fahimtar juna.. Mu uku ne kawai Aaima kece mace dan Allah kar ki fara irin haka tun yanzu, please..” Ajiyar zuciya ta sauk’e, kafin ta kalleshi eye to eye, babu alamun wasa ko tsoro tace “Wallahi!! Muddin Hudan zaka aura to tsakanin mu ba zai yi kyau ba!.” Tana gama fad’in hakan ta mik’e ta bar mishi wajen a fusace… Sai da ta kai stairs tukunna ta juyo tace “Ya Aslam bashi da lafiya, Yana side d’insu ana k’ara masa ruwa. Kaje ka kula da shi pls, shi kad’ai ne, ni kuma yak’i yarda In zauna da shi, sai amai yake yi.” Har tayi gaba kuma sai ta sake juyowa tace “If Hudan permits.” Bata sake juyowa ba tayi sama abunta. Ya dade a wajen, tukun ya mik’e ya je ya watsa ruwa ya sa pyjamas ya nufi gidan su Aslam d’in: Direct d’akin sa ya wuce bayan ya bawa Gwaggo Asabe ruwan adduar. Akan gado ya ga cannula da bandage da alamun wadda aka saka mishi ce ya cire! Yana shirin fara neman shi ya jiyo shi a toilet yanata shek’a amai. Toilet d’in ya nufa ya tura k’ofar ya shiga.. Sai da gabanshi ya fad’i ganin yanda duk Aslam d’in ya fita daga haiyyacinshi cikin wuni guda tak!. Taimaka mishi yayi suka fito bayan ya yi brush ya wanke fuskarshi. Yana kwantar da shi ya d’auki waya ya kira Doc.. Bayan ya ajjiye wayar, cikin sanyin murya yaji Aslam d’in yace “Yanzu fa Doc d’in ya tafi, wanne kuma ka kira?” Banza Arshaad yayi da shi kawai yaci gaba da had’a mishi tea d’in da ya fara. After kamar 20min haka, Doc d’in suka shigo tare da Gwaggo Asabe…. Sai da ta sa baki tukunna ya yarda ya tsaya aka sake duba shi, dan shi already ya riga ya san me yake damunshi tun kafin zuwan first Doc d’in kuma baya so Arshaad d’in ya sani… Ba yadda ya iya shiyasa kawai ya kyalesu, bayan y’an gwaje gwaje Doc d’in ya tabbatar musu da ‘jininshi ne ya hau sai kuma fever mai zafi da ta ke damunshi.’ Gwaggo Asabe har da kukanta take ce mishi “Jikin Mommyn fa yanzu da sauk’i Alhamdulillah Gashi kusan satinshi biyun a gidan amman shiru bata yi komai ba! Ta warke sosai fa, ita abun har mamaki ma yake bata, amman in ta tuna yadda aka duk’ufa akan neman lafiyarta ta hanyar kad’aita Allah shi kad’ai da taimakon ayoyin shi, sai ta ga ba abun mamaki bane ba!” K’arshema cewa tayi “ya taso suje ko da ta window ne ya lek’a ya ganta, in ba fad’a maka akai ba ba zaka tab’a yarda ma ta tab’a yin rashin lafiya ba! Har waya fa suke yi da Dad”. Shiruu, kawai Aslam d’in yayi a zuciyar shi yana godewa Ubangiji, sannan yana adduar Allah ya kawo ranar da zata warke baki d’aya su zauna inuwa d’aya shi da ita….. A d’akin suka zauna bayan Doc ya tafi, shi Aslam har haushi ma suka fara bashi dan sai kace wani jariri haka suka maidashi wai duk dan Doc yace kar a barshi da damuwa ko loneliness. Sai wajajen 11 Arshaad ya k’arasa karatunshi shi da Aslam da Gwaggo Asabe tukun yayi musu sallama ya tafi bayan ya tabbatar Aslam din ya sha maganinshi. Dariya Arshaad yake bawa Aslam, shi ala dole fushi yake yi dashi wai akan yak’i fad’a mishi damuwarshi dan ko kallonsa ma baya yi amman kuma shi yayi jinyar shi yanzu. Arshaad, ya fito kenan a babban parlourn suka had’u da Jalila, yayi matuk’ar mamakin ganin yanda ta rame. Bai kula ta ba ya d’auke kai kawai ya yi wucewarshi, ga mamakinshi shi kawai yaga tasha gabanshi ta tsaya. Tamke fuska yayi kafin ya tsareta da lumsassun dogayen idanuwanshi cikin dakakkiyar murya yace “Jalila!” Jin yanda ya kirata, da yanayin data ganshi ya mugun tsoratata dan haka ta kasa magana ta kasa cewa komai chaaan! Kuma sai ta hau kame kame tana wasa da y’an yatsunta “Em, Ya Arshaad wai dagaske Gwaggo Asabe take?” “Da gaske take me?” “Maganar aurenku kai da Huda…” Sai kuma ta fashe da kuka. Da mamaki yake kallonta kafin yace “Eh” Kawai ya juya ya fita dan ya san indai ya ci gaba da tsayuwa Inuwa d’aya da ita tou tabbas za a samu matsala! Ya san babu kyau ka tsani d’an uwanka musulmi but he cant help it! Wallahi tunda yake a rayuwarshi bai tab’a jin tsantsar tsagwaron tsana kalar wacce yake yi wa Jalila ba. Da gudu tayi hanyar d’akin ta tana zuwa ta dannawa Umma kira! Ko gaisawa bata bari sun yi ba ta fara magana “Umma, Huda aure zatayi! Ya Arshaad zata aura. Umma wallahi mutuwa zan yi in ya aureta Umma dan Allah kiyi wani abun, wallahi ina sonshi.” Cikin katseta Umma tace “Dalla malama ki tsaya ki nutsu kiyi min magana yanda zan fahimceki” Cikin kukan jalilan ta hau yi mata bayani tiryan tiryan akan yadda taji Gwaggo Asabe suna maganar auren ita da wata mai aiki satin baya daya wuce data tambayeta kuma ta gasgata mata hakan sannan yanzu ma Arshaad d’in ya sake tabbatar mata. Cikin b’acin rai Umman tace “Kece ai Jalila da shegen son abunki! Nace miki ki kawo kud’i kin k’i ki bayar ya kikeso in yi? Babanku ma yanzu haka baya nan ya gudu saboda ba zai iya rayuwa ba Maryam ba! Ga Ja’afar ba lafiya! Ga Junaidu ya b’ata! Matsalalo gasu nan burjik sunyi mana yawa ke kuma kin matse bakin aljihu ya kike so inyi???. Ni kaina sai na mutu dan bak’in ciki in dai Huda ta auri Arshaad d’innan ba ke kad’ai ba! Haba dan Allah mana sai kace su kad’ai Allah yake so?? Baban ta mai kud’i sannan ta auri mai kud’i! Inaa, ba zai yiu ba gaskiya!” Umman ta k’arashe maganar cikin tsananin tashin hankali. Cikin kuka Jalila tace “Umma yanzu meye abun yi? Dan Allah karta aure min shi wallahi Umma ina son Ya Arshaad sosai.” Ajiyar zuciya Umman ta sauk’e kafin tace “Ki bani kud’i! Ki turo kud’i! Ki zuba mini ido kawai, shine abun yi.” A hankali Jalila ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace “Tam shikenan, Ta accnt d’inki ko?”. “Eh” Kawai Umman tace saboda tsantsar tashin hankalin da take ciki ba zai iya barinta tayi magana sosai ba. “Tam” kawai Jalila tace ta kashe wayar daganan ta tura mata ragowar kud’in accnt d’inta da ta ishi Auwal, ya tura mata da kyar.............. Bayan Arshaad ya tafi sun d’an tab’a hira tukunna Gwaggwo Asaben tace “itama bara taje ta bawa Mommy maganin nata ta sha ta shaafa dan yanzu ita take yi da kanta” Har ta yi gaba sai kuma ta juyo tace “Ka zo muje kaga jikin nata mana”. Ahankali ya girgiza kai kafin yace “Gwaggo na san da sauk’i tunda gamu waje d’aya amman lafiya, kuma kin ce tayi garau yanzu to ai Alhamdulillah! Inaga ba sai na je ba, kar muje a samu matsala.” Shiruuu, Gwaggo tayi.. Ita har ga Allah so take Aslam d’in yaje ya ga Mommy watak’il In ya ga ta warke shima ya samu ya rage damuwar da ta hau kanshi. Amman tunda taga baya so bara kawai ta kyaleshi. Ganin dayayi kamar bata ji dad’in musun da yayi mata bane yasashi mik’ewa kafin yace “muje to” Murmushi ta saki tace “Yauwa d’an albarka, muje.” Itace a gaba shi a baya Haka suka nufi saman ba don ranshi yana soba gashi k’irjinsa In banda dukan uku uku ba abunda yake yi. Wutar parlourn a kashe suka tadda, suna k’ok’arin kunna flash d’in wayoyin su haske ya gauraye ko Ina! Bata lura da shi ba tace “Yanzun fa nake shirin kiranki na jiki yau duk shiru! Sai kuma nace bara in yi wanka kafin ki zo, kin ga banma ida shiga d’akin ba naji motsinki.” Tana maganar tana tahowa garesu. Aslam mutuwar tsaye yayi! Dukda a cikin zuciyarsa hamdala yake yi na ganinta a hakan, amma kuma bayaso suyi ido biyu dan bai san ya zata kaya ba! Hakan ne yasa shi fara ja da baya dan barin wajen Ita kuma kamar ance ta d’ago karaf! Suka yi ido biyu da ita...... Ta k’uraa mishi idanu ko kiftawa bata yi tana kallonshi kamar da mamaki akan fuskarta… Lura da hakan da Gwaggo Asabe tayi ne wadda itama ba k’aramin firgice ta shiga ba ya sanya ta daure taje ta fara jan hannunta tana “Muje ga tofin naki kisha In kin fito wankan sai ki shafa ko?” A hankali suka ji Mommy tace “Aslam!” Aslam wanda already ya juya da niyyar tafiya har ya d’aga k’afar shi jin ta kira sunanshi ya sanyashi dakatawa ba tare da ya sauk’e k’afar shi ko ya juyo ba! Sai da ta sake cewa “Aslam” Tukunna ya ajjiye k’afar ya juyo yana kallonta da idanuwanshi da suka rine lokaci guda!. Dafe kanta tayi da k’arfi, ta runtse idanuwanta kamar mai son tuno wani abun… Ganin haka yasa Gwaggo Asabe ta sake kamo ta kafin ta ce mata “Muje ki huta dan Allah” Sannnan ta baya ta yiwa Aslam d’in alamar ya tafi da hannunta. A hankali Mommy ta bud’e idanunta tana sake kallonshi kafin tace “Asabe me ya faru da ni? Kin ce nayi rashin lafiya meye ne ya sameni? Na shekara nawa?. Kinga fa Aslam kina ganin abunda nake gani kuwa? Shekara ta nawa a kwance? Dan Allah kimi.....” Gigitacciyar rungumar da Aslam wanda ba suba tahowarshiba yayi mata ne ya sanya ta kasa k’arasawa… Tana shirin yin magana taji Gwaggwo Asabe ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi cikin kukan banda kalmar “Alhamdulillah!” Ba abunda take ta nanatawa. Da kyar Mommy ta iya b’amb’aro Aslam daga jikinta, a hankali da hawaye sharkaf akan fuskarta ta shafa fuskarshi wadda ta koma jajir kafin tace “Loosing memory nayi ko?” Ta fad’i hakan tana mai fashewa da kuka. Rasa wanda zai rarrashi wani akayi tsakanin ita da Gwaggo Asabe.. Aslam kam banda ajiyar zuciya ba abunda yake sauk’ewa! Shi kanshi yau so yake hawaye ya zubo ta idanunsa amman abun ya gagara! A hankali ya cika mata hannunta dake cikin nashi ya dan jaa da baya kafin ya seseta gabas ya durk’usa yayi sujjada! Da sauri itama Gwaggwo Asabe tayi sujjjadar, ita kam Mommy tsayawa tayi tana kallonsu tana hawaye da mamakin abunda ya sameta haka… ….Wani abun mamakin still shine yanda ta kasa tambayar inda Aslam d’in yake har sai da ya baiyyana a gabanta! Wanne irin loosin memory tayi haka ita kam? Aslam wanda ta san shekarunshi basu wuce 12 ba shine yanzu haka wanda ta tabbatar yafi 30! Daman tun kwanaki 7 da suka wuce tayi noticing yanda Gwaggo Asabe tayi aging da kuma ita ma kanta! Mai ya faru? Wanne irin ciwo tayi haka? Innalillahi wa inna ilaihirrajiun Allahumma ajirni fi musibati… Take ta maimaitawa cike da rud’ani da alajabi gaba d’aya kwanyarta ta cunkushe............ A hankali Aslam ya mik’e ya kama hannunta suka shiga d’akinta ya zaunar da ita kafin yace “Ina yake miki ciwo, yanzun?” Murmushi tayi ta shafa fuskarshi a hankali tace “Ba ko ina” Sai kuma ta sake fashewa da kuka. Hugging d’inta kawai yayi yana tapping bayanta. A hankali ya d’auko wayarshi, ya hau kiran Dad video call, bai damu da time ba. D’auka Dad yayi suka gaisa yana tambayarshi “ya shirye shirye na bikin su Arshaad?” A hankali Aslam yace “Alhamdulillah” Sai kuma ya gyara zamanshi ya matsa kusa da Mommy ya kamo hannunta cikin nashi ya d’an kalleta yayi murmushi yana ganin yanda ta k’urawa Dad d’in ido, kafin ya juyo ya kalli Dad shima yace “Alhamdulillah Dad..” Bai ida rufe bakinshi ba, yaji Dad d’in ya saka kuka, cikin kukan shima yace “Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!” Sannan yace “Aslam ganinan zuwa yanzun nan, in shaa Allah” Da sauri Aslam d’in yace “No dad, kabari sai gobe yanzu dar....” Kit! Dad ya kashe wayar ba tare da ta tsaya jin maganar Aslam d’in ba. Anan aslam ya zauna, ya rik’e mata hannu gam kamar ance za a kwace mishi ita! Sai kallonta yake yana murmushi yana sauk’e ajiyar zuciya in yaji hakan bai mishi ba yasa hannu yai hugging d’inta. Ita ma Gwaggo Asabe a daren ta kira Yaranta duk biyun ta fad’a musu halinda ake ciki, murna a wajensu ba a magana, suka ce “in shaa Allah, za su tambaya. Za su taho suma in shaa Allah.” A haka Mommy ta sha addu’o’i ta shafa da hannu d’aya dan Aslam yak’i cikata, Gwaggo Asabe tana musu dariya tana kuka at the same time. Ko cikakkiyar awa biyu Dad bai yi ba, sukaji tsayawar mota. Aslam ne yace “Oh Dad, dana sani da ban fad’a mishi ba. Waye ma ya d’auko shi a airport d’in sai Allah tunda gashi bai kira ni ba.” Murmushi Gwaggo w tayi kafin tace “ai ko kaine a matsayin shi na tabbatar sai ka zo” Murmushi shima yayi kafin yace “Kuma fa hakane” Cikin minti goma ya iso cikin d’akin! Yadda ya gansu a zaune ne yasa hawayen da yake ta koma run yaga ya danne suka samu nasarar zubowa. A hankali ya k’araso ya had’asu waje guda ya rungume .. Shi kuka Mommy da kanta ya d’aure da komai kuka Gwaggo Asabe ma kuka Da kyar Aslam wanda duk ya fi su son yin kukan ma ya samu ya lallashesu, daga nan aka hau murna k’arshe dai ba wanda ya runtsa a cikinsu har asuba. Kafin gari ya gama wayewa kuwa, labari yaje kunnuwan kowa a estate d’in, har su Abba. Daga masallaci Arshaad ya biyo Aslam suka zo tare dan ya ganewa idanuwanshi, ai kuwa shima har da kukan shi na tsananinfarin ciki. Haka shima Auwal yazo da daddare tare da Daddy da Abba duk a b’oye kar e ya gansu. Sun ji dad’in ganinta kuwa, sukayi barka suka tafi . Mommy kuwa tunda aka bata labari sannan taga su Arshaad da Aaima yadda suka girma da shi kanshi Aslam d’in, ta shiga alhinin ‘shikenan tayi missing teen age d’insu, da yanda suka taso kenan har abada?’ Gaba d’aya tausayin kanta da Aslam d’in sai ya lullub’eta.. Da kyar ta iya cin abinci, in banda kuka ba abunda take yi, tun ba ma da Dad ya gaya mata irin abubuwan data dinga yiwa Aslam d’inba, da irin rayuwar da yayi, gaba daya sai ta sake birkice musu, tana kuka tana cewa Aslam do yayi hak’uri ya yafe mata. K’arshe dai barin gidan ma yayi dan ba zai iya tsayawa tana kuka haka tana neman gafarar sa ba bayan ya san ba laifinta bane ba. Dad kanshi kasa zama yayi sai gidan su Abba yaje, ya d’an zauna yana dana sanin fad’a mata d’in da yayi. Sai dare aka samu damar kaita wajen Granpa, dan Gramma ita tunda taji labari ta taho itama suna tare ranar har dare. Ba yabo ba fallasa ya amsa gaisuwarta ya yi mata ya jiki. Ba abunda yake b’ata mishi rai irin yanda Gramma take ta faman yayatawa cewa “Ai Hudan ce ta bada shawarar yi mata sauk’ar Qur’ani kullum”. Har sai da ya kwab’eta ta hanyar cewa “Ta daina cewa ‘Huda’! Kawai ta dinga cewa Allah ne ya bata lafiya ya warkar da ita.” Gramma ta so yi mishi bayani, amman ganin kamar ranshi a d’an b’ace yake kuma ta son ba ya son jayayya yasa kawai tace “In sha Allah, Granpa. Zan gyara.” Tun daga kan Gramma har Aaima ba wanda bai bada zakka da sadaka ba na ban mamaki! Sauk’a kuwa ba su daina ba ana kan yi dan Dad cewa yayi “zuwa k’arshen watan nan ma in Allah ya yarda aka kammala na Mommy to ba dainawa za ayi ba duk sati sai an yi sauk’a a cikin eatate d’in a tsakanin su, in shaa Allah”. Yau kusan sati d’aya da warkewar Mommy, har su Hudan sai da suka zo suka yi mata sannu da barka a b’oye da daddare. Mommy tayi matuk’ar murnar ganin Sudais da Shuraim ita daman tana son twins, kuma tunda taji labarin suna da twins a family d’in taketa so ta gansu da su da Huda. Tunda Mommy taga Huda Allah ya d’aura mata k’aunarta, especially ma da taji gudummawar data bayar akan rashin lafiyarta.. Tayi mata godiya yafi a k’irga! Ita kam Hudan wani tsoron Allah da girman zatin shine ya sake shigarta, tana tunawa ko 2 month ba ai ba ta ganta a hargitse amman kalleta yanzu garau! Tabbas a rayuwa, in dai mutum yana neman sauk’i! Waraka! Taimako! To kuwa ya nema a wajen Ubangijin Talikai wanda bashi da kishiya. Da kyar ranar ta barsu suka tafi, ita Huda mamakin ma yanda matar take mata take yi, kamar ta santa tun daa chan amman da ta tuna yanda Mommyn ta bata labarin shak’uwarsu ita da Mama sai tayi tunanin ko saboda Maman ne yasa take yi mata haka.... Sannan itama a lokaci d’aya taji girma da k’aunar matar ya shige ta. A b’angaren Mommy kuwa, kawai tsintar kanta tayi da tsananin k’aunar Huda, dan koda bata kasance y’a ga Maryam ba tabbas Ubangiji ya d’aura mata k’aunar Yarinyar a ranta. Ba abunda yafi sosa mata rai irin da taji cewa ‘an sa ranar ta da Arshaad!’ Saboda ita har ga Allah tun da ta d’aura idonta akan Yarinyar ta fara kwad’ayin ganinta da Aslam d’inta a matsayin maaurata! Amman kuma da ta duba taga abunda yayi Aslam shi yayi Arshaad sai ta hak’ura ta barwa Allah komai sannan ta bisu da fatan alkhairi......................... BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 50. Yau saura sati biyu auren su Hudan, sai shirye shirye ake yi. Yayinda jikin Mama yayi sauk’i sosai abun har mamaki yake bawa jamaa kamar ba wadda ta karye ba, follow up kawai take zuwa abunta. Abba da kanshi yaje ya siyowa y’arsa kayan d’aki na gani na fad’a, hatta cokali bai bari ba sai da ya siyo mata komai bayab ya tambayeta taste d’inta, wasu kuma yana daga chan d’in yake turo mata Sakina ta tayata zab’a. Sannan ya had’a mata gara nan ma na gani na fad’a. Lokacin da bikin ya rage saura sati d’aya already kayan gara da kayan d’akin amarya suna gidanta. Duk da ba wai zama za suyi anan d’in ba, kai ta kawai zaayi gidan daganan su wuce karatunsu amman hakan bai sanya an k’i yi mata kayan d’aki ba saboda time to time za su ke zuwa hutu. Shima Arshaad a nasa b’angaren hakan bai hana sa siyan gida ba! Daa a cikin estate d’in zai zauna amman da yake Granpa ya san Hudan zai aura haka nan k’iri k’iri sai ya hana sa gida! Da farko Granpa d’in cewa ma yayi ya bar mishi estate d’inshi, tun kafin auren! Da kyar Aslam ya lallab’ashi ya hak’ura amman dukda haka sai faman neman fad’a yake yi kuma fa sai da Dad ya tambayeshi tun farko lokacin kafin ma a saka rana amma sai ya nuna irin shi ba ruwanshi d’innan su yi abunda sukeso.. Yanzu kuma da bikin ya taho sai neman rigima yake yi yana neman abokin fad’a! Shiyasa kowa ya sha jinin jikinshi dan duk wanda yayi rashin sa’a ya yarda ya samu matsala da Granpa a wannan yanayin da yake, tou tabbas kashin shi ya bushe! Wannan dalili yasa Arshaad ya sayi gidanshi da kanshi daman kuma shi har ga Allah ya ma fi son ya yi komai da kanshi, dan da kyar ma ya yarda ya bari Daddy ya bawa Mommy mak’udan kud’ad’e take had’a mishi zazzafan lefe.. Gida kuwa da Abba yace zai siya mishi yi yayi kamar zai yi kuka, shi kuma Abban ya dage! Sai da Mommy ta saka baki tukunna Abban ya hak’ura ya bar Arshaad d’in ya sayi gidanshi mai hawa biyu d’aki bakwai da parlour hud’u har da d’an k’aramin bq a gefe a nan cikin Nasarawa sai dai da d’an tafiya tsakaninsu da gida da estate.... Su Ummu da Mommy ne suka je suka yi mata jerenta tsaf! Wanda yanzu kawanchen Mama da Mommy ya dawo sabo fil! Dan har gida Mommy taje ta dubota, duk da Dad ba wani son yawan fitar tata yake yi ba amman indai abu ya shafi Maryam to ya kan bari saboda Mommyn tana yi musu campaign a lamarin Abba, sai ita kuwa Mama duk maganganu da Mommy take mata akan Abban amsa d’aya zuwa biyu take bata kullum ‘Allah ya zab’a mafi alkhairi’ ko kuma tace ‘ita fa ta riga ta hak’ura da Abba har abada! Ba akan dalili d’aya ba sai akan dalilai barkatai’. Amman duk hakan bai sanya Mommy ta hak’ura ba, haka nan suke fama kullum......... Yau sauran kwana uku d’aurin auren! Su Hudam basu samu komawa wajen Mama ba sai a yau d’in. Kafin su wuce Abba ya nemi ganinta.. Kamar ko wanne uba haka nan ya zaunar da ita yayi mata nasiha mai ratsa jiki! Yana hawaye tana kuka haka su Sudais suma da suka zo yi mata sallama… A haka dai ba dan suna so ba suka yi sallama Abba ya sanya mata albarka. Mommy da kanta ta kaita har gidan Shuwa gaban Mama Hudan tayi mamakin ganin baki y’an Maiduguri da suka zo dan gidan a cike tap! Suka tarar anata hada hada. A yau d’in zasu fara event! Dan haka suna isa suka tarar har mai kwalliya ta k’araso tana jiransu, waensu a cikin friends d’in su ma duk sun zo, da yake mai kwalliyar da tayi mata ita ce za tayi musu saboda Arshaad Maiduguri style yayi..duk shi ya biyawa friends d’inta kud’in makeup da anko. M T Tunda Mommy ta warke kullum itake ce take yiwa Aslam girki… Wani special kulawa take bashi amman ta rasa dalilin damuwarshi dan ko jiya ma sai da Doc ya zo ya dubashi kuma ya tabbatar musu jininshi ya k’i sauk’a instead ma k’ara hawa yayi! Sannan ga zazzab’insa shima ya dawo. Gaba d’aya hankalinsu duk a tashe yake, dan sun rasa gane kan Aslam kwata kwata. Arshaad tun yana kulashi, yana tambayarshi meke damunshi yana lallab’ashi, har ya zo ya hak’ura kawai ya watsa shi a kwandon shara Dan Arshaad d’in gani yayi kamar ma Aslam d’in haushinshi yake ji! Idan ma yana waje Arshaad d’in ya shigo kawai sai dai ya tashi ya fice ya bar mishi wajen, ko magana baya so ta had’asa da shi! Kamar ma wanda yake k’ok’arin yin gaba da shi ta k’arfi da yaji! Shiyasa Arshaad d’in kawai ya rabu da shi amman a chan k’asan zuciyarshi mamakin abubuwan da Aslam d’in yake mishi a wannan lokacin da ya kamata yafi kowa tayashi murna, yake yi. Hatta Dad Abba da Daddy sun lura da hakan, basa son shiga tsakaninsu tunda sun fi kusa shiyasa kawai suka zuba musu ido a ransu suna mamakin mai ya had’a best friends haka??……. Da yamma, Mommy na d’aki tana jera kaya a wardrobe Dad ya shigo.. A bayanta ya tsaya yayi hugging d’inta. A hankali tayi murmushi kafin ta juyo still yana rik’e da ita tace “ina wuni Dad” Murmushi shima yayi mata yana jin tsananin k’aunarta tana nunkuwa a cikin zuciyarshi, a hankali yace “Bayan waennan akwai wasu kuma da kike buk’ata??” A hankali ta girgiza mishi kai alamun ‘a’a’. Ajiyar zuciya ya sauk’e, kafin ya jawo hannunta suka nufi gadon dake d’akin. Sai da ya zaunar da ita shima ya zauna a daff da ita tukunna yace “Aisha, magana nake so muyi dake ta gaskiya da gaskiya” Da sauri ta mik’e tana k’ok’arin kawar da kanta daga gareshi kafin tace “Not again Dad, na gaya maka ban tuna komai ba, please Dad ka bar maganar nan.” Mik’ewa shima yayi ya sake rik’o hannunta kafin yace “Look at me kice mini ‘wallahi Dad ban tuna komai ba‘.” Hannunta ta fara k’ok’arin kwacewa a cikin nashi ta had rai sosai cikin fushi tace “Tunda baka yarda da ni ba, shikenan!” Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace “Jiya da yamma kin manta wayarki a d’akina kin tafi kitchen, naje kai miki wayar saboda a nata kira.. I didn’t mean to eavesdrop but i have no choice! Naji komai maganan ku da kuka yi ke da Asabe!.. Mai yasa kika b’oye min?”