DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN K’AI. So da Buri Free Book 01. 3 years ago..... A cikin garin kano,a unguwar gandun albasa,cikin wani d’an matsakaicin gida… kana ganin gidan kai tsaye za ka kirashi da na mai k’aramin k’arfi…daga waje k’ofa ce idan ka shigeta zaka biyo ta wani k’aramin soro,a soron akwai k’ofar d’aki mai band’aki a cikinsa kafin ka karaso cikin tsakar gidan wanda babu ko siminti rairayi ne a malale wanda ya ke nan a share dukda yanada d’an girma amman hakan bai hana an share shi tsaf ba! Daga gefe guda akwai d’akuna guda hud’u a jere,daga chan ta wajen k’arshen tsakar gidan kuma akwai bayi wanda aka sakaye shi da k’ofar langa langa duk tayi tsatsa,sai kuma opposite d’inshi kitchen ne da ko k’ofar langa langar ma shi babu amman baka iya hango cikin kitchen d’in saboda duhunsa sakamokon bangon da duk yayi bak’i wuluk ta dalilin girki da itace. Wata y’ar matashiyar budurwa da ba zata gaza shekaru 14 ba ce a tsakar gidan sai uban zufa takeyi,ta yi kneel down ta d’aga hannayenta sama,a kan tafukan hannayen nata kuwa wasu maka makan takalman ball ne d’aya a kowanne hannu… D’an motsi ta yi wanda hakan ya sanya takalmin dake kan hannun hagun ta ya kusan fad’uwa,tsabar yadda duk ta rikice ta fita a hayyacin ta ga rana ga tsoron bulala ne ya sanya ba ta san lokacin da ta yar da na hannun daman nata tai saurin rik’e na hannun hagun nata ba… ai kuwa bata k’arasa rik’ewa ba ya d’aga zabgegiyar bulalar dake rik’e a hannunsa ya zabga mata a kan hannayen nata,hakan yasanya ta k’arasa zubar da takalmin itama ta zub’e a nan k’asan saboda ba kad’an ba dukan ya shigeta. Kamar jira yake yi kuwa ya rufeta ta duka! Babu ji babu gani… ihu takeyi sosai tana kwala kiran “Mama!, mama!!,mama!!!” Mama da ke a d’aki,wadda tun farawar abun take jin su, ta runtse idanunta hawaye na gangaro mata tana adduan Allah ya kawo wanda zai ceci y’ar tata. Kamar daga sama ya ji an fizge bulalar,juyowa yayi a fusace zai yi masifa suka had’a ido da wani kyakkyawan saurayi!mai manyan idanuwa..yanada cikar gashin kai da na gira da dogon hanci sannan bakinsa bai cika girma ba…skin colour d’insa chocolate ne me d’an haske da shek’i,dan ko kad’an ba za ka kira sa da Bak’i ba..... cikin b’acin rai Junaidu yake kallon yayan nasa wanda suke mugun kama da juna bambancin kawai Junaidun ya fi yayan nasa kyau da manyan idanuwa da haske,sannan lips d’insa bai yi duhu ba kamar na yayan nasa da suka yi bak’ik’irin instead nasa shi light pink ne….. tun cikin bacci yake jin hayaniyarsa a tsakar gida sama sama har ya kaiga farkawa ya watstsake yafara jiyosu sosai. Kallon kwayar idanunsa Junaidun yayi…a zuciye ya yar da bulalar a k’asa kafin ya doka wani uban tsaki sannan yace”yanzu fisabillillahi ya Ja’afar abinda kake yi ya dace kenan??idan za ka hukunta Yarinyar nan ka dinga hukunta ta a lokutan da kake cikin haiyyacinka mana!!! kalla fa idanunka! ka je ka yi high!!kawai ka zo sai jubgar y’ar mutane ka ke yi so kake ka illatata?? kuma zan iya dafa Qur’ani akan cewa ba wani laifin kirki ta yi maka ba…a kan laifin da bai taka kara ya karya ba ka zo kanata dukanta haka! me ta yi maka??” Ya yi masa tambayar still yana tsare shi da manyan idanuwansa. Mitsi misi ya Ja’afar d’in yayi da idanuwansa da suka yi jazir sannan ya yi baya kad’an ya d’an yi tangal tangal kamar zai fad’i sai kuma ya dawo daf da Junaidun ya tsaya ya zuba hannayensa cikin aljihun wandonsa sannan ya zuba masa idanuwa kafin yace “Kai,dan uwarka ni sa’anka ne?” Shiru Junaidun ya yi yana kallon shi kafin a hankali ya d’an sassauta murya yace “yi hak’uri,mai tai maka??” Tsaki ya Ja’afar d’in ya yi sannan yace “Akan gyaran d’akin da suke yi mini it da Jalila ne,Jalila ta yi mini bayanin ta ta wuce, Ita wannan makirar sai ta tsaya shara wai Umma ce ta sakata sharar tsakar gida, abun haushin da na shiga d’akin nawa fa ko tsinke ba’a d’aga ba komai yana nan a yadda na barshi…” shiru Junaidu yayi don in dai zai iya tunawa to jiya da shekaran jiya duk ya ganta tana gyaran d’akin ya Ja’afar,kuma a ka’idarsa shi ya Ja’afar d’in kwana bibbiyu sukeyi itada jalilan…to ya za a yi kuma yau ma yace still itace zatai mishi gyaran d’aki… Juyawa yai yana kallon hanyar d’akunan gidan kmr yana neman wani abun kafin da k’arfi ya fara kwala kiran “Jalila!Jalila!!Jalila!!!” Ya jafar ne ya d’an tab’o hannunsa sannan yace masa “kai ta tafi jarabawa fa” juyawa Junaidu ya yi ya kalle sa kafin yace “ya Ja’afar yau a ka’ida waye zai yi maka gyaran d’aki???” shiru yayi kafin cikin maganarsa ta y’an shaye shaye yace “Kagane ko! a k’a’ida Jalila ce,to ita wannan makirar sharar da ta yi jiya da shekaran jiya duk basu fita ba kai gyaran ma kwata kwata bai yi ba shiyasa yau sai d’akin yayi kmr ba a tab’a gyarawa ba sannan Jalila jarabawa ta tafi,shine na shigo na ganta tana shara kuma Jalila ta sameni a waje ta ce mini ta rok’eta ta gyara d’akin ita ta makara amman ta zazzageta har da marin ta fa tayi!!! ita dan uwarta a gidan ubanta ba a alfarma ne eh? Shine fa na shigo na sameta tana kwashe shara,ni kuma na d’auki alwashin sassama mata kamanni a yau d’innan tunda ta raina ni,ai ba Jalila ta zaga ba ni ta zaga tunda d’akina ne,kai marin ma ni ta mara tunda ai dai duk akan d’aki na ne” Junaidu da ya fara fahimta makirci ne kawai Umma da Jalila suka had’a saboda sunga an kwana biyu ba a jibgi baiwar Allah n ba,sannan su Baba ya hana su dukanta shine suka biyo ta hannun ya Ja’afar tunda sunga shi in dai ya bugu to ba iya gane gaskiya da k’arya yake yiba sannan ko baya ga hakama daman chan shi ya tsani Yarinyar…. Sunkuyawar da ya ga ya Ja’afar nayi yana k’ok’arin sake d’auko bulalar ne ya dawo dashi daga nazarin daya tafi,da sauri ya rik’e hannun ya Ja’afar ya shiga lallab’asa akan ya yi hak’uri ya barta za a gyara masa d’akin nasa,amman fur ya k’i hak’ura… k’arshe dai naira ashirin Junaidu ya d’auko daga aljihu ya basa tukunna ya hak’ura ya karb’a yana murmushi yace ta bar gyaran d’akin ma gobe sai ta yi,idan kuma Jalila bata da jarabawa goben sai ta bari jibi ta karb’i aikinta. Juyawa ya Ja’afar ya yi yai hanyar fita daga gidan shikuma Junaidu ya juyo yana kallonta anan a durk’ushe tana kuka tana ajiyar zuciya ta kifa kanta a k’asa…. A hankali ya sunkoyo kanta,kafad’unta ya kama duka biyu ya juyo da ita sannan ya sa hannunsa a hab’arta ya d’ago fuskarta. Da sauri ta runtse idanuwanta da suka yi luhu luhu fuskarnan tayi jawur tsabar kukan dataci..shiruu ya yi yana kallon ta..tun daga kan lafiyayyan gashin gaban goshinta wanda suka kwanta sukai lub lub akan farar fatar ta,zuwa kan gashin girarta masu kyau da shape kamar ta yi cavn da madaidaitan idanuwanta, zuwa kan dogon hancinta wanda yai kmr M daga k’arshe amman ba sosaiba da dan mitsitsin bakinta…. Cikin seconds d’in da ba su fi uku ba ya yi mata wannan kallon..a hankali ya sauk’e ajiyar zuciya kafin ya kira sunanta“HUDAN”saurin bud’e idanunta tayi ta kallesa! kamar kuma wadda ta tuna wani abun sai ta yi saurin ture hannunsa daga jikinta ta tashi da gudu tai hanyar d’akin Mama. Shiru ya d’an yi,chan kuma a hankali ya mik’e tsaye, ya juya da niyyar komawa d’akinsa. Juyowar da zai yi ya ga Umma a tsaye tana kallonsa sai kuma Anty zainab wadda ke tsaye a chan bakin k’ofar gidan tana d’an lek’a waje da alama bayan Ja’afar wanda ya fita yanzun ta ke bi da kallo.Daga gani ka san basu dad’e da shigowa cikin gidan ba dan ga lullub’i a kanta da kuma jaka a hannunta,itama anty zainab dake bak’in k’ofa haka amman tabbas ta gansa tare da Huda dan gashi ranta a mugun b’ace yake! Cikin in inar da bai san yana da ita ba yace “um um umma dddagaa ina ku ke?” K’arasowa ta yi gaban sa ta tsaya sannan cikin b’acin rai tace”daga gidan ubanka nake!!….”. Shiru ya yi ya sunkuyar da kansa yana sauraronta tana fad’a baki da kumfa,Anty Zainab da ta k’arasa shigowa yanzun tana tayata , Umma ce tace”wato da ka d’auka ba yanzu zan dawoba ko?shine kaje harda wani d’ago ta kana kallon ta,idan za ta had’iyi zuciya ta mutu Junaidu ina ruwanka da damuwarta?? Ka ga ta inda Ja’afar ya fi ka ko?Yaron nan ko kyalle ne indai nace banaso to kuwa shima ba zai so shiba,anya ni na haifeka kuwa?a ce Yaro kwata kwata baya kishin uwarsa!!anbi an lashe ka an shanye ka to wallahi ba’a isa ba,ni naci uwar boka ma ballantana malami…ka ci gaba da b’ata mini rai har sai ka ja nai maka baki tunda baka jin magana ta dudda dai na san ba yin kanka baneba.” Anty Zainab itama tace “ke kuwa Yarinya ta yo gadon munafurci ai ba zai tab’a ganin laifin taba,mu mun buga da wadda ta haifo ta ma ta hak’ura ta barmu,ballantana ita…..” Ta inda suke shiga ba ta nan suke fita ba hakanan suka yi ta habaici a tsakar gidan babu wanda yace musu ci kanku sukayi suka gama suka shige d’akin Umma suna huci,anan d’in ma maganar sukaitayi,da suka gaji Umma ta bawa anty zainab sak’onta ta mik’e tai mata sallama ta fito ta tafi,har ta fita a gidan mamakin Junaidu takeyi…ba irin yadda ba su yi ba akan ya fita harkar Yarinyar tun bata kai haka ba amman a banza Ajiyar zuciya ta sauk’e a ranta tana adduar Allah yasa Junaidu dai ba gadon wahala ya yo daga wajen ubansa ba . Chan d’akin Mama kuwa Hudan ce kwance akan gado ta d’aura kanta a kan cinyar Mama tanata kuka,Mama bata hanata yin kukan taba sai da taji ta d’an sassauta kukan nata tukunna a hankali ta shafa kanta tace”Huda ba na hanaki shiga harkar Junaidu ba?? Dukda a cikin y’an gidan nan shi kad’ai ne baya zaluntarki yake kuma kare ki amman na san kin san cewa banason alak’ar ku ko? Yanzu duba ki ga irin zagin da kika ja mini da ke kanki”. Shiru Hudan tayi da kukan da takeyi kafin ta dago kanta ta share hawayenta ta kalli mama sannan a hankali cikin sanyi tace”Maamaa ni fa ban kula shi ba Allah,kawai dai ya karb’e bulalar da Ya Ja’afar yake duka nane ya bashi hak’uri amman ni bance masa komaiba.” Shiru Mama tayi tana kallon y’ar tata kafin tace”to ke Huda mai yasa da Jalila tace ki gyara mishi d’aki kika k’i kika hau shara??” Raurau Hudan ta yi da idonta kafin tace “Mama jalila k’arya ta yi mini, daman jiya akan ya Junaidu ya hanani wanke mata uniform d’in makarantar ta tace mini wallahi sai ta saka ya Ja’afar ya zaneni, wai tunda na shiga tsakaninta da d’ayan yayan nata bara sai ta sa d’ayan ya zaneni.” Shiru kawai Mama tayi tana tunani….ko ba a fad’a ba daga yanayin fuskarta ka san ranta a b’ace yake. Gaskiya ita dai hak’urin ta ya kusan k’arewa,taya still za a mayar mata Yarinya kamar wata jaka,dan ma ta samu sauk’i tun lokacin… ………. Da ta je wajen Kaka (Baba Bashir) ta kai masa k’orafi akan su Umman da jalilan. Ran kaka ya yi mugun b’aci a lokacin hakan yasa ya kira Baba ya ja masa kunne akan yayi musu gargad’i mai zafi dan in har ya sake jin ko da marin Hudan ne anyi a tsakanin Umma ko Jalila to bai yafe masa ba. Baba ya shiga rud’u a wannan lokacin domin kuwa a duniyar nan idan akwai abunda yake jin tsoro to shine b’acin ran Umma amman kuma yanzu ga abunda mahaifin sa ya fad’a wanda ko hauka yakeyi ba zai bari Allah ya isan iyaye ta hau kansa ba,hakan yasa yana dawowa gida ya rufe ido ya tara su a d’akinsa ya cewa Umma da Jalila “kar su k’ara dukan Huda,sannan kar a sake d’aura mata talla,wankinsu su dunga yi da kansu ko sukai gidan wankau,sannan wanke wanke da wankin band’aki tsakanin Huda da Jalila duk ranar da mamanka keda girki kai ne zaka yi,indai har kuwa aka k’etare abunda ya fad’a to a bakin auren Umma Abunda kawai ya yarda aikin Huda ne parmanent shine sharar tsakar gida domin ita Jalila nazuwa makaranta.” Umma a wannan lokacin kusan daskarewa ta yi tsabar mamaki..mutumin da ko maida mata magana baya iya yi shine yau harda ik’irarin cewa ‘a bakin aurenta!!’ Tabbas da sake, kasa yin shiru tayi dan haka ta yi gyaran murya sannan tace “Alhaji ka bani mamaki matuk’a amman ba zan yi jainja da kai ba a gaban Yara,abu d’aya wanda na sani shine kana dab da b’ata tarbiyar Yarinyar nan kai da uwarta dan ba zai yiu ace kab gida Yaro babu mai kwab’arsa ba,ga yayunta nan maza amman an nuna mini iyakata,Alhaji ance babu mu ba Huda ko? Saboda ita shafaffiya da mai ce? ni za ka yiwa haka akan wad’annan mutanen???” Ta yi maganar tana dukan k’irji da kafe Baba da manyan idanunta waenda yake hango tsantsar b’acin rai a cikinsu. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 02 Shiru Baba yayi yana tunanin ta hanyar da zai bi ya d’an kwantar ma da Umma hankali…chan ya yunk’ura yai gyaran murya kafin yace “Sadiya ni bance harda yayunta maza ba,dokar iyaka kanki ne ke da Jalila shima kuma saboda Kaka yayi mini kashedi mai zafi shiyasa, ko kina so Allah ya isan shi ta hau kaina?? yayunta maza sunada ikon hukuntata indai ta yi laifi kuma ai....” “Aikin banza ma kenan!!!”tsawar Umma ta katse shi Kafin ta ci gaba da cewa”ai kaga wannan matar” ta yi maganar tana nuna Mama wadda tunda aka fara maganar bata ce uffan ba. Cikin huci ta d’aura da cewa”tabbas in dai baka taka mata burki ba tunda ta samu Kaka yana goya mata baya zata sake komawa wajen shi ta kai k’arar su Junaidun suma..tunda naga kamar ma tsoronta kafara ji.” Ta k’arashe maganar tana huci. Shiru Baba yayi kafin ya d’ago kanshi ya kalli Mama “MARYAM” ya kira sunanta cikin kakkausar murya.D’agowa Mama ta yi ta kalleshi kafin a hankali tace “naam” Nisawa yayi sannan ya ce “kin kai k’arata wajen mahaifina,an yi miki abunda kike so ko? To nima ga nawa sharad’in, Indai Huda ta yi laifi kika hana su Ja’afar hukuntata kema a bakin aurenki,don kamar yadda Sadiya ta fad’a ba zai yiu ace Yaro babu mai kwab’arshi a gida ba, Ita dai da Jalila ga sunan sun bar miki y’ar ki.” Yana gama fad’in haka ya d’ora da cewa “Shikenan kowa zai iya tafiya na riga na gama magana.” Ahaka aka tashi kowa yai d’akinsu . Umma sam ba haka ta so ba,dan ta san daman auren Baba ba wani d’ad’a Mama yayi da k’asa ba,kawai dai saboda Hudan yasanya take hak’uri take zaman gidan. Hakanan ranta babu dad’i suka k’arasa d’aki tanata k’ulla ta inda zata b’ullo wa alamarin a ranta. Mama atunaninta sauk’i zai zowa y’artata sai dai sam abun ba haka yakasance ba domin kusun kullum sai ansan sharrin da aka had’a mata an saka Ja’afar yai mata shegen duka,sannan sharar tsakar gidan da aka ce shine aikinta kullum,tofa a rana sai Umma ta sakata ta yishi sau uku ko fiye da haka duk kuwa da girman shi,da gangan Jalila za ta jefar da abunda bai taka kara ya karya ba ace sai ta share duka ai daman yayi datti. Sauk’i d’aya zuwa biyu ta samu shine na talla da wankin su,amman ko wankin band’aki ranar na Jalila kwara ruwa kawai takeyi kusan ita ce za’ace take wanke band’akin duk ranar yinta....... ………………. K’arar buga k’auren ne ya dawo da Mama daga duniyar tunanin da ta tafi K’arar bata gama barin dodon kunnenta ba ta ji an shigo gidan ana wak’a,ko ba a fad’a mata ba ta san Jalila ce. Huda Mama ta juya ta kalla tace “kikace bata ce miki ki gyara d’akin yayanku ba ko?” Kai Hudan ta d’aga mata alamar ‘eh’ Mik’ewa Maman tayi ta juyo ta kalli Hudan tace mata “zauna kar ki fito” daga haka ta yi waje. wata budurwa ce take K’arasowa tsakar gidan…ba za’a kirata da bak’a ba sannan kuma ba fara bace fat!!shekarunta ba za su wuce goma sha shidda ba,tanada manyan idanuwa da d’an matsakaicin hanci sannan bakinta ba k’arami bane ba kuma k’atoto bane ba yayi dai dai da yanayin fuskarta kallo d’aya za ka yi mata ka kirata da kyakkyawa sannan yanayin shigarta zai tabbatar maka da irin y’an matan nanne marasa kunya…tana tafe tana wak’a had’i da taunar cingum wanda hakan yabawa gefen kumatunta damar lotsawa. Uniform d’in jikinta koren wando ne da farar riga da farin hijabi wanda hakan ke nuni da makarantar da take zuwa ta gwamnati ce…da alama tanada wani muk’amin a makarantar tasu domin d’an kwalin kanta yellow ne ba Fari ba ba kuma kore ba,ta zaro shi daga cikin hijabin nata tayi daurin ture kaga tsiya ta saman hijabin….daga makaranta take amman ta rambada uban jan jambaki,sannan ga idon nan yasha kwalli ya sake fitowa rambad’au!!!! tubarkalla,y’ar k’aramar jakarta da ba za ta ci littafi biyu ba na sakale a gefen hannun damanta. Ido suka had’a da Mama wadda ta gama fitowa daga d’akinta yanzun hakan yasa ta jan wani dogon tsaki had’i da tofar da cingum d’in bakinta kafin tace”Ni fa na tsani kallo.” Sannan ta yi hanyar shiga d’akin Ummansu. “dakata Jalila, magana za mu yi dake” Mama ta fad’i hakan tana k’ok’arin K’arasowa inda take. Juyowa ta yi ta zuba mata ido ta gyara tsayuwarta tare da nad’e hannuwanta akan k’irjinta irin ina jinki d’innan. Kallon ta Mama ta yi sannan tace”yanzu Jalila saboda Allah dukan da kike sakawa yayanku Ja’afar yana yiwa y’ar uwarki ba tare da hakkinta ba kina ganin ya dace kenan? Ke kenan kullum ba za ki ja k’anwarki a jiki ku zauna lafiya ba? Ki duba fa saboda Atule d’in fa da kike sakawa Yara suna yi mata kullum hakan ya sanya dole Babanku ya chanza mata islamiyya aka maida ita ta dare da asabar da lahadi na safe. Yarinyar da ta taso da k’aunarki acikin ranta kina k’ok’arin maida mata rayuwa kurkuku?Meyasa kike hakane Jalila?mai ya faru kika chanja?” Umma ce ta hankad’o labule ta fito daga dakinta cikin masifa tace “Kawai kinga munafuka ki fito fili b’aro b’aro kice tunda na dawo gidan nan na chanjata,akan wanne dalilin za ki tasa mini y’a a gaba kina wani cewa ta chanza hali? To bari kiji in gaya miki Allah ne ya tsameta a cikin munafukai ya dawo da ita cikin masu gaskiya,kuna abu simi sumi da ke da y’arki nankuwa kunfi kowa iya munafurci da cin dunduniyar mutum!.” Juyawa Mama ta yi ta kalli Jalila wadda ta ga ta yi shiru tana kallon gefe kamar bata wajen,a tunanin Mama nutsuwa ce ta zowa Jalilan, Juyawa tayi ta kalli Umma wadda har yanzu take fad’a baki da kumfa tace mata “kinga Sadiya ba dake nake ba, ya Ina shirin shirya tsakanin Yara ke kuma kina k’ok’arin kiga kin b’ata?ki daina shiga fad’an y’an uwa fa dan wataran za ki ji kuny.....” “In sha Allah ke ce za ki ji kunya ba dai Ummana ba!” maganar Jalila ta katse ta, “kuma da kike ta cewa wani wai y’an uwa da ni da Huda shin wai Ubanta ne d’an uwan Baba? ko kuwa ke uwarta ce y’ar uwar Umma???” Shiru Mama ta yi tana kallon Yarinyar da ta rena ta goya a bayanta ta ci kashinta taci fitsarinta tana rera mata rashin kunya. Cikin son fahimtar da ita Maman tace “Jalila ai ko babu y’an uwantaka ke kin san Hudan k’anwarki ce.” “Chan ki je ki nemo y’an uwanta wallahi ba dai ni ba.” Jalila ta fad’a cikin d’aga mata Hannu kafin ta d’aura da cewa”kiganni nan kaf y’an uwana na dangin Ummana da Babana suna da nasabarsu kuma suna amsa sunan iyayen su!…da za ki ce wani Ummana za ta ji kunya dan kawai ke kinji kunya shine za ki so kowa ma ya ji?kinje kin Haifo shegiya kin kawo ta cikin gidanmu still za ki yi ta lak’aba mini ita kina wani y’ar uwartace ita? Idan ba tsoroba ki nuna ubanta mana ki kaita wajenshi Yarinyar da ko sunanta Babanta ba ya so yaj.....” Jalila bataga k’arasowar Mama daff da ita ba sai kawai wani haske da ta gani sakamokon marin da Mama ta d’auke ta da shi,ai kuwa batai wata wata ba itama ta d’aga hannunta za ta mari Mama. Ji ta yi an rik’e hannun hakan ya sanya da sauri ta juyo,nan suka had’a ido da Junaidu ya had’e rai. Matse hannun nata yai da k’arfi sai da tayi k’ara sannan yace mata “baki da hankali Mama za ki mara?” Nan Umma daga bakin d’akinta toyo wata super tayi kan Junaidu ta rufe shi da duka tana cewa”saketa ta rama ka saketa nace!!” duk irin dukan da Umma take yiwa Junaidu hakan bai saka ya saki hannun Jalila da taketa tsalle tana k’ok’arin fizge hannunta ba tana kallon Mama tana”Ya Junaidu ka cika mini hannu in rama Allah yau Mama kin tab’o tsuliyar dodo,idan sama da k’asa za ta had’e sai na rama!!” duk ta birkice ta tada k’ura tana k’ok’arin fizge hannunta a cikin na Junaidun. Junaidu da ya ga dambe ma take shirin yi da shi ne yasa ya fizgo ta ya juyo da ita ya d’auke ta da wani irin gigitaccen mari yace “ke ki nutsu!” ya daka mata tsawa,ganin haka yasa Umma tayi kan Mama ta d’aga hannu zata mareta Mama tai saurin rik’e hannun ai kuwa gida ya kacame Umma kawai k’ok’arin ta ta mari Mama ta yi dambe da ita ita kuwa ta k’i bata daman yin hakan ta dai rik’e mata hannu shi kuma Junaidu yana gefe yana fama da Jalila. “kai!kaii!!kaiii!!!!,lafiyarku kuwa?” sukaji muryar Baba wanda ya gama parking machine d’in sa a soro yana k’arasowa cikin gidan da d’an sauri ga leda a hannunshi da alama yanzu dawowarsa kenan. Umma ce ta saki hannun Mama cikin fushi tace”Alhaji gara da Allah ya dawo da kai yanzu,dan yau za ayita ta k’are a cikin gidan nan,matar nan ta kwashi k’afa ta kai k’arar mu gurin kaka,kaka ya goya mata baya an hanamu ni da Jalila ko kallon banza mu yiwa Huda,shine yanzu ni ta d’aga hannu ta zabgawa Jalila mari saboda Allah duba fuskar Yarinyar nan.” Ta finciko Jalila daga gaban Junaidu da ya sake mata hannu ta hankad’ata wajen da Baba yake tsaye,aikuwa kamar jira take ta fashe mishi da kuka,lallashinta Baba ya shiga yi cikin rawar jiki kafin a fusace ya d’ago ya hau Mama da fad’a,Umma ce ta katseshi ta hanyar cewa “Ai matar nan ta raina ka,tun ranar da ka hanamu shiga harkar Huda a cikin gidan nan muka daina bi takanta,amman ita da ka ce in an hukunta Hudan kar ta yi magana shine saboda tsananin raini yau tun safe bata barmu mun sha ruwa ba a cikin gidan nan,saboda an tab’a y’ar gwal kalla yadda ta mari Jalila saboda Allah.” Junaidu ne ya kalli Baba sannan ya juyo yana kallonta yace “Umma ba fa hakane ya faru ba,yau tun safe Ina cikin gidan nan babu inda naje,a idona aka yi komai, ita Jalila ce bat...” Tsawar da Umma ta daka masa ne ta sanya shi yin shiru “Junaidu!! Bar nan”ta nuna mishi hanyar fita da yatsarta manuniya,baki ya bud’e zai yi magana ta sake daka mishi tsawa tace “bar nan nace!!” sum sum haka ya juya ya fita ba yadda ya iya. Juyowa ta yi ta kalli Baba tace “Alhaji a bi mana hakkinmu.” Shiru ya yi yana kallon Mama wadda ta yi k’asa da kanta, ...Harga Allah yana son Mama, babu abinda ya chanza daga soyayyar da yake yi mata tun suna Yara amman idan ya tuna da yadda ta yi fatali da soyayyarshi saboda waninshi sai yaji wani haushin ta yana shiga masa rai yadunga jin babu abinda yakeda Buri sama da ya cusguna mata itama ta d’and’ana ta ji ya zafin cusgunawan yake... Umma ce ta katse masa nazari ta hanyar cewa “Alhaji muna sauraronka.” Takawa yayi inda Mama take ya tsaya,yai mata nuni da yatsunshi guda biyu sannan ya fara magana “Maryama a cikin zab’i guda biyu da zan baki yanzu ki d’auki d’aya…. na farko ko ki tsaya Yarinyar nan ta rama marin da ki ka yi mata na biyu ko kuma ki bata hakuri tare da alk’awarin ba za ki k’ara ba, kuma muddin kika k’ara to tabbas a bakin zaman Huda a cikin gidan nan!.” a razane Mama ta d’ago kai tana kallon shi da idanuwanta da suka kawo kwalla…tausayinta ne ya kama shi tashi d’aya yaji zuciyarsa tana neman yi mishi gardama dan haka cikin sauri ya juya ya daina kallonta yana me cewa “zab’i ya rage naki.” Jalila da Umma kuwa zuciyoyinsu sun yi fess sai faman murmushi sukeyi,Jalila har da tattare hijabinta ta yi gaba d’aya ta jefa shi baya ta wajen wuyanta tana hurawa hannun damanta iska ta matso daff da Mama… ganin da Mama tayi Jalila na neman kifa mata mari, ne ,ya sanya ta yi saurin runtse idanunta tace “Jalila na mareki tsautsayi ne ki yi hak’uri na yi alk’awarin ba zan sake ba!.” Da sauri kafin su Jalila su ce wani abun Baba yai saurin cewa “barka to!! kin shafama kanki lafiya,wuce ki tafi d’akinki.” Jalila kuwa ta b’ata rai za tai magana Umma ta yi saurin rik’o hannunta tai mata alamun ta yi shiru kafin ta juya ta kalli Baba tace “Alhaji mun gode da adalci” Daga haka ta ja hannun Jalila suka yi d’aki. Suna k’arasa shiga d’akin Jalila ta wafce hannunta a cikin na Umma sannan tace “haba Umma!!mai yasa kika hanani yin magana?”gashi yanzu ban rama marina ba,harfa Ya Junaidu sai da shima ya mareni,kuma abun haushin ni Baba ya hanani dukan Hudan da a kanta zan huce,ni dai gaskiya da kawai kin barni nace ban hak’ura ba na rama marina! yanzu Ina kikeso in kai wannan d’acin da zuciyata take yi mini??” Ta yi maganar tana mai zama da dukkan k’arfinta a kan y’ar kujerar su two seater da take ita d’aya a d’akin duk ta yayyage. Murmushi Umma ta yi kafin ta zo ta gabanta a hankali ta d’aura dukka hannayenta akan kafad’arta sannan ta durk’usa a gabanta tare da sauk’e ajiyar zuciya kafin tace “ta Yaro kyau takeyi bata kwari, ai Jalila ko da ace ta zab’i ki rama marin nan da ta yi miki to fa da ni da kaina ba zan bariba,saboda zab’i na biyun nan da Alhaji ya fad’o shi ji na yi kamar an tsunduma ni a cikin aljanna” Shiru Jalilan ta yi tana kallon Umma sak’ak’e alamun tana buk’atar k’arin bayani, fahimtar hakan da Umma tayine yasata sauk’e numfashi sannan tace “menene babban burinmu a yanzu??” Shiru ta yi na y’an sakanni sannan tace “in auri mai kud’i kuma mu ga bayan Mama da Huda” Murmushi Umman ta yi kafin tace “yanzu idan Hudan ta bar gidan nan tanada wajen zuwa? Girgizama Umman nata kai tayi kafin Umman ta sake cewa “wane hali kike tunanin Maryam za ta shiga?”Babu b’ata lokaci Jalila tace”tashin hankali”sannan ta kyalkyale da dariya sai da tayi mai isarta tukunna tace “Umma idan na fahimceki so kike in sake yi mata abunda zai b’ata mata rai har ta kai ga sake mari ko dukana” “Abinda nakeso kenan” Umma ta fad’a tana murmushin jin dad’i mai had’i da dariya kafin ta mike tsaye tana kallon k’ofa kamar mai tunanin wani abun tace “Jalila ki tuna ata dalilin matarnan na bar gidan nan na rabu dake naje nai rayuwar wahala, itakuma ta dinga gallaza miki azaba ki tuna da cewa bakiji dad’in tashi a gaban uwa ba kamar ko wacce y’a ki tuna yadda ta ci amanata ta aure mini miji, ki tuna! ki tuna!! ki tuna!! dayawan abubuwan da ta yiyyi mana.” Murmushi Jalila ta yi sannan tace”Ummana kar ki damu, zan tattaro gaba d’ayan abunda na san bataso in yi ta zuba mata har sai ta kai ga tab’a ni,kuma na riga na gano abinda yafi b’ata mata rai shegiyar y’artan nan ce bataso akira da shegiya ni kuwa yanzu na fara….” Zuciyar Umma fess ta dawo ta zauna kusa da Jalila sukaci gaba da k’ulla yadda za su k’untatawa Mama….. A chan d’akin Mama kuwa tana shiga ta saki kukan da take ta k’ok’arin rik’ewa,da sauri Hudan ta taso ta zo ta rungumeta itama kawai sai ta fashe da kuka kowa ya kasa lallashin d’an uwanshi,sai da sukayi mai isarsu tukunna Mama ta d’ago da fuskar Hudan tace mata “mai ya saki kuka?” Shiru tayi kafin tace “Mama gani nai kina kuka kuma naji abinda ya faru a tsakar gida” Sharemata ragowan hawayen nata tayi kafin tace “bakomai ki kwantar da hankalinki”sannan ta mik’e tayi kan gado ta kwanta ta lumshe idanunta….ganin hakan ne yasa itama Hudan ta mik’e taje ta kwanta a kusa da ita tana sauk’e ajiyar zuciya kafin bacci ya yi awon gaba da ita…. SHARE PLS. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 03 A hankali Mama ta bud’e idanunta da suka d’an kumbura ta juyo tana kallon fuskar Hudan kafin ta kai hannun a hankali ta shafa kumatunta tausayinta yana sake shigar mata zuciya. Nasarawa GRA, Kano. Wani dogon dattijo ne ke tsallako titin da sauri had’e da d’an gudunshi,hannunsa na dama rik’e da agwaluma guda uku a cikin farar leda,na hagun kuma yana amfani da shi wajen mayar da y’an chanjin sa cikin aljihun gabar rigarsa,da alama agwalumar ya tsallaka siyowa. K’ara saurin gudun nasa yayi sakamokon ganin har motocin da ya hango sun iso bakin mahaukacin gate d’in makeken estate d’in. Da saurinsa ya zaro wani d’an k’aramin makulli a cikin aljihun gefen wandonsa ya isa gaban wata had’add’iyar k’ofa wadda ke a ta gefen makeken gate d’in wadda colour d’inta da design d’in exactly irin na gate d’in ne, cikin sauri ya zura mukullin a ramin mukulli sannan ya murza k’ofar ta bud’u ya tura da sauri ya shiga har yana tuntub’e, shigarsa ke da wuya waennan motocin da ke jiransa a ta wajen gate d’in suka fara danna masa horn babu k’akk’autawa…tashi d’aya duk ya bi ya rikice hakan yasa ya yi sauri ya fad’a d’akinsa na mai gadi ya d’aga k’asan pillow ya d’auko mukullin babban gate d’in ya fito yanata sauri ya k’araso jikin gate d’in ta baya ya bud’e padlock d’in sannan ya bud’e wani lock kafin ya durk’usa k’asa ya zare wata makekiyar sakata tukunna ya mik’e ya fara k’ok’arin tura gate d’in jikinsa duk yana rawa kana ganinsa ka san a rikice yake gashi an k’ara rikita shi da uban horn d’in da ake ta maka masa babu k’akk’autawa… , Bai kai ga k’arasa tura gate d’in ya bud’u duka ba motar farko k’irar benz G wagon Bak’a wuluk! ta danno kai da mugun gudu ta biyun na binta a baya, ba don ya yi hanzarin barin wajen ba da babu abunda zai hana gilashin motar tafiya da y’ar sharar jikinsa. Ganin motocin sun shige ne yasanya shi K’arasowa bakin gate d’in ya fara turawa domin rufewa, da kyar yake iya turawa saboda tsabar girma da nauyi. Wani gate d’in motocin suka nufa a cikin jerin gidajen estate d’in da a kalla sun kai 15 kuma gaba d’aya ginin gidajen yanayin tsarin 3D ne masu hawa biyu,tsayuwa fad’an haduwar ginin gidajen b’ata lokaci ne. Wani kakkauran mutumi ne zaune a bakin gate d’in da suka nufa,sanye cikin uniform d’in sojoji,da alama shi ke gadin wannan particular gate d’in, mik’ewa ya yi sakamokon hango motocin sannan ya shiga ta k’aramar k’ofa ya bud’e musu gate d’in wanda hakan ya bawa farfajiyar gidan damar baiyyana..mahaukacin makeken mansion ne yanayin tsarin ginin 3D shima… Ma sha Allah aljannar duniya kenan domin kuwa ya had’u har ya gaji da had’uwa da tsaruwa ga kyau ga girma duk ya had’a. Wajen da aka tanada domin ajijiye motoci suka nufa sannan suka yi parking. Wani mutum ne ya bud’e motar farko,ta wajen mazaunin driver ya fito ya zagayo ta wajen owners corner da d’an saurin shi ya bud’e murfin motar ya koma gefe ya tsaya . ....K’afarshi ta dama wadda ke sanye cikin had’add’en black d’in covershoe mai tsananin tsada ya fara zurowa waje, kafin ya sauk’o da d’ayar sannan ya mik’o ya fito gaba d’ayansa, ba matashi bane ba ko magidanci ko kuma dattijon Alhaji, tsohon mutum ne ,tukuf da shi!! Sanye yake cikin wasu zazzafan suit,ash colour, kai kana ganin yanayin kayan ka san ya kai kud’in jarin mai k’aramin k’arfi,idanunsa sanye cikin wani farin glasses wanda kana gani ka san na k’arin k’arfin gani ne,walking stick d’in dake rik’e a hannunsa for sopport ma kanta abar kalloce!! Ka na gani ka san an zuba mak’udan kud’ad’e wajen siyar ta,ga wani had’add’en Rolex watch a hannunsa, Tsohone amman skin d’insa glowing yake yi wanda kana gani ka san tsabar hutune..to cut it short dai,every part of him is screaming ‘I’M RICH!!’. Sandar hannunsa ya d’aga domin yin tafiya har ya d’an tura k’afarsa gaba sai kuma ya yi amfani da ita ya juyo ya tsaya yana kallon motar da suka shigo tare. Wani kyakkyawan saurayi ne ya fito daga mazaunin driver da alama shi ya tuk’o motar da kansa, yana d’an fizgen kama da tsohon sannan kalar fatar su iri d’aya ce. Ganin da Auwal ya yi kakan nasa ya kafeshi da idanune ya sanya shi K’arasowa wajensa da d’an sauri, tukunna ya d’an rissinar da kansa yana mai kallon k’asa kafin yace”Garanpa,u need something??.” Ya yi masa tambayar ba tare da ya kallesaba . Juyawa Grandpa d’in ya yi ba tare da ya sake kallonsa ba,har zuwa lokacin da drivern d’insa ya d’auko suitcase d’inshi ya gama rufe motar yana taka mishi baya…. yana tafiyar ba tare da ya tsayaba cikin muryarsa ta tsofaffi yace”Go and give iliyasu 50k,ask him to leave this house foreva,he is fired!! Sannan ka cewa Daniel ya nemo sojan da ya san zamu shirya ni da shi,ya fara gadin main gate,within 3 hours.” Yana magana yana tafiya ko sake waigowa bai yi ba balle ya amsa Auwal wanda yake cewa”Ok Granpa consider it done”. Ya shige. Wani shu’umin murmushin jin dad’i Auwal d’in yayi, daman shi ya tsani Malan iliya, domin kuwa kamar gadin sa shi kad’ai yakeyi a gidan,ya saka masa ido dayawa, kullum idan ya dawo dukda kuwa motarshi tinted glass gareta sai Malan iliya ya san yadda yayi ya d’an lek’a ta gaban dukdan ya ga shi kad’ai ya dawo ko kuwa tare da wata yake,sannan bai isa yayi dare ba,yana wuce 12 zai fara ganin kiran Daddyn sa ko da kuwa Daddyn nasa baya gari,ko me yayi in dai malan iliya ya gani to a kunnen Daddynsa, kuma sai an hukuntashi hukunci mai tsanani, ya zame masa kamar wani cctv camera sam ya hanasa sakat duk dan kawai idan ya kai wa Daddyn nasa rahoto yana bashi kud’i da kaya, and the most annoying part of it Daddyn nasa ya hanashi ko da hararar mallan iliya ne,balle wata banzar magana. Yana wannan nazarin da murmushi akan fuskarsa ya k’arasa bakin gate d’in granpa ya fad’awa Daniel sak’on granpa sannan ya nufi main gate wajen mallan iliya. Daniel kasa b’oye zumud’in sa yayi , a take ya d’au waya ya kira wani abokinsa solomon wanda ya san irin halinsu d’aya, nan da nan kuwa Abokin nasa ya amince bayan Daniel ya fad’a masa nawa ake biyan malan iliya, yace masa ya jira zuwanshi nan da 2 hours yanzunnan zai sallami mamanshi da sistern shi ya taho. Shikuwa Auwal yana isa maingate ya sanar da malan iliya sak’on granpa,tsabar mugunta dubu hamsin akace ya bashi amman yabashi dubu ashirin,kayansa kuwa kala uku ya bari ya d’iba waenda ya zo gidan da su,ragowar kuwa yace “ba zai d’auka ba ai ta wajen Daddynsa ya samu ta hanyar kai gulmarsa.” Sai da ya tabbatar ya bar gidan tukunna ya k’ulle kayayyakin da ya hanashi tafiya da su ya jefar a babban garbage bin na Estate d’in, ya koma ciki abinsa. Cike da annashuwa ya nufi wani Triplex a cikin jerin gidajen estate d’in, kamar yadda kowanne yake gate d’inshi daban da compound haka shima wannan, knocking ya yi sannan ya d’an ja ya tsaya, cikin y’an seconds wani tsohon mutumi ya bud’e y’ar k’aramar k’ofar gefen gate d’in gidan ya d’an lek’o, ganin waye a tsaye ya sanya tsohon saurin bud’e k’ofar sannan ya d’an rissina yace “Barka da yamma.” “Lafiya” kawai Auwal d’in yace dashi daga haka ya kutsa kai ya nufi cikin gidan wanda yake zagaye da flowers kala kala,an shafe k’asan compound d’in gidan da interlock, ta tsakiyan compound d’in kuwa wani k’aramin roundabout ne,ta left side na roundabount d’in wani k’awataccen garden ne wanda yake d’auke da su porch swing,hammock chairs da k’ananun kujeru domin hutawa sannan ga shuke shuke kala kala, ta right side kuma parking space ne, sai ta gaba hanyar shigowa,gate kenan, sannan ta bayan roundabout d’in kuma anan ne k’ofar shiga gidan ta main parlour take. Kasancewar gidan a zagaye yake..idan ka wuce main door d’in ka yi hanyar baya akwai k’aramar k’ofar kitchen ta shiga kitchen da wajen wanke wanke da d’an k’aramin fili. Yadda ginin gidan nan yake haka gaba d’ayan gidajen estate d’in suke apart from gidan granpa ,wanda ya fi kowanne girma da tsaruwa. Karasawa yayi ya shiga y’ar k’aramar varander da aka dan zagayeta da k’arafuna da flowers,sannan ya isa bakin k’ofar parlourn ya danna doorbell. Wata farar budurwa wadda ba zata wuce shekaru goma sha biyar bace ta bud’e k’ofar,hannunta rik’e da waya kirar iPhone tana daddanawa tana murmushi,da alama chatting d’in da takeyi ya tafi da hankalinta, dan bata ma lura da waye ta bud’ema k’ofar ba,kawai ta juya ta nufi k’aton parlourn nasu mai d’auke da set d’in kujeru uku da katon dining area ,sai staircase biyu. Juyawa Auwal yayi ya rufe k’ofar sannan da d’an sauri ya biyota ta baya yasaka hannu ya warce wayar, da sauri ta juyo suna had’a ido da shi ta saki wani sassanyan murmushi. B’ata rai ya yi sannan yace “da wa kike chattn haka??” Ya yi mata tambayar yana maida idanunsa kan wayar domin ganin da waye take chattn d’in. Zaro ido ta yi sannan da sauri ta kai hannunta kan wayar da niyyar warcewa amman sai ya yi saurin kama hannun ya rik’e da d’an k’arfi har sai da ta yi k’ara,ganin k’ok’arinsa na ya karanta mata chat ne ya sanya a karo na biyu ta sake yunk’urin karb’ar wayar tata cikin shagwabarta tace “Ya Auwal dan Allah ka bani waya ta.” Murmushi ya yi ganin chat d’in nata ita da wata friend d’inta ne, tana bata labarinsa, expressing how much she loves him, har tana ce mata ta fi son smile d’insa saboda hakan yana fitar da dimples dinsa,sake fad’ad’a murmushin nasa yayi sannan yace “D’ago kanki mana ,ungo wayarki.” Shiru ta yi,sai hannunta d’ayan da bai rik’e ba da ta d’ago da niyyar karb’ar wayar amma sai ta ji ya had’a da nashi hannun da wayar ya rik’e, da sauri ta d’ago kanta ta yi kalar tausayi tace “Da zafi fa,ka bani wayata mana.” Yanayin kallon da yake yi mata babu ko kyaftawa had’e da murmushi ne ,yasanya ta yi saurin mayar da kanta k’asa. Taku d’aya ya yi ya matso daf da ita,sannan ya yi k’asa da murya a hankali yace “Da gaske kina son dimples d’ina?” D’aga masa kai ta yi alamar ‘eh’. Sannan ta d’an yi taku d’aya ta yi baya Sake takowa ya yi kamar d’azun ya matso da gefen fuskar sa kusa da tata yace “Tou bara in goga miki,kema ki zama mai dimple, kinga sai mu Haifa Yara masu dimples hud’u.” Yayi maganar yana matso da gefen fuskarshi har yana gogar kumatunta,ba ta san ya akayi ba kawai ta ji ya sakar mata light peck a gefen fuskartata, tana k’ok’arin matsawa taji ya yi saurin ruk’ota ta hanyar rik’e mata gefen cikinta. “AAIMA!!!” Suka ji an fad’a cikin tsawa, Da sauri ta juyo,a tsorace. Karkarwa jikinta ya fara yi sakamokon had’a ido da tayi da yayaynta ransa a mugun b’ace. Sak’k’owa ya fara yi daga benen cikin sauri mai had’e da d’an gudu,yana tafe yana k’ok’arin kwance belt d’in jikin wandonsa, kafin ya k’arasa sak’k’owa kuwa har ya k’arasa zaro belt d’in ya rik’e ta a hannunsa,gadan gadan ya yi kansu. A take Aiima ta fashe da kuka tun kan a daketa,ta fara kiran “Mammy!!” da k’arfi. Mammy da anty Adama da suke kitchen ba su ji shigowar Auwal ba amman tun lokacin da ARSHAAD ya kwala kiran Aiima sukaji suka fito da saurin su. Ganin Arshaad ya yi kan Aiima da belt ne ya sanya Mammyn k’arasowa da sauri ta shiga gabanta ta tsaya tace”Arshaad meye haka?lafiyarka kuwa?” Anty Adama kuwa ganin Auwal a tsaye yasa ta kafeshi da idanu kafin ta ce”mai ya faru?” Sai a lokacin ma shi Arshaad ya lura da Anty Adama a wajen dan gaba d’aya idanunsa sun rufe ransa ya yi mugun b’aci!! Ya so ace yau ya damk’i Yarinyar nan wallahi da sai yayi mata mugun dukan da sai ta yi jinya tunda ya lura kunnen k’ashi gareta kuma ta raina shi, ba sau d’aya ba ya sha ja mata kunne ya hanata shiga harkar Auwal amman ta k’i yarda inda ace Aslam ne ya yi mata magana ya san da tuni ta bari…… Maganar Anty Adama ce ta katse masa tunani,jin ta sake cewa “Wai kai Auwal ba da kai nakeba?mai ya faru wai?me kuka yi mata take kuka??” Saurin katse ta Auwal yayi yace”Nooo,Mom bani baneba!!”ya yi maganar cikin d’aga tafukan hannayensa biyu kamar za a yi arresting nashi yana tab’e baki,alamun shi fa ba ruwanshi,kafin ya ci gaba da cewa “ta yaya zan sakata kuka? Zance na zo fa. D’azu da muka yi waya da ke kika ce mini kun dawo,shine nace bara inzo in ganta kuma in gaida Mammy,kin ganni daga office wallahi ko wanka banje na yi ba na zo nan mu gaisa,shine fa yana hango mu tare ya zaro belt ya yo kanmu zai dakemu!” Kallon mamaki Arshaad ya tsaya yana yi mishi ganin yadda ya d’aure sa da jijiyoyin jikinsa,dukda kuwa yadda ya san halin Auwal sarai na iya juya al’amari….haka yake tun suna Yara kamar mace wajen iya makirci,kaf cikin mazan estate d’in sai da ya san yadda yayi kutun kutun ya kawar da kowa ya zama na right hand d’in granpa,yanzu haka shine MD , granpa ya d’aurasa a kan komai saboda shi sai end of the month yake shiga office , ko kuma in akwai Manyan Bak’in da suka zo ya kanje ya gansu, ko kuma wani important meeting,shima still Auwal d’in yana nan manne da shi baya barin kowa ya je jikinshi sosai, idan ma ya ga kuna shiri da granpa d’in to sai ya san yadda yayi ya had’a maka gurmi an maka fata fata. “Wai Arshaad sai yaushe za ka bar wannan mugun abu daka d’aukarwa kanka ne?” Ya ji muryan Mammy cikin fad’a, da alamun maganar Auwal ta yi tasiri akanta har ta kai ga b’ata mata rai. Anty Adama ce ta kalli Arshaad da duk kunyarta ta rufesa,gashi shi mutum ne mai kawaici ba zai iya fad’i a gabanta abinda ya ga Auwal d’in yayi ba . Takowa ta yi ta zo gaban sa ta tsaya sannan ta sa hannunta ta kamo nashi, cikin yin k’asa da murya tace “Son, please ku zauna lafiya kai da d’an uwanka mana,kowa yana son had’in nan nasu shi da Aiima ko dan zumunci ya k’ara k’ulluwa, but if there’s anything da kake gani ya sanya baka san Auwal d’in a tare da sistern ka just name it,I promise zanyi putting into consideration and if kanada gaskiya I’ll support u 100%.” “Bafa shi da wani reason da zai baki,kawai ke kin san halinsa ai tun suna Yara ba shiri sukeyi ba,abu kad’an sai fad’a,shine har yanzun basu san sun girma ba!!!ki barni da shi na san maganin sa” inji Mammy. Ganin bashi da niyyar yin magana ne yasanya Anty Adama ta cika hannunsa ta kalli Auwal tace masa “lets go””Mammy za mu k’arasa tattaunawa a waya.” “Ok” kawai Mammy tace mata…bayan sun fita ne ta maida hankalinta ga Aaima wadda ke durk’ushe a k’asa har yanzun tana gunjin kuka, Kamo ta tayi ta mik’ar sannan tace mata “goge hawayenki,daina kuka kinji auta wuce ki tafi d’akin ki.” Da saurinta ta zo ta wuce ta gaban Arshaad dan gani takeyi kamar zai kamota. Juyowa Mammy tayi ta kallesa sannan tace “Ko ba komai ni na haifeka atleast idan ka so abunda nakeso zan ji dad’i,ko dan Adama da zumuncinmu ya kamata ace ka yi hak’uri ka zauna lafiya da d’anta. Dukda na san taurin kanka da kuma yadda ka raina ni ba lalle ya bari ka yi abinda nakeso ba amman ni dai ba zan gaji da fad’a maka gaskiya ba.” tana gama fad’in haka ta wuceshi…har ta d’an tsaya kamar za ta sake yin magana sai kuma ta juya ta nufi hanyar kitchen,suka barshi a tsaye a wajen..... Su Auwal suna shiga main parlour ya yi hanyar staircases d’in da yake a hannun dama,da alama ata nan side d’insa yake. “We’re not finished.” Ya ji muryan Mom d’insa. Juyowa ya yi ya kalle ta sannan yace “Let me freshen up first,Ina zuwa . Ya fara hawa stairs d’in da d’an sauri. “What did u do??” Ya ji ta sake tambayar shi. “A peck.” kawai yace mata, da ga haka ya ci gaba ta tafiyar sa ba tare da ya juyo ba. BULAMA✍️ So da Buri Free Book 04 A nan ya tafi ya barta a tsaye kamar wata statue, kana ganin fuskarta ka san ranta a b’ace yake, ita sam! ta kasa gane kan Auwal kwata kwata,bata son halayyar nan tashi, kalli yanzu k’iri k’iri ya had’a uwa da d’anta fad’a, shikuma Arshaad ta tabbata kunyar ta ce ta sanya ya k’i cewa komai,gashi Daddy ya rok’eta akan dan Allah su taru ita da shi su dinga rufama d’ansu asiri…shi kad’ai Allah ya basu su daina yayata wasu halayyarshi da kansu a cikin family, domin kuwa duk ranar da aka yi rashin sa’a granpa ya ji to tabbas kashin Auwal ya bushe…. Tana cikin wannan tunanin ta ji an dafa ta…tana juyowa suka had’a ido da Mijinta Alhaji Yusuf MT murmushi ta yi kafin tace “Daddy yaushe ka dawo?” Sai da ya d’an k’ura mata ido kafin yace “Auwal ne ko?” Murmushin ta sake yi sannan tace”amsa tambaya da tambaya, are we??” Sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya ya yi kafin ya fara magana”Ta windown kitchen na hangoku Ina waya da doctorn ABBA, shine na fita ta k’aramar k’ofa na rufe na tsaya a k’aramin compound saboda bana son Auwal ya ji ni. Kin san yadda suke shi da granpa,ba k’aramin aikin sa bane ya kwashe komai ya fad’a mishi Tunda ya san in dai da granpa a case babu abinda zan iya yi masa.” Shiru yayi da alamun damuwa a kan fuskarsa kafin ya sauk’e ajiyar zuciya yace “Adama akwai matsala fa, don sun sake yin wani fad’an da granpa har ya ma fi na last time, sannan shi kuma ya sakawa kanshi damuwa over gashi yanzu har ya kusan shiga next stage.” “Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”shine abinda Mom tace idanunta suna kawo kwallah kafin ta kalle sa sosai tace “To ai ni da ka bari Auwal d’in ya ji ya fad’a ma granpa d’in watak’ila hakan ya sanya shi ya d’an sauk’o daga fushin. Na ga kwana biyun nan ma ai kamar yad’an yi sanyi ai ba kamar da ba,ko?” D’an murmushi Daddy ya yi tukunna yace”babu fa abinda ya chanja daga halin granpa,kawai dai kwana biyun ba a samu wanda ya tab’o sa bane ba shiyasa kika ji shiru…d’azun fa malan iliya ya kirani ya ke ce mini Auwal ya fatattake sa,da na tambayi drivern granpa d’in yace mini shi granpa d’in ne yace a kori mallan iliyan d’azu daga dawowarsu daga meeting,wai dan ya bar bakin main gate ya tafi siyan agwaluma.” “Allah ya kyauta” Shine abinda Mom tace, sannan ahankali tace “wai menene ma to abunda ya taso da fad’an nasu shi da Abban?? daa fa har muna murnar almost 2 years lafiya k’alau tsakaninsu,shima kuma Abban ciwon nasa ko tari babu.” Sai da Daddy ya d’an furzar da numfashi tukunna yace”Wai mafarkai yakeyi da Maryam! da jariri a hannunta,tana kuka tana cewa ya zo ya taimaketa, abun ya kai 3 months yace kullum in ya kwanta sai yayi shinefa ya d’aga hankalinsa… Da farko,Dad ya samu ya fad’a mishi. Shikuma Dad yace mishi ya yi ta addua kawai… shine fa tsabar ganganci kawai ya je ya tunkari granpa da maganar.. akan wai yana so yaje ya ganta,ya tabbatar babu Yaro a tsakaninsu,saboda mafarkan da yake ta yi.” Ba shiri Mom ta zaro ido waje sosai kafin ta yi k’asa da murya tukunna tace”me granpa d’in ya ce??” “Cewa za ki yi me ya yi masa,ba me yace ba! In banda abun Abba kai da ka san mutumin nan yanata fushi da kai for morethan 24 years ko ga miciji ba kwa yi da shi, amma shine zaka kwashi k’afa ka je ka tunkare sa da irin wannan zancen? Ni wallahi Adama nima na fara tunanin ko dai asiri ne matar nan ta yi masa,saboda ki duba kiga yadda he’s willing to risk everything just to talk to her again. Dukda irin bak’ak’en maganganun da ta dinga rubuto masa har da fa threatening nashi da kotu fa ta yi… Daga k’arshe fa idan ta aiko da sak’o ba ya nuna mana! daina nuna mana yayi ni da Dad Allah kad’ai ya san irin maganganun da suke a ciki Shikuma a wannan lokacin kullum cikin bata hak’uri yakeyi yana aikawa. Da kyar granpa ya samu ya rabasu, shine yanzu yake son tada zaune tsaye, shi ko ta jikinsa da lafiyarsa ma bayayi, gashi yanzu granpa ya yi masa horo mai tsanani….. ..Kinga da farko ya sallame shi a duk wani company da kika sani namu a yanzu babu Abba a ciki,sannan ya hanashi share d’inshi. Kuma ya bashi notice akan ya bar masa estate d’inshi kar ya k’ara ganin shi ko y’ay’ansa. Yace kuma duk wanda ya bashi hak’uri sai ya had’u da tsananin b’acin ranshi,hatta gramma.” “Ya subahanallah” shine abunda Mom ta fad’a sannan a hankali tace “bara inje wajen Zainab.” “To” kawai yace mata ya juya ya nufi dining area ya nemi guri ya zauna ya fara zuba abinci, kana ganin fuskarsa ka san yana cikin matsananciyar damuwa. Fitowa ta yi tana zancen zuci ta k’arasa bakin gate sannan ta fita ta k’aramar k’ofa,ta nufi d’aya daga cikin gidajen tana d’an sauri,tana isa tayi knocking,kamar kowanne gida nan ma mai gadi ne ya zo ya bud’e mata,ya gaidata ta amsa sannan ta shiga. Tana shiga ta hango wata k’atuwar moving van ga jakankuna a ajiye a waje da boxes, sannan ana ci gaba da fitowa da wasu. K’ara saurin tafiyar tata ta yi ta nufi hanyar k’ofar shiga main parlourn wadda ke nan a wangale anata shige da ficen kwashe kaya. Da sallama a bakinta ta shiga, tana shiga ta hango wata farar mata zaune a kan 2sitter na d’aya daga cikin jerin kujerun falon,matar ta zabga uban tagumi,kana ganin ta ka san tana cikin damuwa sannan tayi nisa a tunani. K’arasawa Mom tayi kusa da ita sannan ta dafa ta,ganin kamar ma ba ta san ta dafa tan bane ya sanya ta kira sunanta”Zainab!“ Firgigit!! Ta yi ta juyo,suna had’a idanu da Mom kuwa kamar jira takeyi ta fashe da kuka,sannan ta kamo hannayenta duka biyun kafin ta fara jujjuya kai ahankali tana kallonta tace “Adama inata kiranku yau kwana biyar wayanki baya tafiya,komai ya zo mini k’arshe kashina ya bushe!! I never saw this coming!! Shikenan na san yanzu zai yi finding out kum......” Mom bata bari ta k’arasa ba ta yi saurin zare hannunta wanda ta rik’e ta yi amfani da shi wajen toshe mata baki sannan ta juya tana kallon falon tana rarraba ido cikin fargabar kar wani ya jiyoso. Ganin da ta yi ba kowa a falon masu kwasar kayan ma duk sun gama na k’asa sunyi sama ne ya sanya ta kamo d’ayan hannaunta da har yanzu yake cikin nata ta mik’ar da ita sannan ta jata suka nufi d’aya daga cikin d’akunan parlour. Sai da Mom ta tabbata ta saka key,tukunna ta juyo tace “Yanzu menene abun yi?” Share kwallarta Zainab ta yi sannan tace “Granpa ya koremu shiyasa kikaga anata kwash..” “Na sani“ Mom ta katse ta sannan tace “Daddy ya fad’a mini komai.” Shiru Zainab tayi, sannan ta jingina da bango ta d’aga kanta sama ta rufe idanunta a hankali tace “In dai muka bar gidan nan,kin san cewa babu abunda zai hana Abba bibiyar Maryam ko? Saboda ya kasa yarda da takarda har yau,kin san cewa ko a kwanakin baya dama na gaya miki Ina ganin kokwanto a fuskarsa….ita kuma mayyar gashi yanzu har a mafarki zuwar masa takeyi.” Bud’e idanunta ta yi ta kalli Mom sannan ta ci gaba da cewa “4 days ago fa yana tashi yace shi wajenta zai je, ya gaji da wannan mafarke mafarken,da ya je wajen granpa suka yi fad’an nasu da suka saba,dan bai samu an goya masa baya ba shine tun a chan ya zube,sai kwasar shi aka yi ,akai asibiti da shi. Kwanan mu d’aya da wuni bai san inda kanshi yake ba ana fama.” Shiru ta yi kafin ta ci gaba da cewa “Adama granpa shi kad’ai yake iya takawa Abba burki akan Matar nan yanzu ya bashi freedom!!Saboda wannan abun fa da akayi da granpa da mutane ne suke ganinshi as punishment amman a wajen Abba freedom ne. Can u imagine in 2 weeks time fa granpa yace “mu bar gidan nan amman Abba a jiya da sassafe ya kira masu penti aka fara pentin gidanshi na kundila yanzu kinga yau da safe yace mufara parking, na tabbatar ko kammala pentin ba a yi ba. Atleast ai ya jira ya dawo daga asibiti ko? Ya samu ya d’an warware maybe b4 then ma granpa ya saukkk’o.” Murmushi Mom ta yi kafin tace “Haba Zainab,ke har yanzu ba ki san waye uncle d’inki ba ne? If there’s one thing that I’m sure of shine granpa ba zai goge decision d’inshi ba sai dai in ya sassauta,yanzu mafita itace abar nema ba wai wannan dogon labarin ba Dan ba ke kad’ai ba hatta ni da Mammy sai mun raina kanmu idan zance ya fito…. Na san granpa Hates Maryam with passion But what we did is something da bai kamata ace mu bari a kamamu da laifinshi ba!.” Ajiyar zuciya Zainab ta sauk’e kafin ta juyo ta kalli Adama sannan ta kama hannuwanta biyu tace” ki taimakeni… at any cost kar mu bar gidan nan,you always come out with the perfect solution, do something. Har yau ban samu soyyayyar Abba ba,I’ve been trying my best wajen ganin na yi winning nashi kuma na san I’m almost there but in dai matarnan ta dawo cikin rayuwarsa komai lalacewa zai yi.” Shiru Mom ta yi tana d’an tunani ta kusan 5minutes sannan ta yi murmushi tace mata “kawo kunnenki kiji wata magana” Matsowa ta yi sannan ta fara rad’a mata maganar….. Da farko juyowa ta yi ta kalleta da alamun mamaki mamaki sai kuma ta juya ta ci gaba da sauraronta ahankali ta fara murmushi.... “Ummi!Ummi!!Ummi!!!” Suka ji murya ana kwala kira a parlour. Da sauri Zainab ta juyo tace inaga ga su shuraim sun dawo d’azu suka tafi asibiti.” Har ta kai bakin k’ofa ta murza key d’in za ta fita sai kuma ta juyo ta kalla Mom tace mata “Kin tabbata babu matsala?” Murmushi mom ta yi sannan ta d’aga mata kai,alamar’eh.’ Juyawa tayi ta fita itama ta biyo bayanta suka fice a d’akin. Wani Yarone yake shigowa cikin parlourn fari tass da shi kyakkyawa,suna had’a ido da Zainab ya kalli sama yana kallon d’ayan Yaron da ba zai wuce 10 years ba yanata hawa Bene yana kwala kiran “Ummi!!” , da d’an k’arfi ya ce “Sudais!” Da sauri wanda aka kira da sudais d’in ya juyo yana kallon d’an uwanasa wanda juyowar da ya yi ne zai sanya ka fahimci ashe twins ne dan komai nasu iri d’aya ne. Nuna masa Zainab ya yi sannan yace “ga Ummin nan.” Da saurin sa kuwa ya sauk’o ya zo ya rungumeta kafin ya d’ago kai yacee mata “Ummi Abba ya dawo,Dr yace ya warke!suna waje shi da ya Arshaad yanzu zai shigo da shi.” bai gama rufe bakinsa ba kuwa Arshaad ya shigo Shi da wani mutumi kyakkyawan gaske,dogo d’an kakkaura amman bashi da k’iba kwata kwata,fari tas da shi, kyakkyawar fuskarshi cike da tsananin kyau haiba da kwarjini ‘ABBA’ ya rik’e hannun Arshaad d’in na dama shikuma Arshaad d’in ya ruk’o kafad’arshi da dayan hannun for support suna tafiya a hankali,kana ganin mutumin ka san bashi da lafiya. A hankali suka k’arasa Arshaad ya kaisa har kan d’aya daga cikin kujerun parlourn ya zaunar da shi tukunna ya juyo ya kalli su Ummi ya gaida su. Sai da suka gama gaisawa sannan Ummi ta k’araso kusa da su tace “Abba ya jiki? Yaushe aka sallameka? Mai yasa baka kirani ba?” D’an gyaran murya Arshaad yayi, saida ta d’ago ta kalle sa sannan a hankali yace “Ummi Dr yace kar a dameshi fa,and yana buk’atar Hutu,sosai!.” Juyawa ta yi ta kalla gefe ta d’ayan staircase d’in yadda aketa sak’k’owa da kaya ana shige da fice kafin tayi murmushi tace “To Arshaad yanzu daka kowoshi ka ga alamun rashin hayaniya anan d’in? Kalla fa parking aka hau yi yau d’innan gadan gadan,nima Ina dawowa daga asibitin na tarar da su suna jirana a gate da na tambaya sukace wai Abban ne yace su zo su fara kwashe kaya suna kaiwa sabon gida, yanzu saboda Allah idan bai ji da lafiyarsa dan kanshi ko ni ba,ai ya duba Yaran nan”ta yi maganar tana nuna su Sudais tare da share kwallar da ta zubo mata. A hankali Abban ya yi d’an tari sannan ya gyara zamanshi tukunna yace “Arshaad.” “Na’am Abba.” Arshaad d’in ya fad’a cikin girmamawa ya d’an rankwafo ta saitin shi. Sai da ya kuma yin tari sannan yace “Ka duba moving van d’in dake a waje akwai boxes da Ghana most go a ciki ka d’auko empty ones d’in dayawa,ka shiga parlourna da d’akina duk wani abu ka had’a su ka tattare,sannan ka rubuta sunan items d’in da suke ciki a jikin kowanne box da makar saboda kar ya bada wahalar tantancewa idan anje chan. Ka yi sauri idan ka gama za su shiga yanzu su kwashe furnitures, naga har sun kusan gama chan side d’in.” Ya k’arashe maganar yana d’an tari. “To Abba” shine abinda Arshaad yace,daga haka ya nufi waje domin d’auko boxes d’in. Juyawa Abba yayi ya kalla su Sudais sannan yace “kuma ku je ku d’auko ku had’a naku kayan.” Har ya gyara zaman ya d’an jingina ya lumshe idanunsa, sai kuma ya d’ago ya kalli Ummi sannan a hankali yace mata “Za ki bimu ko a nan za mu barki!” Yunk’urawa ta yi za ta yi magana ranta na sake b’aci, Da sauri Mom wadda ke a bayanta ta rik’o hannunta ta d’an matse alamar ta yi shiru. Shurun kuwa ta yi sannan Mom ta yi gaba tace “Abba sannu da jiki, Allah ya sa kaffara ne. Bara muje saman in taya ta had’a kayanta. Idan kana buk’atar wani abu muna sama sai ka kiramu a waya....” D’aga kanshi ya yi alamar ‘to’ sannan ya mayar da idanunsa ya lumshe ya koma ya jingina a jikin kujerar. SHARE PLS. BULAMA✍️ So da Buri Free Book 05 Jan hannunta Mom ta yi sannan suka yi sama,suna shiga d’akinta tace “Adama ba fa inda zanje sannan suma babu inda za su je.” “Na sani” Shine abinda Mom tace sannan ta fara dube dube kamar tana neman wani abu. Drowern gaban mudubi ta kai hannunta ta bud’e,aikuwa ta ci karo da abinda take nema..da sauri ta d’auko littafin da ta gani da biro sannan tace “oya d’auko mini takardar gidanki wanda ya baki in kalla signature da wani note haka da ya tab’a rubutawa.” D’an tsayawa Ummi ta yi tana kallon ta da alamar tsoro a fuskarta. Ganin haka ya sa Mom ta kawo gabanta ta tsaya sannan tace “I’m just trying to help,ba mu da ishesshen lokaci,ki daina dogon nazari. Besides har yanzu ukune akan ki so don’t worry about one ballantana ma bashi da masaniya,so babushi a lissafi. Kowa ya sani a estate d’innan kece weakness d’in granpa,ki duba ki ga abubuwan da yake yi just to make sure u stay happy..I can assure u ba zai bari Abba ya tafi ko Ina ba idan ya ga wannan.” tayi maganr tana nuna mata takardar da ta yaga daga jikin book d’in. Shiru Ummi ta yi kafin tace “Adama I love my husband, banaso in shiga tsakaninshi da mahaifinsa..” Wannan karon tsaki Mom ta yi sannan tace”Zainab kin fara bani haushi wallahi zan yi tafiyata, shiga tsakani kuma na nawa?? Waye ummulaba’isin fad’an nasu?sai da abu ya zo gangara za ki fara tunanin tsame hannunki? To bari kiji! ta inda akabi aka hau ta nan ake sauk’a sannan na san Dr Abba farin sani If things get out of control zan yi paying nashi ya maka masa case na memory loss, a ce yayi for a day ne, a time din kuma yayi ta misbehaving,sai mu ce a lokacin ne yayi shi kansha kenan bai san yayi ba. Dan mutumin da ya kwana ya wuni bai san inda kansa yake ba ai zai yi morethan this,kuma babu wanda ya isa ya musa.” Da sauri Ummi tace”ok ok”sannan ta nufi wardrobe d’inta ta d’auko key a k’asan tulin kayanta sannan ta saka key d’in a jikin wani d’an k’aramin locker wanda yake nan ata k’asan kayannata ta murza mukullin ya bud’u. Wani suitcase ta d’auko ta yo kan gadon da shi,a tare suka hau bincikawa har sai da suka d’auko wani file da wata envelope. File d’in takardun gida ne, envelope d’in kuwa da suka bud’e ta wani had’add’en rubutu ne ya baiyana a cikin da alama wasik’a ce . Zama Mom ta yi a kan gadon sannan ta saka wannan wasik’ar a gaba ta yi shiruu…ta kai kusan 2 minutes tana k’are mata kallo kafin ta ajjiye ta a gabanta tukunna ta hau rubutu akan wannan blank papern data yago….exactly handwriting d’in irin na wannan wasik’ar takeyi. Ta d’auki y’an mintuna tana rubutawa kafin ta d’auki dayan file din ta bud’o dai dai wajen signature ta kalla da kyau sannan ta ajiye ta yi irinta a k’asan takardaar da ta gama rubutu a kai. Tashi tayi daga kan gadon sannan ta juyo ta kalli Ummi tace mata “Done!!” Mik’a hannu Ummin ta yi ta karb’a ta karanta sannan ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace “Yanzu ta Ina zan wuce?? kin san fa yana falo.” “D’auko mayafinki” inji Mom. Cikin wardrobe d’inta ta bud’e wajen mayafai, sannan ta jawo abinda hannunta ya kai kai . Warewa ta yi tana shirin saka hijabin Mom tace a’a bani nan zan saka a cikin nawa maya fin in fita in yaso sai ki sak’k’o daga baya ki yi kamar kin shiga kitchen,ni kuma zan jiraki a k’aramin compound ta baya,sai ki fito mu wuce.” Har ta juya za ta fita,sai kuma ta dawo ta k’ara rad’a mata wata magana sannan ta fice. Yadda Mom d’in ta tsara hakan kuwa akayi… Bayan sun fita daga gate d’in gidan suka nufi na granpa. Suna zuwa daniel ya gaidasu suka shige suka isa k’ofar main parlor. Suna shiga kamar kullum sukaga ba kowa,shiruu sai k’arar ac Ganin hakane ya sa suka nufi kitchen a tunanin su ko za su ga granma ta yi musu iso,amman nan d’in ma ba su sameta ba,sai masu aiki. Ganin suna b’atawa kansu lokacine yasa Mom ta d’auko wayarta, ta kira gramma,bugu biyu ana ukun ta d’auka. “Assalamu alaiki, Adama.” Aka fad’a daga d’ayan b’angaren. Cikin girmamawa mom tace “Ameen wa alaiki assalam,Ina wuni gramma” “Alhamdulillah” Shine abinda gramma tace. Cikin ladabi Mom tace”daman yanzu Zainab ta zo ta sameni akan wata magana,shine muke son ganin granpa,ban sani ba ko yana nan?.” “Yana nan.”Ta ce,daga haka ta katse kiran. Kusan mintuna talatin suka yi a kitchen d’in, har sun fara gajiya sukaji k’arar bud’e k’ofa. Da sauri suka fito a kitchen d’in dai dai k’ofar da take kallon kitchen d’in aka bud’e sosai wata farar tsohuwa ta fito,bata da tsayi sosai amman tanada k’iba,idanunta sanye cikin medicated eye glasses, tana sanye cikin wata royal blue d’in atamfar super xclusive ta yi d’aurinta irin na tsoffi. A hankali take tafiya tana tunkaro k’ofar kitchen d’in tana yin mitsi misti da idanu alamun so take ta fahimci su d’inne a wajen domin kuwa dudda glass d’in ba kasafai take iya hango abu idan yayi nesa sosai ba. Gane hakan da suka yi ne ya sanya suka yi saurin k’arasawa inda take sannan suka d’an rissina suna sake gaida ita. Cikin kulawa ta amsa sannan tace “ina fata dai abu mai muhimmanci ke tafe da ku ba shirme ba,dan kar ku je ku yi ta shiririta,kun san ba yawan son surutu yake ba,yanzu hakan ma da kyar ya yarda zai ganku..” Takardar hannunta kawai Ummi ta mik’a mata. Kallonta gramma ta yi sannan ta sa hannun ta karb’a takardar ta fara dubawa….gyara glases d’in idanunta ta yi da kyau cikin zaro ido kafin ta d’ago ta kallesu sannan tace “Shi Yakubun ya baki wannan???yaushe!??” K’asa Ummi ta yi da kanta sannan a hankali tace “Shekaran jiya” Cikin fad’a gramma tace”kuma to me kika tsaya yi tun shekaran jiya baki zo nan ba? Ai cewa yayi ki tafi wajen iyayenki,ko kina da iyayen da suka fi mu ne?”. Da sauri Ummi ta girgiza kai tana share hawaye. Cikin tausayawa,gramma ta kamo hannunta ta rungumeta tana bubbuga bayanta,sai da ta yi shiru sannan tace su je wajen granpa d’in. Ta cikin parlourn da gramma ta fito suka shiga,suka bi ta wani had’add’en staircase suka isa wani tafkeken parlour sannan suka sake bin bene kafin su iso wani had’add’en parlour. A tsaye suka hangosa gaban wani k’atoton glass wanda gaba d’aya bangon wajen glass d’in ne ya cinye…ya juya baya yana kallon glass d’in wanda ta cikin k’atoton glass d’in kana iya hango har compound d’in estate d’in. Waje gramma ta nuna musu sannan ta k’arasa gabansa ta mik’a mishi takardar,kafin ahankali tace”ga abinda yake tafe da su”. Ya kusan 2 minutes tukunna ya ce “Read it loud” Cikin nutsuwa grmma ta fara karantowa. “Ni Yakubu Umar Farouk mai turare, na saki matata Zainab Umar Farouk mai turare,saki d’aya…dalilin kuwa Ina gudun shiga hakkin aure domin na kasa bata kulawar da ta kamata da waje a zuciyata ta koma gidan iyayenta ta ci gaba da zama,nima zan tafi nawa gidan, idan ta samu miji ta yi aure.” Shiru kakeji d’ip! Kamar ba halitta a parlourn. Da farko tari Ummi ta fara a hankali,chan kuma sai ta farayi da k’arfi har da kamar kakarin amai kafin a hankali ta sulale daga zaunen da take akan kafet ta kwanta a wajen. “Ya subahanallah jini!!!” shine abinda suka ji Mom ta fad’a….da sauri gramma ta yo kansu,itama tana zxuwa ganin alamun jini jini a cikin bakinta yasa a rud’e ta ce “Adama mai ya faru?innalillahi wa inna ilaihirrajiun, maza d’auko ruwa ga firij chan ki zo ki yayyafa mata…” Ruwa aka d’auko aka fara yayyafa mata amman a banza sai ma jinin da yake ta biyo yawu yana dalala a k’asa….da sauri gramma tace maza kira wani a cikin samarin nan ya zo a taimaka a kaita asibiti,da sauri mom ta mik’e sai kuma ta tsaya tace “gramma duk basa nan na manta,amma d’azu naga Dr ya zo duba Abba,in kirashi??” Da sauri gramma tace “Eh kirawoshi,Allah ya kawo sauk’i ma ai.” Nan ta fita gramma kuma ta cigaba da jijjiga Zainab tana tofa mata addu‘o’i. Cikin mintunan da basu gaza ashirin ba Mom ta dawo Dr na biye da ita,suna zuwa aka gyara wa Ummi kwanciya anan kan kafet din Dr ya shiga duba ta da kayan aikin da ya shigo da su. D’agowa ya yi ya kalli Mom sannan yace”tun yaushe ta fara?” “Bata tab’a suma irin wannan ba gaskiya,sai dai tarin jini kuma ba ya zuwa sosai kamar na yau.” “Tun yaushe ta fara?” Doctor ya sake jeho mata tambayar ba tare da ya kalleta ba dan ya duk’ufa ya tarkata hankalinshi duk a kan Ummi burinsa kawai ya ga ta farfad’o. Kwanaki ta yi a gaba na har sau biyu,na yi mata magana tace “wai ta je absibi ance ba komai.Yau kuma sau uku kenan har da wannan,shima da naga ta yi ta sakeyi na tamabayeta tace mini ba komai fa.” “Unhm“ Shine abunda Dr yace yana zuk’o wani ruwan allura sannan ya saita jijiyan hannun Zainab d’in ya juye mata shi a ciki ya ci gaba da bata taimakon da ya kamata. Bayan wasu y’an mintuna… A hankali take bud’e idanuwanta waenda suka yi jazir…da sauri gramma ta k’araso gabanta ta fara k’ok’arin mik’ar da ita tanata faman jera mata sannu,Allah sarki gramma duk ta rud’e. “Doctor mai ka fahimta yana damunta???” Granpa ya yi mishi tambayar yana dogara sandarshi yana mai k’arasowa wajen. Mik’ewa tsaye ya yi sannan ya zare farin glasses d’in idonsa ya d’an mutsitsika idon ya maida glass d’in kafin yace “Heart d’inta ke da matsala, and da alamar ya yi serious gaskiya tunda har ga jini,ban san dalilin da ya sanya ta b’oye ba ta gayawa kowa ba,but this is very serious,idan ba damuwa yanzu zan tafi da ita mu yi ECO, saboda mu san matakin d’auka,dan ba a d’aukar issue na heart irin wannan likely.” “A wanne asibiti za a sameka?” Granpa ya sake mishi tamabayar. Card d’insa ya mik’awa granpa mai d’auke da suna da address na diagnostic center d’inshi sannan yace “nan waje nane it’s a private place. I’m a consultant a AkTH,idan hankalinku ya fi kwanciya da chan sai ayi mata a chan d’in, dai nasu zai d’auki time kafin a gama. “Za a sameka a chan (nakan)nan da 1 hour,get every thing ready” “Ok sir,”shine abinda Doctor yace sannan ya juya ya fita. “Let me show him the door” Mom tace sannan ta bi bayanshi. A hankali ya k’arasa takowa inda suke kafin ya kalli gramma yace mata “Leave us” A hankali gramma ta mik’e ta juya ta fita. K’arasowa yayi ya zauna a kan kujerar da take zaune a gefenta kadan a kan kafet sannan yace “Since when kika yi realizing baki da lafiya??” “2 years ago”tace. “Wa kika fad’awa?” “Ba kowa.” “Mai ya yi causing abun?” Shiruu ta yi wannan karon. Zan b’ata miki rai Ummi,kin san ba na son kame kame da kyaliya. Hawaye ta share kafin tace “Abba ne”cikin sheshshek’ar kuka. Tari ta fara yi sai da ya d’ab tsagaita sannan ta ci gaba da magana “Ba ya bani time d’inshi,kullum cikin zancen Maryam yake,i tried very well inga na daidaita relationship d’inmu amman na kasa,yak’i ya bani had’in kai at the end ma gashi ya zo ya rabu da ni gaba d’aya. Inaji yana waya da Abokinsa wai ya san idan ya had’amu ni da Maryam ranar lahira da shanyayyen b’arin jiki zai tashi…..tunda yanzu ya samu chance d’in da zai iya maida ita…..kuma wai yana jin tausayina,gara ya sauwak’e mini inyi aure nima In samu wanda zai iya bani kulawa tun kafin lokaci ya k’ure. Granpa it’s like har yanzu suna tare a yanayin maganarsa.” Tana kaiwa nan ta fara tari irin na marasa lfy,abun tausayi. A hankali ta ji granpa ya dafa ta sannan yace “ki huta,ya isa haka.” Waya ya d’auka ya fara lalube sannan da kyar ya nemo numbershi,yayi mamaki da ya samu number dan ya jima basa waya…ko abu zai fad’a mishi sai dai ya gayawa Dad ya fad’a mishi, ko Abban ya kirashi domin ya gaidashi baya amsawa. Sometimes kuma yayi rejecting shiyasa tun yana kira har ya zo ya daina shima. Abba yana zaune Sudais yanata zuba masa surutu ya ji k’arar wayarshi,zaro ta yayi daga aljihun gaban rigarshi ya kalla screen d’in, k’ara kalla yayi ya d’ab bud’e idonshi…ganin da gaske ne yasa yayi saurin d’auka had’e da toshe wa Sudais baki “Assa...” Kafin ya k’arasa sallamar ya ji ance “Ina falona,ka sameni yanzu” Kit!! Ya ji an kashe wayar. Mik’ewa yayi a take sai dai da kyar k’afafuwansa suka iya d’aukar sa saboda sanyi da rawar da suke yi dama kuma ga yanayin rashin lafiyar da yake ciki. Ajiyar zuciya ya sauk’e,ya tattaro dukkanin kuzarinsa sannan ya fara tafiya a hankali domin amsa kiran mahaifin nashi. Gaban Ummi ne ya fara dukan uku uku gashi Mom bata kusa…dukda sunada mafitar abinda za su fad’a amman hakan bai hanata jin tsoro ba,da kyar ta samu ta saisaita kanta gudun kar granpa ya fahimci wani abu,dukda ta san shi ba mutum ba ne mai zurfafa bincike iyakar abinda akai akan idanunsa da shi yake aiki sannan bashi da time d’in bibiyar abinda bai shafeshi sosai ba above all ya yarda da Ummi yana ji da ita sosai ba ya son abinda zai b’ata mata rai ita kad’ai ce in abu ya shafeta yake sawa ya sauk’o daga dokin zuciya…….tana cikin wannan tunanin suka ji sallamar Abba. Granpa ne ya amsa sannan yace”k’araso ciki.” Shigowa ya yi, sannan ya k’araso inda ya ga Ummi a zaune ya nemi guri ya shima ya zauna a d’an gefenta kad’an. “Barka da yamma” shine abinda Abba yace da granpa, kanshi na kallon k’asa. Juyowa granpa ya yi ya kalleshi sannan yace “Ai ban yi tunanin har yanzu Ina da darajar da zaka gaidani ba.” Bai jira jin abinda zai ce masa ba ya d’aura “Bara in baka wani gajeran labari,dukda na san ka sani amman bara in sake maimaita maka.” Mik’ewa ya yi yana dogara sandarsa ya koma wajen da su Ummin suka shigo suka sameshi d’azu ya tsaya yana kallon waje,a hankali ya fara magana........... ……. “Asalina d’an k’asar Chad ne, mahaifin mahaifiyarmu ma haka,saidai mahaifiyarta ce ta fito daga yankin Niger,Agadaz. Mu biyu iyayen mu suka haifa a duniyar nan,da ni da d’an uwana…gudun hijira ya sanya muka baro k’asarmu ta haihuwa,domin a lokacin har kakanninmu sai da aka kashe da kyar muka tsira,kasancewar Fulani bamu da yawa a yankin ya sanya aka yi galaba akanmu. A lokacin inada shekaru tara a duniya d’an uwana kuma yanada 11,tun a hanya na lura mahaifin mu bashi da lafiya,da na tambaye shi sai yace mini gajiyar tafiya ne.. Yanayin gudun hijira ba abu bane mai sauk’i don ko ruwan da mutum zai sha ma aikine. Mahaifin mu ya zab’a mu bi ta Agadaz domin mu duba ko zamu had’u da dangin mahaifiyar mamana ko zasu taimaka mana akan mu tafi garin da bamu san kowa ba. Mahaifiyarmu ta so yin tirjiya akan gara mu bi ragowar mutanen rugarmu waenda suka yi saura, saboda ta san a wannan lokacin danginta kowa yayi nashi wurin sannan y’an uwanta idan ma za ta samu yanzu mutun d’aya ce, wadda take aure a chan, don mahaifiyar tata su uku aka haifa a gidansu kuma itace auta,Babbar yayyarsu a ghana take aure. K’in yarda da zancenta da mahaifinmu ya yi ne ya sanya muka nufi Agadaz Amma sai muka yi rashin sa’a muna zuwa aka tabbatar mana ciwon k’afa ya kamata an kaita Yemen neman magani. Da kyar wani makwafcinsu ya bamu gurin kwana da abinci mukai wanka da safe muka nufi marad’i,don Yemen akwai nisa sannan babu ko sisi a wajenmu, dayake mahaifinmu ya tab’a zuwa daura ya sanya shi cewa mu zo daura ko marad’i inyaso idan ya d’an samu aiki yayi ya tara kud’i daga baya sai mu tafi Yemen d’in mu dubota. kasancewar hanyar Sahara ce ko ina,yasanya muka wahala babu ruwa babu abinci kowannenmu idan ka kalla a wahale yake Shiyasa da zaran mahaifinmu ya nemo d’an abinci ko abun sha sai ya bamu mu ci yace mana shi ya ci a hanya saboda yana gudun kar wani abun ya samemu dan a ganinsa laifinshi ne saboda babu yadda mahaifiyar mu batayi da shi ba akan mu bi tawagar y’an hijira mu gudu tare amman ya k’i. A lokacin naga amfanin ilimi domin da muka k’arasa marad’i babu wanda yake jin yarenmu, sannan muma bama jin nasu, sannan bama jin turanci ballantana mu yi communicating da su. Hakanan muka kwana a y’ar kasuwarsu da kyar mai k’osai ta bamu sadaka mukaci,da safe muka samu wanda zaije daura ya tausayamana muka bishi a motar katakon shi (kiya kiya ). Ga wahala ga yunwa ga kuma yin tafiya mai nisa a kiya kiya a wannan lokacin ba dadi . Tun kafin mu k’arasa mahaifinmu ya fara jijjiga idanunsa suka k’akk’afe, muna isa garin aka taimaka mana muka yi asibiti da shi, ba a jimaba Allah ya karb’i ransa ta sanadin rashin abinci likitoci suka tabbatar mana da cewa ya shiga hypoglycemia ne, sannan bai samu taimakon gaggawa akan lokaci ba. A lokacin bamu san kowa ba, ganin haka yasa Likitan ya nemo mutane aka sallaci mahaifin mu aka kaishi gidanshi na gaskiya, bayan ya tabbatar da mu Musulmai ne. Bayan an dawo daga mak’abarta lokacin tafiyar sa gida yayi still ya ga bamu da niyyar tashi, dan haka ya zo ya sami Mamanmu yace mata idan ba damuwa mu bishi gidanshi, kafin a san ya za a yi. Muna isa gidan kuwa matar sa tace ba za ta rik’e mutum uku ba sai dai a kaimu gidan marayu da ni da d’an uwana In yaso ita mamanmu ta dinga mata wanke wanke da shara. A lokacin rigima ce ta b’arke tsakanin Likitan nan da matarshi, domin ita tace ‘ba za ta rik’e tsintacciyar mage ba ai ya ma yi sa’a da ta yarda za ra d’auki Maman namu aiki’ Shi kuma ya dage akan sai mun zauna ai daman ba yau ta saba yi mishi irin haka ba! Taya yana miji amman ita ace ita za ta dinga zartar da hukunci. Rigima suka hau yi sosai,har ta kai ya fara ik’irarin rabuwa da ita. Ganin hakan ya sanya Maman mu tace”Ta yarda a kaimu gidan marayun In yaso idan ta yi aikin ko na wata hud’u ne ta d’an tara kud’i sai ta fara sana ‘a taje ta d’auko mu ta kama haya.’ Hakan kuwa aka yi muna kuka muna komai aka kaimu gidan marayu…. Maman mu mace ce da baka iya gane tak’memen abun da yake cikin zuciyar ta amman zan iya cewa a wannan lokacin na ga tsananin tashin hankali da k’unci a fuskarta domin kuwa itama harda kukanta. Every weekend take zuwa ta dubo mu A lokacin ne kuma yayana duk da k’arancin shekarun shi ya dage wajen koyan sana‘a, dan zan iya cewa duk wata sana ar da ake koyarwa a gidan marayun nan babu wadda bai iya ba,ba ya isheshen bacci kullum cikin aiki,idan nace mishi ya huta yakan ce mini ‘ba dan kanshi yakeyi ba,saboda ni da mama yakeso ya yi sana’a ya tara kud’i ni da shi mu koma makaranta sannan ya siya mana gida.’ A kullum maganarshi kenan. Tun muna Yara mun kasance masu tsananin k’aunar juna,soyayyar da yayana yake yi mini ba kad’an bace ba,ba ya son ya ga rai na a b’ace duk da kuwa ni d’in na kasance Miskili ne amman in dai ina tare da shi sai ya san yadda yasa na ware sosai saboda baya bari na ma har sai ya ga Ina dariya. Kamar yadda mahaifinmu ya dinga sacrifice yana bamu abincin da ya samu(lokacin gudun hijira)haka shima ya dinga yi mini a gidan marayu,gashi ya hanani aikin komai,shi yake had’awa nawa da nashi ya yi,zan iya cewa ni kam ban san wahalar gidan marayu ba kwata kwata. Mun shafe wata uku a gidan Marayu muna neman shiga na hud’u. Ranar wata lahadi muka tashi mukai wanka da sassafe muna jiran mahaifiyarmu,kasancewar ranar zuwanta kenan amman har yamma bata iso ba,sai da daddare wannan Likita ya xo ya tura aka kiramu. Muna fitowa da ya had’a idanu da mu kawai sai naga ya fashe da kuka,da sauri muka k’araso gabanshi muka hau tambayarshi amman sai bai amsa mana ba kawai ya cewa shugaban wajen yayi checking namu out zai tafi da mu. Sai da muka je gidan nasa muka gane dalilin kukanshi…ciwon zuciya mahaifiyarmu take fama da shi tun watanni uku da suka shud’e tanata nuk’u nuk’u babu wanda ta fad’awa yau kuma da safe ta yanke jiki ta fad’i jininta yai high sosai,babu irin taimakon da basu bata ba amman rai yayi halinshi. A ranar kam mun sha kuka iya kuka hatta wannan matar Likita sai da ta tausaya mana. A ranar sadakar uku ne kuma ta tada balli tace ‘sai dai mijin ta ya nemi wani wajen ko ya kama mana haya mu koma dan ba zai barta da Yara maza a gida ba bayan ita mata ne nata kuma k’anana, ai mu maza ne ko aikin k’arfi ne za mu iya mu samu mu rik’e kanmu.’ Hakan kuwa akayi Sai dai kud’in da mahaifiyarmu ta tara bai isa kama haya ba balle a had’a da Sana’a. Shawara Likita suka yi da yayana aka kama haya shima sai da ya cika mana. Gefen gidan wata tsohuwa da y’ar jikarta aka kama mana haya, sannan Likitan ya bata amanar mu. Kasancewar Yayana ya iya sana a kala kala ya sanya yake fita sana a,Allah kuwa ya sanya mishi albarka domin duk abinda yayi ko ya tab’a sai ka ga bud’u da karb’uwa ta koina dukda kuwa k’arancin shekarunshi..hakan ya sanya masu shago suka rik’esa kowa yanaso ya yi aiki da shi. Acikin shekaru biyar yaya ya bud’e shagon d’inkin sa,da wajen had’a hula da takalma, da turarurruka,sannan ya koma makaranta nima yasaka ni a makaranta,kuma cikin ikon Allah har gidan wannan y’ar tsohuwa shi yake ciyarwa,domin ta zame mana kamar uwa jikarta kuma y’ar uwa Likita kuma ya kan zo duk wata ya duba mu,haka nan muka zama kamar family. A lokacin da shekaru na suka ja,naje na samu yayana da batun inaso inyi aure don a lokacin ina matuk’ar k’aunar mahaifiyarku, kuma babanta har ya fara shirin maganar zai bata wani d’an uwanta za ai musu aure, to a wannan lokacin shima d’an uwana Ashe yanada tashi budurwa harya gama hada kudin lefe da na siyan gida da komai amman ganin yadda hankali na ya tashi yasanya ya bani kudin lefen muka je ya siya mini gida da duk wani abun da za a buk’ata, sannan ya bani wajen had’a turarenshi a matsayin kyauta yace in kula da Iyalina da shi. Both mahaifiyar ku da budurwar da yayana yake nema, y’ay’an masu kud’i ne neman auren su ba abu ne mai sauk’i ba hakan ya sanya da yayana ya nemi da a k’ara mishi lokaci ya sake shiryawa, mahaifin ta ya k’i amincewa barema da ya ji k’aninsa zai yi aure sai ya yi tunanin raina musu hankali yake son yi… haka nan yanaji yana gani aka aurar da ita kuma ya b’oye mini don ya san ba zan bari ba shi kuma ya fi son ya fi son farin cikina akan nashi. Shi ya wuce mini gaba ya tabbatar na auri Maijiddah , Likita ya yi mini wakili. Bayan nan muka ci gaba da karatu da business gadan gadan,Yaya iyakacinshi masters amman ni har PHD sai da ya tabbatar nayi, ya rik’e gaba d’aya companies d’in harda na turare na daya bani wanda a lokacin ya bunk’asa , yace zai iya inje inyi karatun nawa. Yaya bai yi aure ba,sai bayan shekaru goma mutane sunata gulmace gulmace amman ya toshe kunnuwanshi,saboda shi tunda aka aurar da wacce yake so aure ya fice mishi akai. Sai da na saka baki ni da Likita tukun ya yarda ya yi auren a lokacin har kai an Haifa. Matar Likita wadda ta dinga m korarmu a gidanta itace ta kawo d’aya a cikin y’ay’anta tace ‘ta bashi ya aura’. Don a lokacin Yaya yayi kud’i na ban mamaki,sai kuma akayi dace ya yarda don yana ganin ta ta kwanta mishi,sannan kuma ko da ace bayaso yaci ace ya karb’i y’ar Likita a matsayin mata ko dan halaccin ubanta. Tunda na yi aure nake burin in haifi y’a mace, sannan ina son in saka mata sunan Mahaifiyarmu, amman Allah bai bani ba, da kai da Yusuf da Yahaya Allah ya bani. Bayan auren Yaya kuwa da shekara d’aya aka haifi Zainab(Ummi) Da ni da Yaya ban san wa ya fi wani sonta ba gashi sunan mahaifiyarmu gareta. A lokacin ne kuma Yaya suka yi wani accident wanda akai mishi aiki aka tabbatar mana magudanar kwayayan haihuwanshi sun sami matsala,ba zai sake haihuwa ba! Mun girgiza sosai amman kasancewar mu masu tawakkali ne sai muka mik’awa Ubangiji lamuranmu muka rungumi k’addara. Abu d’aya muka sa a gaba shine faranta ran Ummi,Yaya ya tab’a gaya mini yana neman kud’ine saboda faranta raina da na mahaifiyarmu amman hakan bata faruba a b’angaren mahaifiyarmu domin mun rasa ta tun kafin ta ji dad’in da muka so bata,shiyasa yayi alk’awarin d’aura dukkan wani gata na duniyar nan akan tilon y’ar sa tunda takwarar ta ce,ya kance idan ya ga Ummi tana dariya gani yake yi kamar mahaifiyarmu ya sanya farinciki, domin kusan halinsu d’aya dan itama Ummi tun tana da shekaru biyu da y’an watanni muka fahimci tanada nuk’u nuk’u da b’oye abu a rai. Shiyasa ya zama har y’ar rige rige muke ni da Yaya wajen cika mata burinta,muddin ta furta. Shekararta biyar a duniya Yaya da Likita suka tafi Abuja,a hanyar su ta dawowa suka yi wani mummunan hatsari!! Likita tun a lokacin ya cika sai da aka kawoshi emergency yanata cewa yana son ganina… a lokacin Ina office aka sanar mini ana san ganina a asibiti tun a lokacin gabana ya fara fad’uwa,Ina zuwa kuwa a reception aka ce mini ai y’an uwanane suka yi hatsari d’ayan ya rasu d’ayan kuma yana wanchan d’akin aka min nuni da d’akin da Yayana yake ciki… A gigice na shiga inda yake,ina ganinshi cikin jini nai kanshi da gudu na rik’esa ina kuka. Dukda halin da yake ciki bai hanashi lallashi ba,sai da ya ga na yi shiru tukunnan ya kamo hannuna duka biyu yana d’an tari da nishi da kyar... Kalmarshi ta k’arshe itace Dan Allah dan Annabi ka kula mini da Zainab ka bata duk wani farin cikin da kake da iko ga amanarta nan na bar maka sannan ya yi kalmar shahada daganan na ji jikinshi ya sake idanunsa suna kallon sama. A lokacin na yi kuka mai yawa dan na rasa rabin jiki na sannan bani da kowa bani da wani bani da elder mai kula da ni. Maraicin sai ya dawo mini sabo fil.” …… Hawaye granpa ya share ya gyara tsayuwar shi yace “Ko mutuwar iyayena ban ji ta ba kamar yadda na ji ta Yaya..na yi alk’awarin faranta mishi ko bayan ranshi ko da kuwa ace hakan zai sanya in karya tawa k’aidar. Ga matarka nan,ko ka san tana d’auke da ciwon zuciya???” Ya yi maganar tare da juyowa yana kallon Abba wanda ya juya a razane yana kallon Ummi da kamar mamaki a fuskar shi. Juyawa granpa ya yi ya ci gaba da cewa “U won Yakubu, ka yi amfani da weakness d’ina and ka ci nasara a kaina! This time around,zan iya yafe maka laifin da ka yi mini tunda na ga alamar so kake ka dawo da baya yanzu. Komai ya wuce!!sannan ka rushe maganar tashinka daga estate d’innan babu ita. Abu d’aya zuwa biyu zan baka umarni shine “Ka maida matarka yanzunnan, sannan ka kaita asibiti ga katin nan,Dr yana chan yana jiranku. And Kamar yadda na fad’a maka a baya,babu kai ba Maryam,amma in dai har ka shiryawa tsinuwa ta to bismillah Ka je ka bibiyi rayuwarta.... SHARE PLS. BULAMA✍️ So da Buri Free Book 06 Shiru Abba ya yi yana so ya gano inda kalmar ‘ka maida ita!’ Ta nufa,dan bai gane ba. Fusata granpa ya yi jin yadda yayi masa shiru Dan haka ya daka mishi tsawa ta hanyar cewa “Ko baka ji na ne Abba!!!” Tuni Abba ya hau cewa “to granpa in shaa Allah..yanzu yanzu….” Duk ya bi ya rikice. Ganin hakan ya sanya Ummi share fuskarta da ta jik’e da hawaye ta faki idon granpa ganin ba su yake kallo ba ya sanya ta d’an tab’a Abba tace “Ka taso mu tafi,yake nufi.” Kallon ta Abba ya yi sannan ya mik’e ya ce “taso mu tafi.” Dan ba ya so ya fara zazzage mata ta cikinsa a gaban granpa. Har ya juya sai kuma ya dawo ya zo ta gaban granpa ya tsugunna yace “Dan Allah ka yi hak’uri na san na yi maka laifi, ka yafe mini, in shaa Allah duk abinda kace inyi zan yi daga yau ba zan sake k’etare umarnin ka ba.” Kusan 1 minute tukunna granpa ya juyo ya kalleshi sannan yace “Yafe maka da na yi ba wai yana nufin na manta da abunda ka yi bane,na yafe maka ne saboda ni kaina in samu peace of mind na zama a same environment da kai tunda ka zame mini dole, it’s all for Ummi’s sake, so idan kanada hankali do your best to keep her happy hakan ne zai sa ka gujewa b’acin rai na, ka samu mu rabu lfy. Yana gama fad’in haka ya juya ya fara dogara sandarshi har ya kai k’ofar d’akin shi ya juyo yace mata idan bai yi abunda nace ba, ko kuma ya yi trying anything stupid ki zo ki sameni.” Daga nan ya shige ya barsu a palon. Kallon ta kawai Abba yake yi, ji yake kamar ya shak’e ta ya huta, gashi ya yiwa granpa alk’awari…idan ya fahimci kalmar granpa ta ‘ka maida ita’ Tabbas Yaji Ummi ta yo Ta karkad’e zani ta kawo k’arar sa kenan. Sannan for her sake ne ma aka hak’ura zai ci gaba da zama a estate d’in…. Muryarta ce ta katse masa tunani “Doctor is waiting” Kawai tace ta kama hanyar fita tana d’an tafiya da kyar tana tari irin na marasa lafiya. Ta zo daff da fita kenan ta ji muryar gramma tana kiran Abba. Da k’arfi Ummi ta runtse idanunta domin ta san yanzu kam k’arya ta ta k’are. Kamar kuwa yadda ta yi zato gramma tana k’arasowa ta rufe Abba da fad’a akan sakin da ya yi, sannan ta hau bada umarnin ya maida ita nan take kuma karya k’ara. A rikice yake kallon gramma sannan ya juya a fusace yana kallon Ummi wadda kana ganinta ka ga mara gaskiya…gashi babu Mom a wajen bare ta ceceta, fahimtar rashin gaskiya k’arara a kan fuskarta ne ya sanya kawai ya juya ga gramma ya fara k’ok’arin fahimtar da ita. Hakan ne ya bata damar zaro wayar ta ta hau kiran Mom a rikice. Abba kuwa hak’uri ya hau bata yana ta rantsuwa a kan “shi bai san da wata maganar saki ba ma, wato shiyasa granpa ya zuciya sosai!! Haba no wonder Ai kuwa yanzu sai an koma wajen granpa an wanke shi wallahi” Ya k’arashe maganar a fusace yana kallon Ummi. A fusace itama gramma ta cillo masa takardar hannu nata tana cewa “Wallahi zan yi matuk’ar b’ata maka,bana son rainin hankali, ko a mafarki In aka tasheni na san rubutunka kai da y’an uwan ka.” Durk’usawa ya yi ya fara k’ok’arin d’aukar takardar yana kallon gramma a ransa yana cewa ‘yanzu kam ya samu mafita k’arya Ummi ta k’are!! Dama ace cewa ta yi a baki ya fad’a mata tou da da sauk’i, a rubuce kuwa ai ko hauka ake dole a gano inda rubutu ya bambam ta.’ Hannu ya kai kan takardar ya d’auka,bai kalla ba sai da ya mik’e… A take gabansa ya yi mugun fad’uwa ya k’urawa takardar idanu yana k’ok’arin tuno yaushe ya rubuta…. Tilastawa kwakwalwarshin da ya yi ne ya haddasa masa jiri ya tafi yuuuu zai fad’i. Da sauri Likita da suka shigo tare da Mom yanzu ya yi saurin taroshi yana “Be careful,wat happen again??” Ya yi maganar yana kallon su gramma. Mom kuwa rufe Ummi tayi da fad’a sosai tana cewa “Wai ke Zainab so kike ki k’arasa shi ne? Baki ji abinda Likita ya fad’a bane? Ina ce magana ta riga ta wuce? dan na tabbatar granpa ya sanya shi ya mayar da ke! To hayaniyar kuma ta mecece? “. Kuka Ummi ta saka sannan tace”Adama cewa fa yayi wai bashi baneba.” Ajiyar zuciya Likita ya sauk’e kafin yace ki kwantar da hankalinki,ba shi d’in bane” Da mamaki duk suke kallonshi. Ajiyar zuciya ya sake sauk’ewa sannan ya ci gaba “Yanzu haka takardun nan na dawo zan baku,inata sauri d’azu na hawo ba tare da itaba. Ban so shi Abban ya sani ba gudun abunda ka iya zuwa ya dawo but now I have no choice..” Hannu gramma ta mik’a mishi sannan tace “bani nan” Cikin ladabi ya mik’a mata ta saka hannu ta karb’a, Abba bai yi wata wata ba ya lek’a suka hau karantawa suna dubawa a tare. Sai da suka gama tukunna gramma d’in ta kalleshi da alamun buk’atar Karin bayani. Gyaran murya Likitan ya yi yace “Tabbas hakane,results d’in basu gama had’uwa ba sai d’azu da safe, daman a yadda na gansa yana behaving lokacin a asibiti na yi tunanin hakan shiyasa na yanke shawarar yi masa waennan tests d’in and result d’in gashi yadda nake tunani suka fito. But wannan duk ba damuwa bane ba, ku kwantar da hankalin ku, in sha Allah babu wata matsala muddin aka kiyaye b’acin ranshi… Black out ne da d’an loss of time ya samu due to stress d’in da ya saka shi misbehaving wanda hakan ya janyo mishi loss of memory,minor. Tun a lokacin da ya farfad’o na yi mishi magana sai nake ganin kamar ma bai san me ya faru ba shiyasa na d’ab bincika shi. A nuna wa granpa shima, d’azu mantawa nayi ban hawo da takardar ba, saboda yadda na ga Adama a rikice. Dan Allah a kiyaye, tun kafin In ga wannan result d’in ma sai da na ja musu kunne akan yawan b’ata mishi rai, yanzu haka kar yayi komai ya huta sosai for some days saboda kwakwalwarshi kanta ta samu sukuni, If not zai yi ta dinga loosing time gaskiya, dan abun yakan samu mutum ne mostly a old age sosai but shi gashi har ya fara,idan an yi tackling zai tsaya in ba a yi ba kuma gaskiya ban san ya abun zai kasance ba. Abba kaima amman sai ka dinga taimakon kanka sosai kana kawar da tunani, Allah ya baka lafiya.” Ya yi maganar yana dafa kafad’ar Abba wanda ya daskare a wajen. “Na barku lafiya” Ya fad’a yana mai juyawa saboda ya bar patients da yawa a clinic suna jiransa. Ahankali gramma ta ja shi ta kai parlourn sannan ta zaunar da shi ta fara lallashinshi da kalamai masu dad’i,dan ta lura maganar likita ba k’aramin girgiza shi ta yi ba, ita kanta ta girgiza ga kuma tausayin d’an nata da ya yi mata rufdugu lokaci guda. Haka itama Ummi ta shiga tausar shi da kalamai har da Mom suka taru…. Suna a haka granpa ya fito da alamun masallaci zai je dan an fara kiran sallah. “Wats going on” Ya tambaya yana mai kafe su da idanuwa. A hankali gramma ta k’arasa ta je gaban sa ta hau nuna mishi takardar da bayani daga k’arshe ta d’ora da cewa “Likita yace a guji b’ata mishi rai da abunda zai b’ata mishi ran.” Granpa bai ce komai ba ya taka gaban Abba ya tsaya sannan ya fara magana “Allah ya baka lafiya. But yadda baka da lafiya itama matarka haka, so karka bari inji wani abu ya taso daga gareka dan tabbas za a ji kanmu ba tare da na duba health problem d’in ka ba, tunda kai ne ka d’orama kanka since day 1. Kana iya nemawa kanka sauk’i ta hanyar yayewa kanka idam kuma taurin kai da tirjiya ka zab’a! Ka dai ji abinda Likita yace. Second option d’inka kuma ‘chanja uba da y’an uwa’ dan muddin nine ubanka to babu kai ba Maryam. Lokaci yana wucewa ku tashi ku wuce ka kaita asibiti.” Yana gama fad’an haka ya yi hanyar fita. A hankali Abba ya juya ya share hawayen da ya taho ta gefen idonsa ba tare da ya bari wani ya gani ba. Kamar minti biyu parlourn ya yi shiruuu… Daga baya gramma tace”su wuce kawai,Allah ya sauwwak’e.” Hakanan suka tafi ba tare da wani yace da d’an uwanshi k’ala ba. Ganin da ya yi ba zai iya tuk’i ba ya sanya shi kiran Arshaad…shi ya tuk’a su babu mai magana a motar shiru har suka isa…aka shiga da ita dan yin investigations d’in,shi dai Abba yana zauna yana mamakin ciwon Ummi Ta ya aka yi Ummi ta samu ciwon zuciya? matar da kullum burinshi ya faranta mata ko dan hakkin aure!! Sam ba ya so tana gani kamar bai damu da ita ba… Sannan ga sabuwar matsalarshi shima yanzu da akace..Tabbas ya yi mugun tsorata da jin wannan lamari dan ko lokacin da aka ce yana da ciwon zuciya abun bai tsorata shi kamar wannan ba. Kiran sallar masallacin arean ne ya sanya suka mik’e jikin su duk babu kwari.. A haka dai suka je shi da Arshaad suka yi sallah suka dawo suka ci gaba da jira yanata tufka da warwara. Muryar Likitan ce ta katse mishi tunani jin yana cewa “Ha’a Abba!!” D’agowa Abban yayi suna had’a ido da sauri ya mik’e yace “Dr ya aka yi haka? Da gaske heart problem ne da ita?” Kafad’unsa Likitan ya dafa sannan ya zaunar da shi kafin yace “Haba Abba!!Ba nace ka huta ba? Kai da akace ka zauna ko hayaniya kar ayi a kusa da kai.” Shiru yayi jin Abba yace “Granpa ne yace in kawota da kaina,shiyasa ka ganni a nan.” Mik’a mishi takardun kawai yayi sannan yace na d’aurata akan magunguna ku tsaya ku siya babu a nan,Allah ya k’ara sauki. Dan Allah ku koma gida da wuri, sannan ka huta sosai.” Yana gama fad’in haka ya yi gaba. Kallon takardun Abba yake yi yana sake maimaitawa, da gaske Ummi ciwon zuciya ne ke damun ta. A hankali ta fito daga d’akin investigation d’in, Arshaad ne yayi saurin mik’ewa ya ruk’ota ya na jera mata sannu a haka suka fito suka wuce. A wani pharmacy suka biya suka sayi drugs d’in masu mugun tsada sannan suka wuce gida,zuciyar Ummi fessss. Arshaad yana gama parking Ummi ta bud’e k’ofa ta fita ta nufi ciki,kai tsaye d’akinta ta shiga ta rufe kofa sannan ta nemo wayarta ta danna kiran Mom, bugu biyu a na uku ta d’auka. “Har kun dawo?” Shine abinda Mom tace. “Eh!yanzun nan.” Ummi ta bata amsa. “To ya jikin?” Mom ta kuma tambayar ta. Murmushi Ummi ta yi kafin tace “Ke ni kad’ai ce fa Ina d’aki ma.” Wata shu’umar dariya Mom ta yi kafin tace “Kinga amfanin beetroot yau ko??” “Hmm” Ummi tace sannan ta cigaba da cewa “Nifa na tsani abun nan, Abba ya sha gaya mini in dinga jik’awa ina sha yana k’ara jini amman ko ya saka an siyo sai dai ya bushe ko in bawa Lami idan ta tashi tafiya ta tafi da shi.” Mom ce ta katse ta ta hanyar cewa “Aikuwa yau inda ace za a gwada jinin ki da kaf estate d’innan sai kin iya yi musu donation.” Dariya itama Ummin ta yi kafin tace “Aikam!! Ni da akace in dinga jik’awa Ina sha, yau nice na dinga taunashi Ina fitar da ruwan Ina had’iye tik’ar..” A tare gaba d’ayan su suka kwashe da dariya kafin Ummi tace “Adama thankyou, komai ya tafi according to plan,zan shigo anjima. Yanzu bara in je in wanke hannuna, kafin abin nan ya zame mini k’unshi… Yau ba dan hijabi na saka ba da babu abunda zai hana asirina tonuwa.” “Ok.” Kawai Mom tace mata sannan ta kashe wayar tana dariya. Ummi, tana fitowa daga toilet ta gama wanke hannunta tana tsane wa da towel ta ji bugun k’ofa… Ko ba a fad’a mata ba ta san Abba ne, dan haka ta d’an tsaya a gaban mudubi ta duba fuskarta kafin a hankali ta je ta bud’e mishi. A hankali ya shigo ya k’arasa bakin gadon d’akin ya zauna jikinshi duk a sanyaye. Sai da ya d’ago ya kalle ta sannan yace “Zo nan ki zauna, we need to talk.” Sum sum ta zo ta zauna a daf da shi sannan tasa hannayenta ta kamo nashi tun kafin tace wani abu a hankali yace “I’m sorry,so sorry! Ga drugs d’inki nan ki dinga sha akan time dan Allah And, I think zan tafi Uk.” Da sauri Ummi ta kallesa. Bai bata daman yin magana ba ya ci gaba da cewa “I want to go and check on Aslam dama, dukda yace mini zai d’an lek’o soon amman I just want to go and check on him Sannan Ina buk’atar serious investigation Ina tunanin za mu biya a yi mini checkup d’in a chan. Ummi I’m scared, so scared… kun ce na yi wuni d’aya ina misbehaving I even slapped you,and...” Sai kuma yayi shiru,d’an numfashi ya ja sannan ya ci gaba “What if brain d’ina ya fara samun matsala ne? What if I hurt someone in the process?” Da sauri Ummi ta d’aura hannunta a kan bakinsa sannan tace “Abba duk fa zafin ciwo ne, ai tun ranar ya yi checking naka sosai, kowa ya tsorata matuk’a da marin da ka yi mini tunda baka tab’a yi ba. Ko d’azu ya tabbatar da zafin ciwo ne kawai nothing else, pls ka kwantar da hankalinka And I’m so happy da ba da gaske kake zaka iya rabuwa dani ba…I was scared hankalina ya tashi sosai shiyasa na tafi wajen granpa, I’m sorry for that,ba zan k’araba Ka yafe mini.” Tayi maganar tana murmushi tare da sake matse hannunshi dake a cikin nata. Ganin da ta yi yayi shiru yana sauraronta ne ya sanya ta yi ta lalallashinsa, had’e da tsarashi…. Ba ta barshi ba sai da ta tabbatar ya nutsu kuma ya yarda da maganganunta.............. Gandun Albasa Yau sunday,Jalila na gida kasancewar babu makaranta. Tun safe take k’ulle k’ulle akan abunda zata yi domin chusgunawa Mama.. Kamar an tsikare ta kuwa ta mik’e daga kan katifar da take kai ta fito tsakar gida kanta ko d’ankwali babu gashi ba kitso a kan gashin nan ya zubo wani yayi baya wani ya zubo ta gefen kafad’arta har saman k’irjinta.. Tana fitowa Ya Ja’afar ya na shigowa cikin gidan..ya bugu ya yi nak!! yana tafe yana layi. “Ke!!!” Ta ji ya ce mata. Tsaki ta yi kafin ta juyo ta kallesa tace “menene?” Aikuwa kamar jira yake ya nufota, yana tafe yana magana cikin layi da muryarsa wadda ke fita da kyar yace “Ni kike yi wa tsaki?? Amman Yarinyar nan baki da kunya! Kalli kanki ko d’ankwali babu, so kike ki shiga wuta?” Tsaki ta k’ara ja,kafin tace “Wallahi Ya Jafar kana da damuwa! Ni yanzu ka wani kama ka shigo za ka b’ata mini plan.” Tayi maganar tana lek’en hanyar kitchen tana so ta hango ko Hudan na chan ta fara wanke wanken ta kasancewar yau Mama ke da girki…ai kuwa chan ta hange ta a tsugunne bakin rijiya hanyar toilet har ta kusan gamawa. Ajiyar zuciya ta sauk’e sannan cikin sauri ta juya za ta nufi inda take ta ji Ya Jaafar ya rik’o hannunta yana cewa “Ke Jalila, ban gama da ke ba. Dan ke kin samu Ina sarara miki bana laftar ki kamar waccar Hudan? to kema idan ba so kike yau ki ji a jikinki ba ki biya ni kamar yadda kika saba, ko yanzun nan in sauya miki halitta. Dan ke na lura dake duk wani aikin zunubi kin iya Kina yawo babu d’ankwali Sannan Ina a matsayin Yayanki amma kina yi mini tsaki Gashi yau na ga alamar baki da niyyar sallamata.” Jalila kam zuwa yanzu ta k’ule sosai tana k’ok’arin kwace hannunta tana juyawa tana kallon Huda wadda ke aikin ta cikin nutsuwarta kamar yadda ta saba, har ta juyo za ta yi mishi masifa sai kuma wata dabara ta fad’o mata. Murmushi ta yi sannan tace “To naji,zan baka kuma yau naira d’ari ma zan baka.” Ai kuwa ba shiri ya hau fara’a yana mai sakar mata hannu yace”To to,kin ceci kanki, maza je ki d’auko.” Juyawa ta yi cikin gudu ta fad’a d’akin nasu…so take ta samu ya kyaleta kafin Hudan ta k’arasa aikin ta dan wallahi yau sai ta kifar da kayan wanke wanken nan a cikin chab’in bakin rijiya tunda ta yi niyya. Tana d’aga k’asan pillown ta, ta ci karo da naira Hamsin bayan ta san d’ari ta ajjiye a wajen(Hamsin biyu) Tsaki ta yi tace “Umma!!! Na san d’azu da za ta tafi gidan Baba Laraba ne ta d’auke mini, aikuwa bara ta dawo sai ta biyani, da ace ta san kalar k’arya yunwar da na yiwa malamin maths shekaran jiya a makaranta ya bani d’ari uku, da ba zata tab’a mini kud’iba. Cikin mita ta d’auko Jakarta ta makaranta ta zaro littafi ta bud’e tsakiyan,ta ci karo da y’an chanjin hamsin da ashirin. Tsaki ta ja ta ci gaba da mita “Gaskiya Umma ta b’ata min budget,yanzu ga wanchan shima yana jirana,dama tunda na dawo taketa faman tambayana ko na yi chanji na san kud’i takeso..in banda abun Umma ko me naira hamsin zata yi mata oho… yanzu na san Ina tambayar ta cewa za ta yi cikawa tayi suka yi kud’in mota ita da Baba Laraba…..” Tanata mita haka ta d’auko ta fito. D’an juyowa tayi jin motsi a bayanta suka hada ido da Mama da take k’ok’arin yafa mayafi ga jaka a hannunta kana gani ka san fita zata yi kuma cikin sauri take. “Kaii!! Allah yana sona.” Shine abinda Jalila ta fad’a a ranta,dan har wani plan d’in ya kuma zuwa kanta ganin Mama fita zata yi, “plan har biyu yau akwai show a gidannan” ta fad’a a k’asan zuciyarta “Huda! Huda!” Mama ta kwala kiran Huda.. Da saurinta ta iso inda Maman take tana goge hannunta da gefen zanin jikinta. Mama da ta k’araso tsakar gidan ce tace “Zan fita,yanzunnan Ummu ta kira ni Sumayya ba lafiya ciwon ciki takeyi tun safe har da suma.. Sun je asibiti an mata allura ance ta je gida ta huta, yanzu suna gidan Hajiya Shuwa. Zan je in dubo ta.” Shiru Huda ta yi, ganin Mama ta kama hanyar fita ya sanya tace “Mama dan Allah zan biki nima in dubo jikin nata.” D’an tsayawa Mama tayi ba tare da ta juyo ba tace mata “A’a, ki k’arasa aikinki…yanzun nan zan dawo.” Takowa Hudan ta yi ta d’an biyota murya kamar zata yi kuka tace”Mama na gama, share wajen kawai zan yi in d’auko hijabina.” This time around da fad’a Mama tace “A’a” Still bata juyo ba. Dariyar Jalila ce ta sanya Mama juyowa. Cikin wata irin dariyar raini Jalilan tace “Kai, amman Hudan ban tab’a ganin dabba mai kwakwalwar kifi kamar ki ba, shiyasa fa muka bawa Baba shawara ya cire ki a makaranta dan asarar uniform da kud’in break kawai za a dinga yi. In banda abinki, kwanaki fa har gidan nan ita kanta shuwa ta zo ta samu Baba tace ‘kar ya k’ara barin ki ki taka mata k’ofar gida, tunda shi ya ga zai iya rik’e ki ya je yai ta yi ita bata buk’atar ko ganin ki’.” Shiru duk suka yi ba wanda ya tanka mata illa Mama da ta juya ta fara k’ok’arin saita kanta ta hanyar danne abunda take ji yana taso mata. Jalila kuwa, cikin takun ta ta k’arasa gaban Hudan ta tsaya sannan ta ci gaba da cewa “Ba ta son ganinki a gidanta, ba ta son ki Hudan, duk ba’a son ganinki kowa ba ya sonki. Yanzu ki bar Mamanki ta je gidan, Allah yasa itanma kar Shuwa ta yi mata korar kare! Ki je ki ci gaba da wanke wanken ki kinji k’anwata.” Ta yi magnar tana dafa ta sannan tace “Domin shi aka haifo ki duniya, da shara da ragowar ayyukan gida.” Sharkaf haka fuskar Huda ta jik’e da hawaye, da sauri ta juya ta nufi d’aki tana goge fuskarta. Murmushi Jalila ta yi, sannan da d’an k’arfi yadda ta tabbatar za ta jiyota tace “Shegiya kawai.” Sarai kuwa Maman ta ji ta amma ba ta ce komai ba kafin ma Jalilan ta juyo ta yi sauri ta fice daga gidan tana share hawayen fuskarta. Ganin Mama har ta fice yasa ta ce”In kin gama kukan munafurcin ki yi sauri ki fito ki k’arasa tattare wajen wanke wanken nan, dan har k’udaje sun taru.” Sannan ta juyo ta mik’awa Ya Ja’afar naira hamsin. Karb’a ya yi ya jujjuya ta kamar yana neman wani abun a jikin hamsin d’in kafin yace “Hamsin nake gani!” “Eh,ai wai da d’ari nace zan baka, yanzu kuma sai na ga sauran ashirin da hamsin biyu shine zan baka naira hamsin sai a siyo mana zob’on saba’in a gidan mai tuwo tuwo.. Kaga kenan Naira d’ari da ashirin ma na baka.” Shiru ya yi yana son ya had’a lissafin amma sam sai ya gagara…ganin hakan yasa tace “To bani kud’ina na fasa, kawai yau daki kud’inka.” Da sauri yace “A’a, barshi kawo in je In siyo.” Kallonshi ta yi kafin tace “Wato har ka manta da bashin da take binka ko? Ranar nan fa har gidan nan waenan k’artin mazan masu tuk’a mata tuwo suka biyoka za su dakeka, da kyar Baba ya basu hak’uri.” Shiru yayi kafin yace “Kuma fa hakane,to yanzu ke zaki je kenan?” Da ido Jalila ta nuna masa Huda wadda ta fito yanzun nan tace “Ai ga k’arama chan,sai ni za ka aika? tsoronta kakeji ko?” Da sauri yace “Haba deee!! a’a.” Ganin ta fara cin nasara,ya sanya ta ci gaba da cewa “To kirata mana ga kud’in ka bata, amman wannan Yarinyar ma na san k’arshenta tace ba za ta je ba saboda d’azun nan na ji Mamanta tana cewa indai ka sake aikenta kar ta je , kuma idan ka daketa ta rama!!” Ai tun kafin ta k’arasa ya wafce kud’in ya hau kwalawa Huda kira yana hura hanci. Da saurinta ta k’araso tana “Na’am” tace “gani” Kud’in ya watsa mata yace ‘maza ta je ta siyo mishi zob’o a gidan mai tuwo tuwo’. Zaro ido ta yi kafin tace “Maama ta hanani zuwa gidan saboda akwai y’an shaye shaye da maza da yawa, kuma ni ban ma san hanya ba yanzu.” Cikin zuga Jalila tace “Ai dama na san za a yi haka, ka ji ko?” Sai kuma ta kalle ta tace “Tukunna ma shaye shaye me kenan??” Ba ta jira ta bata amsa ba tace”Yaya irinfa d’an maganin ciwon kan nan da kake sha yake d’an saka ka jiri shine take zagi! Tab!! kaga kenan ta had’a har da kai ta zage tasss!!!.” Ai kuwa Jalila ta yi nasara dan Ya Ja’afar cewa yayi “wallahi yau idan Huda za ta suma sai ta je kuma wallahi ta dawo gidan babu zob’on gidan mai tuwo tuwo sai na lahira ya fita jin dad’i.” Hakanan tana kuka tana komai ta zo ta wuce, sai da ta kai k’ofa ta juyo tace “Yaya Jalila dan Allah to ko kwatance ne ki yi min.” Cike da son sake dilmiyar da ita Jalilan tace “Idan kika fita ki mik’e, ki yi kwana sau bakwai sai ki yi tambaya.” Haka kawai Jalilan tace da ita sannan ta juyo tai hanyar d’aki har ta tura k’ofar sai kuma ta juyo Sanin cewa Huda bata da wayo kwata kwata, tunda ba shiga mutane take yi ba ya sa tace mata “Kuma saura ki biya gidan shuwa ki kai k’ara, ranar da kunne na na ji tace ‘sai ta yanka ki a duk ranar da kika yi gangancin zuwa mata gida’.” Hawayenta ta share cike da fargaba da tsoro ta juya ta fita daga gidan. Kamar yadda Jalilan ta yi mata kwatance haka ta yi amman sai aka ce mata ‘ai nan arean kwata kwata babu gidan mai tuwo tuwo’. BULAMA✍️ So da Buri Free Book 07 Tun 11 na safe take bulayin neman gidan mai tuwo tuwo har 4 na yamma bata samu ba, kusan kaff Unguwar ta Gandun Albasa har kwargiji da wajejen Gada duk babu inda ba ta duba ba. Ganin ta kusa shiga g r a d’in Sharad’a ne ya sanya ta koma da baya ta ci gaba ta kutsa kai tana nema. An nuna mata gidan mai tuwo tuwo har biyu amman ba nan bane ba kuma su ba sa siyar da zob’o. Idan ka ganta sai ka tausaya mata, duk ta yi wujiga wujiga ga yunwa ga gajiya sannan ga k’ishirwa. Tana cikin tafiya ta ga ta fara hango kwandila a tsallaken titin side d’in da take, sanin da ta yi cewa gidan mai tuwo tuwo ba a kwandila yake ba ne ya sanya ta yanke shawarar komawa gida kawai! Ko da kuwa Ya Ja’afar zai kashe ta da duka ne. Har za ta juya sai ta hango tuk’a tuk’a, k’ishin da take ji yasa ta yanke shawarar ta tsallaka ta sha ruwan inya so sai ta tsallako ta koma ta tafi gida. Da kyar ta samu ta tsallaka, ta rok’i wani almajiri ya buga mata, ta samu ta sha. Ta gama sha kenan! D’agowar da zata yi sukayi ido biyu da wani mahaukacin kare, da alama shima k’ishin ruwan yake ji dan ya k’urawa ragowan ruwan da bai gama tsiyaya ta kan famfom tuk’a tuk’an ba ido. Yunk’urawa ya yi ya tunkarota cikin sauri, ai kuwa babu shiri ta nannad’e zanin jikinta ta kwasa a guje, a tunanin ta ita ya biyo. Shikuwa Karen ganin ta hau gudu kamar jira yake yi kawai sai shima ya bita a guje….. Tsere suke zubawa ita da Karen nan tana ihu tana neman Agaji, musamman ma da ta tuno da wata magana da Sakina ta tab’a gaya mata “Indai kare ya kama saman dunduniyar k’afar mutum ta baya to cirewa yakeyi gaba d’aya. Kai da tafiya har abada.” Ai kuwa nan ta k’ara k’arfin gudun nata…. Wasu su yi mata dariya wasu su ji tausayinta wasu kuma ta basu mamaki….gatanan dai doguwa kyakyyawa y’ar budurwa da ita amman ta zage tana tik’ar gudun ceton rai a wajen Kare. Ganin da tayi k’afafuwanta sun fara zafi sosai, gashi ta gaji!! Ya sa kawai ta yi kalmar shahada ta tsaya chak! sannan ta juyo ta durk’usa…dai dai Karen ya iso dab da ita, ta rufe idanunta da mugun gudu da k’arfi ta hau had’ashi da Allah tana cewa “Dan Allah dan Annabi ka yi hak’uri, kar ka cijeni, na gaji ka yi hak’uri…” Ta kusan mintina 2 a haka.. Jin shiru yasa ta bud’e idanunta a hankali k’irjinta na dukan uku uku. Cikin ikon Allah kuwa babu Kare babu alamar shi. Hamdala ta yi ta mik’e da niyyar tafiya gida…sai ta ganta a tsakiyar kwandila. Layin shiruu ba kowa sai maka makan Gidaje, mota d’aya ta hango a k’ofar wani had’add’en gida da alamar mamallakin motar yana jira ne mai gadi ya bud’e masa ya shige. Bayan wannan motar babu komai kuma babu kowa a layin. Dubawa ta yi sosai ta ga ba ma ta san a ina take ba, sai a lokacin ta fashe da wani irin kuka ta zauna dab’ass!! A wajen ta cusa fuskarta cikin cinyoyinta....... Bai dad’e da shigowa cikin Unguwar ba, akwai wasu takardu da Abba ya sanya shi zuwa ya d’auka dan yana son yin amfani da su kuma har an tarkato an kawo sabon Gida. Yana shirin danna horn kenan ya ji kamar ihu!! Kasancewar bai rufe gaba d’aya glass d’in motar tasa ba. Yana kallon direction d’in da ya jiyo ihun nata kuwa ya hango ta ita da Karenta. Da farko abun dariya ya bashi, sai kuma ta fara bashi tausayi…da har zai je wajenta sai kuma ya fasa ya dannawa sabon mai gadin da aka saka a Gidan horn ya bud’e masa ya shige. Bai b’ata lokaci ba ya shiga, inda takardun suke ya je ya d’auko ya fito ya shiga motarsa ya sake yin horn aka bud’e mishi gate d’in ya nufi waje. Kamar ance ya juya, yana juyawa ya ganta this time around ta cusa fuskarta tsakiyan cinyoyinta kuma babu Karen a wajen. Kawai tsintar kansa yayi da son zuwa wajen ta, da farko kamar ba zai je ba sai kuma yayi tunanin inda Aaima ce a wajen ai da ba zai so a barta ita kad’ai haka ba. D’an rivers ya yi sannan ya karkata hancin motar ya nufi inda take. Yana isowa ya d’an tsaya, ya kasa fitowa kawai yana kallonta, dan ji yakeyi kamar ya juya. Ya d’an jima a haka sai kuma yayi tsaki ya bud’e motar ya fito ya zo ta gabanta ya tsaya. “Hey!!” Ya ji shiru…sake maimaitawa yayi tukunna a hankali jin kamar mutum a tsaye a kanta yasa ta d’ago fuskarta wadda ta jik’e da hawaye tana kallonsa. Da k’arfi ya ji zuciyarsa ta wani irin bugawa sakamokon had’a idanun da suka yi, ita kuma ganin sa da tayi ya sanya da saurinta ta mik’e tana karkad’e zaninta d’ayan hannun kuma tana goge hawayen da ya k’i tsayawa da bayan hannun. Tsayawa yayi yana k’are mata kallo a ransa yace”Who’s she?? How can someone be this beautiful??.....” “Ina yini” d’in da tace masa ne ya dawo da shi daga duniyar lissafi da k’are mata kallon da ya tafi. Da kyar ya iya tattaro kalmar “Alhamdulillah” Dan zuciyarsa bugawa take yi ba kad’an ba. “Dan Allah ka san hanyar gidanmu?” Ya sake jin muryarta. This time around sai da ya lumshe idanunsa ya bude tukunna ya iya ce mata “A’a, why are you crying?”. Ta fahimci tambayar da yayi mata, dukda cewa a iya primary ta tsaya. Amman kuma sai ta tsinci kanta da kasa bashi amsa…ta ga yawan maganarsa turanci ne, kar taje ta bashi amsa da Hausa ya kasa ganewa kuma tana tsoron yin turanci dan ba wani iyawa ta yi ba, kar taje yayi mata dariya kamar yadda su Ya Jalila suke mata a duk lokacin da ta yi turanci. Ganin ta yi shiru yasa ya fara tunanin ko bata jin turancin ne domin kuwa yanayin duk’unk’unennen hijabinta da kod’add’en zanin jikinta kad’ai sun isa su fad’awa mutum ita d’in ba wata shahararriyar y’ar Boko bace ba. Dan haka ya yanke shawarar maimaita mata tambayar da Hausa. “Me ya saka ki kuka??” Da mamaki a fuskarta, ta ke kallon sa jin Hausar tasa tarr!! A ranta tace “To ko dai koya yayi??” Dan tabbas ita dai ta san wannan ba bahaushe bane ba, ko dai balarabe ko kuma d’an India , Saboda yanayin cikar gashin kansa, gashi a kwance sai kyalli yakeyi, shigen na larabawa, gashi fari sosai, dukda cewa itama bakinta pink ne amman ta san nashi ya fi nata zama pink sosai, ga hancinshi mai kyau d’an dogo, sannan idanunsa irin manyan nan kuma a kwance dogaye, kuma wani ikon Allah yanayin shape na gashin girarsu iri d’aya..ba irin cika d’innan ne da girarba, amman shape d’inta na medium arch ya fito sosai…… Shi kam Arshaad zuwa yanzu ya fara tunanin ko dai kurma ce Yarinyar nan?! To amman kuma ai d’azu har gaida shi ta yi. A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya ya sake ce mata “Umm?” Yana mai tsare ta da idanuwa dan yaga kamar ba ta ji na farkon ba. K’asa ta yi da kanta ta fara wasa da y’an yatsun hannunta kafin tace “Ya Ja’afar ne yace in siyo mishi zob’o, na manta gidan, tun Ina Yarinya aka hanani zuwa, kuma yanzu na b’ata.“ Ta yi maganar tana share siririn hawayen da ya zubo mata da bayan hannunta. Shi kam he don’t know Y amman yanayin maganarta burgesa yake yi, komai nata a nutse take yinsa, ya dad’e bai ga mace mai magana cikin nutsuwa da kamewa ba kamar ita. A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya ganin ta d’ago kai ta kalleshi a karo na biyu bayan gama yi masa maganar, sai kuma ta sake yin k’asa da kanta ta cigaba da goge hawayen. Wani white handkerchief ya zaro daga cikin aljihunsa ya mik’a mata. Da farko k’in karb’a ta yi sai da yace “Ungo ki goge fuskar ki,ya b’aci da yawa da hawaye, Yara za su yi miki dariya.” Tukunna a hankali ta sanya hannu ta karb’a ta fara goge fuskarta tana lumshe idanu saboda wani fitinannan k’amshi da yake shigar mata hanci. Sai da ta goge hawayen tass sannan yace “Zo,mu je ga mota sai in kaiki Gida.” A hankali ta girgiza masa kai sannan tace “Ban san ka ba, ba zan shiga motar ka ba.” Wani d’an cute smile ya yi, kafin yace “To in tarar miki napep za ki shiga??” Da sauri ta d’aga mishi kai alamar ‘eh’. Smiling ya yi har sai da hak’oransa suka d’an baiyyana, sannan yace “To shi a ina kika sanshi? me napep d’in!” Rau rau ta yi da idanunta, har za ta yi magana sai kuma tayi shiru tana wasa da yatsun hannunta, dan bata da amsar da za ta bashi. Ganin hakan yasa yayi locking motanshi daga inda yake da key d’in, sannan ya fara tafiya yace “mu je In saka ki a napep d’in.” Da saurinta ta bi bayanshi…a hanyar yake tambayar ta sunan ta, tace masa “Huda.” Basu wani dad’e suna tafiyar ba, tun kafin su fita a kwandila suka samu napep, ta fad’a mishi inda zai kaita ta shiga. D’an sunkuyowa ya yi yana kallonta a cikin napep d’in…ji yake kamar kar su rabu amma da ya tuna ya ji sunan layin Gidan nasu yanzun har ma da d’an guntun kwatancenta da ta yiwa mai napep d’in duk ya haddace. Sai kawai yace mata “ki gaida gida da su Mama.” Daga haka ya zaro 1k a aljihunshi ya bawa mai napep d’in, kafin ya yi waving nata yana smiling suka yi gaba suka barshi a wajen. Har ya isa inda motarshi take ya shiga ya ja yai gaba, yana smiling. Ita kuwa Huda mamakin kyau da had’uwa da gayunshi take ta yi, dukda ta san su Ya Junaidu ma kyawawa ne sosai amman wannan kam ya fi su, gashi da kirki. Ahaka suka shigo layin su, ta nuna k’ofar gidansu aka ajjiyeta. K’irgo y’an chanji mai napep d’in ya yi(950), har ta d’an yi gaba ya kirata ta dawo ya mik’a mata. Sai a lokacin ta ji gabanta ya fad’i domin kuwa ta san tabbas ba za ta b’oyewa Mama abunda ya faru ba, gashi kuma har da sakota a napep har k’ofar gida, ta ina za ta fara bayani, waye shi?? ya aka yi ma ta sake da shi haka bayan jan kunnen da Mama ta sha yi mata a kan maza!? Mai ya sa duk wannan tunanin ba su zo mata ba d’azu??. Muryar mai napep d’in ce ta katse mata tunanin da take yi “Ungo mana, ko bakya so?” D’aga mishi kai ta yi a hankali tace “Ka rik’e na bar maka.” Daga haka ta juya ta nufi gida da sauri. Tana d’ago kanta gabanta ya fad’i da k’arfi sakamokon had’a ido da suka yi da Baba ya hard’e hannayenshi a k’irji ya jingina da jikin bangon gidan da tafin kafarshi kwaya d’aya da bayanshi, yana kallonta yana kallon mai napep d’in. Da sauri ya d’ago daga jinginar da ya yi ya zira silifas d’insa guda d’ayan wanda ya cire ya jingina da k’afar, ya tunkari mai napep d’in da yake shirin buga mashin d’insa ko gaisuwarta bai amsa mata ba. A hankali ta tura k’auren ta shiga…tun daga soro ta fara jiyo maganar Jalila da Umma, Umma tanata masifa Jalila na zugata, tana ida shiga tsakar gidan kuwa ta hango Mama a zaune a bakin k’ofar d’akinsu tana kuka, Ya Junaidu ya durk’usa a ta gefenta da alama hak’uri yake bata, Umma sai ce masa take yi “shanyayye!! ya tashi a wajen kafin ranshi ya b’aci!!” Jalila kuma tana cewa “ai dama ya fi son Mama a kan Umman tasu. Sallamarta ce ta sanya duk suka juyo suka zuba mata idanu. Ganin Mamanta na kuka yasa da sauri ta yi inda take ta durk’usa a gabanta ta saka hannu ta hau share mata hawaye. D’an kama hannunta Mama ta yi sannan ta goge hawayen da d’ayan hannunta kafin tace “Daga ina kike? ya aka yi kika dad’e? Jalila tace Ina fita kema kika fita.” Mama ta jero mata tambayoyin tana kafeta da idanu. Za a wani tsaya ana yi mana kukan munafurci kamar ba ki san Ina ta tafi ba!! Kawai ke dai kice baki san waye saurayin ba amman sarai kin san me ta je ta yi.” Cewar Umma sannan ta d’aura da cewa “Yo Allah na tuba daman Yaran yanzu ka haifo su ta hanya mai kyau ma ya aka k’are, ballantana ta hanyar da ba ta dace ba!!”. Da k’arfi Mama ta runtse idanunta wasu zafafan hawaye suka shiga tsiyayo mata… Umma bata damu ba ta ci gaba da cewa “Sannan sai ki dinga goya mata baya tana abubuwan da ta ga dama idan anyi magana ki ce sharri aka yi mata saboda bakin ku d’aya ko?? Kina samu tana kawo miki taro da sisi.” Hudan ce ta mik’e ta k’arasa kusa da Umma tace “Umma dan Allah ki yi shiru kinga fa maganar ki yadda take saka Mama kuka.” D’an zaro idanu Umma ta yi kafin tace “Eh lalle Yarinyar nan kin rik’a!!!! Ko da yake ba zan ga laifin ki ba, yanzu ai gani kike yi daidai kike da ni tunda duk abinda na sani kema kin sanshi, zafin ciwon nak’uda kawai ya rage.…..” Da sauri Mama itama ta mik’e ta k’arasa daff da Umma ta ce “Dan Allah dan annabi Sadiya ya isa haka! Za kisa Yarinya ta san abunda shekarunta ma basu kai ba, tun d’azu kinata aibantata da bakinki kuma yanzu kin zo kina irin wannan maganar a gaban Yara saboda Allah.” Mamaki ne ya cika Umma saboda ta dad’e ba ta ga b’acin ran Mama kamar haka ba, cikin matsowa kusa da sosai itama tace “Lalle Maryam!! na jinjina miki. Son y’arki ya rufe miki ido har kina gaya mini magana dan na fad’i gaskiya??”. Mama bata bari ta k’arasa ba tace “Wallahi ba gaskiya kika fad’a ba!” Sannan ta juya ta kamo hannun Huda wadda take ta kuka ganin ana fad’a a kanta, ta kawo ta gaban Umma tace “Zan iya dafa Al Qur’ani akan sharri kuke yi mata, Allah ne shaida ta na san kalar tarbiyyar da na yi mata. Idan kuma kina da shedar da zaki tabbatar da abinda kike cewa gaskiya ne to Bismillah Ina sauraron ki.” Hudan garin k’ok’arin goge hawaye bata saniba handkarcheif d’in da Arshaad ya bata ya fad’o k’asa! Karaf! kuwa a kan idon Jalila, da sauri ta k’araso inda ta ga handkarcheif d’in ya fad’i,har tana gurd’ewa. Duk sai suka zubawa inda ta nufa ido, cikin sauri ta durk’usa ta d’auka,sai a lokacin Hudan ta lura aikuwa ta fara rarraba ido gabanta na mugun fad’uwa kana ganin ta ka ga mara gaskiya. K’arasowa Jalilan ta yi kusa da Mama, dai dai fuskarta ta d’ago handkerchief d’in ta yi mata fifita da shi a dai dai setin fuskarta kafin tace “kowa dai ya ga lokacinda ya fad’o daga hannun Huda ko? Tambayata a nan itace ‘shin a ina kamila nitsatstsiya Huda ta samu handkerchief mai kyau haka da k’amshin turare wanda na tabbata na maza ne?’.” Ya Junaidu wanda kishi ya turnuk’e sa a take ne, yace “Kawo in gani!” Mik’a masa ta yi ya k’arasa warewa…Farine tas! Hanky d’in, kana gani ka ga had’add’en personalize handkerchief, ta chan k’asa an rubuta ‘AY’ da wani had’add’en glitter gold, ga uban k’amshin da yake ta zubawa na had’add’en designer perfume. Da kyar ya samu ya d’an yi controlling temper d’inshi tukunna ya kalli Huda yace “na waye???“ Ya yi mata tambayar yana tsareta da manyan idanuwanshi da suka fara chanja kala. Shiru Huda tayi ta fara goge hawayenta da suke zuba a yanzun babu k’akk’autawa. Mama ma da gabanta yake ta fad’uwa tana kiran sunan Allah da k’ok’arin kawar da mugun tunani akan y’artata tace “Huda tambayar ki fa akeyi, kin yi shiru ki bamu amsa!” Baba wanda ya shigo yanzu ne yace “Ku barta ai ba zata tab’a cewa komai ba! Gani nan, ni ne zan baku amsa!.” BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 08. Duk juyowa suka yi suna kallonshi da mamaki a kan fuskokinsu. K’arasowa yayi ya kalli Mama yace “Nace miki Yarinyar nan yawonta ta tafi irin wanda kika yi amma kin k’aryata ni ko?? To mai adaidaita sahun da ya kawota shi na bi na tsare na tambaya ya kuma tabbatar mini da cewa ‘Ita da wani saurayi dogo fari tass suka tsaida shi a wajen kwandila, bayan ta shiga har yana ce mata ta gaida su Mama har ya bada dubu d’aya a kawota, da mai napep d’in ya bata chanji tace ta bar masa.’ Haka akayi ko ba haka ba?” Ya k’arashe tambayar yana kallon Huda wadda jikinta a yanzu yake mugun karkarwa ga hawaye sai zuba sukeyi ta gagara controlling d’insu. Mama ce ta k’arasa ta kamo hannunta ta share mata hawaye sannan a hankali tace “Huda da gaske ne abinda mai napep ya fad’awa Baban ku? Dan Allah kar kiyi mini k’arya.” Addua Mama take yi a ranta Hudan tace mata ‘A’a’ amman sai taga tana d’aga mata kai alamar ‘Eh’. Wata uwar gud’a Umma ta rangad’a sannan tace “Huda Allah dai ya yi miki albarka, gwara da kika fara fitowa fili kina fad’in gaskiya, yanzu sai a daina janta d’aki a na b’oyewa.. Don kowa yanzu ya san hali! har shi Junaidu mai goya mata baya yau kam ya ji kuma ya gani. A bi dai a hankali kar a kwaso k’anjamau.” A fusace Mama tace “Bana son mugun alkaba’i, dan an ganta da wani sai kuma akace wani abun ke tsakaninsu?? Ki fad’i alkhairi ko ki yi shiru mana! Mai ya kawo maganar k’anjamau a nan?” Baba ne yace “Wallahi Maryam zan yi mugun sab’a miki!!! Ya da girman mu kina raina mana hankali? Uban mai ya had’ata da shi to da har ya sako ta a adaidaita sahu? To bari kiji in gaya miki!! Malam Iro mai kayan Miya da kika rainawa arzik’i kika hana shi auranta, yanzu zan je ince ya turo!! Dan ba zan zauna Yarinya ta lalata mini gida ba. Amman kafin nan sai na sauya mata kamanni ta yadda shi kansa d’an iskan saurayin nata ba zai iya ganeta ba, kuma gobe ko ance ta je ba za ta je ba.” Junaidu ne ya sha gaban sa ganin ya yo kan Hudan, kafin yace “Baba a yi bincike dan Allah, kar a yi saurin yanke hukunci.” Cikin fushi Umma tace “tou shanyayye!! binciken me kuma bayan wanda akayi?” Da sauri yace “Umma mu tambaye ta mana mu ji, kina gani fa bata b’oyewa kowa ba ta fad’i gaskiya bata k’aryata mai adaidaita sahun ba, ko?” Yanzu wannan munafukar Yarinyar za ka tambaya??? Kuma kana zaton za ta fad’i gaskiya? Tou Bismillah bari mu ji.” Umman tace tana mai gyara tsayuwarta da d’aurin d’ankwalinta. Ahankali cikin nutsuwa Junaidu ya tambaye ta “hanky d’in na waye? sannan waye wannan mutumin da aka gansu tare,a ina ta sanshi?” Amsa d’aya ta iya bashi, “hanky d’in na mutumin ne amman ita wallahi ba ta sanshi ba.” Ta kuma bashi labarin tun daga yadda kare ya biyo ta har lokacin da ya sakota a adaidaita….. Dariya Umma da Jalila suka saka kafin Jalila tace “Lalle Huda kin cika tantiriyar mak’aryaciya!” Junaidu kuwa ganin raina masa hankali ma zata yi yasa ya jefar da hanky d’in kawai ya juya ya fita ranshi a mugun b’ace…..A hanyar fita suka had’u da Ya Jaafar yana shirin shigowa shi kuma, yana tafe yana tangad’i. Yana shigowa ya hango Mama a gaban Huda ta na k’ok’arin kare ta daga dukan da Baba yake shirin yi mata tana kuka tana bashi hak’uri..saboda ita har ga Allah ta yarda da labarin da Hudan ta basu. Da saurinshi ya k’araso yace “Ke dan ubanki Ina zob’o na???tun jiya na k’i shan ruwa ke nake jira, Jalila tace mini tun jiya da yamma muka aikeki, a gidan ubanwa kika kwana?” Ita Hudan sai yanzu ma ta tuna da kud’in aiken kuma indai za ta iya tuna a inda ta zubar to a wajen gudun kare ne…. Hak’uri ta shiga bashi tana cewa “Bata ga gidan mai tuwo tuwo ba, ta duba duk wani lungu da sak’o na Gabdun Albasa. Sannan kud’in sun fad’i, ya yi hak’uri dan Allah.” Zancenta na kud’in sun zube kawai ya iya fahimta, dan haka ya yo kanta zai daketa nan ma Mama ta kuma karewa, ta hau rok’on Baba tana cewa “Dan Allah ka bawa Jaafar hak’uri, ka ga a yanayin da yake ciki, baya cikin hankalinshi kar ya je ya ji mata ciwo.” Umma ganin kamar Mama za ta yi nasara a kan Baba ne yasa ta sanya gaba d’ayan k’arfin ta ta ja Mama ta cilla ta gefe har saida ta fad’i k’asa. Ya Jaafar kamar jira yake yi ya hango wani tsohon katako a gefe kawai ya nufe shi ya d’akko. Mama na ganin haka ta fara k’ok’arin mik’ewa da sauri ta nufi inda suke amma kafin ta k’araso har ya bugawa Hudan a cikinta da dukkan rogowan k’arfinsa. Aikuwa dukan ya shige ta ba kad’an ba, k’usoshin da suke jikin katakon suka chaketa wanda hakan ya sanya jini ya fara zuba, a take ta fad’i a wajen ta sume. Sai da numfashin Mama ya d’auke da jinta da ganinta na y’an sakanni tukunna a hankali ta taka ta k’araso ta durk’usa ta fashe da kuka, tana dudduba ta tana neman pulse….. Da sauri ta mik’e ta nufi d’aki ta bud’e jakarta ta zaro waya ta hau kiran Ummu.… Shi kuwa Ya Ja’afar yana ganin ta sume, shi ya d’aukama ko ta mutu ne, dan haka ya kwasa a guje ya yi waje. Umma da Jalila kuwa d’akinsu suka nufa, haka shima Baba….babu wanda yace uffan a cikinsu. Ummu, an ci sa’a har yanzu suna gidan Hajiya Shuwa, dan ya fi kusa da asibitin, shiyasa suka zauna a nan gudun kar su koma gida ciwon Sumayyan ya sake tasowa. Suna cikin hira ta ji k’arar wayarta, ganin sunan Mama wanda tayi saving da sister a kan screen d’in ya sanya ta yin murmushi kafin ta d’auka tana mai cewa “Mama jikin nata fa da sauk’i, ki kwantar da hankalinki bacci ma takeyi yanz....” Jin sheshshek’ar kuka yasa tace “Me ya faru? Ya naji kamar kina kuka??”. Salati ta fara lokacin da Mama ta fara gaya mata halin da Hudan take ciki… ba ta tsaya jin ba’asi ba ta zaro mayafinta ta yi waje, ganin hakan ya sanya Sakina biyo ta. A bakin gate suka ci karo da Madu, ganin yanayinta ya sanya shi tambayarta “mai ya fati?” shi a tunaninsa ma ko jikin Sumayyan ne…nan ta hau gaya mishi abunda ya samu Hudan….Shiruuu! yayi ba tare da yace komai ba, chan kuma a hankali ya rab’a ta gefenta ya wuce cikin gida. Wani siririn kuka Mama ta sake fashewa da shi sarai Ummu ta san ta ji yadda sukayi da Madu yanzu da yadda Madun ya nuna halin ko’in kula da lamarin…. Shiru kawai ta yi ta cigaba da tafiya da sauri domin ta je ta iske su ita da Hudan akan lokaci tunda yanzu shine priority. Sauri takeyi still da wayar kare a kunnanta dan ta cewa Maman “kar ta kashe har ta k’araso.” A bakin layin suka ci karo da Junaidu, ganin ta da yayi a hargitse yasa ya shiga tambayar ta “mai ya faru??” Ce masa kawai ta yi “Ya nemo mai adaidata ya kawo k’ofar gidan Baba yanzun nan.” Da farko kamar ba zai yi ba, domin kuwa shi Yaji! ma yake shirin yiwa gidan gaba d’aya saboda kwata kwata baya son ya had’u da Huda don idan yana ganin ta kishi zai iya sakawa ya bubbugeta, shi kuma baya son hakan ta faru. Dan haka ya yanke shawarar barin gidan for some time. Ji yayi zuciyar shi tana bashi shawarar ya yi abinda Ummun tace dan haka kawai ya nufi titi.... Ummu sai da ta zo shiga gidan tukunna ta lura da Sakina, dan haka a tare suka kutsa kai suka shige. Suna isa tsakar gidan kuwa suka hango Hudan a kwance malale cikin jini, ga wani makeken katako a kwance a kan cikinta ragowanshi kuma yana jan k’asa, kanta a kan cinyar Mama wadda taketa kuka tana rik’e da waya a kunnenta dayan hannun kuma tana ta shafa kan Hudan. Kukan da Sakina ta fashe da shi ne ya janyo hankalin ta garesu, aikuwa ganin y’ar uwarta yasa ta fashe da wani sabon kuka abun tausayi. Ummu ma bata san lokacin da ta fara kukan ba, Sakina kam da gudu ta k’arasa inda suke ta hau kiran sunan “Huda!” Jin kamar k’arar adaidaita sahu ne yasa Ummu juyawa tana addua Allah yasa Junaidu ne, aikuwa a soro suka had’u da shi yace mata “mai napep d’in yana waje” sannan ya juya zai fita, da sauri tace “dan Allah Junaidu zo ka taya mu d’aukar Huda.“ Da mamaki yake kallonta sai kuma kawai ya bita suka shiga ciki…gabanshi ne yayi mugun fad’uwa da ganin halin da Hudan take ciki, da gudu shima ya k’arasa yana kiran sunan ta yana tambayar Mama “mai ya faru?” Duk a lokaci d’aya. Da kyar Mama ta iya ce mishi “Ja’afar ne.” A zabure ya mik’e ransa a b’ace zai yi waje Ummu ta taro shi, tace “Yanzu ba lokacin wannan bane ba, mu ji da lafiyarta tukunna.” “Sakina, d’auko zanin gado ko wani babban hijabi mu samu mu raba ta da wannan mugun katakon, mu danne jinin sai mu kaita asibiti.” Hakan kuwa aka yi… Daga nan suka kinkimeta da taimakon Junaidu aka sakata a napep aka nufi asibitin kusa da su dan emergency ne…. Sai da Umma da Jalila suka ji fitarsu tukunna suka sauk’e ajiyar zuciya a tare Jalila ta saka dariya kafin tace”Ai ko banza ta wahala!. Da farko fa amma tsorata nayi Umma dan wallahi na d’auka ta mutu ne, sai da na ga Mama ta duba hannunta da wuyan ta tace ‘Alhamdulillah’ tukunnan hankalina ya d’an kwanta, amman da har na fara shirin guduwa wallahi.” Umma ce tace “ke dalla chan rufe min baki!!! Banza kawai!! kina nan zaune gashi ita har ta yo saurayi mai kud’i!, ke kina fama da malamin maths wanda sai dai yayi ta lissafa uban kud’ad’e amma ba zai iya baki ko sisi ba. Wannan kuwa kina gani kin san mai kudi ne, kalli kyallen da ya bata, k’amshin turaren jiki duk ya cika gidan nan. Tunda na dawo kike ta ce mini kin had’a bomb in jira yau burinmu zai cika ashe ke shirme kika had’a ban sanib..” Cikin katseta Jalila tace “Wallahi Umma da gaske ni plan d’ina shine Ya Ja’afar ya zaneta sannan ta yi dare sosai tunda kinga ai ba lalle ta gane gidan ba tunda ta dad’e bata je ba, sannan ita kuma Mama idan ta ji mun aiketa gidan ai kinga ranta zai b’aci Daganan ni kuma inyi ta fad’an maganganu a kanta yadda Mama zata ji haushi ta fusata. Ni sam ban yi tunanin za ta yo saurayi b...” “Aikuwa gashi ta yo kuma mai kud’i, kina jin kan zanjen nata kin san Yaron sonta yake yi.” Cewar Umma. Shiru Jalila ta yi kamar mai tunani chan kuma tace “Umma kema kin yarda da labarin da ta bayar kenan?” “To ai shine gaskiya.” Inji Umma, kafin ta d’aura da “idan ba hakan ba ta Ina wachchar gab’uwar Yarinyar ta san wani zuwa wajen saurayi??? Ni yanzu babban tashin hankalina kar ya zo ya zubewa Babanku kud’i kin san halinshi in dai yaga kud’i, mu je ya yarda ya bashi ita! Gashi ita kuma wawiya ta yi kwatancen gidan nan kuma nasan ya ji, zai zo….” Shiru duk sukayi Umma in banda huci ba abunda take yi kana ganinta ka san hankalinta a mugun tashe yake sannan tayi zurfi cikin tunani. Me ta tuna? Allah kad’ai ya sani, haka nan ta fara murmushi kafin tace “Allah ya kawoshi lafiya.” Kawai, ta fad’i hakan still da murmushi a fusakarta. Jalila dai ba fahimtarta ta yi ba, hakan yasa ta hau gado ta kwanta tana sinsinar k’amshin jikin handkerchief d’in a haka bacci ya yi awon gaba da ita, ta bar Umma tanata faman tufka da warwara. A chan asibiti kuwa, suna zuwa aka yi emergency da Huda. Likitoci suka rufu a kanta, Allah sarki Junaidu har da kukan sa shima Ummu da Sakina suma suna taya Mama..Har sai da wata nurse ta zo ta fara musu fad’a tana cewa “Addua za ku yi mata ba kuka ba, sanna kai kana Namiji kana kuka wa zai basu hak’uri??” Tukunnan a hankali Junaidu ya mik’e ya fice ya nufi masallaci Su Mama suma suka shiga k’ok’arin tsayar da kukan su, suna masu addu’ar Allah ya bata lfy ya kawo mata sassauci, dukda hawayen ba daina zuba yayi ba. Sai da aka yi! aka yi!! Tukunna suka tsayar da jinin, da kyar suka fito wajen awan su 4, dan numfashinta k’in daidaituwa ya yi da farko. Likitan ne yace “su godewa Allah k’usoshin basu tab’a komai ba. An yi mata tetanus da duk wani abunda ya kamata, an kaita d’akin hutawa za su iya zuwa.” Daga haka ya mik’a musu takardar bill. Cikin mutuwar jiki Mama ta fara k’ok’arin mik’a hannu za ta karb’a, Ummu ta yi saurin amsa tana dubawa, kafin ta cewa Sakina “ta hau Napep ya kaita gidan Hajiya Shuwa ta fad’a musu halin da ake ciki ita da su Baabaa Talatu sannan ta d’auko mata jakarta da atm d’inta.” A take Sakina ta wuce. Wasu zafafan hawayene suka zubowa Mama, a hankali tasa hannuta ta goge sannan ta mik’e ta nufi d’akin da aka yi musu kwatance, inda Hudan take. Ummu kawai binta ta yi a baya dan ta san abinda ya zo mata rai yanzun har yasa ta kasa yi mata magana. Kusan a tare suka shiga d’akin, Ummu ta zauna wajen k’afarta ita kuma Mama ta zauna a kan kujerar dake kusa da kanta a gefen gadon. A hankali ta shiga gayawa Ummu abinda ya faru har Ja’afar yayi mata wannan aika aikar… Share kwalla Ummu ta yi sannan tace “Gaskiya Mama ni kam zan d’auki Huda mu tafi gidana da ita, koda kuwa Hajiya Shuwa zata yi fushi. Dan naga alamar burinsu Sadiya su kashe ta ne, wannan wanne irin abu ne?? Ana sallamrta za mu tafi tare ba za su sake ganin ta ba.” Da sauri Mama tace “a’a Bilkisu, kar kiyi haka, dan Allah. Fushin Hajiya Shuwa bashi da dad’i ni zan fad’a miki wannan, ba zan so saboda ni ki samu matsala da ita ba. Kawai ki barmu a yadda muke, Allah yana sane da mu... Wani irin tausayin su ne ya rufe Ummu, ganin tana shirin fashewa da kuka yasa ta yi saurin mik’ewa tana cewa “Bara inje inda Sakina ta barmu in jirata, kar tazo tayi ta nemanmu bata ganmu ba.” Tana gama fad’in haka da sauri ta fita tana sakar kukan daya taho mata babu shiri. Murmushi Mama tayi dan sarai ta gano k’anwar tata. A hankali ta fara shafa kan Huda wasu zafafan hawaye suna tsiyaya daga idanunta sakamokon kwakwalwarta da ta fara tariyo mata wasu shud’ad’d’un al’amura da suka wakana shekaru ashirin da shida baya......... ……………….. Alhaji Muhammad Madu shine asalin sunan Mahaifin Mama, Mahaifin sa Babarbarene gaba da baya, Mahaifiyarsa kuma y’ar jahar Yobe ce, Fune, Jajere . Ya fi kama da Mahaifiyarsa domin idan ka kalle sa yanayin farar fatar sa da siririn jikinsa komai nasa irin na fulani ne. Iyayaensa shi kad’ai suka haifa, sannan sun rasu ne tun yana Yaro. Mahaifin Anum (Hajiya Shuwa ) shine ya d’auke sa ya rik’e shi kamar d’an sa. Bashi da d’a Namiji, Shuwa da yayunta mata biyu Allah ya bashi, shiyasa ya rik’e Madu a matsayin d’ansa, sannan an yi zaman mutumci a lokacin da iyayenshi kafin su rasu. Mahaifin Hajiya Shuwa da Mahaifiyarta gaba d’aya dangin su Shuwa Arab ne. Mahaifin ta ya kasance Malami Babba a Maiduguri, domin babu inda zaka tsaya a lokacin ka ambaci sunanshi ace ba a sanshi ba. Shekarun Madu suna d’an ja suka fara zazzafar soyayya shi da Anum. Mahaifin ta yana fahimtar hakan kuwa, ya tsaida wata biyu aka d’aura musu aure, dukda Mahaifiyarta ba wani so take yi ba, dan Anum d’in a wannan lokacin shekarunta 13 kuma tafiso y’ay’anta duk su yi aure a k’abilarsu, gashi Anum d’in tana da masoya sosai a cikin y’an uwa, dan duk Yara masu shekarunta a wannan lokacin babu mai kyau da gashinta, shiyasa ma sunanta ya b’uya daga Anum kowa yake kiranta da Shuwa. Shikuma Mahaifin Anum, hazak’a da k’ok’ari irin na Madu ya gani dan kaff cikin d’alibansa babu wanda ya taka sawunsa kamar Madu. Daman chan tun kafin Mahaifinshi ya rasu ya d’aura shi a kan ilimin addini, yanzu kam kusan tare suke tafsiri a masallatai, gashi da k’ok’arin neman na kai. Ana d’aura musu aure ya nemi zai tafi Kano tare da iyalinsa… domin akwai business kala kala da Abokin sa yake kwad’aita masa ya zo su yi. Tare suke kasuwanci shi yana chan kuma yana ganin idan yana kusa harkar zata fi bud’ewa. Shuwa sai a lokacin ta yi kukan Aure saboda ita da a tunaninta a gida za su zauna tunda ta auri Yayanta. Haka suka tarkato suka yo Kano tana kuka da kyar ya lallasheta a hanya. Suna isowa Gandun Albasa suka nufa, domin nan ne Unguwar Abokin kasuwancin nasa ‘Bashir’ wanda suka had’u shekaru biyar baya a wani zuwanshi da ya yi Maiduguri shi da uncle d’inshi saro huluna…a lokacin Madu ne Yaron shagon ya yi musu sauk’i sosai, dan haka da suka ji dad’i, suka rik’esa…. Ya kan yi musu aiken sak’on ma wani lokacin, daga baya su bada kud’in, ko huluna aka yi sai ya fara zab’ar musu tukunna ake fara saidawa jama’a, wannan karamcin nashi yasa Bashir wanda yake tsarar shi shima duk wata hanyar samu sai ya san yadda yayi ya sako Madu a ciki(dukda kuwa k’aranci na shekarunsu a wannan lokacin). Daga nan kuma sai Abota mai k’arfi ta shiga tsakani. Shima Bashir ya kan tura musu kaya daganan Kano idan farashinsu ya fi tsada a chan domin su saida su samu tasu ribar suma su Madun haka. Tun a lokacin Madu yaso dawowa kano, dan farashin kaya suna d’an fin hawa anan kamar su huluna da shadda zai a na turo musu daga Maiduguri sannan akwai business kala kala da Bashir d’in ya kwad’aitawa masa a Kanon. Mahaifin Anum shi ya hanashi a wanchan lokacin saboda k’arancin shekarunsa, sannan bai kammala secondary ba,yafi son at least ya samu certificate d’insa kafin ya fara tafiye tafiye, kar ya ji dad’in business ya k’i karatun boko…. Suna isowa direct gidan Bashir suka nufa, A lokacin shi ya dad’e da yin aure ya na tare da matarshi Aisha wadda ake kira da talatu da Yaransa biyu maza Jamilu da Usman, Jamilu shekarshi uku sai Usman wanda bai gama rufe d’aya ba. Alllah sarki Bashir a gidan sa ya bawa Madu da Shuwa d’aki suka zauna na y’an wasu lokuta har Madu ya samu ya tara kud’in haya. A layin ya kama haya tukun suka tashi, sannan ya sayi wani d’an Fili a gefe kad’an duk cikin layin, ya fara gininsa shima. A wannan lokacin layin nasu dogo ne sasai kuma Babba amman kwata kwata gidaje hud’u ne a layin ragowar kuwa duk filaye ne. Gidan farko a layin shine gidan K’asimu yana da mata d’aya Khadijah ana kiranta da Laraba da Yaranshi uku Salmanu Umaru da Hansa’u. Sai gidan Audu da ya yi aure watanni uku da suka wuce da amaryarsa,sai Bashir sai Madu. K’asimu, tun lokacin da Madu ya zo basu samu good start ba, hakanan Madun bai kwanta mishi ba saboda shi K’asimu irin mutannen nan ne masu kishi hassada da kyashi. Madu yana zuwa layin akwai wani masallaci a bayan layi aka bashi ladani, daganan kuma ya koma Limami, sannan ga gida ya kama haya ga kuma fili yana gini ga karatun daya ci gaba na boko (daman ya gama secondary school tun a Maiduguri)ga kuma kasuwanci, hanya bud’e mishi take yi ta ko Ina, gashi kaff layin matansu basu kai tashi kyau ba. Waennan abubuwa su suka taru suka k’ara rura wutar k’iyayyar Madu a zuciyar K’asimu, saboda shi tunda ya yi aure yau Yaran shi uku amman yana fama da gidan haya, sannan ya so a bashi wani matsayi a masallaci amma an k’i, gashi kasuwancin ma har yau Yaron shago ne shi Amman shi Madu daga zuwansa ko shekara biyar bai yi ba kalli yadda ya zama shahararre kusan kowa ya sanshi d’aukaka ta ko Ina ya sameta. SHARE PLS. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 09 Tun K’asimu yana b’oyewa har ya zo ya fara nunawa a fili…daga ya je chan ya tsugunna ya zagi Madu sai ya je chan ya tsugunna ya yi masa sharri. Babu inda zai zauna ya tashi bai zage sa ba, shi kuwa Madu harkar gabansa kawai yake yi sam baya bi ta kan K’asimu dan ya lura ko sallama idan yayi masa ba amsawa yake yi ba. Tsananin tsanar Madu bata sake tabbata a zuciyar K’asimu ba sai a lokacin da kud’in hayar shi K’asimun na wajen shekaru uku ya taru, anyi anyi ya biya ya k’i biya, gashi gidan na marayu ne suma suna fama da yanayin rayuwa…jin labarin sabon limamin da a ka nad’a ba da jimawa ba mai aiki da addini gashi yayi karatun lauyoyi duk unguwa ana girmamashi ne ya sanya waennan Marayu suka garzayo wajen Madu akan ya taya su fad’in gaskiya a basu hakkinsu, ai kuwa Madu bai yi k’asa guiwa ba sai da ya tabbata ya karb’a musu hakkinsu har saida ta kai ga tirsasa K’asimu siyar da y’an dabbobim shi ya biya su hakkinsu da kud’in…. Jarumta da tarin ilimin Madu ne ya sanya aka nad’asa ‘mai unguwa’ a lokacin shekarar sa goma da zuwa garin Kano. Sai kuma a lokacin ne Allah ya bawa Shuwa ikon samun ciki. Kusan a tare suka haihu ita da matar Bashir da matar K’asimu. Matar kasimu itace ta fara haihuwa,ta haifi y’arta mace aka sakamata Halimatus Sa’adiyyah sai matar Bashir ta haifi y’arta itama mace Zainab Shuwa itama ta haifi mace, Maryama. Duk a tsakanin haihuwar watanni bibbiyu ne. Murna a wajen Madu kuwa ba a magana, saboda daman shi akwaishi da son Yara, shiyasa su Usman da Jamilu sunfi sakewa ma da shi fiye da Mahaifinsu dan idan ba sani ka yi ba ko fad’a maka akayi ba to ba zaka tab’a cewa Madu da Bashir ba y’an uwa baneba saboda tsananin shak’uwa da k’aunar junan dake a tsakaninsu, gashi yanayin jikin su iri d’aya…. Maryama ta taso cikin gata saboda tsananin so da k’aunar da Mahaifin ta yake nuna mata, ga kuma yayyunta guda biyu Usman da Jamilu dan wani lokaci har fad’a akeyi wajen d’aukar Maryam tsakanin Jamilu da Usman dukda kuwa ga Zainab k’anwarsu. Idan Maryam tace tana son abu nan da nan Mahaifinta zai nemo sam baya bari ta sake tambayarshi a karo na biyo dukda kuwa ba wani k’arfi ne da shi ba, Law ya karanta a lokacin albashinsa ba wani yawa ne da shi ba amman idan kaga Maryama ko y’ar gidan wani hamshak’in mai kud’in sai haka, suturar jkinta kad’ai abun kallo ne. Tana isa shekara hud’u Madu ya had’ata da Zainab ya saka a makaranta, a wannan lokacin har sai da Talatu ta bawa shuwa shawarar a nemawa Maryama maganin baki da mayu saboda babu inda zata je ba a tankataba…Yarinyar chubby da ita gata fara farin ta irin mai yellow d’innan, gashin gira da idonta a ciccike ga gashin kai har gadon baya mai sulbi, idan ka kalle ta dole ka k’ara. A haka rayuwa ta ci gaba da tafiya har Maryam da Zainab suka kai shekaru goma a duniya, sai a lokacin ne kuma aka saka y’ar gidan K’asimu (Sadiya)a makaranta da kyar! Don a lokacin duniya ta yi masa zafi, yanayin rayuwa sai a hankali kuma shi ya dage ba zai sakata a makarantar gwamnati ba, a dole ta kud’in da su Maryam da Zainab suke zuwa nan itama zata je, a cewarsa ‘ai tare aka haifesu’ Bayan shi basussukan da suke kanshi kad’ai ma abun mamaki ne,dan idan aka gaya maka zaka rasa Ina yake kai kud’in, abu guda d’aya dai shine ko takalmi ne idan Madu ya sauya yau to tabbata sai ka ga irinshi sak a k’afar K’asimu washegari, duk wai dan ya nunawa duniya ‘ai Madun bai fi sa kud’i ba’ (a cewarshi), sai dai kuma duk inda aka yi sati 1ko2 nan zaka nemi takalmin ko suturar ka rasa saboda ya siyar ya cinye kud’in a banza. Yaransa duka uku babu mai zuwa makaranta da kyar ya saka Sadiya. Layin nasu zuwa yanzu ya cika sosai dan a k’alla gidaje sun kai sha biyar, Bashir ya sayi filin jikin gidanshi ya had’e ya kuma yin wani had’add’en gini, Madu shima ginisa a layin gwanin ban sha’awa daman shi filin sa tafkeke ne ya siya, amman shi K’asimu har yanzu yana wannan gidan haya na marayu wanda k’arfi da yaji yake so ya danne ya mayar da gidan nasa. Matarshi ta so ta had’u da Talatu da Shuwa amman tunda ta so had’a su fad’a Allah ya taimaka sukai saurin ganewa munafuka ce, sai suka yi saurin ja baya da ita, amma duk da ja bayan da suke yi da ita hakanan sai ta yi ta nanik’e musu. Inda Allah ya taimake su sai wata dillaliya ta tare, nan ta koma suka jone, aikuwa tun daga wannan lokacin in dai ka ji hayaniya da fad’a a layin to ko daga gidan dillaliya, ko gidan K’asimu dan basa barin takwana, ko kallo ne kayi musu bai musu ba nan za su fara surfa ruwan bala’i, ga rashin sanin ya kamata da munafurci...... Wata rana cikin azumi K’asimu yana zaune a bakin titi…duk magidanta da samarin unguwar suna masallaci ana sauraron tafsirin Modu amman shi ya k’i shiga tsabar bak’in hali, saboda baya shiri da Madu kuma akwai maza guda hud’u a cikin masallacin waenda yake gaba da su, dan haka ya gwammaci ya zauna shi d’aya har lokacin shan ruwa ya yi yaje ya amshi abun sadaka yayi gida domin dashi suke karya azumi….ko kwayar shinkafa babu a gidanshi. Suna cikin masallaci sukaji kamar k’arar jiniyar y’an sanda, sunan nan zaune suka ji k’arar tana ta matsowa. Kasancewar lokacin addu’a ya yi ya sanya suka rufe sukai addua masu son yin alwala suka mik’e suka yi waje…suna fita kuwa sukaga Yara sunata gudu sunayin titi,wani a cikin su ne ya tare wani Yaro ya tambayeshi “mai ya faru” shine Yaron yake ce musu , “wai motar sojiji ne mota uku, da na y’an sanda suka zo za su tafi da Baba K’asimu.” Da sauri wasunsu suka yi bakin titin wasu kuma suka koma cikin masallaci domin sanar da ragowan mutanen. Waenda suka yi bakin titin ne suka hango K’asimu ana ta k’ok’arin dannashi a motar y’an sanda yana tirjewa,yana bada hak’uri amman kafin su k’araso wajen har an tafi da shi. A bakin Yaran gurin suka ji cewa wai “Kud’in wani kurtun soja ya amsa ya sayi mota tun watanni biyar baya, kuma yace zai biya kud’in amman har yanzu be biyaba.” Cike da tarin mamaki suka koma masallaci domin lokacin shan ruwa ya yi, suna isa suka bud’a baki da dabino da ruwa akai Sallah kowa yayi gida domin karyawa. Basu samu lokacin bin bayan K’asimu ba sai da suka idar da asham Da Madu da Bashir da wasu mak’oftansu guda biyu (Kabiru da Nafi’u)suka tafi a motar Madu. A cikin motar ne su Kabiru suke hira da Baba Nafi’u wanda yake tambayar “shin wai yaushe K’asimu ya sayi mota ne shifa bai tab’a ganin motar ba.” Nafi’u ne yace “ai tun watanni shida da suka wuce lokacin da Madu ya sayi mota shima ya tada hankalinshi ya dinga bi yana tambayar bashi kusan kaf layin duk wanda baya gaba da shi saida ya tambaya bashi aka hanashi.” Nafi’un ya d’aura da cewa “nima sanadiyyar ya tambaye ni aron kud’i nace masa bani da kud’i ya sanya ya fara gaba da ni har da ce mini ‘wai ni ba makwafcin gaskiya bane ba, Ina yi mishi bak’in ciki….’ To dai na ganshi da mota after one month kuma ina kyautata zaton a wajen wannan kurtun ya karb’a Aron kud’i dan bai dad’e da tarewa ba a bayan layi lokacin.” Kabiru Yace ”Ikon Allah to ai ni ban tab’a ganin motar ba.” Dariya Nafi’u ya yi yace”Ai motar ba ta kwana ba inaga damfarar sa masu siyarwan suka yi. A ranar da ya siyota ya kawo ya zo yayi parking, haka nan ta dunga hayak’i ta cika unguwa saida athmar d’in Laraba ya tashi…nifa da na fara ganin hayak’i wallahi na d’auka gobarace ta tashi a gidan nasa, lokacin dawowa ta kenan daga kasuwa ko gidana ban shiga ba na ce bara in duba gidan nashi inga, Ina lek’awa kuwa na hango shi da salmanu da Umar sunata bulawa motar k’asa don k’ok’arin kashe hayak’in. Hansai kuma tanata kuka ita da Sadiya suna jijjiga mahaifiyarsu wadda ta sassank’are tana numfashi da kyar. Ban bi ta kansu ba naje da kyar na nemo abun hawa aka kai Laraba asibiti, shikuma ya tafi kai mota gyara…kusan duk d’an abin hannunshi saida ya k’are a wajen gyaran motar nan. Daga karshe ya maidawa wanda ya saya a wajenshi shi kuma ya ce an kwak’ule motar a wajen gyara bata da wani amfani, inaga a dubu hamsin ya saida motar da kyar,ya amshi kud’in, dan ta tashi a aiki....” Madu ne ya katse musu hirar su ta hanyar ce musu “Mun iso!!” Suna shiga kuwa sukaci sa’a inda suka je d’in aka kaishi, bayan sun buk’aci ganinsa ne aka fiddoshi Har an fara sauya mishi kamanni. Da farko ya so yayi tirjiya da b’oye b’oye,amma da yaga ba sarki sai Allah sai kawai ya hak’ura ya gaya musu gaskiya “kud’in kurtu ya karb’a ya sayi mota kuma shi yanzu bashi da halin biya.” Madu da Bashir su suka had’a kud’i sukai belling shi, bayan ya dawo gida Modu da Bashir suka bada rabin kud’in mota, shima K’asimun d’an kud’in hannun shi ya tattaro ya had’a da adashin Laraba aka had’a duk amman dukda haka kud’in bai cika ba…Da kyar da taimakon wasu makwaftan aka had’a ma kurtu kudinshi dan cewa ya yi “Wallahi bai san Asara ba!.” Bayan sun dawo gida ne da washegari, Modu ya samu Baashir yace masa “su taimaka su had’awa K’asimu kud’i su bashi ya ja jari ya daina yawon neman bashi,tare aka taso bai kamata su barshi a haka ba.” Dama shi Bashir da kyar ya yarda, ai kuwa!!…..a cikin azumi suka bashi kud’in lokacin yanata murna yayi ta godiya har da rungume Madu. Bayan Sallah tana yi K’asimu ya rangad’a sabon Aurensa, ya auro baffulatana Yarinya y’ar k’arama shekara d’aya Jamilu ya bata. Ai kuwa gidan nan nasa ya sake hargitsewa, gashi shi ba wata tsayayyiyar sana’a garesa ba dan haka kowa zuciyarsa a kusa! kullum cikin fad’a, daman itama amaryar irin marasa kunyar nan ne, kowa baya ragawa kowa. Yadda basa ragawa junansu hakanan y’an waje ma ko kallo ka yiwa d’aya daga cikin Yaran In bai musu ba duk girman mutun haka zasu zuba maka tujara, shiyasa ake yiwa gidan Lak’ami da ‘Gidan marasa tarbiyya,’ sun kuwa tsani sunan idan sukaji sunan a bakin wani tofa ranar rigima sai inda k’arfinsa ya k’are. A wannan lokacin ne kuma Shuwa ta sake d’aukar ciki, Maryam da Zainab da Sadiya sunada shekara goma a duniya. Murna a wajen Maryam da Zainab ba’a magana dan har sun fara shirya kalar party d’in da za su yi idan Shuwa ta sauk’a lafiya. Kullum kuma cikin addua suke Allah yasa k’anwa za a haifa musu don su dinga yi mata kitso suna yi mata kwalliya. Wani abun mamaki, Zainab k’awar Maryam ce sosai a da amma tunda ta fara zuwa makarantar su sai suka had’ewa Maryam kai, ita Zainab ashe dama tuntuni tana d’an jin haushin Maryam saboda su Ya Jamilu sun fi sonta, da taimakon zugar Sadiya kuwa k’iyayyar Maryam ta samu waje a zuciyar Zainab, daman chan ita Sadiya ta tsani Maryam domin kuwa ita ya’yan masu kud’i ta so yin huld’a da su amma sam basa kulata Maryam suke so da k’awance duk da ita kuma Maryam d’in bata kulasu sosai dan bata da hayaniya. Duniya ta fara yiwa Maryam zafi a lokacin da k’awarta kwalli d’aya ta juya mata baya. A yanzu ko kaisu makaranta Zainab bata yarda a yi tare balle a d’aukosu, ta gwammaci ta biyawa Sadiya su tafi a k’afa su dawo a k’afa! Wanda har su je su dawo kuwa basu da aiki sai na zagin Maryam ita ba amma ta san suna yi ba. Ana cikin haka ne Shuwa ta haihu, ta samu y’arta mace ranar suna taci suna ‘Bilkisu’ , bayan suna Maryam ta had’a party duk wani Yaro saanta ta gayyata ana I washegari amman Sadiya sai ta hana Zainab zuwa sannan ta sakata ta sato kud’in Babanta da ya ajjiye, abinda bata taba yi ba. Haka nan dinga bin Yara suna raba musu kud’i akan ‘ “kar su je Partyn Maryam’ wai ta saka guba a lemo, su jira su gani babu wanda zai je saboda bak’in jini ne da ita.” Ai kuwa hakan akayi ko wanne Yaro ya karb’i kud’i yak’i zuwa party kar ya je a bashi guba. A ranar Maryam kwana tayi tana kuka, tun daga ranar kuwa bata isa fitaba sai Yara su fara mata wak’ar ‘mai bak’in jini’ Sadiya ta kafa ta tsare duk wanda taga yana shirin fara yin k’awance da Maryam nan da nan za ta saka Zainab ta je ta sato kud’in mahaifinta ta bawa Yaran tace su zab’a ko kud’i ko k’awance da Maryam. Bashir tun baya fahimta har ya fara fahimtar ana d’aukar masa kud’i… A haka shekaru suka yi ta shurawa abun tun yana damun Maryam harta hak’ura ya daina damunta da taimakon Shuwa. Ranar wata Juma’ah Baba Bashir ya tafi masallaci aka y rashin sa’a ya manta bai d’auki darduma ba kuma ya makara don Madu yayi tafiya so ba tare za su tafi ba, hakan ya sanya ya dawo…yana shiga d’akinsa kuwa ya kama Zainab dumu dumu, ai kuwa ta daku a ranar kuma ya titsiye ta sai da ta fad’a mishi komai plan d’insu da Sadiya ba abinda ta b’oye….. Kunya! kamar k’asa ta tsage Bashir da Talatu su shige haka sukaji…mutumin da yake biya mata kud’in makaranta bai tab’a nuna gajiyawa ba shine take yiwa y’ar sa haka??. A lokacin suna aji biyu a js amman babu shiri aka siya mata form ta yi junior waec , aka fara shirin tura ta boarding. Madu yana dawowa Bashir ya rok’esa yace “yanaso zai had’a da Maryam ya kaisu makarantar kwana, anfi karatu dan kwata kwata Zainab bata karatu”. Sam Madu bai so hakaba don baya son yayi nesa da Maryam amman kawai sai yayi kawaici ya amince, Bashir a tunanin sa Zainab da Maryam za su shirya ne idan an kaisu boarding tare tunda daman chan k’awaye ne, kuma yana kyautata zaton Sadiya ce ta had’asu fad’a. Sai dai kuma ko da akaje boarding d’inma, farin jinin da Maryam take da shi a wajen Malamai da d’alibai sai ya sake jawo mata bak’in jini a wajen Zainab, sannan Yayanta Usman sai ya zo makarantar sau da yawa wajen Maryam amman ita sai dai ya bada sak’o yace a bata, kuma sai ya cukowa Maryam leda da kayan kwad’ayi amman ita sai ya bada kad’an yace a bata.. Abunda ba ta sani ba a ko da yaushe sai Maryam d’in ta k’ara mata a kan wanda Ya Usman d’in ya bayar yace bata. Haka kurum sai ta daina kulata ko ta hau yada magana idan ta ganta, shirin da akeso dai su yi bai yiwu ba domin kuwa alamarin k’ara tab’arb’arewa ma yayi don kwata kwata Zainab da Maryam basa shiri,duk mates d’insu sun sani. Har sai da Zainab ta kai Maryam bango duk kuwa hak’urinta sai da ta tanka mata sukayi wani damben da suka jiwa kansu ciwuka har aka kai ga kiran iyayen su, sai a nan ne Madu ya ji abinda ya faru har Bashir ya kaisu boarding duk dan ya samu daidaita tsakaninsu. Ganin k’ok’arin Bashir na ganin zaman lafiya ya wanzu ya kuma tabbata a tsakanin Yaran nasu ne ya sanya kawai shima Madu ya barsu sukaci gaba da boarding d’in. Wanda bayan sun dawo hutun gama ss1 ne Ya Usman ya zo da zungureriyar wasik’ar shi ya bawa Maryam ta inda ya ke bayyyana mata cewa shi fa sonta yakeyi tun tana y’ar k’aramar ta…. Ita dai Maryam ba zata ce bata son Ya Usman ba saboda Yayanta ne kuma ya kula da ita sosai, amman a gaskiya so na soyayya sam bata yi masa kwata kwata. Ko da ta gayawa Umma Talatu da Hajiya Shuwa..kalar murnar da ta gani a kan fuskokinsu ne ya sanya kawai ta amince suka fara soyayyarsu ita da Usman gwanin ban sha’awa. Zainab kuwa (duk da kaita boarding school d’in da akayi hakan bai saka sun rabu da Sadiya ba, don indai aka aike Zainab to sai ta biya wajen Sadiya a b’oye). Ai kuwa tanajin labarin soyayyar Maryam da Usman, Sadiya ce kawai ta fad’o mata a rai, dan ba zata iya irga adadin wasik’un da Sadiya ta bata ta bawa Ya Usman ba..tun tana y’ar shekara sha d’aya take son Ya Usman, shi kuma Ya Usman idan akwai wadda ya tsana a duniyar nan to Sadiya ce! Idan ka kalli Sadiya sam ba zaka tab’a ce mata mummuna ba, ba doguwa baceba amman tanada manyan idanuwa da matsakaicin hanci bakinta dai dai misali ga dimples a fuskarta sai dai bak’a ce amman tanada dirin jiki mai kyau sannan tanada gashi wanda ya sauk’o har kan kafad’arta, sai dai sam waennan qualities na Sadiya basu d’ad’a Usman da k’asa ba hasalima shi ya tsane ta kwata kwata bata kwanta mishi ba.. A cewarshi Yarinyar bata da kamun kai, ga munafurci irin na Ubanta dan sarai ya san ita ta shiga tsakanin Maryam da Zainab, shiyasa daya ga nacin nata yana neman yi mishi yawa ya had’asu ita da Zainab d’in ya ci ubansu, tun daga ranar ya samu sa’ida. Sai dai fa dukda hakan da yayi sam soyyarshi a zuciyar Sadiya ba abinda ya ragu sai ma k’aruwa da tayi…. Da wannan tunanin Zainab wadda ta saci hanya ta isa gidansu sadiya, bayan sun gaisa da Baba Laraba ta tambaye ta Ina Sadiya tace mata “Tana d’aki”. Tana shiga ta sameta a kwance tana bacci, jijjigata Zainab ta shiga yi har sai da ta farka sannan ta shiga koro mata halinda ake ciki A ranar Zainab ta sake gasgata soyayyar Usman a zuciyar Sadiya domin kuwa kuka ta dinga yi harda ihu kamar wata y’ar k’aramar Yarinya da kyar suka lallasheta ita da Baba Laraba bayan ta shigo Zainab ta gaya mata halin da ake ciki. kafin ta bar gidan kuwa zazzab’i ne mai zafi ya rufe Sadiya dan ko idanunta bata iya bud’ewa. Satin Sadiya uku tana rashin lafiya, idan ka ganta sai ka tausaya mata, duk ta rame ta fita a haiyyacinta, har shagon d’inkin Usman taje tai sallama da shi daya fito tayita masa kuka, ganin da yayi abun nata na gaske ne yasa ya lallasheta ya rakata gida, wannan itace rana 1 daya mata magana mai dad’i shiyasa tana dawowa gida har mamakinta Laraba ta dinga yi saboda yadda ta ware kamar ba ita ba. Hutun makaranta ya k’are! su Maryam an fara shirin komawa, wannan karan Baba Bashir ne ya yi musu provision da kyar Madu ya bari kuwa. Ranar Lahadi Usman da Madu suka maidasu makaranta. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 10 Ranar Monday aka yi chanjen aji, sannan da yamma aka nad’a shadow prefects wanda a ciki har da Maryam, Maryam ta so an bawa Zainab itama domin zuwa yanzu Maryam ta lura a duk lokacin da ta samu abu Zainab d’in bata samuba ne suke samun matsala da ita. Duk da k’ok’arin ganin an zauna lafiya da Maryam d’in take yi hakan bai hana Zainab kyarar ta ba kasancewar hostel d’aya suke room d’aya aji d’aya kuma seat d’aya. washegari Tuesday, suna zaune suna jiran first period na English, English theacher d’in ya shigo tare da wani kyakkyawan saurayi sanye cikin khakin sa na nysc, kusan duk matan ajin ido suka zuba mishi…. Har suka k’araso bakin board suka tsaya da shi da English teacher d’in idanunsu na a kanshi, shi kam bai ma san suna yi ba don idanunsa suna a k’asa yana kallon k’asa yayinda su kuma ko fahimtar bayanin English teacher wanda yake cewa “ga sabon copper shi zai dinga yi musu English a yanzu for 10 months, daganan idan ya gama service d’inshi ya tafi aiki zai dawo hannunshi kamar farko” basa yi, har sai da yace “Are u guys with me??” Da d’an k’arfi, tukunna hankulansu ya dawo jikinsu, suka ce “Yes sir.” Banda Zainab wadda tayi mutuwar zaune, dan a lokaci d’aya ta ji bawan Allah n ya tafi da imanin ta. Kasancewar Madu da Bashir sun gayawa Malaman su su dinga zaunar da su sit d’aya ita da Maryam ya sanya akoda yaushe suna tare, hakanan wani lokacin zainab sai ta kawo jaka ta saka a tsakiyar su wai kar jikin Maryam ya goge ta ta kwashi bak’in jini, Amman yau kam zainab bata san lokacin da ta kamo hannun Maryam da k’arfi ba! Ita maryam d’inma tsorata ta yi dan kwata kwata hankalinta baya ajin, ya tafi ga takardar da take hannun ta tanata bitar debate d’in da za suyi da safen nan, kawai ta ji an damk’o hannunta kamar za a karya ta. Kallonta ta yi amman sai ta ga hankalinta gaba d’aya baya tare da ita, wani wajen ma daban take kalla. Da sauri ta kalli inda zainab take kallo ta ga englishi teacher yana ta zuba bayani a gaban board da wani balarabe a gefen sa da koren kaya a jikin sa….dan haka ta juyo gareta cikin kulawa tace “Zainab menene?” Kallon ta zainab d’in ta yi sannan tace “Maryam kinga wannan kyakkyawa ko?. Dama haka ake ji a lokacin da ka ga wanda kake so? kinji yadda k’irjina yake bugawa kuwa? haka kike ji idan kika kalli ya Usman?” Ta yi mata tambayar tana mai sake kallon saitin da copper d’in yake. Wani farin ciki ne ya lullub’e Maryam dan rabon da zainab ta yi mata magana mai tsaho haka har ta manta…dan haka ta saki wani k’ayataccen murmushin da ya sake fito da ainihin kyawun fuskarta sannan ta d’ago kanta domin ta kalla wanda y’ar uwarta ta haukace a kai haka cikin lokaci k’ank’ani. Tana d’ago kan nata dai dai shikuma English teacher ya mik’a masa chalk yana cewa “introduce yourself to them.” Karb’a yayi sannan ya d’ago daidai ita kuma Maryam ta juyo tana murmushi a take idanunsu suka sark’e a cikin na juna! Bai san ya aka yi ba kawai ya ji chalk d’in dake hannunsa ya fad’i k’asa! Lokaci d’aya zuciyarsa ta hau bugawa da sauri da sauri…. Itama Maryam kusan hakan ne a nata b’angaren, jin yadda zuciyarta ke bugawa gashi ya tsareta da manyan idanuwanshi farare k’al masu kama dana mai jin bacci, hakan ya sanya ta saurin sunkuyar da kanta k’asa. Maganar Mr Solomon ce ta dawo da shi daga duniyar daya tsinci kanshi a ciki dak’ik’un k’alilan da suka wuce. Chalk d’in da ya yar yaga yana mik’a mishi sannan ya sake cewa “introduce yourself to your students.” A hankali ya saka hannunshi ya karb’a sannan ya sake juyawa ya kalli inda Maryam take a ranshi yana adduar Allah yasa ta sake d’agowa ya kalli fuskarta, domin kuwa baya jin akwai abinda ba zai tab’a gundurar sa a duniyarnan kamar kallon fuskar wannan extraordinary beautiful young lady d’in ba. Ganin tak’i d’agowa ne yasa shi juyawa…a hankali ya k’arasa jikin black board d’in ya rubutu sunan shi kamar haka ‘YAKUBU UMAR FAROUK M.T’ Sannan ya juyo ya kalli students d’in yace “that’s my name, but u can all call me ‘ABBA’ I’m your new English Teacher....” Cikin nutsuwa ya karanto musu tsarinshi kamar ‘baya son surutu a aji sannan yana son in ya bada assighment a dinga maida hankali ana yi......’ Sai da ya gama tukunna Solomon yace “akwai debate d’in da ya basu as an assignment group A B and C”. sannan ya mik’a mishi textbooks d’in da suke hannunshi ya juya ya fita…. Cikin kwarewa da nutsuwa Abba yake koyar da su, sun nutsu kuwa suna fahimta sosai don duk hankalin su yana a kanshi, sai da ya gama yace “Ina masu debate?” Maryam ita take representing group A, dan haka ta mik’e tsaye. A hankali cikin sauk’e ajiyar zuciya yake kallon ta, kafin ya janye idanunsa ya mayar kan group leaders d’in B and C da suka mik’e sannan yace “su fito gaban board”. Topic d’in yana magana ne a kan who is more responsible a karatun Yara A, parents B, teachers C kuma both. Maryam itace mai parents. Haka suka dunga mahawarar a tsakanin su har kowa ya kawo gaba d’aya points d’inshi. Points d’in da Maryam ta kawo ko kai shed’an ne dole ka san itace winner! Danhaka ya bawa group d’inta 10/15 ragowar groups biyun kuma ya basu 6. Bayan sun koma seats d’insu sun zauna ya tambayesu ko “akwai mai question”, sukace “a’a”hakan yasa ya tattare books d’inshi, ya duba time table yaga sai Friday shida ya sake shigowa ajin. Daga haka ya yi musu sallama ya fita. Ai kuwa kamar jira sukeyi yana fita kowacce ta hau tofa albarkacin bakinta, wasu su ce balarabe ne wasu suce d’an India wasu kuma pakistan, gashi daga ganin sa ka san d’an masu kud’i ne! Nan ajin ya haukace da zancen sa har sai da malamar next period ta shigo tukunna aka samu ajin ya nutsu da zancenshi. Kafin kwana biyu, gaba d’aya makarantar ta d’au zancen copper Abba balarabe (sunan da suka saka mishi kenan) Hatta junior section ba’a barsu a baya ba, masu love letters suma yi suke yi su je su zira ta saman glass d’in motasa Inda yake d’an bari kad’an a zuge saboda iska ya d’an dinga shiga. Zainab tun ranar da ta fara ganinsa ta haukace bata da labari sai na Abba, hannuta kuwa kullum da kalar design d’in da za ayi da biro a cikin heart d’in a rubuta ‘Abba’ duk inda kuwa akace Fridays Mondays ko Tuesdays ( ranakun da suke da English kenan) hakanan za ta rambad’a kwalliya ta yi skipping assembly kuma, dan kar a goge mata. Kamar yadda y’an makaranta suka haukace da ganinsa hakanan shima zuciyarsa ta haukace tunda ya ga Maryam. Yau satin sa biyu da fara koyar da su kuma zuwa wannan lokaci kam ya gama fahimtar son Maryam yake yi domin kuwa tun ranar farko daya ganta ya rasa nutsuwarshi gaba d’aya bashi da burin da ya wuce yayi ta ganinta, har Allah Allah yake ranar da zai shiga ajinsu ta yi ya samu ya sake sakata a idanunsa. Through out this week ko me yake yi kawai tunanin ta yake yi. Ganin da yayi yana b’atawa kanshi lokaci yasa kawai ya yanke shawarar gaya mata in his next period, dukda kuwa yana fargabar mai amsarta za ta kasance, duba da yanayin k’arancin shekarunta amma kuma ya san ‘a bari ya huce shi ke kawo rabon wani.’ Yau Monday!! kasancewar Abba ba’a staff quarters yake da zama ba..gida ne guda mahaifin shi ya siya mishi saboda service d’in da aka turo shi…ya sanya ya tashi da sassafe dan baya son ya makara, kuma akwai d’an tazara tsakaninsu da makarantar. Har yayi wanka yayi breakfast yana murmushi jifa jifa shi kad’ai, kawai idan ya tuna zai ganta yau sai yaji wani farin ciki ya lulllub’eshi . Duk saurin shi kuwa sai da aka gama assembly tukunna ya samu ya zo. Zainab yau sneaking ta yi bataje assembly ba saboda ta shafa jambaki da powder ga kwalli ta saka kuma ta san indai aka ganta to punishment ne bayan an sakata ta goge. Y’an aji suna fara shigowa suka ganta a zaune, wata classmate d’insu ce tace “wato yau sneaking kika kuma yi ko?Hmm bai ma fa san kina yi ba! Dan ko kallonki baya yi.” Dariya tayi kafin ta sake cewa “tou shadow sai ki rubuta sunan y’ar uwarki, a cikin masu sneaking in dai ba son kai bane abun” Ta yi maganar referring to Maryam. Ko gama zama ba su yi ba Abba ya shigo ajin hakan yasa zainab ta had’iye masifar da ta taso mata take shirin juyewa classmate d’in tasu tahau murmushi tana kallonsa. Cikin dabara ya kalli wajen zaman Maryam yaga tana goge wajen zaman ta da duster kafin a hankali cikin nutsuwarta ta zauna sannan ta fara yiwa Zainab magana a hankali… Ajiyar zuciya ya sauk’e a hankali sannan ya amsa gaisuwar da suka shiga yi masa. Bayan ya kammala duk abunda ya kamata yace dasu “su ciro takarda zai yi test”. Hakan kuwa aka yi…. Lokaci yana cika ba tare da ya b’atawa kanshi lokaci ba ya kalli Maryam yace “ta tattare gaba d’aya papers d’in ta kai mishi office.” Sai da ya ga fitarta tukunna ya bi ta a baya. Jin kamar mutum a bayan ta yasa ta juyo, ganin shine ya sanya ta d’an tsaya sai da yayi gaba tukunna ta bishi a baya saboda daman ko taje Admin d’in sai tayi tambaya tunda ba sanin office d’insa tayi ba. Office d’inshi kusan shine na k’arshe a jerin k’ananun offices d’in da suke wajen…suna zuwa ya saka hannu cikin aljihun wandonshi ya zaro key ya bud’e ya tura ya shiga sannan a hankali yace mata “Bismillah”. Sallama tayi ta shiga…office d’in d’an k’arami ne, sai dai ya had’u sosai, sai k’amshi yake fitarwa, ga wata k’ofa a gefe wanda tanada tabbacin toilet ne…. Maganar sa ce ta dawo da ita daga duniyar k’arewa office d’in nasa kallo data tafi, jin yana cewa “Zauna mana, ga seat.” A hankali ta ajjiye takardun a kan tebur sannan ta girgiza kai ta juya za ta fita taji yace “I order u to sit.” Sai da tayi kusan 1 minute sannan ta zo ta zauna kan kujerar da take facing tashi benci ne kawai a tsakaninsu. Sai da ya d’an sauk’e ajiyar zuciya kafin yace “from which state are you ?” “Kano” ta bashi amsa. “Which area??” “Gandun albasa” Ta fad’a a tak’aice. “Are u sure?” Yai mata tambayar kafin yace “cos banga alama ba, at all” Da mamaki ta kalleshi, kafin tace “U too” Sannan ta mik’e tace “Please sir zan tafi muna da test.” Mik’ewa shima yayi yana murmushi kafin yace “sai yaushe? Ba kiyi mini kwatancen gidanku ba balle in kawo miki ziyara idan an yi hutu, ko bakya so in zo???“ Da sauri ta d’aga mishi kai alamar ‘eh’. With surprise yace “Y” “Nothing” Kawai ta iya ce mishi sannan ta sunkuyar da kanta k’asa, tana adduar Allah yasa ya bata izinin tafiya, dan bata san daliliba in dai suna waje d’aya ji take tamkar zuciyarta za ta faso k’irjinta ne ta fito waje, tsabar bugawa. Abba fahimtar da yayi kamar yana yin komai cikin sauri..kar kuma yaje ta k’i shi idan taga zalamarshi…hakan ya sanya ba dan ya gamsu da shawarar da zuciyarshi ta bashi ba kawai ya bata izinin tafiya. Ai kuwa da sauri ta juya ta fita a office d’in. Zama yayi a kan kujerar sa, sannan ya bud’a hannunshi kafin ya kaisu duka biyu bayan k’eyarsa kamar zai yi filo da su… Lumshe idanuwanshi yayi sannan ya fara tunanin duk wani possible hanya da zai b yayi getting close to her, dan ya lura he needs her attention first. A bakin Admin block d’in taci karo da Zainab tana ta faman kai kawo, tana hango ta kuwa ta iso tana tambayarta inda office d’in nashi yake..kwatance Maryam d’in tayi mata daga haka tayi gaba, bata san ya sukayi ba.... A b’angaren Abba kuwa, a da k’arfe 2 yake tashi ya tafi gidanshi, amman yanzu voluntarily yayi exceeding time d’inshi har 10 pm (Time d’in tashi daga night prep) ko tsoron hanya baya yi, hakanan yacewa mai principal kawai zai dinga supervising evening and night prep, Friday kuma zai samu aji ya dinga k’ari a sms. Da murna kuwa principal d’in ta yarda, dan yace ba sai an bashi ko sisi ba. Kasancewar Maryam shadow ce ya sanya ba a ajin su take night prep ba, a jss2 take zama tana supervising d’insu. Tana zaune kawai ta ji kamar an shigo tana kallon k’ofa kuwa suka yi ido biyu….kujerar teacher ya janyo ya kawo dai dai gefen sit d’inta ya ajjiye sannan ya zauna kafin yace mata “Good evening ma.” Da sauri ta kalleshi sai kuma ta yi k’asa da kanta tace “evening sir.” Murmushi yayi kafin yace “na takura ki ko?” Girgiza kanta kawai tayi ta ci gaba da karatunta… Jifa jifa yake mata hira har aka tashi. Tun daga ranar kuwa haka kullum zai shigo ajin da sunan supervising zai yi amman su daya kamata ace sun hana Yara surutu har a tashi bakin Abba baya yin shiru na minti goma. A haka har aka yi sati… Yau friday Maryam tanata murna ba zasu had’u ba atleast zuciyarta sa ta huta da bugawa da take yi. Sai dai kuma tana zuwa sms d’in ta ganshi a bakin gate na main mosque yana tarar y’an makara, ai kuwa ganin tazo a makare ba k’aramin dad’i yayi masa ba, sai da ya bawa kowa punishment sannan ya juyo ya fara tanbayarta “mai yasa ta makara bayan tana matsayin shadow?” Uzurinta ta fad’a mishi…maimakon ya barta ta tafi ko yayi punishing nata, instead, sai kawai ya hau tambayarta ajin da take. Yaso ace itama d’aliba ce amman sai ya ji tace “ajin y’an Izu 60 take koyarwa, thou he was amazed.” Ganin zata makara sosai ya sanya ya barta ta shiga taje wajen d’alibanta…. Sai da ya samu ajin da tabarmar su take facing tata tukunna yace su zai koyar...... Idan ana maganar ‘Nacii!!’ tou shi Abba yake yiwa Maryam, tun bata sakewa da shi har ta fara, dan ya iya labarin ban dariya, sannan yana burgeta , thou har yanzu bata gama sanin ma’anar bugawar da zuciyarta keyi idan suna tare ba. Ahaka aka shafe 3 weeks. Kamar kullum yau ma suna zaune a night prep yana bata labarin Mahaifin sa….tanata mamaki saboda ita dai ita da Mahaifinta they are like best friends sab’anin shi dan a yadda yake bada labarin Mahaifin nasa kamar wani boss na horror movie, he is not even close to him kwata kwata kuma wai a haka duk cikin y’aya’ansa yafi sonshi, saboda ya ci sunan mahaifinsa ne… Hayaniyar wasu Yara ne ya juyo da hankalinsu suna waigawa kuwa suka ga ana dambe! Da sauri ta tashi ta isa wajen, shima ganin hakan yasa ya biyota….garin k’ok’arin raba damben d’ayar Yarinyar jin an rik’e hannunta ta d’auka y’an class d’insu ne nan ta buge hannun Maryam d’in da k’arfi!! wanda bai sauk’a a koina ba sai a kan louvers na window kuma daman a fashe yake, nan da nan kuwa ta yanke jini ya fara tsiyaya… Abba bai san lokacin da ya finciko Yarinyar ya wanka mata marin da har sai da ta fad’i kasa itama gefen bakinta ya fashe, sannan yayi sauri ya kamo hannun Maryam, ganin jini ta koina yana zuba duk ya ma rud’e bai san lokacin daya kama k’asan rigar shaddar jikinsa ba ya yaga ya kamo hannun ya d’aure da kyallen sannan ya fara janta yana cewa “ta zo su tafi clinic, a dubata.” Duk ya rikice, dan har kwalla Maryam ta hango ya taru a idanunsa. Suna fita suka had’u da prep mistress d’in hakan yasa suka d’unguma har ita aka je akayi mata dressing, a tafin hannuta ta yanke amman Allah ya taimaka ba’ai mata d’inki ba. Har sukaje suka dawo yana jera mata sannu ko motsi tayi sai ya tambayi “mai takeso?” Har bakin unity gate ya rakata tukunna ya juya dan a lokacin an tashi daga prep. Kusan bai samu yayi ishashhsen bacci ba, juyi kawai ya dinga yi yana Allah Allah gari ya waye. Allah ya taimaka ma washegari za ta kasance Tuesday ne, so yanada su har double period. Kamar kullum yau ma Zainab tayi kwalliyarta suna zaune suna jiran shigowarshi, yau kamar da rashin mutunci ta tashi dan sai hararar Maryam take yi, tana fama yada mata magana har da cewa “ idan ma za ta ware gara ta ware tun wuri dan ba abinda za ta tayata da shi.” Ita dai maryam ta yi shiru tana fama da zugin da hannunta ke yi mata, ga idanunta da suka yi jaa, dan jiya bata samu isheshshen bacci ba. Shigowarsa ce ta sanya ajin yin shiru kowa ta maida hankalin ta gareshi, shi kam yau k’arara kowa sai da ya lura da kalar kallon da yake yiwa Maryam dan tunda ya shigo daga bak’in k’ofa ya kafeta da idanu har ya isa inda bench d’inshi yake, garin kallon ta ma har da d’an yin tuntub’e. Ganin tak’i d’agowa ta kalleshi yasa kawai ya amsa gaisuwar y’an aji sannan ya fara lesson..dictation ya fara kamar kullum dan baya musu note a board amma yaga Maryam d’in ta kasa yi, k’ok’ari takeyi ta rubuta da hannun hagu amma ta gagara, ganin tana neman fama ciwonta ga ciwon kan da ya addabeta yasa kawai ta tura littafin gefe ta kifa kanta a benchi. Abba kam zuwa yanzu ji yake kamar ya kori gaba daya y’an ajin ya lallasheta, ganin gaba d’aya hankalinshi baya ajin kar yaje ya fara musu dictating shirme yasa yayi rounding up, sannan yace “akwai mai question?” Mutane uku ne suka yi question ciki harda Zainab tanata faman karairaya, shi bai ma san tana yi ba, ya bata amsa daga haka yace “Let’s call it a day”. Sai a lokacin Maryam ta d’ago ta juya ta tambayi wata classmate d’insu ta ara mata note d’inta, bayan ta mik’o mata ta had’a da nata ta ajjiye a kan bench, duk a kan idonsa.. Har ya yi hanyar fita sai kuma kawai ya dawo ya d’auki littafin nata da na wadda ta karb’a za ta kwafa d’in, ya juya ya fita da sauri. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 11 Yana fita y’an ajin suka fara tofa albarkacin bakin su, har da masu cewa ‘ai tayi sneaking ta shigo da waya dan da gani free call suka kwana suna yi jiya shiyasa daga ita har shi idanuwansu suka nuna alamun rashin barci. Wata Ramlat wadda hostel d’insu d’aya kuma k’awar Zainab ce k’ut da k’ut tace “Tab! Yanzu girman kai zai k’aru, su o’o ba’a da had’add’en saurayi ma ana kallon mutane a kan hanci, ballantana yanzu anyi..” D’agowa Zainab tayi ta kalleta a take tayi shiru bata k’ara cewa uffanba. Abinda ya bawa Maryam mamaki shine har suka koma hostel, aka yi lesson na evening, suka sake fitowa night prep kwata kwata Zainab bata ce mata uffan akan maganar ba. Sai dai kawai ta ga tanata yawan kallonta. Straight jss2 ta nufa tana shiga ta gansa a zaune a gefen sit d’inta kamar ko yaushe. Yana jin shigowa ya d’ago kai ya kafeta da ido har ta k’araso ta zauna ta gaidashi. A hankali ya amsa sannan yace “Ya hannun??” Itama a hankali tace “ da sauk’i.” Sannan ta fara k’ok’arin bud’e jakarta domin da d’auko littafi ta samu ta fara karatu. Littattafan d’azu ya mik’o mata yace “gashi, gobe sai ki bata nata ko?!” D’agowa ta yi ta kalleshi sannan ta d’auka littafin ta bud’a da niyyar ta d’an k’ok’arta ta kwafa, saboda Yarinyar har ta fara mata maganar littafinta wai ‘tanaso za tai karatu’, amma kawai sai ta ga wani had’add’en rubutu ya baiyyana daga dai dai inda suka tsaya, dubawa tayi tai comparing da na k’awar tata taga Note d’in nata ya zama complete, kallonshi tayi taga shima Itan yake kallo da murmushi a kan fuskarshi kafin yace “Ko ban iya rubutu ba?”