🕊️ RAINON YARO BOOK ONE Chapter1 ✍️ Hafsat Umar Dangoro (SAFHAT) --- 🌟 KASHI NA FARKO “Rayuwa tana da sirri. Wasu ana haifarsu don su rayu, wasu kuma ana rayuwa da su.” --- ✨ MARUBUCIYA SALWA AFNAN AMATULLAH MARATUS SALIHA BABBAR SAKAYYA DEPRESSION BABANA NE SILA UMMU AMANIH ZUCIYATA BURINA MU, AZZALUMI MECE RAYUWAR? BA MAHAIFIYATA BACE RAYUWAR KASKANCI E.T.C --- 💎 JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION (SADAUKARWA GA: MUJAHID) To Mujahid, jarumi ne cikin duka, wanda da sunansa nake kiran karfi da kwarin gwiwa. Wannan littafin na musamman ne gare ka — kaine farko, kai ne gata. Allah ya kara maka haske da albarka a rayuwa. Ameen. --- 🕊 GODIYA Dukkan godiya da yabo sun tabbata ga Allah (ﷻ), Mahaliccin zuciya da fasaha. Mai bayar da iko da kaifin tunani. Tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (ﷺ), wanda shi ne ginshikin rahama a doron ƙasa. Na gode wa masoyana, masu karatu, abokan shawara, da waɗanda suka bani goyon baya cikin shiru da addu’a. Ku ne hujja akan dalilin da yasa nake rubutu da bege. Ina alfahari da ku. --- 🎨 KIRKIRA Littafin RAINON YARO ƙirƙirarren labari ne. Duk wani suna, masarauta, ko al’amari da ke cikin wannan littafi na soyayya, sirri, da gwagwarmayar zuciya — dukkansu ƙirƙira ne da nufin nishaɗi da ƙarfafa zuciya. Idan ya yi kama da rayuwarka, to ƙaddara ce ta labari, ba da gangan aka yi ba. --- ....._*🌒بسم الله الرحمن الرحيم🌒*_ Wata rana... wata rana da ba zan taɓa mantawa ba. Rana ce da na buɗe ƙofar duniya da hannu guda, na tare bakin wahala da kafada ɗaya, kuma na rungumi jaririya — a lokacin da ban kai shekaru goma sha bakwai ba. Sun ce namiji baya kuka. Amma jiya na kuka. Na yi kuka kamar yaro. Ko da yake... ni yaron ne. Zaune nake a bakin bed din idanuwana a lumshe ,hannayena Kuwa gaba kidaya na Dora kan kunnena na rufe, alamar banason Jin karar da take tashi,gefe guda Kuma jaririne a lullube da zani sai faman ihu yake da alama yana bukatar mahaifiyar sa, tsaki naka na zaune a gefan gadon rai a bace, Jikina Babu kwari nake taka kafata har na isah zuwa Inda jaririn yake, a hankali nasamu guri na zauna a gefan gadon hadi da Mika hannu na dauke ta, kekkewar yarinyar da a kalla bata huce shekara Daya a duniya ba ko wata 6 , abin mamaki ina daukar ta tayi shiru hadi da kama hannunsa ta ruke gam ,juyi nashiga Yi da hannuna alamar wasa can Kuma sai na ce "kash baby yanzu jibi fa kin hanani bacci ,ba kyjin tausayi na ne?" Nayi maganar kamar tababbe batare da sanin Wanda zai bashi amsa ba, mikewa na sakeyi da yarinyar a hannuna na dorata a kan kafadarta nashiga jijjigata alamar rarrashi, tun iana zagaye dakin iana Jin motsinta har bacci mai nauyi ya dauketa, Dan murmushi na saki hadi dacewa "yauwa nima kinga yanzu sai nasamu nayi bacci Kona awa 3 ne" na karasa maganar hadi da karasawa bakin bed din, sun kuyawa nayi a hankula na ajiye ta Sannan nima na kwanta a bayanta, bacci nakeson Yi Amma na kasa ,hakan yasa na Dan rankwafo na zubawa yarinyar ido iana kallonta, haka kurum na tsinci kaina da sakin murmushin na shafa kwantaccen kan yarinyar, a haka har bacci mai nauyi ya daukeni. In the morning 🌄 Misalin karfe' 9 nasafe MJ ya bude ido, lokaci guda ya furgita ganin Wanda yake Kansa , a hankula ya furta "lafiya?" Namijin dake tsaye a gabansa sanye da uniform na bakaken kaya, Wanda a kalla ya bawa MJ kusan shekara 18 a duniya, saurin cewa yayi "Allah ya karamaka lafiya ranka shidade ganinai shiru baka fito ba ,har anzo daukarka Kuma yau idan ba mantawa nayi ba ina da exam" Mika MJ yayi hadi da cewa "uhm wallahi jiyane bansamu bacci ba shiyasa har nakai wannan lokacin ko sallar asba banyi ba ,jiya baby ta dameni da kuka, Allah yaso ma sai 12 Zamu shiga exam din" murmushi wannan mutumin yayi yasake cewa "Allah ya kara Maka lafiya ba daban kada kace nafiye shiga abin da Babu ruwana ba danace wani abu" " uhm inajin ka fadi komai ne" yayi maganar hadi da kafe shi da idanun sa "am nace ranka shi dade da zaka dauki shawarata danace ka Kai baby gidan marayu ko ka mai da ita sauba gidan sarauta, inaganin hakan sai yafi yaro da Kai baza ka iya RAINON BABY ba kaima yanzu baka huce a Raine kaba Sha..... " Saurin dakatar dashi MJ yayi hadi dacewa " Babu mai rabani da 'yata" abin da kawai yace kenan ya mike ya shiga bathroom, shikuwa wannan mutumin da kallo ya bishi, a cikin zuciyarsa Kuma yace "oh yau baga ikon Allah wai 'yarsa" daga haka ya fice daga part din gaba daya . MJ Yana shiga alwala kawai ya dauro yazo ya gabatar da sallah, Sannan ya Yi addu,a sosai kana ya mike, bakin gadon ya karasa ya zauna ,Ananne ya tarar da baby ta farka, sai kalle kalle take, zuba mata ido yayi Yana kallonta itama shi take kallo, "good morning baby" abin da bakinsa kenan ya furta Sannan ya saka hannu ya dauketa , bathroom ya nufa da ita, rigarsa ya tattare ya daure a kugunsa Sannan ya saka hannu ya nade dogon hannunrigar, Sannan ya zame buri da wandon dake jikin ta, ta koma daga ita sai famfas ,zame famfas din yayi ashema har tayi Kashi, ya tsine fuska yayi hadi da sa hannu ya toshe hancinsa wai wari, Ashe bai sani ba ya lakuto Kashin aikuwa ya shafa a hancinsa, da sauri ya tsuguna ya ajiye baby acikin kwamin wankan, yashiga wanke fuskarsa ,a she abin da bai sani ba lokacin da ya ajiye baby a cikin kwamin wankan,ruwa ya taru,aikuwa baby duk ta duru ruwa acikin ta ,a razane ya dago yaganta bata ko motsi ,nan take MJ yasaki kuka ya dakkota, Kai tsaye waje ya nufa Yana fita, masu bashi tsaro sukayi sauri tararsa hadi da bude masa murfin motar, yashiga motar suka shiga ja ,Daya daga cikin sune yayi karfin halin cewa "yanka shidade ina muka nufa" Afusace mj yace "asbiti mana " daga haka MJ ya cigaba da kukansa Yana bubbuga bayan Baby Yana Kiran sunan ta "baby ! Baby!! Baby help me " har suka shigo harabar asbitin MJ bai daina kuka ba, suna tsayawa da motar ma,aikatan asbitin suka karaso sakamakon ganin lambar motar da sukayi ,MJ bai jira an bude masa kofar ba ya bude ya fito da sauri, ya Mika musu ita" da hanzari suka amsheta sukayi ciki da ita, shikuwa MJ tsaya wa yayi yashiga juyi a harabar gurin yakai ya komo yakai ya komo yama rasa mai yake masa, dadi. Misalin karfe 12:30 yaji wayarsa na ruri, Yana dakko wayar a aljihu yaga Ashe lecturer dinsune, shaki yaja ya kashe wayar gaba daya Dan ma kada a damesa , can Kuma sai yaji karamar wayarsa na ruri itama ko kallonta bai ba balle ya dakko yaga ko waye, Daya daga cikin masu gadinsane ya kawo masa wayarsa yace "am ranka shi dade mai martaba Yana magana" da kamar bazai amshi wayar ba can Kuma sai ya karba ya kara a kunnensa, tun kafin yayi magana yaji muryar mai martaba Rai a bace yace "Abee meyake damunka ne? Kasan Kuwa yanzu karfe' nawa kana ina akace baka shiga exam ba" "am uhm am Abba ina asbiti" "asbiti Kuma Abee mai yakai ka asbiti lokacin jarabawa yayi wane abune haka har yafi exam dinka mahimmanci?" "Am am Abba Daman babyce bata da lafiya yanzu ma ko motsi batayi bansani ba ko tamutu ko Tana raye" MJ ya karasa maganar hadi da fashewa da kuka " innalillahi wa inna ilaihirraju un yanzu Abee har yanzu kana tare da wannan yarinyar,wai ni Dan ubanka ina kasamo 'yane?" Abba yayi maganar Rai a bace , batare da MJ yasake cewa komai ba ya katse wayar hadi da hullawa mutumin wayar sa Rai a bace tace "ko Abba na yasake kira kasake bani sai ranka ya baci wallahi Anakin aikin ka" daga haka MJ ya karasa bakin dakin da aka shiga da baby. Na tsugunna a gefen gadon wata tsohuwa domin tai Maka mata , sai ga yarinya — ba girma ne da ita ba, amma kuka nata ya fi ƙarfin zuciyata. Kuka mai sanyi, mai buƙatar kulawa. Kuka da ya fashe min zuciya fiye da buƙatar abinci. > “Kai ne mahaifinta?” Tambayar da ta katse min tunani, daga bakin wata matar asibiti da ke kallona kamar ba dan adam ba ne. Ban ce komai ba. Sai dai na lumshe ido... na ɗago jaririyar, na manna bakinta a kirjina kamar za ta shanye zuciyata. Ni ne mahaifinta. Ko ba na da ƙarfi, ina da ƙauna. Abin da na fadawa ma,aikaciyar asbitin kenan, Mutane za su ce, Ina mahaifiyarta? Ina danginta? Ina kake so ka kai wannan rainon? Zan ce musu: “Na rasa iyayena tun ina ƙarami. Amma bana fatan ita ta rasa ni.” Sunanta Fatima Amma ni ina ce mata baby. Sunana MUJAHID Amma anfi Sanina da MJ . Littafin nan ba wai labari bane kawai — ba soyayya kawai ba — ba tausayi kawai ba... Kai dai karanta ki ji. *Sauba* "Wai yau ni Abee yake kashewa waya?" Sarauniya abida wadda ke gefansa ce TA danyi murmushi tace "ranka shi dade ai ba a banza ba ,tun farko Saida nace kada a tura Danan karatu wata kasar kaki saurarata sabi da kafin kaunar uwarsa a kaina ,ai ga irinta Nan yaro tun Yana Dan shekara 15 har da 'ya andaiji kunya wallahi" "ya Isa haka abida Indai har bazaki fadi alkairi akan Dana ba to ki saurara Kuma insha Allah abin da kike fada akansa bazai zama gaskiya ba" kwafa mai martaba kawai yayi ya mike hadi da cewa "sarauniyar agadas ina miki izini akan ki biyoni muje misra yanzunan" Babu musu ammi ta mike hadi da yin dakinta. sarauniya abuda kallon mai marta ba tayi tace" ranka shidade nikuma Dan bani na haifi MUJAHID ba shine baza a Dani ba kenan" shiru mai martaba yayi can Kuma sai yace "tashi ki shirya mutafi ,amma da sharadi bana son fitina nafada miki" itama mikewa tayi tashiga daki, shikuwa. Mai martaba sarkin garin sauba ci gaba yayi da juyi a a tirakarsa yakai ya dawo ya Kai ya dawo hakadai ya dingayi Yana cigaba da sunbatun sa.... "Yaron nan ba zai iya ba." "Waye shi da zai raini yarinya?" "Ko shi ne ya yi mawa wata ciki har aka haifi baby?" "Wannan jariri ba nasa bane — to ba nashi ba ne... Nawane kenan?" *MJ* Maganganun mutane sun fi ƙonani fiye da rana. Amma wallahi ban damu ba. Saboda kowanne kalmarsu na sa ni ƙara matse Fatima a kirjina. Na tsinci kaina ina kallon fuskarta mai ɗauke da dumin sabuwar haihuwa. Wannan jaririya... wannan ƙaramin numfashi da ke motsa hannuwanta a wuyana... ita ce burina. Ba saboda na haifeta ba. Sai dai saboda... ni na zabi rainonta. “, ka tuna kai yaro ne,” cewar Malam Lawal, Daya daga cikin masu gadina. “, babu tsari, babu uwa, babu uba… yanzu kai kuma kana tare da jaririya?” Tsaki nayi cikin facin Rai n girgiza kai ina kallon jaririya a hannuna, kamar ƙaya ce da zan nutse da ita. Lokaci guda Mujahid yashiga tunani a zuciyar sa kamar wani mai yin mafarki Wata rana na yi mafarki. Na ga Fatima ta girma, tana dariya, tana cewa: “Na gode, dady Na gode da ka zamo mahaifina ba don jini ba — sai don ƙauna.” Na farka da hawaye a idona. Sai na kalli ta — tana bacci, hannunta a hannuna. Na furta da ƙasa da murya: “Wallahi sai na ba ki rayuwa... ko da ni zan rasa tawa.” Ban an kara ba naji muryar malan lawal Yana cemin ranka shidade Zamu iya tafiya gida tunda baby tasamu tafiya?" Batare da nace masa komai ba na mike muka bar harabar asbitin zuwa parking space, mota na shiga idona kur akan baby kamar Wanda za a rabani da ita haka nake kallon kekkewar fuskar ta. A haka har muka karasa gida. **********"" Na sake mafarkin nan yau. A cikin mafarkin, na tsinci kaina ina dariya — ba dariyar wauta ba, sai dai irin wadda ke zo ne idan mutum ya ga abin da yake ƙauna cikin aminci. Wata ƙaramar yarinya ce, mai idanu kamar tabon ruwa, tana ta gudu da ƙafa ba safar kafa ba, tana cewa: "Dady! Dadyna! Ka kama ni, ka kama ni!" Ta durfafi ƙirjina kamar bazata, na ɗauketa, na juyo da ita sama. Sai dariyarta ta cika sararin mafarki — dariya mai dumi, mai tsarki. A wannan mafarkin na ji kalma guda da ba zan taɓa mantawa ba. “Na gode da ka bani duniya... ko da ba kai ka kawo ni ba.” Na farka da hawaye a cikin dare. Na juyo a gadon katifa mai kyau wadda mahaifina sarkin garin sauba yasa aka kirkira domin ni kadai, sai ga Baby — tana barci, tana nannade a bargon mara nauyi. Na matso kusa da ita. Na sanya hannuna a gefen fuskarta. Na daɗe ina kallonta kamar na rasa nutsuwa. “Shin ke ce? Ke kika zo cikin mafarkina?” Amma shiru. Ko mafarki ne kawai? Ko kuwa zuciyata ce ta fara saka min hoton da ba na kallon sa da ido? ** Mutane da yawa suna kallona da tambaya a idonsu. > “mj wace ce wannan?” “Yarinyarka ce?” “Ka samu ciki da mace?” “Ko dai shirme kake yi?” Amma ba zan ce komai ba. Domin bana da amsar da za ta gamsar da su. Sai dai ina da zuciya da ba ta bar ni na kawar da ita ba — Baby. ******* Wata rana wata mata ta tsaya a kofar shagon sayar da burodi, ta kalle ni da Baby a bayana. > Sai ta ce, “Wannan dai ƙaddara ce... ba ’ya ce kawai ba. Wannan zata saka ka zama mutum.” Na kalle ta, amma sai ta wuce kafin in tambaya. Kamar mafarki — kamar kalmarta ta zo daga wata duniya. ** Na ci gaba da rike Baby, fiye da yadda ake rike rai. Wani lokaci ina tambayar zuciyata: 🕊️ RAINON YARO Chapter 2 “Shin me ke tsakanina da ke, Baby? Me ya haɗa rayuwarmu?” Tambayar da nakeyi wa kaina akullum. A kullum da safe, kafin rana ta huda samaniya, na saba kallon fuskar Baby. Kafin na yi addu'a, sai na kalli idanunta — ko da tana barci, kamar tana jin zuciyata. Kullum ina cewa da kaina: “Ina tsoron in rasa ki, fiye da yadda nake tsoron rasa kaina.” After two year ***** Yau na yanke shawara: zan nemi aiki — ko da kuwa aikin gadin tsafta ne a makaranta, ko share titi. Ban danmu da cewar ni Dan sarki bane. Domin Baby tana buƙatar madara, da rigar sanyi, da bandir na diapers. Tun da dai mahaifina sarkin sauba ya ce Indai har zan cigaba da rayuwa da baby babuni Babu shi, Dan haka dole nanemi kudi da karfina domin na ciyar da baby da gumina. *******Na shirya tsaf Na shiga unguwar Attarin Bab Zuweila, cikin ƙanƙanin lokaci na sami masu tambaya: “Kai, wannan yarinyar taka ce?” “Ina uwar ta?” “Ko tsintarta Kai a hanya?” Kullum tambaya ce, ba amsa. Domin babu amsar da ta dace da sirrin da zuciyata ke ɓoye. A haka dai ina tafe da baby a bayana har yamma tayi ban samu aikin Yi ba, Babu yadda na iya haka na koma gida jikina duk ya mutu Babu kwari, Ananne nasamu mahaifiyata da abbana sun zo har sunayi wa masu gadina fada akan meyasa zasu na barina ina fita, basu an karaba suka ganni na shigo a gajiye duk na gala baita GA baby a kwance a bayana. Baki mahaifina ya saka yace "innalillahi wa inna ilaihirraju un Abee !! Batare da nace musu komai ba na shige falon, biyoni sukayi a baya abbana ya dakamin tsawa Yana cewa: “abee,” ya faɗa da ƙwaryar murya mai izza, “ka zo nan.” Mujahid ya janye Baby daga bayansa cikin nutsuwa, ya gyara mata hijabi, sannan ya ce mata: “Tafi ɗaki, Baby. Zan zo nan da mintuna kaɗan.” Ta jinjina kai da ƙaramin murmushi, ta tafi tana jinginar da ƙafarta kamar mara nauyi. ** Sarki ya yi masa kallon da ya saba yi masa tun yana yaro – kallo mai cike da ƙauna, amma kuma ƙa’ida. Na yi shiru tsawon lokaci, saboda ina son