. Gabanta ne ya yanke ya fad’i! A hankali ta tsaya tayi tsit ta nutsu ba tare da tace komai ba, sannan ta kasa d’agowa ta kalleshi… Hannu yasa ya kamo hab’arta ya juyo da fuskarta ya d’ago fuskar, da sauri ta runtse idanuwanta. Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sake sauk’ewa kafin a hankali yace “Maimaita min abinda ya faru that very day da kika fad’o, waye ya turoki?! Ina so inji daga bakinki, don’t lie, kin san naji komai.. Kawai i want you to tell me.” A hankali tace zan fad’a maka amman sai ka yi min rantsuwar ba zaka fad’awa kowa ba sannan ba zaka nuna ko da a fuskarka ne ba.” Cika fuskarta yayi cikin fad’a yace “Ba zan iya ba Aisha! Ya zama dole in fad’a sanann in nuna fushi kuma in d’auki mataki! Dole ne in hukunta mai laifi! Kin san irin ciwon da kika yi kuwa? Kin san irin wahalar..” Cikin katseshi tace “To kaga dalilin da ya sanya na b’oye maka ko?” Cikin karyewar zuciya taci gaba da cewa “I have lost a lot, shekaru sun jaa.. Na ci burin yiwa y’ay’ana tarbiyya especially ma Aaima da ta kasance mace amma kalli fa duk nayi missing Mai ya rage yanzu?. Ni za kayi wa abun nan ko? A kaina kake so ka hukunta me laifin ina? To ni d’in nace ‘na yafe har abada har gaban abada!’ Meye kuma na dawo da abunda ya riga ya wuce??. All i need to do now shine ibada dan kwata kwata ban gamsu da sallolina da kuka ce inayi ba, Nafilfili da ibada su kawai nake buk’atar inyi a halin yanzu, ba wai case da holding grudges ba! I want peace.” A hankali ganin ya d’an nutsu yana kallonta kawai, ta kamo dukkannin hannuwanshi biyu ta rik’e tace “Dad, duniyar ma duk nawa take? Idan fa mukayi hak’uri ma duk mutuwa za muyi! Yanzu idan kace zaka d’auki mataki wallahi square one zamu koma, mutane ba za su tab’a duba laifin da aka yi mini ba instead gani za suyi kamar ka fifita ni ne wanda fifita Aslam da Granpa yayi tun farko ni na tabbatar shiyasa aka zamo silar zabgemin kusan rabin rayuwata haka nan na yi ta a wahala! Please dan Allah let it go, for me..” Mommy ta dad’e tana kwantar mishi da hankali, da nuna mishi ita kwanciyar hankali kawai take buk’ata yanzu, tukunna da kyar da mugun kyar ya yarda da buk’atarta akan ba zai yi komai ba, kuma ba zai nuna ba ko a fuska! Tukunna a hankali ta hau fad’a mishi abunda yaji tana fad’awa Gwaggwo Asaben..... In banda ajiyar zuciya ba abunda Dad yake sauk’ewa a jejjere… Ji yake kamar ya mutu dan tashin hankali da takaici gashi ta saka shi yayi mata alk’awari. A haka Aslam ya shigo ya samesu.. Tabbas ya lura akwai abunda suke tattaunawa but yadda Dad yayi ta k’ok’arin ganin ya danne ne yasa kawai ya basar dan ya fahimci koma menene to bai shafesa ba. Gaidasu yayi ya nemi waje ya zauna a k’asa kan kafet yana kallonsu k’aunar iyayen nashi tana sake shigar mishi zuciya yana jin wani farin ciki yana taso masa ta k’asan zuciyarshi just by looking at them. Suma d’in shi suke kallo wanda tashi d’aya In ka kalleshi zaka hango tsananin damuwa da k’uncin da yake a ciki... “Ya baka shirya ba? Yanzu muka gama waya da Arshaad, yace yanzun za a tafi gudun kar ayi dare, kai da Aaima kawai ake jira. Na kira Aaiima tace min ta shirya tun d’azu, a tunanina kun wuce ma.” Ajiyar zuciya Aslam d’in ya sauk’e kafin a hankali yace “Am, daman sallama nazo in yi muku.” Da mamaki suke kallonshi. Bai jira jin me za su ce ba yace “Inaso zan wuce Uk! Akwai ayyukan da nake so In k’arasa a chan. K’uraaa mishi ido kawai yaga sun yi, har ya fidda ran za suyi magana yaji Mommy tace “Mai yasa? Ka fad’i mini gaskiya dan na san akawai dalili Aslam” Murmushi kawai yayi kafin yace “Please ku barni in tafi, dan Allah” Mik’ewa Dad yayi ya nufi hanyar fita kawai ba tare da yace mishi komai ba, ya fice. Hannu Mommy ta mik’a mishi, a hankali ya sa hannun nashi cikin nata ya mik’e ta dawo dashi kan gadon inda Dad ya tashi. Cikin kulawa ta kallesa tace “Aslam meye damuwar ka? Ko har yanzu kana jin zafin abubuwan da nayi maka ne?” Ta fad’i hakan muryanta na d’an rawa kamar wadda zata fashe da kuka. Da sauri yace “Mommy please mana, ki daina tunanin hakan sam a haka bane, ai ba laifinki bane ba.” Cikin katseshi tace “To yaya ne? Menene? Talk to me dan Allah! Ko kanada wadda ta fini? Talk, kai kanka za kaji nauyin zuciyarka ya ragu. Waye ya b’ata maka rai? Ko kana da masaniya akan abunda ya faru ranar dana fad’o? Fad’a kukayi da Granpa? Ko Daddy ko wani? Ko Arshaad ne? Ko company d’in ne? Naji Dad yace it was successful kun bud’e kai da Abba, akwai wani abun ne?” Duk ta rikice tambayoyi kawai take jero mishi barkatai. A hankali ya lumshe idanunsa, sannan ya d’auko Dayan hannun shi ya d’aura akan hannayen nasu! Ganin haka yasa itama ta d’auko Dayan free hand d’inta ta d’aura akai ta bashi dukkannin attention d’inta a hankali tace “Talk, I’m your mother, I can help you.” Bud’e idanuwanshi da suka yi jaa yayi, a hankali ya fara magana “I know I’m trying to be selfish here, but.......................... .” Wata k’akk’arfar ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e bayan ta gama sauraran tilon d’an nata, a hankali ta janyo shi jikinta ta rungume, ta fara hawaye, cikin karyewar zuciya tace “I’m soo sorry son, ba zan iya taimakonka akan wannan al’amarin ba!.” Murmushi yayi wanda yafi kuka da ihu ciwo a hankali ya zaro ta ajikinshi kafin yace “I know, kawai ki tayani addua, thats all I need maybe zan samu sauk’in rad’ad’in da nake ji, please Mommy.” Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace “Maybe i’m not destined to be happy, a duniyar nan!! Haka Allah yake son ganina, if not why? Tayaya zan kasa cire......” Da sauri ta sa hannu ta toshe mishi baki, tausayinshi yana sake shigar mata zuciya… Ahankali yasa hannu ya zare hannun nata sannan yace “Pls Mommy ku barni In tafi, dan Allah.” Tana shirin bashi amsa, Dad ya shigo.. Kallonsu yayi kamar zai yi magana sai kuma yayi shiru ya juya kawai, yace “Ku zo duk ku biyun gidan Granpa, yana son ganinmu, an dawo da su Adama!” Yana gama fad’in haka ya juya ya fice........ Sanye take cikin bridal gown, peach colour anyi kwalliya da white stones masu shek’i da d’aukar ido a gabad’aya k’irjin da kuma half d’in k’asan rigar ta tsaye har ta bayan side d’in inda yake flowing…. Ta d’aura jewelry’s white, yayinda takalmi, tauban, mayafi da head d’inta suka kasance peach…. Fuskarta ta sha casual makeup simple! Dan cewa tayi itama ayi mata casual d’in inyaso ranar wuni, traditional day d’in da Shuwa da su Mama za suyi sai ayi mata bridal d’in. Tayi masifar yin kyau kuwa gashi kwalliyarta ta tafi da shigarta matuk’a. Bridesmaid d’inta su 10 har da Sakina 11, Khadijah bata zo yau ba tace sai gobe zata fara zuwa saboda tana laulayi kuma jikin ya d’an motsa. Kusan duk Sakina ce ta gayyatosu (bridesmaids d’in) Y’an makarantar su ntic kuma aka ci sa’a suka karb’i gayyatar aka shirya anko da su kasancewar ta fad’a musu da wuri… White gown ne a jikinsu, sai peach head, takalmi da jewelry’s sai vails d’insu white.. D’inkin su iri d’aya sak dan saboda ma gudun samun mishkila dama tailor d’aya ne yayi d’inkunan ( bama anan ba ) Makeup d’insu komai iri d’aya. Tana tsaye Sakina tana yafa mata mayafi Mama ta shigo, suna had’a ido kawai suka fara hawaye a tare! Sakina wadda itama taji idonta ya cicciko ne tace “Mama dan Allah ku daina” sai kuma ta fara kuka itama, ahaka Ummu ta shigo ta samesu, itama tana ganinsu ta hau kuka. Da kyar friends d’insu suka lalllashesu aka d’an yi musu hotuna suka yi abunda ya kawosu, suka juya suka fita. Sai da aka sake gyarawa Hudan da Sakina makeup d’in su Allah yaso mai makeup d’in bata riga ta tafi ba. Ana gamawa, mai makeup d’in ta fara had’a kayanta, tana shirin tafiya kiran Auwal ya shigo wayar Sakina. Taso tayi ignoring amman kawai sai fa daure ta d’auka, albarkacin biki dan ta lura yafi kowa zak’ewa, so dole ta san sai ta had’u da shi one way or the other sannan ta lura da yanda shi kuma Ya Arshaad ya sakar mishi komai , it’s like ya ma manta da abunda yayi mishi akan Jalila.. a k’asan ranta kuma sai tace “Ko da yake ba’a shiga tsakanin y’an uwa dama m, blood is thick!” Da wannan tunanin ta d’auka wayar ta kara a kunnenta tace “Assalam akaikom” Yana zaune cikin motar shi, a Ahankali ya lumshe idanunta da jin muryarta! Sai da ta cire ran za ayi magana tukun taji a hankali taji yace “Sakeena..” Da sauri cikin fad’a fad’a tace “Menene!!?” Dan jikinta ya fara yi mata abunda yake mata a duk lokacin da suke tare wanda ta tsana fiye da tunani.. Murmushi yayi kafin yace “Mun iso, ku fito mu wuce, ko?” Bata bashi amsa ba ta kashe wayar…. After kamar 10 minutes haka suka fara fitowa.. Tunda suka fara fitowa camera man da mai video coverage suke d’auka. Sakina da k’anwar Ashraff saurayin Sakina da Hudan ne suka fito a k’arshe. Motocine a jere tun daga farkon layin har zuwa k’arshe! Gaba daya irin su d’aya bak’ak’en benz! Sai ta tsakiya da aka d’ora wata y’ar k’aramar peach flower a gaban glass d’in ce kawai ba bak’a ba instead ita fara ce ta sha tint! Amman itama k’irar ragowar motocin ce kawai kalar ne ya bambanta, kana gani ka san itace ta Amarya da Ango dan haka su Sakina suka ruk’ota suka nufi motar da ita. Suna zuwa bakin motar Arshaad yasa hannu ya bud’e seat d’in baya inda yake zaune ta gefe… Wata zazzafar suite ce a jikinshi white, hatta neck tie d’in shi white ne da takalmi, sai wani d’an kyalle da ya d’an d’aura a jikin aljihunshi na suite d’in nasa d’an mitsitsi peach..... Lokacin da yace mata kar su damu ya gama order da had’a komai kayan da za ayi using, aranta ta gama aiyyanawa ‘ba wani kyau za suyi ba’ dan tayi tunanin maza ba su iya zab’e ba amman yau kam ta tabbatar Ya Arshaad k’arshe ne wajen zab’a, had’a kaya da colours. Murmushi Sakina tayi kafin tace “Ango irin wannan kyau haka?” Dariya ya d’anyi sannan yace “Ai ban kaiki ba. K’anwar Amarya” Yana mata magana idanunshi na kan Hudan! Da kyar ma ya amsa gaisuwarta ita da k’awarta. Lura da Sakina tayi hankalinshi baya kansu yasa ta saka mishi Hudan a motar ta rufe a ranta tace “Gata nan ai sai ka cinyeta da kallo” Tana d’an murmushi. Ba dan hancinta ya jiyo mata k’amshin turaren Auwal ba da ba abunda zai hanata afkawa kanshi In ta tashi juyowa domin barin wajen. A hankali ta d’an juyo jin k’amshi da mutum a bayanta daff! Suna had’a ido kuwa ta zabga masa wata uwar harara.. A wajen k’anwar Ashraff kawai ya samu gaisuwa, bai damu ba ya amsa ta kafin ya juya ga Sakina yace “Kin yi kyau over!” Yad’an yi mata alamar perfect da hannunshi yana murmushi.. White suite ce shima a jikinshi da d’an ratsin black, yayi masifar yin kyau sai dai askin sa da yayi yau d’in ne ya b’ata mata rai. Hannu yasa ya bud’e gaban motar, kafin yace “Bismillah” yana kallonta still da murmushi akan kyakkyawar fuskarshi. A hankali ta d’auke idanunta daga kanshi, daman tun d’azu da ta sunkuya suna magana da Arshaad ta ganshi zaune a mazaunin driver! A tunaninshi zata yarda ta zauna kusa dashi kenan, tab! Ai ko hauka take ba zata yarda ta zauna kusa da shi ba ita da take k’ok’arin ganin ta kauce mishi ta kowacce hanya, besides Ashraff ma yana jiranta tare za su tafi..’ Da wannan tunanin ta kamo hannun k’anwar Ashraff ta saka ta a cikin gaban motar ta rufe, ta yi gaba abunta. Guiwa a sace Auwal ya bita da kallo har ta isa inda motar Ashraff d’in take a chan gefe bama a cikin convoy d’in nasu ba, ta shiga. Da kyar ya iya dedeta kanshi ya juya yaje ya shiga ya kunna motar dan har an fara yin gaba... Suna isa inda za ayi event d’in ya bud’e motar shi ya fito. Sai hotuna ake d’auka amman shi bai damu ba, neman ta kawai yake yi.. Ganin ba ita ba dalilin ta yasa ya zaro waya ya hau kiranta! Kowacce mota ta k’araso, har ta masu d’aukar hoto amman tasu bata iso ba.. Arshaad ne ya d’an kira sunan shi dan haka ya juya, da hannu Arshaad d’in ya yafito shi, yana zuwa yace “Ana ta hoto babu kai, me kake nema?” D’an murmushi kawai yayi ya tsaya aka yi musu, daga nan aka fara k’ok’arin shiga hall d’in. K’awayen Amarya, a baya Abokan Ango a gaba Auwal da Jamil su ne daf da Ango da Amarya dan sune suka saka suit kamar Angon ragowar mazan kowa kayan shi ya saka. Shi dai Auwal har aka shiga bashi da nutsuwa dan haka Amarya tana zama ya juya ya fita yana mai cewa Jamil yayi jawabin da da shine zai yi, yana da uzuri. Arshaad bai yi mamakin rashin ganin Aaima da Aslam a wajen ba! Amman tabbas ranshi ya sosu, baya son b’ata wannan ranar ta musannan dan haka ya kawai sai ya basar ya ci gaba da huld’ar gabanshi. Tsarin wajen ba k’aramin had’uwa yayi ba Tebur da kujeru uku a zagaye wajen guda ashirin! Sai chan wajen sit d’in Amarya da Ango gefen dama da hagun su kuma akwai kujeru goma goma da dogon tebur a lamun nan ne wajen zaman best friends dan har ma sunje sun zazzauna matan masu anko mazan kuma waenda suka zo tare. Kwata kwata friends d’insu da suka tarar a wajen ba sufi ashirin ba! Cool music ke tashi ba wani hayaniya.. Cocktail ne da cake da sweet da hot chocolate da kuma menu mai d’auke da abubuwa daban daban akan tebur d’in, sai waiters a gefen tebles d’in a tsattsaye su wajen 30 da uniform, duk abinda kake buk’ata sai ka kira ka gaya musu a menu d’in aje a kawo maka In ka gama su d’auke. After kamar 20 minutes da fitar Auwal, motar su Sakina ta shigo wajen.. Ranshi a mugun b’ace ya k’arasa inda motar take! Bai yi wata wata ba yasa hannu ya bud’e side d’inta ya kamo hannunta ya fito da ita. Da kyar ta iya tsayawa ta gyara mayafinta wanda yake k’ok’arin zamewa… Ko lura da guy d’in da ya fito shima ya zagayo inda suke Auwal d’in bai yi ba ya fara magana “Ina kuka tsaya?? Kin san mintunku nawa kuwa? Almost 30 minutes kowa ya k’araso banda ku, Ina kuka biya haka?” Ya k’arashe maganar cikin tsananin b’acin rai, kamar wani ubanta… Kallon shi take yi kawai. Sai da ta barshi ya kai aya tukun ta fara k’ok’arin wuceshi ba tare da tace uffan ba!. Tafarfasar da zuciyarshi keyi ba kad’an bane dan haka cikin zafin nama ya sake sa hannu ya fincikota ya dawo da ita unintentionally ta bugu da jikin motar. Da sauri Ashraff ya k’araso inda suke ya juyo da shi ya cukumi wuyan rigar shi! Cikin tsananin b’acin rai yace “Meye ne matsalar ka? Who the hell are you? A iya sani na bata da yaya! Ka fito kawai ka fara yiwa mutane hauka.. Ka godewa Allah ni ba mahaukaci bane Irin ka dan wallahi da sai na gyara maka zama a wajen nan!” Ya k’arashe maganar yana sakin mishi kwala da k’arfi. Auwal ya taso kenan yana shirin yin magana a zafafe Idanuwansa suka sauk’a kan Sakina wadda ta fara hawaye. A take yaji duk jikinshi yayi sanyi… Tun lokacin da ya tura ta jikin mota har yanzu bata motsa ba tana a yanda take sai dai hawayen da ita kanta ta rasa na menene waenda suke zuba akan k’uncinta. Kamar an tsoma shi a ruwan sanyi haka yaji, ya kasa motsawa zuciyarsa na dukan uku uku, gashi tak’i yarda ta kalli inda yake. A hankali Ashraff ya k’arasa inda take ya fara yi mata maganar da Auwal d’in baya jin me yake cewa. Goge hawayenta tayi ta gyara tsayuwarta. Sannan Ashraff d’in ya bud’e bayan motar ya d’auko k’aton cake d’in da suka tsaya karb’a. Daganan suka zo suka wuce shi ba tare da sun ce mishi komai ba!. Sam ya kasa motsi ya kasa yin komai. Kawai iya hawayen da ya gani daga idonta ne ya kashe mishi guiwa ya sanyaya mishi jiki. Yafi 10 minutes a wajen kafin da kyar ya samu ya wuce ciki, yana zuwa ya nemi waje ya zauna.. Ba abunda ya iya ci a wajen yana nan zaune a wajen shi kad’ai amman dukkannin hankalinshi na a kan Sakina wadda itama ya lura bata da sukuni ga Ashraff a gefenta wanda yake ji kamar yaje ya rufe da duka, sai wani shishshige mata yake yi. Su y’an matan wajen a tunanin su tsabar kyau da had’uwar sa ne yasa yake shan k’amshi yak’i shiga mutane basu san shi kuwa zuciyarshi ce take shirin tarwatsewa ba! Gashi ank’i a tashi daga wajen....... Sai after kamar 2 hours tukunna aka ce Amarya da Ango su yanka cake! Bayan sun yanka Huda na k’ok’arin durk’usawa ta bashi yayi saurin tarota ya karb’a shi ya durk’usa ya bata! Ai kuwa aka hau tafi ana ta videos da pictures. Daga nan masu bada gifts suka bada aka yi addua aka tashi a lokacin already Auwal ya dad’e da komawa cikin mota su kawai yake jira. Suna fitowa kowa ya fara kama gabanshi…. Bai yi tunanin Sakina zata shigo motar ba! Dan haka ya fara k’ok’arin tada motar bayan su Hudan sun shigo Arshaad ne yace “Wait Auwal, bara mu d’an jira Sakina” Yana juyawa yaga sun yi sallama da k’awarta da wanda ya gansu tare sun tafi.. Sai da taga wucewarsu, tukunna ta zo ta shiga a lokacin ita kad’ai ce ma ta rage a harabar wajen. Har suka isa gidan su Mama bai ko kalli inda take ba Motar shiruuu sai hirar su Arshaad da suke yi k’asa k’asa ba wanda yake jin me suke cewa.. Sallama Sakina tayi da Arshaad Hudan kuma ta cewa Auwal sun gode, daga nan Arshaad ya dawo gaba su kuma suka wuce cikin gida....... Dad, Mommy, Gramma, Aslam Arshaad sai Aaima kawai Granpa ya buk’aci gani tunda a ganinshi ya riga ya cire Dad da Abba da su Hudan acikin zuriarshi….. Mammy da Mom kawai suka tarar a parlourn dan Ummi kusan a sume ma aka kawota, shiyasa Granpa ya kira Doc akai d’akin Gramma ma da ita domin bata taimakon gaggawa. Aaima tana shigowa da suka had’a ido da Mammy sai tayi kanta ta gudu ta rungume kawai tasa kuka. A hankali Aslam yaje ya gaida Granpa tukunna ya dawo wajensu ya gaidasu yana mai shafa kan Aaima alamun lallashi, haka itama Mommy bayan ta je ta gaida Granpa d’in ta dawo wajensu…. Gaba d’aya hankalinsu yana ga Aaima, wani abun mamaki kwata kwata basu lura da Mommy ba har sai da muryarta ta yiwa dodon kunnuwansu dirar mikiya! A firgice duk su biyun suka d’ago suna kallon ta! Itanma su d’in take kallo da murmushi akan fuskarta especially ma Mammy wadda bakinta yake rawa ta kasa furta uffan! Mom na shirin yin magana Granpa yayi gyaran murya. Duk nutsuwa suka yi suka maida hankalin su a kanshi bayan sun d’an gyaygyara zama.. Kallonsu yayi d’aya bayan d’aya, kafin yace “Ina Muhammad?” A hankali cikin girmamawa Aslam yace “Yana wajen event d’insu an fara yau” Da mamaki Mom da Mammy suka kalleshi, suna shirin yin magana suka ji Aslam d’in ya sake cewa “Ni da Aaima ma da yanzu zamu wuce to kuma sai kiranka ya riskemu”. “Call him! Kace ya bar duk abunda yake ya zo yanzun nan!” Cewar Granpa. A hankali Aslam yace “Granpa plss..” Cikin d’an fad’a fad’a abunda bai tab’a yi mishi ba yace “Call him now!!” Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace “Ok, Granpa.” Sannan ya zaro wayar shi ya hau kiran Arshaad… Har ta tsinke ba a d’auka ba, ya sake kira nan ma ba a d’auka ba, zai kira a karo na uku Granpa ya d’aga mishi hannu, yace “Leave him” Daga nan ya fara magana “2 months ago! Adama, Rukayya da Zainab Sun yi wa wannan family d’in babban laifi wanda hakan ya kai ni ga yanke hukunci a garesu mai tsauri! Dalilin tara ku a nan da nayi shine Inaso In jaa muku kunne akan ‘magana ta riga ta wuce!’. Mazajen su Adama da ita Ummi basa kusa dan haka kai Yahaya kai ne zaka sanar da sak’ona garesu! Banaso ko da wasa inji makamanciyar maganar nan ta sake tasowa! Sun yi laifi an hukuntasu magana ta mutu!! Duk kuma wanda ya k’etare umarnina ko a fuska ya nuna musu wani abun yi zai gamu da fushina tabbas. Su Yusuf kar suga wai basa tare da ni, muddin suka yi wani abun da bai kamata ba a matayensu to tabbas zan yanke musu hukunci mai tsanani! Ka gaya musu hakan. Ku kuma” Ya juya kan su Mammy “Wannan hukuncin da na yanke muku kuka yi going through for the past 2 months ba komai bane! Ku k’irga azabar sau ashirin tou tabbas ita zaku fuskanta muddin kuka bari naji wata matsala daga gareku. Sai magana ta biyu! Duk da Muhammad ya b’ata min rai a yanzu, hakan ba zai saka In chanja abunda na shirya ba… A kwanaki yayi laifi wanda ya kai ni ga rage mishi matsayi Auwal ma haka. Tou yanzu Alhamdulillah naga progress da ci gaba a tare da su, dan haka ranar Monday Auwal ba dan halin ubansa ba sai dan kwazon shi zai koma assistant md tunda Aslam ne md yanzu shi kuma Muhammad ya koma matsayinshi, treasurer. In shaa Allah Nan da shekara d’aya za a fidda wanda ya chanchanci a malllakawa MT gaba d’aya na uk da na Abuja da na nan Kano, a tsakanin su uku. Yahaya In Zainab ta warke ka mik’a ta gidan Mijinta inda ya k’aura ya koma, amman yanzu ka fara kai Adama tukunna ta samu ta huta, Mammy kema ki wuce d’akinki. Allah ya bamu alheri.” Yana gama fad’in haka ya mik’e, ya shige d’akin shi. Shiruu, d’akin ya d’auka. Da kyar Mammmy ta iya mik’ewa dan jikinta ba energy ta isa inda Mommy take tana zuwa kawai ta fad’a jikinta ta fashe da kuka tana cewa “Alhamdulillah!! Na ji dad’in ganinki a haka y’ar uwa ta, Alhamdulillah Alhamdulillah” Mom ita ma rarrafawa tayi inda suke, ba yabo ba fallasa ta d’an rungume Mommy kafin tace “Alhamdulillah, Allah ya k’ara mike lafiya” Ba wadda Dad ya k’urawa ido irin Mammy! A hankali yace musu “ku taso mu tafi” kawai, ya mike. Aaima ce taje ta kansu ta tayasu mik’ewa, dan ko kuzarin kirki babu a jikinsu! Duk sun yi bak’i sun rame sun kod’e sun k’anjame! Banda kuka ba abunda take yi. Aslam tare suka tafi da Mommy kamar yanda suka zo tare. Dad kuwa sai da ya fara kai Mammy gida ita da Aaima tukunna ya wuce da Mom dan kaita sabon gidan da su Abba suka koma. Side d’in Daddy ya shiga tana biye da shi a baya.. A zaune suka samu Daddyn a parlourn k’asa yana shan coffee da suit d’inshi a jikinshi ko takalmi bai cire ba da alama yanzu ma ya dawo daga aiki dan ga suitcase d’inshi a gefe. Sallamar Dad ce ta jawo hankalinshi gare su, mik’ewa yayi yana d’an murmushi da muryarshi dake nuni da a matuk’ar gajiye yake yace “Yaya ina wuni, ai da ka kirani na zo..” Muryarshi ce ta mak’ale sakamokon ganin Mom wadda ta fito yanzu daga bayan Yayan nashi. A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya, yana kallanta.. Rabonshi da ita wata d’aya kenan, tun last zuwanshi da yaje tayi ta kuka ya yanke shawarar sai dai ya kira police d’in ya had’asu dan ba zai iya jurar ganinta a wannan halin ba!