. Bata san lokacin da murmushi ya sub’uce mata ba saboda yadda yayi maganar yana wani langab’ar da kansa, kuma harga Allah tayi mugun jin dad’in taya ta d’in da yayi dan bata san ya za tayi ba, bata da wanda zata rok’a ya tayata dan kusan kaff y’an class da room d’insu daga safe zuwa yanzu kamar haushin ta duk suke ji wanda ita bata san dalilin su na Jin haushin nata ba. Ganin tana murmushi kawai ya tsaya yana ta kallon ta dan ji yake kamar kar ta daina. A hankali ganin ya kafe ta da ido tace “Ni ka daina kallo na.” D’auke idanunsa yayi daga fuskanta yana murmushi….idanunsa suka kai kan hannun rigarta, dayake da d’an jini jini a jiki tun na jiya, har zai tambayeta dalilin da ya sanya bata wankeba sai ya tuna da hannunta, kuma a yadda take da shiru shiru d’innan ya san ba zata iya saka Junior wanki ba. Dan haka kawai sai yace mata “Ki dinga kawo kayan wankin ki zan na kai miki wajen wanki har zuwa lokacin da zaki warke .” Murmushi kawai tayi tace mishi “to” Sannna yace duk note d’in da bata yi ba ta kawo, da kyar ta bashi na physics, ragowar kuma tace “za ta k’ok’arta da hannun hagu.” Har aka tashi suna hira yau kam ta sake dashi, hakan kuwa yayi mishi dad’i sosai. Washegari kam da bata zo da wankin nata ba taga b’acin ransa matuk’a, dan kicin kicin yayi, kuma ko da aka tashi da kyar ya yarda ta tafi bayan ya sanya ta ta rantse akan washegari za ta kawo.” Hakan kuwa akayi, washegari ta saka a leda ta sako a skul bag d’inta ta kawo mishi. Ko da yaje gida akwai washing machine, ga dry cleaning a arean da wajen wanki dai kala kala, amman haka Abba ya zage ya tik’i wankin nan nata da hannunshi, abinda bai tab’a yiba kenan tun tasowarshi, cook d’insa kam da mai yi masa gyaran gida tsayawa suka yi suna kallon ikon Allah, dan babu yadda basu yi da shi ba akan ya kawo su wanke ba amma sam ya k’i. A wajen ya zauna ya jira ya bushe, ya kwashe ya tafi d’aki ya goge mata, yana yi yana murmushi…… Hakanan ya mayar da abun aikin sa….note da wanki shi zai yi mata ko jinkiri ta d’an yi wajen kawowa ya dinga mita kenan yana fushi, hannun nata ya warke amman kwata kwata ya hanata wanki k’arfi da yaji. Zuwa yanzu shak’uwa sosai ta shiga tsakaninsu, bak’in jini kuwa a wajen y’an class da hostel d’inta ta kwasheshi ba ‘a magana, dan zuwa yanzu kowa ya sani saboda indai ya shigo aji har ya fita hankalinshi gaba d’aya yana a kanta suna had’a ido kuwa zai sakar mata murmushi ba ruwanshi da inda suke. Ganin da yayi shak’uwa da sabo ya shiga tsakaninsu ya yanke shawarar fad’a mata shifa sonta yake yi, dukda ya San zuwa yanzu ta fahimci hakan, amman dai gara ya fad’a mata baki da baki. Dan haka ya yanke shawarar sai ranar da za a tafi hutu tukunnan zai gaya mata daganan ya karb’i land line d’insu (idan suna da shi) ta yadda za su dinga communicating. Ranar hutun kuwa! Sunyi ita da shi a kan za su had’u 11, amma sai aka yi rashin sa’a ana bud’e gate motar gidansu ce ta fara shigowa, abunda bai tab’a faruwa ba….suna hostel ma lokacin suna shirya wasu kayyayakin su metron ta zo ta kira su, a gurguje suka k’arasa shiryawa suka yiwa ragowan mates d’insu sallama… Kamar kullum Madu da ya Usman ne suka zo d’aukar su kasancewar shi Ya Jamilu ba mazauni bane ba, kafin yayi wayo yake nacin zama soja shiyasa tun yana k’arami su Madu suka mik’a sa nda.... Tana isowa bakin Admin ta hango Ya Usman wanda tun fitowarta shi alredy ya riga ya ganta ya kafeta da ido yana tsaye da Madu a gefensa, tana k’arasawa ta fad’a jikin Madu ta rungume sa, sannan ta juyo ta gaida Ya Usman, itama Zainab hugging Madun nasu tayi sannan ta yi huggin Ya Usman shima wanda yake ce musu “suyi sauri su shiga su kama hanya…..” Sai da suka shiga motar tukunna suke ji, ashe ‘Madu da Shuwa da Ya Usman ne za su tafi Hajji, jirginsu 7 na dare zai tashi yau shiyasa aka zo d’aukar su da wuri dan a samu a kintsa komai a kan lokaci’…ai kuwa nan suka hau murna. Usman shi yake driving amman har kusan zubar da su yayi a hanya tsabar yadda gaba d’aya hanakalinsa ya tafi kan Maryam wadda ta fara gajiya da kallo da murmushin da yake da zuba mata ta glass d’in saman motar tun tasowarsu. A haka suka iso gida, ita Maryam gaba d’aya zuciyarta a cunkushe take saboda rashin yin sallama da Abba, shi kuma Usman mamakin girma da kyan da Maryam d’in ta k’ara yake yi…..dan haka yana shiga gida bayan an d’an yi oyoyo ya samu Baaba Talatu da maganar “shifa gaskiya ya kamata a fara maganar auren su shi da Maryam” Har sai da Baaba Talatu ta fara yi masa tsiya tana cewa “shi, ko irin y’ar kunyar nan baya ji??”, tukunnan ta samu ya kyaleta ya tashi ya fita yana murmushi. K’arfe 5:30 kuwa, da Baba Bashir da Ya Jamilu da Maryam da Zainab da Bilkisu wadda take kuka sai ta bi Shuwa, suka rankaya suka yi musu ranki ya zuwa Airport. Sai da suka zo rabuwa tukunna itama Maryam taji kwalla na shirin zubo mata, dan haka ta yi saurin barin wajen. Suna komawa gida, Baaba Talatu ta saka Maryam ta k’arasa had’a kayanta da na Bilkisu, daman Shuwa ta kusa gama had’awa, kafin su tafi. Suna gamawa kuwa aka rufe gidan suka dawo gidan Baba Bashir. Sai yanzu Maryam ta gano tabbas son Abba take yi…ta yi mugun dana sanin rashin yi mishi kwatancen gidansu da tayi, babu yadda bai yi da itaba amman ta k’i. Duk da cewa bai tab’a gaya mata ba ta san shima yana sonta…a haka da kyar a daddafe take gurgura hutun Allah Allah kawai take yi a koma…. A b’angaren Abba kuwa kusan d’an k’aramin hauka ya yi….ya je gandun albasa sau babu adadi, yana tambayar gidansu Maryam Muhammad amman bai samu ba (kasancewar Maryam d’in a file dinta ne kawai take amfani da Madu). A haka aka kusan gama hutun yanata faman zirga zirga…daga k’arshe kawai rashin lafiya ta rufesa, sai da yayi doguwar jinya tukunna ya samu kanshi, yana ta Allah Allah a koma makaranta, dan duk tsawon rayuwarshi bai tab’a ganin hutun da aka yi yayi masa masifar tsaho kamar wannan ba. Haka akayi Sallah lafiya, a tsakanin Zainab da Maryam in dai sun yi magana tou a gaban mutane ne, sanin yadda Maryam take son Bilkisu ne ya sanya haka kurum idan Zainab ta lura ba kowa a wajen sai ita da Maryam kawai sai ta hau dukan Bilkisu, haka kurum ba abinda ta yi mata duk dan kawai ta bak’antawa Maryam rai, itakam Maryam sai dai taje ta janye Bilkisu uffan ba zata ce da itaba, domin itakam yanzu sha’anin Zainba ba ya d’ad’ata da k’asa. Yau tun safe a gidan Baba Bashir aketa shirye shirye, dan sun yi waya da su Shuwa yau za su taso tun asuba amman har wajen d’ayan dare shiru. Washegari ma shiru, wata washegarin ma haka! A haka har aka shafe sati d’aya da kwana biyar... Zuwa wannan lokacin y’an unguwa kowa hankalinshi ya tashi Baba Bashir kam shi da Jamilu shiryawa suka yi suka nufi Abuja. Baaba Talatu kuwa sau uku ana mata k’arin ruwa, idan ka ga Maryam Zainab da Bilkisu sai baka tausayi, basu da aiki sai kuka, yau kam har da Baaba Talatu aka zauna ana shan kuka…Baaba Laraba wadda ta shigo ita da Sadiya ba da jimawa ba ne suke ta basu baki, duka kuwa itama Sadiyar kukan take yi. Abun yayi musu yawa gashi Babba Bashir da Ya Jamilu ma da suka je Abuja yau kwanan su hud’u suma basu dawo ba, ko ta landline ba su kira ba. Suna cikin kuka kawai suka ji ana bud’e gate, da sauri da sauri suka hau rige rigen fitowa tsakar gidan, suna isowa suka ga motar Baba Bashir. K’arasawa suka yi bakin motar da sauri, ta cikin glass d’in suka hango su Shuwa, ai kuwa da kyar suka iya barin su suka samu suka fito dan duk sun rufe motar anata kukan murna. Sai da suka nutsu suka huta, sannan Madu ya hau basu labari... “A cikin room mate d’in Usman na hotel d’in da suka sauka ne aka kama cocaine a jakar wani, shine aka kama Usman dan mai jakar yace shi ba tasa baceba ta Usman d’in ce. Har an tafi da Usman d’in sai wani bawan Allah d’an Nigeria (ambassador) ya tsaya musu tsayin daka dan yaga alama larabawan suna k’ok’arin yin son kai ne saboda wanda aka kama da jakar balarabe ne shima, amman d’an morocco. Bawan Allahn nan da ya tsaya musu shine ya bada kud’in beli, mak’udan kud’i ba kad’an ba, sannan ya d’auko y’an rahoto aka tafi airport aka nemo vid wanda cctv camera ta yi capturing ranar da suka isa k’asar. Allah ya taimaka ba a ga Usman da jakar ba, iyaka jakankunan su shi yake tare da. Bawan Allah bai bar wajen ba sai da ya tabbata an binciko video na ranar da wannan Yaro d’an Morocco ya zo, ai kuwa sai ga jakar ta fito a hannun wata Yarinya wadda ta zo tararsa, suna gaisawa ya amsa jakar suka ci gaba da tafiya suna hira.” Baaba Talatu ce cikin tarar numfashin Madu, tace “Shi kuwa wannan bawan Allah wanne irin godiya kuka yi masa? a gaskiya ya kamata mu d’unguma gaba d’ayan mu muje gidansa domin yi mishi godiya”. Usman ne ya tari numfashinta ta hanyar cewa lWallahi Baaba abinda zai baki takaici, mutumin ya na gama had’a takardun komi da komi ya dank’a a hannun Abba Madu, yace su je su taho da ni. Tun a hanya da ake bani labari nake ta son In zo in ganshi dan banma san wacce kalar godiya zan yi masa ba…amma muna zuwa airport d’in bamu same sa ba sai note kawai ya rubuta yace a bamu wai ‘emergency ya taso mishi, ya tafi, an kwantar da k’aninsa a emergency.’ Su kuma suka k’i su bamu information a kansa ballantana mu ga garin da ya tafi, saboda kin san babban mutum ne. Amman na san garin a yake ba zai wuce Abuja ba.” Shuwa ce tace “ai ba lalle Abujan ba, kawai dai yanzu muyi ta saka shi a addu’o’in mu muna yi mishi fatan alkhairi, inda rabo wata rana za a had’u ai.” “Haka ne kam!” Cewar, wadda ta k’i tafiya ita da Sadiya sai da sukaji kwakwaf. Haka dai kowa yayi ta tofa albarkacin bakinsa…sannan aka ci gaba da murnar dawowar su, daga baya Madu da Shuwa suka tafi gida, aka bar Bilkisu da Maryam a gidan Baaba Bashir saboda gidan yayi k’ura sosai, aka bari akan washegari idan an gyara sa dawo. A ranar Ya Jamilu ya koma saboda daman saboda case d’in ya dawo kuma akwai abubuwa da dama a kanshi. Da daddare wajajen 8 Ya Usman ya aiki Bilkisu yace ‘ta kira mishi Maryam’. Tana zaune tana tunanin Abba Bilkisu ta shigo ta fad’a mata sak’on Yayan nasu ta juya ta fita wajen Baaba Talatu… Da farko kamar ba zata je ba, sai kuma kawai ta mik’e ta fita. A can waje babban tsakar gida ta iskeshi zaune a kan tabarma, gefen sa ta nema ta zauna ta gaidashi sama sama tunda ga nan daga ‘um’ sai ‘um um’. Ko ba a gayawa Usman ba ya san cewa Maryam ta chanza mishi, dan gaba d’aya hankalinta baya gareshi, shi gani yayi ma kamar haushinsa take ji, dan tunda ta fito bata yi mishi dariya ba. Da kyar! Ya samu ya kawar da tunanin da zuciyar shi take k’ok’arin dasa wa kwakwalshi, dan shi dai ya san makarantar mata take yi, babu maza ballanta tayi saurayi! Da wannan tunanin ya sallameta ya sanyawa ranshi maybe ko bacci take ji yau d’in. Amman ga mamakinshi washegari ma haka ta yi mishi wata washegarin ma haka, sai da aka shafe kwana biyar suna a haka. Da yaga abun yayi yawa yau sai ya chanja lokaci, around 4 na yamma ya aika aka kirata a zatonsa ko yana hanata bacci ne amman yau sai yaga ma b’acin ran da take ciki ya fi na kullum, dan tun daga nesa ta had’e rai! Ita kuma Maryam a nata b’angaren takaici ne ya rufeta…shi wannan Ya Usman d’in baya tashi kiranta sai ya daidai ci daidai lokacin da take tsakiyan tunanin Abba.. Kasa jurewa Usman yayi, hakan yasa ya ce mata “Maryam anya har yanzu kina sona kuwa?” D’agowa tayi ta kalle shi, kafin ta yi k’asa da kanta ta fara tunanin... ‘Gara fa ta fad’a mishi gaskiya, ita daman chan ba sonshi take yi ba! Kar taje su yi aure tana tunanin wani ta yi ta kwasowa kanta zunubi!’ Wata zuciyar ce tace mata ‘to ke Abban aka ce miki sonki yake yi? ko ya tab’a gaya miki ne?’ Da sauri ta rumtse idanunta dan she can’t begin to think of the fact that wai Abba baya sonta! Sai yanzu ta kuma tabbatar wa kanta ta kamu da sonshi ba kad’an ba, dan da basa had’uwar nan ta yi kewarshi ba k’adan ba!’…… “Maryam kin yi shiru@ Muryar Ya Usman ta katse mata tunani.. Bud’e idanuwanta ta yi waenda har sun chanja kala! Zuwa yanzu kam tabbas Ya Usman ya fara kaita bango…domin kuwa ita a gaskiya bata son naci babu abunda ta tsana kamar takurawa, bata son yawan magana! kuma ya sani. Shiyasa a makaranta ake mata kallon mai girman kai..mutane ma dayawa tsoron mata magana suke yi karta yarfa su, a cewarsu masu kyau daman ance girman kai ne dasu. Itakam basu san kawai yawan maganar ce bata so…. “Hmmm, tou inaga dai kin d’auko kuramen aljanu a boarding d’in taku.” Ya Usman ya sake fad’in haka. A yanzu kam ta gama yanke shawarar… ‘Ko Abba baya sonta, za ta fad’awa Ya Usman gaskiya dan indai ta aureshi a haka tabbas ba zata iya yi mishi biyayya ba, hakan yasa a hankali ta sago ta kalleshi! Ya kuwa kafe ta da ido ko kyaftawa bayayi, nauyinshi taji shiyasa ta maida kanta k’asa ta fara magana a hankali…. “Ya Usman ka daina cewa bana sonka, Ina sonka a matsayinka na d’an uwana mana, ai kai Yayana ne.” Shiruuuu!! Ne ya wanzu a wajen, dan ya kai kusan mintuna biyar bai ce mata uffan ba, ita tama yi tunanin ya bar wajen ne dan haka a hankali ta d’ago tana juyowa kuwa suka had’a ido! gabanta ne yayi mugun fad’uwa sakamokon idanuwansa da taga sun koma tamkar garwashi, bata gama fassara yana yin da fuskarshi take ciki ba taji yace “A matsayin saurayin ki fa? mijin da zaki aura uban Ya’yanki??” Ya yi mata tambayar yana mai kallon cikin kwayar idanuwanta. K’arya ba halin Maryam bace ba, zuwa yanzu ta so ta d’an b’oye masa ko dan halin da taga yana shirin shiga a cikin y’an mintunan da basu gaza goma ba, amma sai ta tsinci kanta da girgiza mishi kai. Wannan karon ta tsorata dan hawaye ta gani ya sauk’o ta idonsa d’aya, bata ankara ba taga d’ayan ma ya sake sauk’owa. Dasauri ya mik’e ya bar wajen yayi cikin gida ba tare da yace mata uffan ba. A hankali itama ta tashi ta bi bayanshi tana mai jin wani nauyi yana sauk’a daga kan m k’irjinta.... Sai da tayi kwana biyar bata sake saka Ya Usman a idonta ba, a lokacin kuma sauransu kwana d’aya su koma makaranta, mutumin da tun tasowarta in dai yana gari to sai yazo gidansu sau hud’u a rana. Tana zaune tana had’a kayanta a jaka Shuwa tace “ta je ta kira mata Zainab, Abba Madu yace a tambayeta idan akwai abinda take buk’ata bayan provision d’insu.” Tana shiga gate d’in gidan gabanta ya fara fad’uwa, ba kowa sai motar Baba Bashir a parke a chan gefe, a hankali ta k’araso ta tura k’ofar k’aramin tsakar gidan ta shiga, nan d’in ma ba kowa. Har ta wuce zata isa k’ofar d’akin Zainab, ta ganshi yana fitowa daga corridor d’in kitchen da plate a hannunshi, bata san dalili ba kawai taji jikinta ya fara rawa kamar wadda ta yi laifi, sosai take mamakin ramar da yayi…tana tafe tana waigen shi dan a tunanin ta zai yi mata magana, bata yi auni ba kawai taji ta yi tuntub’e ta kusa fad’uwa, da sauri ta saita kanta ta tura k’ofar d’akin Zainab ta shige…. Wani abu da ya bata mamaki shine tabbas ta san Ya Usman ya ganta to amman kuma mai yasa bai ce mata komai ba?! Har fa kusan fad’uwa tayi amman bai kulata ba! Mutumin da ada idan ana hirar tsakar gida ko sauro baya so ya hau jikinta, ya dinga yi mata fifita kenan har a tashi. Yo ai ko babu soyayya shi Yayanta ne so ya kamata ace ya kulata, lallai indai hakane kuwa to hakan yana nufin Ya Usman yayi zuciya kuma da alama ya hak’ura da ita kenan, a cikin zuciyarta tace “barka na”. “Malama lafiya? Za ki shigo babu sallama?” Muryar Zainab ta katse mata tunaninta. Sak’on Shuwa ta fad’a mata, bata jira amsar da zata bata ba ta juya kawai ta fito gudun rikici dan yanzu kam itama bata ragawa Zainab. Har ta kai k’ofa, sai kuma ta kalli y’ar barandar da zata kaita d’akin Baaba Talatu, tunani ta yi akan bari ta shiga su d’an gaisa dan haka ta nufi k’ofar d’akin nata! Tana isa bakin k’ofar ta saka hannu kenan zata tura taji muryar Ya Usman yana cewa “Baabaa to ai ni a tunanina sharetan da zan dinga yi kamar zai janyo mini in sake fita a ranta ne, yanzu fa har kusan fad’uwa tayi ban kula ta ba, ku.....” Cikin fad’a fad’a taji Baabaa Talatu tana cewa “Yanzu Usman Ina uwar ka amman ba zaka bi abinda nake gaya maka ba? Yo ai maganar fita a rai kuma ta faru ta k’are! Sai dai bayan auran ku ka nuna mata so ta yadda zata dawo kamar da, ka ji ai da kunnenka Zainab tace ‘Yaron balarabe ne!’ Shi ne ya rud’eta….kawai abunda nake so da kai shine ka nuna mata kamar ka hak’ura ta yadda za ta sakankance, ni iya in sha Allah da kaina zan je in samu Madu…ba zata k’are makarantar nan ba sai da auranka a kanta bi izinillahi. Ka kwantar da hankalinka, dan k’ank’aninka da kai ka bi ka d’aga hankalinka! Ai kana ji dai abinda Likita yace ranar ‘jininka ya yi mugun hawa, Allah kad’ai ya taimaka baka samu stroke ba, lokacin da ka fad’i ka suma wallahi na d’auka mutuwa ka yi, nayi mugun tsorata. Zancen banza ma kenan!!! Ita daa chan ta san bata sonka amma shine ta bari aka kawo har i yanzu?? Ko da yake na san ba yin kanta bane ba, wannan Yaron ne yake neman juya mata tunani. Amma ba komai na san abunda zan yi kai dai kawai ka kwantar da hankalinka kaji ko??” A hankali yace “tou Baaba.” Jin kamar zai fito yasa Maryam ta yi saurin barin wajen ta fice tana tafiya tana share hawayenta, da kyar ta kai gida dan har wani duhu duhu take gani ga jirin da yake k’ok’arin zubar da ita, tana shiga ta wuce d’akin su ta kwanta a kan gado ko bi ta kan kayanta da take had’awa bata yi ba. Banda tashin hankalin da yake a ciki sosai mamakin Baaba Talatu ya turnik’e ta yake juya mata Kai! Tabbas tsakanin ‘da da uwa sai Allah, Baaba Talatu da take nuna mata tsananin so har fa dukan Zainab take yi saboda ita amma wai yau itace take shirin k’ulla mata auren dole kawai dan taga d’anta ya suma, wata zuciyar ce tace mata ai itama tana da tata uwar, taje ta fad’awa Shuwa tun kan ayi mata auren dole. Da sauri ta shiga girgiza kai ita kad’ai dan ta san yadda gidansu da nasu Baba Bashir yake, Irin tsananin shak’uwa da zumuncin da yake tsakani ba na wasa baneba, ita kanta bama ta san ba brothers bane iyayen nasu sai kwanaki da suka je Maiduguri karkarsu take fad’a mata. Tabbas kuwa ta san Shuwa ba zata d’auki wannan shirmen nata ba. Sai a lokacin ta fahimci kuskurenta, ta kuma gane ta d’aukowa kanta hanyar da ba zata b’ulle ba dan ta san iyayenta ko giyar wake suka sha ba zasu tab’a hana Usman itaba. Kamar ma Shuwa da Madu sun fi son Usman a kaf cikin y’ay’an Baba Bashir, don gashi Madu ya biya mishi hajji sun tafi tare ko Baba Bashir d’in bai biya ma ba. A take ta yanke shawarar rabuwa da Abba duk da ta san za ta sha wahala, dan da wuya in wannan ba shine ajalinta ba, amman ya ta iya? a haka bacci ya kwasheta sai la’asar ta farka. Toilet ta fad’a ta yi alwala ta fito ta yi sallah, sannan ta mik’e ta yi waje, a hanyar kitchen suka had’u da shuwa tana tsugunne kan kujera a bakin kitchen d’in tana gyaran alaiyyahu. Gaidata Maryam tayi sannan ta zauna a kan takalmanta tasa hannu ta fara tayata. Lokaci zuwa lokaci Shuwa tana lura da ita…sai da suka gama har za ta mik’e ta kai kitchen ta ji Shuwa tace “Zauna Ina so za mu yi magana” Da sauri ta kalleta sai kuma ta koma ta zauna a kan takalmanta da tayi kujera da su. Cikin nutsuwa Shuwa tace “Mai yake damunki? D’azu naga kin shigo kina kuka! Ga idon ki duk sun kumbura Da alamun kukan kika yi ta yi ko? A zuwa yanzu ba san kin daina yiwa Zainab kuka dan haka ba matsalarta baceba, ko?” A hankali ta d’aga mata kai Alamar ‘eh’. “Fad’a min to? menene?” Inji Shuwa. Shirun da Maryam ta yi ne yasa ta sake tambayar ta tare da cewa “Ko kinada wadda ta fini da za ki gayawa? Kin manta tun lokacin da Zainab ta daina k’awance da ke na yi miki alk’awarin na zama babbar k’awar ki?” Cikin murmushi Maryam ta share kwallar da ta zubo mata tace “a’a” A hankali Shuwa ta kamo hannayenta duka biyu sannan tace “fad’a min to, menene?” Tun daga ranar da ta had’u da Abba ta hau gayawa Shuwa har yau d’innan bata b’oye komai ba… A hankali Shuwa ta sauk’e ajiyar zuciya, bayan Maryam d’in ta gama, sannan cikin nutsuwa tace “Maryam na san menene so, kuma zan so ki auri wanda kikace kina so a yanzu, amman idan muka da ni dake da babanku za ayi mana kallon butulu. Abu na biyu kuma ki yarda dani idan nace miki, har yanzu k’iba son Usman, tunda ai da kina son shi, kyale kyale na wanchan Yaron shi ya rufe miki ido har kike nema ki guji Usman wanda na san in sha Allah bayan auranku komai zai daidai ta. Sannan abu na uku, wanchan Yaron daga yana yin labarinki na fahimcei d’an masu kud’i ne, na gaske! Maryam ke Yarinya ce har yanzu, Yaran masu kud’in nan b’atawa mutum lokaci kawai suka iya. Tabbas idan kika bincika already akwai Yarinyar da zasu aura wadda aka riga aka had’a su dan basa tab’a yarda su auri y’ay’an talakawa. Shawara ta anan shine ki auri Usman, ki zauna a cikin y’an uwan ki, ki manta da batun Abba kar ki bi zuciya ki zama butulu, daa chan baki ji rashin son auranshi ba sai yanzu? Usman zai kula da ke, tun kina k’ank’anuwar ki yake d’awainiya da ke dan zan iya ce miki laulayi da nak’udarki ne kawai Usman bai yi ba amma har Goya ki yake yi, kashi da fitsari babu kalar wanda baki yi masa ba. Kiyi ta Addu’a zaki ji zuciyarki tana yin sanyi, kinji ko? Allah ya yi miki albarka.” A hankali tace “Ameen.” Ta yadda kuma ta gamsu dukkanin abunda Shuwa ta fad’a gaskiya ne, sai dai kuma tanata so tace mata itafa tun farko daman murnar da taga sunayi ita da Baabaa Talatu ne ya sanya ta yarda da soyayyar ya Usman, amma sanin ko ta fad’a hakan ba lalle a fahimceta ba tunda da chan bata fadaba sai yanzu da take son rabuwa da shi saboda Abba, hakan ya san kawai ta yi shiru ta mik’e ta koma d’aki. Tana shiga ta nemi bakin gado ta zauna a hankali ta sauk’e ajiyar zuciya, sannan tace “Abban ma da nake ta abu a kanshi maybe ma shi bai san m inayi ba.” Ahaka dai sukuku ta k’arashe wannan ranar washegari da sassafe Ya Usman da Ya Jamilu wanda ya dawo jiya da daddare suka maida su makaranta, har suka juyo Kano Usman ko kallon inda take bai yi ba, Ya Jamilu ne dai dukda ya kasance Soja baya yawan dariya amman hakan yayi ta janta da hira ganin kamar tanata tunani. Ana gama checking d’in kayanta ta fara k’ok’arin kaiwa hostel. Isowarta bakin Unity gate kenan kamar ance ta d’aga kanta gabanta ya yi mugun fad’uwa sakamokon had’a ido da suka yi da Abba, ya kafeta da ido da alamun ya dad’e da ganin tahowarta, yana zaune gefen house mistress d’insu wadda ta mayar da second checking d’abiarta dan duk dawowa hutu bayan an gama duba maka kaya a main gate to itama sai ta sake nata a bakin Unity gate. Da alamun checking d’in yake tayata, amman sai magana take yi mishi hankalinshi baya wajenta har sai da ta d’an zungureshi tukunna ya mik’a mata abun hannunshi ya taso ya taho inda Maryam d’in take, tana k’ok’arin k’arasowa wajen tana k’ok’arin kaucewa ya sha gabanta…had’a ido sukayi tana mamakin ramar da taga yayi, taji yace “Maryam I could hug u right now! Kin san yadda na dinga nemanki kuwa? You said za mu had’u 11 tun 10 nake Admin Ina jiran ki har kowa ya tafe, and now kin ganni k’ok’ari ma kike yi ki wuce kawai ki tafi, bakiyi missing d’ina ba??” Ya yi mata tambayar yana kallon ta da yanayin sa kamar na mai shirin yin kuka. Ahankali tace “sir, i want to pass, u are blocking my way.” Shek’ek’e!! haka ya tsaya yana kallonta, anya kuwa Maryam ce? to ko dai wani abun yayi mata ana I gobe hutun, maybe ma shiyasa ta tafi ba ta jirashi ba… Yana cikin wannan tunanin yaga tana k’ok’arin zagaye shi ta wuce. Shan gabanta ya kuma yi, sannan yace “Wai me yake damunki ne? Kin san halin da na shiga kuwa? Ina ta Allah Allah a dawo makaranta don in sake ganinki, wallahi kinji na rantse har a asibiti na kwanta, all because of u and yanzu shine za ki zo mini da wannan sabon attitude d’in? To wallahi baki isa ba! Idan ma wani misunderstanding ne u better talk mu yi clearing d’inshi right away cos u can’t turn your back on me like this, ba zan iya jurewa ba, not now, not ever!!!” Ya fad’a da d’an k’arfi da alamun ranshi ya soma b’aci. A hankali Maryam cikin sanyin ta, tace “Y? Meye had’ina da kai?” Ga mamakinta sai taga ya fara murmushi, kafin yace “do I really have to say it?” Yayi mata tambayar yana kafeta da idanuwanshi data kasa jurewa kalla ta yi k’asa da kanta. Y’an tsirarrun students ne a wajen, most of them ma y’an ajin su ne, kasancewar sai yamma sosai ake cikowar dawowa, sai house mistress d’in da take checking… Tafa hannunwanshi Abba ya fara yi yana cewa “attention everyone.” Cikin k’ank’anin lokaci ya had’a kan y’an mutanen wajen da basu da wani yawa, sai da ya tabbatar attention ya dawo kansu sannan ya durk’usa a gaban Maryam, ya sago yana kallonta ya fara magana. “Maryam i Found the reason for my smile, the day i found you! In you, my life becomes whole, with you my days become bright. In your hands i would love to lay, for the rest of my life, you’ve got everything i’ve been searching for in life, i would love for you to grow old with me! The best is yet to be and it begins from the moment you say yes! I love you, so much Maryam, will you please be my soulmate?, will u marry me?, will u stay with me till death do us apart??”. Ai kuwa nan students suka hau tafi, suna “Say yes, Maryam say yes!!” Ihun su ne yasa house mistress d’in ta k’araso wajen. “Stand up!” tace mishi. A hankali ya mik’e, tukunna tace “you know all this is not allowed right?” Cikin sanyi jiki yace “yes” Murmushi yaga tayi sannan tace “but I’m willing to sopport you a hundred percent, because I’ve never seen a perfect match like yours! But don’t do too much of zance at school because it’s not allowed, don’t cause problems for her, you can visit her as much as u want whenever she gets back to her fathers house.” “Ok.” Ya cewa house mistress d’in yana d’an murmushi sannan yace “tnx”. Kamo hannun Maryam tayi tace “ta wuce hostel tayi freshening up, kafin wannan oyinbo boyfriend d’in nata ya hanata.” A hankali ta wuce…Abba k’ok’ari yake su had’a ido amman tak’i ta bashi damar hakan. Sai da suka yi kwana biyu tukunna aka fara night prep, ta so ta yi dodging kawai tayi class d’insu amman sai ta kasa. A hankali ta k’arasa js2, tun ta window ta hango shi zaune wajen zamanshi, yana hango ta ya kafeta da ido har ta k’araso. Cikin nutsuwarta ta gaidashi ya amsa mata yana kallonta. Bayan sun d’an gaggaisa sun d’an yi hira tana ta jin nauyin sa ita dai, yace mata ”ya baki fito da wankin ki ba?”. Da mamaki ta kalleshi tace “ai yanzu na warke!” Kicin kicin yayi da kyar da nacin da yayi ta zuba mata washegari ta kawo mishi wanki. .…….. Duk wani gatan da ya dace Abba yana tabbatarwa ta samu, sai dai kamar yadda house mistresses d’insu ta fad’a mishi, baya takurata sosai gudun kar ya ja mata matsala, kuma itama house mistress d’in ta rufa musu asiri kar ya bata kunya, hatta prep d’inma yanzu sai ranar karb’ar wanki da dawowa da shi ne kawai yake zuwa, yana bada tazarar kwana bibbiyu dukda yana takura da hakan amma ya san hakan shine dai dai. Soyayyarsu sukeyi gwanin burgewa, Maryam ta ma manta ta wani Ya Usman sannan tunda yanzu Abba yace yana son ta,za ta fad’ama Shuwa itafa daman chan ba son Ya Usman take yi ba, don haka a d’aga mata k’afa. Addu’ar ta d’aya Allah yasa su fahimceta su kuma yadda da Abba. Kamar kullum yau ma suna zaune a night prep suna y’ar hirar su, yake bata labarin yayanshi da irin son da yake yi masa, har yake ce mata yace masa first born d’inshi in Namiji ne takwara zai yi masa. Murmushi tayi tace “D’an gatan Yaya.” Tana dubanshi ta k’asa k’asa, dan a yanzu kam kunyarshi takeji kwana biyun nan, kuma take ji bata bari ta kalleshi dan suna had’a ido zai ce mata I luv u. Garin kallon ne ta kalli fingers d’inshi, sai taga sun d’an kumbura ba kamar ko yaushe ba, hakan yasa tace masa “Mai ya samu hannunka?” One thing about him bai iya k’arya ba, dan haka ya hau bata labarin tun ranar da ta fara bashi wanki, yadda yake wankewa da gogewa ya ce “maybe yawan tab’a ruwa ne ya sa hannun nasa ya yi haka” shi kam ya ma manta bai kamata ya gaya mata hakan ba. Maryam haushin kanta ta fara ji, dan a yanzu kam yadda Abba ya damu da ita itama ta san sarai ta damu da shi. Dan haka tayi fushi yayi yayi ta k’i kulashi, har aka zo tashi. Ganin tana shirin mik’ewa yasa shi ya rik’e mata jaka, ya fara bata hak’uri, ganin ya k’i sakin jakar kuma Yara har sun fara kallonsu yasa ta koma ta zauna. Sai da aka gama fita tace “zan hak’ura amman ba zan k’ara kawo maka wanki ba, ai hannun ya warke.” Shi kuma yace “ba zai barta ta tafi ba har sai ta rantse zata kawo wankin, dan ba zai barta ta dinga shan wahala ba.” Wasa wasa basu ankaraba, kawai alarm d’inshi na 11 wanda yasa dan lokacin exercise d’inshi kenan b4 going to bed kawai sukaji yana k’ara. Maryam da taga time a firgice ta mik’e, ko sauraronsa ma bata yi ba ta suri jakarta tayi hostel tana adduar Allah yasa ba a rufe ba. Shima Abba ganin yadda duk ta rud’e kuma yaga dare yayi yasa bai tsaida ta ba, ya tattare kayan shi ya tafi. Adduar ta kuwa ta karb’u, dan ba a rufe unity gate d’inba sannan hostel d’insu ma ba a rufeba. Room d’inta nema aka rufe dan sai da tayi knocking tukunna Zainab ta bud’e mata. Tana ganinta ta juya taje suka ci gaba da hira da ragowan mates d’insu ba tare da ta kalleta ba. Fitsarin daya isheta tun a chan ga kuma tsoron daya sake ingizo shi yasa itama bata kalli Zainab d’inba kawai kan gadonta ta nufa ta ajjiye jakarta ta zari torch ta fice ta nufi toilet. Bayan ta gama fitsarin ne taga ashema period d’inta ya d’auke, daman yau take expecting hakan ko gobe da safe, kasancewar ana tsula sanyi ga duwatsun garin na kusa da makarantar, ta san ba zata iya yin wanka da Asubah ba ga kuma isha hakan yasa kawai ta koma d’akin nasu taje k’asan gadonta ta jawo bokiti mai ruwa. Towels d’inta guda biyu data sak’ale a jikin bunk ta kai hannu ta zari d’aya, ta wuce toilet ta je ta yi wankaan ta, ta dawo. Hular kanta da ta yi sharkaf da ruwa ta cire, gashin ya zubo. Ita dai ta san ta bar towel d’aya a jikin bunk amman da tazo da nufin d’auka domin tsane gashin kanta, sai ta neme shi ta rasa…dube dube ta fara yi har su k’asan gado, tana d’agowa suka kusan yin karo da Zainab tana mik’o mata towel d’in, sannan tace “Sorry na wanke face d’ina ne kuma duk towels d’ina sun yi datti shine na ara na goge fuskana, ungo.” Murmushi Maryam d’in tayi tasa hannu ta karb’a. Zainab d’in ce tace mata “Me za kiyi ba ga wani a jikin ki ba?” “Gashina zan tsane” Ta bata amsar tana k’ok’arin fara goge kanta. Bata kawo komai a ranta ba, ta hau goge gashin da towel d’in, har ruwan ya d’an fallatsar wa Zainab. Juyawa Zainab d’in tayi ta nufi Majalisar su. Ita kuma Maryam sai da ta gama gogewa ta nad’e shi a kanta ta shiga corner d’inta ta shafa mai ta saka kaya, tayi addua abinta ta kwanta . Har lokacin tana jin k’us k’us d’in maganar su Zainab dan ba suyi bacciba amman a hankali suke maganar sunata k’us k’us, daga bayama tashi Zainab d’in tayi ta fita ita da wata k’awarta,ita dai Maryam bata san lokacin da suka dawo ba bacci ya kwasheta. Kiran sallar farkon da aka maka a mosque d’in dake tsakiyar hostels d’in ne ya farkar da ita daga baccinta mai cike da mafarkin Abba….. ‘yana ta zuba mata murmushi ya rik’e hannunta yana janta ita kuma ta kasa zuwa garesa, kamar akwai wani abu da yake janta baya’, haka ta ji a mafarkin. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 12 Da ‘bell’ ta yi amfani wajen tashi y’an hostel d’in nata tukunna ta wuce ta yi alwala ta fice mosque. Sai da gari ya d’an yi haske tukunna y’an mosque d’in suka fara dawowa. A hanya ne wata roommate d’insu da suka fito daga mosque d’in tare take ce mata “gaskiya Maryam kin b’ata wayonki, ban yi expecting haka daga gareki ba, gashi yanzu kin janyowa kanki! Allah kad’ai ya san hukuncin da za’a yanke miki.” Da mamaki Maryam take kallonta kafin tace “Ban gane ba Hafsa, mai nayi?!”. Tsaki Hafsat d’in tayi kafin tace “Ai ga irinta nan, daman Zainab ta fad’a.. k’aryata mutane zaki yi! Ni dai shawara ta idan an je wajen principal ki rungumi laifinki, dan wallahi kin san halin principal idan kika yi mata k’arya laifin ki k’aruwa zai yi.” Zuwa yanzu kam gaban Maryam ya fara dukan uku uku gashi sun iso bakin gate d’in shiga hostel, hakan yasa tayi saurin rik’o hannun Hafsat tace “Hafsa dan Allah d’an tsaya, kin saka ni a duhu, kiyi mini bayani, sai magana kike ta yi a baibai.” Har Hafsat ta bud’e bakinta zata yi magana, wasu y’an mata biyu suka fito da bokiti a hannunsu, suma duk y’an d’akinsu ne, kallonsu sukayi kafin d’ayar tace “Ah lalle Hafsa, me ake koya miki? lalube ko shafa mai??.” Hararar su Hafsat tayi sannan ta cire hannunta a na Maryam ta yi cikin hostel ba tare data waiwayi kowa ba. Su kuwa dariya suka saka sannan suka nufi unity tap d’in dake tsakiyar hostels d’in domin d’ibar ruwa. Ita dai Maryam har ta shirya…taje dining aka nufi assembly ground, duk tayi sukuku, k’ok’ari take yi ta fassara kalmar ‘lalube ko shafa mai’ amman ta kasa, saboda amsar da kalmar take bata ba abune mai ma’ana a tsarin rayuwar da take yi a makarantar ba. Ana shirin roundin up assembly d’in Principal ta rambad’a kiran sunan ta a mic tace kar taje class ta sameta a office d’inta. To fah!! Dan yanzu kam Maryam ta gama rud’ewa. Da kyar a daddafe ta k’arasa office din principal d’in, gaba d’aya jikinta in banda karkarwa ba abunda yake yi, gashi gabanta sai fad’uwa yake. Knocking tayi, ta ciki aka bata izinin shiga. Tana shiga mamaki ya kamata sakamokon ganin Abba, metron da house mistress d’insu duk a zazzaune a cikin office d’in. Da kyar ta iya k’arasawa ta zauna ta gaishesu, principal d’in ce kawai ta iya amsa ta Abba kuwa kanshi a k’asa yake tunda ta shigo, bai d’ago ba. Gyaran murya principal d’in tayi sannan ta mik’o mata wata takarda, tace mata “ta karb’a tayi signing.” A hankali ta mik’e taje ta amsa, tun kafin ta dawo wajen zaman ta ta fara dubawa….ai kuwa bata iya k’arasawa wajen zaman nata ba sakamokon rikicewar da ta sake yi tashi d’aya ta shiga matsanancin tashin hankali…… Karantawa take yi tana sake duba takardar ‘expell’ d’in da aka bata ga sunanta b’aro b’aro a jiki, hankalinta bai gama tashi ba sai da taga dalilin korar! “Innalillahi wa inna ilaihirraji’un” shine abinda ta fara maimaitawa idanunta na zubar da kwalla, a hankali ta k’araso ta durk’usa a gaban teburin principal d’in ta fara magana muryar ta na rawa “Ma, wallahi this is not the truth, pls don’t expel me, i promise I won’t talk to Abba ever again!. I don’t want my parents to find out about this. I have been framed here I swear….” Cikin rashin walwala principal d’in tace mata “Don’t worry your parents already know about this since yesterday, they are on their way now as we speak.” Rushewa Maryam tayi da kuka, ta fara magiya, tana cewa “sharri aka yi musu” …..tana alk’awarin rabuwa da Abba har abada, amman principal d’in bata saurareta ba kawai dai tace mata “Ita fa ta riga ta gama magana, so ta jira zuwan iyayenta kawai.” Metron kuwa munafuka in banda zuga principal babu abunda take yi, hadda cewa “ai ranar tun a clinic ya fara rungumeta. Waye waye” Sai faman zuba dai take yi, ba ita tayi shiru ba sai da principal ta aiketa ta je ta kira Zainab da wasu class mates d’insu. Su Zainab sun shigo bai fi da minti goma ba Madu da Shuwa da Ya Usman suka shigo. Da gudu Maryam taje ta fad’a jikin Shuwa tana kuka tana cewa “wallahi k’arya ake mata.” Kama kafad’unta Shuwa tayi sannan ta ajjiyeta a kujerar gefe, ba tare da tace da ita komaiba! Ta k’arasa suka je suka zazzauna a kan kujerun suka gaisa da mutanen wajen. Bayan an gama gaisawa ne principal d’in tayi gyaran murya ta nuna Zainab tace “ Yarinyar nan ta zo ta sameni last week akan maganar sister d’inta da wannan Yaron” ta yi maganar tana nuna Abba kafin ta d’aura da cewa “I was surprised because irin haka bai tab’a faruwa ba, dan it’s a very strict rule ‘ba a soyayya tsakanin malami da d’alibi’! I don’t know why they choose to break the rule. I called their house mistress first, Ina so ince mata ta sakama Yarinyar ido but to my surprise sai take ce mini ‘ai ta riga ta sani already, amman kawai dai gaisawa suke yi, kuma basa zance. Dai ya fad’a mata yana sonta ne amma basa soyayya a makaranta because she warn them and sun yi biyayya da abunda ta fad’a’ She gave me good reasons, wanda reasons d’in da ta bani ne ya sa na yi deciding to just let it go, dukda na san it’s not allowed but kamr yadda tace if basa soyayya a makaranta I see no reason da zanyi interfering. After two days ina zagaye da daddare, wanda ba kowa ne ma ya san ina yin hakan ba, saboda Ina yi ne to make sure all is fine. A time d’in na bi ta jss2 block and I saw them together, I know Maryam very well tunda shadow prefect d’inmu ce and Abbas shima ba b’oyayye bane shiyasa nayi saurin ganesu….ban ji d’ad’in yadda na gansu ba! He was holding a book tana so ta karb’a ya hanata, and they are sitting too close to each other! Na so inyi musu magana but a yadda raina ya b’aci a time d’in sam bana zan ma iya kallon Yaran. So na yanke shawarar fara yiwa house mistress d’insu magana first, i was very disappointed a ita da su. So, na sameta nayi mata magana and ta gaya mini cewa ‘wallahi bata san suna zama guri d’aya ba, that was when I called their metron, and she told me ‘ai tun time d’in da Abba ya fara zama night prep tare suke zama kullum, and sometimes they even hug, kuma basa tafiya sai kowa ya watse, in sun gama abinda zasu yi’.” Kukan Maryam ne ya k’aru kafin tace “wallahi k’arya ne, Hajiya Shuwa dan Allah ki tsaya kiji nawa kar ki yarda da maganar su…..” Cikin tsananin b’acin rai Ya Usman yace “Wallahi Maryam idan bakiyi mana shiru ba sai na b’abb’allaki a nan!!” Ganin yadda ya taso yayo kanta kuma taga alamar ranshi a mugun b’ace yake dan bata tab’a ganinshi a irin wannan yanayi ba, ya sanya ta yi shiru, ta hau k’ok’arin tsaida kwallarta ta… Numfashi principal d’in taja sannan ta ci gaba “Na kira 2 to 3 children a js2 and sunce gaskiya su basu tab’a ganin komai ba, kawai dai basa tafiya tare da su kamar yadda metron tace. So hankali na ya d’an kwanta but dukda haka sai na kira Zainab saboda Ina son sake jin bayaninta dan Insan ta Ina zan fara “A nan ne ma take sake tabbatar mini da cewa ‘ai Maryam d’in already tana da mijin da zata aura a gida!.’ Na kira Yayan Abba dan in fad’a mishi halin da ake ciki ince yayi wa Abban magana ko In d’auki mataki, amma wani abun mamaki kamar had’in baki sai shima yake gaya mini cewa ai shima Abba tun bai kai hakaba already Mahaifinsu ya zab’a mishi wadda zai aura cousin sister d’insu, kuma kowa ya san da maganar…. Shi Ya’yan nasa ma he was very surprise da yaji wai Abba yana soyayya da wata….. So definitely kunga ba soyayyar gaskiya Maryam da Abba suke yiwa juna ba kenan, ko?. A time d’in bana son yanke hukunci cikin sauri, shiyasa na saka Zainab da those two” ta yi su maganar tana nuna k’awayen Zainab da suka shigo tare, tukunna tace “nace su saka musu ido sosai.! Yesterday around 11 metron taje gidana, saboda nace musu ko k’arfe nawa ne idan abu ya faru su sameni a gidana na quaters in dai inanan…. Banji dad’in abinda metron ta gaya mini ba at all, although shine abunda nake suspecting but Maryam is one of our best students sannan d’a na kowa ne. Kasa bacci nayi da jin maganan metron that’s why nima kawai immediately na nemi land line d’inku…..” Shiruuuu!! kowa yayi kafin principal d’in tace “Zainab, ku maimata musu abinda kuka fad’a mana.” Zainab ce tafara magana “Daman kullum idan ya shigo aji sai yayi ta kulata, tun yana b’oyewa har ya daina, tou akwai k’anwar k’awar mu a jss 2 itace ta fad’a mana abunda sukeyi, itace ta zo ta samemu jiyama tun kafin a tashi tace wai gashi chan ya d’auketa sun fita ba a san ina suka je ba!. Mun yi ta jiranta a hostel bata dawo ba, daga k’arshe dai sai after 11 tukunna suka dawo kuma data shigo har wanka tayi dan sai da na tab’a gashinta na tabbatar!. Shiyasa naje na samu metron ita kuma tace yanzu zata je wajen ki ba sai gobe b..” Sai a lokacin Abba ya d’ago kai ya kalli Zainab da idanuwanshi da suka chanja kala..wanda hakan ne ya sa ta kasa k’arasa maganar ta. House mistress d’insu ce tace “amman ku, kun tabbatar fita sukayi kuwa? Because d’azu da sassafe naje wajen gateman yace min jiya Abba shi kad’ai ya fita kuma sai wajajen 11.” Da sauri Zainab tace “Ai gidansu na coppers na staff quaters suka je……” Ita kam Maryam zuwa yanzu muryarta har ta dishe tsabar kuka!! Madu ne ya kirata yace “ta zo!” Tana zuwa yace “Da gaske ne???” Da sauri ta fara girgiza kai tana kuka, abin tausayi…. Metron sarkin zuga tace “ki ji tsoron Allah har wanka fa sukace kin yi!”. Cikin k’ok’arin son fahimtar da su Maryam tace “Eh nayi wankan amman wallahi ba wank.....” Bataga k’arasowar Ya Usman ba sai sauk’ar marin da taji wanda yasa ta fad’uwa a wajen gefen bakinta ya fara zubda jini, tana k’ok’arin tashi taga ya sake yunk’urawa da nufin rufeta da duka….. Ta gama sadak’arwa tana jira taji sauk’ar dukan! Jin shiru yasa ta d’ago, Abba ta gani ya kare mata…a hankali ya sunkuyo kanta ya kamo hannunta ya mik’ar da ita cikin tafin hannun nata ta ji yana cusa mata takarda karb’a tayi tana kallonshi shima Itan yake kallo da idanuwanshi da suka yi jazir!! A hankali yace “I luv u Maryam.” Bai tsaya jin fad’an da su metron suke mishi ba na ‘ya kama hannunta a gaban iyayenta!’ Kawai ya juya ya fita. Madu ne ya cewa Shuwa su tashi su tafi, hakan yasa ta mik’e ta yiwa principal sallama wadda take ta bawa Shuwa hak’uri tana cewa “She is just looking out for Maryam, ba dan hakanba da ta barta a makarantar, gara ta tafi gidan iyayenta su saka mata ido.” Jinjina kai Shuwa tayi sannan tace “ba damuwa.” Ta juya ta fice. Ko kayanta su Shuwa basu bari ta koma hostel ta d’auko ba, cewa suka yi ‘Zainab ta taho mata da shi’. Hakanan tana kuka tana komai suka shiga mota aka ja aka yi gida da ita. Zainab kuwa yau farin ciki a wajenta ba a cewa komai, murna takeyi ai tunda Maryam ta tafi to fa duk wata hanya da zata bi sai ta bi ta cusa soyayyar ta a zuciyar Abba, kasancewar yau suna da period d’inshi daman yasa tun kafin su k’arasa class ta tsaya ta wanke fuskarta a tap, akayi y’an shafe shafe, k’awayen ta suka duba suka tabbatar mata tayi kyau tukunna aka nufi class ana tunanin hanyoyin da za a bi a karkato da zuciyar Abba gareta! Sai dai kuma har period d’inshi ya shiga ya fita bai shigo ajin ba, washegari ma haka….ahaka suka shafe kusan sati babu Abba babu alamar shi. Zainab har office d’inshi taje ta tarar a rufe….haka ta dawo jiki duk ba kwari zuciyarta ta a cunkushe, haka take rayuwa a makarantar gaba d’aya komai baya mata dad’i, sauk’inta d’aya ma ba Maryam. A b’angaren Maryam kuwa tun da suka shiga mota take kuka har suka isa gida, a tunanin ta za a yi mata fad’a ko duka amman ba wanda yace mata komai, amma fa ko gaisheda Shuwa ko Madu tayi a cikinsu babu mai amsa mata, ko suna zaune idan ta zo ta zauna to zasu tashine su bar mata wajen, hatta Bilkisu da suka shak’u sosai a duk lokacin da Shuwa ta gansu tare sai tazo ta d’auketa ta kuma hau yi mata fad’a, tun Bilkisu tana kulata a b’oye har ta daina saboda a d’aki Shuwa take sakata ta kunna mata kallo, ko girki an daina girkawa da Maryam a gidan! A wajen mutum d’aya kawai take samun sauk’i itace Baabaa Talatu dan a gidan ta ma take cin abinci sai kuma Ya Usman wanda yake wani sabon shige mata kwana biyun nan ta kasa gane mishi kwata kwata, itafa ko ba Abba ba zata auri Ya Usman ba! She is not suppose to be feeling this towards Ya Usman amman she can’t help it, kawai ita all she knows bata sonshi kwata kwata bata sonshi ba zata iya zaman aure da shi ba. Yau satinta d’aya da kwana d’aya da dawowa daga boarding, gaba d’aya duniyar ta yi mata zafi, zuwa yanzu rashin kulata da iyayenta sukeyi ya fara bata tsoro dan har ta rame ba kad’an ba. In ba wajen Baaba Talatu taje ba tou kullum tana d’aki ita d’aya. Yau ma ganin shiru zai haddasa mata wata damuwar bayan wadda take ciki ya sanya ta yanke shawarar fita dan shan iska ko ta samu ta d’an ji sauk’i. Hijabinta ta d’auka ta nufi wajen Baaba Talatu, tana shiga a babban tsakar gidan ta had’u da Ya Usman tare da wani Abokin sa suna hira yana ta dariya, ta dad’e bata ga dariyar sa irin haka ba, tun kafin ta k’araso taji yana cewa “To kai ba ka tsaya wasa ba?! Kawai ka jira zan baka y’ata ta farko” Magana Abokin yake mishi amman bata ji sosai sai dai taji kamar yace “Ranar juma’ar nan ne wai da gaske?”. Ita dai bata gane me suke nufi ba ta zo ta gaishesu. Sai a lokacin ma Ya Usman ya lura da ita, Abokin ne ya amsa yana cewa “uwar gida ya gida?” Da kyar tace “Lafiya” Dan in Abokanan Ya Usman suka ce mata uwar gida duk sai taji wani iri, shiyasa bata tsaya biyewa tsokanarta d’in daya shiga yi ba tayi wucewarta cikin gida. Ta isa k’ofar Baaba Talatu kenan har zata tura taji suna magana, sai da ta kara kunnenta tukunna ta gano ita da Ya Jamilu ne…mamaki da murna takeyi a ranata tace “yaushe ya dawo?”. Har ta fara k’ok’arin shiga sai kuma taji maganar da yake yi daga ji ran shi a b’ace yake dan yana maganane cikin d’aga murya… “Habaa Baaba! Yanzu abunda za a yi an kyauta kenan??? Shi fa Usman d’in da kansa yake ce mini tace ‘bata sonshi’! Garin son sake k’ulla zumunci sai kunje kun yi abinda zai tarwatsa komai!! Ku kanku fa kun san halin Maryam tun tana Yarinya tanada mugun taurin kai!! Ya kamata ku fahimci tunda har tace muku a yanzu wanchan Yaron take so to shi d’in take so a yanzun! Amma baku tsaya kun yi nazari ba, tashi d’aya kun rabota da shi sannan kuma kawai rana tsaka kun zo kun ce zaku d’aura mata aure wannan juma’ar ita da Usman?? Idan wanchan Yaron ne bakwa so kwata kwata ai at least dai kwa bari idan ma auren ne ita da Usman d’in ya kamata a bari su sake fahimtar juna, dan wallahi idan aka yi auren nan bata sonshi a haka a wannan yanayin da take ciki to ba zata tab’a son shi ba.” Baba Talatun ce itama ta rufeshi da fad’a tana cewa “To ubana!!! wanda ya san salon so! Yaushe aka haife ka ne Jamilu?? Bari kaji….rud’u ne yake damun Maryam amman ba wani Abba da takeso ni na san Usman take so, kuma bari kaji, ko da ace bata auri Usman ranar Juma’ar nan ba to tabbas Abban ta zai aurar da ita a sadaka ranar dan yayi wannan alk’awarin, furucin nasa ne ma ya sa Babanku yace ‘ga Usman’ to kaga ai taimakon tama zai yi! Wai dan ma ban ce d’a na ba zai auri ragowar wani ba!?” “Haba! haba!! Baaba, bai kamata ku yarda da zancen su Zainab akan Yarinyar nan ba fa, idan y’an layi suna yamid’id’i kema sai ki biye su? Maryam fa kamar y’a take a wajen ki, kuma kin san basa shiri da Zainab dama.” Da sauri Baaba ta karb’e tana cewa “Ai Maryam bata d’aukeni uwa ba tunda gashi k’iri k’iri tana so ta guji Usman. Kuma kana nufin dan basa shiri da Zainab d’in za ta k’ulla mata sharrine??” Ji tayi Ya Jamilu yaci gaba da magana “Ni dai in za ‘a j....” Maryam kasa tsayawa ta cigaba da jin maganar tasu tayi. Zuwa yanzu ta fahimci komai, tuni fuskarta ta jik’e sharkaf da hawaye da uban gumi…nan da nan ta fara ganin dishi dishi! Da gudu ta fita a gidan ko bi ta kan Ya Usman da yake kiran ta bataiba! Taya mahaifinta wanda yake masifar sonta zai yi sadaka da ita??? lalle kuwa zata kashe kanta, wato sun yarda da maganar mutane akan ta kenan?…. Da wannan tunanin ta isa gida tana shiga falon sukai kicib’us da Madu wanda yake shirin fita .. Goge hawayenta tayi sannan ta durk’usa a gaban shi ta hau magiya “Abba dan Allah ka yi hak’uri, na rantse da Allah sharri aka yi mini, wallahi Abba bana son Ya Usman, kar ka aura mini shi dan Allah…” Zagayeta Madu yayi ya wuce ya fita ba tare da yace mata komai ba. Mik’ewa ta yi ta nufi Shuwa wadda ta fito daga kitchen yanzu itama ta fara yi magiya tana “Hajiya dan Allah ki kulani yau, ki yarda dani wallahi sharri aka yi mini, baba son Ya Usman kar ku yi mini auren dole, wallahi k’arya su Zainab aka yi mini! Yanzu kin yarda da abinda suka ce??” Da sauri Shuwa tace “Na yarda!!! Duk wani abu da aka fad’a na yarda, ko da ace zuciya ta tana son k’aryatawa, to zan tirsasa mata in tilastawa kaina in gasgata hakan ne. Tunda har zaki iya k’etare umarnina! Maryam a nan” Ta yi maganar tana nuna k’ofar kitchen, sannan ta ci gaba “A nan na zaunar dake nace miki ki rabu da wannan Yaron, kika nuna mini kin amince, amman saboda kin raina ni, ban isa in baki shawara ki d’aukaba, kuma ki nuna ban isa dake ba shine kika ci gaba da kulashi!! Jiya principal d’inku duk sai da ta fad’a mana komai har yadda yace “yana son ki a gaban kowa da yake shi bashi da kunya ke kuma kika biye masa bayan kin san da zancen Usman!! Daman na riga na gama yanke shawarar ko ba a kore ki ba to baza ki ci gaba da zama a makarantar ba! Maryam kin bani mamaki matuk’a wallahi, banyi tunanin haka daga gareki ba sam, kuma nima zan baki mamaki, dan wallahi idan baki tsaya kin auri Usman ba to ki saka a ranki babuni babu ke! Idan taurin kai kike tak’ama dashi ina so ki san cewa a wajena kika gada! Da ni dake aga wanda zai janye.” Kuka Maryam ta sake fashewa dashi, ita kuwa Shuwa ta wuce tayi hanyar d’akinta ta barta a wajen…Bilkisu ce ta zo tayi ta lallashinta har aka samu ta d’an yi shiru ta tashi suka tafi dakinta. Haka ta wuni har dare sukuku, tana d’akin taji Baaba Talatu ta shigo tana tambayarta, wai “Usman yace mata d’azu taje ta lab’e mata ita da Jamilu” Shuwa ce tace “Ai yanzu Maryam komai ma akace tayi ba zan musa ba, kiji fa har da lab’e ta koya, tabbas ta yi kam dan nan ta shigo tana ta faman yi mana haukan k’arya….” Nan dai Shuwa ta hau labarta mata yadda sukayi d’azu… “Allah ya kyauta” Baaba Talatu tace. Daga nan suka hau shirye shirye. Bayan sun gama ne taji Baaba Talatu tana cewa “bari ta lek’ata kafin ta tafi, da mugun sauri ta shige bargo ta hau barcin k’arya, tana jinta ta lek’a har fuskarta tana cewa “Ashe ma tayi barci” Ita dai bata kula taba har ta juya ta fita, dan ita yanzu Baaba Talatu ta fara bata mamaki, k’iri k’iiri take nuna son y’ay’anta, sab’anin su Shuwa. Da daddare tana daki ta idar da sallah abun duniya ya mata yawa, ita ta rasa ta gudu ne ko ta tsaya bama ta san ta Ina za ta fara ba amma idan akawai abunda yake da yak’ini akai shine ‘ko sama da k’asa zasu had’e ba zata tab’a yarda da auren Ya Usman ba!!’ Idan ta yarda kenan tama karb’i laifin sharrin da aka k’ala mata ta yarda ta yi d’in kenan!!!Shigowar Shuwa ne ya katse mata tunani. Da sauri ta mik’e ta hau gaisheta, bata amsa mata ba kawai ta juya tace “kije parlourn Abban ku yana son ganinki.” Daganan ta sa kai ta fita. Ninke sallayar Maryam tayi ta bi bayanta ta nufi parlourn Abban nasu. Tana shiga ta sameshi yana shan shayi, da Al’Qurani a hannunshi…sai da ta jira ya kai aya ya rufe sannan ta gaida shi…cikin kulawa ya amsa mata kafin ya ce “Maryama.” A hankali ta amsa kanta a k’asa. Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya fara magana cikin nutsuwa… “Ki sani ko da ace duk duniya zasu yarda da abinda akace a kanki ni ba zan tab’a yarda ba.” Da sauri ta d’ago kanta ta kalleshi wasu hawayen farinciki suna gangaro mata, bata san lokacin da murmushi ya sub’uce mata ba. Gyad’a mata kai yayi sannan yaci gaba “na san halinki na san tarbiyyar ki, fiye da kowa. Amman Maryam ya zama dole a d’aura miki aure ranar juma’ar nan!!”. “Innalillahi wainna ilaihir rajiun.” Shine abunda Maryam ta fara maimaitawa, tana hawaye sannan tace “Abba yanzun fa kace ka yarda da ni.” Jinjina kai yayi alamar ‘eh’, kafin yace “Tabbas Maryam na yarda dake amman kuma auren shine mafi alkhairi a tattare dake, makarantar nan da kika yi sananniyar makaranta ce, yanzu sun baki expel!! Ko kin san cewa babu makarantar da zata d’auke ki da saninsu? Sannan mahaifiyarki tace ‘ba zaki k’ara komawa makaranta ba!’ Zaman me to za ki zauna yi?? Sannan abu na biyu, ban san ya akayi zancen nan ya zagaye gari ba, amman jiya har meeting aka had’a da dattijawan unguwa, saboda ke!! Abun takaicin anan shine ba zan iya kare ki ba saboda all evidences are against u, abunda nake tsayawa tsayin daka dan ganin al’umma basu fad’a ciki ba, yau nine ake zargin y’ata da shi... Maryam da ace kin yi abunda ya kaiki makarantar kawai baki tsaya kula Yaron nan ba da duk haka bata taso ba, yanzu idan shekaru suka yi gaba, ba lalle ki auru ba domin kusan kaf layin nan maganarki akeyi, kuma kin san idan miji ya fitowa mace a wajen y’an unguwar su da makarantar da tayi ake bincika halayenta wanda inada tabbacin ba zasu bada shaida mai kyau a kanki ba! Maryam hakan zai fi yi mini ciwo fiye da aurar dake da zanyi a yanzu, ko ba komai hankalina a kwance yake da Usman, na san zai kula dake matuk’a. Ki yi hak’uri, wanda ya riga ka zama dole zai riga ka tashi, ki rungumi k’addararki, baki da wayo shiyasa aka yi saurin k’ulla miki sharrin da ba zaki iya fitar da kanki ba….” Kukan da Maryam take yi ne ya sanya shi sak’k’owa daga kan kujerar da yake, ya shiga lallashinta da fad’a mata kalamai masu kwantar da hankali har sai da yaga tayi shiru tukunna ya sallameta, jikinta a mace haka ta tashi ta fita. A hankali ya saka yatsarshi ya d’auke kwallar data taru a idonshi, sannan ya koma ya zauna ya jingina da jikin kujerar had’e da lumshe idanuwanshi……. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 13 Maryam tana shiga d’aki ta fad’a kan gado ta fashe da wani mugun kuka…ta kusa awa d’aya tana abu d’aya, idanuwanta duk sun kumbura fuskarta tayi jajawur!!! Sai da tayi mai isarta tukunna ta hak’ura ta shiga sauk’e ajiyar zuciya akai akai…. Kamar wadda ta tuna da wani abun ta mike zumburr!! ta nufi wajen kayanta, k’asan ta d’aga ta zaro wata farar takarda..tun ranar da Abba ya bata takardar bata duba ba, warewa ta shiga yi a hankali, tana gama bud’ewa idanuwanta suka sauk’a kan wasu y’an nambobi a jere waenda ko ba a fad’a mata ba ta san number landline d’inshi ce. “Lalle ma Abba!! wato ma nice zan kirashi!! despite the fact that na yi mishi kwatancen gidanmu!! he didn’t even bother to come. Sannan kuma all this time already yanada wadda zai aura ya tsaya b’ata mini lokaci……Allah ya isanaa!!” Ta fad’i hakan a cikin zuciyarta cikin d’aci da zafin zuciya. Jin zuciyarta tana shirin fashewa ne yasanya ta duk’unk’une takardar ta jefar da ita ta koma ta zauna a kan gado ranta yana sake b’aci. Gaskiya Shuwa ta fad’a da tace mata “b’ata mata lokaci kawai zai yi amma yanada wadda zai aura.’ Dan kuwa gashi ashe Abba yaudarar ta yake yi ita bata sani ba, dan inda ace son gaskiya yake mata ai da zai lek’o ta. Ganin zuciyarta tana shirin fashewa tsabar takaicin abinda take tunanin yayi mata gashi zaai mata auren dole kuma duk shi ya ja amman bai ma damu da ya san halin da take ciki ba, kuma duk yadda ta k’ok’arta ta kasa rabashi da zuciyarta! Hakan ya sanya kawai ta yanke shawarar ta d’auki number ta kirashi, ta fad’a mishi ta fa san yaudararta yayi, at least zata rage wani b’angaren na damuwa takaici da tashin hankalin da take a ciki!! kwana biyun nan. Sai dai kuma Allah yasa yana gidan, dan ta san maybe a time d’innan yana school yanzu…. Da wannan tunanin ta mik’e ta isa inda ta yar da duk’unk’unanniyar takardar….da kyar ta iya bud’ewa dan har sai da ta d’an yage tsabar yadda ta d’unkuleta ta jefar d’azun…Haddace nambobin tayi a kanta sannan ta nufi falo. Kamar ko da yaushe landline d’insu yana kan tebur kusa da tv, kamar munafuka haka ta lek’a kitchen ta tabbatar Shuwa bata nan maybe ko ta fita ne Itada Bilkisu dan gidan shiruu, a hankali ta isa ta murza nambobin ta d’aga ta kara a kunnen ta…ba‘a wani dad’e ba aka d’aga. “Hello who is there?” Taji ance mata A hankali tace “please i want to speak with Abba.” “Ok! hold on, let me tell him.” Mutumin yace sannan taji yana magana “Sir, someone wants to talk to you.” Daga chan nesa taji muryar Abba yana cewa “Who’s it?”kamar bashi da lafiya Jin muryar tasa kuwa da tayi , sai taji kamar rabin damuwarta ya kau, dukda haushin sa da take ji. Mutumin ne ya sake tambayar ta “Ma’am pls what’s your name?” “Maryam” Ta bashi amsa. Tanaji mutumin yace mishi “Maryam.” Kafin kace kwabo muryar Abba har ta iso cikin dodon kunnen ta, da alamun har ya k’araso ya amshi wayar, muryarshi har wani rawa take yi taji yana cewa “Maryam! da gaske kece? Ya kike? how is everything? Zan zo soon, in shaa Allah…i missed you a lot!” Ya fad’a kamar zai yi kuka wanda hakan yasa Maryam ta ji tausayinshi a d’ayan b’angaren zuciyarta kuwa tana ganin rainin hankali irin na Abba wai ‘he missed her!’ amman kuma shine ya kasa zuwa ya ganta?. Murmushin takaici tayi sannan tace “Ai ba zaka damu ka zo ka ganni ba tunda kana da wadda zaka aura, Abba I just call saboda Ina so in tambayeka dalilin da yasa ka tsaya b’ata mini lokaci, bayan ka san an yi maka mata??” Tayi mishi tambayar ranta yana sake b’aci. Murmushi taji yana yi, kafin yace “Even your anger sounds sweet to me Maryam, i‘m just happy Ina jin muryar ki yanzu..” Maryam zuwa yanzu ranta ya b’aci sosai kamar ta fashe da kuka haka take ji… Jin tayi shiru yasa yace “Maryam kema idan kin san kina da wanda zaki aura mai yasa kika tsaya kulani??” Jin tayi shiru yasa shi sake maimaita mata tambayar. A hankali tace “Ni bana sonshi, tun farko” Da sauri yace “nima haka wallahi & Inaso ki san cewa ‘ni Abba na yi miki alk’awarin ke! Zan aura duk runtsi, ko menene zai faru after that I don’t care, i‘ll choose our happiness akan koma.......” Kukan da ta fara yi ne ya saka shi kasa k’arasawa.. nan ya fara tambayarta “mai ya faru??” Cikin sheshshek’ar kuka tace “Abba duk wannan ba shi da amfani yanzu, da ace ka zo ka lallab’a Abban mu da duk hakan bata faru ba, amman ya....” Cikin tare numfashin ta yace “Maryam Yayana ne yayi grounding d’ina for 2 weeks!! Ya ma k’i ya tsaya ya saurareni kwata kwata, gaba d’aya baya kulani… Bayan tafiyar ku ya zo nema mini transfer, shinefa wannan matar ta tisa shi a gaba ta dinga yi mana sharri…Amman kar ki damu, duk fushin da Yaya zai yi dani na san 2 weeks d’innan yana cika ya huce, kuma zai saurareni, daga nan zan zo in sha Allah.. Yau sauran 5 days ai kwanankin su k’are.” Ya fad’a sounding so relieved. “Kafin nan an d’aura mini aure” Ya ji Maryam d’in ta fad’a.. Ba abinci ko ruwa yake sha ba amma wata muguwar kwarewar da yayi sai da ta d’auke shi kusan minti uku yana tari tukunna ya dawo dai dai. Cikin tsananin tashin hankali yace “kiyi mini wasa akan komai Maryam amma banda wannan!! me hakan yake nufi???” Yayi mata tambayar da kakkausar murya… Duk abinda ya faru daga dawowarta zuwa yanzu babu abunda Maryam ta b’oye mishi. Ga mamakinta bai ce mata komai ba, kawai taji ya ajjiye wayar. Ta kai kusan minti d’aya da kan wayar a hannunta, tukunna ta share hawayenta ta ajjiye ta juyo da nufin komawa d’aki suka yi ido biyu da Shuwa. Gabanta ne yayi mugun fad’uwa, cikin rawar jiki da na murya mai cike da in ina ta k’arasa inda Shuwan take ta hau kame kame “Da da ddmn kawai nn ccemishi bai kky…” Wani wawan marin da Shuwa ta kwasheta da shi ne yasa ta kasa k’arasawa, bata dawo dai dai ba ta k’ara mata wani wanda yasa har sai da ta kai k’asa tana shirin tashi ta rufeta da duka….. Sai da Shuwa tayi mata lilis!! kamar ba ita ta tsugunna ta haifeta ba, dan har sai da takai bata iya kuka tsabar azaba, tukunnan ta kyaleta tana mai cewa “Tunda na lura kin daina fahimtar yaren magana watak’il ki fahimci wannan!. Gani kike yi yanzu kinfi k’arfin kowa ko? To ni da ke mu zuba mu gani.” Tana gama fad’in haka ta wuce ta isa wajen landline d’in, ta gwada yafi sau nawa amman dai ko ba’a d’auka bane ko kuma bai tafi ba. A haka tazo ta wuce ta tsallake ta, ta tafi ta barta a kwance a falon tana kukan wahala.. Ganin ba zata iya taimakawa kanta bane yasa kawai ta hak’ura, a wajen baccin wahala ya kwasheta. Kamar a mafarki taji ana tab’a fuskarta ana haskawa da tochila, bud’e idanuwanta taci gaba da yi, bata ganin komai sai hasken fitilar…sama sama take jin muryar Ya Usman yana cewa “Abba ba sai ka kira Likitanba, ta farfad’o. Da sauri Madu ya k’araso yana tamabayarta “mai ya faru? Mai ya sameta?” Bata ida bashi amsa ba Shuwa wadda ke shigowa yanzu tace “Ni da itane.” Da mamaki ya mik’e ya juya yana mata kallon tuhuma kafin yace “ke da ita? ban ganeba.” “Dukanta nayi” ta fad’a tana k’ok’arin wucewa. Da sauri yace “mai yasa??dakata mana!! Ina zakije ana magana! Mai ta yi miki?” Ya fad’i hakan yana k’ok’arin hanata wucewa. Da mamaki Shuwa take kallon shi dan bai tab’a yi mata haka ba. Kallon Maryam d’in tayi da take k’ok’arin zama, sannan tace “Kamata nayi ta kira wanchan Yaron na makarantarsu, tana cewa za a yi mata auren dole… shiyasa na zane ta! tunda kunnenta ya daina jin magana watak’il idan aka tab’a lafiyarta zata fi fahimta tun……” Madu bai bari ta k’arasa ba ya rufeta da fad’a, shi kanshi ya manta rabon da yayi mata fad’a hakan suna a su kad’ai ma, ballantana a gaban Yara. Sai da yayi mata tatas tareda kwakkwaran kashedin kar ta sake dukar masa Y’a, tukunna ya juya ya fita ranshi a mugun b’ace! Shi a ganinshi yanzu Maryam ai ta wuce mari ma ballantana irin wannan dukan, kuma abun haushin ta tsallaketa ta barta ko bi ta kanta ma bata yiba, idan ma mutuwa zatayi bata damuba kenan.! Sai da yaje masallaci ya zauna shi d’aya, daga baya yayita karatun Qur’ani tukunna ya d’an samu zuciyarshi tayi sanyi. Shi kanshi ya san idan akwai abu mafi soyuwa a rayuwar sa to Maryam ce, bayajin akwai uban da yake son Y’arshi a duniyar nan kamar yadda yake son Maryam, shi yasa idan ya tuna ranar Jumaar nan zai aura mata wanda bata so sai yaji gabanshi yana ta fad’uwa, amman bashi da yadda zai yi ne shiyasa, hakan it’s the right thing to do. Ita kuwa Shuwa da kyar ta fita daga shock d’in data shiga na fad’an da Madu ya rufeta da shi, aikuwa akan Maryam itama ta zazzage nata fad’an, kafin ta juya tayi d’akinta. Maryam mamakin yadda Shuwa ta juya mata baya lokaci d’aya take yi, ita kam zata yi k’ok’arin yin yak’i da zuciyarta ta rabu da Abba dan taga abun nasu yana shirin tab’a har zaman lafiyan iyayenta. Muryar Ya Usman ce ta katse mata tunani, da sauri ta d’ago ta kalleshi…a hankali yake ce mata “Ya jikin?” “Da sauk’i” tace dashi, tana k’ok’arin kawar da kanta daga kallonshi, dan bata son ganin fuskarshi! Gani take yi shine ummulabaisin haddasa mata duk wata fitinar da take ciki a yanzu. Sake fuskantar ta yayi ya d’an tsugunna a gabanta sannan yace “Inane yake yi miki ciwo?” Chan k’asa a hankali murya ciki ciki tace “Babu ko ina.” Ta fad’i hakan tana turo baki tana k’ok’arin tattaro ragowar k’arfinta domin ta samu ta mik’e. “Mai kike buk’ata??” Ya sake tambayarta. “Ba komai.” Tace dashi a d’an hassale sannan ta mik’e da sauri dan so take ta bar wajen. Mik’ewa shima yayi, sannan yace “Maryam!”. Tsayawa kawai tayi ba tare da ta amsa ko ta kalleshi ba, dan zuwa yanzu ta fara tunanin anya su Ya Usman basu had’a jini da mayu ba kuwa?…. Maganarshi ce ta katse mata tunani “Ba kya sona ko?” Yayi mata tambayar yana isowa dab da ita. Shiru tayi bata ce komai ba. A hankali ya fara magana.... “Maryam ko baki fad’a ba na san bakya sona a yanzu! Amman inaso ki san wani abu guda d’aya! ‘Ko da ace bana sonki, auran had’i za ayi mana, kika yi wannan tawayen, kika nunawa duniya bakya sona kika zab’i wani a kai na to tabbas ko sama da k’asa zata had’e wallahi sai na aureki!! Ballantana kuma Ina sonki! A yanzu bani da burin da ya wuce In aureki saboda abu uku: ‘Soyayyata a gareki ‘In nuna miki kuskuren ki ‘sannan inaso ki gano soyayya ta da take a cikin zuciyarki wadda wanchan Yaron yake k’ok’arin binnewa… Dan haka shawarata a gareki itace ki daina d’aga hankalinki kina k’ok’arin hana abunda ba zai tab’a hanuwa ba’.” Yana gama fad’in haka ya juya ya fita. Maryam bata samu daman tafiya d’akin da tayi niyya ba, hakan ta koma ta zauna a wajen taci gaba da kuka, har sai da Bilkisu ta zo tayita lallashinta tukunna ta mik’e ta isa d’aki tayi ta jero nafilfilinta.. Dan sai a lokacin ma ta lura ashe dare yayi. Washegari da safe taga anata shirye shirye, zuwa k’arfe d’aya motocin y’an Maiduguri suka fara sauk’a, sai a lokacin ta tabbatar tabbas aurenta za ayi, kuma tayi alk’awari idan son Abba zai kasheta ba zata sake kiranshi a waya ba, dukda ta karb’i uzurin shi da ya gaya mata, kuma ta yadda ba son Yarinyar yake yi ba amman mai yasa zai kashe mata waya? kuma bai ma fad’a mata magana mai dad’i ba da zata d’an kwantar mata da hankali….. Tana wannan tunanin wata cousin d’inta ta shigo ta, suna ganin juna suka hau murna, dan ba laifi suna shiri sosai da Maryam d’in. Bayan sun d’an gaisa tace “turota aka yi ta kirata” Tayi sauri ta je kafin fushin Inna ya k’aru…. Tunda Maryam taji an ambaci inna gabanta ya hau fad’uwa! Haka ta zari gyalenta ta fita jiki ba kwari, cousin d’in tata na biye da ita. Tun kafin ta k’araso Kakar tasu ta fara surfa mata fad’a, da yaren Shuwa da Hausa duk had’awa take yi, dan kaf Shuwa ta labarta mata halin da ake ciki…….tana yi sister’s d’in Shuwa suna tayata, ahaka dai suka yi mata tattass sai kuma aka koma nasiha ana cewa “ta bi zab’in da iyayenta suka yi mata, ta kyale wanchan Yaron waye waye….” Ita dai Maryam tayi shiru tanata kad’a kai kamar k’adangaruwa, sai da suka gama tukunna suka hau yi mata gyaran jiki, bayan nan akace taje tayi wanka anjima akwai kaulu. Nan suka shirya kayayyakin Al’ada da su tabarma wai zasu kai gidan ango, Shuwa kam sai ce musu take yi “ai da sun bari, dan babu wani shirin aure da akayi, babu ma fa tambaya ba komai kawai dai Madu yace jumaar nan zai aurar da ita ga koma waye shi kuma Baban Usman yace ga Usman nan, to maybe sai a masallacin gobe za ai komai a lokaci d’aya kuma a d’aura auren” Amma su dai basu biye taba sai da suka kai kayan tukunna hankalinsu ya kwanta, a cewarsu ai wannan dolene dan ma babu lokaci ne da duk wata al’ada sai sunyi….. Gyaran jikin da aka yiwa Maryam na iya wuni d’aya yayi masifar karb’arta, tayi kyau sosai!! Tana zaune gaban mirror tana shafa mai fitowarta kenan daga wanka, cousin d’inta ta d’azu ta sake shigowa tace mata “Wai Shuwa tace tayi sauri taje parlourn Madu yana nemanta yanzu yanada bak’i.” A gurguje ta shirya ta saka doguwar riga y’ar kanti ta zumbula uban hijabi kalar blue black, ta fita da niyyar idan ta dawo sai tayi shirin Kaulun. Kowa ya kalleta sai ya k’ara, ana ta yaba kyawun da tayi haka tazo ta wuce su ita dai bata cewa ‘k’ala’ sai dai murmushi. Tunda aka ce mata Madu yana kiranta haka nan gabanta yake fad’uwa, tana k’arasowa bakin k’ofar falon taji fad’uwar da gabanta yake yi ya tsananta!! Da kyar ta iya saisaita kanta tayi knocking, ta ciki taji muryar Baba Bashir yana cewa “ta shigo” Hannu tasa ta murza handle d’in k’ofar sannan ta tura had’e da tura kai ta shiga, kanta a k’asa. Haka nan ta kasa d’agowa sakamokon yadda zuciyar ta ke bugawa sosai sosai, sai da ta samu waje ta zauna tukunna ta d’ago kanta da niyyar gaishesu...... BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 14 idanunta suka sark’e a cikin na Abba wanda ya kafeta da ido ko alamar kyaftawa bayayi..... Mutumin dake zauna a gefen sa mai tsananin kama da shi ne taji yana cewa “Ma sha Allah, mun sameki lafiya??” Cikin d’an jin kunya ta sunkuyar da kanta sannan tace “ina wuni.” Yana murmushi ya amsa mata, Ita kuma ta juya ta gaida Madu da Baba Bashir, sannan ta gaida Abba wanda ya kasa daina kallonta, ko kunya ta kasa hanashi kallonta a gaban iyayenta. Da kyar ya iya cewa “Lafiya” Wanda ba ma kowa ne ya ji ba sai ita d’in da take kallon fuskarsa. Madu ne yayi gyaran murya sannan ya fara magana “Maryama wannan shine Yayan Abba” Yayi maganar yana nuna wannan mutumin da yake zaune a gefen Abba. Jinjina kai Maryam tayi sannan ta sake gaidashi kanta a k’asa Murmushi shima yayi ya sake amsawa dan a gaskiya Maryam ta burge shi, yanayin nutsuwa da hankalinta sun burgeshi. Madu ne ya cigaba da cewa “Lokacin da muka dawo daga hajji mun baku labarin wani bawan Allah da ya taimakemu aka tseratar da Usman ko?” Jinjina kai ta kuma yi. Ajiyar zuciya Madu ya sauk’e kafin yace “To gashi nan a zaune” yayi maganar yana sake nuna mata Yayan Abba, da sauri ta d’ago ta sake kallonshi wanda shi kuma a yanzu Abba yake kallo har yana d’an tab’ashi da alama nuni yake yi masa da ‘kallon ya isa haka’. Modu ne ya d’aura da cewa “Sunanshi, Alhaji Yahaya Umar Farouk mai turare, d’azun nan aka yi sallama ana son ganina, abun mamaki ina fita sai na ganshi, mutumin da muke nema ruwa a jallo sai gashi yau har gida. Daman ni tun ranar da naga Abba a makarantar ku naso tambayarshi saboda tsananin kama da naga sunayi, amman kasancewar yadda abubuwa suka kasance a ranar ya sanya ban samu dama ba.” Alhaji Yahaya ne yayi gyaran murya sannan yace “Ina mai baku hak’uri, da kuma rok’on mu manta da wanchan zancen har Abada! Saboda hakan ba abune mai maana ba especially idan muka yi duba da yanayin hankali da tarbiyyar Yaran. Laifin su d’aya da suka yi shine da suka tsaya kula juna a makaranta, kowa yasan hakan sab’a doka ne, wanda hakan ne ya sanya ma maganar ta samu gurbi. Ban san waye ya had’a kuma ya fad’i wannan labarin ba amman tabbas na san k’arya ne…. Mu uku mahaifin mu ya haifa a duniyar nan, bani da d’an uwa mafi kusanci dani kamar Abba, shiyasa ko a lokacin da nayi aure ma tare muka tare a chan part d’ina dashi kuma har yau a gidana yake…. na san abinda Abba zai yi na san wanda ba zai yi ba, dukda ance ba a shedar mutum amma ni kam zan shedi Abba a duk inda yake. Na hanashi fita ne tun dawowarshi ba dan komaiba sai dan saboda ita Yarinyar, saboda na san ko wanne Uba idan aka fad’i irin wannan maganar akan y’arsa dole zai d’au zafi ba kad’an ba, so shiyasa na hanashi zuwa nace masa ya d’an bari abubuwa su lafa tukunna sai mu zo, dan already daman na saka a raina zamu zo neman aurenta, dan a duk fad’in duniyar nan bata da mijin da yafi dacewa ta aura kamar Abba. Sannan Abba ya tabbatar mini da soyayyar ta a cikin zuciyarshi, nutsuwa da hankalinta duk ya gamsu dasu sai a lokacin ne ma yake fad’a mini ashe lokacin da yayi rashin lafiya har na taho ban samu munyi sallamaba wai duk a ta dalilin ya nemi gidan nan ne bai samu ba. Kuma ya fahimtar dani Yarinyar da aka zab’a mishi a gida sam baya sonta, ko ya aureta ba zasu zauna lafiya ba, shiyasa naga ya dace muje mu samu Mahaifin mu muyi mishi bayani yadda zai fahimta tukunnan muzo nan To amman kuma jiya sai ya zo mini a hargitse wai jibi za a d’aurawa Maryam aure!! Da na koreshi nace ‘ya jira har sai lokacin da na d’iba mishi yaga maryam d’in yayi tukunna zamuzo’ dan ni a tunanina kawai fad’a yakeyi ba wani aure, dan naga ya k’agu ya ganta d’in A take ya sume min, da kyar ya farfad’o yau da safe, bayan Likita ya tabbatar mana jinin shi ne ya hau saboda damuwar da take neman yi mishi illa, shiyasa a take na saka shi yayi wanka ya d’an ci abinci ko mai d’akina ma ban samu damar gayawa ba muka taho.. A labarin Maryam, ta gayawa Abba cewa ka ce ranar Jumaah zaka aurar da ita, so a iya yadda na fahimta watak’il baka riga kun tsaida mijin ba,ko? Saboda haka gamu nan mun zo neman aurenta ban sani ba ko za a amince a bamu… …….Very short ya d’an basu biography d’in familyn ‘Mai turare’.” Dayake sanannen family ne, nan suka ce “ai suna jin ma sunan familyn..” Baba Bashir ne yace “Alhaaji munji abinda yake tafe da kai, amman kafin komai da farko muna so mu fara yi maka godiya!! Mun gode sosai da taimakon da kayi kwanakin baya, Allah ya saka da alkhairi. Sannan magana ta biyu, ni dai kamar uba nake a wajen Maryam dan haka na bawa Abba ita halak malak!! Idan Allah ya kaimu gobe Jummah indai a shirye kuke za’a d’aura aure, sai dai In wani mugun hali muka ji a kansa (dan za muyi bincike kamar yadda ake yi In sha Allah) amman bayaga haka gobe iwar haka bi’izinillahi ta’ala an d’aura musu aure.” Da sauri Madu ya kalle shi, kafin yace “Bashir maganar Usman fa, ya zamu yi?”. Murmushi Baba Bashir yayi sannan yace “kar muso kanmu anan mana, Usman fa shi kad’ai yake son Maryam ita bata sonshi, wannan Yaron kuma” yayi magana yana nuna Abba sannan yace “yana sonta itama shi takeso. Sannan abu na biyu, wannan bawan Allah” ya nuna Yayan Abba sannan yace “Tun ranar da ya taimaki Usman muke son sake ganinshi dan mu gode mishi, yau gashi Allah ya kawoshi yana neman abu a wajenmu! Mai zamu tsaya jira???? Ka tuna shine fa silar fitar da Usman a wanchan had’arin wanda ba dan an gano gaskiya ba, da watak‘ila babu Usman a doron k’asa yanzu. Kuma dani da kai duk na san auren nan nasu sai yafi kwantar mana da hankali, saboda abubuwa da dama..” Shiruuu! Madu yayi…..tabbas duk abinda Baba Bashir ya fad’a babu k’arya a ciki, dan haka shima ya yanke shawarar ya bi bayan Baba Bashir d’in a take! Juyowa yayi ya fuskanci Maryam sannan yace “Maryama kina sonshi ko?” Dariya Baba Bashir da Yayan Abba suka yi sannan Baba Bashir yace “Kaima dai neman magana kake yi.” Murmushi yayi kafin yace “kawai ina son inji ta bakinta ne, ta fad’a a gaban kowa.” Sannan ya sake maimaita mata tambayar……cikin jin nauyi a hankali ta d’aga kanta alamar ‘eh’. “Alhamdulillah” shine abinda Madu yace, sannan shima ya tabbatarwa Abba ya bashi Maryam… Yace “Ba sai ya wani had’a lefe ba sadaki kawai suke buk’ata su zo da shi gobe.” Yayan Abban ne yace “Maganar b’oye b’oye babu ita a tsakaninmu kuma ni mutum ne daman straight forward…. A gaskiya! Ba lalle mahaifinmu ya yarda da d’aurin auren a gobe ba, duba da yadda ya riga yayi wa Abban mata kuma a yau zamu gaya mishi d’aurin auren, na san za a d’an kai ruwa rana, watak’ila yace sai nan da sati biyu dan zai d’anyi gayyata… Amman wannan duk ba matsala baceba, za azo a goben ko iya mu uku ne in sha Allah zamu d’aura auren, dan na lura Madu yana so ayi auren a gobe, inyaso daga baya sai a sake sabon aure mai taro idan mahaifinmu ya tsayar da rana…..” A hakan kuwa aka bar maganar. Murna a wajen Abba ba’a magana, dan ko kunya bayaji, haka nan ya zage ya dinga jero godiya ga su Madu, har sai da Baba Bashir ya fara tsokanarshi……: Sallamar Maryam suka yi ta tafi su kuma suka ci gaba da hirar su cikin mutunta juna kafin daga baya suka yiwa juna sallama suka tafi akan gobe za’a had’u a masallaci in sha Allah….. Da kyar Alhaji Yahaya ya lallashi Abba ya hak’ura ya bishi suka tafi saboda da shi ya dage ne akan sai ya ga Maryam tukunna zai tafi….. Shuwa da ragowar mutane sai bin Maryam suke da kallo, Yarinyar da take ta koke koke akan ita bata son auren, amman dubeta yanzu yadda ta ware dan ko makaho idan yaji muryarta sai ya tabbatar da tana cikin farin ciki, haka nan aka sakata a lalle aka yi kaulu lafiya tanata washe baki kamar ba itaba. Bayan sallar isha kowa ya watse….Madu da Baba Bashir suka nemi ganin Ya Usman, Baaba Talatau Ya Jamilu, Maman Shuwa, Shuwa da y’an uwanta..... SHARE PLS. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 15 Ba tare da b’ata lokaci ba Baba Bashir ya fad’a musu duk abinda ya faru d’azu… Tun kafin ya k’arasa Baaba Talatu tace “zancen banza ma kenan!!! Ai indai gaskiya za a bi to haramun ne neman aure a cikin aure”. Cikin b’acin rai Baba Bashir yace “waye kenan yake yi miki zancen banzan?? Sannan ban gane maganarki ta ‘neman aure cikin aure’ ba! Shin a tsakanin ni ko Madu waye kika tab’a ji ya cewa Usman ya bashi Maryam?? Shiyasa fa d’azu na kyaleku ban kiraku ba, dukda yadda na so ace ke da Shuwa kun zo kun yiwa mutumin nan godiyar abinda ya yiwa Usman kwanakin baya, amman kawai sai na fasa domin na san k’aramar kwakwalwa gareku, indai kuka lura shine yayan Abba sai kunsa munji kunya…” “Ko kuma dai an so shirya munafurci shiyasa aka k’i kiran nasu ba!” Maman Shuwa ta fad’i hakan sannan ta mik’e tace “Madu na lura ba zaka iya tsawatarwa Yarinyar nan ba! Ba zaka iya tirsasa mata tayi abinda ya dace ba, a k’a‘ida fa babu ita a hurumin zab’arwa kanta mijin aure, ku iyayenta ku ya kamata ku zab’ar mata. Allah na tuba yaushe ma Maryam d’in ta NuNa ne wai? Da har ta san wani soyayya?. Daman ni tunda naga sauyi a tattare da ita d’azun na san da wata a k’asa!. Son da kake yi mata ya sanya baka son ganin b’acin ranta kwata kwata, to inaso ka sani wannan Maryam d’in da kake shagwab’awa ko bayan raina zaka ce na fad’a maka ‘Wallahi sai ta kunyataka!!’ Ai shi Yaro ba a yi masa haka kwata kwata. Taya ma za ayi ka bari ta auri wanda suka gama lalacewa a waje? Allah na tuba Yaro ka auresa da mutuncinka ma ya aka k’are ballantana wanda ya sanka tun a waje?? Ai ni wallahi na ma ga k’ok’arin wannan Yaro Usman da ya amince zai aureta, ga mahaifiyarshi itama y’ar albarka bata k’i jininka ba!! Ana k’ok’arin a rufa maka asiri, kana son tonawa kanka asiri da hannunka. Ba Baki zan yiwa Maryam ba amman duk daren dad’ewa indai wanchan Yaron zata aura to kuwa auren ba zai d’aure ba! Sai ta dawo gida kuma sai kun yi dana sani!!!”. Madu kasa jurewa yayi dan haka yace “Inna na rok’e ki da girman Allah kiyi shiru!! A matsayinki na Babba ba a so ki dinga mugun alkaba’i haka!! Kawai ki bita da fatan alkhairi…” A hasale Innar tace “Ank’i a bita da fatan alkhairin!!! Ai sai mutum yaso alkhairi tukunna za a bishi da alkhairi! Masifa kuke son janyowa kanku kai da ita k’iri k’iri!!! Yaron nan ko bincike na tabbata ba kuyi ba….Kai nan kaga mai arzik’i ko? Shine zaka fake da wani wai ‘Yayansa ya taimaki Usman’, ai taimako daban neman aure daban. Wannan karon Baba Bashir ne yace “Inna tunda suka zo suka tafi muke bincike akan shi, kuma bamu samu wani mugun abu a kanshi ba kowa alkhairi yake fad’a.” Cikin fad’a sosai Innar ta katseshi ta hanyar cewa “Amman tabbas yau na tabbatar Yaran nan baku da hankali wallahi!!! Binciken wuni d’aya shine Bincike????” Madu ne yace “ai ba a son tsananta bincike ko a addini!” Ga mamakin su kawai sai sukaga Inna ta fashe da kuka a cewarta wai ‘Madu da Bashir sun rainata! taya za a yi tana fad’a suna mayar mata saikace sun samu sa’ar su!?. Nan ta hargitse musu harda cewa “Sister’s din Shuwa su shirya a daren nan zasu wuce Maiduguri ba zata sake kwana a gidan Madu ba!! Dan yaga ba itace ta haifeshiba shiyasa zai yi mata rashin kunya a gaban Yara, kuma sai ta kira Babansu, zata gaya mishi duk halin da ake ciki, wallahi indai tanada rai ba zata bari Maryam ta auri wanchan Yaron da suka gama lalacewa ba, shagwab’ar ai tayi yawa!! Taya Yarinya tayi laifi kuma still lallab’ata akeyi sai abunda takeso tukunna shi za ayi mata??. Madu ne yau har da yi mata rashin kunya duk akan y’arsa???” Da kyar su Shuwa suka d’an lallab’ata ta sassauta kukan, sannan ta hak’ura da tafiya amman tace ‘tabbas maganar auren Maryam da Abba babu ita indai tana raye! Dan sai ta hukunta Maryam akan laifin ta, da fari taso ta kyaleta amman yanzu ubanta ya janyo mata.” Hayaniyar su ta sanya har su Maryam d’ib da ke a d’aki suka d’an firfito. Tarin da Ya Usman ya hau yi ne ya karkato da hankalinsu gareshi, gaba d’aya suka nufe shi….kafin su k’arasa har ya zub’e ya fad’i a wajen sumamme…. Nan kuwa Baaba Talatu ta fashe da kuka, tashi d’aya ta rikice! Hankalin kowa a tashe aka fara k’ok’arin kinkimarshi..ganin baya motsi ko kad’an kamar gawa, ya sanya Baba Talatu ta juyo a zafafe tayi kan Maryam wadda take k’ok’arin k’arasowa wajen, tana matsowa kawai ta d’auketa da mari!! Ta fara magana cikin kuka “Maryam mai nayi miki a rayuwar nan in banda alkhairi da kike shirin yi mini gib’i a rayuwa?? Tun tasowarki banda soyayya muraran babu abinda nake nuna miki har iyau, mai Usman yayi miki a rayuwa haka? Muguwa kawai!! Wallahi idan wani abun ya samu d’ana ba zan tab’a yafe miki ba!!.” Madu ne ya katsesu ta hanyar cewa su d’an matsa su bawa Usman d’in iska sannan ya umarci Ya Jamilu da ’ya d’auko mishi makullin motar shi a d’aki’. Da Baba Bashir da Madu ne suka d’auki Ya Usman, suka yi waje dashi, Ya Jamilu kuma ya fito da mukulli ya bi bayan su da gudu, ganin haka yasa suma su Shuwa suka bi bayansu…. Da kyar aka lallab’a Baaba Talatu ta hak’ura bata bisu ba. Tunda suka koma cikin gidan kuwa Baaba Talatu take kuka, su Innaa da Shuwa kuwa in banda tsigale Maryam ba abinda suke yi…Shuwa ta tabbatar mata ta sake tabbatar mata cewa ‘muddin ta auri Abba to sai dai ta nemi wata uwar amma ba ita ba!!!’ A daren Innaa ta kira Baban su Shuwa a landline d’in gidan ta sanar masa komai! Yayinda shi kuma ya tabbatar mata da ‘in shaa Allah, gobe da sassafe idan Allah ya kaimu zai taho.’ Sai bayan awa hud’u, tukunna Madu da Baba Bashir suka dawo daga asibiti.. Nan suke gaya musu cewa “an kwantar da Ya Usman, Ya Jamilu yana tare da shi and the bad news is ‘ya samu stroke!!’ A sakamokon jinin shi da yayi mugun hawa.” Kukan da Baaba Talatu take yi sai ta baka tausayi, haka itama Shuwa. Gaba d’aya duk sai Maryam taji ba dad’i.. Gidan ranar babu wanda ya runtsa, da sassafe suka yi shirin zuwa dubo Usman har Maryam amman k’iri k’iri da Shuwa da Baaba Talatu suka hanata bin su… Bayan sun tafi da awa d’aya tana zaune gidan shiru duk ba dad’i ga damuwa tashin hankali da tunani, daga ita sai y’an tsoffin da su Innaa suka taho dasu. Sallama aketa kwad’awa a waje, hakan yasa ta sanya hijabi ta fita. Wani Yaro ta gani a tsaye bayan ta bud’e k’ofar gate d’in, Yaron ya kalleta sannan yace “Wai Maryam taje inji Abba.” Sai da gabanta ya yanke ya fad’i…abun ya bata mamaki ‘Abba da sassafen nan?, to Allah dai yasa lafiya.’ Ko cikin gida bata komaba, ta k’arasa gaban motar inda ta hango shi a tsaye cikin shigar shadda tazarce fara k’al tayi masa mugun kyau!!. Cikin kulawa ya amsa bayan ta gaidashi, sannan a hankali yace “Baki da lafiya ne? Naga idanuwanki duk sun kumbura.” Kwallar da ta zubo mata ta sa hannu ta share sannan ta shiga koro mishi abubuwan da suka faru tun daga jiya har izuwa yanzu bata b’oye masa komai ba. Nannauyar ajiyar zuciya ya sauk’e sannan yace “Maryam kin yarda dani?.” A hankali ta d’aga mishi kai alamar ‘eh’ Cike da bata umarni yace “Inaso yanzu! Ki shiga cikin gida, duk wani abunda zaki buk’ata ki d’ebo ki zo dasu, zamu d’anyi tafiya ne, maybe sai nan da shekara d’aya ko d’aya da rabi tukunna zamu dawo.” Cikin rashin fahimta da d’an tsoron daya bayyana akan fuskarta tace “Tafiya kuma? Zuwa Ina? Kai da wa?.” Ba tare da b’ata lokaci ba, yace “Ni da ke! K’asar nan zamu bari bayan an d’aura mana aure yau! In sha Allah.” Da sauri ta shiga ja da baya tana girgiza kai kafin tace “Kana nufin fa mu gudu kenan!! Abba mai yayi zafi har haka??” Da sauri ranshi a b’ace yace “Maryam komai ma yayi zafi!! Babu abunda bai yi zafi ba.! Kinga idan na saka k’afa na bar k’ofar gidan nan naku a yau batare da kin bini ba, to ki tabbata ba zaki sake ganina ba har abada!! Ta b’angaren ki ta b’angarena ko ina yayi zafi!! Ya kamata mu tashi mu tsayawa kanmu, saboda iyayenmu basu damu da farin cikinmu ba.” D’an sassauta murya yayi sannan yace “Jiya bayan mun bar gidan nan, direct wajen mahaifina mukaje. Bayan Yaya ya gama yi mishi bayani, Ina tunanin goyon bayanshi amman sai naji yace ‘Shi bai hanani in aureki ba, amman tabbas sai na fara auran cousin sister d’ina wadda ya zab’a mini tukunna bayan shekara biyar sai in aureki!’. Maryam ko a duniyar matattu muke na tabbatar idan na barki nan da kwana biyar ma to kina gidan Usman. Mahaifiyata itama ta goyawa Mahaifina baya d’ari bisa d’ari! Yaya shi kuma wanda nake tunanin zamuzo ni da shi a d’aura mana auren dashi a yau, shima ya juya mini baya. Dan Mahaifinmu d’aki ya kirashi suka shige, bayan ya fito dana yi mishi magana yace mini ‘kawai in hak’ura!!!’. Maryam, ya kikeso inyi?? still ba zaki yarda ki bini ba?.” Cikin kuka Maryam tace “Tunda nake a rayuwata ban tab’a ganin Hajiya da Abba suna fad’a ba sai da zancen mu ya fara! Bana son zama silar lalacewar zaman lafiyar su. Abba kawai muyi abinda suke so, watarana za muga alkahiri.” Wannan karon hawayene suka zubo daga idanun Abba “A hankali yace “Maryama, ko da ace mun auri waenda iyayen namu suka zab’a mana abun bazai yi kyau ba!! Domin kuwa za muyi ta cusgunawa Abokanan zaman namu ne muna d’ibarwa kawunanmu zunubai a wajen Allah, kuma case an dinga yin shi kenan watak’il ma k’arshe a lalata zumuncin gaba d’aya! Ga uban zunubin da za muyi ta d’iba a wajen mahaliccinmu, especially ma ke da kike a matsayin mace dan na tabbatar ba zaki iya yiwa Usman cikkkiyar biyayya ba sannan inaso ki rantse mini yanzu akan ‘shin bayan kin auresa ba zaki dinga tunaninaba?!”. Da sauri ta runtse idanunta. Bai jira jin me zata ce ba ya cigaba “to ki sani duk wani tunanin ko wish ko feeling da kika samu a kaina kina da zunubi!. Ni kuma na tabbatar Idan na auri Zainab (cousin sister d’insa) to tabbas ba za muyi sati ba zan saketa, idan kuma aka tilastamin zama da ita na tabbatar tsakanina da mahaifina sai dai kallo daga nesa, domin kuwa na dinga bak’anta mata kenan shi kuma ba zamu shirya da shi ba muddin zan yi hakan and na tabbatar ba zan tab’a iya zaman aure da ita ba!. Me kenan aka yi a nan Maryam?? Mun lalata rayuwarmu fa kenan mun lalata ta Abokanan zaman mu. A yanzu inaso ki rufe idanunki, karki duba kowa a duniyar nan, karma kiyi tunanin akwai wata halitta bayan mu biyu kacal a duniya! I want you to be selfish Maryam just for today for my sake! Mu so kanmu fiye da kowa mu sanya kanmu a farin ciki, na tabbatar miki, bayan an d’aura mana aure zamu dawo mu basu hak’uri, komai zai dawo dai dai in sha Allah, koma waye yake fushi damu daga baya za kiga ya daina, an dawo an zauna lafiya da kowa. Please Maryama, pleaseeee. SHARE PLS. BULAMA ✍️ So Da Buri Free Book 16 Cikin sheshshek’ar kuka Maryam tace “Hajiya fa fushi takeyi dani, yanzu idan na gudu zata kuma jin haushi na.” Hannu biyu Abba ya d’aura a kansa, kafin yace “O my God!!Maryam da wanne yare kikeso in yi miki bayani ne?? Ko bayan auren ki da Usman zata ci gaba da jin haushin ki ne….in dai kika auri Usman to kun yi ta janyo fad’a kenan a tsakanin iyayenku har azo a lalata zumuncin…” A hankali ya matso kusa da ita yace “Nace miki kar ki duba kowa yanzu, just ki duba mu biyu kawai, and trust me! Please Maryam, this is the right thing to do….” Cikin share hawaye tace “Abbana fa?” “Abban ki ya riga ya zab’a miki ni, so Abbanki ba zai ji haushin komai ba, this is his choice Maryama. Itama Hajiyan blackmailing d’inta aka yi, sannan kunyan Baaba Talatu take ji shiyasa amman da zarar mun yi aure idan taga kina cikin farin ciki tuni zata manta da komai! Burin ko wacce uwa taga farin cikin Y’arta Maryam i assure you Usman cannot give you the happiness you deserve!.” Ya k’arashe maganar kamar zai fashe da kuka.. Shiruu, tayi tana tunani.. Tabbas duk abinda Abba ya fad’a haka ne sannan ta yarda dashi d’ari bisa d’ari! Cikin katse mata tunani a hankali taji yace “muje..idan komai ya d’an lafa na yi miki alk’awari zamu dawo mu bawa su Hajiya hak’uri, na san zata hak’ura in sha Allah. Abba kuwa na san shikam farin ciki ma zaiy yi, dan munyi abunda ake k’ok’arin hanasa, wanda hakan shine zab’in shi. Na tabbatar idan mijin Innarku ya zo ba zai bari a d’aura aurenmu ba, kuma Inna da kanta kinji tace ba zata tab’a bari muyi aureba wanda na tabbatar Abba ba zai tab’a iya shallake umarnin su ba.” Cike da gamsuwa da maganganunsa Maryam ta hau d’aga kai alamar amincewa kafin tace “Amman zamu dawo anjima mu gansu, ko iya Abba ne shi kad’ai, na san ya san yadda zaiyi ya lallab’a Hajiya Shuwa watak’l ta hak’ura, kayi mini wannan alk’awarin?”. Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace “Nayi miki! Amman nima kiyi mini alk’awari idan mun gama ganinsu, anjiman zamu wuce, saboda ina so in yin nesa da mahaifina ko da na wata d’aya ne. Ba zan iya fuskantarshi a yanzu ba, dan ban san hukuncin da zai yanke mini ba.” Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin tace “Na yarda!.” Ahankali yace “Alhamdulillah”sannan ya juya ya bud’e mata gaban mota. Har ta wuce ta shiga, ta zauna sai kuma ta juyo ta kalleshi yana shirin rufe mata k’ofar tace “Abba, kana ganin ba matsala?” Murmushi yayi sannan yace “Yes Maryam, in shaa Allah, just trust me please..” “Na yi, amma dan Allah kar ka sa in yi dana sani” Murmushi yayi yace “i promise, I won’t!”. Sai da ya juyo ya shiga, ya tada motar tukunna idanunta suka sauk’a akan Sadiya wadda take tsaye a k’ofar gidansu gaba d’aya hankalinta yana a kansu….. Tafiya mai d’an nisa sukayi dan Maryam kam kanta har ya juye abunka da wadda bata fita sosai, tana cikin y’an kalle kallenta suka iso wani tafkeken masallaci a d’an gaba kad’an akwai hotel… Wuce masallacin sukayi ya shiga cikin hotel d’in wanda ya gaji da had’uwa ga securities ta koina, ya nemi waje yayi parking. Babu yadda bai yi da ita akan ta fito ta shiga cikin hotel d’in saboda shi yanaso ya je ya samu limamin yayi mishi bayanin komai, kuma akwai y’an shirye shiryen da yake so ya fara so zai kama mata d’aki ita d’aya shikuma ya fara preparations amman tak’i tace “ita a mota zata jirashi har yaje ya dawo”, hakanan ba yadda ya iya ya kunna mata AC ya bata mukullin ya kwashi abubuwan da zai buk’ata. Sai da yaje wajen Limamin suka tattauna sannan ya fito ya tari motar haya ya shiga aikin gabanshi. Sai wajajen 12 tukunna ya dawo Maryam har tayi bacci ta tashi ga tsoro ga yunwa, yana zuwa ya kwankwasa, da kyar ta iya bud’e k’ofar ya shigo mata da abinci sannan yace bara yaje yayi Sallah idan an idar zai zo su wuce. Haka kuwa akayi sai wajen 2:00pm Time d’in masallacin kowa an watse tukunna ya dawo. Yana zuwa ya sa key sannan ya umarce ta da ta koma baya, bayan ta koma ya tada motar yaja suka isa bakin masallaci. Wani dattijo cikin alkyabba da rawani suka tsaya suka d’auka a bakin masallacin sannan suka hau titi, basu yi wani tafiya mai nisa ba suka gangara kan hanya suka shiga wani layi, a bakin wani gida sukayi horn aka bud’e gate d’in suka shiga. Bayan sunyi parking sun fito dattijon ya nuna musu babban parlourn gidan yace wa mai gadi “ya kaisu gurin Hajiya” Shi kuma ya nufi parlourn bak’i dan yanada bak’i. Matar mai kirki sosai bayan sun gaisa ta dinga yi musu hira aka kawo musu abinci kala kala, Maryam kam fitsarine yake neman yi mata illa ga Abba a wajen balle tace zata yi fitsari, Allah ya taimaketa matar ta shiga tambayarta “ko tayi sallah?” Da sauri ta mik’e tana cewa “a’a” Nan ta nuna mata d’aki ta shiga….sai da tayi sallah tukunna ta fito suna cikin cin abinci wannan dattijon ya shigo….. Sake gaisawa suka yi kafin ya juya ga matar tashi yace ne “Yakubu ne k’anin Yahaya, kin ganesa ai ko” Da mamaki matar take kallonshi, nan ta hau yi mishi tsiya tana cewa “baya ziyara.” Gyaran muryar da dattijon yayi ne ya katsesu, sannan ya kalli Abba yace “nayi waya da Yahaya yanzu ya tabbatar mini da abunda ka fad’a min d’azu, yace tare kukaje dashi jiya. Amman ni da zaku bi ta shawarata da ko Mahaifinta ko wani d’an uwanta a samu a wajen tukunna, ina ganin hakan zai fi, ko?”. A hankali cikin girmamawa Abba ya hau yi mishi bayanin komai…sai a yanzu matar take fahimtar ba amarya da ango baneba yet. Bayan ya kai aya ne dattijon ya sauk’e ajiyar zuciya sannan cike da gamsuwa da zancen nasa yace “ai shikenan!! In dai maza sun riga sun gama magana batun mata ba biyeshi akeyi ba…” Bai gama rufe baki ba wasu magidanta responsible su uku suka shigo, d’auke da huhunan goro da packs d’in alawowi. Zama d’ayan yayi sannan yace “Akaramakallahu barka da rana ga sak’on da kace in taho dashi nan.” Amsashi yayi sannan yayi mishi nuni da su ajjiye. Bayan sun ajjiye an gaggaisa anan yake shaida musu “Aure za a d’aura, za suyi shaida”. Nan suka amince. Limaminne ya umarci Yakubu da “ya kawo sadaki.” kamar jira yake, nan ya zaro dubu talatin a aljihun shi…a take aka gudanar da duk abunda ya kamata, Yakubu ya kanshi wakili, limamin nan kuma ya yiwa Maryama. A take a falon aka d’aura auren Yakubu Umar Farouk mai turare Da Maryam Muhammad Madu akan sadaki naira dubu talatin…. Aka raba goro da alaawa a y’an falon sannan aka kwashe ragowar domin rabawa In an fita masallaci dan har an fara kiraye kirayen sallar la’asar. A gidan suka yi har sallar Magrib…matar mai kirki tanata nan nan da Maryam, ita dai Maryam Allah Allah take su tafi dan ta k’agu su koma gida, dukda yadda gabanta ke ta fad’uwa amman dai tanaso taje ta tunkaresu a tura ta k’are!. Suna idar da Sallar Magrib d’in wani Yaro ya shigo d’akin da alamun d’an matar ne yace “wai ance Maryam ta fito zasu tafi.” Ai kuwa zumbur!! Haka ta mik’e har matar har tana tsokanarta….ita dai tayi mata godiya ta kimtsa suka fito tare da matar. Y’ar guntuwar nasiha mai ratsa jiki Limamin nan yayi musu sannan yai musu fatan alkhairi suka mik’e suka yiwa juna sallama suka nufi k’ofar fita daga parlourn. Abba ne a gaba sai Maryam wadda ke bi mishi baya bumper to bumper.. …goshi da k’irjinta ne taji sun bugu da gadon bayan shi sakamakon burkin da ya jaa ya tsaya chak! Lokaci guda, yak’i yayi gaba yak’i yayi baya. Daga yadda yake tsaye zaka iya ganin yadda jikinsa yake karkarwa sannan duk ya rikice tashi d’aya!. Magana yake son yi amman sai ya hau in ina sam ya gagara furta koda kalma d’aya mai ma’ana. Bata dawo daga mamakin abinda ya firgita Abba haka lokaci d’aya ba taji an d’auke shi da wani mahaukaciin marin da saida ya kai ga kaiwa k’asa ya tsugunna a gurin. Tsugunnawar da yayi ne ya bata damar ganin mutumin da yake gaban su ya tare k’ofar, kana ganinshi ba sai an fad’a maka ba ka san shine Mahaifin Abba, dogo ne sosai fari k’al kyakkyawa yana mugun kama da Abba da Yayanshi da suka zo tare jiya, sai dai shi ya d’an manyanta, kana gansinshi kaga tsohon dattijo. Muryarshi ce ta dawo da ita daga nazarin data tafi jin ya daka wata uwar tsawa yana cewa “Out of my way! stupid boy!!!”. Maryam bada ita ake ba amman da sauri ta matsa ta koma bayan matar gidan da itama duk ta rikice ta b’uya. Shima Abba da sauri ya tashi ya matsa yana shafa marin da aka yi mishi. Cike da k’asaita mahaifin nasu ya k’araso cikin parlourn Yayan Abba da wasu maza biyu suna binshi a baya, sai kuma wani Yaro matashi da kayan sojoji a jikinshi. Kujera inda wannan Limamin yake tsaye ya samu ya zauna ya d’aura k’afa d’aya kan d’aya, ko takalmin shi bai cire ba haka ya shigo mishi tsarkakakken falon da shi. Ahankali Limamin ya d’an zauna akan tum tum d’in kan kafet sannan yace “Barka da dare Daddie!”. Batare da ya amsa shi ba yace “Did u just got them married??.” Cike da kwarin guiwa yace mishi “Na’aam.” Gyara zamanshi yayi ya fuskanceshi da kyau kafin yace “D’ahiru you know I can sue you right??”. Wannan karon murmushi Limamin yayi, kafin yace “A tsarinka zaka iya suing d’ina, amman a musulunce ba zaka iya ba, dan Yahaya ma magabacinshine, dan haka kuwa kaga ba zaka iya suing d’ina ba!. Bayaga haka, Abba iya shi kad’ai ya isa yiwa kanshi wakili….” “I’ll get back to you later.” shine kawai abinda Granpa yace dashi cikin katseshi sannan ya mik’e ya isa gaban Abba ya tsaya. Hannunshi ya mik’a baya alamun yana so a mik’o mishi wani abun, da sauri Daniel ya zaro wasu takardu da international passport ya mik’o mishi. Ajiyar zuciya ya sauk’e, kafin yace “Abba, d’azu da Dahiru ya kira Yayanku muna tare!. Jiya na bawa Yayan naka sak’o nace ya fad’a maka, ashe bai gaya maka ba, right?” Bai jira jin amsar shi ba ya cigaba “I’m really disappointed in you, and bana so inyi punishing d’inka harshly which is why I’m doing this… Take this!” Yayi maganar yana mai mik’a mishi passport d’in hannun shi. Jiki a mace Abba yasa hannu ya karb’a, passport d’inshi ne da wasu takardun da bai gama dubawa ya gano na menene ba muryar Mahaifin nashi tasa ya maida hankalinshi gareshi jin yana cewa “Ga passport d’inka, nayi k’ok’ari wajen ganin na had’a har da na amaryar taka in yi muku tare, amman sai na fahimci ita d’in y’ar gidan talakawa ce bata tab’a fita koina ba, so wannan aikinkane yanzu zaka yishi, tunda kaika kwaso ta. Na baka 5 hours ka bar k’asar nan! Bana son ganin ka…ba zan iya zama a country d’aya da kai ba. Abba ko labari idan ka ji zanje k’asar da kake, to ka tabbatar ka bar wajen ko kuma duk yadda zaka yi to ka tabbata bamu had’u ba. I don’t think zan iya yafe maka laifin da kayi min sannan bana son in yi punishing naka harshly kuma na san indai Ina ganin fuskarka ko kuma kana kusa dani to tabbas zan yi maka abunda ba zaka tab’a mantawa ba. So, as you can see I’m doing my very best to stay calm! All I want from u shine ‘wannan ya zama last time da idona zai ga naka!! You want freedom right? Kana so kayi abinda kakeso ka auri wadda kakeso ko? Well, Abba ga freedom nan! I’m giving it to you….Idan ka kuskura muka had’u, ko kak’i barin k’asar nan, u pretty much know wat I’m capable of! Dan wallahi i promise sai nayi making life d’inka a living hell!!. Kayi addua In iya yafe abinda kayi mini kafin In mutu, maybe I can forgive and call u back.” Har ya juya zai fita, sai kuma ya dawo ya zo inda su Maryam suke ya tsaya, cikin kakkausar murya yace “Maryam!” Maryam jikinta har tsuma yakeyi, cikin sake b’oyewa a bayan matar liman kamar zai daketa ne, tace “Naa ‘aa mm.” Cike da tsana yake kallonta kafin yace “D’a na kikeso ko? A kanshi kika bar iyayenki kika gudo kika aure ko? Well congratulations to you, da shigowa familyn MT! But let me assure you! Wallahi karnukan family d’ina sai sun fiki daraja! Sannan ko bayan raina ban amince Y’ay’anki suyi bearing family name d’ina ba. Kuma inaso ki sani, zan iya yafewa Abba kamar yadda na fad’a amman ke kam nida ke karki kuskura ki bari muga juna suma kuma Y’ay’anki haka, bana so su zo ko kusa da inda nake ma talkless of mu had’u da su. Idan kika kiyaye wannan watak’ilan ki zauna lafiya, idan kuwa baki kiyaye ba to kinga mahaifinki da mahaifiyarki da wannan k’anwar taki, I’ll make sure na kulle su a prison d’in da ko kusa dashi baki isa zuwa ba ballantana ma kiyi tunanin fito dasu, this is my promise to you!!” Yana gama fad’in haka ya bawa Daniel umarnin ‘ya kai Maryam da Abba suyi preparations d’in tafiya sannan ya ajjiye su a airport, within 5 hours!’. Yana gama fad’in haka ya juya ya nufi hanyar fita, yana mai yiwa Limamin alk’awarin dawowa idan ya samu lokacinshi, dan ba zai barshi haka ba wallahi!…. Kuka Maryam ta dinga yi kamar ranta zai fita. Tsoro gaba d’aya duk ya rufeta!! Tayaya za a ce babu ita babu family d’in Mijinta waenda sune garkuwar y’ay’anta?? da wanne dangin y’ay’anta za suyi tutiya idan sun taso? dan ba a ado da dangi d’aya! Daman Abba ya san haka mahaifinshi yake amman shine bai sanar mata ba?? Tukunnan ma taya za a fara tunanin barin ta k’asar nan har abada?? Dan in har lissafinta ya bata daidai ana nufin ita da Abban zasu tafi……. Waennan al’amura da tunanin ne suka kuma hargitsa ta, ta dinga rusa kuka ko sauraronsu Abba da suke ta bata hak’uri bata yi… Daniel ne ya d’an rankwafo kan Abba yayi gyaran murya sannan ya nuna mishi agogon hannunshi, harararshi Abban yayi sannan ya mik’e ya fita Daniel d’in yabi bayan shi suka hau shirye shirye gadan gadan. Bai sha wahalar yi mata passport ba, daman yanada k’aramin hotonta daya cira a file tun suna makaranta, amman da aka zo kan visa ba k’aramin wahala ya sha ba, duk inda yaje ‘embassy’s d’in Kano’ sai ace visar gari dole sai mutum ya jira. Dakyar ya samu Yayanshi ya kulashi dan shima duk ya tsorace kar Mahaifin nasu ya juyo kanshi..Nacin da Abban ya dinga yi masa ne yasa ya amsa wayar da cook d’in gidan yaketa rok’on shi ya karb’a, yana karb’a Abba ya kwararo mishi abubuwan da yake da buk’ata….. Da kyar da taimakon sa da taimakon kuma wani baban Abokinsa Maryam ta samu visiting visar Madina, amman shima sai nan da 7 days jirgin zai tashi kuma a Lagos, gashi sauran 1 hour 5 hours d’in da aka bashi ya cika. Da sauri ya shiga nema musu wani ticket d’in daga Kano zuwa Lagos. Aka yi sa’a kuwa ya samu da wuri, zai tashi in the next 20 minutes, a lokacin sauran 15 minutes time d’in da Mahaifinsa ya basu ya cika. A gurguje suka samu suka k’araso gidan Limamin shi da Daniel wanda yake ta binshi a baya yana nuna mishi agogo duk bayan minti talatin, Abba ji yake kamar ya shek’e sa amman kuma sanin da yayi ba laifinshi bane shima saka shi akayi kuma bai isa ya hukuntashiba yasa kawai ya rabu da shi. Yana shigowa a gurguje suka had’u da Limam suka nufi d’akin da Maryam take. Ai anan kuwa ta birkice!! Ta dinga kuka tace “wallahi babu inda zata je, idan ma zata tafi tou sai taje taga su Shuwa tayi musu sallama sun saka mata albarka.” Tabbas sun san ta fisu gaskiya ata koina amman zuwa unguwar su Shuwa ma kad’ai sai ya d’auki minti ashiri bare dawowa, nan kuwa suna kusa sosai da airport… Daga Liman har Abba hadda ma matar Liman d’in duk sun rikice rok’on Maryam kawai suke suna lallab’ata suna mata nasiha akan tayi hak’uri ta bi mijinta su tafi watarana sa dawo…amman fur tak’i!!. Daniel ne yayi knocking ya shigo, har Abba zai yi mishi masifa dan ya ishesa! Sai yaga ya mik’o mishi envelope. Sai da yasa hannu ya karb’a sannan Daniel d’in yace “driver d’in Daddie ne ya kawo yanzun nan yace wai a baka.” Jikin Abba har rawa yake yi haka yasa hannu ya zaro takardar ya fara karantawa… “Sauran minti goma jirginku ya tashi, yanzu munzo wucewa na sake ganin motar Daniel a k’ofar gidan Liman, which means baka tafi ba and still kuna ma gidan, jirginku zai tashi in the next 10 minutes, I know maybe nan da 7 minutes zaku iya isa airport, which means zaku k’ara 2 minutes akan time d’ina…. Already daman d’azu mun tafi da motarka, tunda ni na siya maka! Kayanka da credentials d’inka da Yahaya ya had’a maka suna boot d’in motar Daniel… Ina umartarka da ka bawa Daniel atms d’inka da komai na kadara ya taho mini da su… If u like ku ci gaba da wasting time, and I’ll not hasitate to keep punishing u. Ina sane da duk wani single movement d’inka.” Kawai gani sukayi Abba ya durk’usa a gaban Maryam ya kama hannayenta duka biyu ya fashe da kuka, cikin kukan yake rok’onta yana “Dan Allah dan Annabi Maryama ki tashi mu tafi yanzu shine abu mafi amfani, duk tirjiyarki a k’arshe tafiya zamu yi…. wannan b’ata lokacin da muke yi baki san abubuwan da kike janyo mini ba, zamu dawo idan nayi settling I promise!!!” Kuka yake yi kamar k’aramin Yaro, hakan yasa Liman shima ya ci gaba da lallab’ata tareda yi mata zazzafar nasiha mai ratsa jiki…. Jikinta duk yayi sanyi hakan yasa tace “zata tafi amman sai yayi mata alk’awarin zasu dawo very soon, kuma hadda su Liman za aje a bawa su Shuwa hak’uri.” Duk suka amince hakan yasa suka mik’e da sauri sukayi hanyar fita, su Liman suna ta binsu da fatan alkhairi haka suka shiga mota suka tafi, sai sauri sukeyi, dan tuni lokaci yayi.! Allah ne ma ya taimakemusu aka d’an samu delay da tuni sunyi missing flight d’insu. A gurguje ya had’a duk wani abun da Granpa yace ya bada. Ya bawa Daniel d’in yace “ya bashi” sannan suka hau layi. Sai da Daniel ya tabbatar yaga tashin girjinsu tukunna ya juya ya koma mota ya nufi gida da tunani barkatai a ransa….. SHARE PLS. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 17 Hakanan yana ji yana gani ya bayar da komai ya d’auki d’an briefcase d’inshi na credentials d’insa suka wuce Lagos. Yaso su zauna a Lagos d’in har zuwa lokacin da Mahaifin nasa zai d’an sauk’o daga fushin da yayi. Amman ranar da suka cika kwana biyar a garin! Granpa yayi musu chune! Y’an sanda suka zo suka tafi dasu…aka dinga bincikensu akan laifin da basu san dashi ba. Kwanan su d’aya a station daga k’arshe wani police ya kawowa Abba takarda, yana dubawa yaga sak’on Granpa d’in ne ‘shine ya saka aka kamasu! As a punishment na 5 days d’in da suka k’ara, sannan he should either choose barin k’asar ko kuma zaman station dan zai saka suyi ta zama a wajen ne har abada ba tare da sun san laifin su ba.’ A take Abba ya zab’i tafiya, yayi signing inda aka nuna mishi dan Maryam har ta fara zazzab’i sakamokon sauro da wahalar wajen, shi kansa da yake Namiji daurewa kawai yake yi. Suna fitowa ya mayar da ita masauk’in su ya fita y’ar buga buga dan kud’in da Yaya ya saka mishi a gaban suitecase d’in credentials d’insa sun k’are tass. Bai wani samu kud’i sosai ba har dare haka ya dawo, gashi jirginsu 4:00am zai tashi. Tunda ya tashi Maryam yace “ta fara shiri” take faman yi mishi kukan data mayar sanaarta tun ranar da aka d’aura musu aure. A haka suka isa airport har ana d’an kallonsu… Bayan y’an bincike…jirginsu ya d’aga zuwa k’asa mai tsarki. Tun kukan Maryam yana iya fita har muryarta tazo ta dishashe, ji take yi kamar ta rufe Abba da duka!!! Duk shine ya ja mata shiyasa duk faman aikin lallashin ta da yake ta yi ta yi banza dashi ta k’i kulashi, shi kam babu abunda yake yi sai aikin lallashi dukda kuwa shima kamar ya fashe da kukan haka yake ji, saboda in suka sauk’a bai ma san ta ina zai fara ba, duk wani means na kud’i an kwace a hannunshi! Gashi bai san tayaya zai samu aiki ba, ga iyali a tare dashi…tabbas ya zame masa dole ya tashi ya nemi abunyi Suturarsu kanta kwata kwata set bibbiyu ne dasu, daga waenda suka baro Kano dasu a jikinsu sai waenda ya saya musu set d’aya d’aya a Lagos….. Yana cikin wannan tunanin jirgin su ya sauk’a a garin Madina. Maryam ya d’an tab’a a hankali wadda bacci ya fara kwasa. A hankali ta bud’e idanuwanta da suka kumbura suka k’ank’ance suka yi jaaa. “Mun iso.” Shine abunda yace mata sannan ya fara k’ok’arin mik’ewa itama ya kama hannunta ya mik’ar da ita suka bi ayarin y’an jirgin da suke ta sauk’a, suma suka sauk’a. Bayan an gama sauk’a mutane suka nufi wajen d’aukar kayansu.. Su kuwa su Abba suite case d’inshi ce kawai garesu, tana da d’an girma shiyasa ta cinye har ragowan kayansu set d’aya d’aya. Waje ya samu ya zauna ya fara duba suitecase d’in, bayan sun fito, kamar yana neman wani abu. Allah yaso su kuwa akwai y’an chanji a ciki…so da yawa idan Yayanshi zai zo yakan biyoshi su taho tare yayi masa rakiya dan yana son garin, ya tuna lokacin daya dawo da kud’in yana taso ya chanja su bai samu time ba haka ya hak’ura ya d’aga k’asan suitecase d’in credentials d’in nashi ya saka. Shiyasa yanzu da wannan ranar ta fad’o mishi a rai ya duk’ufa yana dubawa had’e da adduar Allah yasa har yanzu kud’in suna nan, ai kuwa ya tsince su yadda ya barsu. Abun hawa ya fara nema musu, da kyar kuwa ya samu, daganan yace “a kaisu wani d’an hotel haka mai d’an saffa saffa.” Suna zuwa ya kama d’aki d’aya. Sai da ya kai Maryam d’akin yace mata “tayi wanka ta huta” tukunna ya fito domin ya siyo abinci, acikin hotel d’in ya siyo abincin, sannan bai yarda ya bar wajen ba sai da ya samu aiki a restaurant d’in cikin hotel d’in, bayan ya nuna musu takardunsa kuma sunji yana jin larabci suka bashi aikin ‘waiter’!! Bai wani damu da k’ask’ancin aikin ba ya amsa yana mai farin ciki. Yana dawowa da abincin ya tarar da Maryam a yadda ya barta tana kuka, hawaye ne ke fita kawai amman ba sauti tsabar yadda muryarta ta disashe. Da sauri ya k’araso ya d’agata ya zaunar sannan ya ci gaba da aikin lallashi. Da kyar ta yadda taci abinci sannan ta shiga tayi wanka ta fito. Shima mik’ewa yayi yaje yayo wankan sannan ya fito ya tarar da ita a zaune ta mayar da kayanta. A hankali ba tareda ta kalle shi ba tace “Inane gabas? Zanyi sallah.” Shima kayan nashi ya maida sannan yaje ya d’aga window ya hau duba garin Alk’iblar masallacin da ya hango ya duba kafin ya zo ya nuna mata. D’ankwalinta ta shimfid’a tayi sallar walha…. Yana zaune ya baza takardu yana dubawa dan neman mafita..ta ida sallarta ta nemi waje ta kwanta yana ta duba tarkadun shi da had’a su waje d’aya a haka barci ya saceta don tunda suka je station basu samu nutsuwa ba. Kiran sallar azahar ne ya tayar da ita. Tana juyawa taga Abba shima yana baccin a inda ta barshi da takardun shi a baje da alamun ma a zaune yayi baccin wahalan… Zuciya da abunda take so sai taji gaba d’aya ya bata tausayi. A hankali ta k’arasa taje ta durk’usa a gabanshi tana k’are mishi kallo, kana ganin yanayin fuskarshi ka san ba dad’in baccin yakeji ba kawai dai yana yinsa ne. Hannu ta saka ta d’an tab’a gefen inda yake jingine. A hankali ya bud’e idanuwanshi, ganin ya farka yasa da sauri ta mik’e tana cewa “ka tashi kayi sallah”daga haka ta fad’a toilet ta yo alwallah. Tana fitowa shima ya shiga bai fito ba saida ya sake yin wanka. A zaune ya tadda ita tayi shiru da alamun tunani take yi. A gurguje ya shirya, ya tada sallah. Bayan ya idar da sallah ne ya zo ya kwashe ragowar chanjin da suka yi sannan ya juya ya fita. Bai wani dad’e ba ya dawo da abinci da y’ar rigar da suka bashi da hula. A hankali ya zo ya zauna a kusa da ita. Da farko kamar ba zata yi mishi magana ba sai kuma tace “Ina wuni.” Amsawa yayi, sannan yace “Ga abinci nan, d’azu naso gaya miki zan fara yi musu aiki a restaurant saboda kinga muna buk’atar kud’i a hannunmu, amman sai naga kinata kuka. Zan d’an fita yanzu In k’aro mana kaya ko set bibbiyu ne kafin muga abinda Allah zai yi. Zan fara neman wani aikin. Kiyi hak’uri yanzu muji da yadda zamu yi surviving… In sha after that immediately zan san yadda zan yi ko ke kad’ai ce kije ki wajen su Abba kinji ko?” A hankali ta d’aga mishi kai sannan ta mik’e. Gani tayi shima ya mik’e sannan ya kamo hannayenta. D’agowa tayi ta kalleshi taga shima itam yake kallo, a hankali yace “That’s all? Babu irin adduar ‘Allah ya bada sa’a dinnan? Maryama, kuma still har yanzu ranki a b’ace yake.” “Allah ya bada sa’a.” tace, sannan tayi niyyar matsawa amman furr! Ya k’i ya tare hanya, shifa sai tayi murmushi kuma tayi mishi addua tukunna zai fita. Hakanan ba yadda ta iya ta k’ak’alo murmushi tayi sannan ta yi mishi addu’ar. A hankali yasa hannu yayi hugging d’inta yafi 5 minutes tukunna ya sauk’e ajiyar zuciya yace “Ameen.” Sannan ya juya ya fita. Sai yamma tukunna ya dawo ya kawo mata abinci, kana ganinshi a gajiye yake dan restaurant d’in ana cika sosai kasancewar a hanyar airport d’in yake kuma shi kad’ai ne sannan daman basuda waiter sai shi kad’ai. Sallah kawai yayi ya d’an ci abincin kad’an sannan yace “mata zai koma.” Gaba d’aya se sai tausayinshi ya sake kamata. Ganin ya tsaya yasa tace “a dawo lafiya.” “Ameen” yace, kafin yace “Murmushin fa??.” Wannan karon ba k’ak’alo shi tayi ba, ji tayi kawai ya sub’uce mata. Sai k’arfe goma sha d’aya na dare ya dawo. Kamar yadda yayi alk’awari da kaya ya taho musu dashi.. AlQurani mai kyau irin mai pieces d’innan izu sittin amman duk izu biyar a rabe ya siyo, da inner wears d’inta set biyu, sai abaya da hijab. Shi kuma ya siyawa kanshi gajeran wando da jallabiya Sai lotion, brush da toothpaste sponge da soap na wanka da na wanki da omo. Gaisuwarta ta sannu da zuwan da take yi mishi ya amsa, kasancewar a gajiye yake sai da ya d’an huta tukunnan yake gaya mata “Ya tambayi mai restaurant d’in nasu ita ta had’a shi da ogan su kai hotel d’in, so ya tambayeshi ko zasu iya zama a d’akin sai a dinga cira a cikin albashin shi? Mutumin ya yarda amman kasancewar idan an cira zai yiwa albashin gib’i sosai yasa aka d’auke room service, dai an basu d’akin ne amman su za suyi komai…” Abinci suka fara ci yana ta bata labari, yau kam ta d’an sake ba laifi, haka nan suka sha hirarsu sosai. Sai da suka gama tace zata yi wanka daga nan ta wanke toilet, so tana so ya bata omo, amman k’iri k’iri yace “taje tayi wankan ta, idan ya shiga shi zai wanke toilet d’in har kayan data cire ma ta barsu a ciki zai wanke!.” Babu yadda bata yi dashi ba amma ya k’i, hakanan ta je tayi wankan, kamar ya sani bayan 10 minutes ya mik’e ya shiga aikuwa ya kama ta tana shirin wanke kayan, sai da yayi da gaske tukunna ta barshi ta fito har inner wears d’inta saida ya had’a ya karb’a, ba yadda ta iya. Tukunna yayi wanka ya wanke toilet ya wanke musu kayansu. Tana zaune tana karatun Al’Qur’ani, ya fito. Sai da ya shirya sannan yazo kusa da ita ya zauna ya kamo hannunta yasa a cikin nashi. Bata kulashi ba sai da ta kai aya sannnan ta juyo bayan ta ajjiye Quranin da d’ayan hannun damanta a gefe,tace “Abba amman kana ganin Mahaifin ka zai hak’ura?? sannan maiyasa baka gaya min haka yake ba? Taya za’ace Yaranka ba zasu shiga familyn Baban su ba? A Ina aka tab’a yin haka?” Ajiyar zuciya ya sauk’e sannan yace “Maryam, i don’t want to lie to you or give u any false hope! Maganar gaskiya ba lalle ya hak’ura ba!. Ai wannan abunda yayi fa bai ma yi komai ba. Idan na fara baki labarin halinsa, ba lalle ki yadda da wasu abubuwan da yake yi ba. Kuma kinga a case d’innan fa laifi nane, nine na tab’o shi To be sincere I was expecting more than this from him.” B’ata rai tayi sannan ta fara k’ok’arin zare hannunta a cikin nashi kafin tace “yanzu ka kyauta mini kenan??? Abba ba wai fata nake yi ba amman ba a san gawar fari ba!! Yaran mu nake dubawa anan…” Rik’e hannunta yayi sannan yace “Maryam idan akwai abinda zan iya rantse miki akai shine ‘ko bayan taina na san sai dai Yaya da mahaifin mu su raba gari, suyi baram baram indai akan Y’ay’a nane, dan Yaya ba zai tab’a k’in kula Y’ay’ana ba, sannan ga d’ayan Yayan nawa shima na san ba zai yi abandoning Y’ay’ana ba ko da ina raye talkless of ba na raye’. Kawai dai one thing is for sure, na san zan had’a rigima ne, da kuma fad’an da ni kaina ba zan iya kuncewa ba, because..definitely mahaifinmu zai so hana brothers d’ina kulani su kuma ba za suyi mishi biyayya ba when it comes to that! Bar ganin Yaya ya k’i kulamu yanzu, I assure u ba za ayi 3 months ba zakiga ya zo ya fara bibiyata.” With surprise Maryam take kallon shi kafin tace “Amman ka san da duk wannan mai yasa kayi taking risk d’in to? Why do you want to tear apart your own family??.” Murmushi yayi sannan ya matso kusa da ita sosai yayi cupping face d’inta a cikin tafukan hannayensa sannan yayi mata light peck a forehead d’inta… a hankali da idanunsa a lumshe ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace mata “This is worth it!” Tana k’ok’arin janye face d’inta yayi mata wani a kan hanci a hankali ya sake furta “And this” Bai jira d’aukar lokaci ba dan ya fahimci so take ta kwace fuskan nata yayi mata a lips d’inta yace “And this….” Daga nan kuma Maryam ta ji Abba kamar ba shi ba! Duk wani k’ok’arin ta na ganin ta karb’i kanta kasawa tayi, bata tashi sanin abun nashi na gaske bane ba saida taji azaba na shirin d’auke ranta. A b’angaren Abba kuwa yaso suyi sallah kafin komai amman duk yadda ya k’ok’arta hana kanshi sai ya gagara, domin kuwa tun a karan farko shikam ya manta hanyar garinsu ma balle azo kan maganar hana kai! Shiyasa duk kalar kuka da magiyar Maryam d’in tashi ya zamana ba jinta yayi ba...... Ahankali yake shafa kanta yanata murmushi kafin ya janyota jikinshi ya rungume a haka bacci ya kwashesu, ita baccinta na wahala ne shi kuwa na cikar farin ciki da nutsuwa ne. Kiran sallar farko ya tada shi, jikinta yaji yayi zafi da alamar zazzab’i. Wanka ya fara yi ya taimaka mata itama tayi, sannan yaje ya siyo musu abinci da maganin zazzab’in ta! Dariya taso ta bashi dan kwata kwata tak’i kallonshi gashi sai kumbura baki take yi ita ala dole fushi take dashi amman kuma komai idan zata yi sai da taimakon shi. Sai da ya tabbata komai ya kimtsu sannan bata buk’atar komai tukunna ya fita aiki, sai dare ya dawo….yau ma kamar jiya Abba bai kauda kai ba… Maryam tun tana k’i harta daina….. Idan ta ce Abba yana son ta, to tama ragewa soyayyar da yake yi mata a zamansu daraja, dan kalmar so tayi kad’an wajen fasaltawa. Duk wani abu na kulawa da k’auna shi yake gwada mata, ko tsinke baya bari ta d’auka saidai In a bayan idonshi ko In baya nan tayi sauri tayi, ta yadda idan ya dawo aikin ba zai zama dayawa ba. Shi zai yi shara yayi moping ya wanke toilet yayi wanki, sannan duk abinda tace tanaso sai ya nemo mata. Zaman nasu gwanin ban sha awa, yadda yake kyautata mata itama haka take yi mishi biyayya….. Idan aga Maryam indai ba bakinta ta bud’e tayi maka Hausa ba to bazaka tab’a cewa ba balarabiya bace ba…tayi k’iba ta k’ara fari tayi freshi da kyau abinta. A hankali ya siya musu d’an electric gas da d’an kayan abinci suka ajjiye a d’akin, wai ko da wani lokacin tana sha’awar yin girkin gida, amman kuma the funny thing is ‘ya hanata yin girkin’, kasancewar a restaurant yake yanata koyan girki kala kala,idan tace bana sayarwa take son ci ba to yana dawowa break ko kafin ya fita ko bayan ya dawo a aiki zai zage ya girka mata!. Zaman lafiya da k’aunar juna kankat, shine zaman da Maryam da Abba suke yi a Madina. Abu d’aya yake damun Abba rashin tsayayyen aiki, ya kai takardun shi wajaje mabanbanta amman bar yau shiru, bai san daliliba. A kwana a tashi har suka yi 4 months. Yau ma kamar kullum yana wajen aiki, wasu bak’i suka zo Larabawa, da alamun manya ne dan yaga yadda managern nasu yake ta rawar kai, ya jere abinci wajen kala goma yace duk a fitar musu… Tray d’in farko ya fara d’auka ya nufi table d’in da akace suna nan… Tun kafin ya k’araso yaga d’ayan ya kafe shi da ido, yana k’arasowa ya d’an gaidasu kafin ya ajjiye ya fara niyyar juyawa dan ya d’auko musu wani yaji ance “Ya’akub!” Da sauri ya juya jin wannan balarabe ya kira sunan shi rad’au. Suna had’a ido dashi ya tuna shi Abokin Yayansa ne sosai dan yana yawan zuwa gidansu na nan idan sunzo. Sake maimaita sunan balaraben yayi, da d’an murmushi Abba ya amsa sannan ya sake gaishe shi. Amsawa yayi sannan da mamaki yace mishi “aiki yake yi anan!” D’aga mishi kai kawai Abba yayi. D’an jimm!! balaraben yayi kafin ya hau bawa Abokanan tafiyartasa labarin waye Abba. Da mamakinsu suma suka dinga kallonshi kasancewar duk sun san Yahaya MT. Wannan balaraben yake gaya musu irin tarin alkhairan da Yahayan yayi mishi kafin ya juyo kan Ya’akub d’in yace masa “bai yi karatu bane? Maiyasa yake aiki a matsayin waiter?” Da murmushi yace “yazo k’asar ne yayi sabon aure kuma bai san kowa ba shiyasa.” Da d’an fad’a mutumin ya fara cewa “ya za a yi suna garin nan amma Yahaya ya bar k’anin shi haka? ai ko shi waya d’aya kawai zai yi a dauki k’anin shi a aiki, bara yana komawa gida zai kirashi…” Abba bai b’oye musu komai ba yace “Ya d’an samu matsala da Mahaifinsu ne, so idan Yahayan ya taimaka mishi, zai iya involving nashi a case d’in shiyasa.” Cike da gamsuwa balaraben yace “Ina credentials d’inshi? ya kwaso ya zo su tafi yanzu ba sai anjima ba.” Cike da farin ciki ya nufi d’aki, yana murna, ya isa d’akinsu. Yana shiga ya tarar Maryam tana bacci, yaso ya tashe ta ya fad’a mata amman kawai sai ya barta ya kwashi abubuwan da yake buk’ata ya fita a hankali gudun kar ya tada ita. Yana zuwa ya tarar har sun mik’e abincin kad’an suka d’an cachchalkala shi kawai suke jira, shiyasa yana zuwa suka wuce. Bai sha wahala ba kasancewar companyn Baban d’aya daga cikin mutanen da Yayan nashi ya tab’a taimakawa ne, da Mutumin da Baban nasa ne suka yi mishi interview, Allah sarki mutumin da alama yaji dad’in abinda Yahaya yayi mishi dan a wajen ma yanata gayawa Mahaifinshi ai k’anin Yahaya ne. A take ba b’ata lokaci bayan an gama interview aka d’auke shi aiki. Har da ardrobe allowance aka had’a mishi. Sai wajen 5 tukunna ya dawo, da mamaki Maryam take kallonshi yadda ya shigo cike da fara’a..yana shigowa yayi hugging d’inta ya d’agata sama yana juyawa. Sai da ya ajjiyeta yana dariya ya shiga bata labari, ba k’aramin godiya ga Allah da farin cikin tayi ba, ahankali ya sake hugging d’inta yace “Maryam ke good luck ce, kiga fa a yadda muka shigo garin nan amman ko wata biyar bamu yi ba yau nine harda office, sannan ko daidai da rana d’aya bamu tagaiyyaraba.” Cikin murmushi itama ta sa hannu ta rungume shi, suna a haka sukaji knocking!! Mik’ewa yayi yaje ya bud’e aikuwa yana bud’ewa suka yi ido biyu da manager, ko gaisuwarshi bai amsaba ya hau sirfa mishi bala’i yana cewa “Ya bar bak’i d’azu bai k’arasa kai abinciba sai cook d’inne ya kai da kanshi, saboda tsabar yana so ya nuna hotel d’in bashida tsari ko? Sannan tun d’azu aketa neman shi baya nan, ina yaje?” Bai b’oyewa manager d’in ba nan yake gaya mishi “ai aiki ya samu!”. A tunanin Abba managern zai taya shi farin ciki amman sai yaga sab’anin haka dan daga k’arshema cewa yayi ya kwashe kayanshi ya nemi waje tunda ya samu aiki, ai daman ba k’aramin discount suka yi mishi ba, wajen 49%! Dan haka indai yana son yaci gaba da zama to saidai ya ajjiye wanchan aikin yaci gaba da yi musu aiki, yabashi 30 minutes yaje yayi making up mind d’inshi.” Yana gama fad’an haka ya juya ya fita. Tuni Abba ya yanke shawarar barin wajen ya kama haya tunda da d’an kud’i a hannunshi, amman dai sai da ya sake neman shawarar Maryam wadda itama tunaninta ya zo daidai da nashin. Dan haka a mintunan da basu gaza 20 ba sukayi parking komai nasu suka fito. Managern yana ganinsu da kaya ya fahimci decision d’in Abba na barin wajen nasu ne kenan, dan haka ya kuma b’ata rai ko godiyar da Abba yake yi mishi bai amsaba. Shi dai Abba bai damu ba yayi mishi sallama suka nufi cikin kitchen d’in dan ko ba komai ba zai manta da manager ba, kuma idan an d’an kwana biyu in sha Allah zai d’an dinga lek’owa suna gaisawa. A kitchen d’in daman sun tab’a hirar apartments masu sauk’i da cook d’in da suje shiri dan haka ya tambayeshi “inane yake ganin zai fi dacewa ya zauna?” Cike da farin ciki cook d’in yace “apartment d’in da yake zaune akwai security a estate d’in! Ya bashi 3 minutes ya chanja kayanshi ya zo suje sai ya rakashi har gidan mai estate d’in, daman Neighbour d’inshi bai dad’e da tashi ba sai ya karb’i gurin.” Cook d’in yanata murna da taya Abba murnar samun sabon aiki, a haka suka d’unguma, saida suka biya apartment d’in cook d’in, 2 bedroom da parlour da kitchen, anan suka ajjiye kayansu, sannan shi da Abba suka tafi gidan mutumin, aka bar Maryam da matarshi mai mutunci tanata janta a jiki Yaransu uku. Kamar yadda cook d’in yaso kuwa, apartment d’in gefen su aka bawa Abba, bayan ya biya kud’i ya cike duk wani abun buk’ata. Sai wajen 1 suka gama settling…har moping sai da mutumin nan da family d’inshi suka tayasu sannan suka yi musu sallama suka tafi nasu gidan. Washegari da safe Abba ya nufi wajen aiki. Da kyar Abba ya yarda Maryam ta fara aikin kitchen, shima sai da ta saka mishi kuka, saboda ba fita take yi ba sannan ba aikin da take yi, shiyasa gaba d’aya kafafunta har wani kumbura suka yi. Sai da yaga dai rashin exercise d’in ka iya yi mata illa tukunna ya yarda, amman dai shara wannaan aikinsa ne idan ya dawo, wankin toilet kuma kafin ya tafi office da safe tare sukeyi idan sun shiga wanka, wanki kuwa yanzu sunada washing machine abunsu............ Kano, Nigeria. 5months ago… Da mugun gudu Sadiya ta shiga cikin gidansu Maryam bayan taga tashin motar Abba, tana shiga takaici ya rufeta ganin babu kowa. Gidansu ta koma ta sanarwa Baaba Laraba halin da ake ciki dan ta d’an jiyo maganar Maryam d’in da Abba sama sama…Baaba Laraba kuwa sarkin y’an tsurku nan ta zari mayafi tayi waje…Gidan aminiyarta dillaliya ta fara lek’awa ta fesa mata. …Wannan gayawa wannan, kafin awa d’aya labari ya baza unguwa ‘Maryam ta gudu da saurayinta wanda aka kamasu a makaranta suna lalata!’. Har majalisar maza zancen da akeyi kenan, magana har ta kai kunnen tsofaffin unguwa ana ta cewa “Y’ar gidan mai unguwa kuma Limami ta gudu ta bi saurayinta!’. Ana cikin haka Madu da su Shuwa suka dawo, har da Ya Usman wanda jikinshi ya d’anyi sauk’i dan a asibitin a gabanshi aka yanke shawarar aura mishi Maryam da zarar an dawo gida!. Duk da sun san ba a neman aure cikin aure amman zasu je su yiwa Yayan Abba bayani su nemi alfarma a wajensu. Baaba Talatu ma da farin cikin ta ta dawo. Tun kafin su shigar da mota gida K’asimu ya tsayar da motar da yaga Madu da Bashir a ciki, parking Madu yayi a gefe dan ya bawa motar da Ya Jamilu yake tuk’awa damar wucewa, bayan sun fito, ko gaisawa K’asimu bai bari sun yi ba ga y’an unguwa da ganinsu yasa suka k’araso suma domin suji k’arin bayani….ba tare da tauna zance ko lafazi mai kwantar da hankali ba K’asimu ya shiga koro musu bayani kamar a gabanshi aka yi, har da cewa “sai da Maryam da Abban suka gama rungume rungume ma tun kafin su shiga motar su gudu.” Ba tare da Madu ya kula kowa ba ya kamo hannun Baba Bashir suka nufi cikin gidan Baba Bashir d’in, tun kafin su k’arasa shiga ya fara jiyo kukan Shuwa, suna shiga tsakar gidan ciki suka tarar da Baabaa laraba da dillaliya suna ta kora mata bayani tana kuka!. Ya Jamilu ne yace “dan Allah ya isa haka!!” Sannan ya cewa su Sadiya “an gode, ku je, za muji da lamarin!.” Suna fita kamar jira Shuwa take yi ta mik’e ta fara yiwa Madu bala’i kamar ba Mijinta ba, gaba d’aya laifin ta d’aurashi a kansa, a cewarta “Ai shi ya shagwab’a Maryam d’in ,ba dan shi ba da duk haka bata faru ba! Sannan saboda rashin lissafi yaje ya bawa Yaron da bai gama sani ba Y’arsu, gashi yanzu ya gudu da ita!! Wannan wanne irin abin kunya ne, da wanne ido zata kalli jama’a??? Mai zata ce wa mutane?. A yanzu haka Innaa tana kasuwa taje siyowa Maryam kayan d’aki! Shin ta Ina zata fara yi mata bayani idan ta dawo? Mai zata ce mata???” kuka take kamar ranta zai fita tana cewa “Madu ya cuceta duk shi ya jawo mata.” Baba Bashir ne yace “suje gida su duba koina, a dudduba sosai.” Dan shi bai gama yarda da maganar su Sadiya ba......... BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 18 Babu inda ba a duba ba, amman babu Maryam babu alamar ta, gaba d’aya hankalin kowa a tashe yake, tunba ma da Innaa ta dawo daga kasuwa nik’i nik’i da kayan d’aki ba!. Babu kalar zagin da bata yiwa Madu ba, Mallan shima yana k’arasowa ya iske mummunan labari. Har dare basu zauna ba domin shi Madu ya dage akan ‘bai yarda Maryam guduwa tayi ba!’. Sune har police station da daddare bayan sallar Isha……..da kyar suka iya cin abinci tun safe….. Suna zaune a gidan Madun, Inna tana ta yada magana tana cewa “Madu ya janyo musu abun kunya! Itakam Allah ma yaso ta tunda idan aka bi tsattso ba a jikinta ya fito ba!! Kuma kowa ya san Shuwanta bata da laifi…”waye waye…. Har sai da taga ran mallan ya b’aci ya fara yi mata bala’i shima, tukunna tayi shiru. Sallamar da aka yi da Madu ce ta katse mata guna gunin da take yi akan ‘itafa shiyasa tun farko bata so auren Shuwa da Madun ba’….. Cikin mutuwar jiki Madu ya mik’e Baba Bashir yana binshi suka fita tare domin amsa kiran da ake yi mishi a waje!. Suna fita suka tarar da dattawan unguwar, da sauri Madu ya k’arasa ya shiga basu hannu yana tambayar su “ko lafiya??” Dan shi a tunanin sa anga Maryam ne. Amma sab’anin hakan sai yaji wai ‘su meeting d’in gaggawa suka zo ayi saboda guduwar da y’arsa tayi, domin kuwa y’an unguwa sunce ya kamata a chanza sabon Limami.!’ Da mamaki yake kallon su, shi yana ta neman y’arsa, su kuma suna ta muk’ami! shiyasa ba tare da b’ata lokaci ba ya sanar musu da ‘ya sauk’a!’. Amman hakan bai sanya sun barshi ba saida suka jashi akaje wajen meeting d’in. Suna zuwa yaga dubban mutane, su kawai ake jira.! Sai a wannan lokacin Madu ya san ba K’asimu kad’ai ba ne mak’iyinsa a layin!! Harda waenda yake ganinsu Abokanan sa duk cikinsu babu ya bi bayanshi.. Mutum uku ne kawai suka bi bayan Baba Bashir wanda Allah sarki dudda halin da Usman yake ciki bai sa ya juyawa Madun baya ba. A lokacin mutanen gurin rabuwa sukayi kashi uku Kashi na farko ‘sune su Baba Bashir su hud’u!’ Kashi na biyu ‘sun ce, y’ar Madu tayi laifi kuma shi ya janyo tunda shine ya shagwab’ata kuma baya son laifinta, amman bai kamata ace laifinta ya hau kanshiba, har a kai ga sauk’e shi ba’. Kashi na uku kuwa (su K’asimu) sunce ‘ai laifinshi ne y’arsa ta gudu yawon karuwanci, tun farko shine ya yi mata lagalaga ya shagwab’ata, baya tsawatar mata duk abinda takeso baya hanata! Haka k’iri k’iri aka koreta a makaranta saboda abunda take yi amman ya rufe yak’i gayawa kowa idan an tambayeshi sai dai yace chanza mata makarantar yake son yi! Ai y’an unguwar da aka taso sama da shekaru ashirin da biyar tare ya kamata ace yanzu an zama d’aya dan haka su ba zasu dinga bin mutumin da yake ha’intarsu! Sallah ba. Su idan matsala ta taso a nasu gidajen tuni sunzo sun saki baki dan neman shawara da yarda da juna, amman shi y’arsa daya kamata ace tun kafin abun ya kai haka a taka burki yak’i yarda ya bada k’ofar yin hakan kuma shima ta bangarenshi bai yi ba, gashi yanzu ta tafi tabi saurayi. Saboda haka.. Su baza su bi uban karuwa ba a masallaci har ma da unguwa.’ Harda cewa ‘ci yake yi da addini.’ Nan suka fara jidar kaya za suyi zanga zanga! Dattawan unguwa na ganin haka suka hau basu hak’uri, sannan a take aka sake sauk’e Madu daga matsayinshi na mai unguwa ma gaba d’aya! Dan a samu a zauna lafiya. Babu kalmar da ta fi b’atawa Madu rai irin na kiran ‘Maryam karuwa da aka yi’ Shiyasa tun baya mayar musu har ya zo yafara mayar musu da martani, da kyar Baba Bashir ya janye sa suka bar wajen sukayi gida. Dishi dishi kawai Madu yake gani, bai san ta Ina zai fara ba, Da kyar ya iya kai kanshi gida. Yana shiga Inna ta tisa shi a gaba da tata mitar, harda d’akko mayafinta tace ‘sai ya kaita gidan Yayan Abba! Ai sunce sun yi bincike dan haka ya kaita ko wajen wani nashi ne…’ Madu kuwa tun rana, suke ziryar zuwa ganin Alhaji Yahaya amman mai gadi yace musu wai yace ‘kar a barsu su shiga!!’. Shiyasa ma abun ya kuma dagule musu, amman dai basu fad’awa kowa ba suna so suyi settling ne a tsakaninsu, shiyasa yanzu furucin Inna ya sake rikitashi!. Ba yadda ya iya hakanan kawai ya sanya Jamilu ya jasu a mota suka nufi gidan, dan bashi da wani sauran energy. Har da Inna da Mallan aka tafi, suna zuwa, daidai motar Alhaji Yahaya tana k’arasowa. Da sauri Madu ya fita ya isa gaban motar tashi ya tsaya!. Alhaji Yahaya ganin an ritsa shi yasa kawai ya fito dan babu yadda zaiyi, a hankali ya k’arasa inda Madun yake wanda isar tashi tayi daidai da k’arasowar su Inna wajen. Duk da rikicin da Madu yake a ciki hakan bai hanashi tsayawa suka gaisa da Alhaji Yahaya wanda ya kasa had’a ido dashi ba. Inna ce ta matso sannan tace “Kai Yaro!! Ina kuka saka mjni jikata?? fito min da ita dan tun yanzu anan zan fara cin uwar ta kafin mu k’arasa gida.” Ajiyar zuciya ya sauk’e sannan ya juyo ya fuskanci Madu ya fara kwararo masa bayanin duk abinda ya faru tun daga safiyar yau har kawo yanzu, hatta furucin da granpa ya yiwa Maryam akanshi da Shuwa da Bilkisu duk bai b’oye ba. Sannan ya k’ara da cewa “Shima dalilin da yasa, yaketa dudging karsu had’u shine ‘mahaifinsu yace indai ya yarda ya sauraresu to ranshi sai yayi mugun b’aci, kuma sai ya kulle zuri’ar su Madu gaba d’ayansu!’.” Yace “Mahaifin nasu yace ‘babu su babu duk wani abunda ya shafi Maryam da Abba’.” Ajiyar zuciya ya sauk’e sannan yace “A tunanina zamu iya shawo kanshi, amman ranar da nazo gidan ka bayan mun koma naje na sameshi, b’acin ran dana gani a fuskar shi tabbas yayi matuk’ar tsoratani, shiyasa na cewa Abba ya hak’ura! Amman Yaran zamani kaga abunda suka je sukayi… Ni ban san ta Ina zan fara baka hak’uri ba, amman yanzu dai Ina rok’on ka da kuyi saurin barin nan, mahaifin mu yana da c i ds da yawa especially ma yanzu da case d’innan yake going! Idan yaji labarin na ganku akwai babbar matsala.” Yana gama fad’in haka yayi saurin komawa cikin motarshi ya danna horn mai gadi ya bud’e mishi ya shige ciki da gudu. Da kyar Baba Bashir da Ya Jamilu suka ja Madu suka saka shi a mota, dan daskare musu yayi a wajen kwata kwata yak’i motsi. Duk tsauri da k’ok’arin Madu sai da hawaye ya zubo ta idonsa….. Yanzu wannan itace kalar rayuwar da Maryam d’insa zata yi? Da irin wannan mutumin a matsayin suriki?? Wanda d’an cikinsa ma daya haifa bai sarara wa ba ballantana ita karan kad’a miya!! Gashi k’iri k’iri ya nuna ya tsane ta! Tabbas Maryam guduwa tayi amman aure tayi! Abu d’aya daya sani shine idan zai had’iyi AlQurani yana rantsuwa yana fad’awa mutane Maryam aure tayi babu wanda zai yarda. He is very disappointed in Maryam! Sam bai tab’a tunanin zata iya aikata haka ba! Bai ankaraba yaji fuskarshi ta jik’e sharkaf da hawaye!!! Baba Bashir ma tausayinshi ne yasa ya share tashi kwallar da yake ta k’ok’arin b’oyewa saboda yanaso nunawa Madun kwarin gwiwa. Inna ma duk surutunta tayi shiruuuu! Kamar ruwa ya cinyeta, tabbas ta san Maryam bata kyauta ba, amman ko da irin wannan surikin aka barta hukuncinta yama yi yawa. Haka Mallan shima da Ya Jamilu suma duk sun yi shiru….motar shiru baka jin sautin komai sai na sauk’ar ajiyar zuciyar Madu. A haka suka k’araso, suna shiga suka tarar dasu Baaba Talatu sunyi cirko cirko, nan suka hau tambayarsu, Innaa ce ta fara labarta musu…… Salatin da Shuwa tasa tare da kuka a lokaci daya ne ya juyo da hankalinsu kanta, aikuwa da gudu suka k’araso , sakamokon ganin Madu a k’asa wanwar kamar babu rai a tare da shi… A take su Ya Jamilu suka kinkimeshi aka saka a mota suka nufi asibiti dukkan su. Sai da Likitoci sukayi da gaske tukunna suka samu numfashin sa ya daidaita… Bai farka ba sai bayan kwana hud’u amma ya samu stroke mai k’arfi dan hatta bakinshi da hancinshi sun koma b’angare daya a fuskarshi. Idan ka ganshi abun tausayi dole kayi kuka, Likitocin ne suka yi ta basu kwarin guiwa akan zai dawo daidai da yardar Allah da taimokon therapy da excercise d’in da za’a d’aurashi akai. A hankali ahankali zai dinga samun sauk’i in sha Allah. Hakan kuwa akayi dan jikin nashi da kad’an kad’an ya fara gyaruwa… Ya Usman kuwa shaye shaye ya fara gadan gadan babu kama hannun Yaro, cikin wata uku ya lalace gaba d’aya, tun iyayen basu fahimta ba har suka gane, Ya Usman wanda a daa yake fari tass yanzu kam sai ka k’ura ido tukunna zaka iya tantance hasken fatar tashi, dan sai dai a kirashi da chocolate colour, duk ya yamushe ya fige ya rame over!!! Da aka yi k’ok’arin hanashi sai ya nemi haukacewa, dan basu saniba ashe abun ya shiga jikinshi sosai, idan yazo sha ashe shi over dose ma yake yi! Shiyasa yanzu abun yake neman tab’a kwakwalwasa, ko zuwa kayi kusa dashi idan bakayi masa ba sai dai kaji duka!! Wannan dalili ya sanya kowa yake tsoron rab’arsa, Sadiya! Kad’ai ce take iya zuwa inda yake, duk da kuwa itama d’in idan taje sai ya mareta ko yayi mata duka amman bata gajiya….ita zata je ta kai mishi abinci ta share mishi d’aki ta wanke mishi band’aki!. Tun Laraba da K’asimu suna hanata suna zaginta har suka daina badan suna so ba sai dan rashin kunyar da take zuba musu a duk lokacin da suka so hanatan kuma ba yadda za suyi da ita. Watan Madu hud’u yana fama, da ikon Allah a wata na biyar ya warke dama anata samun cigaba a hankali a hankali. Bayan ya dawo gida hankalinshi yayi matuk’ar tashi da halin da yaga Usman shiyasa ya duk’ufa ya dinga yi mishi addu’o’i ta tofi, a hankali a hankali kafin wata d’aya shima Allah ya bashi lafiya amman dai kana ganinshi ka san yana cikin damuwa saboda lokuta da dama ma idan ka shiga sai dai ka tarar dashi yana kuka… D’agawa K’asimu hankali da Sadiya tayi ne yasa ya taso ya zo wajen su Madu akan maganar ta da Usman d’in. Da ‘to’ kawai suka bishi amman ko suna hauka baza su bari su had’a Jini da K’asimu ba….dan a lokacin da Al’Amarin Maryam ya faru shi yafi kowa zak’ewa, kusan shi ya yayata maganar ma har kowa yaji, kuma ya tsaya tsayin daka saida aka hukunta Madu (Da kyar ma aka barshi ya cigaba da sama a unguwar dan da cewa sukayi Madu sai ya bar unguwar). Sannan sam K’asimu bashi da hali mai kyau! Shima Usman duk da alkhairin da Sadiya tayi mishi hakan bai sa ya amince da auren ba, dan shi yanzu sana’a ma zai yi ya tara kud’i ya tafi Madina neman Maryam! Sai ya dawo da ita ko da bala’i ne. Shiyasa ranar da Sadiya tazo mishi gyara, yaji tausayinta dan sai nan nan take yi dashi, dan haka ya yanke shawarar ‘gara ya fad’a mata gaskiya’ saboda a yanzu yana ganin mutunci ta ko ba komai ita ta kula dashi a lokacin da kowa ya k’i shi. Zaunar da ita yayi ya fad’a mata cewa “shifa babu maganar aure a tsakaninsu, akwai abinda yasa a gabanshi, in ma saboda haka ne taketa kula dashi gara ma ta daina ta nemi wani suarayin tayi aurenta!. Amman yana mai tabbatar mata da bazai tab’a mantawa da irin alkhairin da tayi mishi ba, har abada!! Ya gode ya gode sosai.” Kuka kawai yaga ta fashe mishi dashi, da kyar ya samu ya lallasheta, ta tashi ta tafi gida. Tana zuwa gida ta tarar da Baba Laraba da dillaliya suna hira a tsakar gida da gudu ta fad’a kan Baba Laraba tana rusa kuka, nan ta koro mata abunda Ya Usman d’in yace.. Baba Laraba ce ta hauta da fada tana cewa “idan ita ba mayya baceba to ta hak’ura da Usman.” Dillaliya ce ta katse su ta cewa Sadiyan “ta tashi ta tafi ta daina kuka” sannan ta matso kusa da Baaba Laraban ta rad’a mata wasu maganganu…. Bayan kwana uku da safe, sai ga Baaba Talatu tazo gidansu Sadiya, da yamma Baba Bashir da Ya Jamilu, duk akan neman auren Sadiya….har wani b’oyewa Modu suke yi. Shi kuwa Madu da yaji labari abun ya bashi mamaki amman daya je ya samu Usman yaga yadda shima ya haukace akan Sadiyar sai kawai ya biyesu aka shiga neman auren…. Wata biyu aka saka dan ana so a had’a dana Ya Jamilu, lokaci yana cika da ikon Allah aka sha biki aka d’aura aure. Sadiya ta tare a gidanta wanda Baba Bashir da Madu suka bawa Ya Usman d’in anan bayan layi nasu, shi kuma Ya Jamilu dake ya samu sabon posting a Ibadan zai sake komawa yayi shekaru hakan yasanya ya d’auki amaryarsa suka tafi tare amman shima akwai gidanshi anan kusa da na Ya Usman d’in, sanin da yayi ba kwana kusa zai dawo garin ba ya sanyashi zuba haya........... Bayan shekaru bakwai!. Madina… Wani d’an mini duplex ne mai d’auke da d’an k’aramin compound da 3 bedrooms 3 parlours sai kitchen da dining area, Maryam da Abba sukaje gani domin yanaso ya siya, a wannan lokacin apart from work na office yana business kala kala so Allah yayi mishi bud’i. Bai yi wata k’iba ba saboda ba yanayin k’irarsa kenan ba amman ya murmure yayi haske yayi fresh kana ganinshi kaga hutu, kyawunshi ya sake fitowa . Tsayawa fad’ad kyauwun da Maryam ta k’ara ma b’ata lokacine. Suna tsaye a cikin gidan yana magana da masu gidan da lawyer, ita kuwa in banda cika da batsewa ba abunda take yi, jira kawai take a tab’a ta ta fashe da kuka. Daman already sun gama magana da ganin gidan a hoto Dan Abban ma ya tab’a zuwa sau d’aya yau ya kawo Maryam d’in ne akan idan gidan yayi mata sai a siya. Koda ya tambayetan kuwa kawai d’aga kai tayi ba tare da tace k’ala ba. Murmushi kawai yayi ya juya wajen mutanen…har da lauyanshi suka zo, shiyasa kawai aka fara cike cike bayan an gama suka karb’i keys suka nufi apartment d’insu dan suyi parking. Kamar jira takeyi suna shiga tun a falo ta fara kuka tace “ita wallahi babu inda zata je kawai ya mayar da ita gida, tunda har yayi kud’in da zai iya siyan gida a nan ai zai iya nema mata jirgi taje Nigeria, kuma kwanaki tayita tambayarshi ‘ko waya yaje’ amma yace mata ‘waya bai je Nigeria ba’, nan kuwa waya yaje, jiya neighbour d’insu take ce mata akwai anty d’inta a Nigeria kullum sai sunyi waya. Kuma tace landline ma yana iya tafiya sometimes…” Abba tun yana yiwa rigimar tata dariya har ya daina dan yaga abun nata na yau dagskene, dan tace “wallahi ba inda zata je, ko Yaya ne ya kira. Tunda yanzu ai duk k’arshen shekara yana zuwa dubasu, kuma k’arshen shekara ya zo dan haka ya taho mata da numbern su Shuwa ita ko waya ne ta samu tayi dasu, kafin taje gaskiya hak’urin ta ya k’are!.” A b’angaren Abba kuwa, duk zuwan da Yayan nasu zaiyi, sai yayi yunk’urin binsa su koma, amman sai Yayan nashi ya hanashi, saboda ba sau d’aya ba Granpa ya kan gaya mishi ‘in dai yaje Madina suka yi tsautsayin had’uwa da Abba to ya gaya masa yana nan akan bakarshi babu abinda ya chanja’, kasancewar ya san yanayin aikin Yahayan a chan yake kuma yana zuwa akai akai(ambassador) shiyasa ba yadda ya iya ya san dole wani lokacin zasu had’u, kuma ya fad’a ya sake maimaitawa yace ta kan Maryam d’in zai fara. Duk lokacin da Granpa zai zo Madina kuwa sai ya aikawa Abban da sak’o, hakanan In ba lokacin hajji bane zai d’auki Maryam ya d’au leave a wajen aiki su bar k’asar gaba d’aya.. Volume d’in kukan nata data k’ara ne ya katse mishi tunani. Kallonta yayi cike da tausayi ba tare da yace mata komai ba ya hau tunowa shekara biyu da suka wuce shi da kanshi ya rok’i Yayan nashi akan yaje wajen Madu ya kirasu su gaisa da Maryam d’in ko hankalinta zai d’an kwanta. Hannu bibbiyu Madu ya karb’i Yahaya, amman ga mamakinsa daya ce ‘bari ya kira waya su gaisa da Maryam sai Madun ya nuna mishi bai ma san wa yake nufi ba!. Duk hak’urin duniyar nan Yahaya ya bashi tare da bayani da k’ok’arin lalllab’a shi da fahimtar dashi, amman furr!! Madu yace “shi bashi da wata y’a mai suna ‘Maryam’. Y’a d’aya tak Allah ya bashi a duniyar nan kuma sunanta ‘Bilkisu’. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 19 Jiki a mace haka Alhaji Yahaya ya tashi ya fito, Madu har wajen mota ya raka shi yana mai sake yi mishi godiyar taimakon da yayi musu shekarun baya da suka wuce na Usman. Bayan Yahayan ya koma ne ya d’au waya ya shaidawa Abba halin da ake ciki. Hankalin Abba ba k’aramin tashi yayi ba a wannan lokacin, idan ya kalli Maryam sai yaji gaba d’aya tausayinta ya rufeshi. Dan, in dai ya fahimta to Mahaifinta disowing d’inta yayi kenan! Duk sai yaji haushin kansa dan a ganinshi shine ya ja mata… Baya son gaya mata komai a yanzu, yafi so sai ya lallab’a Granpa ya barshi ya koma Nigeria in yaso sai suje tare da shi da Yayansa har ma da Limamin da ya d’aura musu aure ya tayasu bawa Madun hak’uri. Amman yanzu idan taji ta waya ko ta tafi Nigerian ita kad’ai ta samu wannan labarin ya san it’ll break her!!. Da kyar ya samu ya lallab’ata tayi shiru bayan yace mata “idan Yaya zai taho k’arshen watan nan zai zo mata da numbar Madu. Karshen wata nayi Yaya yazo, kamar kullum tare da matarsa da d’anshi mai shekara bakwai mai sunan Abba ana kiranshi da ‘ASLAM’. Maryam ita ta zab’a mishi suna Aslam, dan bayan an rad’a mishi sunan YAKUBU, sai Yayan ya tura musu sak’o yace Abba ya nemi sunan da za ana kiranshi dashi, shi kuma Abba ya cewa Maryam ta zab’a mishi…a wannan lokacin lokacin watanninsu shida da zuwa Madina aka haifi Aslam. Aslam ya shak’u da Maryam sosai, dan kamar yadda Abba ya fad’a suna yin shekara Yayansa ya fara bibiyar shi duk k’arshen shekara kuwa sai yazo, tun yana zuwa shi kad’ai har ya fara zuwa da Aslam da Mamansa. Dan Abba d’aga mishi hankali yayi akan ‘yazo mishi da takwaranshi ya gansa. Ai kuwa ranar da aka fara zuwa dashi Yaron yaga gata a wajen Maryam da Abba, shi yasa ya saba dasu sosai, yana son Maryam over itama tana son Yaron gashi yana da hankali. Mamanshi ma tanada kirki, dukda cewa ta girmi Maryam d’in amman hakan bai hanata k’ulla k’awance da Maryam dan tashi d’aya taji Maryam d’in ta kwanta mata a rai. D’ayar matar Yaya kuwa (amaryarsa) so d’aya aka zo da ita, ita ma ta haihu a lokacin d’anta d’aya sunansa ‘Muhammad (Arshaad) amma bata zo da shi ba. Tunda matar ta zo Maryam d’in ta lura y’ar rainin wayo ce, dan sai wani cika da batsewa take yi sannan tak’i sakewa da Maryam kwata kwata, idan aka zauna ana magana kuwa bata da labari sai na company’s da kadarorin Mahaifinta, bama ta cika yin magana da Hausa ba.! Ita Maryam a tunaninta maybe ko dan ta san uwar gidan Yaya (Maman Aslam) k’awarta ce shiyasa ta had’a take kishin harda ita. Sai bayan tafiyar su ne take tambayar Abba “Wai shin mecece matsalar amaryar Yaya da ita ne? Dan ta fahimci bata sonta.” Abba bai b’oye mata ba yace “ai best friend d’in Zainab ce (cousin d’inshi da ake so ya aura), sannan y’ar Abokin Granpa ce, shine ma ya had’a auren tun da dad’ewa a lokacin Allah bai bawa Maman Aslam haihuwa ba, a tunaninsu bata haihuwa, to ita kuma Maman Arshaad d’in sai mahaifinta yace “sai ta kammala karatunta wanda saura shekaru uku ta kammala”! Anyi komai an saka rana, Maman Aslam ita tayi ta k’arfafawa Yaya guiwa a kan auren dan bata son abinda zai jawo matsala tsakaninshi da Granpa kuma ita a nata tunanin ko da gaskene bata haihuwar! Amman cikin ikon Allah ba a yi shekara da yin baikon Yaya da Maman Arshaad ba! Maman Aslam ta haifi Aslam. Murna a wajen Yaya ba a magana dan yana mugun son matarshi a tunaninshi mahaifin nasu zai janye batun auren. Sai dai kuma Maman Arshaad tana kammala karatunta aka d’aura aure tare dana d’ayan brother d’insu Yaya Yusuf wanda ya auri cousin d’in Zainab ne shima, ta b’angaren Uwa.” Maryam ba k’aramin tashin hankali ta shiga ba data gama jin bayanin Abba. Dan sai da Abban yayi dana sanin bata labarin.. Daman chan rashin haihuwa shine main problem d’insu gashi kuma yanzu taji wagga zance!! ‘Kar fa taje itama Granpa yasa ayi mata kishiya!!!’ Da kyar Abba ya lallab’ata amman shi kansa a chan k’asan zuciyarshi hankalinshi ba a kwance yake ba.. Shi bama ta Granpa yake ba, a rayuwarshi bashi da burin daya wuce yaga jininsu shi da Maryam.….. Tunda su Yaya suka iso aka gaggaisa, Maryam take ta faman kasa kunne amman bataji Yaya yayi mata maganar wata number ba. Karshe dai cire kunya tayi ta tambaya. Shiruu, Yaya yayi, kafin ya umarcesu da ‘su basu waje’. Sai da suka fara tattaunawa shi da Abba tukunna Shi da kanshi ya kirata ya lallab’ata yace “Dan Allah ta k’ara hak’uri sunada dalili…watarana zata je ta gansu, in sha Allah.” Da kyar dan tana jin kunyar Yaya sosai ta iya tausar kanta sannan ta hak’ura Abba kuma ya duk’ufa da adduar ‘Allah ya daura shi akan Granpa’ ...... Bayan Shekara uku!.. Abba yana zaune suna hira da Maryam, Granpa ya kirashi a waya… Da kyar Abba ya iya d’aukar wayar saboda bai san me zai ji ba. Ko amsa gaisuwarshi Granpa bai yi ba kawai ya sanar da shi mahaifiyarshi bata da lafiya, tana son ganinsa… Har zai yi hangin up, sai kuma yace “Don’t come here with your wife!!” Tukunna ya kashe wayar. Tsabar farin ciki sai da hawaye suka gangaro a idanun Abba. A hankali ya share hawayen sannan ya d’au waya ya kira Yayanshi, yana d’auka yace “Yaya it works, i’m coming home!.” “Alhamdulillah” shine abunda Yayan yace kafin murya k’asa k’asa yace “amman fa kayi sauri, dan Granpa yana shirin neman kwararren Likita a dubata!! Kar muje ya gano wani abun.” “In sha Allah, zuwa nan da dare kuyi expecting d’inmu.” Cewar Abba. Maryam wadda ke gefen sa ce ta fara tsalle tana murna bayan ya kashe wayar. Cikin murnar da take yi ne tace “I wonder why! Bamu yi tunanin wannan plan d’inba all this time. Let me go and start parking….” A hankali shi kuma yace “let me start the preparations..” Da murna ta haye sama, Abba kuwa da farko yayi farinciki amman bai san daliliba haka nan kawai sai yaji baya so su tafi kwata kwata. Jiki a mace ya mik’e ya fita ya hau shirye shirye… Basu samu jirgi a ranar ba sai a washegari suka bi jirgin 8:00am. 1:30pm, jirginsu yayi landing a gida Nigeria. Yaya ne da Aslam a lokacin suka zo d’aukar su, ba gidan Granpa suka nufa ba,direct daga airport d’in suka nufi gidansu Maryam. Wani farin ciki take ji yana ratsa zuciyarta tun tasowarsu har kawo yanzu barema da taga anzo unguwar su. Suna shigowa layin su ta fashe da kukan murna, komai ya chanja kamar ba unguwar ba, gidansu da na Baba Bashir an d’aura bene an sake gyarawa da kyar ta iya gane gidajen. Tun kafin a gama parking ta bud’e mota ta fito da gudu ta shiga cikin gida. Da wata fara kyakkyawar budurwa ta fara cin karo a tsakar gida tana shanyar kayan makaranta, da wani Yaro kyakkyawa a gefenta yanata zuba mata surutu yana tayata shanyar kayan, a k’alla Yaron zai kai shekaru tara a duniya. Ragowan kayan cikin bokitin ta kwashe sannan ta mik’awa Yaron bokitin ta ce “Jaafar! Ungo bokitinan kaishi chan baya sai kazo kaje ka siyowa Jalila alawarta, naji har ta fara rigima.” Kalar tausayi Yaron da aka kira da Jaafar yayi sannan yace “Anty Bilkisu nima harda tawa zan siyo ko?”. Murmushi tayi sannan ta d’an sunkuyo kanshi kamar zatayi ruku’u ta kama kumatunshi kafin tace “Yaya babba!! kai baka san ka girma bako?”. Rau rau yayi da ido kamar zai yi kuka hakan yasa tace “to shikenan harda kai, sai ka had’a har da na Junaidu shima ka siyo da shi kafin ya zo ya fara zuba mini mita.” Tsalle Jaafar d’in yayi kafin ya d’auki bokitin ya nufi bayan gidan da gudu yana cewa “To Anty Bilkisu mun gode ganinan zuwa inje in siyo yanzun nan.” Maryam mamaki takeyi..kenan wannan Bilkisu k’anwarta ce?? tabbas ga kamanninta nan kuwa! Wannan inda ace a hanya suka had’u ai ba zata iya gane ta ba! Ta girma sosai kamar ba ita ba, ta zama budurwa… Mamaki sosai take yi, irin wannan girma haka? anya kuwa itace ko dai wata Bilkisu ce? Koda yake shekara goma ai ba nan kusa ba…. D’an matsowa tayi kusa da Bilkisu wadda ta bi bayan Jaafar da kallo tana murmushi. Kamar tana jin tsoro a hankali ta sa hannu ta tab’a ta tace “Bilkisu” Bilkisu jin an dafata an kira sunanta da kamar muryar da ta sani wadda ba zata tab’a mancewa ba yasa ta waiwayowa, aikuwa tana ganin Maryam ta gane ta!! Da sauri ta k’arasa juyowa tace “Ya Maryam!!! Sai kuma ta fad’a jikinta da gudu ta fashe da kuka tace “Ya Maryam kece da gaske…..” Itama Maryam d’in kuka ta sake fashewa dashi tana d’aga mata kai alamun ‘eh’. Da kyar ta iya zaro ta a jikinta ta shiga girgiza mata kai tana share mata hawaye alamun tayi shiru, dan farin ciki ma ya hanata magana. Fitowar Shuwa da Baabaa Talatu yayi daidai da k’arasowar su Abba cikin gidan … “Karka kuskura ka k’araso nan!!!, ka d’auketa ku koma inda kuka fito bama buk’atar ku!!” Muryar Shuwa ta daki dodon kunnuwansu. Da sauri Maryam ta cika Bilkisu ta nufi Shuwa da nufin rungumeta amman tana k’arasawa Shuwa ta d’auketa da mari! Cikin b’acin rai tace mata “idan kika yi gangancin tab’ani wallahi saina illataki!! Wai Yakubu baka jina ne?! Nace ka zo ka d’auketa ku bar nan tunkafin raina ya b’aci!!!”. Da mamaki cikin zazzaro ido Maryam take kallonta kafin ta kai k’asa ta fashe da wani marayan kuka gwanin ban tausayi… Gyaran murya Yayan Abba yayi zaiyi magana nan ma ta katse shi ta hanyar cewa “Ina ganin mutuncin ka, kar kayi abunda zai saka ni zuba maka rashin mutunci a tsakar gidan nan!”. Baaba Talatu ce ta fara lallashinta amman Shuwa tayi burus tace “wallahi sai sun fitar da Maryam a cikin gidan.” Kusan a tare duk suka sauk’e ajiyar zuciya tare da yin hamdala sakamokon jin muryar Madu da Ya Usman a waje, suna k’ok’arin bud’e gate. A tunanin su Madu zai tsawatarwa Shuwa amma koda ya zo, kamar yanda ya gayawa Alhaji Yahaya, haka ya sake tabbatarwa jama’a cewa “shi bashi da wata y’a Maryam, wannan baiwar Allah n kuma”yayi maganar yana nuna Maryam da aketa ce mishi yayi hak’uri ga Maryam ya yafe mata, yace “shi bai tab’a ganin ta a rayuwarshi ba.” Daga k’arshe abunda Madu yayi musu hatta Shuwa sai da jikinta yayi sanyi, dan Yara ya kirawo yace “su jefe su idan sunk’i fita!!” Kowa mamaki ne ya kama shi dan wannan kwata kwata ba d’abiar Madu baceba, shiyasa tun kafin a jefe su Ya Usman da Baaba Talatu suka d’aga Maryam suka yi gidansu da ita, dan Madu yace “wallahi ko k’ofar falon shi ba zata k’arasaba.!” Suma su Abba haka suka juya suka fita, da kyar suka iya janye Aslam wanda yake ta kurma ihun ‘shi sai ya bi Anty Maryam, ba za a barta anan ba!’ Ahaka dai suka tafi suna mamakin abunda suke tunanin zai yi sauk’i, ga yadda ya kasance! Ya zama babban case. Sai bayan kwana uku tukunna Abba ya samu ya zo yaga Maryam. Da ta ganshi sai da gabanta ya fad’i hankalinta ya tashi dan gaba d’aya ya rame ya fita a haiyyacin shi a cikin kwana uku kacal!. A take ta hau tambayarshi ‘mai ya faru?!’ duk ta rikice, dukda kuwa itama tana fama da tata damuwar dan y’an unguwa sai yamud’id’i akeyi da ita akan cewa ‘ba aure tayiba, saurayi tabi, yanzu kuma ya gaji da ita ya dawo da ita’. Sadiya har wani shishshige mata take yi, kasancewar yanzu babu Zainab tayi aure da yaranta biyu ta na Kaduna, kuma duk Yara mate d’insu ba a kusa suke aureba. Haka nan zata zo ta zauna tayi ta bugar cikinta batasan sarai Maryam d’in ta gane me take yi ba, dan indai ta zo ta tafi to sai taji sabon zance ya fito a unguwa. Gashi kuma Madu kwata kwata yak’i magana wanda shine ya kamata ace ya ya fito ya gayawa mutane aurene ya kaita Madina, amman sam yak’i cewa komai ya nad’e hannu yayi shiru sai zaginta akeyi. Gaba d’aya hankalinta a tashe yake, sai kuma ganin halin da Abbanta yake a ciki ya sake d’aga mata hankali….shiyasa ko duguwar gaisuwa bata bari sunyi ba tahau jera mishi tambayoyi…. Bai b’oye mata ba, nan ya hau kwararo mata bayanin halinda ake ciki .....Suna tunanin sun yiwa Granpa wayo ashe ya san plan d’insu…da gangan ya bar su suka dawo gida.! Ummi(Zainab) cousin d’insa wadda aka tab’a cewa ya aura ya gudu! Wai itace ta gama phd d’inta yanzu shine za ‘a d’aura musu aure next week ....... Maryam mutuwar zaune tayi da jin wannan sabon tashin hankali, dan kwata kwata kasa motsawa tayi sai da ya tab’a ta tukunna ta fashe da kuka… Ba k’aramin tashi hankalinshi ya shiga ba…. Tashi d’aya ya hau ce mata “kawai ta d’auko passport d’inta su gudu kamar yadda suka yi da farko.” Bata kuka shi ba duk maganar da yake ta faman yi sai da ta ji zuciyarta ta d’anyi sauk’i tukunna tace “babu inda zan koma in bar su Shuwa suna fushi da ni haka! Ka je ka auri cousin d’in naka Abba ba komai ai daman kai Mijin mata hud’u ne, Allah ya sanya alkhairi.” Tana gama fad’in haka tayi saurin ce mishi “ya tafi sai da safe.” Tun kafin ya kuma tsayar da ita tayi cikin gida da gudu tana kuka. Da kyar Baaba Talatu ta lallab’ata ta fad’a mata halinda ake ciki, ba k’aramin tausayamata tayi ba kuwa, dan har saida ta kusan yin fad’a da Shuwa a wannan ranar saboda Maryam d’in tana cikin gaya mata Shuwa ta shigo, nan itama take jin abunda yake faruwa b’udar bakin Shuwan sai cewa tayi “Allah ya k’ara.” Maganar ta bakanta ran Baaba Talatu sosai!! Taya kina uwa zaki na yiwa y’ar wannan maganar?. K’arshe dai Shuwa bata zauna a gidan ba ta tashi ta tafi. Tun wannan ranar Abba bai sake dawowa ba.! Shiru da kad’aici nan suka taru suka yiwa Maryam yawa dan da farko Bilkisu tana d’an lek’o mata ashe itama sauran sati biyu bikinta lokacin da d’in Maryam ta dawo, Y’an Maiduguri suna zuwa kuwa aka hanata zuwa dan had’uwa akayi har Shuwa aka had’e wa Maryam kai kamar ba ita ta haifeta ba. Wani abun ma sai ranar da akayi bikin Bilkisu Maryam taga abu dan dangin Shuwa kakaf suma nunawa suka yi basu santa ba, waenda taci sa’a suka kulata kuwa! Yada mata magana suka dinga yi. Da akazo za a kai Bilkisu gidanta har Maryam ta shiga mota Shuwa ta fito da ita a gaban mutane, kunya da bak’in ciki suka sanya ta kawai ta koma cikin gida tana kuka, tun daga ranar kuwa rashin lafiya tace ‘bismillahi’ ko abinci bata iya ci...... Yau kusan sati biyu kenan, da abun ya Ishi Baaba Talatu nan ta kwasheta sukayi asibiti. Suna zuwa bayan y’an gwaje gwaje aka tabbatar da Maryam tana da ciki wata d’aya. Maryam duk kunyar ta kasa b’oye murnar da take ciki tayi ita kuwa Baaba Taraba kamar tayi mata kuka dan bata sani ba sunk’i gaya mata ne , .......Amman Abba Mahaifin shi ya tura shi honeymoon da amaryar sa Uk kuma ya tula mishi uban aiki!! Bayan haka yace mishi sai nan da a k’alla shekara tukunna yakeso ya dawo, yayi magana mahaifinshi yace idan ya kuma yi mishi musu, sai sunyi shekara goma tukunna zasu dawo kamar yadda yayi da Maryam. Sarai ya san me Granpa d’in yake son yi ‘so yake ya had’a shi fad’a da ita ta k’arfin tsiya’ Tunda ya san ko zuciyar gold gareta idan taji zancen tafiyar sai ta d’aga hankalinta. Shiyasa ranar ya zo har kuka yayi a gaban Baba Bashir yace mishi kuma ya cewa Maryam tazo su sake guduwa tace babu inda zata tafi tabar su Shuwa suna fushi da ita. Yana ganin kawai b’oye mata zancen tafiyar zai yi inyaso sai yayi k’ok’ari ya dinga zuwa duk bayan wata d’aya koda a b’oye ne, saboda baya so ta d’aga hankalinta ko tasa wani tunanin a ranta saboda daga haka ne Granpa zai yi nasara a kansu. Gaba d’aya In ka ganshi hankalinshi a tashe yake Baba Bashir ne yayi ta bashi baki, dakyar ya lallab’asa ya tafi yace zai yiwa Maryam d’in bayani, in ta d’an samu nutsuwa. Saboda shi a ganinshi bai kamata a b’oye mata ba........ Baba Talatu tana cikin wannan tunanin suka k’araso gida. Jikinta duk a mace dan har Maryam d’in saida ta lura da hakan. Suna isowa d’aki ta d’au waya ta fara neman layin Abba, duk fushin da take yi dashi na k’in zuwa ya washe. Ta gwada yafi sau nawa amman not reachable, hakanan ba yadda ta iya ba dan ranta yaso ba ta hak’ura. Tun daga ranar ba Abba ba labarinshi tun tana b’oyewa har ta kasa, dan in ka ganta sai ka tausaya mata ga tsohon ciki har wata Takwas!! Amma duk wannan halin da take a ciki bai sa Shuwa ko Madu sun sauk’o daga fushin da suke yi da itaba, ko gidan Baba Bashir Shuwa ta daina shiga tayi saboda ita. Bilkisu kam in zata zo wajenta sai dai tazo a b’oye! Bilkisun ce ma take d’an kwantar mata da hankali, duk abunda ya same su bayan ta bar gidan sai da ta fad’a mata har rashin lafiyar Madu da Ya Usman da rasuwar Malan da Inna…. Maryam kuwa taji ba dad’i daga jin labarin, tabbas dole kam suyi fushi da ita. Amman rashin sanin ranar sauk’owarsu shike daganan mata hankali, ga Abba ya d’auke k’afa!! Wayarshi kuma bata tafiya. Tsabar yadda ta d’aga hankalinta ne ya sanya lokacin haihuwanta bai yi ba amma ta fara labour gadan gadan!! Ga jininta yayi mugun hawa nan da nan duk ta kumbura ta fita a haiyyacinta…ganin ba zata iya haihuwa da kanta bane yasanya Likitocin yanke shawarar yi mata ‘C S’. Babu irin kalar rok’on da Baaba Talatu bata yiwa Shuwa ba akan taje ta dubo Maryam kafin ayi aikin amman k’iri k’iri tak’i zuwa. Haka aka shiga da Maryam aka yi mata aikin… Ma sha Allah! It was successful, an ciro mata Baby girl k’atuwa mai kama da Mahaifinta sak!!! Tun a jinjirarta yana yin idanunta da eyebrows dinta na Mahaifinta ne exactly!! Shiyasa in dai ka san Abba to kuwa kana d’aukarta zaka san y’arsa ce. Ranar Maryam taci kukan farin ciki, da kuma na tunanin mai yasa Abba zai yi mata haka a lokacin da tafi buk’atar shi?!.. Ya sha fad’a mata bashi da buri a rayuwarnan wanda ya wuce yaga babynsu shi da ita, abunda suka riga suka cire rai dashi gashi yau Allah ya azurtasu dashi…. Don haka ta cewa Bilkisu “ta nemo mata biro da takarda!! Idan wayarsa baya tafiya ai akwai letter.” Haka kuwa akayi ta rubuta mishi cewa “ta haihu sun samu baby girl… Tare da sunan asibitin da take.” A lokacin ko sunan MT Idan ka kira a garin Kano babu wanda bai sansu ba. Shiyasa ta bawa Bilkisu tace “taje k’ofar estate d’insu ta nemi alfarmar ganin Daniel daga nan tace masa ya had’ata da Abba Tana son ganin shi ko da na minti uku ne.” A b’oye Bilkisu ta tafi, dukda itama a lokacin tsohon ciki gareta har na wata bakwai. Ta kusan 2 hours tukunna ta dawo duk da cewa gidan babu wani nisa tsakaninsu. Sai da su Baaba Laraba da Sadiya waenda suka zo ganin Baby suka tafi tukunna Bilkisun ta mik’a mata takardar da ta dawo da ita. Da sauri Maryam ta karb’a ta fara karantawa.. Kafin ta k’arasa tuni fuskarta ta jik’e sharkaf da gumi da hawaye. Idanunta jazir!! Ta d’ago ta kalli Bilkisu dashi wadda itama ta lek’o tana duba rubutun cikin takardar! Kai kana ganinsu ka san hankalinsu a tashe yake matuk’a!!. Maryam tana so ta k’aryata amman ko a mafarki idan taga rubutun Abba sai ta gane …….Naji kin haihu, congratulations to you a lone Maryam. I choose to obey my Dad. Ki reni Yarinyarki ke d’aya! Don’t ever tell her my name.. Akwai sak’on da na bawa Madu ya baki wanda daga dukkannin alamu bai kai ga isowa gareki ba.!…………. Ta karanta sak’on nan ta kuma maimaitawa yafi so babu adadi, so take yi kawai ta gano ta inda zata ce wannan ba rubutun Abba bane ba. Jikinta ba kwari da kyar ma take iya wasu abubuwan amman haka ta fara k’ok’arin tashi, tace “wajen Madu zata je yau ko zai yankata zata je wajensa ta karb’i sak’on da Abba ya bayar yace a bata!! She needs some elaborations.” Bilkisu ce take kokarin hanata tana cewa “Likita fa yace kar ta d’ago kanta karta zauna…” Amma sam Maryam bama ta jinta…. Suna a haka Baaba Taraba da Baba Bashir da Madu suka shigo.. Tana ganinsu ta fashe da kuka abin tausayi. Baabaa Talatu ce ta karb’i takardar hannunta ta karanta. Ajiyar zuciya kawai ta sauk’e sannan ta mik’awa su Baba Bashir.. Bayan sun gama karantawa suma da d’an kokwanto akan fuskar su amman kawai sai suka share. Baba Bashir ne ya fara magana, yace “Daman akwai maganar da muke so muzo muyi dake to gashi shi Abban ma ya riga ya fara fad’a miki.” Takarda ya mik’o mata, ta sanya hannu ta karb’a kafin ta bud’e takardar Baba Bashir yace “Maryam duk abinda kikaga ya samu bawa to muk’addari ne daga Ubangiji. Shekaran jiya da kika fara labour munje mun samu Mahaifin Mijin ki dashi kanshi Mijin naki wanda ya dawo daga tafiya, akan batun haihuwarki dan mun lura ma kamar bai ma san kina d’auke da ciki ba! Da muka je da farko mai gadi ne ya hanamu shiga Sai da muka lallab’ashi tukunna ya kira wani Yaro da kayan sojoji ya nuna mishi mu yace mu fad’a mishi me ke tafe da mu! Hakanan, muka bashi sak’on muka ce yaje yace ‘iyayen maryam ne suka zo tana asibiti zata haihu, ana buk’atar jini kuma ana buk’atar Abba a wajen saboda wasu y’an cike cike.’ Munfi awa biyu a wajen a tsaye, daga k’arshe ko harabar gidan ba’a barmu mun shiga ba Abba da Mahaifin shi suka fito. Ko gaisuwar kirki bai bari mun yi ba, a take kawai Abba ya mik’o mana wannan takardar yace ‘gashi dan Allah mu yi hak’uri, mu baki’. Mahaifinshi bai bari sun koma cikin gida ba sai da ya tabbatar Abban ya fad’a mana abunda yake cikin takardar da bakinshi tukunna suka juya suka barmu a wajen. Tsabar yadda jikin mu yayi sanyi munfi minti goma a tsaye a wajen tukunnan muka juya da nufin zuwa inda mukayi parking da niyyar tafiya amma bamu kai ga shiga motocinmu ba mutumin nan ya sa aka sakar mana mahaukatan karnukan estate d’in nasa wai saboda mun dad’e mun tsaya masa a bakin estate bamu tafi da wuri ba!!! Tsabar wulakanci!. Gudun ceton ran da muka hau yi ne ya sanya muka bar motocinmu a wajen sai da daddare tukunna Usman da Abokinshi suka je suka kwaso mana… Maryam Dan Allah ki ha’ura da Yaron nan, wannan itace kawai alfarmar da nake nema ki yi mini. Kalli nan gefen cinyata cizon kare ne! Maryam duk surukin da zai yi maka haka ba sirikin arzik’i baneba ba sirikin da za a so a ci gaba da rayuwa dashi da zuri’ar sa baneba… Ki kyale mishi d’ansa, dan Allah .” Ita dai Maryam, zuwa wanna lokacin ta daina ji ta daina gani tun daga lokacin da Allah ya bata ikon karanta takardar ‘saki d’ayan’ da Abba yayi mata .....….. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 20 Kamar yadda Baba Bashir ya rok’eta akan ‘ta rabu da Abba’ hakan take k’ok’arin yi. Dan ko da ace bai fad’a ba tabbas ba zata sake bi ta kan Abba ba, tayiwa kanta wannan alk’awarin! Ya ga soyayyar ta yanzu kuma zaiga fushinta In sha Allah ko shine autan maza ta hak’ura da shi. Abu d’aya ne wanda Maryam tayi domin Abba shine ‘sakawa y’arta suna Huda’ da tayi saboda shi, dan tun lokacin da take boarding school indai suna hira yakance “Idan Allah ya basa y’a mace zai saka mata suna ’Huda’ saboda yana matuk’ar son sunan, idan kuma Namiji ne zai saka mishi ‘Aslam’. Zai barta ta zab’i duk sunan da take so a duniyar nan amman lak’abin ya zama Huda ko Aslam.” Da matar Yayanshi ta haifa mai sunanshi shiyasa ta zab’i lak’abin ‘Aslam’ yanzu kuma ta sakama Yarinyarta suna Maryam ana kiranta da Huda ba dan komai ba sai dan kawai tasan ba a tab’a chanjawa tuwo suna….tanaso wannan ya zama last abu da zatayi mishi a matsayin sa na Mahaifin Hudan.. Bayaga haka! Duk wasu memories na Abba k’ok’ari kawai take yi ta goge su, ta samu ta ciresa gaba d’aya daga kanta har abada…. A lokacin data dawo Sadiya shiri take yi da ita sosai,musamman ma data lura da yadda y’ay’anta suke son Maryam d’in da Bilkisu, idan zata tafi yawonta haka nan zata kwaso su ta kawowa Maryam d’in suyita wasa suna d’ebe mata kewa….dama ita Maryam tana da son Yara sosai suma suna sonta, musamman ma Jalila wadda a lokacin da Maryam ta dawo shekararta 1 yanzu kuma tana shirin rufe biyu.. Har sati Jalila takanyi a wajen Maryam, sunanta ta fara kira a duniya kafin ma na Mahaifiyarta! Tun tana ce mata ‘miya’ har ta fara ce mata ‘mama miya’ daga baya ta koma ce mata ‘Mama’ kawai. Shak’uwa ce sosai ke a tsakaninsu, ana yayeta kuwa Maryam dukda a lokacin tsohon ciki gareta, haka Jalila ta dawo wajenta dan tak’i yarda da kowa sai Maryam d’in…… Yanzu kuwa da Sadiya taga auren Maryam ya mutu!! gashi ko idda babu a kanta, tun daga lokacin taje ta d’auke Jalila, su Junaidu suma ta hana su kula Maryam d’in sai dai suyi a b’oye. Tashi d’aya Jalila duk ta bi ta rame kullum cikin kuka take tana cewa “ita wajen Mama zata tafi amman furr!! Sadiya ta hana. Dan zuwa wannan lokacin ko gidan taje ba kula Maryam take yi ba sai dai idan ita Maryam d’in ce ta kulata tukunna za ta amsa da kyar shima kuma ciki ciki take amsata ba tare da ta kalli ko inda take ba! Idan kuwa iyaka su biyu ne a guri tofa in Maryam zatayi mata magana sau goma ba zata kulata ba! Duk akan Mijin da bata saniba shi tun lokacin da Maryam ta dawo yake ta addua Allah ya bashi ikon raba aurenta da Abba! Ranar kuwa da Abba ya saki Maryam a gaban shi suna gama gudun famfalak’in karnuka bayan sun dawo gida ya cewa su Madu idan ta fita idda shi har yanzu yana sonta! Ranar da ta haihu kuwa shi so yayi ma a d’aura musu aure a ranar! Sai da su Baaba Talatu suka yi masa da gaske! Tunkunna ya hak’ura. To yanzunma ya sake tada balli Hakan yasa kawai su Madu suka yanke shawarar d’aura musu aure amman Baba Bashir yace “zai fara tambayar Maryam d’in tukunna, tunda ita yanzu bazawara ce basu da hurumin zab’a mata Miji.” Shi dai Madu bai biye Baba Bashir d’in ba ya tashi ya fita yana mai ce masa “idan yayi fixing date ya fad’a masa zai bayar a sanar a masallaci!dan shi kam ya gama zab’awa Maryam Usman.” A b’angaren Maryam kuwa duk yadda ta kai ga k’in Ya Usman bata isa tace ‘a’a’ ba a gaban Mahaifin shi wanda yayi mata gata!….Bai duba yadda ta gudu ta sanya d’anshi a garariba haka ya rik’eta kamar komai bai faru ba! Shiyasa yana zuwa mata da maganar tashi d’aya ta amince nan take. A cikin sati d’aya aka gama komai aka d’aura auren Usman Bashir Da Maryam Muhammad Madu akan sadaki naira dubu ashirin lakadan ba ajalan ba. Murna a wajen Ya Usman a wannan rana abun har sai da ya bawa wasu mamaki!!! Sadiya kuwa daman b’oye musu auren akayi…. Ranar taje wajen Baba Laraba suna hira kawai taji ana d’aura aure a masallaci, tun a lokaci ta fara hauka kamar tab’abb’iya! Tana cewa “Maryam taci amanarta, dan haka wallahi sai ta koya mata hankali!.” Tun lokacin take hauka kwata kwata ya ma k’i ta saurari kowa, babu yadda Baaba Laraba bata yi akan ta tsaya ta nutsu ba amman tak’i! Ko y’ar kissar nan ma ta mata ita kam ta kasa kwatantawa. Tsautasayi ya kaita bayan an kai Maryam ta shiga har d’aki kafin Ya Yaman ya shigo, wai sai ta yi mata duka!! Ita kuwa Maryam ta tare ta! Dambe suka fara gadan gadan dai dai Ya Usman yana turo k’ofa ita kuma Sadiya tayi sa’ar kifawa Maryam mari a kan idanunsa! A zuciye ya k’araso, sai da yayi mata Mari kwarara guda uku!! sannan ya k’ara mata da saki biyu daman ya tab’a yi mata d’aya!. Hankali a tashe! Sadiya ta fara bashi hak’uri, ita kanta Maryam d’in ta tsorata dan bata yi tunanin wannan hukuncin a Sadiya daga wajen Ya Usman ba duba da Yaran dake a tsakaninsu. Ganin da Sadiya tayi ba zai saurareta ba yasa ta mik’e ta zari mayafi ta nufi wajen su Madu… Duk inda aka bi aka duba babu aure a tsakaninsu! Idan ma zata koma to sai tayi wani auren, kuma da sharad’in ba na kisan wuta ba. Tana gama idda wani gurgu ya fito mata. A nan bayan layin su Amaryar sa take amman shi yana Sumaila da Matan sa biyu. Bata wani damuba ta amince bayan ta fito k’iri k’iri ta gaya mishi auren kisan wuta take so suyi shi kuma ya amince. A lokacin nuna mata yayi ya amince aka yi shirin komai, ranar da aka d’aura aure iyayenshi suka zo suka tafi da ita sumaila, bayan da farko ce mata yayi a kano zata xauna dan kayan d’akinta ma d’akin daya nuna gefen na Amaryarshi a nan aka jera mata. Haka nan ta tafi Sumaila ta bar kowa nata daga ita sai Jalila suka tafi. Bayan sati biyu ya zo da kansa ya kwashe kayan jeren ta aka kai mata Sumaila aka jera wasu, dan kusan rabin kayan karshe sai siyarwa tayi saboda ba zasu shiga d’akin ba. Sadiya bata tashi sanin Garbati yaudararta yayi ba sai ranar daya fito mata a mutum yace mata “shi fa ba zai saketa ba!” Jalila ma data taho da ita cewa yayi “ba zai rikeba” haka nan tanaji tana gani aka karb’e Jalila aka dawo da ita gidan Babanta wajen Maryam bayan shi ga nasa y’ay’an guda goma sha takwas kuma duk ranar girkinta sai ta girka musu abinci ta basu… Sadiya taci kuka ranar da aka karb’e Jalila kamar ranta zai fita! Ita kuwa Jalila murna ma ta dinga yi ta dawo wajen Maman ta. Maryam duk wani kulawa haka ta had’a Yaran nan guda hud’u take basu kamar ita ta haifesu duka….Jalila ta taso da k’aunar Huda a ranta dan babu wadda takeso kamar Huda! Abu kad’an ‘k’anwata’ komai ita dai k’anwarta, ko abu taci a makaranta sai ta rago ta kawowa k’anwarta. Lokacin da aka saka Huda a makaranta kuwa taga gata wajen Jalila da Junaidu wanda tun a lokacin Junaidun yake cewa “shi kam inama ana auran k’anwa to da zai auri k’anwarsu Huda” Gata kala kala ba wanda baya nuna mata, ita ma Jalila yadda take ji da Huda kamar tsoka d’aya a miya! In ka tab’a Huda to ko d’an gidan uban waye kai sai taje har d’akin uwarka da jibgeka…dan one thing about Jalila bata da kunya kuma bata da tsoro ko kad’an! Dan ma Mama tana taka mata burki. Ya Jaafar ne kawai baya shiga harkar Hudan sosai, saboda shi daman chan akwai shi da son girma kuma miskiline na ajin k’arshe. Shekarunsa suna d’an yin sama ya daina yi musu dariya ma kwata kwata, ko hira akeyi haka nan shi sai dai ya shige d’aki. Shiru shirun sa ya fara damun Mama dan haka ta saka mishi ido, ai kuwa nan ta gano ashe yawan baccin da yake yi shaye shaye yake yi tuk’uru. Hankalin Mama ba k’aramin tashi yayi ba dan a lokacin kwata kwata shekarun Jaafar 15 kuma koma ba dan ta shekarun ba shaye shaye ba abu bane mai kyau. Shiyasa ta dage ta tsaya tsayin daka da addua da komai da kyar aka samu ya shiryu ya daina. Tsakanin Maryam da Ya Usman kuwa! Soyayyar sati uku kawai ya nuna mata bayan aure daganan ya birkice ta kasa gane kansa… Haka kurum sai ya tisa ta a gaba wai sai ta fad’a mishi wa tafi so tsakanin shi da Abba! Wasu lokutan a rana d’aya sai ya buka’ceta sau hud’u idan ya ga dama ko sama da haka a cewarsa ‘sai yayi wanda yafi na Abba yawa!’ Gaba d’aya waensu irin abubuwa yake yi marasa ma‘ana wanda sam ta kasa gane kanshi kwata kwata. Tabbas Ya Usman yana sonta ta yarda da hakan amma wasu lokutan har hanata abinci yake yi wai yana so ta ji yadda yaji a lokacin data gudu ta barshi dan a wannan lokacin har kwana hud’u ya sha yi bai ci abinci ba….. Hanyar gidansu Abba kuwa ko waye ata arean bata isa ta bi ta je ba, ko dubiya ne ko kasuwa taje in dai yaji labarin sun wuce ta hanyar gidansu Abba to sai tayi sati tana shan azaba a hannunsa. Babu abinda ya fi sosa mata rai kamar yadda Ya Usman yake nunuwa k’iri k’iri kaff a fad’in duniyar nan babu wadda ya tsana sama da Huda! Haka kurum sai yayi ta kyarar ta yana hantarar ta, wani lokacin har duka! Tun Hudan bata gane ba har ta gane, dan sai da ya zamana ko muryarshi ne idan taji da gudu haka zata shige d’aki…. Hakan ya sanya hatta Jalila da Junaidu da suka fahimta suma sai daina kula shi,har sai da Maman ta gane ta bud’e musu ido tace “basu isa gaba da Mahaifinsu ba”, tukunnan ba yadda suka iya suka sak’k’o amma idan yana yiwa Huda abu wani lokacin har kuka suke yi. Lamarin Ya Usman ya kai idan gida akwai mai suna Abba to zai hana Maryam mu’amala da y’an gidan kwata kwata! A cewarsa wai ‘da gangan take zuwa gidan saboda idan an kira sunan Abba ta dinga tuna Abba…’ Abubuwa kala kala dai…tun abin yana damunta har ta hak’ura ta rungumi y’ay’anta ta yaye lamarin shi a kanta. A b’angaren Sadiya kuwa sai da tayi shekara 9 tana shan azaba a hannun Garbati, k’arshe ma rufe mata baki yayi ita da iyayenta suka daina neman saki a wajenshi, Allah ma ya taimaki Sadiyan bata yarda ta haihu a gidanshi ba saboda dama tace ‘bata ga guri ba!’. Su Jalila sukan je su dubata su kai mata kayan abinci da zannuwa, da farko da Maryam suka fara zuwa amman tun zuwan farko da ta saka Yara suka yi mata ihu shikenan Ya Usman da yaji labari ya hanata zuwa kwata kwata. Sai da zama ya Kare tukunna Allah ya karb’i ran Garbati a hanyar shi ta zuwa Niger (minna) ganin Mahaifiyarsa…. Yaranshi ne kad’ai suka yi kukan rashinsa amman matan sa da y’an unguwa har ga Allah murna suka yi domin kuwa kai tsaye zaka kira Garbati da mai mugun hali gashi duk wani hali na mugunta ya sani ya kware a kai. Tana gama idda ta fara yiwa Usman zirya.. Haka kurum za taci kwalliya ta ta zo gidan wai ta zo ganin y’ay’anta! Shi dai Usman ba ma ya bi ta kanta dan yace ‘daman a rashin Maryam ne ya hak’ura ya zauna da ita!’