na ba ka damar fahimtar rayuwa, tsawan shekara biyu kana tare da wannan yarinyar. Amma yanzu dole na tambaya.” Mujahid ya lumshe ido. “Ina ka samo wannan yarinyar?” Ya yi shiru. “Ba ‘yar gidanmu bace. Ba a ɗaukota daga danginmu ba. Kuma ka fara ɗaukarta kamar ‘yar jini.” Mujahid ya haɗe hannuwansa a ƙirjinsa, yana kallon ƙasa. “Ta rasa gida, abbana.” “Toh akwai orphanage a gari. Akwai gidajen ‘yan uwa. Me yasa ita ce ke ɗaukar hankalinka fiye da sauran?” Shiru ya sake dawowa. Sai daga baya Mujahid ya ce da ɗan murya: “Saboda idan Baby ta kalle ni, ina jin kamar ni ne abin da ta rage dashi. Kuma ita ce ma kawai take tunasar da ni da zuciya.” Sarki ya ɗan daga gira. Idonsa ya rikice kaɗan. “Kana ɓoye min wani abu ne? Ko kuwa ita ce…” Mujahid ya ɗago, cikin sauri: “abba, wallahi ba zan ɓoye maka gaskiya ba, amma yanzu... yanzu ba lokacin bayani bane. Ina roƙonka ka barni in ci gaba da rainonta.” Sarki ya danyi murmushi mai raɗaɗi. “Toh, ka sani, ranar da gaskiya ta bayyana, zata zo da ƙarfi fiye da kowane jiki. Kuma ni, a matsayin sarki, ba zan yarda da kowanne abu da zai ɓata sunan gidan sarauta ba.” Batare da MJ yace komai ba ya mike yace "burina shine na kula da baby Dan Allah ka taimaka kada ka rabani da ruhin da baisan komai ba sai maraici" Yana gama fadar haka ya bar dakin, zuciyarsa kamar ta nitse da nauyi. Yana da burin kare Baby, yana da sirrin da zai iya tarwatsa komai, kuma yana cikin dangi da ba su yarda da “mara jini” a matsayin “ɗa” ba. MJ Yana shiga daki ya zauna a gefan bed yayi shiru, sai Jin baby yayi ajikinsa Tana murmushi Tana masa gwaranci. A hankula ya dago jajayen idanunsa ya soma magana cikin nutsuwa Yana cewa: “Baby, ke ce ruwan da nake ɗora wa a zuciyata. Amma ruwan nan, idan ya zubo a fili… zai iya ƙone ni gaba ɗaya.” Daga haka ya janyo ta jikinsa hadi da lumshe ido . Su Abba Kuwa jiki Babu kwari suka fita daga gidan suka hau mota, zuwa airport. In the night 🌉 A wani dare, ina zaune a gefen Baby tana bacci, sai na ji kamar zuciyata na cika da tambayoyi. Shin me ke faruwa da ni? Shin ina rike wani abu da ba nawa ba? Shin mafarkin da na gani yana nufin wani abu ne? Shin Baby ba yarinyata bace? Ko kuwa ita ce, kuma kawai duniya na kokarin kwace min ita? Na kalli hannunta — ƙarami, mai dumi, da ɗan zafi kadan. Sai na ruƙe shi da lafazin da ya fito daga ranta — ko da bata furta ba: “Ka rike ni, dadyna… ni zan tsaya da kai.” Sai na furta: “Ko wacece ke — ’yata ce a zuciyata. Kuma idan duniya na so ko ba ta so, wannan ba zai canza ba.” Sake rungumota yayi Yana cewa "yanzu kenan yazanyi ni yarone meyasa har yanzu matarnan bazata dawo ba, ai ba haka mukayi da itaba , meyasa zataminn haka har iyayena su soma zargina akan ko nayiwa wata cikine?" Kara gyra kwanciya ta nayi Ina kallonta tana barci, hannunta na kan kirjinta, tana numfashi a hankali kamar furucin wardi. Baby ta yi sanyi, amma zuciyarta bata daina zafi a raina ba. Kullum idan na kalle ta, nakan manta ni saurayi ne da burin kammala makaranta, neman rayuwa, da mafarkar nasara. Yanzu mafarkina shi ne ta buɗe idonta, ta ganni — ta gane ni. A haka bacci mai nauyi ya daukeni. ***********†*********** In the morning..... Misalin karfe' 9 na safe Yau zan kai ta wajen wata mata mai suna Maman Gambo, wata tsohuwa ce da ake kira da yar gani da faɗi. Duk da ban yarda da dukkan maganganun mutane ba, amma zuciyata ta tura ni. Na zauna a gabanta, Baby na hannuna. Tsohuwar ta ɗauki lokaci tana kallona. Sai ta ce da kakkausar murya: “Wannan yarinyar ba ta zo maka ba don ka cika rayuwarka — ta zo ne domin ta fara taka.” Na girgiza kai. “Ban gane ba…” Ta ce: “Zaka gane. Amma kada ka yi saurin tambaya. Sirrin da bai kai lokacin bayyanarsa ba — idan ya fito, sai ya tarwatsa gaskiya, kuma kadaina tunanin cewar bazaka zauna da ita a masarautr kuba, zaka zauna da ita acan Amma masifar da kake cikin ayanzu na tuhumar da mutane suke Maka ayanzu tafi Maka sauki ,akan wadda zaka tarar a masarautar sauba.” Lokaci guda jikina yayi sanyi batare da nasake cemata komai ba na mike na saka baby a bayana ,sanan na dakko zanin danake goyata a gefe na daureta kam, kamar mace ,Na tafi da wannan magana a zuciyata, cikin dare mai duhu da rana mai zafi. Ina zaune a ƙarƙashin bishiyar mangwaro, Baby na barci, sai wata mace ta zo ta tsaya a kaina da kallo mai zurfi. “Wannan yarinyar ba taka bace.” “Ina kika san haka?”mj ya tambayeta cike da mamaki. “Idan kai ne mahaifinta, da ba za ka kalli idonta da wannan tsoron ba.” “Ko kuma ni uba ne da zuciya…” na amsa a raina, ban faɗa ba a fini. Ta juya ta tafi, amma kalmarta ta barni da tambaya gaba daya so suke su haukatani ,nakasa Gane shin aljana nake rainon ko mutum, meyasa nake yawan mafarki ,meyasa nake ganin kamar aljanu na bibiyata?" Ganin Babu Wanda zai bani amsa yasa na mike na koma cikin gida ,baby na sauke a kan kujera na dakko mata Madara na Mika mata, ita Kuwa sai murmushi take baiwar Allah tana kallonsa kamar mai shirin fadamin wani bu, bance mata komai ba na mike nashiga daki, jakata na dakko na fito da wani book na felli faifa guda Daya ,sanan na dauki biro na dawo na zauna kusa da baby na soma rubuta wasiƙa — ba don wani ba, sai don Baby. Wasiƙar da za ta karanta wata rana idan ta girma. Ko kuwa… idan ta gano wacece ita. “Baby, Ba na da tabbacin daga ina kika fito, Amma na tabbata cewa kin fito daga inda Allah ke ajiye zuciya, Domin tun lokacin da kika zo, ban sake sanin kaina ba — sai dai sanin ke, ina ji ajikina ke kyau ta ce daga Allah ,Kuma nayi alkawarin cewa koda zan karar da numfashi nazan raineki da soyayyata, .” daga haka ya rufe' takardar ya ajiye gefe guda, sun kuyawa yayi kamar mai yin rarafe baby ta hau yashiga jankafa Yana mata doki, suna wasa ita Kuwa sai dariya takeyi. ** Washegari na koma makaranta, sai malamai suka ce: “Kai ne saurayin da ke zuwa da jaririya a hannunsa?” “Yanzu kana rainon yaro?!” “Ka ajiye rayuwarka don wata yar tsana?” Nai murmushi. Sai kawai na ce a raina: “Eh, don wata yar tsana ce — amma ita ce ta sake sosa ni, ta gyara ni, ta sake gina ni.” Na san ba kowa zai fahimce ni ba. Amma ba don su nake rayuwa ba — don Baby nake ƙoƙari. “Wata rana, sai ku gane cewa akwai nauyin da ba’a iya shi da jiki — sai da zuciya.” Daya daga cikin malaman nawane ya dakamin tsawa "ya Isa Mujahid kada kaga Kai Dan sarkine kanemi ka fada mana duk abin da yazo bakinka ,ka kula mu malamanka ne Kuma iyayenka, Wannan yarinyar da kake raino masiface a gareka, ta hanaka komai karatu kadaina kacan rayuwarka zuwa kamar ta mace kullum Kai da goyo abaya ,Anya kana cikin hayyacinka Kuwa, haka jiya kayi asarar exam kawai sabi da wannan abar.... Saurin katseshi MJ yayi dacewa Indai ina raye komaine zai iya aikatawa akan baby" daga haka ya fice daga office din. Kai tsaye ban koma cikin class ba ,na dawo gida, ina dawowa na shirya ma,aikatana suka rakani kasuwa domin yin siyya,sosai nasha wahala lokacin da na Isa kasuwa, ganin yadda kowa ke kallona da mamaki yadda naci damara da zanyi da baby a goye a bayana masu gadina Kuwa, kowanne zuciyarsa cike take da bakincikin yadda nake zubar da ajina a ko ina, a haka dai har na Kammala siyayyata Babu abin da ya dameni ,muka taho Muna dawo daga kasuwa da Baby — na siya mata wasu riguna 'yan rago da turare mai kamshi. Sai dai abinda na fi saya yau, shi ne abin da ba a sayarwa — hasashen cewa lokaci yana kokarin bayyana sirri. Yau babyna ta soma zuwa makaranta kullum ni nake kaita na dawo da ita sabi da na kaitane akwai don ta huta itama badan karatu ba, tun da dai shekarunta basu Kai ta soma zuwa school, nakai ta makaranta domin Nima nagaji da zancen da ake akaina ,ko ina kashiga sai kaji ana gulmata. To yau ma kamar kullum bayan baby ta dawo daga makaranta A ɗaki, ina wanke rigunanta sai na ji kamar wani abu ya fito daga gefen jakar da ta zo da ita. Wani ƙaramin envelope ne, fari fat-fari, an nade shi sosai. Ya shige cikin ramin zipp ɗin da har yanzu ban taba buɗewa ba. Na buɗe a hankali. Hannuna na rawa. Zuciyata na bugawa kamar karar ƙaho. A ciki, akwai hoto — hoto na mace da Baby tana jaririya sosai a cikinta. A bayan hoton, an rubuta da ink mai launin shuɗi: "Idan wannan ya kai hannunka, to nasan kai ne — wanda zai iya riketa har zuwa ƙarshen gaskiya." "Ka riƙeta — har zuwa inda zata gane kanta." Na shaƙi hoton. Na ji kamar numfashina ya canza. Na kalli Baby, tana barci… amma kamar tana motsa bakin ta cikin mafarki. Na ce a hankali: “Wacece ke a gaske, Baby…?” “Shin ni Allah ne ya ɗora wa amanarki — ko kuwa duniya ta jefa ki a raina don wata ƙaddara?” “Shin ina wannan matar ta shiga ta ajiye ki — ko kuwa rayuwa ce ta ƙwace ki daga hannunta ,mai take nufi tana nufin naci gaba da rukon ki, mai na iya mai zan miki ,ko ta manta da cewar ni yarone mai kananun shekaru?" 🕊️ RAINON YARO Chapter 3 ** Tun daga wannan rana, nake ganin mafarki iri ɗaya. Ina zaune da Baby a bakin rijiya. Wata mata ce ke tsaye a bayanmu tana kuka, tana cewa: “Mujahid… ka riketa kafin su dawo.” “Kar ka faɗa wa kowa komai. Komai.” “Idan ka faɗa — zata ɓace da sirrinta, sanan zasu kasheta da ranta,domin basa da Imani..” ** Ina farkawa da zufa. Sai na duba inda Baby take — tana nan, amma kamar numfashinta na haɗa da wani sirri. Sai nakan furta a hankali: “Wannan ba kawai raino ba ne — wannan alƙawari ne.” “Ni zan kareki — ko da kuwa ba zan taɓa gane wacece ke ba.” Hannu nasaka na jayo baby jikina Sannan na kara kanka meta da karfina ,hadi da lumshe ido ina tunanin abin da zaije ya dawo. "Lokaci yayi nakusan Kammala karatuna yanzu yazanyi kenan ,ta ina zan fuskanci su Abba da maganar su barni na zauna da baby a masarautar mu" MJ yasake lumshe ido hadi da sa hannu yashiga shafa kwantaccen sumar kan baby. Ina jin dumin jikinta kamar wuta a cikin sanyi. Duk lokacin da na lumshe ido, numfashinta yana shigowa cikin zuciyata kamar kalmar da ba a taɓa faɗa ba amma na fi kowa fahimta. “Baby... ke kadai ce da kika yarda da ni a lokacin da duniya ta kalli rainona a matsayin laifi.” Na lumshe idona sosai — sosai har sai da hawaye suka latsa gefen kuncina. Ba kuka bane na karaya, a’a. Wannan hawaye ne na soyayya, hawaye ne na alƙawari da niyyar kare rayuwa. Na zura hannuna cikin mayafin da na lullubeta , na shafa gashinta mai laushi. Ina nishi kamar wani ƙaramin jariri da bai san ko ina bane, amma ya yarda da numfashin mahaifinsa a matsayin amana. “Zan kasance wurinki, Baby... ko da kuwa na rasa komai.” 👑👑👑👑👑👑 Lokaci ya tafi. Kwanaki sun zame min kamar watanni. Karatuna ya kusa ƙarewa, amma kuma zuciyata tana ɗaure da wata tambaya da babu wanda zai iya amsawa sai Abba. Ta yaya zan je gaban Abba in ce masa 'ka barni na kula da yaron da na haifa tun kafin a bani damar aure'? Sassanyar iska ta daki labulen dakin. Sai da ya girgiza, ya shafe fuskata da danshi. Sai na yi dariya — irin dariyar da yake da kyau amma kuma cike da ɗaci. Baby ta motsa a jikina, sai na kara matseta, na dan busa mata iska a kai kamar zan kore mata duk damuwa. “dady... ka tashi kai min labari? Yaji muryar baby tana magana cikin gwaranci. Ban san yaushe ba, amma na soma jin wani zafi a kirji — zafin soyayya ce. Irin wacce zata sa ka fuskanci duniya baki ɗaya domin mutum guda. Wata zuciya ce ke furta min cewa: “Ka je gaban Abba. Ka zauna. Ka ce masa ka fi kowa sanin darajar wannan yarinyar.” Sai na furta a hankali: “Zan tsaya tsayin daka. Domin wannan ba raino bane kawai... wannan kalma ce: Zan zama uba kafin a bani damar zama miji.” Wannan shi ne karfina. Wannan shine mafarkina. Ina so a karanta labarin RAINON YARO a ce: “Wannan ba littafi bane — zuciya ce da take rubuta kanta da hawaye.” **************** ---Washegari da safe, MJ ya farka da kukan baby yana ƙara sama da ƙasa. Kamar wata ƙarar ƙararrawa ce da take faɗakar da zuciyarsa cewa lokaci na tafiya, kuma ba za a iya tsaya masa ba. Ya ɗago da gajiya, cikin wani irin yanayi na tunani ya rungume baby kam a kirjinsa yana shafa bayanta a hankali kamar yana mata sannu da safe da ƙauna. "Shhh... Daddy's here. No one will ever hurt you. Not while I still breathe." Sai MJ ya nufi gaban madubi. Idanunsa jajaye, alamun rashin barci da damuwa. Ya dafa kan madubin da hannunsa guda, ɗayan hannun na goye da baby. Ya kalli kansa, ya furta: "What kind of father am I if I let fear make my decisions?" “Ni zan iya tsayawa in fuskanci masarauta saboda yarinyar da na haifa. Sai me?” Dawowa yayi bakin gadon ya zauna Sannan ya sakko da baby daga bayan sa yace: “Ni ba wai na yanke shawarar zama uba bane. Allah ne ya bani wannan damar. Kuma bazan tsaya gefe ba in zuba ido.” “Sometimes, love is louder than bloodline. Kuma wuta ta ƙauna ce kadai ke iya kone dambar masarauta.” Cikin zuciyarsa: Yasan cewa a yau ne zai fuskanci Abba. A yau ne zai ce: “Ku bani damar zama da baby da na raina — ko da kuwa hakan zai sa ku kore ni daga gado, daga masarauta, daga tarihi.” Sai MJ ya ɗauki baby ya ɗago ta sama, tana dariya mai cike da hawaye: "You are not a mistake, my daughter. You're the reason I'm brave." “Ke ce ƙarfin zuciyata, baby... Ke ce RAINON YARINYAR DA YARO KAMATA YAKE RAINA..” [Yau – 8:00am | Gaban Gidan mj] Hasken safe ya ratsa tagar dakin MJ. Iskar safe tana busawa cikin sanyi da nishadi. MJ ya fito cikin farin kaya masu tsafta, kansa a lulluɓe da hula mai launin zinariya. A bayansa, Baby ta kwanta a cikin baby carrier, tana baccinta da kyakkyawar fuskarta da kwalliyar fuska irin ta su MJ. sannu a hanakli Ya sauka daga step ɗin gida, ya zuba ido sama, ya furta: “Bismillah. Wannan ba tafiya ce kawai ba. Wannan dawowa ce. Dawowa cikin tarihin da zan gina da hannu na.” 9:35am | Filin saukar jirgin saman masarauta Jirgin su MJ ya sauka cikin sanyi da sheƙin sarauta. Masu gadin masarauta suka nufi inda aka bude kofa suka matsa gefe cikin girmamawa. Da MJ ya sauka, kaya masu sauƙi ne a jikinsa amma kamanninsa sun kai da nisa – kyan fuska, nutsuwa da nutsuwar zuciya. A bayansa, Baby na kwance, har yanzu cikin bacci. Sai murmushi kawai ke sauka a fuskarta kamar tana mafarkin amininta MJ. A cikin masarauta kuwa... Da MJ ya taka ƙasa, kowa ya tsaya kallonsa. Masu gadi, bayin fada, hatta manyan dattawan fadar suka kalli goyon a bayansa da mamaki. “Subhanallah, wannan ne ɗan Sarki da yake shan wahala da ɗiya?” “Goyo fa! Cikin masarauta?” “Innalillahi... Irin wannan tausayi ne sai mutumin Allah!” Matan sarki suka fito da alkyabba da mayafi, kowacce da kallon mamaki da kishi a idonta. Matar Sarki gimbiya zubaida ta harare shi, amma daga bisani sai ta ce: “Toh haka za a bar wani namiji ya shigo da jaririya kamar wata matar shi? To wallahi bazan ta sabuba" Sittatu, wata matashiya da aka tanada domin auren MJ nan