… Muryarta ce ta dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi, a hankali yaji tace “Ina wuni” Jinjina kai yayi kafin a hankali yace “Alhamdulillah” Sannan ya koma ya zauna ya shiga gaida Dad wanda ya nemi waje shima ya zauna. A k’asa kan kafet Mom ta zauna tana ta sun sunkui da kai! Tausayinta fal zuciyar Mijinta dan ya hango tsantsar nadama da shiryuwa a matar tashi, daman chan shi ya san sharrin shaid’an ne! Ba abunda yafi d’aga mishi hankali irin bak’i da lalacewar da tayi, in shaa Allah nan da 3 days zai shirya musu fita suje ayi mata checkup….. Muryar Dad ce ta katseshi jin yana cewa “Abba ya dawo kuwa?? Inason ganinku ne tare.” “Eh to i don’t think so but bara in kirashi” Daddyn ya fad’a yana mai zaro wayarshi daga aljihun wandonsa......... Da kyar ya iya kai wa 2 yau a waje, duk da tarin aiyukan da suke a kanshi haka nan ya baro su birjiki! Ya dawo gida. Yana d’aki shi kad’ai sallah kawai yake iya fita yayi… Anya bai yi gaggawar aurar da Hudan ba kuwa? Kar yaje garin gudun b’atawa su Yaya da Daddy rai ya cuci kanshi fa! He just knew her amman har ya d’auketa d’ungum ya bama wani kuma bama a Kano kusa da shi da anytime yaso zai je ya ganta za su zauna ba! A Uk za su zauna, sai after 4 ko ma 5 years tukunna za su dawo!. Da k’arfi ya sauk’e ajiyar zuciya A ranshi ya raya zai nemi Alfarmar Arshaad akan su d’an zauna anan gidanshi for some time, ko da ace duniya za tayi mishi kallon the most selfish father ne!! Tsaki ya jaa tunawa da yayi Arshaad d’in har ya biya mak’udan kud’i na course d’inshi da zai yi da kuma karatun da Hudan zata fara… Yana wannan tunanin yaji kira ya shigo wayarshi.. D’auka yayi ba tare da ya kalla sunan ba ya amsa ya kara a kunnenshi, sai da Daddy yace “Abba” Tukun ya fahimci wanene dan haka ya gyara zama yace “Ina wuni, ya aiki?” Amsawa Daddy yayi daganan yace masa “yazo ya samesu ga Dad ya zo yana son ganinsu”. “Ok” kawai yace, sannan ya kashe wayar ya mik’e ya fice jikinshi duk a sanyaye. Ko mintuna hud’u cikakku bai rufa ba, ya k’arasa parlourn. Waje ya nema ya zauna suka sake gaisawa.. Ba tare da b’ata lokaci ba, Dad ya fad’a musu sak’on Granpa! Shi ababa wallahi har k’asan zuciyarshi yama manta da wata halitta wai ita Ummi! A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya, ya koma ya kwantar da kanshi a jikin saman kujerar ba tare da yace da su komai ba! Dan in ya cewa Dad zai iya yin abunda Granpa yace a yanzu dai tou gaskiya k’arya yake yi, sai dai maybe ko in gaba. Mom ce ta katse mishi tunanin shi ta hanyar cewa “Abba Ina mai baka hak’uri game da kuskuren da muka aikata maka! Bisa ga biyewa son zuciyoyinmu, ka yafe mana dan Allah.” Shi sai a lokacin ma ya gane ita ce a wajen. Mik’ewa kawai yayi ya cewa su Dad “Bara inje in sha magani In d’an kwanta kaina yana min ciwo, sai da safe.” Daga nan kawai ya nufi hanyar fita…. .....inda ace Mom ta san tunzurashi d’in da maganar ta tayi, da ba zata soma ba! Kawai wani sabon haushin su ne ya sake lullub’e shi.. Hudan is soppose to get married at this age duk wani uba zai so hakan amman dalilin su ya sanya har yake having second thoughts akan abunda ya san shine farin cikin ta, yakamata ace yana taya ta murna yana sopporting d’inta d’ari bisa d’ari amman because of them gashi har yana son aikata abunda za aganshi kamar selfish, kuma ya san inba da kyar ba, su Yaya za su iya jin haushin sa wanda hakan abunda bai tab’a faruwaba ne… Daddy yana shirin yin magana da sauri Dad ya dakatar dashi ta hanyar d’aga mishi hannu! Har Abba ya fice ba wanda yace komai. Yana fita shima Dad d’in ya mik’e yayi musu sallama ya fice. Mik’ewa Daddy yayi daga inda yake ya koma k’asa wajen Mom. Tun kafin yace wani abun ta fad’a jikinshi ta fashe da kuka tana rok’on shi akan “yayi hak’uri shi da y’an uwanshi, in shaa Allah ba zata sake ba! Sharrin shaid’an ne dan Allah kar ya dinga kallonta da abun ya taimaka mata ya goge komai a ranshi…” Lallashinta ya shiga yi yayi hugging d’inta yana jin tausayin ta na sake shiga zuciyarshi.. Da kyar ya samu tayi shiru daganan yace “tazo taje tayi wanka ta huta” Dan da gani tana buk’atar ta tsaftace jikinta da kuma hutu ba na wasa ba.......... Hatta kujerun personal parlour d’inta na chan sama, sabbi dal Daddy ya saka mata Bedroom ma ya saka mata sabbin furnitures duk don ya dan rage mata zafi. Har k’asa kuwa ta durk’usa ta kama k’afafunshi tayi godiya sannan ta sake bashi hak’uri. Shi kam Daddy tausayinta kawai yake ta ji, yaga duk tayi sanyi ta koma kalar tausayi, sai wani nan nan yake yi da ita.... Ko da Auwal ya dawo bai san da labarin dawowarta ba, gashi kuma ranshi a mugun b’ace yake ga gajiya, dan haka direct side d’inshi ya nufa, yayi wanka yayi sallah ya bi lafiyar gado, da kyar sai da yayi da gaske tukunna hoton Sakina da Ashraff yabar idanuwanshi sannan ya samu bacci ya d’auke shi. Auwal yana ajjiye Arshaad ya shiga gida shima. A mugun gajiye yake dan haka tun a hanyar shiga ya zare suite d’in shi ya rik’eta a hannu kafin ya fara k’ok’arin zare necktie d’in! Kana ganinshi ka san bacci kawai yake buk’ata. Ko kallon cikin parlourn bai yi ba ya nufi side d’inshi…. “Ango!!” Yaji muryar Mammy. Da sauri ya d’ago yana kallon setin inda yaji muryar tata ta fito, “ai kuwa ita d’in ce” ya fad’i hakan a ranshi. Da murna ya k’arasa inda take zaune ita da aiima… Ita kam ko wankan ma bata samu tayi ba! Tana nan a yanda ta fito a cell! Yo ina zata iya wanka, ko sama bata samu ta hau ba tun da Aaima ta fad’a mata mummunaan labari take zaune take jiran dawowar Arshaad. Huggin d’inta yayi kafin ya d’ago yayi kissing forehead d’inta tukun yace “Welcome home Mammy, we miss you.” Murmushin takaici tayi kafin ta mike tsaye, cikin tsananin b’acin rai tace “Ba kayi missing d’ina ba Arshaad, da kayi missing d’ina to da ba zaka yi min yaji ka daina zuwa inda nake ba” Kamar zai yi kuka yace “Mammy bana son ganin b’acin ranki, abunda kike so inyi ne ba zai yi ba, kiyi hak’uri please.” Cikin katseshi tace “Ka san cewa Aslam baya yin kwana uku bai lek’o mu ba? Haka Auwal shima! Daddy kuwa kullum sai ya kira waya an had’ashi da Adama Ummi kam daman kowa ya san Mijinta ba zuwa zai yi ba tunda shi ne ya kulle mu! Kai fa? Arshaad da kai da uban ka laifin me nayi muku, a rayuwa? Anya ni na haifeka kuwa Arshaad?” Da sauri ya matsa sosai inda take idanuwanshi har sun cicciko kamar zai yi kuka ya d’aura hannunsa ya rufe mata baki kafin yace “Mammy pleas...” Bai k’arasa ba ta buge hannun cikin tsananin b’acin rai tace “Kar ka yi mini ‘please’ bana son ji! Kun riga kun nuna min matsayi na da kai da ubanka! Naji nagani kuma na fahimta, akwai lokacin da na ware muku kai da shi zan waiwayeku amman ba yanzu ba dan wallahi sai kun san kun wulak’anta, hak’urina ya k’are a cikin gidan nan! Amman yanzu akwai boss d’in da ya kamata mu fara kashewa ni da kai a yau kafin komai.” Bata jira jin me zai ce ba taci gaba “Naji labarin za kayi aure! Jibi ko? To wallahi bari kaji In dai sunana Rukayya kuma nonona ka sha to wallahi muddin ka auri wannan Yarinyar ni kuma a ranar zan tsine maka......................” “Innalillahi wa innailaihirrajiun” Itace kalmar da Arshaad yake ta nanata wa a ranshi! Ya kasa motsi ya kasa cewa komai…… A ranshi yace “Wannan shine abunda nake gudarwa since day 1, ya zan yi da Mammy, ya zan yi da zuciyata wadda na san muddin aka fasa aurena da Hudan tabbas tarwatsewa za tayi”. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 51 Mammy tana gama fad’in haka ta wuce sama, haka Aaima itama ta bi bayanta tana jin kamar an tsundumata a Aljannah! Suka barshi shi kad’ai a tsaye. A hankali ya nemi kujera ya zauna ya sunkuyar da kai sannan yasa hannu ya dafe kan da hannu biyu.. Yafi minti ashirin a haka, chaan! Ya ji an dafa shi, yana d’agowa suka had’a ido da Dad. Kallon shi Dad d’in yake yi trying to fassara yanayin da yake ciki. Da sauri Arshaad ya mik’e tsaye ya fara k’ok’arin saita kanshi, cikin k’ok’arin danne abunda ya tokare mishi k’irji yace “Ina wuni Dad” Sai da Dad d’in ya d’an k’uraa mishi ido tukun yace “Lafiya kake kuwa?” Murmushi kawai Arshaad d’in ya k’ak’alo kafin yace “Alhamdulillah! All is fine na gaji ne kawai, bara inyi freshening off in kwanta” Ya k’arashe maganan da k’ok’arin barin wajen dan ya lura da kallon da Dad d’in yake mishi so yake ya gane yanayinshi ne. Har ya d’anyi gaba yaji Dad d’in yace “Arshaad” Tsayawa kawai yayi ba tare da ya juyo ba. Ajiyar zuciya Dad d’in ya sauk’e kafin a hankali shi ya taka ya k’arasa inda yake ya tsaya a gaban shi yasa hannu ya dafa kafad’ar shi, cikin kulawa ya fara magana “Son, irin haka is normal! Most a times couple basa tashi samun matsala sai ya rage y’an kwanaki kad’an aurensu.. Ka kwantar da hankalin ka kar ka sa komai a ranka, za ku hirya soon komai ya wuce kamar bai faru ba. Wannan duk aikin shed’an ne so karka bari yayi galaba a kanka. Allah yayi muku albarka.” Cikin sigar zolaya ya ci gaba da cewa “Nan da jibi fa ka zama magidanci, a nan ne zaka fara facing real life da real issues So garama ka shirya! Kar ka bari small things irin haka suyi breaking naka.” Da k’arfi Arshaad ya taune lip d’inshi na k’asa, yana jin yadda zuciyarshi take tafarfasa! Ba k’aramin kokawa yayi da makogwaro da harshenshi ba kafin ya samu su bashi had’in kai wajen furta kalmar “In shaa Allah Dad, thanks a lot.” Murmushi Dad d’in yayi kafin ya d’anyi tapping kafad’ar shi da hannunshi ke a kai yace mishi “good night” daga nan ya nufi hanyar side d’inshi, ya bar Arshaad tsaye a wajen… In banda ajiyar zuciya babu abunda Arshaad yake sauk’ewa a jere a jere. Ganin ya fara ganin duhu duhu, kar yaje ya fad’i a wajen yasa ya lallab’a ya nufi side d’inshi shima dake nan a k’asan. Da kyar ya kai kanshi toilet bayan ya ajjiye suite d’in hannunshi akan gadon. Ko agogon hannunshi bai samu ya cire ba ya yana shiga toilet d’in ya sakarwa kanshin shower ta ko’ina da ruwa mai mugun sanyi! Ya dad’e a haka kafin da kyar ya samu ya fito kayan jikinshi na d’igar ruwa.. Dai dai nan ya ji wayarsa ta hau ringing, hannu yasa a aljihu kafin ya zaro wayar k’irar iphone 13 ya kalla screen d’in! A take damuwar da ya samu ta d’an ragu ta dawo mishi sabuwa ta sake hauhawa sakamokon ganin mai kiran nasa.. Har ta tsinke bai d’aga ba kuma bai daina kallon screen d’inba! Yana a yanda yake wani kiran ya sake shigowa… A hankali hannunshi na rawa ya d’auka ya kai kunnenshi kawai yayi shiru bai ce komai ba. Cikin sanyin muryarta yaji tace “Ya Arshaad.” Ajiyar zuciya ya sauk’e ya lumshe idanuwanshi da suka yi jaaa wanda hakan ya bawa hawayen da yake ta addabar zuciyarshi daman zubowa ta ido d’aya! Kafin d’ayan idon shima ya samu damar zubo da nashi hawayen... Ajiyar zuciya kawai taji yana sauk’ewa a jejjere Hakan yasa a d’an rud’e tace “Ya Arshaad ka yi mini magana pls, baka da lafiya ne yanzu? Mai ya faru” Da kyar ya iya k’arasawa bakin gadonsa ya zauna dan ya fara rawar sanyi ba kad’an ba! Yana zama wata wawiyar atishawa ta kece mishi wanda yasa Hudan mik’ewa daga kwancen da take, kafin tace “Mura ko? Sorry sannu ka sha magani tou?” Sai a sannan taji yayi magana “Hudan!” “Naam” tace da sauri dan daman so take taji ya furta wani abun dan shirun nashi ba k’aramin tsoratata yayi ba. A hankali ya d’an yi tari kafin yace “Do you love me??” Ta d’anji kunyar tambayar amma jin yanayin shi da kuma muryarshi wata iri yasa tace “Yes, a lot” A hankali yace “Say it” Shiruu, ta d’anyi kafin a hankali yaji tace “I love you” Sai da yad’an lumshe idanuwansa kafin yace “To what extent??” Ya sake jeho mata wata tambayar. Zuwa yanzu kam yad’an fara birkita mata lissafi hakan yasa tace “Ya Arshaad meye ne yake damunka?” Tayi masa tambayar kamar zata fashe da kuka. Cikin tsare gida yace “Just answer me! How much?? To what extent za ki iya zuwa domin kiga mun mallaki junan mu??” Ita dai ba abunda take fahimta daga shi zuwa yanzu, gashi tana jin yanda numfashinshi yake seizing sama sama! Daurewa tayi tace “Kamar yaya?” Dan da gasken bata fahimta ba. Da kyar ya dedeta numfashinshi kafin yace “Idan Mama tace ki hak’ura da ni, za ki hak’ura?? Sai da ya sake maimaita mata tambayar tukunna tace “Maama ba zata tab’a cewa In hak’ura da kai ba! Meyene ya faru na kasa gane komai” Bai bata amsar ba sai cewa yayi “Idan Maama tace ki hak’ura da ni, za ki hak’ura??” Ta kasa fahimtar inda ya dosa, kawai sai ta yanke shawarar ce mishi “Ya Arshaad ai albarkar iyaye shine abinda ake buk’ata! In basu da niyyar sakawa meye amfanin auren da za ayi babu albarka?” Rintse idanuwansa yayi da k’arfi! Tuni numfashinshi suka fara korar juna… She can feel it dan haka duk sai ta sake rud’ewa ta hau kiran sunan shi amman yak’i kulata, k’arshema wani irin tari taji yana yi, yayi kusan 3 minutes yana tarin Hudan tana kuka tana kiran sunanshi amman shiru wanda hakan har sai da ya farkar da Sakina da Khadijah amarya y’ar Anty Zainab da suke d’aki d’aya da ita daga bacci. Ganin yanda duk ta rud’e ne yasa Sakina ta shiga tambayarta…. Karb’ar wayar Sakina tayi itama ta shiga kiran sunan shi tana “Are you there? Are u okay??” Amman tsit kake ji ko tari babu. Rikicewa suka yi… Da kyar idea ta fad’owa Sakina hakan yasa da sauri ta d’auki wayarta ta danna kiran Aaima! Sai da kiran ya kusan tsinkewa tukunna aka d’auka, cikin gigita Sakina tace Aaima ina wuni, sorry na tashe ki, Ya Arshaad ne bashi da lafiya, dan Allah ko zaki gayawa Dad in yana gida a duba shi ko kuma ki tura wani wanda yake kusa….” Shiruuu, Sakina taji anyi! Hakan yasa ta sake cewa “Aaima” Ajiyar zuciya taji Aaiman ta sauk’e sannan ta fara magana “Ki turo Hudan mana ta zo ta duba shi! Daga nan ma sai su yi sorting out decision d’in da ya kamata su yanke.. Besides a nan ba wanda zai kulashi saboda rashin lafiyarshi ba zamu iya yi mishi maganinta ba. Spoiler alert!! Bara kiji abunda na san ya jawo mishi ciwon...... Mammy ta dawo d’azu at last ita da su Mom! And tace masa ‘ya hak’ura da auren Huda ko kuma ta tsine mishi!’ Wannan shine abunda ya janyo mishi rashin lafiya na riga da na sani.” Tana gama fad’in haka ta ajjiye wayar. K’amewa Sakina tayi ta kasa cire wayar daga kunnenta! Sai da Hudan ta tab’ota tace “Ya ake ciki Sakina?” Tukunna tayi firgigit ta dawo daga tunanin tashin hankalin data fad’a na y’an sakanni.... ….Dama da ita bata tab’a fadawa kowa ba ne amma haka kurum idan ta tuna Mammy bata san dalili ba sai taji gabanta yana ta fad’uwa! Dan bata san ya tsakaninta da Huda zai kasanceba. Kuma ta lura kamar Arshaad d’in yana ta saurin ayi ayi ai auren su samu su bar k’asar! Tabbas sai yanzu ta fahimci dalilinshi.. To amma mai yasa Ya Arshaad zai so ya had’a ta da surukar da ba zata amsheta ba? Duk kuwa da tsananin k’aunar da suke yiwa juna ai da sun hak’ura!…… “Sakina, akwai matsala ne?” Muryar Hudan cikin rauni, ta katse mata tunaninta…. Juyawa tayi suka had’a ido! A take wani tsananin tausayinta ya rufeta dan bata jin a cikin shekaru ukun nan akwai lokacin da take hango tsantsar k’aunar Arshaad a idanun Hudan kamar wannan lokacin. Da kyar ta iya ce mata “Aaiman bata gida, bara in kira Auwal kawai.” Ta fad’i haka tana me mik’ewa ta fice daga d’akin gaba d’aya. Hudan kwata kwata bata gamsu da maganar tata ba dan haka ta mik’e ta bi bayanta. Suka bar Khadija wadda itama bata wani yarda da maganar Sakinar ba dan ta lura da yanayin da ta shiga tun fara wayarta da wadda suka kira da ‘Aaima’. Tana fita ta samu damar zubar da kwallar da take ta k’ok’arin rik’ewa! Yanzu Ina mafita? Meye abunyi ? Sune tambayoyin da suka toshe mata kwanya sannan ta kasa samun mai bata amsar su. Daman y’an layi har sun fara k’ananan maganganu suna cewa ....Allah dai yasa tarihi kar ya maimaita kanshi Ita maryam bata daddara da family d’in Abba da abunda shi kanshi Abban yayi mata ba shine zata aurawa Huda nephew d’inshi dan kawai taga yana da masifar kud’i! Ga dai Ummu ita da ta auri saffa saffa hankalinta a kwance rayuwarta gwanin ban shaawa amman ita har yau bata samu kwanciyar hankali ba a ta dalilin So da Buri! Ta mannewa mutumin da yafi k’arfin ta nesa ba kusa ba.... Jin k’arar bud’e k’ofar d’akin nasu ne ya sanya Sakina goge hawayenta da sauri, sannan ta lalubo number Auwal ba dan ranta yana so ba ta fara kiranshi…. Bacci bai dad’e da d’aukarsa ba dan bai dad’e da kwanciya ba amman yana fara baccin ya hau mafarkinta............. Yana cikin mafarkin nata k’arar wayarshi ta katse mishi mafarkin…. Kamar ba zai juya ba bayan ya farkan sai kuma yayi tunanin ko Granpa ne dan haka yayi tsaki ya lalubo wayar akan bedside ya amsa ya kara a kunnnen shi ba tare daya duba mai kiran nasa ba. Jin shiru yasa tace “Ya Auwal” A hankali. Bude idanuwansa yayi da kyau kafin ya zaro wayar daga kunnenshi ya kalla sosai ya tabbatar itan ce tukunna ya mayar da wayar kan kunnensa ya mik’e zaune yana adduar ‘Allah yasa lafiya’ dan ya san ba k’aramin abu bane zai sanya Sakina ta kirashi kuma cikin daren nan ba. Sai da ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace “How far” Dan lokaci d’aya ranshi ya b’aci bayan ya tuno ta Ita da Ashraff d’azu. Ba tare da b’ata lokaciba tace mishi “Ya Arshaad ne suke tunanin bashi da lafiya dan yanzu ma kamar suma yayi suna cikin waya da Hudan.” Ta san maybe Hudan ce ta fito d’azun kuma maybe tana tsaye a bayantata dan haka sai ta tak’aita maganar tata sannan tace “Dan Allah yaje ya dubo shi” “Okay” Kawai yace daga nan ya kashe wayar ya mik’e ya fad’a toilet yad’an d’auraye fuskarshi ya chanja zuwa jallabiya tukunna ya fita.......... Sai da ya daddannawa gate man d’in zagi, tukunna ya barshi ya fita A cewar shi (gateman d’in) Daddy ya hana a na barinshi yana fita cikin dare. Sai mita yake yi shi kad’ai a mota haka ya isa gate na estate d’in MT ..a ranshi yana aiyyanawa ‘Da mutane sun san halin da yake ciki to da ko kallonshi ba zasu dinga yi ba! Komai b’ata mishi rai yake yi tun d’azu...’ Allah ya so shi bai samu matsala da mai gadin main estate d’in ba, sai dai ya rok’esa akan ‘ya bi a hankali kar ya bari Granpa ya ganshi dan zai iya cewa a bakin aikin shi’ Jinjina kai kawai yayi ya wuce ciki. Ya dad’e yana knocking jin shiru yasa ya yanke shawarar kiran Aaima yace mata ‘ta kira layin wata a cikin masu aikin gidan tazo ta bud’e mishi k’ofa.......’ Tunda Sakina ta kira ta bacci ya k’aura daga idanunta, tana cikin chatting kiranshi ya shigo wayar tata. Ta dad’e tana kallon number, kasancewar ta dad’e da goge numbershi amman ta na nan a kwakwalwarta bata gogu ba! A take jikinta ya mutu.. Sai da wayar ta kusan tsinkewa tukun ta samu damar amsawa, cikin sanyin jiki ta kara a kunnenta tace “Hello” Ba tare da ya amsa ba yace “Aaima Arshaad is sick, na zo duba halin da yake ciki kuma k’ofan ank’i bud’ewa.. Can you do me a favor ki kira wani wanda kika sani a cikin gidan yazo ya bud’e min? It’s an emergency” Tunda ya fara magana ta lumshe idonta har ya kai aya a hankali tace “to” kawai, ta tsinke kiran. Kamar 5 minutes yaji ana k’ok’arin bud’e k’ofar, ana bud’ewa ya kutsa kai ciki ba tare da ya kalli bayan k’ofar ba inda take, yayi hanyar side d’in Arshaad direct kawai. “Ina wuni” Yaji muryar ta. D’an juyowa yayi ya kalleta a ranshi yace “Ashe ta dawo.” Ba yabo ba fallasa yace “Lafiya” Kawai ya juya ya nufi hanyar part d’in Arshaad. “Ya k’ara haske, sai dai yad’an rame kad’an! Ya k’ara kyau.” Ta fad’a a k’asan ranta! Bata san dalili ba amman taji zafin yanda yayi mata, taso ta koma sama kawai abunta amman sai ta tsinci kanta da kwad’ayin bin bayanshi, dan haka ta rufe k’ofar ta nufi side d’in Arshaad. Direct main bedroom d’in dake side d’in Auwal ya nufa. Yana shiga ya ganshi yashe a k’asa da jikakkun kaya. Da sauri ya k’arasa wajen ya durk’usa ya hau jijjigashi yana kiran sunanshi…. Dai dai nan Aaima ta shigo, duk da fushin da take yi dashi hakan bai hanata fashewa da kuka ba da ganin halin da yayan nata ke ciki. Da sauri Auwal ya juya gareta yace “Yi maza Aaima d’ebo ruwa a toilet yi sauri plss..” Ya fad’a cikin gigita da kid’ima. Da gudu ta nufi toilet d’in ta d’ebo ruwan ta fito ta na zuwa Auwal ya amsa ya hau yayyafa mishi…. Sai da suka fidda ran ma zai farfad’o tukunna yayi wata wawiyar ajiyar zuciya wadda ta taho mishi tare da tari! Auwal ne ya d’an d’ago shi kad’an yahau bubbuga mishi baya yana jera mishi sannu. Da kyar ya samu tarin ya tsaya ya shiga jejjera ajiyar zuciya.... Sai da Auwal ya kamashi ya kaishi kan gadonshi, tukun ya zaro waya ya fara k’ok’arin kiran family doctor d’insu…. Kamar Arshaad d’in ya san me yake shirin yi, yace nasa “Kar ka kira kowa Auwal, i’m fine. Please.” Kallonshi Auwal d’in yayi kafin shima yace “Dan Allah kar ka gwada yin wannan taurin kan! Ka bari a kirashi ya duba ka kawai.” Cikin d’an fushi Arshaad yace “Auwal zamewa nayi na fad’i na buga kaina! Yanzu kuma na farfad’o… Ka gaya min in akwai abinda Doc zai yimin idan ya zo d’in bayan wanda kukai min.” D’an k’uraa mishi ido Auwal d’in yayi kawai ya tsaya yana kallonshi. A hankali Arshaad d’in ya koma ya jinjina a jikin gadon sannan yace “sorry” Ajiyar zuciya Auwal ya sauk’e kafin yace “Are you sure that’s all?” Jinjina kai kawai Arshaad d’in yayi. Auwal bai wani gamsu da maganan shi ba but yaga kamar he wants to be alone shiyasa yace “Shikenan, Allah ya kare gaba, ka kira su Hudan hankalinsu ya tashi sosai. And dan Allah ka sauya kayan jikin nan naka, sai da safe.” “Ok” shine abunda Arshaad yace sannan ya k’ara da cewa “Thanks a lot” Murmushi yayi kawai yace mishi “Good night” Daganan ya nufi hanyar fita. Kallonshi (Arshaad) itama Aaima tayi tace “Ka kira wayana if you need anything” Jinjina mata kai kawai yayi sannan ya fara k’ok’arin mik’ewa dan chanja kayan jikinshi. Ganin haka yasa Aaiman yi mishi sai da safe itama ta juya tabi bayan Auwal wanda har ya kusan ficewa… Sai da ya kusan isa k’ofar fita ta main parlour tukun ta samu ta cin mishi ta wuce ta isa bakin k’ofar ta sa hannu ta bud’e. Ba tare da ya kalletaba dan shi har ga Allah ta fara k’ular dashi Ya sa kai zai fice. Daurewa tayi tace “Mun gode sai da safe” “Allah ya kaimu” yace daga nan ya fice. Ta jima a parlourn bayan ya fita.. Daga k’arshe ta nufi side d’in Arshaad har bedroom ta lek’a ganin yayi bacci yasa ta fito ta nufi sama ta koma d’aki. Da kyar ta samu bacci ya d’auketa. Shi kuwa Arshaad yanda yaga rana haka ya ga dare! Yana jinta lokacin da ta shigo, baya san ganin kowa shiyasa yayi baccin k’arya, ko Hudan text kawai ya iya tura mata cewar ‘he’s okay’. Kafin safiya ya gama deciding yanda zai yi da abunda zai cewa Mammy amman still yana d’an d’arr! Ga fargaba ga tunani barkatai shiyasa zazzab’i yace salama alaikom........... Zazzab’in da ya rufar masa ne yaasa da kyar ya iya mik’ewa yayi sallah a daddafe! Kafin 7 kuwa zazzab’in yayi masa rufdugu…. Ganin yana shirin mutuwa ya sanya shi kiran family Doctor d’in da baya so, dole! Ya kira fad’amshi yana zazzab’i mai k’arfi. Ba a rufe 30 minutes ba Doctor d’in ya iso.. Allurai yayi mishi bayan ya duddubashi dan ya san Arshaad ya tsani magani, daga nan ya jona mishi drip yayi mishi sallama… Sai wajajen 11 drip d’in ya k’are da kansa ya zare ya danne, bayan some minutes ya mik’e ya fad’a wanka. Yaji dad’in jikinshi ba kad’an ba kuwa. Yana fitowa ya d’an shafa mai da turaruka ya zura wata cream jallabiya mai gajeran hannu… A hankali ya k’arasa bakin gadon ya d’au wayarshi ya fara kiran Hudan dan tun da safe yaga message d’inta. Bata wani dad’e tana ringin ba ta d’auka! Bayan sun gaisa ya tabbatar mata da ‘he’s okay daman kawai dan zazzab’i ne’. Tace mishi “Anjima around 1 ana buk’atar shi za suyi traditional event d’insu na yaren Shuwa kuma dole sai yana wajen! Inda hali ya turo driver kafin nan, yazo ya karb’a mishi kayan tradition d’in da aka tanada domin shi (wanda zai saka a event d’in) Kayan ba su iso ba sai d’azu shiyasa bata bashi da wuri ba.” Da “to” ya amsa ta daga nan suka hau hirarsu dan yaga kamar hankalinta still a d’an tashe yake. Sun jima suna hira dan sun fi 30 minutes kafin suyi sallama. A hankali yayi shiruuu, yana y’an tunane tunane.. Chaaan! Ya turawa driver d’in da zai karb’o mishi kayan nashi message daga nan ya mik’e yayi kalmar shahada ya fita ya nufi sama wajen Mammy. A stairs suka had’u da ita tana k’ok’arin sauk’owa! Kamar bata ganshiba haka tazo ta wuceshi. Hannunta yayi saurin rik’ewa ya juyo a hankali yace “Haba Mammy.. Ki saurareni please mana.” Ya fad’i hakan kamar mai shirim fashewa da kuka. Ba tare da ta kalle shi ba tace “Ka bari idan Allah ya kaimu gobe naga kayi abunda nace sai in saurareka” “Meye abunda kike so yayi miki goben??” Suka ji muryar Dad a bayan su!. Da sauri Arshaad ya juya yana kallonshi gabanshi na tsananta fad’uwa! Ba tare data juyo ko ta damu da Dad d’inba tace “Ai gaka ga shi nan! Kana iya tambayarshi.” Tana gama fad’in haka ta nufi k’asa wajen bakinsa da take expecting dan sune ma suka ce mata sun kusan shigowa ba daban su ba da babu abinda zai sauk’o da ita k’asan! Tana buk’atar time ita kad’ai, dan ita kanta bata san daliliba amman komai ya kunce mata.. Kame kame Arshaad ya fara bayan ta sauk’a… Babu yadda Dad bai yi da shi ba amman yace mishi “ba komai! Kawai sun d’an samu issue ne shi da ita lokacin tana cell shine yake so suyi settling”. Sam Dad bai yarda da shi ba dan kwata kwata babu kamanceceniya a cikin maganar shi da tata!. Fahimtar da Dad yayi Arshaad d’in ba zai gaya mishi komai ba ne yasa kawai yace “to, shikenan ka samu ku shirya d’in kafin ka bar gidan nan.” Yana gama fad’in haka ya wuce shi shima yayi k’asan. Sai a sannan Arshaad ya sauk’e ajiyar zuciya He needs to talk to Mammy! Idan tak’i ta lallashi tabbas zai b’ullo mata ta hanyar da bata zata ba! Akwai abubuwa da dama waenda ya sani amma yayi shiru kuma ta san ya sani but it’s like kamar ta manta, so he has to remind her!. Sannan ya san ta inda zai b’ullo mata ta yarda dan yaga alamun ba lalle ta yarda cikin sauk’i ba gashi babu enough time!…. Ya jima a wajen kafin ya juya ya wuce sama da niyyar d’an bata time Kafin ya sake ganinta! Yana da full hope d’in zai yi nasara bi izinillahi. Mammy na sauk’a k’asan ta fara shan mamaki.. Kulolin abinci kala kala da su drinks ake ta shigowa da su! Bata ida fita daga wannan mamakin ba taga friends d’inta da sisters d’inta har da Mahaifiyarta suna ta shigowa har da ankon super d’in su da suka yi a jikinsu…. Da sauri ta k’arasa kusa da yayarta ta kamota tace “Me kenan? Wats the big idea?” Murmushi Haj Binta tayi kafin tace “Wunin d’an mu za muyi mana! Anjima kad’an kuma muje muga Amarya naji Dad yace za suyi traditional day d’insu suma daga nan mu bata kyaututtuka Naga ke baki son zancen shiyasa ma na zagayeki na kira Dad. Anko kuwa ni na fitar kuma gashi kowa yayi, ni da su Hajiya ( Mahaifiyar su) tun lokacin da aka sa rana dama muke ta shirye shiryen mu. Matsowa Mahaifiyar tasu tayi kusa da su ( ita da sister d’in tata ) kafin itama ta fara magana “Ki nutsu ki bari ayi komai a gama daga nan sai a san abun yi! Ni na hanasu su fad’a miki komai akan lamarin auren, gudun samun matsala dan na san halinki. In dai ni na haifeki to inaso ki kwantar da hankalinki kiyi hak’uri, ni kaina ba wai son had’in nake yi ba! Amman ki bar ni da su kawai ai in sun san wata basu san wata ba! Kuma kar ki bari kowa ya fahimci halin da ake ciki, ki nuna kina so inda hali ma ki shirya muje ki bawa ita Yarinyar kyauta da hannunki a gaban kowa…” Ganin friends d’in Mammyn sun tunkarosu ne yasa Mahaifiyar tata yin shiru ta fara yak’e.. Suna zuwa kuwa suka hau tayata murna kowa na farin ciki tare da yi mata ya jiki (dan ce musu aka yi ita da su Mom duk sun yi inhealing dangerous abu shine aka fitar da su k’asar waje suka yi jinya sai jiya suka dawo). Haka nan suka k’arasa tsakar falon aka zazzauna… Masu decoration suka shigo suka hau d’an gyaggyara parlourn Yayar tata ce tace “bara taje ta ajjiye abu daga nan ta cewa Arshaad ya shirya, su d’anyi hotuna a nan kafin a tafi event d’in su Hudan..” Sama ta nufa da niyyar ajjiye abu tukun ta je ta kira Arshaad d’in Tana shirin hawa suka had’u da Dad yana sauk’owa… Cikin mutunta juna da barkwanci suka gaisa daga nan yace mata “Ta kirawo masa Mammy, su sameshi su biyu a side d’in Arshaad.” Mammy na zaune a cikin friends da y’an uwanta amman kwata kwata hankalinta baya a garesu! K’ok’ari take taga ta tirsasa zuciyarta ta aminta da abinda Mamanta tace mata yanzun, amman furr ta kasa... A wannan yanayin sister d’in nata tazo ta rad’a mata sak’on Dad a kunne daga nan ta wuce ta nufi parlourn Arshaad. Da kyar Mammy ta iya mik’ewa tabi bayan ta.. Sauk’owar Arshaad kenan yaga sun nufi side d’inshi, A ranshi yace “perfect” Duk fa bai san me za suyi anan d’in ba. K’arasawa yayi ya gaggaisa da bak’in, kakarshi tana ta tsokanarshi, daga nan ya wuce shima. A parlourn suka tarar da Dad yanata faman kai kawo.. Suna shigowa ba tare da b’ata lokaci ba yace “Binta, ga y’ar uwarki nan, ki tayani tambayarta.. Akwai abunda suke b’oye min ita da Arshaad wanda ban sani ba! Na san halinta da sanabe kala kala dan haka idan akwai wani abun gara tun farko ta fito ta fad’a kar taje ta yiwa mutane shirme!..” Hajiya Binta tana shirin yin magana Mammy tayi caraf ta amshe ta fara magana “Ai kai da kanka yanzu me kace? Muna b’oye maka, ko? To kuwa ai kaga tunda muka b’oye maka d’in to bai shafeka ba kenan! Infact babu abunda ma ya shafeka na daga rayuwar ni da y’ay’ana. Da kace kana kirana i thought welcoming d’ina zaka yi” Murmushin takaici tayi kafin ta juya ga Hajiya Binta tace mata “Ko kin san tun jiya dana dawo ban ga k’eyar bawan Allah n nan a kusa da ni ba balle ya tambayeni lafiyata ko ya nake? Ai ko ni kad’ai na aikata laifin b’oye y’ar gold d’inku wallahi ban chanchanci haka daga gareka ba ko dan darajar Arshaad da Aaima!” Ta fad’i haka tana takawa inda yake, daga nan taci gaba “Sannan yanzu ka wani kwaso k’afa kazo kana wani waye waye… Kai har kana da kunyar yi min wannan maganar? Bayan abunda ka yi? To bari kaji bai shafe ka ba! Ka zuba ido zaka gani tare da kowa idan Allah ya kaimu gobe.” Tana gama fad’in haka ta juya ta nufi hanyar fita. “Idan kika taka k’afarki kika bar min parlourn nan ba tare da kin fad’a min abunda nake son ji ba to a bakin auran ki.” Ba mammy ba hatta Hajiya Binta sai da gabanta ya yanke ya fad’i. Juyowa tayi tana kallonshi da idanuwanta da suka fara chanja launi, cikin tsananin takaici tace “Namiji k’anin ajali! Ai Aisha ta dawo dole ka yi min haka. To bari kaji in gaya maka wallah ko ka sakeni babu inda zanje sai dai in kai ka fita ka bar mana gidan nan ni da y’ay’ana!” Cikin katseta yace “Rukayya kar ki yi underestimating d’ina! Dan wallahi zan yi miki abunda ko me sunana aka kira sai kin ji kin tsani wanda ya kira sunan! Baki san a ya’ya nake ganin ki ba a halin yanzu, kar ki kaini bango! Wallahi ba dan darajar Aaiima da Arshaad ba da tuni na dad’e da sauya miki rayuwa.. Bana son dogon magana dan bana jin iya zama mai tsawo a inuwa d’aya da ke! Ki fad’amin abunda nake son ji in fita.” Ya fad’i haka cikin kakkausar muryar da take baiyyana tsanannin b’acin ran da yake ciki. Haj Binta ce tace “Kayi hak’uri dan Allah, Mammy ke kuma ba a haka! Ki bari wannan matsalarku ce daga baya za ku yi settling ke da shi Yanzu ki fad’i abunda yake son ji tunda ya nuna yana da buk’atar hakan” Cikin tsananin b’acin rai Mammy tace “Ba zan fad’a ba! Wallahi ba zan fad’a ba” Sannan ta juya gareshi tace “In kana buk’atar ji Yahaya ka zo ka shak’eni sai in fad’i maka ta k’arfin tsiya!! Da kake wani maganar sauya mini rayuwa, na nawa kuma? Bayan azabtar da mu d’in da ku kayi me ye kuma kuke tunanin za ku yi kuma wanda yafi wannan??. Ba dai rashin sanin ya kamata ka d’aurawa kanka ba, rana d’aya? To wallahi dede nake da k’ugunka! Maganace nace ba zan fad’a ba In kuma ka matsu to kazo ka shak’eni In fad’eta.” Cikin tsannnin fushi ya tunkarota kamar wanda zai rufe ta da duka! Dasauri Arshaad wanda shigowar shi kenan yanzun ya shiga gaban Mammy ya tsaya Hajiya Binta kuma taci gaba ta k’ok’arin hana Dad d’in k’arasawa inda Mammyn take! Dukkannin k’arfin da Allah yayi mata tayi amfani dashi wajen ingije Arshaad d’in sannan kafin yayi nasarar tsaidata ta tafi gaban Dad ta tsaya! Tana mai jin wani tuk’uk’in bak’in ciki yana taso mata, babu abunda idan ta tuna yake k’ona mata rai irin yanda taga Daddy yana ziryar zuwa wajen Adama last zuwanshi da yayi har kusan kuka taga yayi daga nan ma yace ‘ba zai iya sake ganinta a haka ba’ Tun daga ranar kuwa idan bai kirata sau d’aya ba tou zai kira sau biyu! Amman ita ko lek’enta ko waya Dad bai tab’a yi yace a bata ba, ita tana chan tana tunanin sa ashe shi yana nan Aisha ta d’auke masa hankali! Kalli fa sarai ya san ta dawo amman ko lek’enta bai yi ba kuma suna cikin gida d’aya, sai yanzu dan rashin kunya da tsaurin ido ya buk’aci ganinta kuma ko alamar tambayarta ya take bai yi ba instead ya hau wani tsattsare ido yana hucin banza.. Waennan takaicin ne suka sanya ta kasa cewa komai kawai ta zube a wajen ta fashe da wani mugun kukan bak’in ciki. Cikin son kawar da lamarin Arshaad yace “Dad, dan Allah ka bar maganar nan, na fad’a maka ba komai fa”. Banza Dad yayi da shi kawai ya juya ya fice! Yaso ace Mammy tayi mishi wani shirmen yau wallahi da sai ya yi mata abunda bata tab’a tsammani ba! Ya san at least zai samu peace of mind at last. Yana fita Mammy ta mik’e! Tunda take a rayuwar ta bata tab’a jin kishi da takaici da tashin hankali da bak’in ciki irin na yau ba! Ta rasa dalili amma ko y’ar kissar da ta saba yiwa y’ay’an nata da Dad d’in ta kasa kuma bata jin zata iya, babu abunda take so kuma take buri irin taga ta b’atawa Dad rai ko ta samu zuciyarta ta d’anyi sanyi. Tayi imani yanzu haka wajen Aisha zai tafi yaje ya ganta yad’an samu nutsuwa hankalinshi ya d’an kwanta alhalin ita kuma gashi ya k’unsa mata bak’in cikin da bata jin zata iya mantawa da shi har abada! Taya zai yi mata haka? Taya zai banzantar da ita har haka saboda Allah kamar wata dabba? ‘Inaaa!! Ba zai yiu ba Wallahi’ Shine abunda ta fad’a ta gyara tsayuwarta tana k’ok’arin yin hanyar waje….. Da sauri Hajiya Binta ta tareta tace “Meye haka ne wai Mammy? Ba a isa a fad’a miki kiji bane? Ina za ki ji yanzun?” Cikin kukan Mammy tace “Kina ganin fa abubuwan da Yahaya yake yi mini Ya gama b’ata min rai ya fice ya tafi wajen uwar gidan shi ya bar ni ni anan zuciyata ta kama da wuta kenan ko me? Ki cikani kawai, wallahi bai isa yayi farin ciki ba, ba inda zai je yau, kullle k’ofar gidan nan zan yi sai dai mu kashe juna ni da shi a cikin gidan nan!” Da sauri Arshaad ya matso kusa da su ya rik’eta, wani tsananin takaicin sa take ji hakan yasa ta juyo da sauri ta kifa masa Mari! Sai kuma ta fashe da kuka, cikin kukan tace “Ai kaima baka kishina Arshaad, a tunanina ko Hudan y’ar gwal ce wallahi ba za ka so auren ta b. Taya za ka had’ani da ita mu zama surukai!? Ko kasan cin mutuncin nan da aka yi min shine abu mafi muni a rayuwata?. Na fad’a na k’ara fad’a yanzu ma zan maimaita maka ‘Wallahi idan ka aureta sai na tsine maka!’.” Arshaad bai san lokacin da ya tsugunna a wajen ba ya fashe da wani mugun kuka. Cikin b’acin rai da kafiya Mammy tace “Kuma ko event d’in yau da suka gaiyyaceka ban yarda ka je ba! In kaje kuma wallahi Allah ya isa ban yafe ba! Zan ga wa zaka zab’a tsakanin ni da ita.” Da sauri ya mik’e yace “Haba Mammy ya kike so inyi ne? Ki tsaya ki saurareni kuma kin k’i.. Dad ne ya nema min aurenta Abba kuma ya bani, idan nayi miki biyayya su kuma bijire musu kike so in yi?” Da sauri cikin katsesu Hajiya Binta tace “Rukayya ban tab’a tunanin baki da hankali ba sai yau wallahi! Ni, na fad’a miki! Mahaifiyarmu, itama ta fad’a miki! Amma ba za ki ji ba? Waye a cikinmu zai fad’a miki abunda zai cutar da ke? Munce kiyi hak’uri ko? Waennan irin y’an iskan aljanu masu shegan taurin kai kika kwaso a cell d’in ne wai?” In banda gunjin kuka babu abunda Mammy take yi. Cikin son su kad’aita iyaka su biyu dan ta samu damar lallashinta da fahimtar da ita Hajiya Binta ta cewa Arshaad “wuce ka tafi ka shirya ku je ku yi event d’in, idan ka dawo sai mu k’arasa” Ai kuwa Mammy na jin haka ta tafi da gudu hanyar k’ofar fita ta tsaya tayi stretching hannunwanta sideways ta kare k’ofar tace “wallahi idan ka fita sai na tsine maka!!” Da sauri Hajiya Binta tazo ta kama hannun tana k’ok’arin janyeta tana cewa “Arshaad zo ka wuce” a ranta tana aiyyanawa ‘Tabbas akwai abu a kan Mammy’ “Zo ka wuce nace kar ka bari tayi maka spoiling day d’inka!” Hajiya Binta ta sake maimaitawa ganin Arshaad d’in ya k’ame a waje d’aya abun tausayi. A hankali ya k’araso ya shiga lallab’ata, Hajiya Binta itama tana yi, amman fur!! Mammy ta yi kane kane a hanyar tana ta faman maimaita kalma d’aya ‘Idan ka fita sai na tsine maka!!’ Basu ji lokacin da akai sliding k’ofar aka shigowa ba sai dai kawai suka ga an juyo da Mammy an wanke ta da mari! Diff!! haka parlourn yayi tsit! Cikin b’acin rai Maman Mammyn tace “Yi maza kaje ga Aaima chan driver ya bata kayan da zaka saka ta kawo. Jeka ka shirya yanzun nan za muzo mu rakaka.” Har ya d’anyi gaba sai kuma ya juyo yace “Tace fa In na fita sai ta tsi..” Cikin katseshi Maman Mammyn tace “Nace ka fita ko! Ta tsine makan in gani.” A hankali yad’an kalli Mammyn yaga ta d’auke kai daga kallonshi, cikin nutsuwa yayi sliding door d’in ya bud’e ya fice, yana mai share ragowar kwallar dake kwance akan fuskarshi. Yana fita ta fashe da kuka, cikin kukan tace “Da wanne kuke so inji ne wai? Ya kuke son inyi? Wallahi ko sunan Yarinyar bana so a kira! Ji nake yi kamar zan mutu, ku duba fa kuga yanda yake kuka shab’e shab’e dan kawai nace ba zai aureta ba! Idan ya aureta kuma ya kuke tunani??” Hugging d’inta Mahaifiyar tata tayi tana d’an bubbuga bayanta… Sai da ta tabbatar tayi shiru tukun cikin sigar lallashi tace “Kiyi hak’uri Rukayya, ke fa da kanki kikace Mijinki yana share ki! Ki duba fa ko wajen ki baya zuwa kuma da kika dawo bai nemeki ba, ko ya yi miki magana bayaga yanzun?” Cikin sheshshekar kuka Mammy ta hau girgiza kai alamun ‘a’a’. Ajiyar zuciya Maman nata ta sauk’e kafin tace “Kinga ko! Wannan ma kad’ai abu ne wanda ya kamata a tsaya a duba da kyau. Yanda kikace Matar nan tasa ta warke, da kuma dalilin da ya sanya yake ta faman jin haushin ki wanda bamu san daliliba yanzu shine abun a tsaya a duba a gyara bawai wannan k’aramin alhakin ba.” Da sauri Mammy tace “Wallahi Hajiya Hudan ba k’aramin alhaki bace ba! Ki dubafa ki ga tun daga ranar data shigo estate d’innan nake cikin tashin hankali..” Cikin d’an b’acin rai Maman nata tace “To yanzu ya za ki yi? Kinga fa wannan abun da muka san za kiyi wallahi shiyasa muka k’i mu fad’a miki maganar auren tun kina cell! Ki tsaya ki danne zuciyarki yanda kika saba, ki fara gano matsalar da ta shiga tsakaninki da Mijinki a samu a gyara a shawo kanshi in yaso daga baya sai kiyi yadda kikeso Amman yanzu idan kikayi yunk’urin hana auren nan, wallahi kowa bak’in ki zai gani, kuma hatta Arshaad d’in dakike ta haukar ‘kar Hudan ta janye miki shi’ Ke ce da kanki gashi kike k’ok’arin kawo matsala a tsakaninku da kanki gashi kina turashi away from you dan Wallahi kinji na rantse miki yadda Arshaad ya kwallafa rai akan Yarinyar nan muddin kika sake kika zama silar da ya rasata to kuwa ba zai tab’a yafe miki ba! Kuma sai kin yi dana sani. Ki bari ayi auren sai mu san abunyi. Yanzu kar ki fito b’aro b’aro a matsayin wadda ta hanashi aurent....” Cikin katseta Mammy tace “Ki kwantar da hankalinki ni na san ta inda zan b’ullo mishi yana jin maganata ai yana yi min biyayya. Matsalar da za a samu shine In har na bari ya aureta! D’azu fa muka gama waya da Adama wai ashe ma k’asar za su bari gaba d’aya! Haba dan Allah taya ba zan yi kuka ba? D’ana kwalli d’aya a duniya zata d’auke shi su tafi sai ta gama mallakeshi tukun a dawo min da fanko? Dama yanzun ma ya aka k’are?? Ballantana kuma yaje yayi spending years da ita! Ni kawai ku kyaleni dan girman Allah, dan na tabbatar ranar da Arshaad ya aureta to ni kuma zan iya barin duniyar nan a ranar.” Ta k’arashe tana sake fashewa da wani sabon kuka. Cikin fad’a Maman nata tace “Baki rabu da su Adaman nan ba har yanzu ko? Na ce miki ki tsaya ku fara shiryawa da Mijinki ki fara gano matsalar da ta shig..........” Da sauri Mammy tace “Matsalata da Dad, Aisha ce! Na rigada na sani. Ki bari kawai in fara kashe wannan boss d’in after that idan na tashi bi ta kan Aisha wallahi duk wanda ya ce zai shiga tsakani sai na had’a da shi”. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 52 Cikin fad’a Maman nata tace “Baki rabu da su Adaman nan ba har yanzu ko? Na ce miki ki tsaya ku fara shiryawa da Mijinki ki fara gano matsalar da ta shig..........” Da sauri Mammy tace “Matsalata da Dad, Aisha ce! Na rigada na sani. Ki bari kawai in fara kashe wannan boss d’in after that idan na tashi bi ta kan Aisha wallahi duk wanda ya ce zai shiga tsakani sai na had’a da shi”. Tana gama fad’in haka ta juya ta fice da sauri tana share hawayenta. Ko bi ta kan y’an parlourn bata yi ba, ta wuce sama abunta tana huci. Tana fita Maman nata ta sauk’e ajiyar zuciya! A hankali ta kalli Hajiya Binta tace “Allah ya rufa asiri..tunda tak’i jin maganata ni uwarta! Ni zan tafi yanzu, idan ta yarda aje wajen event d’in su Amaryar to ku rakashi Idan kuma ta hana sai ku zuba mata ido. Sannan ki samu y’an uwanki ki jasu gefe kice nace ‘ko me zata yi kar wanda yayi yunk’urin hanata’ Ita ta sani. Taje tayi yadda taga ya dace.” Tana gama fad’in haka itama tayi hanyar waje cikin y’ar tafiyar su ta tsoffi... Sallama ta yiwa matan dake babban parlourn daga nan ta wuce abunta. Har k’ofar mota ragowar sister’s d’in Mammy guda biyu k’annenta suka rakata, suka bud’e mata gidan baya ta shiga suka rufe driver yaja suka tafi. Su duk basu san wainar da ake toyawa ba Hajiya Binta wadda ta kasa fitowa parlourn tun tafiyar Mahaifiyar tasu ce kawai ta sani dan haka suna komawa aka shiga bidiri ana ciye ciye ana ta hotuna! Fitowar Ango da Aaima ne ya k’arawa abun armashi, ba a dad’e ba Mom da Ummi wadda ta d’an ji sauk’i suka shigo, nan suka had’u aka yi ta hotuna…. After kamar 30 minutes haka, aka fara shirye shiryen tafiya gidan su Amarya, anata had’a gifts.. Dai dai nan Mammy ta sauk’o. Sai da gaban Arshaad ya yanke ya fad’i amman ya dake ya k’arasa inda take ya fara k’ok’arin jan hannunta yana cewa “ta zo su yi hoto” Ko alamar zata motsa bata yi ba dan haka ya tsaya ya d’an kalleta yace “Mammy dan Allah mana, mutane suna kallo fa, ki zo muje” Ya fad’a yana sake k’ok’arin janta. Suna a haka sisters d’inta da Aaima suka iso wajen. Fisgewa tayi da mugun k’arfi, kafin tace masa “Idan baka je ka cire wannan wata kalar shigar ba wallahi Arshaad sai na ci ubanka!! Sannan ni za ka mayar y’ar iska mai magana biyu? Mu gama magana da kai amma ka je ka wani shirya tsaf sannan dan tsabar raini kazo kana ce min wani muje muyi hoto? Da kai da hoton kun ci kutumar ubanku!” Runtse idanunsa yayi da mugun k’arfi! Dai dai nan Mommy da Aslam waenda suka shigo yanzun suka nufo su, suka k’araso! Kusan duk sun ji furucinta. Da mamaki suke kallonta, a hankali Aslam yad’an dafa kafad’ar Arshaad d’in, dukda bai gama sanin wainar da ake toyawa ba amman yad’an fahimci wani abun, hakan ya sanya shi jin mugun tausayinsa ya rufeshi.... Da mamaki Mommy take kallon Mammy kafin tace “Lafiya kuwa? Me naji kamar kin ce?” “Amin, wa alaiki Assalam Aisha!” Mammy ta fad’a cikin tsareta da ido tana jin wani mugun tsanarta na taso mata… Murmushi Mommy tayi kafin tace “Assalam alaikom, me yake faruwa ne Arshaad?” Ta yi maganar tana me mayar da akalar tambayar tata kan Arshaad saboda tsananin mamakin Mammy da ya rufeta.. Tunda suke tare ko da wasa Mammy bata tab’a yi mata kwatankwacin irin haka ba. Arshaad Yana shirin yin magana Mom ta k’araso tace “Ya dai? Kukayi cirko cirko duk anan?” Kafin ta kalli Mommy tace “Ina ta yi miki magana Mommy, kika k’i kulani kika wuce. Ina wuni.” Dai dai nan Ummi itama ta k’araso wajen nasu. Cikin kulawa Mommy tace “Yi hak’uri Adama, hankalina ya yo kansu ne dan naga kamar ba k’alau ba.” Da sauri Mammy tace “K’alau d’in....” Cikin katseta da d’an k’arfi Mom tace “Haba k’alau ne mana, komai normal Ina?” Ta fad’i hakan tana kallon Mammy da d’an sign d’in tayi calming down mana… Tsaf Mammy ta fahimceta.. Itafa ta rasa gane dalilin da yasa su Adama da y’an uwanta suke tunanin zata iya yin wata kissa a wannan stage d’in! Taya ma zata iya danne wannan duka dubu d’in da akai mata? Ya an dake ta kuma suna so su hana ta kuka??