. Idan tazo gidan ta dinga habaice habaice kenan, ko Jalila ba kulata take yi ba sai Maryam tayi da gaske tukunna suke gaisheta, Jafar ne kawai yake biye mata. Ana cikin haka aka yiwa Mijin Zainab transfer shima ya dawo Kano, lokacin Yaranta uku mata biyu Aisha (momy) da khadija sai auta muhammad, itama dayake malamar makaranta ce sai ta nemi transfer aka kaita makarantar mata ta nan gandu take koyarwa. Ai kuwa tun daga nan duniya ta yiwa Mama zafi, domin kuwa k’awancen Zainab da Sadiya sake k’ulluwa yayi dayake itama Zainab d’in nan kusa Mijinta ya kama haya ba nisa, dan haka kusan kullum suna tare. Haka nan za suzo gidan suyi ta neman ta da fad’a! Ita dau ba kulasu take yi ba. Bilkisu a lokacin Yaranta biyu Itama ta kammala karatunta na law tana aikin ta! Kowa dai da y’ar sana’ar shi ko wani means of samun kud’i dan hatta Sadiya business d’in kaya take yi, amma ita Maryam a duk lokacin da tace tana son yin karatu ko sana’a tashi d’aya Ya Usman zai ce “a’a!! Salon tayi kud’i ta gujesa!.” Ranar da abun ya isheta daman ko kayan sallah baya yi musu ita da Huda idan ka gansu kullum cikin tsumma, Baba Bashir da Baba Talatu ne suke dan k’ok’artawa suyi musu sai ko Bilkisu, hakan yasa ta d’auki waya ta kira Baba Talatu tana kuka tana gaya mata. Ashe Shuwa na gefen ta a lokacin suna tare Baba Talatu batayi auni ba taji Shuwa ta karb’e wayar! Maryam zata iya cewa ta manta rabon da taji muryar Shuwa amma maimakon magana mai dad’i sai kawai Shuwan ta rufeta da fad’a ko gaisuwarta bata tsaya amsawaba, tace hau fad’a tana cewa “Ai ta riga tabar gini tun ran zane! Lokacin da su Zainab da Bilkisu suka yi nasu karatun a lokacin daya dace ai ita saurayi tabi, sai yanzu god’ai god’ai da itane zata wani ce tanaso zata koma makaranta??!. Kawai ta zauna idan Usman d’in yaga dama yaayi mata to, idan kuma bai yi mata ba ta hak’ura, sannan tama daina k’ok’arin had’a kanta ‘jahila! mara aikin yi! Da su Bilkisu masu ilimi masu aikin yi dan indai tace haka zata yi to kuwa wahala zata sha!.”… Tana gama fad’in haka ta kashe wayar. Haka rayuwa taci gaba su Shuwa ko k’ofar gidansu har yau har gobe sun hana Maryam zuwa ballantana Huda, ko Bilkisu ta je gani idan emergency ya taso sai dai su had’u a waje ko a gidan Baba Bashir.. Sunce ‘ai tun ranar data saka k’afa tabi Abba suka cireta a matsayin y’arsu, su bama su da ita ba.….. Ana haka rana d’aya kawai Usman Ya mayar da Sadiya aka d’aura aure. Da farko su Baba Bashir sun so hanawa amman yadda ya nuna kamar idan bai auri Sadiya a ranar ba to tabbas zai iya mutuwa! Ne ya sanya kawai aka d’aura musu aure ta tare… Tun daga wannan lokacin kuma Ya Usman d’in sai ya zamana kamar irin tsoron Sadiyar ma yake yi ,baya son ganin b’acin ranta baya iya hanata abu. Tana dawowa gidan ta janye y’ay’anta duk wahalar su da Maryam taci ba ayi shekara uku ba gaba d’aya hankali Jalila ya koma kan Mahaifiyarta, tun bata kulata har ta fara kulata daga baya data gane uwar ta kuma sai ta fara yiwa Maryam rashin kunya da rashin mutunci kala kala tun bama data lura da Maryam d’in bata so a tab’a Huda ba, nan ta samu abunyi… Saboda ita aka cire Huda daga makarantar islamiyyar da suke yi aka chanjamata boko kuwa sai da suka san yadda suka yi k’iri k’iri aka hanata zuwa.. Junaidu tun yana dukan Jalila har Sadiya ta bud’e mishi ido ya daina. Haka kurum sai su rufe Huda da duka babu laifin tsaye babu na zaune.. Maryam bata samun sauk’i a kaf fad’in duniyar nan sai in tana karatun Alqurani ko kuma idan Bilkisu da Yaranta sun zo Sakina itace Babba watanni uku Hudan ta bata amman irin Yaran nanne masu garin jiki shiyasa ta zama kamar ma ta girmi Hudan, sai k’anwarta Sumayya. Sakina irin Yaran nan ne da basa barin takwana, takan zo wasu lokutan tayi weekend a gidan itama Hudan takan je musu, ammanfa duk ranar da Sakina tazo sai an kwashi y’an kallo ita da Jalila duk da kuwa Jalilan mugun duka take yi mata amman takanci nasara itama akanta itama wasu lokutan. Akwai ranar da suka yi wani dambe! Jalila tayi mata duka ita kuma da taji zafi ta rarumi dutse ta bugawa Jalilan a kai wanda har saida ya kaita ga suma. Ya Usman da Sadiya kuwa suka d’aukowa Sakina y’an sanda, su kuma y’an sanda da son banza suka zo zasu tafi da ita. Suna shirin sakata a mota kenan daman Babansu ya taho d’aukarsu kuma Mama ta kirasa dan haka ya k’araso a rikice. Ya ji haushin abun sosai dan haka fad’an ya koma na manya akai baram baram da shi da Ya Usman. Tun daga nan suka hana Yaran su zuwa gidajensu. Shiyasa ko lokacin da Bilkisu tace zata d’auki Huda Shuwa ta hanata a cewarta ba zata bari matsalar Maryam ta shafi aurenta ba................. ……………………………… Mama bataji shigowar Sakina da Ummu ba, dafa ta d’in da Ummu tayi ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin data lulaaa.. A hankali ta juyo gareta tana kallonta fuskarta sharkaf da hawaye. Numfashi Ummu ta fesar kafin ta tsugunna a gabanta sannan ta shiga share mata hawayen har sai da taga tayi shiru tana sauk’e ajiyar zuciya… Motsa hannun da Huda tayi ne ya katsewa Ummu maganar da take shirin farawa. ..A hankali take bud’e idanuwanta da suka chanza kala suka k’ank’ance. Tana gama bud’ewa hawaye suka shiga zubo mata. Rad’ad’i take ji har yanzu a wajen da Ya Ja’afar ya daketa da katako ga ciwon kan da take ji kamar zata mutu!. Sakina ce ta hau kan gadon ta zauna ta wajen kanta kafin ta kamo hannunta ta kuma shiga share mata hawaye tana cewa “ta yi hak’uri tayi shiru karta k’arawa kanta ciwon.” Da kyar dai itama Hudan tayi shiru. Bayan Likita ta shigone ta chanja mata d’aurin ruwa sannan tayi mata wasu allurai tace “ba zai yiu a sallamesu yau ba sai dai gobe” Kasancewar dare yayi sosai hakan ya sanya Mama ta lallab’a su Ummu suka wuce gida. Ya junaidu kam sai da ya tabbatar sun kintsa ya nemo musu duk abun buk’ata tukunna ya wuce shima. Washegari da sassafe su Ummu suka zo musu da breakfast, bayan sun biya gidan Hajiya sun ajjiye Sumayya dan itama jikin nata sai a hankali. Kamar jiya yau ma har dare Ummu tana wajensu, saboda zazzab’in da ya sake lullub’e Hudan ya sanya Likitocin suka fasa sallamarsu aka kuma k’ara mata allurai masu nauyi da magunguna ta wuni tana barci. Sakina Ummu ta sake aikawa taje gida tayo musu girki ta dawo. Suna zaune wajajen 8 daman kamar Mama ta sani tana ta cewa Ummu ta tashi su tafi sa dawo gobe amman tak’i! Kawai sai ga kiran Hajiya Shuwa, Ummu na d’auka ko gaisuwarta bata amsaba ta hau zazzaga mata bala’i tana cewa “taya zata tafi ta bar mara lafiya haka!? Tabi duk ta wani d’aga hankalinta akan wata Huda, koma meye ya sameta ai sune suka jawa kansu! Tayi maza ta dawo yanzun nan idan ba hakaba ranta sai ya b’aci!”. Sarai Mama taji abinda Hajiya tace saboda wayar Ummu irin mai volume d’in nan ce amman sai ta nuna kamar bata ji ba. Ummu kam jikinta duk yayi sanyi ko tambayar jikin Huda Hajiya bata tsaya yiba tace a taho a barsu su suka sani. Haka nan dai jiki duk ba kwari, ta d’auki jakarta bayan ta tabbatar ta biya komai kuma tabar musu isheshshen kud’i a hannu da alk’awarin gobe da sassafe za su dawo In sha Allah. Suna shirin fita Junaidu kuma yana shirin shigowa da ledoji a hannunshi. Gaisawa suka yi da Ummu sannan yayi mata sai da safe ya shigo. A gefen gadon wajen k’afafunta ya nemi waje ya zauna bayan ya gaida Mama. A hankali yake kallonta yana jin wani zafi a ranshi kafin yace mata “ya jikin?”. Sai da ta gaisheshi bata damu da rashin amsawar shi ba tace masa “da sauk’i” Shiru d’akin yayi babu mai cewa komai kafin a hankali Hudan tace “Mama zan yi sallah.” “To” Maman tace sannan ta mik’e ta fara k’ok’arin d’aga Hudan wadda azaba tasa ta fara yin wani kuka mara sauti abin tausayi. Runtse ido Junaidu yayi kafin yace “Mama idan ba zata iya ba gara kawai a nemo kwano da ruwa, tayi alwala anan tunda daman yanzu jikin nata zai yi tsami sosai.” Hakan kuwan akayi da kyar ta iya zama sannan ta samu tayi alwala tayi sallar. Bayan ta idar ne ya janyo ledojin da ya shigo dasu ya fara bubbud’ewa…. D’ayan fresh milk ne da su maltina, sau d’ayan kuma gasassun kaji ne mai yawa, da zafin su sai maik’o da kamshi suke yi. Mik’ewa yayi ya d’auko plate da cup, kazan ya fara zuba mata kamar rabi, har ya d’auko fresh milk zai zuba mata sai kuma ya d’ago manyan idanuwanshi ya kalleta yace “Me zaki sha??” Cike da jin kunya, dan ya kamata tana kallon kazar daya zuba mata ta nuna mishi Maltina. Murmushi yayi sannan ya ajjiye fresh milk d’in ya d’auki Maltina ya zuba mata kafin ya sake mik’ewa ya dawo kusa da ita ya ajjiye plate d’in akan cinyarta, cup d’in kuma a kan drawer gefen gadon, shi kuma ya tsaya a kanta kafin yace “Bismillah” Har ga Allah so yake yad’an zauna kusa da ita amman kuma yana jin kunyar Mama. Da kyar ta iya cin rabi, daga nan tace masa “ta k’oshi” dan ji tayi cikinta har ya cika taf! Amma da farko lokacin da yana zubawa kamar tace masa ya juye duka. Gyara tsayuwar shi yayi sannan yace “ko ta cinye ko ya d’ura mata!” Ba yadda ta iya haka ta dinga turawa saida yaga tana k’ok’arin yin amai tukunna ya kyaleta. Gaba d’aya Mama itama a takure take, kayana kunya da nauyi duk ya kanainaiyeta. Har ga Allah idan aka tsareta ba zata iya nuna makusa guda d’aya a tare da Junaidu ba. Yaron yana da hankali, gashi yayi karatun shi yanzu haka ma masters yake yi, part time. Yana kuma sana’a dan yana da zuciyar nema, sanna ta san yana son Hudan tsakaninsa da Allah,sosai. To amman matsalar d’aya itace iyayen shi, da ace Junaidu ba d’an Sadiya da Usman baneba da ita da kanta zata tsaya tsayin daka ya auri Huda. Tsakanin d’aa da uwa sai Allah dan ta d’auki lesson akan Jalila, duk runtsi wata rana dole yabi maganar Mahaifiyar shi kuma itama Hudan dole ta yiwa Sadiya biyayya tunda uwar Mijinta ce……ta san Huda ba k’aramin wahala zata sha a hannun Sadiyar ba… Ita kuwa tana ganin wahalar da Huda ta sha daga yarintarta kawo yanzu yaci ace ta samu kwanciyar hankali a gidan aurenta! Apart from all this ma, ta san Sadiya da Usman ba zasu tab’a yadda da auren ba sai dai wani tsananin rabo.. Sallamar Baba Bashir da Baaba Talatu ce ta katse mata tunaninta..ta yi saurin d’agowa tana kallon k’ofa......... BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 21 Murmushi Mama tayi kafin ta mik’e ta shiga yi musu ‘sannu da zuwa’. Baba Bashir ta jawa kujera ya zauna, Baaba Talatu da d’an gidan Ya Jamilu mai sunan Madu su kuma ta shimfid’a musu darduma. Bayan sun gaggaisa ne Kaka (Baba Bashir) ya ke tambayar Mama “mai ya faru?,d’azu Bilkisu ta kira take ce musu Hudan na asibiti.” Shiru Maama tayi dan ita harga Allah bata san ta ina zata fara ba, gashi tanajin kunyar su. Junaidu ne yayi gyaran murya, ya hau zayyano musu duk abunda ya faru. Ai kuwa nan Kaka ya hau fad’a! Ta inda yake shiga bata nan yake fita ba A take ya sa aka kira mishi Baba yace masa “yazo yanzun nan yana son ganinshi a asibitin da aka kwantar da Huda.” Bayan kamar minti biyu Baba ya kira Junaidu ya tambayeshi “ko ya san sunan asibitin?” nan ya fad’a mishi harda number d’akin. Suna zaune Baaba Talatu itama tanata bawa Mama baki Baba ya turo k’ofa da sallama a bakinsa ya shigo. Tun kafin ya zauna Kaka yace “Wato Usman ban isa da kai ba ko? Wato na hana su Sadiya zaluntar Yarinyar nan shine ka b’ullo ta hannun Ja’afar ko!? Tayaya ma zaka bari shi da ba ishashshiyar nutsuwa garesa ba ya bugi Yarinya haka?! Haba Usman, katako fa mai k’usoshi a jiki ya maka mata, a ciki!!!. Yaro gaba daya duk ya bi ya haukace? Yo hauka mana, idan ba hauka ba wa zai yi wannan ta’asar saboda Allah? Sannan ku kuma kai da uwar sa sam baku son kuji laifinshi. Lokacin da yake hannun Maryam ai tun farkon fara lalacewar shi sai da ta nutsar da shi amma tun dawowar Sadiya gaba d’aya ya sake tab’arb’arewa! Daga ya saci akuya sai ya saci kaza! Shekaran jiya sai da aka kawo mana k’arar sa akan ya saci zakara!. Kuma abun haushi naira ashirin ko talatin yake saidawa k’arshen tsadar d’ari ko d’ari da hamsin. Mai unguwa da kanshi yace mini ‘dan kawai ya ga jikanmu ne shiyasa yake d’aga mishi k’afa. Usman kai ka san a irin unguwar da muke Abu kad’an suke jira a fara gustiri tsoma! Dan haka tunda kun kasa tsawatar masa ni zan dauk’i mataki! Tun kafin yaje ya janyo mana maganar da tafi wannan in dai baku tashi tsaye a kanshi ya shiryu ba to wallahi kaji na rantse ‘Ni da kaina nan zan kaishi gidan mahaukata!!’.” Da sauri Baba ya d’ago ya kalleshi.. “Kwarai kuwa!” Shine abinda Kaka ya fad’a kafin Baaba Talatu itama ta d’aura da cewa “Yo ai Usman dole a kai sa gidan mahaukata, domin kuwa kwata kwata Jaafar baya yin abun masu hankali, kuma gashi kun barshi a gida yana shirin yin kisan kai!! Idan k’ungiyar masu kare lafiyar d’an Adam taji maganar nan Ina mai tabbatar maka da ‘su zasu fara kaishi kafin mu mu kaishi’! Shekaran jiya fa da Jamilu da iyalinshi suka zo… ga Abba k’arami anan ka tambayeshi kaji ‘a bakin kwata suka sami Jaafar ya tsugunna yana ta shak’a!’ Babbar kwatar layi mai uban d’oyi. Yau Huda ya yiwa zamu iya rufa asiri, gobe ka san wa zai yiwa?? Gaskiya ce muke gaya maka tun wuri kusan abunyi kai da uwarsa da bakwasan jin laifin shi….” Shiru d’akin ya d’auka, a hankali Kaka ya mik’e ya isa inda Hudan take…..shafa kanta yayi yai mata sannu sannan ya cewa Abba k’arami ”su taso su tafi.” Baba talatu ce itama ta mik’e tana mai cewa “Yanzu inda ace Jaafar mai hankali ne ai da tuni shima ya tara iyali Kalli Abba shekara d’aya aka haifesu amma shi y’ay’ansa biyu…. Idan kuka bari so ya rufe muku ido zaku yi dana sani a gaba, dan gaba d’aya rayuwarshi kuke neman lalatawa ba tare da kun sani ba.” Tana gama fad’in haka itama ta yiwa Mama sai da safe sannan tayi hanyar fita tana cewa “ita kuma Hudan idan ta warke ki turo min ita inji waye wannan Yaron da suka ce ya sakota a napep d’in.” “To in sha Allah” Shine abinda Maama tace tana mai sake yi mata “sai da safe” Har zata fita sai kuma ta juyo tace mata “Sadiyar sun zo??” Shiruuu Mama tayi nanma ta kasa magana. Girgiza kai kawai Baaba Talatun tayi tace “Hmmm” Daga haka ta sa kai ta fita. Jikin Mama har rawa yake yi, dan a tunanin ta Baba zai sauk’e mata buhun masifa ne amman sai taga kawai ya juya shima yabi bayansu ya fita. Junaidu ne yace “Ai da idan ina magana akan Ya Ja’afar gani suke yi abin kamar wasa ne.. Gashi yanzu daga anyi zancen ‘gidan mahaukata’ hankalinsa duk ya tashi! Tun ba a je ko’ina ba.” “Allah ya kyauta” shine abinda Mama tace sannan suka d’an shiga tab’a hira ita da Junaidun dan already Hudan tayi bacci. Sai wajen 10:30 tukunna da kyar Mama ta lallab’a shi ya tafi dan daa cewa yayi “a wajen zai kwana” Ita Mama da farko ma dariya ya bata sai da taga dagaske yake tukunna ta nuna mishi ba zai yiu ba…. Washegari da safe wajen k’arfe sha d’aya aka sallameta bayan su Ummu sunzo da Sakina harda Sumayya wadda ta ji sauk’i. Ya Junaidu shima ya zo tare suka zo da matar Ya Jamilu da safe, su suka kawo musu abun kari, bata dad’e ba tace “ya mayar da ita saboda su fara shiri anjima zasu koma.” Ya tafi maidata dake motar mijinta sukai using, bai kai ga dawowa ba aka sallamesu. A motar Mijin Ummu aka mayar da Huda gida, bayan sun siya mata duk magungunanta. Suna zuwa a bakin k’ofa suka tarar da Jalila tana zance da malamin maths d’insu, ko kallonsu bata yi ba haka ma ta nuna kamar bata san dasu a wajenba..da Ummu da Mama ne suka kamo Hudan tana tafiya da kyar, sai da suka zo daff da su kawai Jalilan da doka tsaki ta tofar da yawu a daidai inda zasu taka su wuce su shiga cikin gidan! Sakina ce ta yunk’ura zata tanka mata amman Ummu ta daka mata tsawa tace “ta wuce tayi ciki!” Ba yadda ta iya dolenta tayi shiru, kamar zata fashe ta shige ciki tana gunguni… Haka nan suka wuce ciki ko bi ta kan Jalilan basu yi ba. Tun safe su Ummu basu tafi ba sai daff da Magriba..haka wuni sunata hira ana wasa da dariya a tsakaninsu, d’an uwa mai dad’i! Gaba d’aya sai Mama da Huda suka nemi damuwar su suka rasa…… Haka rayuwa taci gaba da tafiya…. Har Hudan ta warke a tsakanin Sadiya ko Jalila ba wadda tace mata ci kanki! Gidan kuwa haka nan ya koma kacha kacha dan Jalila ba gyarawa take yiba tace waec take yi itama bata da lokaci. Ranar asabar da yamma Hudan ta dawo daga islamiyya kenan, Yaro yayi sallama yace “wai ana son ganin Hudan a waje” Da k’arfi Jalila wadda take m cin abinci ta kware, sai da tayi kusan minti d’aya tana tari idanunta harda hawaye da kyar ta dawo dai dai. Maganar da Yaron ya sake yi ne ya sanya Mama fitiwa tacewa Yaron “kaje kace inji wa?” Fita yayi cikin k’ank’anin lokaci ya dawo yace “Yace wai ace mata Arshaad ne” “To” kawai Mama tace sannan ta koma ciki ta shiga tambayar Huda wadda take chanja uniform d’inta “Waye Arshaad?” Shiruuu! Hudan tayi kamar tana so ta tuna wani abun chan ta d’ago ta cewa Maama “wannan mutumin da ya bani handkerchief d’inshi ne, ranar da su Ya Jalila suka aikeni siyo zob’o.” Ajiyar xuciya Mama ta sauk’e sannan tace “ki maida mishi handkerchief d’insa sannan kice mishi baki fara zance ba!” Zaro ido Huda tayi tace “Mama bafa zance muka yi ba ranar ba ma, kuma yau ma ba zance yazo ba, ba saurayina bane ba.” Kallonta Maman tayi sannan tace “kije ki gaya mishi haka ki dawo da wuri!.” Tana gama fad’in hakan ta juya ta fita zuwa kitchen ba tare data tsaya sauraron amsar da Hudan taketa nanatawa ba akan “itafa ba zance aka zo wajenta ba.” Yaron ne ya sake dawowa da same sak’o! Hakan yasa Hudan ta zira hijabinta ta fito. A soro ta hango Jalila, ta kasa tsaye ta kasa zaune, da alama lek’en sa take yi amman tana ganin Hudan sai ta baasar kawai tayi cikin gida. Arshaad, yana cikin mota a zaune, Abokinshi wanda ya rakosa yanata tsokanarshi, yana cewa “Yanzu Dude!! Saboda Allah a nan kayo matar da kabi ka isheni da ‘kayi mata’ take? may be ma ba right kwatance bane gaskiya, tunda kaga fa har yanzu bata fitoba! Kaga kawai mu juya, kai kanka kace Yarinya ce, maybe ma ba zance take yi ba! Kar ka sa yayanta ya biyo mu da sanda.” Murmushi Arshaad yayi sannan ya juyo ya kalli Jamil wanda shima shi d’in yake kallo! Nuna kanshi yayi da yatsa sannan yace “Ni, In juya?? Hmm tab!! Ai ba wannan zancen! Ka shirya kwana a nan dan yau za aga naci!!.” Dariya Jamil ya kwashe dashi kafin yace “So makaho! Yau ga wanda y’ay’an senators da governors suke hauka akai ya mato akan y’ar gidan Malan shehu!.” Duka Arshaad ya kai mishi sannan yace “Bana son rainin wayo…you beta learn on how to talk about my in-laws dude! And you b……” maganar tasa ce ta sark’e sakamokon hango Hudan da yayi ta fito tana d’an duddubawa da alamun neman wanda aka ce yana neman nata take yi. Motar ta kalla sannan ta d’auke kai tana kallon d’ayan gefen dan ba da motar da suka had’u da shi waccchar ranar yazo ba. Sai da ya duba fuskarsa a mirror d’in gaban motar tukunna ya sa hannu zai bud’e marfin motar ya fita yaji Jamil ya rik’e mishi hannu. Cikin dariyar mugunta Jamil d’in yace “haba Man! Ka d’an ja aji mana..” Fisge hannunshi Arshaad yayi sannan yace “na bar maka ajin yau, ka had’a da naka idan kaje wajen taka sai kayi.” Daga haka ya murd’a hannun murfin motar ya fita. Fitarsa tayi dai dai da sake juyowar Huda, aikuwa suka had’a ido. Tana ganinsa ta gane shi…. Yana sanye da blue jeans mai kyau da wata bak’ar riga mai k’aramin hannu data d’an kama jikinsa, ga wani takalmi sau ciki kamar canvas da bak’in agogo a hannunshi Yayi kyau sosai.! “Me kuma ya kawo shi? oho!” Shine abunda ta fad’a a ranta sannan ta ci gaba da tunanin “Lalle, da ace Mama taga wannan da ba zata ce zance ya zo wajena ba! Wannan ko a mai aiki ba lalle ya yarda ya d’auke niba.” Tunawa tayi da handkerchief d’inshi mai kyau, da Mama tace ta kawo mishi abinshi, wata k’ilan shi ya biyo dan haka ta fara tunanin kalar hak’urin da zata bashi dan ita bata san inda yake ba…… Sallamar da yayi mata ce ta katse mata zancen zucin da take yi. A hankali ta sannan tace masa “ina wuni” tana mai shak’ar wani nutsatsen k’amshin turare da yake tashi daga jikinshi. Murmushi yayi kafin yace “Lafiya Huda, ya gida?” A hankali ta sake cewa “lafiya” dan ji take kamar k’amshin turarensh za sanyata bacci. Ganin tayi shiru yasa yace “Tun last two weeks naso zuwa, amman sai nayi tafiya. Jiya na dawo inata Allah Allah in zo, but sai naga kamar I’m not welcome..” Kamar an fisgi maganar a bakinta tace “Kayi hak’uri ya b’ata ne”. Da mamaki yake kallonta kafin yace “Me??” “Handkerchief” ta bashi amsa. Dariya ma ta bashi….tabbas ya san ya bata handkercheif amman shi yama manta dashi, dan haka kanshi tsaye yace “bashi na biyo ba ai, wajenki na zo.” Still yanzun ma kamar an fizgi maganar a bakinta, tace”Mama tace ince maka bana zance” Sai kuma taji kamar ta nutse a k’asa, taya zata ce mishi haka? bayan ta tabbatar ba wannan ne ma ya kawo sa wajenta ba. Jin shiru yasa ta d’ago kanta cike da jin kunya. Tana d’agowa kuwa suka had’a ido dan shima itan yake kallo yana murmushi…. kafin ya sauk’e ajiyar zuciya yace “To sai yaushe zaki fara zancen??” “Nima ban san lokacin ba” Ta bashi amsa. “To yanzu ya za ayi kenan?” Ya sake tambayarta. Shiruuu, tayi dan ta rasa bakin magana yanzu kam. A hankali yace “ko sai kin tambayi Mama?” Da sauri ta d’aga kai alamar ‘eh’. Murmushi yayi yace “Yaushe zan dawo to inji me tace??” Da sauri tace “a’a bara in shiga In tambayo ta.” This time around sai da yayi dariya kafin yace “No, ki bari jibi zan dawo sai inji me tace, ko?” “To”kawai tace. Ganin yak’i tafiya yasa tace mishi “sai anjima”. Murmushi yayi kafin yace mata “bye” sannan ya fara tafiya da baya yana waving d’inta, har ya kusan motarsa tukunna ya juya ya isa ya bud’e ya shiga. Ita ma ta juya tayi cikin gida… A soro suka kuma cin karo da Jalila, ita dai Huda bata ce mata k’ala ba tayi wucewarta. D’aki ta wuce direct dan bata hango Mama a kitchen ba. Tana zuwa ta fad’a mata yadda suka yi dashi.. Sai da Mama ta d’anyi jim!! Tunkunna tace mata “ta tashi taje da d’aura ruwan miya” dan already Maman ta tuk’a tuwon tun kafin ta dawo a makaranta. Tana fita Mama ta janyo waya ta hau kiran Ummu….. Bayan sun gaisa ne, Cikin d’an rage murya dan taji kamar akwai mutum a k’ofar d’akinta! Ta fad’a mata halin da ake ciki sannan ta k’ara da cewa “Na san cewa Hudan tayi Yarinta yanzu, amma akwai abubuwan da na hango nakeso in taka musu burki tun kafin su zo su fi k’arfin mu. Kinga na farko.. Furucin Baba da yayi na ‘zai aura mata mallan iro mai kayan miya’ nake jin tsoro. Ga su Sadiya su kuma kinga kar su k’ulla mata wani sharrin da zai sanya hatta su Kaka suma su zuciya su bada goyon baya a aura mata mallan iro. Mutumin nan matanshi uku kin sani, kullum ana bala’i a gidan sa ga asirce asirce a tsakaninsu, sannan uwar gidanshi kin san k’awar su Laraba da dillaliya ce, abun ba zai zo da dadi ba! Ni ba wai arzik’in shi na raina ba wannan shine dalilina. Sannan yayi mata girma har ga Allah. Na san su Kaka ba lalle su yarda su bata malan iro ba amman fa munafuki ko d’akin mahaifiyarka ya riga ka shiga to sai ya had’a ku, su Sadiya sunga ta d’an fara tasawa kinga ai har sun fara k’ulla mata sharri, Allah kad’ai ya san me zasu ce a gaba, Ina tsoro kar a b’ata mata suna a zo hatta su Kaka su daina goyon bayanmu! Mai gata ma idan sunan shi ya b’aci ya yake k’arewa? ballantana ita da Mahaifin nata ma cewa yayi kar a fad’a mata ko da sunan shi ne. Abu na biyu kuma shine Junaidu! inaso tun kafin yaje ya samu su Kaka da maganar son auran Hudan, ya zaman ace tanada tsayayye already.. Dan naga take takenshi kenan kwana biyun nan. Harga Allah ba zance miki ga laifin Junaidu ko makusarshiba amman idan Hudan ta auri Junaidu ban san wacce kalar rayuwa zata yi a hannun Sadiya ba, yes na san Junaidu shine Mijin amman ina gudun sharrin Sadiya kina gani fa yanzu yadda ta mayar da Ya Usman sai fa abinda tace tukunna shi akeyi a cikin gidan nan ko b’acin ranta baya so ya gani. Sannan shi kanshi Ya Usman d’in ba son Hudan yake yi ba! Ba zan so ta zauna da irin waennan surakan ba na san zafin k’iyayyar suruki sam babu dad’i kwata kwata! Bana so Huda tayi irin rayuwar da nayi a baya, a wahalar rayuwa da Hudan tasha tun daga tasowarta inaso ace taji dad’i a gidan Mijinta. Sannan abu na uku.. Hudan fa tana zaune ne kawai Ita ba makaranta take zuwa ba ballantana ace tayi facing karatunta, duk wata hanya da suka san zata samu ci gaba k’ok’ari kawai sukeyi su datse. Kaka yana iya bakin k’ok’arin shi amman shima wani lokacin baya iya tankawa saboda halin sharrin mata, akan batun karatun Hudan yadda kika san an datse bakinsu shi da Baaba Talatu. In Allah ya taimaka ta samu mai kishin karatun sai ya barta tayi a d’akin ta, bana so Hudan ta k’are kamar ni kwata kwata… Waennan dalilan ne suka sanya da akace yana son ganin ta kawai na bata sak’on da amsarshi zata sanya in fahimci manufarsa a kantaZ Ni dai a ganina kawai a samu a bincika ko shi waye idan aka dace sai kiga komai ya zo da sauk’i.” 100% Ummu ta yarda da duk bayanan da Mama tayi, dan ji tayi ma kamar Maman ta shiga zuciyarta ne. Dan haka tace mata “Yanzu ya kike ganin za ayi?? Kina ganin idan yaje wajen su Kaka maganar ba zata jewa shi Junaidun ba?” Ajiyar zuciya Maman ta sauk’e kafin tace “Baban Sakina zaki yiwa magana. Yaron zai zo ya gaidashi.. In maganar tayi k’arfi muka ji manufarshi aka sanshi sai ya zo wajen Kaka, Tunda yanzu hasashe ne muke yi.” Furzar da numfashi Ummu tayi sannan tace “to shikenan ba damuwa, amma sai dai abun nan fa ya zama sirri, dan kin san In Shuwa taji mun shallake su Kaka to kashin mu ya bushe!!” ‘Na’am’ Mama tayi da hakan. Sannan suka d’an tab’a hira kafin ta kashe wayar. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 22 Kamar yadda Arshaad d’in ya fad’a, ranar litinin da yamma sai gashi ya zo. Wannan karon bai zo da Jamil ba shi kad’ai ya zo dan bayan tafiyar su ranar asabar Jamil d’in yayita yaba kyawun Hudan yana cewa “ai yaga dalilin da yasa Arshaad d’in yazo ya mak’ale a irin wannan arean” har da cewa “In tanada k’anwa mai kama da ita ya had’a su, yanaso.” Shiyasa yau ya k’i zuwa dashi, dan in yana yaba Hudan ji yake kishi na neman kumbura mishi zuciya. Kamar ranar farko, yau ma Yaro ya kira ya aika yace ace “Hudan tazo inji Arshaad” Yau d’in Jalila tana makaranta suna tsakiyar jarabawa Umma kuma ta tafi yawonta ita da wata bazawara y’ar k’anwar dillaliya da take zaune a gaban dillaliyar shiyasa abun ya zo da sauk’i. Yauma Hudan bata dad’e da dawowa daga makarantar ba, suna tsakar gida ita da Mama suna d’an tab’a hira, tana cin d’umamen tuwon masararta da miyar kuka Yaron ya shigo ya fad’i sak’on ya juya ya fita… Rau rau Hudan tayi da ido sannan tace “Mama na ce mishi kin ce bana zance shine ranar yace ‘yau zai dawo’ ai na fad’a miki ko?” Murmushi Maman tayi ganin yadda duk Hudan ta bi ta rud’e. A hankali Mama ta mik’e ta shiga d’aki ta d’auko wayarta da pencil da y’ar k’aramar takarda sannan ta fito. Har lokacin Hudan tana zaune tana cin tuwon ta. Umartata Mama tayi da ta tashi taje ta wanke hannunta ta kai masa sak’o. Yadda Maman tace haka akayi Bayan tayi copying number Baban Sakina ta rubuta da sunanshi a jikin takardar ta bawa Hudan tace mata “gashi ta kai masa.” D’aki Hudan ta shiga ta d’auko hijabinta sannan ta fita zuwa wajenshi. Motar ta fara ganewa dan da ita suka fara had’uwa, yana tsaye ya jingina a jikin motar yana daddana waya… wata dakakakkiyar sky blue d’in shadda ce a jikinsa, d’inkin Boda mai d’an k’aramin hannu da hularshi zanna bukar itama sky blue mai d’an ratsi ratsin black a jiki, sai takalminsa na fata black wanda kana gani ka san mai mugun tsada ne dan sai wani kalar shek’i yake yi yayi wa fararen sawunshi mugun kyau. Bai san ta k’araso ba dan gaba d’aya hankalinshi yana kan chatting d’in da yake yi da Yayansa. Sallamarta ce ta dawo da hankalinshi wajen… A hankali ya d’ago ya zuba mata kyawawan idanuwanshi kafin ya sakar mata wani tsadadden murmushi sannan a hankali ya amsa. K’asa tayi da kanta ta gaidashi, Yanzun ma a hankali ya kuma amsawa yana mai tambayarta “ya gida” “Lafiya” kawai ta iya ce mishi sannan ta mik’a mishi takardar hannunta tace gashi inji Mama, dan ita Allah Allah take ta koma gida saboda yadda yake ta faman kallonta…. Babu wani datti ko squeezing a jikin kayanta dukda iya hijabin yake iya gani baya ganin rigar dan hijabinnata ma ya kusan rufe zanin jikinta gaba d’aya amman yadda kayan suka kod’e tashi d’aya zaka tabbatar da sun ji jiki kuma sun gaji da ruwa! Tausayinta ne yaji ya lullub’e shi, ahankali ya fara tunanin ta yadda zai yi ya taimaka mata dan gaskiya suna buk’atar taimako. Ga gidan nasu ma kanshi yana buk’atar a d’an gyara shi Gabansa ne yaji yayi mugun fad’uwa da ya tuno da Granpa domin kuwa ya san ko a verge of death yake wallahi Granpa ba zai tab’a yarda ya barsa ya auri Yarinyar data fito daga irin wannan gidan ba! Ajiyar zuciya ya sauk’e a ranshi yana cewa “tabbas he has to do a lot kafin ma yaje ya fara nunata…..dan he don’t think he can keep on living idan aka yi tunanin rabashi da Hudan! Shi fa har mamaki yake yi ta yadda kawai lokaci guda yaji yana mugun mugun sonta! Dan ko lokacin da yayi tafiya ji yake kamar yayi hauka, a gaggauce ya gama aikin da aka turashi ya dawo dan kawai ya samu yazo ya ganta……. “Zan tafi, sai anjima.” Shine abinda tace masa wanda yayi sanadiyyar dawo da hankalinshi wajen. Murmushi yayi sannan ya ware takardar ya duba… Number waya ne a ciki an rubuta Alhaji Muhammad a saman. Kallon ta yayi kafin yace “Your Dad??” Yayi mata tambayar yana mai nuna mata number. Kallon sunan tayi, sai da ta had’a gumi tukunnan kwakwalwarta ta iya karanta mata ‘Muhammad’ d’in amman abun farkon kam sam ta gagara karantawa ita dai taga ‘A’ da su ‘L’. Kalmar Muhammad d’in ta furta mishi. Kallonta yake yana mamaki yadda karatun yake bata wahala dan tun farko ya lura da hakan dama shiyasa yana sane ya bar mata ta karanta dan yana son ganin iyakar ilimin nata. “Eh, Alhaji Muhammad.” Yace da ita sannan ya janye takardar kafin ya sake cewa “Your Dads number, right?” A hankali tayi k’asa da kanta ta shiga girgiza mishi kai, kafin tace “Ba na Baba na bane ba, shi bamu da number shi wannan number Baban su Sakina ne mijin Anty na.” Da mamaki yake kallonta ‘taya zata ce bata da number Babanta?’ Ya so ya tambayeta ‘a ina baban nata yake?’ Amma kuma fahimtar da yayi tun lokacin da yayi mata maganar Baban nata gaba d’aya kamar ranta ya dagule dan har idanunta ma sun kawo kwalla ne yasanya kawai ya kyaleta ya zaro wallet d’inshi ya saka takardar a ciki with care sannan yace mata “I’m going to call him Ina barin nan, in shaa Allah. And pls ki cewa Mama na gode sosai sosai, Ina so In shiga In gaidata amman maybe sai dai next time tunda ta bani number, bara in fara zuwa inda ta turani inji komai tukunna ko?”. A hankali ta d’aga mishi kai alamar ‘to’ sannan tace “sai anjima” tana mai k’ok’arin juyawa. Yunk’urawa yayi da sauri daga jinginar da yayi a jikin motar kafin yace “Saurin me kike yi ne? Ko irin y’ar hirar nan babu? Ko har kin gaji da ganina ne?” Ya jero mata tambayoyin yana kallonta. A hankali ta girgiza kai sannan tace “Mama zata ga na dad’e” Murmushi yayi yace “ba za tayi fad’a ba. Bani labari ko guda d’aya ne tukunna sai ki tafi.” Shiru tayi dan ita bata san ta Ina zata fara ba. “D’aya kawai, sai ki tafi” Ta sake jin muryarshi a shagwab’e. Ita dai bata da labari shiyasa tace mishi “Wanne iri tou!” Cikin son fahimtar wani abu yace mata “School, wanne subject kika fi ganewa wanne ne kuma yake baki wahala?” Ta gane me yake nufi amman sanin bata da amsar wanchan yasa kawai tace masa “nafi son hadisi” Murmushi yayi kafin yace “A boko fa?” Sai da tayi k’asa da fuskarta sosai sannan tace “An cire ni tun tuni, bana zuwa.” As he was suspecting! Dan haka da sauri ya d’an matso yace “mai yasa bakya zuwa? Tun yaushe aka cire ki?” Cikin wata kalar angry voice sukaji ance “Saboda baka saka ta ba, shiyasa bata zuwa!”. Da sauri ta d’ago ta kalli Ya Junaidu wanda yake kallon Arshaad kamar zai rufeshi da duka!! Tunda take bata tab’a ganin wannan kalar b’acin ran a kan fuskar Ya Junaidun ba. Juyowa yayi ya daka mata tsawa “Bar nan kafin In b’abb’allaki!!!” Ai kuwa a take tayi cikin gida da sauri har tana tuntub’e. Bata san ya suka k’are da Arshaad d’in ba. Sai bayan kusan minti uku ya shigo cikin gidan.. Har d’akin Mama ya biyota! Yana shiga Hudan tai saurin b’uya a bayan Mama dan har ga Allah ta mugun tsorata da lamarin sa na yau d’in. Sai da ya d’an daidaita kanshi kafin yace “Mama kin san a waje naga Huda da wani a tsaye?” Kai tsaye Mama tace mishi “Eh, na sani.” Da mamaki yake kallonta kafin yace “Waye?” Mama bata b’oye masa ba nan ta sake cewa “Wanda kuke tunanin wajenshi taje kwanakin baya.” Zuciyarshi na wani irin mugun tafarfasa cikin b’acin rai, yace “Kenan wajen nashi taje da gaske tunda gashi yau ma ya biyota!”. A d’an fad’ace Mama tace “Junaidu fitar min a d’aki tunda rashin kunya kaima zaka yi min!” Runtse idanunsa yayi da k’arfi! Ya kusan minti biyu bai fita ba bai kuma bud’e idanun nasa ba. Tukunna a hankali ya bud’e idanunsa ya zuba su akan Hudan, da sauri ta sake shigewa bayan Maama, takowa yayi ya k’araso ya zo gaban Mama kafin yace “Kiyi hak’uri Mama ba rashin kunya zan yi miki ba, a tunani na bai kamata ta fita ta kula waani ba! She’s still young and na san kin san inason Hudan ko da ace ban kai ga furtawa ba, shiyasa sai naga kamar hakan cin fuska ne aka yi mini. Ban fad’awa su Kaka ba saboda a tunanina Hudan tayi k’ank’anta, amman Mama da k’arancin shekarunta kin barta tana kula wanchan mutumin! Kin ganshi kuwa? Irin waennan yaudarar ta kawai zai yi, a zamanin yanzu fa kwarya tabi kwarya ake yi. A tunani na ya kamata ace kin fara sanin waye shi kafin ma ayi tunanin barin ta fita wajensa…” Ji yayi muryarshi ta fara sark’ewa, tsabar b’acin rai! Gashi sai k’ok’ari yake ya danne! Ganin haka yasa ba tare da ya sake cewa komai ba kawai ya juya ya fita. Shiru d’akin yayi sai k’arar sheshshek’ar kukan Huda. Chan Mama ta juyo ta zaro ta daga bayanta ta dawo da ita gabanta ta tsayar sannan ta dafa kafad’unta da hannu biyu kafin tace “Hudan me Junaidu yake nufi da wanchan mutumin da yace ‘yaudararki zai yi?’ Wani abun ya gani?.” Da sauri ta shiga girgiza kai, ta ce “wallahi Mama a’a.” Ajiyar zuciya Maman ta sauk’e sannan tace “to me yasa yace ba auran ki zai yi ba?” Ahankali tai k’asa da kanta sannan tace “Mama nima tun farko ba na gaya miki ba? Da kike ta cewa zance yazo, Ni na san ba zance yazo ba wannan ba zai kula ni ba mai kud’i ne fa sosai kullum motar da yake zuwa da ita daban! sannan kayansa masu tsada ne daga gani. Yana dai jin Hausa, amman daga ganin shi balarabe ne ko kuma d’an India.” Cikin mutuwar jiki Mama ta saki kafad’un nata, kafin ta koma dab’ass!! Ta zauna a kan gado tayi shiruu…. Kana ganin ta ka san ta dulmiya duniyar tunani ne. A hankali Hudan ta koma gabanta ta tsugunna tana kallonta kawai. Sai da ta sauk’e ajiyar zuciya sannan ta ce “Tashi kije kiyi alwala an fara kiran sallah.” A hankali ta tashi ta fita ba tare da tace komaiba...... Junaidu kuwa yana fita d’akin shi ya nufa ya shiga ya sa sakata! Ya rasa mai yake yi mishi dad’i kwata kwata, tabbas ko makaho ya shafa yaji tofa ba zai tab’a comparing nashi da Arshaad ba! Ya fishi da komai ya ninninka shi! Ya san koda ace ya tilastawa Hudan ta aureshi to zai zamana gangan jikinta kawai ya aura, bai tab’a ganin koda d’igon sonshi a cikin idanunta ba hasalima idan babu Mama a waje to tana ganin shi take guduwa ya rasa dalili…amma shi wannan har ta san ta fita ta tsaya dashi kuma yadda take sunssunkui da kai a gaban shi irin kunyar nan, ya san tabbas tana sonshi ko da ace ba wani sosai ba. Umman shi tana zagin Mama tana cewa bata da kirki, shima kuwa tabbas yau ya yarda da hakan!! Tayaya zata bar Hudan ta kula wanin shi???… Yafi awa biyu a d’akin dan daga k’arshema zazzab’i ne ya rufe shi, da kyar ya iya tashi ya fito yayi alwala ya koma yayi magriba da isha. Sai da ya nemi Paracetamol a d’akin nashi ya sha tukunna ya samu ya d’an ware… Tunani ya fara yi akan ta wacece hanyar zai bi yayi kud’i dan tabbas ya gama yarda da zancen da ake cewa ‘Mama mayyar kud’i ce, shiyasa tun farko tak’i auren Baba ta tafi wajen wanda daga k’arshe ya gudu ya barta da y’a…amma still gashi yanzu tana son maimaitawa akan y’arta, kuma itama da alamun y’ar ta tsotso a Nono dan gashi daga ganin mai kud’i tana neman biyeshi! Everything is fair in love and war, dan haka ko ta wacce hanya shima sai ya bi yayi kud’i! Ya san muddin Mama da Hudan suka ganshi da kud’i to kuwa da gudu zasu amince dashi, kuma ya san su kaka shi zasu bawa In anzo neman aure amman yanzu first thing first sai ya tabbatar ya raba Hudan da wanchan saurayin nata tukunnan, dan muddin suna tare to kuwa kafin shi yayi kudin ma tsaf zai iya ji ana shafa Fatiha. Haka nan dai ya kwana yana ta tufka da warwara shi kad’ai a d’akin da tunani barkatai aranshi......... Bayan kwana uku. Ranar alhamis, sai ga Ummu da su Sakina, lokacin da suka zo Anty Zainab itama ta zo suna tsakar gida itada Umma da Jalila, sai k’us k’us suke yi….. Umma tana bata labarin “Arshaad da ya zo wajen Huda, ita takaicin ta ranar bata nan wallahi da Jalila ce zata fita! ita kuma Jalila gab’uwa ko yunk’urin ta fitan ma bata yi ba hakanan zungui zungui a gabanta ta bar Hudan ta je wajenshi. Amman ta iya zagewa ta bata labarin kud’insa bayan ta dawo, ta ce mata motar da yazo da ita ma abun kallo ce, salon ta kumbura mata zuciya da takaici” Nan Anty Zainab ta rufe Jalilan da fad’a..tana yi tana kitsa mata abubuwa ana had’awa da zagi da dunguri, wai su ala dole Jalilan bata da wayo sai uban tarin rashin kunya. Haka nan suka tusa Jalilan a gaba sunata zaginta har da dungure mata kai, a haka su Ummu suka shigo suka samesu. Wayencewa suka yi, da kyar Anty Zainab ta iya amsa gaisuwar Ummu da Sumayya, ita kuwa Umma kauda kai gefe tayi ta hau wak’a. Sai da Ummu ta dallawa Sakina harara tukunna ta gaida su ko amsawarsu bata jira ba tayi wucewarta d’akin Mama da sauri. Murna wajen Mama da Hudan ba’a magana. Sai da suka gama gaisawa sannan Ummu ta cewa Sakina, Huda da Sumayya “su fita tsakar gida tana son yin magana da Maman, kuma kar suyi fad’a da kowa!! Ko me Jalila zata yi musu kar su tanka!.” BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 23 Sai da Ummu taga fitarsu tukunna ta juyo ta cewa Mama “At least ai in suna wajen babu mai yi mana lab’e! Sannan su kansu bana so suji zancen yet.” Ajiyar zuciya Mama ta sauk’e kafin tace “Tun shekaran jiya nake zulumin ganin ki, gashi bani da ko sisi a waya ta, ke kuma baki kirani ba.” “Wallahi aiyuka ne suka chakud’e min suka yi mini yawa shiyasa kika jini shiru, yau ma Baban su Sakina ne ya taso ni yace ‘in zo In faiyyace miki yadda sukayi da wannan Yaron da kika tura wajensa.” Cewar Ummu. D’an matsowa Mama tayi kafin k’asa k’asa tace “Au yaje? Ai ni akansa ne naketa neman ki. Bilkisu na chanja shawara fa, ni ban san haka yake ba! Ina tsoron masu kud’in nan A bayanin junaidu da huda na fahimci cewa Yaron ba tsaran aurenta bane ba. Dan haka gara mu bari kawai Allah ya kawo mata wani… Shine dalilin neman da kikaji nace Inata yi miki.” Dariya Ummu tayi kafin tace “Ai Mama yanzu kam bakin alk’alami ya riga ya bushe! Dan bawan Allah n nan da gaske yake… Shekaran jiya inaga yana barin nan ya kira Baban Sakina, da yake a lokacin yana gida dawowarshi kenan muna zaune na gama bashi labarin za a kirashi kenan kawai sai ga kiran…. Bayan sun gaisa yace mishi ‘shine Arshaad yana zuwa wajen Huda ne so mamanta ta bada numbershi tace a kirashi zai iya zuwa yanzu ya same sa ba damuwa?‘. Ganin yana free d’in ne yasa Baban Sakinan yace masa “eh, ya zo.” Cikin y’an mintuna k’alilan San gashi yazo. Sun jima sosai dan sai bayan isha tukunna ya tafi. Bayan tafiyar sa, nayi tunanin ko Baban Sakina yaji ko yaga wani mugun abu a tare dashi ne, dan sai naga duk jikin shi yayi sanyi sosai, har wajen biyun dare yanata tunani yayi shiru shi kad’ai! Kuma sai waya yaketa fita yanayi da wani Abokin shi, jikinshi duk yayi sanyi…. Jiya wajajen k’arfe 12 ga mamakina sai ga Arshaad d’in ya dawo, dan har parlour na ya shigo muka gaisa. Da zasu fita Baban Sakina ya kirata ta kai mishi abu sai da ta dawo ne take cemin wai passport d’in Huda suke tambaya. Bayan tafiyarshi ma babu yadda banyi da Baban su Sakina akan ya gaya min halin da ake ciki ba amman yak’i, kuma naga ya bashi takardu a cikin envelop. Yau da safe ma ya dawo amman ban ganshi ba , Sumayya ce tace mini yazo dan ita baban nasu ma yasa ta kai mishi ruwa har yanata tsokanarta ya bata kud’i ma tak’i karb’a, to yana tafiya ne Baba su Sakina ya kirani yace ‘inzo yana son ganina’. Ina shiga na sameshi a zaune Bayan na zauna ne nake ce mishi ‘dan Allah in akwai matsala ka fad’a min naga gaba d’aya jikin ka yayi sanyi tun jiya.’ Sai a lokacin yake cemin ‘ba issue d’in Arshaad ne yasa shi tunani ba, wata y’ar matsala ce a office kuma yanzu sun magance ta. Maganar Arshaad kuma ranar da yazo yayi mishi tambayoyi ne akan family d’inshi, and ya gaya mishi komai kuma bayan ya bincika ya gano iyayenshi, and basu da matsala, yayi bincike a kanshi, har makarantar da yayi a Dubai Herriot watt dan akwai wani d’an Abokin yayanshi dama daya sani yayi makarantar shima so ya tambayeshi ko ya sanshi and an yi sa’a kuwa ya san Arshaad d’in sosai kuma ya bada kakkyawar sheda akanshi…. So daman tun a ranar shi Arshaad d’in yake yi mishi magana akan ita Hudan tace mishi bata zuwa makaranta a ina ta tsaya dan yanaso taci gaba, saboda har ga Allah ba zai b’oye ba family d’insa y’an boko ne sosai. So yace mishi ‘iya js ta fara js 1 kenan aka cireta. Jiya daya tashi zuwa kawai sai gashi da form na makaranta ‘Nigerian Turkish’ wai suna d’aukar y’an scholarship, saboda da farko cewa yayi zai sakata a makarantar ya dinga biya mata shi kuma Baban Sakina yaga abun kamar ana sauri saboda yaushe ma aka san juna da har za a bashi damar fara biya mata kud’in makaranta? Shikuma Arshaad d’in ganin da yayi Hudan bata da foundation na karatu mai kyau ne yasa yake son sakata a babbar makaranta dan ta samu ta taddo mates d’inta tunda dai yanzu ba zai yiu ace Huda ta shiga js1 ba. To shi dai Baban Sakina a lokacin yace mishi ‘gaskiya A’a’ sai kuma ga maganar scholarship ta b’ullo. Bayan ya gama mishi duk bayanin abubuwan da ake buk’ata saboda jarabawar ranar litinin d’innan za ayi ta…tou Huda bata da indigine, bata da certificate d’in junior waec.. Mama abunda zai baki mamaki mutumin nan tsakanin jiya da yau yayi komai ya kawo kawai sunanta ya tambaya ya karb’i passport d’inta, sai ga takardu sun fito. To ashe wai a ranar da yaga Sumayya shine yake cewa ‘wai ko itama za a had’a da ita tunda harda na js1 za a yi jarabawar, to Sumayya tayi k’arama a boarding tunda kinga makarantar kwana ce za su yi In Allah ya taimaka sunci jarabawarc. Shiyasa yace mishi a’a sai dai akwai yayarta kusan tsarar Hudan ce, itama ta gama junior waec. To yanzu itama ya karb’i abubuwan buk’ata ya fara nata takardun yace zuwa anjima zai kawo…dukda cewa akwai k’anwarshi da zai had’a da Hudan yana so ace Hudan tanada wanda ta sani a kusa da ita saboda ita k’anwar tashi a ss3 take.” Ajiyar zuciya Ummu ta sauk’e kafin tace “To, yanzu dai ga takardun Hudan nan komai da komai, zata cike ayi submitting gobe da safe, in Allah ya kaimu Monday sai suje su zana jarabawar, amman still Baban Sakina yana dad’a yin bincike a kan makarantar da yanayin security d’in makarantar, in dai yaga akwai wani insecurity, to yace baza suje ba! Dukda cewa an bincika a halayen Arshaad d’in ba a ji wani wani mugun abu ba amman d’an yau sai Allah, kar aje a kai Yarinya makaranta yayita zuwa babu control!.” Hannu Mama ta saka ta karb’i takardun sannan tace “Bilkisu a duk lokacin da zan saka goshina a k’asa sai na yiwa Huda adduar miji da dangin miji na gari sannan da karatu! Ina so Huda tayi karatu amman yanzu bani da wani burin daya wuce in raba ta da Yaron nan. Yadda yake zak’ewa d’innan yake yin abubuwa kina ganin bashi da wani mugun agender??” Murmushi Ummu tayi kafin tace “nima nayi tunanin haka da farko amma ntic na Kano da muka bincika basu cika d’aukar y’an scholarship ba sai wannan karon kuma suna ta sanarwa for good 3 months sannan ranar monday d’innan shine date d’in basu chanja ba! Abinda nakeso ki gane shine komai yazo ne a k’urarren lokacine kuma right time, shiyasa muke ganin gaggawarshi. In sha Allah ba komai. Ke da kanki kina cewa Hudan bata da foundation na boko da waye da waye idan har ba irin waennan makarantun muka samu taje ba, ba lalle kwakwalwar tata ta taso ba! Ni dai har ga Allah Mama Ina hango alkhairi a tattare da bawan Allah n nan, in dai muka bincika security na school d’in mukaga is good kawai suje idan har sun ci, mu bisu da addu’a. Ballantana ma na san cewa makaranta mai kud’i irin haka ba abunda zai hana ta samu kwakkwaran security. Kar ki duba Yaron ki duba karatun Huda da future d’inta kuma kiyi addua, ba ko wanne mai kud’i bane aka taru aka zama d’aya ba! Wasu zakiga ba ruwan su… Sannan Baban Sakina ce mini yayi ‘in sha Allah, yana hango silver lining a rayuwarki ata dalilin relationship d’in Huda da Arshaad! Addua kawai shine namu…..” Ummu bata bar Mama ba sai da ta tabbatar ta yi convincing d’inta. Sannan suka tsayar akan Ummu zata je ta gayawa Madu Mama kuma ita zata sanar wa Kaka...... Su Sakina suna fita suka nemi waje gefe kad’an dasu Umma mai d’an Inuwa suka zauna suka fara hira, Sakina tanata tsokanar Hudan wadda ta turb’ine fuska kamar zatayi kuka ita ala dole a daina cewa Arshaad saurayin ta ne! Su Sakina sunata yi mata dariya….. Umma kuwa suna gefe, ta tak’ark’are sai zabga musu uwar harara take yi, su kam bama su san tana yi ba! A zuciyarta kuwa cewa take yi “ai dole kuyi farin ciki daku da iyayenku, tunda ga mai kud’i nan yazo yana son d’aya daga cikin ku!!” Ita babban tashin hankalinta shine d’akin da taga Ummu da Mama sun shige, gashi sun turo Yara waje da alama magana mai mugun mahimmanci suke yi! Tanaso taji me suke cewa amman ba dama tunda ga Yaran a waje. Gabanta ne yayi mugun fad’uwa a lokacin da zuciyarta ta raya mata ‘to ko dai Arshaad d’inne yace zai turo!! Shiyasa suke ta k’us k’us’. Bata san lokacin da tace “Kaii!! inaaaa, ai Allah ma ba zai yi haka ba!” A fili sannan da k’arfi!!. Hakan yasa su Jalila da Anty Zainab juyowa suka kalleta, suma su Hudan zuba mata idanuwa suka yi suna binta da kallon mamaki. Sakina ce ta matso kusa da kunnen Hudan tace “Da alama fa matar nan ta fara haukacewa.” A d’an zabure Hudan tayi saurin juyowa ta rufe mata baki! Ita tsoranta kar su Umman suji shiyasa tashi d’aya duk ta bi ta rikice. Su kuma su Sakina yadda Hudan ta rikice d’inne ya basu dariya nan kuwa suka hau kyakyatawa Sumayya har da rik’e ciki. Ai kuwa Umma kamar jira take ta hau zagin su tana “Shegu y’ay’an y’an iska kawai! Uwar ku kuke yiwa dariya ba dai mu ba wallahi.” Da sauri Sakina tace “shegu y’ay’an y’an iska suna layin baya! Idan kikaje layin su Kaka ki tambaya kice a nuna miki ‘gidan marasa tarbiyya’ za a nuna miki gidan yana nan kusa da gidan dillaliya!”. Ba umma ba hatta Jalila mik’ewa tayi za suyi kan Sakina, itama Sakinan ganin haka yasa ta mik’e, jira kawai takeyi su k’araso dan ta lura tabon goshin Jalila ya warke da alamun tana buk’atar wani kuma daman tun ranar da Ya Jaafar ya sumar da Hudan take adduar Allah ya kawo abinda zai had’ata fad’a da su!. Ita kuwa Jalila ko da ace taje ma ba ta kan Sakina take shirin zata bi ba, tun ranar da taga Hudan da Arshaad take ji kamar ta mak’ureta, Yarinyar da bata yi makaranta ba wata kuchaka da ita amma wai itace har zata yi saurayin da ya fi nata?! Shiyasa so take kawai ta isa wajen ta samu ko da marin Hudan ne tayi atleast ta san hakan zai rage mata rad’ad’in da take ji a ranta…. Gashi su Umma suma sun gama tunzurata! Ji take kamar ta fashe…. Ganin dai da gaske Umma fad’a zata yi da Sakina ne ya sanya Anty Zainab ta sha gabanta ta rik’e hannayen Jalila sannan ta cewa Umma “haba! haba dan Allah, abun har ya kai haka? Y’ar cikin ki fa! ai girma sai ya fad’i. Ku zo muje d’aki kuji, dan Allah.” Shiru Umman ta d’anyi tana kallon su Sakina tana huci sai kuma kawai ta juya a fusace ta shige d’aki. Sai da Anty Zainab ta dakawa Jalila tsawa tukunna ta wuce tayi d’aki tana mai dannawa Sakina zagi!. A d’akin su Mama kuwa! Mama har zata fito amma sai Ummu tace mata “ta rabu dasu kawai! In dai Sakina ce daidai take dasu.” Dan haka suka zauna suka ci gaba da tattaunawa…. Sai da Anty Zainab tayi da gaske tukunna ta iya lallab’a Umma da Jalila suka hak’ura Danna k’ad’an ba sun d’au zafi!k’arshe ma Umma cewa tayi “in taci gaba da zama a cikin gidan, zuciyar ta zata iya bugawa, dan haka suka fita tare da Anty Zainab, aka bar Jalila. Ko kallon inda suka bi Sakina bata yi ba, dan ita har mamakin Anty Zainab d’in take idan taga tana biyewa su Umma. So take yi ta fita a gidan shiyasa ta cewa Hudan tazo ta rakata ta karb’i kud’i a wajen Ummu suje gidan kitso, dan su Umma suna fita Jalila ta sake fitowa ta zauna a tsakar gidan tana wani ciccin magani kana gani ka san neman bala’i take yi. Har Sakina ta mik’e zata je d’akin Maman sai Hudan tace “dan Allah su zo su tayata tsefe kanta sai su tafi tare, ba zata iya tsefewa ita kad’ai ba.” Sakina ce ta dawo tana cewa “Huda Allah ya nunamin ranar da zaki koyi tsefe gashinki da kanki” Da d’an k’arfi Sakinan ta kuma cewa “Dan ma dai Arshaad d’in naki mai kud’i ne, nasan y’an aiki a ciki harda mai yi miki tsifa zai nemo, idan bayanan ta dinga tayaki, In kuwa yana nan na san shi zai dinga yi miki dan yadda yake nacin son nan naki ba zai bari ki sha wahalar komai ba.” Ta fad’i hakan tana mai kunce d’ankwalin dake a kan Huda wadda take cewa “Allah Sakina za muyi fad’a dake ni daina ki daina, banaso.” Ai kuwa kamar yadda Sakina taso haka maganarta tayi tasiri a kan Jalila, dan har wani huci taga tanayi daga nan inda take a zaune. Haka nan Sakina tana dariyar mugunta ta hau tsefewa Huda kalbar kanta da suka sauk’a har chan gadon bayanta. Jalila tana zaune tana kallon su…tabbas ta san tanada kyau dan ana yawan gaya mata sannan tafi Hudan manyan idanuwa amman idanun huda sunfi nata kyau nesa ba kusa ba dan ita nata idon ba cycle baneba irin dogayen nan ne sannan farare tas kuma kamar tana jin bacci, gata da dogon hanci ga bakinta mai kyau d’an k’arami. Ta san a iya fuska ma Hudan ta fita…maganar kalar fata kam ba’a magana, ta san ita ba bak’a baceba amman ba zata tab’a had’a farinta dana Hudan dayake da sirkin yellow yellow, kuma mai d’aukar ido, ba. A kyauwun sura kuwa, Hudan a iya yanzu ta kusan kamo ta tsayi duk da ta grime ta, dukda cewa k’irjinta yafi na Huda cika a yanzu amma ta san ko tak’i Allah ba zata had’a hips d’inta dana Huda ba dan Hudan ta fita nesa ba kusa ba dan idan ta juya tana tafiya zaka d’auka wata shahararriyar budurwa ce. Jalila bata gama sarewa ba sai da ta kalli gashin Hudan da Sakina ke tsefe mata y’ar kalbarta guda biyar har ta kusan gamawa, Gashin bak’i k’irin, gashi har gaban gashinta ga wani saje da takeda shi mai mugun kyau.. Tsayawa Jalila tayi tana kallon gashin dukda ba yau ta fara ganin gashin Hudan ba amman tabbas ta san ya Kara tsayi kwana biyun nan, tana zaune amman kamar zai tab’o k’asa! Bata san lokacin data sa hannu ta shafa nata ba, wanda ya wuce kafad’arta da kyar, d’aurin ta na ture kaga tsiya ta gyara dan ji tayi gaba d’aya ranta ya dagule! Tabbas a yanzu idan taje wa Arshaad d’inma ba kula ta zai yi ba, ahaka ma bai ga gashin Hudan ba, gaskiya tun kafin ya gani ko ruwan batir ne sai ta kwara mata a gashin wallahi….. Da sauri ta muk’e ta shige d’aki jin Sakina na cewa “bara inje In d’akko mike ribbon da comb sai in gayawa Ummu In taho mana da kud’in kitson.” Jalila tana shiga batayi wata wata ba ta d’aga k’asan kayan ta inda take da wani ajiyeyyen almakashi, ai kuwa ta d’auko tayi waje da sauri, ta b’oye a k’asan zaninta. ji tayi Hudan na cewa Sumayya “dan Allah ta d’auko mata hijabin ta a cikin kayanta”. Cike da murmushin mugunta tayo inda take zaune kamar zata wuce, tana ganin d’aga labule da shigar Sumayya d’akin Mama ta k’araso inda Hudan take da sauri ta kama gashin kamar zata ribbon!! Ita Huda da farko dake bata ga tahowarta ba ta d’auka Sakina ce, sai da taji an damk’i gashin da k’arfin sannan ta juyo zata cewa Sakinan baki taje mini ba zaki sa ribbon d’in? Kawai suka had’a ido da Jalila….. Ai kuwa a take ta fara k’ok’atin kwace kanta, amma kafin ta kufce tuni Jalila ta zaro almakashinta ta daidaita gashin Hudan da iya k’arfinta ta yanke shi kitt!!!!! Iyakar wanda ta bar mata wanda za a iya had’awa ayi parkin ne kawai, shima kuma jelar sai dai yayi kamar bindin kaza! Hakan yayi daidai da fitowar Sakina da comb da ribbon a hannunta dan Ummu cewa tayi “su bar kitson sai gobe suje da wuri yanzu yamma tayi” Huda da sauri ta juyo tana kallon k’asa jin abu ya fad’i, wani razanannen ihu tayi sakamokon ganin gashinta wanwar a k’asa! ita abun ma mugun tsoro ya bata shiyasa ta shiga shafa kan tana wani irin kuka…. Jalila bata ga k’arasowar Sakina ba sai wani mugun mari n da taji ya sauk’a a kan kumatunta, kafin ta yunk’ura Sakina ta rufeta da duka ta koina….dukda tazarar shekarun dake a tsakaninsu yau kam Jalila ta daku a hannun Sakina dan k’arshe ma ihu Jalilan ta fara tana neman taimako. Su Mama jin abun yayi yawa dan su duk a tunani su su Umma sunan nan, sanin halinsu yasa suka k’i fita kar su fita su Umman su had’a dasu a fad’an Yara Shiyasa har Sumayya data shigo d’aukar hijabi suka hanata fita. Amman ihun Jalila daya k’arashe ko Ina lungu da sak’o na gidan ne ya sanya sanya suka fito. Turus!!! Haka suka ka suka tsaya sakamokon ganin gashin Huda a tsattsaye, ga uban tulin gashi a k’asa tanata k’ok’arin tattarewa tana d’aurawa a kan cinyarta tana kuka, gefe guda kuma ga Sakina a gefe sai jibgar Jalila take yi da iya k’arfinta. Kafin su k’arasa tuni Ya Junaidu wanda shigowarshi kenan yayi saurin yin kansu Jalilan. Da kyar ya iya kwatar ta a hannun Sakina amman fa ta fasa mata hanci har da baki, ta yi mata jina jina! Su Mama ne suka hau tambayar ba’asi, nan Sakina ta hau kwararo musu jawabi iya abinda ta gani… Junaidu ji yayi da ma bai kwaci Jalila ba ji yake kamar ya juya yaci gaba da dukanta tun bama da yaga yadda Hudan take kuka ba abun tausayi, juyawa yayi kan Jalilan a fad’ace har zai fara magana kamar kuma wanda ya tuna wani abun sai kawai yace mata “wuce ki shige d’aki” Tana tafiya ya juyo ya kalli Hudan, wadda take mishi kallon ‘ya yau bai shigar mata ba!’ Gashi kuma abunda aka yi mata yau d’in ma yama fi na kullum… Da sauri ya d’auke kanshi ya juya ya nufi hanyar d’akin shi ba tare da yace musu komai ba. Sakina ce tace “Kinga irinta ko!! Saboda Allah ai atlest ya kamata ko fad’a ne yayi mata.” Mama da Ummu kuwa sarai sun san dalilin da yasa Junaidu yayi hakan, dan labarin abinda ya faru shekaran jiya Mama take bawa Ummu sukaji ihun Jalila! Shiyasa ba tare da sunce komai ba, suka tattare gashin kawai, suka d’aga Huda suka yi d’aki da ita tanata faman kuka. Sai da suka rarrasheta da kyar! Aka samu bacci ya kwasheta tukunnan suka tafi bayan Ummu ta tabbatarwa da Mama kafin ta tafi gida sai taje ta samu su Baaba Talatu kuma daga nan zata fad’a musu zancen makarantar da su Hudan zasu tafi, ta san ko su zasu yarda dan yanzu kam abun na su Umma ya zama hauka k’arara!! Dole a d’auki mataki sannan kuma Hudan tayi nesa da su…… Tanata fad’a baki da kumfa haka ta tusa k’eyar su Sakina suka tafi. Ita dai Mama tayi shiruu! Dan tama rasa bakin yin magana. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 24 Successfully, Kaka da Baba Talatu suka amince da batun makarantar Huda, Kaka shi ya sanar wa Madu wanda shima bai hana ba bai kuma ce taje ba kawai dai ya jinjina kai alamar ya ji kuma ya fahimta. Kaka ne ya yanke shawarar Hudan ta tafi gidan su Ummu tayi koda sati ne, bayan ya kira Baba da Umma da Jalila yayi musu fad’a sosai!! Sannan ya cewa Jalila “tunda y’ar daba take son ta zama kuma iyayenta sun kasa tsawatar mata to ta tabbata tana gama ssce d’inta ta fito da Miji idan ba hakaba to zai bada hotonta a masallaci duk wanda ya zo kuma shi zata aura koda kuwa gurgu ne!.” Jalila kuka wiwi haka suka baro gidan Kaka, Umma sai mita take yi wai ‘anyi son kai!’ Idan ba haka ba dan maiyasa ba a yiwa Sakina fad’an dukan da ta yiwa Jalila ba?!. A Daren ranar da su Ummu suka koma gida suka samu takardun Sakina itama har sun zama ready.. Duk wani preparation na exams d’in yi suke dan Arshaad har wata lesson teacher ya d’auko tayi musu isashshen lesson ranar asabar da lahadi wanda da farko shi yaso yi musu lesson d’in amman sai aka tura shi wani aiki Abuja sai monday da yamma tukunna zai dawo. Sakina tana fahimtar lesson d’in sosai amman Hudan kam sai dai godiyar Allah, matsalar da aka samu shine ita lesson teacher bata jin Hausa ita kuma Huda turancin sai a hankali. Sai da ya zamana duk abinda lesson teacher ta fad’a sai an mata translating da Hausa! Duk k’ok’ari da hak’uri irin na matar sai da ta k’ule a cikin kwana biyun. Da kyar Hudan ta tsinci iya abubuwan da zata iya tsinta ranar Litinin kamar yadda aka fad’a Baban Sakina da Ummu suka kaisu makarantar domin su zana jarabawar. Hudan har kusan kukan murna tayi da taga jarabar tasu zab’i ka tik’a ce! Saboda daman adduar da take ta yi kenan. Sai dai kuma duk da hakan da kyar da sid’in goshi ta iya amsa question biyar a cikin guda d’ari biyun da take tunanin ta gane wanda hakan ya d’auketa sama da awa d’aya. Tayi kokari wajen ganin ta amsa ragowan dan bata so ace ta fad’i jarabawar nan tana mugun son tayi karatu a rayuwarta amman kwata kwata sai ta kasa. Har kuka tayi a exams hall d’in, bata ankara ba taji ana cewa “20 minutes remaining!!” idan ta fahimta sauran minti ashirin kenan a tashi! Hakan ya sanya kawai ta rufe idanunta ta karanto sunayen Allah ta nemi nasara da sa’a sannan ta d’aga pencil d’inta ta fara sheding, duk shed d’in da zata yi sai ta kira sunan Allah tukunna ta tik’a… Haka tayi daga Ar Rahman zuwa As Sabboor, ta sake dawowa Ar Rahman a haka har ta gama wanda yayi dai dai da fara amsar takardun nasu. Sai da ta tofe takardarta da addua tukunna ta bayar invigilator d’in yana ta tsokanarta. Kasancewar y’an hall d’in su Sakina sun rigasu shiga yasa tana fitowa suka had’u da Sakina a k’ofa tana jiranta. Sakina na ganinta ta k’araso da murnarta tana cewa “Hudan jarabawar tayi sauk’i ko? kinga duk abinda malamarnan ta koya mana kusan duk sun fito, kamar ta sani.” Da mamaki Hudan ta kalleta kafin tace “Tab! Ni fa biyar kawai na gani irin wanda tayi mana, a maths d’in kuma naga irin wannan mai kamar triangle d’in wanda kika sake koya min da daddare dayawa amman duk sun chanja nambobin.” Lumshe ido Sakina tayi a hankali sannan ta bud’e, kafin tace mata “Ai numbers d’in kawai suka chanja, kin dai yi ko?”. Hudan bata b’oyewa Sakina ba ta gaya mata yadda tayi.. Jikin Sakina duk sai yayi sanyi amman gudun kar ta sace mata guiwa ya sa kawai tayi ta bata kwarin gwiwa. Suna shirin wucewa aka ce “kowa ya tsaya akwai d’an guntun orientation da za ayi musu, babu isheshshen lokacine amman da it’s sopposed to be for weeks..” Haka nan suka d’unguma aka fara orientation d’in. Ita kam Huda zuciyarta duk a dagule, bare ma da aka fara orientation d’in nan ta sake ji makarantar ta shiga ranta, duba kuma da abunda ta rafka a exams d’in duk sai hankalinta ya sake tashi. Sai da aka yi rounding up sannan suka kama hanyar inda su Ummu suka yi parking, Hudan har da y’ar kwallarta, da kyar Sakina ta d’an lallasheta ta bata kwarin guiwa tukunna aka samu hankalinta ya d’an kwanta. Suna zuwa nan ma Ummu da Baban Sakina suka shiga tambayarsu, ita dai Hudan k’arshe ma kuka ta saka, dan gani take yi kamar har ta fad’i ne, sai da su Ummu suka yi ta bata baki tukunna ta hak’ura tayi shiru. A haka dai duk jikinsu yayi sanyi jin Hudan bata yi wani abun kirki ba, suka k’araso gida. D’aki suka wuce ita da Sakina sai da suka yi wanka suka shirya suka yi waya da Mama sannan suka fito suka ci abinci suka d’an yi hira da kallo sama sama isha nayi kowa ya nufi gado. Ranar Hudan bata yi bacci ba kwana tayi tsayuwar dare tana rok’on Allah yasa suci jarabawar nan… Washegari ma da safe haka ta tashi duk jiki ba kwari har dare, kamar jiya yau ma bata yi bacci ba, kwana tayi tana sallah.. Haka ta kasance kullum, itama Sakina daga baya tayi joining d’inta a sallar daren, a haka aka yi sati. Ranar litinin da yamma sai ga Arshaad ya zo. Su bama su san yazo ba, suna falo suna kallo, sun gama waya da Mama kenan! Wayar Baban Sakina ta shigo layin Ummu, d’auka tayi suka yi magana bayan ta ajjiye ta kalli Sakina da Huda tace “kuje Babanku yana son ganinku, Arshaad yazo da result d’in jarabawar da kuka yi.” Da kyar gabansu yanata fad’uwa suka iya mik’ewa suka nufi d’aki, bayan sun d’auko hijabansu suka tafi parlourn Baban Sakinan. Sakina ce tayi sallama aka basu izinin shiga, ita ta fara shiga sai Hudan a bayanta kansu a k’asa suka gaida Arshaad. Cikin kulawa ya amsa yanata satar kallon Huda wadda ta kusan yin fitsari a wando tsabar fargaba! So take kawai taji me za a ce. Baban Sakina ne ya mik’a musu takardun yace “ga results d’inku” Da kyar Sakina ta iya mik’ewa taje ta amso sannan ta dawo kusa da Huda ta mik’a mata d’aya… har rige rigen bud’ewa suka hau yi. Hudan tana bud’ewa taga 149/200 sai kuma daga chan k’asa anyi stamping ‘PASS’ da green rubutu! Sai da ta kalli sama sai taga sunan ba nata bane ashe takardar Sakina ce. Murna ta hau yi dan taji dad’i duk da fargaban rashin ganin nata amman atleast Sakina ta wuce. Ita kuma Sakina tana bud’ewa taga sunan Huda, da sauri Hudan ta lek’o, bata san lokacin data ce “Kaiii!! nawa ne kuwa?” Da taga 185/200 itama an mata stamping ‘PASS’. Ai kuwa da sauri suka rungume juna a wajen suna dariya suna maimaita kalmar “Alhamdulillah” Hudan har da kwallarta a ranta tana aiyyana “Yanzu kenan itama zata yi karatu kuma a wannan makarantar y’an gayun data gani zata je tayi karatunta.” Wani irin farin ciki ne ya lullub’e Arshaad a ransa yace “So she’s this happy and it’s all because of him? Ai kuwa In shaa Allah he will make it his life’s mission to keep her happy.” Ya ji dad’i sosai dan bai san lokacin da shima ya fara murmushin ba. Tabbas Yarinyar tana son karatu, he wonders why iyayenta basu barta tayi ba, ko saboda halin babu ne maybe shiyasa…. Maganar Baban Sakina ce ta katse mishi tunani… Godiya ya sake yi mishi kafin ya juya ya cewa su Hudan “murnar ai ta isa haka ko? Ko godiya fa baku yi mishi ba.” Nan suka had’a baki suka ce “Mun gode, Allah ya saka da alkhairi.” “Ameen, ba komai.” Kawai yace dasu daga nan Baban Sakina yace su tashi su tafi. Sai da suka fita Arshaad yace “akwai interview d’in da ake zuwa ayi kuma du, amman dai shi ba wani issue bane tunda sun riga sun yi passing wannan.” Godiya Baban Sakinan ya k’ara yi mishi. Bayan Arshaad d’in ya sanar dashi date na interview d’in ya wuce. Successfully, suka je suka yi interview d’insu daga nan kuma aka fara preparation d’in tafiya. Baban su Sakina ne yayi yayi musu provision da komai da komai har books, da farko Asrshaad yaso yi amman ya hanashi kwata kwata. Sai a lokacin kuma Shuwa taji labarin tafiyar Huda da Sakina makaranta. Ita dai bata cewa Mama komai ba tunda daman ai ta dad’e da cire harkar ta a ranta amma Ummu kam ta sha fad’a! Wai “taje ta had’e kai da y’ar uwar ta sun b’oye mata abu, kuma Baban Sakinan da Mijin mama yayiwa rashin mutunci shine yanzu ta tura shi yake yiwa Maman abu salon wani abun ya sake faruwa ta jawowa kanta matsala a Auranta!” harda cewa “ta raba Huda da Sakina dan ita tana da nata asalin.” Haka nan dai tayi ta mita. Ita dai Ummu hak’uri tayi ta bata, sannan tace “Kaka ne yace Hudan taje gidanta ta d’an zauna” Tukunna Shuwa ta d’an sauk’o. Sai ranar lahadi tukunna Ummu ta bar Huda tazo gidansu.. Washegari da safe ta saka sabon uniform d’inta ta shirya tsaf sai a lokacin Mama taji kuka ya zo mata, itama Hudan kuka tayita yi ahaka Ummu da Sakina itama data shirya suka zo suka samesu. Da kyar suka lallashi kansu sannan Ummu ta kai Huda da Sakina d’akin Umma dan su yi mata sallama. Kasa b’oye bak’in cikin su suka yi, tun ba ma da sukaji sunan makarantar ba! Ita dai Ummu bata bi ta kansu ba ta sanya suka yi musu sallama suka fito suka tafi. A gate d’in makarantar suka had’u da Arshaad da k’anwarsa Aaima wadda tana ganinsu Huda ta dinga jansu a jiki kamat sun shekara da sanin juna. Duk wasu formalities aka yi aka gama sannan Aaima ta sanya aka taya su kai kayansu hostel, sunata kuka ita tayi ta lallashinsu ta jasu suka tafi. Su Ummu da Arshaad ma suna ganin shigewarsu suka juya suka wuce bayan doguwar godiyar da suka yi ta jera mishi, shi kam abun ma sai ya fara bashi kunya.............. Bayan shekara uku! After 3 years (present day). Yau Monday kuma yau su Hudan za suyi graduating. Arshaad tare da Aaima suka zo, su suka fara zuwan ma su Huda dan sun riga su Ummu ma zuwa................. Bayan an kai su Sakina makarantar shekaru uku da suka wuce Aaima ce ta tsaya a kansu especially Huda har personal lesson take yi musu. Tana son Yaran ba kad’an ba, ranar graduation d’inta kam sunci kuka, da kyar suka warware daga baya suka yi friends. Daga nesa ta hango su cikin graduation gown d’insu sun yi kyau sosai sun zama y’an mata sun yi fresh hasken fatar su ya k’ara fitowa. Basu lura da ita ba saboda duba wayar da suka ara domin kiran su Ummu da suke ta k’ok’arin yi, dan sunga har an kusan farawa amman shiru basu k’araso ba. Sai da Aaima ta k’araso ta dafa kafad’ar Huda, tukunna suka lura da ita. Ai kuwa da sauri suka yi hugging d’inta suka hau murna, nan shima Arshaad ya k’araso, da murmushi a kan fuskarsa yake bin Hudan da kallo… Dukda cewa duk visiting yakan zo ya ganta amman yau d’in sai yaga gaba d’aya ta chanza, tayi wani kyau kamar yayi irin shekaru d’innan bai ganta ba. Sakina ce ta fara gaidashi sannan itama Hudan ta sunkuyar da kanta ta gaidashi dan ita har ga Allah yanzu wata kunyar shi take ji saboda tun lokacin da zasu fara zaman extension da yazo kawo musu books da abubuwan buk’ata yake gaya ‘yana sonta’ shikenan har yau bata iya ko had’a ido da shi. Murmushi yayi ya amsa gaisuwar yana mamakin kunya irin ta Huda. Sallamar da su Ummu suka yi ne ya juyo da hankalinsu.. Tun da suke zo makarantar sau biyu taje gida hutu a lokacin tana ss1, bayan nan a gidansu Sakina take hutunta kuma Mama bai fi taje sau d’aya ba dan ko visiting Baba hanata zuwa yake yi. Shiyasa yau take ta adduar Allah yasa azo da ita, ranar farin ciki ya kamata ace tana kusa da ita. Ai kuwa tana d’agowa da Maman suka fara had’a ido, ba tayi wata wata ba ta tafi da gudu ta fad’a jikinta, ji tayi kawai kuka ya sub’uce mata Itama Maman harda y’ar kwallarta amman sai tayi saurin sharewa…. Sai da ta cewa Hudan “zata koma idan bata yi shiru ba”tukunna tayi shiru ta goge hawayen ta tana mai sauk’e tagwayen ajiyar zuciya. Aaima ce ta fara matsowa ta gaida Mama dan ko ba’a fad’a mata ba ta san itace mahaifiyar Huda, daga nan ta gaida Baban su Sakina da Ummu sannan ta hau tsokanar Sumayya tana cewa “ta zama y’a mata” ita kuma Sumayyan tana murmushi tana cewa “bata so” daman sun saba. Sai da Sakina ta k’arasa dai dai gaban Arshaad ta tsaya tayi snapping fingers d’inta tukunna yayi firgigit! Ya kawar da idanunsa daga kan Mama da ya kafe da idanu, sannan yayi saurin juyo da hankalinshi kan Sakina yana murmushi. Kallon da yaga Sakina tana yi mishi tana kuma waiwayawa tana kallon inda taga yana kallo ne yasa shi cewa “Itane Maman Huda??” Murmushi Sakina tayi sannan tace “Ai ni na d’auka wata kake kallo, baka ga har na had’e rai ba? Ashe Mama kake kallo.” Ta k’arashe maganar tata tana murmushi. Shima murmushin yayi sannan yace “kina tayata kishi bayan ita ko kishin nawa batayi, I don’t even think ma tana sona!” Yayi maganar yana langab’ar da kai yanayin kalar tausayi. Dariya Sakina tayi sannan ta d’an matso ta sa hannunta ta kare bakinta ta gefe kamar zatayi rad’a, tace “Kar ka damu zan yi maka campaign mai zafi!” Dariya yayi yace “Woow!! really? tnx sis, you are the best!” Yayi maganar yana yi mata tumbs up. Dariya tayi tana d’aga kanta alamar ‘eh’ sannan at the same time tana d’aga girar ta, hakan yasa gaba d’aya suka kwashe da dariya, sannan tace mishi zo muje ka gaisa da surukarka, yau ne had’uwar ku ta farko so you better act decent!” Dariya kawai yayi, sannan ya bi bayan ta suka k’arasa inda su Maman suke tsaye. Sai da ya d’an russuna sannan ya gaida Mama. Cike da kunya ta amsa dan tunda ya nufo su Ummu tace mata “ga Arshaad” Su ummu ma cikin ladabi ya gaida su suka amsa mishi da kulawa. Daga nan suka d’unguma gaba d’ayan su suka yi hall d’in da ake taron bayan sun gaggaisa cikin mutunta juna… Suna zuwa kamar su kad’ai ake jira nan aka fara gudanar da programs of event, Hudan aka kira ta bada speech wadda in mutun yaji kalar turanci da accent dining Hudan sai yace ba ita bace ba. Bayan ta gama aka fara raba gifts sai da ta karb’i hud’u!!Best in English Physics Most decent da most beautiful. Sakina kuma ta karb’i Best in maths Most popular da Da gift d’inta na social prefect da aka had’a mata. Mama dai sai share kwalla take yi sunata murna. Bayan nan akayi pictures da ragowan abubuwa daga nan kowa ya watse. A waje ma sai da Aaima ta sake yi musu kowa da kowa Sannan tace sai Huda ta tsaya anyi mata da Arshaad, da kyar ta tsaya kuwa dan sai da ma ta fakaici idon su Mama taga sun d’an juyo sun basu baya. Haka nan cikin farin ciki suka nufi gida. A gidan su Sakina suka yada zango. Arshaad a falon Baban su Sakina suka tsaya, a nan aka kai musu ruwa da abinci suka ci. Su Hudan suna cikin cin abincin suma Baban Sakina ya shigo ya cewa Hudan “taje falonshi” sannan ya nufi hanyar d’akin shi. Sai da Ummu ta sake maimaita mata tukunna ta mik’e kamar munafuka tana jan Sakina tana kallon Mama wadda ta d’auke kai tayi kamar bata ji su ba. Sai da suka je d’aki suka chanzo hijabai sannan suka nufi falon…. Babu yadda Sakina bata yi da ita akan ta fesa turare ta shafa powder ba amman fur tak’i! Haka suka fito Sakina tana ta faman b’alla mata harara ita kuwa Hudan sai dariya take yi. Suna zuwa dai dai k’ofar falon kuwa bayan sun bud’e Sakina tasa duka k’arfinta ta turata ciki sannan ta juya da gudu tana yi mata dariya itama… Cike da kunya ta d’an juyo tana kallon Arshaad wanda shima dariyar yake yi mata dan ya san wannan aikin Sakina ne. Turo baki tayi kafin tace “Ya arshaad kana gani ta turoni kuma baka ce min sannu ba kake min dariya?” Murmushi yayi kafin yace “Nasani ko tirjiya kika yi? Kika ce ba zaki zo wajena ba shiyasa ta turoki?”. Sake turo bakin tayi. Ganin haka yasa yayi saurin kama bakin nashi da y’an yatsun shi yana dariya k’asa k’asa, kafin yace “Afuwan wifey! Zo ki zauna tou nayi shiru ba zan sake cewa komai ba.” Yayi maganar yana mata nuni da gaban kujerar da take facing d’inshi. Da sauri taja gaban hijabinta ta rufe idanunta sannan tazo ta zauna a wajen da ya nuna mata ta sake sunnar da kanta k’asa. Tafi minti uku a haka jin shiru yasa ta d’ago kanta a hankali a tunaninta ko wani abun yake yi a waya amman tana d’agowa sukai ido biyu dashi da sauri ta kuma sunkuyar da kanta. Murmushi gefen baki yayi kafin yace “Hudan”. “Um” Tace. “Hudan” Ya sake kiranta. A hankali tace “Na’am” Sai da ya d’an yi jim! Tukunna yace “Pls ki cire wannan hijabin daga idonki, I want to talk to you about something that is very important, kinji”. A hankali ta d’an jashi sama, face d’inta ya fito. Ajiyan zuciya ya sauk’e kafin yace “Last time da naje wajen ki a school! I told u what i feel towards you amman baki ce komai ba har yanzu. Inaso in san matsayina dan i think is about time da ya kamata in san where i stand ko?” Yayi maganar yana d’an lek’o fuskarta. Shirun da tayi ne yasa yace “Um? Please don’t say you need more time Hudan, Allah kad’ai ya san what I’m going through! Ko menene just say it, in ma bakya sona ne ki fad’a min zan d’auki k’addara.” A hankali yaji tace “Ya Arshaad nifa ban ce bana sonka ba.” Zuciyan shi har wani bugawa take yi, cikin k’aguwa da son jin amsar ta yace “Does this means kina sona?” Murmushi tayi sannan ta d’aga kanta alamar ‘eh’ “Alhamdulillah” Taji ya furta tare da sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya kafin ya sake cewa “zaki aureni right?” Murmushi tayi sannan ta d’aga kanta still alamar ‘yes’ Kunyace taji tana shirin nutsar da ita shiyasa ta tashi da sauri ta fice a falon, tana jinsa yana cewa “No pls wait bamu k’arasa ba” amman ta fice cikin sauri…. Arshaad ya kusan 1 hour a parlourn shi kad’ai a zaune yanata murmushi da day dreaming na yadda rayuwanshi zai kasance tare da Huda. Yanata plans shi kad’ai kala kala, bai san lokaci ya ja har haka ba! Kiran sallar la’asar ne ya fargar dashi, gashi yanada meeting d’in gaggawa a company wanda Granpa ya turo mishi d’azu akan za suyi su biyu @5pm! Bai san akan menene ba. Da sauri ya d’au wayar shi ya buga kiran Aaima yace “ta sameshi a mota yanzu yanzu.” A gurguje Aaima ta yiwa su Mama sallama, dan taji kamar Yayan nata yana cikin sauri ne. Tana zuwa kuwa ta fad’a motar yaja suka fita daga gidan… Gudun da taga yana yi ne ya sanya ta tambayeshi Nan yake ce mata “Granpa ne yace mishi ya sameshi a office bai san mai ya fari ba.” “Allah yasa lafiya.” shine abinda Aaima ta fad’a sannan ta jingina da jikin kujera ta lumshe idanunta ta fara tunanin Auwal… Yau kwana biyar kenan bata gansa ba kuka ko ta kirashi baya d’auka! Daman kwana biyun nan rashin mutunci yake ji dashi, dan kawai yace tayi mishi abu tak’i yi! Ita wani abun na Auwal sai take ganin kamar iskancine amman friends d’inta na nile su ce mata suke yi ‘hakan wai wayewa ce, its a normal thing and dan yana sonta ne shiyasa yake demanding, inda iskanci ya so yi to da ba zai na demanding peck da kisses ba, he would have ask for something different!’. To ko dai tayi mishi kawai tunda ba wani abun bane ba, dan ita dai har ga Allah Allah ya d’aura mata son Auwal, bama ta san wanne irin so take yi mishi ba! She don’t ever want to see him angry, besides she is in level 2, tana ganin yadda mates d’inta suke kula da samarin su...... Maganar Arshaad ce ta katse mata tunani jin yana cewa “Wai tunanin me kike yi ne haka?” Cikin fad’a. Firgigit!! Ta bud’e idanunta. K’ura mata ido yayi sannan a hankali yace “anjima around 9, ki sameni a parlourna.” “To” kawai tace, sannan ta bud’e k’ofar ta fita, binta yayi da kallo har ta shige sannan ya nufi mosque d’in jikin estate d’in yayi sallah, yana idarwa ya d’anyi addua, sannan ya fito ya shiga mota ya nufi office.... Yana zuwa bai tsaya b’ata lokaci ba ya nufi hanyar office d’in da yake mallakinsa a cikin building d’in dan Granpa yace mishi “a nan zasu had’u” kuma kamar yaga d’aya daga cikin motocin da Granpa d’in yake hawa a parking lot shiyasa a gaggauce ya dinga amsa gaisuwar securities da wasu ma’aikatan da suke ta gaidashi yana mai k’arsawa office d’in nasa. Key ya zaro zai bud’e k’ofar amman yana d’aurawa yaga ashema k’ofar a bud’e ne hakan ya bashi tabbacin Granpa ya rigashi k’arasowa kenan!! Agogon hannunshi ya kalla yaga ya k’ara 5 minutes akan time d’in da yace masa ya sameshi. Ajiyar zuciya ya sauk’e kawai yayi ‘bismillah’ ya tura kai ya shiga. Yana shiga ya hango Granpa a kan kujerar shi ya juya baya. Sai da yayi addua sannan ya k’arasa inda yake… D’an gyaran murya yayi sannan cikin girmamawa ya gaidashi. Ba tare da ya amsa gaisuwar tashi ba yace “I’ve waited for you, for six minutes!” Arshaad zai yi magana Granpa ya katseshi ta hanyar mik’o mishi wasu takardun. Karb’a yayi ya fara dubawa…… Cikin no nonsense voice d’inshi yaji Granpa d’in yana cewa “3 days ago mun samu embezzlement, ko kuma in ce theft from an insider, munyi ta bincike da ni da Auwal at long last mun gano waye!” Dai dai nan idanun Arshaad suka kai kan abunda takardar ta k’unsa! Gabanshi ne ya hau fad’uwa babu k’akk’autawa! Naira miliyan dubu d’ari tara ne suka b’ata! Kuma shine yayi signing, gashi kuma a d’ayan takardan an nuna ya shiga personnel account d’inshi!. Da sauri ya d’ago ya kalli Granpa a mugun firgice yace Grandpa, i don’t know anything about this! Maybe mistake ne ko kuma someone is trying to frame me, amman wallahi i have no clue......” Kura mishi idon da yaga Granpa yayi ne ya sanya shi yin shiru. Cikin kakkausar murya Granpa yace “Who’s trying to frame you? Um? Ni ko Auwal? Use your words! Dan mune muka yi binciken, just the two of us!.” Shiruuu, Arshaad yayi ya sunkuyar da kanshi k’asa. Granpa yaci gaba da cewa “For your information nayi suspending Auwal d’in kanshi for a week! Did you know wat he did?? I ask him to investigate, and after he finds out kai ne b’arawon he hid it from me! Bawan Allah n nan was even trying to pay back the money from his own pocket duk dan kar in gane kaine mu samu matsala da kai….” Da k’arfi Arshaad ya runtse idanunshi, har ga Allah Auwal fa ya fara kaishi mai’ura da makirce makircensa! Shi da yake a matsayin MD amma wai yana yi mishi bak’in cikin treasurer d’in da aka bashi! For wat!?? Sai kace ba y’an uwa suke ba? Maganar Granpa ne ya dawo dashi daga tunanin daya fad’a jin yana ce mishi “take this!” Hannu Arshaad yasa ya karb’a jikinshi duk yayi sanyi. Mik’ewa Granpa yayi ya gyara suit d’in jikinshi, sannan ya fara tafiya yana dogara sandarshi, sai da ya kai bak’in k’ofa ya juyo ya kalli Arshaad Sai a lokacin yaga bai ma duba takardarba, yana nan tsaye yadda ya barshi ya lumshe idanuwanshi… Bud’e k’ofar Granpa yayi sannan yace mishi “the door is open and ranar Monday zamu fara zaman kotu da kai!” Da sauri Arshaad ya kalleshi sai kuma ya hau duba takardun hannunshi, ta farkon takardar kora ce ta biyun kuma takardar sammaci ce!. Da sauri ya k’araso gaban Granpa yace “Granpa pls i ....” “OUT!!” D’in da Granpa yace mishi da k’arfi ne ya sakashi saurin yin shiru dan yaga alamar kamar ran Granpa ya soma b’aci dan haka kawai sai ya yanke shawarar tafiya…. Jiki a mugun sanyaye ya sa kai ya fice daga office d’in! Yana fita yaga Granpa ya d’aga sandarsa ya buga a jikin k’ofar dai dai inda glass d’in da aka rubuta sunanshi yake ‘Muhammad Arshaad Yahaya MT’ Nan take sunan ya tarwatse ya zube a k’asa. Da sauri Arshaad ya juya ya fara tafiya da sauri…. Bai tsaya a ko ina ba sai a bakin motarshi, yana zuwa ya bud’e ya shige ya kunna ya bata wuta… Ikon Allah ne kawai ya kaisa gida, saboda uban gudun da yake zubawa. Yana yin parking ya fito ya nufi gidansu Auwal.. A parlourn farko yana shiga ya hango shi a bakin kitchen da cup yana kurb’a da waya a hannunshi! Gadan gadan yayi kanshi yana zuwa ya zuba mishi naushi! Auwal bai ga shigowar mutum bama, kawai naushin da aka yi mishi yaji wanda yayi sandiyyar fad’uwar waya da cup d’in dake hannunshi da kuma fashewar hancinshi. Jikin bango ya kama dan sauran kad’an ya shima d’in ya zube k’asa! Sannan da sauri ya d’ago dan ganin waye… Suna had’a ido da Arshaad kawai ya kwashe da wata mahaukaciyar dariya har da rik’e ciki! Arshaad bai kula shi ba sai da ya barshi ya d’an tsagaita tukunna yace masa “why? And how do you do it??” Murmushin gefen baki Auwal yayi sannan ya lakato jinin da yake bin hancinshi wanda ya sauko har kan k’irjin shi, kallon jinin yayi kafin ya gogawa Arshaad d’in a daidai kan kirjinshi wajen heart d’inshi, sannan yace “Na tabbatar zafin da nake ji a face d’ina da jinin dana zubar bai kai wanda kake ji anan ba” Buge mishi hannu Arshaad yayi kafin yace “ I don’t have time for this, just tell me, me nayi maka haka? What do you want from me?”. Murmushi Auwal ya sake yi kafin yace “Yanzu kam i want nothing from you, a time d’in da nake neman abu a wajenka ai k’in yi mini kayi. Kai ka san waye ni bana mantuwa kuma bana yafiya! Zaka iya tuna ranar da Khadija tazo wajenka akan kayi mata signing ka k’i yi!? A time d’in I called you Arshaad a whole me ina a matsayin MD nace maka kayi signing d’innan, I’ll explain later amman saboda taurin kai irin naka da kuma son kayi proving wasu silly principles d’inka ka k’i yi! A whole me ace wai in saka ka kayi abu amma ka k’i yi! Who do you think you are??” Da mamaki Arshaad yake kallon Auwal, kafin yace “Yanzu saboda wannan ne kake son lalata mini image da carrier da future d’ina gaba d’aya? Auwal Granpa ya kai ni court!! I’ve been sued by my own family for theft!! wanne company ne kake tunanin zasu bani aiki da wannan pent d’in da kayi mini??”. Gyara tsayuwanshi Auwal d’in yayi kafin yace “Actually Arshaad maganan court was my idea, although ban fad’awa Grandpa direct ba kawai dai na bashi labarin wani Abokina da yayiwa mahaifinshi haka shikuma Mahaifin nasa ya kaishi court! That’s all i said i was hoping yayi same thing to you, and look! He did!!” Ya fad’a yana murmushi kafin ya ci gaba da cewa “Arshaad!!you should have known me by now, bana son shishshigi…actually akwai abubuwan da kayi mini dayawa a company d’innan, tun dawowarka da aka baka position d’inka shikenan ka saka mini ido dayawa, I’m the MD bai kamata ka dinga bin al’a’mura na ba amman kwanaki har investigation ta k’ark’ashin k’asa kayi mini. Duk wasu abubuwan da kake yi ina sane da kai. I warned you twice amma baka ji ba! A tsarina bana maimaita magana sau uku… Da Khadija ta zo, na kiraka nace kai signing mata, ko nawa ne zasu fita ta acc d’in company Ina ruwanka?? amma still u refuse. On a serious note Arshaad nayi tolerating Dinka more than yadda nake tunanin zan iya ma. And you should stop saying wai nayi tarnishing image naka akan small thing cos this is not a small thing to me, remember i hate nonsense, and small thing su suke komawa manya shiyasa nayi deciding in yi dealing with you now!.” Yana gama fad’in haka ya juya har ya d’an yi gaba sai kuma ya sake juyowa yace “sai mun had’u a court, i‘ll make sure na kawo wasu takardun da zasu sake girgiza ka!! Don’t underestimate the power of your MD, wannan ma ina baka san ya aka yi suka fito ba ko?” Bai jira jin me Arshaad d’in zai ce ba ya ci gaba “A daa abokin fad’a ne da kai! Yanzu kam you’ve made an enemy that too a powerful one so be afraid!!” Yana gama fad’in haka yayi hanyar sama ya kyale shi a wajen…. A hanyar main k’ofa na shigowa ya hango Mom da alamun yanzu ta shigo amman tabbas taji komai dan da mugun mamaki take kallon shi, d’an takowa tayi tana lek’a inda Arshaad d’in yake taga bai juyo ba har yanzu, Yana ganin ta matso kusa dashi da alamun tausar shi zata yi a take ya b’ata rai yaja d’an gajeren tsaki kafin k’asa kasa ciki b’acin rai yace “What a terrible timing u have! duk inda ake abunda bai kamata ki sani ba sai an ganki a wajen!! Anyways it’s on u, cos I’m not gonna change or do anything for you. Kece kika ce inyi k’ok’ari nayi winning MT and that’s wat i’ve been trying to do.” Yana gama fad’an haka ya wuce yayi hanyar stairs d’in side d’inshi. Mom bata so Arshaad ya ganta a wajen, amman shock d’in da Auwal ya bata ya sa ta daskare a wajen ta kasa matsawa… Gaba d’aya kullum Auwal sake rainata yake yi kamar kashin gindinshi, why?. Tana a haka har bata san Arshaad d’in ya k’araso ba, sai muryarshi taji yana gaisheta. Da kyar ta iya amsawa tana tunanin yadda zasuyi da Mammy idan case ya fito…ta san Mammy k’awar ta ce amma yadda take son Arshaad ko uwarta fad’a suke yi da ita akansa… Amsawa tayi cikin basarwa da nuna kamar bata ji conversation d’inshi da Auwal ba. Arshaad kam bai ma wani lura ba ya wuce dan duk jikinshi a mace yake, sannan har ga Allah bai san ta ina zai fara zaman court da Granpa da Auwal ba!!… Mom kuwa ta dad’e a wajen tana lissafin nemo yadda zata b’ullo wa alamarin, ganin bata da wata mafita ya sanya kawai ta hak’ura ta wuce d’akinta tana mai jiran k’arasowar Mammy dan ta san tana hanya muddin zancen yaje kunnenta....... BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 25 Jiki a mace haka Arshaad ya shiga gida, bai tarar da kowa a parlour ba, dama kuma hakan yake hoping dan ya san in dai Mammy ta ganshi a wannan situation d’in to sai ta fahimci yana cikin matsala, kuma ta dinga tambayar shi kenan, shi kuma a halin yanzu baya buk’atar yin magana ma, he just need rest, peace and quite!. A haka ya k’arasa side d’inshi ya wuce bedroom, yana shiga ya fad’a kan gado rigingine yayi pillow da hannayenshi ya lumshe ido ko takalmin k’afarsa bai cire ba. Ya dad’e a haka, tukunna ya zaro wayarsa daga aljihu ya shiga contacts ya fara scrolling, yana zuwa kan ‘bff’ yayi dialing da alamun daman number yake nema… Bugu uku a na hud’u aka d’auka! Wata murya very calm cike da jarumta da dad’in sauraro mamallakinta yayi amfani da ita wajen cewa “Assalam alaika!” Nannauyar ajiyar zuciya Arshaad ya sauk’e kafin yace “Ameen, wa alaika assalam. Ya aiki?” “Alhamdulillah, wats up!?” Aka ce daga d’ayan b’angaren. “A lot!” Shine abinda Arshaad yace, sannan cikin nutsuwa ya hau kwararo mishi bayanin yadda suka yi da Granpa da Auwal d’azun, da kuma zancen shiga kotu!… Shiruuu, kowannen su yayi bayan Arshaad ya gama bayani. Chaan!! daga d’ayan b’angaren akace , “I’m coming home this Sunday, in sha Allah.” Da k’arfi Arshaad wanda a take yaji kusan 70% na damuwarshi ya kau, yace “Really?? Woow!” Sai a lokacin ’ASLAM’ yayi murmushi, sannan yace “Yeah really, Bro. I was planning nayi surprising naku gaba d’aya, but naga u need something to brighten up your mood, so i have no choice but to tell u.” “U really did brighten up my mood kam. Allah ya kawoka lafiya and i also have a surprise for you.“ Cewar Arshaad. “Ok, sai na zo d’in in sha Allah.” Cewar Aslam, har zai kashe wayar sai kuma yace “karfa ka gayawa kowa, remember it’s a surprise.” “Yeah i won’t, i promise.” Shine abunda Arshaad yace yana murmushi. D’an tattaunawa suka yi akan case d’in da Auwal ya had’a, bayan sun gama Arshaad yayi mishi godiya sannan yace “bara ya barshi ya ci gaba da aiki.” Dan ya san maybe abunda yake yi kenan ya tsayar da shi. Shiruuu, Aslam yayi bai kashe ba kuma bai yi magana ba….chaan! Ya sauk’e ajiyar zuciya sannan yace “how is she??” Lumshe ido Arshaad yayi a hankali, sannan ya bud’e su kafin yace “She’s fine, sai ka dawo.” Fahimtar da Aslam yayi k’ok’arin hanging up Arshaad yake son yi yasa da sauri yace “No, pls wait!”