gaba, ta buɗe baki da kishi: “ya Mujahid da kuka ce zai zama sarkinmu bayan karatunsa, ashe tun yanzu yana da amarya da baby? Wallahi ba zan iya ba Kuma bazan yarda ba.” Zuwaira,wadda duk cikin su tafisu hatsari da masifa ta ce cikin sassauƙan murya: “Amma ku duba yadda yake goyo kamar uwa. Haka kawai zuciyata ke kiransa da mijina.to wallahi ko wace ta mallaki abin da ba nataba sainayi ajalinta "zuwaira ta fada Rai a bace. MJ kuwa yana tafiya cikin nutsuwa, bai duba hagu ba ko dama. Baby na cigaba da baccinta, idonta a lumshe, kamar tana karatun zuciyar MJ ne. Sarki ya kalli MJ daga nesa, ya furta a ransa: “Wannan yaron ba karamin sauyi yayi ba. Ya dawo mana da zuciyar jagora. In har zai iya kare jaririya, zai iya kare masarauta, bana ce muddum zai zauna da wannan jaririyar sai dai ya zaba komu ko ita ba, to mai yakawosa? Saiki ya furta a zuciyarsa Rai a bace. A hankula MJ ke takowa zuwa gaban abba. Zaune suke a babban falon masarauta. Gidan ya cika da shiru mai nauyi, irin wanda yake kashe kuzari. Kowane bango yana da tarihin sarauta, kowace kujera na da nauyin da ake so a ɗora wa kai. MJ yana tsaye, yana fuskantar mahaifinsa — Sarki UMAR, wanda ke zaune cikin cikakken kaya na sarauta, hannunsa a jingine bisa sandar mulki. Idanun MJ sun cika da natsuwa amma cikin zurfin shawara. Ya durƙusa, ya gaishe, sannan ya ce: "Abba, yau ban zo matsayin ɗa na sarki ba. Na zo matsayin uba. Wani uba da yake neman hakki." Abba ya kalle shi ba tare da motsi ba, sai kuma ya girgiza kai kaɗan. "Ka san cewa duk wanda ke cikin gidan sarauta, ba shi da ‘hakkin kansa’ gaba ɗaya. Hakkin masarauta yafi nashi." MJ ya haɗiye yawu. Ya haɗa hannayensa, ya matse su kamar yana da abin da zai fashe dashi idan bai furta ba: "Na ɗauki yarinyar nan da hannuna. Na raine ta cikin dare da rana, hawaye da dariya. Ba raino kawai bane, Abba. Wannan amanar zuciyata ce. Kuma ko duniya zata ce ba nawa bane, na riga na ce — NA SA ta A ZUCIYA." Abba ya ɗan ƙara ƙarfafa muryarsa: "Wai kai ka manta da dokar masarauta? Duk wani ɗa da ba'a haifeshi da sunanmu ba, ba zai shiga cikin gado ba. Ba za a karɓe shi cikin zuriyya ba!" MJ ya ɗaga kansa, cikin nutsuwa amma da ƙarfin zuciya: "To idan haka ne, na fi son in rasa gado, amma in samu zuciya. Baby tana da ni. Kuma hakan ya isheni fiye da komai." 🕊️ RAINON YARO Chapter 4 Sarki ya zuba masa ido... har ya sauke ajiyar zuciya. Kamar zuciyarsa na faɗuwa da sautin gaskiya da tausayi daga bakin MJ. Sai ya ce: "Kayi kama da mahaifinka fiye da yadda ka sani. Ni ma na yi haka da mahaifina saboda mahaifiyarka..." "...amma ka sani, Abee,zuciyar sarki tana da wuta da ruwa. Kuma kai kake da zabi wanne ka zuba.” MJ ya durƙusa, idanuwansa sun kada, amma ba ya kuka. Sai ya ce a hankali: "I will choose love, Abba. Even if it burns me." “Zan zabi ƙauna, ko da kuwa wuta za ta ƙone ni.” Abba ya ɗago sandar mulki, ya ɗan doka ƙasa da ita a hankali. Sannan ya ce: "Ka tashi, abee. Ka cigaba da rainon yarinyar ka. Amma ka sani, daga yau kai ubanta ne a rubuce da Kuma fili da boye. Idan ka fadi — masarauta ce ta fadi. Idan ka yi nasara — to zuriyarka zata cigaba." MJ ya miƙe, ya lumshe ido — da yarda, da godiya, da kwanciyar zuciya. --MJ ya miƙe a hankali, kamar an ɗebo nauyin duniya daga kafaɗunsa. Ya juya, sai idanunsa suka sauka kan wata ƙaramar yarinya wacce take zaune a gefe, tana wasa da sandar tambarin sarauta da MJ ya bari lokacin da ya shiga. Baby. Jininta. Numfashinta. Hankalinta da zuciyarsa tamkar an daure su da igiyar rayuwa guda. Ya taka zuwa gareta, ya tsuguna yana fuskantarta. Sai ya sanya hannunsa a kumatunta, yana murza fuskarta da murmushi mai nauyin albarka. “Let’s go home, Baby. Home is where love raised us.” Baby ta kalleshi, ta ɗaga hannayenta biyu kamar tana neman tsira daga dukan duniya. MJ ya ɗauke ta, ya daura ta a goyo — kamar ya ƙudiri aniyar: duk wanda zai ƙi ta, to shi ma MJ ya ƙi. suna fito daga zauren masarauta, suka fuskanci jerin mata da aka tanada domin a haɗa MJ aure da ɗaya daga cikinsu bayan ya gama karatu. Amma yau... ba gaisuwa, ba murmushi — sai kyama da surutu. “Kalli ya Mujahid goyo fa yake wannan ai a bin kunya ne kamar matarsa ta haifi shege!” “Wannan yarinyar, wani irin kazanta ne haka... ai ba daga gidan masu tarbiyya take ba.” “Idan wannan ce amana tasa, to wallahi ni da shi ba zamu tab jutuwa ba!” Wata daga cikinsu — Farida, wacce aka fi sa rai za a ɗaura MJ da ita — ta matso da wani irin kallon ƙyama, sannan ta ce da wata a bayanta: “Gashi yana da kyau, amma wallahi zuciyarsa ba ta gari ba. Wanda zai zauna da shegiyar wata marainiya, me zai hana ya ji kunyar abin kunyar Dan ya aikata?” Wasu daga cikinsu har suka danna Baby da yatsa, suna faɗin: “Banza ce kawai... wallahi duk wannan kyau da kulawa sai ta gama cikin wulakanci. Ba daga zuriyar mu ba ce ba dai ya zabi ta zauna a cikin gidannan ba wallahi sai ta gwammaci shegiyar da ta haifita bata kawota duniya ba!” Baby ta matse hannun MJ. Duk da ƙarancin shekarunta, tana fahimtar mugunta. MJ kuwa ya tsaya cak. Bakinshi ya bushe. Amma ba ya fushi — sai ka ce yana jiyo ƙara ne daga cikin zuciyarsa. “You hate what you don’t understand,” ya furta a hankali. “But I will raise her until you all bow to her greatness.” Sai kawai ya juya — ya tafi ba tare da ya waiwaya ba. Duniya na kallonsa da kallon raini, amma zuciyarsa ta fi kowace sarauta. Ya ɗauki Baby ya tafi da ita — kamar wanda ya ɗauki addininsa. ---Daren ranar... Siririn fitila guda daya ke kunnawa a dakin MJ. Dakin da ke bangaren nesa da sauran masarautar. Dakin da babu komai sai karamin gadon kwanciya, kujera daya, da kwandunan kayan wanka. MJ yana zaune a bakin gadon, ya cire rigar rigimarsa, ya nade hannayensa, yana kallon Baby da ke zaune a tsakiyar tabarma. Tana murmushi masa, duk da irin maganganun da aka jefar da ita da su yau. "Duniya ta fara koyar miki darasi, Baby," MJ ya furta da daddadɗar murya, yana jan ruwan zafi daga flask ya zuba cikin karamin bokiti. "But don’t let them break you. I didn’t carry you this far just for you to bend." Ya daga ta a hankali, ya cire mata karamin riga, sannan ya soma wanke kafarta da tawul. Hannunsa da taushi kamar yana tabawa da so da tausayi. "Sannu...sannu, kin ji?" ya ce, yana murza gashin kanta da yatsunsa. Baby ta kalleshi da idanu masu launin rana. Kamar tana son tambayar: “Me yasa suke ƙi na?” "They don’t hate you, Baby. They fear you. Saboda ke ba irin su bace," MJ ya ce yana murya kamar mai kiran sallah daga zuciya. Ya ɗauke ta, ya nannade da zani, ya zauna da ita a cinyarsa. Ya sanya mata man shafawa, yana hura mata iska a kunne, tana dariya kaɗan-kaɗan. Sai ya kalli kanta... ya lumshe ido. "Na rantse da kaina, Baby... ba zan bar kowa ya taɓa ki ba. Even if I have to fight my own blood." Sai kwatsam aka buga ƙofa. MJ ya miƙe tsaye da Baby a goyo. Kamar sojan da aka tsinkayo daga mafarki. "Waye ne?" “It’s Zuwaira... open the door.” Zuwaira — ɗaya daga cikin 'yan matan da aka tanada don MJ. Ita ce wacce ba ta cewa komai yau lokacin aka zagi Baby, amma tana kallon MJ da idanu masu ƙuna. MJ ya buɗe ƙofar. Zuwaira ta tsaya tana kallonsa. Sai kallon Baby. “I didn’t come to insult her like the others,” ta furta da ƙarfin zuciya. “But I came to ask — me ya sa ita? Me ya sa wannan marainiyar ta kai matsayin da duk mu ba mu kai ba?” MJ ya kalleta. Sai yayi shiru. “Saboda ina da zuciyar da ba ta neman fari, ba ta tsoron baƙi. Ina so ne, ba domin ta cancanta — sai domin ta cancanta.” Zuwaira ta nisa. Sai ta juya, tace: “Then may your love protect you both. Amma ka sani... ba kowacce ƙauna ake sakawa ba da hura wuta — wasu ƙaunuka na cin wuta ne har abada.” Ta juya, ta barshi a tsaye da Baby a bayansa — Daya mai ƙauna, ɗaya mara tsoro. ---Safiyar fari, rana ta biyu da MJ da Baby suka dawo masarauta… MJ na tsaye gaban madubi, yana daura agogon hannu, yana sanye da farar shadda mai tsabta da hula riga ɗaya, da takalmin fata na sarauta. Baby kuwa tana zaune a gaban kofar ɗaki, tana wasa da ƙaramar jar-takar da ya siyo mata jiya — sabuwar motar roba mai launin ja. MJ ya kalleta ta madubi, sannan ya juya ya durƙusa gabanta. "Yau zaki fara makaranta, Baby. Karki ji tsoro. Komai zai dai-daita, okay?" Baby ta kallesa, sai ta yi murmushin da ke haskaka zuciyarsa fiye da fitilar dakin. Ya ɗauketa, ya goya a baya — ta lumshe ido tana jin dumin fatarsa da ƙamshin man shafansa. --- Bayan ƴan mintoci... a kofar makarantar da ke cikin masarautar: Yara da dama suna fitowa daga motoci, wasu daga cikin dangin masu fada aji, wasu 'ya'yan sarauta. Wasu daga cikinsu sun tsaya suna kallo da mamaki lokacin da suka ga MJ ya sauka daga motar sarauta da goyo a bayansa. "Waye wannan kuma? MJ ne da baby?!" "Wato har yanzu yana riƙe wannan yarinyar?" "Ko da girmansa, da bai samu matar aure ba, sai marainiya?" Zuwaira da wasu 'yan mata biyu daga cikin waɗanda aka tanada domin MJ sun tsaya gefe suna kallon sa. Zuwaira ta runtse ido, tace a hankali: "He’s really not letting go..." Ɗayarta ta ce da ɗan gajiya: "To idan har Baby zata girma a masarauta, mu fa? Auren da muka zata...?" "Yanzu duk za mu zama masu kallon soyayya kenan?" Wani daga cikin malamai ya ƙaraso wajen MJ. "Ranka ya daɗe, ka kawo yarinyar kenan?" MJ ya gyaɗa kai. "Eh, I want her to be raised with knowledge. Ku koya mata — amma kada ku ci mata mutunci. She's a child. And she's my child." Malamin ya ɗan kaɗa kai da ladabi — amma mamaki bai ɓoye a fuskarsa ba. --- Lokacin break... a makarantar: Baby tana zaune cikin yara a gefe, amma wasu daga cikinsu suna harararta. "Ke daga wace gida kike?" "Me yasa na ganki da MJ?" "Ko ke ce yarinyar da suke cewa ba jinin sarki bace?" Baby ta ɗan lumshe ido. Duk da ƙarancin shekaru, zuciyarta na gane bambanci tsakanin tambaya da tsana. Ta miƙe, ta ja littafinta ta koma gefe. Daga nesa, MJ na kallonta ta cikin gilashin ofishin malamai. Ya dafe fuska, yana tunanin... "I’m trying... amma me zai hana wannan duniya ta daina cutar da mai rauni?" Sai aka ji murya daga bayansa: “Za ka rasa komai saboda ita.” MJ ya juyo — Sarki Umar ne ya tsaya a bayan ofishin, yana kallon Baby. “Na riga na rasa abin da ba na so. Idan ita ce komai — I am ready to lose the world.” **************** Dare ya rufe masarauta. Fitilu na haskakawa, iska na busa cikin sassanyar ƙamshi na tsiron jajjaye. MJ yana tsaye a zauren barandar sashen sa, yana duba wayarsa. Jikin sa yana ɗaure da gajiya, amma zuciyarsa cike take da damuwa. Baby tana cikin ɗaki, tana bacci, bayan kuka da ya daɗe kafin ta lallaɓa ta kwanta. Sai ga Uncle Faruq, ɗan’uwan Abba, wanda aka fi sani da dattijon fada, ya ƙaraso da takalman fata masu amo. “MJ, akwai abin da nake son na fada maka. Ka shirya ranka.” MJ ya ɗago kai. “Uncle, lafiya?” Uncle Faruq ya gyaɗa kai, yana jan kujera ya zauna kusa da shi. “Akwai wani tsarin da 'yan mata uku daga cikin gidan sarauta suka fara. Sun fara ƙoƙarin ganin an hana Baby shiga makaranta gaba ɗaya.” MJ ya dafe kansa. “Me suka yi ne?” “Sun yi ƙaryar cewa tana janyo rikici a cikin aji. Wata daga cikin su ta sa yaronta ya tura Baby, har ta fāɗi, sai aka ɗauki hoto aka nuna kamar ita ce ta fara faɗa.” MJ ya miƙe tsaye. Idanunsa sun canza launi. “Why would they do that to a child?” “Wani kuskure ne a rayuwa da yasa mutane ke jin haushin wanda bai taɓa cutar da su ba?” Uncle Faruq ya juyo da ido mai nuni: “Wannan ba cuta ba ce ta zuciya kawai — kishin duniya ne. Sun fi tsoron yadda kake ƙaunar Baby fiye da yadda kake ƙin su.” MJ ya ɗaga wayarsa, ya kira principal ɗin makaranta. “Gobe da safe, zan zo da lawyer. A buɗe min cctv footage na makarantar. Ina son ganin komai.” --- Washegari da safe... MJ ya sauka cikin makarantar da manyan jami’an tsaro biyu. Baby na goye a bayansa, amma yau ta saki jiki kamar ta saba da waje. Sai dai idanun ta suna kallon kowa da tausayi. Principal ya fito cikin girmamawa. “Ranka ya daɗe, ga footage din.” A gaban kwamfuta suka kunna bidiyon. A can aka ga ɗaya daga cikin yara ya ture Baby. Ta faɗi. Sannan wata yarinya ta kira wata da suna: "Kira hoto! Ce mata ita ce ta fara!" MJ ya dafe ƙirji. “So that’s it…” Ya juyo ga principal: “You will issue an apology letter to my daughter. And you’ll suspend the students who lied.” Principal ya lumshe ido: “Yes, Your Highness. I apologize.” --- Wajen ‘yan matan masarauta… Zuwaira na zaune da su Sa’ada da Fa’izah. Sun samu labari cewa MJ ya gano duk abinda suka shirya. “Yanzu fa... he’ll hate us,” Sa’ada ta ce tana shafa gashin kanta. Zuwaira ta tashi tsaye, ta ce: “Sai ya tsani mu kenan saboda waccan yarinyar?” Fa’izah ta ce: “Ba saboda ita ba. Saboda yadda muke ƙi wanda MJ yake so.” “Well,” Zuwaira ta fadi da zafin rai, “Let’s see how long this love will last. She’s just a child. But she’s living a queen’s life.” Hakadai aka gama kashe wanan matsalar daker MJ ya hakaru ya kylesu , a hakanma Saida mai martaba ya saka baki a maganar. ••••••••••••••••••••••••••••••••••••••• Wata rana da safe, rana na fito da dumin ta, iska na kadawa cikin furanni a cikin masarautar. Baby na zaune a gaban teburin MJ, tana riƙe da fensir, tana ƙoƙarin rubuta sunanta. MJ na zaune a gabanta, yana kallonta da murmushin da bai daina haskawa ba tun daga lokacin da ya ɗauki rainonta. “Write it again, sweetheart. Slowly this time. B...A...B...Y.” Baby ta lumshe ido, ta ce da harshenta mai rauni: “Baby MJ.” MJ ya bushe da dariya, ya ɗago ta ya rungume. “No, sweetheart. Just Baby. You’re enough on your own.” Kallon da suka yi wa juna ya cika da soyayya irin ta jini da rai — ba sai an furta uba da ɗiya ba, zuciya ta riga ta furta fiye da haka. --- Cikin masarauta... A wani bangare na fadar da aka fi kira "Zauren Shawara", wasu dattijai daga cikin gidan sarauta sun zauna suna tattaunawa. Wani dattijo, Alhaji Kaura, ya ce: “Wannan ƙaunar da MJ ke nuna wa waccan yarinyar zata iya dagula tsarin masarauta gaba ɗaya. Ya kamata a sa dokar hana ta shiga ayyukan masarauta gaba ɗaya.” Wani ya ce: “Amma fa yaron nan yana da ƙarfin zuciya. Ya fi mahaifinsa darewa daga sama ba tare da faduwa ba.” Sai wani tsoho ya girgiza kai: “Mu bar su suyi wasa, amma mu sa ido. Saboda idan wuta ta samo asali daga soyayya, tana ƙonewa fiye da wutar fushi.” --- Daren ranar... Baby ta dawo daga makaranta. A yau ta zo da 'report card'. MJ ya zauna a tsakar gida yana shan shayi, lokacin da ta karaso da takarda a hannunta. “Daddy , see!” Ya karɓa, ya karanta — tana da 'A' a kan karatu, da kyau sosai a tarbiyya da halayyar aiki tare da yara. Ya ɗago ido da murmushi mai dumi: “You are the best daughter anyone could ask for.” Ya ɗago ta sama yana juyawa da ita, suna dariya. Har lokacin Zuwaira na tsaye daga nesa tana kallo, zuciyarta cike da wani abu mai kama da kishi, da kuma rashin fahimta. “Why is it so easy for her to have him all to herself?” To Washegari da safe, lokacin rana na sosa fuska da haske, MJ ya zauna a wani ɗan gindin mango a fadar gida. Ya ajiye Baby a jikin sa tana cin dankali mai zafi. Sai kuma wata mace ta fito daga cikin gida, ta zauna a gefensa cikin kulawa. Hajiya Rasheeda, mahaifiyar MJ — mace ce mai tsafta, dattaku da natsuwa. Idonta yana da zurfin gani, kamar mace da ta rayu da hikima. Ta kalli MJ, sannan ta dora hannunta a kafaɗarsa. Hajiya Rasheeda: “Ka girma, ɗana. Amma zuciyarka bata fasa kasancewa tamkar ta yaro ba. Wannan yarinya... ba kawai karamin sakamako bane. Ita ce kaddara da zuciyar ka ta karɓa tun kafin ka gane.” MJ ya ɗan juyo ya kalli mahaifiyar tasa, idanunsa sun cika da godiya. MJ: “momy, na san duniya zata yi mini tambayoyi da yawa. Zasu ce ‘ta wacece ita?’ Ko ‘me yasa ba waiyanda suka haife ni suka haife ta ba?’ Amma bana da amsar komai... sai dai: ina son ta.” Hajiya Rasheeda: (ta shaƙi gashin Baby) “To ka ci gaba da ƙaunarta. Akwai yara da yawa da iyaye suka haifa amma basu raina su ba. Amma kai... kai ka ɗauki yaro ba naka ba, ka saka a zuciyarka, ka saka a shiryayyen makomarka.” Sannan ta matsa kusa da Baby, ta ce da dariya: “Yanzu dai Baby zata san tana da ‘granny’ mai son ta sosai.” Baby ta ce da ƙanana murya: “Gwanny...” MJ ya sa dariya har da hawaye. Ya kalli mahaifiyarsa, ya ce: “Kina bani kwarin gwiwa,Momy. Wannan yarinyar — ita ce tsintuwa ta. Na tsinta aljanna daga cikin rikici.” Hajiya Rasheeda: “To ka kula da aljannarka. Domin irin wannan baiwar, idan aka raina — duniya ba zata sake kawo maka irinta ba.” 🕊️ RAINON YARO Chapter 5 °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° A cikin babban lambun masarauta, inda furanni ke sheƙi kamar zinariya, an shirya wani taron ‘yan mata na fada. Ana nan ana hira, ana dariya, wasu suna kallon MJ daga nesa yayin da Baby ke wasa a kusa da shi, ta zura riga ta ja wando, tana dariya da ɗan fashi. Kallon da ake musu ba na ƙauna ba ne — na ƙyashi ne, tsana, da hassada. Sai Zuwaira, ɗaya daga cikin kyawawan ‘yan mata da aka tanada domin MJ, ta juyo ga wata daga cikin kawayenta ta ce da murya mai ɗaci: Zuwaira: “To ai ba komai bane. Kamar yana raina mu ne — yaro ya dawo da shegiya a bayansa ya goya, ya mayar da ita ‘yar gida!” Kawarta: “Ai kuwa da ni ne, da na ce ko dai su fita daga fada, ko mu fita. Ba za mu yarda da haka ba.” Suna cikin maganganu, sai Hajiya Rasheeda ta iso. Tana cikin kaya na kamala, murya nata cike da nutsuwa, amma tana ɗauke da ƙarfi da izza da ba’a sabawa da ita. Hajiya Rasheeda: “Ina jinku. Kuma ban zo don jin abinda kuke faɗa ba. Na zo in faɗa muku cewa — idan har zuciyarku na iya jin hassada akan jaririya, to ku sani ba ku da matsayi a cikin gidan nan.” Zuwaira: “Umm... Hajiya, ba komai, muna hira ne kawai…” Hajiya Rasheeda: (ta ɗaga hannu) “Kada ki ƙara ɓata lokaci da ƙarya. Na haifi abee da rainonsa. Kuma duk wanda zai masa mummuna — to shi ne ya ɓata ran sarki da uwar sarki. Ku saurara da kunnuwanku, Baby da kuke zagi — ita ce jininki da ke shigowa cikin masarauta da rahama.” Kawarta: “To amma ai ba ta da gata ko asali...” Hajiya Rasheeda: “Gata ba daga jininka yake ba — daga zuciyarka yake. Idan Baby ta sami gata a zuciyar abee da kuma a zuciyata — to ku manta da kowane masarauta. Ita ce masarauta.” MJ ya nufo wajen, ya tsaya yana sauraron mahaifiyarsa, sannan ya ce: MJ: “Wannan ita ce mahaifiyata. Idan kuka ƙi Baby, ku sani — kun ƙi ni. Idan kuka ƙi ni, to kun ƙi gata. Kuma ba zan zabi gata akan amana ba.” Zuwaira ta ja hancinta, suka juya cikin kunyarsu. Baby ta zo da gudu, ta riƙe gwiwar MJ, sannan ta ce da murya: “Daddy, I love you.” MJ ya durƙusa, ya rungume ta. MJ: “And I will protect you, even if the whole world turns against us.” After one day A cikin zauren majalisar sarauta, ana ta jira Sarki ya fito. Kowane dattijo da mace mai mukami ta zauna cikin natsuwa, amma zuciyarsu na yawo. Ganin MJ da goyo a baya — ya tayar da kura. Amma jin bayanin mahaifiyarsa, Hajiya Rasheeda, ya ɗan kashe wutar – ko da kuwa wutar tana ƙasa tana ci. Sarki Umar ya shigo cikin shigar zanna bukar mai masarautar Kano, sandarsa a hannunsa, idonsa yana haska kowa. Sarki: “Na ji dukkan maganganun ku. Na karanta yadda murya ke ƙasa tana ƙona zuciya. A yau, muna da batu guda: Shin wannan yarinya – Baby – tana da wuri a gidan sarauta ko a’a?” Wasu suka yi murmushin mugunta, wasu suka yi shiru. Sai MJ ya tashi ya tsaya gaban su, da kwanciyar hankali, yana goye da Baby. Sai ya ce: MJ: “Babu wata rigima idan masarauta ta ƙi karɓar Baby. Amma ku sani — idan Baby ba ta da matsayi a nan, to Mujahid ma bai da matsayi.” Kukan ƙasa-ƙasa ya cika zauren. Wani dattijo: ya kalleshi yace “Amma yaro… dokar sarauta bata amince da wannan aikinba. Wannan yarinya bata fito daga cikin hantar masarauta ba.” MJ: ne yace “Sai dai zuciya. Kuma idan akwai masarauta da bata iya jin tausayi — to wace irin sarauta ce hakan?” Sarki ya danna sandarsa ƙasa. Duk suka yi shiru. Sai ya ce: Sarki: “Ina neman mahaifiyar abee — Rasheeda.” Ta tashi da kamala. Sarki: “Kin goyi bayan wannan yaron akan rainon wannan yarinyar?” Hajiya Rasheeda: “Na goyi bayansa kamar yadda na goyeshi a bayana tun yana jariri. Idan har abee yana da matsayi — to Baby ma zata yi.” Sarki: “To ni ma zan yarda. Amma ku sani, “Na yarda a hukumance — cewa wannan yarinya, Baby, za ta zauna cikin masarauta. Za a bata kariya, za a bata matsayi. Za a raineta da mutunci. Kuma daga yau, duk wanda ya kalle ta da ƙyama, ya ci amanar masarauta.” MJ ya lumshe ido — zuciyarsa cike da farin ciki da godiya. Ya durƙusa, yana jin kamar an rage nauyin da ke kansa. Sai Sarki ya ɗan dakata. Idanunsa sun sauka kan MJ. Sai ya ƙara da cewa, da ƙarfin murya: Sarki Umar: “Amma Abee — kai ne ɗana, kai ne magajina. Kuma kai ma ka sani: masarauta bata rayu da ruɗani ba. Saboda haka, zan sa sharadi guda ɗaya...” Zuciyar kowa ta tsaya cak. Sarki: “Baby — wannan yarinya da ka raina — daga yau zuwa gobe, za ta rayu a matsayin 'yar masarauta, 'yar ka, amma ba matar ka ba. Idan ta girma, ba za ku taɓa zama a matsayin miji da mata ba. Wannan ne sharadin da ke tsakaninka da gadonka.” Zuciyar MJ ta buga! Ya dago kai da sauri kamar ba ya jin daidai. Wani sanyi ya shige shi, kamar ruwa mai sanyi ya zubo a kansa. Ya dubi Baby, tana bacci a bayansa — ba ta san da komai ba, amma rayuwarta na juyawa da wani hukunci. MJ: “Abba... amma…” Sarki: “Babu ‘amma’, abee. Wannan shine farashin matsayin da kake so. Idan ka yarda da amanar Baby — to ka yarda da ita a matsayin ‘yarka, ba wata ƙari.” Akwai shiru mai nauyi da ya cika dakin. MJ ya runtse ido, ya saki numfashi, ya lumshe idanunsa, sannan a hankali — ya ce: MJ: “Na yarda. Na yarda da rainon Baby — komai farashinsa. Zan zauna da ita kamar ‘yata, zan tsare ta fiye da yadda na tsare zuciyata.” “Zan so ta — ba don auren ta ba, sai don cewa ni nake da hakkin sanya mata dariya.” Sarki ya ɗago sandarsa, ya danna ƙasa da ita. “Da wannan, masarauta ta amince. Amma kada ka manta: ka ƙi auren duniya — ka zaɓi zuciyar jaririya. Ka zaɓi soyayya mai tsafta. Kada ka karya wannan alkawari.” Hannu ya ɗaga, majalisar ta buga tambari. MJ ya lumshe ido, Baby na bacci a bayansa — amma zuciyarsa ta sami kwanciya kamar an sauke tsauni. To Daren ranar ya kasance kamar bakan gizo — komai shiru, amma kowanne bango na masarauta yana ɗauke da tunani da ɓoyayyiyar magana. MJ ya zauna a dakinsa, yana kallon Baby da ke kwance a kafadarsa. Hannunsa yana shafa bayanta a hankali, kamar yana ƙoƙarin tabbatar da cewa duniya ba za ta taɓa cutar da ita ba. “How can I love you this much… and still have to pretend it’s just fatherly?” “Yaya zan iya sonki haka, amma in ce wai da na raino ne?” MJ ya furta cikin siririn murya. Baby ta buɗe idonta, ta kalle shi da murmushin rashin sani. Ta sa hannunta ƙarama a fuskarsa — kamar ta san da rikicin da ke zuciyarsa. --- Bayan kwana uku MJ ya fara fita da Baby zuwa sashen sarauta, inda ake shirye-shiryen bikin cikar shekara da kafa da sabbin matasa da za a aurar da su ga ‘yan gidan masarauta. Zuwaira na daga ciki — ita da ‘yan uwanta biyu, Ameerah da Ramla. Da zarar MJ ya shigo, da Baby goye a bayansa — dukan matan suka kafe shi da idanu. Zuwaira: “Kai, ni dai ban fahimce shi ba. Ya ɗaure kansa da ‘yar da ba a san asalinta ba. Yanzu duk wata kyakkyawar baiwar Allah ta zama ba ta da wurin shiga?” Ramla: “To ai idan baby ce matsalar, mu ma za mu iya rainon ta. Sai mu raba raino da soyayya.” Ameerah: “Shiru ku yi. MJ ba saurayi bane kamar sauran. Zuciyarsa ta fi soyayya — kuma irin zuciyar da ke iya ƙin buɗewa, ita ce mafi laushi idan ta buɗe.” ---......... Wasu matan cikin masarauta sun fara nuna ƙiyayya da hassada a bayyane. A sashin da Baby ke yawan zuwa, sun fara watsa maganganu: “Wannan yarinyar, ta fito daga ina ne? An ce ba a san iyayenta ba…” “To ai duk mai kawo bakar rana cikin masarauta sai ta ɗauke haske!” “Gashi ya Mujahid ya mayar da ita kamar sarauniya. Tana da karamin jiki, amma tana da babban zargi.” --- MJ da mahaifiyarsa – Rasheeda A wannan daren, MJ ya zauna a dakin mahaifiyarsa. Ita ce Rasheeda — ta fi kowa fahimtar zuciyarsa. Bayan ya bayyana mata komai, sai ta janyo shi kusa da ita, ta dafa kafaɗarsa. Rasheeda: “Kayi kamar mahaifinka. Amma kai ka fi shi — domin kai ba kawai ka tsaya tsayin daka ba ne. Kai ka yarda da rauni.” “Baby zata girma. Zata ji. Zata gane. Kuma wata rana, zata tambaya — me yasa ba za ta iya zama matar wanda ya so ta tun tana jaririya ba?” MJ ya ɗan sunkuyar da kai, yana kallon tabon zuciyarsa da ba a iya gani da ido. MJ: “Sai dai idan zuciyarta ta farka kafin nasan yadda zan ce mata 'no’.” --- Mai Shigowa – Gari-gari A sashin sarauta, wani bawan Allah ya shigo da saƙo daga wani ɗan sarki daga wata masarauta makwabta — ya nemi a aurar masa da Baby, domin yana da masaniyar cewa ba ‘ya ce ta jini ba. MJ ya ji wannan labari a wajen falon sarauta. Ya tsaya cak. Numfashinsa ya sarke. Zuciyarsa ta fara dukan da bai taɓa ji ba. “She can’t belong to anyone else... even if she never belongs to me.” Yarinyar har nawa take daza a fara zancen neman aurenta bayan ko jinin al,ada bata faraba "innalillahi wa inna ilaihirraju un MJ ya furta afili, hadi da kifa Kansa a bakin bed din. Washegarin Asabar Gari bai gama wayewa ba, MJ ya buɗe idonsa ya kalli Baby da ke kwance gefensa, tana bacci. Amma wannan baccin — ba irin na jiya bane. Sai da ya kalli fuskarta sau uku, sannan ya fahimci wani abu ya canza. “She’s growing... And I can’t stop it.” Ta girma... kuma ba zan iya dakatar da hakan ba. Ya lumshe ido, ya sauke ajiyar zuciya. A jikinsa yana jin zuciyarsa tana ce masa "kar ka manta da alkawarin ka". Amma jikinsa na jin wani sanyi daban — kamar Baby ce ke ƙoƙarin faɗa masa "ka daina ɓoye gaskiya." --- Ranar Lahadi MJ ya shigo dakin Baby da kayan gyaran kai. Ya zauna a bayanta yana yi mata kitso — da kansa. Baby na zaune a ƙasa cikin doguwar riga, tana ɓoye fuskarta a hankali. Yau tana jin wani abu dabam... cikin jikinta na sauyawa. Bata san dalili ba — amma zuciyarta kamar tana faɗa mata daddy ba kamar sauran ba ne. Sai dai ta kasa fassara. Baby (muryarta a kasalance): “daddy… inaso ka sani, ban san iyayena ba… amma idan zan fassara ƙauna, to kaine na farko da na taɓa sani.” MJ ya tsaya da hannunsa, ya rasa abin da zai ce. Ya dan sauke murya yana cewa: “You don’t need to know where you’re from. Because I know where you’re going. And I’ll take you there.” “Ba sai kin san inda kika fito ba. Ni nasan inda za mu je. Kuma zan kai ki da kaina.” Baby ta lumshe ido, hawaye ya zubo. Amma ba na baƙin ciki ba ne — na jin ƙauna ce. Kuma wannan hawaye ya tsaya ne a gefen kumburin idonta da ke nuna alamun ta fara jinin balaga. --- Da daddare, MJ ya shigo da abinci, sai ya hangi rigar Baby a gefe, tana sanye da sabuwa. Idonsa ya sauka kan jinin da ya ɓata rigar farko — ya tsaya cak. Numfashinsa ya tsaya na biyu. MJ (a ransa): “The day I feared… has come.” Ranar da na ke tsoro… ta iso. Sai ya juya baya ya dafa bango. Yana jin kamar yana kallon ƙaramar yarinya tana barin duniyar yara, tana ƙwanƙwasawa a ƙofar manya. Ya dawo kusa da ita, ya zauna a gefenta, ya ce a hankali: “Zaki iya tambayata komai. I’ll never judge you. Ever.” “Koda tambayarki zata ɓata min rai, sai dai in amsa da ƙauna.” Baby ta ɗago kai, hawaye a idonta: “Yanzu na shiga duniya ne?” MJ ya lumshe ido, ya dafa kafaɗarta: “Duniya ta shige ki.” --- Sashen Masarauta – Wasu daga cikin matan sarauta sun fara jin tsoro — Baby na girma, MJ na kara nisa da su. Suna jin wata rana zata jefa su cikin rana. “Yanzu yarinyar nan ta balaga kenan? MJ fa zai iya aurenta nan gaba!” “Ko da dokar Sarki tace a’a… idan MJ ya ce ‘eh’, wa zai ce a’a masa?” “Yakamata mu yi wani abu kafin al’amari ya fita daga hannunmu.” ---MJ na zaune a gefen tagar ɗakinsa, yana kallon Baby da ke barci cikin natsuwa. Hasken rana yana daddafa fuskarta kamar Allah na shafa mata albarka da haske. Ya dafa kansa a hankali, yana furta da zuciya: "Allah Ka sani… ba wai ina sonta da wata manufa ba. Ina sonta ne kamar yadda zan so rainon da na shuka da hannuna — wanda na zuba jini da hawaye akai." Ya mike, ya rufe labulen. Kamar yana ƙoƙarin rufe zuciyarsa ne. --- A Dakin Mahaifiyar MJ – Yau MJ ya kai Baby sashen mahaifiyarsa, momy domin ya tafi wani taron sarauta. Momy ta zauna tana kallon Baby da dariya da ƙauna a idonta. Momy (cikin murmushi): "Wannan yarinya... tana da ƙwazo. Kuma tana da haiba. Kamar ita za ta cika wannan gidan da farin ciki da zaman lafiya." Baby ta ɗago kai: "Umma… daddy yana sona ne?" Momy ta daka mata Kai da murmushi: "Abee ya fi ƙaunarki fiye da yadda za ki fahimta. Amma ki sani… ƙaunar da ba ta da sharri ce za ta rike masarauta." “Kada ki bar zuciyarki ta wuce inda hankalinki bai kai ba.” Baby ta sunkuyar da kai, sai ta ce: "Ina jin kamar ni ba kamar sauran yaran masarauta ba..." Momy ta jawo ta jiki, ta ce: "You don’t need to be like them. You are chosen differently." “Ba sai kin zama kamar su ba. Allah ya zaɓe ki daban.” --- MJ Yana dawowa daga taro, MJ ya tarar da Baby na barci a ɗakin mahaifiyarsa. Ya tsaya yana kallonta na wasu mintuna, sannan ya zauna yana shafa gashinta da hannunsa. MJ (a ransa): “You are still a child. I will guard that truth with my life.” “Ke har yanzu yarinya ce. Zuciyata zata kare wannan gaskiya har abada.” Ya lumshe ido, ya sauke ajiyar zuciya — irin wadda ke ɗauke da gagarumin alƙawari: ba soyayya, ba sha’awa — sai dai kariya da amana. --- Rashin