… Mom na shirin yin magana taji Ummi tace “Arshaad akwai matsala ne? Yi magana mana, kar lokaci ya k’ure! Kaga yanzu tafiya za mu yi.” Da sauri Mommy tace “Dankuwa har na cewa Maryam d’in ma mun kusan fitowa, na san mu suke jira yanzu haka.” Ajiyar zuciya Mom ta sauk’e tana ji kamar ta shak’e Mommy ! ‘Wato irin ita har ta jone da Maryam d’innan’. Mammy na shirin yin magana Arshaad wanda ya ga b’oye b’oye shi ba inda zai kaisa dan kwata kwata ya kasa shawo kan Mammy kuma yana ganin in dai ya gayawa Mommy maybe a samu sauk’i ta hanyar Dad da Gramma ne, yace “Mommy cewa tayi ko a fasa auren ko ta tsine min” Da sauri Mommy tace “Whatt!!” Cikin firgici kafin ta juya kan Mammy tace “Rukayya wanne aure kike so a fasa?” Ba tare da b’ata lokaci ba cikin b’acin rai da tarar numfashin ta tace “Auren Huda da Arshaad, Aisha! Shi nake so a fasa Idan kuma kina da ja to sai in ji...” Sai a sannan Aslam ya d’ago ya kalleta, bata san mai ya faru ba amman sai Yaron yayi mata kwarjini ta kasa ci gaba da magana. Mommy ta yunk’uro za tayi magana kenan taji Aslam d’in ya rik’e hannunta, ba tare da yace mata uffan ba kawai ya juya da ita suka fara tafiya. Har suka fice a parlourn bai ce uffan ba ita kuma bata yi mishi tirjiya ba, sai da suka isa tsakiyar compound d’in tukunna ya zaro waya ya danna kiran Dad! Ba tare da b’ata lokaci na ya gaya mishi halin da ake ciki… Suna gama wayar, ya ga tana k’ok’arin komawa A hankali yace “Mommy please kar ki koma ciki, kina jin fa yanda take yi miki magana ba respect. Please dan Allah kar ki je.” Za tayi magana yace “Please Mommy, i can’t take it” Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin a hankali tace “To kaini gidansu Huda. I have to be there, suna ta expecting d’inmu.” Da k’arfi yaji zuciyarshi ta buga ! Sai kuma yaji zafi kamar an soka mishi wuk’a… Sai da ta sake maimaita maganar tata tukun yace “Tam” Daga nan suka fara tafiya suka wuce inda motarsa take a chan wajen gidan, suka shiga suka wuce. A chan parlourn kuwa Zuwa wannan lokacin gaba d’aya hankalin matan parlourn ya koma kan su Mammy. Su Mommy suna fita Ummi ta hau lallab’a Mammy tana bata baki, basu kulata ba sam daga ita har Mom dan tun a cell daman sun fita harkarta saboda ta zama wata salaha doluwa wawiya! kamar ba ita ba. Arshaad kuwa ji yake kamar ya chaka wa kanshi wuk’a! Babu abunda yafi d’aga mishi hankali kamar kalmar ‘sai ta tsine mishi’ da taketa faman ambata, hakan yasa kawai ya juya zai bar wajen suka yi karo da Dad! Fuskarshi sam babu alamun annuri dan hatta Arshaad d’in sai da ya d’an tsorata da yanayin shi. Ganin yana shirin fara zuba musu tujara a gaban jama’a ne ya sanya Mom tace “Dad da mun d’an shiga daga ciki ko mu hau sama Kalla kowa ya zubo ido mu yake kallo” Juyowa yayi yana kallonta wanda hakan yasanya ta sha jinin jikinta. Da kakkausar murya yace “Granpa ya san kina nan?” A hankali jikin a mace ta girgiza kai, Snapping fingers d’inshi yayi kafin ya nuna mata hanyar main door straight! Ba k’aramin sanyi jikin Mom yayi ba! Kunya da takaici kuwa kamar su kashe ta, a hankali tace “Sai anjiman ku” daga nan ta fara k’ok’arin wucewa taji Ummi tace “Adama d’an jirani in je in d’auko wayata a side d’in Granpa In zo mu wuce. Ya sallameni tun jiya.” Ba tare da Dad ya kalleta ba yace “Ki jirani zan maidake anjima, ina son ganinku tare, ke da Abba.” “Ok” kawai tace Mom kuma ta wuce ta fita. Sai a sannan Dad ya kalli Mammy yace “Magana d’aya zuwa biyu nake son gaya miki… Na farko shawarace Na biyu kuma zan iya kiranshi as treat.. Ki kwantar da hankalinki ayi auren Hudan da Arshaad cikin lafiya da kwanciyar hankali Ko kuma wallahi idan kika yi wani abun da ya b’ata auren nan tou ki tabbatar sai na sauk’e igiyoyin aure na da suka yi saura a kanki.” Yana gama fad’in haka ya juya ya wuce. A rikice Aaima da sisters d’in Mammy suka hau cewa “Kawai ta hak’ura dan Allah kar ta b’ata aurenta” Bata bi ta kansu ba, cikin b’acin rai ta kalli Arshaad tace “Arshaad kaje ka cire waennan kayan na gaya maka babu inda zaka je! Wallahi idan ka fita a gidannan yau ni da kai ne.” Daga haka ta juya ta wuce sama. Sai a sannan Hajiya Binta ta k’araso tanajin abinda tayi tace “Suje kawai a sallami y’an wuni suma su zo su wuce gida tunda ba za a je kaulun ba!” Nan take gayamusu ma sak’on Mahaifiyarsu da tace a fad’a musu… Jiki a mace haka duk suka bar gurin aka je aka rarraba souvenirs d’in k’atuwar jaka an rubutu sunan Amarya da Ango a jiki a cikin jakar an zuzzuba turaruka da atamfofi guda biyu da vail da jaka da takalmi, a each bag.......... Mom, bata tab’a tunanin Dad zai iya yi mata hakaba! Wai me ya shigi mazan estate d’in nasu ne da duk suka bi suka rainasu suka tsanesu haka? Daddy ne kawai yake musu mutunci yake tausayinsu amma hatta Auwal da Arshaad sun renasu Aslam kanshi tana gani d’azu yanda yayi musu sannan ya wani ja hannun uwarshi suka fita Ala dole shi mai zuciya! Inaa, gaskiya rayuwa fa ba zata yiu a haka ba, dole su gyarawa mazan MT zama dan yanzun taga wani tashen rashin mutunci suke yi especially Abba, ta kanshi zata fara wallahi! Wannan shine damuwar da ya kamata su tsaya su magance ba wai shirmen Mammy na hana auren Arshaad ba! Abunda sai sun so ma tukun Hudan zata zauna a gidan Arshaad d’in! Bata san me yake damun Mammy data kasa fahimtar simple abu ba....... Ji tayi kawai an yi hugging d’inta A d’an razane ta zare wadda tayi hugging d’in nata tana shirin cewa wani abun suka yi ido biyu da Jalila.. B’ata rai tayi tamau ta tamke fuskarta. Jalila ta lura da hakan sarai amman ta manna mata hauka cike da shak’iyanci tace “Oyoyo Mom d’inmu ashe kin dawo ni banma sani ba. Dama wallahi zaman gidan su Gwaggo Asaben chan ya dameni, girkin kuku fa nake ci baki ga har na rame ba? Yanzu kuwa tunda Allah ya dawo dake na san k’ibata zata dawo. Taho muje, ko kayana ba zan d’auka ba wallahi Auwal yaa zo ya d’auka anijima, k’afata k’afar ki, mu tafi. Ashe alkhairin ganin ki ne yasa naji ina kwad’ayin lek’owa nan dan tunda naji Gwaggwo Asabe tace ana biki anan na kasa sukuni.” Lumshe ido kawai Mom tayi, sai da ta tabbatar da zuciyar ta ta dedeta tukunna ta bud’e idanuwanta da sukai ja ta zubasu akan Jalila wadda tayi mata k’urr! da ido. “Muje” Shine kawai abunda Mom d’in tace, ba tare data sake bi ta kanta ba tayi gaba Jalilan ta bita a baaya daman neman wanda zata k’untatawa take yi ta san watak’il ta samu tashin hankalin da take ciki ya d’an ragu! Duk da Umma ta bata assurance d’in ‘ba matsala an tabbatar mata da babu aure tsakanin Huda da Arshaad dan haka kar ta damu da wani bikin da suke ta yi’ Amman ta kasa nutsuwa kuma zuciyarta ta k’i ta daina tafarfasa…… Sannan zata fita daga estate d’in nan, da Auwal ya maida mata shi kamar kurkuku. Murmushi tayi aranta tace “Zan jefi tsintsu biyu da dutse d’aya!” Driver ne ya jasu su duk biyun a baya, kamar yadda tayi zato kuwa masu gadin da kyar suka bari aka fita da ita.... Sai da Mom ta nuna mata d’akin da zata zauna a sama, daganan ta wuce nata d’akin. Sai da Ummi ta tabbatar kowa ya watse tukun tabi bayan Mammy Sisters d’inta( Mammyn) kuwa ko sallama basu yi mata ba suka wuce suka rabu da ita. A d’aki ta sameta sai faman safa da marwa take yi ta hana zuciyarta sukuni sam!. Ta ganta sarai taga shigowarta amman sai tayi banza da ita taci gaba da kai kawon da yake yi. A hankali Ummi ta nemi waje ta zauna tukunna tace Mammy Da sauri Mammy tace “Zainab tashi ki fita! In dai shawararki kika san zaki sake bani to tashi ki fita tun kafin raina ya b’aci!”. Murmushi Ummin tayi sannan ta fara magana “Dama ai in dai kinga mutun yana farin ciki idan ana bashi shawara in yayi ba daidai ba to ki tabbata ba gaskiya ake fad’a mishi ba! Nazo in baki shawara ne Mammy kuma zan yi matuk’ar farin ciki idan naga kina jin haushin shawarar tawa dan na san gaskiya ce nake fad’a. Bari kiji in fad’a miki abunda na San Baki sani ba.. idanuwanki ne suka kulle ba kya ganin komai ba kya ganin kowa sai k’iyayyar Huda da Aisha wadda kika gani abkan k’afafuwanta!” Da sauri Mammyn ta kalleta kafin tace “Magana zaki fad’amin? Me kike nufi? Use your words! Ta fad’i hakan tana me k’arasowa daff da ita. Mik’ewa Ummin itama tayi sannan tace “Ba zan yi using words d’ina ba Mammy dan na san kin san me nake nufi! So yanzu ba lokacin tashin tashina bane ba, yanzun lokaci ne wanda ya kamata ace kin farka idanuwanki sun bud’e sannan kin kalli rayuwa da idon gaskiya da basira. Bari in baki wani d’an misali , watak’il ki gane abunda kowa yake son fahimtar da ke wanda kika kasa nutsuwa ki fahimta.. For instance ace, ki samu kare ki kulle shi yayi kwanaki baki bashi abinci ba! Rana d’aya ki samu dogon lungu, a k’arshen lungun ki ajiiye nama da k’asusuwa da ruwan sha sannan ki kawo zarto k’usoshi da wuk’a ki ajjiye a daidai ta saman lungun a saman wannan naman sannan ki d’ana mishi tarkon da in dai yabi ta kai ya taka to wannan wuk’a da zarton zasu sauk’o su chakeshi su kasheshi murus har lahira ba tare da ya ci wannan naman ba.” Ajiyar zuciya Ummi ta sauk’e kafin tace “Ki gaya min in akwai mahaluk’in da ya isa ya hana wannan karen cin naman nan? Ko kuwa shin wannan karen zai iya hankalta da wannan tarkon da yake a gaban naman? Amsar anan itace ‘a’a’, sai dai In d’auke shi za ayi ta k’arfin tsiya a sama mishi sabon nama a bashi yaci. Sannan ne za a samu sauk’i. Wannan karen ba kowa bace face, ke. Naman nan kuwa, Hudan ce da Aisha waenda k’iyayyarsu haushi da takaicinsu ya sanya kika kasa ganin komai da kowa hatta tarkon dake gabansu wanda in dai kika taka to tabbas wuka zata fad’o kanki ta kashe ki har lahira ba tare da kin tab’a su ba! Waennan tarkon da wuka’ak’e ba komai bane Mammy face Dad da Arshaad da auren ki da mutuncinki da k’imarki, da kike k’ok’arin lalatawa ki kashe rayuwarki jin dad’in ki kwanciyar hankalinki da farincikinki da aurenki, duk akan rashin hak’uri. Second option kuma da na baki na ‘sai dai a d’auke karen a bashi sabon nama’ Shine wanda ni, y’an uwanki da Aaima muke ta k’ok’arin fahimtar da ke!. Idan kika yi hak’uri kika sawa kanki da zuciyarki salama, zaki samu peace of mind za ki samu farin ciki amman fa sai kin yi tunani irin na mutane bawai irin na karnuka da basa ji basa gani idan suna jin yunwa ba. Ki daure ki kwantar da hankalinki, wata rana sai labari. Kar kije maybe akwai babban rabo a tsakanin Hudan da Arshaad ki kashe kanki ba tare da kin hankalta ba...” “Attakhbir! Allahu akhbar! Mai k’aramar kwakwalwa da zuciya. Naji na gode reformed Zainab! Na lura tunda kika ji azabar cell shikenan zuciyar ta mutu. To bari kiji in gaya miki Wallahi! Kin ji dai na rantse gara rabon dake tsakaninsu ya kashe ni! Akan in zauna a gaban idona a d’aura musu aure inaji ina gani dan na tabbatar bak’in ciki ne zai k’arasa ni muddin Arshaad ya auri wannan Yarinyar!. Kinji dai kankat! Kenan, ko?. Oya jeki na gode duk ranar da fargabar cell ta bar jikinki, kya iya zuwa mu yi magana.” Cewar Mammy. Bak’in ciki ne ya hana Ummi sake ce mata komai, dan haka kawai ta juya ta fita cike da takaici da tsananin mamakin Mammy. Da harara Mammyn ta rakata, sannan tayi tsaki ta koma kan gadonta ta zauna. Ummi na fita suka had’u da Daddy da alama d’akin shi zai yi amman yana ganinta yace “ta zo suje ya kaita kawai ya gama tukun ya huta.” Ba ta san taya zata fuskanci Abba ba, bata san taya zata fara bashi hak’uri ba! Hakan yasa tunda taje ta yiwa su Granpa sallama suka d’au hanya zuciyarta take ta faman tsitstsinkewa..... Ba kowa a parlourn dan su Shuraim tun safe suka tafi gandun albasa. Basu dad’e da gama waya da Dad ba yace mishi yana gida don haka suna zama ya kirashi yace “ya sauk’o gashi ya kawo Ummi” Wallahi Abba har ga Allah har cikin zuciyarshi shi mantawa ma yake yi da wata Ummi. Mike’wa yayi kawai ya je jikin drawer inda yake ajjiye important documents d’inshi ya d’auko takardar da ya dad’e ajjiye da ita, ya fice yayi k’asa. Da kyar ya iya daurewa suka yi cikakkiyar gaisuwa shi da Dad. Ummi na shirin gaidashi da fara sake bashi hak’uri har da d’am zamowarta daga kan kujera taji yace “Ke! Zo ki karb’a nan” Ganin ya mik’a mata farar takarda ya sanya gabanta ya hau dukan uku uku! Ba ita ba hatta Dad sai da ya shiga rud’ani. Bata gama gigicewa ba sai da ya daka mata wata uwar tsawa! A take jikinta ya d’au rawa. Gudun kar ta b’ata mishi rai ya sa ta mik’e da kyar ta k’arasa inda yake tasa hannu biyu ta karb’a…. Dad ne yace “Abba meye wannan ka bata?” Yana mai tsareshi da idanu. Cikin nuna halin ko in kula yace “Ta karanta za ta gani” Da kyar Ummi ta iya bud’e takardar, jikinta na karkarwa tana adduar Allah yasa ba abunda take tunani bane… Zuwa yanzu ran Dad ya soma b’aci da attitude d’in Abba dan haka cikin b’acin rai ya yunk’uro da niyyyar fara zazzzage mishi ta cikinshi dan yaga alamun da renin wayo ya sauk’o k’asan shi kuwa yadda Mammy ta gama chaza mishi kai wallahi ba Abba ba ko waye ya shigo gonarshi yau sai ya ci ubansa! Ya bud’e baki kenan, yaji k’arar fad’uwa! Da sauri ya maida hankalinshi a direction d’in Ummi, ya ganta zube a k’asa. Dan haka ya mik’e a mugun firgice ransa na k’arasa dagulewa. Abba kuwa ko gezau bai yi ba Yana nan zaune a yanda yake ko motsi ma ba shi da niyyar yi. A gigice Dad ya mik’e cikin sassarfa ya k’arasa inda suke yana cewa “Subahanallah, Abba suma tayi ko me? Duba ta mana, tashi mana, ya kamar baka ga abunda ya faru ba ne?” Ya fad’i hakan yana mai durk’usawa a inda Ummin take. Cikin nuna halin ko In kula ya mik’e tsaye ya karkad’e farar jallabiyar dake jikinshi, kafin yace “At least na sakata tayi mai dalili ai yanzu ba fake ba.” Yana gama fad’in haka ya juya zai hau sama.. Da sauri Dad ya mik’e ya sa hannu ya juyo da shi, bai yi wata wata ba ya d’auke shi da wani mahaukacin mari dan tun lokacin daya durk’usa akan Ummi idanuwanshi suka sauk’a kan takardar saki biyun da Abba yayi mata. Da sauri Auwal wanda ya shigo yanzun ya k’araso inda suke yana cewa “Subahanallah, mai ya faru? Dad wace..?” Maganarsa ce ta katse sakamakon Idanunshi da suka kai kan fuskar Ummi, da sauri ya durk’usa ya hau tattab’ata yana tambayar mai ya same ta?. Cikin b’acin rai Dad yace “Maida ita yanzunnan ko ka fuskanci fushina Yakubu!” Da mamaki Abba yake kallonshi jin yana yin yanda Dad d’in yayi mishi magana da kuma yanda ya kira sunanshi haka! Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace “I can’t Dad, I’m really sorry Wallahi baz..” Wani marin ya kuma sakar mishi kafin yace “Kar ma ka rantse! Dan ko ka rantse sai kayi azumi saboda Ummi sai ta koma d’akinta a yau wallahi! Kaji dai na rantse.” Bai ankara ba yaji hawaye yana zuba ta idanunshi.. Cikin kuka yace “Dad bana son ganin fuskar matar nan, tayi ruining komai nawa saboda selfish reason d’inta! Ba zan b’oye maka ba wallahi Ina having second thoughts akan auren Hudan da Arshaad saboda kwata kwata bana son yin nesa da y’ata because i just knew her, all because of ummi. Ka san irin azabar da Hudan ta sha a hannun Usman kuwa? All because of Ummi. Ka san yadda nake jin Maryam a cikin zuciyata? Amma ba yadda na iya dole haka inaji Ina gani ta auri wani ta rayu da shi for almost 20 years!! All because of ummi Komai fa Yaya ita ce sila! Itace silar ciwon zuciyana! Itace silar bak’in cikina! Itace silar lalacewar soyayya ta! Haba haba dan Allah.. sannan yanzu kace In maida ita? Gaskiya kayi hak’uri Yaya, ban tab’a maka gardama ba amman kam yau zan yi maka!. Wallahi ko sunanta ba na son ji kwata kwata..” Ya k’arashe maganar cikin d’acin zuciya sannan yana gama fad’in hakan ya wuce sama ya barsu shi da Auwal wanda yake ta yayyafa wa Ummin ruwa yana son yaga ta farka. Da kyar Dad ya iya juyowa ya kalli Auwal d’in, sannan yace “Kamata mu kaita asibiti, Allah yasa ba wani babban abun bane ya sameta......” Gandun albasa (2:30 pm) A tsakar gidan Madu, akayi decoration na traditional kaulu! Wajen yayi masifar yin kyau. Taken wak’e wak’en Shuwa Arab ne ke tashi in a very low tone. Su Sudais da wasu Yaran sai y’an tsofaffi tsilla tsilla ne a zazzaune a kan kujerun da aka k’awata tsakar gidan da su. Gaba d’aya y’an mata da manyan matan suna ciki, wasu suna had’a takeaway da souvenirs wasu kuma suna shiryawa dayake mostly family ne sai na jiki sosai suka zo dan Mama ba wani taro tayi ba Ita dama ba wani sanin jama a ma tayi sosai ba, sai y’an unguwa da suke ta zirya tun safe waenda rabinsu duk munafurci ne yake kawosu dan an san yau za a kawo lefe. Umma bata da lafiya tana fama da hawan jini amman tun sassafe suka zo ita da Baaba Laraba da yayarta Hansai, kuma wani abun mamaki tunda tazo d’in tak’i kula Mama dan wani mugun zafinta take ji, sun dai gaisa da Shuwa da Ummu Ita kuma Mama sun gaisa da Hansai da Baabaa Laraba amman Umma kam tama k’i bari su had’u dan tana hango ta zata kauce hanya ko ta fad’a d’aki ta shige band’aki. Da Mama ta fahimci hakan kawai sai ta tattarata ta watsar ta shiga sabgar gabanta dan ita mamaki ma Sadiyar take bata duk tabi da d’aurawa kanta wahala gaba d’aya a takure ma kamar ta ganta ga kuma rashin lafiyar Bp da take ta fama. Sai da Anty Zainab ta zo tukunna ta d’an samu ta ware. Itama Anty Zainab d’in da kyar ta iya daurewa suka gaisa da Maman wadda tayi wani irin fresh! Sannan idan ka kalleta ba zaka tab’a cewa sa’ar su bace ita da Sadiyar Sai dai kace Antys d’inta ne dan ba za ma ka ajjiyesu a matsayin yayunta ba! Musammam ma Sadiya wadda ta zama kamar wata mahaukaciya kwana biyun nan! Tun lokacin da taji labarin maganar auren Huda har yau bata san inda nutsuwarta take ba……… Mama na gama gaisawa da Anty Zainab ta juya ta wuce abunta. Anty Zainab kuma ta nufi wajen Umma! Nan kuwa suka hau hassada da zagin Mama har da suna cewa wai “bazawari take nema shiyasa taci wannan uwar kwalliyar”. Laffaya Maman ta nad’a itada Ummu, kalar laffayar ja sai blue d’in flowers, sun yi kyau sosai dan har d’an light makeup sai da Sakina ta tirsasa su suka tsaya aka yi musu. Itama Sakina laffayar ce a jikinta, amma bata nad’a ta har ka ba, instead sai tayi d’aurin Zahra Buhari da mandil a kan nata shi kuma mayafin layyafar ta nad’a a kafad’ar ta. Amarya kuwa ta sha traditional kaya abunta! Hatta hair style d’inta ma irin nasu aka yi mata, daga sama ta nad’a wata had’add’iyar blue black d’in laffaya, aka yafa mata mandil akai. Tun daga kan sark’ok’in k’afarta har na wuya da y’an kunneta da wanda ta sa a kanta na sisin gold duk na asalin gold ne! Wanda Madu ya bata kyauta jiya da daddare, yace “tun na mahaifiyar mahaifinsa ne! Maryam yaso bawa Allah bai yi ba. Ashe rabon ta ne..” D’akin isu isu ne ita da k’awaye ta, anata d’aukar hotuna amman kallo d’aya za kayi mata ka san hankalinta baya ma gidan gaba d’aya! Tun da gari ya waye take jin fad’uwar gaba, gashi yanzu kuma sai kiran Arshaad take yi baya d’auka….. Shuwa ce ta shigo ita da Baabaa Talatu sanye cikin wata rantsatsiyar milk laffaya sun yi anko su biyu suma abun su ita da Baabaa Talatun. Basu dad’e ba wasu mata suka shigo su biyu, daga nan suka umarci Hudan da ‘ta mike a fita da ita’ Aranta ji take kamar ta tambayesu ‘Ya arshaad ne ya zo? Sai kuma taga rashin kunya da zak’ewarta Kuma ta tuna jiya Sakina tace mata ‘Ta bar nuna mishi ta damu sosai fa, idan ba haka ba tabar ganin wai yana sonta Wallahi wahala zata sha....’