. Shiruu, ne ya sake biyo baya chan Aslam d’in yace “Tayi maganata? Did she ask about me? Dan Allah ka gaya min gaskiya.” Gaba d’aya zuwa yanzu Arshaad ya fara regretting kiran sa d’in da yayi! Wani yawu mai mugun d’aci ya had’iye da kyar kafin yace “A’a! Amman tana.....” ‘Kit!!’ yaji an yanke kiran… Da k’arfi Arshaad ya runtse idanunshi tare da damk’e hannunshi kamar zai yi boxing! Ya fi minti biyar a haka tukunna a hankali ya fara bud’e idanuwan nashi da suka sauya kala tukunna ya samu ya iya janye wayan daga kunnenshi… Yana mugun jin tausayin Yayan nasa, da ace yana da yadda zai yi to da ko nawa ne zai biya in iyakar kud’in shi kenan to zai biya ya yaye mishi wannan damuwar!. Duk fad’in duniyar nan ko wajen Mammy yaje bata samo mishi solution d’in problems d’inshi amma minti goma yayi yawa Aslam zai nema mishi solution d’in matsalar shi ko wacce iri ce. But shi gashi matsala guda d’aya tak! Wadda ya taso ya ganshi a cikinta sam ya kasa taimaka mishi… Gaba d’aya Arshaad sai ya fara jin haushin kanshi… Haka nan ranshi babu dad’i yana zaune har aka yi kiran sallar Magrib! Toilet ya wuce yayi alwala, ya fice zuwa masallaci.. Bai dawo d’akin ba sai da yayi Sallar isha. Yana shiga ya fad’a toilet bai dad’e ba ya fito d’aure da bathrub kanshi yana digar ruwa da alamun wankeshi yayi… Tsadaddun mayuka da turarrurruka yayi amfani dasu wajen shafe jikinshi, sannan ya nufi wajen kayayyakin shi ya d’auko wani three quarter wando cream colour, da wata armless riga itama cream mai ratsi ratsin red a jiki ya saka, kayan ya mugun karb’ar shi, yayi kyau sosai. Bai damu ya tsaya taje sumar tasa ba, ya d’auko wayar shi. Kunyar kiran Ummu yake yi amman ba yadda zai yi, tun d’azu yaketa daurewa akan ya bari sai gobe su had’u amman ya kasa. Dialing number Ummu yayi yana adduar Allah yasa Sakina ce zata d’auka ta yadda cikin sauk’i zata had’ashi da Huda. Adduar shi kam bata amsuba dan ana d’aukar wayar ya gane Ummu ce “Assalama alaikom, Arshaad ya gida.” Ummun tace “Lafiya Alhamdulillah Ummu ina wuni.” “Lafiya k’alau ya su Maman ka?” “suna lafiya kowa lafiya.” Sai kuma yayi shiru, kafin yace “ya su Sumayya?” Nan take Ummu ta gano shi, hakan yasa tayi murmushi kafin tace “Sumayya lafiya k’alau, su Huda kam da Sakina d’azu sun bi Mama datazo tafiya sai jibi zasu dawo. Kana da number Maman ko?”. Kamar yana gabanta haka ya hau sosa kai, yana sunkuyar da kai sannan yace “Eh, ina da shi.” Murmushi ta sakeyi sannan tace “to a gaida mutan gidan Arshaad, mun gode sosai.” “Tam zasu ji, in sha Allah sai da safe.” “Mu kwana lafiya.” Ummu tace, sannan ta kashe wayar, tana murmushi da mamakin kunya irin ta Arshaad ! Shi kam wannan shi ya cika cikakken bafulatani, ta san sarai ba zai tab’a kiran Mama a yau ba, tunda ya lura ta gano shi, talkless of ya nemi magana da Huda. Mikewa tayi ta nufi kitchen ta d’auko tray ta isa dining…. Tun d’azu take jiran Baban Sakina ya fito suci abinci, amma yana dawowa a sallah ya shige ciki har yanzu shiru. Dan haka ta d’aba musu abincin ta d’aura a tray ta wuce d’akin shi. Sai da tayi knocking ya bata izinin shiga tukunna ta shiga da sallama. A kan gado ta hangoshi ya kwanta rigingine, yayi pillow da hannunshi d’aya d’ayan hannun kuma ya dafe goshinsa da shi. Kan tebur d’in d’akin mai d’auke da kujeru biyu da suke d’an gefen gadon kad’an taje ta ijjeye sannan ta dawo bakin gadon kusa dashi ta zauna. A hankali ya juyo ya kalleta kafin ya k’ak’alo murmushi sannan ya mik’e ya zauna ya kamo hannunta duka biyu a nashi hannayen bayan ya gyara zama ya fuskanceta. Itama murmushin ta mayar masa sannan tace “kazo muje kaci abinci.” Bai musa mata ba ya mik’e suka nufi inda ta ajjiye abincin… Sai da suka gama ci sannan tace “Me yake damunka? Naga kamar kana cikin damuwa.” B’oyayyiyar ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace “ba komai, aiki ne kawai, an ma yi settling. Kawai dai ina wasu y’an lissafe lissafe ne.” Ummu kwata kwata bata gamsu da amsar daya bata ba, amman gudun ja inja da zargi a tsakaninta da Mijin nata yasa kawai ta kawar da zancen ta kawo wata hirar.. Sun d’an jima suna hira kafin yace mata “D’azu Arshaad ya same ni akan yana son ganin Mahaifin Huda.!” Da sauri Ummu ta d’ago tana kallonshi. Ganin hakan yasa yaci gaba da cewa “Ban b’oye mishi ba, na fito na fad’a mishi cewa ‘an samu matsala tsakanin kakanninta na wajen uwa da mahaifinshi dashi kanshi Mahaifin nata, yanzu dai Huda a hannunmu take. Nayi matuk’ar mamaki da Arshaad ya gaya mini cewa ‘iyayensa zasu amince da auren ko da babu Mahaifinta!’.” Murmushi Ummu tayi kafin tace “Ai fa Baban Sakina ba koina ne aka taru aka zama d’aya ba! Inaga shi nasa dangin in dai suka bincika suka ga tarbiyyar Yarinya kuma suka tabbatar babu wani mugun abu a kanta ai dan dai fad’an iyaye ba sai sunbi diddigi ba, shiyasa yace maka ba matsala, danginshi basu da zafi kenan tunda kaji ya fad’a maka hakan!” Jin yayi shiru yasa Ummu ta sake cewa “Ko?” “Um, yes! maybe.” Shine abunda Baban Sakina yace da alamun hankalinshi baya gareta… A hankali ta d’an matso ta sake cewa “Kayi bincike sosai ko, i mean a kan shi Arshaad d’in.” “Eh, nayi sosai, ba wata matsala fa.” “Alhamdulillah” shine abunda Ummu tace sannan ta cigaba da cewa “ina so ma inje wajen Maman shi, inyi mata godiya akan yadda Aaima da Arshaad suka yi ta d’awainiya da Yaran nan.” K’ura mata ido Baban Sakina yayi har sai da ta d’an sunkuyar da kanta, kafin ahankali yace “Ki bari ba yanzu ba tukunna ko?” Sannan ya d’aura da cewa “Yanzu dai a halin da ake ciki yana buk’atar zuwa wajen su Madu ne, dan yace mini in dai suka gama daidaitawa da ita Hudan to baya so auren ya d’auki lokaci mai tsayi.” Murmushi Ummu tayi sannan tace “Allah ya tabbatar mana da alkhairi, abun nan yayi min dad’i Baban Sakina, ko ba komai hankalin Mama da ita kanta Hudan zai kwanta zata rabu da masifar su Sadiya, ita kanta Mama kullum fargabarta kar a aurawa Huda Junaidu, to dai yanzu babu wannan zancen, tunda gashi Arshaad zai ruga Junaidun zuwa. Murmushi Baban Sakina yayi sannan yace “Kuma yace min maganar karatu har sai tace bataso, duk inda take so shi kam zai kaita tayi.” “Alhamdulillah” Ummu tace cike da farin ciki sannan ta k’ara da cewa “Yaron nan d’an albarka ne, Allah ya tabbatar da alkhairi sannan Allah ya had’ata da surukai na gari inda zata huta ta samu cikakken kwanciyar hankali da kulawar da bata samuba a baya…” A hankalii Baban Sakina yace “Ameeeen” Tattaunawa suka d’an yi kafin Ummu ta mik’e ta hau tattare kwanukan tana mai cewa “bara inje in sanar da Mama, yaushe kace mishi yaje wajen su Kakan? Ko sai an tuntub’e su tukunna anji?” “Eh” kawai yace mata daga haka ya mik’e ya nufi toilet ita kuma ta k’arasa kwashewa ta fice tanata murna....... Arshaad yana kwance da waya a hannunshi….yayi dialing number Mama ya kashe before ya fara ringing yafi sau biyar! Yana cikin wannan yanayin ya fara jiyo sallamar Aaima a falonsa hakan yasa ya ajjiye wayar ya mik’e ya fita. Kusan karo suka yi a k’ofar d’akin, tana k’ok’arin fara knocking. Baya taja tana cewa “ai na d’auka ma kayi bacci.” Girgiza mata kai kawai yayi alamar ‘a’a’ sannan ya wuce cikin parlourn, kujerar 3 seater ya nema ya zauna, kusa dashi Aaima taje itama ta zauna sannan ta fara gaidashi.. A hankali ya amsa yana mai dafe kan shi daya ji yana neman fara ciwo. A hankali cikin kulawa tace “Ya Arshaad baka da lafiya ne?” Jinjina mata kai yayi sannan yace “it’s nothing serious kawai kai nane ke min ciwo.” Da sauri ta hau tambayr shi “tun yaushe, mai ya faru ,ya sha Magani??” Ganin yadda duk ta rud’e ne ya sanya yayi murmushi kafin yace “Yanzu auta wacce tambayar kike so in fara amsa miki, um?” D’an murmushi tayi kafin tace “Yaya to baka da lafiya kuma sai ka na zaunawa a d’aki? Na tabbatar ko Mammy ma baka gayama ba, tunda yanzun nan muka rabu da ita tana tambayata ‘kana Ina?’.” Murmushi ya sake yi sannan yace “Ban sha magani ba tukunna sai nazo bacci. Mammy kuma bana so ta ganni a situation d’innan ne, sai mun gama settling in shaa Allah!” Sai da ya furzar da numfashi tukunna ya ce “d’an k’awarta ne ya kunno min wuta! Banaso mu zama silar b’ata musu friendship. Idan munyi settling before Monday tou Alhamdulillah, in kuma bamu yi ba, i don’t know ya abubuwan zasu kasnce gaskiya.” A hankali Aaima ta ke kallon shi sannan tace “Fad’a kuka sake yi kai da Ya Auwal??” Arshaad bai b’oyewa Aaima komai ba, nan ya hau gaya mata yadda sukayi kamar yanda ya gama fad’awa Aslam d’azu. Allah sarki Aaima har da kukanta! Da kyar ya iya lallashinta tayi shiru kafin yace “in shaa Allah ba za muje court d’inba, kud’in suna accnt d’ina, although i don’t know tayaya suka shiga kuma ko alert ban gani ba sai da nayi checking balance tukunna na gansu. Zamu je mu samu granma mu bata kud’in ita kuma ta bashi ta taya mu kuma bashi hak’uri, Allah yasa ya hak’ura.” Cikin sake share hawaye tace “Allah ya isan ka Ya Arshaad, ban san mai yasa Ya Auwal yake wannan abubuwan ba.” Murmushi yayi kafin yace mata “MT mana! Saboda kud’i ne Aaima, duk dan kud’i ne, so yake ya had’e komai, sannan ya zama superior akan kowa, ta yadda za aga capability’s d’inshi a mallaka masa MT! Nothing more than that. Shiyasa idan ya ga wani yana shirin yin sama a company d’in ko kuma yana k’ok’arin ganosa yakeyin sauri ya had’a mishi tuggu, just like wat he did to me! Da idona fa naga ya saci more than 5 hundred million a cuwa cuwa da wasu ways d’inshi! Bana son issue shiyasa kawai nayi shiru…” Da sauri Aaima tace “to ai Ya Arshaad kaima da sai ka fad’a kace ga abinda yayi” Murmushi kawai Arshaad yayi sannan yace “You know what Aaima, just forget all this, let’s talk about reason d’in da yasa na kiraki. D’azu da muna dawowa, you look disturbed Mai ya ke damunki?” Shiru tayi ba tare data bashi amsa ba ta fara wasa da y’an yatsunta tana kallon k’asa. Gaba d’aya nutsuwarshi ya tattaro kafin yace “i just finish sharing my problems with you, ki fad’a mun ko mene yake damunki, ko kina da wanda zaki fad’ama apart from me and Aslam??” A hankali ta girgiza kai kafin ta zayyano mishi halin da suke ciki itada Auwal…. Shiru yayi yana kallonta for some minutes, kafin yace “Do you love him?” Shiru tayi hakan yasa ya fahimci amsar ta! Sai da ya sauk’e ajiyar zuciya kafin a hankali yace “Aaima kiyi ta addua nima zan taya ki, Allah ya cire miki sonshi a rai. Auwal ba Mijin aure bane ba. Not because of wai bana shiri da shi yasa bana son aurenku Not at all! Kinga na farko Auwal bai san mutuncin mutane ba, both Babba da Yaro, hatta mahaifiyar shi baya ganin girmanta! All that matters to him is money, dukiya da abun duniya, kuma zan iya rantse miki ba abunda ba zai iya aikatawa ba domin ganin ya tara. Secondly, humanizer ne first class, yanzu haka a company d’innan inda muke ni da shi, za a iya samun mata morethan five da za suyi testifying haka a kanshi. The last and worst shine bai damu da addiniba dan zan iya ce miki tun dawowa ta daga Dubai ban tab’a had’uwa dashi koda a hanyar masallaci ba! Sannan munafuki ne, ke kin san haka dan tun muna Yara abunda ya fara had’ani fad’a da shi kenan, Auwal ya kan shiga tsakanin d’a da mahaifi ya had’a su fada na har abada.. Idan nace zan tsaya lissafo miki munanan halayenshi zamu jima anan, all I’m saying is ki yi k’ok’arin rabuwa dashi kuma kiyi ta addua Allah ya yaye miki sonshi saboda Aaima is not the type of man da nake miki fatan kiyi spending the rest of your life with, ba.” Aaima, ita kam waennan halaye na Auwal sun sake tabbatar mata ba sonta yake yi ba, wato yana tare da ita ashe yana chan da wasu y’an matan amman kullum k’arya da yake shirga mata ‘Bashida kowa sai ita’ A hankali tace “in sha Allah, Yaya.” Dan ita kam har ga Allah ko son Auwal zai kasheta ta fita a hanyar shi kenan har abada m. She can’t live with this type of man as a husband… Arshaad ne ya katse mata tunani ta hanyar cewa “Sai maganarmu ta biyu, it’s about Huda.” Da murmushi ta d’ago tana kallonshi kafin tace “what about her?” Murmushi yayi sannan yace “kin san taste d’inta? As in abubuwan da takeso. Ina so in d’an yi mata shopping ne, kuma Ina son siya mata waya.” Murmushi Aaima tayi sannan tace “Tou na farko dai tana son perfumes, da abaya da rings and her favorite colour is blue, irin royal blue d’innan. About the phone kuma ko jiya da taga wayana sai da tayi ta yabawa tana cewa wayan yayi kyau, tun ranar farko data fara gani time d’in munje musu visiting tayiya juya wayan ta dinga game tana kallon pics, tace min ya burgeta sosai.” Kallon wayan Aaima yayi mai k’irar iphone 12 mini kafin yace “Aiit, shikenan iya abunda takeso? Abaya perfume rings is that all?” “Gaskiya i think shine dau abunda tafi so but u can add abunda kaga ya kamata, ko?” Cewar Aaima. Hamma Arshaad yayi kafin yace “No p. Gobe In Allah ya kaimu sai ki rakani muje muyi mu kai mata ko?”. “Owk” shine abinda Aaima tace tana murmushi. Mik’ewa Arshaad yayi yana mik’a sannan yace “Sai da safe bacci nake ji.” Sallama itama Aaima tayi mishi….har zata fita sai kuma ta juyo ta ce “Ya Arshaad ka samu lawyer ne? Naga baka wani shiri, gashi ance Monday.” Murmushi yayi sannan yace zan ga lawyer, Aslam yace zai yi mishi magana so zan ganshi gobe around 11 na dare. In sha Allah ma ba za’a shiga court d’inba, ki dai taya ni da addua.” “In sha Allah” Aaima tace, tana kallonshi har ya shige bedroom sannan itama ta juya ta fita ranta ba dad’i duk tayi laushi tanata tunani.. A Haka ta fito daga corridor d’in side d’in nasa. Kwata kwata hankalinta bai kai kan main parlour ba, ta nufu hanyar staicase d’in da zai sadata da side d’inta. Muryar Mammy ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin da take, jin tana cewa “Ke Aaima wai bakya ji ne? Tunanin me kike tayi ne haka?“ Da d’an k’arfi. Da sauri ta juyo….da kyar ta iya janye idanunta da suka sark’e cikin na Auwal wanda ya wani hakimce akan kujera gefen Mammy yana binta da kallo. D’auke kai tayi sannan ta k’arasa cikin parlourn ta nemi waje ta zauna a ranta tana mamakin guts irin na Ya Auwal! Despite abunda ya yiwa Ya Arshaad kalla yadda ya zo ya baje a parlourn su yana hira da Mammy tsabar tsaurin ido! Wata zuciyar ce ta hau tunzurata ta fad’awa Mammy halinda ake ciki, sai kuma ta tuna da Anty Adama, da kuma yadda shima Ya Arshaad d’in yayi shiru yana hoping a yi settling case d’in b4 Monday..kar taje ta had’a gurmi kuma azo case d’in ya mutu amman fad’a tsakanin iyayensu bai mutu ba…. Muryar Mammy ce ta dawo da ita daga wannan tunanin jin tana cewa “Auwal gaskiya tou akwai matsala tattare da Aaima, bafa jin ka takeyi ba, ke wai me yake damunki ne? Ina Arshaad d’in yake? Daga fitowa daga wajenshi duk kin yi sanyi haka sai tunani? lafiya dai yake ko? Umm bara dai inje In ganshi kawai.” Mammy ta k’arshe maganar tana mik’ewa direct ta nufi hanyar side d’in Arshaad, ko Aaima wadda take ce mata “he’s fyn” bata tsaya sauraraba. Mammy tana shigewa Auwal ya taso ya zo kan handle d’in 1 seater n da Aaima ta ke zaune a kai, ya zauna. Yana zama tana mik’ewa da sauri ko bi ta kanshi bata yi ba ta wuce tayi hanyar sama… Da sauri ya sha gabanta yana k’ok’arin kallon kwayar idanunta amman tak’i bashi had’in kai. Hab’arta ya kama da k’arfi ya d’ago fuskarta har sai da tayi Kara kafin yace “Ban son raini, wannan attitude d’in fa?” Dukkan k’arfinta ta saka ta buge mishi hannu itama sannan tace “Out of my way, zan je d’aki, i have better things to do!!” K’ura mata ido yayi na y’an mintuna chan taga ya fashe da dariya har da d’an rik’e ciki. Sai da ya d’an tsagaita sannan ya d’ago yana kallon hanyar side d’in Arshaad yana murmushi yana shafa lallausan sajenshi a hankali yace “Arshaad! Arshaad!! hmm..” Kafin ya juyo ya ce mata “ya min spilling beans ko? Me yace?” “Ban sani ba!” Shine abunda Aaima tace sannan ta yunk’ura zata wuce… Da k’arfi yasa hannu ya fisgota ta dawo gaban shi kafin yace “bamu gama maganaba dan haka you are going nowhere, idan kina so ki tafi you better drop this attitude and talk!!”. Ya k’arashe maganar yana mai had’e rai. Mamaki kawai take yi yadda ya juye mata lokaci d’aya kamar ba Auwal d’inta mai lallab’ata ba. Tabbas ta kusan tafka babban kuskure a rayuwar ta, Allah ya taimaketa data farga da wuri! Kwallar da taji tana shirin zubo mata yasa ta ja vail d’in doguwar rigarta ta hau k’ok’arin sharewa. Binta ya fara yi da kallo from head to toe… chaaan! Ya ja akiyar zuciya ya sauk’e sannan a hankali ya matso ya dafa kafaf’unta yace “Baby this is all your fault…kiyi hak’uri to na fisgo ki kinji don’t cry, unhm?” D’aga kai kawai tayi ba tare da tace komai ba. Ahankali ya saki wani killer smile sannan yace “yauwa dear. To yanzu about that kiss” Ya fad’a yana kallonta da murmushi a kan fuskarsa.” Da sauri ta d’ago tana kallon shi, a zuciyarta taji tabbas it’s about time da ya kamata ta yiwa Auwal wankin babban bargo dan ta lura bayan mugayen halayenshi har da tab’un hankali ma yana damunshi. Sai da tayi murmushi sannan tace “It’s clear abunda kake so daga wajena, Auwal ya kamata ka farka ka daina deceiving d’in kanka, dan ba sona kake yi ba wallahi!! Kuma abunda kake buk’ata daga wajeni ni Aaima ba da niba! Mai zai hana ka tafi wajen y’an matan ka, i’m pretty sure za suyi maka wanda yafi wannan without any hasitation, and please kar ka sake shigowa gidan mu, tunda har zaka iya yiwa Ya Arshaad abunda kayi to i don’t think kayi deserving any love or kindness from his family, and yes Allah zai fitar dashi daga tuggun daka had’a mishi… Ka sani mai gaskiya kullum shine a sama!! Look at u, akan abun duniya you have turned into a monster, baka da aikin daya wuce ka had’a wannan da wannan ka had’a wanchan da wanchan duk saboda kud’i! Alhamdulillah! Mu ba wannan ne a gaban mu ba. And one more thing Allah ya isa na deceiving d’ina daka dinga yi, i tot you love me truly ashe kai chan wani shirme ka kake tunani… I’m like a sister to you, so ba zan ce maka na tsaneka ba but inaso ka ajjiye wannan at the back of your mind ‘ko ni da kai kad’ai muka rage a duniyar nan ba zan had’a ko wanne irin relationship da kai ba!’.” Tana kaiwa nan ta watsa mishi harara sannan ta ce “Humanizer irin ka.” Da mamaki yaketa kallonta tun lokacin data fara magana tana dasa aya ya hau tafi!! yayi kusan sau hud’u sannan yace “What a great speech, Aaima. Hope you are done saboda now it’s my turn. Abu biyu kawai zan iya fad’a miki yanzu First You are right, bana sonki, you are not my type, sometimes idan muna zance ji nake kamar inyi kuka tsabar takaici, kawai daurewa nake yi, ke to be sincere ni ko irin soyayyar y’an uwan takan nan ma bana yi miki!! Dan haka don’t even think of wai kinyi rejecting d’ina ne Aaima i never loved u you day one….kuma kin da wayo fa for that i salute u sannan Allah ya taimakeki da kika gano gaskiyar lamari, and Yayanki shima yayi playing role wajen ceton rayuwarki because i was planning in yi using naki ne sannan nai dumping saboda Ina so in koyawa Yayanki hankali akan takura min d’in da yake yi. Abu na biyu Kinga ba sonki nake yi ba ko? But abunda Arshaad yayi min ya min ciwo, so ga sak’o inaso ki bashi from me to him, yadda ya rabani dake to kar ya bari in had’u da girl d’insa.” Yana gama fad’an haka ya juya fuuu, ya fice kamar zai tashi sama. Aaima a wajen ta tsugunna ta fashe da kuka, so kawai all this time yana kallontane as a fool?! Sai kuma ta fara maimaita ‘Alhamdulillah’ da Allah ya tseratar da ita. Gabanta ne ya fad’i da ta tuna da abunda ya gama fad’a a kan Huda yanzun, a hankali tace “Allah yasa kar ya yiwa Huda komai.” Tana gama fad’in haka ta mik’e tana goge hawayenta wanda hakan yayi dai dai da fitowar Mammy daga side d’in Arshaad. Salati Mammyn ta saka sannan ta k’araso wajen Aaima ta rik’eta tana “Me yake damunki? wani abun ne ya had’a ki fad’a da Auwal d’in? Mai ya faru???” Murmushi kawai Aaiima tayi kafin tace “ba komai Mammy abune fa ya fad’a mini cikin ido.” Cikata Mammy tayi sannan tace “ke wallahi zan ci Uban ku! Daga ke har Arshaad d’in shima tun d’azu nake ta fama dashi akan ya fad’a min damuwarsa sai k’arya ba komai yake min kuma kina ganinshi kin san yanada matsala! Sannan kema yanzu kin ce min ba komai, kunada wata uwar da ta fini ne??” Share hawaye Aaima tayi tace “Mammy ba komai fa, dan Allah kiyi hak’uri, zan je in kwanta kaina ke ciwo.” “Ba fa inda zaki je sai kin gaya min matsalarki yanzun nan!” Mammyn ta fad’a tana sake rik’o Aaima wadda take k’ok’arin wucewa. Ahankali Aaima tace “Tou shikenan Mammy i promise zan fad’a miki, amman sai gobe da safe plss Dan Allah yanzu kaina ke ciwo.” Cika ta kawai Mammy tayi tace “Allah ya kaimu.” Da alama ranta ya baci dan fuuu ta juya ta nufi nasu hanyar staircase d’in. Sai da Aaima taga shigewarta sannan itama ta kama hanya tayi sama…. Dank’areren parlournta ta wuce ta shige bedroom wanda shima girman sa ya kusan parlour d’in, a hankali ta k’arasa k’ofar toilet ta kama handle dinner ta bud’e, sannan ta shiga…had’add’en band’akin ne mai d’auke da different wajen wanka har uku, shower normal bathtub da wani makeken jacuzzi sai wani had’add’en closet da aka warewa waje shima daban kana hangowa ta toilet d’in. Wayar ta kawai ta ajjiye a kan doguwar drawer gaban k’aton mirror d’in dake cikin toilet d’in sannan ta nufi bathtub ta fad’a ko bathroom slippers d’in dake a k’afarta bata cireba… Ajiyar zuciya ta sauk’e sannan ta sakarwa kanta showern saman bathtub d’in. Ta dad’e a haka jin mura har ya kama ta yasa ta mik’e ta fito tana d’igar ruwa, da kyar ta iya cire kayan jikinta ta d’aura towel ta fad’a gado, tana yin addua ko minti goma ba’ayi ba baccin takaici yayi awon gaba da ita....... Washegari tana fitowa zata yi breakfast a main parlour Mammy ta hau tambayarta. Gaba d’aya ta rasa ya zata yi mata, suna a haka sai ga Arshaad shima ya fito nan ta had’a su tayi ta tambaya.. Aaima ce tace “Mammy bafa wani abun bane ba, kinga shi Yaya wani d’an fad’a suka yi da budurwarshi, shiyasa kika ganshi a haka kuma k’awata ce, shine nima ya had’a dani ya min fad’a wai ai laifi nane.” Da sauri Mammy tace “Wacece wannan d’in? a ina take?” “Huda” Shine abunda Arshaad yace yana mai k’ok’arin b’alle cuff links d’inshi sannan ya k’araso yazo ya kama hannunta yayi kissing kafin yace “Good morning Mammy” “Morning, wait Arshaad Hudan dai wannan d’ayar Yarinyar da Aaima ta tab’a bani labarin an kaisu school d’insu a scholarship har tana yi musu lesson??” “Yep” Shine abunda Arshaad yace yana mai k’arasawa dining table yana cewa Aaima “hurry kin san zamu fita Ina so mu k’arasa b4 12 dan zan je kd a yau.” “Ok” Aaima tace, itama tana k’arasowa dining dan yin break fast d’in. Da sauri Mammy ta k’araso tace “Arshaad wai me yake damunka? Ka san dai ba zan tab’a bari ka auro mini Yarinyar nan ba ko?? Ke kuma Aaima munafuka ai kin san da zancen amma shine baki tab’a gaya min ba!! To bari in gaya maka!! Ka san senator Bashir ai ko? To akwai dota d’inshi takwara tace tun kuna Yara idan zaka tuna Mamanta da sirikina take kiranka, ni a tunani na you are not ready for marriage shiyasa ban fara maganar ba ashe kai kana chan ka lik’ewa y’ar da ubanta ba kowan kowa ba!! Har da wani rashin lafiya jiya a kanta saboda kun yi fad’a!! Tou wallahi ka fita a idona in ba haka ba ranka zaiyi mugun b’aci dan ba zan had’a iri da talakawa ba wallahi!!!.” Murmushi Arshaad yayi sannan ya ajjiye spoon d’in ya mike yace “Mammy Hudan is not poor, ok? She’s is very rich! Kawai dai ban san dalilin da ya sanya iyayenta suka zab’i ta tafi a scholarship ba. Please Mammy dan Allah kar muyi haka dake mana! I luv her a lot so dan Allah kar problems su fara rising daga wajenki plsss. In kikai min auren dole da wanchan Yarinyar da kike magana akai tabbas zaku samu matsala ne dake da friend d’in taki, saboda I cant take care of her daughter tunda ba son ta nake yi ba!. I need your support a kan Hudan please Mammy dan Allah.” Kallonshi ta tsaya tana yi hakan yasa ya sakar mata murmushi yace “thanks, you are the best!!” Bai jira jin mai zata ce ba ya fice yana cewa Aaima “ta sameshi a mota da wuri!”. Da ido Mammy ta bisa har ya fice! Kwafa tayi sannan ta juyo kan Aaima…. Aaima tana ganin haka ta mik’e da gudu tayi hanyar sama tana cewa “Mammy bara in shirya In je kar Ya Arshaad yayi fad’a yace na shanyashi.” Bata wani dad’e ba ta sauk’o, ta d’auro abaya da vail akan English wears d’in jikinta.. Nan ma da gudu ta fita tana cewa “kinga Mammy Yaya har ya fara jera min misscalls, bara in je in na dawo zamu yi magana.” Sarai Mammy ta fahimci dodging d’inta Aaima take yi saboda bata son tayi mata maganar. Ta so tsayar da ita amman kafin ma ta lek’a tuni har an bud’e musu gate sun fice........ BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 26 Abun duniya duk ya bi ya taru ya ishi Mammy.. Hakan yasa ta mik’e, hijab d’inta kawai ta d’auka ta nufi gidan Mom. Tana shiga kuwa kamar had’in baki ta tarar da Ummi itama a falon. Sai da ta nemi waje ta zauna suka d’an gaisa tukunna tace “Alhamdulillah! Da na sameki a nan.” Murmushi Ummi tayi kafin tace “Me kuma ya faru yanzu?” Ajiyar zuciya Mammy ta sauk’e sannan tace “Aaima da Arshaad ne! Wai ace Yaran nan har sun san su had’e mini kai suna k’usk’us a tsakanin su?” Sai a lokacin tukunna Mom tayi magana, tace “Haba Mammy, ai abin farin cikine ma ace y’ay’anka sun had’e kai, kinga bakida matsala kenan dan babu mai iya shiga tsakaninsu!” Murmushin takaici Mammy tayi kafin tace “Na san da wannan Adama, amman abunda nake so ki gane shine ‘da ace abun kirki suke k’ullawa to da sai nafi kowa farin ciki !’. Kin tab’a jin labarin wasu Yara da Aaima take gaya min Arshaad d’in ya kai ya had’ata da su?” Shiruu, su Mom d’in suka yi kamar masu k’ok’arin tuna wani abun kafin chaan! Mom tace “‘Sakina’ kamar naji tace ko? Waenda take cewa d’ayar Yarinyar tana kama da Aslam.” “Allah yayi miki albarka Adama, su dai. To wai d’ayar fa yake so, shine suketa k’us k’us d’insu. Jiya Arshaad d’in inaga har kuka yayi wai ko tak’i d’aukar wayarshi ko fad’a sukaa yi, Oho musu dai.” Ummi ce tace “amman Yaron nan anyi ja’iri! Yanzu ya za muyi da maganar Khadija?? Kin san ko jiya sai da na had’u da Mahaifiyarta a wajen gyaran farce… Tanata tambaya ta ya sirikinta harma take gaya min next week khadijan zata dawo ta kammala masters d’inta.” “Banda Arshaad ma dai da abinshi, da class d’insa da komai amma shine zai je ya d’auko mana wachchar?? Daman wallahi ni jikina sai da ya bani. A yanayin labarin Aaima kamar fa har provision shi yake yi mata lokacin da suke makaranta.” Cewar mom Da sauri Mammy tace “Kinji ko! D’azun nan kuma ya gama cemin ‘ai she’s very rich waye waye kawai dai iyayenta sunyi choosing ta tafi a scholarship ne waye waye’.” Murmushi Mom tayi tace “k’arya yake yi! Aaima ai ta tab’a bawa Auwal Labari, tace Yaran ko ishashshen turanci basu iya ba, ita ta dinga yi musu lesson lokacin tana chan…da zata tafi ma sai da ta had’asu da wasu. Waenna Yara da suka samu good foundation a makarantar kirki ne za a ce basu iya turanci ba saboda Allah?? Kawai dai k’ok’arin watsa mana k’asa a ido yake yi.” Mammy kamar zata yi kuka tace “Ni ba wannan ne problem d’ina ba, dan bai auri Khadijah ba (ya watsamin k’asa a ido) shi ya sani!! Ni babban bak’in ciki na kar ya d’auko min Yarinyar da bata waye ba! Bana son had’a jini da su kwata kwata, zuciyata zata iya bugawa! Kuma yadda yake son Yarinyar nan, in dai ya aure ta to shikenan ni da shi sai dai kallo daga nesa! Dan na san janyeshi zata yi gaba d’aya, gata kuma y’ar matsiyata na san ta dinga sakawa yana yiwa iyayenta abubuwa kenan, a gindinsu kud’insa zasu k’are!”. Murmushi Ummi tayi sannan ta dafa kafad’arta kafin tace “Ki kwantar da hankalinki, Granpa fa ba zai tab’a yarda da wannan had’in ba, kin san yadda yake.” “Um um fa! Granpa d’innan ba a gane mishi alk’ibla, kar mu dogara dashi yaje ya watsa mana k’asa a ido, mu dai nemo wani solution d’in gaskiya, dan wallahi koni naji bana son Yarinyar tun kafin a je ko’ina, kuma daga gani yana sonta over ma kuwa! Kina ji fa wai jiya har da kuka , k’ato dashi.” Cewar Mom. Ummi ce tace “na san ba a ganewa Granpa alk’ibla amman dai kin san ya fiki k’in son had’a jini da talakawa ko? Ki tuna Aisha fa.” Mom ce ta katseta ta hanyar cewa “Ai bamu gama confirming ya yanayin gidan su Yarinyar yake ba! In aka yi rashin sa’a kuma ta fito daga middle class kinga ai an gama magana, dan Granpa ba lalle ya hana ba. Kawai mu bama son Yarinyar ne, in ya aure ta akwai matsala kar ya manta da mu da uwar shi, and ke kinfi kowa sanin ulterior motive d’inmu akan aurenshi da Khadija, ko?” Shiru Ummi tayi sannnan tace “hakane kam gaskiya, to anjima ki sa Auwal ya bugi cikin Aaima mana, na san ba zata san lokacin da zata fad’a mishi komai ba.” “Bama magana da shi, amman zuwa anjima d’in ke ki kirashi ki tamabayeshi maybe zai yi.” “Me ya had’aku, har ba kwa magana?“ Ummi ta tambayeta da mamaki akan fuskarta. Murmushi Mom tayi sannan tace “ba komai, ki manta kawai wani issue ne daban” Tana maganar tana satan kallon Mammy… Ita kam Mammy gaba d’aya hankalinta baya kansu, ta tsunduma duniyar tunani….kawai zooming take yi ‘gashi har anyi auren Hudan da Arshaad, Hudan tasa Arshaad ya daina kulata, ita kuma sai bauta yake yi mata daga ita sai iyayenta! Yana ta kula da ita ‘Hudan’ baya son ganin b’acin ranta Ita kuma ‘Mammy’ an ajjiyeta a gefe. Sai da Ummi ta d’an tab’a ta tukunna ta dawo daga duniyar tunanin da ta tafi. Fahimtar yadda duk ta gigice da suka yi ne yasa sukaita k’ok’arin kwantar mata da hankali tare da alk’awarin zasu saka Auwal ya bugi cikin Aaima, daga nan sai su san abun yi. Da kyar dai suka samu Mammyn ta d’an kwantar da hankalinta. Da yamma kuwa, Auwal yana dawowa daman Ummi tayi mishi message ‘tana son ganinsa’, hakan yasa wanka kawai yayi ya nufi gidan… Bayan sun gaisa ne take gaya masa dalilin kiran “So suke yi ya bugi cikin Aaima..akwai wata Yarinya budurwar Arshaad da suka fahimci yana mugun so har Mammy yake yiwa jainja a kan Yarinyar, bayan already anyi maganarshi da Khadija! Therefore, suna son sanin gidansu da yanayin Yarinyar, daga nan sai su san abunyi.” Murmushi kawai Auwal yayi bayan ya gama ji, sannan ya mik’e tare da yi mata alk’awarin ‘in shaa Allah zai binciko musu!’. Daga haka yayi mata sallama ya fita a gidan ranshi fess!!! Yana komawa b’angaren su direct d’aki ya wuce ya d’au waya ya kira main driver na estate d’in na yanzu, dayake daman shima duk bakin su d’aya Micheal! Cikin girmamawa, Micheal ya gaishe da Auwal, nan Auwal ya zayyano mishi abunda yake so yayi mishi sannan ya kashe wayar, yana wani killer smile. A ranshi yake tunanin abunda zai yiwa Arshaad….tunda dai gashi an tabbatar mishi yana mugun son Yarinyar! Su Ummi kuma ko sun sake yi mishi maganar kawai zai ce musu ya manta ne dan bayaso su shigo case d’in ba tare da ya gama abunda ya shirya ba..... Su Arshaad suna fita a farm center suka fara tsayawa, ya na shiga direct shagon wani mutum inda yake siyan abu a wajenshi especially games ya tsaya. Yana zuwa mutumin ya dinga gaidashi yana cewa “ai da yayi waya da kawai gida za a kawo mishi” Murmushi kawai Arshaad yayi yace mishi “sauri yake yi shiyasa, sunada iPhone 12, mini?” Da sauri mutumin ya zagaya ya hau fito mishi da su birjik kala kala sabbi k’al sannan yace suna da second ma..”Da sauri Arshaad yace “No need for second!” Duk colours d’in ba suyi mishi ba dan babu blue a ciki, hakan yasa ya tanbayi mai shagon. “Eh bamu da blue gaskiya, amman akwai case blue kala kala sak wanda ka zab’a!” Jinjina kai Arshaad yayi yace “a kawo”. Colour d’in da Aaima ta gaya mishi royal blue ya zab’a mata mai mugun kyau sannan yace “a saka mishi d’aya a leda a bashi accnt number” har zai tura kud’in sai kuma yace “a kawo iphone 11 mai kyau itama da case” Nan aka bada, ya sayi sim biyu ya had’a yayi mishi transfer mutumin sai godiya yake yi, har mota ya rako shi. Suna shiga ya nuna mata wayoyin, murna sosai ta dinga yi tun bama da taga harda ta Sakina ba, ta san za suji dad’i sosai. Daga nan shopping mall suka nufa suka yi mata siyayyar duk abunda suke tunanin tana so, itama Sakina suka d’an siya mata, sannan suka fito suka kama hanyar gidan su Huda. Jikin Aaima ba k’aramin sanyi yayi ba, da taga yanayin gidan, duk sai taji tausayin Hudan ya lullub’e ta duk da kuwa cewa an mugun gyara gidan ga sabon fenti anyi wanda duk aikin Junaidu ne, business din gidan gona yake yi kuma sana’ar ta mugun karb’ar shi dan har mota ya siya da fili, yana gininshi mai kyau…. “Ya naga kin yi shiru? Nace ki d’auka ledan da zaki iya ki shiga, sai ki ce mata Ina waje.” Muryar Arshaad ta katsewa Aaima tunani…. Ledan wayoyin da wata k’arama a baya Aaiima ta d’auka ta shiga gidan… Tun kafin ta k’arasa shiga ta hango Huda na sharar tsakar gida….. a hankali ta k’arasa shiga ta ce “assalama alaikom” Hudan da taji kamar ta san muryar ce ta d’ago, ai kuwa suka had’a ido! Dariya tasa tace “Laaaa Aaima!” Wanda hakan ya jawo hankalin Sakina da take wanke wanke a bakin rijiya, itama tana ganin ta kuwa ta taso tayo wurin da sauri… Bud’e hannuwanta Aaiman tayi ta d’an kar katar da kanta tana murmushi kafin tace musu “Surprise!!” Ai kuwa da gudu suka je suka yi hugging nata sunata dariya. Mama da take a d’aki, jin hayaniya yasa ta fito tana cewa “Huda, waye ne?” ita a tunaninta ma Ummu ce ta zo.. Ganin yadda suka ruk’unk’ume Aaima suna k’ok’arin kayar da ita ne yasa Mama ta hau salati ta fara yi musu fad’a tana “meye haka, ni Maryama yaushe Yaran nan zaku girma ne? Ku cikata mana ta k’araso.” Cikata suka yi sannan ta samu ta k’araso cikin gidan. Har k’asa ta durk’usa ta gaida Mama. Da sauri Mama ta kamo ta tace “sannu da zuwa Aaima, ya gida? Yau kece kika zo mana….barka bismillah shigo.” Dariya Aaima tayi tace “a’a Mama bari dai in ajjiye mayafi na in yaso sai in taya Anty Huda aikin.” Da sauri Hudan ta b’uya a bayan Sakina tace “Kaii Aaima Allah bana so.” Murmushi duk suka yi sannan Mama tace “Ai sun ma k’arasa, shigo ki huta, ko?” Ba yadda Aaima ta iya haka nan tabi Mama d’aki, sakina ta kawo mata ruwa sannan ta koma d’an k’arasa wanke wanken data kusan k’arasawa. Sai after kamar 5 minutes haka tukunna Hudan ta shigo ta zauna suka sake gaisawa da Aaima. Ledojin da ta shigo dasu ta mik’awa Mama tana cewa “wai gashi inji Ya Arshaad, d’ayan na Huda ne, wannan kuma, tayi magana tana zaro iphone 11 d’in tace “na Sakina ne” Dai dai kuwa da shigowar Sakina. Da sauri ta k’araso, tana kallon ledar, tana gama ganin yanayin wayar ta daka uban tsalle tana murna!. Hannu ta sa zata karb’a wayar a hannun Mama, Maman ta buge hannunta tana harararta. Tura baki tayi tana sosa wajen, nan kuwa Aaima da Huda suka dinga yi mata dariya…. Mama ce ta katse dariyar tasu ta hanyar cewa “Aaima ba za’a yi haka ba! Waennan wayoyin ai sun yi musu girma! Ina lefin irin tawa mao tachila tafi sauk’i sauk’i ai, duk da ban san kud’in waya ba amma waennan wayoyin daga ganinsu na tabbata za su yi tsada! Ba a son maida hannun kyauta baya, shiyasa ba zan ce ba za a karb’a kwata kwata ba amma ga wayoyin in kin koma gida kice mishi nace ‘ya chanjo musu mai tochila irin tawa, an gode’.” Aiima har zata yi magana kawai suka ji Sakina ta fashe da kuka!! Maficin da yake ajjiye a gefen gado Mama ta hango, ai kuwa ta rarumoshi ta yunk’uro kanta, da gudu ta mik’e tayi hanyar k’ofa tana share hawaye tana cewa “haba Mama taki wayar fa bata chatting!” Kanta da taga Mama tayo gadan gadan tana shirin maketa ne yasa ta k’arasa fita da gudu.! A bakin k’ofar tana fita suka yi gware da Jalila wadda ta lab’e har da d’an sake turo kai! Ture ta Sakina tayi tace “Shegiya munafuka!! A haka zaki k’are!.” Jalila dake duk kunya ta isheta ga kuma kishi da al’ajabin daya rufeta ‘tabbas wannan Arshaad d’in da gaske yake fa!!’ Shiyasa kawai bata kula Sakina ba ta wuce ta kyale ta tayi d’akin Ummanta. A tsakar gida Sakina ta nemi waje ta zauna tanata karantowa Mama addu’o’i akan ‘Allah yasa ta barsu su rik’e wayoyin’, irin wayoyin da take gani a hannun Malaman su y’an gayu da kuma wasu students ne fa da suke shigowa dasu a b’oye!. A d’aki kuwa babu yadda Aaima batayi ba, amman Mama ta dage akan ‘sai dai a mayar a karb’o musu mai tochila!’ Haka nan Aaima ta hak’ura ta cewa Mama “Ya Arshaad d’in ma yana waje yana son ganin Huda ne.” Fad’a Mama ta hau yiwa Aaiima tana cewa “ai da ta fad’a tun wuri, an barshi a waje ko ruwa ba a kai mishi ba…” Huda ta cewa “ta nemi ruwa ta kai mishi akwai ragowan pure water a cikin randa ta nema cups ta d’aura a tray ta fitar mai da shi.” Hakan kuwa aka yi, Huda ta fita iya kuma Aaima ta je tsakar gidan wajen Sakina. Yana cikin mota a zaune yana waya da Aslam… Tana fitowa kamar ance ya d’ago..yana d’agowa ya ganta sanye cikin wani maroon hijab har k’asa wanda ya sake fito da ainihin kyau da hasken kalar fatarta, tayi kyau matuk’a! Ba wani kwalliya tayi ba dan ba komai a fuskarta sai k’asan eyelid d’inta da ta zizirawa kwalli amma tayi kyau sosai. Tsayawa kawai yayi yana kallonta! Ya bar Aslam yanata ‘hello hello’ shi kad’ai! Karshema ajjiye wayar yayi a gefe ya d’aura hab’arsa a kan sitiyarin motar yanata kallonta. Ta cikin glass d’in gaban motar taga irin kallon da yake yi mata hakan yasa ta ja hijabinta ta rufe fuskar gaba d’aya…. Murmushi yayi ya bud’e motar ya fito ya k’araso inda take yasa hannu ya karb’a tray d’in sannan yace “Thankyou, but pls ki bud’e fuskanki, dan wallahi idan kika fad’i anan dariya zan yi.” Hannu tasa ta d’an ja hijab d’in fuskarta ta bayyana amman ba duka ba, yana kallon yadda take chuno d’an k’aramin pink lips d’inta. Murmushi kawai yayi sannan yace “how are u?” yana mai k’arasawa inda motar take ya d’aura tray d’in a kai. “Alhamdulillah” tace mishi sannan ta gaidashi. Cikin kulawa ya amsa kafin yace mata “tana son wayar? Tayi mata ko a chanzo?” Murmushi tayi tayi masa godiya, kafin tace “Amman Mama tace sai dai a mayar a karb’o mana mai tochila.” “Woow!” yace, yana zaro ido sai kuma ya d’an yi dariya kafin yace “Haba Mama dan Allah tayi hak’uri, mai torchlight kuma? Tayaya zamuna yin chattn tou da su video calls?” Murmushi kawai tayi tace “Haka itama Sakina tace” sai kuma tayi dariya tace “Sakina har da su kuka.” “Ai da gaskiyan ta, bari kiga da kaina zanje in rok’i Mama.” Da sauri Hudan tace “A’a Ya Arshaad, kayi hak’uri Mama fad’a zata yi min bayan ka tafi.” Murmushi yayi yace “zan yi yadda ba zatayi miki fad’a ba, kinji cute Baby.” Tafukan hannayenta ta sa da sauri ta rufe fuskarta tana murmushi k’asa k’asa… shima murmushin yayi yana bin hannun da kallo kafin yace “Yaushe zaki yi k’unshi? irin black henna d’innan da ake zanawa a bayan hannu, yana kyau sosai, i like it.” Murmushi tayi kafin tace ana yi a mak’otan gidan Kaka, daman yana nemana yace ‘inje gobe’, idan naje daga nan sai in yi.” “No ki bari akwai wata ta iya sosai a instagram na gani zan kaiku ayi muku har da su Sakina.” Dasauri tace “Suma wannan d’infa sun iya sosai ma…” Murmushi kawai yayi kafin yace “Okay, as u wish, my cute Baby.” yana d’an kallonta yana murmushi.. Murmushi itama tayi sannan tace “Ya Arshaad” “Naam, Babyn Arshaad” Ya amsa still yana kallonta yana murmushi. Sunkuyar da kanta tayi sannan tace “Na gode sosai, dani da Sakina mun gode da yadda ka taimaka nayi karatu, if not bcause of you da ba zan yi ba, i don’t think i can ever repay you.” Murmushi yayi yana d’an cizon lower lips d’inshi kafin yace “Babu godiya fa a tsakaninmu Baby, na fad’a miki tun rannan, so ki daina yi mini godiya Ok??” D’aga mishi kai tayi alamr ‘to’. Dariya ya d’anyi sannan yace “Idan ma akwai wanda za muyi wa godiya tou wannan Karen ne daya tuso ki ya kawo ki har inda nake.” ya fad’a yana dariya. Itama dariyar tayi sannan ta d’an b’ata rai tace “Allah ni ka dena, bana so” cikin sigar shagwab’a. K’ok’arin gimtse dariyar yayi yasa hannu ya d’an d’aura akan lips d’inshi sannan ya ci gaba da cewa “Dama ace zan sake ganin Karen nan…to da waje guda zan ware a gidan gonata a gyara a yi ta kiwon shi har k’arshen rayuwarshi. Saboda a ta dalilinshi ne na gano cewa real true love da kuma love at first sight yana existing…. Maganar ‘yadda za kiyi repaying d’ina kuma just marry me Huda, promise to be mine forever shine kawai abunda zaki yi, and also ki soni kamar yadda nake sonki, koma bai kai haka ba, just try ki soni ko yaya ne kuma ni kad’ai, saboda I don’t think it’s possible ki soni ma the way I’m loving you dan son zai iya haukataki! Saboda ni kaina wani lokacin in kika fad’o min a rai sai na had’a da addu’o’i, sometimes fa har gizo kike yi min. So kawai ni dai just love me, love only me and marry me yadda zan nuna miki ragowan so da k’aunan da nake miki! That’s all I’m asking for, it’s more than enough.” Gani yayi Hudan na shirin nitsewa cikin k’asa sannan sai k’ok’arin b’oye fuskarta take yi. Shi dariya ma ta bashi, shi kam wannan kunyar ta Huda gaskiya tana cutar dashi da yawa, shi kenan bashi da daman expressing abunda yake ji….. Murmushi kawai yayi yace “To nayi shiru na daina, kar ki nutse k’asa Dan Allah.” Still bata d’ago ba dan ita kam ya gama kafe ta ne awajen yau kam. Murmushi ya sake yi Sannan cikin k’ok’arin son ganin ta sake dashi yace “tou bara in baki satar amsar kiran da Kaka yake miki, kina son ji?” Da sauri ta d’aga mishi kai alamar ‘eh’ amman bata d’ago ba. Kamar wani k’aramin Yaro haka ya mak’e kafad’ar shi sannan yace “Na k’i wayon, sai kin d’ago tukunna zan fad’a.” Murmushi tayi kawai ba tare da ta d’ago d’in ba, hakan yasa yace “ok shikenan, kyaji In kinje gobe. And one more thing, ranar Sunday in Allah ya kaimu zan kawo miki babban bak’o! Yayana zai dawo daga Uk Saturday in sha Allah so Sunday za muzo.” Murmushi tayi kafin tace “Allah ya nuna mana.” Hira sosai Arshaad yayi mata (dan ita Hudan duk kunya ya hanata sakewa) daga baya yace “ga kaya ta shiga dasu sannan tayi mishi iso shima zai shiga ya gaida Mama.” Hakan kuwa aka yi bayan ta gayama Mama ta shimfid’a darduma a y’ar varender simintin gefen d’akinsu Sannan ta fita ta ce mishi ya shigo kamar yadda Mama ta umarceta. A tare suka shigo gidan da tray d’in d’azu a hannunta hakan yasa ta wuce kitchen bayan ta nuna mishi inda zai zauna. Tana ajjiyewa ta shiga d’aki ta cewa Mama yana waje ita kuma suka zauna suka ci gaba da hira da Aaima. Mama tana fitowa, a chaan nesa da shi ta samu waje ta zauna suka d’an gaisa… Bayan sun gama gaggaisawa ne yace mata “kyauta ne, wasu ma suna mota, kawai dama yaga ya dace ne ya bawa Sakina da Hudan, dan Allah a karb’a kar ace a’a.” “Angode” kawai Mama tace, dan bata iya doguwar magana da shi, gaisuwar ma da suka yi duk gefe take kallo tana ta faman sunkuyar da kai. Sallama yayi mata yace “ya gode, bari su tafi yanzu.” Bayan ya fita Mama ma mik’ewa tayi ta shiga ta cewa Aaima yana jiran ta sannan ta had’o mata su tsami gaye da gullisuwa da alawar madara harda kuka da tsamiya ta bata tace “ta kaiwa Mamansu tace tana gaisheta.” Aiima ba k’aramin dad’i taji ba, har ga Allah Mama ta shiga ranta, in ka kalli matar kwata kwata ba zaka tab’a bata shekarunta ba, baza ma kace ta haifi Hudan ba! A hakan kuma Hudan tace mata ‘sai da aka yi 10 yrs ma tukunna aka haifeta’ Ga matar kyakkyawa over, gata da son ado ba zaka tab’a cewa bata dashi ba kullum tas tas da ita, tun ranar farko da suka fara had’uwa taji matar ta burgeta, ga kawaici da kirki…… “Muje ko in raka ki sannan in yiwa Ya Arshaad godiya.” Aaima taji muryar Sakina, itama Hudan mik’ewa tayi suka d’unguma suka fita dan yi mata rakiya. A bakin mota suka ganshi a tsaye, tun daga nesa da ya kalli Sakina ya gane tayi kuka dan fuskar nan tayi jajir abunka da farar fata sannan manyan idanuwanta har sun k’ank’ance. Murmushi yayi dai dai suna k’arasowa yace “Sakina rikici! Sis kuka ya k’are ko? Mama ta bar ki ki rik’e wayarki.” Murmushi tayi tace “Ya Arshaad ai Maman ce Allah kuwa, wai fa me tochila dan Allah, ita gani take yi me tochilan nan itace first class a duk wayoyi, ai bari inyi charging wayana idan na kunna mata flash sai ta tsorata.” Dariya sosai Arshaad yayi sannan yace “Mama ma fa kenan, wannan ban san ya kike yiwa grannies d’inki ba” Itama dariyan tayi sannan tace “Ya Arshaad mun gode sosai Allah ya saka da alkahairi.” “Ba komai sis take care, but register fa ya za ai dashi na sim d’in?” Kar ka damu ana yi a nan ba nisa harma settings na wayoyin anjima duk zan je in sha Allah.” “Ok, hakan yayi” yace sannan ya zagaya ya d’auko ledojin biyu yace “Naki d’azu Aaima ta shiga dasu, ungo wannan ki taya wifey d’auka!” Ya fad’a yana kallon Huda wadda ita shi d’in take kallo… B’ata rai yayi dan kar ma ta fad’i abunda yake tunanin tana shirin fad’a… Ganin ya b’ata rai yasa kawai tace “Mun gode” Sannan ya zaro kud’i a aljihu bandir y’an 500 ya bawa Sakina yace “su saka kati kuma gobe ta raka ta gidan k’unshi ta tabbata anyi mata, jibi zai zo ya gani in sha Allah.” Dariya Sakina tayi tace “kar ka damu Ya Arshaad ko gida yanzu haka ba zan shiga ba zan wuce in kama mana layi, gobe In mukaje ko waye a wajen dole ya matsa ayi mata.” Dariya Aaima da Arshaad suka yi, ita kuwa Huda sai k’ok’ari take su had’a ido da Sakina tayi mata warning da ido dan bata san taya zasu shiga gida da wannan kud’in ba! Kayan ma tunanin da take tayi kenan. Sakina sarai ta ganta amman ta shareta… A haka cikin raha suka rabu kamar kar Aaima ta tafi…. Motar tana wucewa Hudan ta finciko Sakina tace “Sakina baki da hankali ko? Kin iya jan rigima!! Mama zaki nunawa kud’in nan kice mata ‘an bamu mun sa hannu mun karb’a’, ko wa kike tunanin nunawa??” Dariya Sakina tayi dan k’arara take hango tsoro da firgici a idon Hudan… Hannu tasa ta fakaici idonta ta fincike mayafinta sannan ta k’arasa soro ta ajjiye ledan hannunta da kud’in akai tace “gashi ki k’arasa da su ciki na tafi kama layi, a yi miki fad’an ke kad’ai!” Tana dariya haka ta wuce ta barta a wajen…. Hudan rasa ya zata yi tai, idan tace itama ba zata shiga ba, za ace sun dad’e, idan kuma ta shiga fad’a ne! Ba yadda ta iya haka nan ta kwashi kayan ta kai d’ayar ledar ta ajjiye a bakin k’ofar d’akinsu, ta dawo ta d’auki d’ayar itama ta wuce ciki. A bakin k’ofar d’akin nasu taga Mama tana duba ledar…. Kallonta take yi tana kallon ledan da kuma wadda ke rik’e a hannunta kafin tace “Daga ina?” K’asa Huda tayi da idonta tace “duk shi ya bayar.” Ai kuwa nan Mama ta rufeta da fad’a….har da cewa ta kai k’arar ta wajenshi shiyasa ya shigo yace “tai shiru” waye waye……..ta inda take shiga bata nan take fita ba, tunba ma da Hudan ta nuna mata kud’in k’unshi da ya bayar ba. Sai da Mama ta yiwa Hudan tass tukunna ta kyale ta, kuma tace “ko da wasa in ya sake bata abu ta karb’a ranta sai yayi mugun b’aci, kuma kar ta kawo mata shi ya rok’eta!”. Allah sarki Hudan har da kukanta, dan in akwai abunda ta tsana to fad’a ne, gashi Mama yau tafi awa d’aya tana abu d’aya, sai tayi shiru sai taci gaba…… Wani abun takaicin Sakina bata dawo gidan ba sai wajajen 5, tana shigowa Hudan ta had’e rai! Ba yadda bata yi ba amman tak’i kulata, daga k’arshe dai hak’ura tayi ta kyaleta taje ta samu Mama tace mata “bara taje ta kai wayoyin register daga nan tanaso zata je gidan su Kaka sunada solar, sai ta saka charji.” “Ai kun fi k’arfi na yanzu, kuyi duk abunda kuke so.” Shine abunda Mama tace. “Kiyi hak’uri Mama” Sakina tace tana d’an rausayar da kai.” “Umm” kawai tace taci gaba da aikinta da Huda tayi tayi akan ta bari ta tayata tak’i yarda…. Ganin gidan ya koma kamar gidan makoki yasa kawai Sakina ta d’au wayoyin ta d’auki abun buk’ata ta fice… Bayan ta gama yi musu register taje ta jona musu wayoyin su….bata dawo ba sai bayan isha lokacin har Hudan tayi bacci… Kusan tare suka shigo gidan ita da Umma wadda ta fita unguwa tun safe!! God knows where. Sakina ko gaisheta bata yi ba tayi wucewarta dan har yanzu tana jin haushin abunda Jalila tayi… Tanajin Umman tana zaginta harda ce mata “y’ar karere! Gidan sai kace na ubanta ne.” Uffan Sakina bata ce mata ba, ita abun ma dariya ya bata. Umma kuwa takaici kamar ta had’iyi zuciya… Haka ta shiga d’akinta tana cewa “Allah ya kaimu gobe sai dai Alhaji ya zab’a ko ni ko wannan mara kunyar Yarinyar data raina mutane kamar kashin gindinta!” Duhu d’akin sosai! Hakan yasa tace “A’a Jalila wai har kin kwanta ne? Ko kuwa dai kawai yau bid’ar zama a duhun kike yi?” Tana maganar tana k’ok’arin kunna fitilar wayarta. Tana kunnawa fitilar ta haske dai dai kan fuskar Jalila wadda ke kwance kan gado! Ba a gane fuskartata tsabar kukan da taci, tayi sharkaf da gumi! Da sauri Umma tayi kanta tana rafka salati……. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 27 A hargitse ta k’arasa kanta ta d’ago ta, sannan ta hau dudduba ta tana cewa “Ke!! Wai lafiya kike kuwa?? Meye haka? Dukan ki suka yi? Mai ya faru???” Rungume ta Jalila tayi ta fashe da wani sabon kukan… Duk da kwakwazon tambayoyin da Umma take jero mata hakan bai sanyata ta sarara ta amsa mata ba, sai da tayi mai isarta tukunna ta share hawayenta tace “Umma anya Kaka shi ya haifi Baba kuwa? Ki duba fa kiga yadda yayi talla ta a masallaci shekaru uku baya wanda ba don na gudu na b’uya Gidan kawu Usman ba to da fa tuni yanzu ina gidan malam mati mai wanki! Kuma kina gani fa har yau ya dage akan shi zan aura, ba dan munata addu‘o’i ba na san da tuni yanzu an kawo kud’in an saka rana…. Ya dage ya hura min wuta ya hanani auren saurayi amman ita Huda kiga yadda yake k’ok’arin aura mata mai kud’i saurayi kuma kyakkyawa!! Kamar ba ni ce jikar sa ba?” “Ban gane me kike nufi ba! ‘Yana k’ok’arin aura mata’! Kamar yaya? Shin kin ji wani zancen ne bayan na fita?” Umma tayi mata tambayar da alamun tsoro wanda ya bayyana k’arara a kan fuskarta. Murmushin takaici Jalila tayi sannan tace “Umma, a gaban idona Huda ta tafi d’aya daga cikin makarantun da ake ji da su a kaff fad’in Nigeria!! Kullum ce mini kike yi zaki saka ta dawo gida gashi har sai da tayi candy ta gama bakiyi komai ba! Kuma na tabbata wannan saurayin nata yadda yake d’innan na san nan da nan zai nema mata jami’a ta tafi ni kuma ina nan ina wasan y’ar b’uya da Kaka! Wannan wacce irin rayuwa ce saboda Allah?? Wallahi Umma sai dai in kashe kaina dan ba zan tsaya ina ji ina gani ta auri wanchan mutumin kuma tayi karatun da ni ban yi ba!.” Da sauri Umma ta buge mata baki, sannan cikin fad’a tace “maganar kashe kanki ma bata taso ba!. Sannan kin san Allah idan baki gaya mini abunda ya faru yau d’innan kin bar ja mini rai ba to sai na bubbuge ki yanzun nan.” Share hawaye Jalila tayi sannan ta kwashe komai abunda ya faru yau d’in ta fad’awa Umma Dan ko lokacin da Sakina ta ganta tana lek’e da ta komo d’akin nasu ci gaba da lek’a su tayi, tsaf sai da taga komai…… Sannan ta k’ara da cewa “kuma na san har wajen su Kaka ma yaje dan da wuya in ba a saka rana ba ma, tunda gashi har kud’in k’unshi ya bayar… Umma gashi wallahi tallahi ina son shi, sosai Umma!!..” Ta k’arashe maganar tana mai fashewa da kuka…. Takaici! Da ya ishi Umma bata san lokacin da ta daddage ta d’akawa Jalila duka ba! Sannan cikin fad’a tace “Wallahi Yarinyar nan tun da nake ban tab’a ganin dak’ik’iya kamar ki ba! Tun zuwan Yaron nan na farko nace miki ‘idan ya zo ki fita! Idan yazo ki fita!!’ Amman da yake y’ar iska ce ke!! Kina kuma so kisa inga abunda zuciyata zata buga shine kika yi zaman ki a d’aki kamar kumama!!” Cikin kuka Jalila tace “Umma wai taya zan fita? Ko na fita na san ba lalle ya kulani ba! Ki kallafa yadda Hudan ta koma sannan ki kalle ni..” Katseta Umman tayi ta hanyar cewa “Dan uban ki ban san abunda nake yi bane ba? Tunda nace miki ki fita d’in ai na san me nake yi ko? Naki aikin kawai shine ki fita ki tabbata kun had’a ido da shi daganan ki bar min sauran aikin…Amman sam kin kasa! Abu guda d’aya za kiyi tak Jalila amma kin kasa yi wajen shekara uku yanzu!! Kalle ki, sai dai ki zauna kina ta kuka, tou wallahi idan baki yi wayo ba a haka zaki k’are!! Tunda ni dai ba nice zan yi aikin da kece ya kamata ki yishi ba! Shegiyar Yarinya kawai…. Idam kika ga wanda Bilkisun kawun ku Nasiru ma zata aura sai kin yi mamaki!! D’azun muka je ganin gidanta a sabuwar gandu, tamfatsetse mai gate da bene! Da ke da ita da Hudan duk kusan tare kuka taso, ga y’ar gidan Zainab itama mai kud’i sosai ya fito mata nan da wata biyu za a sha biki in sha Allah… Ke kuwa kina nan a d’aki, ke ko irin samarin nan masu motoci ma basa biyoki in kin fita, kina nan dai da malamin maths dan buhun uba mai shegiyar rowa, ni Allah yasa ma ba shine yayi miki asiri ba!” Fashewa da kuka Jalila tayi…. Ta fi minti biyar tana abu d’aya! Sai kuma ta fara bawa Umman tausayi, hakan yasa ta janyo ta ta rungume ta hau lallashinta..sai da taji tayi shiru sannan tace mata “Jalila gaskiya nake gaya miki, ki fahimceta kin ji? Ba zan so ki je inda zaki sha wahala ba bayan ga sa’anninki suna jin dad’i ina gani. Yanzu abunda nake so dake shine ‘duk ranar da saurayin nata ya sake zuwa to ki fita, ki tabbatar kin fita kafin ita ta fita, sannan ku had’a ido!’ Daga nan ki bar min aikin a hannuna kin ji??” “To” tace, sai kuma tace “umma Kaka fa? Kina ganin ko Arshaad d’in ya dawo gurina Kaka zai yarda kuwa? Kinga fa ya dage sai Mati!.” Ajiyar zuciya Umma ta sauk’e kafin tace “Jalila ki yi yadda nace kawai, ta Kakanku mai sauk’i ce kin ji? Ai ko ina gadon asibiti ba zan yarda da Mati ba shima ya sani, ballantana kuma da lafiya ta.” D’aga mata kai tayi tana share hawayenta… Dafa ta Umman tayi itama ta goge mata hawaye kafin tace “yauwa y’ar albarka, ki kwantar da hankalinki kin ji auta ta…” Haka nan ta d’an saki ranta suka d’an yi hira kad’an, wadda rabin hirar duk k’ulla tuggu ne…daga baya kowa ta ja pillow suka hau bacci….. Washegari da safe Sakina cikin zumud’i ko karyawa bata yi ba, taje ta amso musu wayoyin su… San wayar bai k’ara shiga ransu ba sai da suka kunna, already an d’anyi setting d’in da suka kamata…. Sakina har da ihunta tana daka tsalle, sannan ta d’auko slum book d’inta na school ta hau juye nambobin k’awayenta tana saving.. Mama na d’akin Baba tana shara taji ihun Sakina, girgiza kai kawai tayi tace “Allah ya shirya” Baba wanda ya daya fito a wanka yana shiryawa ta kalla sannan tace “Jiya, wanda yake neman Huda ya zo baka nan! Ya kawo musu kayayyaki har da waya ya kawo musu ita da Sakina.. Har cikin gidan nan ma ya shigo muka gaisa.” Shiruu, Baba yayi bai ce da ita komai ba. Sai da ya gama shirinshi tsaf ita har ta ma manta tayi maganar, dan har ta fad’a wata duniyar tunanin… Yana dedeta zaman Hular kanshi ya kalleta yace “Ko da wasa!! Idan kika sake bari Yaron nan ya shigo mini cikin gida to duk abinda nayi miki kar ki ji haushi na ki kuka da kanki! Tunda ke abinda kwad’ayi ya ja miki bai kai ga zama izina a gareki ba, k’iri k’iri gashi zaki tura y’arki itama ta bi sahunki!!! To duk iskancinsu da za suyi su tsaya iyaka k’ofar gida kuma shima ki gayawa Hudan nace tace mishi ya daina yi min parking daf k’ofar Gidana! Tunda na san yanzu ina yin magana Kaka bayan ki zai bi!. K’iri k’iri bani da yadda na iya an d’aura mini ruk’on shegiya tun tana jinjira! Amman ku tsabar baku san kara ba! Jalila na cikin gidan nan aka yo siyayya dan cin fuska babu ita kuma har kike iya gaya min ya kawowa Hudan da wata Sakina wadda itama bani da ikon hanata zuwa gidan, abubuwa. Sannan na tabbatar ko tsinke baku bawa Jalilan ba!! Ba wai Ina gaya miki bane saboda kwad’ayi ko kiyi tunanin ina son abunku, ni abunku bai dameni ba, kawai dai inaso ki gane ta wajaje da yawa da na fiki!!” Yana gama fad’an haka ya juya ya sa takalmanshi ya fice, ko ‘a dawo lafiyan’ ta bai amsa ba. Girgiza kai kawai tayi tace “Allah ya kyauta!” Sannan ta k’arasa aikinta ta wuce d’akinta. Kamar yadda tayi zato su Huda har sun gama abun karyawan gida, daman ita da safe ta yiwa Baba nashi tace musu ‘in sun shirya su d’aura na mutan gida’. Tana shiga d’aki ta tadda su suna ninke kaya. Waje ta samu ta zauna a kan cafet d’in da yake malale a tsakiyar d’akin d’an gefe kad’an dasu sannan tace “Sakina kwaso min kayan da Arshaad ya kawo jiya, duka” “To” Sakina tace sannan ta nufi wardrobe ta bud’e locker d’in chan k’asa ta d’auko kayan gaba d’aya waenda har yanzu suke cikin leda. Juyesu suka yi a k’asa gabaki d’aya, sannan Mama ta hau rabawa gida biyu, abaya sunfi kala ashirin haka ta rabasu dai dai, hatta da rings dede ta raba su da su bracelet, bayan ta gama rabawa ta ware kashi d’aya a gefe sannan ta sake raba d’aya kashi Dayan gida biyu ta cewa “Huda da Sakina su d’auki kashi d’ai d’ai. D’aya mai yawan kuma ta ce “su kwasa su zuba a leda su kaiwa Jalila.” Har Sakina ta yunk’uro zata yi magana Hudan tayi saurin rik’e mata hannun alamun tayi shiru sannan tace “to Mama” Ba yadda Sakina ta iya haka tana ji tana gani suka juye a leda suka fito.. Suna fitowa tace “yanzu dan Allah an.....” Da sauri Huda tace “Dan Allah Sakina ki yi shiru mana meye a ciki idan mun bata? Ni daman ko Mama bata yi hakan ba ma dama inada shirin kai mata.” Da sauri Sakina tace “Ai ni ba wai batan da akayi bane ya b’ata min rai ba, fin namu yawa da nata rabon yayi shi yafi yi min ciwo.” Ita dai Huda shiru tayi mata dan har sun k’araso k’ofar d’akin Umma hakan yasa ta fara sallama.. Ta yi kusan minti biyu tana sallama tukunna aka ce “shigo” Tsaki Sakina taja sannan tace “Zan jiraki a nan dan ba zan iya kwasar takaici ba!” Haka Hudan ta shiga ta same su, da kyar Umma ta amsa gaisuwarta Ita kam Jalila iskar da ta kwasota ma bata kalla ba. Hakanan jiki ba kwari ta ajjiye k’atuwar ledar da wata y’ar k’arama tace “gashi na Ya Jalila ne” sannan ta mik’e ta fito.. Kamar ta biya su bashi ko godiya babu wadda tayi mata a cikinsu.. Suna fitowa kitchen suka nufa suka hau zuzzuba abinci. Sun zubawa Ya Ja’afar da su da su Umma nasu suka ajjiye, dan tun dawowarsu ba su ga Junaidu a gidan ba Hudan tana son tambaya amma tana jin tsoron Mama. Nasu suka d’iba suma ita da Sakina da Mama a kwano d’aya, daga nan suka fara k’ok’arin barin kitchen d’in…. Hudan ce ta d’auko kwanon ita kuma Sakina tana biye da ita a baya suna magana…saura k’iris ta juyewa Ya Junaidu abincin a gaban rigarsa sakamokon gwaren da suka yi da shi. Kwata kwata bata san yana bakin kitchen d’inba, gashi tana tafe tana kallon baya ne… Da sauri ta ja baya ta rik’e kwanon da kyau, sannan ta hau sosa gurin da suka yi gwaren dan mugun zafi yake yi mata har idanuwanta sun kawo kwalla…. Hannunsa ya d’aura a kan goshin nata saman hannunta, da sauri ta janye hannun nata ta d’an ja baya kad’an… Ganin da yayi wajen ya d’an yi jaaa kad’an yasa ya kalleta a hankali kamar wanda baya son yin maganar yace “Sorry” Jijjiga kai tayi alamun ‘ok’ sannnan tace “ina kwana” Yanzun ma kamar ba zai amsa ba a hankali yace “lafiya” sannan ya kalli Sakina itama da tace mishi “In kwanan” ya amsa. Hannunshi yasa ya karb’i kwanon hannunta ya mik’awa Sakina sannan ya cewa Hudan “Zo, ina son ganin ki.” Yana gama fad’an haka ya juya ya wuce ya nufi hanyar d’akinsa. Hudan, yi tayi kamar ba zata je ba, sai da Sakina tace “kije mana, baki san me zai gaya miki ba, kuma ko ba komai dai ai he’s your brother ko? kuma shi ai da hankalinshi a cikin y’an d’akin nasu.” Shiru tayi hakan yasa Sakina kawai itama bata sake magana ba ta wuce tayi d’akin Maama. Ta kusan minti uku a tsaye tukunna kamar mara gaskiya ta nufi hanyar d’akin bayan ta ware d’an kwalin doguwar rigar atamfar jikinta ta yafe shi daga kanta zuwa k’irjinta. Tana isa tayi sallama a bakin k’ofar d’akin, ko k’arasa rufe bakinta bata yi ba akace “Come in”. A hankali ta tura k’ofar ta shiga. Yana tsaye a tsakiyar d’akin, kallon d’akin take yi tana sakewa dan ya koma kamar ba shi ba, yadda ya gyara gidan gaba d’aya, haka ya yiwa d’akin nasa nutsetsen gyara! Ya sha penti mai mugun kyau har da pop, ga tv k’atuwa! Dayake d’akunan gidan suna da girma sosai har yanka yayi aka yi mishi bayi a d’akin dan ga k’ofa nan. “How have you been??” D’in da yace mata ne ya dawo da hankalinta gareshi. A hankali tace “Alhamdulillah”. Kujera ya nuna mata yace “Zauna mana.” A hankali ta girgiza kai “Ok” yace, ya jinjina kai kafin yace “Baki nemi ni ba, kin kyauta kenan??”. Sunkuyar da kanta tayi tace “kayi hak’uri, ai babu wanda zan tambaya kai, Ya Jalila ka san ba wani shiri take yi da ni ba.” A hankali ta sunkuyar da kai tana tunanin rabon ta dashi tun farkon shiganta ss2, haka kurum ya daina zuwa mata amman da farko farkon zuwanta makarantar kafin lokacin visiting ma yayi ya kan zo sau biyu sometimes har uku, sannan kuma duk visiting sai su Ummu sun zo da shi, dan har sak’o Mama take bashi ya kai mata kuma in yaje suyi waya da Maman! A ranta taji ya kamata ta tambayeshi, ko ba komai Ya Junaidu yana da kirki, dan haka tace “Meyasa ka daina zuwa min visiting?” Murmushin yayi, kafin a hankali yace “ashe dai an damu dani, ko?” Bai jira jin amsarta ba yaci gaba “Visiting da zuwa da nake yi akai akai Arshaad ne ya hana! Dan akwai time d’in da naje gate man d’in yace min ‘wanda ya kawoku yace kar a k’ara barina ina shiga!’ Wai yazo akace mishi anyi exceeding zuwar miki sai dai ya jira next month.. Shine yayi ta fad’a yace ‘kar a sake barina In shiga’.” Murmushi Hudan tayi kafin tace “Ya junaidu baka san halin mai gadin mu bane ba wajen iya had’a mutane.. Ni na san ba wani Ya Arshaad da ya hana kawai dai baiga daman barin ka ka shiga bane! Amman shi Ya Arshaad ina ma ya iya fad’a, ba ruwanshi… Sannnan in da ace yayi hakan to da zai fad’a min… To gidansu Sakina fa? Me yasa baka je ba chan ba?” Shiruuu, yayi dan ji yake kamar zuciyarshi zata fashe!! Yadda ta tak’ark’are take yabon Arshaad a gaban shi abun yayi mugun b’ata mishi rai! Inama laifin tace zata tambaye Arshaad d’in amman ji yadda directly ta fito tayi backing d’in shi…. “Ya Junaidu!” Yaji muryar ta, da kyar ya iya controlling kanshi, ya d’an seseta kanshi kad’an amman still idanuwanshi har sun sauya kala! Danne abunda yake ji yayi kafin yace mata “Bayan naje school d’inku an hanani shiga, i think after a month aka yi muku hutu, and wallahi Huda that’s the longest month dana tab’a gani a rayuwana.. Kullum Ina cikin duba date, ranar ana yi muku hutu daman na san ba nan zaki zo ba dan naji Baba yana yiwa Mama kashedi a tsakar gida ‘kar kizo mishi kuma itama idan taje a bakin aurenta!’ Yana fita na shirya zan je wajenki… A tsakar gida Mama take bani sak’o in kai miki ke da Sakina ashe Umma tana d’aki bamu sani ba, sai kawai gani muka yi ta fito mana.. A take tace mini ‘in dai na taka k’afata naje gidansu Sakina to bata yafe min ba....’. D’azu na dawo daga Abuja, flight d’in asuba na biyo, kawai cikin bacci na ke jiyo muryar ki sama sama I tot qizo voice d’in naki ke yimini saboda yadda nake tunaninki day and night, sai da naji muryan Sakina tukunna na tabbatar ku d’in ne.. Ya aka yi Baba ya barki kika zo? Yaushe kuka dawo? Kun gama ko?” Ya jero mata tambayoyi yana kafeta da manyan idanuwanshi. Cikin nutsuwarta tace “Wajen Kaka Mama taje, as usual….shine ya yiwa Baba magana. Jiya muka yi graduating a jiya muka zo nan ni da Sakina. Na ma yi jamb, kuma duk mun ci.” “Alhamdulillah!” yace, sannan yace “Huda i think Mama itama is against our relationship, tunda tana ganin fa yadda naketa son ganin ki but kin dawo ko a waya bata gaya min ba, kumafa jiya ma na kirata na gaisheta.” Shiru tayi sannan tace “Kawai dai bata son fad’a da Umma ne” Bai ce mata komai ba, ya matso kusa da ita sannan yace “Forget all that. Yanzu let’s talk about us, ko?” Kallonshi tayi sai kuma ta d’anyi k’asa da kanta ganin yadda ya tsareta da idanuwa. “Um?” Ya sake cewa, sannan ya d’aura da “Ina jinki, let’s talk tunda kin k’i yarda ki zauna a d’akin nawa, sai muyi a tsaya.” Cikin rashin fahimtar shi take, “kamar akan me kenan za muyi maganan?” Kamar an fisgi maganan a bakinshi taji yace “Yaushe kike planning yin aure?” Da sauri ta d’ago ta kalleshi “Sai kuma ta maida kanta k’asa tace “duk sanda Allah yayi” sannan ta juya zata fita tana cewa “Mama zata nemi ni” “Hudan!!” taji ya kira sunanta. Tsayawa tayi ita bata juyo ba kuma bata tafi ba… Takowa ya sake yi ya zo inda take tsaye sannan yace “I know what you are afraid of! Umma da jalila ko? I promise you har k’arshen rayuwan mu zan kareki daga garesu… I won’t let them harm you in any way.. Jalila sister nace, i have full control over her Umma kuma Mahaifiyata ce amman na yi miki alk’awarin sai kina so ma tukunna zaki zauna a garin da take. Hudan ko k’asar nan ne in kikace bakya son zama to zan yi k’ok’ari inga na fitar dake! Duk inda business yake k’ok’ari nake yi inyi duk saboda ke, sannan ina aiki I promise you i‘ll give you all the happiness and luxury’s that you deserve!.” D’agowa tayi ta kalleshi sannan tace “Ya junaidu gani kake yi kaiima kamar kwad’ayi ne da ni?” Ganin da yayi kamar ranta yad’an b’aci ne yasa yayi saurin girgiza kai sannan yace “Sorry Hudan not at all, akwai abunda nake tunani ne wanda in ma hakan ya faru to ba za a iya yi min shige ba, kar kiyi misunderstanding d’ina, please.” Ya k’arashe in a low tone. “To” kawai tace Ganin yadda ya marairaice duk sai taji wani iri… Tunanin ‘kar su tsaya b’atawa juna lokaci’ ne yazo mata dan haka kawai ta dake ta fara magana ba tare da ta yarda sun had’a ido ba…... …”Ya Junaidu kai Yaya nane, ba zan so In yaudareka ba, kuma ya kamata in fad’a maka gaskiya tun yanzu.. Babu amfani muyi aure iyayenmu basa farin ciki da auren, kai ka sani a duk duniyar nan babu wadda Baba baya so kamar ni, a ta dalilin Kaka kawai nake zaune a cikin gidan nan! Sannan Umma ita ma bata sona! Ga Ya Jalila itama sannan Ya Ja’afar! Duk fa kowa naka kai kad’ai ne kawai kake sona And ba zan b’oye maka ba Mama itama bata son auren mu, duk a ta dalilin su Umma.” Da sauri ya katseta ta hanyar cewa “Huda na fad’a miki i’ll take care of them, all of them i promise, ba wanda za a cuta in sha Allah.” Shiruuu, tayi chaaan kuma, kamar an fisgi maganar daga bakinta tace “Na yiwa Ya Arshaad alk’awarin aure.” Junaidu, da kyar ya iya had’a 1+1 d’in maganar a cikin kwakwalwarsa… Ji yayi jiri yana neman zubar da shi dan haka ya nemi waje ya zauna, a hankali yace “Says the person that just finish saying ‘bata da kwad’ayi!’.” Hawayene ya gangaro daga idanunta, a hankali tace “Bafa ka tab’a cewa kana sona ba tun farko and kuma kaga......” K’arar fashewar center table din dake a tsakiyan d’akin ne yasa tayi saurin yin shiru sannan ta sanya tafukan hannayenta ta rufe kunnuwanta, tare da rumtse idanuwanta duk a lokaci daya!. A zuciye ya taso yazo ya kama k’afafunta da k’arfi kamar zai karyata har sai da tayi k’ara! Bai damu ba ya fara magana cikin tsananin b’acin rai da d’aci!! “Ni kike cewa ban tab’a cewa ina sonki ba?? Makauniyace ke ko sokuwa? Ko kuwa dai renin hankali ko kuma Yarinya ce ke da zaki ce baki fahimceni ba tuntuni? Hudan tun kina baby, y’ar baby!” Yayi maganar yana kwatanta d’aukar baby da hannunshi, sannan ya ci gaba da cewa “nake gwada miki so! I don’t think akwai need na inyi amfani da fatar baki in fad’a miki domin kuwa na san ko wanda bai tab’a sanin me kalmar so take nufi ba, abunda nake nuna miki, ya ci a ce ya bada full definition na wat luv is!!! Kin san irin bak’ar wahalar da na sha first zuwana Abuja da Lagos kafin in samu inyi settling kuwa??? All because of you!!!” Ya k’arashe maganar cikin d’aga murya sannan ya girgiza ta da k’arfi!. Fashewa tayi da kuka…. Tunda Mama ta kawota duniya bata tab’a ganin b’acin ran Ya Junaidu irin haka ba, gabaki d’aya ya birkice kamar ba shi ba, sannan idanuwanshi sunyi jazur! Sun cika da kwalla kamar zai fashe da kuka… Kukan da yaga tana yi ne ya sanyashi yin shiru sannan ya runtse idanuwanshi!…… Ya fi 3 minutes a haka kafin ya bud’e idanunsa, ya kalleta tayi k’asa da fuskarta still kukan take yi… A hankali ya cika mata kafad’a sannan ya juya ya fara tafiya yayi hanyar gado kafin yace “Get out!” Har ta juya zata fita sai kuma ta juyo tace “Ya Junaidu dan Allah ka fahimce.......” Da sauri ya juyo ya had’e hannuwanshi guri guda alamun rok’o, sannan yace “Huda dan girman Allah ki fita, please!!”. Hawayenta ta share sannan ta juya a hankali ta fice a d’akin....... BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 28. Babu yadda Mama da Sakina basu yi da ita akan ‘ta fad’a musu abunda yake damunta’ ba amman tak’i! Mama data gaji mik’ewa tayi ta nufi hanyar k’ofa tana cewa “Ai daman tunda aka ce ya kirawo ki na san a rina! In banda rashin hankali ma me ya kaiki shiga har d’akin shi? Ai kad’an kenan daga aikin ‘d’an da Sadiya da Usman suka haifa’, tunda ke dai ban isa in fad’a miki ki ji ba!” Tana gama fad’in haka ta sa kai ta fice tana cewa “Sakina su yi sauri Kaka na jiransu.” Sakina bata ci gaba da takura mata da tambaya ba. Da ta k’i cin abincin ma kyale ta tayi ta kwashe ta kai waje dan tana so ta d’an huce tukunna sai ta sake tambayar ta. Haka nan suka shirya suka nufi gidan Kaka.. A hanya ma Sakina labarin Yayan wata k’awar su wanda tun suna ss2 yake sonta ta dinga bata, nan take ce mata “ai jiya tana yiwa k’awar tasu magana a watsapp ta turawa Yayan nata numberta, daman duk lokacin da suka had’u idan anje visiting sai ya tambayeta bata da waya, ita kuma tsoron bashi na Ummu take yi sai gashi kawai yau ya kirata.” Murmushi kawai Hudan tayi…. Tun lokacin da ta fito daga d’akin Ya Junaidu take ta tunani kuma a kaff lissafinta duk in da taje ta dawo to lissafin nata nuna mata yake yi ‘bata kyautawa Ya Junaidun ba!’. Sai da suka jira Kaka, dan suna zuwa suka tarar ya fita sadaka shi da Madu a masallaci kuma sai sun yi azahar tukunna za su dawo.. A nan Sakina ta samu damar sake tambayar Hudan Nan Hudan ta kwashe duk yadda suka yi da Ya Junaidu ta fad’a mata sannan ta k’ara da cewa “ban yiwa Ya Junaidu halacci ba, duk tsahon zamana a gidan nan shi kad’ai ne in yana nan yake k’ok’arin kareni a ko da yaushe baya bari a cutar dani, ni yanzu ban san ya zan yi ba!” Da mamaki Sakina take kallonta kafin tace “Ban gane maganar ‘ba ki san ya za ki yi ba!? Hudan kina buk’atar peace a rayuwarki kuwa? Ya Junaidu fa d’an Umma ne Yayan Jalila k’anin Jaafar sannan d’an Baba!! Kin san me kike yi kuwa? Son shi kike yi?” Sakina tayi mata tambayar da tsantsar mamaki shimfid’e a kan fuskarta. Shiruuuu, Hudan tayi kafin chan tace “ba wai maganar so bane, ba zaki gane ba Sakina, ko tayaya zan yi miki bayani ba zaki tab’a ganewa ba.” A hassale Sakina tace “Rabbi yasa kar in gane!! Duk abunda zai saka in yarda In amince ki auri Ya Junaidu ki bar Ya Arshaad to kuwa Rabbi kar ya fahimtar da ni!” Shiru kawai Hudan tayi mata tana jin ta tanata faman k’ok’arin fahimtar da ita, k’arshe ma rufe ido tayi kamar mai bacci, nan kuwa Sakina ta k’ule ta rabu da ita ta koma gefe ta d’auko wayarta ta hau chatting…. Har suka mik’e suka yi sallah ba wadda ta kula y’ar uwarta.. Hudan ta koma ta lumshe ido Sakina ta ci gaba da chatting d’in ta A haka Kaka ya shigo ya same su. Cikin ladabi suka gaishe shi, bayan ya amsa ya cewa “Sakina ta tashi ta fita.” Mik’ewa tayi ta cewa Hudan “ta sameta a d’akin Baaba Talatu idan sun gama zancen” Sai kuma ta cewa Kaka “Kuma koma dai menene nice uwar gida!!” Dariya Kaka yayi yace “Ja’ira!” yana mai kallon fitarta sannan ya juyo ga Huda. Babu b’ata lokaci ya sanar da ita……’Arshaad ne yake so ya zo ya gaidasu, sannan a saka ranar da iyayenshi zasu zo…’. A hankali tace “Zan yi shawara da Mama tukunna!” Da mamaki Kaka ya kalleta kafin yace “Ita Maman naki ce tace min ai kun dedeta da shi Yaron sannan Muhammadu yayi duk wasu bincike a kanshi.” “Eh” tace, sannan ta k’ara da cewa “Amman dai ya d’an jira ina buk’atar lokaci….” Shiruuu, Kaka yayi na y’an mintuna sannan yace “To! Amma tunda dai yace zai zo ya gaishe mu ba wani abun bane ba za a barshi ya zo d’in, maganar turo iyayen nashi kuma sai a jira in kin gama d’aukar lokacin naki ko?” “To” tace. Daga nan ya tambayeta ‘makaranta’ da kuma ‘gidan ba matsala ko?’ Nan tace mishi “komai Alhamdulillah….a taya su da addua result d’insu yayi kyau!” Y’ar hira kad’an suka yi sannan ya sallame ta ta tashi ta tafi…. Tun kafin ta k’arasa d’akin Baabaa Talatu take jiyo hayaniya. Da sallama ta shiga nan ta tarar ashe Hajiya Shuwa ce suke ta hira da Sakina kamar wasu k’awaye itama Baaba Talatu tana taya su. Har k’asa ta durk’usa ta gaida Baaba Talatu dayake itace a farkon d’akin, cikin kulawa da sakin fuska ta amsa mata. Nan ta k’arasa wajen Shuwa itama ta gaida ita amman ko alamun taji ma bata yi ba! Maimaitawa tayi ta sake maimaitawa amman Shuwa tayi mata banza!. Nan Baaba Talatu tace “Taso ki zo ki zauna, zo ki bani labarin makaranta…” Haka jikinta duk yayi sanyi taje ta zauna kusa da Baaba Talatu, tana zama basu wani jima ba Sakina tace “ta zo su tafi k’unshi kar a haye musu layi.” Nan suka yi musu sallama suka fito. A hanya sai da Sakina ta bata hak’uri akan halin Shuwa, tace “wata rana zata daina.” Murmushi kawai Hudan tayi tace “ba komai.” Haka suka k’arasa wajen k’unshi aka tsantsara musu mai kyau Ma sha Allah, sai yamma suka koma gida a gajiye… Hudan bata waiwayi wayarta da ta bari a gida tun safe ba sai dare shima dan zata haska tayi wanka ne kasancewar garin da zafi sosai. Tana d’auka kuwa taga misscalls d’in Arshaad, da messages kala kala. Sai da tayi wankan ta sannan ta kira shi, bai d’auka ba sai da ya katse tukunna ya kirata. Tana d’auka yace “in sun gama waya ta tura mishi number Sakina, dan yaga ita tata wayar bata da amfani.” “Tou” kawai tace tana murmushi, sannan ta bashi hak’uri… Hirarsu suka sha sosai Hudan kamar tana gabanshi sai rufe ido take yi, Sakina na gefe tana chatting tana ta tab’e baki k’arshe ma barcinta tayi ta kyale ta. Washegari da yamma ya zo, da yaga k’unshi nata kamar ya cinye hannun, yace mata ‘yayi kyau!’ Ya fi sau ba adadi.. Dukda tace masa ‘Sakina ta d’auka zata tura mishi anjima amma hakan bai yi nasa sai da shima ya d’auka da wayarshi… Suna tsaye mota tayi parking a k’ofar gidansu, ita bama ta san Junaidu bane ba dan motar akwai tint.. Sai da ya fito tukunna ta ganshi! Ai kuwa nan jikinta ya hau karkarwa….. A tunaninta zai yi wani abun amman ga mamakinta ko kallon inda suke beyi ba, yayi wucewarshi cikin gida kamar ma bai gansu ba! Juyowa tayi taga shima Arshaad d’in Junaidun yake kallo…har ma Junaidun ya shige amman bai bar kallon k’ofar ba, da alama kuma wani tunanin ya tafi….. Sai da ta kira sunan shi sannan ya juyo ya kalleta! D’an k’uraa! mata ido yayi Kafin yace mata “How are you related to him??” Cikin nutsuwarta ta fad’a mishi yadda suke a gidan da kuna yadda kakanninsu suke! Ajiyar zuciya ya sauk’e sannan yace “Hudan hope ba matsala dai ko? Dan gaskiya na d’an tsorata kad’an! Tunda kinga shi na gida ne.” Shiruu, tayi kaman tana tunanin wani abun sai kuma da sauri tace “Yauwa, Ya Arshaad, wai kai ne kace ‘kar a sake barin shi ya shiga wajenmu In ya je, a school?” Shiruu ya d’an k’ura mata ido sai kuma yace “Inji wa?” Ajiyar zuciya ta sauk’e, wanda har sai da yaji kafin tace “Daman tun jiya na fad’a mishi ‘k’arya me gadin mu yake maka, nasan ba zaka tab’a yin haka ba!’ Wai fa har da cewa kaje kanata fad’a! Ni kuma na san bama ka iya fad’a ba! Shiyasa tun a nan na gane sharrin me gadin ne.” Murmushi yayi sannan yace “ni ina na iya wani fad’a, um?. Jiyan kun yi magana kenan?? I mean da shi Junaidun.” “Eh!” Tace. Shiru yad’an yi kafin yace “Kin je gidan Kaka??” A hankali tace “Eh” Bai yi magana ba itama bata yi magana ba. Chaan! Tace “Ba wai ina son Ya Junaidu ba ne..amman gara komai ya d’an lafa tukunna... …Nan ta zayyano mishi yadda suka yi da Junaidun jiya sannan ta k’ara da cewa “Idan nayi haka ban kyauta masa ba, yayi mini halacci sosai, tun ina k’arama yake raino na, har Mahaifiyarsa yake sab’awa fa duk saboda ni, in dai kaji suna fad’a da ita to akaina ne! Jiya naga b’acin ranshi sosai, kuma ban yi zaton ni yake ta jira ba har ga Allah! Yanata plans ashe, ni duk ban sani ba. Yanzu idan yaji na banzatar da shi despite abunda ya faru tsakanina da shi a jiya amma kawai na sharesa naje an saka ranana or something like that a yanzun, it’ll break him. Dan Allah ka bani time abubuwa su d’an yi settling. In sha Allah nan da y’an wasu kwanaki, idan ya sak’k’o daga fushin I’ll talk and explain everything to him, daga nan sai ayi maganan mu. Amman yanzu idan wani abun ya faru gani zai yi kamar i don’t even care about him! Shiyasa ma jiya da naje gidan Kaka......” …Nan ta fad’a masa yadda sukayi da Kakan! Sannan tace “Please Ya Arshaad don’t get me wrong, babu abunda ya chanja daga promise d’inmu, ba wai ina son Ya Junaidu bane, kawai Ina so ne in yi mishi halacci ko ta yaya ne, saboda abunda yayi min a rayuwa idan nayi mishi haka lokaci guda ban kyauta ba.” Tunda ta fara magana Arshaad ya kafeta da ido ko kyaftawa ya kasa yi! Sai da ta kai aya sannan yace “1 question please” Bai jira jin me zata ce ba yace “If to say, let’s just assume.. Junaidu yace miki yana sonki tun kafin ki tafi school tun farko, zaki kula ni???” Sunkuyar da kanta tayi sannan tace “Muna da issue sosai da family d’in Ya Junaidun, ko da ace na yarda Mama ba zata yarda ba.” “Ba wannan nake tambayar ki ba! Abunda nake son ji shine ‘A zuciyarki, ki cire family d’inshi, just assume kamar ma babu family d’in nasa a duniya! Zaki iya aurenshi?? Do you love him?’.” Shiruuu, tayi sannan tace “Ya Arshaad ai kai zan aura yanzu, mun gama wannan maganan…” Da d’an fad’a yace “Still kin k’i kiyi answering question d’ina! inda bana nan da.....” Ganin yadda take kallon shi ne yasa yayi shiru…ya dafe kanshi, ya lumshe idanunsa for some minutes! Kafin ya bud’e yace “Sorry”. A hankali tace “Ya Arshaad kai zan aura, please ka fahimceni…ba wai ina sonshi bane kawa...” Da sauri ya katseta yana murmushi yace “I understand dear, kawai dama i just want to check ko ‘you have feelings for him’ ne! That’s what the questions are for…..” Zata yi magana yayi saurin sake katseta, ta hanyar cewa “Bara in tafi, ko?” Yayi maganar yana murmushi! Bai jira jin me zata ce ba kawai ya bud’e motar ya shiga ya d’aga mata hannu sannan yayi reverse tana kallonshi ya fice a layin…. Jiki a sanyaye haka ta koma cikin gida. Ko hijabinta bata cire ba Mama wadda gama wayarta kenan da Kaka ta rufeta da fad’a! Kamar zata cinyeta d’anya.. Sannan tace “su tattara kayan su ita da Sakina gobe da sassafe su tafi gidan Ummu Tunda ganin Junaidun da take yi ne yasa take k’ok’arin chanja ra’ayi. Duk ranar data dawo cikin hankalinta sai ta dawo gidan ayi maganar aurensu ita da Arshaad! In ma bata son Arshaad d’inne tou ta nemo wani amman ba Junaidu ba!.” Ita dai Huda karshe ma kuka ta saka. Ta rasa meyasa mutane suke yi mata gurguwar fahimta akan halaccin da take son yiwa Ya Junaidu. Da kyar Sakina ta lallasheta tayi shiru, kamar zata kira Ya Arshaad amman kuma sai tace bara ta kyaleshi dan dukda bai nuna mata komai ba amma gani takeyi kamar ranshi ya b’ac ....... Washegari da safe da kyar Mama ta yarda suka tayata wanke wanke da girkin safe dan daa cewa ma tayi su tafi kawai, ita Hudan har mamakin Mama take yi…ko d’an motsi taji a hanyar d’akin Junaidu ko alamun za a fito nan zata ce mata ta tashi ta shige d’aki da sauri ko ta turata kitchen! A haka dai har suka kammala aikin, ita bata ma yi wani aikin sosai ba dan k’arshe kawai Maman ma ce mata tayi ta shiga d’aki daganan bata sake kiran ta ba! Suna gama breakfast lokacin Mama tana d’akin Baba tana aiki suka yi sauri sukayi wanka dan Sakina cewa tayi “wallahi ba zata fita fuska duk kwantsa ba”. Suna cikin shafa mai Maman ta shigo, tace su yi sauri su tafi ta mik’o musu kud’in mota. Sakina ce ta amsa suka ci gaba da shiryawa a gaggauce dan Mama tsayawa tayi a bakin k’ofa tace ba zata tafi ba sai taga fitar su.. Sakina har hijabinta ta saka Hudan kuma tana cikin d’aura zani sukaji kamar jiniyar y’an sanda… Kafin k’iftawar ido suka jiyo ta a kusa kusa, sai kuma da wani irin k’arfi suka ji an bugo k’ofar gidan!!! Nan suka tabbatar gidan aka zo… Hakan ya sanya Sakina da Mama saurin fita itama Hudan ta rarumi hijabinta ta saka ko ribbon da d’ankwali bata tsaya nema ba! Tana fita jikinta ya hau karkarwa sakamokon sojiji da y’an sanda data gani sunfi ashiri dan taff sun cika gidan. Kusan a tare Hudan da su Umma da Jalila suka fito..suma duk jikin su karkarwa yake yi ganin sojoji fuskar nan a murtuke, ga uban bundugu. Wani a cikinsu ne ya k’araso gaban Mama, da kayan sojiji a jikin shi amman nashi ba kalar na ragowan ba ne, yana zuwa ya nuna musu id card d’insa kafin yace “Muna neman Junaidu Usman Bashir! Mun samu order daga sama! Here” ( yayi maganan yana nuna musu wasu takardu ) Yace “We have a search warrant and arrest warrant!” Umma ce ta matso kusa da Huda, a hankali tace “Me kenan??” Kallonta Hudan tayi sannan ta juya ta kalla mutumin tace “Sir, for what please?” Hannu mutumin ya mik’a baya nan wani ya taho da gudu ya bashi wasu takardu sannan ya sara mishi ya k’ame! Takardan ya hau bincikawa, sai da yazo kan wata ta tsakiya tukunna ya zarota ya mik’awa Hudan.. Da sauri ta sa hannu ta karb’i takardun ta shiga karantawa… Sakina wadda ta matso suke karantawa tare ce ta rafka uban salati sannan tace “Sir this cannot be true he h...” Bindigar da d’ayan ya saita mata a kai ne ya sanyata yin shiru lokaci guda! Jikinta na mugun karkarwa. Umma kuwa fashewa tayi da kuka tana cewa “Me yayi ake nemanshi har da bundugu? Ku fad’a mana dan Allah!” D’akunan gidan mutumin ya yiwa ragowan sojojin nuni sannan ya basu order! Nan da na suka shishhiga suka hau bincike… Su Umma duk suna tsakar gida banda k’arar fashewar abubuwa da fad’uwa ba abunda suke ji… Har kitchen da band’aki sai da suka duba amman babu Junaidu ba labarinshi.. basu samu komai ba. Mutumin ne ya kalli Sakina yace “how are you related to him!” Nan ta fad’a mishi sannan yace mata “Akwai siblings d’inshi ko Mamanshi a nan?” (Duk da turanci). Direct ta juya ta nuna mishi Umma… Nan kuwa Umma ta sake rud’ewa ganin mutumin ya nufota tana cewa “Dan uban ki me nayi kike nunani?” Da gurbatacciyar Hausar shi yace mata “Ina wayanki?” “Tana d’aki” tace, sannan jiki na rawa ta cewa Jalila “ta shiga ta d’auko!” Ana kawo wayar ya karb’a ya mik’a mata sannan yace “Ki kira Yaron ki, kice duk abunda ya kayi ya baro yazo yanzun nan, and kar ki bari ya zargi komai! If not, sai na fasa miki kai da bindigar nan” Jiki na rawa Umma ta hau kiran Junaidu bayan ya umarceta data saka wayar a handsfree…. Sai da ta kusan katsewa tukunna ya d’auka! Daga muryarshi zaka fahimci bacci yake yi.. “Kana Ina?” tace mishi. Shiruuu, yayi. Chaan! Yace “I don’t really know! Ina zuwa, zan kira ki” Har zai kashe tace “dan Allah duk inda kake kazo yanzun nan kaji??” “To” kawai yace sannan ya tsinke wayar. Minti talatin mutumin ya bayar, dan haka yana cika yace “Umma ta sake kiran shi”… Misscalls biyar tayi mishi bai d’auka ba, tana shirin yin na shidda suka ji k’arar parking d’in mota! Bai dad’e ba ya shigo cikin gidan… Kayan jikinshi ne na jiya da yamma a jikinsa, amman kamar harda jini jini sannan duk ya yamushe kamar wanda yayi kokawa. Gabanshi ne ya fad’i dan daman tun a waje yayi karo da wasu sojojin, a tunanin shi ba gidan suka zo ba amma yanzu kam ya tabbatar gidan nasu aka zo. Dan haka ya k’araso da wuri! Yana zuwa yana k’ok’arin yiwa su Umma magana sojojin suka rufar mishi suka hau k’ok’arin datsa mishi ankwa! Ganin haka yasa gaba d’aya suka fashe da kuka har Mama…. Da kyar Sakina ta iya tambayarsu ‘ina zasu kaishi?’. Ba b’ata lokaci mutumin yace mata “K’irik’iri maximum security prison!” Babu irin kuka da burgimar da Umma bata yi ba har waje amman haka aka saka shi a mota aka tafi dashi! Duk ta tara jama’a. Shi kam Junaidu yama kasa magana dan gaba d’aya kanshi a d’aure yake… Da kyar su Mama suka ja Umma suka maida gida sannan Mama ta kira Baba da su Kaka ta gaya musu halin da ake ciki. BULAMA ✍️. So da Buri Free Book 29 Kafin minti ashirin Kaka, Madu, Shuwa, Baaba Talatu, Baaba Laraba da K’asimu sun k’araso cikin gidan!. Baaba Laraba sai lallashin y’arta take yi itama tana nata kukan. Baba ne ya shigo a k’arshe daman shi ake jira, dan haka yana zuwa su Kaka sukace “ba b’ata lokaci, bara a bi sahun su…”. Sai a lokacin tukunna Sakina tayi magana, tace “Sun tafi da shi Lagos fa!”. Wani uban ashaar!! K’asimu ya buga sannan yace “Wai wannan wanne irin rashin mutunci ne! Haka kurum sun zo sun tafi da Yaro, kuma bama zasu barshi a nan ba sun kama sun kaishi har Lagos!! Sai kace wanda akace yayi kisan kai! Sun fad’a muku laifin da yayi??”. Cikin Kuka Hudan ta share hawayenta sannan tace “A jikin takardan cewa aka yi wai ‘sun yi fashi su uku a gidan cheif justice jiya kuma sun kasheshi sun kashe y’ay’an shi hud’u!”. Salati tsakar gidan ya d’auka, gaba d’aya. Baba kuwa dab’ass!! Haka ya zauna a k’asa… Da sauri Umma tace “wallahi k’arya ne, sharri aka yi mishi, Junaidu tun yana Yaro ko cinnaka idan ya cije shi baya kashewa ballantana mutum, wallahi k’arya ne.” Kaka ne yace “Sadiya ki yi shiru, kowa anan ya san k’arya ne, abun da ya kamacemu yanzu shine addua sai kuma mu nemo lawyer mu fara k’ok’arin fitar da shi ko? Tunda kunga har an tafi dashi.” ….. Nan suka hau shirye shirye aka ware masu tafiya Lagos d’in, sannan suka kira Ya Jamilu (Yayan Baba) shima. Kuma suka nemo lawyer sannan aka yi shirin tafiya….. Gidan Ummu za su fara zuwa su tambayi Mijinta akan ya barta a tafi da ita tunda lawyer ce itama mai zaman kanta.. Hakan kuwa aka yi a ranar zasu bishi. Sai da suka raba sauk’ar Al Qurani da addu’o’i a wajaje daban daban, sannan suka d’au azumi kaff d’insu, har Jalila wadda rabonta da azumi har ta manta wai tana da ulcer Umma kuwa ko da yaushe cewa take yi “ai Allah ma ya ga zuciyarta kuma shine ya d’aura mata rashin lafiyar”. Baba, Madu, Ummu, Kaka sai d’ayan lawyern da aka tafi da shi ne suka kama hanyar Lagos, sai washegarin ranar tukunna suka samu kansu bayan sunyi settling a hotel d’in da suka kama lokacin Ya Jamilu shima ya k’araso dan haka ba tare da b’ata lokaci ba suka nufi inda aka kaishi!. A nan ran Kaka ya sake b’aci da yaga wajen da aka kaishi d’in! Shi da ba a gama tabbatar da laifin shi ba saboda Allah meyasa zasu kawoshi prison?! Haka nan yayita fad’a su Ummu suna bashi hak’uri… da kyar yayi shiru suka nufi gate d’in.. Kalar binciken da ake yi musu duk wanda ya gani zai yi tunanin ‘sun zo ganin wani hamshak’in d’an ta’adda ne’. Kuma dukda haka cewa akayi “sai dai mutum uku su shiga ba zai yiu su shiga su duka ba!”