Jin Daɗi Daga Wasu Matan Masarauta A bangaren matan masarauta, tsoro da kishi na ƙaruwa. Gani suke kamar MJ ya fi kowa kulawa da Baby. “Ta ina MJ zai auri wata daga cikinmu, idan har zuciyarsa tana gefen yarinyar nan?” “Yakamata mu nemi Sarki ya tsawatar masa. Wannan rainon ya fara zarce gona da iri.” --- MJ & Sarki Umar Sarki ya jawo MJ gefe, yana kallonsa da kulawa da nisa. Sai ya ce: "Ka tuna da sharadin da na baka, Abee Zaka iya kula da Baby har abada — amma ba za ta taba zama matar ka ba." "Do you still stand by that promise?" MJ ya daga kai da kwanciyar hankali: "I still stand, Abba. I’m her guardian, not her groom." "Ni mai kare ta ne — ba mai neman aurenta ba." Sarki ya kalli idonsa da zurfi, kafin ya ce: "If you can keep that boundary till the end, then maybe you’re stronger than I ever was." “Idan har zaka iya kare wannan iyaka har ƙarshe, to ka fi ni ƙarfin zuciya. Huce ka tafi Abee Allah yayi Maka albarka " °°°°°′°°°°°′°°°′°°°°°°°′°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° Wata rana da asuba, MJ ya tashi daga barci, ya juya ya kalli gefen gadon inda Baby ke kwance cikin rigarta ta riga da wando, tana barci cikin salama, hannunta na rataye a gefen pillow. Hasken fitilar bango na haskaka yatsunta kamar ana tsaga lu’ulu’u da rana. Ya lumshe ido ya furta da zuciya: “Yarinyar nan tana girma… kuma tare da kowanne girma, zuciyata tana ƙara tsorata.” yanzu baby baro dakin ki kikai kika dawo Nan, kash ni bansan yazan yiba yanzu fa TA girma Amma nakasa rabata da gangar jikina ,domin tasaba kwanciya a gefena tanajin dumina tamkar na uwa." Ya mik’e, ya nufi toilet don wanka. Har ya fito ya shirya cikin farin shadda da hula mai launin sarauta. Daga nan ya kama gyaran gashinta — ya fara taje kanta da kulawa da lallashi. Duk sanda ya samu ƙulli, sai ya ja da sauƙi, yana cewa: “Ki daina motsi mana Baby, ba so nake ki ji ciwo ba.” Baby ta langwabar da kai a kafadarsa tana dariya. "Kai ne daddy, ka fi ko wane gyaran kai da taushi.” Ya murmusa, zuciyarsa na ɓoye wani abu mai nauyi — tsoron lokaci. --- YAYIN DA BABY KE GIRMA... Kwanaki sun ja. Watanni sun shude. Baby ta fara nuna alamomin balaga. Jikinta na sauyawa da ƙanƙanin zane, murya na canjawa da laushi da tsawo. Amma abin da ya fi firgita MJ shine... tana fara ganin jini. Al’ada a Karo na biyu ta zo mata a rana da aka shirya babban liyafa a masarauta. Tana cikin ɗaki ita kaɗai, tana kuka, tana cewa: “Na ɓaci… daddy zai tsaneni.” Amma kafin ta gama maganar, MJ ya shigo da kulawa, yana ɗauke da abin tsafta da gyaran kai da sabuwar rigar bacci. Ya durƙusa gabanta, ya kama hannunta: “Baby, wannan ba cuta bane. Wannan alama ce cewa kina girma. Kuma ba komai bane a ciki sai alfahari. You are becoming a woman, and that’s okay.” Ya share hawayenta da tissue, sannan ya ce: “Zan koya miki yadda za ki kula da kanki. Amma ki sani — ko kin zama budurwa, ko kina yarinya — ni har yanzu daddy ɗinki ne.” Baby ta kalle shi da wani irin natsuwa da tsantsar amincewa. Sai ta jingina da kafadarsa ta ce: “Na tsorata daddy… amma na fi tsoron rashin jin daɗinka.” Ya shafa gashinta: “Bana jin daɗin duniya, sai dai idan kina murmushi.” --- 🕊️ RAINON YARO Chapter 6, A gefe guda kuma, masarauta ta fara lura da girman Baby. Kallon da ake mata ya fara canjawa — daga na raino zuwa na tambaya da tsoro. “Wannan yarinya tana girma da kyau. Idan MJ bai kange zuciyarsa ba, masarauta za ta shiga rikici.” “Yakamata a maida Baby wani wuri kafin zuciyar MJ ta fita daga layin alkawari.” Sarki Umar ya zauna da MJ a daren ranar, bayan sallar Isha’i. Sarki: “abee, ka lura cewa lokaci yana ƙara jefa zuciyarka cikin jaraba. Baby ba ƙarama ba ce yanzu. Har wani daga cikin masu sarauta yana cewa ka fi dacewa da ita fiye da sauran.” MJ ya sunkuyar da kai, ya ce: “Na san hakan. Amma har yanzu zuciyata bata saba da cutar da amana ba. I promised to protect her, not to touch her.” Sarki ya dan lumshe ido: **“Good. Amma idan zuciya ta fara jin wani abu, ka gaya min — kafin duniya ta gane kafin kai.” "In sha allah ranka shi dade" daga haka ya mike ya bar gurin. Masarautar tana da tsarin da ba kowanne zai iya jurewa ba. Duk inda Baby ta wuce, idan ba kallon mamaki ba, to kallon tsana ne ke binta. Amma duk da haka, MJ bai bar hakan ya tsorata shi ba — balle ya rage kulawar da yake mata. Wata safiya kamar kowace, Baby na tsaye a bakin gado tana kokarin daura ɗamarar jakar makaranta, sai MJ ya shigo da murmushi. "Let me help you with that, princess." Ya durƙusa ya ɗaura mata ɗamarar, sannan ya gyara zip ɗin rigarta da hannunsa a hankali. Sai ya dafa kanta kamar yadda ake shafa albarka. "You’ll do well today, I can feel it." Baby ta gyara tsayuwarta, ta zuba masa ido, sai ta ce a hankali: “Thank you… daddyna.” Ya ɗan lumshe ido cikin jin daɗi. Wannan kalma "daddyna" ta fi masa komai. Kamar kalmar da ta tabbatar da alkawarin da ya ɗauka shekaru baya. Yana kaita makaranta da kansa. Hatta idan yana gajiya, ko yana da taron masarauta, Baby na da fifiko. Suna zuwa tare, suna dawowa tare. to bayan wani lokacin MJ ya je ya dakko baby daga makaranta ,suna dawowa yaga 'yan matan masarauta sun tsaya a kofar ɗakinsa — su Hajja Zuwaira, Hauwa’u da Salamatu. Suna kallon Baby da dariya mai ma’ana. "Oho! Ga sarkin uwa da diyarshi sun dawo." "Ai kamar ita ce ‘yar ce da za a raina mu da ita nan gaba!" Zuwaira ta ce da ihu kamar tana barkwanci amma Baby ta fahimta. Kamar yadda MJ ya fahimta. Amma MJ ya daure fuska. “Zuwaira, if I ever hear that again, even jokingly — I’ll report you to Daddy.” Zuwaira ta yi dariyar rainin hankali, amma ta ja jiki. MJ ya kama hannun Baby suka wuce ciki. --- °°′°°°°°°°°°°°°°° Washe gari Baby ta shigo ɗaki da kuka. MJ yana duba wasu takardu ne, ya juyo da sauri. "What happened? Did someone hurt you?!" Ta girgiza kai tana sharce hawayenta, ta ce: "No… amma daddy jini Yana fito… daga… daga can…" MJ ya dafe kansa. Yana matukar sanin wannan lokaci zai zo, amma bai shirya ba. Bai da wata mace kusa da su da zata koya mata ba. Yana tsaye cikin rudani,gashi Karo na uku kenan Yakasa fahimtar da ita tunda yanzu ita TA girma b yarinya bace, sai ya kira mahaifiyarsa. --- Mahaifiyar MJ, Hajiya rasheeda, ta iso da sauri. Da zarar ta fahimta me ke faruwa, ta rungumi Baby da kulawa da tausayi. "Kar ki ji komai yarinya… wannan alama ce kina girma. Zaki zama mace mai daraja." Ta dubi MJ ta ce: "Kai kuma, ka tsaya gefe. Wannan aikin mata ne." MJ ya yi dariya da sauke ajiyar zuciya. ya ce “Alhamdulillah, an ceto ni.” Daga wannan rana, Hajiya rasheeda ta fara ba Baby darasi kan yadda mace ke girma da tsafta. MJ kuwa ya rage shiga lamarin jikinta kai tsaye, amma soyayya da kulawarsa sai karuwa suke. --- Kulawa Mai Narkar da Zuciya Kullum MJ ke ɗakko ta daga makaranta da kansa. Idan yana da lokaci, yana jiran ta fito. Idan ba zai iya ba, sai ya aiko da wani amintaccen masarauta. Amma kullum da ta dawo, tana samunsa a gida da ruwa mai sanyi da ’ya’yan itatuwa. Yana karanta mata littafi, yana mata lacca akan karatu, rayuwa da juriya. “Your mind is your sword, Baby. One day, the world will try to cut you — but your mind will protect you.” --- *Bayan wasu kwanaki* Wata rana da suka dawo daga makaranta, Baby ta buɗe jakarta tana neman wani takarda, sai MJ ya lura tana ta kai-da-kawo cikin ɗan rudani. “Where’s your assignment?” “It’s... it’s not here,” ta ce da murya mai rauni, “Salamatu ta cire min shi aji tana cewa 'ya'yan karuwa ba sa karatu.'” MJ ya dafe kansa, zuciyarsa na tafarfasa. Bai yi magana ba sai da ya juyo gareta, ya zauna a gefenta, ya dafa kafaɗarta. “You are not what they call you, Baby. And you will never be. Your name is dignity.” Ya fice daga ɗakin, zuciyarsa cike da tsawa. A cikin dare, MJ ya rubuta wasiƙa zuwa ga shugaban makarantar da kwafin ta zuwa ga mahaifinsa, Sarki Umar. Washegari Salamatu ta samu kiran gaggawa daga gidan Sarki — kuma daga wannan rana, an dakatar da cin zarafin Baby a makarantar. --- Duk da cewa Baby tana rayuwa cikin masarauta, tana ci da 'ya'yan sarki, tana saka irin tufafin ’yan masarauta — amma ba su taba yarda da ita a ransu cewar ita 'yar masarauta bace. “Yarinya mai dogon buri,” “Shi MJ ya raini kansa wallahi,” “To in da ce shi ba dan Sarki bane fa?” Wannan maganganu na yawo cikin masarautar, musamman daga matan sarki da sauran dangin sarauta. Amma Baby ba ta ma sanin hakan gaba ɗaya — MJ ya ɓoye mata komai. Kullum sai ya saka dariya a fuskarta, ya boye mata gaskiyar wuta da take ƙone masa zuciya. --- ✅ Wata rana, Hajiya rasheeda ta kira MJ da Baby. Sun zauna a ƙaramin daki, wuri mai kamshi da natsuwa. “Baby,” ta ce da ita cikin tausayi, “zaki fara shiga duniya mai wahala. Wannan masarauta ba gidan ƙauna ba ne — idan ba da zuciya ba, zaki ɓata rai. Amma karki taɓa jin kanki ƙarama ce. Kin fi kowa a nan, saboda kana da wanda ya tsaya miki fiye da zuriya — ƙauna.” Baby ta juya, ta kalli MJ. MJ kuwa ya ce: “Idan duniya bata karɓi ki ba, ni zan yi mata dole.” Hajiya rasheeda tayi murmushi a zuciyar ta tace "yaro kenan ,lallai har yanzu bakasan bakasan makirci gidan sarautar sauba ba. --- Zuciyar Sarki Tana Da Ganuwa Sarki Umar na lura da wannan raino da MJ ke yi da kulawa ta musamman, wanda duk masarautar ta lura da shi. Yau ma kamar kullum sarki ya kirawo MJ domin ya kara fahimtar dashi akan jabaya da baby ,tun da dai watara na dolene. Baby zatayi aure su rabu, Kallon sa yayi cike da nuna alamun damuwa yace “Ina so ka fahimta, abee,” sarkin ya faɗa masa a wata tattaunawa ta sirri, “kamar yadda ka kula da ita yanzu, haka za ka dinga kare martabar masarauta idan wani abu ya same ta.” MJ ya sunkuyar da kai. “I know, Abba. Kuma zan ci gaba da kare ta — ko da kuwa hakan zai haifi hatsari.” Sarki ya ɗan murmusa da gefen baki. “To yanzu, daga yau, Baby zata koma makarantar gwamnati tare da jami’an tsaro — domin ta koyi rayuwar talaka da kima. Idan ta girma, zata dawo ta karanci tsarin masarauta.” MJ ya kasa amincewa da maganar abban sa, duk da zuciyarsa na ɗan cika da fargaba,wai yau babynsa ake wulakanta wa? ---"Abba kayimin aikin alfarma ,Dan Allah ina rokonka ka bar baby TA cigaba da zama Dani" Shiru mai martaba yayi kafin daga bisani Kuma yace " shikkenan kaje zanyi ruanni". *************** To Shekaru biyu sun shige. Baby yanzu yarinya ce mai wayo, mai nutsuwa. Tana karatu sosai, tana samun lambobin yabo. MJ kullum na zuwa makaranta ya dauko ta, ya yi mata nasiha, ya sayo mata ice cream ko juice. Idan dare ya zo, suna karatu tare. Wani dare MJ ya ce mata: “One day, you’ll understand everything. But for now, just promise me this...” “Wane abu ne, daddy?” ta tambaya tana dariya. Ya ce: “Just promise me you’ll never stop learning. Never stop dreaming.” Ta ce: “I promise, Daddy.” ---hannun ta ta dago ya kawo nasa hannun Sannan tayi murmushi tace " inama kowa zai samu mahaifi kamarka " murmushi MJ yayi batare da ya sake cewa komai ba ---Daren ya lafa. Hasken fitilar dakin karatu yana dumi kamar zuciyar MJ. Baby ta kwanta bisa kujera, kanta a kafadarsa, hannunta sanye da zoben roba da MJ ya saya mata ranar ta ci nasarar farko. MJ ya shafa kanta a hankali, yana jin wani abu da ba zai iya fassara ba. Ƙauna ce — ba irin soyayyar masoya ba, amma irin wacce take zamewa fatalwar rayuwa. Ya ce da ita a hankali, yana kallon wata daga tagar dakin: “Someday... you’ll be everything you dream of. And more.” Baby ta ce da ƙasa da murya: “As long as you’re here to see it.” MJ ya lumshe ido. Bai ce komai ba. Amma zuciyarsa na magana: "Ko ba ni da damar rayuwa, zan bar miki mafarkin da zai tashi da safe." --- RANAR KARRAMAWA — Washe gari, masarauta ta cika da jama’a. Wani babban wuri an kawata shi da tutocin masarautar. Muryar masu watsa shirye-shirye na yawo a cikin rediyo da talabijin. Kafin Baby ta fito, MJ ya taimaka mata da gyaran rigarta — rigar royal blue, mai ado da zinariya. Ya saka mata ɗan karamin sarkar wuya da rubutun "Shine Bright." Ya ce: “Today, you speak for every girl that ever felt invisible.” Ta ce da nutsuwa: “I’ll speak for me… and for you.” Suna isa wajen taron, ido ya koma kansu. Baby da MJ — mahaifi da 'ya — wanda ba jini ya haɗa su ba, amma zuciya.ta hadasu Wajen jawabinta, Baby ta tsaya gaban jama’a. Ta ɗan girgiza kafadarta. Ta kalli MJ a gefe — wanda ke murmushi, yana daga yatsarsa alamar "Na yarda dake." Sannan ta ce, da ƙarfin murya mai natsuwa: “Ni ba jini na sarauta bane. Amma ina da zuciya kamar kowacce ‘ya mace. Ina da mafarki kamar kowanne ɗan adam. Kuma yau na tsaya anan... saboda wani mutum ya yarda da ni kafin na yarda da kaina.” Jama’a suka yi shiru. Sai ta cigaba: “Wanda ya ce min ilimi ne garkuwata. Wanda ya ce min ƙauna ba takalmi ba ce da ake cirewa — ita ne hanya. Kuma yau... na zo ne in ce: ‘A ƙaunaci yara, a koya musu mafarki. Su ne masarautarmu ta gobe.’” Ƙarshen jawabin ya jawo tsit. Sai kuma tafi — tafi mai ƙarfi, har da hawayen wasu, musamman daga mahaifiyar MJ da ke zaune a bayan kujerar sarki. --- Bayan an gama taro, MJ ya zo ya rungume Baby sosai. Ya ce da ita: “You made me proud. You made me... complete.” Ta ce da murmushi: “Because you made me possible.” ---Tunda Baby ta kammala jawabin nata a wancan rana, abubuwa sun fara sauyawa a cikin masarauta. Ana girmama ta a bainar jama'a, amma a bayan-gida, kalamai masu zafi na yawo kamar iska mai ɗauke da ƙura. Zuwaira da ‘yan uwanta mata guda biyu — — su ne aka fi shirya wa MJ tun shekaru da suka wuce. Amma yanzu, gashi Baby tana ja da MJ cikin kulawa da girmamawa, sai dai wannan ba karɓa ba ne a idanunsu — zubar da daraja ne. Zuwaira ta ce wata rana cikin ɓacin rai, yayin da suke zaune a gefen harabar masarauta: “Ke da aka dauko daga titi, ke za ki zo ki tsaya gabanmu a dakin sarauta? Wallahi duniya ba ta da adalci.” Nafisa ta ɗan hara baki: “Ai ba kowa ne ya san ainihin asalinta ba. Su dai suna gani kawai MJ na kula da ita. Amma mu muna ganin bakin ciki ne — ya mayar da masarauta gidan reno.” Yagana ta ce da dariya mai cike da cin fuska: “Kuma idan ta girma fa? Me zai hana ya ce zai aure ta? Sai ace ita ce aka tanada tun daga haihuwa — ciki da goyo — a matsayin matar sarki!” Suka yi dariya, amma babu dariya a zukatansu. Tsana da kishi ne ke cin su. --- Ita dai baby batace musu komai ba, sai da ta shiga dakin Sannan ta shiga goge hawaye. Wasu lokuta idan Baby ta yi wani kuskure, ko da ƙanana ne, to gori zai biyo ta kamar guguwa. Wata rana, tana gefen wani katafaren bangon makarantarsu a cikin masarauta, tana karanta littafi, sai Nafisa ta zo da wasu ‘yan mata biyu, suka tsaya suka kalleta. “Hmm… ke da ya Mujahid ke muku wa'azi kullum. Ashe duk wannan wayon sai kike rubuta