. Lumshe idanuwanta tayi ta dedeta nusuwarta sannan ta bawa Sakina wayarta ta mik’e, ta jaa mandil d’inta ta rufe kaf fuskarta, su kuma suka tik’eta sukayi waje. Suma su Sakina suka take musu baya. Hudan, so take ta yakice tunanin Arshaad a kanta amman ta kasa! K’arshema bigewa tayi da adduar Allah yasa tana fita ta ganshi amman yanayin yanda taji an zaunar da ita a doguwar kujerar da aka k’awata domin ita da shi ne yasanya ta fahimci bai zo d’inba. Ummu ce ta fito ta bud’e taro da addua sannan ta fara gabatar da al’ada a Huda, A matsayin uwa. Mama suna parlourn Madu, tun lokacin da Mommy da Aslam suka zo suka buk’aci ganinta har yanzu bata samu damar fitowa ba. Wata distant relative d’in Shuwa wadda zata d’an girmi Shuwan kad’an ce ta k’arasa wajen sannan cewa Ummu “Ina uwar Angon? Ta zo ta zauna a kusa da ke yadda kina gamawa zata karb’a. Sannan ba ayi welcomin Ango ba kuma ba aga shigowarsu ba besides ai dole sai yananan ma tukunna za ayi komai. Na ga bai riga yazo ba amman kin yi wuff kin fara abu haka bayan kuma akwai abubuwa da yawa before wannan.” Karaf! A kunnen umma. Daman neman abun yi suke yi ita da Anty Zainab shiyasa suka zo suka zauna a k’asa gefen kujerar Amarya. Da sauri sannan da d’an k’arfi yadda ta tabbatar kowa zai ji Umman tace “Eh kam tabbas!” Sannan ta mik’e tsaye kafin tace “Uwar Ango! Tana Ina? Ana buk’atar Uwar Ango a nan yanzu yanzu” Da k’arfi ta yadda kowa ya iya jiyota tunda daman wak’ar da aka kunna a low tune yake kuma iya murya ne kawai babu kid’a. Da sauri Ummu tace “Umma meye haka? Idan kin yi min magana ba zan je In kirata baneba? Ko hakan da kika yi kina tunanin shi zai sa ta fito?” Still da k’arfi Umma ta sake cewa “A’a, ai ji nayi kamar kince bata zo ba! Gashi shima Angon shiru. Duk da dai ni ba Shuwa bace ba amman Tabbas na asan cewa Ango da Amarya a tare ake shafa musu lalle, manshanu, da ragowan abubuwa! Dan har yau ina tuno naki, a tare aka shafa muku ke da Muhammadu wanda ya zo wurwuri bai tsaya b’ata lokaciba, Ita kuwa yayarki daman ba a yi mata ba shiyasa gaba d’aya auren nata duk biyun suka tab’arb’are! To kuwa kinga ai ba zan so auren Huda itama ya samu matsala ba ko? Dan haka gara mu jira Angon ya zo ko nan da k’arfe taran dare ne mu masu iya jiransu ne har sai shi da uwarshi sun zo an yi alada yadda ya kamata!”. Ta k’arashe maganar har wani karkarwa jikinta yake yi, wanda kana gani ka san bala’ine kawai yake cinta. Ummu bata ga k’arasowar Sakina ba sai tayi tana cewa “Eh tabbas kam Hajiya Umma kya zauna ai kiyi ta jira tunda daman kallon kwaf da munafurci ne ya kawo ki! Mu nan dukkannin mu munada aikin yi kuma ba mu da lokacin zaman jira har k’arfe taran dare! In dai Ango kike son gani to ki bada nan da awa biyu zaki ganshi sun iso tare shi da iyayenshi maza da za su kawo lefe wanda na tabbatar abunda ya tsaidasu kenan ba wai abunda makirar zuciyarki ta shirya miki ba!” Umma na shirin k’arasowa inda Sakinar take taga Ummu ta d’auke ta da mari! Cikin yaren Shuwa Ummu ta hau yiwa Sakinar fad’a k’asa k’asa yanda ta tabbar ba kowa ne zai ji su, tace “Baki da hankali ashe? A cikin dangi da y’an uwa za ki bud’e baki kina yiwa babbar mata rashin kunya haka? So kike a tafi dake a baki? Wuce! Wuce ki tafi chaan sama d’akin Shuwa ki rufe! Idan ba ni na neme ki ba wallahi kika fito sai ranki yayi mugun b’aci!”. Juyawa kawai Sakina tayi ta wuce tana ji kamar ta had’iye zuciyarta! A kan Umma aka mareta a gaban mutane haka!? Kuma ta tabbatar tunda Umma ta fara wannan maganganun to fa idan taka mata burki aka yi ba ko kuma Arshaad d’in ta gani ba tabbas ba zata tab’a barin mutane su sha ruwa ba. Ita daman tun d’azu da ta ganta tazo da sassafe ta san ba alkhairi ne ya kawota ba. Ita da take da abun fad’a a gindi amma shine har take da audacity d’in yin magana! Wallahi yau da Ummu ta barta da sai ta yiwa Umma zazzagar kwanyo.... Da wannan tunanin ta k’arasa d’akin Shuwa, sai a lokacin hawayen bak’in ciki suka samu nasarar zubo mata… Daga Shuwa sai Baabaa Talatu ne a d’akin suna shirya tukuicin da za a bayar in an kawo lefe. Baaba Talatu tana ganin ta shigo tana kuka ta mik’e tana “Subahanallah, mai ya faru? Ke da waye?” Da sauri ta k’arasa ta hau shafa fuskarta inda hannun Ummu ya fito tarr!! Ya kwanta akan farar fuskarta Cikin fad’a Baaba Talatun tace “Wanne d’an iskan ne ya mare ki??” Fashewa tayi da kuka cikin kukan tace “Umma ce take ta abubuwa a waje, shine Ummu ta mareni wai dan....” Ai bata tsaya jin k’arshen ba, tayi waje. Shuwa ce ta iya daurewa ta tsaya ta ji labarin Sakinar tukunna ta mik’e itama tace mata “ta zauna a d’akin, kar taje ko ina . Bari taje taji ba’asin abunda yasa Angon bai k’araso ba...........” BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 53 Shuwa ce ta iya daurewa ta tsaya ta ji labarin Sakinar, tukunna ta mik’e itama tace mata “ta zauna a d’akin, kar taje ko ina. Bari taje taji ba’asin abunda yasa Angon bai k’araso ba.” “To” Kawai Sakina tace, tana mai sake goge fuskarta sannan ta koma gefe ta fara warware laffayar jikinta da d’aurin d’ankwalin dake kanta.. Sai da ya rage daga ita sai long camisole d’inta wadda ta saka a ciki mai dogon hannu yayinda dogon gashinta ya kwanta a gadon bayanta sannan ta fara k’ok’arin kiran Arshaad... Tayi mishi misscalls sun fi ashirin amman shiru. Dan haka nan da nan hankalinta ya sake tashi…. Tun jiya take danne zuciyarta take k’ok’arin kawar da maganar da Aaima ta gaya mata a cikin kwakwalwarta amman kuma attitude d’in Arshaad da k’in zuwanshi a yanzu ya yi matuk’ar bata tsoro. Ba wadda take jin fargabar taji wannan batu irin Hudan shiyasa jiya ta kwana Sallah akan Allah yasa maganar Aaima ta zama k’arya idan kuma gaskiyace Allah yasa su Abba su gyara lamarin cikin sauk’i… Gaba d’aya hankalinta a tashe yake dauriya ce kawai take yi, tana kuma k’ok’arin taga ba wanda ta bari ya ma ji zancen har a samu a gyara lamarin in sha Allah. Ganin arshaad d’in bashi da niyyar amsa ta ne yasa kawai ta kira Auwal dan taji me ke faruwa a ina aka tsaya.. Shi sai a bakinta ma yake jin wai ‘Arshaad d’in bai je ba’ Saboda shi suna asibiti. Ganin kamar bai san me yake faruwa ba ya sanya taja bakinta tayi shiru saboda ance yawan yayata magana kan iya tabbatar da gasgatuwar ta. Dan haka kawai sai tace mishi “ya duba musu Arshaad din pls” Daga haka suka yi sallama. Daman shima yana da shirinshi zai je wajen So yanzu zai duba Arshaad d’in sai su wuce tare kawai dan haka ya cewa Dad “Bara yaje gida, Sakina ta kirashi wai har yanzu Arshaad be k’arasa ba.” “to” kawai Dad d’in yace masa. Yana fita shima Dad din ya d’au waya ya kira Gwaggo Asabe yace “Dan Allah tazo ta ji da Ummi. Zai yiwa drivern da zai kawota kwatancen asibitin da suke....” Drivern da ya kawota (Gwaggwo Asabe) shi ya maidashi mansion d’in. Yana zuwa ya tarar da Daddy ya shirya chap yana jiranshi da akwatuna dozen biyu sun sha decoration sai kuma basket na gift guda biyar, da akwatunan uwa uba gwaggwo da kawu.. Duk sun had’a. Tun sassafe Mommy ta aiko da kayan shi kuma ya duba ya tabbatar komai dai dai. Sai da aka gama loda kayayyakin a motoci wajen goma tukunna Abba ya fito da shirin shi shima da alama rakasu zai yi! Dad, yana shirin shiga mota har driver ya bud’e mishi k’ofar motar ya hango tahowar Abba! Wani takaici ne ya d’ebesa bai san lokacin da ya daka masa tsawa ba! Yace “Idan ka k’araso nan wallahi sai mun kwashi y’an kallo ni da kai! Kaji dai na rantse wallahi!!” Ya k’arashe maganar yana mishi nuni da yatsar shi manuniya yana nuna sama. Ajiyar zuciya Abban ya sauk’e kafin yace “Dad nimafa rakaku zan y....” Cikin fushi Dad d’in yace “Kaga mota nan, zo ka shiga! Amman direct Asibitin da aka kwantar da Ummi zaka je Idan kuma ba haka ba to ka koma ka zauna a ciki. Zab’i d’aya!” idanuwa direbobin da masu aikin suka tsura musu..Ganin da Abba yayi har sun fara kwasar y’an kallon kamar yadda Dad d’in ya ambata ne yasa kawai ya juya ya koma ciki ranshi a mugun b’ace!. Tsaki Dad yayi ya shige motar yana mai cewa “Ba za ku haukata ni ba, wallahi!”. Shi dai Daddy shiga yayi ya zauna a kusa da shi, yana son tambayarshi wata zuciyar kuma sai ta bashi shawarar ya bari ya Dad d’in ya d’an sauk’o tukunna sai suyi magana… A haka drivern ya ja su suka nufi Gandun Albasa Daddy yana mamakin meye haka yake damun Dad?? Dan tabbas ya san akwai abunda aka yi mishi...... GANDUN ALBASA. Baaba Talatu tana fita harabar gidan ta tarar gurin har ya fara kachamewa! Dan bayan Sakina ta bar wajen Umma da Anty Zainab kan Ummu suka dawo wai “ai itace bata yi mata tarbiyya mai kyau ba shiyasa ta raina manya har haka...” Ga kuma wannan tsohuwa ita ma ta kafa ta tsare tace “Sai Ango ya fito tukunna za a fara gabatar da komai!” Yayinda Ummu da wasu cousins d’inta suke ta k’ok’arin ganin sun yayyafa wa lamarin ruwa amman abun ya faskara!. Baaba Talatu ce ta k’arasa ta ja wannan tsohuwar gefe suka had’u ita da Shuwa suna mata magana k’asa k’asa… Ganin kamar ana shirin fara traditional event d’in cikin kwanciyar hankali ne yasanya Umma ta sake cewa “Nima fa kamar uwa nake a wajen Hudan! Dan haka ba zan bari kowa ya tab’a ta ba har sai Angon nata ya k’araso.. idam kuma fasawa yayi ne to kawai a fito a fad’a wa mutane sai a fasa sakata a lallen, dan ba girman mu bane mu tsaya muna yiwa mutane wasa da hankali! Ko ya kuka gani?” Ta k’arashe maganar tana kallon cousins d’in Ummu waenda suke gefen ta! Ba su kad’ai ba kusan kaff wajen babu wanda bai ji abinda tace ba hatta su Shuwa. “Ga Angon nan” Muryar Mommy wadda suka fito su uku yanzu ta daki dodon kunnuwansu! Da sauri Mama da Aslam suka kalleta! Ba tare da ta kallesu ba ta kama hannun Aslam ta fara janshi Mama na binsu a baya kamar rak’umi da akala shi kuma yana binta!.. Bata cikashi ba sai da ta kaishi gefen Hudan sannan ta zaunar da shi. Da sauri Ummu ta matso k’asa k’asa tace “Mommy a Al’ada fa dole sai Angon zai.... Cikin katseta Mommy tace “A addini fa?” Bata jira Ummu ta bata amsa ba ta sake ce mata “Kalla nan kinga” Tayi maganar tana nuna mata Huda wadda sai a lokacin Ummu ta lura da yanda mayafinta ya jik’e sharkaf! Wanda kana gani ka san ruwan hawaye ne… Mommy bata jira jin me zata ce ba ta ci gaba da yi mata magana k’asa k’asa irin na masu hankali, tace “Saboda ita kawai ki bari ayi a gama! Na tabbatar ba wai rashin zuwan Arshaad kad’ai bane ya saka ta kuka ba! Har da maganganun matar nan! Tun muna parlourn bayankun nan muke juyo komai. Dan Allah kar kice a’a! Kalla kiga mutane kowa ya zuba ido an fara k’ananun maganganu, na tabbatar in dai ba Angon suka gani ba to haka za a tashi ana gulmace gulmace shima kuma sai idan an samu waenchan matan sun bari anyi d’in kenan. Na tabbatar mutane k’alilan ne kuma na jikinku sosai suka san ba Arshaad bane wannan, ba kowa ne zai gane ba so dan Allah ki kwantar da hankalinki ayi abun nan a gama without any more dramas. Saka lalle ai ba d’aurin aure bane ba, ba komai kawai bidi’a ce so mu bisu kawai ayi a gama.” Tana gama fad’an haka ta juya ga jamaar wajen tace “Kuyi hak’uri mun yi latti wani d’an uzuri ne ya tsaida mu! Sunana Hajiya Aisha Maman Ango, mun gode kwarai da zuwanku dan taya mu farin ciki.” Daga nan ta juya ta cewa Ummu “Ni zan fara ko ke?” Da murmushi kwance akan fuskarta. Kallonta kawai suke yi daga Ummu har Mama.....…… Mama da Ummu sun so hana mai video coverage da pics d’auka amman ganin yanda hankalin kowa yake a kansu da kuma Mommy wadda tace ‘su bari kawai tunda ga wasu ma a gefe suna ta d’auka da waya’ ne ya sanya kawai suka hak’ura. K’awayen su Huda kuwa abun ba k’aramin d’aure musu kai yayi ba dan tabbas sun san wannan ba da shi akayi cocktail jiya ba, kuma ba shine a pre wedding ba! A haka dai suka bar maganar akan in an tashi za suni komai a bakin Sakina.... Aslam kuwa so yake ya mik’e amman sam ya kasa! Ya rasa dalili..tun da yake bai tab’a jin fargaba irin wadda yake ciki a halin yanzu ba! Ana cewa k’afafuwa da gangar jikin mutun suna sagewa ya koma kamar gunki bai tab’a yarda da hakan ba sai yau da ya faru a kansa dan hatta kwayar idanunsa ya kasa juyawa, so yake ya runtse idanuwanshi ya samu ya dedeta zuciyar shi amman sam ya kasa! Yana nan a haka yaji Ummu na rufa mishi wata jibgegiyar alkyabba akan jamfar jikinshi Akan hular kanshi Ummu ta d’aura mishi wani jan kyalle mai tambarin moon a gaba golden colour (Allah yaso suna da extra) Daga nan ta mik’a mishi wata sanda wadda ta ci ado! Tace masa “ungo, rik’e” Mommy ce ta kama hannunshi ta sanya mishi sandar sannan ta had’a da nata hannun ta maste! Sai a lokacin ya samu nasarar lumshe idanuwanshi sannan ya d’an bud’e su kad’an yana kallon k’asa.... Ba tare da b’ata lokaci ba aka fara gudanar da alada…….. Bayan uwar Amarya da uwar Ango sun yi, ragowar jama a suma suka zo suka sanya musu suka basu gift daga nan aka fara serving abinci. Sai a lokacin Anty Zainab da Umma suka samu suka iya zama…Umma so take yi ta sake mik’ewa tsaye tace “To Ina y’an unwan Ango!?” ta sake creating scene amman sam ta kaasa dan in banda dishi dishi babu abunda take gani! A ranta ta shiga aiyyana …..Tabbas sai taci uwar malan ado! Wallahi sai ta saka an yi mishi yasin mai walk’iya! Ba Malami ba ko uban waye shi. Kuma sai ya bata kud’inta. Jiya jiyan nan fa ta sake komawa wajenshi dan ta sake nanata mishi, shi kuma ya tabbatar mata da “babu aure tsakanin Hudan da Arshaad ya riga ya gama aiki kuma ya buga k’asa ya tabbatar ba Mijin ta bane ba sannan ya ingiza zuciyar iyayen shi (Arshaad) ya rura wutar k’iyayyar Hudan a cikinta ta yanda ba zasu tab’a bari ayi auren ba musamman ma Mahaifiyarshi (Arshaad)…” Amman kalli yadda Maman nasa taketa jan Hudan a jiki, anyi musu hoto yafi kala nawa tare sai faman fara’a take yi tana washe baki kana ganinta ka san tana cikin tsantsar farin ciki….Inaaaaa!!!!! Taya ma zata tsaya ta yarda Hudan ta auri wannan No1 kyakkyawan da ita tunda take a rayuwarta ko a telebijin bata tab’a ganin mai kyawunsa ba! Ga uban kud’i ga kyau kamar aljani Allah sarki Jalilan ta dole ta mutu akan soyayyar Arshaad, ai kuwa idan zata yi yawo tsirara wallahi sai ta raba auren Huda da Arshaad ko sama da k’asa zasu had’e Wallahi sai dai in rabo ya kasheta akan dai ta zauna ta nad’i wannan abun takaicin da ta san k’arshe in dai bata d’auki mataki ba to shine ajalinta! Kuma ko yana so ko baya so sai ya auri Jalila! Wannan alkawari ne ta d’aukarwa Jalila da ita kanta! D’an halal ka fasa…….. Anty Zainab ce ta tab’o ta wanda hakan ne ya katse mata tunani. Da kyar ta iya motsa wuyanta dan ji take kamar ba jini da rai a dukkannin ilahirin jikinta Suna had’a ido taga itama Anty Zainab d’in idanuwanta sun kad’a sun yi jazir! Kafin Umman tace wani abu taji tace “Sadiya taso mu tafi, kai na ciwo yake yi min” Suna shirin mik’ewa suka fara jiyo gud’a daga parlourn Madu sai a sannan ma suka lura Shuwa da Baaba Talatu da wasu y’an tsirrun mutane basa wajen A bakin matan wajen sukaji an fara k’us k’us d’in “Ashe tun d’azu mazan gidan Ango suka zo sun kawo lefe yanzu suka wuce da yake falon Madu yana da k’ofar shiga da fita ta waje, shiyasa har suka zo suka tafi ba wanda ya sani Sai da suka tafi yanzu akace aje a fito da shi” Sunaji anata k’usk’us d’in “ai motocin da suka zo da su ma kansu abun kallo ne! Gasu kana ganinsu kaga manyan mutanen da kud’i ya zaunamawa” Da kyar Umma take iya jan numfashi, dan ji take yi gaba d’aya iskar wajen bata isarta!. Ummu ce ta d’an matsosu kafin tace “Umma kuzo muje a fito da lefen nan kowa ya gani ko?” Anty Zainab ce ta iya ce mata “eh” Itanma da kyar, daga haka ta mik’e ta d’an dafa Umma kana tace “Muje Sadiya” Da kyar ta iya mik’ewa k’afafun ta suna rawa suka jera ita da Anty Zainab suka bi bayan Ummu suka yi parlourn b’aki. Mutane kam wasu basu ma samu damar shiga ba dan akwatunan sun cike parlourn tap! Ganin kowa cirko cirko a tsaye iya y’an k’alilan kuma na a ciki suna mik’owa ana fitowa da shi ne yasa suma suka ja suka tsaya a gefe kai kana ganinsu ka san basa cikin hayyacin su.. Ta gabansu aka fara wucewa da akwatuna nan kuwa suka maida hankali suka hau k’irgawa! Ana wucewa da goma Umma ta nemi d’an dakalin slop ta zauna dan jiri ne taji yaana d’ibarta ba na wasaba! A tunaninta su kenan amman ga mamakinta sai taga ana ta sake fito da wasu! Ganin ta k’irga ashirin da d’aya basu k’are ba ya sanya ta janyo Anty Zainab wadda itama tayi mutuwar tsaye kafin tace “Zainab zo mu bar wajen nan, tabbas kwakwalwa ta ta d’an samu matsala sannan bana gani sosai! Gani nake yi anata wucewa da akwatuna fa har yanzu basu k’are ba.” Da sauri Anty Zainab d’in tad’an dafa ta dan yanda take magana da sauri kuma da k’arfi kamar wata zararra ya sanya mutane har sun fara d’an juyowa ana kallonsu. A hankali tace mata “Ba idonki bane! Ashirin da hud’u ne cass! Gasu chan ragowar ukun Sai kuma waenchan baskets d’in da ban san na menene ba” Bata ida rufe bakinta ba aka fara fito da na Gwaggo da Kawu. Ai kuwa Umma bata san lokacin da ta mik’e tsaye ba tace “Amman dai Maryam sayar da y’ar nan tata tayi ko!? Haba mana wannan abu kuma ai ya zama hauka! Meye hakan? Me sukeso su nuna?” Cikin takaici Anty Zainab tace “Wallahi Sadiya za kiyi hanyarki nima inyi tawa har a tashi daga bikin nan gaskiya! Maganar Allah kenan, haba mana! So kika mu zama abun kwatance? Sai wasu abubuwa kike yi kamar tab’abb’iya? Kiyi controlling kanki mana Haba?” Ta fad’i hakan tana mai wucewa ta barta a tsaye nan dan a yanda take jin zuciyarta yanzu, tsaf zata iya sauk’e ruwan bala’i da fushinta akan matan dake k’ok’arin maidasu telebijin…. Sai da Umma taga an gama fito da kayan an watse daga wajen sannan ta samu da kyar taja y’an k’afafuwanta ta isa harabar tsakar gidan. Banda gud’a da hayaniyar mata ba abunda yake tashi A lokacin har an bud’e akwatunan farko an fara dubawa…. Sai a sannan ne Aslam ya samu ya tatttaro nutsuwar shi da d’an ragowar kuzarinsa ya mik’e tsaye! Yana mik’ewa Ummu da Mommy suka k’arasa wajensu.. D’an b’ata rai yayi kafin yace “Mommy zan wuce wannan bidi’ar bada ni ba gaskiya” Murmushi Mommy tayi ta shafa kanshi kafin ta juyo ta cewa Ummu “Zai iya tafiya?” Murmushi Ummun tayi kafin tace “eh, zai iya ai an gama komai” A hankali yace mata “Sai anjima” Cikin kulawa tace “Mun gode kwarai Aslam, mun gode.” Ajiyar zuciya kawai ya sauk’e daga nan ya ajjiye sandar hannunshi a gefe ya juya dai dai nan su Sudais suma suka mik’e Shuraim yana ta b’ata rai shi ala dole ya gaji.. Ummu da Mommy ne suka yi musu rakiya har waje, shi da Sudais da Shuraim bayan ya kira drivern da zai maida Mommy gida yace masa ya taho yanzun… Mutane in banda kallonsu ba abunda suke yi sunata yaba kyawun Angon Gashi bai wani zak’e ba irin yanda Angwayen yanzu suke yi! Instead shi ya kama kanshi matuk’a, hakan kuwa ba k’aramin burge jamaar wajen yayi ba. Su Mommy suna komawa suka tarar anata ware lefe an yi filla filla ana gani… Tun daga kan atamfofi Umma ta raina kanta… Zata iya cewa tunda Laraba ta kawota duniya bata taba shiga tashin hankali irin na wannan lokacin ba! Hankalinta bai gama tashi ba sai da aka zo kan akwatunan jewelry’s kit kit waenda aka ware guda biyu aka shak’e taff da sark’a da y’an kunne Na farkon fashion ne Na biyun kuwa gold ne zalla! Matar dake gefen ta ce taji tana cewa “Ai dama su family d’in MT haka suke lefe duk matan gidan da aka tashi aurar su ko wacce sai da aka yi mata kit d’in gold! Yanzu kuma wannan kinga shine jika na farko da yayi aure. Kaii ammanfa wannan Yarinyar ta tako, gaskiya tayi goshi Allah yasa y’ay’anmu a danshinta. Zata sha gata ba kad’an ba! Naji ma kamar ance wai k’asar zai bari ma da ita gaba d’aya!”