. Baba, Ummu sai d’ayan lawyer d’in da aka tafi da shi ne suka shiga, shi kam Ya Jamilu ID card kawai ya nuna musu ya wuce… Bayan y’an gwaje gwaje aka kaisu wajen zama (chan gaba da parking lot) aka ce “su jira shi a nan” Anfi 30 minutes tukunna aka fito da shi. Daga nesa da ya taho basu gane sa ba sai da aka matso dashi aka zaunar, tukunna. Kuka kawai Baba yasa yayi saurin tashi a wajen. Mai tsaron da ya kawo shi ne ya had’asu ya bashi iya lokutan da yake dasu sannan yad’an koma gefe kad’an ya tsaya. Ganin basu da isheshshen lokaci yasa Ummu tace “Junaidu, how are you?” Ahankali muryar shi baya fita sosai yace “Alhamdulillah” Ba tare da b’ata lokaci ba tace “ya aka yi? Mai ya faru? Me ka sani?”. D’an gyara zama yayi tukunna ya fara magana….. “…...shekaran jiya da daddare ina d’akin Abokina. Ba a Kano yake ba, a nan Lagos yake, amma yana da apartment a Kano d’in. Shekaran jiyan ya kira ni yace mini ‘zai shigo gari amman a jiya zai koma kuma akwai wani aiki da za muyi akwai samu a ciki sosai! In da hali yana son ganina sharp sharp’. Nan da nan nace mishi gani nan zuwa. Ina zuwa ba tare da b’ata lokaci ba ya hau yi mini bayanin business d’in.. ..’Wake ne zamu kawo daga Taraba, ko wanne a kan 9k zamu siya amman idan yazo Kano zamu iya siyarwa a kan 23k! Kuma kud’in mota dududu bai fi mu biya dubu arba’in ba dan ya san wani me mota da suke irin wannan harkar, sannan za a kawo mana buhu sama da d’ari, a mota daya!’. Nan da nan na amince… Muna cikin maganar wata ta shigo har d’akin ta kawo mana Lemo.. Ban kawo komai a raina ba dan irin gidan hayan nan yake kowa da dakinshi, da band’aki mai kyau sosai, compound dinsu ne kawai d’aya, and tsarin d’akin har da d’an mini kitchen a ta chan gefe da d’an k’aramin dining kamar dai na turawa. Na san shi, bashi da sakewa da mutum bashi da saurin yarda in ba wai ya san ka sosai ba! Yadda suke wasa da barkwanci da wadda ta kawo lemon yasa na gane ya santa sosai shiyasa na aminta ba sha… Amman wani abun mamaki sip d’aya kawai nayi wa lemon ko ciki na bana jin ya k’arasa shiga na fara ganin uku uku! Daga nan ban sake sanin inda kaina yake ba....... K’arar k’aramar wayata ce ta farkar dani daga wani irin bacci… Mamakin d’akin da na tsinci kaina na dinga yi dan ban san inane ba! Amman har da mukullin mota na a hannu na. Sai dai babu wallet d’ina kuma ba babbar wayata. Yadda naji muryar Umma a waya ne ya sanya nayi saurin fitowa, ban ma san layin ba! Gidane mai bene mai kyau sosai amman duk k’ofofin a bud’e da alama an bud’e mini ne dan in fita!. Ina fitowa naga motata a parke, dan haka nayi gaggawar shiga na taho… Sai da na fito titi tukunna na gane ashe a chan cikin Farawa nake......... Tun lokacin da suka taho dani kwakwalwata take min flashin wasu abubuwa kamar mafarki Amman na gane a shekaran jiya abun ya faru dan da kayan nan na jikina nake ganina!”. Ajjiyar zuciya Ummu ta sauk’e sannan tace “suna interrogating d’inka ne?” “Sosai ma!” yace, sannan yaci gaba “In fact sai sun dake ni ma idan na suma most in zan farfad’o ne memories d’in suke flashing… Amman d’azu da safe around 8 sun kawo wasu takardu har da flash! Ina wajen suka ce a maidani ciki tou tun daga lokacin basu sake yi min komai ba. D’ayan d’an sandan ne yake ce min wai ‘Allah ya taimakeni amman still in ci gaba da addu a’.” Sauke ajiyar zuciya lawyer d’in da Ummu suka yi a tare bayan sun gama rubuce rubucen su!.. Tabbas this is a very serious case, kisan kai ga fashi, ko da ace bai yi komai ba in dai dashi aka je wajen to hukuncinshi d’aya ne da waenda suka yi aikin, wanda definitely ‘kisa’ ne!. Maganar shi ce ta dawo da Ummu daga duniyar tunanin data tafi jin yana cewa “Ummu na rantse da Allah gaskiya na fad’a miki duk maganar nan Wallahi ban tab’a fashi ba, ballantana kisan kai, ko bayan rai na, ki fad’awa Hudan wannan maganar, wallahi ni ba d’an fashi bane ba!” Yana gama fad’in haka ya fashe da kuka. Tausayin shi ne ya sa Ummu itama ta fara hawaye.. Tabbas ta yarda da Junaidu to amman wannan k’atamurmurar Allah kad’ai ne zai fitar da shi! Dan bama taga ta inda zasu fara neman evidence domin kare shi ba!. Wani mutum sanye cikin suit da sojoji biyu a gefe da gefen shi ne ya tunkaro su. Suna hangoshi Ummu tayi saurin goge hawayenta sannan suka mik’e tsaye. Ba tare da b’ata lokaci ba ya cewa su Ummu su biyoshi sannan a mayar da Junaidu inda aka d’auko shi .......... Bayan kamar 2 hours su Ummu suka fito suka tarar da su Madu a inda suka barsu. Suna ganin su tun kafin su k’arasa wajen motar su suka iso garesu suka hau tambayarsu halin da ake ciki D’ayar lawyer d’inne yace musu “su k’arasa mota za suyi musu bayani a chan.. Ganin basu fito tare da Junaidun ba gashi kuma sun k’i yi musu bayani ya sanya tun a nan jikin su Madu yayi sanyi. Ko a motar ma Ummu da taa yunk’ura zata fara bayani sai kuma tayi shiru dan bama ta san ta ina zata fara ba! Sai da suka k’arasa hotel d’in, bayan sun fiffito Kaka yace “su je garden, su tattauna a chan!” Zama suka yi aka kawo musu d’an abun sha tukunna bayan sun huta Ummu tace “Kaka Junaidu is innocent! duk da cewa na san duk mun san da hakan amma yanzu haka suma mutanen da kansu sun san cewa bashi da laifin komai.” “Alhamdulillah” Gaba d’ayansu suka furta kafin Kaka yace “tou dan maiyasa suka kamashi saboda Allah? Sannan maiyasa baku taho da shi ba?”. D’ayan lawyer d’in ne yace “A jiya da suka zo suka tafi da shi basu san babu shi a laifin ba! Asalima shine prime suspect saboda wayarshi da wallet d’inshi dake a wajen sannan bindigar da aka yi amfani da ita aka harbi mutumin da aka duba hannun Junaidu ne ya fito a jiki… Babu kalar duka da horon da basuyi mishi ba amman shi dai magana d’aya yake maimaita musu, itace maganar daya fad’a mana d’azu ni da Ummu ‘He’s innocent!’ iya abunda ya faru da shi na gaskiya yake fada.. Shiyasa suka d’an saka kokwonta a lamarin. Kuma tun jiya da daddare suka tsananta bincike a gidan mutumin…nan kuwa aka samu wata b’oyayyiyar camera a parlour wadda babu wanda ya isa ya ganta, dan su kansu sai da camera detector tukunna suka iya ganota a jikin chandelier! Nan da nan kuwa suka d’auka suka turo nan. D’azu muna tare da shi Junaidun, aka zo aka kira mu, a ofice d’in muka samu Ya Jamilu shima.. Ba tare da b’ata lokaci ba mutumin ya nuna mana video din...... …’Shi Junaidu a sume ma wasu mutane guda biyu da mask suka shiga da shi, bayan wasu k’arti biyar sun firfito da CJ d’in da Yaran shi sun d’add’aure, ana shiga da shi d’ayan yayi mishi wata allura sannan ya hau yayyafa mishi ruwa yana marin gefen fuskarshi… Da kyar ya farka sai dai kana ganinshi ka san baya hayyacinshi sannan suna mik’ar dashi tsaye ya koma ya sume… Babu yadda ba suyi da shi ba amma yak’i farkawa. Nan d’ayan wanda suka shigo dashi ya koma gefe ya fara waya, bama jin abunda suke fad’a kwata kwata saboda camerar babu voice. Yana gama wayar ya d’auki video d’in Junaidu da parlourn ya turawa wanda muke tunanin ya gama waya dashi. After some minutes aka sake kiranshi, yana gama wayar ya zo ya kama hannun Junaidu (bayan ya sakawa nashi hannun socks da leda) ya damk’e bindigar da hannun Junaidu wanda yake ta baccinshi..sai dai okaci zuwa lokaci ya kan d’an bud’e idanununshi sai kuma ya maidasu ya kulle… Bayan sun damk’a mishi bindigar ba tare da b’ata lokaci ba suka saita kan CJ d’in suka harba daga nan ragowar suka harharbe Yaransa… Da alama k’arar jiniya sukaji dan lokaci d’aya suka rikice! Kan kujera d’ayan ya hau ya dan daddaki p.o.p d’in wajen kamar yana knocking Daga nan yasa hannu ya d’an fara jaaaa! Kamar akwai mai taimaka mishi a take suka janye ya d’aura a kan kujera. Ladder, d’in da aka zuro mishi ne yasa muka gane akai wani a saman a cikin ceiling d’in. Sai da d’ayan ya cire wallet da wayar Junaidu ya yar a tsakar falon da bindigar da aka kashe CJ d’in da ita sannan ya ciccib’eshi ya fara haurawa da shi saman.. Yana gama hawa ragowar ma suka ciccib’i maka makan akwatunan da suke a parlourn da alama kud’ad’e ne a ciki suka bi bayanshi suka haye. Last one d’in ne ya d’auko dakin pop d’in da suka cire suka taimaka mishi suka jaa wajen suka rufe tsaff yadda duk k’urillar mutum bai isa ya gane wajen a fashe yake ba....” Ajiyar zuciya ya sauk’e sannan yace “Ba yadda bamu yi da shi akan ya barmu mu tafi da Junaidu ba amman yace mana “kasancewar wanda aka kashe babban mutum ne! Wallahi an basu kwakkwarar doka akan kar a sakeshi har sai an gama case d’in! Kuma kafin ma a samu ayi settling a gama mourning rasuwar nan sai anyi wajen wata d’aya ko sama da haka. Guda biyu masu mask d’in an rasa su, dan waenda akayi fashin da su ragowar mutane ukun d’ayan tun a jiya aka ga gawar shi ba a san wa ya kashesa ba! Su kuma ragowar biyun awa biyu da suka wuce aka samesu da kyar a Bauchi An harbi d’ayan dan yayi attempting guduwa ne Shi kuma d’ayan yace ‘wallahi bai tab’a ganinsu ba bai san ya yanayin fuskarsu ta asali take ba! Dan tun a lokacin da suka zo musu da tayin aikin ma da mask a fuskokinsu….dan haka basu tab’a ganin fuskokinsu ba kuma basu damu da su gani d’in ba saboda su ta kud’in kawai suke kuma sunyi musu alk’awarin in dai aka yi fashin duk kud’in da aka samu nasu ne dan su ba zasu tab’a ko sisi a ciki ba, basa buk’ata......” Kuka Baba ya saka kafin yace “Yanzu kenan Junaidu a wannan waje zai yi ta zama kenan har sai an yankewa waenchan hukuncinshi?? Har zuwa yaushe kenan?” Ummu ce ta share hawayenta kafin tace “Wallahi Baba muma bamu sani ba. Kawai dai mu ci gaba da addu’a, dan na tabbatar addu armu ce da taimakon Ubangiji ya sa aka ga wannan b’oyayyiyar camerar! Kuma mutumin yayi min alk’awarin ba zai bari a bashi horo ba ko ta yaya. Dan a office d’in wani Abokin Ya Jamilu ma suka nuna mana suka ce zai ci gaba da zama. Sannan Ya Jamilu har yanzu yana chan yana dubawa in an samu rara anytime from now zasu iya tahowa, in kuma sun k’i yarda to sai dai mu yi hak’uri mutu ta addua. Dan mutumin yace zuwa gobe za‘a rufe ganin su sai ranar da za a fara zuwa kotu! So in dai Ya Jamilu bai dace a yau ba, sai dai mu jira ranar. Amman mutumin yayi mana alk’awari ya sake yi mana alkawari a kan ba zai bari a cutar da shi ko ya wahala ba..........” Sun yi zaman jira kam har washegari, da safe ganin Ya Jamilu ya dawo shi kad’ai yasa duk jikinsu yayi sanyi. Haka nan su Ummu suna ji suna gani washegari suka shirya suka tafi suka bar Junaidu a Lagos tare da addu’o’i bila adadin.. Dan da safe ma su Baba basu sare ba sai da suka koma sai dai ba yadda ba suyi ba amma aka hana su ganinshi.......... Haka nan suka dawo jiki duk a mace. Umma tayi kuka tayi kuka kamar ranta zai fita. Itama Jalila kamar mara lafiya. Duk gidan ma sai ya koma kamar na marasa lafiya in ka shigo sai ka d’auka rasuwa aka yi! Tun ba ma da su Kaka suka dawo suka sanar musu halin da ake ciki ba, sai kawai suka d’au kuka dukkansu, sai da Madu da Kaka suka tsawatar musu, sannan, suka ce “ai kamata ma yayi suyi murna, tunda an gano bashi da laifin komai, kawai dai d’an zama ne zai yi a wajen kafin a gama yanke hukunci daganan ya dawo gida in sha Allah.” Tukunna fa aka samu gidan ya d’an nutsu. ............. Nasarawa gra. Saturday. MT estate. A gajiye Auwal ya dawo yau dan aiki yayi mishi yawa! Kwana biyun nan. Saboda Granpa ya had’a mishi har da aikin Arshaad yace “ya dinga yi”, shi kuma son gwaninta baya so aga kasawar shi shiyasa yake aiki tuk’uru! Jiya ko rintsawa bai yi ba. Yana shiga ya gama parking motarsa kenan wayarsa ta hau ringing! Da farko kamar ba zai d’auka ba sai kuma ya lalumo wayar a sit d’in gefen shi inda ya jefata tun jiya da rana (idan zai tuna kenan) daga nan bai sake bi ta kanta ba! Hannunshi ya kai kan wayar yayi tsaki kafin yace “Wannan tsohon so yake yi ya kashe ni da aiki wallahi!”. Yana duba screen d’in sai yaga sunan ‘Micheal’ dan haka ya amsa yana kaiwa kunnenshi kafin yace “Talk to me Mik’e, just get straight to the point plss.” “Sir, I followed him day b4 yesterday and naga yaje wani unguwa, ban san sunan unguwar ba but zan gane zan iya kaika! I hid myself dan kar ya ganni. Yana fitowa naga ya d’auko waya yayi kira.. After kaman 5 minutes wata fine yellow girl! Ta fito da abaya maroon colour, the way he’s talking and smiling na san itace…. Suna tsaye wani ya zo a moto ya shiga gidan da Yarinyar ta fito. Bayan Arshaad ya tafi sai nake tunanin ya za ai in san sunanta ban sani ba, kawai sai wannan saurayi da ya shiga gidan naga ya fito ya zo wajen mai pos sunata hira sosai, i wanted to go and ask (mai pos) amman inaso sai saurayin ya bar wajen dan maybe ko brother d’inta ne kar inje inyi tambaya a gabanshi yasa question mark a kaina. To dai inata jira inata jira ashe nayi bacci a moto ban saniba..sai da gari yayi duhu na farka naji ana kiran sallah, me pos kuma ya tashi!.” Tsaki Auwal yayi sannan yace Ji banza, anyways your information will help meet me yanz…” Da sauri Mike ya katseshi yana dariya kafin yace “Sir, ai na koma jiya, na tambayo shiyasa ma kaga ban kiraka tun shekaran jiyan ba, i wanted to complete my job fully. Jiya da safe naje na samu mai pos d’in! Nace mishi ‘jiya nazo wucewa wata Yarinya da abaya maroon a nan gidan’ (na nuna mishi gidan) Sannan nace ‘naga ta jefar da takarda maybe bata sani ba, please meye sunanta zan aika In ce tazo ta karb’a.’ Da farko bai ganeba, dan ce mini ma yayi ‘bai ga wata Yarinya ta fito daga gidan ba jiya dan ya d’an fita!’ Sai da nace mishi ‘k’anwar wanda ya zauna suka yi ta hira jiya da ya fito daga gidan shima’. Tukunnan! Da farko cewa yayi In kawo takardan zai bata ni kuma na k’i yarda… Haka nan k’arshe dai ya hak’ura yace min sunanta ‘JALILA!’. Ina barin wajennasa na nufi k’ofar gidan, nayi kamar naje gidan, na d’an jira kad’an. Da naga baya kallona na dawo na zo na shiga moto nayi tafiyana… Shiyasa tun jiya nake ta kiranka kai kuma baka amsa waya. i wanted to tell you akwai good news bu...” Auwal wanda surutun Michael ke neman k’ara mishi ciwon kai ne yace “Ok Mike, ai ka gama fad’a min all i want to hear ya isa haka!! Meet me nan da 30 minutes sai muje ka nuna min gidan!” Har zai kashe yaji Mike d’in yana d’an murmushi k’asa k’asa yana cewa “Sir about the money fa?” Da d’an k’arfi Auwal yace “Meet me nan da 30 minute!!!” Sannan ya kashe wayar. Da kyar yake tafiya dan sai yanzu baccin da bai yi jiya ba ya fara d’ibarsa! Yana isa side d’inshi kuwa wanka kawai yayi ya fad’a gado, a take yaji wani bacci mai mugun dad’i yana fisgar shi, gudun kar a katse mishi baccin shi yasa ya kwaso gaba d’aya wayoyinshi ya saka su a silent. Bai tashi ba sai pass 9! Da mik’a ya farka sannan ya wuce toilet…. Sai da ya d’an yi freshening up yayi alwala tukunna ya fito ya jero sallolin shi!. Yana idar wa ya hango d’aya daga cikin wayoyinshi tana haske. Tsaki yayi sannan ya nufi gadon yana zuwa yaga sunan ‘Granpa’ b’aro b’aro a kan screen d’in! Kafin ya d’auka har ta tsinke Da sauri ya d’auka wayar ya bud’e ga mamakinshi yaga wajen 30 misscalls! Tsaki yayi ganin wajen 20 duk na Mike ne. K’ok’arin dialing number Granpa yayi amman sai nashi kiran ya shigo! Hakan yasa ya d’auka bai kara a kunne ba ya saka ta a speaker. “Meet me, right now!” Kawai Granpa yace mishi sannan ya kashe wayar. Tsaki ya sake yi a karo na ba adadi sannan yace “D’an masu da bada order!” Yana ta k’unci haka nan ya shirya cikin pyjamas sky blue da d’an ratsin black, yayi mai kyau kuwa sosai. Wayarshi guda d’aya ya d’auka ya sanya a aljihu ya bar ragowan ya fito ya nufi side d’in Granpa. A compound d’inshi ya sameshi, a wani had’add’en garden haske ta koina tarr!!kamar rana. Daidaita kanshi yayi sannan ya d’an saki fuska kafin ya k’arasa wajenshi. Ko gaisuwarshi kuwa Granpa bai amsa ba ya rufeshi da fad’a! Ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, sannan daga k’arshe yace “idan ba zai iya bane ya bar mishi company d’inshi ai daman ragowar ma ba shine yake kula mishi da su ba! Wannan d’in dama dan yaga a tsakaninsu (jikokinsa ) yake son bawa mutum d’aya shiyasa yake d’orasu a kai saboda yana so yaga ko zasu iya, but tunda yaga kamar ba lalle su iya d’inba! Kawai zai chanja shawara ya bawa Yahaya ko Yusuf dan ba zai yiu ya d’auki something that is so dear to him ya bayar a wrong hand ba! Company d’in is very dear to him ne it’s like something da suka yi shi da brother d’inshi. Bayaso Company d’in ya samu matsala ta koina shiyasa yake son bawa individual dan sai anfi kula da shi ta hakan, sab’anin idan mutum ya san ba nashi bane shi kad’ai, to ba lalle ya zage damtse kamar yadda zai yi idan nashi ne shi kad’ai ba. Yana buk’atar jajirtacce tsakanin shi(Auwal), Aslam ko Arshaad! Yana ganin su Dad yanzu girma ya fara zuwa musu, besides kuma duk akwai companies d’in da ta mallaka musu each, ba lalle su iya ba. To kuma gashi su d’in (jikokinsa) da ya kwallafa rai gashi suna k’ok’arin bashi kunya! Meye amfanin su? wish d’inshi na passing company d’in to an individual from generation to generation ya tashi a aiki kenan? Gaba d’ayan su basu da amfani daga shi har Arshaad, har gara ma Aslam wanda dukda tarin aikin da yayi mishi yawa hakan bai sa ya nuna gazawa ba a b’angaren kula da branch na company d’in nasu da yake a chan! Aiki yake yi tuk’uru bil hakk’i da gaskiya! Su kuwa a nan daga b’arawo sai mai son jiki.” Sai da Granpa yayi mishi tatas!! tukunna ya tashi ya barshi a wajen ko kallonshi bai kuma yi ba, ballantana ya tsaya sauraron hak’urin da yake ta faman bashi. Auwal ji yayi kamar ya shak’e kanshi da kanshi tsabar takaici! He tried so much for all this amman sai da abu ya kusan zuwa gangara zai fara nuna gajiyawa a time d’in da ya kamata ya zage damtse?! Tabbas maganar Babansa (Daddy) da yake cewa “babban companyn Granpa… Ya tab’a cewa kyautar shi zai yi a mutum d’aya tak! To amman ba lalle a tsakanin su brothers su uku zai bawa ba, tunda company d’in flour n su a hannunshi( Yusuf) yake, na textiles kuma Dad (Yahaya) ne akai a chan Abuja shiyasa ma bai cika zama ba, na oils kuma Abba (Ya’akub) ne dudda yanzu an cireshi an sake bawa Daddy( Yusuf) d’in shiyasa ma aiki yayi mishi yawa. To wannan babban na MAI TURARE and Co. wanda har a Uk suna da branch tabbas kyautar shi zai yi amman a tsakanin jikokin su uku, duk mai rabo.” Gaskiya ce kenan? A hankali Auwal ya sauk’e ajiyar zuciya, yace “Daa chan, da na d’auki maganar under probability ma nayi k’arfi da k’arfe wajen ganin na mallaki company d’in, ballantana yanzu da naji daga bakin oga kwata kwata ai sai inda k’arfi na ya k’are!.” Juyawa yayi ya kalli hanyar da Granpa ya bi ya wuce.. Murmushi yayi kafin yace “Old man, you may be older but I’m smarter.. Lokacin da zaka sauk’o daga fushin nan ma, baka sani ba.” Yana gana fad’in haka ya juya ya wuce tare da plans barkatai a ranshi. Ko da yaje kwanciya ma sai da ya gama shirya yadda zai wanke kanshi a wajen Granpa ta hanyar yin aiki tuk’uru ba tare da an saka shi ba ma! Dan ya samu ya dawo da martabar shi a idon Granpa, sai wajen 12:30 bayan ya zab’i dandatsetsiyar shaddar da zai saka gobe idan zai je wajen Jalila, tukunna na ya kwanta........ 1:00am a airport tayiwa Arshaad, duk da kuwa sun yi waya ba da jimawa ba yace mishi “sun samu delay gashi akwai transit so sai 2:30 flight din zai yi landing a Kano!.” Amman tun 12 ya shirya da kyar ya bari 1:00 d’in ma tayi, ya fita. Kamar yadda Aslam ya fad’a masa ‘2:30 am’ d’in tana yi, Arshaad d’in ya isa wajen arrivals ya tsaya. Har ya d’an fara gajiya dan ya fi 20 minutes a tsaye kuma sai kiran shi yake yi baya d’auka! D’ago wayar shi yayi a karo na ba adadi da niyyar sake kiran nashi sai kuma ya sauk’e wayar yana kallon setin shi ya hau murmushi…. Sanye yake cikin normal sleeve golden color ta ciki, ta waje kuma ya d’aura slim fit suit a kai white colour, takalminshi da wandonshi suma duk white sai agogon hannunsa ne shi kuma ya kasance gold jaguar special edition!. Dogo ne, dan ya fi Arshaad tsayi.. Sannan kyakkyawane ajin farko! Hasken fatarshi bai kai na Arshaad ba, amman dai shima ba bak’i bane ba. Yana da doguwar fuska wadda take zagaye da lallausan saje da gashin baki, baki wuluk! Yana da madaidaitan idanuwa masu oval shape da straight cikakkiyar gira, hancinshi dogo ne sosai kamar yadda yanayin fuskar tashi take.. Sai d’an mitsitsin bakinshi wanda ya k’arawa fuskar tashi tsari da ainahin kyau mai aji!. Tafe yake yana jan d’an matsakaicin trolley d’inshi yana amsa waya. Magana yake yi amman kamar baya so yayi…da alama ma bai lura da Arshaad d’inba K’arasawa yayi towards inda yake dede lokacin yana hanging up call d’in. Ji yayi anyi hugging d’inshi kawai, wanda ko bai ga waye ba ya san Arshaad ne “Welcome back bro” yace mishi kafin ya cika shi yana murmushi yace “I miss u, a lot.” Kallonshi Aslam yayi, a hankali yace “mee too”. Trolley d’in tasa Arshaad ya karb’a suka k’arasa mota Arshaad d’in yana tambayarshi “ya uk?”. “Alhamdulillah” kawai Aslam d’in ya iya cewa. A haka suka k’arasa motar suka shiga suka zauna Arshaad ne ke ta magana Aslam kuma daga ‘ummm’ sai ‘um um’ k’arshema ajiyar zuciya ya sauk’e daga haka ya d’an jingina kanshi ya runtse idanuwanshi… Ganin haka yasa Arshaad d’in yin shiru shima bai sake cewa komai ba har suka iso. Gidansu Aslam suka nufa direct! Arshaad ya d’anyi horn kad’an. Mai gadi ne ya d’an lek’o ganin motar yasa shi saurin bud’ewa ba tare da tmbayar dalilin zuwanshi da mota cikin dare ba. A hankali ya k’arasa da motar kamar baya so yayi parking d’inta a parking space kafin yad’an kalleshi, in a calm voice yace “Mun iso.” “Tnx” Kawai Aslam yace bayan ya d’ago ya bud’e idanuwan nashi sannan ya fara k’ok’arin bud’e motar… A hankali Arshaad yace “Are you sure a nan zaka sauk’a?! Ka zo kawai muje chan mana, a side d’ina akwai rooms sai ka zab’i d’aya.” Juyowa Aslam d’in yayi ya kalleshi sannan yace “I’m good, open the door pls it’s late.” “Well, you don’t seems good!! Ina lura da mood d’inka tun d’azu ai, you look disturbed and scared! Ka zo muje gobe sai a san abun yi!” Arshaad d’in ya fad’a cikin d’an tsare gida. Komawa kawai ya ga Aslam d’in yayi ya kwantar da kanshi a jikin seat d’in sannan ya mayar da idanuwansa ya lumshe. Ganin haka kawai yasa Arshaad ya bud’e mishi lock d’in, dan ya san tunda Aslam d’in yayi haka to idan zasu dauwwama a nan shi fa ya gama magana kenan!. Yana bud’e mishi kuwa ya sa k’afa ya fice… fitowa Arshaad d’in yayi shima ya zagaya ya d’auko mishi trolley d’inshi. Har bakin main door na parlour d’in ya rakoshi tukunna yace “Zan juya daga nan” Hannu kawai ya saka ya karb’i trolley d’in sannan yace , “Thankyou Arshaad.” Har Arshaad ya juya zai tafi sai kuma ya juyo yace “You sure about this??” “Yeah” kawai Aslam yace mishi sannan ya k’arasa ya danna door bell. Ya jima a wajen sosai tukunna wata y’ar dattijuwa mara jiki sosai tazo ta bud’e k’ofar. Tana ganin shi tace “ai kuwa kai d’inne, tun d’azu nake ta lek’owa ta ramin nan inaso in tabbatar! D’an albarka….” Sai kuma kawai ta fad’a jikin shi ta fashe da kuka. Murmushi yayi sannan ya d’an yi tapping bayan ta alamun rarrashi kafin yace “Kin tare ni a k’ofa ko dai in koma ne? Daman Arshaad sai tallar ‘inje In kwana a gidansu’ yake ta yi min.” Da sauri ta cika shi tana d’an murmushi, sannan ta bashi hanya ya wuce…. “Home sweet home” shine abinda ya furta kafin a hankali ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya, sannan ya d’an lumshe idanuwanshi da suka fara chanja launi a hankali ya bud’e su. Murmushi ‘Gwaggo Asabe’ tayi tana k’ara girmama k’ok’ari da k’arfin hali irin na Aslam! Sarai take hango abubuwa barkatai a idanunshi amman shi k’ok’ari ma yake ya b’oye har da janta da wasa duk dan kar ta gane kuma ta damu. “Dad, yana Abuja ko?” Taji muryar shi. “Eh” tace, sannan tace zauna in kawo maka wani abun ka d’an sakawa cikin naka, ko?”. Har tayi hanyar kitchen yayi saurin dakatar da ita ta hanyar cewa “No, I’m full fa. Naci abinci sosai a jirgi, sai dai gobe da safe pls ayi min d’an wake, i miss it.” Murmushi tayi bayan ta juyo sannan tace “Tam shikenan Aslam, sannu ko” Har yayi hanyar side d’inshi dake a nan k’asan, sai kuma ya juyo yace “Ta fara baccin dare kenan! Na ji shiru” Ajiyar zuciya Gwaggo Asabe ta sauk’e kafin tace “Bata dad’e da yi ba, dan ko minti ashirin bana jin anyi, shiyasa ma ka tarar dani idanuna biyu. Amman dai gaskiya yau kusan shekara biyar ai na fada maka tun a waya, wannan koke koken duk babu, har takan zauna ayi hira da ita fa wasu lokutan, matsalar sai an sauk’k’o k’asa! Tana yin ido biyu da b’angaren ka zata fara!”. Da sauri Aslam yace “Bara inje in yi wanka.” Bai jira jin me zata ce ba ya tura sliding glass door d’in side d’in nashi ya shige sannan ya mayar ya rufe…… Bayan yayi wanka ya sha tea. Kwata kwata sai ya kasa bacci, hakan yaasa kawai ya mik’e ya fito daga side d’in nashi, parlourn ba kowa hakan na nufin Gwaggo Asabe har tayi bacci kenan dan duk bulbs d’in ma an kashe su. K’arasawa yayi Inda staircase na hannun dama yake sannan ya kama ya fara hawa… A hankali yake kallon parlourn yana nan yadda ya sanshi! Da sauri ya runtse idonuwanshi ya tsaya cak! Sakamokon wasu memories da suka fara flashin….. Sai da yayi y’an addu’o’i sannan nutsawarshi ta dawo, ya samu ya ci gaba da tafiya. A hankali ya k’arasa inda bedroom d’inta yake! Sai da ya sauk’e tagwayen ajjiyar zuciya kafin yasa hannu a kan handle d’in ya d’an murd’a a ransa yana adduar ‘Allah yasa a bud’e ne’ Aikuwa yana murd’awa k’ofar ta bud’u!. Ajiyar zuciya ya sauk’e sannan ya kutsa kai ya shige d’akin tare da mayar da k’ofar ya rufeta.... BULAMA ✍️. So da Buri Free Book 30 D’akin da d’an duhu amman ba chan sosai ba sakamokon side lamps d’in da suke a kunne wanda hakan ya bashi daman hango ta kwance a kan gadon. A hankali ya k’arasa ya zauna a gefen gadon. A kwance take, rigingine.. pillows wajen uku aka d’aura kanta a kai hannayenta duka biyu tayi folding d’insu a kan cikinta! Kalar fata ta iri d’ayane da ta Aslam, sai dai shi ya d’an fi ta haske kad’an. Babu d’ankwali a kanta, wanda hakan ya bawa gashin kanta damar baiyyana wanda yake nan rabinsa bak’i rabi furfura! Mai santsi da shek’i had’e da tsaho sosai. Shekarunta ba zasu wuce hamsin ba…kallo d’aya tak! Zakayi mata ka gano kyakkyawa ce ajin farko. Yanayin hancinta ne Aslam d’in ya d’auko sai dai nata har ya d’an so yafi nashi tsayi da tsaruwa amma saboda yanayin na Yarinta yasa za’a iya cewa ya fita kyau..... Hannunshi ya saka ya kamo nata sannan ya d’aura d’ayan hannun nasa a kai ya dunk’ule a hankali ya saka guiwowin hannayenshi a kan gadon for sopport kafin ya d’aura fuskarshi a kan hannayen nasu ! Tunani ya fara ‘rabonshi da ita yau shekaru bakwai! Kenan.... ........Tun lokacin da psychiatric Doctor d’inta yace musu “the last option d’in da suke dashi shine a kulle su a d’aki d’aya, daga ita sai shi sannan a d’aure hannayenta da k’afafuwanta gudun kar ta cutar da shi ko ita kanta. Hatta abinci ana so ya zamana shi ne zai dinga bata a baki, yayi mata alwala yayi mata komai for 24 hours! May be daga hakan tayi snapping out, ta dawo cikin hankalinta.” Tun a 12 hours Aslam ya ga ba zai iya ba domin kuwa tak’i chin abinci kuma daga ya matso kusa da ita sai ihu! K’arshe ma suma ta fara yi… Gaba d’aya duk ta firgice. Ganin haka yasa ya d’auki waya ya kira Dad wanda shima d’in jin da yayi tanata suma yasa yace “bara ya zo ya gani.” Sannan ya kira Doctor, shima Doctor d’in yace gashi nan zuwa. Dad d’in yana zuwa yayi knocking k’ofa Aslam ya bud’e, basu ankara ba kafin ya shigo ta taho da gudu ta hankad’o Aslam d’in waje ashe ta kunce hannayenta ba tare da ta bari ya lura ba! A take ta saka key… Ba suyi wata wata ba Aslam ya fara k’ok’arin b’alla k’ofar Dad kuma ya tafi ya d’auko spare key!…Amman ko da ya zo ya saka k’ofar k’in bud’uwa tayi sakamokon barin key d’in da tayi a jiki ta ciki.. Suna cikin kiciniyar bud’ewa suka ji k’arar fad’uwar abu kamar kujera, a rikice Aslam yayi kan 3 seater d’in da take a parlourn ya cewa Dad “ya zo ya kama mishi”. Haka suka kinkimi kujerar da kyar, suka yi kan k’ofar da gudu da k’arfi suka buga! Allah ya taimake su kuwa ta bud’u…. Aslam kasa motsi yayi sakamokon ganin k’afafuwanta a sama suna lilo kanta kuma tayi hanging a jikin chandelier d’in d’akin, sai dai k’afafuwan nata still suna d’an motsi!!. Dad ne yayi k’arfin halin shiga da gudu ya d’auki kujerar data taka ta sak’ale kan nata ta yar! Ya saita mata ya d’aura kafafun nata a kai sannan ya hau ya kunto ta, sai dai zuwa wannan lokacin bata motsi!. Shi dai Aslam duhu kawai ya fara gani daga nan bai sake sanin inda kanshi yake ba. Sai da ya farfad’o tukunna ya fahimci ashe suma yayi… Yana farfad’owa Dad da Arshaad suka yo kanshi suna tambayar shi jiki… Cikin tsananin tashin hankali , muryarshi tana rawa yace “Dad ta mutu ko? Shikenan nayi silar mutuwar mahaifiyata!!” Da sauri Dad yace mishi “Bata mutu ba Aslam, suma kawai tayi.” A tunanin Aslam kwantar mishi da hankali kawai Dad yake k’ok’arin yi, shiyasa yak’i yarda da zancenshi har sai da Dad d’in ya kaishi ya ganta ta window tana zaune Gwaggo Asabe tana bata abinci a baki hannunta kuma ana mata k’arin ruwa!. Ajiyar zuciya ya sauk’e sannan yace “Alhamdulillah” Ba a dad’e bai aka yi discharging d’inshi.. Auna komawa gida ko gama dedeta parking d’in mota bai bari Dad yayi ba, ya fito cikin hanzari ya nufi cikin gidan.. A d’akinsa Dad ya sameshi…yanata kiciniyar had’a kayayyakinsa, gaba d’aya ya sauk’o da akwatina ya hargitsa d’akin da alamun komai da komai yake son tattarawa dan hatta games d’insa suka har yayi parking nasu a daban.! Da sauri Dad yaje ya rik’e mishi hannu.. Yana juyowa yace “Dad please! Don’t stop me i’ve to do this..” “Shh” d’in da Dad yace mishi ne ya sanya shi yin shiru. Ji yayi Dad d’in ya rungume shi ya fashe da kuka….. Sai da Abba da Daddy suka shigo tukunna suka iya lallashin Dad! Dan Aslam shi kam ya ma kasa cigaba da magana in banda ajiyar zuciya babu abinda yake ta faman sauk’ewa!. Bayan sun yi shiru ne Abba yayi suggesting “Aslam d’in ya je side d’inshi ya zauna, ba lalle su dinga had’uwa da ita ba in yana chan.” Ajiyar zuciya Dad ya sauk’e kafin yace “Abun nata kamar har da aljanu fa, dan indai suna a waje d’aya tou bata sakewa koda kuwa basu yi ido biyu ba! Daman wajen da yafi dacewa yaje idan irin haka ta faru shine gidan Gwaggo Asabe tou itama yanzu mijin nata ya rasu a gidan itama take! Sannan y’ay’anta(Gwaggo Asabe)duk ba wani girman Aslam d’in suka yi ba ballantana a ce yaje gidansu ya zauna! Babbar 3 years ta bashi, k’aramar kuma 2 months. So kawai ni a nawa tunannin gara in tafi dashi Abuja…” Aslam d’in ne yace musu “Dan Allah kawai yanason barin k’asar gaba d’aya! In komai ya lafa sai ya dawo…” Haka nan ba yadda suka iya, ganin halin da yake ciki yasa suka amince ya tafi...............’. ……. Kiran sallar farko ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi! A hankali ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya, idanuwan nan nasa sun kad’a sun yi jazir! Sannan jijiyoyin goshinsa duk sun yi rud’u rud’u! A hankali yace “Mommy, please this time around don’t push me away! Ko menene kike ji ki yi k’ok’ari ki danne ki yi fighting…..i don’t want to run anymore! All my life tun Ina js 1 nake boarding school, hutu kuma sai dai inje inyi a wani waje! I don’t want this life anymore, it sucks it hurts, i need you…” A hankali yace “I’m all alone, please get well.” Motsi yaga ta fara alamun zata farka hakan yasa ya d’an matso da hannunta (wanda tun d’azun yake a cikin nashi) saitin lips d’inshi, a hankali yayi kissing hannun nata sannan ya mayar mata shi kan cikinta ya mik’e da sauri ya fita dan yaga motsin nata ya tsananta….. Sai da yayi sallah yayi azkar.. Ya dad’e yana karatu tukunna bacci mai dad’i ya kwasheshi around 8:40 am. Jin ana tab’a shi ne yasa ya fara k’ok’arin bud’e idanunsa, dishi dishi yake ganin Arshaad kafin ya fara ganinshi sosai yana yi masa murmushi. Mik’a yayi yai salati sannan ya d’an Mike ya gishingid’a a jikin gadon kafin yace “Morning, You look energetic! Amman ni kam to me yau d’in lazy Sunday ne..so good bye, baccin bai ishe ni ba.” Yana shirin sake komawa ya kwanta Arshaad ya rik’esa, sannan yana dariya ya zaro wayarshi ya nuna mishi screen d’in. Kalla Aslam yayi sai kuma ya zaro idanu yana kallon shi kafin yace “you serious!! 2:00 as in 2:00 na pm?” Dariya Arshaad yayi, cikin gatse yace “a’a,na am.” Da sauri Aslam ya sauk’o akan gadon yana cewa “subhanallah ya akai time ya tafi haka! Ban yi sallah ba fa!” Sannan ya fad’a toilet cikin sauri, bai fito ba sai da yayi wanka.. D’aure da bathrobe bak’a ya fito kanshi na digar ruwa, a gurguje ya zura jallabiya sannan ya tada sallah. Sai da yayi addu’o’i bayan ya idar, tukunna, ya mik’e ya nufi akwatinshi........ Arshaad wanda yake chattn da Huda, yanayi sama sama yana kallonshi yana mamaki yadda Aslam d’in yake shiryawa, dan duk k‘ak’ale k’ak’alenshi Aslam kam ya fi sa… Ya shafa wannan ya fesa wanchan ya goga wannan duk shi kad’ai! Sai da ya gama tsaf tukunnan ya zaro wasu riga da wanda masu masifar kyau, wandon black rigar kuma grey. Sai da ya fara saka wandon tukunna ya zare jallabiyar ya saka singlet da rigar ya sake fesa turare sannan ya zo inda Arshaad yake ya zaune tukunna ya sa hannu ya warce wayar!. Kallon screen d’in yayi sai kuma da sauri ya mik’awa Arshaad d’in wayar sakamokon heart heart d’in da ya fara gani tun kafin ma ya kai ga karanta chat d’in. Dariya Arshaad d’in yayi kafin yace “saikace kaga dodo?Shine surprise d’in da nake ce maka zan nuna maka, yau za muje ma ku gaisa, i’ve told her already.” Shiruuu, Aslam yayi for some minutes, chaaan! Ya nisa kafin yace “Arshaad a brotherly advise.. Ka tabbata Yarinyar da kake so is suitable for Granpa, kar kaje ka d’auko wadda kai da ita duka zaku sha wahala! Idan har ka san she’s not fit to be in this family to kar ma ka fara, kar ka wahalar da kan ka itama ka wahalar da ita… Saboda i’ve seen a lot! A duk lokacin da na zauna nayi tunani sai inga duk matar da aka auro cikin family d’innan ba tare da yarda Granpa d’ari bisa d’ari ba to sai tayi ending somehow! Take my Mom for example, ita da Anty Maryam Those two ladies, zan iya ce maka they are the nicest of all amman ka duba ka gani halin da suka tsinci kansu a ciki, har gara ma Anty Maryam dan na san yanzu kam ita maybe tama yi wani auren kuma definately sun shirya da iyayenta, Mommy fa? She‘s still in hell!! Both me and her! I’m not saying wai Granpa ne ya d’aura mata rashin lafiya or something like that, tunda God knows waye ya jefota a bene that very day! But case d’in Anty Maryam da Abba kam laifinsa ne Dan ranar ina nan a gaba na yace “ko Abba ya saketa ko kuma ya d’aureta a jail! Kuma bama a Nigeria ba, daga ita har iyayenta zai d’aure sannan kuma ya tsine mishi! Wai ai daman ya gayawa ita Anty d’in cewa ‘babu ita ba gidanshi da family d’inshi kwata kwata!’ Amman shine relatives d’inta suka kwaso k’afa suka zo mishi estate, dan haka she has to pay a price, for not listening to him...” Gramma tana kuka tana bashi hak’uri Abba ma haka amman tsohon nan haka ya tursasa su. The only person da nake jiyewa ni a wannan time d’in is Anty Maryam, saboda idan kaga kalar korar Karen da Mahaifinta yayi mata time d’in data koma gida zaka yi mamaki!” Shiruu, Aslam yayi, chaan kuma ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace “idan nace zan tsaya baka labari to ban san ranar barin mu d’akin nan ba. All I’m saying is kar ka zab’o wadda zaka sha wahala itama ta sha wahala, kuma azo ayi ta case! Shiyasa nake jiranshi nake kuma addu’a, saboda ni kam idan nayi mixing up issue na love da wanda nake ciki a yanzu! I don’t think i can make it out…” Ahankali Arshaad ya sauk’e ajiyar zuciya sannan yace “Thanks” Kafin ya mik’e yace mishi “muje ka fara gaida su Granpa se sai wuce ko?” “Not now, ai muna da aiki a gabanmu, although lawyer d’inka yace min za ayi postponding case d’in wai an kashe C J ko?” “Eh fa” Cewar Arshaad. Ajiyar zuciya Aslam ya sauk’e kafin yace “Ina son zuwa gaisuwa ma fa!” Kallonshi Arshaad yayi kafin yace “Ka san shi ne?” “Eh. Yayan wani classmate d’ina ne Immediate i think! He’s not that old.. Da kyar ma aka bashi Saboda age d’inshi, bai ma dad’e da yin aure ba.” Da mamaki Arshaad ya d’an kalleshi kafin yace “Naji ance har da yaranshi biyar…” Cikin katseshi Aslam yace “yeah, yana da triplets!” Cikin son kawo k’arshen maganar yace “Allah yaji k’anshi. Let’s talk, na san ba za a d’u lokaci ana mourning d’inba. Mu san abun yi tun lokaci bai k’ure ba.” A hankali Arshaad ya koma ya zauna ya fad’a mishi dalla dalla yadda Auwal yayi tricking d’inshi yayi signing pappers d’in da komai da komai… Ajiyar zuciya Arshaad ya sauk’e kafin yace “to kayi mishi zancen zaka mayar da kud’in??” K’asa Arshaad yayi da kai sannan yace “shiyasa yanzu nake so idan mun je ka tayani bashi hak’uri ya yarda ‘ya karb’i kud’in ayi withdrawing case d’in’. Kuma ai kasan Granpa yanzu abun ma fitar mishi a kai zai yi, tunda ka san yadda yake baya son jira kwata kwata…inaga idan aka d’aga k’arar ba lalle yayi ta jira yana jira ba maybe ya hak’ura. “Understood” Shine abinda Aslam yace sannan suka d’an sake tattaunawa kafin yace “muje in fara gaida Mammy tukunna kafin muje mu sameshi.” Suna fita a babban parlour suka tarar da Gwaggo Asabe. Tana ganinshi ta mik’e kafin tace “Yau kam an sha baccin gajiya gaskiya ga d’an wake shima ya gaji da jira..” Murmushi yayi sannan ya gaidata bayan ta amsa suka nufi dining ya zauna. Babu yadda bai yi da Arshaad akan yaci d’an waken ba amman yak’i, yace “shi yana reacting to kuka.” Haka nan Aslam ya cinye abinshi daga nan suka mik’e suka nufi gidan Mammy…. Basu sameta a k’asa ba sai da suka haura sama a parlourn sama suka sameta a gaban makeken show glass d’inta tana zuba turaren wuta a burner! Arshaad ne gaba sai Aslam a bayanshi, shiyasa da Mammyn ta juyo bata lura dashi sosai ba. Kallon Arshaad d’in tayi tace “kai da waye? har ka dawo? Ya naga baka dad’e ba?” Murmushi yayi sannan yace “Eh, bak’o na kawo miki ne, shiyasa.” Da fara’arta take k’ok’arin lek’a bayan Arshaad d’in tana cewa “waye? to matsa mana in gan shi....” “Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!!!!” Shine abunda ta furta a mugun tsorace!! Bata san lokacin da burner d’in turaren wutan nata ya fadi daga hannunta ba a lokacin da Arshaad ya matsa Aslam ya baiyyana a gabanta! Duk tsayawa suka yi suna kallonta…. Da sauri ta juya ta kaiwa Arshaad d’in duka kafin tace “Uban ka!!! wannan ai sai kasa zuciyata ta buga! Shekara bakwai ban ganshi ba kawai yanzu In ganshi a gabana ya kake tunanin zan ji?” Dariya dukkan su suka sa kafin Mammy ta share kwallarta ta jawo Aslam d’in jikinta ta rungumee tace “Welcome home son, we really miss u.” A hankali ya zare jikinshi yana d’an murmushi kafin ya sa hannu ya share mata hawayen daya sake zubo mata Yace “Miss u too, Mammyn mu.” Yana d’an murmushi….. Kafin minti biyar tuni Mammy ta cika gaban Aslam da kayan chiye chiye sai tambayarshi takeyi “me za a dafa mishi?” Arshaad kam ya koma gefe sai faman kumbura yake yana mitar “shi an share shi daman ai ya san tafi son Aslam a kan shi!”. Suna cikin haka Aaima ta shigo.. Ihun da tayi sai da suka tsorata duk suka d’ago suna kallonta Ai kuwa da gudu ta taho ta fad’a kanshi tana murna itama har da hawaye, duk ta kanainaye shi… Sai da yayi mata fad’an ‘bata san ta girma ba?’ tukunna ta d’aga shi tana d’an jin kunya ta koma gefe ta zauna… Nan suka hau gasar bashi abinci a baki, sunk’i ma su bari yaci da hannun shi! Sai da Aslam ya cewa Mammy “zai yi amai!!” tukunna ta kyaleshi. Ranshi fess!! Haka suka baro b’angaren Mammy a ranshi yana yaba so da k’aunar da familynshi suke yi mishi babu wani maganar y’an ubanci a tsakaninsu!. Suna fitowa daga gidan da shirin shiga gidan Granpa suka ji ana kiran sallar la’asar! Hakan yasa suka nufi masallaci kawai, suna zuwa suka yi alwalla aka tada sallah. Sun idar kenan Aslam ya juya yana y’an kalle kallen yadda aka tsara Masallacin aka sake gyarawa karaff! Ya had’a ido da Granpa wanda ya tsareshi da idanu, murmushi yayi sannan ya cewa Arshaad “taso mu je” Suna mik’ewa suka ga shima ya mik’e ya fice waje, da sauri suka fito Arshaad yana cewa “da alama yau za kuyi fad’an farko kai da mutumin naka!”. A bakin wata bishiya suka sameshi, suna zuwa Arshaad ne ya fara cewa “Good afternoon Granpa” Banza Granpa yayi dashi bai ko juyo ba shiyasa ya koma gefe ya tsaya Aslam ma ya matsa yace mishi “Good afternoon Granpa.” Shima yayi banza da shi. Murmushi Aslam d’in yayi sannan ya k’arasa inda yake yayi hugging d’inshi ta baya… Sai a lokacin ne na tab’a ganin murmushin Granpa!, ashe har dimple gareshi…. A hankali yasa hannu ya d’anyi tapping hannun Aslam sannan ya d’an juyo lokacin da Aslam d’in ya cika shi.. Still da k’ayataccen murmushi kwance a kan kyakkyawar tsohuwar fuskar shi. Yana juyowa yace “yanzu ka dawo?”. “A’a jiya around 2:00 am”. “A time d’in da muka yi chat ma ka taho kenan?”. “Eh, ai its a surprise.” Murmushi Granpa d’in ya sake yi sannan yace “I’m amazed! Welcome home. How have you been?” “Alhamdulillah” Aslam yace. A hankali Granpa d’in ya juya sannan yace mishi “walk with me..” A tare suka d’an fara tafiya….. Haka nan sai da suka kusan zagaye estate d’in, suna tafe suna hira, Granpa yana tambayarshi yanayin aiki da kuma zamanshi a chan shi kuma yana bashi amsa… Duk wanda ya ga Granpa a wannan rana to ya san yana cikin farin ciki. Zagayowa suka yi ta wajen gate d’in shi dan haka ya cewa Aslam d’in “bara ya shiga ciki akwai wasu y’an takardu da zai duba.” Har ya juya yaji Aslam d’in yace “Granpa pls i need a favour” Juyowa Granpa d’in yayi kafin yace “If it is about Arshaad don’t even go there, i won’t change my decision he must pay for wat he did!!” Da sauri Aslam yace “Wallahi Granpa framing d’inshi aka yi, kuma zai dawo da duk kud’in suna accnt d’inshi bai tab’a komai ba tunda daman ba sata yayi ba ballantana ya tab’a.” Shiruuu, Granpa yayi, na d’an lokaci, chaan! Kuma yace “Framing?” With full confidence Aslam yace mishi “Yes, zamu iya maka presenting evidence! Please Granpa, give us a chance.” “Aslam, today I’m in a very good mood saboda na ganka…so zan iya yi mishi sassauchi. Sassauchi na shine ‘ya kawomin evidence d’in cewa framing d’inshi aka yi, ni kuma daga nan zan janye case d’in, for your sake!” Durk’usawa Aslam d’in yayi cike da farin ciki yace “Thanks a lot Granpa, za a kawo evidence d’in in sha Allah.” A hankali Granpa ya shafa lallausan gashin kanshi sannan yace “Allah yayi maka albarka.” “Ameen” yace sannan ya mik’e yace zai shigo zuwa anjima su gaida gramma in sha Allah.” Daga haka ya juya ya tafi, shima Granpa ya shige. A bakin masallaci inda ya bar Arshaad a nan ya sameshi “Sorry. Na barka kana ta jira ko?” Murmushi kawai Arshaad yayi sannan yace “Um um! Someone kept me busy.” Yayi maganar yana nuna mishi chat d’in da yake yi da Hudan. Murmushi Aslam yayi kafin yace “muje dai inga Yarinyar da ta haukatamin kai haka.” Dariya Arshaad yayi Da sauri Aslam yace “Um good news! Granpa yace muyi presenting evidence to him daga nan case ya mutu!.” Cikin murna Arshaad yayi hugging Aslam sannan yace “Thanks a lot na gode!” A hankali Aslam yayi murmushi yace “NVM”. Sannan suka fara tattauna akan yadda zasu nemo evidence d’in…suna maganar suna tafiya….. A hanyar shiga gidansu Aslam Arshaad ya hango motar Auwal da gudu ta taho… Har Auwal d’in ya wucesu sai kuma yayi reverse ya dawo ya fito a motar ya zagayo ya zo inda suke. Yana zuwa ya kalli Aslam sannan yayi murmushi yace “Ashe ka dawo! Shine ba ko irin ‘Hi’ d’innan?”. Murmushi Aslam yayi kafin yace “Hi, Auwal. Ya gida?”. “I’m gud, gida kuma ai tunda kana tare da little brother d’inka i’m pretty sure ya fad’a maka everything da cases d’in da suke faruwa da komai, right?” Auwal yayi maganan yana kallon Arshaad yana murmushi! Kafin ya d’an juyo da sauri to Aslam d’in yace “Oh I almost forgot, na san ba zai tab’a fad’a maka wannan ba or maybe shi kanshi bai sani ba” A hankali ya matso kusa dasu yad’an kare gefen bakin shi da tafin hannunshi kamar bayaso a ji kafin a hankali yace “Because nima, i eavesdrop” Sannan ya matsa yana d’an murmushi kafin ya fara magana “last 3 months an fitar da Mommy India and her psychiatrist yayi conforming ‘she’ll never get better, domin kuwa duk wani therapy medication treatment duk sunyi amman duk a banza!’. I don’t know why you choose to come back now, saboda home is not a fit place for you anymore! Anyways, it’s gonna be fun dan zan dawo ma gidanku ne da zama saboda in dinga watching dram.....” Naushi kawai yaji Arshaad ya d’auke shi da shi yana huci!!! Ya daga hannu zai k’ara mishi wani Aslam wanda idanuwanshi suka koma kamar garwashin wuta yayi saurin ruk’o shi.. K’ok’arin fisgewa Arshaad d’in ya fara yi, da k’arfi Aslam ya daka mishi tsawa yace “Mu shige ciki’” Juyowa Arshaad d’in yayi zai yi mishi magana amman sai ganin yanayin da yake ciki yasa kawai ya juya zai shiga yaji an ruk’o shi, ya riga ya san Auwal ne shiyasa ya juyo a fusace amman bai gama juyowan ba ya rama naushin da yayi mishi sannan yace “This should be the last time da zaka yi punching nawa, if not kaga ta wanchan gidan!?”yayi magana yana nuna gidan su Arshaad d’in kafin yace “Wallahi a kanta zan rama, ko ban rama da hannu na ba zan saka ayi mata and it might not end well! So be very careful.” Yana gama fad’in haka, ya juya ya shiga motar shi ya ja Aslam kuma ya ja hannun Arshaad suka shige cikin gidan. Direct side d’inshi suka wuce ba wanda yace ‘k’ala’ asalima Arshaad d’in d’aki ya shige ya bar Aslam a nan kwance a parlour kan 3 seater, dan ko had’a ido da shi baya son yayi sakamokon tausayinshi da kuma haushi da suka hadu mishi guri guda! Abun Auwal kullum k’ara gaba yake yi ya rasa dalili… Shi kuwa Auwal Sai da ya koma gida ya chanja kaya dan waennan duk sun yi squeezing! Tukunna ya saka turare ya zira wayoyinshi a aljihu ya fito ya fice daga estate d’in. Kamar yadda suka tsara..motar mike tana gaba tashi tana baya, suna zuwa unguwar gandun albasa layin su Huda, mik’e din ya fito daga tashi motar ya nuna mishi gidan daga d’an nesa… Sallamar sa Auwal yayi sannan yace mishi “zai iya tafiya” Shi kuma ya tada motarshi ya k’arasa k’ofar gidan. Da mamaki yake ta kallon gidan! A take kuma sai yayi murmushi yana rayawa a ranshi ‘winning d’in Yarinyar da entire family d’inta will be an easy job ta hanyar kud’i tunda ya lura basu da shi!’. Yaron da yazo wucewa ya d’an yafito alamar ‘yazo’. Yaron yana zuwa ya d’auko 1k a wallet d’inshi ya bashi kafin yace “ya shiga gidannan yace wai Jalila ta zo inji Arshaad.” Da gudu Yaron yayi cikin gidan bayan ya karb’i kud’in. Yana shiga ya tarar da Umma tana wanke wanke! K’arasawa yayi inda take ya gaisheta sannan yace “wai ana kiran Jalila a waje inji Arshaad!” Umma da kamar bata ji ba tace “me kace?” Sake maimaita mata yayi, aikuwa da sauri tasa hannu ta toshe bakinshi gudun kar Mama ta jiyo. Kallan k’ofar d’akin Maman tayi sai kuma ta juyo…k’asa k’asa tace “kaje kace gata nan zxuwa yanzu.” Sannan ta mik’e har tana tuntub’e ta nufi d’akinta har da d’an gudun ta!. Tana isa ta tarar da Jalila ta bararraje akan gado tanata uban bacci! Duka ta tak’ark’are ta maka mata.. Aikuwa da ihu Jalilan ta tashi. Da sauri ta sa hannun ta toshe mata baki kafin ta jijjagata tace “Watstsake dan uban ki!! Ki tashi ki je ki wanke fuskar ki yanzun nan! Ga Arshaad chan a waje yana jiranki.” Jin an anbaci sunan ‘Arshaad’ yasa ta bud’e idanuwa da sauri sai kuma ta mik’e tayi waje. A bakin rijiya ta wanke idanunta da bakinta, kafin ta dawo cikin d’akin, tuni har Umma ta fitar mata da kayan da zata saka da powder da jan baki da turarurruka kala kala da takalmi, duk a cikin kayan da su Huda suka kawo mata. Tana zuwa ko minti biyar ba tayi ba ta shirya. Har zata fita Umma ta sake janyota ta mik’a mata janbakin tace “ta k’ara bai yi ba, sannan ta sake fesheta da turarurruka har suna tari! Tukunna tace “ta je!” Har da binta har tsakar gida ta karantto ta tofa mata alhamdu k’afa d’aya! Daga nan ta dawo d’akin ta hau tattare inda suka zuzzubar da kayan da ta cire tana cewa “Yau gashi da kanshi yace Jalila yake son gani! Maryam sai naga ta inda zaki nunamin d’agawa yanzu ai!! Shima Arshaad d’in shegen Yaro! Wato ya gama da Huda shine yanzu ya dawo kan Jalila! Ai kuwa baai san inda ya zo ba, dan nan kam idan mutum ya shigo to baya fita!. Na san yau kam har kakan had’a ido sai kun yi! Magana ta k’are! Kuka na ya zo k’arshe daga yau in sha Allah.” Ranta fes! haka ta tattare d’akin ta fito domin k’arasa wanke wanken ta. Jalila tana fita ta hango wata dandatsetsiyar mota a parke! Murmushi tayi sannan ta k’arasa inda motar take ta kwankwasa marfin… Sai da ya d’an jima yana k’are mata kallo ta cikin tinted glass d’in…a ranshi yace “not bad tana da kyau! Amman bata yi yellow d’in da mike yake ta faman zuzutawa ba!”. A hankali ya d’an zuge glass d’in iya idanuwanshi suka fito sannan yace “zagayo ki shigo mana.” Jalila ba wani sanin Arshaad tayi sosai ba tunda duk ganin ta dashi ta lek’e ne amman dukda haka taso ta gane ba shi bane ba daga yanayin muryar da idanun! Jin hucin sanyi da yake tab’ota da wani azababben k’amshin turaren da yake fesowa ta cikin motar da kuma kwad’ayi shiga taga ya yanayin motar take ta ciki yasa kawai ta zagaya ta bud’e ta shiga ta zauna. Tana juyowa kuwa suka yi ido biyu wanda ko da ace bata san shi sosai ba ta san wannan ba Arshaad bane ba, hakan yasa a d’an tsorace tace “Waye kai? Kace sunan ka Arshaad!”. Murmushi yayi, sannan yace, “Relax ni k’anin shi ne.” Ajiyar zuciya ta d’an sauk’e sannan tace “Aiko ka yayi?” Girgiza kai yayi sannan yace “ni na aiko kaina.” Bai jira jin me zata ce ba dan yadda take kallon motar da yanayinta tun farkon fitowarta ya gano zata yi saurin shiga hannu! Musamman idan an yi amfani da kud’i. A hankali yace “Listen Jalila, ni mutum ne mai magana d’aya kuma idan zan yi abu kai tsaye zan yishi babu b’oye b’oye! Farko farkon zuwan Arshaad ya tab’a zuwa dani sau d’aya amman ban fito ba a mota na tsaya thats when i saw u and since that day i have feelings for you! Kawai daurewa nake yi saboda babu yadda zan yi.. Har satar wayar Arshaad nake yi in yi sending pics ba tare da ya sani ba So something happened last week i don’t know if you are aware, ko kuma ya b’oye miki.. An zab’a mishi matar da zai aura a gida har an kai kud’i Na san maybe baki sani ba dan naji yana cewa Mammy “he is going to hide it from you till after d wedding, honestly i don’t know wat he is planning on doing with you. Ni dai aurene ya kawo ni wajenki, kuma mu a family d’inmu idan Namiji yayi aure sai yayi 20 years ya zama stable sosai tukunna za a barshi ya sake yin wani auren Are u ready to wait for him for 20 years??” Yayi mata tambayar yana kafeta da idanuwa… Matsowa yayi kusa da ita, ya kama hannayenta sannan yace “Ba zan taba yaudarar ki ba nikam, just trust me, zan so ki tsakani na da Allah and a shekarar nan in sha Allah za muyi aure!” Ahankali yaji tace “Tam.” Sannan ta sunkuyar da kanta k’asa. Murmushi yayi amman chan k’asan zuciyarsa yana mamakin saurin amincewarta haka.. Cikin son k’ara gasgatar da wani abu taji yace “But promise me, ba zaki gayawa Arshaad muna tare ba, saboda abun zai iya zama case, and na san definately sai ya rabamu, bayan shi yana chan da tashi amaryar! Nafi so sai ranar da aka d’aura aurenshi, da kamar 1 week tukunna ya sani, muma kinga kafin nan an fara maganar namu auren ko?” A hankali ta d’aga mishi kai, alamun amincewa. D’an murmushi yayi kawai ya sake rik’e hannunta…..a haka ya d’an dinga janta da hira yana nan rike da hannunta gam yana d’an matsawa lokaci zuwa lokaci. Sama sama take amsa mishi iya wanda ta fahimta dan rabi da turanci yake magana kuma slanz, Gaba d’aya ta k’agu yace zai tafi dan yadda ya matso gab da ita da yadda ya rik’e mata hannu kwata kwata she‘s not comfortable! Sun yi kusan 1 hour a motar tukunna ya mik’o mata wayarshi yace “ta saka mishi numberta!” Shiruu, tayi chaan! Tace “zan kiraka idan na saka layin a wayar Umma anjima, kai ka bani numberka.” Shiru yayi yana d’an kallonta kafin yace “Baki da waya?” A hankali ta d’aga mishi kai. Da mamaki ya d’an kalle ta yace “Taya kuke waya to? Ko bakwa yi kwata kwata?” Girgiza kai tayi alamar ‘a’a’ kafin tace “Ai ina saka layi na a wayar Umma lokaci zuwa lokaci.” D’aya daga cikin wayoyinshi ya zaro….wadda bai dad’e da fara anfani da ita ba! Gf d’inshi ce ta bashi ranar birthday d’inshi. Bincika wayar yayi sai da ya tabbatar bashi da wani abu important a ciki kafin ya cire sim d’in shi ya mik’a mata wayar sannan yace “Idan kin shiga sai ki saka layin naki a nan.” Kallonshi tayi sai kuma ta kalli wayar kafin ta sa hannu ta karb’a… D’an zuba mata ido yayi alamun jiran godiyarta yake yi amman sai yaga ita murmurshima take ta yi tanata dudduba wayar tana juyawa Ganin dayayi batama da shirin yi mishi godiya ne yasa kawai ya share ya zaro card d’inshi ya bata yace “ta kirashi ga number shi” Kafin ya sake zaro y’an bandir d’in 5hndred ya mik’a mata yace gashi “ta saka kati!” This time around ko d’an jinkirin da tayi first time na karb’ar waya ma bata yi ba da saurinta ta sa hannu ta karb’a tana murmushi. Shi kam kasa daurewa yayi hakan yasa ya ce mata “Ba ko y’ar godiyar nan?” Kunya ta d’an ji sai kuma ta sunkuyar da kanta k’asa kafin tace “Na gode.” Murmushi yayi ya d’an kalli agogon hannunshi kafin yace “Bara in wuce sai naji kiranki ko?”. D’aga kai tayi ta juyo ta kalleshi tana murmushi. Shima murmushin ya mayar mata sannan ya d’an yi waving nata yace “bye” kafin yad’an matso ya bud’e mata marfin motar.. Sai taji kamar kuma kar ta fita saboda bata son barin sanyi. A hankali tasa k’afarta ta fita sannan ta d’an juyo tace mishi “sai anjima.” Har zata fara tafiya taji yace “Remember, don’t talk to him about me yet!” “To” kawai tace kafin ta juya ta wuce cikin gida. Binta yayi da kallo yana mamakin ‘me Arshaad yake planning akan Yarinyar nan? Da farko da yaga gidan ya d’auka maybe ko saboda kyau ne! Da kuma ya ganta, thou se is beautiful but not to the extend da zaace a guy like Arshaad yayi laying down level d’inshi yazo nan ba Sai ya fara tunanin may be nutsuwa da hankalinta da tarbiyya ne ya jawo hankalinshi gareta! But in less than 1 hour ya fahimci kwata kwata Yarinyar bata da nutsuwa da kalan tarbiyyan da ya kamata ace Arshaad ya sota!. So wat is he up to? Saboda ya san ko giyar wake yasha ba zai tab’a tuntub’ar Granpa a kan auren Yarinyar nan ba! Sai dai idan ko yayi secret marriage ko ya siya musu gida b4 the wedding Ko kuma ma kwata kwata ba aure ne ya kawoshi wajenta ba! Dan ya lura Yarinyar in dai za a bata kud’i to da alama zata yi komai ma! A ranshi kuma sai ya ce “But ai Arshaad is not a humanizer” Wata zuciyar ce tace mishi “Kai dai kawai kaga mutum ka kyaleshi, baka san me yake aikatawa behind closed doors ba!”.’ Murmushi yayi kafin yace “Koma dai menene, na san cewa its important to Arshaad! Ni kuma nayi alk’awarin sai na lalata komai in sha Allah. But Yarinyar nan anya kuwa zan iya tolerating d’inta ko dai kawai mu dinga waya ina turo mata kud’i dan gaskiya she is not my type! Amman kuma anya zata yarda da ni yadda nake buk’ata? Ba tare da ina zuwa muna had’uwa ba kuwa?......” Da waennan tunane tunanen ya ja motarshi yayi gaba.... BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 31 Cike da farin ciki Jalila wadda take ji kamar an tsundumata a Aljannah ta shiga cikin gida! A tsakar gidan ta tadda Umma da alama ita take jira.. Ko k’arasowa Jalilan bata yi ba Umma ta hango wayar hannunta da kud’in! Tana zuwa ta bud’e baki zata yi magana kenan Umman ta rufe bakin, ta jata d’aki. Har da rufe k’ofa bayan sun shiga wai duk dan kar a jiyo su! Abunda bata sani ba ‘su Sakinan su kam ba ma sa cikin gidan’ dan tun safe Khadija ta kira su tace “dan Allah su zo ita da Huda su taya ta zab’ar kayan da zata yi amfani dasu da bikin nata.” Suna shiga d’akin k’asa k’asa Umma tace “Ya kuka yi da shi?baki yayi??” Tayi maganar tana kallon hannun Jalilan kafin ta sa hannu ta karb’i wayar ta hau jujjuyawa. Ajiyar zuciya Jalila ta sauk’e sannan ta jefar da mayafinta a kan gado ta nemi guri kan kujera ta zauna kafin tace “Ba Arshaad bane ba! Wai k’aninsa ne, sunanshi Auwal!”. Da mamaki Umma take kallonta kafin tace “Ikon Allah, me ya ce miki tou? Me ya kawoshi? Arshaad d’inne ya turo shi?”. “A’a, wai ce mini yayi wai Arshaad d’in aure zai yi, wai an zab’a mishi wata a gida…Shi kuma Auwal d’in wai yana sona ne zai aure ni! Sannan wai in yi shiru kar inyi magana da Arshaad d’in de komenene dai ni dai ban gane ba gaskiya.” “Ikon Allah!” Shine abunda Umman tace kafin ta sake cewa “Tou ai Alhamdulillah.” Nufar wardrobe d’insu tayi mai b’allalliyar k’ofa. Wajen kayanta ta hau bincikawa da alamun akwai abunda take nema… Cike da son jin k’arin bayani Umma ta matso kusa da ita tace “Jalila ki juyo ki yi mini bayanin da zan gane dan ni sam ban fahimci zancen ki ba.” A d’an razane kuma sai ta tab’ata sannan tace “Ince dai ba Hudan zai auraba ko? Shi Arshaad d’in!”. “A’A” Jalilan tace, kafin ta sake cewa “Kina jina fa nace miki ‘a cikin danginsu aka zab’ar mishi mata! A yadda na fahimta kamar ma fa bai gayawa ita Hudan ba har yanzu.” Wata kalar dariyar mugunta Umma tayi sannan tace “Allah shi k’ara! Sai wani faman hura hanci suke yi su a dole y’arsu zata auri mai kud’i! Ai ga irinta nan.” Sai da ta d’an yi shiru kamar mai tunani kafin ta sake cewa “Ikon Allah, wani hanin ga Allah baiwa ne…Kiga fa babu yadda ban yi dake akan ki fita ku had’u da Yaron nan ba amma Allah bai yi ba! Yanzu fa da tuni ke zai yaudara ya gudu yaje ya auri wata kinaji kina gani. Daman nifa an dad’e ana gaya min cewa ‘In kwantar da hankalina, ba Mijinta bane ba!’. To Amman shi wannan d’in in ce dai mai kud’i ne sosai shima, ko Arshaad d’in ya fishi?”. Juyawa Jalila wadda ta nemo layin ta da kyar a k’ark’ashin hargitsatstsun kayanta, tayi, tana murmushin tambayar! Sai da ta amshi wayar daga hannun Umma ta k’arasa ta zauna a kan yagalgalalliyar kujerar d’akin ta fara neman inda zata saka layin a wayar tukunna ta fara magana “Ai Umma, ba wai Arshaad d’in ne mai kud’in ba Inaga kamar Babansu ne mai kud’in! Domin kuwa shima wannan Auwal d’in yadda kikaga Arshaad tou haka yake.. Da had’add’iyar motar da gayun da yanayin turancin duk! Kina gani kin san ya tsumu a naira! Kinga fatar jikinshi kuwa? Tafin hannunshi laushi kamar.....” Shiruuu, Jalila tayi ta daina k’ok’arin neman inda zata saka layin a wayar, kamar tana tunani…. Mik’ewa ta yi taje inda Umma take tsaye kafin tace “Amma Umma gani nake yi kamar d’an iska ne wannan d’in, ina shiga motar fa ya hau rik’e min hannu! Gaba d’aya ma ni kasa sakewa nayi da shi sosai. Kuma ni Umma har ga Allah Arshaad nake so! Inaga gara kawai ki san yadda zakiyi kawai a fasa auren nashi! Dan ni ya fi kwantamin a rai, shi wannan Auwal d’in gaskiya jinina bai wani d’auke shi ba! Watak’ila mafa kinga d’an iska ne!. Idan ya zo kar In sake fita ko? Harda fa matsa mini hannun ya dinga yi!.” Kallonta Umman tayi na y’an dak’ik’u, kafin tayi k’asa k’asa da murya tace “Jalila anya kin san ciwon kan ki kuwa? Idan kika kuskura kika yi wasa da damar ki Wallahi ki kuka da kanki! Tayaya aka samu kika yi saurayin ma?. Kiga fa Yaron nan wannan shine zuwansa na farko amma kalli abun arzik’i!” Tayi maganar tana nuna waya da kud’in da Auwal ya bayar sannan taci gaba da cewa “Su su Hudan kika san me suke yi?. Ni dai a ganina dan dai rik’e hannu a wagga Yaro mai arzik’i ba laifi bane ba. Yanzu fa rayuwar ta sauya ne gaba d’aya…. A matsayina na uwarki! Ina mai baki shawara ki samu a lallab’a ko ta halin k’ak’a ne a samu ayi auren nan! Muma mu samu muji dad’in rayuwa a dama damu.. Kina gani dai ga yayanki chan a kulle wanda na tabbatar inda ace mu wasu hamshak’an masu arzik’i ne wallahi da tuni sun sake shi. Ki tashi ki tsayawa kanki Jalila, Junaidu yanzu sai ta Allah wanda kin san shi ne yake taimaka mana da kud’i, kuma na san kin san ba don kud’in da yake bani ba da tuni yanzu bana cikin gidan nan! Jiya banyi ishashshen bacci ba tunani kawai nake yi ta yadda zan biya malan Yusuf kud’in aikin da yake bina dan har ya fara yi mini tuni! Sai gashi Allah ya dubamu ya kawo mai bamu amma shine kike k’ok’arin yi mana bak’in ciki ko? Ni dai ban ce kije kiyi abunda bai dace ba amma a iya tunani na da wayo ‘Rik’e hannu ba matsala bace ba’.” Tana gama fad’in haka ta hau dudduba d’akin… Chaan! Ta rarumo mayafinta tana cewa “Bari ma kiga in tashi inje gida! Akwai maganar da ya kamata muyi da Baabaa Laraba. Kin san ance da zafi zafi a kan daki k’arfe.” Shiruu, taga Jalilan tayi kamar mai tunanin wani abu hakan ya sanya ta koma ta zauna a kusa da ita ta dafa ta tace “Ki kwantar da hankalinki, komai zai tafi dai dai. Ki cire wani Arshaad a ranki Allah na tuba me za kiyi da mayaudari? Abu na biyu kuma Kin ga masu kud’in nan sun fimu iya shige shige Idan muka ce zamu raba aurenshi da wachchar y’ar uwar tashi tsaf sai y’an kud’ad’enmu sun kare tass!! Dan haka kawai kiyi abunda yake mai sauk’i, kin ji ko?”. Har zata mik’e sai kuma tace “Yanzu shi wannan d’in a ina yace ya ganki? Sannan shi Arshaad d’in ya aka yi yayi mishi maganar ki? Ni fa ban gane komai ba gaskiya ki fahimtar dani ta yadda zan iya yiwa Baabaa Laraba bayani dalla dalla.” Tsaki Jalilan taja sanann tace “Wallahi Umma yadda baki fahimta ba nima hakan take. Sam sam ban gane me yake nufi ba!.” Da d’an fad’a Umman tace “Kuma baki damu da ki tambaya ba!? Kan ki yanata rawa…” “Umma wai so kike yi in disga kaina ne? Na fad’a miki da turanci yayi ta bayaninshi kuma irin mai saurin nan! Kina ji kin san irin na turawa ne, shiyasa nace miki shima akwai arzik’i dan daga ji ba a k’asar nan yayi karatu ba… Yanayin nasa kalar turancin ba irin nasu Ya Junaidu bane ba. Gashi shima kyakkyawa fari tass kalar hutu.” “Tam shikenan, bara inje mu gani.” Umma tayi maganar tana gyara mayafinta sannan ta d’auki wayarta tana cewa “Alhamdulillah wayata zata huta! Shegen malamin maths mai son bati, saura kuma inji kin kirashi da wannan wayar, ke! Ni kima fita a harkar shi dan yanzu kam kin fi k’arfin shi.” Dariya Jalila tayi itama ta mik’e tana cewa “Wallahi kuwa Ummata.. Bari nima ki ga yanzu inje gidan su Jidda sune masu manyan wayoyi in basu su sakamin sim d’innan dan na kasa. Sannan In d’an saka charji inaga ya manta bai had’a min da charger ba, anjima ina kiranshi zan ce ya taho min da ita idan zai zo, kar in manta.” Haka nan suka fice a gidan, Umma tayi gidansu Ita kuma Jalila ta nufi layin gidansu wachche ta kira da Jidda. Umma tana zuwa gidansu ta tarar ana fad’a da Baaba Laraba da K’asimu da Anty amarya… Ganin kalar zagi da cin mutuncin da K’asimu yake yi wa Baaba Laraba a tsakar gida gaban Yara da ita kanta Anty amaryar ne ya sanya Umma ta jaa Baaba Laraban suka shige d’aki suka bar su sunata rashin mutuncinsu!. Umma ji take kamar tayi super ta dira kan Anty amarya taci ubanta, amma kuma gudu da tsoron karta janyowa uwarta saki yasa kawai ta ja bakinta tayi shiru…..ta san duk bala’in ta K’asimu ya dama ta ya shanye! Yanzun nan zai yi musu abunda basu tab’a tsammaniba. Suna shiga Baaba Laraba ta sa kuka, cikin kukan take cewa “Sadiya wallahi uban ki ba d’an halak bane ba!. Saboda Allah dan yaga yanzu amarya ke bashi kud’in kashewa shike nan ni sai in zama bola? Wanne irin gata ne ban yi mishi ba? Shifa ya karyani a sana’ar tawa saboda yadda nake bashi kud’ad’ena kyauta da bashi! Amman yanzu dan yaga bani da shi shikenan na zama banza kenan?? Da gangan fa Yarinyar nan zata takalo ni da fad’a ina tankawa shikenan zai shigar mata su tisa ni gaba da cin mutunci tsofai tsofai da ni.” Ajiyar zuciya Umma ta sauk’e kafin ta matso ta share mata hawaye sannan tace “Kiyi hak’uri, ki kyalesu, ki daina shiga harkar ta, komai zata yi miki ki kar ki kulata. Ki kwantar da hankalinki in dai na haifu y’ar halak to wallahi sai ta bar gidan nan!! Dama ai babu ce tasa muka barta muka zuba mata ido ko? To yanzu Allah ya kawo mana mafita .......” Nan ta zayyano mata zancen Auwal da Jalila, da kuma maganar auren da Auwal d’in ya zo dashi, da maganar auren Arshaad!! Duk bata bar komai ba. Murmushi Baaba Laraba ta hau yi sannan tasa hannu ta goge ragowar hawayen fuskarta kafin tace “Yanzu ba gwara hakan ba? Ai sai sun fi jin ciwon hakan yanzu akan ace an rabasu tun farko! Abunda nake ta gaya miki kenan tun lokacin da aka ce mana ‘ba Mijinta bane ba’ Wannan ranar nake kwad’ayi gani! Ke kuma duk kika bi kika d’aga hankalinki kika gaza nutsuwa ki fahimceni…akan yana kawo mata abubuwa kuma ita tana fita Jalila tana zaune.. Yanzu tou ba gashi itama Jalilan Allah ya kawo ba?”. Murmushi Umma tayi kafin tace “Ai dama Baabaa kin san ance duk abunda Babba ya hango Yaro ko kan dala ya hau ba zai ganiba. Yanzu menene abun yi? Dan idan mukayi sagegeluwar da su Maryam suka yi to fa muma hakan na iya faruwa da mu.” “Kud’in hannunta da aka bata kin taho da su?” Cewar Baaba Laraba. Baki Umma ta kama kafin tace “Niiiii? Kin dai san halin Jalila da shegen son abunta! Yanzun ma ina lure da ita sai wani kaffa kaffa take yi dan kar ince ta bani. Shiyasa na kyaleta sai munje kwanciya tukunna zan yi mata wayo In karb’a.. Kinga a ciki ma sai ki samu na jari.” “Ya kamata kam”. Shine abunda Baabaa Laraban tace. Daga nan suka hau k’ulla yadda za suyi da Auwal, K’asimu da Anty amarya........ BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 32 Tun azahar! Sai bayan sallar magrib tukunna Hudan da Sakina suka baro gidan Baaba Talatu suka nufi gida. …Tun azahar d’in suna tare da su Anty Zainab wadda suka zo ita da y’arta Khadijah (amarya) ana ta shirye shiryen biki… Yarinyar tana son Hudan sosai sai faman sakota take yi acikin lamuran bikin Anty Zainab ita kuma tana ta gwasalewa har sai da Baaba Talatu ta d’an tsawatar mata….. Ganin Hakan ne ya sanya Hudan ta mik’e ta shige d’akin Baaba Talatu ta barsu nan. Tana shiga ta hau video call da Arshaad, sai da aka kira Magrib tukunna suka yi sallama.. Suna shiga d’akin suka k’arasa da sauri wajen Mama sakamokon hangota da suka yi kwance a duk’unk’une cikin bargo! Dama sun fita sun bar ta tana d’an zazzab’i da ciwon kai!. Sakina tana zuwa tasa hannu ta tab’a goshinta! Aikuwa a rikice ta hau salati… kafin ta shiga cewa Hudan “ta zo maza maza, su fita su nemo adaidaita a kai Maman asibiti! Ko kuma su kira Ummu.” Dan jikinta ba k’aramin zafi ya d’auka ba wanda hakan ya sanya gaba d’aya suka rikice lokaci guda.! Da kyar Maman ta lallab’a su suka hak’ura suka bari akan ‘sai gobe da safe za a kaita asibitin’ A cewarta “ciwon nata, it not that serious.” Tsumman d’ankwali suka jik’o suka hau d’ad’d’aura mata a jiki… A hankali ta fara jin zazzab’in yana sauk’a, dan haka ta mik’e ta nufi bayi domin yin alwala.. Bayan ta idar da sallar ne ta juyo ta kallesu, kafin tace “Kika ce d’azu Arshaad zai zo kuma naga baku dawo ba.” Sakina ce ta karb’e ta hanyar cewa “Eh! Ya kira waya… wai Yayan nashi da zasu zo taren ne bashi da lafiya. So sai gobe za su zo, in sha Allah.” Kamar Maman ba zata ce komai ba, sai kuma tace “D’azu naji kamar Yaro ya shigo yana cewa ‘wai Jalila taje inji Arshaad!’.” “Around what time?” Hudan ta tambaya tana d’an kallon Mama.” “Wajajen biyar dai haka, zuwa, kafin Magrib naji ta shigo.” Murmushi Sakina tayi kafin tace “Iskancin su ne kawai! Maybe wani abun nasu suke son k’ullawa.. Amman ya Arshaad bai ma tab’a ganin Jalila ba! I don’t even think ya san ma tana existing. Ko kin tab’a gaya mishi akwai Jalila a gidan nan?” Ta k’arashe maganar tana kallon Huda.” “A’a” shine abinda Hudan tace Sannan ta d’aura da cewa “Tun wajajen hud’u da rabi ma muke video call da shi, sai da aka kira Magrib tukunna muka kashe.” Jinjina kai Mama tayi alamun cikakkiyar gamsuwa da zancen nasu! Daganan ta mik’e ta gabatar da sallar isha dan har an fara kira… Da kyar ta d’an tab’a abinci (‘ta zarcen’ da suka yi tun rana) shima kuma dan su Hudan sun takura mata ne daga nan tabi gado, su Hudan kuwa basu kwanta da wuri ba! Dan bayan sun yi sallah sun ci abinci sai da suka d’an tattauna akan bikin Khadija wanda da farko Hudan tace “ba zata je ba!” Sai da Sakina tayi mata nuni da yadda amaryar take k’aunarta tukunna ta yarda suka bari akan zata je d’in amma ba zata je har Kaduna ba (dayake a chan za ayi bikin) Ta yarda dai zata je wunin da Baaba Talatu ta had’a anan (Kano) Saboda jama’arta bayan an kawota an dawo Kano, za kuma taje bud’ar Kai gidanta amma gaskiya ba zata je har Kaduna ba! Ta san Mama ma ba lalle taje chan d’in ba.. Dan haka za suyi zaman su idan an dawo Kano suje events d’in Kano…. Haka nan Sakina ta hak’ura, dan taga Huda ta riga ta kafe a kan bakarta. Kamar yadda Umma tayi zato! Bayan ta koma gida… Sai da suka kai ruwa rana tukunna Jalila ta yarda ta bata rabin kud’in shima kuma dan taji Umman tace ‘akan Auwal d’in yayi ta kawowa sannan ya turo da wuri za ayi aikin!!’ Ba dan hakan ba to da ba zata bayarba…. Daga nan ba suyi barci ba sai da Umma ta kokkoyawa Jalila d’abi’u da dabarun karb’ar kud’i a hannunshi. Arshaad yana gama waya da Huda, ya mik’e yayi alwalar Magrib ya fito da zummar zuwa masallaci. Ga mamakinshi a position d’in da ya bar Aslam a haka ya fito ya sameshi! K’arasawa inda yake yayi da sauri ya zauna a kusa da shi… Yana kallon yadda jijiyoyin kanshi suka firfito waje Idanuwanshi suka yi wani irin jaaa! Har abun tsoro. A hankali Arshaad ya shiga lallashinshi..yana kwantar masa da hankali yana bashi baki. Aslam, bai iya ce masa komai ba dan ya kasa magana ma! Ji yake kamar ya b’intike zuciyarshi da kan shi ya jefar sakamokon azababben ciwon da suke yi mishi.. Da kyar ya samu ya iya had’a sentence, yace “Jirani inyi alwala mu tafi mosque”. Yana gama fad’in haka ya mik’e yayi ciki. Bai d’ad’e ba ya fito. Daga nan suka fita a side d’in. Sai da sukayi sallar isha tukunna suka dawo. A parlourn k’asa suka samu Mammy Da kyar Aslam ya iya tsayawa ya gaida ita daganan ya hau jero mata tambayoyi “Tun yaushe?? Mai yasa basu gaya mishi ba??” Shiruuu, Mammyn tayi dan bata da amsar da zata bashi. Ganin haka yasa yace “Bari kawai ya je ya samu Granpa! Dan dole a nemo wani option din saboda ba zai yiu ace dashi da Mahaifiyarshi su d’auwwama a haka ba! Ba zai yiu ba!!” Duk ya bi ya hargitse! In ka ganshi muddin kana da saurin kuka to sai ka koka. Da kyar Mammy ta samu ta lallab’a shi ta hanyar ce mishi “Shima Granpa d’in bai gamsu ba! Yana nan yana ta shirin ganin best neorologiat na kaff duniya a dalilin case d’inta! Sannan Granpa yayi warning d’insu ne akan kar su kuskura su bari Aslam d’in yaji maganar Yanzu Idan ya san yaji ba zai yi duba da ‘Ai Auwal ne ya fad’a ba!’ Ta san had’a su zai yi gabad’ayansu yaci k’aniyarsu Tunda shi dai ya san iyakar parents d’inne suka san zancen so one of them ne ya fad’awa Auwal d’in kenan!. Yayi hak’uri ya kwantar da hankalinshi dan Allah Ko ya samu Granpa ko bai sameshiba dole ta san sai inda k’arfin shi ya k’are wajen nemawa Mommy lafiya Samun nashi kuma da yake shirin yi kawai matsala zai jawowa su Abba Dad Daddy da ita da su Mom. Ya yi ta addu’a a samu a dace adduar ce ta kamata ba wai tado da case a kan case d’in rashin lafiyarta ba, mara lafiya baya buk’atar hakan.” Da kyar da mugun kyar Aslam ya hak’ura da taimokon kalaman Mammy masu k’arfafa guiwa sannan bata barshiba sai da ta bashi full hope akan samun sauk’in Mommy Bi’ixnillah Duk da hakan dai, bai wani sake sosai ba! Haka nan shi kad’ai sai ya zauna yayi ta tunani throughout abun tausayi… Wasan b’uya kuwa gadan gadan ya d’aura d’amarar yi da Mommy dan kayansa ma Arshaad ya sanya yaje ya d’auko ya kawo mishi gidansu side d’inshi (Arshaad) Saboda jikin nata ya motsa wannan karon sosai! Kamar ta san yazo wanda hakan ne yasa da Mammy tayi mishi tayin ya koma chan d’in kawai ya tattara ya koma za suke zama da Arshaad a side d’inshi. Gwaggo Asabe kwata kwata bata so hakan ba amman gudun kar ta sake d’aura mishi wata damuwar a kan wadda yake kai ya sanya kawai ta amince ta bishi da addu’o’i Bilaadadin. Yau da safe suna tashi ya shirya yaje ya gaida su Mom da Ummi da Granmma. Sai wajen 3:00 pm tukunna ya samu ganin su Daddy da Abba A hakan ma wai yau sun dawo da wuri kenan… Daddy aiki yayi mishi yawa har Sundays sai yaje office. Abba kuma akwai company d’insu shi da Aslam d’in da suke son bud’ewa wanda shine abunda ya fitar da shi, ya kuma sanya ya zama busy those days. Sun ji surprise d’in kuwa dan kawai ganinshi kawai suka yi. Sun yi matuk’ar jin dad’in hakan ba kad’an ba Daddy har da y’ar kwallar shi…. Bayan sun gaggaisa ne aka hau hirar yaushe gamo daganan kuma Abba da Aslam d’in suka hau tattaunawa akan company d’in nasu wanda za su bud’e nan da y’an kwanaki k’alilan. Su Daddy kuma suna taya su da wasu shawarwarin… Sai yamma suka rabu bayan sun yi sallar laasar tare. Da kyar da sid’in goshi Aslam ya yarda zai raka Arshaad wajen hudan bayan Mammy ta saka baki. Babu yadda Aaima bata yi akan aje da ita ba amman suka k’i. Haka ta haye sama tanata kumbure kumbure Mammy nayi mata dariya, tana ganin fitarsu tayi murmushi a ranta tace “Bara ku dawo, lokacin da zan bugi cikin Aslam ma ya fad’amin komai akan Yarinyar ba zaka sani ba Tunda naga Auwal ya kasa.” Arshaad ne yake tuk’in Aslam na gefe yana sanye da Top mai gajeran hannu maroon color da d’an ratsi ratsin blue black a jiki sai jeans, blue black . Yayi kyau sosai dukda kuwa simple dressing ne yayi. Arshaad kuma shadda ce a jikinshi yanayin d’inkin zamani mai mugun kyau! Kalar ruwan zuma, ya murza zanna bukar, wadda ta sake fito da ainahin kyawun fuskarshi… Da bak’in agogo da takalmin fata kalar shaddarshi. Kad’an kad’an yake jan Aslam da hira har sai da yaga yad’an saki fuska, dan idan akwai abunda baya son ganin shine Yaga Aslam a irin wannan mood d’in. A k’ofar gidan yayi parking kafin ya zaro waya ya nemo layin ta a recent ya kira yace “Suna waje” Da mamaki Aslam yake kallonshi, kafin yace “Arshaad kana da ishashshen hankali kuwa? Ba kaji shawarar dana baka ba ko? Karka cuci Yarinyar mutane ka b’ata mata lokaci! Kasan ko bayan ran Granpa ba lalle auren nan ya yiu ba dan na san Mammy ma won’t allow it I know her too well!!”. Murmushi kawai Arshaad yayi kafin yace don’t worry, I already have a plan.. Ka bari kawai lokacin yayi.” Da d’an fad’a Aslam yace “What plan? Who are you planning on deceiving? Parents d’inmu? Ko su Yarinyar! Dan dole sai an yi deceiving 1of 2 d’innan tukunnan auren nan zai yiu.” Ajiyar zuciya Arshaad ya sauk’e kafin yace “I love her! Sosai!! Ba zan iya hak’ura ba Aslam. Kar ka damu, nothing will go wrong! In shaa Allah.” Wanann karon a harzuk’e Aslam yace “How will....” Ganin ma ba shi yake kallo ba ya sanya shima ya juya yana kallon inda yaga yana kalla… Ko ba a fad’a mishi ba, ya san itace Hudan! Ya jima yana kallonta!! Kafin da kyar ya samu ya iya janye idanunsa daga kanta. Tun kafin ta k’araso Arshaad ya bud’e k’ofar ya fita. Sai bayan kamar 20 minutes haka tukunna Arshaad d’in ya bud’e motar ya lek’o…… a zaune ya ganshi ya kwantar da kanshi a jikin seat! Ya lumshe idanuwanshi kamar mai bacci. Murmushi yayi kafin yace “Ka fito mana, ku gaisa.” Jinjina kai kawai Aslam yayi alamar ‘to’ ba tare da ya juyo ko ya bud’e idanunshi ba. Ganin haka yasa Arshaad d’in komawa tare da maida murfin motar ya rufe. ….Sam ya fidda ran Aslam d’in zai fito dan kusan 30 minutes kenan da yayi mishi maganar! Gashi ya san suna sauri ne saboda sunada appointment da Khadija GF d’in Auwal ta company wadda ta yarda da kyar zata gansu a yau, around 6pm ba tare da Auwal d’in ya sani ba. Haka yasanya kawai ya fara yiwa Hudan sallama bayan ya kalli agogon hannunshi yaga time. Kamar zata tambayeshi ina bak’on saboda d’azu yace mata ba shi kad’ai baneba kuma har cewa yayi bara ya lek’a yace ya fito su gaisa.. Amma kuma ganin bai sake yi mata maganar ba yasanya kawai tace “ya gaida Aaima” Tana shirin tafiya suka ji k’arar bud’e motar… Ya kusan minti d’aya tukunna kawai yayi tsaki ya mik’e ya fito ya zagayo inda suke tsaye. Murmushi Arshaad yayi ya kalli Huda wadda take kallon k’asa tana mamakin yadda k’amshin turarenshi ya karad’e wajen, daga fitowarshi dan gashi har ma yana shirin k’orar na Ya Arshaad daga gurin gaba d’aya.. Muryar Arshaad taji yace “Dan milki kenan! Don’t mind him.” Sai kuma yace “Hudan ga yayana ‘Aslam’.” D’agowa tayi tana kallon wanda ya kira da Aslam…wanda shi kuma sam kwata kwata yak’i yarda ya kalli inda take, chan wani waje ma taga ya juya yana kallo…. A ranta ta hau rayawa ….kwata kwata basa kama da Arshaad, Arshaad ya fishi hasken fata, amma fa tunda take a rayuwarta bata tab’a ganin skin colour d’in da yayi mata kyau!! Kamar na Aslam d’innan ba. Yafi Arshaad tsayi, dukda kuwa shima Arshaad a sahun dogaye sosai za a sakashi. Yanayin fad’in k’ashinsu shima kusan d’aya ne amman Arshaad ya d’an fishi k’iba…… Gyaran muryar da Arshaad yayi ne, ya dawo da hankalinta gareshi.. Ganin yadda ya kafeta da idanu ne ya sanya ta yi saurin sunkuyar da kanta k’asa A hankali tace “Ina wuni Ya Aslam” Jin bai ce komai ba ne ya sanya ta d’ago kanta ta kalleshi sannan ta sake maimaita abinda ta fad’a da farko tare da d’an d’aga murya.. Sai da ya sake had’e rai tukunna yace “lafiya” Ba tare da ya kalleta ba!. Arshaad, sam bai ji dad’in yadda Aslam d’in yayi mata ba! Ganin kamar itama jikinta yayi sanyi ne kawai ya sanya yace “Baby, bara mu tafi. We have somewhere else to go. Sai mun yi waya, ko?”. “To” Kawai tace, sannan ta d’an d’ago tana kallon Aslam tana mamakin kalar miskilanci da mugun hali irin nashi. Ji yayi kamar ance ya kalleta yana juyowa kuwa akai sa’a itanma shi take kallo dan haka idanuwansu suka sark’e cikin na juna! Wanda sai a lokacin ne taga kwayar idanunsa… Da sauri kawai ya juya ba tare da yace komai ba! Ya nufi inda ya fito ya bud’e ya shiga ya zauna ya jingina kamar d’azu ya mayar da idanunsa ya lumshe. Ajiyar zuciya Arshaad ya sauk’e kafin yace “Ki gaida Mama da Sakina.” daganan ya bud’e motar ya shige. Sai da taga wucewar motar tukunna ta shige gida ranta duk ba dad’i...... A tsakar gida ta tarar da Sakina da Mama sun shimfid’a taburma dake yau garin akwai zafi da alamun hadari ne ke had’uwa. Mama na kwance kanta akan pillow tana bacci Sakina kuma tana zaune a gefenta tana yi mata firfita. Jiki a mace Huda ta k’arasa inda suke ta zauna sannan tace “Ya jikin nata??”. A hankali Sakina tace “Alhamdulillah. Ni na d’auka ma zaki shigo da Ya Arshaad, na san idan shi yayi mata magana watak’il yayi convincing nata ta tafi asibiti..” Ajiyar zuciya Hudan ta sauk’e kafin tace “Naso in fad’a mishi, sai kuma naga kamar yana sauri ne.. Sannan ya zo da wani Yayan shi mai fuskar shanu! Sai wani ciccin magani yake yi kamar ance mishi gasar dambe za’ayi…” K’arar wayar Mama ne ya katse musu maganar tasu. A hankali Mama ta bud’e idonta ta mik’e zaune sannan tasa hannu ta lalumo wayar tata a k’asan pillow Har kiran ya tsinke. Dannawa tayi ta kalla screen d’in, da d’an mamaki ta d’an ware ido sai kuma ta mik’e da sauri tayi hanyar d’aki tana danna wayar. “Hmmm” Sakina wadda ta bita da kallo tace kafin tayi k’asa k’asa da murya tana cewa Hudan wadda itama hanyar da Maman tabi take kallo “Nifa na yiwa Ummu message na fad’a mata.” Shiruuu, Hudan tayi sai kuma tace “Ai gara, dan nima daaa har na fara tunanin In kira Baaba Talatu..” daga haka tayi shiru bata sake cewa komai ba. Ganin da Sakina tayi kamar ta d’anyi zurfi a tunani ne ya sanya tace mata “Tunanin me kike yi?” Tayi maganar tana tsareta da dara daran idanuwanta. Sai da ta cire mayafin abayar jikinta ta ajjiye a gefe ta jaa pillown da Mama ta tashi a kai ta kwanta rigingine sannan tace “Ya Arshaad zasu sake komawa wajen su Kaka this time around ba shi kad’ai ba har da parents d’inshi! Maganar aure!! D’azun na bashi, go ahead.” Murmushi Sakina tayi kafin tace “To ai Alhamdulillah! Damuwar me kuma kike yi tou?” “I don’t know” Shine abunda Hudan tace sannan ta mik’e ta zauna tace “Allah dai yasa ragowar danginsa ba irin halinsu d’aya da yayan nan nashi da suka zo tare ba ne, dan in dai dukkansu haka suke to Ina ruwa! I hope kowa a gidan ya zama kamar Aaima kuma i just hope I did the right thing about amincewar da nayi da zuwan nasu wajen Kaka. …Thats all.” “Kamar ya ‘you hope you did the right??’ Are u having second thoughts?” Shine tambayar da Sakina tayi mata tana kallonta. “No! Kawai dai… Maybe I’m nervous ne inaga or something like that. Kinga manta kawai…” Ajiyar zuciya Sakina ta sauk’e kafin tace “Meye halin yayan nashi!” Kai tsaye Huda tace “Bashi da kirki!! kwata kwata, gaskiya. Kinga yadda ya dinga had’e fuska kamar ta shanu.” Dariya Sakina tayi, kafin tace “Fuskar shanu kuma? Mummunane?”. Da sauri Huda tace “Nooo! Not at all… Dan ni kam i don’t think ma na tab’a ganin mutum mai kyan shi! Tun da nake, wallahi. Kinga hancinshi kuwa? Idanunsa daya kalleni sai da na tsorata! Farare kall!! Sannan kamar an zuba ruwa a ciki irin kad’an d’innan, har fa wani haske k’asan idon yake yi kamar irin ya saka kwallin haske....” “Yafi Ya Arshaad kyau kenan?” Sakina wadda ta kafeta da idanu tayi mata tambayar. Hudan bata san lokacin da tace “Nesa ba kusa ba, sosai....” Sai kuma tayi shiru ta kasa k’arasawa, ta koma ta kwanta tana kallon sama. Ajiyar zuciya Sakina ta sauk’e kafin tace “Hmm” Daga nan ta d’auki wayarta wadda taji tana k’ara alamun shigowar sak’o, nan ta hau dubawa… Murmushi tayi kafin tace “Ya Arshaad ne! Wai In tura account number d’in da zai turo mana kud’in ankon bikin Khadijah.” Da sauri Huda ta mik’e ta fisge wayar ta hau duba sak’on kafin ta dago tace “Sakina dan Allah kar ki tura masa! Ya tambayeni nace mishi mun riga mun sayi komai har mun d’inka. Sakina ta bud’e baki zata yi magana kenan k’amshin turaren Jalila wadda ta fito tana waya ya katseta… Da sauri ta juya ta kalleta, suna had’a ido Jalilan da gangan aka ce “Baby gani nan zuwa” Tayi maganar yadda ta tabbatar za suji, tukunna tasa kai ta fice daga gidan. Tab’e baki Sakina tayi tace “Ba zama fa! Duniya kowa sai ya san Jalila anyi waya anyi saurayi!”. Hudan, wadda ko kallon inda take ma ita bata yi ba ce tayi dariya sannan tace “Kinji Sakina! Dan Allah kar ki turawa ya Arshaad accnt no d’in. Kinga halin da Mama take ciki kar mu b’ata mata rai kin san ta hana bata so! Wallahi har da son inga na kwantar mata da hankali yasa nace Ya Arshaad d’in ya tura parents d’in nashi wajensu Kaka, a samu ayi komai yadda take so. Ko a samu hankalinta ya d’an kwanta, dan ko bata fad’a ba na riga na san jininta ne ya hau! Tunda kika ga tanata yawan ciwon kan nan. Kin ji, Dan Allah.” Hudan ta k’arashe maganar kamar zata yi kuka. A hankali Sakina tace “Okay sis, shikenan in sha Allah ba zan tura ba. “Tnx” Huda tace mata. Sannan suka ci gaba da hira. Suna zaune kusan minti bakwai haka Ummu da Sumayya suka yi sallama suka shigo… Ummu na hada ido da Huda (wadda take k’ok’arin mik’ewa dan ta k’arasa wajenta tayi mata oyoyo) ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace “Ai da na d’auka kece mai zance a cikin mota mai uban tint ta koina har gaba da baya! Tunani nayi akan ‘in fara shigowa tukunna in na tabbatar ke d’in ce, har cikin motar zan je in fincikoki a gaban Arshaad d’in.” Dariya suka yi ita da Sakina sannan suka k’araso sukayi huggin d’inta sannan Sakina tace “Ummu ai kema kin san ba kalar yanayin training d’in da kuka bamu ba kenan! Ya Arshaad d’in shima bai dad’e da tafiya ba. Wadda kuka gani a mota yanzu kuma zak’ak’ura Jalila ce da zak’ak’urin saurayinta!”. Da sauri Ummu ta buge mata baki…. Ita wallahi inda ace ma ta san jalilace a motar da ba zata tsaya jin k’arashen zancen ba. Ai kuwa abinda Ummun take gudu sai da ya faru! Dan haka nan tashi d’aya sukaga Umma ta banko k’ofa ta fito kamar an cillota… Nan ta hau zage zage har da su cewa “Bak’in ciki ake yiwa y’arta saboda anga tayi saurayin da yafi na Hudan… Ita Huda ai har makarantar kwana aka kaita saurayin ya dinga zagayawa amma babu wanda ya tab’a cewa uffan! Sai ita yanzu dan anga Jalila tayi goshi!!”. Sakina kamar ta had’iye zuciya ta mutu tsabar bak’in ciki dan k’iri k’iri tanaji tana gani Ummu ta hanata magana ta kad’a su suka shige d’aki gaba d’ayansu bayan ga amsoshin bak’ak’en maganganu barkatai a kanta!. Hakanan suka wuce suka bar Umma kamar wata tab’abb’iya tanata faman zage zage… Suna shiga suka ga Mama zaune a bakin gado Fuskarta da idanuwanta sun yi jaa! Ga kuma ragowan hawayen da suke silalowa. Ganin su ya sanya tayi saurin saka hannu ta share hawayenta a karo na ba adadi. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 33 Da sauri Ummu ta k’arasa inda take ta hau tambayarta “Mai ya faru??”. A hankali Mama ta share hawayen da suka sake zubo mata sannan tace “Bilkisu, barin garin nan zan yi!! Na gama deciding. Ba zan iya ci gaba da zama ba.” Ummu na shirin yin magana Mama ta katse ta ta hanyar ci gaba da magana “Duk tsawon shekarun nan da aka d’auka….ina hak’uri, ina rok’on Allah yasa su Hajiya su sauk’o daga fushin da suke yi da ni amman har yanzu ace sam babu chanji babu wani sassauci daga ita har Abba Madu?? Abun yana damuna ba kad’an ba! Saboda Allah idan ni nayi mata laifi Ita Hudan meye nata a ciki?. Yanzu fa naga kiranta ina bin kiran ta d’auka ko gaisuwata bata tsaya amsawaba tace ‘Wai taga Khadijah ta warewa Hudan da Sakina ankon su, In tabbatar na hana Huda zuwa saboda ba zata iya yiwa mutane bayanin wacece ita ba!’