answer a jikin tafin hannu?” ai kamata yayi ki rubuta a kokon zuciyar ki shine Zamu tabbatar da soyayyar ta Kai soyayya ". Baby ta ɗago kai cikin nutsuwa, ba ta ce komai ba. Sai Yagana ta ƙara da karfi: “Mu mun san irin ki. Kuma ba girma ko lambobin yabo ne zasu mayar da ke yar masarauta ba. Ke dai rainon ya Mujahid ke miki — ba ƙima ba ce hakan, Ton da yanzu har TA Kai takawo daki Daya han yanzu kuke kwana". Zuwaira ta karɓa da sakin baki: “To i ai, kamar yadda aka gina ta da kulawa, haka za a rushe ta da haƙiƙa. Wannan masarauta ce fa, ba gidan yara marasa gata ba.” Baby ta ja numfashi. Ta mike. Ta ce cikin kwanciyar hankali, amma da ƙarfi mai tasiri: “Kuna ganin raino ne. Amma ni ina ganin gini ne. Wanda ake yi da so, da hakuri, da tarbiyya. Kuma ko kun raina ni, ban raina kaina ba.” Sannan ta juyo ta tafi, zuciyarta na cike da bakin ciki, amma tana ɗauke da darajar kalmomin MJ da mahaifiyarsa: “Never stop learning. Never stop dreaming. Kuma kada ki taɓa barin su su rushe ki da kalmomi.” --- Daga nesa MJ ya gan ta tana dawowa daga wannan fushin. Ya tare ta a tsakar hanya. Ya kalli idanunta. “Waye ya taɓa miki zuciya?” Ta ce da murmushi mai rauni: “No one, Daddy. They can’t touch what they can’t reach.” Ya janye wata goge tears daga gefen idanunta. “Don’t let anyone measure your worth by your roots. You are not what they think — you are who you decide to be.” Zuwaira ta ɗauki alkawari a zuciyarta: “Zan gano asalin wannan yarinyar. Ko da sai na dauki rana da dare, zan tona sirrin da zai kifar da ita.” Kuma wallahi Indai ina raye sainaga bayan baby Ta fara tuntubar tsofaffin bayin masarauta. Wata rana ta je dakin tsohuwa Halimatu — wata tsohuwa mai zane, wadda take zaune tun zamanin Sarki Balarabe, kakansu MJ. A cikin shakku da kishi, ta ce: “Tsohuwa, kin san wata yarinya da aka kawo masarauta fiye da shekaru bakwai da suka wuce? Wadda MJ ya rike kamar nasa?” Tsohuwa Halimatu ta tabe baki, sannan ta zuba mata ido. Da wata murya mai cike da hikima da zafi, ta ce: “Ke da baki san asalin ki ba, kina son sanin asalin wata? Ki farka daga mafarki, ‘yar sarki. Wannan yarinyar da kike tsana, ita ce silar zaman lafiya a cikin zuciyar MJ. Kuma gaskiyar haihuwarta... na da nauyi fiye da abin da kike tunani.” Zuwaira ta kurma ido, zuciyarta na dukan tamkar ana bugunta da tabarya. “Tsohuwa... kina nufin akwai sirri?” “Akwai. Amma sirrin nan, idan ya fito, ba ke kadai zai jefa cikin duhu ba. Masarauta ma ba za ta tsira ba.” Zuwaira ta fita a ruɗe, amma zuciyarta na ƙonewa da son sani da kuma ƙoƙarin ganin Baby ta faɗi. --- A BANGAREN BABY... Baby ta fara fahimtar kishi, zagi, da gorin da ake mata. Amma ba ta daina daraja MJ ba. Ta fara tambaya a zuciyarta: “Me yasa mutane basa son na? Me na yi musu?” Sai MJ ya kama hannunta wata rana, bayan ya kawo ta daga makaranta, suka zauna a bayan falo. Ya ce: “Baby, kin san wani abu? Akwai mutane da ba sa son haske saboda yana nuna inuwa a gare su. Amma ke... kina haskaka.” Ta ce da dariya mai ɗan ɗaci: “To idan ina haskaka, me ya sa suke so su kashe fitilata?” Ya ce: “Saboda suna jin tsoro. Tsoron wanda suka raina, ya wuce su da gaskiya.” Sannan ya ce mata: “You don’t have to fight them. Just grow. Haske ba ya takura — yana tsage duhu ne kawai.” "Uhm wataran daddy idan kana magana kana bani kwarin gywa sainaji kamar nagama dacewa a rayuwata" "Kidaina kokonta baby kinma dace da dacewar ubangiji insha Allah kinfiso dole su kyleki, ayanzu kinsoma zama mace Kuma suna son suga suncutar min dake sabi da ke basa,ar su bace kaunata ---🫂🫂🫂🫂🫂🫂🫂🫂🫂 --- Shekara na 14 kenan da MJ ke rainon Baby. Yanzu tana da shekaru 15,kyawunta yana ƙara bayyana fiye da kullum. Idan ta wuce, idanu na bisarta. Koda kuwa mutane suna ƙoƙarin ɓoye sha’awar su, murmushinta da ɗabi’arta na jan hankalin duk wanda ya kalle ta. A makaranta, ƙawaye sun fara fadin: cewar wanna yarinyar idan sukai wasa zata janyewa kowa saurayinsa ,basu da aiki kullum cikin gulmarta ,to yauma kamar kullum suna zaune suna cewa: “Baby ke nan, wadda ko ɗan Minista ya kalle ta sau biyu!” "Hmm kadai bari abin Yana batamin Rai ,daga gefansu sukaji wani saurayi na fadawa a bokin SA cewar :... “Ni zan aika mata gift jibi, wallahi. Koda MJ zai ƙone!” " Kai haba abokina wai da gaskiya kake? " "Ina Maka wasane Daman" gaba kidaya su suka tafa lokaci guda. To tafiya tatafi girman baby na daukar hankalin kowa a yanzu har takai ta kawo Har ‘yan masarauta suna aika sako da kyaututtuka — iPads, zoben zinariya, katunan soyayya... Amma Baby tana karɓa da godiya kawai, ba ta amsawa da ƙauna. Domin ita aganina Babu Wanda zai sota a duniyarnan fiye da Daddynta. ****** Wani rana suna zaune a harabar gidan masarauta, MJ na gyara mata Dan kwali, tana dariya, tana zuba masa kwantar da hankali. Sai wayar Baby ta yi kara. Tana duba, sai murmushi ya bayyana a fuskarta. “Wa ne ya turo miki?” MJ ya tambaya, da murya mai sanyi. Ta ce, “Yayan wani classmate ɗina ne... ya turo min poem wai saboda birthday dina.” MJ ya yi shiru na dan lokaci. Ya kalli hannunta, sai ya ce da ƙasa-ƙasa: “Ni ban iya rubuta poem ba. Amma nasan duk poem da za a rubuta, ba zai iya bayyana yadda nake ji ba idan kika tafi da wani, Kuma ta itana har yasan kwanan watan haihuwarki?" Baby ta dubeshi. Zuciyarta ta buga da sauri. Amma kafin ta yi magana, MJ ya sake murmushi — murmushin ɓoye gaskiya. “Ke fa karatu, ba soyayya. Ko kin manta?” "Ban mantaba daddy kayi hakuri insha Allah bazan sakeba" daga haka ya kwantaeda kanta kan cinyarsa ya shiga duba kunnenta Yana cire mata datti. ******* Sarki Umar....... Sarki ya fara lura. Wani dare, ya kira MJ cikin ɗakin karatu. Tana kwance, MJ na shirin fita daga dakin ta. Sarki Umar ya ce masa: “Abee… kana rainonta sosai. Kana kyauta mata sosai. Kana duba ta fiye da yadda uba ke duban ’ya.” MJ ya lumshe ido. Ya ce: “Abba, ita ce farin cikin zuciyata. Amma na sani, babu aure tsakanina da ita. Na ɗauke ta tamkar ’yata ne.” Sarki ya girgiza kai: “Ba ina cewa kana son ka aure ta ba. Amma ita tana girma. Kuma idan wani ya so ta — ya fi ka dacewa da ita — kada ka tsaya a gabanta. Ka tuna da sharadin da aka yi, abee.” MJ ya lumshe ido. “Na tuna. Amma zuciyata... tana da wahala ta yarda da hakan.” Sarki ya yi ajiyar zuciya, ya ce: “Kayi ƙoƙari ka yanke kanka daga zuciyarta kafin lokaci ya kure. Ko kuma ka bar zuciyarta ta yanke ka.” Kai kawai MJ ya nunnar kana yadan Yi murmushin karfin hali yace "in sha allah Abba, za a kiyaye. Daga haka sarki Umar yayi gaba Mujahid ya koma cikin dakin. 🕊️ RAINON YARO Chapter 7, --- Babyna zaune a daki ta fara jin wasu raɗaɗi a zuciya. Tana tambaya: “Me yasa duk abinda nake jin game da daddy... ba irin na ɗa da uba bane?” Kullum cikin wanan tambayar takewa kanta Amma tana ɓoye komai a fuskarta — sai dariya, sai ladabi, sai kwanciyar hankali. MJ kuma yana ƙara fuska, amma zuciyarsa na ƙonewa a hankali. Yana tare da ita, amma kamar an raba su da wani bango da ba a iya gani. WATARANA..... Wata rana a makaranta, wata sabuwar mota ta tsaya — black SUV mai tinting da tambarin jami’an gwamnati. Kowa ya tsaya kallon wanda zai fito. YARO NE. Tsawo, fari, sanye da school uniform, amma yana da salon shigowa irin na manya. Yana da karsashi da walwala. Sunansa: HAFID. Hafid ya kasance ɗa ne ga wani sanannen dan siyasa a garin, kuma ya canja makaranta zuwa inda Baby take karatu. Bayan sati biyu kacal… kowa ya lura da yadda yake kulawa da Baby. Yana kokarin zama kusa da ita a dakin karatu. Yana rike mata littattafai. Wani lokaci yana dan raira mata waka idan suna kan break. MJ YA LURA DA HAKAN A RANAR TARON YABO. Ranar da Baby ta samu Award na Best Student, MJ ya shirya sosai — ya sa blue shirt da hula mai mutunci. Ya zauna a bango yana kallonta tana karɓar kyautarta. Hafid yana gefenta, ya sa mata zobe na gem-stone da cake mai rubutun "To the best mind I know." MJ ya matso kusa da ita, yana murmushi, ya ce: “Wow, look at you. Kina haskaka kamar rana yau.” Ta ce, “Nagode Daddy.” Ya ce, “Ki zo mu tafi gida.” Sai Hafid ya ce da dariya, “Uncle, zamu je café ɗin makaranta kafin su tafi.” MJ ya lumshe ido. Ya ce da nutsuwa: “Ita yarinya ce. Ni ne ke da alhakin ta.” Sai ya juya ya kalli Baby, yana ce mata: “Let’s go. You’ve done enough celebration today.” Ta amsa da “Okay Daddy…” Amma kafin ta tafi, ta kalli Hafid tana dariya. Hafid ya ce: “Zan aiko miki da notes dinnan da kika tambaya.” MJ bai ce komai ba. Amma zuciyarsa ta fara girgiza. Yana jin wani abu yana tashi a cikinsa — kishin da ba ya iya furtawa. --- ZUWA GA SARKI… Sarki ya kira MJ, yana zaune cikin natsuwa. Ya ce: “Kana jin haushi ne yanzu?” MJ ya ce: “A’a, kawai bana son wani ya kawo mata rudani a karatu.” Sarki ya kalle shi. “ayanzu baby ta Kai matakin da bazaka iya hanata kula samariba tun da dai ita macece dole gidan wani za a kaita a matsayinka na mahaifinta farinciki yakamata kayi 'yarka tana da farinjinin da za a sota har a aureta" "Abba gidan wani fa?" Ya fada idonsa ya kada yayi jajur . "Eh ko Kai zaka aureta ne? Yayi maganar cikin tuhuma. "A,ah Abba Amma ..... "Amma me tashi ka bani guri Abee kafin ranka ya baci." Babu musu MJ ya mike jiki Babu kwari ya fita Yana fita ya huce lanbun masarauta sabi da yau su Baby suna picnic na makaranta a cikin masarauta. Sarkin masarauta ya bada izini, don haka an ware wuri na musamman ga dalibai masu hazaka da iyayensu ko guardians su taru. Baby ta saka farin rigar ‘flower gown’, kanta ya sha tsaf da kitso mai kwalliya. MJ ne ya taimaka mata kwana biyu da suka wuce wajen gyaran sumar kanta. MJ ya zo daukarta . Yana sanye da kayan casual masu kyau — t-shirt da wando, gashinsa yana sheƙi, kamar bai da damuwa, amma a zuciya, mamaki da fargaba sun hade. Yayin da picnic ya fara, dalibai na rawa, wasu na wasanni, wasu suna cin abinci. Hafid ya zo cikin sabuwar kaya, ya karaso wajen Baby da MJ. Yana dariya yana sanye da hular gwaninta. "Look who’s glowing today — you again," ya ce yana kallon Baby. MJ ya zuba masa ido. Bai ce komai ba. Hafid ya ce da MJ: "Uncle, zamu ɗan ɗauki hoto tare da Baby mana… group picture ne." Baby ta dubi MJ, kamar tana neman izini. MJ ya ce da murya mai laushi: "Go ahead." Sun ɗauki hoto. Amma MJ yana gefe, yana karanta motsin Baby da na Hafid fiye da hoton kansa. Zuciyarsa na harbawa da tausayi, da kishin da bai iya furta ba. --- Can defe guda Kuma ... Zuwaira ta kalli Baby tana dariya da Hafid, sai ta ce: “Kalla yanda take dariya kamar budurwa da saurayi, gashi Ya Mujahid na kallon su shiru — yana mugun son yarinyar nan wallahi.” Qawarta ta ce: “Ba da ban ba, sai na zubar da mutuncinta a gaban dukan su…” Zaro ido zuwaira tayi tace ",me rufamini asiri kekuwa mai yasa" "Sabi da kowa sonta yake --- ********************** MJ ya ce da ita a hanya: “Kinji dadin picnic din?” Baby ta ce da murmushi: “Ina jin dadin duk inda kai kake.” MJ ya kalle ta, yana jin yadda zuciyarsa ke ɗaure da zuciyar baby. “Kada ki bari duk wanda ya ɗora miki tunani da ya zame miki nauyi. Karatu ki maida hankali… ki kare hankalinki,da mutunci ki Baby.” Ta ce: “To Daddy. Amma kai fa? Kana jin dadin ganin mutane suna tare dani?” MJ ya yi shiru. Ya ce a ƙarshe: “As long as you’re safe… I’m fine. Even if it hurts.” a haka har suka karasa cikin masarautar. --- 💞💞💞💞💞💞 Washegari, Sarki ya sake kira MJ. Ya ce masa: “Abee, kana yin ƙoƙari. Amma wannan yarinya… ta fara girma. Kuma idan baka kula ba, mutane za su fara zargin ta, ko kuma kai.” " Abba to meyasa zan a fara zarginmu?" Sabida tayi girman da Yakamata ku rabu wanna kualwar da kake bata mijinta ne kadai ya kamata ya bata" “A yanzu dai, ka ci gaba da nuna kulawa — amma ka fara janye kanka a hankali. Saboda zuciyar mace idan ta fara buɗe ido, zata fara kallo fiye da kallon uba kawai.” MJ ya ce da siririyar murya: “Abba… zuciyata na da amanar Baby fiye da nawa. Zan rene ta har sai ta fahimci duniya da kanta.” Sarki ya ce: “To ka cigaba da hakuri. Idan rana ta fito, kai za ka fi jin zafi fiye da kowa.” To yauma kamar kullum a makaranta cikin rana mai ɗumi, makarantar Baby ta gudanar da inter-house sports competition. Akwai taron manyan mutane, iyaye da jami’an gwamnati. Baby na cikin ‘yan kwallon tseren mita 100, saboda ta kware wajen gudu — daidai da lafiyarta da horon MJ a gida. Zuwaira da kawarta Ameenah, sun shigo makarantar cikin kaya masu ƙyalli, ba don su kalli gasar ba, sai don su jefa ruwan zafi a zuciyar Baby. “Kalla ita can. Yarinyar nan da ko ba MJ ba da tuni bata wuce ragowarmu ba.” Ameenah ta ce: “Mun shirya mata yau. Wallahi zamu nuna wa kowa cewa wannan ‘yar banzar da MJ ke raino — bata da mutunci.” --* Bayan an gama tsere, Baby ta samu nasara — ta lashe zinariya. Ana nan ana murna, sai wata karamar yarinya ta zo tana kuka. An tambaye ta me ya faru? “Waccan yarinyar Baby ce ta sace wayata! Na ajiye ta a bag dinmu tana kusa... yanzu babu ita, babu waya!” A hankali ake kara jefa zargi — wasu daliban da ke kishin Baby suka fara cewa “ai dama can tana jin kamar ita ce komai a makaranta, ta saba dauke dauke.” --- MJ, wanda ke gefe da sauran masu kallo, ya ga yadda Baby ke rikicewa. Yana kallonta ta kururuta: “Wallahi bani na dauka ba! Ban ma san da wayar ba…” Zuwaira ta murɗa murmushi. Ta ce: “Ehhh... yarinya mai gaskiya fa ba ta kuka. " MJ ya shigo harabar gasar. Bai ce komai ba. Ya tsaya a gabansu, ya kama hannun Baby, wanda hawaye ke shirin gangarowa. “Come with me.” “Daddy... suna zargin—” “I know. But your eyes are clean. That’s enough for me.” Yana rike da hannunta suka bar wajen. Kowa ya zuba musu ido. Wasu suna mamaki, wasu suna harara, wasu kuwa suna jin haushi — amma MJ bai kalle su ba. --- A GIDA… Da dare, Baby na zaune kusa da MJ. Ya rike hannunta, yana goge mata hawaye da tawul. “Idan duniya ta juya miki baya, ki kalli ni. I will always be your front.” “But I don’t want to disgrace you, Daddy... suna cewa ni ban dace da kai ba…” MJ ya dafa kanta, ya furta da nutsuwa: “You don’t have to match me, Baby. You only have to match your truth. And I know your truth is pure.” ****** --- SARKI YAJI ABINDA YA FARU… Da safe, MJ na shirin kai Baby makaranta, sai aka kira shi a fadar Sarki. Sarki ya kalle shi da tsantsar basira: “Abee... lokacin da yarinya ta fara fuskantar ƙiyayya, to zata fara girma da karfi. Amma ka san me ke cutar da mace da wuri? Idan ta dogara da soyayya kafin ta girma da zuciya.” “Kayi hattara. Zuwaira da irinta... ba ƙiyayya suke ba — kishin rikonka suke.” MJ ya ce: “Zan kare Baby, ko da kuwa sai na hana zuciyata kwanciya. Tana min kamar wani bangare na rayuwa wanda babu wanda zai iya cike shi. Kayi hakuri Abba ammani bazan taba iya zuba ido ina kallon masu chutar