. Tabbas zuwa wannan lokacin Umma ta daina ganin komai in banda duhu! Maganar ma sama sama ta dawo ji daga nan kuma jinta da ganinta suka d’auke d’iff!! Mutanen wajen kowa hankalinshi yana kan kallon lefe mai abun mamaki da alaajabi Saboda kaff cikin su babu wadda zata ce ta tab’a ganin lefe kwatan kwacin wannan.... Dimmm!!! K’arar fad’uwar Umma ta sa jamar dake kurkusa da ita zabura suka jujjuyo….. “Subahanallah! Mai ya sameta!! D’in da aketa maimaitawa ne ya janyo hankalin mutanen gurin kaff kowa akayi kanta akai mata rumfa...... A zaune Auwal ya tadda shi, a d’akinsa. Ya jinginar da kanshi a jikin gadon ya lumshe idanuwanshi fuskar shi tayi jajawur! Kana ganinshi ka san yana cikin tashin hankali. Auwal bai damu da yanayinshi ba dan shi ganinsa ma da yayi a zaune ko shirin tafiya bayayi shi yafi komai b’ata masa rai! Cikin muryar b’acin rai yace “Haba Arshaad! Ka sa mutane sun tara jama’a kai kawai ake jira kazo ka wani zauna anan, me kake jira? Gaka nan dai a shirye tsaf! Mai kuma ya hana ka tafiya tun d’azun? Nace maka ina zan taho karka jira ni. Ka san yanda hankalinsu ya tashi kuwa? Dagajin muryar Sakina ka san ba lafiya ba! Taso mu tafi da sauri dallah” Wata nannauyar ajiyar zuciya Arshaad ya sauk’e kafin a hankali ya samu ya d’an bud’e lumsassun dogayen idanuwanshi, sai da Auwal ya d’an zabura sakamokon had’a ido da suka yi da Arshaad d’in! Da kyar ake iya hango maroon eye balls d’inshi da suka b’uya cikin jajawur d’in idanun nasa. Sai a lokacin Auwal ya lura da yanda jijiyoyin kanshi suka fito sukai rud’u rud’u! Da sauri ya k’arasa ya zxauna a gefen shi kafin yace “Lafiya kake?? Me ya sameka haka?” Ya jera mishi tambayoyin duk ya rikice. Banda ajiyar zuciya ba abunda Arshaad yake ta faman sauk’ewa yama kasa yi mishi magana Da kyar ya samu yace “Mammy ce ta….” Sai kuma yayi shiru. Cikin firgici da tsoro Auwal yace “Ta hana ka zuwa?? Lumshe ido Arshaad yayi kafin a hankali yace “Har ma auren! Tace idan aka d’aura sai ta tsine min!” A zabure Auwal ya mik’e kafin yace “Innalillahi wa innailaihirrajiun! Shine kuma ka zauna za ka kashe kanka haka? Zama ai bai ganmu ba! Bara in je in samu su Dad in yi musu bayani, idan ta kama har Granpa sai a sa a case d’in. Mai yasa Mammy zata yi mana haka?” Ya k’arashe maganar kamar mai shirin fashewa da kuka. A hankali Arshaad d’in yace “Ba wanda bai sani ba. Kowa ya san da case d’innan. Har mamanta da sisters d’inta duk an bata hak’uri amman tak’i hak’ura.” Wata kakkausar ajiyar zuciya Auwal d’in ya sauk’e kafin yace “Ya aka yi Mammyn ta sani? Last time da naje na dubasu naga kamar duk basu san da zancen ba.. Na san dama suna iya causing problems shiyasa nima ban yi gigin fad’a musu komai ba! Ko maybe Ummi da aka kawo ce ta kirasu ta gaya musu?” Da d’an mamaki Arshaad d’in yake kallon shi kafin ya sauk’e ajiyar zuciya yace “Baka had’u da Mom ba hala? Sun dawo jiya. All of them” Da mamamki shima Auwal d’in yake kallonshi ya ma kasa cewa komai. A hankali Arshaad ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace “Auwal do me a favour.. Ka kira Sakina, inaso kayi mata bayanin komai amman kace kar ta fad’awa kowa kawai a san yanda zaai a gudanar da event d’in ba tare da an jira ni ba! Yanzu na san Mammy idonta a kaina yake dan tun d’azu nake lura tanata turo Aaima tana mata patrol so ba zan iya fita ba. Sakina is smart she’ll know what to do yanzun In shaa Allah ni kuma anjima da daddare za mu je Ina son ganin Hudan na san abunda zan yi. For now amman kawai ka lallab’a mun Sakina tayi handling komai, kafin nan da anjima.” Cike da gamsuwa Auwal d’in ya d’aga kai alamar to sannan ya zaro waya ya fara kiran Sakina. Tun lokacin da aka fara rangad’a gud’a taji dan haka ta mik’e ta lek’a ta windown d’akin Shuwa.. Ji tayi kamar ta zuba ruwa a k’asa ta sha sakamokon hango su su biyu a zaune da ta yi! Bata ganin fuskar su especially Huda da har yanzu tata fuskar a lullub’e take sannan windown a rufe ne kuma sun yi mata nesa.. Bata san lokacin da hawayen farin ciki suka zubo mata ba! Tana gani yanda mata suke zuwa suna d’an d’aga mayafin kad’an suna shafa mata da hannuwanta shi kuma a tafukan hannunshi da goshinsa ake shafawa sannan su ajjiye musu gift a cikin d’an kwanon da aka ajjiye wasu kuma kud’i. Ba k’aramin burgeta suka yi ba, banda kalmar ‘Alhamdulillah’ ba abunda taketa nanata a ranta tana mamakin dalilin da ya sanya Aaima karkacewa ta gilla mata wannan uwar k’aryar haka Wata zuciyar kuma tace maybe an gyara abunne Mammyn ta sauk’o cikin kawar da tunanin a ranta tace “Chan ta matse musu” Sannan ta hau raya yanda zata yiwa Arshaad in sun had’u na k’in d’aukar wayarta da yayi. K’arar wayarta dake kan gado ce ta katse mata tunani dan haka ta isa ta d’auki wayar.. Kamar ba zata d’auka ba ganin sunan Auwal ne sai kuma ta d’anyi murmushi a ranta tace ‘Kar In zama kaza mana’ dan haka ta d’auka ta kara a kunnenta kafin yace komai tace “Gashi chan Ya Arshaad d’in yazo suna zaune ana saka su a lalle. Thanks for your time” Tana gama fad’in haka ta katse kiran. Da mamaki suka kalli juna shi da Arshaad dan a hands free wayar take Shiruu, d’akin ya d’auka chan kuma Auwal yace “Bara inje wajen maybe ko fushi suka yi shiyasa tayi min gatse” Cikin katseshi Arshaad yace “Kaje wajen Mom mana. Kace bama ka san ta dawo ba bayan a gida d’aya kuka kwana. Kaje wajenta daga nan ka d’an lallab’ata may be in tasa baki Mammy ta hak’ura.” Har ya d’anyi gaba sai kuma ya juyo yace “Su kuma fa?” “Kar ka damu na gama tsara komai, zuwa anjima da daddare za muje in shaa Allah. Zan sameka a gida.” Cewar Arshaad yana mai maida kanshi da lumshe ido dan kanshi ba k’aramin ciwo yake yi ba amma kuma har ga Allah y’ar maganar da ya samu suka yi da Auwal ya d’an ji sassauci a ranshi. “Allah ya kaimu” Shine kawai abunda Auwal yace yana me fita daga d’akin da waya kare a kunnen shi still yana sake kiran Sakina sai dai har ya tsinke bata d’auka ba. A tsakiyar main parlourn suka kusa yin karo da Aaima, kasancewar hankalinshi naga wayarshi yana turawa Sakina message. D’agowa yayi yana kallonta itam ma shi take kallo kafin da kyar ta iya cewa “Ya Auwal Ina wuni” “Fine” kawai yace yana me wuce ta. Da sauri ta sha gabanshi kafin tace “Am dan Allah gida zaka je?” Maida hankalinshi yayi a wayar kafin yace “Eh” A hankali tace “Owk, d’an jirani plss Mammy ta bani sak’o wajen Mom ina so zan kai mata. Bara in d’auko vail d’ina”. Ba tare da ya kalletaba ya k’arasa kan d’ayan daga cikin kujerun parlourn ya zauna still yana danna wayarshi. Ta fahimci yaren kuramen nashi dan haka ta wuce sama da d’an sauri … Bayan 5 minutes ta sauk’o! Ta chanza kaya daga atamfar ankon dake jikinta ta d’aura bak’ar abaya tayi rolling, ta sanya lipstick da powder. Ta yi kyau kuwa ba laifi. Gabanshi tazo ta tsaya sannan tace “muje” Tun kafin sauk’owarta daman ya san ta taho sakamokon k’amshin turarenta da ya karad’e parlorn! Tana sauk’owa kuwa ya lura da ita amman sai ya kawar da kai… Wai me Aaima take nufi ne? Ya kasa gane kanta kwana biyun nan! Har magana take mishi ta WhatsApp yanzu. Yana tunawa lokacin da suke tare yasha gaya mata yana matuk’ar son yaga mace da black abaya tayi rolling abun yana burgeshi shiyasa kusan duk lokacin da zasu fita tare takan yi irin wannan shigar kuma ta san baya son native cloth kwata kwata Inba riga da wando ba to abaya….. “Mu tafi, na shirya” Muryarta ta katse shi. Kallonta yake yi tun daga sama har k’asa! Hakan kuwa ba k’aramin dad’i yayi mata ba. A hankali taji yace “Ina sak’on??” Diriricewa tayi kafin da kyar tace “Yana cikin purse d’innan” Tayi maganar tana nuna mishi purse d’inta wadda ta saka iya wayarta da lipstick a ciki. Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya mik’e yayi gaba…. Shi fa har ga Allah kunyar ta yake ji a halin yanzu..idan ya tuna irin yanda ya fito mata k’iri k’iri ya fad’a mata abunda yake buk’ata daga gareta da kuma yanda ya furta mata kalmar ‘ba ya k’aunarta’ Wasu abubuwan da yawa da ya yiyyi idan yana tunasu a yanzu sai ya dinga ji kamar k’asa ta tsage ya shiga! Tabbas Daddy yayi gaskiya daman ya tab’a gaya mishi ‘’’Akwai ranar dana sani!Ranar da zaka ji inama ana yin reverse ayi maka domin ka samu ka aikata alkhairi ka kuma goge duk wani abun da kayi marar kyau. Ranar tana nan zuwa, ko bayan raina za kace na fad’a maka‘’. Tabbas kuwa tun kafin aje ko Ina gashi ranar ta zo Ya san dalilin da ya sanya Sakina take gudunshi ta kuma k’i sa! Bai wuce akan tunanin da take yi na alak’ar shi da cikin jikin Jalila ba ne…..bai san wanne kalar kallo zata yi masa ba idan taji tabbas cikin nasa ne! Ballantana kuma azo kan maganar halayyarshi da baya fatan Allah yasa Sakina ta sani! So yake ya gyara komai ya zama mutumin da ta ambata tana son kasancewa tare da! Gashi already yana da competition, yanzu ahaka ma ta riga ta nuna mishi ta zab’i Ashraff a kansa ina kuma ga idan taji wata magana akanshi! Ya kenan?…., “Innalillahi wa innailaihirrajiun” Itace kalmar da ya ambata yana mai dafa motar shi dan har sun iso bakin motar. Da sauri Aaima tace “Subahanallah Ya Auwal mai ya faru?” Tana mai matsowa inda yake. Sai da ya d’an runtse idanunsa kafin ya dawo dai dai tukunna ya samu yace mata “Ba komai, shiga mu tafi” Yana mai zagayawa ya bud’e mazaunin driver ya zauna. Tana shigowa ya tada motar yaja suka fita. Har suka isa mansion d’in nasu babu wanda ya samu damar furta kalmar ‘a’ a cikin su. Shi ya fara fita daga nan itama ta fito suka nufi ciki. Suna shiga parlourn suka tarar da Jalila ta d’aura k’afa d’aya kan d’aya ga remote a hannunta tana ta chanja channel… Lumshe idanuwanshi yayi a hankali ya shak’i iska ya furzar sannan ya bud’e idanuwan nashi a hankali a fili yace “My worst regret!!” Ya kasa gaba ya kasa baya. Aaima ce tayi k’arfin halin k’arasawa tsakiyar parlourn inda Jalilan take tana kallon ta da d’an mamaki dan kamar bata tab’a ganinta ba. Fitowar Mom daga kitchen ne ya katse mata tunani har shi Auwal d’in Uwa mai dad’i suna had’a ido yaji wani sanyi a ranshi… Takawa yayi har inda take yana zuwa ya sa hannu yayi hugging d’inta..... Tun a cell Mom take aiyyana kalar abubuwan da zata yiwa Auwal kala kala In Allah ya maidota gida lafiya dukda kuwa tana shakkarshi, babu yadda bata yi mishi shi da Arshaad akan su basu kud’i su samu su fito ba amman suka hana su saboda suna shakkar Granpa sannan basu san darajar su uba and sun rainasu! Sannan ta dawo amman tun jiya take zuba ido but bataga k’eyarsa ba. A hankali yace “welcome home“ Ta manta rabon da Auwal ya nuna wani affection a kanta irin haka, ba ta san lokacin da wata kwalla ta zubo mata ba, a hankali tasa hannu ta share tana jin duk wata wutar masifar da ta shirya juye mishi tana sauk’a daga k’irjinta. Muryar Jalila ce ta katsesu jin da d’an k’arfi tace “Adama ina shayin nawa??” Da mamaki Aaiima take kallonta sai kuma ta juya tana kallon su Mom. Da sauri Auwal ya cika Mom ya yunk’ura zai yi wajen yaji ta rik’e mishi hannu yana juyowa ta girgiza mishi kai daga nan ta koma kitchen ta d’auko tea d’in daman ta gama had’awa waya take so tayi shiyasa ta manta ta fito d’aukar wayar. Zata nufi wajen Jalilan amma ga mamakinta sai taga Auwal ya tare, yace “Ba zata kaiwa Jalilan ba wallahi!. Idan tana son sha to tazo ta d’auka anan d’in!” Ya fad’a hakan yana mai karb’ar tea d’in ya d’aura akan dining sannan yaja hannun Mom d’in za suyi sama. Da kyar mamakin Auwal ya barta ta iya ce mishi “Ban ci abinci ba, Bara in na gama sai muyi saman dukkanmu ko?” Ajiyar zuciya ya sauk’e ya watsawa Jalilan wata uwar hararar da sai da y’an hanjin cikinta suka kad’a! Daga nan ya cika hannun Mom d’in ya wuce sama. Tabbas Jalila ta d’an sha jinin jikinta kuma it’s like kamar akwai abunda yake damunshi sannan tanada buk’atar kud’i daga hannunshi da kuma alfarmar ya barta ta je wajen Umma dan she can’t afford to loose Arshaad, duk da kuwa Umman tace mata akwai nasara amman tana son zuwa yau ta bita ta je da k’afafuwanta, shiyasa ta barshi kuma bata sake yiwa Mom wani yunk’uri ba ta hak’ura kawai ta barshi akan idan ya d’an huce kamar nan da 20 minutes haka zata kirashi ta zayyane mishi buk’atun ta. Hira sosai Mom da Aaima suke yi, Jalila kuwa tana gefe tanata hura hanci. Chan Mom ta cewa Aaiman tazo suje suci abinci. Haka suka mik’e suka isa dining d’in sukai lunch d’insu cikin kwanciyar hankali. Sai a sannan Aaima take tambayar Mom wacece jalila? Murmushi kawai Mom d’in tayi sannan tace mata “no one” kawai, daga nan tace “Ta mik’e ta je ta jirata a parlourn sama. Hakan kuwa akayi, Mom na ganin wucewar Aaima ta mik’e itama tayi kitchen….. Dama tun d’azu ta sallami cooks da masu goge gogen gidan! Tace musu “su tafi part d’insu In akwai wani abun zata neme su!” Har ta shiga ta d’auko abunda zata d’auka ta fito hankalin Jalila yana kan kallo. A dai dai stairs na bakwai ta tsaya ta zuba abunda zata zuba tayi sama abunta da cup d’in cikin sand’a. Kamar minti biyu ta dawo bayan ta ajjiye abun hannunta a d’an gefe kad’an a nan saman ta tsaya a saman bata sauk’o ba kafin ta d’an fara sauk’owa sai kuma ta tsaya tana lek’en parlourn k’asan kafin tace “Jalila ga Ummanki tayi miki message, ungo wayarki, tunda na hau nake ta jin k’arar wayar shine na duba d’akin naga misscalls da messages Za ki zo ki karb’a? Ko kuma ma kawai bara in karanto miki kina daga zaune dan na san mik’ewa yanzu aiki ce a gareki saboda yanayin da kike ciki.” Ba tare da b’ata lokaci ba Mom ta fara karantowa “Aslm Jalila ya gidan, yau banjki....” A zabure Jalila ta mik’e tayi hanyar stairs tana masifa “Adama bana son rashin mutunci! Yanzu ke inda ace uwarki ce tayi miki message zaki yarda a karanto miki….?” A fusace take maganar tana tahowa da d’an cikinta wanda ya d’an fara tasowa! K’arfen stairs d’in ta kama cikin sassarfa ta fara taka stairs d’in har da d’an gudunta, tana zuwa kan na bakwai kuwa ta zulme santsi ya d’ebeta a take ta hantsila ta gangara ta koma k’asa ta fad’a ruf da ciki a kan cikinta! Wata azababbiyar k’ara ta saki daga nan ta saki jiki bata sake motsi ba!. Da sauri Mom wadda daman da tsummanta har biyu ta ajjiye a gefe farkon stairs d’in dan haka ta d’an juya ta d’auka ta sauk’o, dai dai wajen na bakwai d’in ta saka wet one d’in da ta jik’a a ruwan omo ta goge wajen tass kafin ta saka dry one d’in ta goge wajen sosai shima. Dai dai nan Auwal da Aaima waenda k’arar Jalilan ya janyowa hankali suka taho a tare… Da sauri Mom ta d’ago ta kalleshi a rikice kafin tace “Yauwa Auwal zo ka duba inaga jiri ne ya kwasheta kaga ta fad’i kamar ma ta suma bara in d’ebo ruwa.” Ta fad’i hakan tana mai sake duk’unk’une tsummokaran a hannunta Yayinda su kuma gaba d’aya hankalinsu ke a kan Jalila… Idan idanuwansu ba gizo suke musu ba kamar jini ne yake fitowa ta k’asan ta! Shiyasa ma kwata kwata basu lura da Mom d’in ba suka fara sauk’owa har suna y’ar rige rige, ita kuma ta wuce wuff!! Tayi kitchen tana mai cewa “bara in kawo ruwan” Hankalin Aaima ba k’aramin tashi yayi ba ganin kamar ma ta mutu ne! Ga kuma jinin da taga yanata kara b’ulb’ulowa, shi kanshi Auwal duk da cewa babban burinshi a halin yanzu yayi getting rid of Jalilan ne amman sai da ya firgita ba kad’an ba. Suna a haka Mom ta fito, ruwan da ta zo da shi a jug gaba d’aya sai da ta juye mata shi amman ko gezau Jalilan bata yi ba! Ganin haka yasa Auwal yin sama da gudu ya je ya d’auko makullin motarshi ya dawo ya zo ya kinkimeta yayi waje su Mom suna binshi a baya…. Yana gama sakata a bayan mota motocin su Dad na shigowa ganinshi a d’an firgice yasa suka tsaidashi suka hau tambayarshi.. Da kyar ya iya ce musu Jalila ce ta fad’o a bene ta suma ya shige ya tada motar ya fice a 70 ya bar su Mom suna sake yi musu bayani “Allah ya sauwwak’e” suka ce. Shi kam Dad bai ma san wacece suke magana akai ba daga haka suka nufi side d’in Abba dan Dad yad’an yiwa Daddy bayani a mota So ya kamata su sameshi ya maida Ummi first kafin granpa ya tsine mishi, sannan kuma ayi maganar ta yanda za a b’ullo wa haukar Mammy dan sun yi alk’awarin in dai sune mazan mt masu fad’a aji to tabbas gobe sai an d’aura aure bi izinillahi! Babu fashi….. GANDUN ALBASA “Ku bata iska mana ya duk kuka lullub’eta haka ne??!!” Cewar Baaba Talatu wadda take k’arasowa wajen da kyar. Da sauri duk aka fara matsawa gefe. Hansai da Anty Zainab da wasu mata Baaba Talatu ta umarta da su d’auketa a kaita parlourn da ga nan ta cewa Maryam “ta kirawo Likitan da take zuwa tana dubasu.” Hakan kuwa aka yi Nan tace mata “gata nan zuwa tana ma kusa dama, su bata nan da minti goma.” Ko da Likitan ta zo da kyar ta samu Umma ta farfad’o amman ta bada shawarar a kaita emergency a take dan jininta ba k’aramin hawa yayi ba! A motar Abba k’arami wanda suka iso yanzun nan shi da iyalinshi da Mahaifiyarsa da Baban sa aka kaita asibitin. Duk da halin da take ciki da suka had’u da Ya Jamilu a waje bakin motar sai da ta tambayeshi “ina Baba?” “Yana nan” kawai ya iya ce mata daga nan ta shige ita da Anty Zainab wadda ta zauna a gaba suka wuce asibitin. Da kyar Mama ta iya tsayawa aka gama kallon lefen da ita daga nan ta wuce ta shige tayi sama… Tun a corridor d’in d’akin Shuwa ta saki kukan da take ta k’ok’arin dannewa. Da sauri ta tura k’ofar ta shige tana wani matsanancin kuka a tunaninta ba kowa amman tana shiga suka yi ido biyu da Sakina. K’ok’ari take yi ta danne kukan ta wayance amman ta kasa dan haka kawai sai ta durk’usa ta sake sakin shi a wajen da dukkan k’arfinta tanayi kamar ranta zai fita......... BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 54 Da sauri Sakina ta k’arasa wajenta ta hau tambayarta “mai ya faru?” Bata iya bata amsa ba, sai da ta d’an dedeta kanta da kyar tukunna ta d’ago jajayen idanunta tana kallon Sakina tace “Kina da number Abba? Baban Huda.” A hankali Sakina ta hau girgiza mata kai..kamar wadda ta tuna wani abun kuma sai ta mik’e ta isa gado inda ta ajjiye purse d’inta, tana cewa “Amman ga wayar Hudan, bara in kira miki shi ta nan” Da sauri Mama ta mik’e ta isa inda take dai dai Sakina ta fara dialing number Abban, Mama ta sa hannu ta karb’a wayar ta kara a kunnenta. Sai da kiran ya kusan tsinkewa tukunna ya d’auka! A hankali taji yace “Princess, how was your day?” Sai da Mama ta lumshe idanunta na sakanni wasu zafafan hawaye suna zubo mata tukunna tace “Horrible, Abba! Her day was horrible!”. Da sauri ya gyara zamanshi kafin yace “Maryam” Cikin son sake tabbatarwa. Cikin kuka tace “Lalata mini rayuwa da farin cikin da kayi bai isheka ba sai da ka had’a da Huda ko? A haka sai faman ik’irari da pretending d’in kana k’aunarta kake yi!.. Abba in dai har kana son ta mai yasa ka jefa ta a irin wannan relationship d’in??? Da ka san mahaukaciyar matar yayanka ba zata so auren Arshaad da Hudan ba mai yasa tun farko kuka had’a? Saboda ku maidamu abun kwatance ko me?? An tara mutane k’iiri k’iri Ango yak’i zuwa! A Ina aka tab’a yin haka? To bara kaji in gaya maka Tunda har Mahaifiyar Arshaad da kanta ta furta cewar bata son y’ata a matsayin suruka To Wallahi ko ta dawo tace tana so, Ina so ka san cewa ‘maganar aure babu ita!!’ Sak’o ne wannan na baka, ka gaya mata ka gayawa Arshaad da wakilin shi! Dan ba zan tab’a yarda in kai Huda gidan da ba’a k’aunarta ba wallahi. Saboda na san zafin k’iyayyar surukai” Ta fad’i haka tana fashewa da wani matsanancin kuka. Da sauri Abba wanda yakejin zuciyarshi tana wani mahaukacin racing yace “Maryam listen to me dan Allah ki bar wannan kukan” Cikin tsananin b’acin rai tace “Abba kuka yanzu na fara! Na san zan yi kuka especially idan Allah ya kaimu gobe aka yi calling off auren y’ata na ganta a cikin tashin hankali dole zan yi kuka.....” Kasa cigaba ta yi da maganar dan haka ta yi jifa da wayar akan gadon ta durk’ushe a k’asa tana kuka. Sakina na shirin yin magana Ummu da Mommy suka shigo. Ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e tanaji itama kamar ta fashe da kukan, a hankali ta d’an matso Maman sannan tace “Wannan dalilin fa shiyasa nak’i gaya miki tun farko, kin yi min alk’awarin ba zaki d’aga hankalinki ba yanzu menene haka? Ki kwantar da hankalinki ni na san Mammy bata isa ta hana komai ba! Dad ba zai barta ba.” Cikin katseta Mama tace “Wallahi ko Dad ya barta ko bai barta ba babu maganar aure tsakanin Huda da Arshaad Idan ita ta hak’ura to gobe ni zan hana! Ta yaya kuke tunanin zan bar y’ata ta rayu da surukar da bata sonta? Mommy na san mecece k’iyayyar surukai! Kullum addua ta Allah ya had’a Huda da surukan da zasu k’aunaceta. Taya za ki yi tunanin yanzu zan amince ta auri Arshaad??” Cikin katseta Mommy tace “Kar kiyi haka dan Allah, kawai mu zuba ido amman kar kice zaki shiga tsakanin kaddara! Idan kika yi hakan ai kun zama d’aya ke da Mammy kenan.” Cikin katseta tace “In zuba ido y’ata ta tafi inda ba a k’aunarta kome kike nufi? In zuba ido rayuwar Huda ta lalace kamar yadda tawa ta lalace?” Cikin rashin jin dad’i Mommy tace “Haba Maryam, rayuwarki bata lalace ba, da ni da ke fa kusan mataki d’aya muka taka a rayuwar aure. Tabbas mun jigatu kuma mun sha wahala amman a ko da yaushe idan na kalli Aslam wallahi ji nake gaba d’aya wahalar it’s worth it! Dan Allah yayi mana kyauta. Kuma dama a rayuwa dole akwai jarabta da kuma gwajin imani. Ni dai shawarar da zan Baki itace Dan Allah kar kiyi interfering ki zuba ido ki barwa mazan komai, su sun san me za suyi.” Cikin sharar kwallah Ummu tace “hakane tabbas! Mama dan Allah ki gwada yin hak’urin da kika saba wata rana sai labari.” Da sauri Baaba Talatu wadda bama su san ta biyo su ba ta k’araso tace “Taya zaku ce mata haka? In dai uwar Yaro tace batayi to muma ba zamu kai jikarmu mai tsada inda ba’a k’aunarta ba wallahi! Allah na tuba maza da yawa a gari.. Ga mai sunan kakan ta nan, d’an wajen Jamilu, idan Arshaad d’in zai kawo matsala ana iya d’aura musu aure gobe in sha Allah. Na san ba zai tab’a cewa a’a ba, saboda daman ni na d’an so in fahimci take takenshi tun ba yau ba.” Gyaran murya Shuwa wadda ta shigo yanzu tayi, dan haka duk suka juya suna kallonta. A hankali ta k’araso cikin tafiyar ta wadda ke nuna tsufan da ya rufar mata. Sai da tazo gaban Maryam tukunna ta kama hannuwanta duka biyu ta fara magana “Dan Allah dan annabi kar ki yi komai kar ki yi kuka kar ki d’agawa y’ar ki hankali. Ki bar komai a hannun Ubangiji, tun kafin ki haifi Huda already an riga an gama rubuta k’addararta da komai nata. Kar ki yi interfering wai dan kina tunanin zaki iya kub’utar da ita! ki zuba ido ki yi mata addua komai zai tafi bisa yanda Ubangiji ya riga ya tsara. Bamu isa mu saka ko mu hana komai ba. Kin ji y’ar albarka?” Ta k’arashe maganar tana mai sa hannu ta share mata hawayenta duka biyu. Kuka Mama ta sake fashewa da shi ta fad’a jikin Shuwa suka rungume juna. Ita kanta Shuwan k’arfin hali ne kawai da dauriya suka hanata kukan Ta rasa gane wachche iriyar k’addara ce A rayuwar Maryam da Huda, Astaghfirullah..... Shigowar ta tare da matan da suka ruk’o ta ne ya sanya d’akin yin shiru. Har yanzu fuskarta a rufe take amman kana gani ka san kuka take yi. Sakina na ganinta taji kuka na shirin kufce mata dan haka da sauri ta fita a d’akin. Suna zaunar da ita a bakin gado Mama ma ta saki Shuwa ta fice. Shuwan ce tayi k’arfin halin cewa “Mommy da Ummu da kuma mata biyun da suka shigo da ita “Su je akwai motoci a fara kwasar kayan Amarya ana kaiwa gidanta, dan ba zata yarda da ajjiye wannan dukiyar a gidanta ba, tunda kowa ya gani kawai su kai mata abunta gidanta.” Murmushi Mommy tayi kafin tace “Ni kam gida zan wuce.. Ina a matsayin uwar Ango ina ni ina ziryar gidansu Ai nayi jere sai kuma in ta haihu nan da wata tara in sha Allah ni da in koma.” Da sauri cikin raha ragowar matan suka ce “In shaa Allah” Ba a wani dad’e ba suka fito dukkansu a tare Mommy ta d’anso ta sake ganin Mama amman kuma kawai sai ta rabu da ita, a cewarta ‘in ta d’an sauk’o zuwa anjima zata kira ta a waya’….. A tare suka fito da Ummu, su suka fara yin gaba da akwatuna ita kuma ta shiga mota ta nufi MT estate dan already drivern ya zo tun d’azu. NASARAWA g r a. Daddy da Dad na zaune sai zazzagawa Abba fad’a suke yi akan ‘ya mayar da Ummi tun kafin zance ya isa kunnen Granpa’ shi kuma ya tubure ya k’i!. Suna a haka wayar Mama ta shigo… Tsaf! Duk sun ji abubuwan da ta fad’a, dan wayar a high volume take kuma suna kurkusa da juna. Yana gama wayar Dad yace “Abba ka mayar da Ummi yanzunnan in dai na isa da