.” Kuka ne mai k’arfi ya kufcewa Mama, cikin kukan tace “Saboda Allah sai kace wata shegiya?… Shiyasa kawai na gama yanke shawara zan bar garin nan inaga zaman da nake yi a kusa da su ne ya sanya har yanzun bamu daidaita ba! Watak’il idan muka d’anyi nesa da su abun zai yi sauk’i in basa ganinmu akai akai! Kuma nima har ga Allah hankalina zai fi kwanciya..” A hankali Ummu ta d’an juyar da kanta ta share hawayenta kafin ta juyo ta cewa Mama “Maganar ‘barin gari’ bata taso ba Mama Ki tuna fa barin garin nan da kika yi a farko shi ya janyo komai in the first place! Ki kwantar da hankalinki duk abinda kika ga yayi zafi tou zai yi sanyi da izinin Allah. Kiyi hak’uri wata rana sai labari……” Cikin tausasawa da lafazi masu tsuma zuciya Ummu tayi ta kwantar mata da hankali.. Sai da taga ta d’an yi sanyi sannan tace “Yanzu alfarma d’aya nake nema a wajen ki ‘ki tashi mu tafi asibiti dan Allah’.” Shiruu, Mama tayi, chaan! Ta d’auki wayarta ta kira Baba.. Sai tayi mishi 3 misscalls tukunna a kira na hud’un ya amsa. Bayan sun gaisa ne take ce mishi “tanaso zata je asibiti, Ummu zata rakata.” Ba tare da ya tambayi mai yake damunta ba yace “A dawo lafiya, kar kiyi dare!.” Daga haka ya katse kiran. Shiruu, tayi still da wayar a kunnenta bata cire ba.. ….Jiya har amai tayi a gabanshi amman bai damu ya tambayi me yake damun ta ba! Kuma wai a haka ne yake cewa ‘yana sonta’… Dafa ta d’in da Ummu tayi, tana mai cewa “mai ya ce?” ne, ya dawo da ita daga duniyar tunanin data tafi “Ba komai” Kawai ta iya cewa sannan cewa Ummu “ta mik’o mata hijabinta a wajen kayanta” daganan suka fito tsakar gidan... Jikin Huda ba k’aramin sanyi ya sake yi ba dan kasa zama ma tayi a d’akin! Tun lokacin da taji bayanin Mama akan abunda Hajiya Shuwa tace ta juya ta fita, daga d’akin gaba d’aya! Sakina da Sumayya ma suka bi bayanta.. Kamar yadda ta shawo kan Mama da kyar haka nan itama Sakina tayi fama da Huda dan da farko itanma cewa tayi ‘guduwar zata yi!’ Wai “tunda Mama ta haifeta bata huta ba har yau! Maybe idan bata nan Maman ta samu sauk’in wasu abubuwan… Ta gaji da ganinta cikin tashin hankali kullum.” Sai da Sakina ta bud’e mata wuta daga baya ta dawo lallashinta tukunna ta saduda. A gida suka bar su Sakina Ita da ummu suka tafi asibitin basu dawo ba sai wajajen k’arfe 10:00pm dan sai da aka k’ara mata ruwa Jikinta yayi weak sannan jininta ya hau.. Da kyar ma asibitin suka barta ta taho gida da ragowar drip ukun da bata gama shanyewa ba bayan Ummu tayi musu bayanin ‘akwai wata nurse mai chemist a bayan layin su da zata na chanja mata (drip d’in) sannan zuwa gobe da yamma in shaa Allah za su dawo’. Kamar kullum yau ma Ummu ce ta biya bill.. Kusan a tare Adaidaita sahunsu suka tsaya a k’ofar gidan da motar Auwal. Sam Jalila bata lura da su Mama ba, da yake duk a rud’e take kuma tayi dare tsoronta kar taje Baba ya dawo ya nemeta bai ganta ba! Dan bata san lokaci ya tafi haka ba Sai ta kalli wayarta yanzun tukunna ta gani.. Shiyasa ta zo ta wuce su tanata sauri nik’i nik’o da ledoji ta shige gidan. Kallonta Ummu tayi sannan ta kalli motar kafin tace “Allah ya kyauta!” Daga nan taci gaba da k’ok’arin taimakawa Mama ta samu da sauk’o daga napep d’in saboda har yanzu jikin nata babu kwari. Suna shiga suka tarar Sumayya tayi bacci Sakina da Huda kuma idonsu biyu sun yi tsuru tsuru da alamun hankalinsu ba a kwance yake ba dukda kuwa sun kira tace musu jikin nata da sauki.... A hanzarce bayan Ummu ta samu Mama ta kwanta ta cewa Sakina “Maza ta tashi Sumayya Babansu yayi mata waya ya kusan k’arasowa, su samu su wuce.” Kalar tausayi Sakina tayi kafin tace “Ummu dan Allah ki barni mana. Kinga Mama bata da lafiya.. Itama Huda ba zata ji dad’in zaman haka ba.” Nan itama Hudan ta saka baki suka hau rok’ar Ummu.. Shiruu, Ummu tayi kafin tace “to muje ki yiwa Babanku bayani.. Gashi nan ma na san shi yake kirana.” Tayi maganar tana d’aukar wayar ta kara a kunnenta.. Hakan kuwa akayi Allah ya taimaka ya barta. Sai da Ummu ta je ta samu mai chemist d’in tabbatar mata ‘gobe da safen dan Allah taje ta sauyawa Mama drip d’in kafin ta k’araso’ tukunna suka wuce ita da Baban Sakina da Sumayya........ Jalila tana shiga d’akin taga duhu, dan haka ta zaro wayarta ta d’an haska… Ga mamakinta sai taga Umma kwance tana ta sharb’ar barcinta!. Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin tace “Barka na, gobe idan ta tambaya sai ince da wuri na dawo..” Sad’af!!sad’af!! Ta wuce ta ajjiye ledojin ta fara k’ok’arin kashe wayar gudun kar Umma ta farka tana yi tana d’an kallonta. Sai dai kuma bata kai ga kashe wayartata ba taga Umman ta bud’e idanunta. Nan take ta diririce ta hau kame kame “Au um Umma k kin farka? Na d’auka kin yi bacci mai nisa ne.” “Zo nan Jalila” Shine abunda Umman tace tana mai mik’ewa ta zauna a kan gadon. A hankali ta k’arasa kusa da ita ta zauna. Kallonta Umman tayi ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace “Jalila, amma kin dai san halin Babanku ko? Ga waennan munafukan y’an bak’in ciki suma har sun fara k’ananun maganganu.. Nan gaba idan kin san za ki dad’e ki dinga fad’amin sai inyi k’aryar ‘nice na aikeki’ ko kuma ince kin yi bacci tuntuni. Allah ne yau ya taimake mu lokacin da Baban naku ya dawo bai nemeki ba! Na san da sai mun gane kuranmu daga ni har ke dan na san kowa sai yaji kanmu da shi, gashi gida ba mu kad’ai ba cike da y’an bak’in ciiki… Da kyar ma na lallab’a na bud’e miki k’ofa bayan naji ya shiga wanka Amman da har ya rufe.” “To Umman mu, in shaa Allah.” Shine abunda Jalila tace, had’e da sauk’e ajiyar zuciya dan Ita har ga Allah tayi tunanin Umman zata yi mata fad’an da yafi wannan.. Umman har ta koma zata kwanta idanunta suka kai kan manyan ledojin da Jalilan ta shigo da su! Dan haka ta mik’e. Kallonta tayi sannan ta mayar da idanunta kan ledojin kafin tace “Ke kika shigo da su?” Mik’ewa Jalilan tayi ta nufi inda ta ajjiye ledojin ta d’auko sannan tace “Eh, shopping muka je shiyasa ma muka yi daren.” Tana fad’i hakan tana mai k’arasowa ta ajjiye ledojin a gaban ta. Sauk’owa Umman tayi ta hau bubbud’ewa tana cewa “Nifa daman k’amshin ne ma ya farkar da ni Da farko mafarki na fara yi ‘inacin kaji’ sai kuma na fara jiyo k’amshi a hankali a hankali harya zo yayi mini yawa… Ashe d’an kirki ne ya had’o ko da su…” Tana maganar tana bud’e ledojin one by one.. Ledar farko Fresh milk ne masu sanyi da chocolate masu mugun tsada da ice cream da popsicles birjik! D’ayar ledar kuma kaji ne an yayyanka ledarsu daban sai k’aramin pizza da su shawarma da burger. Ledar ice cream d’in Umma ta sake dubawa dan d’azu kamar taji wani abun a ciki bayan abunda idanunta suka gani, ai kuwa nan ta zaro kud’i! Tun kafin tace wani abun Jalilan tace “Ni kinga ban ma san ya saka ba.” Jinjina kai Umman tayi kafin tace “Hmm, Jalila ina hango waenda za a kwantar a emergency ranar aurenki!” Tana magana tana juya kud’in. Rabawa tayi biyu, ta d’auki rabi ta bata rabi.. Jalila kwata kwata hankalinta ba a gurin yake ba sannan jikinta duk yayi sanyi shiyasa ma bata wani damu ba, tasa hannu kawai ta karb’a tana kallon Umma wadda ta mik’e taje ta ajjiye kud’in ta dawo ta zauna tana cewa “Ai gobe mai kankat! Zan cewa malan Yusuf yayi mishi.. Yarinya burin mu ya kusan cika, Allah ya kashe ya bamu.” Daga nan ta janyo ledar kaji ta hau ci sannan ta b’alle marfin fresh milk tana ci tana korawa da shi… Daman yau bata wani ci tuwon dare ba dan har ga Allah tuwo ya ginsheta wallahi ko sunanshi bata so taji an kira. Sai da Umma taci kusan rabi, ta shanye fresh milk roba d’aya, tayi gyatsa!! Tukunna ta juyo ta kalli Jalila wadda kwata kwata hankalinta baya d’akin kana ganinta ka san tunani take yi, ta k’urawa waje d’aya ido kawai tanata kallo!. Magana Umma tayi mata taga bata kulata ba, kamar ma bata jita ba! Dan haka ta kama k’afarta ta jijjiga sannan da k’arfi tace “Ke!!” Firgigit! Jalila tayi ta juyo tana kallonta, itama Umman ita take kallo tana sake nazartarta kafin tace “Tunanin me kike yi haka??” Ajiyar zuciya Jalila ta sauk’e sannan tace “Umma nifa Auwal d’innan na kasa gane kanshi! A iya fahimta ta fa kamar yana tunanin ni budurwar Arshaad ce. Sannan Umma, kwata kwata zuwanshi na biyu kenan amman na fahimci d’an iska ne! Kinga ranar farko rike min hannu kawai yayi ko? Amman, wallahi idan na fad’a miki abubuwan da yayi mini yau ke kanki sai kince ‘kar in sake kulashi’.” Kallonta Umman ta hauyi irin kallon k’urillar nan! Kafin ta ajjiye robar hannunta tace “Kuma na ganki Garau!!” Cike da rashin fahimta Jalila take kallonta… Fahimtar hakan (Jalilan bata fahimce ta ba) da Umman tayi ne yasa tace “Hmm” Kawai. Sai kuma ta sake cewa “me yayi miki?” Kame kame ta hau yi kafin tace “Har da rungumeni yayi, sannan ya dinga.......” Sai kuma tayi shiru. Tsaki Umman tayi sannan tace “Iyaka wannan ne Ina?? Jalila naga alamar bakida labarin ‘Hudan! Ita har makarantar kwana aka fake da kaita.’ Ni na haifeki, inaso ki fahimci ba zan tab’a cutar da ke ba! Yanzu duniyarnan ta chanza! Kuma Yaron nan burinmu a kansa ‘aure’ Allah na tuba ko me ma yayi miki ai dai shi d’in ne zai aurenki a k’arshe ko? Yanzu abinda nake so dake ‘Ki bishi a hankali kawai! Gudun kar ya sub’uce mana’ Ki bishi kawai a duk yadda yace! Ki barni da shi, ni na san me zan yi.” A hankali Jalilan tace “Umma to ba yadda wai za ayi In auri Ya Arshaad? dole sai wannan? Nifa shi nake so!”. Cikin fad’e Umma tace “Jalila wallahi zan ci buhun uban ki daga ke har Arshaad d’in! Nace miki ki hak’ura da shi ko? Ga hanya nan mafi sauk’i amman kin gagara fahimta? Da me Arshaad d’in yafi wanann??. Cikin katseta Jalila tace “Umma shine a zuciyata da haka kawai ya fishi...” Buge mata baki Umman tayi kafin tace “Bara kiji in fito miki a mutum!! Wallahi ba zan iya kokawar bin Malamai da masu kud’i ba! Ba zai yiu inje in bada dubu talatin mai kud’i ya zo ya ajjiye dubu d’ari ko d’ari biyu sannan kiyi tunanin za ai mana aiki iri d’aya ba! A nawa tunanin fa kenan, bansan ya naki yake a k’aramar kwakwalwarki ba. Ki cire wata soyayya a ranki… A zamanin mu ne muka bi soyayya, kuma gashi muna cin ubanmu! Gata nake yi miki Jalila ki bari mu nutsu waje d’aya mu yi abinda zai yiu, kar ki je kiyi saki reshe kama ganye! Na dai fad’a miki.” Tana gama fad’in haka ta mik’e tace mata “Asubah ta gari Bara in je ki saki net dan yau akwai sauro .” Daganan ta fice ta nufi d’akin Baba. Jalila ta dad’e tana tufka da warwara daga k’arshe ta yankee shawarar tabi zab’in Umma! Haka nan ta hak’ura da Arshaad ba dan zuciyarta tana so ba. Ta zo kwanciya kenan kiran Auwal ya shigo wayarta! Tana gani har ta tsinke bata d’auka ba! Tabbas duk tsaurin idonta da rashin kunyarta yau ta had’u da kakanta! Kuma kalli ba kunya ba tsoron Allah kiranta ma yake yi Ita kam kafin ta samu ta sake iya had’a ido da shi ma ai sai nan da kwana biyu ko uku ma.. Miss call d’aya ta samu daga gareshi daga nan bai sake kira ba! Dan ba zai tsaya kuchaka kamar ta tana ja mishi aji ba! Although ya san a d’an rikice take har yanzu wanda hakan ne ma ya sake tabbatar mishi da ‘Yarinyar sabon hannu ce!’ Ko banza ya san zai tsinci dami akala! Amman dukda haka zai yi sauri ne kawai yayi abunda zai yi ya gama ya kuma gano dalilin alak’arta da Arshaad daga nan ya had’a mishi bomb d’in da yaga ya dace dashi! Ita kuma ya wurga ta a dustbin! Tun kafin wani a cikin Abokanayen sa ya gano yana kula mace irinta… Although, she’s beautiful, tabbas tanada kyau, ta fanni daban daban wanda hakan ne ma ya sanya ya d’an sake janta a jiki amman dai still ba zai bari Abokanayensa su ga yana kula a girl like her, ba!. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 34 A meeting point d’in da suka yi zasu had’u… A nan suka tarar da Khadijahn tana jiransu. Ba tare da b’ata lokaci ba Aslam ya zaro blank check ya mik’a mata yace “Ta rubuta ko nawa take so muddin ta san zata fad’i gaskiyar abunda ta sani game da case d’in Arshaad.” “Mai yasa kake so ka sani” Ta yi musu tambayar tana mai kallonsu. Fahimtar da Aslam yayi za ta yi taurin kai ne ya sanya kawai yace mata “Ko ta fad’a ko kuma ya d’auke check d’in ya hanata kud’in kuma dole in za a shigo court sai anje da ita dan sunanta ya fito! Dan Auwal ya ambato sunanta a cikin case d’in.” Cikin tsanannin tashin hankali da b’acin rai tace “Auwal d’inne ya ambato sunana? Sannan abun naku har da court daman?”. Arshaad ne, yayi mata bayanin komai sannan ya d’aura da cewa “ina da recording d’in wayar da muka yi da Auwal lokacin da ya ambato sunanki a ciiki” Saboda haka ki taimaki kanki ki taimaki Auwal ta hanyar fad’in gaskiyar iyaka abunda kika sani. If not zata rufta da ke da Auwal d’in, duk ranar da aka zauna a kotu…. Domin kuwa shi Auwal yana tunanin yayi mini sharri! Sai dai kuma bai san iyaka wannan evidence d’in na voice call ya isa ya d’auresa tamau!! Kuma dole abun ya shafe ki. Jikinta har rawa yake yi tace “Dan Allah….zan gaya muku komai amman kar ku gayawa Auwal ni ce na fad’a!” ….Nan ta hau zayyano duk abunda suke da buk’atar ji da zai taimaka wajen wanke Arshaad! Daga k’arshe tace “gobe da sassafe su had’u a nan, zata kawo wasu takardun duk akan bayanan da zasu taimaka wajen wanke Arshaad d’in ne..” Sannan ta sake rok’ar su akan dan Allah dan Annabi kar su bari Auwal ya san itace ta fad’a musu, dan in dai ya sani to sai ya koreta a aiki bayan wulak’ancin da Allah kad’ai ya san kalar wanda zai yi mata… Sanann su yi k’ok’ari kar a shiga court kar sunanta ya fito dan ta san nan ma zata samu matsala da CEO! Bayan an yanke mata hukunci kuma kora ta biyo baya.. Da wannan aikin ta dogara su uku ne a family d’inta Ita , mamanta, sai k’anwarta Babanta ya dad’e da rasuwa ita take providing a family d’in su taimaketa! Dan Allah. Ta k’arashe maganar cikin had’e hannunwanta alamun rok’o!. “Thankyou Khadijah!.” shine kawai abunda Aslam yace mata daga nan ya mik’e tsaye yana cewa “Nayi miki alk’awarin ‘sunanki ba zai fito ba’.” Kafin yace “Rubuta kud’in da kike buk’ata za mu wuce. Da farko cewa tayi su barshi kawai. Sai da Arshaad yace “Ai alk’awari suka yi mata tun farko kuma ta fad’i abunda sukeson ji don haka dole su cika mata alk’awarin da suka d’auka.” Tukunna ta d’auki blank check d’in ta rubuta 300k! Sukayi signing mata suka wuce… Suna yin gaba Aslam ya zaro wayarshi a gaban aljihun rigarshi ya katse video d’in da ya saita tun kafin su fito daga mota. Basu samu sun je wajen Auwal a ranar ba! Saboda busy d’in da Aslam da Abba suka shiga har ma da Arshaad dan so suke su yi su gama shirye shirye su samu su bud’e company d’in nasu soon. Around 9:00 pm washegarin ranar bayan kowa ya dawo a office an yi dinner da isha suka nufi gidansu Auwal.. Da Mom suka fara cin karo a k’asa tana waya. Faram faram ta karb’esu bayan y’an gaishe gaishe Arshaad yace “Auwal yana nan?”. “Eh, yana sama har ya kwanta ma. Wai ya gaji yau sosai.”Ta basu amsa, a tunaninta za su bari ne amman sai taga Aslam ya mik’e yana cewa “yana nan a side d’inshi na daa har yanzu ko?” “Eh” ta sake basu amsa. “Muje” Aslam ya cewa Arshaad, daga haka suka nufi saman. Mom ji take yi kamar ta bisu ta lab’e taji meyene ya kawo su dan tabbas ta san ba lafiya ba! Tunda dai Auwal ba shiri yake yi da either of them ba. Tana shirin mik’ewa Daddy ya shigo! Kamar ta kurma ihu haka taji, haka nan tana ji tana gani ba yadda ta iya…ba dan ta so ba ta hak’ura da lab’en data shirya yi. Kamar yadda Mom ta fad’a musu, Auwal d’in har ya kwanta! Har cikin bedroom d’inshi suka shiga Arshaad ya lalubo switch ya kunna!. Baccin nasa bai yi wani nisa ba shiyasa yayi saurin farkawa yana mitsi mitsi da idanuwa. Da mamaki yake kallonsu kafin ya mik’e ya zauna a kan gadon yace “Lafiya! Zaku tashi mutum yana bacci? Infact baku san babu kyau invading privacy ba?”. Murmushi Arshaad yayi ya k’arasa inda yake ya zauna a gefenshi kafin yace “Ai baka taki zaman lafiya da kwanciyar hankali ba! So ka cire bacci a agenda d’inka for now and start worrying about yourself.” Tsaki kawai yayi ya fara k’ok’arin komawa ya kwanta. Dai dai nan Aslam ya k’araso yayi masa playing video d’in da suka yiwa Khadijah jiya ba tare da ta sani ba. Jin muryar Khadijah ya sanya ya d’ago yasa hannu ya karb’a dan da farko k’in kallon wayar ma yayi. Sai da video d’in ya k’are tukunna Aslam ya jawo stool ya zauna a kai yana facing Auwal d’in! A hankali ya fara magana “Auwal da kai da Arshaad ba ku da bambanci a wajena amma i have to sopport wanda yake da gaskiya! Ka taimaki kanka ka taimaka mana mu kashe case d’innan if not kai kanka ka san ba zatayi maka kyau ba! In ka yarda kayi sopporting d’in mu Ni na san ya yadda zan yi in rufa maka asiri In rufawa ita Khadijah asiri Case d’in ya mutu ba tare da sunan either of you ya fito ba! Amman if you try to act stubborn and rude to bani da wani choice d’in daya wuce In saki video d’innan! And the first person da zan turawa shine ‘Granpa’ Followed by su Dad Daga nan su Mom After them kuma har a MT estate da company sai kowa yaji kuma ya gani! Wallahi. Shiruuu, Auwal yayi yana lissafi… Duk ta inda ya duba ya zagaya ya zagayo bashi da mafita! Dan haka kawai ya yanke shawarar hak’ura. Amman fa sai ya gasawa Aslam aya a hannu wallahi! Zai san ya tab’o shi.. But first zai bari komai ya lafa zuwan nan da kamar 2 ko 3 months haka A lokacin zai san wayene Auwal! And he will make sure yayi takunshi da kyau ta yadda ba za su samu damar kamashi ta ko wacce hanya ba…. “Kai muke jira!” Ya ji muryar Arshaad. Ajiyar xuciya ya sauk’e sannan yayi murmushi ya d’ago ya kalli Aslam kafin yace “Selfish bitch!! Kar in sake jin kace ‘da ni da Arshaad d’aya muke a wajenka!’ Bana son munafurci gara kawai ka fito a mutum ka bi bayan brother d’inka ka bar yin wasu kwana kwana..” Mik’ewa kawai Aslam yayi ya cewa Arshaad “muje! He’s not ready to negotiate.” Sai da Auwal ya runtse idanunsa da k’arfi! Yana mai jin takaicin abunda zai fad’a, tukunna a hankali yace “Truce accepted!” Murmushi Aslam yayi ya juyo yace “Good boy! First of all.. Zaka kawo takardun da kace ka had’a na wasu laifuffukan da zaka sake d’aurawa Arshaad idan an je court. Sannan Akwai papers d’in da nake buk’ata ka yimin zuwa nan da 24 hours.. ( nan ya zayyano mishi abunda takardun za su k’unsa) “Zan had’a tare da na Khadijah In kaiwa Granpa Once yayi accepting, shikenan case ya mutu! Daga nan sai ka sameni ni kuma zan goge video d’innan a gabanka har wanda na tura a laptop duk zan goge.” “Sounds fare” Shine abunda Auwal yace daga nan ya juya ya kwanta yace “Ku kashe min bulb in kun tashi fita.” Har zasu wuce Aslam ya juyo yace “Ina so kayi promising d’ina ‘ba zaka yiwa Khadijah komai ba’ Saboda na riga nayi mata alk’awarin kareta ta ko wacce hanya.” Sai da Aslam ya kira sunanshi tukunna yace “To!!” Ba tare da ya juyo ya kalle su ba. Arshaad ne ya fara ficewa sannan Aslam bayan ya kashe mishi bulb d’in ya jawo k’ofar d’akin, suka wuce. Suna fitowa a d’akin Arshaad yace “Thankyou! Case zai mutu ba tare da sunan kowa ya b’aci ba.” Murmushi Aslam yayi sannan yace “ka fahimceni kenan.. Gara hakan ai dan ni a ganina idan muka had’ashi da Granpa rigima ce babba da Allah kad’ai ya san k’arshenta. Ni da in da ace za a bi ta tawa To da an bar maganar bada company d’innan a mutum d’aya da Granpa yake son yi! Rivalry kawai hakan zai janyo da bitterness d’in da Allah kad’ai ya san k’arshen shi.......” Da safe kamar yadda Khadijah ta fad’a, haka ta kai takardu. Auwal ma 24 hours suna cika ya cika alk’awari….. Da mamaki a kan fuskokinsu suka dinga kallon sharrin da Auwal ya k’ukk’ulawa Arshaad kala kala! Wanda tabbas idan takardun suka fita to da wuya in Granpa ba zai saka Arshaad ya k’are rayuwarsa a jail ba! A take suka yaga takardun sannan Aslam ya had’a da na wajen Khadijah da ragowar takardun daya had’a yake kuma buk’ata Ya nufi wajen Granpa da su. Sai da Aslam ya tabbatar Granpa ya yarda kuma ya hak’ura sannan case ya mutu! Tukunna ya dawo ya goge videos d’in Khadija a gaban auwal kamar yadda yayi alk’awari.. Sai dai kuma Auwal d’in bai kai ga barin wajen ba ma Message d’in Granpa ya shigo wayarshi../ “He’s not serious, ba shi da lura he’s reckless!! Shiyasa aka samu har kud’i masu yawa haka suka shiga account d’in Arshaad instead of account d’in turawan da ya kamata ace an tura.. Gashi yanzu sun yi loosing contract d’in! Saboda haka gobe yana zuwa office ya kwashe kayanshi daga office d’in md ya maida ground floor.....”. Da kyar Auwal ya iya jan k’afafuwan shi yana ganin dishi dishi ya fice daga side d’in nasu ba tare da ya cewa d’aya daga cikin su uffan ba! Ikon Allah ne kawai ya maidashi gidansu. Yana fita ba da dad’ewa ba Message ya shigo wayar Arshaad shima.. ‘An maidashi aiki But ya samu demotion kamar Auwal A ground floor zai koma aikinshi.’ Murmushi yayi bayan ya gama karantawa, ya turawa Granpa d’in “Thankyou Granpa A lot.” Sannan ya mik’awa Aslam wayar yana mai cewa “Da babu gara ba dad’i.” Kwata Kwata Aslam bai ji dad’in hakan ba! Ganin haka yasa Arshaad d’in yayi ta mishi nuni da ‘daman ya san sai an hukuntashi ko da ace an yafe mishi, so shi a ganinshi babu wata damuwa.. Dama shi burin shi case ya mutu kuma ya mutu! Dan haka Alhamdulillah Ya san k’ark’ari a rage mishi salary wanda shi salary d’in da ake biyan shin ma kamar bonus ne saboda company d’in shine ja baya a harkoki daban daban d’in da yake yi wajen kawo mishi kud’i! Kuma yanzu ya san tunda a ground floor yake to duk inda 3 tayi ya tashi! Hakan zai bashi dama wajen focusing a kan ragowar businesses d’in da yake yi…’. Sai da yaga Aslam d’in ya fahimceshi tukunna ya kyaleshi haka suka fad’a wata hirar. Tun a Daren ranar Granpa ya gama deciding sannan ya rubuta ‘Kujerar md ta koma hannun Aslam!’ Daga nan ya kira Baban Auwal yace “ya ci gaba da managing branch d’in ‘Mai Turare’ na Uk ko wata wata ne ya dinga lek’awa saboda ya san a anan ma akawai wani company d’in su daban da yake kula dashi. Tunda yanzu Aslam ya dawo nan to shi zai zama MD na nan, saboda Arshaad da Auwal wawaye ne basu san aiikin ba! Sannan baya buk’atar Aslam d’in ya sake komawa UK! Ya isa haka.. Maganar Mahaifiyarshi kuma in shaa Allah yana sa ran dacewa dan yayi booking appointment da ‘best neorologist in the world’ za a kaita ta ganshi, in shaa Allah akwai alaman nasara.. So ayi arranging papers na change of position d’in da aka samu da office In shaa Allah gobe shi da kanshi zai yi introducing Aslam as their new MD na wannan branch d’in! Next week kuma sai suje UK d’in nan ma a yi y’an tsare tsare………” Yana gama fad’an haka suka yi sallam bayan Baban Auwal d’in ya nuna mishi fahimta da amincewar hakan 100%. Yana ajjiye wayar ya kasa juyowa ya kalla inda Mom take dan tun lokacin da ya fara wayar yaji ta mik’e ta zauna a kan gadon. Sarai ya san ko bata ji komai ba to ta fahimci wani abun! Bai san ta ina zai fara yi mata bayani ba, dan in dai a kan Auwal ne to gaba d’aya yanzu notikan kanta za su kwance! Shi kuma har ga Allah bai shiryawa hakan ba cikin daren nan, kanshi ciwo yake yi besides kuma yana tunanin rik’e manyan company’s har biyu! Dan bayan ‘Mai Turare’ company na oils d’in da yake rik’e dashi is the second largest a family d’in…. Yana cikin wannan tunanin ya ji lallausan tafin hannunta a kan kafad’ar shi. Shiruuu, yayi bai kulata ba, hakan ya bata daman fara magana.. “Ka san dai na fahimci akwai matsala, ko? Rashin sanar dani da yin shirun ka sake saka zuciyata cikin zullumi zai yi! Dan Allah ko menene komai d’acinsa ka fad’amin, please Mijina.” Tayi maganar tana amfani da tafin hannunta wajen shafashi. Juyowa yayi gareta ya kamo hannun ya rik’e sannan ba tare da b’oye b’oye ba, ya hau fad’a mata yadda suka yi game da ‘zai koma MD na branch d’in Uk, tunda Aslam ya dawo..shi kuma Aslam d’in an bashi MD na nan!’ Tun kafin ya k’arasa rufe bakinshi tace “Auwal fa?” Ajiyar zuciya ya sake sauk’ewa kafin yace “Ya samu demotion! Da shi da Arshaad Granpa yace ‘they are not capable’….. Mom wadda ranta ya b’aci hankalinta ya tashi bata san lokacin da ta manta da duk wani karatun kissar ta ba tace “Zancen banza kenan!!! Daga bakin mutanen banza, wallahi ba zai yiu....” Tsawar da Daddy ya daka mata ce ta sanya ta d’an seseta hankalinta ya d’an dawo “Bana son raini fa Adama!!!! Ni ne mutumin banzan ko mahaifina?? Hukuncine ya riga ya yanke kuma dole uban kowa ya bi! Idan kuma kina da ja na tabbatar kin san inda zaki iya samunshi. Ai tun Auwal bai kawo haka ba! Tun bai gagaremu ba nake gargad’arki… Yanzu gashi anzo gab’ar da bamu da wani choice d’in da ya wuce muna ji muna gani mu dinga take laifukanshi muna b’oyewa saboda rufun asirin mu baki d’aya! Ko kin san irin kalar b’arnar da yake tafkawa a office kuwa?? Baki da abinda kika d’orasa a kai tun tasowarshi kawo yanzu sai ‘ya bi duk wata hanya da zai bi don a Mallakaa mishi Mai Turare!’ Ko kina tunanin ban san me kike yi ba? Baki damu da kare mutumcinshi ba! Baki damu da d’orashi a kan addini ba! Baki damu..baki damu…baki damu ba da yawa, Adama!!!. Tarbiyyar ma ba bashi kika yi ba instead ina yi kina warware min! Gashi yanzu ya addabeni ya addabeki kuma kwad’ayin Mai Turaren da kike yi…due to yadda kika maidashi ya sanya yana abu kamar psyco psyco gashi yanzu instead of daga MD ya wuce CEO gashi an maidashi ground floor!!! Wa gari ya waya kenan?? Daga 10th maimaikon ya k’are yin sama amma instead ya dawo ground flour! Kinga garin neman gira an rasa ido……” Hakanan Daddy yayi mata tatass! Kamar ya ari baki.. Mom kam kasa danne bak’in cikin ta tayi haka nan ta dinga kuka wiwi har da majina kamar wata k’aramar Yarinya.. Ganin haka ya sa Daddy ya d’an sassauta muryarshi yace “Kiyi hak’uri Adama, da Auwal da Arshaad da Aslam duk abu d’aya ne! Koma waye aka bawa MT duk dai y’ay’an mu ne.. Kuma daman ni na dad’e da fahimtar Aslam d’in yake son bawa ko duba da d’umbin soyayyarshi a zuciyarsa da kuma tausayinshi… Auwal ya rainaki amman still mu muka haifeshi! Lokaci yayi da zaki fara nuna mishi dai dai duk d’acin ta da kuma akasin haka. Idan muka zuba ido a kansa especially yanzu da yaga Aslam ya dawo Ina jiye mishi kar yaje yayi wani shirmen da za a kwace gaba d’aya shares d’insa a duk k’ananan company’s d’in sannan kuma a koreshi gaba d’aya! Kina gani dai irin tarin soyayyar da Granpa ke yiwa Abba! Na san duk da abunda ya shiga tsakaninsu har yanzu yanajin shi a rai amma ki duba kiga yadda ya rufe ido ya tsameshi a kan komai yanzu.. Tou har gara Abba dan yanzu shirin ma bud’e construction company suke yi shi da Aslam Kisa a ranki Auwal aka yiwa abunda aka yi wa Abba Shin wacce sana a kike tunanin zai yi?? Gashi girma ya zo mishi, lokacin tara Iyali yayi.” Shiruuu, Mom tayi ta nutsu ta bama Daddy dukkan hankalinta tana sauraronshi.. Ba k’aramin dad’i hakan yayi mishi ba kuwa, dan haka ya gyara zama yaci gaba da yi mata nuni da abinda ya dace da wanda bai dace ba da kuma yadda zasu had’u su gyara d’ansu tare da neman had’in kanta… Sun dad’e suna tattaunawa ganin ta aminta da hakan ga kuma nadama k’arara a kan fuskarta dan har hak’uri ta bashi tare da alk’awarin yin amfani da shawarwarinshi.. Hakan yasa ya janyo ta yayi hugging d’inta zuciyarshi fes! Cike da farin ciki, ba abunda yake buri a yanzu sama da ya ga Auwal d’insa ya nutsu ya zama kamar su Aslam shima. A haka ya jata suka kwanta yana mai karanto addu’o’in bacci ya shafe jikinsu dashi, yana d’an shafa gashin kanta har bacci yayi awon gaba da shi. Ganin da Mom tayi yayi bacci yasa ta share hawayen da suka zubo mata sannan ta mik’e ta zauna ta galla mishi wata uwar harara a ranta tace “Sakarai kawai! Ana nuna maka Annabi kana runtse ido, ko su y’an uwan naka dakake ta tak’ama kana nuna y’ay’ansu nakane bari kaga ranar da za a bawa wani Mai Turare a nan zaka sha mamaki! Infact shekaru ma suna ja nan zaka fahimci da mai shi ake yi!”. Pillow taja ta saka a bayanta sannan ta kishing’ida a kan gadon dan ita bata ga ta bacc ba! Ai kuwa bata yi minti talatin ba idea ta fad’o mata! Murmushi kawai tayi sannan tace “Alhamdulillah” Tana mai ayyanawa a ranta ‘Gobe! Zata je ta samu Maman Aslam ta sanar da ita Aslam ya dawo! Bayan ta san yadda tayi ko ta halin k’ak’a ne ta d’auki video d’in Aslam da Arshaad ko dai wani a cikin estate d’in ba tare da an farga ba, ta yadda Maman nasa zata fi yarda idan ta gani.’ Juyowa tayi tana kallon Daddy wanda yake ta baccinshi.. Murmushi tayi tace “Yi baccinka Mijina! Auwal shi ke da Mai Turare, Bi‘izinillahi Ta ala.” Auwal, shi kam yana chan abun duniya yayi mishi zafi! Ya rasa ta Ina ma zai fara. Wayarshi ya zaro ya hau online wai ko zai d’an samu ya rage zafi! Sai dai yana hawa yaci karo da message d’in Jalila a sama sama da alamun yanzu ta turo.. Tsaki yayi ya jefar da wayar dan kwata kwata ya kasa fahimtar spelling d’in nata sannan ya gaza ganewa shin da Hausa tayi mishi magana ko da turanci!. Shifa ya kasa fahimtar alak’arta da Arshaad kwata kwata! Ya bugi cikinta shekaran jiya amman bai fahimci komai ba.. Ganin she’s not worth his time ya sanya kawai ya kawar da tunaninta gefe ya fara wanda ya san zai fishshe shi….. Gandun Albasa ! Yau kwana uku kenan rabon Jalila da Auwal Tun ranar da ya kirata a waya bata d’auka ba bai sake nemanta ba! Umma tana ankare da ita shiyasa da taga kamar basa waya kuma bataji tace mata zai zo ba ta tambayeta.. Jalila bata b’oyewa Umman komai ba, tace mata “Tun ranar da suka je shopping da ya kirata bata d’auka ba har yau ba suyi magana ba.” “Innalillahi wa innailaihirrajiun!!” Shine abunda Umman tace tana dafe kanta. Da sauri Jalila tace “Umma mai ya faru??” Cike da takaici tace mata “Ke kika faru! Mahaukaciya dak’ik’iya irin ki, banza kawai!.” Tura baki tayi ta koma gefe tana gunaguni dan sai yanzu ta fahimci dalilin salatin nata Cikin gunagunin nata tace “Umma nayi mishi magana fa a watsapp bai ce min komai ba.” Cikin tsananin b’acin rai Umman tace “Wallahi ko nice ba zan kulaki ba! Anya Yarinyar nan kin san ciwon kanki kuwa?” Tsabar bak’in ciki Umma kasa ma ci gaba da yi mata magana tayi, dan haka kawai ta mik’e ta fice a d’akin ta zauna a tsakar gida. Ganin yadda ran Umma ya b’aci sosai ne ya sanya kawai ta d’auki waya ta kirashi… A na farkon bai d’auka ba sai ana biyun! Shiru, yayi bai ce komai ba! Jin yayi shiru yasa tace “Ina wuni” “Lafiya” kawai yace mata. A hankali tace “Kwana biyu”. “Umm” Kawai ya sake cewa. Jin tayi shiru yasa yace “Kina da abun fad’a ne?”. Taji zafin tambayar amman kawai ta daure tace “A’a kawai dai na kira mu gaisa ne.” “Hmm” Kawai yace daganan duk suka yi shiru. Kamar ba zai ce wani abun ba chaan! Kuma ya sauk’e ajiyar zuciya yace “Shekaran jiya baki ga miscall d’ina ba??” A hankali tace “Na gani.” “So?” Yayi mata tambayar a gajarce. Dabara ce ta fad’o mata dan haka tayi saurin cewa “Bani da kati ne, sai yau Umma ta saka min.” A hankali taji ya sauk’e ajiyar zuciya “Na d’auka kyaliya ce ai, shiyasa daa har nayi fushi.” Murmushi tayi sannan tace “Kayi hak’uri” Shima murmushin yayi daga nan yace “Ina aiki, zamu yi magana anjima.” “Allah ya taimaka” tace mishi. Daganan ya yanke kiran. Bai sake kiran taba har bayan kwana biyu… Yau ma Ummance ta tusa ta a gaba sai da taga ta kirashi ya amsa a kira a hud’u! Tukunna ta fita daga d’akin. Ya d’an sake yau ba kamar ranar ba…har d’an janta da hira ma ya dinga yi! Amman wata maganar idan ya fad’a sai taji kamar k’asa ta tsage ta shige ciki… Sai da suka kusan k’are wayar tukunna yace mata “ta shirya gobe zai zo da safe zata rakashi unguwa! Tunda weekend ne.” Sai da ya maimaita mata tukunna tace “Allah ya kaimu” Daganan sukayi sallama. Sun gama wayar kenan Umma ta shigo. Ganinta tayi zaune da waya a kunnenta amma kamar ba wayar take yi ba, da alamun tunani ta tafi… Sunanta ta kira dan haka tayi firgigit! Ta juyo tana kallonta kafin ta sauk’e wayar daga kunnanta tana mai sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya. A hankali Umman ta k’araso ta zauna a kusa da ita kafin ta dubeta tace “Tunanin ne yau ma?” Wata ajiyar zuciyar Jalila ta sauk’e kafin tace “Wai cewa yayi zai zo in rakashi unguwa gobe! Da safe.” Murmushi Umma tayi sannan tace “kice kar inci d’umame da abinci rana gobe, ke har ma na dare ba zan ci ba.” Tana gama fad’in haka ta mik’e ta isa bakin wardrobe ta sunkuya ta d’auko ledar da su Huda suka kawo mata kwanaki ta zaro dandatsetsiyar riga tace “ungonan ajjiye ta a gefe ita zaki saka gobe.” Cikin rashin jin dad’i Jalila tace “Haba Umma! Daga yace in zo ni kuma sai kawai in bishi zungui zungui? Sati d’aya fa kenan yau d’in da had’uwa ta fa dashi. Sannan, kin ga dai bai gaya min inda za muje ba ko? Amman wallahi tunani na ya bani! A yanayin maganarshi da hirarshi ta yau sarai na fahimci inda ya dosa! Saboda haka gaskiya ni babu inda zan je!!”. Tayi maganar tana had’e rai sannan ta gyara ta kwanta a kan gadon rigin gine. Takowa inda take Umma tayi bayan ta ajjiye rigar a kan kujera Tana zuwa tace “Kin san Allah Jalila Wallahi sai kin je!!” A zabure da d’an mamaki a kan fuskarta ta mik’e ta zauna tana kallonta “Kwarai kuwa! Kin jini da kyau! Cewa nayi wallahi sai kin je! Idan ta kama in jaaa ki ne To ina iyawa In fitar dake!Muddin ya zo gobe kika yi taurin kai. Tunda na lura so kike ki kasheni da raina y’ar bak’in ciki Yarinyar da bata san ciwon kanta ba! Ana nuna mata Annabi tana runtse ido!.” Tana gama fad’in haka ta juya ta fice fuuu kamar zata tashi sama. Har dare Umma k’in kula Jalila tayi. Washegari da safe ma k’in kulata tayi… Ko tayi mata magana sai dai ta d’auke kai ta fara wak’a! Sanin abunda ya had’asu fad’a da Umman nata ne ya sanya kawai ta mik’e ta shiga wanka ta fito ta tsantsara kwalliya ta sanya doguwar rigar da Umman ta zab’a mata jiya.. Tayi masifar yin kyau kuwa kamar ka saceta ka gudu! Tana cikin rolling Umman ta shigo, tana ganinta a shirye ta hau Fara’a! Sai a lokacin taga tayi murmushi tun jiya. “Hmm” Kawai Jalilan tace daganan ta koma kan kujerar d’akin inda ta ajjiye purse d’inta ta d’auka da wayarta tace “Bara inje yana waje.” “To d’an yi dariya mana Autata! Haba mana.. Haka zaki fita kina fushi da ni?”. Umma ta fad’a cikin sigar zolaya. Murmushi kawai Jalilan ta iya yi daga haka ta sa kai ta fice daga d’akin...... A hargitse Anty Zainab ta shigo gidan sakamokon abunda Umman ta gaya mata a waya tana kuka… Bata bi ta kan Hudan wadda ke sharar tsakar gidan ba ta shige ciki kamar zata hantsila, kai kana ganinta ka san ba lafiya ba! Tana shiga d’akin ta hango Umma zaune akan kujera tanata faman sharb’ar kuka! Kamar jira take yi suna had’a ido da Anty Zainab ta sake sakin kukan da k’arfi. Da sauri ta k’arasa inda take kafin tace “Haba mana Sadiya, ba kuka za kiyi ba! Tashi za kiyi a fara nemanta In ta kama har gidansu shi Yaron sai aje.” Cikin kuka Umma tace “Ina na san gidan su Yaron? Sai dai In Huda za a kira ta fad’i inda gidansu Arshaad d’in yake sai aje Na san za a samu Jalila a wajen” Gaba d’aya kan Huda d’aurewa yayi lokacin guda! …Parker take nema a tsakar gidan bata samu ba Chan ta hango wata a bakin k’ofar dakin Umman dan haka ta k’arasa don ta d’auka! Ba abunda kunnuwanta suka jiyo mata sai “Inda gidansu Arshaad d’in yake sai aje Na san za a samu Jalila a wajen.” Da mugun sauri ta bar wajen kanta a d’aure.. Har ta kwashe sharar ta zubar ta wuce d’aki hankalinta sam baya jikinta… A Chan d’aki kuwa cikin rashin fahimta Anty Zainab tace “Arshaad dai saurayin Huda?” Da sauri Umma tace “eh, ai Yaron k’aninsa ne.” Ajiyar zuciya Anty Zainab ta sauk’e kafin tace “D’an gwada sake kiranta muji ko zata d’auka!” Cikin kuka Umma tace “Tun shekaran jiya fa wayar a kashe! Yau kuma da safe a kunne amman nayi mata miss call yafi dari biyu bata d’auka ba.” A hankali Anty Zainab tace “Tou ko Baba zamu gayawa? Lamarin nan bafa lalle mu iya handling d’inshi mu kad’ai ba.” Cikin firgici Umma tace “Ki rufamin asiri Zainab! Tun a jiyan ya fara sintirin nemanta.. Babban abunda yafi d’aga min hankali shine ‘Nace mishi yau zara dawo daga gidan Hansai! Dan ce mishi nayi nan taje sai kuma aka yi rashin sa a Hansai d’in ba lafiya shine nace ta d’an zauna tunda Yaranta ita duk maza ne ba zasu iya jinya ba!’ Wallahi Zainab In kinga yadda mutumin nan yayi min fata fata d’azu da safe za ki sha mamaki Kin sanshi a kan Jalila da Ja’afar.. To yanzu kafin ya fita kasuwa sai da yayimin gargad’in ‘In tafi gidan Hansai da kaina In d’auko mishi y’arsa idan ba hakaba na bari ya dawo babu Jalila a gidannan duk abunda yayi mini in kuka da kaina!’ Har kud’in mota ya bani Yanzu gashi yamma tayi na san duk inda isha tayi ya dawo gidannan Ta Ina zan fara? Ya zan yi? Ina zan ga Jalila ni Halimatu!!”. Ta k’arashe maganar tana fashewa da kuka. Da kyar Anty Zainab ta samu ta lallasheta. Sun jima suna tattaunawa daga k’arshe suka yanke shawarar fad’awa kowa ba a san inda take ba! Tasan su Kaka zasu san abun yi kuma in sha Allah za a ganta ba tare da asirinsu ya tonu ba! Amman muddin suka tunkari su Ummu da Huda da zancen aka tambayi Arshaad to sai gaskiya ta fito Sukuma ba zasu so a san asalin dalilin b’atan nata ba. Umma tana kuka wiwi da majina suka nufi k’ofar fita daga d’akin dan zuwa wajen su Kaka. Anty Zainab ce a gaba Umma a baya Kicib’is!! Haka taja ta tsaya tana kallon Jalila wadda ta shigo yanzun nan.. Da sauri Umma ta ture Anty Zainab d’in tayi kan Jalilan ta hau duddubata kafin ta jawota jikinta ta rungume ta sa kuka Ga mamakinsu sai sukaga Jalilan itama ta fashe da kuka!! Shiruuu, Umman tayi ta hau lallashinta tana tambayarta amman tak’i kulata! Nan suka jata suka kaita bakin gado suka zaunar da ita suka hau tambayarta suna lallashinta… Bata ce dasu k’ala ba in banda kukan da take yi kamar ranta zai fita! Da kyar da sid’in goshi bayan kamar awa d’aya aka samu tayi shiru.. Bata ko kalli inda suke ba ta ja pillow ta kwanta ta juya musu baya Tanaji Umma tana yi mata magana tayi banza da ita! Ko minti biyar bata yi da kwanciyaba baccin wahala yayi gaba da ita… Bata san lokacin da Anty Zainab ta tafi ba Ta dai ji lokacin da Baba ya haska ta da tochila yana cewa “Ya naga fuskarta duk a kumbure?” Tanajin Umma tana yi mishi magana bata gama fahimtar zancen nata ba wani baccin ya sake kwasheta….. Ba ita ta tashi ba sai washegari wajajen 10:00pm Da Umma ta fara yin tozali dan haka tayi saurin kawar da fuskarta ta mik’e ta zauna. Bata kalletaba ta sauk’o daga kan gadon ta duba wardrobe d’inta ta d’auka brush da makilin tayi hanyar waje “Jalila zo nan!” Taji muryar Umman. Sai da ta juyo ta kalleta tukunnan ta d’auke kai ta fice daga d’akin, ta bar Umman nan zaune da baki a sake. Umman ji take kamar ta bita har wajen sai kuma ta tuna ba su kad’ai bane a gidan dan haka ta hak’ura ta zauna tana zaman jiranta a d’akin! Bata dawo d’akin ba sai da tayi wanka! Tana shigowa, ko gama ajjiye kayan jikinta data fita da su waenda yanzun ta cire ta ruk’o a hannunta bata yi ba Umma ta hau ta da fad’a! kamar zata had’iyi harshenta ta inda take shiga bata nan take fita ba.. Ko kallon inda take Jalilan bata yi ba…shirinta kawai take yi cikin nutsuwa.. Hakan kuwa ba k’aramin sake fusata Umman yayi ba Dan haka ta fincikota cikin b’acin rai tace “Wai aljanun rainin wayo kika je Auwal d’in ya saka miki? Wacce sabuwar d’abi’a kika d’ebo ne? Ya Ina yi miki magana tun jiya kin banzatar dani kamar ba uwar da ta tsugunna ta haifeki ba??” Ta k’arashe maganar cikin d’aga murya. Wasu zafafan hawayene suka zubo a kan kumatun Jalila! Cikin tsananin d’acin zuciya tace “Umma abunda nima nake ta so in tambayeki kenan ‘Anya kuwa kece uwar da kika haife ne?’ Kece uwar da kika reneni a jikinki?” Bata damu da yadda kalamanta suka sake b’ata ran Umman ba taci gaba da magana “Umma da na nuna miki bana son alak’a ta da Auwal ya kamata ace kin fahimceni a matsayin ki na Mahaifiyata! Ban tashi sanin na tafka babban kuskuren biyewa son zuciyarki da nayi ba sai shekaran jiya da kika kasa kwata ta kika kasa cetona! Sai a lokacin na lura da yadda ni da ke muka taru muka jefe rayuwata a cikin tsanannin tashin hankali!” Kuka mai k’arfi ne ya kwace mata, cikin kukan tace “Umma yanzu wa kike tunanin zai aureni a haka? Me kikaso In cewa Mijin da zan aura? Bari kiji in gaya miki, Auwal har fyade sai da yayimin da na k’i in bashi had’in kai a farko! Sannan yau ya ce mini ‘ko kiransa Idan nayi raina sai ya b’aci!’ A kan kawai ya tambayeni in fad’a mishi alak’a ta da Arshaad nace mishi ‘ba komai’ Kuma ya tabbatar mini da ba aurena zai yi ba! Yace kawai ya fad’amin haka ne saboda In saki jiki da shi sannan maganar auren da yace Arshaad zai yi Wannan itama k’arya ce!. Umma har ‘Akuya’ ya ce mini! Yace bai tab’a ganin macen da aka yi winning d’inta a cikin sati daya tak ba Sai ni. A cikin sati d’aya kika tunzura ni na bi wanda ban sani ba kika jefa rayuwata cikin tashin hankali da rud’ani! Duk ata dalilin burin ki wanda na tabbatar yanzu bazai tab’a cika ba!. Umma ni kinga rayuwata ta riga ta lalace ko? To ki zuba ido ki gani! Muna nan zaune a cikin gidan nan Arshaad zai zo a d’aura mishi aure da Huda ya d’auketa ya kaita gidanshi taji dad’i ta huta tayi rayuwarta cikin kwanciyar hankali! Saboda ita Mama ta bata tarbiyyar data kamata, ta kama kanta ta kama mutuncin ta...........” Mahaukacin marin da Umman ta d’auketa da shi ne ya sanyata had’iye ragowar maganganun ta! A take ta durk’ushe a wajen ta fashe da wani matsanancin kuka… Umma kanta bata san lokacin da hawayen tashin hankali suka zubo mata ba! Kasa magana tayi kawai ta suri mayafinta tayi gida wajen Baaba Laraba. Ita kanta Baaba Laraban ba k’aramin tashin hankali ta shiga ba daga jin labarin da Umman ta zo mata dashi.. Tabbas Yaron nan shak’iyi ne! Amman ko d’an shed’an ne shi wallahi sai ya dawo ya auri Jalila Ko da kuwa ace za suyi yawo tsirarane! Sanann sai sun raba Huda da Arshaad rabuwa ta har abada!! Kamar mahaukata haka suka zama….a iya ranar kad’ai sai da suka je wajen mutane uku!! Sannan suka hak’ura suka koma gida Shima dan sunga dare yayi. Haka nan duk a gajiye suka nufi gidajensu da niyyar fitar sassafe washegari idan Allah ya kaimu............ BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 35 Washegari Kamar yadda Mom ta yi niyya… Haka nan ta d’auki video d’in da ta shiryawa! Ta saman balcony d’in d’akin Mammy ta d’auki video d’in Aslam da Arshaad lokacin suna shirin fita.. Ko ta kan Mammy wadda take ta faman tambayarta “me za tayi?” Bata bi ba, ta fice abunta tana cewa “In na dawo zan yi miki bayani”… Sai dai kuma tana zuwa gidansu Aslam d’in ta tarar su Gwaggo Asabe sun yowa Mommyn rakiya Flight d’inta nan da awa d’aya (9:00pm) zai tashi!! Lokacin appointment d’inta da Neurologist d’in da Granpa yayi mata booking yayi… Kamar Mom ta had’iye zuciya haka taji, ba yadda ta iya haka nan ta hau yi musu fatan alkhairi suka wuce ita da Aaima. Flight d’in Abuja za su bi, idan sun sauk’a a Abujan Aaima zata wuce makaranta ita kuma Mommy su wuce tare da Dad… BAYAN WATA D’AYA! (After a month!!). Da gudu Jalila ta fito daga d’akin Umma.. Bata kai ga k’arasawa band’akin da ta fito na niyyar zuwa ba! Ta hau kwarara aman da ya taho mata babu shiri a nan bakin rijiyarsu wajen wanke wanke!. Da sauri Mama ta fito daga d’aki jin mutum yana amai Dai dai nan itama Umma ta fito da waya kare a kunnenta tana cewa “Haba Zainab! tafiyar taku ba sai gobe ba? Kiyi sauri kizo muje mu kaita asibitin mu dawo a san abunyi. Kinga yanzun ma fa tana sa ruwa a bakinta kinganta ta fito ta hau amai! Gara a yita a gama dan ni wallahi jikina ya na bani c.....” Ganin Mama ne ya sanya ta had’iye ragowar maganar tata. Ita kam Mama ta Jalila ma takeyi, dan haka tayi saurin k’arasawa inda take ta hau shafa mata baya tana yi mata sannu…. Dama fa ita kwana biyu ta d’an ga wasu changes a tattare da Jalilan Kuma tana lura da yadda Umman ta hanata zaman tsakar gida kwata kwata! Maybe ko dan ta lura da kallon kurillar da take yiwa Jalilan ne? Oho! Da kyar Jalila ta samu ta amayar da d’an ragowar ruwan da yake a cikin ta sannnan ta d’ago tana mayar da numfashi Dai dai nan Umma ta k’araso wajen nasu tana hararar Mama.. Da mamaki Maman take k’arewa Jalilan kallo!..Tayi wani haske na ban mamaki Bakinta sun yi pink sosai! Sannan k’irjinta yayi mugun cika! A hankali Mama da taji k’irjinta ya buga da k’arfi ta lumshe idanuwanta tace “Innalillahi wa innailaihirrajiun” Kafin ta bud’e su ta zubasu a kan Jalilan wadda itama ta kafeta da nata idanun… A hankali Maman tace mata “Sannu, me yake damunki?” Jalila ancikin wata d’ayan nan ba k’aramin sanyi tayi ba, yanayinta ma gaba d’aya ya sauya kamar ba Jalila ba.. Ta bud’e baki za tayi magana kenan Umma tace “Ina ruwan ki!? Sannan da kike wani salati shin aljana kika gani ko me? Kinga! Maryam!! wallahi ki fita a harkaata ni da y’ay’ana.. Ina jin ku jiya ke da Bilkisu kuna munafurcin Ja’afar Bayan ke Huda ta fi sati bata a gidannan Allah kad’ai ya san inda ta tafi wannan karon!! Ki fita a idona tun muna sheda juna wallahi….” Tana ga fad’in haka ta jaa hannun Jalilan fuuuu suka shige d’aki. Mama kam kasa motsi tayi a wajen…duk kalar tarin rashin d’aa’ar da Jalila ke zuba mata hakan bai hanata jin tsananin tausayinta ba! Tabbas idan idanuwanta sun gane mata daidai to d’anyen ciki ta hango a jikin Jalila! Bayan yadda ilahirin jikinta ya nuna Aman da ta gama yi yanzu mai mugun k’arni ya sake tabbatar mata…. Salati kawai take yi tana sake nanatawa a cikin zuciyarta… Ta ma kasa d’aga k’afafuwanta ta bar wajen! Da kyar ta samu ta d’an motsa ta jawo ruwa a rijiya ta d’auraye wajen daga nan ta sake luluwa duniyar tunani….. A haka su Ummu suka shigo suka sameta. Sai da su Sakina suka yi hugging d’inta tukunna tayi firgigit ta dawo daga duniyar tunanin data lulu. Ummun ce ta d’an k’ura mata ido sanann tace “Tunanin me kike yi haka?” Wata nannauyar Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin tace “Ba komai” Daga nan suka d’unguma suka yi d’aki. Ba kalar tambayar da Ummu bata yi mata ba amman tace mata “ba komai” kawai! Saboda hasashen alkhairi ake so a yayata, na sharri kuwa ba a fad’i! Harshe na da kaifi!. Ganin tak’i fad’a ya sanya Ummu kawai ta kyaleta dan ta san da tanaso ta sani to da tuni ta fad’a matan.. Shiyasa bata sake yi mata maganar ba ta sako wani zancen ta hanyar cewa “Mama anata shiri.. Gobe da sassafe duk zamu wuce. Dan Allah ki zo kema mu tafi mana Kin san In babu ke ba zan ji dad’in bikin ba.” Murmushi Maman tayi kafin tace “Bilkisu ke kad’ai fa kike ta gayyatata! Jiya ina ji Zainab da Sadiya suna yada min magana bayan kin wuce.. A haka kikeso In kwashi k’afa in tafi bikin y’arta har Kaduna? Besides kin san ba ishashshiyar lafiya gare ni ba those days kar inje su yi mini wani abun itama Hajiya ta d’aura da nata inje jinina ya hau!. Dan Allah na rok’eki da girman Allah ku barmu a nan Ai naji Baaba Talatu ma tace ‘In an d’aukota daga Kaduna a nan gidan Kaka za a fara sauk’a saboda y’an tsofaffin da basu je su Kadunan ba! Bayan an d’auke su sai a wuce gidanta’. Nayi miki alk’awarin k’arfe takwas zan shirya ga anko na nan ma na wunin kai amarya an d’inko…duk inda takwas da rabi tayi ina gidan Kaka kuna zuwa sai mu wuce tare gaba d’aya. Banda abinki ma, In dai ke da Sakina kunje ai kamar munje ne ko?” Ta k’arashe maganar da d’an murmushi a kan fuskarta. Murmushi Ummun itama tayi. Ba dan ransu ya so ba haka suka hak’ura akabi tsarin yadda Maman tace… Sakina itama daa cewa tayi ba zata je ba Sai da Mama ta lallab’a ta tukunna ta yarda zata je d’in. Kamar minti talatin da yin wayar Umma da Anty Zainab sai gata nan! Tana shiga d’akin Umma tace “Yauwa Zainab! Na gode da kika bani lokacinki, mu je ko?” Tayi maganar tana k’ok’arin tashin Jalila wadda tayi bacci. Dakatar da ita Anty Zainab d’in tayi ta hanyar cewa “Tsaya tukunna Yanzun nan Baban Khadija ya kira yanata faman masifa wai danginshi suna chan sun fara mitar ya uwar amarya har yanzu bata k’arasoba! Yanzu haka da nake yi miki maganar nan drivern da akayi shata zai kaini Kaduna yana bakin k’ofar gidan Kaka yana jira!. Yace ba zai you ince sai gobe zan je ba! Dole in tafi a yau… So kiyi hak’uri ba zan iya rakaki asibiti ba gaskiya Amman ga wannan” Tayi maganar tana zaro pt a jakaar ta, sannan ta ci gaba “Yanzun nan na tsaya na siya na taho dashi.. Scanning ne kawai ba zai nuna ba! Amman ciki in dai akwai shi ko na kwana biyar ne to zamu gani. Tashe ta yanzun nan ta gwada mu gani.” A hankali Umma ta sauk’e ajiyar zuciya sanann ta k’araso ta tada Jalila. Dalla dalla Anty Zainab ta yiwa Jalila bayanin yadda zata yi amfani da abun sannan ta d’aura da cewa “In babu za muga layi d’aya In kuma akwai za muga layi biyu” Karb’a tayi ta fita zuwa band’aki! Kamar minti biyar haka sai gata ta dawo.. Anty Zainab ta mik’awa, cikin rawar jiki Umma ma ta taso tazo ta hau lek’awa… A tare suka saka salati kafin Umma ta zauna dab’ass!!! A k’asa ta d’aura hannu a ka ta fashe da kuka!. Da sauri Anty Zainab ta tsugunna ta shiga lallashinta… Ita kam Jalila tunda ta shigo ta mik’a musu suka karb’a ta wuce kan gado ta zauna ta rafka uban tagumi! So take tayi kuka amman ta kasa… Wani irin tuk’uk’i ne yake taso mata daga k’asan zuciyarta! Inda ace zata ga Auwal yanzu wallahi da sai ta kasheshi! Ba abunda yake b’ata mata rai irin yadda ya dinga muamala da ita a wulakance! Kamar ma irin kyamarta d’innan yake yi sai kace an yi mishi dole!. Da kuma yadda ya fito k’iri k’iri ya zazzage ta ya gurza mata rashin mutunci!!! Taya zata haifi cikin nan?? Ta san ko sama da k’asa zasu hadu Auwal ba zai tab’a accepting cikin ba! Ace ma ya karb’a yayi accepting….shikenan ta zama bazawarar k’arfi da yaji kenan?? Dan ita dai ba zata zubar da ciki ba! ‘Tana tuna wani lokaci…akwai wata a ajinsu… Ta tab’a yin ciki! Malamin da yayi mata ya kwasheta zuwa wani asibiti dan basaso makarantar ta sani da kuma iyayen ita Yarinyar. Haka nan aka zo garin cire ciki Yarinyar ta mutu!. Sannan Akwai wata ma a bayan layin su Itama b’arin ciki kawai tayi ta mutu…..’ Wata zuciyarce tace mata “ba gara to kema ki mutun ba! A haka ma tun baki haihu ba kina tunanin ta yaya Arshaad zai soki Ballantana yanzu idan kika haihu ko kallon ki ba zai yi ba.“ Tunda Jalila take a rayuwarta bata tab’a jin tashin hankali irin na wanann rana ba! Ji take inama ace ba a haliccetaba Banda wani irin huci da ajiyar zuciya ba abunda take yi… Chan!!! Kamar an tsikareta, da mugun gudu suka ga ta mik’e tayi waje dan haka suma suka tashi suka rufa mata baya. Da kyar bayan sun fita suka jiyo motsinta a kitchen dan kafin su fito har ta b’ace musu kamar wata aljana. Da gudu kamar mahaukata haka suka nufi kitchen d’in! Tun kafin su k’arasa warin d’an kalanzir d’in da suke kunna icce da shi ya bakwanci hancinansu… Suna shiga suka ganta tana k’ok’arin kunna ashana tana wani irin kuka zata had’iye zuciyarta! Ga jikinta sharkaf!! Ta kwarara kalanzir ta koina. Umma kasa k’arasawa wajen tayi… Ba abunda take jin tsoro sai ‘Kar taje tana matsawa Jalilan kuma ta kunna ashanar taje wutar ta tashi da ita!’. Anty Zainab ce tayi k’ok’arin k’arasawa ta gudu ta kwace ashanar ta jefar sanann ta d’auketa da mari!!! A take ta durk’ushe a wajen tana wani irin kuka abun tausayi. Sai a lokacin Umma ta samu ta iya matsawa kusa dasu. Tana zuwa tasa hannu ta d’ago ta ta rungumeta a jikinta tana shafa bayanta tana lallashinta. Da kyar suka samu tayi shiru. A hankali Umma ta d’ago fuskarta tana shafawa, tace “Ki kwantar da hankalinki ki nutsu ki daina kuka ki bani hankalinki mu nemo mafita! Sannan dan Allah kar ki sake yunk’urin kashe kanki Jalila Ni Sadiya na yi miki alk’awarin ba zaki wulak’antata sanann zan bi miki hakkinki za kiyi dariya za kiyi farin ciki in shaa Allah Amman fa sai kin nutsu, sannan sai kina raye tukunna za kici ribar bak’in cikin nan da kike ciki a yanzu! Kin ji ko?”. A hankali ta d’aga mata kai tana sauk’e wasu tagwayen ajiyar zuciya. Nisawa Umma tayi kafin tace mata “Jalila ko da wasa bai tab’a gaya miki sunan unguwarsu ba?” Shiruuu, ta d’anyi kamar tana tunani…fuskarta tayi mugun kumbura idanunwanta sun k’ank’ance sun yi jazir! A hankali tace “A jikin duk motocin da yake amfani da su Ina ganin ‘MT’ a sak’ale a jikin glass d’in gaban motar tashi Amman turarene irin wanda ake sawa a d’aki ko band’aki ko office dan k’amshi yake fitarwa na tab’a tab’ata ma hannunna ya kwana yana k’amshi. Sannan na tab’a ganin wasu takardu a motar tashi shima an yi rubutun ‘MT’ Babba sosai! Sai kuma wasu bayanai a k’asa a cikin envelope mai kyau irin mai shara sharan nan. Inaga ko yana da alak’a da company d’in ne…watak’ilan in mukaje ‘MT’ d’in mu sameshi a chan.” Ajiyar zuciya Umma ta sauk’e kafin ta juya wajen Anty Zainab tace “Kiyi tafiyarki kawai Zainab Kar yayi ta jiran ki! Zan dinga gaya miki halin da ake ciki ta waya.. Bara mu tafi MT ni da Jalilan.” Ajiyar zuciya Anty Zainab ta sauk’e kafin tace “Kar ki bari ya raina muku hankali! Ku bud’e mishi wuta sosai!! Jalila kar ki bari ya ga lagonki ki daina wannan kukan. Sannan kar ki k’ara attempting abunda kika so kiyi yanzu Komai yayi safi maganinshi Allah kin ji ko?” A hankali Jalilan ta d’aga mata kai. Shafa kanta tayi tana d’an murmushi tukunna ta yi ma Umma sallama ta wuce. Tana fita Umma ta kamo hannun Jalila suka fito a kitchen d’in. Sai da ta dallawa k’ofar d’akin Mama harara a ranta tace “Munafukai na san sarai kuna jin mu.” Tukunna suka shige d’aki…. Babu abunda yafi bawa Jalila mamaki irin yadda taga Umma ta had’e mata kayanta kakaff!! Hatta inne wears! Gashi Umman tace mata “Kar ta kuskura tace komai Kawo yanzu har zuwa suje wajen Auwal a gama magana kar tace komai! Ta bar mata komai a hannunta.” Sai da ta had’a Ghana most go uku manya!! Tukunna ta fice taje tayi wanka ta dawo d’akin. Tana gama shiryawa ana kiran azahar, dan haka ta cewa Jalila “ta taso su tafi! Kar su makara ya tashi a office d’in.” Umman ce tayi jigilar kayan ta fitar ta tsare musu adaidaita sahu suka kama hanyar Mai Turare & co. A bakin tangamemen had’add’en company d’in mai adaidaitan ya sauk’e su. “Hmm…yana aiki a nan ai dole yayi ta wasa da kud’i yana yiwa mutane rashin mutunci.” Umma ta fad’i hakan a ranta bayan ta gana k’arewa k’ererren ginin kallo. Kayan su suka kwasa sannan suka sallami mai adedeta sahun suka nufi bakin gate d’in shiga… Suna zuwa wani soja a cikin masu gadin ya fito ya tsaresu yana yi musu kallon tara saura kwata kafin yace “Where to? Maam!”. Sai da ya sake maimaita tambayar tukunna tace “Muna son ganin Auwal.” Da mamaki yake sake k’are musu kallo dasu da kayansu kafin yace “Sir Auwal? Mai Turare?”. Da mamaki Umma ta d’an juya ya kalli Jalila da sauri sai kuma ta juyo gareshi tace “Yes yes shi.” Dariya sojan yayi kafin cikin gurb’atacciyar Hausar shi yace “Bar nan wajen! Bana son raina.” Yana gama fad’in haka ya juya Sai a lokacin Jalila tace “sir” Yana juyowa ta mik’a mishi wayarta. Kallonta yayi kafin yasa hannu ya karb’i wayar Da mamaki yake kallonta yake kallon hoton da suka d’auka ita da Auwal a cikin mota! Yafi minti d’aya a tsaye yana kallonta da hoton Daga k’arshe ya sauk’e ajiyar zuciya yace “ok” ya mik’a mata wayarta ya juya yayi ciiki… Kallon hoton take yi a hankali tana shafa fuskar wayar tana tuna lokacin da ta d’auki hoton… Lokacin zuwan sa na biyu ne, tanata y’an hotunanta Ita d’aya shi kuma yana driving, ba tare da ya sani ba ta d’an karkato ta d’auke su. Gashi nan ya fito tarr! Amman iya gefen fuskarshi sai dai duk wanda ya sanshi yana gani zai san shin d’in ne…. “Jalila kar fa ki fara son Yaron nan! Dan in dai kina sonshi to ba zaki iya abunda na shirya ba. Ki daina kallonshi ki goge hotonnan tunda yanzu na san ya gama aiki.” Muryar Umma ta katse mata tunani. Murmushi kawai tayi ta maida wayar lock ta rik’e a hannunta. A chan office kuwa! Ana gayawa Auwal wata na nemanshi a waje yace “Ace musu aiki yake yi!” Shi bai ma kawo Jalila bace ba yayi tunanin a cikin tarin y’an matanshine wata ta boyisa har office, dan sun saba, sai dai kuma yayi mamakin yadda bata shigo har office d’in nashi ba Instead Ta tsaya a gate!…. Kamar bayan minti goma sai ga mai gadin ya sake dawowa. Yana zuwa yace matar da take tare da Yarinyar tace ace mishi “Dangin Mamansa ne suka zo daga k’auye!” “Dangin Adama?” Suka ji muryar Granpa wanda ya shigo zagaye yanzu a bayansu!!!! Sai da Auwal yaga wani duhu na y’an sakanni… Tukunna ya mik’e tsaye ya gaida Granpa cikin girmamawa. Bai amsa ba sai tambayar d’azu da ya sake jeho mishi!!. A hankali Auwal ya goge wata zufa da ta karyo mishi a goshi sannan yace “Eh, I think so, amman bb ba bamu yi maganar wasu za suzo da ita ba!”. Ajiyar zuciya Granpa ya sauk’e kafin yace “I’m leaving, kazo muje gida sai ka kaisu wajenta! Su yi abunda ya kawosu su wuce.. Make sure basu dad’e ba ka san bana son kwashe kwashe!.” Wani yawu mai mugun d’aci da tauri Auwal ya had’iye kafin yace “Ok Granpa.” Sannan ya bi bayanshi suka fice tare a office d’in hankalinshi a masifar tashe!! Tabbas ya san ba y’an uwan Mom bane suka zo! Ummi ita kad’ai ce cousin d’inta tunda mata biyu kacal kakarsu ta haifa! Da maaman Ummi da Maman Mom Su kuma suka haifi mata d’aya d’aya Ummi da Mom. Sai dai In ko relatives d’in kakar tasu, amman ya san Mom ba huld’a take yi da su ba dan tun tana y’ar k’ank’anuwarta ta kwaso kayanta ta dawo wajen Ummi Gramma ta had’asu ta renesu tare.. Sannan har gobe sai anyi da gaske tukunna take zuwa k’auye wajen Mahaifiyarta ta d’anyi kwana biyu ta dubota ta dawo sam bata son k’auye Sannan Maman nata irin matan nan ne masu fad’in gaskiya da tsananin imani acewarta kenan (mom d’in) D’an mistake kad’an Idan tayi nan zata had’u da fushinta! Hakan ya sanya da taga tafiyar su ba zata zo d’aya ba sannan ita kuma (Mahaifiyar tata) ta k’i zaman birni, ta ajjiye ta a k’auyen ta siya mata gida take tura mata kud’i duk wata, waya ma suna yi amman ba sosai ba. Zuwa kuwa sai tafi shekara bata lek’a ta ba…… Yana wannan tunanin suka k’arasa wajen da suka yi parking motocinsu! Granpa ne ya juyo ya cewa mai gadin da yake tare dasu yana yi musu rakiya “Ina bak’in??” Sai da sojan ya d’an rissina tukunna yace “Suna waje bara inje In shigo da su.” “Okay hurry” Shine abunda Granpa yace yana mai gyara tsayuwar shi a jikin motar. Wasu zufa ne suke tsatsafowa Auwal ta kowacce b’ular gashin dake jikinshi… Da ace Granpa zai lura dashi da kyau to da tabbas a tashi d’aya zai karanto tsananin tashin hankali tsoro da rashin gaskiyar da suke tattare da shi!. Tabbas ya san kashin shi ya bushe yau!! Saboda bashi da tantama wata a cikin y’an matan shi ce ta zo! Duba kuma da irin yanayin halayyarshi tabbas!! Ya san ba alkhairi ne ya kawota ba…. Wata idea ce ta fad’o mishi dan haka da sauri yasa hannu a aljihu ya zaro wayarshi ya shiga message…. Yana gama sending message d’in dai dai su Umma suna k’arasowa wajen tare da wasu masu gadi da suka tayasu d’ibar kayansu. Da mamaki yake kallonsu especially Jalila wadda yaga ta chanza! Itan ma shi take kallo ido cikin ido Tana mamakin yadda ya nutsu a gaban wannan tsohon, kamar ba shin ba. Umma ce ta gaida Granpa wanda taga yana yi musu kallon k’urilla!. Ba tare da ya amsa ba ya cewa Auwal “Did you recognize them?” Sai da ya d’an russunar da kai tukunna yace “No Granpa.” “Call Adama” Granpa ya bashi umarni. Wani sanyi Auwal yaji ya na ratsashi a hankali yace “Ok” kafin ya danna kiran Mom. Ya san ta d’auka amman bai saka wayar a handsfree ba Sai kawai yayi shiru chaan kuma ya kashe! Ya bada kamar minti d’aya dan ta samu ta karanta sak’on nashi sannan ya sake kiranta. A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya ya kalli Granpa yana d’an murmushi yace “Sai yanzu wayar ta shiga inaga ba network ne.” “Umm” kawai Granpa wanda ya fara gajiya da tsauwar yace mishi. Tana d’auka yasa a handsfree a hankali ya gaisheta kafin yace “Ga wasu bak’i nan sunzo wai daga wajen Innaa Ta san da zuwan su?”. Tun kafin yayi shiru tace “Eh! Sun yi chattn da Innar ta gaya mata zuwan su Yarinyar distant relative d’in Innar ce, so za a yi mata aure suna buk’atar kayan d’aki Shine zata d’anyi aikace aikace a gidan kafin lokacin aurenta ya isa! Su biya ta ta tafi.” “Ok tam shikenan.” Auwal d’in yace daga haka ya katse kiran ya juya yana kallon Granpa. Lumshe ido kawai Granpa yayi ya bud’e daga nan ya jinjina kai. “Thankyou Granpa “ shine kawai abunda Auwal yace Daganan ya yafito wasu cleaners ya umarcesu dasu kwashi kayan Jalila su kai motarshi sannan ya zaro kud’i a aljihu ya mik’awa Umma yace “gashi tayi kud’in mota ta koma” Kafin ya kalli Jalila yace mata “muje ko” A hankali ta d’an kalli Umma, da ido Umman tayi mata sign d’in ‘ta bishi’ Kamar ta kurma ihu haka taji amman ba yadda ta iya hakanan ta wuce suka nufi motar tashi… Sai a lokacin Granpa ya juya shima driver d’inshi ya bud’e mishi mota ya shiga yaja suka nufi MT estate.. Motar Granpa na gaba tashi na a baya haka suke tafiya har suka isa makeken gate d’in estate d’in Daga shi har Jalila ba wanda ya kalli wani babu kuma wanda yacl cewa wani uffan! Jikin Jalila har rawa yake yi da aka bud’e musu gate d’in suka danna hancin motar cikin aljannar duniyar da idanuwanta suke gani… Kasa hak’ura tayi kawai ta hau jujjuya kai tanata faman kalle kalle! Tana ganin motar gaban su ta nufi gidan da yafi ko wanne girma aka bud’e ta shige.. Su kuma suka nufi d’aya daga cikin jerin gidajen estate d’in suma aka bud’e musu gate suka shige… Bata san lokacin da tace “woow” tana kallo tana murmushi ba! Tsakin da Auwal ya jaa ne ya d’an dawo da ita hankalinta! A hankali ta d’an muskuta ta gyara zaman ta. Har suka gama ya bud’e motar ya fita bata sake yin motsi ko tace komai ba. Ganin ya fita ne ya sanya itama ta bud’e motar ta fito ta bi bayanshi a ranta tana cewa “Aljannar duniya! Ma shaa Allah.. Wai tab!! Dukiya tana inda take.” K’ofar da taga ya shiga nan itama ta bi ta shige.. A tsaye ta ganshi da wata mata fara y’ar kyakkyawa mai matsakaicin jiki da tsayi suna magana… Tana shigowa duk suka jiyo suna kallonta! A hankali ta tako ta zo inda suke itama ta tsaya: Runtse ido Auwal yayi da mugun k’arfi! Kafin ya juyo inda take tsaye ya d’auke ta da wani mahaukacin marin da saida ya kaita ga kaiwa k’asa!! Bai damu da yadda yaga numfashin ta yana shirin d’aukewa ba! Ya fara k’ok’arin kwance belt d’in wandon jikinshi… Ko takan Mom wadda take ta k’ok’arin tsaidashi bai bi ba Haka ya ture ta gefe ya hau zulawa Jalila belt d’in da ya samu nasarar zarowa daga k’ugunsa! Sai da yayi mata uku tukunna Mom ta samu ta tureshi gefe da kyar!!! Cikin fad’a tace “Baka da hankali? baka jin yadda take kurma uban ihu sai wani yaji ya shigo?” In banda huci ba abunda yake yi, tare da da aikawa Jalila wani k’ask’antccen kallo wanda yake cike da tsana! Dai dai nan Ummi ta shigo. Kallonsu take tana mamakin yadda Auwal yake tsaye da belt a hannu yana ta faman huci, ga kuma Yarinya a kwance a k’asa tanata faman kuka!! Wanda ta tabbatar ihun ta take jiyowa tun a compound. A hankali Jalila ta fara k’ok’arin tashi… Hannu Ummi wadda ta k’araso yanzu ta saka ta d’ago ta ba tare da ta kalletaba tace musu “Lafiya? Mai ya faru?” Tayi maganar tana kallon Mom. Mom ta bud’e baki za tayi magana kenan Jalila wadda ta k’arasa inda take ta d’auketa da mari!!! Basu gama fita daga wannan shock d’in ba kawai suka ga ta wage baki ta fara kwala kiran “Granpa” da mugun k’arfi!!!!. “Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”shine abunda Ummi ta hau maimaitawa kafin a gigice tace “Adama wacce mahaukaciyar Yarinya ce wanna?? Meye haka take yi? Ku yi mini magana mana!! Ke yanzu tsabar rashin d’a’a wannan bata haifeki ba?!” Ummi duk tana maganar ne cikin tsananin tsoro da firgice dan yadda Jalila take kiran Granpa tabbas in dai wani ya zo wucewa ta gefen gidan sai ya jiyota ta!! Gashi estate d’in tsit!! So definitely muryar ta zai iya fita koina ma. Cikin tsananin tashin hankali mamaki da firgici da tsoro Auwal ya k’arasa inda take ya mata wata wawuyar shak’a!! Ba yadda su Ummi basu yi ba amman suka kasa kwatar ta a hannunshi… Ita kanta Jalila hannunta na a kan nashi da niyyar kwatar kanta amman ta kasa b’amb’are hannun nashi saboda ba k’aramin ruk’o ya yiwa wuyan nata ba!. Ganin yana shirin kaita lahira ne ya sanya ta tak’ark’are ta sa dukkannin ragowar k’arfinta ta d’aga k’afarta guda d’aya ta daki tsakiyan k’afafunsa da mugun k’arfi!! A rikice ya cikata ya durk’usa a wajen yana jin azabar da bai tab’a jin kwatakwacinta ba!. Ita kuma ta durk’ushe a wajen ta hau tarin wahala… A tsorace Ummi tace “Adama ku yi mini bayani dan Allah Ina kuka samo wannan y’ar dabar??” Mik’ewa Jalila tayi tana d’an tari kad’an kad’an tace “Y’ar daba ko? Ai gwara ni y’ar daba ce kuma a kan gaskiya ta sannan a wajen kwatar hakkina nake dabancin! D’anku fa? Shi baku ga abunda yayi mini ba? Baya ga dabancin daya gama nunawa a nan kunsan me yayi min? kun san ya alak’a ta take da shi???” A hankali Mom ta lumshe idanunta kafin ta bud’e su ta d’aura akan Auwal wanda ya mik’e yanzun nan tace “Auwal plss tell me you did not!!!” Ta fad’i hakan wani hawayen takaici yana zubo mata daga ido daya. A hankali ta d’an matsa gabanshi ta tsaya ta sake cewa “Dan Allah Of all people Auwal kar ka ce mini akwai wata mummunar alak’a tsakaninka da wannan Yarinyar!.” Murmushi Jalila tayi kafin tace “Tab!! Hajiya Adama ai kuwa ki tanadi drip mota mota dan na san hawayenki sai sun k’are tass kin buk’aci ruwa a wannan jikin naki! Bari kiji in gaya miki bayan mummunar alak’ar dake a tsakaninmu har da jika ko jikar ki nake k’unshe da a wannan cikin nawa da kike gani!” Tayi maganar tana shafa cikin. A zabure gaba d’ayansu suka juyo suna kallonta har Auwal! Kamar zaki haka ya sake fincikota ta matso daff dashi kafin yace “K’arya kike yi wallahi!! K’arya kike yi ki samu ciki da ni bayan magungunan da na baki kike sha kullum da safe for good 3 days!” Tunkud’e shi tayi cikin had’e fuska tace “Auwal in banda kai dak’iki ne! Taya kake tunanin zan ci ko in sha abun da ya fito daga hannunka bayan abunda ka yi mini a waennan kwanaki, ba tare da na san ingancin su ba?? Lura ne baka yi ba amman ko abinci ko ruwa idan ka kawo sai na tabbatar da kaci na gani a gaban idona tukunna nake ci nima… Saboda haka Duk wasu magungunan da kake tunanin ka bani fakar idonka nake yi in b’oye a k’asan pillow sannan inyi kamar nasa a bakina Kana fita nake yin flushing d’insu a Masai! Dan haka In Akwai wadda zakace ba zata yi ciki ba to Masai ce! Amman ba dai ni Jalila bint Usman ba!!!” Dafe kai kawai Auwal yayi ya lumshe idanuwanshi! Wani kalar sarawa yake ji kanshi yanayi bana wasa ba! Shi? Jininshi? Da na Jalila? Inaaaa, ba zai yiu ba wallahi!!! Yana cikin wannan tunanin yaji tace “Idan kuma baku yarda ba Kuna iya zuwa muje akwai wani test da akeyi wani abu ‘NA’ haka dai.. Na san ku kun sanshi Sai muje ayi a tabbatar muku amman kafin nan inaso ku nanamin d’akina in d’an shiga In huta in yi wanka! Dan gaba d’aya ilahirin jikina ciwo suke yi, sam! Ban saba da duka ba… Sannan a had’o min abinci mai rai da lafiya dan....” A fusace taga Auwal ya k’araso inda take, cikin tsananin b’acin rai yace “Kin san Allah? In kika kaini bango zan kasheki In kashe banza wallahi!! Banza dak’ik’iyar Yarinya!! Bari kiji in gaya miki ko taku d’aya ba zaki sake yi forward ciki gidan nan ba sai dai backward!! Sannan cikin nan yanzun nan za aje a zubar da shi! Ko kinaso ko bakya so wallahi!! Daga nan ko suna na kika sake kira by mistake ma, sai na datse miki harshe.” Wata dariyar rainin wayo ta saka wanda hakan ba k’aramin sake k’ular da Auwal yayi ba. Sai da ta d’an tsagaita sannan tace “To shikenan! Naji ba zan shigar muku gida ba amma inaso ka sani Billahilazim Wallahi Tallahi! Na fita daga nan direct gidan da naga wannann tsohon wanda naga kana mugun jin tsoro ya shiga nan!! Nima zan nufa Kuma idan naje sai na fad’a mishi komai!! Sannan ince ayi test da jininka dana d’an da yake cikina aga idan k’arya nake yi” Tana gama fadin haka ta juya zata fita. Da sauri Ummi ta ruk’o hannunta… Fincike hannun nata tayi kafin tace “Ai ke kad’ai ce naga alamar kina buk’atar sulhu amman da shi da uwarsa sam basa buk’ata! Dan haka daga nan gidan Granpa na nufa..” A hankali taji Mom tace “Tsaya” Da sauri Auwal ya juyo yace “Mom! Wannan Yarinyar shed’an ce Ki barni da ita i can handle her wallahi ba zata.....” Cikin katseshi Mom tace “I think you have done enough Auwal!! Zaka barni in gyara kuskurenka? Ko kuma in barka kaci gaba da lalata rayuwarka??” A hankali Ummi tace “Wuce kaje kawai Auwal za mu san abun yi kaji ko?” Ji yake kamar ya rufe Jalila da duka har sai yaga bata numfashi tukunna ya barta. A hankali yaji Ummi ta sake cewa “Kaje kawai, kaji?” Sai da ya sauk’e wata k’akk’arfar ajiyar zuciya tukunna ya dallawa Jalila wadda ta tsareshi da manyan idanuwanta harara! Ya saka kai fuu!! Ya fice daga gidan ko belt d’inshi bai tsaya d’auka ba. Tab’e baki kawai tayi ta d’auke kai “Muje in kai ki d’akinki” Shine abunda Mom tace mata ta juya tayi gaba. A k’asa ta nuna mata guess room amman Jalila furr tace “wallahi ba zata zauna a k’asa ba! Ya za ai tana ganin gida mai bene har biyu amman a ajjiye ta a k’asa?” Ba yadda Mom ta iya haka tasa masu aiki suka kai mata kayanta d’akin sama na bak’i! A chan gefen side d’in Auwal. Sannan suka gyara suka goge aka wanke band’akin. K’iri k’iri tana zaune Mom ta sanya cook tayi mata Girki Bata ce musu ba zata ci ba sai da cook d’in ta kawo ta ajjiye sannan tace “Allankatafir ba zata ci girkin kafira ba! Sai dai Mom ta dafa mata da kanta… Cikin tsananin b’acin rai Ummi wadda take tolerating d’inta tun d’azu da kyar tace “Wannan ne kuma baki Isa ba wallahi sai dai ki kwana da yunwa!” Jalila ta mik’e kenan zata fara zuba tujara sukaji sallamar Daddy Ganin da tayi su Mom sun maida hankalinsu gaba d’aya a bakin k’ofar ne ya sanya itama ta juya tana kallon wajen. A hankali Mom ta runtse idanuwanta da suka yi jaaa ta bud’e tace “zan yi miki” sannan ta nufi wajenshi. Da mamaki yake kallonsu yana kallon Jalilan dan bai gane ta ba! Kuma kamar y’ar hayaniya ya jiyo suna yi, hakan ya sanya ko gaisuwar Mom bai amsa da kyau ba yace mata “wacece wannan?” Yayi maganar yana kallon Jalila da itama ta nufi wajen su. Da sauri Mom tace “Yarinyar wata distant relative d’in inna ce! akwai y’an aikace aikacen da zata tayani, zuwa k’arshen watannan sai in biyata in sallameta saboda suma suna buk’atar kud’in, aure zata yi so suna buk’atar na siyan kayan d’aki!.” Murmushi Daddy yayi kafin yace “Shine kuma har sai tayi aiki? Ko ba relative d’in Innaa naji kin ce ba?. Kamar nawa ne ta fad’a miki suke buk’ata d’in sai a bayar ai ko? Besides muna da masu aiki enough ai wanne kuma zata yi?”. A hankali tace “Muje ka huta kaci abinci ko? Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya amsa gaisuwar Jalilan sanann ya wuce sama. Babu yadda Daddy bai yi da Mom akan ta maida Jalila ba amman k’iri k’iri ta dinga kaucewa tana kawo mishi wasu silky excuses d’inta.. A gajiye yake shiyasa kawai ya rabu da ita. Ba abunda yafi d’aga mishi hankali sai yadda yaga d’akin Jalilan a sama gefen side d’in Auwal! Da daddare bayan Jalila taci ta sha tayi wanka ta zo kwanciya Ta kira Umma.. Tun daga lokacin da suka rabu ta kwashe komai ta gaya mata sannan tace “Umma in gaya mikii jikan Mai Turare ne Unguwa ce dasu guda! Ina ga shida y’ay’an shi ne da jikokinshi.. Anan gidansu Auwal d’in yake. A bakin gate d’in shiga unguwar tasu an rubuta Mai Turare.” Cike da tsantasr farin ciki Umman tace “To ai hakan yayi dede, kai amman naji dad’i sosai! Yanzu abunda neke so dake shine ‘karki kuskura ki raga musu! Da shi da uwarsa da wannan wadda kika ce aunty d’in nan nasa’ Ina fatan kin fahimci rashin tsoronsu d’in da kika nuna shi ya kwace ki har ya kaiki ga ci gaba da zama a gidan?” Da sauri tace “Tabbas kam hakanne” Ajiyar zuciya Umman ta sauk’e kafin tace “To inaso ki tashi ki tsayawa kanki nima kuma Ina nan Ina tayaki! Sannan duk bayan sati biyu ki saka mishi saiya dinga biyanki kud’in kayan kwalliya da buk’atun yau da kullum. Sannan ki tashi ki tsaya ko yaya za suyi dake ki nuna musu ba zaki tab’a yarda ki zubar da cikin ba! Ni na san yadda zan yi daga k’arshe..” A hankali Jalila tace “Umma to ya za muyi da Baba?” “Kar ki damu! Zan ce masa kin bi Hansai Daman ya san da zancen za tayi tafiya Inta kama ma Kaka zan saka yayi mishi magana Yadda ba zai iya cewa a’a ba Kar ki damu na san me zan yi. Sannan abu na gaba Kar ki damu in shaa Allah zan tsaya miki ki auri Arshaad bi’izinillahi Ta’ala Tunda yanzu dai babu maganar aurenshi da kowa in ba Hudan ba Huda kuwa k’aramin alhaki ce dan karki damu ki bar mini komai a hannuna kinji?” Cike da farin ciki Jalila tace “na gode sosai Ummana” Murmushi Umman tayi suka d’an yi hirara su Jalilan tana ta bata labarin bahon da tayi wanka aciki da gadon da take kai da d’akin da komai… Daga baya suka yi sallama bayan Umman ta gaya mata itama gobe da safe zata wuce Kaduna biki. ..... Washegari da safe sai wajajen goma ta samu ta farka. Sai da tayi wanka tukunna ta fito parlourn k’asa. Kamar masu meeting haka ta tarar da Mammy Ummi da Mom sun had’a kai ko sauk’owarta ba su ji ba! A ranta tace “guda d’aya ta k’aru kenan!” Bata ko kalli inda suke ba ta tako ta zo ta wuce su zuwa dining.. Kamar daga sama taji Mammy tace “Baki iya gaisuwa ba?” Da sauri Mom tace “Ki rabu da ita kawai mana! Bana son rikici da safen nan wallahi.” Cikin b’acin rai Ummi tace “Ai dama na gaya miki!! It’s like kamar fa tsoronta ma take ji! Ni kam ba zan iya zaman ganin abun takaici ba! Sai anjimanku.” Tana gama fad’in haka ta mik’e tayi hanyar fita. Jalila tana ganinta amman tak’i matsawa Ita kuwa Ummi tana zuwa tabi ta kan k’afarta ta wuce “Da sauri ta ruk’o mayafinta Sai kuma ta durk’usa a wajen ta kurma wani uban ihu!!! A razane Mom ta taso.. Mammy kuwa tsaki kawai taja tanajin tsanar Jalila na sake shiga ranta! Mom tana k’arasowa wajen Jalila ta mik’e a fusace tayi hanyar fita. Da sauri tace “tsaya Jalila tsaya dan Allah!” Dan ta san abunda take shirin yi. Juyowa Jalila tayi tana musu wani kallon wulak’anci Da kyar Mom ta samu ta danne abunda take ji yana taso mata ta k’arasa gabanta ta tsaya tace “Kiyi hak’uri Itama kuma zan yi mata magana!! In sha Allah ba zata sake ba.” Ummi ji tayi kamar ta d’aura hannu a kai ta kurma ihu!! Yayinda Mammy take ji kamar tayi super ta shak’o wuyan Jalila. Murmushin renin wayo Jalilan tayi kafin tace “Kinga Adama!!! Ta sake ko kar ta sake wannan duk ba damuwa ta bace ba! Kawai abunda nake buk’ata shine tazo ta durk’usa ta bani hak’uri! In ba haka ba to babu abunda zai hana ni yin abunda nayi niyya!!” Tana fad’an haka ta fara k’ok’arin juyawa.. Ruk’o Jalilan tayi da sauri jikinta na d’an rawa tace “Tsaya zata baki hak’uri!” Sannan ta juya da sauri ta koma wajen Ummi ta kamo hannunta… Tun kafin tace wani abun Ummi tace “Adama baki da hankaline? Hak’urin kike so inje In durk’usa In bata ko me? To bari kiji ‘Ba zan bayar ba!!’ Sai dai duk abunda zai faru ya faru!!” Cikin b’acin rai ta kalli Jalilan tace “Idan baki san hanyar gidan nashi ba kizo muje ni zan rakaki!! K’aramar mara kunya kawai!!” Murmushi kawai Jalila tayi kafin ta d’aga kanta ta kalli agogo tace “Na baku minti uku!!”. Kamar Mom za tayi kuka haka ta fara lallab’a ummi tana rok’on ta Allah Annabi amman furr!!! Ummi tace “ba zata bawa k’ask’antacciyar Yarinya kamar Jalila hak’uri ba!” Mammy ma bayan Ummi ta bi d’ari bisa d’ari!. Ganin ba zasu bata had’in kai cikin sauk’i ba! Ga lokacin da Jalila ta bayar ya cika ya sanya kawai ta koma gefe ta tsaya tace “Duk ku biyun nan ba don ni ba da ban san halinda kuke ciki a yanzu ba! A tunanina ko mahaukaciya na d’auko a bola nace ku bata hak’uri saboda rufin asiri na ni da d’ana to za kuyi. Amman ba komai na gode gwara da Allah ya nunamin wannan ranar!!! Sai dai inaso ku sani Wallahi sai dai ta fashe da kowa! Dan k’afata k’afar Yarinyar nan! Tana gama zayyane bayaninta nima zan zauna In zayyane komai!! Dan ba zai yiu in share shekarun Ina taimakon ku ba yanzu kuma tashi d’aya ni in shiga problem ni kad’ai saboda taurin kanku!” Tana gama fad’in haka ta taka inda Ummi take tace “Gaki ga Jalila nan! In kinga dama ki bata hak’uri In kuma kin shiryawa fashewar boma bomai a cikin estate d’innan dan Allah kar ki bata hak’uri.” Tana gama fad’in haka ta koma kan kujera ta zauna ta d’aura k’afa d’aya akan d’aya tana girgizawa… Ummi ta jima tana tunani chan! kawai ta k’arasa inda Jalilan take tsaye ta d’an durk’usa kad’an tace “Jalila kiyi hak’uri nayi laifi ba zan k’ara ba” Bata bi ta kan kowa ba tasa kai ta fice da sauri.. Mammy ma tabi bayanta. Mom kuma ta mik’e tayi sama. Jalila kuma ta nufi dining tana tunani a ranta “menene haka sirrin da su Ummi basa so ya tonuu?”. BAYAN KWANA HUD’U!! (After four days!) Kamar yadda Mama tayi alk’awari haka nan yau ta shirya tsaf! Tun k’arfe takwas ta sanya atamfar ankon Khadijah da niyyar zuwa gidan Baaba Talatu. Tun bakwai suka yi waya da Ummu tace mata “sun fito tun tuni” So ta san duk inda tara tayi sun k’araso in shaa Allah. A kitchen ta fito ta samu Hudan tana d’an had’a musu abun kari da su da Ya Ja’afar dan shi ba a tafi da shi ba. Ganin da tayi Huda bata k’arasa nata shirin bane ba ya sanya tace mata “ta wuce taje ta shirya ita zata k’arasa aikin” Already ma Huda ta ida, zuzzubawa ne ya rage da had’a shayi…. “To” kawai Hudan tace daganan ta wuce d’aki. Mama na shirin zama taji kamar kira ya shigo ya yanke dan haka ta zaro wayar daga purse d’inta.. Tana dubawa taga Ummu ce! Ajjiye purse d’in tayi a gefe sannan ta gyara tsayuwarta ta hau kiran Ummun… Tayi mata misscalls sama da bakwai amman bata d’auka ba! Hankalinta ba k’aramin tashi yayi ba dan haka kawai ta yanke shawarar ta kira Shuwa tunda d’azu Ummun tace mata ‘a mota d’aya suke ita da Shuwa da Sumayya da Abba Madu da Ya Jamilu da suka je d’aurin aure a jiyan. Su Baba kuma suna tare da su Baaba Talatu.’ Bugu uku a na hud’un ta d’auka! Bata ce komai ba ta dai d’auka ta kuma kara a kunnenta!! A hankali Mama tace “Ina kwana Hajiya, Bilkisu tana kusa? Inata kiranta bata d’auka.” “Inaga wayar tana a silent ne” Shine abunda Hajiya Shuwa tace, daganan tayi shiru. A Ahankali Mama tace “Tam shikenan” Har zata kashe sai ta sake cewa “sai kun k’araso.. Muma gamu mun shirya yanzu zamu tafi gidan Baaba Talatu mu jira ku a chan.” Cikin yaren shuwa Hajiya Shuwa tace “Ku yi zaman ku kawai ba sai kun zo ba! Maryam Ina cikin farin ciki kar ki ja a b’ata mini rai kokuma a gaya min magana a yau d’innan!! Na gaya miki kar kuzo mana cikin taro da ke da y’arki amman kin k’i yarda ko?? Taurin kan naki da kika saba shi zaki gwada mini ko?” Cikin fad’a sosai taci gaba da cewa “Wallahi idan naga k’afar ki a inda nake ranki in yayi dubu sai ya baci!” Tana gama fad’in haka ta yanke kiran… Wayar Mama tana da volume sosai…dukda Huda ba wani yaren Shuwa take ji sosai ba amma tabbas ta fahimci abunda Hajiya take nufi… A hankali Mama wadda take jin kanta na masifar juyawa da sarawa ta sa hannu ta share hawayen da ya zubo mata! Juyowa tayi da niyyar d’auko kwano a kwando suka had’a ido da Huda wadda take kallon ta tana zubar da hawaye… Wani tausayinta ne ya lullub’e Mama lokaci guda! A b’angaren Hudan ma hakan take. Da sauri Mama ta zo ta giftata ta wuce ta fice daga kitchen d’in Dan kallon fuskar Yarinyar sake narkar mata da zuciya yake yi.. Tana fita itama Hudan ta juya ta bi bayanta. Duhun! Da ta fara gani ne ya sanya ta d’an tsaya ta dafe kanta… A hankali ta fara jin wani irin jiri yana kwasarta kafin daga haka taji jinta da ganinta da k’arfin jikinta sun d’auke lokaci guda ta tafi ta sulale a tsakar gidan ta fadi!! Kamar matacciya!. Da k’arfi Huda tace “Maamaa!!!” Sai kuma ta yi kanta da gudu tana kuka...... Kuka take yi tun k’arfinta tana kiran sunanta amman ko motsi bata yi ba. Ganin hakan yasa ta sake gigicewa ta rikice ta rasa ma ta Ina zata fara! Tana shirin mik’ewa sai ga Ya Ja’afar ya shigo… Da gudu ta k’arasa inda yake tace “Ya Ja’afar napep dan Allah ka nemo napep mu d’auki Mama a kaita asibiti dan Allah Ya Ja’afar..” ta hau rirrik’esa tana mishi magana duk ta gigice.. Kallonta yayi ya kalli inda Maman take. Kamar wanda zai yi abun arzik’i haka ya k’arasa inda Maman take kwance… Dai dai setin fuskarta ya d’an yayyarfa hannunshi (kamar wanda zai kore mata sauro) A hankali ya d’ago ya kalli Huda wadda take kuka kamar ranta zai fita yace “Wannan ai napep ba zata yi aikin komai ba! Sai dai a d’auko makara!! ayi mak’abarta da ita. Kallifa ko uffan bata ce mini ba! Bafa ta motsi.” Cikin kuka Hudan tace Ya Jaafar asibitin dai! Ka nemo mai napep ka taya ni d’aukar ta Zata farfad’o in shaa Allah suma tayi.” Banza yayi da ita ya juya ya nufi kan baranda sannan yace “bara in d’an rintsa In farka sai munje in yi mata sallah a mik’ata!.” Sai a lokacin Huda ta lura da yadda yake tafe yana tangad’i!!! “Na shiga uku yau!” Tace tana wani irin kuka… Ko myafinta bata tsaya d’auka ba ta fita da gudu gidan da yake a jikin nasu dake suna da mota su wai ko zata samu a tayata a taimaka mata su mik’a Maman asibiti. Sai dai kuma tun kafin ta k’arasa ta hango k’atoton padlock mak’ale a k’ofar gate d’in gidan wanda hakan yake nuni da ba kowa ma a gidan kenan!. A rikice ta juya ta koma cikin gidan tana shiga ta tarar Ya Ja’afar har yayi bacci.. K’arar wayarta ta jiyo a d’aki sai a lokacin tunaninta ya bata kawai ta kira Arshaad. Tana shiga ko bi ta kan misscall d’in bata yi ba ta hau kiranshi babu k’akk’autawa….. MT & co. A lokacin Aslam ya je office d’inshi kenan Granpa kuma ya saka shi wani aiki na gaggawa…. Duk ya rikice hakan yasa ko wayarshi bai tsaya d’auta ba ya wuce wajen da ake sarrafa turarurrukan wanda yake nan a gefen building d’in da yake d’auke da offices bayan ya cewa Aslam d’in ya jira shi a office d’in nasa nan da kamar 20 minutes zai dawo… Yana fita ko 1 minutes bai yi da fitar ba wayarshi ta fara k’ara! Aslam, kamar zai bishi da wayar sai kuma yayi tunanin ‘bara kawai ya jira har ya dawo sai ya bi kiran kawai’ Ganin yadda aka jera mishi kusan 20 misscalls a jere ba hutu ne ya sanya ya yanke shawarar kai mishi wayar kawai, dan ya san dole its important!! Yana d’aukar wayar wani kiran yana sake shigowa tare da wani message da alamun yanzu aka turo! “Life support ❤️” Haka yaga sunan b’aro b’ari ya fito a akan screen d’in. Ko ba a gaya mishi ba Ya san Huda ce! A hankali ya lumshe kyawawan idanuwanshi ya bud’e su kafin ya maida wayar kawai ya ajjiye ya koma ya zauna yayi shiruuu…. Ganin tanata kira still babu k’akk’autawa ne ya sanya ya mik’a hannu ya d’auki wayar a karo na biyu Yana d’auka kiran yana tsinkewa dan haka ya samu damar ganin sak’on data turo ta notification bar! “Ya arshaad Mama ta suma ba kowa agidan sai mu biyu ka taimakamin Dan Allah kazo mu kaita asibiti!” Da mugun k’arfi yaji k’irjin shi ya buga! Tsintar kanshi kawai yayi da mik’ewa tsaya ya fice daga office d’in gaba d’aya bayan ya ajjiye wayar a kan tebur. Ko takan wayar Arshaad d’in bai sake bi ba! Ya isa inda motar shi take ya shiga ya bata wuta ya fice daga companyn da gudu… Babu nisa tsakanin company d’in da gandun albasa hakan ya sanya ya samu damar k’arasawa acikin mintuna k’alilan! Yanayin parking ya fito da d’an gudu ya shiga gidan kanshi tsaye… A tsakar gidan ya hango su Hudan tanata k’ok’arin d’aura Mama a bayanta tana kuka amman ta gagara! Tanajin shigowar mutum ta d’ago idanuwanta tana kallonshi… Shima itan yake kallo! Wani sabon kuka ne ta ji ya kufce mata mai k’arfi ba tare da ta shirya ba! Da sauri ya k’arasa inda suke yana kallon ta yana jin yadda k’irjin shi yake bugawa… Da kyar ya iya ce mata “Muje” Sannan ya durk’usa da niyyar d’aukar Mama. Zabura!! Yayi bai san lokacin da yace “Anty Maryam!!!” da d’an k’arfi, ba… Sai kuma ya sago yana kallon Huda wadda take yi mishi kallon mamaki.. Mayar da dubanshi yayi a fuskar Mama yana yi mata kallon kurilla Kana ganinshi ka san a firgice yake!! Cike kuma da mamaki sannan kanshi a d’aure yake. D’agowa ya sake yi ya kalli Huda! Sai kuma ya sake maida idanunsa akan fuskar Mama….. Cikin kuka Hudan tace “Ya Aslam dan Allah mu je kar wani abun ya sake samunta… Wani yawu mai d’aci ya had’iye kafin a hankali still idanuwanshi suna a kan fuskar Maman ya sanya hannu ya d’auketa yayi waje da ita…. Ita ma Hudan kanta a d’an d’aure yake….sakamokon jin yadda ya kira sunan Mama lokaci d’aya kuma har da ‘anty’ wanda ko lokacin da su Jalila suna Yara ta san ba anty suke ce mata ba! Sanann bata tunanin ko Ya Arshaad ta tab’a gayawa sunan Mama balle tayi tunanin ko shine ya fad’awa Aslam d’in!. Bata wannan take ba yanzu ta Lafiyar Mama take dan itace abun dubawa! Dan haka ta kawar da tunanin gefe… Tana ganin sun fita itama da gudu ta koma ta d’au mayafinta ta d’auko y’an kud’ad’en da suke dashi ta zuba a jakar Maman ta d’auko mata purse d’inta data bari a kitchen tasa a cikin jakar ta fito daga gidan Lokacin Aslam har ya saka Maaman a Bayan mota yana gyara mata ruffin mayafinta daya d’an zame kad’an. Ganin ya juya ya shiga mazaunin driver ne ya sanya itama ta bud’e motar ta shiga baya ta zauna ta d’aura kan Mama akan laps d’inta tana shafawa tana kuka.... Basu kaiga k’arasawa asibitin ba taji yace “Assalam alaikom, Abba Ina wuni! Dan Allah duk abunda kake yi ka bari kazo emergency yanzu akth… Ba zan iya bayani a waya ba Dan Allah Abba ka zo Dan Allah.” Shiru taji ya d’an yi kafin ya sake cewa “Ok tam Nagode.” Ita dai Huda mamakin Aslam take yi yadda duk ya rikice Da kuma yadda ya kira sunan Mama! Sannan yanzu taji ya kira wani ‘ABBA’ yace ya samesu a akth! A hankali a chan k’asan zuciyarta tace “Waye ABBA???”. BULAMA ✍️