da baby ban tsawatar musuba, da ace zuwaira zata Gane abin da zatai na sota, to ta kaunaci baby nikuma zan kaunace ta Amma bawai ta kulla mata sharriba" MJ Yana gama fadar haka ya bar cikin fadar gaba daya. """"""""""""""""""🫂 Bayan dawowa daga makaranta, Baby ta zauna a gaban window tana kallon rana tana faduwa, tana rik'e da certificate ɗinta na zinariya, amma idanunta cike da tambayoyi da damuwa. MJ ya zauna gefenta da cupcake a hannu, ya ce da dariya: “You know what we do when the world frowns at us?” Ta girgiza kai cikin rauni. “We smile back. Amma ba dan muna jin dadi ba — sai don mu nuna musu we’re stronger than their hate.” Baby ta kalle shi, sannan ta ce cikin hankali: “Daddy… yaushe zan daina jin kamar bana cikin nasu? Kamar bana daga masarautar nan?” MJ ya janye gashinta daga fuskarta, ya ce a hankali: “Zaki daina, Baby. Lokacin da kike d'aukan kanki a matsayin tauraruwa, ba dutsen da zai iya hana ki haskaka.” Gyda Kai kawai baby tayi hadi da rausayar da Kai ta Dora kanta a kan kafadar MJ Tana sauke ajiyar zuciya. ---*************** WATA SABUWA... MAHAIFIN ZUWAI RA YA DAWO MASAURAUTA DA ZAMA. A lokacin da Baby ta fara samun karbuwa daga wasu malamai da manyan makaranta saboda kokarinta, sai mahaifin Zuwaira — Alhaji Faruq — ya shigo masarauta da korafi. “Mai martaba Sarki, a yarda da za’a rika dora yarinya ba asalinta ba, bisa manyan mukamai a makaranta da masarauta? Wannan zai lalata tarbiyyar ‘ya’yanmu.” Sarki Umar ya kalle shi, ya dan tsaya kafin ya ce: “Ka tuna cewa ba jinin sarki ke sa mutum mutunci ba — halinsa da zuciyarsa ke gina shi.” “Yarinyar da kake magana akai — Baby — na fi yarda da ita fiye da yawancin yaranmu da aka haifa da zinariya.” Alhaji Faruq ya fita da jin haushi. Ya hadu da diyarsa Zuwaira a waje, ya ce: “Idan baki hana wancan yarinyar nan taka kasa ba, to zan hana ki gado a gidana.” Zuwaira ta dafe ƙirji da ɗan mugun murmushi. “Don’t worry, Abba. She’ll taste salt without soup.” Kai kawai abban ta ya daga ya ya juya ya tafi tabi bayansa da kallo. --- Zuwaira da abokanta suka fara tsananta mugunta. Suna jefa Baby cikin gori a makaranta da gida. A wani lokaci har aka boye mata littafinta na jarabawa. Sai dai duk da haka, Baby ta ci gaba da samun matsayi na farko. MJ na lura da komai. Wani dare ya kira Baby ya ce: “Kinga... I won’t always be able to shield you. Amma zan koya miki yadda ake gina garkuwar zuciya. Ki tsaya da kafafunki, Baby. Don ba zaki iya gudu daga komai ba, watara na bazaki ganni ba dole ni ma zan mutu ,bazai zama kullum nine mai kareki ba.” “I’ll try, Daddy. I’ll try…” --- SHEKARUN GIRMA… KYAU NA BAYYANA Baby ta ci gaba da girma. Yanzu tana da shekara goma sha bakwai 17 wayonta da kwarjinta na bayyana. Komai nata ya cika da ladabi da kamala. A makaranta, kowane yaro na kallonta fiye da sau biyu. Har wasu malamai sukan ce: “Wannan yarinya, kamar Sarauniya ce da ba’a saka mata crown ba tukuna.” Samari ‘yan masarauta, da yayansu masu kudi, sun fara aiko mata da notes da gifts, amma duk MJ yana karantawa kafin ta karanta. Wani dare, MJ na goge mata kai yana mata kitso, sai ya hango wata love note daga ɗaya cikin yayansu Alhaji Faruq. Ya janye karyar murmushi, ya ce a hankali: “Yanzu sun fara rubuta miki wasikun soyayya?” “Na ce musu bana sha’awar soyayya. Ban san me soyayya take nufi ba. Ni dai ina da kai, kuma hakan ya ishe ni.” MJ ya kalle ta. Idanunsa sun kada, amma da murmushin zuciya. Ya ce: “That’s all I needed to hear tonight, Baby.” 🥺🥺🥺🥺🥺🥺🥺🥺🥺🥺🥺🥺🥺🥺 A wani dare mai duhu da hazo, mahaifiyar Zuwaira — Hajiya Sa’adatu — ta ce da diyarta a sirrance: “Zuwaira, idan da gaske kike son ki samu nasara, ki cire jin kai. Wannan yarinyar da kike bari tana daukar hankalin MJ? Kafin ki farka, zata dade a zuciyarsa fiye da rayuwar da kika yi tun kina cikina.” Zuwaira ta dafe kirji. Zuciyarta cike da kishi da azaba. Ta ce: “Mama, ban san lokacin da ya fara jin ta fiye da ni ba. Amma ina so na ga karshenta.” Hajiya Sa’adatu ta saki murmushin mugunta. “To sai mu kai sunansa da nata... gurin boka. Zamu juya duniya, zamu juya zuciyoyi idan kin amince.” Murmushin mugunta zuwaira tayi tace" duk yadda kikace haka za ayi Momyna" --- 🕊️ RAINON YARO Chapter 8 Washe gari da sassarfa suka shirya tsaba suka dauki hanyar zuwa wajen boka , a cikin wani daji mai duhun gaske — boka Malam Gado. Ya karɓi hoton MJ yana dariya cikin mugun sauti: “Wannan saurayi, zuciyarsa cike take da tsarki da ƙauna. Amma zan shafa masa inuwa — yanda duk lokacin da yarinyar nan tazo kusa da shi, sai yaji haushi, kamar jini da toka.” “Za ta shanye hawaye — ki shirya, domin daga yau, duniya za ta juyawa Baby baya.” Malam Gado ya daga hayaki, ya fesa su akan hoton MJ da na Baby, sannan ya fadi wani zazzafan kalma: “Zuciyarsa zata rufe... idonsa ba zai sake ganinta da ƙauna ba. Sai dai tsana. da baƙin ciki...” Godiya sosai sukayiwa boka sanan suka aje tulinn kudin da sukazo da shi, sanan suka koma gida cike da tsantsar farinciki. --- After two days 💍 Kwanaki biyu kacal bayan wannan dare, MJ ya dawo gida da fuskar da ba'a saba gani ba. Yana zaune a falo, Baby ta shigo da dariya a fuskarta tana dauke da wani zanen da ta yi a makaranta. “Daddy, kaga na zana mu biyu... ka gani?” MJ ya kalleta kamar wata ƙasa ce ke neman tsage masa fuska. Ya ce da ƙasƙanci: “Na ce ki barni! Ki fita da wancan shashancin banzan naki!” Baby ta tsaya cak, kamar wuta ta kone mata kafa. Hannunta na rawa, idanunta sun cika da mamaki. “Daddy… me nayi maka?” MJ ya miƙe da fushi, ya yi wurgi da zanen: “Kin takurani! Kin dame ni! Ki fita ki barni!” Baby ta fita daga falon tana kuka, zuciyarta na karaya, kanta na juyawa. Tun daga wannan rana, MJ ya daina mata kulawa. Ko kallonta baya yi. Kullum fuska tamkar yana kallon abinda yake ƙyama. ---**** A makaranta, ko da sauran yara suka fara ganin MJ yana guje mata, su ma suka fara tsanarta. Wasu sun fara mata dariya, wasu suna kiranta “marainiya mai bakin tabo.” Har wasu malamai suka fara janye kulawarsu, suna nuna kyama da rashin yarda da ita. Duk da haka, Baby ta ci gaba da kokari. Amma wata rana, bayan sun dawo daga makaranta, ta tsaya a bakin kofa, tana kallon MJ wanda ke zaune a falo ba tare da kallonta ba. Ta ce cikin muryar da ta ƙarye: “Ka daina sona, Daddy?” MJ bai ce komai ba. Ya cigaba da kallon TV, kamar bai ji komai ba. Baby ta juya, tana tafiya cikin dare, hawayenta na gangarowa kamar ruwan sama, zuciyarta na faɗuwa, kamar bata san gaba ba. --- " Wani mugun asiri na iya juyar da zuciya, amma soyayya ta gaskiya tana da darajar da ko bokaye ba za su iya murkushe ta ba Kai Anya asirine Kuwa" baby ta tambayi kanta har ta isa dakinta Daren dai yadda taga dare haka taga rana sabi da damuwa. Baby ba ta da sauran kuzari. Duk safiyar da ta tashi, hawaye ne farkon kalmarta. Ba MJ ne ke tada ta zuwa makaranta ba. Ba MJ ne ke dakota ba. Ko lokacin da ta yi ciwon ciki a daren Juma'a, MJ ya zauna a dakin sa kamar ba komai ya faru ba. Zuwaira kuwa sai shagwaba take a gaban MJ, tana kawo masa abinci, tana matsa masa kafafu, tana bin umarninsa da murmushi. Amma duk da haka, MJ bai taɓa nuna cewa yana sonta ba — sai dai a ce ya fi nuna mata kulawa fiye da yadda yake yi wa Baby yanzu. Sai dai a fadar sarki, shiru ya mamaye zuciyoyi. Kowa yana mamakin sauyin MJ. Baby ta koma kamar ba a san da ita ba. Ko lokacin da sarki ya ganta zaune ita kaɗai a tsakar gida, yana jin wani irin zafi a zuciyarsa, amma sai ya janye. Ba zai nuna goyon baya a fili ba, domin ya sa sharadi... Dan a tunaninsa MJ Yana nuna ko in kula akan babyne domin tasaba da rashinsa watarana. --- A DARAREN JIYA. MJ na zaune a farfajiyar gida, yana shan iska. Wata rana baby ta taho a hankali da takunta mai nutsuwa. Cikin riga da siket na makaranta, kanta cike da damuwa da tambayoyi. Ta tsaya gaban sa. “Daddy…” ta ce cikin ƙasa da murya. “Ni nayi wani abu ne da ya ɓata maka rai?” MJ ya ɗago kai, yana kallonta kamar ba ya ganinta yadda yake ganinta da. Akwai ƙara da sanyi a idonsa — kamar ba zai iya amsa ba. Ya buɗe baki da ƙyar: “Kada ki kirani da Daddy. Ni ba mahaifinki bane.” Wannan kalmar tamkar sara mata aka yi da wuƙa. Baby ta runtse idonta, ta ce: “To... to meye ni a wajenka?” MJ ya ce da ƙarfi: “Ke? Ke ba komai ba ce! Kawai nauyi ne da aka dora min! Ammani ban saniki ba, Naga mahaifina Yana hadani dake ,kuma Yana tambayata ke bayan ni ban sanki ba, ki fita daga rayuwa ta". Ya daka mata tsawa hadi da tasowa kamai zai dake ta. Ta juyo da gudu, ta nufi ɗaki, tana kuka kamar rai zai fita. Amma bayan ta shiga, ta rushe da kuka a kan gado, tana faɗin: “Ba haka Daddy yake ba. Ba haka ba… Yana sona, wallahi yana sona. Me ya faru da zuciyar sa?” --- ZUWAIRA A gefe guda, Zuwaira tana kallon wannan fadowar, tana murmushi da girgiza kai: “Na gaya miki ba’a karɓar zuciyar da ba taka ba. MJ zai kasance nawa — ko da da kisa ne.” Mahaifiyarta kuma ta ce: “Ki kwantar da hankali. Boka yace duk wata ƙauna da MJ ke ji mata yanzu wuta ce. Sai dai kallo — babu tausayawa, babu kulawa.” --- A DARAREN KWANA GOMA BAYAN HAKA… Baby ta soma sauya hali. Tana shiru fiye da da. Bata sake dariya kamar da ba. Wani dare ta samu wata ƙaramar takarda, ta fara rubutu da tawada mai ɗumi da hawaye: “Dear Daddy... Na san wani abu ya faru. Ban san menene ba. Amma zan yi hakuri. Zan bar komai cikin hannun Allah. Zan girma. Zan koya. Zan jira — har ranar da za ka sake kirana ‘yar zuciyarka.” Ta ɗora takardar cikin litattafinta. Sannan ta kwanta da hawaye a idanu, amma zuciya mai fata. *Sarki Umar* Sarki Umar na zaune cikin dakin karatunsa. Ya buɗe wani tsohon littafi da aka buga a kasar Andalus shekaru da yawa da suka wuce. Amma ba littafin bane a ransa — zuciyarsa na nan wajen MJ da Baby. “Wannan yarinya… tana da wani irin haske. Amma yanzu ina ganin hasken yana dusashewa.” Ya kalli hoton mahaifiyar MJ da ke manne a bango. Sai ya furta: “Halinki ne ke jikin MJ. Amma ko zuciyarki za ta iya jimre da wannan azaba da Baby ke ciki? Kenason kina son baby to Amma meyasa ?.. sarki yayi shiru yanajin kodai yaje yasamu mahaifiyar MJ ya ji ko ita tasan mai ya faru a tsakanin MJ da baby har ya daina sauraronta. --- *School* A makaranta, Baby ta fara zama mai nisa da mutane. Duk da tana da ilimi, tana samun matsayi a ajinsu, amma sunan MJ na bibiyar ta — wasu suna cewa "Meye tsakani su da MJ?" Wasu suna cewa "Ai tana jin girman kai tunda MJ yana goyonta da can." Sai wata sabuwar daliba, Fareeda, ta matso gareta: “Kinyi kyau yau, Baby. Amma kin yi shiru sosai. Kin san me? Ina jin kamar akwai abu da ya dame ki.” Baby ta ɗan murmusa, ta ce: “Babu komai.” Amma Fareeda ta tsura mata ido. “ba Komai? To me ya sa idan MJ ya wuce kusa da ke, kina runtse ido kamar ki ɓalle da kuka?” Baby ta yi shiru. Amma zuciyarta na faɗin: “Kin ce komai… Amma kin fara fahimta.” --- A GEFE GUDA… BOKA NA RIKE DA HOTON MJ A DAKIN DUHU Boka ya kalli MJ da ido irin na sihiri. Yana kara tsafi da gumaka da turare. “Ka fara mantawa da ita gaba ɗaya. Za ka iya ganin ta ba tare da ka ji komai ba. Amma… akwai hadari.” MJ ya ce da murya mai sanyi: “Hadari?” Boka ya ce: “Idan zuciyarka ta taɓa tuna ta... asirin zai rushe. Kuma... kai zaka ji ciwo fiye da kowa.” MJ ya kalli ƙasa. Sai kawai ya furta: “Na rasa yadda nake ji yanzu. Komai ba shi da amfani. Kamar ni ba ni ba ne.” Murmushin boka kawai yayi yace "ai Daman bakai bane daga haka ya kara matse hoton MJ hadi da cigaba da tsafetsafen sa. --- A DAREN WATA LITININ… Baby na dakin karatu tana ɗan rubutu da yatsanta a jikin takarda. Ta rubuta: "Rai kamar ruwa. Kuma ni kamar jirgi ne cikin wannan ruwa. Amma daddy... kai hasken fitilar da ke kan ruwan ne. Ko da baka ganina a yanzu, ina can. Ina jiranka." Sai ta lumshe ido. Ta janyo rigarta, ta kwanta, tana mai jin numfashinta kamar wani zazzafan yaki a zuciya. --- A FADAR MASARAUTA... Sarki ya kira limamin fadar asirce. “Ina jin akwai wani abu mara kyau da ke faruwa a gidan nan. Wani abu da ya shafi MJ da Baby. Ka je ka nemo gaskiya — amma cikin sirri. Kada kowa ya sani.” Limamin ya ce da tausayi: “Zan bi komai da addu’a da bincike. Idan akwai sihiri, insha Allahu za mu bankado shi.” 🥺🥺🥺🥺🥺🥺🥺🥺🥺🥺🥺 Baby na zaune a dakin ta, kanta a jingine jikin window, tana kallon sama mai taurari. Amma ba taurarin take kalla ba – zuciyarta na karayin kuka cikin shiru. “Daddy... me na yi maka? Me ya sa ka barni da wannan shiru da yake cin zuciyata kamar wuta?” Kukan da take shanye ya hana ta magana, amma zuciyarta tana karanta kalmomi da MJ ya taɓa faɗa mata: “I will always protect you.” “I promise, Daddy.” Tayi shiru, sai kuma ta ɗago kai kamar wacce ta yanke shawara. “Na fara fahimtar wani abu. Kuma zan bi saƙon zuciyata, komai za ta fitar min da shi.” --- A MASALLACIN FADAR SARKI... Limamin masarauta yana cikin masallaci yana karanta ayoyi cikin nutsuwa. Sai ga shi ya ɗago kai da mamaki. “La hawla...! Akwai sihiri da aka nannade da wuta da ƙiyayya. Ba MJ bane ainihin laifinsa. Wani abu ne yana sarrafa zuciyarsa.” Ya tashi da sauri, ya nufi fadar Sarki. --- A FADAR ZUWAIRA... Zuwaira na zaune da mahaifiyarta a dakin su. Mahaifiyarta tana girgiza kai tana hurawa boka turaren sa da suka boye a cikin ƙamshi. “Idan har MJ ya ci gaba da mantawa da ita, sannu a hankali, za mu zama dole ga rayuwarsa.” Zuwaira ta ƙara kwafa da wulakanci: “Ai yanzu ma ya daina kulata sosai. Shi fa ba yadda na ke so yake ba — amma tunda ya daina kula da waccan, zan sami damar shiga zuciyarsa.” Mahaifiyar ta ce: “Amma ki kiyaye... idan sihiri ya kama zuciya sosai, ba zai san me zai so ba, balle wacce zai aura. Sahi dai gashi kamar shara.” --- MJ A DAKINSA... A dakin MJ, yana zaune yana karanta littafi. Amma ba ya gane me ke ciki. Sai kawai ya mike, ya kalli madubi. A cikin madubi, sai kawai yaga fuskar Baby — amma fuskar ba ta murmushi ba ce, ba kuma ta dariya ba. Fuskar da ta cika da tambaya da raɗaɗin jin ƙiyayya daga masoyi. MJ ya zabura — zuciyarsa ta yi wani irin bugawa. “Me ya ke faruwa dani?” Yayi wani numfashi mai nauyi. Ya zauna. Ya ɗauki wayarsa — sai ya duba hotonta da ya taɓa ɗauka ranar da ta samu kyautar karatu a makaranta. “Na manta da ke... Amma kuma... me yasa zanji wannan ciwon yanzu?” --- SAFIYAR RANAR ASABAR... Baby na zaune a lambun makaranta. Fareeda, abokiyarta, ta zo kusa da ita da takarda a hannu. “Na samo miki bayanin wata tsohuwa da ke cire asiri a wajen gari. Akwai labarin cewa tana iya tantance wanda aka tsare da sihiri. Idan baki so kowa ya je — mu je mu duba da dare.” Baby ta girgiza kai. Cikin ranta ta furta: “Daddy... ko da ba ka gane ni yanzu ba... zan nemi hanyar da zan dawo da kai.” Afili Kuma tace "nagode sosai kawata da taimakon ki a kaina duk da cewar ban fadamiki abin dayake damuna ba, sai da kikai duk yadda Zaki kika nemo abin da ke damuna, daskiya ke kawar kirkice. ---Misalin ƙarfe 9:00 na safe Fareeda da Baby suka tsinci kansu a cikin wani daji mai zurfi, inda bishiyoyi suka lullube sararin sama, kuma iska ke busa kamar tana ɗauke da sirri. A tsakiyar dajin, wata tsohuwa ke zaune, idonta biyu kamar gilashi — masu tsananin haske da fahimta. Tsohuwar ta kalli Baby tun daga nesa, sannan cikin sauti mai tsawa ta ce: “Kin zo da zuciya mai tsarki. Amma zuciyar wanda kike ƙauna an nannade ta da igiyar asiri.” Ta miƙa hannunta, ta ɗora shi a kan ƙirjin Baby, sai ta ce cikin sanyin murya mai zurfi: “Na fahimci wanda ya aikata wannan asirin. Ya samo asali ne daga cikin masarautar ku. Amma akwai mafita — sai dai farashi mai tsanani.” Baby ta share hawaye, ta kalle ta da karfin zuciya: “Duk abin da ake bukata zan yi. Daddy na ya fi kowa cancanta da a dawo da shi. Ko rayuwata ne za a nema — zan bayar. Indai game da shi ne, na riga na yarda da sadaukarwa!” Tsohuwar ta gyara zama, sannan ta ce da ƙaramin murmushi: “To ki sani… kafin zuciyarsa ta warke, dole sai naki ta sha wahala.” Idanun Baby suka zaro, cike da mamaki: “Me kike nufi da haka? Kina nufin sai na sha wahala kafin a karya shirin da ke jikinsa?” Tsohuwar ta gyada kai a hankali: “Tabbas. Baby, ke wata sirri ce wadda Ubangiji ya ɓoye. Babu wanda ya san hakikanin komai a kanki sai mahaifinki, mahaifiyarki… da kuma kishiyar mahaifiyarki. Ita ce silar da ya mai da ke marainiya, mai rayuwa ba tare da asali ba.” Baby ta ja da baya, zuciyarta na bugawa: “Ke… kina nufin kin san wani abu game da ni?” Tsohuwar ta murmusa kaɗan, tace: “Ba shi ne ya kawoki nan ba. Kin zo ne domin ceton ran mahaifinki.” Baby ta sunkuyar da kai, jiki a sanyaye: “Menene zan yi, wanda zai dawo da shi cikin hayyacinsa?” Tsohuwar ta ce: “Ina so ki zauna a nan — ki zauna da ni har abada. Ki zama ɗiyata. Na jima ina jiranki… ke ce cikon mafarkina.”