kai.” Haka shima Daddy same thing ya fad’a mishi. Ba yadda ya iya haka ya maida ita yana ji kamar yayi ta kurma uban ihu!. Daganan Dad ya mik’e! Kamar Daddy ya san meye a ranshi yayi saurin mik’ewa shima ya tsaya a gabanshi sannan yace “Dan Allah kar ka yi haka. Ka tsaya zan yiwa Adama magana, na san kafin zuwa gobe in sha Allah zata nutsu.” Cikin fad’a fad’a Dad yace “Ba zata nutsu ba! Sam ba zata nutsu ba. Da ace zata nutsu da tun tuni ta nutsu, ku bar ni kawai!!” Ya fad’i haka yana k’ok’arin zagaye Daddy ya wuce. Da sauri Daddy ya kuma tareshi sannan yace “Ya abunda muka gama gyarawa yanzu! Da girman ka kake k’ok’arin aikatawa?” Cikin tsananin b’acin rai Dad yace “This is a different case..” Cikin katseshi Daddy yace “Ba wani different case anan duk abu d’aya ne! Idan kayi mata haka ma ai ka ji haushi kenan, wato ta ci riba ma kenan tunda har kaji haushi ka hukuntata, ai idan mata suna haukarsu ba a biye musu. Tabbas na san dole ana buk’atar albarkar ta amman ka b’ullo mata ta bayan fage. Wani abun fa dole sai ka sauk’o, ka san yadda za ayi a d’aura auren shine ka ci riba! Amman yanzu idan ka biyeta ka saketa aka zo ta sake birkicewa Wa gari ya waya? Abunda ya kamata kayi shine ka san ta inda zaka b’ullo mata ka bawa iska ajiyar ta ka nuna kamar bama ka san me take yi ba! Ka d’aure ta da jijiyoyin jikinta Tana ji tana gani a d’aura auren gobe kamar bata existing a duniyar! This is the best punishment da tayi deserving, amma yanzu idan kayi haka( ka saketa) ai jagula komai za kayi, kuma itace zata yi nasara at the end of the day tunda Uwa ce. Ka ga dai ga Granpa a gefe wanda a yanzu haka jira kawai yake yi a tab’a shi! Kai da kanka kace yayi mana warning a kansu duk mu ukun I assure you wallahi idan kayi wani abun ba zai duba laifintaba zai bi takanka......” Sannu a hankali Daddy ya samu ya shawo kan Dad da kyar! Ya hak’ura. Shi dai Abba yana nan zaune bai ce musu uffan ba! Dan ba fahimtarsu yake yi ba har yanzu ba abunda yake yi mishi yawo a kunne sai kukan Maryam da tashin hankalin da ya jita a ciki. Tabbbas sai ya gasawa Ummi aya a hannunta! Hakan ba halinshi bane ba kuma bai kamata yayi mata hakaba a matsayin ta na mahaifiyar su Sudais amman ba yanda ya iya…Dole ta san waye Abba! Ba ita kad’ai ba har su Mammmy, kasancewar su yayu a gareshi ba zai hanashi ya ja musu fasali ba. A hankali ya mik’e ya yiwa su yaya rakiya, daga nan shima ya fita ya bar gidan. Dad da Daddy direct asibitin da aka kwantar da Ummi suka je, an samu ta farfad’o sai dai har yanzu jikin nata ba kwari. Likitan ne ya ke gaya musu “jininta ne ya hau sannan tana da buk’atar rest mai kyau. Za su iya tafiya da ita gida idan suna ganin gidan will be more comfortable for her dan ba abunda za suyi mata anan (asibitin) sai y’an drip da y’an allurai da maganin bp d’inta. Hutun ta da kwanciyar hankalinta shine abun buk’ata a yanzu.” Dad ne yayi signing discharge papers d’in daga nan suka nufi gida da ita. Tunda aka kamo hanya Ummi take ji inama mutum zai iya kashe kanshi babu zunubi, wallahi da ba abunda zai hanata commiting suicide a yau d’innan! Atime d’in da ta farfad’o taso a ce mutuwa tayi.. Tun da ta taso tayi wayo ta san kanta Soyayyar mutane biyu zxuwa uku ta sani Abba Gramma sai Granpa! Yanzu kuwa da ta kawo yanzu ta san menene so ta san tabbas muddin babu Abba a rayuwarta to mutuwa ce tayi saura! Shiyasa kawai ta koma kamar mutun mutumi Ba abunda ya cika zuciyarta sai d’umbin dana sani Ita inda Abba zai yarda wallahi ya auro Maryam uku! Ya kawo ya had’a da ita su zama su hud’u, ta san za tayi kishi tabbas amma kuma zata hak’ura ta daure ta danne zuciyarta su zauna lafiya…… Tana cikin wannan tunanin taji su Dad suna danna horn! D’ago kanta tayi ga mamakinta sai ta gansu a mansion d’in su Abba instead of estate, addua ta fara yi a k’asan ranta ‘Allah yasa su Dad su saka Abba ya mayar da ita’. Ba wanda yace mata komai. Sai da suka shiga cikin parlourn suka zauna tukunna Dad yace mata “Ummi sai kin yi hak’uri da Abba a yanzu. Kar ki damu In sha Allah zai sauk’o. Kin ji. Ki tashi kije d’akinki ki huta. Ya gyara abunda ya b’ata d’azu. Ki kwantar da hankalinki Naki biyayyane, kin ji?” A hankali take jan numfashi tana share hawayenta tana jin wani farin ciki yana ratsa ta. “Tam Dad mun gode” Tace. Sannan ta fara k’ok’arin mik’ewa dai dai nan su Sudais da Shuraim da Aslam suka shigo! Suna ganinta suka yi kanta da gudu suna Ihun murna Shuraim harda y’ar kwallar shi Itama sai da tayi kwallar murnar ganin gudan jininta. Daga nan suka gaisa da Aslam ta wuce tayi sama ita da su Sudais. Tun a hanya Sudais ya fara zuba surutu yana bata labarin event d’in, da kalar hotunan da suka yi da kuma yanda Ya Aslam ya zauna a kusa da Huda…. Gaisawa kawai Aslam yayi da su Dad daga nan suka fice gaba d’ayansu.. Basu yi mishi zancen event ba shima daman hakan yake so.. Iya kar abunda suka sani shine Arshaad bai yi attending ba!. Shi da Dad suka yi gida Daddy kuma yayi side d’inshi. Sai dare Jalila ta farfad’o! Ba kowa a d’akin sai ita kad’ai. Jiri da ciwo a mararta take ji ba na wasa ba! Tana so ma ta mik’e ta d’an zauna amman ta kasa… A hankali kwakwalwarta ta shiga tariyo mata abunda ya faru da ita d’azu. Da sauri ta zabura ta dafa cikinta, dai dai nan nurse ta shigo. Cikin kulawa ta hau gwada ta tana mai tambayarta “ina da Ina ne suke yi mata ciwo?” A hankali Jalilan tace mata “Mai ya sameni? Marata tana yi min ciwo.” Cikin kulawa nurse d’in tace “I’m sorry ma’am, kin yi loosing baby d’inki ne” “L lo Loosing, me?” Cewar Jalila. Ganin kamar bata fahimceta ba ya sanya tace mata “Kin yi miscarriage! Cikin jikinki ya fita.” Da mugun k’arfi ta mik’e ta zauna sai kuma ta fashe da kuka! Dai dai nan Mom ta shigo. Tana ganin tana kuka tayi sauri ta k’arasa ta fara bata hak’uri sai kuma ta juya ta rufe nurse d’in da fad’a, tana cewa “Ba ance jinin ta ya hau sosai kar a d’aga mata hankali ba? Shine amma lokaci guda zaki zo ki fara zuba mata wannan mugun labarin? Asibitin gwamnati ya kamata ki koma ba private ba! Tunda baki iya tausar patient ba. Ai inda kin bari da mu da kan mu za mu gaya mata idan mun koma gida....” Hakanan dai Mom ta wanke nurse d’in tass!! Ta inda take shiga bata nan take fita ba dag nan tayi signing discharge papers taja Jalila suka nufi mota driver ya jasu….. Ita dai Jalila in banda kuka ba abunda take yi… har ga Allah bata son cikin nan ba taso ta haihu amma kuma yanzu da cikin ya fita ta san tabbas ba abunda zai shiga tsakaninta da komawa gandun albasa!! Sannan ta daina samun kud’i daga Mom da Auwal kenan har abada! Amman kuma yadda Mom take lallab’ata sai ta d’an ji zuciyarta ta d’an yi sauk’i! Maybe tausayinta take ji amma duk da haka ta san ba zai wuce na sati ba zata tarkatata! Dan haka a take ta yanke shawarar nemawa kanta mafita.. Zata lallab’a Mom ta bata hak’urin abubuwan da ta dinga yi mata Idan ta kama ma sai tayi k’aryar aljanune da ita tace mata su ne suke sakata yiwa mutane rashin kunya. Ta samu dai Mom d’in ta ara mata ko da sati uku ne daga nan ita kuma da ita had’a y’an kud’ad’en hannunta ta sake turawa Umma a san abunyi ta auri Arshaad ko ta halin yaya ne da wurwuri cikin gaggawa! Itafa wallahi yadda ta d’and’ana daular nan to kuwa batajin zata iya minti uku a cikin gidan Baba!…. Tanata sak’e sak’e a ranta a haka suka iso gida! Sai wani nonnok’ewa take yi gudun abunda Mom zata yi mata, amman suna shiga sai taji Mom d’in tace mata “ta tafi d’akinta ta huta Coook zata kawo mata abinci yanzu.” A hankali tace “Na gode Mom” Wani kalan murmushi Mom d’in tayi wanda Jalilan ta kasa ganewa.’Daganan Mom d’in ta juya ta nufi hanyar kitchen a ranta tace “Yarinya kenan! Sarai na san zaki iya yi mana bori, kice ba zaki tafi ba ki tada mana hankali Kuma ko yanzu na san idan akai test a jikinki positive za a gani.. Ki jira nan da kwana uku In sha Allah za ki san wacece Adama.” GANDUN ALBASA Tun da garin Allah ya waye Huda take kuka Idan zaka titsiyeta ka tambayeta ba zata tab’a iya gaya maka menene tak’amemen abinda ya sanya ta kukan ba! Ita dai ta san bata da nutsuwa sannan a mugun tsorace take amman tabbas ba wai shariyar Arshaad kad’ai ne dalilin tashin hankalinta ba. Sakina da Khadija sun yi lallashin sun yi har sun gaji sun rabu da ita. Hankalinta bai sake tashi ba sai da k’awayenta suka zo sannan mai makeup itama ta zo ta fara shiryata! Tayi alk’awarin ba zata sake kiran Arshaad ba amman haka ta daure ta kirashi wannan karan kam a kashe ma taji wayar tashi gaba d’aya dan haka hankalinta ya sake tashi! Ba abunda yafi d’aga mata hankali irin kar azo d’aurin aure yace ya fasa! Ita gara ya fito ya fad’a mata gaskiya akan yayi mata hakan... Nasarawa gra. A b’angaren Arshaad kuwa jiya ya gama shirya plan d’inshi amman ga mamakinshi kamar wani ya gayawa Mammy bayan Magrib nayi ta shigo d’akin nashi ta kafa ta tsare! K’arshema a d’akin a kan couch ta kwana tsabar bala’i. Tun jiyan da ta shigo har yanzu k’arfe 10 bata fita ba! Ko wanka ko brush bata yi ba, har gara ma shi yanata watsa ruwa saboda zazzab’in da yake jikinshi.. Yana lura da ita ko mik’ewa yayi ya shiga shiga toilet zai yi wanka ko alwalla sai taje bakin k’ofar ta lab’e mishi har sai ya fito sai kace wani wanda akace mata zai b’ace! Dagashi har ita ba wanda ya samu bacci jiya Idan ka gansu duk a gigice. Ko da Aaima ta kawo musu breakfast ma ba wanda ya tab’a har yanzunnan Tun jiyan da ta shigo har yanzu ba wanda ya cewa wani uffan a tsakaninsu. Amman duk wani motsinshi idanunta na akanshi. Ba abunda yafi d’aga mishi hankali kuma ya bashi mamaki irin yanda ta kasa tashi ko sallah tayi Yanzu haka yana lura da yadda ta kasa zama mai kyau sai faman mutsu mutsu take yi wanda ya tabbatar fitsari take ji amman gudun kar ta shiga ya gudu ta gwammace ta zauna a haka!. Suna a haka Dad ya shigo cikin d’akin. Yayi mamamkin ganinta a zaune amman sai ya d’auke kai kawai ya maida hankalinshi ga Arshaad, ransa a d’an b’ace yace “Ka san fa k’arfe 11:30pm ne d’aurin auren, uban me kake yi a zaune a haka?” A hankali yace “Ina kwana Dad” “Lafiya” kawai yace masa, daga nan ya nemi waje ya zauna kafin yace “Mik’e maza, yanzun nan Aslam zai kawo maka kayanka” A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya yanayin k’asa k’asa yana kallon Mammy wadda ta d’auke kai tana kallon gefe. Mik’ewa yayi jikinshi ba kwari ya fad’a band’aki! Ya kai kusan 20 minutes tukunna ya fito sanye da bathrobe a d’akin ya tarar da Aslam sanye cikin sky blue d’in rantsattsiyar shadda aikin gaban rigar white da d’an ratsin blue ya murza farar hula mai asalin kyau da tsada sai kyalli take yi da farin takalmi hatta agogon hannunshi white ne. Yana rik’e da babbar rigarshi a hannu wadda take a ninke, k’amshinsa gaba d’aya ya cika ilahirin d’akin…. Suna had’a ido ya sakar mishi murmushi a hankali yace “Ango” Murmushi shima Arshaad d’in yayi sannan ya wuce jikin wardrobe d’inshi ya na mamakin ta yanda zai shirya a gaban waennnan body guards d’in! Inner wears d’inshi ya kwasa ya d’auki jakar kayan da yaga an ajjiye akan gadon ya juya ya wuce toilet. Bai yi minti biyar cikakku ba ya fito! Murmushi Dad yayi yana kallon shi yana mai jin wani sanyi a ranshi! Kana ganinshi kaga Ango.. A hankali jikinshi a mugun sanyaye ya k’arasa gaban mirror ya d’an shafa mai sama sama a hannu da fuskar shi sannan da k’afa, ya fesa perfumes ya d’auko takalmin da ya fito da shi a jakar kayan nashi ya sanya… Farar shadda ce k’all! Mai babbar riga sai bak’in takalmi hula da agogo.. Yana gyara d’aurin agogon suka ji knocking Aslam ne ya juya ya d’an bud’e k’ofar dake a kusanta yake. Da mamaki yake kallon Abba da Daddy da Auwal a bayansu. Dad Abba da Daddy duk ankon shadda ruwan goro light suka yi, aikin rigar ciki da babbar rigarsu kuma na kalar kayan amman dark sosai Sai hulunansu zannah bukar d’in da suka amsa sunansu ZANNAH bukar! Amman kowa da design d’inshi, takalmansu kuma na fata kalar ruwan goro masu mugun kyau da tsada iri d’aya. Yayinda Auwal ke sanye da maroon shadda shima ya murza zannah bukar d’inshi mai asalin kyau da tsada. Cikin girmamawa Aslam ya gaida su Abba Daddy ne yayi dariya yace “Kaga yau har da mu a y’an sneaking a shigo estate ko?” Murmushi kawai Aslam d’in yayi. Kallonshi kawai Abba yake yi… Ya manta when last da ya ganshi da manya kaya, ba k’aramin kyau yayi ba, har ga Allah Aslam ba wai favorite d’in Granpa bane kad’ai Har da shima Aslam ne favorite d’inshi! Kawai dai shi d’in baya nunawa ne Yaron akwai hankali da nutsuwa da sanin ya kamata “Ina ma inama! How i wish......” Ya fad’i hakan a ranshi sai kuma yayi saurin kawar da tunanin ya juya suka fara gaisawa da Dad. Daga shi har Daddy ba wanda ya kalli ko inda Mammy take Kuma sarai sun ganta dan har had’a ido suka yi da Abba! Hakan kuwa ba k’aramin sake ingizata yayi ba Tabbas yau sai ta nuna musu ta isa wallahi! Chap!! Arshaad ya shirya dan haka suma duk suka mik’e dan har an fara jera musu kira Abokanan su sun fara zxuwa venue d’in.. Ba tare da Mammy ta motsa ba tace “Arshaad!” Sai da ya sauk’e ajiyar zuciya ya lumshe idanunsa ya bud’e tukunna ya juyo yace “Na’am Mammy” Mik’ewa tayi tsaye tace “Koma ka zauna” Sannan ta dubi su Dad waenda suke kallonta gaba d’ayansu tace “Kuna iya wucewa ku tafi! D’a dai ni na haifa ko? To wallahi tallahi ba wanda ya isa ya yi mini iko da shi! Da kuka shigo kuka wani banzatar dani kamar baku ga mutum ba saboda ban kai ba har kai Abba! Kalla Auwal shima Aslam ne kawai ya gaidani ya kulani a kaff d’inku saboda ka riga ka nuna musu bani da mutunci bani da daraja a idanunka! To Yanzu ni kuma zan nuna muku na isa dan wallahi ba za a d’aura auren nan ba kaji dai na rantse!” Murmushin takaici Dad yayi kafin yace “Dole ba wanda zai kulaki mana Rukayya! Saboda kema baki kula wanda ya kamata ki kula ba, ko kin gaida ni tunda na shigo?” Ganin ta kauda kanta gefe ya sanya kawai ya girgiza kai kafin yace “Kaga Arshaad wuce mu tafi! Zan ga wanda zai hanaka fita yau” Mammy ya kalla, suna had’a ido tace “In dai kana neman albarka a auren nan to ka sani ba zan tab’a saka maka ita ba! Kuma wallahi Arshaad in dai ka fita a d’akin nan to ban yafe maka ba!” Da k’arfi ya runtse idanuwanshi yana ji kanshi na mugun sara mishi. A zafafe Dad ya yunk’ura zai yi magana da sauri Daddy ya katseshi ta hanyar cewa “Dan Allah dan Annabi ka kyaleta, Uwa ba abar wasa bace ba! Dole Arshaad da Huda suna buk’atar albarka ta Dole.” Yana gama fad’in haka ya juya ga Mammyn yace “Mammy mu tsaya mu fahimci juna, wannan maganar bata tasoba. Ki duba shi kanshi Yaron naki mana za fa ki cutar dashi saboda son zuciyarki sannan da ita kanta Hudan, babufa abu mafi gorantawa a rayuwar y’a mace kamar azo aurenta a fasa!..” Cikin katseshi Mammy tace “Yi mini shiru Yusuf!” Sai da Daddy da Auwal suka d’an zabura jin yanda ta kirashi . Bata damuba taci gaba “Babu maganar sulhu fa a tsakaninmu! Maganace na riga na yita na gama, babu kuma uban wanda ya isa ya sanya ni in chanja wallahi!” Cikin tsiwa da masifa tace “Kuma kar ka wani ce mini In duba rayuwar wata Huda dan babu abunda ya shafeni da ita! Allah Ubangiji yasa a yi ta mata gori a had’a har da kyama da hantara daganan har k’arshen rayuwarta wannan ba damuwa ta bace ba.” A hankali Aslam ya lumshe idanuwanshi. Ba tare da Abba ya kula kowa a cikin su ba kawai ya juya ya fita, da sauri Aslam ya bi bayanshi. Takawa Dad yayi ya tsaya a gabanta sannan yace “Rukayya bani da ishashshen lokaci! Ki nutsu ki shiga hankalinki kiyi abunda ya dace, for the last time ina mai shawartarki ki ajjiye wannan haukar ki bari a d’aurawa Yaron nan aure.” Cikin katseshi ido cikin ido ta kalleshi kafin tace “Yahaya! Ko da ace ka bar nan ka tafi kai kad’ai ba tare da Arshaad ba Wallahi muddin ka d’aura mishi aure da Huda wallahi tallahi billahilazim sai na tsine mishi!” Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauk’e kawai ba tare da yace mata uffan ba ya juya, har ya kai bakin k’ofa sai kuma ya juyo yana kallon Arshaad wanda shima shi d’in yake kallo Wani mugun tausayinshi ne ya lullub’e shi lokaci guda, a hankali yace masa “ka zauna, kar kaje koina bara muje mu dawo .” Yana gama fad’in haka ya juya ya fita, su Daddy ma suka bishi a baya. Abba ko Aslam bai tsaya jira ba ya shiga motarshi suka yi gaba tare da su Shuraim, dama suna ciki anan suka barsu. Aslam na shrin shiga motar shi shima yabi bayan Abba su Dad suka fito “Wuce mu tafi masallacin” Haka kawai Dad yace mishi daganan kowa ya shiga motarshi sukai gaba. Aslam ya dad’e a tsaye so yayi ace ya bi bayan Abba dan ya san definately gida ya koma, saboda yaga yadda ranshi yake a b’ace! Ga shi daman shima so yake ya zille maybe he can use this as an opportunity. Har zai bishi sai kuma kawai ya yanke shawarar bin bayan su Dad d’in. Da kyar ya iya tada motar dan yafi minti goma a ciki a zaune bayan ya shiga d’in, daga k’arshe dai ya tada motar ya fice daga estate d’in….. A hankali yake driving, babu nisa sosai dan haka mintuna k’alilan ne suka kaishi masallacin. Da mamaki yake kallon motar Abba a parke a harabar masallacin! Kokwanto ya hau yi akan anya kuwa motar tashi ce? Sudais da ya gani ya nufo shi ne ya tabbatar mishi da Abban nan ya yo.. Chan kuma ya hango suna gaisawa shi da su Madu cikin tsananin farin ciki da nishad’i. Auwal ne ya dafa shi dan haka yayi saurin juyowa Kwata kwata in banda k’unci da firgici ba abunda ya hango a shimfid’e kan fuskar Auwal d’in! Yana mamakin abunda ya sanyashi a wannan yanayin yaji yace “Aslam dan Allah idan sun zo kace......” “Ku wuce muje mana! Ya naga kun tsaya anan?” Muryar Dad ta katsesu. Kallon Auwal d’in yayi ya kalli Dad sannan yace “Ok” Kawai, ya juya ya yi gaba…. Duk taku d’aya ji yake kamar yana kusanta kanshi da kabarinshine! Tabbas badaban Mommy ta rok’e shi akan ya zauna a garin nan ba to da tuni baya nan! Babu yadda bai yi da ita ba d’azu amman nan ma furr! Ta ki yarda, ta nace ta tilastamishi dole sai da yazo wajen nan! He might look calm but tabbas ya san ba lalle k’afafuwan shi su iya fitar dashi daga masallacin nan ba! Wannan wacce iriyar k’addara ce? Mai yasa yake jin hakan har yanzu? Mai yasa yake jin haka? Garin yaya ya bari hakan take faruwa da shi…..? A hankali yaji Abba yace “Aslam” Firgigit! Haka yayi hankalinshi ya dawo daga duniyar tunanin daya tafi, sai a sannan ne ya ga yana daff da yin karo da bango ashe, da sauri ya ja burki! Sannan ya juyo da kanshi yana kallon Abba wanda yake matsowa daff da shi sosai. A hankali ya kama hannunshi ya d’an jashi gefe.. Da d’an murmushi akan fuskarshi yana mai kallonshi sannan ya fara magana “Watak’il yau in yi maka laifi! Amman dan Allah Aslam ko menene ya faru karka bad’a mini k’asa a ido” Da mamaki yake kallonshi zuciyarshi tana dukan uku uku! Dan a take a yanzun tunani d’aya ne kawai ya fad’o mishi daga jin furucin Abba na yanzun! Da mugun sauri ya fara kokawa da zuciyar shi yana k’ok’arin kawar da tunanin dan jiya ma ba k’aramin artabu ya sha ba! Ko rintsawa bai yi ba ata dalilin false hope d’in da Mommy ta sa ya d’aurawa kanshi. Dafa shi Abba yayi sannan yace “mu shiga” Yana gama fad’in haka ya wuce ciki. Da kyar Aslam ya iya jan k’afafuwan shi, ya shiga ya nemi waje ya zauna kusa da Abba daff da liman da su Daddy Opposite Auwal. Kana ganin Auwal tashi d’aya zaka gane bashi da nutsuwa kwata kwata! Ko zaman kirki ya kasa yi a wajen, sai zaro waya yake da alamun kira yake yi amman kuma ba a d’auka! A fili sannan da k’arfi yace “damn it!!” Sannan yayi jifa da wayar tashi wanda hakan ya janyo hankulan mutane kanshi…. Suna had’a ido da Daddy ya zabga mishi harara. A hankali ya sunkuyar da kanshi ya d’au wayar sannan yace “Sorry”. Hannu Dad ya mik’a mishi alamun ya bashi wayar!. Ba musu ya mik’a mishi shi kuma ya sa hannun ya karb’a ya saka ta a aljihu daga nan aka fara gabatar da d’aurin aure…….. Auwal k’ok’ari yake yi su had’a ido da Aslam sai dai kuma Aslam d’in yak’i d’ago da kanshi kuma kamar ma idanuwanshi a rufe suke. A bangaren Aslam kuwa zai iya cewa ya jima bai shiga irin wannan tashin hankalin a rayuwarshi ba! Mai yasa ya yarda yazo nan? Wanne irin heartbreak zai yi facin? Yanzu kenan a gaban idanunsa yana ji yana gani za ayi komai.... “Inna lillahi wa inna ilaihirrajiun....” Ya furta a hankali sosai! Baya ganin komai zuwa yanzu shiyasa ya runtse idanuwanshi kawai yana jiran lokacin da zai farka ya ganshi a gadon asibiti ko kuma yaji ance mishi Man rabbuka?!….. Yana jin su sama sama Daddy ya gabatar da kanshi a matsayin waliyyin Amarya Dad kuma a matsayin waliyyin Ango! Da k’arfi zuciyarshi ta buga jin limamin yace “Waliyyin Ango yana nemawa Yakubu Aslam auren Maryam Huda!” Bud’e idanuwansa yayi tarr!!! Ya fara ganin komai. Kaii inaa bai ji da kyau ba! Ko kuma dai sunan waliyyin Amarya aka ambata dai ko wani abun daban…. Da sauri ya d’ago jajayen idanuwanshi yana kallon Daddy jin yace “Mun bayar” Limamin kuma yana cewa “sun yarda cinta shanta suturarta komai ya koma hannunsu? Hannun Yakubu Aslam.” Bai gama fita daga shock ba Yaji Dad yace “Mun yarda! Mun karb’a!” Zuwa yanzu gaba d’aya jikin Aslam in banda karkarwa ba abunda yake yi gashi ya had’a wata uwar zufa! Tashi d’aya. Tun daga nan kanshi ya kulle jinsa ya d’auke! Binsu kawai yake yi da ido suna gudanar da d’aurin auren!. Yana kallo Dad ya zaro kud’i ya mik’awa Daddy! Limami ya sanar shedu suka shaida… Jin shi bai tashi dawowa ba sai da muryar limami ta fara tashin amo a cikin masallacin “Alhamdulillah!!! An d’aura auren Yakubu Yahaya Umar Faruku MT Aslam Da Amaryarsa Maryam Yakubu Huda akan sadaki naira dubu d’ari biyu! Lakadan ba ajalan ba. BULAMA ✍️