......... 🕊️ RAINON YARO Chapter 9 Baby ta tsorata, amma da ta tuna da MJ da yadda yake mata ƙauna da kulawa, sai ta ce a hankali: “Indai hakan zai dawo da daddyna, na amince.” Fareeda ta yi saurin janyo ta gefe, cikin tashin hankali: “Baby, ba ki da hankali ne? Idan kika zauna anan, burinki fa? Karatunki fa? Rayuwarki fa? Kina so ki lalata komai? Idan MJ ya dawo lafiya kuma ya tarar baki kusa da shi — zai mutu da damuwa! Ki tuna da hakan!” Baby ta numfasa, ta ce cikin murya mai sanyi: “Fareeda, kin san cewa sarki ya ce ba zai taɓa aurar da ni ga daddy ba. Na san babu aure tsakanina da shi. Amma ni ‘yace a wajensa. Koda na rayu da daddy, dole wata rana za a tura ni ga wani. To me zai hana in sadaukar da kaina domin wanda ya fi kowa kaunata? Ka da ki manta Fareeda ,cina, suturata, kulawata, rainona, wankin Kashi, wankin futsari, shayarwata, karatuna,tarbiya ta,komai da kika gani atattare Dani daddyne ya minsu, kinsan mene kadai bai min ba haihuwata, da Kuma haluttata a doron duniya, bazan ma fadamiki wannan maganar ba tunda bani da tabbacin cewar bashi ya haifeni ba,tun da har yanzu na kasa sanin waceceni, Indai har iya zamane zan zauna da ita har abada' muddum zan ceto zuciyar daddy" Tsohuwar ta tashi a hankali, ta nufo Baby da sandarta tana nazarin zuciyarta kamar tana karantawa daga takarda. “Zuciyarki kamar ruwa ce mai tsarki — amma idan aka zuba ƙashi a ciki, sai ta zama baki. A yau za ki yanke hukunci tsakanin zuciyar ki da zuciyar wanda ke kiran ki Baby.” Fareeda ta tsaya gaba da Baby tana girgiza kai, idonta cike da ƙwarin gwiwa: “Wallahi idan kika zauna anan, Baby, na rasa ke. Ya Mujahid ya rasa ke. Kin san yadda zuciyarsa ke karaya ko da yana cikin jama’a. Kin san yadda yake zaune da mugun burin ganin ke kina dariya?” Baby ta sunkuyar da kai, hawayenta suna zuba kamar ruwan sama. Tana jin duniyar na juyawa — tsakanin soyayya da sadaukarwa, tsakanin burin zuciya da ƙaddara. Tsohuwar ta sake magana, cikin sautin da ya haɗa tausayi da rinjaye: “Zaki iya dawowa, amma sai kin cika sharuɗɗa. Sharadi na farko: har sai ran mahaifinki ya dawo cikin nutsuwa, ke ba za ki sake masa dariya ba. Sharadi na biyu: kowanne mutum da kika ƙauna sai ya jarrabtu da rashin ki.” “Wannan ba fushin Allah bane — wannan ne fansar ƙaunar ki da amincin ki.” Baby ta ɗago da idanu masu haske amma cike da hawaye. Ta ce da Fareeda cikin murya mai sanyi: “Na san zan iya rasa komai — amma idan daddy ya daina shan wahala, zan iya jurewa.” Fareeda ta rungume Baby da karfi, tana hawaye: “Sai ki dawo, please. Ki dawo da daddyn mu. Amma ba ki da damar ɓata rayuwarki wajen fansar kowa. Ke har yanzu kina da mafarki, kina da burin karatu... kina da zuciya da ba a gama gane ta ba.” Tsohuwar ta gyara zama, ta ɗauko ƙaramar ƙoƙo daga gefe, ta miƙa wa Baby: “Ki sha wannan ruwan ganyen rai-dore. Zai karɓi wani ɓangare na farin cikin ki. Amma zai ƙara wa zuciyar MJ haske.” “Zan sha,” Baby ta ce, tana girgiza kai da murya mai ƙarfi. “Na amince da ƙaddarata.” Ta ɗauki ƙoƙon — ta kai bakin ta — ta lumshe ido... ta sha. A can masarauta, MJ wanda ke zaune cikin daki, sai ya ji zuciyarsa ta buga... kamar wani abu na tashi daga barci cikin jikinsa. Ya ɗaga kansa da sauri: “Baby...?” MJ ya farka da kyar, kamar wanda aka farkar daga mafarki mai nauyi. Yana zaune a kan gado, yana kallon hannunsa — ya tsinci kansa cikin wani irin nauyi da ba ya iya fassara. “What’s happening to me... why do I feel like I forgot something important?” Ya mike, ya nufi mirror, sai idonsa ya sauka kan takardar gaisuwar Baby da ta rubuta masa shekara guda da ta wuce a ranar da ya kai ta bikin makaranta. Ya ɗauke ta, yana karanta rubutun da bai taɓa dubawa ba kwanan nan: "To the best Daddy in the world. You didn’t just raise me, you rescued me. I will never stop learning, I will never stop dreaming — because you showed me how to live." — Your Baby Girl, fateema MJ ya runtse ido. Kamar zuciyarsa tana harbi da wani sauti... Sai kuma ya furta: “fateema...” Zuciyarsa ta buga. Idanunsa suka cika da ruwa. Sai ya ji wani abu ya shiga tunaninsa kamar sauti yana bayyana: “Ba duk wanda ke kusa da kai ne ke tare da kai ba.” --- A CAN BANGAREN BABY... Baby ta farka daga barci da ciwon kai. Fareeda ta shigo da ruwa, ta durƙusa kusa da ita. “Yau rana ce ta yanke hukunci, Baby. Tsohuwar nan ta aiko sako — cewa idan har aka karanta kalmar da ta ba mu gobe da dare a gaban MJ, zuciyarsa za ta yi yunkurin yaki da sihirin da ke cikin shi. Amma... zai iya mutuwa idan bai da ƙarfi.” Baby ta ce cikin karfi, idonta cike da hawaye: “If I have to lose him to free him, then let it be. Amma ba zan zauna in bar bokan nan su kasheshi da raye ba. , yanzu tsohuwa ta amince idan na tashi muje muyi aikin tare?” Gydamata Kai fareeda tayi tace "eh tace dole sai dake bayan mun Kammala aikin sai in dawo dake batare da MJ ya ganki ba" Kukane yakara taruwa a idon baby a hankula tace "daddy kamar wata zuciyace shi a gareni tsokace da Babu Wanda zai iya rabuwaw,Amma sai gashi yanzu suncu nasara akanmu ,burinsu ya cika fareeda sun rabani da daddy na" baby ta sake fashewa da kuka. Daker farida ta lallasheta tace "kiyi hakuri kitashi bamu da lokaci " --FADAR SARKI... Zuwaira na zaune da mahaifiyarta a bayan wani ƙaton tagar fadar Sarki. Suna jin cewa MJ yana ta kai-kawo, yana tambayar mutane tambayoyi marasa dalili: “Ina Baby?” “Tana lafiya kuwa?” “Me nayi mata kwanan nan?” Zuwaira ta fara zubar da gumi. Mahaifiyarta ta ce: “Sihirin na fara yin rauni. Akwai wani abu da ke tayar da hankali a zuciyarsa.” Zuwaira ta ce da tsawa: “Ba zan bari ya dawo da ita ba! Ko da zan yi asiri na biyu — sai ya manta da ita har abada.” --- *MJ* Yana zaune cikin dakinsa, sai ya kira sunanta a hankali: “Baby…” Zuciyarsa ta cika da ɗoki. Wani hoto yana dawowa a zuciyarsa — hoton ranar da ta ce: “I promise, Daddy.” Sai MJ ya miƙe tsaye. Ya zaro jakarsa. Ya ce: “I need to find her. Something’s wrong. I can’t breathe when I think of her face.” --- DAREN DA AKA FARA KARANTA KALMAR TSOHUWA... Baby da Fareeda sun zauna a wani ɓangare na masarauta — kusa da labulen da MJ zai wuce idan ya dawo daga wajen Sarki. Kalmar nan ce a hannun Baby, sai ta kalli Fareeda, ta ce: “Duk da tsoro na, na yarda — akwai zuciya a cikin zuciyarsa da ba bokan duniya zai iya rufewa ba.” A daidai lokacin, MJ ya shigo falon. Idanunsa suka haɗu da na Baby. Zuciyarsa ta harbi, gaban kansa ya ɓuga — kamar girgiza ya shigo kansa. Baby ta miƙa hannu, ta karanta: "Zuciyar da ka gina da ƙauna, za ta rushe sihiri da ƙiyayya..." MJ ya dafe ƙirjinsa. Ya durƙusa. “Why do I feel this pain... why do I feel like I lost someone?” Baby ta matsa kusa da shi. Tana kuka, amma da murmushi a fuskarta. “Because you did. But now, you’re finding her again.” MJ ya kalli idonta. Na farko cikin tsawon lokaci, ya ce: “baby....…” Yana fadar haka ya yanke jiki ya fadi. Zuciyarta ta karaya, ta furta cikin hawaye: “Yes, Daddy. I’m still here.” TA kifa kanta akan kirjinsa ta saki kuka, fareeda ganin baby tana shirin karya alkairin da tayiwa tsohuwa yasa ta mike daga Inda take da sauri tashiga zan hannun baby, Baby tana kuka har damajina zuciyata na mata daci a haka tabar cikin dakin, suka bar MJ a kwance. Tun da su baby suka fita daga masarautar baby ke juyawa Tana kuka tana tuna irin RAYUWAR da sukayi da Daddynta MJ sai gashi yau ranar daba ta taba tunanin zuwan taba tazo ,wai itace yau zata fara rayuwa da wata wadda ba MJ ba, a haka suna tafe Tana kuka har suka karasa jejin Fareeda da Baby sun yi shiru yayin da suka isa bakin jeji. Kowane mataki da Baby ke ɗauka, kuka ke ƙara ƙarfafa a zuciyarta. Tana jin kamar ana yayyafa mata gishiri a buɗaɗɗen rauni. Kamar kowace ƙwaƙwalwa da ke da alaka da MJ, tana murkususu a cikin zuciyarta. Suna karasawa bakin kujerar dutsen da suka saba zama, sai Fareeda ta tsaya. Ta juyo da ido cike da tausayawa da kuma damuwa, ta ce da Baby: “Na san da wuya, amma lokaci ne ke kira. Dole na tafi.” 🕊️ RAINON YARO Chapter 10 Baby ta rike hannunta da ƙarfi kamar ƙaramin yaro yana tsoron a bar shi cikin duhu. Hawaye na zuba kamar ruwan sama. “Ki yi hakuri, Fareeda… Amma ki rike wannan sirrin. Kada ki faɗawa kowa inda nake. Ko daddy... har sai lokacin da lokaci ya ƙare.” Fareeda ta ja numfashi, ta dafa kafaɗar Baby, ta ce: “Zan yi miki alkawari — zan ɓoye wannan sirrin a cikin raina kamar yanda kike ɓoye ƙaunar MJ a zuciyarki.” “Thank you… my sister.” Suna kallon juna, sun fi magana da idanuwansu fiye da lafazi. Sai Fareeda ta juyo, ta fara tafiya da ƙafafuwa masu nauyi kamar tana barin ranta a baya. Tana ficewa daga cikin dajin, iska mai sanyi ta fara busowa, tana ɗauke da ƙamshin wani sabon juyi a rayuwar Baby. Baby ta tsaya — kanta ya zube kasa. Sai ta juyo da ƙyar, ta shiga cikin dajin inda tsohuwar ke zaune a tsakiyar sararin da fitilu masu asiri suka kewayeta. Tsohuwar ta ɗaga kai tana kallon Baby kamar ta riga ta san zata dawo. Ta ce cikin murya mai kaifi: “Yanzu ne gaskiya zata fara. Na gode da dawowarki, ‘yata.” Baby ta durƙusa a gabanta, tana kuka. Amma a wannan karon, ba kukan rauni bane — kukan ƙarfin zuciya ne, da alkawarin da ta ɗaura a zuciyarta. Alkawarin ta bar ƙaunarta ta ƙone, don rayar da wanda ya koya mata ƙauna. ---To Kwana biyu kenan Baby na zaune a ƙasar tsohuwar. Gurinta na cikin jeji amma cike da tsabta da wani irin shiru mai ɗauke da natsuwa. Tsohuwar ba wai kawai mai ilimin asiri bace — amma wadda ta shafe shekaru tana tsare sirrin dangi da duniya bata san da su ba. Kullum da safe, Baby na farka tana wanke fuska da ruwan itacen tsarki. Sai ta zauna a gaban wata madubi da baya nuna fuska sai ta gaskiyar zuciyarka. Idan ta yi ƙarya — madubin baya nuna komai. Idan zuciyarta ta cika da alhini — madubin yana zubar da hawaye maimakon ita. Tsohuwar na koya mata magana da sararin zuciya — da karanta tunani — da gane zuciyar mutane ta duban idanunsu. Kowanne daren Jumma’a, Baby na zama a gaban wuta, tana karanta kalmomin da ke karya asiri da duhun zuciya. Amma duk da haka... MJ ya tsaya mata a rai. Daga nesa, idan ta zauna a ƙasan bishiya, sai ta rufe idonta, tana tunanin sa. Kamar yadda yake riketa a da, yana mata nasiha, yana yawo da ita makaranta. 👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑 A masarauta kuwa, MJ ya rikice. Koda ya farfaɗo daga faduwar da yayi, tunaninsa ya daina daidaituwa. Yana ganin hotonta a bango, yana jin sautin dariyarta a cikin iska. Ya tambayi Fareeda sau da yawa: “Ina Baby? Me yasa take ɓoye min? Me nayi mata?” Fareeda ta jure da ƙyar.ta ce masa itama bata San Inda baby take ba. Sai dai kullum da dare tana fuskantar kalmar alkawarin da ta ɗaura — ba zata tona sirrin Baby ba. Sarki ma yana lura da MJ yana taɓarɓarewa. A wani zama na sirri ya ce masa: “Ka rikice akan yarinyar da baka da hakki da ita. Na faɗa maka tun da farko — bazata taɓa zama taka ba.” MJ ya miƙe, idonsa jajir: “Ban nemi ta zama tawa ba. Ina neman ta samu lafiya. Ina neman ta dawo cikin duniyarta, ko da kuwa ba zata ƙara kiran sunana ba.” Sarki ya kalli shi da mamaki. Bai taɓa jin MJ yayi magana da wannan zuciyar ba. “Na rasa komai. Kuma yanzu, ko ganin fuskarta ba na i ya yi , Abba bakasan yadda nakeji ba, baby rayuwa tace Kuma duniya ta ,nashaku da baby tun tana tsumma haka nake goyata a bayana, idan tayi Kashi nawanke naciyar da ita da hannuna na raineta da zuciyata Abba , na kwana da ita na tashi da ita tsawan rayuwata ban taba iya minti 30 ban saka baby a ido na ba, ko makaranta taje saina bita, najure duk wata magana da akeyimin akanta, meyasa abba zakace baby batawa bace ? Shin ban cancanci nazama uba bane? Ko ban Kai nayi kukaba sabi da ita? Wallahi Abba hawayena bazai taba tsayawa ba Indai har ban saka baby a idona ba "? MJ Yana gama fadar haka ya fice zuciyarsa na masa zafi da kuna. --- A cikin daji... Tsohuwar ta kira Baby da daddare. Wuta ta ƙone a tsakiyar gidan. Ta ɗora wata kwalba a gaban ta, ta ce: “A yau za mu fara buɗe hanyar zuciyar MJ. Amma ki sani — da zarar mun fara, ba dawowa baya.” Baby ta ce, murya a kasalance: “Na shiga cikin duhu tun da na rasa shi. Bana jin tsoron komai — muddin zan dawo da shi cikin haske.” Tsohuwar ta ɗan murmusa. Ta ɗaga kwalbar, ta ɗora a gaban Baby. “Sha wannan. Idan kin sha — duk asirin da ke kan zuciyar MJ zai fara fashewa. Amma...” Baby ta ɗago kai, ta ce: “Amma me?” “Zaki ga abubuwa da ba’a taɓa bari ranki ya gani ba. Zuciyarki zata cije, zuciyarsa zata ƙone — kafin ku haɗu da juna.” Baby ta rufe idonta. Sai ta ɗago da ƙarfi, ta ɗauki kwalbar, ta ce: “To… bismillah.” Ta kafa ta, ta sha. ** End book one TAKUN FARKO BY HAFSAT UMAR DANGORO PAID BOOK 1000